Tunda Momy ta fita ta bar Nailah sai ta koma ta kwanta,tana jin yadda nan da nan kanta ya ɗauki wani matsanancin ciwo,ga zuciyanta dake cigaba da bugu tamkar ana lugude,sunan ya AA kawai take nanatawa acikin zuciyanta wani mashahurin ruɗani na sake shiganta,kanta ne yayi masifan sake ɗaukan zafi bata san ta yadda ya Anwar zai iya zama da ita alhali tana hango tsananta ƙarara a idanunsa,uwa uba shiɗin yanada xaɓinsa wanda ga dukkan alamu yadda take ji abakin qanninsa suna tsananin son juna shida Hudah,amma tasani bata da wani hanzari ko wani abunyi domin ko xata auri ya Anwar ya dinga yankan naman jikina yana gasawa kullum ne,sabida ƙiyayya ya zama dole ta aureshi sabida halaccin da iyayensa sukai mata,suka ɗakkota daga gidan marasa galihu suka inganta rayuwanta,suka bata duk wani gata da iyaye zasu baiwa ɗan cikinsu har ta zama cikakkiyar mutum,bazata iya bijerawa wannan ahali masu matuƙar karamci agareta ba,bazata iya ƙin duk wani mahaluki daya danganci Momy ba,bare jininta data fi kowa sanin tafi son sa aduk cikin ƴaƴanta,wasu hawaye masu bala’in zafine suka cigaba da biyo face ɗinta na tausayin kanta da irin rayuwan da zata kasance aciki idan ta zama mallakin mutumin da baya ƙaunanta.
Wani zazzaɓi -zazzaɓi taji yana shirin rufeta cikin mutuwan jiki ta sauka daga bed ɗin ta nufi bathroom,tara kanta tayi a shower ruwa na zuba tun daga kanta zuwa jikinta ba tareda ta cire rigan dake jikinta ba,a hankali sanyin ruwan ke ratsa gashin kainta zuwa jikinta har saida ta jiƙe sharkaf,kafin ta zare kayan jikinta ta haɗa ruwa me zafi kaɗan cikin tube ta sake wani wankan,ta fito ɗaure da towel wani ƙarami na kanta tana tsane ruwan daya jiƙe dogon gashinta, handryer ta jona tana busar da gashin,har lokacin zuciyanta na cikin wani hali idanunta har sun tasa kaɗan sabida kukan dataa sha,koda tagama saita sake shiryawa cikin riga da skat na atamfa,kwalli kawai tasa ta murza powder kaɗan,ta ɗauki wayanta da pose ɗinta ta fice,zuciyantace kawai taba ta gara taje gidan Dadah,inba hakaba zatai ta kwanciyane aɗaki tunani na lulluɓe zuciyanta,hakan kuma zaisa Momy ganin bata yi na’am da gudan jininsu ba,wanda bata fatan hakan ta faru dole ta aro duk wata jarumta wajen ganin bata bar wata kafa da zasu fahimci halin da zuciyanta ke ciki ba.Koda ta fito Nafees da Amal ta samu suna kallo a falo ,fitowanta yasa duk suka zuba mata ido ganinta yafe da veil ga pose ahannunta,ita kuma saita saki murmushi tana rigasu faɗin.
“Hey! wannan kallo haka gidan Dadah xani inda me zuwa saita taho muje,ammafa ni motsa jini zanyi aƙafa zan zagaya basai na wahal da Bilya ba.”
Amal ce tasaki dariya cikeda jin daɗin yadda Nailah ta saki ranta,ta furta.” No ni babu inda zani ina gida yau inada baƙuwa Fiddoh zata zo anjima.”
Nafeesa itama tayi saurin faɗin.” Ainima ina gida ya Amal bazan fita ko inaba ƴan mata amotsa jiki lafiya kice muna gaida ƴar tsohuwa.”
Nafeesa taƙare maganan tana sakin dariya,Nailah ta zabga mata harara tana faɗin.”Ai shikenan ni bari inje dama ta aiko ya Hussain tana cigiyata “
Tayi maganan tana nufan hanyan ɗakin Momy don yimata sallama,baƙaramin daɗi ko Momy taji ba ganin yadda Nailah ta saki ranta har zata fita unguwa,ta dubeta tana nuna mata gefen side drawer take faɗin.
“Maza jeki duba ledan can akwai wasu turaruka da aka kawomin su jiya,zaɓar mata masu sanyin qamshi guda biyu kisaka aleda kikai mata,kije kitchen ki ɗauki bowl me murfi akwai dambun kifi da Hajiya Habiba ta aikomin ki ɗibar mata,ku ma duk me so saita ɗiba.”
“To Momy godia muke bari inyi yadda kikace ɗin saina dawo.”
Cewan Nailah da tuni harta saka turaren biyu cikin leda,ta fice don zuwa ɗibar dambun kifin daga can saita wuce abinta.
Cikin takunta me cikeda nutsuwa take takowa,har zuwa haraban wawakeken compound ɗin gidan,hannunta riƙeda leda me kyau da ƙwari data saka bowl me murfi me kyau data zuba dambun aciki,sai ƙaramar jaka data canzo amemakon pose don saka ledan turaren ciki,harta kusa isa gate ta jiyo muryan Dady na kiranta,wanda fitowansa kenan daga part ɗinsa shida ya Anwar ta ƙofar waje,ya hangota tana tafiya Anwar na sanye cikin ƙananun kaya da sukai masifan amsarsa,gashin nan dake cin kuɗi yayi kwance luff,shigan yai masa mugun kyau idan ka dubesa dole ka ƙara domin guy ɗin akwai aji da kwarjini,ga baiwan kyau da cikar kamala da Allah yai masa,dawowa da baya Nailah tayi don zuwa wajen Dady,sai kuma lokacin data kusa isa garesu ne ta gane ashe shida ya Anwar ne,hakan yasa kirjinta bugawa da ƙarfi tana jin matsanancin faɗuwan gaba,shima gogan tunda ta doso yai mata kallo ɗaya ya ɗauke kai yana sake haɗe giran sama data ƙasa,harta ƙariso tareda russunawa tana faɗin.”Dady gani.”
“Malama Nailah sai ina ,zaki fita aƙafa ina Bilyan?”
Nailah ta saki murmushi tana faɗin.” Yananan Dady aiba wata unguwa me nisa bace gidan Dadah zani dama,shine nakeso naɗan motsa jini na tafi aƙafa tunda babu nisa sosai.”
Taƙare maganan tana satan kallon Doctor AA daya sake ɗinke face,sai faman shafa waya yake tamkar hankalinsa baya kansu Dadyn,sai dai tsaf yake sauraren muryan Nailah me shegen zaƙi dake fita very cool,muryan Dady ya jiyo dake cema Nailah.
“A’a baza’ai hakaba ga yayanku nan maza ya saukeki saiya wuce inda zashi,agaida Dadan saina shigo nima.”
Nailah ta amsa da .” To Dady zataji saika shigo ɗin.”
Dady ya maida dubansa ga Anwar yana faɗin.”Doctor kuje ka sauke ƙanwar taka saika wuce ko.”
Tamkar Anwar zai kwarma ihu ya amsa da.” To Dady.”
Ita dai Nailah tuni tayi gaba zuwa wajen data hango haɗaɗɗiyar motarsa afake,wacce ko amafarki bata taɓa sawa ranta xata shiga motar saba,koda ya iso direct mazaunin driver ya shiga batareda yace mata komi ba,yayi reverse yana tsayawa don bata daman shiga,hakan yasa Nailah isa ta buɗe front seat ta shige tareda maida murfin motan ta rufe,kaman jira yake ya fisgi motan aguje,Baba megadi ya buɗe musu gate ɗin yana masa asauka lafiya,hannu kawai ya ɗagawa Baban suka fice,ita dai Nailah kanta aƙasa yake koda wasa batai gigin duban side ɗinsa ba har yaja burki a bakin madaidaicin gate ɗin shiga gidan Dadah,buɗe murfin motan tayi ta zura ƙafafunta don ficewa,kaman wacce aka mintsina tayi saurin juyowa ta dubi face ɗinsa,kafin bakinta ya buɗe harshenta ya furta.” Nagode.”
Wani uban tsaki yaja yana jifanta da wani mugun kallon da yasata babu shiri ta ƙarisa ficewa daga motar,tana tura ƙofar gate ɗin gidan Dadah ta shige zuciyanta na bugawa,sallama ta farayi tun daga shiga cikin gidan can ta jiyo muryan Dadah daga ɗaki tana amsa sallaman nata,Nailah ta isa ƙofar shiga falon Dadah tana sake wani sallaman,muryan Dadah dana sabuwa me aikin Dadah ne suka amsa sallaman nata,ta shiga tana me gaida sabuwa kafin ta ƙarisa gaban Dadah dake zaune ƙasan carfet tana gaidata tareda faɗin.
“To Dadah ance kina cigiyata gani nazo me aka tanadar min?”
“Fura da nono sai kwaɗan zogale gashi can a kitchen shina tanadarwa me sunan ƴan gayu.”
Cewan Dadah idanunta akan Nailah data saki dariya tana dire ledan hannunta agaban Dadah tana faɗin.” Wow Dadah shiyasa nake jinki araina yaushe rabona da fura,aiko zansha yanzuma kuwa ga wannan inji Momy tace in kawo miki.”
Taƙare maganan tana miƙewa tareda aje veil ɗinta ta nufi hanyan kitchen ɗin Dadah,tuni sabuwa ta koma side ɗinta inda aka ware mata ɗaki guda me ɗauke da toilet aciki,da komi da komi hatta kayan kallo ansa mata,Dadah ce tabi bayan Nailah da kallo ƙaunar yarinyan na sake zama acikin zuciyanta,tana me addu’a aranta Allah sa burin ɗan nata da nagartacciyan matansa ya cika na haɗa Anwar da Nailah aure,Nailah data ciko ƙaramin cup da lafiyayyan fura da nono data tsaya ta zabgama uban madara da zuma kafin ta fito,ta isa kusada Dadah tana juya furan da spoon tana sha ahankali,komi nata cikin nutsuwa take yinsa,tana sha suna hiransu da Dadah cikeda barkwanci,duk wanda zai gansu alokacin zaiyi rantsuwa cewa dama can jika da kakace jini ɗaya,jakanta ta janyo tana fiddo turaren da Momy ta bayar ta miƙawa Dadah tana faɗin.” Dadah ƴar gatan Momy kinga bayan dambun kifi har turare ta bayar akawo miki kishafa kita qamshi.”
Taƙare maganan tana dariya Dadah da farin ciki da ƙaunar surukan tata ke sake lulluɓeta ta buɗe bowl ɗin dambun tana faɗin.”Faɗi ki ƙara ƴarnan ni ƴar gatan Fateema ce Allah dai yai mata albarka ya shirya mata zuriya,ya kauda idon magauta akansu itada Amadu.”
“Ameen Dadah kema Allah yaja kwana da ƙarin ƙoshin lafiya.”
Cewan Nailah kenan Dadah ta fara cin dambunta tana santi Nailah na mata dariya,sunanan zaune suna hira har akai sallan azuhur suka tashi suka gabatar,bayan sun idar ne Sabuwa ta shiga jera warmers ɗin abincin data gama,domin aikinta dama yima Dadah girki da gyaran ɗaki sai almajiri dake sharan tsakar gida da wanke wanke,tuwan shinkafane sabuwa tayi miyan taushe lafiyayye da yaji naman kaza da gyaɗar miya.
Sam Nailah ba cimanta bane hakan yasa ta zubo kwaɗan zogalen da Dadah tai mata albishir tun farko,sallaman ya Usman yasa Nailah saurin aje plate ɗin hannunta tana faɗin.” Oyoyo ya Usman saukan yaushe.”
Fuskansa ɗauke da murmushi yake ƙarisowa cikin falon Dadah yana faɗin.”Duka awana biyu da shigowa garin kenan Nailah.”
Dadah ta dubeshi yana zama kusa da ita take faɗin.”Ɗan gombe kenan barka da dawowa.”
“Yauwa Dadah barka da hutawa da fatan mun sameku lafiya.”
“Lafiya Usmanu ya aikin naku to Allah ya cigaba da tsare manaku yai muku albarka.”
Cewan Dadah su Nailah suka haɗa baki suna amsawa da.”Ameen Dadah.”
Ya dubi Nailah yana faɗin.”Me sunan ƴan gayu azubo min tuwan shi zanci Momy rice sukayi da funkaso ni kuma kinsan nafi son tuwan rice ɗin akan waɗancan.”
Nailah ta saki murmushi tana miƙewa don cika umurninsa,shi kuma suka shiga hira da Dadah yana bata labarin gombe,don bai jima da fara aiki da state house na gombe ba.
Bayan la’asar sai ga Dady yazo shima gidan Dadan,sai Nailah ta gudu bedroom ɗin Dadah tabarsu anan falon Dadan,ya jima sosai kafin ya tafi tareda ya Usman,Dady ya zayyanewa Dadah shawaran daya yankene na aurar dasu Amal ɗin gaba ɗaya tareda shaida mata zancen Nailah da Anwar,maganan da yai matuƙar ba ya Usman mamaki yana ji aransa inama shi Momy ta zaɓawa Nailah ba yayan nasu ba,domin ya jima yana ganin tsana da ƙyaman yaran a idanun Anwar ɗin,expecialy Nailah da yafi ɗaurewa face da hantararta mistake kaɗan zatayi ya fara sauke masifa yana mata tsawa,don ma shiɗin ba mazauni bane sai weekend kawai yake shigowa zarian.Har suka koma gida da Dady Usman na juya zancen aransa tareda tausayin Nailah yadda zata rayu da Anwar ɗin alhalin shi Hudah ce zaɓinsa.
Acan gidan Dadah kuwa koda wasa bata nunawa Nailah cewa Dady yai mata zancen aurensu ba,suka cigaba da hiransu ƙarfe biyar Momy ta turo Bilya ya dawo da Nailah gida.Dadah dai sai faman sa mata albarka take har Nailah ta rasa dalilin shigan Dadah cikin farin ciki lokaci guda haka.Haka suka isa gida Nailah na addu’an Allah yasa yau kada ya Anwar yazo yin dinner.
Doctor Anwar Mainasara kuwa bayan ya aje Nailah kai tsaye zango ya nufa,gidansu gimbiyar tasa Hudah tuni ya jima da sanar da ita zuwan nasa,wanda ya zama ƙa’ida baya taɓa barin gari basuyi sallama sunday ba domin sammako yake zuwa Abuja safiyan monday,horn yayi megadi ya buɗe ƙaton gate ɗin gidan tsohon kwamishina Alhaji Abubakar Sabo,saida A.A Mainasara ya gyara parking tareda kashe motar gaba ɗaya,kafin ya zaro wayansa yana dialling number ɗin Hudah da yayi saving da MY QUEEN,bugu biyu ta ɗaga cikeda yauƙi ya sanar mata gashi a parking lot,banji me tace dashi ba nadaiga ya ɓalle murfin motan ya fito tareda maidawa ya rufe ya jingina jikinsa jikin motan yana tsurawa hanyan ƙofar da nake kyautata zaton tanan Hudan xata ɓullo.
Daga cikin gidan su Hudah kuwa wata siririyan matashiyan budurwa na hango,fara tas wacce sam Allah baiyi zubin halitta agurinta ba,single take bata da wani cikakken ƙira irinta mata,inka ɗauke cikan kirji da take dashi kaɗan shima bamai yawa canba,amma bayan nan shirune ashafe yake lam,tana da kyawun fuska ba ƙarya dogon hanci gareta zar da manyan idanu,gashin giranta baƙi cinkis da gashi shiya sake qawata kyawun fuskanta.
Sanye take cikin matsatsiyar doguwar riga daya fidda suranta,kanta da yasha kitson calaba wanda aka ƙara tsayinsa da brazil yakai har tsakiyanta bayanta,shita ɗaure da band ta kafa ɗaurin ture kaga tsiya da ɗankwalin kayan,kusada ita babbar macece da kallo ɗaya zakai mata kasan mahaifiyantace sabida tsaban kamanni da suke da juna, ke miƙama Hudah wani ƙaramin kwalban turare tana faɗin.
“Maza mutstsika turaren nan ki shafa ajikin wuyanki da bayan kunnanki,saiki shafe sauran ajikinki yadda dakin doshe shi qamshin zai fara isa kafofin hancinsa,kafin tasirin turaren yayi aiki a kwakwalwansa,sannan ina jaddada miki koda wasa idan ya ɗakko miki maganan auranku ku biyu kada ki nuna masa komi,ki kwantar dakai ki nuna masa kin amince yayi biyayya ga uwarsa domin malam Nuhu ya tabbatar mana da cewa aurefa babu fashi sai anyisa,kedai kawai ki lallaɓashi kice koda lokacin yazo to afara ɗaura naki auren kafin na waccen karfan,maza jeki ki buɗe masa sitting room kada ya cika tsayuwa.”
Taƙare maganan idanunta akan Hudan da take jin sonta tamkar tayi hauka,don ita ƙadaice ta mallaka ƴa mace acikin jerin ƴaƴa biyar da Allah ya bata,shiyasa taci babban buri akan tilon ƴar nata da sam bata samu isasshiyar tarbiyaba…….✍
NAILAH is for sale idan kina buƙata just 300 zaki biya,0504192664 Aisha Ibrahim Ɗansabo GTbank,wannan shine account ɗin da zaki tura kuɗin,shaidan biyanki tanan line ɗin 08167768704.
Ayshat Ɗansabo ce ✍
DANNA DOMIN KARANTA CI GABA