ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 9 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ciki da wannan rana da Allah ya nun min wacce
ban bar duniya ba sai da Allah ya nuna min har na
zo da kafata na baiwa dan uwana hakuri kan tarin
laifukan da na yi nasa, wanda kuma na samu
goyon bayan yan uwana, don haka ne ma nake
kara neman afuwa a wajensa, Ina neman kuma ku
kara tayani ba shi hakuri kan abin da na yi masa a
baya
Alh Aminu ne ya cafe da “Muka dai yi masa
Yaya Ja’a far, ba don na goyi bayan haka ba, ai da
abin bana tunanin zai kai mu ga haka. Laifi dai
dukkanmu mun yi masa, muna kuma neman afuwarsa. Insha Allah za mu hada kanmu ba za mu
sake barin irin wannan ta sake faruwa cikin

ZURI’A DAYA ba, da yardar Ubangiji za mu
kiyaye sake faruwar hakan
Sai Abba ya muskuta kadan ya yi gyaran
murya sannan ya ce. “Alhamdulillah, kwarai nayi
matukar farin ciki da wannan rana domin ban taba
tunanin zuwanta ba ma ko a mafarki, saboda a
yadda nake hange da tunani, ban taba kawowa a
raina wannan ranar ma za ta zo ba, ganin irin
tsawon shekarun da muka diba wajen watsar da
Juna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hakika laifi an yi min, kuma ban ji dadinsa ba,
ban ma taba kawowa cewa duk ranar da na hadu da
Yaya Ja afar zan iya yi masa duba na mutunCi ba,
haka kai ma Yaya Aminu. To amma saboda kauna
da dangantaka ta jini da kuma soyayyar tsakanı da
Allah da muka taso mu na yiwa juna, ganinku da
na yi ya sake dawo min kaunarku sabuwa a cikin
raina tare da kwarjinin da ku ka yi min. hakan ya sa
tuni na ji na manta da duk wani abu da ya taba


faruwa a baya da kuma soyayyarku ta ainihi da na
JI tana shigata.
Don haka na yafewa kowa, duk wanda ni na
batawa ina neman afuwarsa. Sannan kuma mu saka
a ranmu cewa, abin da ya faru a baya kaddara ce,
tun ran gini tun ran zane. Babu kuma wanda zai iya
Tsallake duk wata kaddararsa da aka rubuta masa.
Saboda haka, ina kira gareku da mu cire duk
abin da ya faru daga cikin zuciyarmu mu fuskanci
abin da zai zo don mu yi gaggawar magance shi.
Gaskiya ne Cewar Alh Lukman, sannan ya
Kara da cewa. Wannan maganar ta Yaya da
Mustapha haka ta ke, dole ne kowa ya cire duk
abin da ya faru a ransa tunda kowa ya yi kokari an
kori shaidan mun samu an shirya, to sai mu san
Yadda kuma za mu gyara Zuriarmu mu manta duk
wani abu da ya faru a baya, yadda ko nan gaba idan
ya’yannmu da jikoki sun taso ba ma za su taba
samun labarin faruwar wannan abin ba bare har su
yi tunanin wani abu.
Dole yanzu zama za mu yi wanda zai sa mu
kawowa Zuri’armu cigaba, amma ya zama dole mu
Cire son zuciya da kuma son ‘ya yanmu da kuma
ba su abin da suke so mutukar
zai kawowa Www.bankinhausanovels.com.ng
Zuri’ armu wata matsala. Mutukar za mu ce duk
abin da yaranmu suke so shi za mu dinga dubawa
to kuwa gaskiya za mu yi ta samun matsala, saboda
kowa dansa zai dinga dubawa ba wai Zuri’ ar ba,
kunga kenan haka za mu yi ta samun nakasu.
Amma idan za mu gina yaranmu akan zumunci
da son juna da kuma nuna musu girman sadaukar
da abin da suke so ga ‘yan uwansu to lallai kuwa za
mu samu cimma nasarar hada kan Zuri’armu baki
daya kuma za mu kai samun zuwa ga hanya mai
billewa har illa masha Allah.
Nan kowa ya girgiza kai alamar amincewa
Saboda kowa ya gamsu da abin da ya zo da shi. Alh
Hamza ne ya karba da cewa
“Kwarai da gaske maganganunka suna kan tsari
mai kyau. Sai kuma ni wani hange da na yi. Dole
ne fa mu yaki wannan bakar al adar da muka tsira
a cikinmu, Wato ta maganar babu maganar auren
zumunci a cikin Zuri ar nan, ni a gani na dole ne
sai mun bar yara Sun so Junansu sanan za mu
samu zama ZURI’ A DAYA.
Nan Alh Aminu ya karbe da cewa. Hamza ban
tari numfashinka ba, ina ganin wannan maganar
mu barta. Idan ka lura da makasudin wannan
matsalar ta mu ai akan matsalar auren ce. Ina ganin
ni dai a nawa hangen da tunanin ko da za a dawo
da maganar auratayya ba yanzu ba, a bari sai nan
gaba gudun kada wata matsala ta sake faruwa ba
dai ma fatan hakan insha Allah
Mu yanzu dai maganar ya ya za ayi zumuncin
namu ya zauna da kafarsa muke so. Amma yara
kowa ya je waje ya samo abin da yake sO ya aura,
tunda har zuwa yanzu akan hakan ake. Alabasshi
idan komai ya daidata sai mu san abinyi.
Muhawara sosai aka yi kan wannan maganar,
dole aka bar maganar cewa za a zaunawa maganar
zama na musamman, saboda kowa ya na da hakki
akan maganar. Don haka aka tsayar da
cewa za’a sake zama nan da kwana hudu, saboda
maganar
kowa ya zo sai a tattauna yadda za a yiwa ZURIIA
DAYA tsari da kuma dokokı ta yadda za a kai ga
samun kaiwa gaci Www.bankinhausanovels.com.ng
A kalla an samu kimanin wata kusan shida
kenan da samun daidaituwar ZURIA DAYA.
burin yara da manya ya samu ga cika saboda an yi
watsi da komai an rungumi juna kullum cikin
farantawa juna rai ake, kusan duk gaba dayansu
sun dawo Kano da zama, idan yaran sun samu
lokaci sai suje can Kaduna, a haka dai har duk gaba
daya suka tattaro suka dawo Kano baki daya.
Haana gani ta ke ta fi kowa farin ciki, saboda
mafarkinta da burinta sun gama cika, duk wani
motsinta cikin ZURI’A arsu za ta yi.
Sai dai kuma akwai wata doka da suka zauna
akanta har zuwa yanzu kuma ana kanshi ne batun
auren zumunCi. Duk zaman da suke wannan ita ce
ke musu tsauri a cikin Zuri’a dinsu. Duk gaba
dayan iyaye kowa ya karbi maganar an amince,
amma Alh Hamza da Haj Babba ne kawai ba su
amince ba, amma kuma babu yadda za su yi saboda
an fi su yawa, dole suka ja bakin su suka yi shiru.
Har yanzu Alh Ja’afar ne da iyalansa ba su
dawo ba don ya ce a ba shi dama zuwa karshen
shekara zai dawo da iyalansa gaba daya nan din
idan har hakan zai yuwu, saboda duk yawancin
business dinsa sun fi yawa a can. Sai kuma bayan
daidaituwar komai zuwansu biyu shi da matarsa
Haj Asiya Najeriya da kuma yaranta guda biyu,
amma sati biyu kawai suka yi sannan suka koma.
Tsaye ya ke kusa da dressing mirror na dakinsa
cikin shigarsa mai kyau, ya gyara tsayuwarsa
sannan ya bi kansa da kallo ta cikin madubin.
Gyran murya ya fara yi sannan ya dora da cewa.
Look Haana, ina so ki tsaya da zuciyarki waje
guda sannan ki bani dukkan nutsuwarki ina son na
bayyana miki tarin so da kaunar da nake miki. Kaf
duniyar nan ke kadai ce macen da zuciyata ta mace
akan sOnta, sam ba na ganin duk sauran mata idan
ba ke ba.
Ina so ki manta da rayuwar Malaminki M.J
tunda ya yi nisa cikin rayuwarki ba kuma dawowa
zai yi ba, ya kamata ki cire komai a ranki ki
fuskanci Reality. Ina matukar jin KUNAR ZUCI
(Littafina mai zuwa cikin yardar Allah) idan na ji
kina ambatar sunansa, ina matukar jin kishinsa har
cikin raina wani lokacin ina ji kamar zuciyata za ta
fito daga jikina. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana iya kawai son da nake miki ya kamata
ace kin manta da wani M.J. please Haana don
Allah ki so ni kamar yadda na ki ya ke hanani
runtsawa cikin barcina. Haana ki ce kina sona
mana kamar yadda nake jinki kamar ba zan rayu ba
sai da ke
Sai kawai ya yi tsaki sannan ya cire hular kansa
ya watsar kan gado. Guri ya samu ya zauna cikin
kenan
mayar da numfashi mai zafi. Yaya Abba kenan
wanda kullum cikin practice ya ke na yadda zai
tunkari kanwar tasa Haana da batun soyayyar da
yake dauke da ita, amma ya kasa. Nan ya shiga
tambayar kansa.
Abba wai me yake damunka ne da za ka tsayaa
kana wahalar da kanka, kamar kai a ce wai ka kasa
fitowa ka bayyannawa Haana abin da yake cikin
ranka, ka tuna fa cewa Haana dinka ce, ya aka yi
ka bari ta canza maka ta koma maka wata wacce ka
ke jin tsoronta wanda ka gaza fada mata abin da ya
ke ranka, amma ita tana tsayawa ta fada maka duk
abin da yake ranta da ma wanda ta ke so.
Ka tuna fa Haana dinka ce, ka tuna lokacin
Kuruciyarta lokacin da ka ke daukarta idan ta na
kuka ka sanya ta a bayanka har sai ta daina kukan,
tare fa za ku yi dariya sannan ku yi kuka tare za ku
ci abinci tare kuma ku tafi yawo tare, za ta fada
maka damuwarta, kaima kuma za ka fada mata
taka. Shi ne kai kuma yanzu za ka nesanta ta da
sanin damuwarka bayan kuma ita ce matsalar
taka.
Kai tsaye ya baiwa kansa amsa da cewa, “Ban
nesanta ta ba da sanin damuwata, sai dai a hanlin
yanzu ba zan iya bayyana mata a halin da nake ciki
ba, saboda bana son na saka ta cikin damuwa
domin na yi mata alkawarin sanyata farin ciki
kuma na kori duk wata matsalarta da zan gani a
tare da ita. Wannan shi ne dalilin da zai hanani na
futa mata kalmar so, zan dai jira har zuwa lokacin
da ya ke shi ne daidai.
Ya na cikin wannan tadin da zuCiyar tasa ne ya
Ji ana Knocking din kofar dakin nasa. Da sauri ya
ce Yes shigo
ZURI’A DAYA
Murda kofar aka yi sannan aka shigo. Haana ce
cikin shigarta mai kyan gaske, Riga da siket ne a
jikinta na Atamfa, sun matukar yi mata kyau, Cikin
fara’a ta ce
Assalamu alaikum, mun fa shirya Ya Abba
tun dazu, kai kawai muke jira
Cikin sauri ya mike ya dauki hularsa ya sanya
sannan ya kalleta cikin kulawa ya ce. “Am so sorry
my Haana, na dan tsaya wani abu ne
Sai ta yi wani murmushi sannan ta ce. “Na yi
tunanin hakan dama. Kai gaskiya fa ka yi kyau Ya
Abba kamar wanda zai je wajen Budurwarsa.
Gaskiya da ni Budurwarka ce ba zan yarda da
wannan shigar mai kyau ba don nasan yan matan
garin nan sai sun yi min kwacenka, ka dai san su
da son mutum mai kyau da class ga uwa uba
Atitude”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Har cikin ransa ya ji dadin yabon da ta yi masa
da kuma koda shi. Sai ya kalle ta cikin murmushi
shi ma ya ce.
Da gaske ki ke?, to idan kuwa haka ne kyan ya
yi yawa bari na canza tunda ba kya so na yi
kasuwa
Zaro idanuwa ta yi waje sannan ta furta. Wa
neni na ce bana son Ya Abbana ya yi kasuwa, a
yadda ka ke high class ina son naga ka samo mana
mace mai class, ta yadda za mu ji dadin yaba ku.
Yanzu dai taho mu wuce zan ji dadin a ganka a
yaba min Ya Abbana Dariya ya yi ya ce. To kenan ba kya taya
Auntyn taki kishina, idan kuma wasu da ba su hadu
ba suka ganni kuma suka dage ni suke so fa?.
Dariyar dai ita ma ta kara yi sannan ta ce. “ba
su isa ba wallahi, zan taya ta kishi tunda tare kuma
za mu fita duk wacce naga ta kalle ka idan ba ta
hadu ba zan bata mata rai, ta yadda za ta yi zargin
cewa ni budurwarka ce don kada ta yiwa Auntyna
Snaching. Ya Abba mu yi sauri mu wuce za mu
dawo kan wannan matter idan mun dawo gida
wallahi. Mun gaji da yawa, dole sai ka fada mana a
ina Auntyn nan tamu ta ke kullum sai kai ta yi
mana hanya -hanya
Kar ki damu. mu dawo din sai mu yi maganar
kinga yanzu jiran mu ake mun tsaya kuma muna
wata sabgar daban
A tare suka fito suna dariya, idan ka gansu sai
ka zaci sabbin couples ne yadda suka jero a
nishadance. Suna zuwa kuwa mota suka nufa. Nan
suka iske Mr. Sameer ya na zuwa. Ya Abba sai
kawai ya ji wanı haushi da kishinsa ya kama shi,
saboda ya gama gane mai ke tsakaninsa da Haana
Ta ke ya sauya fuska, kullum kokarinsa ya
mantar da Haana tunanin malaminta, don ya na
ganin idan ya gama shikenan, amma kuma ga
Sameer yanzu zai zame masa babbar matsala, dole
sai ya yi kokari ya raunata wannan dangartakar ta
Su.Sarai Sameer ya ga sauyi a fuskar Abba, sai dai
ya kasa gane me hakan ke nufi, kullum ya na
kokarin ya ga ne dalilin hakan, saboda akwai wani
abu da ya ke zargi a kasan zuciyarsa, don haka ya
na son ya gama gano komai sai ya san abin da
kuma zai yi a gaba.
Ya na karasowa ya mika masa hannu suka
gaisa idanuwansa kyar akan Haana. Murmsuhi ya
yi sannan ya ce. “Miss Haana ina zuwa ne haka?,
irin wannan gayu haka kamar za ki je zaben
sarauniyar kyau. Amma fa kin yi min kyau
Humm, Mr. Sameer kenan, kai dai kullum
cikin tsokana ka ke, idonka ba ya taba ganin abu
bai tanka ba. To shikenan na gode. Amma ba
neman sarauniyar kyau zanje ba, rakiya za mu yiwa
Ya Abba
Gaskiya ne, shi ne ni kuma ba’a gayyata ta?
Ba ni ce mai tafiyar ba ga shi nan a gabanka,
sai ka fada masa, idan kuma za ka je ne, to ka je ka
shirya Ta karasa maganar cikin dariya.
Girgiza kai yayi sannan ya ce A ah kuje
abinku, nima zan ware wata rana sai a yi min tawa
rakiyar donmu samu damar tattauna wasu
maganganu ma su muhimmanci Www.bankinhausanovels.com.ng
Well, amma ban yi maka Alkawarin haka ba,
sai dai idan kana son haka ka kama kafa da Ya
Abba, tunda shi ne order man dina, ba na yin
komai sai da saninsa da kuma amincewarsa
Murmushin karfin hali ya yi ya ce. “Wannan ba
matsala bane, bari ma na tambaya tun yanzu. Abba
ina bukatar a bani aron kanwarka gobe nima za ta
Yi min rakiya, saboda ina da wani sirri da za mu yi
da ita idan babu matsala”
Cikin dakewa yace “Wannan ai ba wani abin
damuwa bane, kai ma kanwarka ce, matukar dai
inda za ku je din ba mai nisa bane za ku iya zuwa
ko da babu yarda ta”
Da yardar taka zai fi, tunda ita ce ta fadi
hakan, nasan halinta idan ba ka ce ta je ba, to ba za
ta je din ba”.
Ok to shikenan kar ka samu damuwa za ta je.
Bari mu tafi kada mu bata lokaci.
Shikenan za ku iya tafiya'”. Ya fada shima
cikin wani yanayi da shi kadai yake ji a ransa.
Tabbas ya karanci abubuwa da dama cikin maganar
Abba, musamman yadda ya ke magana da shi cikin
daurewar fuska kamar ana yi masa dole.
Ya na Cira kansa ya hangi Rauda cikin mota
amma idanuwanta gaba daya a kansa suke, nan ya
bude baki ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Oh hello Rauda, dama wai kina cikin motar
nan ban ganki ba? Kuma ba ki yi min magana ba
Murmushi ta yi cikin sanyin jiki ta ce. Ai
tunda ka zo kuna magana da Haana na ganka, ni
kuma bana son katse mutum idan ya na magana
saboda ba dadi.
Ban yarda da ke ba na fusanci wani sabon
sauyi dake ko dai ba kya jin dadi kwana biyu ne sai
boye kan ki ki ke yi ba kya shiga jama’a.”
“Kar ku da mu zan sauya na dawo muku yarda
nake da, idan hakan ya yi muku.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.
NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *