WANENE SHI CHAPTER 12

WANENE SHI





CHAPTER 12





“….Amma banyi tunanin cewa raba jikinta da ruhin zai iya tab’a matsalarta ba yarima, saboda ni shaida ne akan wahalar da nasha kafin na iya juya zuciyar mahaifinta zuwa son yi mata aure yanzu, naga irin tarin k’aunar da iyayenta da ‘yan uwanta ke mata, ba zanso ace cikin sati d’aya kawai mun yi mata lahani ba.

Sai dai tunda har an cire….” 

“Ba abinda aka cire.” 

Muryar Imran ta katse shi cikin kaushi. Ya juyo ya kalle shi har yanzu yana zaune so stiff ha tare alamar motsi ba, fuskarsa fayau take babu wani yanayin da zaka iya tsinta a ciki. 

“Kamar yaya? Na tabbatar… 

“Na sani…” Imran d’in ya sake katse shi. 

“…hasken yaje har gidan, amma ba abinda ya faru.” jaamil ya cigaba kallonsa mamaki na nunawa akan fuskarsa ko kuma rashin yarda ne? 

“Amma ta yaya toh…” 

“Nima ban sani ba.” 

Dukkaninsu suka yi shiru na wani lokaci kafin jaamil ya sake juyowa ya tambaye shi. 

“Toh me kake yi anan?” 

“Bugun zuciyarta ne baya bugawa daidai, I wanted to be sure saboda in nemo me ya same ta.” 

“Look yarima, na san cewa a idon mutane yanzu yarinyar nan matarka ce, amma ya kamata ka dinga tunawa kanka matsayinta a gurinka, matsayin da nan da wani lokaci zai shafe, saboda haka bai kamata ka d’auki lamarinta da girma haka ba, ni na zata wani abu ya sameta ne da na ganka anan, amma canjawar bugun zuciyarta kawai shi zai sa ka rud’e da tunanin zaka tafi neman me ya sameta? 

Ka manta da abinda yake gabanmu ne? ko ka manta rantsuwar da ka min na cewa ba son yarinyar nan kake ba kuma intrest d’in da kake dashi akanta ya riga ya tafi, ita kanta Naani da wannan kalaman naka ta dogara bata yi fushi damu akan abinda muka yi ba, ta yarda cewa tunda har baka son yarinyar, rabuwarku ba zata sa ka kasa cigaba da abinda muka fara ba…amma yanzu canjawar bugun zuciyarta kad’ai yasa ka a wannan halin me zai faru kuma ranar da ka rabu da ita?” 

“So, wannan shine jaamil d’in?” 

Muryar Nanne tasa kowannensu ya d’ago da kansa cikin wani irin sauri suka kalleta, tana tsaye d’an taku kad’an daga gabansu tayi folding hannayenta a k’irji. A lokaci d’aya Imran ya mik’e yaje kusa da ita. 

“Me suka ce?” 

Ta d’an kalle shi ta gefen ido amma hankalinta na kan jaamil wanda ya sandare a wajen da tsananin mamakin yadda akayi ta sanshi, ta san sunansa…for real? kenan Allah kad’ai ya san adadin sauran abubuwan da Imran ya fad’a mata, dole ne ya damu da lafiyarta ashe. His sharing a part of him with her! 

“Allaura biyar fa aka min, kuma a hannu d’aya wai duk test ne.” 

Muryarta mai dad’i ta fad’a tana nunawa Imran hannunta. Jaamil yaji wani abu mai kama da tausayinta a cikin zuciyarsa, tana cikin wani sirad’i mai had’ari amma bata sani ba. Her voice was innocent! 

Imran ya murza ‘yan yatsun nata yana fad’a mata wani abu da bai maida hankali yaji ba, sannan yayi kissing saman goshinta, ta ture shi a hankali tana murmushi. 

“Naji dadin ganinka Jaamil, ka taimake shi don har na fara tunanin ko bashi da freinds ko d’aya.” 

Jaamil ya juya ya kalli Imran, da ido yayi masa alamun zaiyi masa bayani daga baya, saboda haka ya kalleta yace. 

“Nine da laifi amarya, kamata yayi inzo har gida in gaishe ki amma na d’anyi tafiya ne.” 

“Tafiya?” Ta juya ta kalli Imran. 

“Bai fad’a ba kuma.” 

Kafin Imran d’in yayi magana wata Nurse ta k’araso tace da Sa’adha likitan da zai fad’a musu result d’in tests d’in na jiranta, tare da Imran suka tagi bayan ta rok’i jaamil akan kar ya tafi. Ba yadda ya iya haka ya zauna har suka fito, daga nan suka koma gida. 

Inda sa’adha ta rik’e shi da hira da d’awainiyarta har sai bayan sallar maghriba sannan ya samu ya tafi, Imran na tayi masa dariyar yadda a dole yau yaci abincin da Sa’adha ta tarkata masa kala-kala, tun yana iya ci har sai da ya fito k’iri-k’iri ya gaya mata ya k’oshi sannan ta daina kawo layin cimar da bai tab’a ci ba kala-kala. 

Imran ya gaya masa cewa ta tambaye shi su waye freinds d’insa ne shi kuma ya rasa sanda bakinsa ya furta mata sunansa, amma ya tabbatar masa bayan hakan babu wani abu nasa data sani. 

Bayan jaamil ya tafi, ya taya ta suka yi tarin wanke-wanken data tara, zuciyarsa cike da farin cikin irin karb’ar da ta yiwa jaamil, yaji dama yana da wasu ‘yan uwan da zasu taya shi ganin kyautatawar matarsa, saboda itama tana masa tambayoyin da suka shafi ‘yan uwansa amma bata cika matsawa sosai ba. 

Zuciyarta a kullum tana danganta shine da abubuwa masu kyau kawai, alhalin shi d’in akasin hakan ne a wajenta. 

Ya tuno bayanin likitan nan da yake gaya musu cewar komai a jikinta lafiya k’alau yake, kawai bugun zuciyarta ne ya ragu kuma shima ‘yan dalilan dake sashi ba masu k’arfi bane. Hankalinsa ya kwanta a lokacin amma tunanin abinda zai faru nan gaba kuma yazo ya rugurza komai. 

Don kamar yadda jaamil ya fad’a masa ne kafin ya tafi, rashin jin komai da suka yi daga wajen Naani ba lafiya bane, dole akwai wani dalilin da har haskenta ya shigo gidan amma bai iya tab’a Sa’adha ba, don haka dole suyi tsammanin jiran koma meye a yanzu. 

“What’s with d’ankwalin kanki yau?” 

Ya tambayeta da daddare lokacin da suke zaune a falo, ya d’auko system d’insa yana k’arasa wani kwantan aikinsa dake ciki, ita kuma tana gefensa tana b’are tulin maggin da take tarawa a cikin wata jar, idonta na kan tv tana kallon wani tsohon indian film da wata channel ke nunawa. 

Ta kai hannu ta tab’a d’ankwalin kamar tana so ta tabbatar in yana nan d’in. 

“Aunty maryamah tace in daina zama ba d’ankwali.” 

Ya juyo ya kalleta. “Saboda me.” 

Tayi shiru kamar ba zata fad’a ba sannan ta kalle shi tace. 

“Wai saboda aljanu zasu iya shiga jikina.” 

Yadda tayi maganar ya bashi dariya kamar itama bata yarda da abinda ta fad’a ba, yayi murmushi a k’asan numfashinsa sannan ya jawota jikinsa. 

“Aljanu kike tsoro?” 

Ta girgiza kanta. 

“Su suke fad’a dai, bana fad’a maka wasu malamai sunce har bak’ak’en aljanu ne wai suke son shiga jikina.” 

Har yanzu da murmushin a fuskarsa yace. 

“Duk ki rabu da wannan zancen Noory, in dai har kina tare dani ba aljanin daya isa ya shiga jikinki…babu shi a duniyar nan!” 

Ta dora idanunta sosai a kansa. 

“Ta yaya ka san hakan?” 

Ya kai hannunsa a hankali ya cire d’ankwalin sannan ya cusa yatsunsa ya warware bun d’in da tayi da gashinta. 

“Saboda su kansu Aljanun suna tsoron irin jinsi na Sa’adha.” 

Kanta ya d’aure da mamaki. 

“Wane irin jinsi ne kai d’in?” 

Ya tura kansa gefen wuyanta yana shak’ar dadd’an k’amshin shampoo d’inta kafin ya amsa. 

“Jinsina na masu yawan addu’a mana.” 

Tana jin hakan mamakin fuskarta ya kwance, sannan murmushi ya maye gurbinsa. 

******* 

K’ARFE BIYU DA RABI. 

K’arfe biyu da rabi na daren wannan ranar abinda Imran ke tsammanin jira ya faru! 

MUZAFFAR! 

Ta tsirawa taswirar fuskarta ido ta cikin garai-garai d’in ruwan dake wucewa a gabanta. Watakila ta shafe awanni biyar zaune a wajen koma fiye da hakan, ba zata iya tantancewa ba, don dad’ewarta a wajen ba damuwarta bane, fatanta kawai abinda take zaman jira ya k’araso, ya k’araso gareta ta sashi a idonta ko ta samu nauyin dake zuciyarta ya kauce, wani nauyi daya taru tun tsawon shekara guda data wuce. 

Tana zaune ne a bakin wani rafi, ta d’age rigarta kad’an ta zira k’afafunta ciki, sunkuyawar da tayi ta zura hannuta yasa dogon gashinta ya bita cikin ruwan, yana motsawa a hankali tare da gudunsa, sannan daga kowanne gefe na lambun tarin hadimanta ne ke tsaye suna gadinta. 

Duwarta ta fara ne tun lokacin da YARIMA ya bar cikin duniyarta da niyyar yiwa Naani wani aiki da har yau bata san mene ne ba, bayani d’aya kawai ta sani wanda ya fad’a mata kafin tafiyarsa na cewar sai tayi hak’urin jure rashinsa don ba zata iya ko jin muryarsa ba daga can inda ya tafi d’in, a lokacin komai zai kasance ne cikin watanni hud’u kawai, amma a yanzu, shekara d’aya itace k’irgen da kowa keyi na tsawon tafiyarsa. 

Tayi hak’urin har ya k’are ta sake lalubo wani ta d’ora ya cigaba cinyeta, cinye siffar da take mutuk’ar so a rayuwarta. Idonta ya sake kaiwa kan ruwan, watak’ila da ita bil’adama ce da in ta samu biyan buk’atunta nan gaba kad’an hankalinta ya kwanta da sai jikin ya koma yadda yake, amma abu ne da ta san ba zai tab’a faruwa ba wanda ya tafi ya riga ya tafi kenan! 

A tsawon rayuwarta ba abinda take mutuk’ar k’auna irin siffar bil’adama da kuma son shiga cikinsu, amma sai ya zama kamar abubuwa da yawa a rayuwar tata, Naani tayi mata katanga dashi akan dalilin da ta san ba zai rasa nasaba da d’aya tilo da idonta kad’ai ke gani ba. Gata d’aya da tayi mata shine mayar da jikinta da tayi ya koma irin na bil’adaman, wani abu da ita kad’ai ke dashi a duk fad’in nahiyarsu. 

Amma duk da haka ta k’udirce a zuciyarta cewa sai ta fanshe duk wata wahala data sha a wajen dukkaninsu, duk wanda keda hannu a cikin bak’in cikin data tashi dashi. 

Mussaman shi yariman, wani halitta data tsana fiye da kowa a rayuwarta, ta tsane shi tun lokacin da hankalinta ya iya banbance tarin k’aunar da Naani ke masa akanta, Bata tab’a ganin Uwar dake fifita d’an wani sama da nata ba irin tata uwar, ita kad’aice ‘yarta a duniyar nan, amma hankalinta da tunaninta baya tab’a zama akanta, ita d’in koyaushe tana zuwa ta uku ne a jerin al’amuranta. 

YARIMA DA JAAMIL sune sunayen data tsana fiye da komai a rayuwarta, kuma sunayen data yi alkawarin sai ta kawar dasu a duniyar nan, sai ta zama ajalinsu, ta yadda dukkan wani abu da Naani ke shirin mallaka musu zai dawo gareta, ya zama dukkan tanadin da take shirya musu ya k’are akanta, yadda bayan taga hakan itama daga baya ta kashe ta. 

Ta dad’e da tsara wannan shirin a cikin kanta, abu d’aya ne ta tsaida faruwarsa har yanzu, shine tafiyar yarima, domin komai zai fara ne bayan ya aureta. Shi yasa a yanzu take zaman jiran wannan nauyin zuciyar tata ya kauce! 

“Ranki ya dad’e sak’on ya iso…yarima ya shigo cikin masarauta yanzu.” 

Wata hadima daya shigo lambun a daidai wannan lokacin ta fad’a kanta a k’asa. 

A hankali wani murmushi ya sauka a gefen kumatun SAREEFA, wani murmushin da tayi tanadinsa tsawon shekara guda! 

Lokacin data k’arasa cikin masarauta, komai ya canja…a jiya ne kad’ai Naani ta sanar da zuwansa amma a jiya kad’ai aka canja fasalin komai gabad’aya. 

K’erarren ginin masarautar yana tsaye kyam! cikin wata irin k’awa da ado na alfarma, an canja launin kalarsa zuwa kalar rawaya da fari, yanayin lokacin yamma ne mai cike da lumshi da kuma iska mai dad’i, amma duk da haka tsuntsaye ne birjik! tun daga hanya sunyi rumfa da fuka-fukansu cikin wani tsari mai ban sha’awa, sannan ga tarin halittu nan taf! jinsi kala-kala suna durfafin isowarsa, ko’ina ka juya fuskoki ne cikin farin ciki, ga kuma tashin wani kid’a mai dad’i dake tashi a ko’ina. 

Story continues below


Zuciyar Sareefa ta matse ganin irin tarin k’aunar dake fuskokinsu, a dawowarta na k’arshe masarautar, bata samu koda rabin wannan tarbar daga wajen kowa ba, hatta daga Naani kuwa saboda ta tabbata k’awata masarautar ma anyi ne bisa umarninta. 

A ranta ta ayyana cewa saura lokacin kad’an duk wannan ikon ya dawo mallakinta, ta tsaida hadimanta daga bin bayanta sannan tabi iskar wajen ta baiyana a cikin masarautar! 

******* 

Nan d’in shine k’asarsa, mahaifarsa inda jinsinsa da duk wani gatansa yake, kuma ya saba da rayuwa a cikinsa tun zamanin k’uruciyarsa, ya saba da wannan matsayin da ake bashi sannan ya saba da wannan yanayin da jikinsa ke ciki, amma a yanzu ji yake komai ya dawo masa sabo, kamar ansa wani abu an goge wani waje a kwakwalwarsa da yayi saving duk memories d’insa na baya. 

Gani yake kamar shi d’in a yanzu baqo ne, komai ya canja masa, komai d’in da baya tunanin d’imbun halittun dake gabansa sun fahimta, koma jaamil dake gefensa, don watakila canjin da yake ji yafi nasaba ne da cikin zuciyarsa, wadda bata tare dasu a lokacin, tunaninsa ya koma can nahiyar da ya baro kusan awanni uku baya, k’irgawa yake cewa Sa’adha ta kusa tashi a yanzu, tunda ya saka mata Alarm a sabuwar wayar daya kawo mata wanda zai tashe ta sallar Asuba. 

Yafi sau d’ari a cikin zuciyarsa yana hasko yadda yanayinta zai kasance in ta farka bata ganshi ba, kowanne reaction na duniyar nan ya d’ora akan fuskarta amma ba wanda ya gamsar dashi cewa hakan zata yi. 

Sweatheart, 

Wani uzuri ne ya taso min urgently kina bacci, i’ll be back soon! don’t panic dan Allah, zanyi miki bayanin komai in na dawo kinji? I love you… 

…like crazy! 

Ya tuno d’an k’aramin note d’in da yayi scrambling a papers wajen hamsin ya ajiye a kusan koina na gidan daya san idonta zai kai. kusa da pillow, kofar toilet, kan slippers d’inta, kan fanfon sink, kan kujera, kan dining table, kan drawers d’in kitchen, kan gas, kan sink, da duk wani waje daya san zata yi amfani dashi, he wanted to make sure hankalinta bai tashi ba ta fahimci uzurinsa. 

“Da alama al’amarin ba zai kasance yadda muke tunani ba, tunda da tayi fushi sosai, ba zata sanar da al’ummah ba har ayi wannan taron.” 

Jaamil ya fad’a lokacin da suke takawa cikin hanyar da zata kaisu ga fadar Naani. 

“Na san koma meye ta riga ta samu hanyar da za’a magance shi yanzu, saboda haka ka yiwa Allah yarima ka karb’i dukkan wani abu da zai faru a yanzu da hannu biyu.” 

Kamar yadda tun lokacin da yazo masa da saqon neman da Naani ke musu wajen k’arfe biyu da rabi na dare baice komai ba, haka ma yanzu baiyi magana ba har suka kai ga cikin tamfatsetsiyar fadar, da bata da wani fasali da kwakwalwar mutum zata iya fahimta. 

Suna isa ciki, jaamil ya nufi wajen mahaifiyarsa ‘Bwama’ da ya hango a gefe, a sannan ne kuma idanun Imran suka hango masa Sareefa tsaye daga gaban karagar Naani cikin siffarta ta bil’adama, bai tab’a d’aukan yanayinta da daraja ba irin yanzu, a da baya ko damuwa yaga banbancin siffarta da tasu don a tunaninsa son da takewa bil’adama shirme ne, matsayin da Allah ya basu ya isa rayuwarsu ba sai sun kwatanta dana bil’adama ba. 

Amma a yanzu, gani yake sareefa ta yiwa dukkan al’ummar daya had’u dasu zarra a idanunsa, kamar tana tuna masa cewa zai koma wajen Sa’adha ne nan da k’ank’anin lokaci. Kafin ya k’arasa tunaninsa ta baiyana a gabansa sannan cikin sauri ta rungume shi. 

“Maraba da sauka yarima, maraba, maraba…nayi kewarka fiye da tunanin duk wata halittar Allah.”

Muryarta ta fad’a a cikin jikinsa. Imran yaji jikinta yayi k’arfi a cikin hannayensa, ya saba da irin wannan rungumar tata a baya sau da yawa, amma yanzu daya saba da jikin Sa’adha na mutane, sai yaji kamar yana rik’e da dutse ne.

“Da kinyi kewata da yawa, da na dinga samun sak’on ki akai-akai wajen jaamil.”

Ya fad’a sanda ya matsar da ita daga jikin nasa, idonta ya nuna rashin gaskiya kafin tace.

“Kullum ya dawo zai koma wajenka, sai na tare shi da saqona, watakila shine baya fad’a maka.”

Rashin gaskiyarta ya fito k’arara har a muryarta, sai kawai yayi murmushi yana kallonta.

“Ka canja yarima, ka canja sosai ka k’ara kyau fiye da baya, watakila duk inda kake ba a cikin wahala kake ba.”

“Babu wahala ko kad’an, na saba da komai kuma ina ji ma kamar…”

Bai k’arasa ba ta katse shi, muryarta cike da mamaki.

“Me ya sami ruhinka? me ya sami b’arin ruhinka?”

Yaso ya manta ne sareefa tana da baiwar ganin duk wani abu dake jikin wata halitta ta duniya, bama iya jinsinsu kad’ai ba.

“Akwai matsala tare da jikinka, ta yaya kake iya rayuwa da b’ari d’aya kad’ai? kuma d’aya b’arin baya kusa da kai?”

Ya lumshe idanunsa a hankali.

Yana kusa dani sareefa! Sa’adha tana kusa dani!

*******

“Me ake ciki game da aikin da ya kaika…”

Muryar ta fito cikin kaushi kamar kodayaushe tare da amo mai girgizarwa, a yanzu da ya dad’e bai jita ba, sai yake jin kamar sautin ta yana tab’owa ne har k’asan zuciyarsa. don yana iya jin yadda zuciyar tasa ke amsawa.

Imran ya d’ago da idonsa ya kalli hallitar dake zaune a gabansa, wata halitta data zama gata da tallafin rayuwarsa, a kullum ya d’aga ido ya kalleta sai yaji girma da matsayinta ya k’aru a idonsa, ya gyara murya a hankali sannan yace.

“Komai ya kammala Naani, a yanzu haka muna jiran wani taro ne da za’ayi na cikar kamfanin shekaru Ashirin. Na tabbatar a wannan lokacin buqatarmu zata biya, tunda a yanzu haka ya riga ya amince dani yadda ba wani abu da ake zartawa a kamfanin ba tare da umarni na ba.

Shi yasa a lokacin da jaamil ya fad’a min lokacin fitowarki, nayi tunanin zamu kammala komai kafin nan.”

“Komai yana nufin har da matsalar data k’aru bayan bana nan?”

Muryar tasa tsigar jikinsa mik’ewa, bata danganta abin da laifinsa ba saboda haka ya samu kwarin gwiwar bada amsa.

“Matsalar data faru Naani wani tsautsayi ne da yafi k’arfin mu, shi yasa muka yi amfani da hanyar da iya tunaninmu ya bamu kawai wajen neman mafita, amma koda mun samu buqatar data kaini cikin bil’adama, zamu jira ne har ki dawo, don ba wanda zai iya raba ruhin da jikinta.”

“Na samu labarin komai tun ina can, kuma na shaidawa jaamil cewa abinda kuka yi garaje ne, akwai hanyoyi da yawa da za’a sami mafita bayan cewa ka aureta, saboda a kowacce halitta aure ba k’aramin zance bane, tunda yanzu in har zaka rabu da ita, sai a nemi wata hanyar da zamu shafe batunka daga tunanin duk wani bil’adaman daya shaida aurenku, wanda hakan ba k’aramin aiki bane.

Sannan nayi k’okarin b’oye wannan zancen daga wajen sareefa, don na sani baza ta tab’a jin dad’i ba, taji kayi aure acan koda na wucin gadi ne, bayan tsawon jiran da take yi maka anan.”

Imran ya had’iye yawu jin hakan, zancen aurensa da sareefa ba sabon abu bane, amma a yanzu da yaji shi sai yake tunanin wane irin tunani ne dashi a da? ta yaya ya yarda da auren sareefa alhali bai tab’a sonta ba? da baije cikin mutane ya had’u da Sa’adha ba haka zai rayu kenan bai taba sanin mene ne so ba?

“Aiki ya riga ya zama guda biyu a yanzu, zan raba yarinyar da ruhinka sannan a fara k’ok’arin hanyar da zaka rabu da ita, abinda na gayawa jaamil kenan, kuma a jiya na duba yarinyar a cikin haskena, sai dai abinda na gani Yarima ya wuce tunaninku.”

Sai a sannan ya d’ago da idonsa ya kalleta, kwarjinin siffarta ya cika kowacce gab’a ta jikinsa.

“Ruhinka ya riga ya had’u da jikinta sosai, ba zan iya raba shi tun daga nan ba, dole ne ka kawo yarinyar nan!”

Gabansa ta fad’i a lokaci guda, zancen ya masa girma.

“Ta yaya hakan zai yiwu Naani? ta yaya zan iya kawo ta cikinmu? har yanzu bata san ni WAYE ba.”

Shiru ya biyo baya kafin ta amsa.

“Ba abu ne mai wuya ba, zamu iya komai mu gama har ka maida ita cikin abinda baifi awa biyar ba, sai dai kawai zata fita daga haiyacinta ne.”

Sa’adha ta fita daga haiyacinta? Shine zaisa ta fita daga haiyacinta? Ta yaya zai iya hakan?

“Da bakinka ka shaida min cewa ba son yarinyar kake ba, kuma jaamil ma ya tabbatar mun da kyar ka yarda ka aureta, toh me ya kawo tunani yanzu fuskarka?”

Ya had’iye yawu a hankali, abu na k’arshe da zaiso a yanzu shine Naani ta fahimci wata matsalar daga wajensa, ita d’in wata halitta ce da duk duniyar nan bashi da kamar ta, kuma baya jin zai tab’a sab’a mata a rayuwarsa.

“Ina tunanin yadda hakan zai kasance ne.”

“Zuwa nan da sati d’aya, zan sanar da kai lokacin da zaka kawota, kafin nan ka cigaba da dukkan harkokinka, komai ya kusa zuwa k’arshe ka dawo cikin rayuwarka, ina baka hak’urin dukkan wahalhalun daka sha.”

Daga haka ya san maganarta ta k’are kenan ta sallame shi. A yanzu zai iya komawa wajen Sa’adha, can nahiyar da rabin ruhinsa yake, don ji yake kamar a takure yake yanzu, ta yaya ne wai ya iya rayuwa shekara da shekaru a wannan wajen?

Ya tattara dukkan zancen da suka yi a yanzu ya tura can k’arshen zuciyarsa, ba zai bi ta kansa a yanzu ba, sai ya koma inda hankalinsa zai kwanta tukunna, inda zaiyi tunanin wata mafitar ba wannan ba, don ba zai tab’a iya cutar da Sa’adha da hannunsa ba.

Bayan ya fita jaamil ya shiga kamar yadda Naani ta umarta, sai dai k’afafunsa suka kasa barin wajen, yaji ba zai iya motsawa zuwa koina ba in dai har ba barin wajen zaiyi gabad’aya ba saboda haka ya tsaya anan yana jiran fitowar jaamil, don ba zai iya komawa cikin tarin al’ummar dake jiran fitowarsa avwaje shi kad’ai ba. A lokacin ne kuma kunnensa ya jiyo masa muryar Naani daga ciki.

“Ka tabbatar Yarima ya bar wajen?”

“Na tabbatar ranki ya dad’e.” jaamil ya amsa.

“Zan fad’a maka wani abu ne dana kasa gayawa masa, don yau shine rana ta farko a rayuwarsa da ya fara min k’arya, shi yasa nima ya zama rana ta farko dana fara b’oye masa gaskiyar lamari na. Saboda haka ina so kai ka bani had’in kai mu k’arashe abinda kuka fara, wanda shine dalilin dawowata da wuri.”

Imran yaji mamaki ya sark’e kafafunsa dake rik’e dashi a wajen, abinda yake ji wani abu ne da bai tab’a zatonsa daga wajen Naani ba, Muryar ta cigaba da shiga kunnensa.

“Abinda kuka yi babbar matsala ce da zata iya jawo tab’arb’arewar komai a cikin rayuwarmu gabad’aya, amma nayi shiru ban fad’a muku bane saboda ina tunanin duka zan samu had’in kanku mu shawo kan matsalar, don haka ko ban sami amincewar yarima ba, kai ka saurareni da kyau kaji abinda zan fad’a maka.

Dalilin da yasa ban iya raba ruhinsa da jikin yarinyar a jiya ba shine ruhin ya riga ya kusa had’ewa da nata, ba zai tab’a yiwuwa a raba su ba kuma a sami dukkaninsu, dole sai an rasa d’aya.

Ko dai in an raba su a sami na yarinyar a rasa na yarima, ko kuma a rasa yarinyar a sami nasa, kuma daga yadda na karance shi, ya riga ya gina wata alaqa da yarinyar da ba zai so ya rasa ta ba, kuma ka san cewa idan har babu cikakken ruhinsa a tare dashi burinmu ba zai tab’a cika ba.

Saboda haka na yanke shawarar zamu cire ruhin nasa koda kuwa yarinyar zata mutu.

Nayi masa bayani akasin naka, kuma zan gaya masa ranar da zai kawo ta nan, idan har mun gama komai sauran abubuwan zasu zo da sauqi tunda in har ta mutu, danginta ma zasu karbi hakan ba tare da wata matsala ba!”

●﹏●

Akwai lauje da yawa a cikin nad’i game da chapter nan.

Da farko munji irin tunanin Sareefa akan Imran…na irin kishin da take yi akan yadda Naani ke fifita shi akanta.

Ga ainihin gaskiyar dalilin da yasa take son aurensa ka kuma son kasancewarta bil’adama, me kuke tunani zai faru in har ta san Imran cikin mutane yaje?

Kuna tunanin cewa da gaske Naani tana son Imran ne kamar yadda kowa da kuma shi kansa yake gani?

Me zai faru a yanzu da ya san ainihin abinda zai faru ga Sa’adha?

“Munyi waya dasu Inna, kowa yace a gaishe ka.” 

Nanne ta fad’a tsaye a gaban Imran wanda yake zaune a hannun kujerar falo, kusan awarsa guda kenan da dawowa gidan amma banda waya ba abinda yake yi, zata iya k’irgawa yayi waya da kusan mutane sun kai goma kuma duk daga kamfaninsu, umarni yake ta bayarwa na yadda zasu k’arashe ayyuka kala-kala sannan a lokaci guda kuma kamar yana neman izinin wani abu daga wajen wasu manyansa. 

Bata san meya faru ba ko kuma me yake faruwa ba tun jiya da ya dawo a gigice, lokacin da yake tambayarta me ya sami zuciyarta da kuma sanda ya kaita asibiti, ita ta san ba abinda ya same ta amma daga yadda taga ya damu, sai zuciyar tata ta fara kokwanton ko dai akwai abinda ya same ta ne, tunda sau da yawa a gida ma inna ce ke fara gane rashin lafiyarta kafin ita ta fahimta, musamman in zata yi zazzab’i. 

Amma tunda likitan nan ya tabbatar musu da cewa a yadda suka aunata bugun zuciyarta ne kawai ya sauka k’asa kad’an mamaki ya kamata…ta yaya Imran ya iya gane hakan? ta yaya mutum zai iya gane abinda ya sami zuciyar wani ba tare da an gwada ba? tayi tunanin zaiyi mata wani bayani bayan sun dawo amma taga ya d’auko aiki a computer ya fara, kuma daga yanayin fuskarsa tunda yamman ta fahimci baya buqatar yawan magana saboda haka tayi shiru da tunanin zasu yi maganar washegari. 

Sai gashi ta tashi baya nan sai tulin takardunsa a ko’ina, notes d’in da basu nuna mata ainihin lokacin daya bar gidan ba, tunda wajen k’arfe biyu na dare ma ta farka ta ganshi a kusa da ita. 

Yanzu kuma k’arfe tara na safe ya dawo da alamun gajiya fal! a tattare dashi amma tun shigowarsa  daya zauna a hannun kujera bai tashi ba, danne-danne kawai yake yi a waya yana lalubo numbobin mutane. Duk abinda tazo ta gaya masa sai yace mata yana zuwa, sai dai har ta gama dukkan harkokinta bashi da alamun tashi daga wajen. 

Saboda haka tazo ta tsaya a gabansa da sak’on dake cin zuciyarta tun tashinta a yau da suka yi waya da dasu Inna, Sadiq ta fara kira kasancewar number Innan a kashe take, suka gaisa dasu Surrayya abin mamaki harda Aunty Amarya da kuma Salim, amma banda Suraj uban ‘yan cusguna, wanda ta tabbatar kuma yana tare dasu a lokacin, a hanyar kaiwa Inna wayar ya had’u da Mama Azumi itama suka gaisa, a cikin d’akin Inna kuma Mama halime taje gaisheta itama ta karb’i wayar, daga k’arshe tana jin muryar Inna hawaye ne suka fara zubo mata, masu d’umi da bata san tayi tanadinsu ba sai a lokacin. 

Imran ya kamo hannunta a hankali yana cigaba da aika message d’in da yake a waya, sai da ya tura sannan ya d’ago da kansa daga kan screen d’in ya kalle ta. 

Nanne taji numfashi ya zarce cikin makogwaronta, ta gagara janye idanunta daga cikin nasa, wanda dogwayen gashin jikinsu yayi musu rumfa, hakan yasa a kullum suke da wani irin yanayi dake tsaida tunaninta, yanzu kuma da yake cikin damuwa sai suka juye zuwa kamar na mai jin bacci, ko kuma wanda ake cewa drunken eyes d’innan, D’an tafiyar da yayi kawai tsakanin tashinta da yanzu taji tayi kewarsa fiye da zatonta. Mata nawa ne wai a duniya suke yin sa’a irin tata? 

“Ina amsawa sosai Noory, yau kika kirasu?” 

Muryarsa a hankali ta fita, kamar wani mai jinya, dole akwai wani abu daya same shi wanda ya kamata ta sani. 

“Eh, d’azu muka gaisa dasu harda su mama halime, kowa na gaishe ka.” 

“Nima ina gaishe su, duk da ina jin gobe ma zamu je muyi musu sallama.” 

Mamaki ya fito a fuskarta sosai. 

“Sallama? wani wajen zamu je?” 

Ya murza ‘yan yatsunta a hankali. 

“Wani wajen nake tunanin zamu je, but I’m not yet sure Sa’adha, na kasa tsaida tunani na waje d’aya…abubuwa da yawa sun had’e min a cikin kaina, and It’s like I’m scared of all of them!” 

Tayi shiru tana juya zancen nasa, kamar lokuta da yawa a baya, bata cika fahimtar duka maganganunsa ba. 

“Me yake faruwa toh? na zata zaka min bayani tun jiya da muka dawo shi yasa ban tambayeka ba, gashi kaima kuma ka canja tun jiyan, kamar baka da lafiya, me ya faru?” 

Taga giftawar wani abu a cikin idonsa kafin ya sunkuyar da kansa kan hannunta ya murza shi a hankali, Sau da yawa tasha tunanin ko Imran jinin sarauta ne, yadda yake abubuwa cike da isa, magana misali…kamar ka’ida ne yin shirunsa kafin ya amsa. 

A cikin tunaninta taji ya janyo kafad’unta k’asa, ya durk’usar da gwiwoyinta a gabansa, sannan ya kalle ta sosai, kamar yana shirin fad’a mata wani babban Secret na rayuwarsa. 

“Na tab’a fad’a miki cewa hannunki na da laushi?” 

“Me yasa kake son canja zancen? ka gaya mun da Allah inda zamu je..” 

Ta fad’a da murmushi tana kwace hannayen nata. 

“Ni wa? Sa’adha ban tab’a ji fa kin kira suna na ba, ko sunan nawa bashi da dad’i ne?” 

Ta kalle shi sosai. 

“So kake in dinga fad’ar sunanka?” 

“A’ah…”  Ya sake kamo hannun nata. 

“…So nake ki samo wani sunan mai dad’i ki dinga kirana dashi, yadda zan san duk duniya sunana daban ne a wajenki.” 

Ta shiga motsi da yatsunta dake k’asan nashi, tun da take a rayuwarta bata tab’a ganin mutumin da a duniya bakinta ke mutuwa a gabansa ba irin  Imran, kowa ya riga ya san halinta, sau da yawa bakinta ke bada amsa ba tare da kwakwalwarta tayi nazari ba, amma in a gabansa take sai ta biya zance a cikin zuciyarta sannan ta fad’e shi. 

Yanzu daya tsireta da wad’annan lumsassun idanun nasa so yake ta shiga jero masa sunayen da zata dinga kiransa dasu kenan? don ba d’aya bane balle biyu, suna nan da yawa ta tara su a kanta sai dai ta rasa hanyar da zata fara fad’a ne. 

Ya sunkuyo da fuskarsa dab da tata, sannan a hankali cikin husky muryarsa yace da ita. 

“Bari in shirya habibty zanyi miki bayanin komai insha Allah.” 

Kalaman sun fito ne kamar yana jin tsoronsu. Zuciyarta ta buga a hankali, ta d’ago da idonta ta kalle shi, tsinin hancinsa ya sauka a gefen nata sannan numfashinsu suka had’e waje d’aya. 

“Kin dafa wani abu yau?” 

K’amshin bakinsa na fresh mint ya hura akan lips d’inta, oh God! this felt so good, taji dama su tsaya a haka tsawon awanni, ta girgiza kanta a hankali wanda hakan yasa hancinsa yayi grazing akan nata, Adam’s apple d’insa ya motsa sama da k’asa kafin yace. 

“Toh kina da ragowar na jiya? yunwa nake ji.” 

Dad’in maganarsa ya rungume zuciyarta, ya mamaye kowanne lungu da saqo na cikin kanta, tayi murmushi mai fad’i tana kallon cikin idonsa. 

“Sai kace dan Allah tukunna.” 

Sai ya d’an karkata kansa dab da kunnenta na dama, ya sauke muryasa can k’asa sosai yace. 

“Dan Allah…iya d’an malam!” 

Ta kyalkyale da dariya jin dad’i kafin ta zare hannunta daga nasa, sannan ta mik’e ta nufi kitchen. k’asa-k’asa yabi takun k’afafunta da kallo, rangad’ed’an jan k’unshin bikinta har yanzu bai gama fita ba. 

Zuciyarsa ta matse da tunanin yadda nan da d’an k’ank’anin lokaci zai karya tata zuciyar da mummunan labarinsa a cikin kwanakin da ya kamata su zama na farin cikin rayuwarta, kwanakin da ko lallen bikinta bai gama fita ba. 


Tun shigowarsa gidan, tunaninsa cike yake da abubuwa biyu da yake ta k’ok’arin daurewa, Rud’ani da kuma tashin hankali, yana cikin rud’anin kalaman da jaamil ya gaya masa tun a Muzzaffar, lokacin da ya shak’e shi a jikin bangon fadar Naani bayan fitowarsa. 

“Me ya same ka ne yarima? me ya shiga kwakwalwarka? wannan dalilin shi yasa Naani tak’i gaya maka ainihin abinda zai faru, yanzu kuma da ka jiyewa kunnenka me ya kamata kayi? kamata yayi ka shak’e ni kana zargin harda ni za’a kasheta? ita wace ce a wajena ko wajenka? kar ka manta fa ta shigo cikin rayuwarka ne saboda kuskuren da kayi tun farko, kuma nine sanadin da yasa ka same ta. 

Sanadin da muka yi na k’arya wanda zai k’are nan da wani k’ank’anin lokaci, nan wajen shine rayuwarka yarima, anan danginka da duk wani tallafinka yake, can d’in da kake hangowa wani abu ne da ba zai tab’a d’orewa ba. Ya kamata ka janyo hankalinka daga duk inda ya tafi, nida Naani da kake tunanin zamu yi maka ba daidai ba mune sanadin duk wani abu daka samu a can, don ba don Naani ba babu ta yadda zaka iya samun jikin bil’adaman da zaka iya rayuwa a cikinsu, ba don ni ba kuma babu ta yadda zaka yi ka samu yarinyar a matsayin matarka. 

Kaje cikinsu ne don aikin da Naani ta saka, ba don ka gina wata rayuwar da a yanzu kake mana kallon wad’anda zasu kwace ta ba, karka manta ko an cire ruhinka daga jikinta kuma ta rayu ba zai tab’a yiwuwa ka cigaba da zama da ita ba. Mun tsara hakan tun lokacin dana same ka da zancen ka aure ta kuma ka tabbatar min da zaka bada had’in kanka mu gyara kuskuren daka jawo tun farko. 

Ko sau d’aya zuciyata bata tab’a yarda da zancenka na cewar baka son yarinyar ba amma nak’i nuna maka ne saboda na san bani da wata mafitar data wuce wannan a lokacin, sannan nayi zaton idan komai yazo k’arshe zaka iya daure zuciyarka mu k’arasa abinda ya kaimu tun farko wato aikin Naani, nayi zaton zaka daure zuciyarka ka farantawa halittar data tallafe ka har ka kai wannan matsayin da kake a yau, na zata zaka iya daurewa zuciyarka kamar sauran abubuwa da yawa a baya da muka sadaukar don samun farin cikinta…amma ban san cewa ka raba zuciyar taka gida biyu ba, ban san cewa ka bawa yarinyar irin matsayin da kake bawa Naani ba, ban san kuma cewa zaka iya had’a Naani da wata k’ask’antacciyar halittar…” 

Imran ya tuna marin daya d’auke fuskarsa dashi a lokacin har saida jini ya fito ta idonsa, sannan a hankali muryarsa tace. 

“Sunanta Sa’adha, ka sake kiranta da k’ask’antaciyar halitta ko sau d’aya ne kaga yadda zanyi kaca-kaca da fuskarka.” ya fad’a kamar iya abinda yaji yace kenan. 

Jaamil yasa hannu ya shafo jinin daya fito sannan ya d’ago ya kalle shi, baice komai ba sai ajiyar zuciya kawai da yake fitarwa kamar yana son danne wata zuciyar dake gaya masa cewa ya rama. 

Imran ya sake shi sannan ya matsa baya yana cigaba da kallonsa. Ya riga ya sani, duk abubuwan daya fad’a gaskiya ne haka suka tsara tun farko, sai dai a yanzu baya jin zai cigaba da biyewa wannan gaskiyar, don zuciyarsa ta riga ta yadda da wata gaskiyar da yake ganin duk duniya babu wata halittar data isa ta kore hakan, gaskiyar cewa yana son Sa’adha kuma ba wani abu da zai bari ya shiga tsakaninsa da ita ko ya kawo k’arshen zamansu. 

Aikin da Naani ta tura shi cikin bil’adama ba zai yiwu ba sai da b’arin ruhinsa wanda yake jikin Sa’adha, abinda suke kwad’ayin samu kenan da har suke ikirarin zasu fitar dashi unrespect of duk wani hali da Noorynsa zata shiga. 

Amma yadda ya tsaya a wajen nan, ya d’aukarwa kansa alk’awarin cewa abinda su Naani ke shirin yi ba zai tab’a faruwa ba, zai kare Sa’adha da dukkan iyawarsa, zai d’auke ta zuwa wajen da d’ayansu ba zai tab’a ganota ba har sai ya sami hanyar da zai iya kawowa Naani abinda take buqata zuwa nan da wata biyun da komai zai faru, zai nemo yadda zaiyi ya iya rik’e DUTSEN NIL da b’arin ruhinsa guda d’ayan ba tare da na jikin Sa’adha ba, zai nemo dukkan k’arfin da zai iya kawo shi har gaban Naani, In ta samu abinda take so ya san zata barshi ya samu damar da zai iya k’arasa rayuwarsa ba tare da takurawar d’ayansu ba. 

Story continues below


Don a yanzu ya riga ya yarda cewa dukkan wani farin cikinsa yana tare da Sa’adha ne, ba zai tab’a iya sake dawowa cikin su ya cigaba da rayuwa ba, zai zauna cigaba da zama a matsayin bil’adama koda Naani baza ta cigaba da tallafarsa ba, koda kuwa hakan zai zama sillar rasa ransa! 

Ya taka k’afafunsa baya a hankali yana cigaba da kallon jaamil kafin ya juya da sauri da niyyar barin wajen. Daga can gabansa tarin cinkoson al’umma ne taf! dake jiran fitowarsa, amma bai damu ba, zai wuce ta cikinsu ya koma wajen Sa’adha tun kafin Naani ta samu labarin abinda ya faru yanzu tsakaninsa da jaamil. 

“Do you think she wants you!?…” 

Muryar Jaamil ta tsaida shi cak! a wajen. 

“Bata san WAYE kai ba yarima, bata san ainihin waye kai ba, labarin wani Imran kawai ta sani, wanda babu shi a duniyar nan…akwai tarin dalilan da zasu k’alubalanci zamanku ko daga ‘yan uwanta. 

Idan kana son shirmen daka tsara a cikin kanka ya cigaba da faruwa dole sai ka sami had’in kanta tukunna wanda ba zai tab’a faruwa ba, daga lokacin da ka gaya mata gaskiya daga lokacin zata rabu da kai, saboda ba kai take so ba, Imran d’in da muka yi planting akanta ta sani kuma shi kad’ai take so!” 

Wannan zancen shi ya kawo tashin hankalin tunaninsa na biyu, don gaskiyane Sa’adha bata san ainihin waye shi ba kuma bashi da tabbas cewa in har ta sani d’in zata cigaba da bashi trust d’in da yake samu a wajenta, saboda haka bashi da zab’i a yanzu illa ya fad’a mata gaskiyar da yake ta yiwa ado da k’arya, in ba haka ba dukkan wani abu daya tsara ba zai tab’a yiwuwa ba. Komai ya riga yazo k’arshe, kuma amsar da zai samu a wajenta ita zata yi determining k’addarar da zata faru nan gaba a rayuwarsa! 

“Toh wanne zaka fara, wankan ko cin abincin?” 

Ya d’ago idonsa ya kalleta tsaye daga jikin dining area, sannan tarin warmers d’in dake zube a gefenta.! 

Yaya rayuwarsa zata kasance bayan yau? 

Me zai faru dashi anjima? 

Zai sake ganin irin wannan kulawar ta Sa’adha? 

Zai sake ganin irin wannan kallon daga gareta? 

Ya Allah! 

***** 

“Me kika dafa mana?” 

Ya fad’a sanda yaja kujera d’aya ya zauna, Nanne ta fito daga kitchen rike da cups a hannunta ta kalle shi, ya canja kayansa zuwa wata jallabiya mai kyau light brown. K’amshin turaren jikinsa ya had’e dana sabulun da yayi wanka. 

“Me kika dafa Noory?” 

Muryarsa can k’asa ta sake fitowa yadda duk sanda yayi hakan yake sata jin wani iri. Me yasa ne muryarsa take da tasiri akanta? 

Ta matso kusa dashi ta bud’e warmers d’in, k’amshin wani abu curry, albasa da kayan k’amshi ya cika hancinsa, bai san cewa da gaske yana jin yunwa ba sai a lokacin don hargitsin dake cikin kansa yasa ya manta da sunan wani abu abinci, kuma a d’azu ya fad’a ne kawai don d’auke lokacinta daga amsarsa sa da take jira, don yana fatan kowanne k’arin lokaci ya taho masa da k’arin karfin gwiwa. 

Ta zuba abincin a plate d’aya kamar yadda suke ci a koyaushe, yadda ya koya mata sannan ta zauna, a lokacin ya lura cewa akwai abinda yake damunta, idanunta sun nuna masa hakan duk da irin k’okarin da take na kar ya gane. 

Shigarta ta dark purple kaya ya mata kyau sosai, duhun kayan ya k’ara fito da hasken fatarta da a yanzu ta zama So fresh mai laushi, d’ankwalin kanta ya zame kad’an yadda yana iya hango lallausar sumar kanta, bak’a wuluk sai shek’i take yi, yaji yana son zura hannayensa ciki yadda zasu lume cikin laushin gashin, ya salam! ya janye idonsa daha kanta da sauri don idan ya cigaba da kallonta zai iya mance duk wani abu dake gabansa a yanzu ya jawo ta zuwa jikinsa. 

“Duk sanda nake cin abincinki Noory sai inyi ta mamakin me nake ci ne a baya.” 

Ta d’age gira d’aya tana kallonsa. 

“For example kinga irin wannan abincin, a kwakwalwata gabad’aya babu irin tunaninsa, ban san ana yi irin su ma ba balle inje in siya.” 

“Irin wanne kake ci toh?” 

“Sau da yawa nafi shan tea ko duk wani abu cereal, amma duk ranar da zanyi girki, to ba wuce taliya ko farar shinkafa…shi yasa a yanzu nake mamakin yadda akayi na rayu a baya.” 

Ta d’anyi murmushi kad’an. 

“Kuma kin san duk sanda zanyi girki ban fiye amfani da plate ba?” 

“A tukunya kake ci kenan?” 

Ya d’aga kansa ya na kallonta. 

“Kuma akan wuta, saboda in nazo d’and’anawa inji ko ya dafu, full cokali nake d’iba kuma sai in d’and’ana fiye da sau ashirin…” 

Dariya ta kamata a lokaci d’aya. 

“Ashirin fa? ai ka cinye abincin.” 

“Kamar kin sani, in na gama sai in ganshi d’an kad’an a tukunya, gashi kuma ni na kusa k’oshi…kinga ba amfanin plate kenan, sai kawai in k’arashe abuna da serving spoon d’in dana fara ci.” 

Nanne ta kyalkyale da dariya tana rufe bakinta, ya lumshe idanunsa a hankali yana kallon yadda take dariyar sosai. 

She’s so innocent! mintuna kad’an tana cikin damuwar da har fuskarta ta nuna yanzu kuma ta koma farin ciki, yaji kamar ya jawo ta ya rungume ta sannan ya b’oye ta daga dukkan wani hargitsin dake gabansu. 

Idanunsa na kanta gabad’aya ranar, yana kallon dukkan activities d’inta kamar yana yi musu kallon karshe, bai san me zai faru ba, so he wanted to capture every single memory of her, yadda daga baya zai samu abinda zai rarrashi zuciyarsa kafin sanda da zata yi rauni ta karye gabad’aya. 

A lokacin da ya dawo daga sallar maghriba, a sannan ya zab’i lokacin ya zama sanadin k’addarar rayuwarsa, ya zaunar da ita a falo lokacin da ta kawo masa yankakkun fruits masu sanyi a cikin bowl, ya zaunar da ita a gaban zuciyarsa dake bugawa kamar zata fito waje. 

Ya zaunar da ita don gaya mata gaskiyar WAYE SHI! 

“Sa’adha kin san a yanzu ke matata ce koh?” 

Nanne ta d’aga kai a hankali tana kallonsa, ya sake damk’e hannuta a cikin nasa kafin ya cigaba. 

“Kin san kuma cewa babu wani secret tsakanin mata da miji koh? tun daga ranar da aka d’aura mana aure komai namu ya zama d’aya, walau farin ciki ko bak’in ciki bai kamata d’ayan mu ya b’oye wa d’aya ba…” 

Yayi shiru tare da yin ajiyar zuciya yana kallon hannusa dake sarke nata, zuciyarsa na tattaro dukkan kalaman da yayi bitarsu  fiye da kirgen mai kiga. Yayin da Nanne ta cigaba da kallonsa blankly tana jiran taji abinda yake shirin fad’a mata, taji dalilin da yasa yake cikin damuwa kwana biyu. 

“Ina so ki fahimce ni sosai a yanzu, ki bud’e kwakwalwarki ki fahimce ni dan Allah…Sa’adha na miki wani babban laifi tun daga farkon had’uwata dake har zuwa yanzu, nayi miki laifi dake dasu Baffa dama duk wanda ya san labarin auren mu..nayi muku laifin da za’a iya kira da yaudara koma wani abu fiye da hakan.” 

Zuciyarta ta buga amma a hankali sakamakon mamaki daya zagaye tunaninta a lokaci d’aya. Laifi kuma? wane irin yaudara? 

Ya sake wata dogowar ajiyar zuciyarsa yana kallon carpet d’in da suke kai unseeingly, sannan ya cije gefen lebb’ensa kamar zai datsa shi. 

Lokacin daya d’ago da kansa, yanayin idanunsa sun canja daga haske zuwa wata kala da tayi kama da silver, wani abu da Nanne bata tab’a gani ba. 

“Sa’adha ni ba irin jinsin halittarki bane, I’m not human.!” 

Ya fad’i kalaman da dukkan wata dauriyarsa yana cije bakinsa kamar baya son su fito, don ba don tana kusa dashi sosai bama ba lallai bane taji me ya fad’a ba. 

Ya cigaba da kallonta da idanunsa so stiff a kanta, yana karantar yadda fuskarta take absorbing kalaman, bata ce komai ba? me take tunani? anya kuwa taji abinda ya fad’a? ya tsirawa idanunta ido bada ko k’iftawa ba amma ya kasa tsinto wata ma’ana guda d’aya a cikinsu, they were blank! watakila can k’asansu lullube yake da tarin tsoro, watakila kuma tana tattara dukkan k’arfinta ne waje d’aya yadda zata kwalla ihu a kowanne lokaci. 

Wani abu mai kama da lokaci ya tsaya cak! a cikin kan Nanne, ta maimata abinda ya fad’a a cikin kanta sau ba adadi, tana rarraba su filla-filla don ta nemo real ma’anarsu. 

“Kai ba mutum bane?” 

She tried the words out, ko zata ji ma’anar ta fito akan lebb’enta amma ta gagara fahimtarsu, sai mamakin yadda harafan suka had’u suka yi forming sentence d’in. 

“Yes, I’m an illusionist, wata halittar daban da taku.” 

Ta tsira masa ido tunaninta baya aiki a lokacin, shima kallonta yake da idanunsa a tsaye kyam! zata iya rantsewa tunda take dashi bata tab’a ganinsa so serieos irin yanzu ba, taji tana nutsewa cikin a idanun nasa zuwa wani k’arshe mai nisa, miles and miles away! amma duk nisan da ta kai ta kasa gano ma’anar abinda ya fad’a. 

“Okay.” Ta fad’a a hankali cike da mamakin yadda muryarta ta fito so calm, watakila don tunaninta ya riga tsaya ne a lokacin. 

“What?” Ya fad’a a fili yana kallonta, gaya mata yayi fa shi ba mutum bane and the best amsar data samo shine Okay? 

“Sa’adha ki fahimce abinda nace kuwa?” 

Ta girgiza kanta da sauri. 

“Ban gane ba Imran, ban gane me kake nufi ba.” 

Da gaske ya yarda bata gane d’in ba, don tunda yake da ita bai tab’a jin ta fad’i sunansa ba sai yanzu. Zuciyarsa ta cika da wani sabon hope d’in daya manta yaushe rabon da yaji irinsa, ya sake damk’e hannunta kamar yana tsoron zata iya kwacewa a kowanne lokaci ta gudu. 

Story continues below


“Ki kwantar da hankalinki kinji? zanyi miki bayanin komai tun daga farko…you don’t have to talk.” 

Ta had’iye wani katon abu a mak’ogwaronta tana kallonsa da idanunta so wide kamar zasu fito. 

“Ni ba mutum bane Sa’adha…” Ya sake maimata abinda bata ganewa. 

Nanne bata san ko akwai iskar dake fita da a kirjinta ba koma tana iya numfashi ba a lokacin, kwakwalwarta ta riga ta gama cakud’ewa, da kyar ta iya maida tunaninta kan muryarsa dake cigaba da magana. 

“Aljanu basu da jiki amma mu muna dashi, suna iya shiga jikin bil’adama mu kuma bama iyawa ba tare da bin wata hanyar ba, sannan jinsin Aljanu yana da yawa a doron k’asa yayin da mu kuma ‘yan kad’an ne a duniya, bamu da yawa sosai. Sannan akwai abubuwa da yawa wanda muka fip aljanu k’arfin yi, sai dai kamar yadda mutane suka fisu daraja haka suma suka fimu daraja saboda suna iya mu’amala dasu, mu kuma bama iyawa 

Wasu daga cikin mutane da suke da sani akan aljanu da rabe-rabensu su sun san wani abu game damu amma ba komai ba, kuma suna danganta mune da jinsin bak’ak’en aljanu tunda sun san muna posessing wasu abubuwan da aljanun basa iyawa sai dai manyansu. 

Akwai wajaje da yawa a duniya inda irin jinsinmu suke rayuwa, amma sunan nahiyar dana fito ‘Muzzaffar” 

“Ta yaya….” 

Muryarta fito daga can k’asan makogwaronta amma yayi saurin katseta. 

“Shshshsh…you don’t have to talk remember?” 

Ta d’aga kanta a hankali, har yanzu hannayenta na cikin nasa. 

“Kin tuna abinda na fad’a miki ranar da aka kawo ki gidan nan? every single word a lokacin gaskiya ne Sa’adha, tun da na tashi a rayuwata ban tab’a sanin iyayena ba, sun rasu tun kafin in san kaina, haka kuma bani da wani dan’uwa na jini dana sani, duk sun mutu a wani yak’i daya had’amu da wasu irin jinsinmu dake wata nahiyar. 

Na tashi babu gata a cikin wata irin rayuwar da babu komai a cikinta sai fafutukar neman yadda zan rayu, nayi bauta a wajen irin jinsinmu da yawa kafin daga bisani na koma bawan wani mai suna ‘Darshan’ na shekara uku a wajensa kafin daga baya ya tattara dukkan dukiyarsa da nufin komawa Muzaffar, don a lokacin muna wata nahiya ne da ake kira ‘Sabeel’. 

Dukiyarsa ta had’a harda tarin bayinsa wanda yayi niyyar zuwa Muzaffar d’in ya sayar dasu da tsada, kuma a cikin bayin nasa har dani Sa’adha. Sai dai a ranar da muka shigo Muzaffar a daren ya rasu, lokacin yana kwance a d’akin hutawar daya kama na cikin kasuwar garin, mutuwarsa tasa kowa ya rud’e a wajen kasancewarsa baqo a gurin, a cikin wannan hayaniyar na samu na kwance sark’ar da aka d’aure ni na gudu. 

Na fad’a can cikin Nahiyar muzaffar na samu wani wajen da ba wanda ya san ni na cigaba da rayuwata. 

Kin tuna na fad’a miki na samu tallafin wata halitta bayan duk wahalhalun dana sha a baya? wannan halittar itace Naani, Shugabar Nahiyar Muzaffar, na had’u da ita ne lokacin dana rasa duk wani tallafi a rayuwa, ita ta rik’e ni da dukkan kulawarta, ta jawo ni jikinta, ta bud’e min sabuwar duniyar dana sami komai dana rasa a baya, ‘yan uwa, d’aukaka, matsayi da kuma tarin abubuwan da a da nake musu hangen nesa. Ta maida ni tamkar d’anta ta lak’aba min sunan YARIMA. 

Nima a lokacin na d’auki dukkan soyayyata na dank’a mata, na yarda cewa bani da wani farin ciki a duniyar nan daya wuce nata, saboda haka duk wani abu daya zama na taimako gareta bana tab’a kasawa wajen aikata shi. 

Story continues below


Jaamil d’a ne a wajen ‘yaruwarta kuma suna zaune su duka biyun a wajenta, tare dashi na taso a masarautar Naani, ya zama tamkar d’an uwa na kuma abokin da nake dashi duk duniyar nan. 

A cikin haka ne ta kirani da buqatarta na son samun wani dutse da take wanda za’ayi amfani dashi don samun k’arin kariya a nahiyarmu, ta shaida min a lokacin cewa dutsen yana hannun bil’adama ne a cikin wani kamfani da suka nannad’e shi a matsayin Award d’insu banda haka su basu san wani amfaninsa ba. 

Naani zata iya bani damar da zan shigo cikin mutane a dare d’aya in d’auko mata shi in koma, sai dai in muka yi hakan ba zai taba yi mana amfanin da muke so ba, dutsen yana aiki ne kawai ga duk wanda ya same shi ta tsaftatacciyar hanya, wato ko dai mai shi ya d’auka ya baka da yardarsa, ko ka same shi ta hanyar guminka ko kuma duk wata hanya da zata kawo shi hannunka da take mai tsafta. 

Saboda haka ta kira ni a lokacin ta gaya min cewa zata tura ni cikin mutane, inje wannan kamfanin a matsayin ma’aikaci, inyi aikin da zaisa har su yarda dani, wannan dutsen a matsayin Award ya shigo hannuna. 

Sa’adha tunda nake a da, ban tab’a bada hankalina akan sha’anin bil’adama ba, a kullum ina musu kallon wasu halittu dake can nesa damu wanda bamu da alaqa ko kad’an tare, a iya inda nake samun labarinsu shine in na shiga cikin Aljanu wanda su suka sansu sosai. 

Saboda haka a sanda ta fad’a min hakan, ban kawo komai a raina ba, naji a jikina ne cewa zanje inyi mata aiki kamar sauran dukkan ayyukan da take sani. 

A cikin abinda baifi wata biyu ba, Naani ta samar mana da jiki mai irin siffar mutanen da zamu shiga cikinsu nida jaamil tunda na gaya miki bama iya possesing siffar mutane, jaamil zai zama mai taimakamin a komai saboda haka Naani ta bashi damar da zai iya komawa ainihin halittarsa a kowanne lokaci kuma ya iya komawa Muzaffar, ni kuma bani da ikon yin hakan saboda kar hankalina ya rabu gida biyu. 

Naani ta had’a ni da wani aljanin daya karanci halayen mutane ya koya min abubuwa da yawa na mu’amalarsu da kuma yadda suke rayuwa. A lokacin na dinga jin kamar ba zan iya komai ba, don ganin rayuwarku nayi kamar irin tamu ta kurkuku, lokacin da za’a kulle ka a hana ka duk wani freedom na pissibilities d’inka. 

Amma tun daga ranar dana sauko cikin mutane Sa’adha, tun daga wannan ranar rayuwata ta canja, ta canja in a way da ban san ta yaya zan miki bayani ba, naji ne kawai kamar a dawo min da rayuwar dana rasa a baya, rayuwar da zanga iyayena da dukkan ‘yan uwana. 

Naje kamfanin ni da jaamil nayi dukkan wasu cike-cike irin na mutane da Naani ta shaida min cewa an gama samo min aikin da komai kawai abinda zanyi kenan, daga nan muka tafi neman gida. 

Aka kaimu wani gida da ake masa gyara har na biya deposit, wannan gidan da yake layinku, inda na fara ganinki kin dawo daga islamiyya…” 

Ya d’anyi shiru kafin a hankali yace. 

“Kin tuna….?” 

Bata ce komai ba sai kallonsa da take kawai tana k’ifta ido, ya sa hannayensa biyu harda wanda yake had’e da nata yayi cupping fuskarta a tsakanin tafin hannun nasu. 

Numfashinta a lokacin fita yake tare da nasa cikin nutsuwa kamar sunyi setting d’insa a tare. Imran ya kalli cikin wad’annan chocolate idanun nata, cike suke da d’imbin tambayoyi da kuma confusion, abinda yake hangowa a cikin kansa zata yi kenan tun ranar da aka d’aura musu aure. 

Sai dai a lokacin ya gano banbancin tunaninsa da yanzu, a tunaninsa bayan duk wannan experessions d’in akwai tarin tsoro fal a cikinsu – amma a yanzu babu koda d’igon wannan tsoron, babu shi ko kad’an! 

“I can’t go on…ki fad’a min me kike tunani dan Allah.” 

Ta sake k’ifta idonta a hankali ba tare da tace komai ha, shima yayi shiru yana kallonta, he yana iya karantar abinda ke idonta clearly…tana cikin rud’ani kuma shima abinda yake ji kenan, sai dai yadda idanunta ke fluttering akansa yasa masa jin wata irin kasala a jikinsa, yaji d’umin  fuskarta dake cikin hannunsa yana tura wani abu kamar electricty a kowacce jijiya ta jikinsa, a cikin tunaninsa ya hango yadda zai iya sunkuyawa a hankali yaji d’umin dake kan lips d’inta. Yayi saurin k’ifta idonsa kafin yace. 

“I don’t want you to be afraid…kar kiji tsorona Sa’adha dan Allah.” 

Muryarsa mai taushi ta fito a hankali kamar cikin rok’o, amma shi kansa a lokacin ya san abinda ya fad’a bashi da ma’ana, abinda ya kamata taji kenen, TSORO. Taji tsoron shi d’in dake zaune a gabanta yana gaya mata cewa shi ba mutum bane, shi wata halittar ne daban sab’anin tata ta mutane. 

Nanne ta sake k’ifta idanunta a hankali tana kallonsa, shima kallonta yake yi kyakkyawar fuskarsa kusa da tata sosai! kamata yayi ta fizge daga rik’onsa, tashi ta bar d’akin, ta bar gidan, ta bar unguwar ma gabad’aya, ta tafi duk wani waje da zai nesanta ta dashi. 

“Bana jin tsoronka…!” 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *