ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 20 KARSHE BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Haana. Ta yi masa alkawarin za ta je har gida ta sa su hadu.
Da sidin goshi ta yarda suka hadu ba wani lokaci ta ba sa sosai ba. Yadda ta gan shi ta tausaya masa sai dai ta ɓoye tausayin a kan fuskarta.
Cikin rauni ya ce, “Raihana me yasa za ki yi min haka bayan kin san ke ce rayuwa ta ke ce farin cikina, shin ba kya tausayin halin da zan shiga idan na rasa ki, ba kya ganin abin da Abba Aminu ya yi min mugunta ce, ki daure ki je ki ce kin fasa auran ni ki ke so.”
“Malam M.J ina son ka ina son rayuwa da kai ina son ganin farin cikin ka, kai komai naka ina so
ai dai bani da ikon hana auran nan don Abba Aminu ya wuce komai a gurina dole hakura za muyi mu karbi kaddarar da ta zo mana.’ Tana gama fadin haka sai hawaye. Wani irin farin ciki ne ya kama shi ya ce,
Raihana-tunda kina sona to ki ce kin fasa auran.” “Ba zan iya ba hakurin kawai shi ne abin yi.”
“Shi ke nan ki je ki yi auran,amma ni ba zan jure ganin kin auri wani ba a gobe zan tattara na koma inda na fito.”To ya batun matar taka Fadeelah?””Ya rage nata ita da wanda suka daura mata auren, ki je ni zan tafi tunda haka kaddara ta rubuta mana. Har ya tafi ba ta iya motsawa ba tashin hankali
da damuwa suka baibaye ta.
Zaune yake gaban Uncle Mukhtar yana sauraren batun da yake masa da yake jin mutuwarsa a wannan lokacin jin babu wata nasara da shi ma ya yi haka ya hakurkurtar da shi jiki babu kwari ya dawo gida. Ya yarda babu wani da yake sonsa da farin ciki a family har ita Raihana karya take masa. Nan ya ajiye abin da yake ganin shi ne mafita a zuciyarsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hada-hadar tafiya wajen daurin aure ake ta yi wanda za a yi a masaLlalcin Alfur kan nan titin Alu Abenue. Angwaye biyar ne, amma uku ne suke cikin farin ciki, Ya Abba, Fu’ad da Muhammad Bashir, M.J da Mr. Sameer kuwa bau wanda ya ga keyarsu, tashin hankalin Mr. Sameer har yanzu
Abbansa bai bari ya san wacece wadda zai aura ba ya dai ji Ummansa na fadawa ‘yan uwansa cewa ‘yar abokinsa ce da suke Hotoro. Tun daga jin haka ya daina walwala. M.J kuwa nemansa aka yi sama ko kasa a ka rasa lokacin da ake haramar tafiya gurin daurin auren.
Abba Aminu da ya ji labarin tsaki ya yi ya ce, Ku bar shi aure dai ko ya je ko bai je ba babu abin da zai sa a fasa wannan daurin auren.
Taro ya yi taro jama’a sai wanda ya gani manyan mutane daga garuruwa sun samu halartar daurin auren. Mr Sameer ma sulalewa ya yi tun kafin a daura auran saboda ji ya yi hajijiya na daukarsa, wani abokinsa Kamal da suke Kaduna ya roke shi da ya dawo da shi gida ba don yana jin tsoron fadan da Abban shi zai masa ba da ba abin. da zai sa ya zo gurin.
Yana zaune a dakinsa ya fara jiyo hayaniyar dawowar jama’a nan take ya fara jin faduwar gaba don bai son jin labarin wadda aka aura masa, don tunda dai an daura ba shi ke nan ba.
Muhammad Bashir da Fu’ad da Ya Abba su ne suka fara shigowa dakin nasa suna nemansa, haka suka zo suna kiransa ya tashi suje gaisuwar surukai. Cikin bacin rai ya ce shi babu inda za shi.
Suna cikin ba shi baki sai ga wayar Abdul cikin wayar Ya Abba yana ce musu ga Yaya Muhammad a gida ya dawo gaba daya suka taho illa Fu’ad da suka bari yana shawo kan Mr. Sameer. Muhammad Bashir shi ne kan gaba ya fi kowa zakewa ala dole wai shi ne zai fara yi wa Muhammad magana, bai yi aune ba ya gan shi ya fado dakin nasa.
Wani irin kishi ne ya kama shi tare da wani irin makokon bakin ciki, ba don da jama’ar da suke take masa baya ba da zuwa zai yi ya shake shi sai dai a dau gawarsa yadda yake jin zafi cikin zuciyarsa.
Hannu ya mika masa ya ce, ‘Assalamu Alaikum dan uwa mu gaisa yau babu wani sauran gaba tunda an daura auren.
Cikin bacin rai ya ce, ‘Kai malam bana son rainin wayo za ka fice min daga daki ko sai na yi kasa-kasa da kai. “Tuba nake angon Raihanatu abin namu bai kai yar haka ba dama na zo maka da albishir ne cewa Www.bankinhausanovels.com.ng
Raihana ta zamo mallakin ka. Wata irin zabura ya yi ya ce, ‘Me ka ce, ban jika sosai ba.”Ka ji ni mana sai dai ka waske.” Tun kafin mamaki ya gama bayyana a fuskar
shi sai kawai ganin Mr. Sameer suka yi ya fado dakin yana haki burinsa kawai ya ga M.J. Cikin wannan yanayi ko sallama bai yi ba yana tozali da M.J ya ce.
“Muhammad ka ji wani abin farin ciki da ya same mu wai kai ne mijin Miss Haana, ni kuma na auri Rauda so amizing ya za mu yi da wannan farin cikin yau?”Cikin sauri M.J ya rike Mr. Sameer ya ce, ‘Dama da gaske ne Muhammad yake fada min?”
Ya Abba ya zo gabansa ya ce, ‘Da gaske ne Muhammad yau burin ku kai da Haana ya cika kun zamo abokan rayuwar juna fatana M.J ka ba wa kanwata farin ciki ka yi min alkawarin ba za ka sa ka ta damuwa ba, ba za ka bari kowane irin hawaye ya zuba a fuskarta ba idan ba na farin ciki ba, idan. ka yi min haka ka gama yi min komai a rayuwata.
Da sauri ya rike hannun Ya Abba ya ce, ‘Abba yau ina cikin tsananin farin ciki wanda ba na jin na taba samunsa a rayuwata, na yi maka wannan alkawarin idan ma da wani abu da ya fi wannan ka sake nema zan yi maka Rahihana tafi komai da kowa muhimmanci a rayuwata tarin son da nake mata bana jin ina yi wa kaina.
Saboda haka na yi maka alkawarin har duniya ta tashi ba zar taba hada son Raihana da kowa ba farin ciki idan har akwai na siyowa zan fita na nemi kudi a fadin duniyar nan don na siyo na ba ta shi mutukar hakan zai saka farin ciki Abba na gode.”
Nan ya mayar da kallonsa ga M.B ya ce Muhammad ka yafe min irin abin da na yi maka a baya.
**Kar ka damu komai ya wuce tunda dama nima tsokana na shigo cikin rayuwarku kai da Raihana na yarda da irin son da ka ke mata, kuma kowa ya gane cewa son da ku ke wa juna Allah ne ya hada ba za ku taba rayuwa ba ba tare da juna ba.”Fu’ad ya ce, ‘Kai ku mu fito mu je gaida iyayen nan namu na matsu na yi tozali da amarya ta.” Dariya aka yi, M.J ne ya rike hannun M.B ya ce ku mu je.M.B ya dakatar da shi ya ce, ‘A’a ango ba za
mu fita da kai haka ba babu shiri kamar ba ango ba.”
Abdul ne ya ja shi ya tura shi bandaki ya ce, ‘Oya Barrister shiga ka watsa ruwa muna jira ga abokanan ka nan suna jiran ka.”
Gabaki daya amare sun hallara a gidan kakaninsu kowacce tana cikin farin ciki babu wata mai damuwa. Raihana ta yi shiru tana tunanin yadda Malam M.J dinta zai samu wannan labarin kai tsaye Ya Abokinta Muhammad Bashir zai je masa da wannan albishir din kamar yadda ya fada mata.Fadeelah ce ta buge ta ta ce, ‘Kai ‘yar uwa ko dai tunanin Yayan namu ki ke yi ne?”
Haaya da take gurin ta ce. Za ta fasa ne ni na
kasa gane tsakaninsu wane ya fi son wani.”
Rauda ta ce, ‘Ku tsaya na yi wani nazari.” Ta wani kaikaice ta ce, ‘Sister kalli cikin idona zan duba wani abu ina son karanto wani abu a zuciyarki.”
Harararta ta yi ta ce, ‘Ku bana son iskanci fa za
ku kyale ni kun san fa ni yayarku ce ba zan dauki shegantakarku ba da iya shege.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Zahra ce ta yi saurin shigowa ta ce, ‘Kai ga angwaye nan sun zo kowacce ta rufe kanta ba mason kowa ya ga fuskar matarsa sa wa za mu yi kowa ya nuna mana matarsa za mu ari al’adar wasu
wato Indiyawa.” Dariya kowa ya yi da yake dam
a tuni sun shirya hakan dalilin kenan da suka yi shiga iri daya duk matan kuma Zahra ce da wannan iya shegen wai don su tsokani malaminsu.
Katafaren falon gidan ne na kakaninsu duk iyaye da ‘yan uwa suna gurin haka kowa ya zauna dama sun shirya gurin an kawata shi sai wani kamshin turaren hayaki yake.
Lokacin da angwaye suka shigo gurin sun kidime da ganin yadda gurin yake ganin amare jere da su kamar matan Indiyawa duk sun yane kansu. Idan ka hango Malam M.J duk ya kidime Allah Allah yake ya yi ido hudu da Raihana dinsa.
Lokacin da suka shigo kowacce amarya tana iya hangen mijinta ta shara-sharan galenta nan ne Raihana ta hangi Mal. M.J dinta yadda ya yi wani rin masifar kyau kamar wani tauraro cikin taurari ya yi mata mugun kyau haduwa da wani irin gwarjini take ta ji wani irin shaukin son shi ya kama ta yau Allah ya cika mata burinta ta auri Malam M.J dinta dole ta godewa Allah.
Bayan an gaisa ne Mama Bara ta fara yiwa kowa fada da nasiha a kan kowa ya zauna lafiya da matarsa a kuma rike zumunci da hadin kai tunda suka taso ake auran zumunci da fatan su ma idan sun taso za su yi wa na su haka yadda ZURI’A DAYA za ta yi ta haBBaka kusan duk iyaye mata kowa ya yi gajeriyar nasiha. Daga karshe jawabi ya koma gurin Zahra.
Ta mike ta ce, “Malam M.J yau ranar ka ce ba za ka ga idon Raihana din ka ba sai mun gwada irin tarin son da ka ke mata nan duk iyayen mu kuma ZURI’A DAYA don haka kada ka ji kunyar kowa ka tashi ka zabo mana Raihana a cikin amaran nan hudu idan ka cika masoyi idan ka kasa za mu ce to lallai son ba duka ba ne.Dariya ya yi ya ce, ‘Ke Zahra malamin ki ne ni
fa idan ki ka yi wasa zan yi kyautar maki sha biyar babu ke.”
Gaba daya aka saka dariya su Salama su Rabi’a suka ce ‘Sir ba ita kadai ba har mu mun goyi bayan ta sai dai mu ma ka hana mu.” Mikewa ya yi ya ce, ‘Zan ba ku mamaki yanzu
kuwa. Nan ya je ya tsaya gabansu yana ta dube
dube kamar ya koma ya nuna wannan sai ya nuna
waccan can kawai sai ya yi tsaye ya janyo hannun
Haaya tana bude fuskarta ya ga ita ce sai ya runtse
ido ya ce, “Kash!”Haba sai gurin aka saka sowa nan duka kowa ta bude gyalen kanta nan ne ya gane Raihana ce ta farko wadda da zuciyarsa ta umarce shida ya nuna. Wani irin kayataccen murmushi suka dinga yi
wa junansu, ganin irin rashin kunyar yaran zamani duka iyaye da kakanin suka mike suka fice.”Raihanah ya a kai haka ya faru yau mafarkina
ya zama gaske.”Mikewa ta yi tsaye ta ce, ‘Me za ka ce min kai da ka kasa nuna ni cikin ‘yan uwana ka janyo min kenan su Zahra suna min tsiya.”Kiyi hakuri zan yi maganinsu gurin rage musu maki na jarabawa.
Zahra ta juyo ta ce, Tuba nake duk ni na janyo amma ai ya yi kokari ai da ke zai nuuna sai ya nuna Haaya kin san da mun tsorata da tashin farko ya isa a kanki you know Malam M.J yana son ki ki rike mana malaminmu idan ba haka ba mu ci tarar ki.”
An dan yi muhawara da nishadi a nan ne M.J ya gane cewa Muhammad Bashir shi ne ya auri Fadeelah, Mr. Sameer kuma Rauda shi kuma Fu’ad, Amal ya aura ‘yar gidan Alh. Lukman wanda babu wanda ya sani, ashe tun tuni suna soyayya a boye tun kafin a san za a shirya a junansu iyayensu mata ne kawai suka san da hakan suka shiga addu’a ga shi Allah ya cika musu su ma na su burin.
Gefe guda ya ja Fadeelah ya ce, ‘Fadeelah ki yafe min na san abin da na yi miki ban kyauta ba na ba ki damuwa da yawa don Allah ki gafarta min ban taba kin ki ba a matsayin ‘yar uwa sai dai ban ji zan iya auranki ba duba da Raihana cikin rayuwata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, ‘Kar ka damu Ya Muhammad haka kaddara take dama Allah ya rubuta cewa dama Yaya Muhammad ne mijina duba da irin son da yake min tun îna karama, ka san Ya Muhammad dan kanwar Daddy dinmu ne da ta rasu tun yana karamin Mommy ta rike shi a gurinta ya girma shi ma fa dan uwa ne don dai a dangin mahaifinsa yake, daga baya bayan ya girma ya kara dawowa gidanmu manta shi fa ka yi.”
Ya cika da mamamki kwanyarsa ta shiga tunanin to ya a kai haka har ya zo ya ce yana son Raihana dinsa ashe shi ma dan uwansu ne, dole ya. samu labarin yadda abin yake. Nan suka fahimci juna take ta yafe masa, ta ce haka Allah ya shiryo mana matar mutum kabarinsa babu mai auran mijin wata, ko matar wani.
Ya yi mata godiya sosai nan ya koma gurin Raihana ya janyo ta ce, ‘Yau za ki amsa quary sai ki fada min yadda a kai ku ka raina min hankali ke da Muhammad.”
Cikin dariya Muhammad ya zo ya ce na ji abin
da ka ce idan kana son karin bayani ka je gurin Abba Aminu duk shi ya tsara mana haka maza bar min kanwa ba ta da laifin komai.”Dariya ta yi, ta yi saurin barin gurin tana masa gwalo ya bi ta da wani kayataccen murmushi yana girgiza kai. Gaba daya suka fito suka nufi wurin reception
da za a yi a can MEENA EBENT su da tawagarsu har iyayensu maza duk can suka nufa.
Wani irin kaunar Abba Aminu ce ta zo masa take jin haushi da tunanin abin da yake a ransa duk ya kau ya kara ganin duk cikin ZURI’A ba shi da masoyi sama da shi saboda jin an ce shi ne ya
shirya komai don haka dole ya nemi Raihana
anjima a kan komai ya sarara idan bai samu ganinta
ba ya kira ta a waya, kamar yadda ya so bai samu ba dole ya kira ta a waya take fada masa. Lokacin da Abba Aminu ya kira ni a kan na fitar da wanda nake so a cikinku ina kuka na ce, ‘Ni babu wanda zna aura cikinku ina son ‘yan uwana su samu abin da suke so ni na hakura.
Nan na fada masa duk yadda abin yake ya ce na tashi na tafi. Ashe daga baya ya kira kowa daya bayan daya cikinmu duk ya ji ta bakinsu.
Daga karshe dai Fadeelah aka samu da matsalar har Abuja ya bi ta da ta bar gidan ranar da ya ji ta bakinta. Zama suka yi sosai a can Abuja da Mama Bara ta dage sai an yi auran ganin sun fara hayaniya da Abba Aminu har tana maganar za ta iya batawa da kowa idan har ba a yi wannan auran ba nan Daddy dinsu Fadeelah ya tsawatar mata ya ce idan ta yi kokarin kirkirar fitina to wallahi za ta yi a bakin auranta.
Da kyar Abba Aminu ya shiga aka sasanta nan ya ce Ya bawa Muhammad auran Fadeelah dama ya dade yana son ta, kuma idan ba a yi auran ba sai dai ita da Fadeelah sai dai su tattara su bar masa gidansa.
Jin haka Fadeelah ta fito daga inda take labe tana kuka ta ringa rokon Daddy dinta a kan ya janye niyarsa za ta auri Muhammad din domin duk abin da Mommy dinta take yi don ta ganta cikin farin ciki ne don haka a dalilinta ba za ta kashe auran Mommy dinta ba ta yarda za ta auri Yaya Muhammad din da Daddy yake so take ta cewa Abba Aminu ta hakura na aure ka tunda dama ka fada mata ni kake so saboda ita ba za ta bari a daina zumunci ba.
Duk suka shiga sa mata albarka a take sai da Mama Bara ta yi kuka nan aka gama magana, nima a wannan ranar Fadeelah ta kirawo ni ta ce ta bar min kai muka shiga rantse-rantse dole na kashe mata waya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokacin da Abba Aminu ya kirawo ni maganar ga wanda ya ce zan aura hankalina ya tashi ban san lokacin da na amsa masa ba. Ganin a cewar da na yi ya yi min addu’a ranar da ya zo ya tafi ya kira ni ya tambaye ni ya yi min ban musa masa ba na ce eh, duk da ya gama karantar ina cikin damuwa har na mike zan tafi ya tsayar da ni.
A nan na cika da mamamki da ya ce game za mu buga da shi duk abin da ka ga ina yi maka duk shi ya tsara min wai don ya gwada kai da Mr. Sameer wane yake so na zai kuma iya juri’a sai ga shi duk gwajin da ya yi kai ne ka yi nasara.
Haka ma ya yi wa Rauda ya ce kada ta sake ta ba wa Mr. Sameer fuska ya fada mata sun daidaita da Fu’ad ya fada masa wadda yake so ya zama dole ta auri Mr. Sameer amma bai yarda ta ba shi fuska ba, kuma ba zai bari ya sani ba har sai ranar daurin auransu.Lokacin da ka samu Uncle Mukhtar da
maganar, Abba Aminu ne ya ce ga abin da zai fada maka duk abubuwan da suke faruwa Abba Aminu ya fadawa duk yan uwansa shi yasa ka ga kowa bai nuna damuwa a kan abin da yake faruwa ba. Haka nima duk abin da yake faruwa babu
wanda yake ɓoye min haka zai kira ni ya fada min da wannan muka shaku muka zama abokai kaf a ZURI’A ba ni da babban aboki kamar Abba na Aminu, the honest person a rayuwata ka ji abin da ya faru da
ba ka sani ba. Ina son shi saboda yardar Allah da kokarinsa yasa na samu SANYIN IDANIYATA BARRISTER MUHAMMAD JAFAR NASEER DANFILLO wanda zai zamo min ABOKIN RAYUWATA na har abada.”Ajiyar zuciya ya yi ya ce, ‘Mu dawo baya da na
ji kin ce har rantse-rantse ku ka yi ke da Fadeelah ba za ki aure ni ba to yanzu me yasa ki ka aure ni kin ga kenan sai kin yi kaffara.”
“To na ji zan yi. amma idan ka fiye zafi sai na ce na fasa auran. Murmushi ya yi ya ce, ‘Ah! Karya ki ke kuma wannan yarinya ai kin riga da kin zo hannu sai yadda na yi da ke ki shirya anjima zan zo mu fita
na kama mana daki a nan Tahir Guest Palace.
“Tab! Aradu ba da ni ba, domin babu inda za ni kar ka yi tunanin don an yi daurin aure ka ce kana da fawa a kaina tun kafin na je gidan ka ka bari na gama exam dina na tare a gidanka tukunna.”
“Kina hauka ne tun yanzu za ki fara yin musu da ni ba ki isa ba ni mijiki ne a yanzu na ce na datse karatun babu mai yin min magana tun da a yanzu na fi kowa iko da ke gwara kawai ki yi min abin da nake so. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kada ka yi min fitinar ka kana takura min kai tsaye gurin honest man dina zan kai ka kara.”
“Hahaha! Yarinya da kenan yanzu ba shi da wannan right din ni dai na fada miki ki shirya duk kayanki har na karatu, domin a can za ki yi karatun dam yadda za mu fi sake wa nine months nake son daukar babyna kin ji na fada miki.”
“Hmmmm! Malam sai anjima ba da ni ba, wannan batun Ammi da Abba da kunya ta suka haife ni.”
Dariya ya shiga yi ya bi wayar da kallo, kamar yana iya gano ta ta ciki nan ya sumbaci wayar ya rungume ta da yake a kan gadonsa yake nan ya dinga jin farin ciki na shigarsa ya sake yi wa Allah godiya da ya cika masa burinsa.
Take ya ji kaunar Abba Aminu ta shige shi nan ya saka a ransa dole ya je ya yi masa godiya, shi ma daga yau ya zamo masa Honest Man dinsa kamar yadda ya zamarwa Raihana dinsa domin duk abin da za ta so ko ba shi da muhimmanci a rayuwarta to insha Allah zai nuna abin shi ma ya fi komai muhimmanci a gurinsa don ya sa ta farin ciki na har abada a rayuwarta.
Duk yadda M.j yaso su kasance da Raihana dinsa abin ya faskara dole ya hakura shi ne ya dage shi zai dinga kai ta makaranta da farkoda ta yarda amma ranar da za su fara exams yasa ta shirya da wuri suka fita kawai sai ta ga ya wuce da ita Tahir guest Place nan fa ta rude ta shiga tambayar me zaasu yi kuma a nan?
Ya bata fuska ya dawo mata asalin Malam M.J din ya ce, Saida ke zan yi.
Ta yi shiru don ta san gatse ya yi mata da ya yi
parking da motar ya umarci ta fito tace ya je ya yi
abin da zai yi tana nan. “Wai me yasa ki ke haka ne ni fa mijin ki ne ina miki magana kina yi min musu za ki fito ko kuwa?”
“Ai ba haka muka yi da kai ba ka san dai idan
zan shiga sai ka sa na bata lokaci..” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Oh! Ke ki ka sani kin ga lokacin ya cika ban kai ki makarantar ba ki duba time ki gani ki na da awa biyu nan gaba. Look bana son musu ki wuce muje.
Ganin tarin bacin rai a fuskarsa ita ma sai ta cukule ta fito yadda ya ga tana shan kunu sai abin ya shiga ba shi dariya sai dai bai
bari ta gano shi ba. Haka suka jera suka tafi sai gani ta yi ya zaro wani kati a hannunsa yana sawa jikin kofar dakin ya bude.
Wani irin kallon tuhuma ta yi masa shiga yayi fuskarsa dauke da murmushi nan ya yi mata nuni da hannu alamar ta shigo gudun kada ta nuna duhun kai ga kuma jama’a na wucewa sai kawai ta shige kawai sai ta bi UMARNINSA. Tana shiga ya rufe kofa, nan ya hada ta da jikinas yana shakar kamshin jikinta, duk yadda yaso ya aiwatar da wani abu mai muhimmanci ta