ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

dan murmusa, sannan ta daga masa kai shi
ma murmushin ya yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sam daren yau ya nemi barci a idanunsa ya rasa
ya rasa me yasa ya ji ya kasa fadawa Haana
gaskiyarsa na cewa ya Jima da sanin Haaya tun a
baya hakan da ya yi duk sai ya ji kamar ya jefa
kansa cikin wani takunkumi. Me Haana za ta dauke
shi idan ta gano cewa dama can sun san juna? Bai
wani jefa kansa cikin wani dogon tunani ba, domin
ya ajiye wa ransa cewa gobe ne zai je su ga juna
kai tsaye da Haaya, yau ya kara sakawa ransa cewa
har abada shi da samun Haana a matsayin matarsa

Uwar ya yansa ya kuma sawa zuciyarsa cewa
Haaya ita ce kaddararsa tunda ga yadda abinya faru
a ranar ya yi kukan zahiri da na zuciya, domin kara
sadadakar da cewa ya rasa Haana ne har abada
cikin duniyarsa da rayuwarsa gaba daya.
Yau kwanan Ya Abba uku da dawowa duk
yadda Haana ta yi ta hada shi da Haaya abin ya
faskara ta ki yarda ban da kuka babu abin da take
duk a tunanin Haana tana kukan dawowar Ya Abba
ne kafin ta samu Mustapha dinta haka shi
Daddy din nasu tun yana lallaba ta har ta zo tana
ba shi haushi, don haka ya fara fushi da ita.
Shi kansa Ya Abba ya shiga damuwa don yana
ma Www.bankinhausanovels.com.ng
Son zuwa su hadu don su yi magana face to face, ta
ki yarda don sai da suka je da Haana tare babu
yadda ba a yi da ita ba ta rufe daki ta ki budewa,
Mommy ta ce Su tafi su bar ta za ta shawo kanta.
A yammacin ranar ne Mr. Sameer ya dawo shi
ma daga tafiyar da ya yi ko wani hutawa bai yi ba
ya garZayo zuwa gurin amaryar tasa.
Yana shigowa da Ya Abba suka yi kicibis yana
shirin fita, musabaha suka yi cikin sakinfuska. Kai
Tsaye Mr Samecr ya ce, Abba na gode fa da abin
da ka yi min, don Allah ka yi hakurin abin da ya
Faru a baya na sani sarai kana son haana amma na
Kasa hakura sai da na san yadda na yi na gabatar
nata da kaina, na ji duk irin namijin kokarin da ka
yi ina can duk Abbana ya yi min bayani, Allah ya
Saka da alheri ya bar mana zumunci.


damu
Dafa ka fadarsa ya yi ya ce, “Kar ka damu
Sameer wannan ba komai ba ne yi wa kai ne, ni dai
fatana ka kawo farin ciki a rayuwar Haana kada ka ‘saka ta kuka ko kawo mata wata bakuwar Www.bankinhausanovels.com.ng
damuwa cikin rayuwarta, idan ka ba ta farin ciki
zan yi farin ciki da haka, saboda ba ni da abin da na
tsana a rayuwata irin ganinta cikin damuwa.
Haka Allah ya tsara min cewa Haana ba ta
cikin kaddarata don haka ko da wasa kada ka taba
fada mata ina son ta ko na taba sonta, tunda ba ta
sani ba, ina son a bar hakan har abada, idan ka yi
min haka ka gama yi min komai a rayuwata.
Har kullum farin ciki nake so in gani a fuskarta
ba damuwa da zubar hawayenta ba.
Jikin Mr Sameer ya yi sanyi ya kara tabbatarwa
da kansa cewa lallai ba karamin so Abba yake yi
wa Haana ba sam irin son da yake mata da
bambanci da irin nasa ya dinga jin kamar bai
kyauta masa ba da ya shigo cikin rayuwarsu ya
dinga jin kamar ya janye ya komawa Rauda, domin
kullum ya kwanta sai ya ganta cikin mafarkinsa
kuma cikin damuwa yake ganinta.
Ya Abba yana ganin irin sauyi da yadda jikinsa
ya yi sanyi ya ce, Come on Sameer ka saki ranka
ka fitar da duk wani tunani a ranka ka sa cewa haka
kaddararmu take ni da dakon son Haana kai kumna
da samunta matsayin matarka dama ba komai bawa
yake samu ba ya kuma same shi.”
Abba na gode Allah ya bar mana zumuncinmu
Yasa mu dore da sadaukar da farin’ cikinmu ga
Yan unanmu.
Ameen Sameer ka shiga tana ciki idan na
dawo ma hadu. Ya dan bubbuga masa kafada.
O.K Haka ya tafi ya bar shi ya bi shi da kallo cikin
alhini har cikin ransa ya ji babu dadi to amma ya
zai yi? Haka ya kama hanya ya shige ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suwar yara da ta ji ana cewa Yaya Sameer
oyoyo! Yaya Sameer Oyoyo!! Shi ne ya ba ta
tabbacin shi din ne ya dawo dazu ta ga kiransa ta yi
buris da shi domin ba ta son dagawa ya ba ta ciwon
kai saboda kullum da sabon salon da zai zo mata da
shi na bacin rai, don haka ta zabarwa kanta rabuwa
da shi domin karfe daya baya amo, sai da dan
uwansa.
Tana jinsa suna gaisawa da Granny da Ammi
da yake tana kicin nan ta sulale ta bi ta kofar baya
ta fice ta nufi sama dakinta tare da abincin da ta
debo.
Har ta gama cin abincin ta ba ta ji ya aiko a kira
Ta ba, sai ta sa a ranta cewa ya ma tafi nan ta haye
gado tana chatting abin ta.
AZIza ce ta shigo ta yi mata sallama ta cire kai
ta amsa mata.
“Aunty wai Ya Sameer ya ce ki zo ba ki ji
ZUwansa ba?
Ubana ne shi don na ji zuwansa sai na debo
Jiki na zO gurinsa, je ki ce masa barci nake yi.
Zaro ido ta yi waje tace, “Aunty a wannan time
din ne zai yarda kina barci please ki taso mu je
wallahi ya ce min zuwansa kenan ko hutawa bai yi
ba ya zo don ya gan ki kin ga ai ba dadi.
Bata rai ta yi tace, Little ki fice min idan ba
kya son raina ya baci ki je ki ce masa ba zan z0 ba,
Idan ya matsu ya zo ya fito da ni na zo na gan shi.”
Tabe baki ta yi ta yi kwafa ta ce, Allah ya huci
Zuciyarki ni ba zan iya fada masa haka ba.
To bace min da gani.
Sum-sum ta fice abin ta ba ta kara bi ta kan ta
ba. Tana fita sai taji Wani iri kamar ba ta kyauta ba mintina kadan sai ga sako Cikin wayarta.
Na san ba barci ki ke ba zuwa ne ba za ki yiba,
ba ki isa ki ba ni haush ba zan dawo anjima idan
ba ki fito ba har saman Zan haw0. Amarsu ta ang0.
Tsaki ta yi ta cillar da wayar ta sauko kasa abin
ta. ko da ta zo babu wanda ya bi ta kanta sai Nur da
ya ce “Aunty yanzu Ya Sameer ya tafi gidansu ba
ki gan shi ba.”
“Ayya Nur na shiga wanka ne kafin na fito ya
tafi, amma ai mun yi waya da shi.
Aziza Little ta wani tabe baki hade da kwafa ta
mayar da hankalinta ga kallon T.B.
Haana ta kalle ta ta watsa mata uwar harara,
don ta san da ita take, daidai lokacin da Granny ta
Z0 gurin ta ce, “Au lna mai gidan nawa ko har ya
tafi ne?
Haana ta ce, Eh, ya tafi.
To babu laifi.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan ta samu guri ta zauna mamaki ya kama
Little ganin yadda Haana take bada amsa cikin
kwarin gwiwa kamar sun hadu, haka suka hadu
suna hilrarsu.
Karfe biyar na yamma sai ga Fu’ ad nan ya zo
neman Haana, cikin murna Haana ta fito suka
zauna a falo ta ce, “Ya Fu’ad yau kai ne da kanka.
Murmusmuhi ya yi ya ce, “Haana gurinki na zo
kanwata damuwa ta na san ban da ke babu wanda
zan iya zuwa ma da matsalar.
Ya Fu’ad ni kuma? Ta fada cikin sakin fu
ska.
Eh, mana kaf cikin family dinmu wane ya kai
ki kusanci da Rauda a kanta na zo gurinki ina ganin
idan nan babu matsala za mu iya zama mu yi
magana idan kuma da inda za mu koma to sai mu
je don bana son kowa ya sani.
To mu koma back yard din gidan nan sai muyi magana a nutse.
Can suka koma nan ya shiga jero mata irin
matsalar da yake samu gurin Rauda, sam ta kasa
sakewa da shi duk lokacin da ya zo ban da kuka
babu abin da take ya kasa gane matsalarta, shi ne
ya zo gurinta ta fada masa gaskiya ko da wanda
take so aka hana ta idan har da wannan maganar to
shi zai hakura zai yi kokarin ganin an yi duk yadda
Za a yi a ba ta wanda take so, tunda dama shi ma
yana da wacce yake so UMARNIN iyaye kawai ya
bi yana tausaya mata ne don babu yadda bai yi da
ita ba ta ki ta yi masa bayani.Hakan ne yasa na zo domin ke Ce mafi kusa da ita, dole kin san wani abu a tare da ita.
Shiru Haana ta yi ta gama saurarensSa, sai da ya
sauko sannan ta ce. “Ya Fu’ad, Rauda tana da
Zurfin Ciki na jima ina fuskantar tana da matsalar
da take son boye min na yi da ita ta ki fada min.
dole na hakura, gaskiya ne Rauda tana da wanda
take so, amma wallahi ta ki ta fada min ta dai fada
min cewa ta fuskanci wanda take so ba ita yake so
ba A TUNANINA tun lokacin da muka yi maganar
ta hakura ashe ta bar abin a ranta, ban da wannan
ban san komai ba, donhaka ka yi hakuri tunda ka
ZO min da wannan maganar Zan je na same ta naji matsalarta insha Allahu ba zan boye maka duk
yadda muka yi da ita ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yauwa Haana na gode shi yasa na zo gurin ki
don ke kadai ce zan samu abin da nake Son ji daga
gurin ki.
Haba Ya Fu’ad ai babu godiya a tsakaninmu
ni ya kamata ma na’ yi maka godiya da ka zo har
inda nake maimakon ka kira ni har gida.
A’a, wannan abin da na yi shi ne daidai.”
Nan suka yi sallama ta raka shi har bakinkofar
get sannan ta dawo cikin gida tana juya abin cikin
Ranta.
Kimar Ya Fu ad ta karu a gurinta ta san cewa
lallai idan har ya auri Rauda zai kawo mata farin
cikin mai tarin yawa cikin rayuwarta baki daya da
wannan tunanin ta dawo ciki
Wayarta ce ta shiga ruri da sauri ta kai hannu ta
dauka tana dubawa ta ga sunan Sister Fadeelah da
sauri ta daga ta ce.
Fadee ya aka yi ne?
Haana guest vhat?
Na ba ki gari ‘yar uwa.
Cikin doki ta ce, “Gobe Ya Muhammad zai zo
don haka gani nan na baro Abuja muna kan hanya.
Daddy ne ya kira Mama ya fada mata, shine na ce
ban ga ta zama ba dole na zo na ga zuwansa Mama
kuma ta ba ni goyan baya.
Wow! I like that, ki zo din na taya ki murna
da dawOwar masoyinki sai kin zo ina nan ina jiran
zuwanki, na y1 kewarki dama. Ta karasa fada
cikin dariya.
Yauwa yar uwata sai na zo sai dai kuma ina
da wata bukata gurin ki
Fadi mu ji kowacce iri ce insha Allahu na yi
miki alkawari babu abin da zai gagare ni da yardar
Allah.”
Promise
Promise Sister, fadi na ji me ki ke so daga
gurina
Haka kawai jikina ya ke ba ni kamar zan samu
matsala ni da Ya Muhammad ina jin shakkar
haduwa da shi jikina yana ba ni da wuya idan zai
karbe ni mazaunin mata don na san yana da wacce
yake so.
Please, Haana ki daure ki taya ni na yi nasara a
kansa yadda zai so ni ya manta da Waccan saboda
na san irin kafiyarsa da taurin kansa babu mai hana
shi idan ya kafe. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kar ki damu Fadcelah na yi miki alkawarin
duk yadda zan yi sai Ya Muhammad ya soki kamar
yadda ki ke son shi ki bar min komai a hannuna za
ki ga yadda za mu yi da shi, ke dai Allah ya kawo
ku lafiya, na yi miki wannan alkawarin zan shiga
Jikinsa har sai na yinasara bai isa ya ce baya son kiba.
Cikin farin ciki Fadcela ta ce. Godiya nake
Haana na yi farin cikin samun ki a mazaunin yar
uwata ta jini ban da ke babu mai iya yi min haka,
duk cikin family dinmu.
Nan suka kashe wayar suna masu yin sallama
da juna.
Tana gama wayar ta fito sai zuwa gidan su
Rauda, ko da ta zo ta samu Rauda na barci Mamah
Me ta ce, Ciwon kai ne mai zafi yake damunta
magani ta sha ta samu ta dan rintsa.
Dakin ta nufa ta ganta tana barci ta jima tana
tare da ita, sannan ta koma idan ta tahsi ta dawo.
Kai tsaye gurin Haaya ta je wannan karon ta samu
sun yi magana sai dai ba ta iya bayyana mata cewa
Ya Abba shi ne Mustapha dinta ba, nan ta roke ta
Cewa don Allah ta jira su anjima za ta rako Ya
Abba su ga juna.
Kuka ta fara yi mata tand cewa, “Haana na roke
ki don Allah ke da Ya Abba ku yi nisa da rayuwata
a yanzu bana son ganinku cikin rayuwata, idan kina
Son ganina cikin takura da damuwa to ki yi kokarin
tursasa nina hadu da Ya Abba, idan kina so na yi
farin ciki to kada ki kawo Ya Abba gidanmu ni
kadai na san irin damuwar da tashin hankalin da
nake ciki please Haana na roke ki da kada ki kuma
Yi min maganarsa, na bukatar nutsuwa da saka
dangana a cikin zuciyata.
Ki bar ni na nutsu yanZu domin zuciyata tana
cikin rudani daga baya zan miki bayani kada ki
takura ni da son na yi miki abin da ki ke so a
yanzu, please Haana na roki wannan alfarmar a
gurinki ki daure ki yi min.
Cikin sanyin jiki ta ce, Shi ke nan Haaya zan
yi duk yadda ki ke so ba zan takura miki ba, na san
irin halin da ki ke ciki Allah ya bayyana
miki
Mustapha din ki, domin na san shi kadai ne farin
cikin ki a yanzu.
Na gode Haana da ki ka fahimce ni sai dai a
yanzu ba ni da buri da hope a kan Mustapha na
hakura da shi har abada saboda bayyanarsa gare ni
ba ta zo min da farin ciki ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haaya me ki ke son fada min kina nufin kun
hadu da Mustapha din naki ne yaushe? A ina?
Girgiza kai ta yi ta ce, Kar ki damu zan miki
bayani amma ba yanzu ba, saboda ZuCiyata tana
Cikin rudani ina bukatar nutsuwa ina Jiran zuwan
Ya Muhammad ne da Ya Abdul gobe kada ki
takura min da son jin kOmai yanzu.,
Shi ke nan kar ki damu Allah ya ba ki dangana
din kamar yadda ki ka fada, ni zan koma sai gobe
din
Na gode Haana don Allah kada ki yi fushi da
ni, ba wai bana son Yayanki ba ne, ina da dalilina,”
Zuwa ta yi ta goge mata hawayen da yake zuba
daga idanuwanta ta ce. “Na fahimce ki fa Haaya
kar ki damu Allah ya kawo mana mafita.” Tana
gama fadin haka ta fito ta yi tafiyarta.
Ko da za ta wuce nan ta iske motar su Fadeelah
har ta ZO da sauri ta karasa gurinta suna ganin juna
suka rungume junansu.
Haana ta ce, Ashe kin kusa karasowa ma mukayi waya.
Mun Wuce Zaria sosai sannan na kirawo ki na
kosa mu hadu ne yasa na kira ki na fara fada
miki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya ta yi nan suka rankaya zuwa gidan
kakaninsu inda Fadeelah take sauka idan sun zo.
Fiye da mintuna talatin suna tare daga nan suka yi
sallama ganin dare ya fara.
Har za ta wuce gida sai wata zuciyar ta ce ta
dan leka ta ga jikin Rauda mana tunda dama ta ce
Za ta dawo.
Lokacin da ta shiga falon su Na’im kawai ta
gani a falo suna kallo ta tambaye su ya jikin Ya
Rauda suka ce tana ciki ta tashi, Ya Abba yana
dakinta yana mata fada ta ki cin abinci.
Da sauri ta karasa don su hadu su yi mata fada,
tana zuwa bakin kofa ta ji muryar Ya Abba yana
Cewa.
Rauda hakurin nan da dangana shi ne mafita
gare ki, ki cire dukkan damuwarki ki karbi kaddara

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *