ABBAS
CHAPTER 11
Suna fita ya fad’awa drivern sa inda yake so ya kai shi, koda suka je kuma basu tarar da kowa ba face mai gadi.
Zuwa yayi ya mi’kawa mai gadin hannu suka gaisa sannan ya tambaye shi inda ‘daliban suke take mai gadin ya sanar dashi.
Abbas godiya yayi masa tare da juyawa ya koma cikin mota driver yaja suka nufi wajen.
Da kwatance drivern ya gane wurin koda ya isa yayi parking a wurin Abbas kamar bazai fito ba kusan 10:mins kafin ya ‘daga hannu ya duba agogon dake hannunsa sai yayi maza ya fito daga motar.
Tsaye yake jingine ajikin motar yana ta ‘karewa ‘dai’dai kun mutanen dake wulgawa kamar me karantar wani abu tattare dasu.
Tafiya ya fara cikin ‘kasaita in ka ganshi zaka zaci daga wani gidan sarauta yafito, ahankali yake tafiya ya nufi hall ‘din daya fi tunanin nan ne ake programme d’in dan anan ya ga anfi taruwa.
Daf da zai shiga hall ‘din daga gefe ka’dan ya idonsa ya hango masa ita cikin gungun ‘dalibai sunata surutu ga dukkan alamu shirin yin pix suke yi ko kuma har sun ‘dauka domin dukkansu zagaye suke da photo grapher ne.
Tsayuwa yayi kamar andasa shi awurin shi bai shiga ba shi kuma be matsa daga inda yake tsayen ba.
Be san mai suke tattaunawa atsakaninsu ba shi dai kawai sai yaga ta fara dariya, yayinda da dariyar tata ta matu’kar birgesa, sosai ya tafi da yanayin tsari da kwalliyar da ta tsantsara ayau d’in.
Aransa sai yaji kamar tunda yake da ita be ta6a ganin kwalliyar sata amsheta irin wannan ba.
Yanda ya ‘kura mata idanu sai ajikinta taji tamkar ana kallonta, tana cikin dariyar sai ta ‘dan fara dube-duben gefen ta.
Garin dube-duben nata sai idanunta ya hango shi take kuwa idanunsu ya sar’ke cikin na juna, Abbas lumshe idaunsa yayi ita kuwa bata gane shi ba koka’dan saboda akwai ‘dan rata atsakanin su kuma bata ta6a zaton ganinsa awannan lokacin ba, hakan yasa kawai tayi masa kallon kamar tasanshi sai ta kauda kanta gefe da sauri.
Sai de kuma sam taji zuciyarta takasa nutsuwa da hakan sai ta ‘kara juyawa ta kallo wurin, wayam tagani babu kowa abin ya matu’kar bata mamaki hakan kuwa yasa tafara tafiya ahankali ta baro cikin mutanen.
Tsoro ta fara ji kardai ace ba mutun tagani ba yanzun, amma ace daga ganin mutun sai kuma tarashi.
Allah yasa dai mutun ne inbahaka ba ai nashiga uku!
Haka taketa nanatawa azuciyarta,yayinda tsoro yake ‘kara cika mata zuciya aduk wani step ‘dinta.
Caraf taji ancafko hannunta tabaya,wani firgita da tayi shi kanshi sai da yaji wani iri, tana shirin k’walla ihu sai yasake hannun nata dawuri ya rufe mata baki da hannun.
Bakinsa ya matsar daidai kunnanta ahankali yace mata ” bana son hauka ki juyo ki ganni I’m your b………..
Sai kuma yayi shiru ya ‘kirasawa, ido ta zazzaro waje dan tana jin amon muryarsa tagane shi, muyrasa ko acikin dubun mutame zata iya ware shi.
Story continues below

Bakintan daya rufe yasake mata, yana sakewa kuwa ta juyo da sauri ta fuskance shi, da ‘karfi tace ” Yah Abbas kaine dagaske”?!
Tsaye yake agabanta ya maida hannayensa duka cikin aljihun wandonsa ya ‘kurawa fuskarta idanu tamkar yau ne farkon ganinsa da ita.
Koda ta tambayeshin ma be ko nuna alamun yaji ta ba sai data ‘kara maimaitawa sannan ya ‘daga mata kai alamar ehh shi ‘dinne.
Take sai ‘yan shagwa6anta suka motsa mata ta ha’de rai ta tura baki gaba yanda tayin sai ya ‘kara mai data ‘yar ‘karamar yarinya.
Murmushi yayi aransa yace ” mai hali kenan”.
Azahiri kuma sai yace mata ” me kuma yafaru naga kin 6ata rai ohh aren’t u happy 2 see me?”.
Sai ta ‘daga kanta sama.
Waje ya fito da idanunsa tare da fa’din ” saboda me”?
“Bakai bane ka tafi ka manta dani?”
” ohh sorry sis who told that na manta dake?, Allah kullun kina raina kinji”
Idanunsa akanta yake maganar da dukkan kulawa amma sai ta’ki yarda tawani karya wuya irin ita bata yadda ba ‘dinnan.
” toh shikenan tunda yanzu nazo bashikenan ya wuche ba”?
Sai ta jijjiga kanta alamar “a’a”.
Daya rasa yadda zaiyi da ita sai ‘daga hannayensa duka biyu yakamo kumatun ta dashi, jijjiga kan yayi yana murmushi yace ” stubborn head ‘dinnan har yanzu yana nan ko?.
Yanda yayi ‘din ita kanta yabata dariya amma sai ta juya masa baya tana dariyar ‘kasa-‘kasa.
A’dan nesa dasu kad’an ta hango wata ‘kawarta dasuka fara ‘kawace lokacin da aka fara waec, ta yaba da hankali da nutsuwa irinna yarinyar shiyasa ma bata yi mata mugun hali ba irin yadda tajewa sauran ‘kawayenta.
Tana ganin yarinyar sai tafara tafiya da nufin ‘kiran ta taga yayanta.
Takunta biyu kafin tayi na uku taji Abbas ya ‘kira sunanta ” FATEEMA” cikin wannan lion voice ‘dinsan nan me ratsa mata zuciya.
Take ta tsaya cak tare da waiwayowa ta kalle shi, ahankali ya tako ya iso inda take tsayen, shima ya tsaya.
“Tafiya zakiyi ki barni anan?”
Da sauri ta jijjiga kanta.
” toh menene”?
ya sake tambayarta?.
Kasa magana tayi awannan lokacin domin irin kallon da yayan ke mata ya banbanta dana kullum, jikinta duk taji ya mutu sai kawai tayi ‘kasa da kanta.
Bata zata ba sai taji yasa hannunsa yakamo hannun ta nadama ya bu’de yasa ka mata wata takarda sannan ya maida hannun ya rufe mata.
Da ido tabi hannun nata da kallo yayinda ta matse hannun nata gam-gam ta ri’ke takardar da kyau dukda bata san ta menene ba amma tanaji ajikinta tamkar takardan nada wani kyakkyawan muhimmanci arayuwarta.
Sai daya sake mata hannun ya maida nashi ‘daya cikin aljihu yayinda ‘dayan ke sau’ke daga gefensa kafin yace mata ” zan tafi Fateemah inada aiki a office banida isheshen time yanzu “
Dasauri ta ‘daga kai takalleshi sai yayi murmushi yace ” sai munyi waya”.
Yana fa’dar hakan yajuya yakoma mota be ko sake waiyowa ya kalleta ba, yana shiga kuwa driver yaja kamar daman jira yakeyi ashigo.
Ita kuwa mamaki hanata motsawa yayi saboda data ganshin ko dawasa bata kawo cewa ze koma dawuri haka ba.
Har suka 6ace daga wurin bata sani ba, tana can tana tunani.
Lokacin da runanin ya tsaya kuma koda ta kalli inda taga yayin gani tayi babu kowa.
Dasauri ta ‘daga ‘kafa ta taho gudu gudu ko zata ganshi amma ina bata ga kowa ba illah ‘kuran wata ba’kar mota data hango awajen gate tana shirin fita.
” wai dagaske ne……yah Abbas …………kuma ka sake komawa”.?!
Kamar ta fasa ihu haka taji amma kuma bazata iya ba.
Tana tsaye bata bar wurin ba taji ana mata horn sai tajuya dasauri takalli wajen zatonta shine yadawo amma sai taga motar gidansu ne wannan ‘din.
Mummy ce ta bu’de motar tafito ta nufo ta dasauri domin yanda taga Teemahn abin ya ‘dan bata tsoro.
Mummy na isowa inda take kawai tafa’da jikinta tayi lamo, sai da mummy ta ‘dan bata 3mins tayi backin up kafin ta ‘dagota ta tsayar da ita agabanta sannan ta tambayeta ” me yafaru?.
” mummy Ya…..yah.. ne “
Tayi maganar tana nuna hanyan gate.
” wani yayan me kuma yafaru dashi?”
Mummyn tafa’da tare da jijjiga ta da ‘dan ‘karfi.
” mummy yah Abbas ne……yatafi…..
Tana gama fa’dan hakan sai ta fa’da jikin mummyn tayi shiru.
Mummy data fahimci ‘yartata sai kawai tabarta ayanda take ajikin nata taringa bubbuga bayanta har tasamu ta d’an dawo daidai kafin tasamu da ‘kyar ta lallesheta har se da taga ta warware sannan takama hannunta suka shiga ciki.
Tun daga lokacin Fateema bata ‘kara yin wani abu da kuzari ba yayinda mummy kuma take jin bada’di tare da tausayin ‘yartata.
Tana tsoron kar dai ace yarinyar nan soyayya ce takamata domin kallo ‘daya zaka mata ka fahimci badaidai take ba, inkuwa hakane ai ta shiga uku!, yaza tayi ta iya sada Fateemah da farin cikin ta, idan yazamana shi’din ba haka bane azuciyarsa?”.
Domin tasan it’s hardly ace mutun kaman Abbas yaso Fateemah, kai Allah ma ya sauwa’ke Alla ya kiyaye ya tsare mu da sharrin zuciya.”.( Ameen)
Atare suka koma gida koda aka tashi a wurin……ahankali Teemah ke tafiya tamkar mai tsoron taka ‘kasa mummy kuma na bayanta itama tana binta ahankali .
Jijjiga kai mummy tayi data ga Teemah ta nufi 6angaren da ‘dakinta yake daga shigowanta parlourn ko tsayawa bayiba ta wuce abinta.
Babu komai atare da ita sai mayafinta da kuma wannan takardan da Abbas ya bata, tun lokacin da yabatan har yanzu bata canja masa ri’ko ba bata kuma bu’de taga miye aciki ba.
Tana shiga ‘dakin ta tura ‘kofar ta datse da makulli sannan tacire head ‘din dake kanta tayi jifa dashi akan gadon tare da mayafin baki ‘daya tana niytan cire rigar ne taji hannunta da abu, da sauri ta bu’de hannun tare da kallon shi da wuri domin sai alokacin ta tuno da cewa Yah Abbas ne yabata takardar.
Amma saboda ri’kon ‘ karfi datayiwa takardan ga kuma gumin hannunta da yake gimtse tsawon lokaci, su suka had’u suka narkar da takardan a hannunta.
Da6as ta zauna abakin gado idanunta nakan hannun nata koda tayi ‘ko’karin raba takardar da hannunta sai taga ya ‘kara yagewa.
Duk iya ‘ko’karinta naganin ta fahimci abinda takardar ke ‘dauke dashi takasa saboda daidai inda akayi rubun daidai wurin ne yafi samun matsala.
Dolenta ta tattara ta cire da me ‘dan girma da wanda
ya raki6e ahannun nata ta ajiyesu acikin side drawernta.
Sannan tacire doguwar rigar dake jikinta yarage daga ita sai pant, underwear da bra, ahakan takoma takwanta rigingine akan gadonta.
Ita kanta bata mecece damuwarta ba, haka kawai sai take jin ta wata iri, tamkar bata da ishashshen lafiya.
Nocking ‘din ‘kofa taji anfara yi kawai sai ta mi’ke ta nufi bayi batare da ko cire ragowar kayan dake jikinta ba, towel ma ahannu tashiga dashi bayan ta jashi akan ‘kofar bayin.
Ba ita fito a bayin ba sai kusan 5:00 hakan ma dalilin tunowa da sallar la’asar ‘din da batayi bane shiyasa tafito dasauri.
Tana fitowa kuwa idanunta suka sau’ka akan wannan kwalin da Abbas ya ajiye ma da tun shigowanta bata lura dashi ba sai yanzun.
Sallar dake gabanta ne ka’dai ya dameta adai dai wannan lokacin, dan haka kallon arziki ma kwalin be samu ta nufi wurin kayayyakinta ta ‘dauko wanda take son sakawa ta sakashi sannan ta shimfi’da dadduma tare da zunbula hijab ta tada sallahnta.
Koda ta idar bata bi takan kwalin ba har yanzu, kwanciyarta kawai tayi sai dai tana kwantawan mummy ta fa’do mata arai kawai sai ta mi’ke da hanzari tatafi wurin mummyn dan tasan dole zata damu idan tajita shiru.
Murmushin ‘karfin hali ta ‘ka’kalawa fuskarta yayinda ta tunkari inda mummyn take, koda mummy taganta ahakan kuwa sai ta ‘dan ji dama dama.
Murmushin tayi itama sannan tace
” yanzu kuwa nake so na aika aduba minke sai kuma gashi kin fito”!
Batayi magana ba sai da ta ‘karasa kusa da mummyn ta zauna kafin tace ” kaina ciwo mummy sosai”
tayi maganar tana wani yatsine fuska tare da dafa goshinta da hannunta ‘daya.
” haya niya ai, bari anemo miki magani kisha zaki d’anji daidai”.
Mummy tayi maganar tata cikin kulawa sai ta ‘kara da fad’in ” ki koma ‘daki ki kwanta ki ‘dan huta idan ankawo maganin sai kisha “.
Kai Teemah ta ‘daga alamar ” toh tare da mi’kewa tsaye ta kama hanyar ‘dakin nata.
Koda takoma ‘dakin kuwa kwanciya tasakeyi, so take tayi bacci amma sam sai taji takasa yin baccin ma fuskar Yayanta ka’dai ke yimata gizo tana ganin tamkar bashi ‘din bane dagaske tagani.
Wayarta da tun safe take ajiye a gefen mirror itace tayi ‘kara alaman shigowan sa’ko kuma ‘karan ne ya yanke mata tunanin yayantan datakeyi.
Kuma sai alokacin ma ta tuna da wayarta saboda tunda tafara shiri bata ‘kara bi takan wayar ba sai da tagama shiryawa ne ta ‘dauko wayar ahannunta ta kashe selfii bayan tafito da nufin tafiya wurin graduation d’in sai kuma ta ji ri’kon wayar ya dameta shine ta aiko aka ajiye mata ad’aki.
Toh shiyasa bata ‘kara bi takai ba sai kuma yanzun dataji wayar tayi ‘kara.
Ahankali ta tashi taje ga wayar bawai dan ‘karar sa’kon dataji ba ” a’a ” kawai jii tayi tana bu’katan ganin cikin wayar tata da ta ‘dau tsawon awanni batare da sun gana ba.
Dawowa tayi ta kwanta rigingine kanta nakan pillow yayin da ‘kafafun ta ke ajiye akan katifa ta wani had’esu guri d’aya.
Koda ta bu’de wayar sa’kon Mahmud tafara cin karo dashi a fuskan wayar ga dukkan alamu shine sa’kon da ya shigo ‘karshe ‘dan mintina ‘kalilan dasuka gabata .
Bud’e sa’kon tayi domin ganin me aka rubuta mata .
” wai nayi laifi ne bansani ba? “
Haka taga anrubuta
Sai tayi reply da ” haba laifin me zakayi kuma yayah”!
Daga nan tabar wurin messages ‘din ta koma taga tarin missed calls ‘din data tara duk daga yayanta Mahmud.
Story continues below

Data ta bud’e tashiga whattsap anan ma takuma cin karo da sa’konni da dama na groups dakuma na wasu contact d’inta ciki kuwa harda na Mahmud inda yake mata good wishes na gama makarantar ta, cikin sa’a kuwa sai taga yana online hakan yasa ta rubuta
” Yayah”
Tayi sending.
” Na’am, lil sis yau me nayi ne haka” ?
Tasan wannan tambayar duk bazai wuce akan tarin missed calls d’in data gani yayi mata bane hakan yasa ta bashi ha’kuri tare da yi masa bayanin rashin fita da wayar da bata yi ba ne shiyasa.
Tace sai yanzu ne dawowarta taga missd calls d’in kuma ciwon kai yasata agaba.
” eyyah sorry lil sis zakiji sau’ki kinji, ina kinsha Magani?”
” a’a mummy ta aika asiya min yanzu”
Yace
” wish u quick recovery owk”.
Itakuma ta rubuta masa ” Thanks”.
Sannan ta ‘kara rubuta ” Yayah “
Shikuma yace
” Na’am ‘kanwa”.!
” Yah Abbas yazo yau “!
” Haba ai be gaya min zaizo ba, amma gaskiya ya kyauta sosai , ki gaishe min dashi before muyi waya”.
” Ai ya riga yakoma ma “
” Ok ba matsala kinsan yanayin aikinsa ai sai a hankali”.
Bata ‘kara yin wata magana ba bacci ya ‘dauke ta da wayar akan cikin ta, koda mummy ta zo kawo mata maganin ma tun a’kofa data hango ta tana bacci sai ta juya kawai batare da ta shigo ba.
Shima Mahmud ‘din daya ga bata ‘kara magana ba sai ya ‘kyaleta azaton shi ko ciwon kan ne ya matsa mata, shiyasa ya barta yace ta huta .
*****
Washe gari bayan ta idar da sallahn asubah tayi addu’o’inta kamar yadda tasaba yi kullun, sai data karanto adduar safiya da maraice ta shafa sannan sai tasa hannu ta jawo wannan kwalin da nufin ganin abinda ke ciki.
Ledan dake jikin ta yage sannan tasa hannu ta bud’e cikin kwalin.
Hannu tasa ta ciro jakan dake sama aciki ta ajiye ta ‘kara ciro wani tagani.
Dogin riguna ne aciki masu kyaun gaske irin ‘yan italy ‘din nan kusan kala hud’u wanda idan ka saka ajikinka ako’ina kowa yasan sunsha kud’i ba ‘karya, sai takalma suma masu tsada guda biyu abinda kad’ai ke cikin kwalin kenan.
Ita kanta sun mata kyau sosai yayin da ‘daya daga cikinsu yafi ‘daukan hankalinta mai kalan coffee.
Tashi tayi ta tsaya sai ta d’aga rigar ajikin ta tana kallo kamar mai gwada tsayi nta da rigar.
Adaidai lokacin kuma sai ga mummy ta turo ‘kofarta tare da yin sallama wanda tazo ne da niyyan ji da ganin jikin Teemahn ko yaya ta kwana.
Kafin Teemah ta amsa sallamar sai mummy a firgice tace.
” ke wannan fah daga ina kika samu”.
“Anan na nagani nima ”
tafa’da tare da nuna gurbin da ta ga kwalin a ajiye.
Da mamaki mummyn takalleta tace
“anan kuma Fateemah”.
Sai Teemah ta d’aga kai alamar ” ehh”
” toh wah ya ajiye”?
Inji mummyn
Sai Teemah ta jefa mata tambaya inda tace ” mummy bake kika siya min bane”?.
Tayi maganar tana kallon fuskar mummyn nata.
Mummy bata kulata ba sai tasa hannu ta kar6i rigar dake hannun Teeman aranta take wassafa kyau da tsaruwar rigar, sannan kuma ga uban kud’i, idan batayi kuskure ba tace rigar tana kaiwa kusan Eighting thousand Naira (18000) akasuwa, zama tayi abakin gadon Teemahn tare da jawo kwalin ta firfito da ragowar kayan dake ciki.
” yah salaam ”
Tace aranta
” toh daga ina haka”
Ta sake tambayar kanta.
tace kuma ba daddyn Teemah bane ya kawo domin shi tasan yariga yabata gift ‘dinta tun lokacin daya dawo daga tafiya and she believe that matu’kar zaiyi abu toh sai ya sanar da ita.!
” toh wannan daga ina haka!”.?
Zuwa Teemah tayi ta zauna akusa da mummyn saboda yanayin dataga mummyn tashiga itama kuma sai alokacin tunani wanda ya kawo kayan ya shige ta musamman data ga duk hankalin mahaifiyarta ya tashi da ganin kayan ,sai ta dafa ta tace ” mummy wani abu ne?”.
” a ‘a ina tunanin ta inda kayan nan suka fito ne”!
Daga nan mummy n tasake yin shiru tana kallon Teemahn badan tariga tasan halin ‘yarta ta ba da sai tace tasan daga inda kayan suke tunda har acikin ‘dakinta aka gani, amma kuma ahalayyar Teemah babu ‘karya sai dai uban rashin ji da taurin kai sannan bata 6oye gaskiyarta ko kad’an ita.
_ABBAS_ shine ya fad’o ran mummy atake wanda hakan yasanya ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tare da hamdala acikin zuciyarta.
Domin da farko har kanta yafara caji hankalinta ya d’an soma tashi narashin sanin asalin takamamman inda kayan suka fito.
Amma tuno cewa Abbas yazo ayau d’in duk sai wad’ancan abubuwan suka kau, mussamman data tuno lokacin data ganshi ze shiga parlour hannunsa rik’e da wani abu wanda tun alokacin bata ‘kara tunowa da neman sanin miye abin ba, zaton ta jakar kayansa ne tagani ahannun nasa , sai kuma yanzu tafahimci menene abin tunda shi da be zo zama ba ina yaga ta shigowa da jaka har gida.
Murmushi tayi abayyane data tuno halayyar Abbas d’in shi sam baya son inzaiyi abu wani yasani komiye dalili oho, sai dai hakan da yakeyi d’in ita kanta yana birgeta domin halayya ce tagari ga dukkan wani musulmi abin kwaikwayo ga kowa.
Kallon Teemah tayi da tun ‘dazu ta zuba mata idanu tun sanda tafara murmushin nan tace
” inajin Abbas ne yakawo dan naganshi da kaya ‘dazu dayazo lokacin hankalina nakan aiki”.
Sake ‘daga rigunan mummy tayi tare da jujjuya takalman ahannunta tace ” size ‘dinki ne kuwa beyi kuskure ba”.
Kar6an takalmin Teemah tayi tana ‘ko’karin gwadawa a’kafarta.
Yayinda mummy taringa sanya masa albarka, fatan alkhairi, da kuma fatan gamawa da duniya lafiya da ganin haske adukkan al’amuransa.
Acikin zuciya Teemah taringa amsawa da Ameen.
Sai mummy tace
” ki ajiye bari anjima anunawa daddynki shima yagani ” .
Da
” toh ”
Teemah ta amsawa mummyn, kuma sai asannan ne mummyn tace ” ya ciwon kan naki “
Dariya Teemah tayi tace ” sai yanzu kika tuna da ni ko mummy”.
” ‘kaniyarki wannan ‘dinma ai duk saboda kene kikaga nashiga tunani.”……
Daganan suka kwashe da dariyar dukkansu har mummyn gaba ‘daya.
*****
Kwana biyar bayan graduation d’in Abbah ya sau’ka a damaturu…………..
Mummy na can uwar ‘dakinta taga daddy ya ‘kirata awaya akan wai tafito parlour yanzu yanzun nan.
” lafiya kuwa?”
Ta tambaye shi
Sai yace ” lafiyar kenan Khadeeja”.
yana gama fad’an haka ya yanke ‘kiran sai kwai ta tashi ta fito parlourn domin ams a ‘kiran Daddyn.
Sai dai tun kafin ta ‘karaso tafara jin zuciyarta na tsinkewa, bata san dalili ba amma sai dole hakan yasa yanayin saurinta ya ragu ba kamar yadda ta farao tafiyan da farko ba.
Koda ta iso parloun ma ciki-ciki tayi sallama bata damu da ko daddyn yaji ko be ji ba domin damuwar luguden da zuciyarta keyi ne ka’dai aganbanta awannan lokacin.
Bata ankara da ko mutune nawa bane zaune a d’akin ba har se da ta iso sannan ta ‘daga kai a’ko’karinta na neman inda ya yadace tazauna sai kawai idanunta suka hango mata yah yusuf zaune agefen daddy.
Yatsa ta ‘daga tare da fa’dan sunan shi cikin tsananin mamaki
” Yah……….. Yusuf………kaine ko…………ko………i”adanuna ne…?
Murmushi yayi mata sannan yace ” Nine nan ba idanunki bane Khadija ‘Karaso ki zauna”.
Ya ‘karasa maganar tare da nuna mata wajen zama.
Bata ‘karaso inda yake ‘din ba sai zune jagwab a inda take tsayen tama kallon shi yayinda idanunta suka da’de da fara zubda ruwan hawaye…..
” Ashe zan sake ganin ‘dan uwana aduniya……..ashe da rabon in sake ganin ka, Yah Yusuf me yasa ka manta dani, kamanta da koni wacece agareka…ka manta da…………
Daidai nan daddy ya dakatar da ita da fad’in ” Khadija ” !
Da ‘karfi yayi maganar wanda yasa dan dolenta tayi shiru sai dai hawayenta dasuka kasa tsayuwa.
Teema ce ta taho da niytan zuwa gurin mummyn ta ta sai ta tarar dasu a parlour dukkansu shiru sai mummynta dake zaune a’kasa kamar me neman gafara tana kuma share hawaye.
A sukwane ta iso gurin mummyn ta zauna itama kusa da ita tafara tayata goge hawayen batayi magana ba amma ga dukkan alamu kukan take shirinyi itama.
Daddy da yaga haka sai ya ‘kirata akan tazo wurinshi sai kawai ta kalleshi batare da tayi niyyan tashi daga jikin mummyn ba tace
” daddy me yasami mummy”?
Rashin sanin abin da zai ce da ita yasa shi yin shiru ” toh me ze mata yasaka mahaifiyarta kuka?”.
Juyawa yayi ya kalli Yah yusuf instead of ya bata amsar tambayar da tayi masa, cikin sa’a kuma daidai nan mummy ta dakatar da kukanta ta kamo Teemah, ta rungumeta ajikinta, tana ‘dan bubbuga bayanta.
Daddy da yah yusuf ne suka ha’da baki wajen bawa mummy ha’kuri.
Sai tace bakomai ai ya wuce tunda taganshi yanzu, tace abinda yasa ma har yaga tana kukan bakonai ba ne face tunawa da tayi da Mahaifansu, ta tuna irin gwagwarmayan da mahaifinsu yasha arayuwa ‘karshe kuma Allah ya kar6i abinsa, daga baya kuma mahaifiyarsu, wacce tayi iyah ‘ko’karin ta wajen ganin ta kula da rayuwarsu yanda ya kama ta bayan ba ran mahaifinsu amma ita ma Allah ya kar6i ranta tun ba aje ko’ina ba.
Story continues below

Tace ” Iyayenmu sun barmu mu biyu da tabbacin zamu had’e kanmu mu kala da kan mu da rayuwarmu, amma hakan sai ya kasa faruwa muka kasa yiwa kanmu wannan gatan, nasan da mahaifan mu na raye sai sunyi Allah wadai da faruwar wannan al’amarin”….
Daga nan ta ‘daga kanta ta kalleshi taci gaba da fad’in ” yah yusuf bansan me yasa ka ‘ki ni ba ka gwammaci rayuwarka takasance babu ni aciki duk da kasance wata matsayin ‘yar uwa agare ka wacce duk iya rayuwata kai ka’dai ne wanda zan yi tutiya dashi amatsayin ‘dan uwana, Allah ne kawai ya dubeni ya bani miji nagari badan haka ba da ban san ya rayuwata zata kasance ba, amma Alhamdulillah ko yanzu na godewa Allah na tunda ban nemi komai na rasa na jin dad’in rayuwa ba “.
Tana gama fad’in hakan tayi ‘kasa da kanta sai Yah yusuf ne ya bud’i baki da kyar fara bata hak’uri yace shi kansa bai san me yasa duk wannan abubuwan suka faru ba amma insha Allahu yayi mata al’kawarin matu’kar yana numfashi kuma yanada lafiya bazai ‘kara maimaita irin hakan agareta ba.”
Bai tsawaita magana ba yayi shiru shima duk tunanin iyayensa ya dawo masa fil aransa .
Sallahr maghrib suka fita da daddy suka nufi masallaci, koda suka suka dawo kuma sai suka zauna aharabar gidan suna tattaunawa akan maganar Mummy anan ne Yah yusuf ya ke cewa shi yanzu wata alfarma zai nema awurinsu duka bayan yafiya yana so idan har zai yiwu su basu auran Fateema saboda kar Khadeeja tayi zaton ko nan gaba zai ‘kara barinta duk da ahima ba ason ranshi hakan ke faruwa shi kansa be san har yaushe ne ya aikata irin hakan ba amma zaiso Khadeeja tasawa ranta salama da kuma yadda akan cewa shi ‘din yana nan amatsayin ‘dan uwan ta bazai ta6a gujan ta ba har abada, yace sai dai yana ganin hakan zai kasance ne idan har sun had’a wata kyakykyawan ala’kar da zata ‘dore har abada.
Daddy kuwa shiru yayi yana sauraransa domin be san manufar maganar Abban ba da kuma inda ta dosa abinda ka’dai ya tsaya matsa shine cewa da Abban yayi ” _abasu_ _auran_ _Fateema_ ”
…………….
” toh shi da su waye?”.
Abbah da yaga daddy yayi shiru batare da ya fa’di ko kalma ‘daya ba kuma daya lura sai yaga kamar ma abokin nasa hankalinsa naga wani tunani sai ya sa hannu ya dafa kafa’dar sa anan daddy ya fuskanceshi sai Abban yace ” baka ce komai ba kabarni inata surutu”.
Gyaran murya daddyn yayi tare da fad’in bana fahimceka ba ne yalla6ai ” ya ‘karasa manmganar yana murmushi.
“Manufar magana ta shine inda hali ina nemawa Mahmud auran Fateema awurinka saboda sake ‘karfafa dan’kon zumunci “.
Kallon Abbah daddy yake yi da kyau sai yanzu ya gama fahimtar me yake nufi tun farko.
Shikanshi da hakan zai faru zaiyi matu’kar farin ciki ko dan saboda sanin irin sha’kuwar dake tsakanin Mahmud da Fateemahn, amma bai sani ba ko kowa ma zai so faruwar hakan bataga shi da Abban.
Bai bawa Abbah amsar maganar tasaba ba ya dai ce ya bari tukunna zasu ‘karasa maganar anjima ko zuwa gobe ne insha Allahu.
Duk da Abbah na tunanin komawa agobem amma be tankawa daddy akan maganar daya fad’a d’in ba dan yana ji aransa cewa in dai akan maganar ne he is ready to sacrice everything dan kawai yaga yiwuwar auran. Saboda shi aganinsa idan akace Fateema natare da su toh hankalin Khadeeja zai fi kwanciya da yayan nata dan indai haka ne zai wuya zumunci ya yanke atsakaninsu.
Sai da sukayo sallar isha’i kafin suka ‘kara komawa cikin gida, suna zuwa yawuce wurin mummy yace 6angaren sa yake so akai musu abincin su acan zasu ci.
Da ” toh ” ta amsa masa shikuma daganan ya juya yakoma 6angaren nasa ya samu Abbah.
Teemah aka saka ta kawo abincin gaba ‘daya, kuma sai alokacin ne ta samu tagaida Abbahn saboda ‘dazu batasamu hankalin gaidashi ba ganin mummynta na kuka.
Muryarta da sanyi sanyi tace
“ina yini”
Yana cewa” lafiya” kan ya ‘kara wata magana harta ma’ke tsaye bata ‘kara yin wata magana ba, saboda ita sam ji tayi mutumin be kwanta mata arai ba musamman data fahimci adalilinsa mummynta ke kuka ‘dazu kuma tun fitar su take ta tambayar mummy akan abinda yasa metan ta’ki gaya mata haka ma data ce mata mutunin ‘kin kulata tayi, tana ganin kamar tasan mutumin awuni wuri amma takasa tuno a inda tasan shi ‘din hakan yasa tayi fishi ta ‘kyale mummyn tayi tafiyarta ‘dakinta bata sake dawo wa ba sai yanzun da mummy tasa ta kawo musu abinci.
Tana cikin tunanin taji yo muryar Abbah yace mata ” angama makaranta lafiya ko Fateema?”
” ehh lafiya ‘kalau”.
” Toh Allah yabada sa’a yasa me amfani ne”
Ciki-ciki ta amsa da ” Ameen “.
Shi kuma daddynta da yaga yanda tayi maganar kamar ranta be so cikin sanyi sai ya ‘kirata zuwa inda yake zaune yace mata
” yah na ganki haka Angel ‘din daddy, meke faruwa ne?
” bakomai daddy”!
Yace ” kin gane wannan ‘din kuwa “?
Ya ‘kara sa maganar da nuno Abbah da hannunsa.
Jijjiga kanta tayi tare da kallon Abban atake sai ta gano kamar da yake da Mahmud da tunda bata lura ba sai yanzun .
Bud’an baki tayi tace.
” Lah daddy kamar yana kama Yah Mahmud”.
Dariya suka sanya dukkansu har Abban Teemah kam sai ta tsaya tana kallon su, hatta da dariyar su ma iri ‘daya ce da yah Mahmud ta fa’di aranta.
” Allah me iko” .
Sai taji daddynta na fa’din ” mamanki bata fa’da miki waye shi ba? “.
Kai ta ‘kara jijjiga wa alamar ” ehh”.
Abbah da daddy duk sunyi mamaki kowa yajinjina al’amarin Khadeejan acikin ransa wanda hakan ‘karara ya nuna azahirance cewa ranta ya 6aci da Yayan nata ne duk da ‘dazu ta ‘dan sau’ko kafin tafiyarsu masallaci.
Abbah beyi mamaki ba domin aganinsa sam koma me tayi bata da laifi ta cancanci tayi fiye ma da hakan saboda ita akawa ba dai dai ba.
Yayinda Daddy yake tunanin irin ‘kunci da damuwan da ta rin’ka shiga abaya duk asanadin rashin ‘dan uwanta amma ace yanzu taganshi yana cikin gidanta amma kuma sai ta tsiri shariya!
Kai abin da mamaki gaskiya, amma yazama dole Fateemah tasan matsayinsa awurin ta da maman nata gaba ‘daya, koma miye yafaru ai be kamata ta’ki sanar da ‘yarta koshi waye ba.”
Azahiri kuma sai ya fuskanci Teemah yace
” Kinga wannan dakike gani azaune anan toh yayan mummyn kine, Uncle ‘dinki ne, kuma mahaifin yayanki ne wato Mahmud.
Ido ta zaro waje tana kallon daddyn alamar mamaki.
Sai ya yayi murmushi tare da jinjina nata kai sannan yacigaba da fa’din ” musamman fah yazo tun daga Lagos dan ya gaishe mu yakuma tayaki murnar kammala makarantar dakika yi”
Yana kawo wa dai dai nan yakamo hannunta yace
” Jeki gaida shi da kyau kinji “.
Duk abin nan dake faruwa Abbah kallonsu kawai yakeyi, ba ‘karamin birgeshi sukeyi ba sai azuciyarsa yake ‘kara jin son faruwar wancen al’amarin musamman ma daya lura da cewa Fateemahn akwai nutsuwa, zai so ‘dan shi ya aureta su rayu dashi, in har Mahmud ya aureta koba komai yasan shi bazai yi rashin dacen iyali irin nasa ba.
Ahankali cikin natsuwa ta mi’ke ta nufi Abban taje ta tsugunna gefe dashi daga ‘kasa ta gaida shi ya amsa fuskarsa kamar gonan auduga.
Tambayarsa tayi yasu Mahmud fah da An..Anty “
Ta tambaya harda Antyn ne saboda sanin sunan Anty datayi a bakin Mummy da kuma Yah Mahmud lokacin data Antyn ke yawan damunsa akan ya koma gida sa’ilin da yana service anan balle data ta6a daka mata wta uwar tsawa wata rana akan ta ‘dauki wayar Mahmud toh tun lokacin bata ta6a mantawa da ita ba.
Abbah kuwa da ‘din hakan yaji sai ya amsa fa’din
” suna nan lafiya tare sanba’da mata ruwan albarkatai.
Bata tashi akusa da Abban ba mummy ta shigo da sallamarta ,suka amsa gaba ‘dayanau har Teemahn
Abin mamaki fuskar mummy wasai tana murmushi tacewa Teemahn
” ke kuma kin wani nutsu kamar me hankali ya baki zuba musu abincin ba haryanzu ?”
Dawo da kallonta tayi gurin Daddy tace ” hala bakwa jin yunwa ne shiyasa.”
” Yah yusuf hu’du ban me kake mata haka har kuka manta da cikin ku.”
Dariyah suka sanya dukkansu cikin jin da’di, Teemah ce ka’dai tayi murmushi ,kowannensu yaji dad’in sakewan da Mummy tayi musamman daya kasance ita da kanta tazo harma tasa su dariya, ta kuma ‘kara da fa’din ” dan ku tashi kuci abinci dare na ‘karayi “.
Da kanta ta zuzzuba musu abincin tace bismillah Teemah kuwa hanyar wahe ta nufah sai Abbah ya hangota sanda take daf da barin ‘dakin ” tafiya zakiyi ko Fateemah”
Tsayawa tayi caka ta juyo tace ” ehh Abbah inajin bacci ne sai da safe”
” toh Allah ya bamu alkhairi”
Abban ya fa’di tare da fara cin abincinsa.
Harta kusan fita a’dakin sai mummy tace ” ki jirani a’dakina ina zuwa yanzu”.
” Toh mummy”
Tace tare da barin ‘dakin.
*BORNO STATE*
Motar su Abbas na fita daga wurin graduation ‘din hanyan Maiduguri suka ‘dauka basu tsaya ko’ina ba sai a wani gidan mai, koda suka sha man kuwa hanya straight suka kama batare da ya sake komawa gida ba.
Hakimce yake a seat ‘din baya inka ganshi zaka zaci wani basareka ne musamman inkayi duba da yanayin zaman dayayi, yawani hakimce baya fa’din komai sai in lokacin da zai yi magana da driver ne kafin zakaji muryarsa, balle ma ba wata maganar kirki sukayi tsakaninsu ba inya wuci aikin bada umarni.
Da ikon Allah kuwa lafiya lau suka isa, Abbas saka drivern yayi ya yi tu’ki a high speed shiyasa suka isa dawuri, kuma cikin kariyar ubangiji babu wani abin da suka ha’du dashi ahanya wanda yake ba daidai bane.
Da shigarsu cikin garin Maiduguri sai suka wuche gidan ogansa me suna Oga philip, suna yin horn me gadi ya bu’de musu ‘kofa.
Ko zama Abbas beyiba ya fara shirin tafiya inda ya fito oga Philip bai so hakan ba amma Abbas yace ana nemansa ne shiyasa, dolen oga Philip ya barshi yagama kintsawa yafito, lokacin ‘karfe hu’du kusan da rabi na yamma 4:28pm , sallama yayi musu tare da godiyah sosai saboda Oga philip mutun ne daya cancanci ayi masa godiya, tun farko Allah ya ha’da jininsu da Abbas tun farkon ha’duwarsu awurin wani course dasuka je bada jimawa ba, yana shiyake kula daduk wani abu dayashafi Abbas ‘din ko kuma zai taso ta 6angarensa yakan yi ‘ko’kari sosai wajen ganin ba’a samu wata matsala ba.
Duk sau’kan da Abbas zaiyi a maiduguri toh Oga philip ne ke bashi masau”ki ko a agidansa ko kuma wani gidan daban, shiyasa ko wannan zuwan ma da yayi sai ya sau’ka agidansa, bashi da matsala komai,inkuwa yaji an’kira sallah baya 6ata lokaci yake isa masallacin dayake akwai akusa dasu, kuma daya sanar dashi cewa yana so yaje damaturu amma yace bazai kwana ba aranar zai dawo sai Oga philip ‘din yace ” toh ba matsala daganan ya ha’dashi da driver suka kama hanya suka zo damaturun atare, yakuma ce da drivern yakula da tu’ki da kyau dan kawai saboda Abbas ‘din.
Yanzun ma sawa yayi aka ‘kara kai Abbas ‘din airport yakuma binshi da fatan alkhairi.
Bai ‘kira kowa ba aranar sai mummy ya mata sallama awaya dayake itan basu ha’du ba lokacin da zai tafi shiyasa ya ‘kirata yace mata ya wuche Porthacourt.
Sai dai kuma tun lokacin da yatafi ya bar Teemah a tsaye yakejin be kyauta mata ba harma dashi kansa, sai yake jin dama ya tsaya ya kar6i leave awurin aiki kafin ya taho ‘din da yasan komin yaya de zai ‘dan yi kwana biyu, da zaiyi irin wannan tafiyar ba.
Amma yazaiyi hakan ma ba laifi tunda yagama abinda yakawo shi dama burinsa yaganta kuma yagantan, wannan ma satan hanya yayi shiyasa and baya son tun ba’aje ko’ina da fara aikin ba ya fara samun problem dasu shiyasa yatafi aranar batare da ya ko tsaya sun yi gaisuwar kirki da su daddyn ba dan ma kar ya shiga cikin lokacinsa.
*DAMATURU, YOBE* *STATE*
Koda fitan Teemah a’dakin direct 6angaren mummyn ta nufa dan cika umarninta, mummy kuwa bata bi bayanta ba sai ma kujera dataja tayi zamanta, su Abbah nagama cin dinner suka sha hirar yaushe gamo da kuma tuna baya da yayan nata wannan karon faran-faran batare da wani damuwa
ba.
Story continues below

Daddy ne yace maza ta tashi ta tafi dan kamar yaji tace Teemah ta jirata a’daki yace tayi sauri taje kar
ta hana masa yarinya bacci.
” su yarinya manya”
Inji mummyn
Tana dariya tabar ‘dakin tare da yi musu sai da safe.
Koda ta isa ‘dakin nata kuwa barci tasamu Teemahn nayi abakin gadonta kamar ma zata zame ta fa’do, aranta tace ” Allah sarki harta gaji da jira tayi bacci.
Taso ta tasheta amma ganin yanda tasake take bacvcn sai ta ‘kyaleta kawai anan ‘din sai dai ta ‘dan bigeta ahankali tace ” ta gyara kwanciyar tata da kyau.
Daddy har yayi shirin bacci sai kuma yaji kamar akwai kukan sauro ka’dan a’dakin kuma gashi yanada ba’ko sai yace bari ya ‘dauko magani dayake shi dama ba so yakeyi ba be fiya anfami dashi ba dama mummy ce dayake ita ko kukan sauro na hanata bacci shiyasa sam bata rabuwa da insecticide a’dakinta.
Mummy nagama shiri kenan saura ta kwanciya, sai kuma tajiyo kamar motsi a parlour da farko harta ‘dan tsorata sai ta tsaya cak a inda take tsayen, tana cigaba sauraron motsin yayinda yake ‘kara tunkaro ta sai kuma tajiyo muryar daddy yana sallama ahankali
saboda dare.
Sai da ta amsa kafin tace ” ai har kaban tsoro ma”
” very sorry, maganin sauro za’a bamu naji kamar akwai ‘dan kukan sauro a’dakin”.
” ah ah kaida kece bakaso?”.
” ehh albarkacin ba’ko za’a bani “
“Hmm kai de fa’di gaskiya ”
Tayi maganar tare da juyawa dan zuwa inda maganin yake ajiye, sai kuma asannan daddy ya lura da Teemah dake kwance, “sai da kika samin yarinya bacci anan ko?”
Sai tayi saurin fa’din ” kafin nazo ma harta yi baccinta”.
” badole ba ina zata iya jiranki kinje kin samu Yayanki kina ta’di kin manata da ita, badole tayi baccinta ba itama, aini banga laifinta ba”.
Batayi magana ba bayaga ” hmm” kawai sai mi’ka masa Insecticide ‘din shi kuma maimakon ya kar6a a’a, sai ya mi’ka hannunsa ya cafko nata hannun yajata zuwa parlour binsa tayi kamat ra’kuma itama.
Zama yaje yayi akan kujera ita kuwa sai takalleshi da mamaki tana daga tsayen tace ” yalla6ai ya haka naga ka zauna?”.
” magana zamuyi Khadija ”
Ido ta zaro waje tare da fa’din yanzun kuma?, da daren nan.”
” ahakan tazo Khadeeja, kuma ahakan za’ayi”
Ya fa’da in a serious tune ,ganin hakan yasa mummy taje ta zaunan itama ta fuskance shi.
” yauwa ki saurareni da kyau kiji, kinsan Yusuf ‘din nan abokina ne shi tunma kafin na ha’du da ke right?
Sai tace ” ehh”.
” toh amatsayinsa na abokina misali idan akace ya nemi alafarma agurina kina ganin ya kamata na’ki saurarensa”?
tace
” a’a “
” saboda me”?
” saboda zumunchi ,kuma ya kamata ka karramashi amatsayinsa na aboki agareka.”
” idan kuma ya ‘kara da zamowa sirki ( in-law) agareni fah “?
“Fiye da hakan ma zakayi masa inda hali”.
“good”.
Yace da jin da’di sannan yaci gaba da fa’din
” Yataso ne musamman all d way from Lagos ya zonan dan kawai yasada zumunci dake tsakani, wanda nake tunanin cewa ada sam babu shi, nasan kinsan da haka ko”?
” ehh”
Tace asanyaye dan tafara jin tsinkewan zuciya akan wannan irin maganganun daddyn.
” Lokacin da zaizo be zo da niyyar neman aure ba face abin da nafa’da miki abaya, saboda ya sanar dani da jimawa akan zezo mana nan amma bai sa rana ba saboda kar ya saka rana yazo tafiyar bata yiwu ba, shiyasa yabari ahaka nima kuma dalilin dayasa na’ki fa’da miki kenan, amma Alhamdulillah sai gashi yazo mana batare da munsan ma yataso ba, sai kawai muka ganshi.
Story continues below

“Hakane”?
Mummy kai kawai ta ‘daga masa domin jikinta yafara yin sanyi da wa’dannan irin maganganun, kardai Yah yusuf ku’di yake bu’kata awurin Daddy, haba no waonder taga ya rame ba kamar da dayake da ‘dan ‘kibarsa ba, ashe ya’dan shiga damuwa ne shiyasa……………
Firgigi tayi tana kallon daddyn domin tana cikin tunanin tajishi yace ” kina jina” da ‘dan ‘karfi, bata sani ba ashe bakinsa na biyu kenan domin na farkon kamma batasan yayi ba.
Ran’kwafowa yayi yana dubanta da kyau sannan yace
” tunanin me kuma kike yi Khadeeja”?
Bakinta har karo yakeyi wajen fa’din ” ba komai”.
Owk
Yace sannan yaci gaba
” Allah cikin ikonsa tun da yaga Fateemah sai ya yaba da hankalinta harma yace yanason aurenta ma ‘danshi Mahmud”
Ido mummy tazaro waje tare da mi’kewa tsaye akan daddyn.
” Mahmud de”
Tafa’di tare da nuni da wani 6angare tamkar Mahmud ‘din yana wajen.
” shi de bawani ba, be yi bane ko me”
Shiru tayi still tana tsayen.
Hannu ya mi’ka yakamo nata hannun
“Zauna mana sai ki yimin bayani da kyau wala Allah zanfi fahimtarki”.
Zaman tayi kamar yadda ya bu’kata amma bata iya yin wata magana ba.
Daddy kuwa sai yaci gaba da fa’din
” Khadija mun kusan kammalawa da maganar ahalin da ake ciki yanzu ‘karshen furuci na kawai yake jira yaji”.
“Toh kace masa baka amince ba kawai”
” awani dalili”
yaddyn ya tambayeta.
” Habah, haba dan Allah Mahmud fah naji kace?
” ehh mana, ko kina da wani wanda kike ganin yafi Mahmud ‘din”
Karka’da kai tayi cikin takaici
“Amma inajin ka manta wacece mahaifiy……….
” hold it pls, lets go straight to d point, ok!”.
Yatari maganan da tayi niyyan fa’din cikin gaggawa harma da ‘daga hannunsa ‘daya sama , wanda hakan ‘karara yake nuni da cewa baya bu’katan jin komai daga gareta.
Shiru mummy tayi tare da binsa da idanu, mamaki ma yake bata daman ta da’de da fahimtarsa aganin ta shi sam baya so yaji anfa’di karkatacciyar magana akan Yah yusuf ‘din sai yayi ‘ko’karin gyarata, shiyasa da datake yawan complain akan sharetan da yakeyi shi daddyn shine me tausarta akullum sai ya nuna kamar wai abubuwa ne suka masa yawa, sai da abin yayi yawane kafin shima ya saduda ya goyi bayanta amma duk da be ta6a nuna mata cewa Yah yusuf ‘din badai dai yakeba, sai de yace suci gaba da addua kawai, kuma duk wannan abubuwan dasuke faruwa ita aganinta bakomai kesa daddy yin hakan ba face akan goya masa baya da Yah yusuf ‘din yayi lokacin da daddyn ya nemi auranta.
Jinsa yayinda shi kuma yaci gaba da fa’din
” munyi magana dashi kuma na fahimce shi, ayanzu kuma gab nake da nuna amincewa ta 100% saboda girma dayake dashi a idanuna, bazan iya ‘kin nuna amincewata ba kuma ina fatan kema zaki goya min baya with all your support”.
Ya ‘karashe maganan yana kallonta.
Itama kallon nasa ta tsayayi daga baya baya kuma ta kauda kanta gefe.
” taya za’ayi na goyi bayanka alhali ina da tabbacin Anty bazata ta6a son zuri’armu ba, balle ma har ace ‘yar da ni na haifa, ‘danta ya aura!”
Gashi kai kuma ka kasa fahimta ta”
Nasiha sosai daddy ya mata wanda ya matu’kar kashe mata jiki tare da kawo ayoyi da hadisai wanda suke nuni akan halayyar ‘dan Adam da kuma bata misalai akan yadda ikon Allah ya buwayi ko’ina yace mutun ba komai ba bane shi compares to mahallici dan haka komai zatayi ta yadda da Allah da kuma ‘karfin ikonsa kafin tasa tsoron wani abin halitta.
Story continues below

Ya ‘karasa da cewa ” ina fatan kin fahimceni kuma zaki bani ha’din kai”
ahanakali tace” insha Allahu”.
“Yauwa, sai da safe”.
Yana mi’kewa ya fa’di hakan yayinda mummy takasa amsa sai da safen dayake mata, ta dai tsaya atsaye duk tunani ya cikata, ” ha’ki’ka gaskiya Daddy ya fa’da kuma tasani cewa Allah ne mafi rinjaye akan komai, toh amma abinda takasa ganewa shine kar dai ace wannan dalilin ne ya kawo Yah yusuf inda take?”
Sosai abin nan ya dameta, washe gari kuwa bata nuna komai ba suka yi gaisuwa cikin sakin fuska har suka gama karyawa sannan ne da suka ke6e da Abbah ta sake jefah mishi tambayar da ke damunta azuci inda tace ” kar dai abin nan daka fa’da jiya shi ya kawo Yah Yusuf garin nan?”.
” ah, ah, ah, khadeeja, kin manta me na gaya miki ne jiya hala?
Ido ta tsura masa tana kallonsa ga dukkan alamu cikakken bayani take bu’kata daga wurinsa.
Ganin hakan sai ya ci gaba da fa’din
” ba abinda yakawo shi kenan ba, kamar yanda na sanar dake ,yazo ne ya sada zumunchi sai kuma yayi katari da Fateemah sai yaga dacewa da sha’awar aurawa ‘dansa ita shine yamin maganan nima kuma na amince,
kinga gara namiki gwari-gwari yanda zakifi fahimta.”
Ya ‘karasa da murmushi
” amma kai kana ganin bawata matsala ko? nifah gaskiya ina tsoron abinda zaije yadawo, kafa san halin Anty ba ‘kaunar mu take ba gaba ‘daya”.
” Kin manta wannan ‘dinma kenan ko?”
Kauda kai tayi gefe tare da fad’in ” ban manta ba”
” toh karki damu kanki dan Allah, ita ‘din ba Allah bane ya halicceta?, ki ringa sawa ranki yadda da ‘kaddara kowacce iri ce, na tabbata ‘kaddaran wannan al’amarin ne yakawo shi akwannan, toh kinga kuwa idan har Allah yace za’ayi toh fitinan wani ko wata be isa yasa afasa ba,dan haka ki saki ranki kinji”.
“Da kai ta amsa masa, dan kasa bu’dan baki tayi ta ce komai.
Ko bayan barin sa ‘dakin ma bata motsa ayanda ya bartan ba, tun yanzun tausayin ‘yarta yafara shiganta.
Daddy kuwa da komawarsa wurin Abbah sai suka kammala magana inda daddy sai alokacin ne ya nuna amince warsa akan lamarin, ‘karyar da yiwa mummy kuwa akan tunruni ma ya amince yayi hakane saboda ta daina sawa ranta kamar maganar zata fasu.
Yayin da Abbah ya nuna tsantsan farin ciki da amincewar daddyn harma ya ‘kara da fa’din ” bada wani jimawa ba zasu ji daga garesu domin baya so a’dauki dogon lokaci akan lamarin”.
” bakomai ai, Allah ya nuna mana “
inji Daddyn Teemah
Zama suka yi suna ‘dan ta6a hira tsakaninsu anan mummy ta tadda su, aka cigaba da hiran da ita, ranta ajagule take jinsa ,amma bata so Yah yusuf ya zargi wani abu daga 6angarenta shiyasa ma ta taho inda suke ‘din, kuma ma dan kar daddy yace ta’ki jin maganarsa.
Da lokacin tafiyar Abbah yayi sosai ya musu alkhairi daga mummyn har Teemah, ya bawa kowa kyautan ku’di daidai yanda yayi ra’ayi saboda acewarsa be taho musu da komai ba wai suyi ha’kuri da wannan sai in ya ‘kara dawowa.
Teemah da bata san abinda ke faruwa ba taringa bashi ‘sakon gaida Yah Mahmud kusan sau hu’du tana maimaitawa jitake kamar tabishi su tafi, shikiwa Abbah sai amsa mata yakeyi yana murmushi da jin da’di, sai da mummy ta banka mata harara kafin tayi shiru ta daina magana.
Da daddy suka tafi domin shima akwai abinda zai kashi can arean Lagos ‘din harkan kasuwancinsa.
*LAGOS*
Koda Abbah ya isa gida Mahmud ne ka’dai ya nuna farin ciki da dawowar tashi, dan tun da yaje ‘dauko shi a airport yake washe ha’kora, wannan na ‘daya daga cikin burikansa dayake son ganin faruwarsu, sai kuma gashi hakan yafaru, ba ‘karamin da’di yaji ba da Abbah yace zaije Yobe , da farko ma yace zai bishi suje tare amma da Anty ta azalzale shi a’daki tayi masa masifah tare da fa’din matu’kar ya ‘dauki ‘kafa yabi Abban nasa toh yasani _babu ita_ _babu shi_ “
Dajin hakan sai ya ha’kura da tafiyar saboda duk yanda yakai da rashin ji sam baya son mummunan kalma daga mahaifansa, ha’ki’ka iyaye iyayena kuma duk girmanka da ikonka yazame maka dole kabisu kodan samun rabauta awurin mahallici, amma be sanar da Abbansa abinda yafaru ba sai kawai ya nuna masa cewa akwai abinda yataso masa ne shiyasa ya fasa zuwa, amma insha Allahu zaizo yaje ko daga bayane.
Abbah be wani damu ba yace ” toh shikenan ba matsala, kai ai daman ‘dan can ne ko bakaje yanzun ba matsala, da’ace baka ta6a zuwa ba ne toh da ‘kafata ‘kafarka amma yanzu kam ka fansheku, Allah ya nuna mana lokacin dazaka sake zuwa ‘din “
“Ameen”
Mahmud ya amsa wa Abbahn dashi, be damu da _yah_ _fanshe sun_ da Abbah yake nufi ba sam ma abin be zo kansa ba, Abbah kuwa nufinsa shi Mahmud ‘din da Antyn sa.
Sai kawai ya ‘kyale Mahmud ‘din yayi tafiyarsa shi ka’dai, domin koshima bazai so bakin uwa yakama ‘dan sa ‘daya tilo da Allah ya mallakawa ba.
Abinda Mahmud be sani ba shine duk abinda Anty ta fa’da kaf yaji ta, kuma wannan dalilin ne yasa ya ‘kara saka himma wa tafiyar tasa.
Koda yatafin kuwa basuyi waya ba har yaje ya dawo gida ko fatan sau’ka lafiya bata yi masa ba ballantana taji yanda ya sauka shine ma ya gwada kiranta sau ‘daya dayaga bata ‘dauka ba sai be sake ‘kiraba yace inhar ba da gangan ta’ki ‘dauka ba toh intaga missed call zata kirasa, ilai kuwa yaji shiru, bata ‘kirashin ba kamar yadda shima be sake ‘kiranta ba har ya dawo sai dai suyi wayarsu shi da Mahmud.
Ko yau ‘din ma da zai dawo Mahmud kawai ya ‘kira ya sanar dashi ,shi kuwa be sanar da Anty ba kawai yaje ya ‘dauko shi.
Anty bata ma gida lokacin da Abbah ya dawo tatafi yawace-yawacen ta acikin gari ita da ‘kawarta Anty chideh.
Koda ta dawo ta ganshi agida kuwa ‘dauke kai tayi tamkar ma bata ganshi ba, shima Abbah sai ya’ki yi mata magana yasan da kanta ma zata kulashi idan nata ya ‘debo ta.
Kwana biyar bayan dawowarsa sannan ya ‘kira Mahmud tare da Anty, yayi musu bayanin abinda ke faruwa, yayin da hankalin Mahmud yakai ‘kololuwa wurin tashi rasa yadda zaiyi ma yayi hakama Anty.
Ita kam tsaye ta mi’ke da gama jin abinda Abban yagama fa’di tace “banji abinda kake fa’da da kyau ba, ‘dan sake maimaita pls”.
Murmusawa Abbah yayi, yana kallonta har kamanninta sun soma sauyawa atake, be damu ba ya sake mai maita mata akaro na biyu duk da yasan ta ji shi da kyau, kawai sha’kiyanci ne ke damunta shikuwa yana daidai da ita awannan karon.
Kwankwaso ta kama da hannunta ‘daya jikinta har rawa yakeyi tsabar masifah.
“Amma kai ko kunyar fa’da ma bakaji?
Kallon ta Abbah yayi wannan karon sai ya koma baya jikin kujera ya zauna ya jinginu yana binta da kallo yana murmushi dama yasan sai ta masa rashin hankali shi kuwa me sashi barin maganan nan se ikon Allah kawai sai yace mata.
” abin kunya nayi ne da har zanji kunyar fa’di”?
“Dakata dan Allah Alhaji, inaga kamar ka manta da maganar da akayi kwanaki agidannan ko, inace kai da bakinka kace zakayi bincike bayan yaro yasanar dakai ga abinda yakeso shine zakaje ku wani ‘kulla ‘kulle-‘kullenku daga zuwanka, ka zo kace ga abinda za’ayi, kai aganinka kayi adalci kenan,? Toh ya kuma kake so ayi da ita waccen da take s…..da Mahmud ‘din yake sonta?
Da wuri ta daidaita harshenta dan kar ta kwafsa.
” kinje kin tambayo auren ne”?
Abban ya tambayeta hankalisa akwance domin shi baya jin yana da damuwa koka’dan saima wani farin ciki dayakeji, yayin da masifar da Antyn keyi yake ‘kara masa kwarin gwiwa dan ganin yacika Burinsa.
” haushi tambayar tasa ta bata, take kuwa ranta ya ‘kara 6aci tafara masifa kamar ta ari baki
” taya za’ayi kace ko na tambayo aure dama mace tana tambayar aure ne?
“Ni na sani ne ko akanki za’a fara”!
yasake fa’da cikin kwanciyar hankali .
” Wallahi Alhaji karka ga nayi shiru akan wannan maganar ka zaci ko maganar ta fasu ne, dama na fahimci take-takenka tun farko so kake ka’ki sa baki amaganar shiyasa ka tsiro da wani batun bincike, toh wallahi bari kaji ba rantse da Allah ko zan tafi tsirara ne sai naga Mahmud ya auri Munira, kuma bari in tabbatar maka wani abu da baka sani ni ‘dana bazai auri wata ‘kazama wai Fatima ba ko da kuwa mata sun ‘kare a duniya toh sai sai ya zauna ba mace amma bazai ta6a auranta ba ,akai kasuwa”.
Tana gama fa’din hakan tayi waje tana ta sababi.
Binta da kallo dukkan su sukayi har Mahmud ‘din wanda yake zaune akan ‘kafafunsa tamkar gunki tun lokacin dauaji bayanan Abban nasa na farko be ‘kara jin komai ba, masifan da Anty tafara na ‘karshe shine ya dawo shi cikin hayyacinsa saboda da ‘karfi tayi maganan.
Story continues below

Sai data 6acewa ganin su kafin suka dawo da kallon su ga juna suna ha’da idanu kuwa Mahmud yayi ‘kasa da idanunsa.
Bayyanan niyar murmushi Abban yayi sai yace ” Mahmud kaima baka so ko”?
Shiru Mahmud ‘din yayi yana rarraba idanu , baya jin ya yiwa Abbah adalci idan yace ” ehh bayaso” inkuwa yace yanaso toh tamkar ya siyawa gidan nan tashin hankali ne, tunda yasanAnty bazata ta6a goyon bayan Abbah akan maganar ba, bayaga haka ma shifa kwatata bayaso yayi aure yanzu, bayanzu ya shirya yin aure ba kuma ko zaiyi auren ma ba dai Fatima ba, sai dai kuma ai da yarinyar da Anty ta keso ya aura ‘dinnan gara Fatima sau dubu akanta, kai bama ha’di, duk itama Fatiman be ta6a yi mata kallon so ba , be ta6a ko kwatanta wai shi ze so ta ba, shi bai ma da plan ‘din yin aure akwana kusa amma be san dalilin Abbah na nema masa auren Fatima ba.
Yace da ace Abbah zai bashi za6i da ita Muniran ze za6a saboda wani dalili.
Yana cikin tunanin ya tsinkayo muryar
Abbah yana sake maimaita tambayar daya yi masa da farko ha’di da cewa ” kar ka damu Mahmud ka bu’de zuciyarki kasanar dani abinda ke ranka ,ni mahaifinka ne, bazan ta6a ‘kin kar6ar kowacce irin uzuri daga gareka ba, matu’kar kaga za6in dana ma ka be maka ba ka sanar dani”
Numfasawa Abban yai jin har yanzu Mahmud be ce komai ba sai ya’kara cewa ” sai dai inason kasan wani abu Mahmud har abada ni mahaifinkane, me ‘kaunarka ne, bazan ta6a yima za6in da nasan zai cutar da kai ba, idan waccen yarinyar ne da mahaifiyar ka ke magana akai i thought na maka bayani, bincekena be nuna min komai na alkahiri tattare da su ba shiyasa bazan ita barinka ka auri yarinyar ba, amma bansani ba ko kana son abinka ahaka, feel free ka sanar dani ra’ayinka kaji Mahmud”!
Da ‘kyar Mahmud ya bu’di baki yace.
” Abbah…….sai kuma yayi shiru.
” Inajinka “
“Abbah ban’ki za6in da kayimin ba, na amince kuma nagode sosai, Allah ya ‘kara girma”.
Albarka Abban nasa yata saka masa saboda farin cikin be watsa masa ‘kasa a idanu ba, ha’ki’ka wannan ranar ta farin ciki ce agareshi ,daga nan ya sallami Mahmud ya tafi.
Koda ya koma ‘dakinsa kuwa zama yayi kawai abakin gado ya dafe kansa dake masa sara ba ‘ka’kkautawa, kasa aiwatar da komai yayi alokacin jin abin yake kamar amafarki, ” _wai shi_ _aure, auren ma_ _kuma_ _Teemah_ ” .
Yana a zaunen wayarsa tafara ringing se ya ‘kyaleta danji yayi ma ta ‘kara masa takaici, kusan ‘kiran zai tsinke sannan yasa hannu ya ‘dauko ha’di da jan tsaki domin da farko beyi niyyar ‘dauka ba amma da ‘karan yayi yawa ne yasashi bashiri ya janyo ko duba sunan me ‘kiran beyiba yayi picking kawai ya kai kunnensa.
Shiru yayi ko daya ‘dauki ‘kiran amma daya jiyo muryar Abbas ne sai ya ‘dan saki ransa ka’dan.
Bayan sun gaisa sai Abbas ‘din ya sanar dashi cewa yana Abuja yau ‘din nan ya sau’ka,
Take sai shima ya bashi amsa da fa’din nima ina hanya insha Allahu”
“Toh se ka iso”
Daganan suka yi sallama kowa ya ajiye wayar.
Mahmud be fito daga ‘dakin nasa ba sai da shirin tafiya Abuja, a harabar gida yasamu Abbah ya sanar dashi cewa zashi Abuja.
” ina fatan lafiya”
Abban ya tambaye shi
Sai Mahmud ya bashi amsa da “ehh lafiya ‘lau kawai zashi ne yana da appointment da wani acan”
Fatan Allah ya kiyaye Abbah yayi masa sannan yace ko akwai wani problem “?
Mahmud yace “a’a
Jinjina kai Abbah yayi.
Daganan Mahmud yayi tafiyarsa yakama hanyan Abuja.
*ABUJA*
Abbas bacci yakeyi lokacin da Mahmud ya isa gidan, wanda baccin ya ‘dauke shi sa’ilin yana kwance akan kujera a parloun dake 6angarensa, yana tsaka da tunanin Fatimansa baccin yayi awon gaba dashi.
Mahmud na shigowa 6angaren nasa sai kuwa shima ya farka daga baccin da yakeyi ‘din, dama shi Abbas haka yake sam baya bacci me nauyi, da salati ya farga daga baccin sai idanunsa ya sau’ka akan Mahmud dake tsaye yana kallonsa yana ayyana dama shine a irin wannan yanayin narshin damuwa amma shi kam be san ranar da farin ciki zata ‘dore agareshi ba.
Da sauri Abbas ya mi’ke zaune yana masa murmushi, ” harka iso ne” Abbas ‘din ya fa’di.
Sai dai ga mamakinsa fuskar Mahmud a ‘daure take tamau babu fara’a balle yayi tunanin samun amasar shi, damuwa ce ‘karara tattare da fuska da kuma yanayin Mahmud ‘din, dama yasan za’a rina domin tun lokacin dasukayi waya da Mahmud ya fahimci ba daidai yake ba sai kuma gashi yanzu daya ganshi da idanunsa sai yafi gasgata zuciyarsa fiye da ‘dazun dayaji muryarsa acikin wayan.
Be ce da Mahmud ‘din komai ba kawai sai ya tashi ya wuce cikin bedroom ‘dinsa, bathroom ya fa’da bayan ya cire kayan dake jikinsa ya watso ruwa tare da canja kayan dake jikin sa zuwa dogon wandon jeans da rigarsa fara sa6anin da dayake sanye da 3quatern wando baki da kuma singlet.
Kayan daya saka ‘din sun matu’kar amsan jikinsa sai suka ‘kara fito da ainahin kyaunsa da kwarjininsa afili.
Sake fitowa yayi cikin takunsa na ‘kasaita ya nufo palourn nasa inda yabar Mahmud, turus shima ya tsaya mamaki ne ya ‘kara cikashi ganin ayanda ya bar Mahmud ‘din ahaka yadawo yasame shi tsaye hannayensa duka zube acikin aljihun wandonsa.
Abbas aransa yajinjina wannan lamari ” lalle Mahmud na cikin damuwa sosai” shi kanshi abinda ke damun Mahmud ‘din sai ya fara damunsa tun ma kafin yaji menene.
Sosai ya tsorata da yanayin Mahmud ‘din kasancewarsa mutun me surutu da haba haba da jama’a, da wuya kaganshi a irin wannan yanayin da yake ciki ayanzun in dai bada wani kwakkwaran dalili ba.
Hakanne ma fa yasa koda yaje yin shirin sa be ‘dau dogon lokaci ba ya kamalla dawuri ya wuri ya fito dan ya yaji me ke faruwa.
Abotarsu daga Allah ne, tun lokacin dasuka ha’du a damaturu sai Allah ya sanya musu ‘kaunar junansu sannan suna mutunta juna tare da damuwa da damuwar junansu tamkar ‘yan uwa na jini.
Abbas na kammala tunanin nasa sai ya wuceh wurin fridge ya ‘dauko fresh milk tare da glass cup guda biyu ahannunsa.
” why are you still standing Mahmud ka zauna mana zaifi ai ko”
Yafa’da bayan ya iso ya tsaya daga bayan Mahmud ‘din.
Ahankali Mahmud ya taka yaje ya zauna akujera me zaman mutun biyu yayin da Abbas yabishi abaya ya joining ‘dinsa suka zauna atare.
Yana zama sai ya fara tsiyaya fresh milk ‘din a ‘ daya daga cikin kofunan daya kawo ‘din bayan ya ajiye su akan centre table dake gabansu.
Abbas mi’kawa Mahmud cup ‘din yayi batare da yayi magana ba, sai alokacin kuma Mahmud yayi ajiyar zuciya tare da huro zazzafan iska da ‘karfi daga bakinsa sannan ya ‘daga lumsassun idanunsa ya kalli Abbas da su.
Shikuwa Abbas sai ya ‘dage masa gira ‘daya tare da nuni da abinda ke ri’ke ahannunsa da idanunsa alamar ” anshi mana” .
Hakan da Abbas yayi ne yasa Mahmud shima ya kallo hannun Abbas ‘din sannan a hankali ya cira hannunsa ya kar6i cup ‘din daga hannun Abbas.
” hmm “
Abbas yace tare da jijjiga kansa bayan Mahmud ya kar6i abinda yake bashi ‘din ,sake jinjinawa wannan al’amarin yakeyi dahar ya iya meda Mahmud haka a ‘dan ‘kan’kanin lokaci,because it’s hardly kaga Mahmud na fishi arayuwarsa.
Shima Abbas tsiyayan fresh milk ‘din yayi yasha sannan ya ajiye cup ‘din ahankali, sar’kafe hannanyensa yayi cikin junansu bayan ya gyara zamansa da kyau ya fuskanci Mahmud ‘din sai yace masa ” naganka wani iri, hope all is well with u”?