ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Cikin farin ciki da dariyarta ta ce, “Ya Abba ka yi min alkawari?” “Na yi miki Haana.”

Dariya ta yi ta ce, “Na gode Ya Abbana daga yau ka dinga ganin farin ciki a fuska ta na kuma yafe maka duk abin da ka yi min na samu sauki yau cikin zuciyata nauyin da ta yi min na ji ta yi sauki na gode Ya Abbana na gode sosai.

Ina son yau ka je gurinta ku daidaita kan ku don haka Ya Abba ina son kamar yadda ka ke

taimaka min a can baya ina son yanzu ma ka taimaka min, domin na kawo nima farin ciki a rayuwar Haaya da Fadeelah ina son kowa ta samu abin da take so ka yi min alkawari za ka taimaka
min. “Na yi miki alkawarin zan taimaka miki da iya dukkan karfina da kuma tunauina.
‘Good Ya Abbana na san dama za ka yi min duk abin da nake so dama wancan wanda ya sani kuka da damuwa ba Ya Abbana ba ne wani Ya Abban ne daban, yanzu nawa ya Abban ya dawo wancan ya tafi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk da yana cikin damuwa shi ma sai da ta sa ya yi murmushi. Ita ma murmushin ta yi ta ce, “Bari na shirya yau kai ne za ka kai ni makaranta tunda mun shirya ko ba za ka raka ni ba?” Ta tambaye shi cikin irin shagwaɓar da take masa a da can.
Dariya ya sake yi yana mamakin kamar ba ita ce mai damuwa ba yanzu amma har ta yi kokarin gayyato farin ciki cikin fuskarta, nan take ya kara jinjina mata da irin wannan juriyar tata..
“Za ni mana ki je ki shirya idan kin gama ki yi min magana duk abin da ki ke so ko me nake zan ajiye na zo na yi miki.”
“To na gode bari na je ciki.” Bin ta ya yi da kallo yana tausaya mata.


Tunda ta shiga daki ban da kuka babu abin da take yi mutum biyu take da burin samu a cikin rayuwarta duk wanda ta samu za ta yi matukar farin ciki da samunsa a matsayin abokin rayuwa,
sai dai dole ta hakura da su domin ‘yan uwanta su
yi farin ciki. Amma tana jin rashin Malam M.J a
rayuwarta zai fi kowa daga mata hankali da shiga, damuwa, amma dole hakan za ta yi don ganin farin cikin ‘yan uwanta ta yarda ta shiga damuwa da ta saka wani damuwa. Kokari ta yi gurin hana kanta damuwa duk da kuwa tana ciki nan da nan wani irin ciwon kai na
gefe daya ya fara mata ciwo.
Cikin sanyin jiki ya koma dakinsa jiki babu kwari tabbas yau ya hangi wani irin tsananin so da kauna a idon Haana ita da Malamin ta dan uwansa Muhammad gaba dayansu su biyun suna cikin wani irin mawuyacin so da sukewa junansu suna wa junansu magana ce cikin so da rudani ba tare da sun san suna yi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya yi matukar karaya da jin irin matsanancinson da ya ji Muhammad yake yi wa kanwarsa wanda yake da yakinin shi ne kadai zai iya ba wa Haanan irin farin ciki da yake so ya ba ta, haka kawai yake jin yana yarda da Muhammad dole ya hakura ya bar masa Haana ba don ya so ba sai don kawai alkawarin da ya yi mata na zai yi mata abin da take so ba wai don baya son ta ba. idan akwai wanda yake son ta a duniyar nan ban da uwa da uba, to shi ne na farko zai hakura ne da ita; domin son ganin farin cikinta.
A yanzu shi ma yana da damar da zai ce shi ma
ba zai hakura ba, domin yanzu ko kadan bai sonSameer ya auri Haana, saboda ko kadan bai dace da rayuwarta ba, sau nawa ta yi kuka a kansa, sau nawa ya jefa ta damuwa, lallai Sameer bai dace da rayuwar Haana ba, saboda yana da yakinin cewa ba zai iya ba ta tarin farin cikin da yake son gani a fuskarta na dindindin ba.
Dole ya tsaya tsayin daka ya ga ya ba ta gudummawar ta auri wanda zai kawo farin ciki rayuwarta dauwamamme sai dai yanzu ya fara samun yakinin Muhammad ne kadai zai iya ba ta wannan farin cikin.
Da yammacin ranar ya hango Mr. Sameer ya dawo daga unguwa maza ya yi ya tare shi cikin wani irin yanayi da shi kansa ya kasa ganewa, tsaye yake yana kallonsa irin kallon raini da tuhuma. Ji ya yi ransa ya ɓaci ya saki wani irin tsaki ya yi wucewarsa da ya yi niyar tsawa ya fasa.
Yana parking din motarsa ya hango Muhammad ya nufo inda yake, kasa motsi ya yi ya tsaya yana jiran Karasowarsa. SAllama ya yi masa ya amsa cikin daurewar fuska, domin ya gama fuskantar Muhammad da sabon rainin wayo da rainin hankali ya zo masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin zafin rai Mr. Sameer ya ce, “Look! Muhammad na gaji da irin wannan kallon tuhumar da ka ke min ka fito ka yi min magana mana na ga kana son raina min hankali, please bana so, ka tsaya a matsayin ka bana son ka na min irin haka.” Ya karasa fada cikin kosawa.Murmushi yake ya yi ya ce, ‘Ka san me ka yi shi yasa tunanin ina tuhumar ka, Sameer ka ba ni mamaki ashe kai ba ka cika namiji ba da ba za ka iya nuna gwanjin ka a fagen so ba, sai ka hada da yaudara da shiga tsakanin masoya biyu.
Ba zan tona maka asiri ba a gurin Raihana ba, saboda abin da ka yi na tabbata ban da kai babu wanda zai tura mata texr din da ka yi kaf cikin zuri’ata babu wanda ya san ina sonta sai kai ka san tsakanin abin da ke tsakanina da Fadeelah domin na ga abin da ka ce, duk da haka na yafe maka saboda ko ba komai ka yi min abin, ni ban yi ba.
Sanya Raihanah na farin ciki ganin hada ta da zuria dinta wanda na san haka shi ne burin rayuwarta. Ka yi min wannan na gode sai dai ba yin kanka ba ne ni na umarce ka da ka yi min haka, dalilin haka na yafe maka kuma ba zan taba fadawa duniya cewa ga abin da ka yi min ba. Shi ne nake rokon ka cikin ruwan sanyi ka janyewa Raihanah ka bar ni ni take so ba kai ba, a rashina na zaton ba zan dawo rayuwarta ba ta ba ka samu  wannan damar tunda kuma na dawo sai ka janye min na dawo mu yi maganar aure na dauki matata na koma inda na fito.”
Cikin tsawa da matsanancin fushi Mr. Sameer ya ce, ‘Karya ka ke Muhammad ba ka isa ba ba ka da wannan right din a yanzu mai raba ni da Miss Haana sai dai mutuwa, amma dai ba kai mutum mai numfashi irina ba.””Sameer ka yi a hankali gurin daga muryar ka kada ka tara mana jama’a na riga da na gama magana da kai idan ka tsaya ja ta karfin tsiya zan raba ka da Raihanah tunda dama ba taka ba ce tawa ce.”
Wani irin kunci ya ji bai san lokacin da ya je ya damki gaban rigarsa ba yana cewa karya ka ke Muhammad a yadda nake jin Miss Haana a raina zan iya daukan ran duk wanda ya yi kokarin shiga tsakanin na da ita na gama tsara rayuwata da ita zan rayu ka zo min da wannan batun, to ba ka isa ba.”
Karaf a kunnen Alh. Aminu mahaifin Mr. Smeer da sauri ya karaso gurin ya ce, “Subhanallahi! Kai Sameer, Muhammad me yake faruwa me kuma na ji Sameer na fadi da
hankalinku da komai, wai me yake faruwa?” Da sauri Mr. Sameer ya sake shi cikin ladabi Muhamamd ya yi kasa ya gaida shi cikin nutsuwa. Bai amsa ba ya ce mike Muhammad ka fada min me yake faruwa ne kuna da hankali kuwa ku yarane?
Duk su biyun shiru suka yi babu wanda ya iya cewa komai da shi. Nan ya dan tunzura ya ce, “Ba magana nake muku ba kun tsaya babu mai ba ni amsa cikinku?”
Cikin ɓacin rai Mr. Sameer ya ce, ‘Abba, Muhammad ne ya zo min da wata banzar magana wai sai na bar masa Raihanah ya aura wai shi ya dace da ita ba ni ba.””Muhammad wai h
aka ne?”
“Eh, Abba haka ne.” Ya fada cikin kwanciyar hankali. Kallonsu ya yi cikin rashin gamsuwar furucin
su su biyun ya ce, “Ku mu je ciki na ji dalilin ku.” Zaune suke a falon nasa suna gabansa ya tsaya yana kallonsu ya ce, “Na ji abin da ku ka ce, amma zan so jin dalilinku. Kai Smeer daga bakin ka nake son jin me yake faruwa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
A nutse ya yi masa bayanin komai tun daga ranar da Muhammad ya zo masa da batun abin da yake so ya yi masa komai bai ɓoye masa ba, ya fada masa kaf, sannan ya ja ya yi shiru.
Shi ma Muhammad ya kwashe komai ya fada masa kaf dalilinsa da yadda ya yi har ya shigo rayuwar Raihana da dukkan burinsa komai ya fada masa.Shiru ya yi ya kasa cewa komai, take ya
sallame su da cewa kowa ya je zai neme su nan gaba.
Taron gaggawa Alh. Aminu ya tara ‘yan uwansa, domin ba shi da ikon yanke wannan hukuncin shi kadai. Iya su maza suka yi wannan zama.
Gabaki dayansu su goma, Alh. Muktar ne kadai baya nan yana can Dubai, babu wanda ya fadawa dalilin wannan taron sai da kowa ya zo, sun hadu ne a falonsa cikin gidansa.Babu abin da ya ɓoye na tsakanin wanda Mr. Sameer ya fada masa haka da wanda Muhammad ya fada masa kaf ya kwashe ya fada musu.
Duk babu wanda bai yi mamaki ba musamman Alh. Jafar da ko kadan bai san dalilin da yasa dansa Muhammad ya zo Nigeria ba sai yanzu ya yi matukar yin farin cikin jin dansa ne tsanin da aka samu zuri’a dinsa suka hadu guri daya cikin zuciyarsa ya yi wa dansa addu’a tare da saka masa albarka ya ji sonsa da kaunarsa a ransa. Babu wanda shi ma bai saka musu albarka ba gaba dayansu.
Abba shi ma ya fada musu komai dalilin da yasa ranar da ake neman Amminsa ba a ganta ba sai dare nan duk abubuwan da suke faruwa wanda kaf cikinsu ba su da masaniya ya fada musu, babu wanda hankalinsa bai tashi ba cikin su, domin jin badakalar da take cikin ZURI’A din.
Alh. Hamza ya ce, ‘Subhanallahi! Lallai mun godewa Allah da ya yi saurin ankarar da mu abin da yake faruwa. Mu da muke ganin ZURI’A DAYA ba ta da wata matsala ashe ba mu sani ba tana nan kasa kwance mutukar ba mu dauki mataki tun yanzu ba to lallai yaran nan za su kawo gagarumar matsala cikin zuri’armu dole mu yi wani abu.”
Alh. Lukman ya ce, “Wannan gaskiya ne kullum burinmu gyara zumunci ba wai bata shi ba, dole ba za mu tsaya son zuciya ba duk yaran nan abu guda ne gurinmu dole ne mu tsaya a duba masalaha da kanmu za mu yanke abin da ya dace hukuncinmu kuwa shi ne dukkan umarnin yaron da yake cikin zuri’a din nan domin ba za mu bari wata matsala da za ta sake taba zumuncinmu ba.”
Alh. Aminu ya ce, ‘GAskiya ne wannan Lukman yara namu ne muna da iko da fawa a kansu dole ne mu san abin yi tun wuri.”
Alh. Jafar ya ce, ‘Duk cikinsu yara biyun nan ne masu matsala, Sameer da Muhammad, don haka dole su bar wa Mustapha karami auran kanwarsa ko sun ki ko sun so, saboda yadda ya sadaukar da son ta tun farko ga shi Sameer din don ganin zumunci ya inganta ina ganin shi ne wanda za mu goyi bayan ya aure ta.
Abba yace, ‘Ni dai ba na goyan bayan haka a dai sake wani tunanin masalaha za mu nemo wanda tun daga mazan har sauran matan kowa farin ciki muke so mu ga ya samu kanta idan ya auri Ammina mai sunan Hajiya Babba fa ko ka manta ita halin da take ciki ita da Mustapha Karami ni dai a tsaya a nemo abin da ba za mu bakantawa kowa ba cikinsu ni ina ganin wannan abin da za mu yi shi ne mafita.”
Babu wanda bai goyi bayan maganar Abba da ya zo da ita ba. Alh. Aminu ya ce, ‘Haka ne ku bari dai yaran duk zan gan su su ukun kowa na ji ta bakinsa, amma ita Ammi zan fara gani, domin ita ce mai dauke da tarin matsalar saboda a kanta ake komai dole ne na fara jin ta bakinta kafin na same su.Da wannan shawarar zaman ya tashi. Tun daren ranar ya nemi Haana a waya ya Www.bankinhausanovels.com.ng
tambaya yaushe za ta je makaranta, kuma wane time za ta dawo ta fada masa hudu za ta gama dukkan lectures din ta ta ranar. Ya ce idan ta dawo wajen shida na yamma ta zo gida yana son ganinta. Ta ji babu dadi don a tunanin ta ko Mr. Sameer ne ya kai kararta gurinsa, ita kuwa idan hakan ne ya za ta iya kare kanta take ta ji za ta iya fuskantar kowa a kan damuwar da take ciki.
Kamar yadda suka tsara hakan kuwa aka yi tun kafin shidan ta yi ya sake kiranta don ya tunatar da ita ta ce masa tana sane ba ta manta ba. Shida saura minti biyar ta fito daga gida zuwa amsa kiran da Abbanta Alh. Aminu ya yi mata.

Addu’a ta dinga yi Allah yasa kada su hadu da Mr. Sameer saboda ta sa a ranta ko sun hadu ba zata kula shi ba. Tana shigowa kuwa falon ta iske baya nan su Ummansu ne da su Farida.
Har kasa ta zo ta gaida Umma, haka ta dinga jin kunyarta tana zuwar mata, haka ita kuma da ta fuskanta ta shiga janta da wasa don ta sake. Farida ce ta yi mata rakiya har zuwa falon Abbansu.
Sallama ta yi ta shiga ya yi mata iso da ba ta gurin zama, a nutse ta zauna tana ta addu’a Allah yasa ba a kan dansa zai mata magana ba, idan ma a kansa ne ta tara irin kalaman da za ta yi masa insha Allahu kuma zai fahimce ta.
Bayan sun gaisa ta ja ta yi shiru tana sauraron ta inda zai fara. Gyaran murya ya yi ya ce,”Amminmu ina son ki saki ranki ki nutsu maganar gaskiya nake son ji daga bakin ki. Kafin nan ina son ki cire duk wani jin nauyi da kunyar da na hango a kan fuskarki ki dauki ne a matsayin uba kuma aboki na kusa don ki ji dadin sakewa da ni a shirye nake da na taimaka miki ki samu farin ciki dauwamamme cikin rayuwarki.

Ki fito ki fada min gaskiyarki game da matsalar da ki ke ciki kan matsalarki da ‘yan uwanki mata me ki ke so a yi miki, kuma me ki ke so ki yi? Ki cire cewa ni na haifi Sameer ki dauka cewa daga. yau sabon aboki ki ka samu da za ki iya fada masa dukkan matsalar ki da damuwarki don ya kawo miki mafita. Ke kadai ki ka samu wannan damar a gurina. Oya, go ahead ki fada min matsalarki ki saki ranki kada ki ji komai.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani irin farin ciki ya kama ta ta ji kamar ta rungume Abbansu don dadi, domin tarin gaskiyar da ta gani a kwayar idanunsa. Duk abin da yake ranta ta kwashe ta fada masa babu abin da ta rage daga karshe ta ce.
“Abba na roke ku da ku bar ni na samu wani a
waje na aura saboda bana son wani ya kara nuna min so cikin zuri’a idan na aure shi wanda ba su same ni ba su dauki tsana da gaba su dora masa. wannan shi ne abin da nake gudu. Dubanta ya yi cikin tausayi da yaba hankalinta
duk sai ya dinga ganin kamar marigayiya Azizah
ce a gabansa yake magana da ita, saboda sak suke

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *