ABBAS CHAPTER 12

ABBAS




CHAPTER 12





” hmm”
kawai Mahmud yace daganan ya kuma yin shiru.

Shirun da Abbas yaji ne yasa ya ‘dago kansa ya kalli Mahmud da kyau,
aransa yake tunanin
” wai yau Mahmud ne haka?
Abin na bashi mamaki sosae musamman da yaga yanda idanunsa suka koma ja alamar yana tattare da 6acin rai sosai.

Sake ‘daukan cup ‘din dake gabansa yayi ya ‘kara kur6an freshmilk ‘din, kafin ya cire kofin abakin sa yajiyo muryar Mahmud yana furta ” Fatima”
irin amamakance ‘dinnan, Abbas bewani damu ba koda yaji ya ambaci sunan domin shi ayanzu bashi da burin da ya wuce yaji meke tafe da Mahmud ‘din dan haka sai yaci gaba da shan abinsa ahankali batare da ya tankawa Mahmud ba.

Kallon Mahmud yaci gaba dayi daya zurawa centre table ‘din dake gabansu idanu tambayr Mahmud ya yanke shawaran yi inda yace ” wacce Fatima kuma Mahmud” yana gama fa’di ya’kara kaiwan cup a bakinsa.

Mahmud kuwa kamar an tsikare shi ya mi’ke tsaye yaci gaba da fa’din

” _Teemah fah_ Abbas, _wai_ _Abbah na Teemah zai_ _aura min “_.

Abbas be san lokacin da ya furzo freshmilk ‘din da ya kur6a ba, wanda ke bakinsa dai dai yasha kenan yaji maganar Mahmud ‘din tamkar atsakar kansa yayi ta, hakan yasa ya furzo shi da ‘karfin da bai shirya ba sai ya zarce da tari.

Sosai tarin ya sar’ke shi tamkar wani me ciwon TB dan har Mahmud dake tsaye cikin 6acin rai ma saida ya taho da sauri kusa da shi yana masa sannu, fridge Mahmud yakoma ya ‘dauko masa ordinary ruwa ya bu’de marfin sannan ya mi’ka masa, ka’dan Abbas yasha sai ya ajiye goran kana yaci gaba da kallon Mahmud tamkar wani sabon halitta ya gani.

Shiru suka yi dukkan su, na ‘dan wani lokaci yayin da Abbas yake ta addu’a aransa cewa ” Allah yasa kunnuwansa ba dai dai suka jiyo masa ba, inma dai dai ne Allah yasa ba tashi Fatiman Mahmud yake nufi ba “.

Murmushi Mahmud yayi wanda ni kaina bansan ma’anar ta ba domin bata farin ciki bace, sannan yaci gaba da fa’din ” kamar de ni, Abbas kaima kayi mamaki ko?

Shiru Abbas yayi yana kallon sa bashi da buri ayanzu illah yaji ‘karshen zancen Mahmud ‘din.

Tunawa da maganar Mahmud yayi wanda yayita bada jimawa ba inda yace ” wai Abbah _Teemah_ _zai aura_ _min_ .

Kauda kansa gefe Abbas yayi da sauri daya tino maganar acikin zuciyarsa in banda innalillahi babu abinda yake iya fa’da.

Yana juyowa sai suka ha’da idanu da Mahmud sai yace. ” kaima kana tayani mamaki ko Abbas, ni bansan me yasa Abbah na ya yanke wannan hukuncin ba batare da ko yin shawara da ni ba, juyowa yayi da sauri kamar zautacce yayi facing Abbas sannan yaci gaba da maganarsa.

“Kasan wani abu Abbas?
Ni ban ta6a kawo faruwar hakan ba ko da a wasa, hasashe na be ta6a kawo min yiwuwar aure tsakanina da Fatima ba not even in my dreams”.

Story continues below


” Fatima fah Abbas, my lovely sis, my lil sis how can I………..

Dafe kansa yayi da sauri ya kasa ‘karasa maganar da yayi niyyan fad’i.

Abbas ma rintse idanunsa yayi da ‘karfi yayi baya ya jinginu da jikin kujerar daya ke zaune.

Mahmud kansa ya ri’ke da ‘karfin gaske dayake mugun sara masa, yanajin da zai iyayin hawaye ayanzu da babu abinda zai hanashi yayi saboda yasan shine ka’dai zaisa ya samu ‘dan sassauci amma ina……

Da ‘kyar Abbas ya daure ya tashi yakoma kusa dashi ya sa hannunsa ya dafa kafa’dar Mahmud ‘din
duk da yanajin wani ‘kuna azuciyarsa da be ta6a experiancing akwai irinta ba, amma yah ya iya akan son zuciyar shi bazai iya ya bar Mahmud ya bijire wa maganar mahaifinsa ba, duk da ba wani sanin Abbahn yayi sosai ba amma yasan Abbah bazai ta6a yanke hukuncin da yasan akwai cutarwa aciki ba musamman ga ‘dansa na cikinsa, kuma ma idan yayi la’akari da yanayin da suke zumunci must especially labarin da Mahmud yabashi farkon ha’duwarsu a Damaturu ya tabbata Abbah ba zai rasa dalilin da ya sa ya za6i hakan ba.

” Laifina ne, nasani laifina ne da ban bayyana kudurina akanta tun farko ba, na ri’ke abuna acikin raina, ina can ina tunanin yaushe ya kamata na mallaketa!, yaushe zata zamo tawa!!, bansani ba ashe BURINAH da mafarkina bazasu ta6a tabbata ba.

” Amma duk da haka bazan iya barin ka acikin wannan yanayin ba, Mahmud ko ba komai kai abokina ne.

Duk acikin zuciyarsa yake wannan tunanin.
Dan a yanayin da yaga Mahmud ‘din sosai ya tausaya masa alamu sunnuna ‘karara shi be yi na’am da wannan ha’din ba.

Da ‘kyar yasamu ya bud’i bakinsa yafara magana

” kayi hakuri Mahmud kasan Abbah yana sonka bazai ta6a ha’da ka da abinda ba dai dai bane agareka, ka daure ka ya’ki zuciyarka kayi masa biyayya na tabbata zaka ga ribarsa wata rana, ko ba komai iyaye abin girmamawa ne nasan kasan wannan, kuma shi aure ba yana nufin tashin hankali bane, Mahmud aure rahama ne, sannan ibada ne, cikon addini ne. Ni agani na Abbah gata yayi maka tunda har yayi maka za6in matar aure da kansa, kuma ma ai kaga Fatima yarinya ce, kasanta, kasan kalar tarbiyyarta ,kasan damuwarta farin cikinta da ba’kin cikinta kaga baka da matsala da wannan kamar yadda nasan bazaka samu problem da ita ba. Idaan kuma batun *so* ne, na tabbata ahankali zaka so ta basai an ‘dauki wani dogon lokaci ba,insha Allahu baza ‘a samu matsala ba musamman inkayi la’akari da sanayya da kuma shakuwar dake tsakaninku, inkuma kana tunanin ba ita kake so ba wacce kake so daban, Mahmud ai kai namiji ne kana da damar dazaka auri mata daga ‘daya zuwa hu’du inkaga zaka iya”

Muryar Abbas har rawa takeyi da ‘kyar yasamu yah dasa ayar maganar tasa tare da numfasawa duk a’ko’karinsa naganin ya taushi Mahmud ‘din.

Da ‘kyar yasamu Mahmud ya sau’ko ya ‘dan kwantar da hankalinsa daga ‘karshe bedroom ‘din Abbas ya shige shima ya watsa ruwa sannan yazo ya kwanta, cikin sa’a kuwa yana kwanciya bacci ya ‘dauke sa.

Se bayan shigan Mahmud ciki kafin Abbas yasamu ya mi’ke akan 3seatern shi fuskan shi na kallon ceilling yayin da ya tsurawa ceilling fan ‘din dake juyawa asaman idanunsa, hannun sa yasa ya dafe saitin zuciyarsa dayake jin yana harbawa da ‘karfin gaske, daga ‘karshe lumshe idanunsa yayi ahankali, wani abu yakeji ya tokare masa ‘kirji wani abu da besan mene ba ke damunsa ba, ehh mana be sani ba shin nauyin da yake ji azuciyar san na son Fatima ne ko kuma na ba’kin cikin rabuwa da ita neh.

Be ta6a tunanin irin wannan abin zai iya zuwa ya yanke masa kyakkyawar ala’kar da zuciyarsa ta ‘kulla tsakaninsa da Fatima ba.

Jijjiga kansa yayi ahankali kamar da wani yake hira akwancen acikin zuciyarsa yace ” ina son…ki..Fati….amma ga dukkan alamu yanzun kinmin nisa”.

Bu’de idanunsa yayi sanadiyyar sallama da kuma ‘karan ‘kofa dayaji alamun anbu’de anshigo.

Hannah ce yagani tsaye ajikin ‘kofan tamkar tana tsoron shigowa, daya ga haka sai ya maida idanunsa ya kuma rufesu kamar yanda suke da farko batare da ya kula. Ko kuma amsa sallamar tata ba.

Itan ma data ga haka sai tace masa
” Ummah ce tace in zo in duba ka wai tajika shiru”.

Baifi tsayuwar second biyar tayi ba bayan tayi maganan sai ta juya takoma inda ta fito, domin tasan Yayan nata ba magana zai yi mata ba shiyasa ma ta juya batare da ta jira amsa daga gareshi ba.

Kamar be ji me tace dashi ba ,sai can sai ya yun’kura ya tashi tare da saka takalmansa yafita a’dakin.

Parlourn Ummah ya nufah inda ya sameta zaune akan kujera me zaman mutum uku Hannah ma na zaune agefenta.

Ciki-ciki yayi sallama sai suka amsa dukkansu atare suna masu maida hankulansu gareshi saboda yanayinsa daya canju.

Agefe dasu ya zauna sai ya gaida Ummahn nasa tare dayi mata barka da yamma, ita kuwa a gaggauce ta amsa domin damuwa data gani ‘karara a fuskan Abbas ‘din harma da muryarsa ga idanunsa da suka yi jajir suma.

Hannah ce ta tashi ta bar ‘dakin Ummah ma bata lura da ita ba sanda ta fitan domin hankalinta nakan Abbas alokacin.

” me yafaru ne Abbas ko de kana bacci Hannah ta taso da kai,”

Be yi magana ba sai ita ce tacigaba da cewa “ka ganka kuwa, meke damunka ne pls?”

Lumshe idanunsa yayi ahankali koda ya bu’de kuwa sai ya sau’ke su akan fuskan Ummah.

Tasowa yayi ya dawo kujeran da take zaunen inda Hannah ta tashi, koda ya zauna ‘din kuwa sai ya zamo ya kwanta tare dayin matashi da cinyar Ummahn, ita kuwa sai binshi takeyi da kallo tana mamakin sa.

“Abbas meke damunka ne wai “
Tasake maimaita tambayar tata akaro na biyu tare da ‘dora hannunta akan sa.

Ahankali yace
” Ummah Abbahn Mahmud yace wai aure zaiyi masa!”.

‘Kwafah tayi tana kallonsa kana tace
” haba Abbas shine kuma kabi ka ‘daga hankalin ka dan Mahmud zaiyi aure”?

” Mahmud baya son auren fah Ummah, kuma ma wai kwanan nan za’a yi auren gashi can duk ya bi ya ‘daga hankalinsa akan maganar da kyar nasamu ya sau’ko Ummah”.

Daga nan yayi shiru domin daman da ‘kyar yake maganar daurewa kawai yayi, in baka sani ba zaka zaton damuwar da Mahmud yake ciki ce shima ta dame shi amma ga wanda yasani kuma sai de yace…….🤔( me za’ace)? _Ni de nace_ _Allah sarki bawan_ _Allah_ .

*ABUJA*

Fa’da Ummah tafara yiwa Abbas atsanake inda take cewa ” wato na fahimci dukkanku ra’ayi ‘daya gareku ko Abbas?
Gaba ‘daya sai kuka ha’du kuka ‘daga hankulanku akan batun aure kawai,! saboda Allah me hakan ke nufi kenan? abin mamaki ma se kace wasu yara ‘kanana, dube ka fah yanda ka koma kaima kenan inaga shi uban gayyar kuma? kaida ya kamata ace ka bashi baki ya amince sai kuma ka tayashi shiga damuwa wannan ai shirme ne Abbas, daga kai har Mahmud ‘dinma ni bansan lokacin dazaku girma ba wallahi, ace dan abokinka zaiyi aure kazama haka toh in kaine kuma ai Allah ne ka’dai yasan ya zakayi…….. hakan da kuke yi fah bakomai yake ‘karawa ba illah ‘kara fito da zallar ‘kiyayyar da kuke yiwa aure”

Baki ta kama tace “anya ma lafiyarku qalau kuwa Babana”.

Shiru yayi mata be bata amsa ba.
aransa yake cewa ” lafiyar mu ‘kalau Ummah ,bazaki gane bane!
kowa na tashi damuwar daga ni har Mahmud ‘din, ni ita nakeso ina sonta sosai Ummah fiyeh da kaina, amma yanzu kam dole na ha’kura da ita domin tayi min nisan da bazan iya kamota ba har abada, da ace ba Mahmud bane da wallahi babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da Fatima ko ma waye shi sai inda ‘karfina ya ‘kare, amma Mahmud kam dole na ha’kura inba zuciyata ha’kuri domin shi mutun ne, mutum ne da kowa zaiyi alfaharin kasancewar sa atare dashi, bazanso akan mace ala’kata dashi ta rushe ba, da irin wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi akan cinyar Ummahn daman aikin sa kenan idan yadawo gida sai de yayi ta bacci wani lokaci sallah ce ka’dai ke tada shi yana idarwa kuwa zai koma, amma idan yana bakin aikinsa kuwa kusan mantawa ma yakeyi da batun bacci arayuwarsa koda yake yanzun ma zuwan Mahmud ne ya tada shi abaccin kuma badan zuwan Mahmud ‘din ba da zai ‘dan ‘dauki lokaci yana bacci abinsa.

Ita kuwa Ummansa idanu ta zuba mishi kawai tana ‘kara mamakin hali irin na sa, shi baya son ace yayi aure sannan kuma ance abokin sa zaiyi nan ma kuma sai duk sauka ha’du suka ‘daga hankulansu, ” kai yarannan kuna da abin mamaki, Allah dai yakawo muku abokan zama nagari”.(Ameen).

Washegari Abbas da Mahmud tare suka fita daga gida bayan Ummah ta ha’da su tayi musu nasiha sosai daganan ta sallame su suka tafi kowa ya nufi inda zashi, bayan Abbas ya sake ‘karfafa wa Mahmud gwiwa akan maganar daya zo da itan tare da jaddada masa muhimmancin bin maganar iyaye kamar yadda Ummah tayi musu.

Haka suka rabu Mahmud na yiwa Abbas ‘din godiya da kuma fatan alkhairi domin zuwa yanzun Alhamdulillah ya ji dama-dama a zuciyar sa, he is now ready to face his reality.

*DAMATURU*

Daddyn Teemah be bari mummy ta sanar da ita ba shine dakansa ya zaunar da ita yayi mata bayani yanda yasan zata fi fahimta, itanma da farko ta ‘dan ji tashin hankali amma aranta, dayake bawani zama takeyi ta fahimci me zuciyarta take ciki ba shiyasa takasa gane inda nutsuwarta ta dosa akan maganar daddyn.

Ji takeyi tamkar tayi na’am da maganar amma deep down tana jin kamar kuma bata aikata daidai ba.

Daddy kuwa kafin su rabu sai da ya tabbatar da cewa ta amince da maganar 100% kafin hankalinsa ya kwanta, daman damuwarsa kenan shine kar Fatiman ta’ki amincewa duk da yana ganin kamar wayo be gama isanta ba kuma hakan bazai barta ta kasa amincewa da maganarsa ba, amma ‘dan adam sai Allah, kowa nada nashi kalan burin arayuwarsa.

Story continues below


Har Daddy suka gama maganar su da Teemah mummy bata saka musu baki ba, ita abubuwa ne suka taru suka yi mata yawa azuci, tunda ranar da akayi maganar auren nan mummy bata sake yin baccin kirki ba, tausayin ‘yarta ta yawa yake yi mata ta fuskoki da dama.

Babban damuwarta shine yanda Anty zata kar6i batun nan, tasan da wahala ta yadda da auren, idan ma ta yadda ‘din toh wani irin zama zatayi da Fatiman. 

Sannan secondly alamu da yawa sunnuna cewa tun ba yau ba Teemah ta fara son Abbas, she can proof that Zuciyar Fatima Abbas takeso, amma rashin wayo irin nata yasa takasa bambance abinda takeso harma gashi ta amsawa mahaifinta cewa ta amince da auren Mahmud.
Yanzu kam mummy ta saduda ta barwa Allah komai ” bani da abin cewa nikam ayanzu sai de nayi ta miki addu’ar Allah ya tabbatar da alkhairi aryuwarki”.

Teemah sai da ta koma ‘daki sannan ta fara fahimtar yanayinta, jin ta tayi  wata iri, kaf sai ta nemi nutsuwa azuciyarta ta rasa sai asannan taji tamkar bata yiwa kanta adalci ba.

Fa’dawa tayi rigingine akan gadonta abun duniya duk sun taru sun mata yawa, Abbas ne ya fa’do ranta karo guda sai taji zuciyarta ta tsinke da ‘karfin gaske, har sai da ta rintse idanunta ta kuma dafe ‘kirjinta da hannunta.

Daga nan abubuwan da suka faru atsakanin su suka rin’ka dawo mata ‘daya bayan ‘daya……
Yah Abbas…..Rashin fara’arsa……Muguntarsa….Masifarsa….
Komai ma nashi yaringa dawo mata azuciya, juyi tayi zuwa ‘dayan 6angaren yayin da ta tuno lokacin da Mahmud ya zo gidan su, basu wani ‘dau lokaci ba suka saba da juna sa6anin Abbas da alokacin ma kullum sai sunyi fa’da dashi.

Tashi tayi ta zauna abakin gadon ta cigaba da tunani haka kawai batare da tasan dalili ba taji zuciyarta tana mata comparing halayyar Abbas da Mahmud amma kwata-kwata ta kasa samun laifin Mahmud aranta ko ‘daya sai de duk da haka zuciyarta takasa nutsuwa da maganar da suka gama da mahaifinta lokuta ‘kalilan da suka gabata, sai take jin ma dama ba Yah Mahmud daddy ya za6a mata da sunan ta aura ba.

Tashi tayi da gaggawa kamar wacce aka bawa umarni ta nufi wurin ajiyan kayanta sanadiyyar tuno wani abu da tayi, bincike tafarayi acikin kayan inda ta ringa ciro kayan da ‘da’dd’aya tana zubo dasu ‘kasa sai da  ta ciro kusan rabi daga cikin kayan nata kafin ta samu abinda take nema ‘din.

Da sauri ta tattara ta dawo ‘kasa akan tiles ta zubasu itama ta zauna dirshan agabansu.

‘Ko’karin ha’da papers ‘din takeyi amma har yanzu ta kasa ha’dasu, haushi hakan ya bata dan ayanzu damuwarta be wuce tasan miye acikin takardan ba da tun ranar daya batan takardan ta lalace da gumi, tun ranar taji ba’kin cikin rashin ganin abinda ta kardan ta ‘kunsa ga dai alamun rubutun da akayi da biro tana gani amma gane ko menene sam ya gagare ta. 

Ko ta ‘dan harha’da sai taga beyi yadda take so ‘din ba ga dukkan alamu guri me muhimmancin ne ya fi ji’kuwa tun awancen ranar.

Haushin bazata ta6a ganewan ba yasata ta dun’kula su tayi jifa dashi kamar zatayi kuka.

Tana watsarwan kuwa sai tajiyo muryar mummy ta ‘kira sunanta tare da ‘karasowa cikin ‘dakin nata ahankali.

Tana ganin mummyn sai taji hawaye ya gangaro mata da bata san dalilinsa ba, tahowa tayi da sauri ta rungumo mummyn  suka zauna abakin gado.

Fatima bata sani ba ashe tun fara binciko kayan da Teeman tayi mummy ke tsaye tana kallon ta dama so take taji asalin ra’ayin ta akan maganar, koda tazo tasameta awancan halin kuwa sai ta tsaya karantar yanayinta tayi zaton ko wani abin ne daban yake faruwa , and now she’s crying.

Sai da ta yi kukanta kusan na mintina biyu kafin nan mummy ta ‘dagota daga jikinta, atsare tasa ta tayi shiru kana tace tasanar da ita meke damunta, menene yasata kuka.

Ido mummy ta zuba mata tana karantar yanayinta da kyau, yayin da Teemah ta maida kanta ‘kasa kamar me jin kunyar ha’da idanu da mummyn sai kawai taci gaba da tsiyayar da hawaye, hawayen ma da sauri suke 6ul6ulowa dan koda mummy tayi ‘ko’karin goge mata ma kasa tsayuwa suka yi dolenta ta barta .

Sai da tasake maimaita tambayar tata kafin ahankali Teemah ta ‘dago tace da ita ” kirjina zafi yake min mummy” 
“Miye dalili” mummyn ta tambayeta. 

Hannu ta ‘dago ta ‘dora akan kirjin nata sannan taci gaba da fa’din ” mummy dagaske daddy yakeyi wai aure zai min?”

” miye saki zafin ‘kirjin “
mummyn tasake tambayarta maimakon ta bata amsar tambayar da Teemahn tayi mata.

Sai tace itama bata sani ba, kawai de tana jin kamar bata son auren ne. 

” bakya son auren ko kuma Mahmud ‘din ne bakyaso”?
Mummyn tasake tambayarta idanunta kafe akan Teemah. 

” Nima fah bansani ba mummy nide kawai zafin nakeji a ‘kirjina”.

Shiru sukayi dukkansu na ‘dan wasu da’kiku sai mummyn tace mata ta share hawayenta kukan ya isa haka.

Tambayarta mummy tasakeyi wai “meyasa ta amince wa mahaifinnata bayan tasan bataso.

Goge hawayen tayi kamar yadda mummy ta bu’kata, amma kuma game da tambayar sai ta rasa amsar dazata bawa mummyn dan  haka kawai sai tayi shiru. 

Ganin hakan da Teemah tayi tasan zaiyi wahala tasamu jin amsarta dan haka sai ta juya ta kallo cikin ‘dakin inda Teemah ta zauna ‘dazu.
” wa’dancan ‘kananun papers ‘din fah na menene su kuma”?

Juyawa Teema tayi ta kallo inda suke itama batare data yi niyyan fa’din komai game dasu ba.

Fahimtar da mummy tayi cewa Teemahn bata da niyyan sanar da ita sai kawai ta mi’ke tsaye tace ” inkin gama kisame ni apalour ina jiranki.” 

Da kai Teemah ta amsa mata daga nan takama hanyar waje.

Binta da idanu Teemah tayi harta 6acewa ganinta, daganan ta tashi sai ta nufi gurin data watsar da pieces ‘din takaddun, ta tattare su gaba ‘daya ta maida su can ‘kar’kashin jerin kayan da suka rage bata wargaza ba.

Tana ‘kokarin fara gyara kayan sai ga Baabah Lami ta shigo da sallamarta tace “Hajiyarki tace kayanki sun zubo ” 

Kai ta ‘daga alamar “ehh” sannan ta matsa daga gurin kayan ta nufi hanyar bayi domin ta watsa ruwa dayake daman bata yi wanka ba lokacin da daddy yakirata.

Daga ita sai towel tafito abayin, yayin da tabaro kayan data cire abayin domin wanki suke bu’kata.

Fitowarta kuwa keda wuya Baabah Lami ta jefa mata tambayar wai yau kuwa lafiyarta ? 

“Uum lafiya ta ‘kalau me kika gani”?
tayi maganar tana ‘ko’karin goge fuskarta da wani ‘dan ‘karamin wiper dake ri’ke ahannunta na dama .

Baabah Lami shiru tayi taci gaba da gyaran kayan da takeyi, Teemah kuma sai ta wuce gaban madubi ta sake duba yananyin fuskarta daganan ta dawo inda kayan tan suke zube aciki tasamu wanda zata sanya sai ta koma ‘daya 6angaren da tuntuni arufe yake ta bu’de shi ,bakomai aciki illah tarkacen inners ‘dinta dasuke kala kala.

Zura doguwar rigarta tayi bayan tasaka ta saka bra da pant ko kunyar Baabah Lami ma bata ji ba tayi shirinta abinta, tana gamawa kuwa ta zari mayafi ta fice a’dakin tare da cewa Baabah Lami ” ina zuwa”
ta nufi gurin mummy.

Tana isa gurin mummyn ko gama daidai ta zamanta bata yi ba mummyn tace ” yanzun muka gama waya da Abbas yace wai agaisheki”

Murmushi ne ya kubce mata har sanda ha’kwaranta suka ‘dan bayyana afili.


Har bata san lokacin da tace
“Kuma mummy dakansa yace agai sheni?
kai mummy ta ‘daga mata, sai ta sake cewa ” lallai Yah Abbas sai yau yaga dama ya tuna dani kenan” 

“Da in cemiki akayi ya manta dake ne?

” ya manta dani mana mummy “!
Teemah ta bawa mummy amsar tambayarta.

Mummy bata ‘kara kulata ba sai de afakaice take ‘kara kula da yanayin ta saboda murmushin da tayi tun ‘dazun yakasa barin kan fuskarta harma sai ya 6oye damuwar da take ciki ‘dan lokuta ka’dan da suka gabata.

Tausayi Teemahn take bawa mummy  sosai zuwan yanzu ta gama harbo jirgin ‘yartata sai de ga dukkan alamu ita kanta bata san me take ciki ba har yanzu, shiyasa kawai zataci gaba ro’kon Allah akan ya takaita mata yabar abin a lullu6e kamar yadda Teemahn bata gane ba Allah yasa yatafi a hakan har abada, domin matu’kar Teemah ta fara gane bambancin soyayyar ‘yan uwan taka da kuma soyayyah me zaman kanta (ta aure) tasan za’a samu matsala ne,fatan ta de Allah yasa har ayi agama lafiya kar asamu problem ‘din komai, tunda aure ma zatayi ai shikenan.

Domin indai Abbas ne tana ganin da kamar wuya, ko yanzun ma babu wani gaida ta da yace yanayi, ita ce mummyn dakanta tabashi labarin abin da ke faruwa a gidannasu kuma ko da ta fa’da masan ma bata wani ji alamun canji atattare dashi ba ko daga muryarsa har yanayinsa, da suka gama wayanne suna sallama sai yace”  agaida mutan gidan ” shine ita kuma mummy tace da ita Abbas na gaidata kuma tafa’di hakanne saboda mitan da Teeman keyi wasu lokuta akan cewa Yah Abbas ya manta da ita. 

Acikin satin aka gama maganar auren Teemah harma aka sa rana sati hu’du masu zuwa.

Daddyn Teemah dakansa ya yanke wannan lokacin domin yana ganin adaidai wannan lokacin zai fi dacewa ayi bikin batare da kowa ya takura ba.

Mummy bata so hakan ba domin ita aganinta lokacin yayi kusa bata so aka yanke lokacin kwana kusa haka ba, koda ta yiwa Daddy maganar ma sai yace mata “kar ta damu ai komai lokaci ne, ba gaggawa sukayi ba wata ‘kila haka Allah ya riga ya tsara lokacin bikin Fatiman yace kinga kuwa mu bamu isa muja da ikon Allah ba”.

Dolen mummy taja baki tayi shiru, 6angare guda kuwa hankalinta yakasa kwanciya sam da wannan auren.Yayin da daddy shikam ba ruwansa, kusan kullum idan ya zauna sai dai kaji yana waya ya sanar da cewa lokaci kaza ne bikin Fatima ‘yar wajensa, acikin lokaci ‘kalilan kusan mafi yawa daga 6angarensa sun san da labarin auren kama daga kan abokansa har ‘yan uwa da dangi ma duk ya sanar dasu.


‘Bangaren Anty kusan hauka taso tayi akan wannan maganar gaba ‘daya ta hana kowa sukuni agidan, gajiya Abbah yayi da halintan datakeyi musu akan auren, wani lokaci ya tanka mata ai kuwa kamar jira ta keyi, shi dama mahaukaci yafi so idan yana abinsa yasamu mataimaki, daga nan haukar Anty ya ‘karu daddy ma ranshi ya 6aci sosai musamman yanda take ha’da ilahirin zuri’arsa ta zagesu kaf abin na masa ciwo sosai, amma sai ya lallashi zuciyar sa ya samu ya ‘dan sassauto domin ji yake a ranar kamar yayiwa Antyn dukan tsiya, amma yasan haka bazai ta6a kawo gyara ba, zagi kuwa har sai da yaji kamar ya toshe kunnuwansa, munafukai takirasu yafi sau a’kirga, shikuwa yariga yayi alwashin ganin faruwar wannan auren yace ko ma miye zai faru sai dai ya faru amma shi kan be ga me hana shi ‘daurawa Mahmud aure ba , mahmud dama ba ya gida tun dawowarsa daga wurin Abbas be fiya zama agida ba, wani lokaci arana sau ‘daya Abbah ke kallonsa amma hakan ba damunsa yakeba, tunda dai be musa masa cewa bayaso ba ai toh “Alhamdulillah zai sau’ko ne idan ma fushi yayi.

Story continues below


Da abin Anty yayi yawa ne sai Abbah ya yanke shawarar sanar da mahaifinta halin da ake ciki, beyi ‘kasa agwi wa ba ya shirya yatafi kano musamman ya je domin yakai ‘karanta agurin mahaifinta Alhaji Muhammad, abinda be ta6a faruwa ba kenan tun farkon auren su sai awannan lokacin.

Yanzun ma yaga abin nata yayi yawa ne shiyasa, dan ko kunya bataji ballantana tsoron Allah take furta maganganu marasa kan gado ciki harda alwashin kisa akan wai inhar suka yadda auren nan yayiwu.

Ran Alhaji Muhammad ba ‘karamin 6aci yayi ba da yaji abinda Abbahn yagama zayyano masa, tun ma kafin Abbah yabar wurin yafara masifah yana nunawa mahaifiyarta illar rashin hankali da kuma 6ata rayuwa da halayyan yaro tun bai je ko’ina ba, yace wannan rashin hankali har ina, maimakon Abbah da za’a bawa ha’kuri sai ya zamana shine ke bawa Alhaji ha’kuri gashi girma ya kamashi yanzun sosai harma baya fita harkan kasuwancinsa sai de a jagoranceshi,maganar ma da ‘kyar yake fizgota yakeyi tsabar ranshi daya 6aci da Antyn.

Da ‘kyar suka samu ya sau’ko daga dokin fushin da ya hau, mahaifiyar Anty har sai da hawayen ta ya ‘diga tsabar yanda taji hankalinta ya tashi domin fa’dan Alhajin kakaf kanta ya tattara ya dawo afa’darsa wai ai duk laifin tane.

Koda Alhajin ya sau’ko sai ya bawa Abbah ha’kuri sosai tare da cemishi idan yakoma yaturota tazo yace mata yana nemanta inda hali ma su dawo tare.

“Abbah yace bakomai za’ayi kamar yadda ya keso”  

Alhaji Mahammad yayi yayi da Abbah akan ya ‘dan kwana musu biyu amma Abbah ya’ki amincewa yace yana so ne yaje yaga ‘yan uwan mahaifinsu”

Alhaji Muhammad dayaji haka sai ya washe baki yace ” ai babu komai hakanma yayi, yace daman ma yanaso ya tambayeshi ko yajeshi ‘din ashe ma abin nacikin ransa, Sai Alhajin ya ‘kara jan hankalin Abbah akan kyautata mu’amala da kuma ri’ke zumunchi yace zumunchi ba’abin yarwa bane akula da ita sosai..

Fatan alkhairi yayi masa shi Alhajin daga nan Abbah ma yayi musu sallama  yafita agidan yana me ‘kara yiwa Alhajin godiya tare da yi musu alkhairi sannan yayi tafiyarsa.

A waya sanar da Anty sa’kon mahaifin nata inda ya ‘kara da fa’din ” nan da kwana biyu tasamu ta je domin yace karta 6ata lokaci” 

Batayi magana ba illah wani dogon tsaki da ta ja sannan ta kashe wayan, Abbah kuwa be damu da yanda tayin ba dan shi fiye da hakan ma yasan zata aikata, transfern ku’di yayi mata a account ‘din ta kafin ya maida wayar cikin aljihunsa wanda
yasan zai isheta duk wani shige da ficenta har taje ta dawo.

Koda Abbah ya isa gurin ‘yan uwan mahaifinsa sun yi farin ciki da zuwansa sosai, ‘dai ‘dai ku daga cikin su ma sun rasu yayinda ma’danda suke rayen ma duk ‘karfin su yakasa ayanzun, wasun da suka rasu Abbah yanada labari wasu kuwa be sani ba sam dan ba wani communication sosai ne atsakaninsu ba, tausayinsu yakeji sosai duk ‘kinsu dasukayi abaya be damu ba yasan ko ada ‘din ma ba laifinsu bane giyar talauci ce tasa su sukayi yadda suyi rayuwa dasu.

Sai ya ha’da yayi musu ta’aziya gaba ‘daya yakuma yi wa iyalansu kyaututtuka sosai wanda zata anfane su tareda wa’dan da  suka rage arayen daga yayu da ‘kannen mahaifin nasa dukka ya ha’da yayi musu alkhairi.

Da ya sanar dasu ma batun auren Mahmud ne yatashi sunnuna farin cikin su sosai harma da dama daga cikin su suka rin’ka zubda hawaye suna masu neman yafiya daga gurin Abbah akan abinda suka aikata musu abaya.

Shima kusan kukan suka saka shi domin idan yagansu akowani lokaci tunowa yakeyi da mahaifinsa amma dole ya daure ya hana nashi kukan tasiri ya ta basu baki yana nuna musu cewa ai tuntuni komai yawuce shi agurinsa be ri’ke su a zuciya ba komai yafaru ai mu’kaddari ne kuma rubutacce ne awajen mahallici.

Kwanan sa uku tare da dangin mahaifin nasu kafin Anty ta iso wai a hakan ma sai da Abbah yayi mata ‘karyan a kwana biyu mahaifinnata ke nemanta amma duk da haka sai da ta ‘kara akan yanda ya sanar da itan.

Be tafi aranar ba sai washe gari sannan yayi sallama da kowa yakama hanya.

Alhaji fa’da yayi wa Anty sosai harma ya jajjada mata cewa matu’kar tace bazata kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan aurenta ba toh kar tayi tunanin tana da mahaifi aduniyan nan. 

Yace kuma datake wani borin hana auren bata tunanin cewa shi Mahmud ‘din da ita ‘yar gidan Khadijan sun fi kusa akan wata daban da takeso ‘dan tan ya aura, yace wata daban ‘din ma girman cikin garin lagos. 

Shi aure mu’kaddari ne kuma lokaci ne, idan Allah ya riga ya tsara abu toh babu wanda ya isa ya canja shi, sannan ba’a jayayya da qaddarar ubangiji koma ayaya tazo maka u must have to accept it, karta bari shai’dan yayi galaba akanta akan abun da ba ita keda ikon sawa ko hana yiwuwarshi ba, yace da ace son ran mutun ne dashi dakansa bazai barta ta auri Yusuf alokutan baya ba saboda yasan halinsu da bambamci , amma miye dayake Allah yariga ya rubuta sai sunyi auren yace bagashi ba , ni ban isa na hana ba, kamar yadda kema kika yi ka’dan ki hana dan haka tun wuri ki maida hanakalinki ki san me kike ciki, idan har kika kuskura na ‘kara jin kinyi irin abu makamanciyar wanda naji ayanzu toh wallahi Maryam kisani zamu raba ala’ka dake ,saboda ni kinga ban aurar dake ga wannan bawan Allahn dan ki ta ‘daga masa hankali ba, yace wallahi da yasan abinda zata aikata kenan ma da tun farko ba zai amince da batun auran ba, amma bakomai wannan duk cikin ‘kaddara ne kuma babu wanda ya isa ya gujewa tasa ‘kaddarar matu’kar tazo.

Da nasiha ya kammala maganar tasa ga dukkansu tare da ‘kara bawa Abbah ha’kuri yace ya ‘kara akan wanda yayi tayi abaya.

Godiya Abbah yayi masa daga nan suna idar da sallahr azahar ya kama hanya ya koma lagos.

Anty kuwa kusan Satin ta ‘daya a kano bayan komawan Abbah, duk da bawani da’din zaman takeji ba amma wani lokaci takanji cewa zama agidan yafi mata wai ko zata hita da taahin hankali, gashi tana ji tana gani abu na nema yafi ‘karfinta abanza kuma takasa ‘daukan mataki.

Kuma ako wacce wayewar gari sai mahaifinta yayi mata nasiha sosai cikin natsuwa akan rayuwar duniya iya yanda yasan zata fahimceshi, ita kanta mahaifiyar tanma yanzu ba kamar da ba, dayake girma yakama ta itama kuma sai tayi sa’a yazo mata da shiriya, wani lokaci takanji tamkar tayi kuka dan ba’kin cikin halin da akace ‘yarta nayi, domin tasan komai akace maryam ‘din tayi laifinta ne komai da aka ‘kirga awurinta ta koya sai dai yanzu tanaji tamkar maryam ‘din tafi ‘karfinta tama kusan nunka mugun halin data koya agurin mahaifiyarta ‘din.

Itama sosai take zaunar da Antyn duk dama bata fiya sauraranta ba domin ba ‘karamin raina mahaifiyartan tayi ba, gara ma shi Alhaji tana ‘dan jin shakkan shi hakan yasa dole take zama ta saurare shi ko bata so ko da ba zata ‘dauki abinda yake fa’da ‘din ba amma dai zata zauna dolenta, tsawon lokaci tana sauraran karatun nasa batare da ta ‘dauki koda abu guda daga ciki ba.

Abinda basu sani ba ayanzun shine, Anty bata da burin daya wuche taji ance babu wannan maganar auren.

Tsana mafi girma take ji azuciyarta game da auren, tana jin koda me nene ze faru sai ta ga ta hana wannan auran faruwa.

Duk da yawan nasihar da Alhaji muhammad ke mata amma dai dai da rana ‘daya tak sam
‘Kudurin Anty be canja ba daga cikin ‘kudurorinta na baya sai ma abinda ya ‘karu domin ‘karan tan da Abbah ya kawo bai gyara komai ba sai ma lalata wa dayayi.
Abu ‘daya ke cin zuciyar Anty akoda yaushe in ta tuna shi kuma shine yafi sata damuwa fiye ma da batun auren Mahmud ‘din haushin hakan kuma shike ‘kara sata takae jin haushin kowa,dan tasan batun aure me sau’ki ne matu’kar tasamu ta ziyarchi gidan _’dan_ _Oga_ (boka) tasan matu’kar ta samu ta ha’du da shi to bata da sauran damuwa. 

Amma prolem ‘dine taya zata ha’du dashi?
Mtsalar ka’dai dake cinta kenan har azuciyarta, ita aganinta maganar auren nan dasuke ta wani 6ata bakinsu akai arana ‘daya zata iya warware shi kaf kuma waru kenan, da ace ta ‘dau mataki toh da dolen kowa ya ha’kura da maganar auren amma kuma sai tayi rashin sa’a ‘kawarta Anty Chideh ta’ki sam ta  taimaka mata akan lamarin, sai ma wasu banzayen sharu’d’da datake faman gindaya akai  kafin wai tayi mata jagora zuwa wajen _’dan Ogahn_ itakuwa sam bazata iya abinda Anty chiden take ‘ko’karin taga ta aikata ba, akullum tunaninta yanda zata samo mafita ne amma taras,shi ‘din nan dai tafi yadda da aikinsa sai dai ta rasa yadda zatayi tunda ‘kawarta ta’ki kaita , tambaya kuwa babu irin wanda batayi ba amma tarasa wanda yasan shima balle ‘kauyen dayake rayuwa.
Idan ta matsa sai akwatanta mata wani wuri daban , da zumu’din ta take zuwa amma kamar ha’din baki kalaman su iri ‘daya ne.

Akwai wani guri da suka je da wata ‘kawarta, bokan ce musu yayi wannan auren babu fashi sai anyi, the same abinda wata matsafiya ta gaya musu da suka je da mahaifiyar Munira harma da ita kanta Muniran.
Anty kamar zatayi hauka dataji abinda suke ta faman sanar dasu. 

Inta matsa wai ko za’a samu wata hanya da za’a awarware maganar takance ita ko nawa ne she is ready to pay it indai auran zai fasu.
Akwai wani bokan dayace mata ehh akwai dama za’a iya warware maganar amma ba ku’di zata biya ba zata tattaro ta dawo gurin na tsawon wata guda akwai aikin daza’a yi.

Sam sai taji zuciyarta be yi na’am da wannan batun ba, auren da ake ‘ko’arin yinsa nanda sati uku masu zuwa taya ya itakuma za’a ce tayi 1month tare dasu da yaushe kenan za’a warware maganar, bayan an ‘daura kokuwa? 
Bata manta labarin da Chide ‘kawarta ta bata ba na wani daya ta6a yi  mata aiki tace satin ta guda agurinshi yana faman sex da ita ba ‘ka’k’kautawa sai cewa yayi wai suna ‘diban abinda zasu ha’da jinin tane da mijin nata alokacin, itakuwa dayake ta ‘kagu taga ta malleka shi sai bata damu ba ta daure tayi ta jure wahalhalun da bokan ke bata, tace har tacika satin ana abu ‘daya, tace data koma gida sai da tayi jinya kusan na. 11days kafin nan ta warware, atlast ma kuma bata ga komai ya canja ba babi wani abinda ya faru sai da ta je gurin wani daban kafin nan tayi sa’a aikin ta yaci.

Tace ballantana ita da ba mallaka ko juyo da hankalin wani take bu’kata ba ayanzun burinta ta warware maganar ne toh dan me zata tattaro ta dawo gurin boka har na tsawon wata guda, yana nufin ita ma so yake yayi mata irin na ‘kawarta kenan Allah ya kiyaye tace afili, _angudu ba’a_ _tsira ba kenan_ .


‘Kin amincewa tayi kawai tayi tafiyarta.

Dama agurin Anty chiden take da hope ‘din samun ingantaccen wurin da tasan za’a share mata hawaye domin itace tasan gurare da dama acikin garin na lagos, amma kuma shara’din Anty Chidehn tazo mata dashi sai ya girmi tunanin ta, sam bazata iya aikata abinda ‘kawartan ta ke son ta aikata ba, how on earth ace tayi irin wannan abin…. 

Story continues below


Koda ta koma gida (Lagos) ma cigaba tayi da neman mafita amma tarasa ta ina zata fara, kullum hankalinta atashe yake, gaba ‘dayan su agidan ma sai suka rasa gane kanta, Abbah kuwa ko kallo ma bata ishe shi ba, kamar yadda itanma bai isheta kallo ba , zaman gidan tamkar wasu abokan gaba aka tara aciki haka suke yinta kowa harkar dake gabansa kawai yakeyi, Anty ta ‘debi abin ne da zafi ‘karfi dayaji take so taga ta hana abinda Allah bai haramta ba, duk kuwa abinda take yi shiga da fitan ta da wasu abubuwan Abbah kallon ta kawai yakeyi yana mamakin taurin kanta, zai yanzu yake ‘kara jaddada wa kansa rashin sa’ar mata yayi, ha’ki’ka shi kan baiyi sa’a ta wannan 6angaren ba, bayaga haka kan be sa me zai ce ba, Alhaji Muhammad mutumin kirki ne dashi kanshi zai iya bada shaida akan haka, sannan yana da tabbacin Alhaji yaja wa Maryam (Anty) kunne akan haka harma ya ha’da da tabbatar mata cewa matu’kar bata kar6i wannan auren ba toh babu ita babu shi, lokacin da Alhaji Muhammad yayi wannan maganar shikanshi Abbah bai ji da’di domin bazai so ace iyalinsa ta samu matsala da mahaifinta ta dalilinsa ba, yaso yayi magana tun awancan lokacin amma sai yayi tunanin wai ko zata yiwa kanta fa’da da wannan kalmar ta saduda ta barwa Allah ikonsa amma sam sa6anin haka yagani wanda be sani bama sai yace acan ta ‘karo taurin kan da taje, ha’kika duk wanda yayi nisa da wuya yake jin ‘kira koda me ‘kiran ya hau kan babban tsauni ne,sai dai kawai Allah ya shiryamu gaba ‘daya.(yasa mu gane gaskiya gaskiyace kuma yabamu ikon yin aikin da ita).

Shima Abbah babu abinda yasa agaba ayanzu illah yaga anyi auren nan angama shi lafiya ko hankalin kowa zai kwanta.

Abbah da kanshi yasa Mahmud agaba suka je gurin wata matar abokinsa suka yi maganar kayan lefe afa’darsa tunda mata suka suka san kayan mata ‘yan uwansu, transfern ku’di kawai yayi mata masu yawan gaske yace ta ha’da masa lefe nagani afa’da yace baya san algus ko ka’dan aciki saboda yarinyar ma ‘yarsa ce ahaka kawai ma zai iya yi mata ballan tana kuma ace aure ne sanadi kuma auren ‘dan cikinsa zata yi. 

Dariya sukayi masa sannan matar ta bashi tabbacin bashi da matsala da wannan ya kwantar da hankalinsa komai zai yi kamar yanda yake bu’kata, dayake daman tana sarin kaya tace wannan satin zata yi ordern su sauran kuma dole sai anan Nigeria za’a siya.

Godiya yayi mata sosai ,sai abokin nasa yace ” ban ta6a jin inda mahaifin ango yayi kane-kane akan kayan lefe ba……………

“Akaina zaka fara gani Alhaji”
Abbah ya karasa maganar yana dariya.

“Asalin tuwona mai na ‘din kenan Alai yusuf lallai zaka kafa tarihi a ‘kasar nan”.

“Kwarai ma kuwa “.
Abbah ya sake bashi amsa still suna dariya.

Mahmud kam tunda suka zo daga gaisuwa be sakeyin wata magana ba sai kawai ya ciro wayarsa yana danne-danne dayaga sun gama maganar sun koma hira suna dariya sai kawai yatashi ya basu wuri, binsa sukayi da kallo har ya ‘karasa barin ‘dakin.

Alhajin ne ya tambayi Abbah abinda ke damunsa shikuwa Abbah be ‘6oye masa ba yabashi labarin yanda batun auren ya kansance ya ‘karasa da fa’din fushin Mahmud ‘din na rashin son yin aure yanzu ne wai shi ba yanzu zai yi aure ba sai nan gaba , laifina anan shine nace yanzu zaiyi aure shikuma ba haka ya tsara wa rayuwarsa ba shine fushin.”

“Allah sarki yaro kenan, inbanda abinsa ai aure bashi da lokaci”
Inji Alhajin. 

” rabu dashi bazai gane hakan ba ai, amma nasan wataran dakansa zai gode min idan yafahimci banyi hakan dan na ba’kanta masa face gata da nake ‘ko’karin yi masa”. 

Inji matar Alhajin
“Hakane kam”.

Ajiyar zuciya Abbah yayi sannan yace 
” Allah shi kyauta”
Tare da mi’kewa tsaye, Alhajin ma sai ya mike yamasa rakiya har inda sukayi parking motar su .

Mahmud na hango su ya tada motar kmar daman jira yake yaga fitowarsun.

Ahanya ne Mahmud  yake tambayar Abbah wai kayan miye zaa siyo? 

Abbah ce mishi yayi “kayan auren kane!” 

“Toh ni Abbah ya baka siya min ba sai ita ka’dai”

“Abu mai sau’ki ne ai wannan babana idan kanaso zan siya maka kwantar da hankalinka.”

Shiru Mahmud yayi yaci gaba da tu’kinsa har suka isa gida bai sake magana ba.

Mahmud yanzu bashi da abokin hira sai ‘dakinsa da kuma wayar sa, hatta Fatima (wife to be ‘din nasa ma daina kulata yayi tunda akayi maganar auren su sau ‘daya suka yi waya dashi daga nan be sake ‘kiranta ba, haka ita ma bata ‘ta6a ‘daga wayarta ta ‘kira sa ba, ko a chat ma babu me kula ‘dan uwan sa yanzu ko wa harkan gabansa yake yi duk wannan sha’kuwan sun manta da ita.

Wayewar wa ta safiyah ne wanda idan aka lissafa 13days yarage wa bikin Mahmud, sai Abbah ya’kira shi yake sanar dashi cewa ya kamata ya ziyarci Fatima ko da sau ‘daya ne kafin lokaci ya iso, duk dama already sun san junansu kuma akwai fahimta atsakaninsu amma sanayyar dake tsakaninsu ada da na yanzu is totally different, yakamata su’kara fahimtar juna, bai musa wa Abbahn ba take ya amince akan zashi
sai Abbahn yace toh yaje duk lokacin da ya shirya tafiya sai yayi masa magana yace ya bashi nan da 3days.

” toh Abbah” yacewa Abbahn nasa kawai sannan yatashi yatafi.

Bai sake bi takan maganar Abbahn ba kawai ya share yayi zamansa har akayi kwana hu’du babu wani alamar yana da niyyan tafiyar da zaiyi, rana na biyar ne da Abbah yaga shiru sai ya sake yi masa tuni akan maganar tafiyan wanda lokacin yayi dai dai da kwana tara cif yarage wa lokacin da aka saka na ‘daurin aure.

Mahmud ‘kasa yayi da kai tare da shafa gashin kanshi sai yace da Abbahn” ai shi yamanta ma kwata kwata , amma insha Allahu kwanan nan zai shirya yaje shi”, 
” yah kamata kam “.
inji Abbahn ya fa’da lokacin yana ‘ko’karin ‘daukan jaridar dake gabansa yaci gaba da dubawa.


Lokaci nata ‘karatowa yayin da shirye shiryen biki ya kankama aduka 6angarorin guda biyu, koda yake a6angaren Mahmud Abbah ka’dai ne ke ta faman shirin sa, yayinda Anty kam ko oho bata damu ba kallonsu kawai takeyi.

Mummy kuwa busy take ako da yaushe bata samun lokacin kanta ‘ko’karinta taga komai yatafi yanda yakamata, duk wani abu datasan hakkin ta ne aiwatar dashi toh bata natsuwa sai taga ta sau’ke shi, sai dai har yau takasa yiwa Teemahn koda abu ‘daya ne daya danganci gyara da ake yiwa amare rasa ta ina ma zata fara tayi ,daga ‘karshe sai ta yanke shawaran barinta ayadda take kawai ta cire wannan a lissafinta, ta daiyi ‘ko’karin tanadar mata duk wasu abu na gyaran fata da gyaran jiki kuma ta tsaya tsayin daka dan ganin komai na tafiya dai dai.

Ummah (mahaifiyar Abbas) ce ma tayi mata maganan wai ko ta ha’dawa Teemahn kayan mata dan taga wasun sukan yi wa ‘ya’yansu idan lokacin auren su yazo, sai mummy tace “ahh’ahh ita kam bata ba ta komai ba tsoro takeji,abinda kullum yake damunta azuci ma kenan amma dai daga bay ta yanke shawarar gara ta barta hakan kawai.

Sai kuma Umman ma tace “yauwa hakan yafi ai gara abarta a yanda take saboda yiwa yara abubuwan da suka shafi wannan 6angaren kafin susan kansu yana da illoli da dama amma tunda ma ba’a matan ba shikenan ,tace dama ta so ma tun wuri suyi maganan amma sai ta sha’afa gaba ‘daya abubuwa sun sha kanta itama”. 


*****
7days to ranar ‘daurin auren Ummahn Abbas ta iso ita da Hannah suka zo dan Hanna damunta tarin’ka yi wai tafiso suje dawuri ayi komai da ita ,bata son komai yawuche ta shiyasa dolen Ummahn ta shirya suka taho, dama nufin ta sai nan da kwana biyu zasu taho, Daddyn Abuja ma yabiye wa Hannah yace ai gara su je tun yanzu duk ‘daya da jibin da Ummahn tafa’di tunda bawani abu suke jira anan ‘din ba ai gara sutafi ayi hidima dasu gaba ‘daya, yace shi sai ranar Friday zasu ganshi ( dayake bikin ranar Saturday ne).

Teemah bata ta6a ha’duwa da Hannah ba amma zuwan Hannah ya yi mata da’di sosai, saboda tasamu abokiyar hira, sosai Hannah ke ‘debe mata kewa surutunta tamkar uwarsu ‘daya da Mahmud itama badama gata da saurin sabo bata da ba’kunta.

Washegari cikin sa’a sai ga wasu daga cikin ‘kawayen Teemah na makaranta kusan su hu’du suka zo, Teemah wani ihu da ta saka ta rungumesu har ma bazaka ce tana da damuwa ba, Hannah ce tace “mata kiyi dai ahankali dan kin kusa ki zama matar gida”.

Bata kula da maganar Hannah ba tajasu gaba ‘daya suka nufi ‘dakinta kowa tasamawa kanta matsuguni, wanda kusan dukkansu akan makeken gadon Teemahn suka zuzzube Hannah ce ka’dai ta ‘dan ‘dosana ‘duwawunta saboda sauran duk kwanciya sukayi so ba space sosai, sai kuma Teemah dake zaune akan side drawer tana facing ‘dinsu, musamman ta janyo shi zuwa gaban nasu dan taringa kallon su da kyau gaba ‘daya.


*****
Aranar da su Ummah suka bar Abuja aranar shikuma Abbas yaje shi, dan ma irin zuwan nan na shi da ba da’dewa yakeyi ‘din nan bane ‘kar’karinta a yayi ‘ko’kari shine yakwana ‘daya shikenan zai ce zai tafi, shi akoda yaushe yafi son yaganshi a wurin aikinsa baya so yaga yayi nisa da su he so much care about his career.


Daddyn Abuja ne ya sanar da Abbas ‘din cewa da safiyar yau suma suka wuche Jihar Yobe, sosai Abbas yaji haushin rashin samun sun da be yi ba, har ma yace wa Daddyn nasa ” me yasa toh suka tafitun yau”?
Cikin jin haushi yayi maganar. 

” haba Abbas ka manta bikin waye za’ayi ne”?
daddyn ya tambayeshi da mamaki. 

Kauda kansa yayi gefe sannan yace ” ban manta ba Daddy kawai naga sunyi saurin zuwa ne ai dasun bari ranar Wednesday ko Thursday sai su tafi”.

“Yanzu kam ai shikenan tunda sun tafi komai ya wuce, in ganin su kake son yi ka bi su can ‘din.”

Shiru yayiwa daddyn nasa bai tanka ba,kawai ya tashi ya nufi 6angarensa domin watsawa jikinsa ruwa.

Daga lokacin da ya iso zuwa daren ranar tsakin da yayi yafi sau a’kirga, abubuwane suka taru suka mar yawa acunkushe ya ringa jin zuciyarsa , koda yaji yunwa ta dameshi sai ya nemi abinci anan ma Daddyn Abuja yace yajira akawo abincin ya aika asiyo.

Ka’dan yarage tsakin da yayi azuciyarsa tafito fili Allah ya taimakeshi azuci yayi ta shiyasa Daddyn nasa be ji ba.

Sai kawai ya tashi ya nufi harabar gida amma sam yarasa inda zai samu nutsuwa, tunani yayi ko de ya shiga cikin gari yawone?,
Toh inka fitan ma ina zaka nufa?
Wani 6angare daga zuciyarsa ta tambayeshi.

Safa da marwa ya fara yi agurin yana tunani ” wai dagaske ne za’ayi auren kenan?,
Dagaske Mahmud ne zai auri Fatima bani ba”. 

” ehh dagaske ne mana tunda gashi su Ummah ma sun tafi domin halartar ‘daurin auren”. 

Wani 6arin zuciyarsa ne ya sake bashi amsa.

Tambayar kansa da kansa yayi wai ” me yasa duk wani abu daya shafi 6angaren Fatima ni nake cutuwa aciki meyasa haka ?,is it because dan ba zan sameta bane ko me,?
_First_ ha’duwarsu da Mahmud, lokacin ba ‘karamib takaici yajiba na yanda yarinyar nan ta nuna tafison kasancewa da Mahmud fiye dashi da ‘kyar ya samu ya lallashi zuciyarsa akan hakan.
Then _secondly_ batun aurensu, wannan kam shiyafi komai ‘kona masa zuciya saboda yanajin kamar bawai ha’din iyaye bane kamar yanda Mahmud yayi masa bayani gani yake tamkar Fatiman nason auren duk da yasan shi Mahmud ‘din baso yake ba amma zuciyarsa takasa amince masa da cewa Auren na ha’di ne kamar yanda zuciyarsan akullun take bashi tabbacin cewa babu wanda zai auri Fatima akaf duniyan nan sai shi,  Fateema Zahra ta Abbas ce shi ka’dai.

And _now_ yayi missing kirkin Ummahn sa duk adalilin wannan banzan auren.

Haushi sosai hakan yasaka shi, yace yanzu da Ummah na nan ai da ba ruwansa da neman abinci, dan ita akoda yaushe idan ka nema toh zaka samu, ya tsani cin abincin hotel shi, yafi son cin abinci agida, shiyasa akoda yaushe yake kan hanyan zuwa gida duk da nisan da gurin ke dashi hakan besa yayi ganda zuwa aduk lokacin dayaso, abu ka’dan ke sa ya kamo hanyar gida baya yin cikakken 2 weeks mai kyau batare da ya le’ko Abuja ba, koda ba zai kwana ba ma amma in ya so sai yazo, wani lokaci dan kawai yaci abincin Ummansa ma yakoma saboda na wajen da wuri suke fita akansa bakamar na mahaifiyarsa ba.

Story continues below


Ko yanzun ma da aka kawo abincin da ‘kyar yasamu ya’dan tatta6a ka’dan yabari, ba danma yanajin yunwa ba da bazai ko bu’de ba.

Washe gari ma Daddynsa ne ya sake aikawa aka kawo musu breakfast, shikan ‘kin ci yayi yacewa daddyn nasa shi lipton kawai zaisha, daddy ne kawai yaci abincinsa, Abbas dakansa yaje kitchen ya tafasa ruwan lipton ‘din yakawo musu da daddyn dan yasan shima Daddyn gwanin shan ruwan lipton ne.

Yana gamawa kuwa yayi wanka ya shirya sai yayi sallama da Daddyn ya kama hanya.

Teeemah na cikin ‘kawayenta suna ta zuba surutu abinku da student in an ha’du ba dama sai an yada hali, musamman na yanzu da ya kasance ‘dayarsu zatayi aure dayake kusan itace ta farko ma bayan gama makarantar tasu kuma classmates ‘dinta yanzune suke SS3 basu gama ba so sai suke ta marmarin ganin lokacin bikin ya iso, itace aka fara saka ranar bikinta shi yasa suke ganin kamar wani abu ne na daban, hira suke tayi abinsu, na dariyane, takaici ne, abin tausayi ne duk suna ta tunowa da school life ‘dinsu lokacin suna tare da ita, ita kanta Teemah ma warewa tayi suna ta shan hirar su, ga Hannah ma acikin su kamar da ma already sun san juna.

Garin yin dariya ne wata acikinsu me suna Naanah ta danne ‘kafafun Teemah dayake ta mi’ke ‘kafafun nata ne a abakin gadon saboda gajiya datayi da yanda ta tankwasu tun farkon zamanta agun ” waashh……. Naanah kin karyan ‘kafata”. 

Ta yi maganar tana wani kwa6e fuska tare da janyo ‘kafarta ta zuwa gabanta.

Duk kan su sai hankalinsu ya dawo kan Teemahn suka zuba mata idanu kowa na mata sannu, sorry, da sauransu.

Fauziyya (Fauzee) ce tace 
” ke Naanah ki riinga kulawa kar kisa ahana mu fita daga gidannan bari kiji “!

Sai Hannah ta kar6e da fa’din ” gaskiya kam, in ba haka ba ina ke ina jiwa amarya ciwo”

“Ai kuwa de ” inji Hauwa da ke ‘ko’karin ja wa Teemah ‘kafar tata”.

“Kuma dai wallahi,  ku kyaleta dallah inta karye banda murakata da sabon wheel chair ‘dinta agefenta, kunga ta kafa tarihi a auranta”.

Dariya dukkansu suka sanya har Teeman, tana cikin  dariyar tace ” wallahi kin iya wula’kanci yarinyar nan. 

” ai gaskiya ne, kya tsaya kina wani yi mana raki anan bayan ciwon bawani na kirki bane…….!

Fauzee ce ta amshe maganar da fa’din 
” ke bata son jikin ta ya samu matsala ne ke baki ga yanda ta koma bane ta wani yi fresh da ita”.

” ‘kwafa Teeman tayi kana tace ” har ina wani abin fresh ‘din anan dan Allah, ahakan ne zaki ce na wani yi fresh dani?, haba Fauzee….. dubeni fa ke baki ganin irin ramar dana yi ne,?Allah mummy da kanta ma cewa take yi wai na rame dayawa sai ta ta sani cin abinci kullum wai ko zan ‘dan murmure”.

“Duk da haka de ke kam ki yadda kin canja, ai rama daban canjawan skin ma daban”
Cewar Naanah.

Fauzee kuwa tace 
” muma dai ya kamata mu fara haramar yin auren nan ko ya kuka gani”?Ta ‘karasa maganar tana rarraba wa sauran idanu.

” toh zakwa’di ai de kya bari ki ‘kare secondaryn tukunna ko?” Inji Teemah

Baki Fauzee ta rufe “au ashe fah da sauran mu mu ‘din bamu gama ba”.

Dariya suka kwashe mata dashi dukkansu sai Jiddah tace ” ‘yar rainin sense….da ‘din mantawa kika yi kenan.”

” Tamanta cewa ni ka’daice na girma acikinku” Teemah ce tayi maganan tana musu dariya.

” ai ki bari wallahi nima da nasani da nace wa Babana zan rubuta waec alokacin nasan da bazai hana ni zai barni, kunga da ina yin candy nima sai asha biki na irin na Fatima Kb”.

sai Teemah tace
” ke kika sani, yanzu kam ai ya wucheki sai ayi ha’kuri ajira next year ” 

Haka suka ci gaba da hira atsakaninsu, gwanin birgewa Teemah kwata-kwata mantawa tayi ma wani batun aure, ji take kamar suyi ta zama ahaka kar su tafi.

Acikin hirar ne
Naanah tace da Fatima itafa gaskiya bata san waye angon ba anuna mata shi ko a pix ne, saboda taji ance wai yayanta ne ‘dan gidansu, kuma yayun nata kusan mutun biyu tasani bata san kuma wanene shi daga cikin su ba so tana so taganshi.

Sai duka sauran ma suka goyi bayanta dan hatta Hannah ba ta gane shi ba, ko lokacin dayaje gidansu ma basu ha’du dashi ba har yatafi shiyasa bata sanshi ba.

Teemah wayarta ta tashi ta ‘dauko ta nemo photon shi ‘daya daga cikin wanda yake tura mata tun lokacin suna chat sosai dashi ta nuna musu kar6ar wayar sukayi suka ringa zuzuta kyanshi dan ba ‘karya Mahmud ba baya bane wajen kyau da cikar kamala.

Koda wayar tashiga hannun Hannah ma ” wow ” tafara fa’di tace gaskiya ya ha’du, ni sai na gama kamar kuna ‘dan kama ka’dan dashi”?

” badole ba ke kuwa abinki da jini ‘daya”
Cewar ‘daya daga cikin su.

Mahmud kyakykyawa ne shi, yana da tsayinsa daidai gwargwado, shi ba fari tas bane kuma ba ba’ki ba skin colour ‘dinshi me kyau ne kuma ya kar6i yanayi da tsarin sa, gashin kansa irin na asalin fulani ne ananna’de yake kuma akwance luf luf dam ma shi yana yawan aske wa be fiya son tara gashin ba sai dai yabar ‘dan daidai, kammanin sa na fulani sak yayi wata ‘kila yabi jinin kakarsa ne mahaifiyar Babansa ( Innah Hansatu) sai de shi yana da ‘dan kauri ka’dan kamar Antyn sa (mahaifiyarsa )
bashi da sirinta ko ka’dan, abinda kenan ya ‘dauko daga wurin mahaifiyarsa.”

” danma baki ga ‘daya yayan nata ba, shi sun ma fi kama da Kb sosai, inji Fauzee tafa’da tana me kallon Hannah

Azaton su ita ‘dinma wata ‘kawar Fatiman ce daga wani 6angare daban duk da akwai ‘dan kama na jini tsakaninsu, saboda duk wanda yaga Teemah yakuma ganin Hannah sai yaga wannan kamar da suke dashi, amma su basu ma lura da hakan ba, shirman su kawai suka sa agaba.

Daga nan suka cigaba da zuzuta kyawu da tsaruwar yayun Teeman dayake sun sansu gaba ‘daya ada lokacin tana zuwa school duk cikin su babu wanda be yi mata rakiyar zuwa makaranta ba daga Mahmud ‘din har Abbas.

Fitsari ne yadami Hannah sai ta tashi ta shiga bayi to ease her self, ko da tayi fitsarin tagama sai kuma tayanke shawarar yin wanka saboda lokacin da Teemah tayi wanka ‘dazu ita daman batayi ba tana kwance tana ta chat abinta har ‘kawayen Teeman suka zo.

Shi yasa data shiga batin sai tace kawai bari taha’da da wanka gaba ‘daya. 

Shiganta ke da wuya kuwa sai akazo akayi kiran Teemah wai suzo inji Ummah ita da Hannah.

Tashi Teemah tayi tace wa ‘kawayen nata “bari inje ina zuwa yanzu, idan Hannah tafito ku sanar da ita Ummah tana nemanta dan Allah”.

“Toh” sukace mata daga nan tayi waje.

Koda taje d’in sai Ummah ta tambayeta ina Hannahn kuma bayan nace kuzo tare, yayanku ne yazo kuma zai wuche yanzu shine nache ya tsaya ku gaisa inajin yana ‘dakinsa, kinsan shi da gaggawa wai yana da abunyi agabansa”.

” Ummah bayi Hannahn tashiga bari in dubota toh sai muje tare”.Teemah tayi maganar tana ‘ko’karin juyawa har muryarta na rawa.


” ah ah kyaleta kar a6ata masa lokaci ke kije ku gaisa kawai in tafito dawuri sai ta samoki”.
Ummah ne tafa’di haka dai dai shigowar Mummy da try ahannunta an shishshirya abinci akai “ingo tafi masa da wannan”inji mummyn tayi maganar tana mi’kawa Teemahn try ‘din dake hannunta.

Kar6a Teemah tayi tafara tafiya ahankali, tunda Ummah tace _yayanku ne yazo_ take jin zuciyarta na harbawa da ‘karfi, bata bu’katar wani dogon ‘karin bayani domin tasan Yah Mahmud ne yazo shi tun da tasan shine future husband ‘dinta dole shine yazo, dan shi ka’dai ne zai bu’kaci ganinta awannan lokacin dole tasan sai hakan yafaru.

Ita duk atunaninta Mahmud ne yazo ,kuma bata san me yasa taji tsoro yashige ta ba, duk da wani tsoron Yah Mahmud ‘din take ba amma sai  takejin wani iri tamkar karta taje gurin shin haka taji, wai yau zata ga Yah Mahmud ‘dinta, her beloved brother, amma ba’a wannan matsayin da ta sanshi akai ba, yau Yah Mahmud amatsayin wanda zai kasance miji ne agareta zata gani.

Bata so tasake ganin Yah Mahmud ba, inda son ranta ne har se bayan anyi auren wata ‘kila alokacin zataji son ganin shi amma yanzu kam da za’a tambayi ra’ayin ta kafin yazo da ta ce yayi zamansa basai yazo ba, bata san me zata ce da shi ba ko da ta ganshin ma yanzu.

Tafiya takeyi ahankali tana tunani har ta isa ‘kofar ‘dakin da tasan na Mahmud ‘dinne wanda iya zaman sa agidan anan yayi rayuwa, hannun ta da abu so babu daman ta tsaya yin nocking a’kofar, thank God ma ‘kofar ba’a rufe gam take ba sai kawai tasa ‘kafa ta tura sai ‘kofar ta bu’du, ciki ciki tayi sallama bata wani jira jin amsa ba ta tura kanta ta shiga ciki.

Bugun da zuciyar ta keyi ne ya ‘karu fiye da na baya, sai ta kasa ‘daga kanta ta kalleshi har taje ta ajiye tire ‘din a kan centre table ‘din dake cikin ‘dakin sannan ta ‘dago ta kallo bayan wanda ke tsaye agurin window tamkar andasa shi.

Maganar mummy ta tuno da kusan kullum sai ta mata tuni akai inda take cewa ” ayanzu baki _da wani makami Fatima face addu’arki da kuma ha’kuri, dan nasan su ka’dai ne zasu jagorance ki ga dukkan al’amuranki, dole ne kiyi ha’kuri da duk wani abu da zai faru ko zaki gani, kawai kisawa ranki daga Allah yake kuma ‘kaddararki kenan, kuma shi yaso ganinki awannan matsayin, domin yawan nuna damuwa akan abu bashine zai kawo miki sau’ki ga al’amarin ba face addu’ar ki, damuwar taki bata da amfani koka’dan sai ma yasake ‘daga miki hankali, tunda ke kanki kinga alamun Daddyn ki ba barin zancen auren nan zaiyi ba inajin mutuwa ce ka’dai zata sa yafasa ‘daura auren nan ayana yin da naga yake ciki, ki daure ki ya’ki zuciyarki kisawa ranki san auren tun yanzu, idan ma kina jin rashin son Mahmud ‘din ne to ki dole ne ki daure ki kauda wannan tunani tun yanzu, Mahmud ‘din nan dai da kika sani shine zaki aura ki kuma zauna dashi, dan haka kiyi ha’kuri na tabbata Allah yana tare da dukkan bawansa me dogaro dashi, Fatima ni mahaifiyarki ce kuma mai tsananin sonki fiye da zaton ki, wallahi da’ace inada wata dama ko hanyar da zan iya hana faruwar wannan auren da zan hanashi ko dan ganin farin cikinki ka’dai ma, amma na tabbata dai dai da ‘kwayar zarra ban kai ubangiji mahalicci sonki ba kuma shine yaga dama ya za6a miki shi Mahmud ‘din dan haka kinga mu bamu isa mu ja da lamarin ubangiji ba, sannan mahaifinki ma basai na sanar dake son da yake miki ba Fatima ke kanki kinsani, kuma shi kanshi bazai ta6a yi miki abinda yasan cutarwa ne agareki ba har abada nasan kinsan wannan, ki daure kiyi masa biyayya kinji…. ina da ya’kinin duk daran da’dewa watarana zaki ga haske arayuwarki insha Allahu_ ”  

Hawayen daya zubo mata tasa hannu ta goge shi tas tana yi tana sake bawa kanta ‘karfin gwiwa 

“Mummy bazan yi kuka ba, bazan sake yin kuka dan zan auri yah Mahmud ba, na miki al’kawari insha Allahu mummy”
Tana goge hawayen fuskar tata take wannan maganar.

Mummy tana nufin insoka ya Mahmud in ‘kaunace ka badan komai ba sai dan saboda Allah mahalicci, dama ni ban ta6a jin bana sonka ba Yah Mahmud amma wani lokaci sai inji dama ba kai Daddy ya za6a min ba sai inji dama ya barmu a yanda muke tun farko kaci gaba da zama amatsayinka na yayana nafi feeling compotable akan haka, ban San me yasa ba amma sau da dama sai inji dama Yah Abbas Daddy yace zai aura min ba kai ba”.

‘Daga kai tasake yi ta dube shi, tun ‘dazu data shigo ahakan yake be canja tsayuwarsa ba tsaye yake hannunsa ‘daya acikin aljihu ga dukkan alamu tunani yake yi wata’kila shi yasa bata samu amsar sallamar ta data masa lokacin data shigo, Yah Mahmud bai fiya yin hakan ba yakan amsa sallama koda baya cikin yanayi na walwala sannan baya ta6a kyaleta matu’kar ta kusanci inda yake koda kuwa tayi masa abin 6acin rai baya ta6a yin fushi da ita amma ji yanzu yanda ya shareta tamkar ma besan tashigo bayan tana da tabbacin yaji shigowarta tunda da sallama tashigo,  gashi ma sai taga ya ‘dan rame mata ‘ka’dan bakamar yanda yake ada ba, kar dai shima baya son auren ne kamar ni,? kardai maganan auren ne yasaka cikin damuwa ?

Ahankali ta ‘dago ‘kafafunta ta har sai da ta iso kusa dashi kafin ta tsaya daga bayansa 

” _Yah Mahmud_ “!
Ta ‘kira sunan shi ahankali kamar bata son yin maganan.

Be amsa ba kamar yadda be juyo ya kalleta ba haka kuma babu abinda yacanja daga yanayin tsayuwarshi.

Sai ta yi tunanin ko beji ta bane sake bu’de bakinta tayi da niyyar sake ‘kiran sunan nashi
_” Yah Mahm…………_ 

Da wannan lion voice ‘din nasa ya daka mata tsawa

_”Shut up da Allah”!_ 
Ya fa’di maganar tare da juyowa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *