KUNDIN KADDARATA CHAPTER 19 BY HUGUMA

Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa’iza ba domin ba halinsa bane,amma halayyar fa’iza har ta kai haka?. "Ina naki abincin?" Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi

“Ya d’aki”
“Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a leda ki saka a shara a zubar,shiga kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai” ya fada yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta fice don aiwatar da abinda ya umarceta.


Cikin kwanakin ta dage sosai da addu'ar neman tsari,ta san tabbas shartin mutum girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa'iza,ta fahimci irinsu matan da suka dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zash iya aikata komai saboda kishi,sosai take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar fa'izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa'izan zata shekara tana takalar tashin hankali bata bi ta kanta,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.


Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar sun makara basu tashi da wuri ba

“Ya mukhtar,kamar kakarin amai nake ji fa a tsakar gida” shi din ma taji amma sam bai da muradin fita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
“Eh nima naji” yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
“Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa’iza ce fa” shiru ya sake mata ganin hakan ya sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da sauraran kakarin wanda yake fita tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsa ya kashingida. Zuciyar musulunci ya sanyata ta kasa daurewa,sai ta miqe ta fidda hijabin jikinga ta nufi qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata

“Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi fita a dubata ba,bamu san meke damunta ba” kai ya girgiza
“Dawo tausa nake so kimin”
“Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar”
“Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan” ya fada yana maida kansa ya kwantar kan pillow,sai jikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka ta juyo a sanyaye tahaye gadon. A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana dariya qasa qasa

“Raguwa kawai sarkin kuka” ya fada yana lakuce mata hanci,dariya ta saki ya shiga mata cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma’aurata wanda hakan shi ya hanasu fitowa da wuri. Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga can bakin qofar dakin fa'izan suka ganta zaune dirshan a qasa,ta wani wargaje can qafa can qafa tana numfashi da qyar,da sauri sumayya ta qarasa inda take tana fadin

“Hasbunallahu lafiya fa’iza?”
“Bani da lafiya” ta fada qasa qasa da qyar,ta daga kai ta kalli mukhtar da bai qaraso gun ba,yana tsaye abunsa bakin qofar dakin sumayyan yana daura agogo
“Yaya mukhtar,ko asibiti zamu?” Baice komai ba sai hannunsa da ya sanya cikin aljihun wandonsa ya zaro naira dubu biyu ya miqa mata
“Gashi sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya” ya sanya kansa soro ya tada machine dinsa ya fice. Tana jin rufe qofar gidan nashi ta miqe tamkar ba itace hajaran majaran ba,duk da yanayin jikinta ya nuna bata da qwari sosai,ta sakarwa sumayya harara sannan ta wafce kudin dake hannunta

“Babu inda zaki rakani munafuka” ta fada tana shigewa dakinta,kada kai sumayya tayi cikin zuciyarta tana fadin
“Allah ka shirya,wato hali zanan dutse”. Tana daki tana shafa mai bayan ta kammala wanka ta jiyo fitar fa'izan. Suna zaune zasu ci abincin dare bayan ya kammala komai,tana gabansa tayi kyau cikin kwalliyar lace ja mai adon baqi tana zuba masa abincin data shirya musamman saboda shi fa'iza tayi sallama ta shigo dakin fuskarta qunshe da murmushi hannubta riqe da farar takarda,daya daga cikin kujerun dakin sumayyan ta samu ta zauna,fuskarsa a hade ya dubeta

” daga ina kike takwas na dare?”sai ta rausayar da ido
“Haba mana muntari,ka tsaya kaji ji da nazo maka da daddadan labari”
“Ba wannan ba ki fara amsa min tambayar da na miki tukunna”
“Kash,labarin da zan baka yanzun duka yafi wannan muhimmanci,amma tunda ka nace sai kaji to daga asibiti jikina ya rikice sai na wuce gida na kwanta acan,sai da magariba na danji dama dama” shiru yayi ya soma cin abincinsa,ganin haka ya sanya tace
“Ka godewa Allah muntari,Allah ya kusa cika maka burinka da ka dade kana fata,ka kusa zama baba,an auna ni ina da juna biyu har na wata biyu”. Qwarewa yayi da lomar abincin da ya kai bakinsa,sai ya soma tari babu qaqqautawa,cikin hanzari sumayya ta miqa masa ruwan tana jujjuya maganar cikin ranta,indai hakan gaskiya ne to ya tabbata ITACE BATA HAIHUWA?. Sai da ya sha ruwan sosai sannan ya ajjiye cup din,hannu kawai ya miqawa fa'iza wadda keta doka murmushi tana tunanin farinciki ya sanya mukhtar qwarewa,tabbas burinta ya kusa cika,zaman sumayya cikin gidan ya kusa zuwa qarshe,ta kusa raba mukhtar da kowa sai ita. Takardar ta miqa masa don ta fahimci ita yaje son gani,ya bude ta sosai ya shiga nazarinta daga farko har qarshe,gashinan rubuce a jiki,cikine dan sati takwas,amma sati takwas fa suka rubuta,har ya bude bakinsa zaiyi magana sai kuma ya fasa,a yanzun ba muhallin yin maganar bane akwai muhallin yinta,saboda haka ya nannade takardar ya cusa cikin aljihunsa ya janyo abincinsa yaci gaba da ci. Dukkaninsu sumayyan da fa'iza sai suka zuba masa ido cikin mamakin ganin bai ce komai ba,fa'izan ce cikin zaquwa da son jin abinda zaya fadi din tace

” ya baka ce komai ba muntari,Allah ya yi maka kyautar da ka dade kana jira amma banga ka nuna komai ko kace min komai ba”kansa ya daga ya dubeta
“Naji ai kuma na gani,zan kuma magantun amma lokacin yin maganar ne baiyi ba,jeki sai da safe Allah ya inganta ko?” Jiki a sanyaye ta miqe ranta cike fal da mamaki,tayi zaton zai dauketa ne suyi rawa suyi juyin murna,ta yadawa sumayya habaici yadda taga dama,amma duk da hakan ai lokaci na zuwa. A sanyaye sumayya ta dubeshi bayan fitar fa'izan

“Amma yaya mukhtar kamar bai dace ba abinda kayin,sai nake ganin murna ya kamata ka nuna irin wadda baka taba nunawa ba,d’a fa da kuje muradi shi Allah zai baka?” Kansa ya daga yana dubanta fuskarsa qunshe da murmushi,sai kuma taga ya qyalqyale da dariya
“Yanzu my sumy koda haka ne ya cancanci nayi murnar hada iri da waccar matar?,fa’iza fa? Wadda ni da ke duka munsan halinta,bani da muradin samun zuriyya da kowacce mace a duniya sai ke,kece nakeso ki zamo ta farko da kika samamin zuria,ki bar maganar nan don Allah bana so in sake jin bakinki game da ita indai na isa da ke”
“Insha Allahu” ta fada zuciyarta na karyewa,ina ma inama,ina ma tana da qarfin yaqi da QADDARARTA?,ina ma tana da ikon baiwa kanta haihuwa?,ina ma ace zata iya samarwa da mukhtar cikon farincikinsa,duk da bata da wannan ikon amma bata jin dai dai da daqiqa daya bakinta zai rufu ko ya gajiya wajen roqon mai badawar da ya albarkaceta ya azurta ta ya kuma bata haihuwa saboda karamci tausayi da kuma jin qansa,sai tayi qas da kai hawaye na diga,da sauri ya daga kanta suka hada idani,da murmushi yake dubanta gami da kada kai
“Bana so sumayya kin sani,ko ya kike sumayya haka nake sonki,sonki so ne na fisabilillahi cikin zuciyata ba don wani abu da kike da shi ko kika rasa ba” bata buqatar itama bata ransa saboda haka ta saki murmushi tasanya hannunta da kanta ta goge hawayen. Sosai fa'iza ta soma tsiro da tsurfa kala kala,gobe tace wannan jibi tace wancan,da fari sumayya na qoqarim yo mata mukhtar na fuskantar haka yace bai yarda ta sake hidimta mata kan komai ba,idan tana so ta tashi ta girka da kanta,nan ma ya fuskanci an shiga babin barna da almubazzaranci shima ya soke yace taci duk abinda ka dafa ko ta haqura,sosai abun ya qona ranta,duk yadda taso samu yaqi samuwa. Sai aka tsiro tsirfar zuwa dubiya kuma,daga bangare mukhtar zuwa na fa'izan,saidai ko da wasa bata ga qafar yaya yahansu ko yaranta ba,saidai fadima da ta zo,ita din ma sama sama fa'izan ta mata sannan ta tattarata ta watsar,sai data gaji da zama ta ja qafafunta ta tafi,gidan sai ya zama kamar wani gidan biki,wuni sumayya take tana karbar habaice habaice daga bakunan maziyartan gidan kala daban daban,bata taba jin tsananin so da buqatuwar haihuwa ba irin na wannan karon,sai ta zama wata mai raguwar zuciya,mikin data jima tana dannewa cikin zuciyarta na rashin magaji ya zame mata sabo fil,duk sanda suka goranta mata sai ta kasa daurewa har sai ta zub da qwalla ta rage radadin da take ji cikin zuciyarta. Cikin hakan mukhtar ya fuskanci ta fara rama,juyin duniya yayi tambaya tace masa lafiya babu abinda ke damunta,tilashinsa ya haqura saidai ya zuba ido sosai bisa yadda lamuran gidan ke gudana. A irin haka katsaham ya dawo gida ranar qarfe uku da minti talatin da takwas ana shirye shiryen kiran sallar la'asar,wasu masallatan ma har sun fara kiran,a lokacin tana qofar kitchen zaune tana hada girkin dare,yayin da dakin fa'iza ke qunshe da baqin da qafarsu bata daukewa zuwa gidan da sunan dubiya,suci na rana wani lokaci idan an kammala na dare ma suci sannan su tafi,musamman ranar girkin fa'izan wanda taso qwarai a dauke mata girki mukhtar yace bata isa ba. Yazo kuwa a gaba dai dai sanda suke jeranto gorin nasu,bai kula kowa ba sai da suka kammala duk abinda suka zo da shi suka karkade qafafunsu,kowacce tazo fita sai tayi turus ganin mai gidan zaune tsakar gida kusa da sumayyan yana tayata aikin kitchen duk da babu wanda yacewa kowa komai cikinsu,sai su kama borin kunya kana su fice sumi sumi. Sai da suka gama ficewa tsaf sannan yayi kirab fa'izan ya kafa mata sharudai,duk randa ya sake ganin qafar wani ya shigo har cikin gidansa ya ciwa matarsa mutunci to sawunta a likkafa ta hada kayanta ta bisu tum gabanin ya dawo gidan,wannan hargagi shi ya sake janyo tsana da jin zafin sumayya mai yawa a zukatan mutane da yawa masu qinta musamman uwar tafiyar fa'izan,ta kuma sake cin alwashi mai yawa akan sumayya,wannan kuma shi ya kawo taqaitar zirga zirgar 'yan bani na iya din

RANA DUBU TA BARAWO Tunda ta tashi yau kanta ke ciwo,don haka a daki ta kusa yini,koda yaranta suka zo ma gida ta korasu don bata son hayaniya,naana ce kawai ta zauna kasancewar duka ta fisu nutsuwa. Har tayi baccin qailula ta farka yarinyar na gefanta zaune,ta miqe tana salati duk da cewar kan nata ya rage ciwo amma bai sauka ba duka,ta cire hijabin data kwanta da shi sabida zazzabin da ta fara ji ya fita tsakar gida ta dauro alwala,cikin takaici taje duban tsakar gidan yadfa yayi kaca kaca,girkin fa'iza ne amma bata damu ta gyara ba haka al'adarta take,matuqar sumayyan bata gyara ba to saidai gidan yayi ta zama haka,to ita din ma bata da qyashi son jiki ko ganin ido batq damuwa wai don bata gyara ba yin abinta take,hatta da wankin toilet zata iya rantsewa bata taba ganin fa'izan tayi ba tunda ta shigo gidan. Tana shiga d'aki ta sanya naana taje ta share mata tsakar gidan ita kuma ta tayar da sallah. Kafin ta kammala sallar nanan ta gama kasancewarta yarinya mai kazar kazar da son aiki shi yasa sumayyan ke sonta,ta dawo gefanta ta zauna tana kallon sumayyan har ta idar. Tana shafa addu'a ga mamakinta fa'iza ta shigo d'akin dauke da cooler dinta ta dire tayi ficewarta,tana nannade abun sallar sai ta lura naana nata kallonta tana kuma satar kallon kwanon abincin,tasan akwai magana a bakinta ne ta kasa fadi,kuma hakan yana da nasaba da hanasu dauko magana daga wani guri su gaya mata. Har ta koma saman kujera ta kwanta don bata da sha'awar cin komai taga yari yar naci gaba da kallonta idan ta lura da kyau ma kamar qwalla ce a idonta,a hankali ta miqe ta zauna tayi kiranta,yarinyar ta iso gabanta ta zauna

“Me ya faru?me ya sameki naga kamar zakiyi kuka,ko yunwa kike ji?” Sai ta girgiza kai
“To mene ne gaya min” cikin raunin murya kamar kukan zai qwace mata tace
“Anty sumayya don Allah kada kici abincin nan” sai sumayyan ta hade rai tana dubanta
“Me yasa?”
“Anty,naga amarya ta bude leda sanda kika sakami yin shara tana ta leqe sannan ta koma kitchen ta bude flask din ta debo wani yalon abu ta barbada a ciki ta juya ta rufe ta wanke hannunta” sosai taji gabanta ya fadi,saidai bata son ta bawa yaran damar da zasu dinga labe ko qoqarin dauko gulmar fa’izan suna kawo mata,saboda haka ta sake hade rai
“Ke me yasa kika labe kina kallonta?” Da sauri ta girgiza kai
“Allah ba labewa nayi ba,tsintsiyar ce ta kunce a bakin kitchen din sai na tsaya daureta shine fa na gani” shiru tayi tana jinjina zancan cikin zuciyarta,sam bata son ta baiwa kanta qofar da zata zargi fa’iza kan abinda idanunta basu gane mata ba,saboda ko ubangiji ya fadi cewa HAQIQA WANI SASHI NA ZATO ZUNUBI NE,kai kawai ta kada bayan ta koma ta kwanta
“Shikenan,bazan ci ba,amma kada ki gayawa kowa abinda kika gani kinji nana?”
“To anty” ta fada tana kada kai
“Zan tafi anty lokacin islamiyya yayi” ta amsa kana ta laluba gefanta ta dauko alawa guda uku ‘yan naura biyar biyar da takan ajjiye saboda su ta miqa mata,bata fiya son basu kudi ba don kada su saba da su ta bata ma iyayensu tarbiyyar yaransu,don ba kowa keson ka yiwa yaronsa kyautar kudi ba sabida gudun kada su saba da su,randa kuma basu samu ba su nema kota halin qaqa,Allah ya kiyaye. Sosai ta zurfafa cikin tunanin maganar da naanan ta gaya mata,sai ta kauda tunanin daga ranta ta shiga addu'a cikin zuciyarta,ALLAHUMMAK FINIHIM BIMA SHI'ITA ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta,tana fata koma mene Allah ya mata maganinsa ya sanya tsarinsa a gareta har wani baccin ya sake daukarta. Koda ya dawo yau bai samu yin wanka ba sai bayan yayi sallar magariba,yasan cewa ba samun ruwan wankan nasa zaiyi ba saidai ya debawa kansa,hakan ne ya sanya yana shigowa ya tara ya shiga bandakin,har ya shiga ya manta da towel dinsa hakan ya sanyashi fitowa. Da hanzarinsa ya dawo zai shige,saidai wani abu da ya fisgi zuciyarsa ya sanya shi dawowa da baya,abinda ya faru watannin baya yake ji a jikinsa tamkar zai sake maimaita kansa ne a yau,a hankali ya zarw slippers dinsa ya taka zuwa qofar kitchen din,idanunsa suka sauka kan cooler din sumayya dake bude gaban fa'iza wadda ke dauke da dafa dukan shinkafa qarshen qurewar girkin fa'iza kenan. Cike da hanzari fata da buri take barbada garin cikin abincin,don ta fuskanci cewa sam sumayya ko bude kwanon abinci bata yi ba,amma wannan karo taci alwashi kota halin qaqa sai ta sanya ta taci ko loma daya ce kai tama yankewa kanta ko dura ce sai tayi mata. Tana karkade hannunta cikin nishadi taji caraf an riqe hannunta,tun kafin ta fahimci wake da alhakin riqe mata hannu gabanta yayi wata mummunar faduwa,a hankali tamkar wadda ta warke daga cutar laka ta daga kai suka hada idanu da mukhtar,wani matsanancin tsoro ya shigeta wanda kadan ya rage ta saki fitsari cikin wandonta sakamakon yadda taga idanunsa sun sauya kala cikin sakannin da basu wuce biyar ba. Wani lafiyayyen mari ya yarfa mata wanda kafin ta ankare da a wanne hali taje ciki ya sake bin fuskarta da wani,hakan ne ya tilasta mata sakin wata gigitacciyar qara saboda ji taje tamkar fuskarta na shirin tsagewa ne,wannan shi yayi silar zaburar sumayya ta miqe ta fito a razane tana tsammanin ko gobara ce ta kama gidan nasu tunda ta bar fa'iza ne cikin kitchen. Fitowarta yayi dai dai da wurgo fa'iza da mukhtar yayi zuwa filin tsakar gidan

“Subhanallahi” sumayya ta fada da qarfi tana nufar inda fa’iza take don ta d’agata
“Kika tabata sai mun samu mummunan sabanin da bamu taba samun makamancinsa ba ni da ke,sai nayi matuqar saba miki” taji mukhtar na ambata cikin wata kakkausar murya da bata taba zata yana da ita ba. Yadda ya sake nufo fa'iza gadan gadan ya tsoratasu baki daya,sumayya ta janye gefe jikinta na rawa,bakinta na ambatar duk wata addu'a da tazo bakinta tare da neman agajin Allah ya kawo sauqin kowacce iriyar masifa da zata faru yau a gidan,yayin da tsoron da fa'iza taji ya sanyata sakin ihun neman agaji domin tsantsar bala'in da zata fuskanta ya fito muraran cikin idanun mukhtar tun kafin ya kai ga aiwatar da shi a kanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *