ABBAS
CHAPTER 17
Umar na tsaye jingine da jikin mota, Fateemah kuwa na gefe har yanzu ‘kirjinta rungume da kayan Munnira idanunta banda ruwan hawaye babu abinda yakeyi, ita kanta bazata ce ga abinda ke sata kukan ba amma yanayin datake jin zuciyarta ayanzun shi yafi komai ‘daga mata hankali, tare da karya mata zuciya.
Abbas ma tsaye ya juya musu baya, sam baya son ganin hawayen Fateema koka’dan hakan na matu’kar soya masa zuciya, baya jin cewa ha’duwar su da Mahmud ze yi kyau koka’dan, jiyake kamar babu wanda ya ta6a 6ata masa rai kamar Mahmud ‘din aduk fa’din rayuwarsa ,hannunsa ‘daya cikin aljihunsa yayinda ‘dayan yake ri’ke da wayarsa bayan ya gama ‘kiran Mahmud yaga baya ‘dagawa, ransa duk a6ace shi tunaninsa yabashi akan Mahmud ya’ki ‘daga wayar ne dagangan dan kawai ya wula’kanta Fateemah .
*****
Cikin ‘kan’kanin lokaci mutane suka zagaye wurin kowa na fa’din albarkacin bakinsa, da ‘kyar akasamu aka ciro motar Mahmud ‘din daga ‘kar’kashin ‘dayan motar se da ma suka ‘daure motar Mahmud daga baya ‘dauri sosai yanda ba ze motsa ba, tare da jan babban motar zuwa baya ka’dan sannan akasamu aka raba tsakaninsu.
Da fitowar Motar Mahmud ‘din kuwa sai da kowa jikinsa yayi sanyi wasu ma kauda kansu sukayi dan baza su iya kallansa ahaka ba.
Sai da ambulance yazo kafin aka ciro shi tare da duk wani abu nashi na amfani dake cikin motar aka me dashi cikin ambulance ‘din zuwa asbiti.
Tun a cikin ambulance aka fara bashi taimakon gaggawa har zuwa asbitin suna zuwa kuwa aka wuce dashi A&E (Accident & Emergency) likitoci kusan uku ne suka ha’du akansa domin ceto rayuwarsa cikin gaggawa.
Da ‘kyar suka samu suka daidaita numfashinsa tare da yi masa dressing ‘din raunikan daya samu.
Bayan hakan ne wani daga cikin wa’danda suka taimaka masa har zuwa asbitin da kuma drivern babban motar da wani likita sune suka fara neman wanda zasu ‘kira cikin ‘yan uwansa.
Misscalled ‘din _Oga_ _Abbas_
Suka fara gani da be wani da’de da ‘kiran wayar ba dan haka shi suka fara dannawa ‘kira.
Abbas na tsaye a inda yake tsayen tun ‘dazu be motsa ba, ya dai ‘kira layin mahaifinsa yasanar dashi cewa yashigo Lagos sannan ya’kira wani abokinsa ma sukayi magana, daganan yaci gaba da tsayuwa jira kawai yake yi yaga zuwan Mahmud gidan tunda kam baya office dole ai idan yagama abinda yakeyi ‘din gida ze dawo.
Wayarsa ce tafara ‘kara alamar shigowan ‘kira, yana ‘dagota kuwa yaga sunan Mahmud na yawo a fuskar wayar.
Da sauri Abbas ya amsa ‘kiran tare da yin shiru danjin wace ‘karya Mahmud ze shirga masa.
Ga mamakinsa kuwa sai yaji ba muryar Mahmud bace ke tashi acikin wayar yake fa’din ” _hello_ !
_helloo_ !!
Da mamaki da kuma izzah Abbas ya amsa da fa’din ” _Yes, who is on the_ _line_ ?
STORY CONTINUES BELOW
Bayani aka yi masa akan abinda yafaru ata’kaice.
Sosai Abbas yaji zuciyarsa ta karye da jin al’amarin amma be nuna afili ba yanda zasu gane koda ya juyo ma cewa kawai yayi da Umar su shiga mota suje wani guri.
Har se da suka hau titi kafin Abbas ya sanar da shi asbitin da zai kaisu.
Teemah kam bata magana sai aikin hawaye bugun zuciyarta ne yasake ‘karuwa fiye ma dana baya koda suka isa asbitin ma ita da ‘kyar take ciran ‘kafa take binsu abaya domin gaba ‘daya ‘kafafun nata nawi suka yi mata, hakan ma bata ji abinda yafaru gaba ‘daya ba dan har suka isan Abbas beyi musu bayani cikakke ba, zuciyarta ce ke gaya mata cewan Mahmud ne ya illata Munnira shine har aka kawota nan shiyasa suka zo.
Daga Abbas sai suka ‘kira layin Abbah shima sukayi masa bayani.
Hankalin Abbah ba ‘karamin tashi yayi ba dan shi baya ma ‘kasar dan haka ya ‘kira Anty ya sanar da ita sunan asbitin yace taje ta duba halin da Mahmud ke ciki kafin ya dawo, yace mata zuwa anjima shima ze dawo insha Allahu.
Isan su Abbas keda wuya sai ga Anty ma ta taho itada da Munnira dayake har alokacin basu rabu ba suna tare lokacin da Abbah ya ‘kira Anty.
A reception suka zauna gaba ‘daya suna jiran ji daga likitocin, domin sun ce sai zuwa nan da 30mins zasu ganshi kafin nan an ‘dan kintsa shi kuma watakila ze farfa’do ya dawo hankalinsa.
Duka abin nan dake faruwa
Abbas da Umar ne ka’dai suka sani shima Umar ‘din be da’de da samun labarin ba,bayan isowansu ne suka je tare wurin likitan inda shi yayi musu bayanin komai, Teemah kam har yanzu bata san abinda yafaru ba.
Shigowarsu Anty ne ma ya ‘dan fara bata mamaki ganin ta tare da Munniran ga kuma Antyn hankalinta duk atashe.
Da farkawar Mahmud kuwa doctor ya basu damar shiga su ganshi, nan suka shiga gaba ‘dayansu zuwa ciki.
Anty ne ta wuce gaba da sauri ta isa gaban gadon tana ‘kiran sunan shi.
Wanda Teemah ma sai alokacin ta farga da wanda ke kwance agadon, ai bata san lokacin da ta zubar da kayan dake hannunta ba ta taho da gudu itama tana fa’din ” _Yah Mahmud kaine anan?_ me _yasameka haka,Yayah Mahmud dan Allah ka tashi, ka tashi kaga Yayah Abbas yazo_ ?”
Anty na kuka tana ‘karawa tare da kamo hannunsa wanda be samu raunin sosai ba, Teemah ce tashiga tsakaninsu dan ita ta na zuwa sai ta shige gaban Antyn tana kukan fitan rai.
Abbas da Umar kam tsayuwa sukayi suna ‘kara jinjina al’amari na ubangiji, Umar tunani yakeyi awanni ‘kalilan da suka wuce rabuwarsu da Mahmud yana cikin ‘koshin lafiyarsa, sai gashi yanzu kwance agado cikin yanayin da bama ze iya fasaltashi ba.
Ahankali ya bu’de idanunsa ya sau’ke su akan Teemah gefe da ita kuma Anty ce yaga dukkan su suna kuka.
Ga Munnira ma daga ‘dayan 6angaren itama tana share hawaye, can tsaye kuma Umar ne shida Abbas da rabuwarsu yanzu kusan wata uku kenan.
Murmushi yayi tare da motsa hannun nasa da ‘kyar ya ri’ke hannun Fateema dake risgar kuka iya son ranta.
” _Yah…..Mahmud me yasame ka haka?….._
Teemah tasake fa’da cikin kuka.
Anty kam kasa magana tayi banda hawaye babu abinda take sharewa, Abbas kansa dauriya kawai yayi beyi ‘kwalla ba amma inkaga yanda jijiyoyin kansa duk suka mimmi’ke, idanuwansa suka yi jajazur take zaka fahimci halin da ke ciki da inda zuciyarsa ta dosa.
” _Yayah Mahmud ina hannunka….. guda ‘dayan yake……waye ya cire maka_ ?
Teemah tasake tambayarsa tana bin jikinsa da kallo har zuwa fuskarsa.
Murmushi yayi tare da waro idanunsa akanta nan ta ‘kara ganin yanda cikin idanunsa suka koma tamkar jini gaba ‘daya sun riki’de sun canza launi.
STORY CONTINUES BELOW
Ahankali takai hannunta saman idanunsa tace ” _Yayah……idanunka ma sun koma jini….Yayah……_
” _Allah ne ya min haka Fateemah kiyi min addu’ah kinji_ “
Yayi maganar da ‘karfin hali domin shi ka’dai yasan abinda yakeji acikin jikinsa, ‘kafafuwansa ma gaba ‘daya sun sami matsala dama ana shirin shiga dashi ‘dakin thearter ne a’karasa cire ‘kafafun domin bazasu sake yi masa amfani ba.
Kafin hakan ne ya nemi ganin iyalansa bayan farkawarsa daga ‘dan gajeran suman daya yi
shine aka shigo dasu.
Toh yanzun ma likitocin da suka ga kamar hayaniyan zai masa yawa zuwa sukayi suka ce su fita su barshi ya samu hutu.
Da kansa yace a’a abarshi yagana da iyalansa bayi son hutun komai.
Gurin shiru ko motsin kirki babu me yi acikinsu, kowa yayi tsit hatta su Fateema ba ihun kuka sukeyi ba sai de hawaye kawai suke sharewa.
Da ‘kyar muryarsa ke fita amma ahakan ya dubi Anty yace ” ku daina kuka mana Anty, ku daina min kuka, ba gani nan ba zan warke ai insha Allahu”
” Haba Mahmud ka dube ka fa bakaga yanda ka dawo bane?
” _Karki damu Anty! haka dama Allah yaso gani na, kuyi min addu’ah kawai kinji Anty, idan kina kuka Fateemah ma bazatayi shiru ba!_
Sai ya juya ya kalli Munnira yace
” _Share hawayenki ki daina kuka kinji, na riga na yafe miki tun lokacin dana san gaskiya, kema ki yafe min nasan nayi ta 6ata ranki abaya, dan… Allah_ _kiyafe min kinji Munnira, ban’ki auren ki dan bana sonki ba kawai de bani da burin yin_ _aure da wuri ne alokacin shiyasa, amma kun kowa ya kasa fahimta_ _ta………._
Kai ta jijjiga masa itama Munniran tare da fa’din
” _kabar ro’kona Mahmud ni ya kamata ince kayafeni, har abada ni me laifi ce_ _agareka nasani ni kaina bazan ta6a yafewa kaina ba, domin nasan na_ _cutar da kai, ayanzu kam bani da kalmar da zan ro’ke’ka gafara_ _sai de fatana Allah ya baka lafiya Mahmud ya in ganta rayuwarka_ _kai da zuri’arka gaba ‘daya_ “
Murmushi yayi mata itama ‘kasan ma’koshi yace ” _nagode Munnira_ “
Hawaye yaji ya sau’ka akan hannunsa, sai ya waigo ahankali ya dawo da kallonsa wurin, ganin Fateemah yayi tana ta na ta 6ul6ulo da hawaye.
Suna ha’da idanu hawayenta yasake 6ul6ulowa fiye da na ‘dazu.
” _Ya…yah Mah…….._
Tanaso tayi magana amma sai taji gaba ‘daya harshenta yamata nauyi.
” _Shiiiiiii_ “
ya dakatar da ita yana murmushi yace
” _Maza share hawayenki kinji, kin manta nace zamu je Katsina tare_ ?
Kai ta ‘daga masa alamar ehh idanunta taf da hawaye.
” _Har Abuja ko_ ?
Ta sake ‘daga kanta sama.
” _Yauwa toh yi shiru kiji, share hawayenki_ “
Hawayen tayita ‘ko’karin sharewa amma baya tsayuwa kamar sake turosu akeyi haka taji.
” _kinji abinda Munnira tafa’da ‘dazu ko_ ?
kai ta ‘daga masa.
Sai yaci gaba da fa’din ” _nima ba nagaya miki ba_ _rannan_ “
Da kai kawai take bashi amsan dukkan maganarsa.
” _Toh ki yafe mana kinji, ni nasan dukkanmu masu laifi ne agareki har Anty, amma Fateemah wani abin sam ni bansan da faruwarsa ba, abakin Umar naji kuma koda na_ _tambayeki ma baki fa’damin ba kika 6oye min, bansan ta yadda zan tunkari_ _al’amarin ba saboda banji daga bakinki, kaina gaba ‘daya ya kulle narasa mafita, cikin haka sai Allah_ _ya kawo Munnira ta bayyana miki komai agabanki wanda Allah yasa nima sai ya fa’da kunne na, hankalina yatashi_ _sosai Fateemah dajin sunan Anty aciki, bansan wani mataki zan ‘dauka akai ba dan Anty mahaifiya tace_ _ita ta haifeni, daga ‘karshe kawai sai na yanke shawaran zamu tafi mu bar_ _musu garinsu, zan ‘dauke ki muyi tafiyarmu yafi amma kafin inje inda kike sai gashi yanda Allah ya maida ni, duk da haka nagode wa Allah na dayasa_ _nasan komai tunda ran numfashi na_ “
STORY CONTINUES BELOW
Bu’dan baki Anty tayi zatayi magana Mahmud yayi saurin dakatar da ita da fa’din
” _Karki ce komai Anty, ni komai yawuce agurina, sai de ko in Fateemah kuma itama nasan tahakura tuntuni_ “
Kan Abbas ya maida idanunsa, suna ha’da idanu sai Abbas ‘din ya taho wajensa ya zauna abakin gadon yace ” _sannu Mahmud Allah yabaka lafiya cikin_ _gaggawa_ “
Ido ya lumshe tare da bu’de su akan Abbas ‘din yace
” _Abbas idan na baka amanata zaka_ _kar6a min_ ?
” _Me ze hana Mahmud zan kar6a_ _mana_ ”
Abbas ya bashi amsa da kulawa dan gaba ‘daya tausayin Mahmud ‘din yabi yacika masa ziciya ya maye gurbin haushinsa da yakeji lokuta ‘kalilan da suka gabata.
” _Amanar Fateema zan bar maka Abbas ka kula min da rayuwarta kaji, dan Allah……. kabata farin ciki dan tunda nake da ita bata ta6a 6ata min ba….. naso Allah ya bani tsawon rai nima in cikata da farin ciki…. amma ban samu wannan damar_ _ba Abbas, dan Allah kacika min burina kaji……_
” _bar fa’din haka Mahmud nasan da yardar Allah zaka warke, ka rayu da matar….. ka cikin farin ciki da walwala….._ “
” _Hmm_ “
kawai yace da Abbas ‘din sannan yakomar da idanunsa kan ” _Fateemah yace bazaki bar kuka ba ko?, in kina kuka fah bazanji da’di ba ko ba kyason in_ _warke ne_ ?
” _inaso yayah inaso ka warke acire maka duk wannan farin abin_ “!
” _Ko anciremin wannan Fateemah ai dole za’a sake sakamin wasu masu yawa ma, amma kiyi shiru kinji share hawayen ki bana son gani, in bahaka ba zan yi tafiyata in barki ke ka’dai…..,Anty kice mata tayi shiru banasan kukan nan_ !
Anty ne ta kamo ta ta share mata hawayen tace ” _bar kuka kinji Fateema kukan ya isa haka_ _nan_ “
Dayaga tayi shirun ne yace mata ” _yauwa Angel ‘din Daddy,_ _zakuje da Abbas kinji Umar ma zai rakaku……..idan kinje kice da Innah ni yanzu bani da lafiya ne shiyasa banzo_ _ba, kice mata taringa yi min addu’ah, duk ranar da na samu sau’ki zanje in dubo su da kaina.”_
Teemah kam wani sabon kukan ne ya ‘kwace mata tace
” _Yayah…..da kai zamuje, ni da kai zani idan kasamu sau’ki zamuje kaji, kai da kanka zaka sa mamanka_ _amakaranta kamar yanda kayi al’kawari da izinin_ ……..
Tun kafin ta ‘karasa maganar tari ya sar’keshi ganin haka yasa likitan cewa su ‘dan fita su barshi ya huta please surutun yayi masa yawa ne”
Anty ce tafara fita sannan Munnira followed by Teemah,
Abbas kam be ko yin yun’kurin tashi ba hakama Umar da sai yanzu ma shikam yasamu damar matsowa kusa da shi.
Godiya Mahmud yake ‘ko’karin yi masa saboda sosai umar yabada babbar gudum mawa arayuwarsa amma karan nan maganan yakasa fita gaba ‘daya, da sauri Umar ya dakatar dashi yace karya damu basai ya gode masa ba,yace komai dayayi yayi ne saboda Allah and for d sake of there friendship bakomai ba, yace Allah ya baka lafiya Mahmud”
Lumshe idanu kawai yayi tsawon mintina uku kafin ahankali bakinsa ya furta sunan _Abbas_
kasancewar yana kusa dashi ne yasa ma yajishi da wuri sai ya amsa masa da fa’din ” _gani nan Mahmud me kake_ _so_ ?
” _Abbas……….’kaina…..kir….jina_ _bayana….._
Sai ya kuma yin shiru.
” _ciwo ko_ ?
Sosai Abbas ke jin tausayin Mahmud, gaba ‘daya zuciyarsa ta karye da al’amarin dan yasan Mahmud ba ‘karamin dauriya yake yi ba har yake bu’dan baki yayi magana, kana ganinsa zakasan yana jin jiki sosai bayaga haka ma ga wasu munanan raunikan dayaji wanda su ka’dai ma masifa ne amma ahakan yake daurewa yayi magana.
Likitocin Abbas ya bawa guri yace su kula dashi suyi masa abinda ya dace.
Har sun juya zasu fita a’dakin sai suka ji shi yana wani wahalallan tari,
Da sauri suka koma kanshi suna yi masa sannu, idanunsa alumshe gefe da gefen idanun kuwa wasu sirarun hawaye ne yake bi ahankali.
Bakinsa duk ya bushe yayi fari fat kamar wanda yayi sati be sha ruwa ba,
” _Ab…bass_ !
” _Na’am Mahmud gani nan agefenka_ “
” _Abbas_ _inajin….tamkar…..laifina_ _ya girmama…..ka tayani ro’kon Fateemah tayafemin dan Allah”_
” _Haba Mahmud ba anwuce wannan gurin ba, ka daina fa’din haka ka_ _kwantar da hankalinka kaji, batace ta yafemaka_ _ba_ ?
Kansa ya ‘daga har sau uku alamar ya tuna.
Daga nan yayi shiru, still idanunsa alumshe.
Matsawa Abbas yayi inda likitoci suka ci gaba da aikinsu, shi da Umar ‘dinne suka juya zasu fita, Abbas har ya ze juya sai kuma yaga kamar bakin Mahmud ‘din na motsi, sai ya dawo da sauri kusa dashi yayi ‘kasa da kansa zuwa wajen bakin Mahmud ‘din.
” _Rasulullah_ ” kawai yaji
Sai ya ‘karasa da fa’din ” _sallallahu alaihi wa sallam_ ” amma beji farkon abinda yace ba, sai de yana kyautata zaton kalmar shahada ya jero, daganan kuwa be sake ganin ya motsa ba, duk da yake dama ba yawaita motsin yayi ba amma yanzun daya ‘kura masa idanu sai yaga kamar yanayinsa yacanja damma yanayin fuskar cike take da murmushi shiyasa ma yake ‘dan jin dama dama.
Umar ne yayi saurin ankarar da likitocin abinda ke faruwa, take kuwa ya iso ya dudduba shi, ganin dayayi cewa nunfashin sa baya tare da shi ahalin yanzun yasa shi jan farin mayafin dake jikinsa ya lullu6e shi zuwa sama har kansa.
Sannan ya jiyo garesu, yanda yaga Abbas ya ‘kuresa da kallo baya ko ‘kiftawa yasa shi tsaida idanunsa akansa yace ” _i’m_ _sorry_ …….”!
Tsam Abbas ya kasa ‘dauke idanunsa daga kallon likitan hakan yasa likitan ganin cewa ko be fahimce shi bane sai ya sake cewa ” _i mean Allah yayiwa ‘dan uwanku rasuwa_ “.
Yana gama fa’din hakan ya juya ya fita sauran biyun dake taimaka mishi suma suka bi bayansa.
Yayin da Abbas ya ‘daga ‘kafafun sa da ‘kyar ya koma gaban gadon ya ‘daga lullu6in da aka yimasa.
Gani yayi fuskarsa shar har yanzu da murmushi, sai ma wani ‘kara yin fari dayayi kamar yace tashi Mahmud amma wai babu shi.
Acikin zuciyarsa yace ” _Allah ya ji’kanka Mahmud yayi maka rahama, Allah ya haskaka ‘kabarin ka yasa aljanna itace makomarka, Allah yasa mutuwa hutunka ce Mahmud_ “
Ahankali suka fito daga cikin ‘dakin tamkar wa’danda basu so suyi tafiyar, kawunan su duk na kallon ‘kasa.
+
Anty ne tafara tambayar su ” ya jikin nasa ? yasamu yayi bacci ne?
Ta jero tambayoyin nata ajere.
Abbas ne yayi dauriyar yin magana dan shi kam Umar yana daga bayan Abbas ‘din yana faman share hawaye.
” _Muje akaiku gida_ “
Abbas yafa’da idanuwan sa na kallan gefe, sosai mutuwar Mahmud ‘din ya bige shi, acikin idanuwansa ka’dai zaka gane hakan.
Anty ne ta hango Umar daga baya ka’dan da Abbas yana faman share hawaye take ta maida hankalinta gurinsa tace.
” _Umar me ya samu Mahmud kake kuka?,nunfashinsa ya tsaya ko_ ?.
Ganin Umar be tankata ba kuma be ‘dago ya kalleta ba yasa ta furta ” _Nashiga uku na Mahmud ya rasu Munnira_ “
Tayi maganar tare da ‘dora hannu akanta, sai luuu ta zube a’kasa sumammiya.
Tsawon mintina ashirin kafin ta farfa’do inda ta tsinci kanta kwance agadon asibiti, farko idanuwan ta akan Teemah ya fara sau’ka dake gefenta azaune tayi tagumi ta ‘kurawa gadon idanu, yayinda Munnira ke zaune agefen gadon da Antyn take kwance itama tayi shiru.
Ita da Munnira ne kawai a’dakin su Abbas kuwa na can suna preparation na tafiya da gawa.
Anty na farkawa ta gansu zaune jigum-jigum ai sai kawai tasa kuka wanda kukan nata ya sa suka farga da cewa ta dawo hayyacinta.
Cikin kukan take fa’din
” _Dagaske ne Mahmud ‘dina yarasu ko Munnira_ ?
_Dagaske ne yarona_ _ya tafi ya_ _barni_ ?
” _Yi ha’kuri Anty dan Allah ki daina kukan nan haka nan, addu’ah zakiyi masa kinji_ “
Cewar Munnira dake ‘ko’karin tallafota .
Teemah kam binsu kawai take da idanu bata san me zata furta ba sam.
Sai da aka wuce da Mahmud gida kafin Umar yaturo driver yazo ya koma dasu Anty gida, kafin nan kuwa gidan harya fara cika da mutane.
Abbah ne yace a ‘dan jinkirta masa ka’dan yazo yaga gawar ‘dansa da idanuwansa hakan yasa aka ‘daga jana’izar Mahmud ‘din sai zuwa bayan sallar juma’ah.
Kafin hakan kuwa jama’ah da yawa sun iso daga 6angarori da dama, ciki harda su Daddyn Abuja, Ummah, da su Daddyn Teemah mutanen Dubai, Abbah ma ya iso tuntuni inda ganin gawar ‘dansan kwance yasa yakasa ri’ke zuciyarsa sai da ya share hawaye kusan sau uku amma be tsawaita ba dan yasan kukan bashida wani amfani koka’dan ga dukkan mamaci.
Amma shi ka’dai yasan me yake ji azuciyarsa , ‘dansa ‘kwaya ‘daya tak daya keso kamar ranshi amma yau gashi kwance agabansa da gawa, wanda yafishi ya amshi abinsa, Allah ka jikan Mahmud ka haskaka masa ‘kabarinsa, nasan beyi gaggawa ba muma kuma ba jin kiri mukayi ba.
Dayake Ummah tariga su Mummy isowa yasa Teemah tunda taga Ummahn ta tafi ta lafe ajikinta tayi shiru gaba ‘daya koman ta ya tsaya mata cak hatta tunani bata iyawa sai de idanuwa da take faman rarrabawa ko rintse idanu bata son yi saboda tana rintse idanun sai taga Yayah Mahmud nayi mata murmushi lokacin dayake kwance a hospital, hakan yasa ta ‘kin rintse idanu koka’dan.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da Mummy tazo sannan tatafi wajen Mummyn ta rungume ta tare da sanya kuka abin tausayi tace
” _Mummy ance wai Yayah Mahmud ya rasu_ “!
” _Yi shiru toh ki daina yi masa kuka, addu’ah zakiyi masa ba kuka ba kinji_ “
tace
” _ai kema kukan kikeyi Mummy_ !
Janta Mummy tayi ta ha’da ta da jikinta sosai ta rungumeta dukkansu na kuka da rashin Mahmud ‘din, ga kuma tausayin Teemahn datake ji sosai ahalin yanzun.
Sai ganin Anty sukayi tsaye akusa dasu tace ” _Khadija kema kuka kike yiwa Mahmud ko_ ?
‘Dagowa Mummy tayi ta kalleta idanun ta duk hawaye.
Murmushi Antyn tayi me ciwo tare zama daga gefen Mummyn sannan tace
” ba ke ya kamata kiyi kuka ba Khadija nice,
kuka dani ya dace, inajin kamar da hannayena na kashe shi, ha’ki’ka na cuci rayuwata na cuci rayuwar mutanen da basu ta6a min koda kallon tsana ba balle su cutar dani, bansani ba Khadija ashe sakayyata me girma ce, ban ta6a tunanin mugun halina ze iya sanadin ‘dana na cikina ba, banta6a tunanin haka ba, sai gashi Allah ya nuna min iyakata ta yanda ban isa inja da yinsa ba koka’dan koda da wasa”
Idanuwa ta lumshe sai ga hawaye sun ziraro mata da gudunsu bata damu ba taci gaba da fa’din ” yaune rana ta farko dana ta6a yin dana sanin aikata mummunan laifi arayuwata, Mahmud ‘dina yarasu Khadija, Mahmud ya tafi ya barni da tarin laifukana bansani ba ko Allah ze ji’kaina ya yafeni”
Wata mata dake zaune daga gefenta ce ta fara bata baki akan tayi shiru ta daina kukan mana tace fa’de-fa’den ma bashi da amfani.
Ko kallonta Anty batayi ba kawai ta jijjiga kanta tace
” baki san yawan abubuwan dana aikata ba ne, na tabbata da kinsani nasan da kema tsanata zakiyi kamar yanda yarona yatafi da mugun tsanata azuciyarsa, juyawa tayi ta kalli matar tace kinsan abinda yakashe min Mahmud ne ? Kinsan sanadin mutuwarsa?
ko kinsan mugun ciwon da ya dasu acikin zuciyarsa kafin ya rasu?
Ni naga wannan ‘kuncin acikin idanuwansa naga hawayensa dayake fitarwa me ciwo kafin yabar gidan nan, duk naga hakan rintse idanu nayi ban ko ji tausayinsa ba, ni de ‘kudurina kawai ke gabana”
Mahmud yaro ne me matu’kar biyayya yana kula da dukkan hakkin iyayensa daya rataya akansa be ta6a yin abu dan ya 6ata min rai ko mahaifinsa ba duk kuwa da surutun da Allah ya bashi hakan be sa ya kasance mara kunya ba, nice nafara ‘kuntatawa rayuwarsa ta hanyar dasa masa ‘kaunar yin makaranta a’kasar waje wanda tun bashi da ra’ayin haka har yazo ya amince saboda yanda yaga na kafe akan hakan , nariga nasan mahaifinsa baso yakeyi ba amma na dage nace sai anyi, sanadiyyar haka har ya ‘debi shekaru kusan biyu batare da yayi makarantar ba, daga ‘karshe me yazo yafaru ?
“anan garin lagos yayi makarantar kuma yagama lafiya, tun anan ya kamata nasan abinda kalmar ‘kaddara yake nufi amma sam ban yadda ba sai ma na ‘kara jahilta kaina da tunanin sakacina ne yakawo hakan, lokacin da Mahmud yace min zai je service ajahar yobe wallahi hankalina ba ‘karamin tashi yayi ba, naso na hana hakan badan komai ba sai dan muguwar ‘kiyayyar da na kewa Khadeeja wanda alokacin ajahar yoben take da zama, anan kam Mahmud yace shi fa sai yaje dole na nayi ha’kuri na barshi yatafi duk da raina be so ba amma haka na ha’kura na barshi se de har yayi yagama hankalina be kwanta, nakan yawaita takura masa akan yazo gida duk da bani da wani takamman dalilin yin hakan amma zuciyata tariga da tayimin muguwar sa’kar ‘kiyayya da be anfane ni da komai ba sai da nasani da bashi da amfani.
Mahaifinsa da kansa ya nema sa auren Fateema musamman dan yabawa da yayi da natsuwarta da tarbiyyarta wanda kafin hakan ni kuma nayi masa maganar auren Munnira duk da ya nuna min baya ra’ayi amma na nace akan sai ya aureta haka abaya so ‘din ya amince min sai de mahaifinsa dayake yafini iko dashi, shine ya nemasa auren Fateema alokacin bazan iya misalta yanda naji ba dan haushi da takaici, nayi-nayi iya ‘ko’karin dan ganin na hana auren amma hakan ya gagareni, hatta bokaye da malamai duk nabi amma ban iya dakatarwa ba, tsana kuwa ‘karara nake nunawa duk wani abu daya danganci auren, sanadin haka mahaifin Mahmud yakai ‘karata wajen mahaifina a kano, sosai mahaifina yaja kunnena, yayi min garga’di, yamin wa’azi amma duk abanza koka’dan ban ‘dauka ba, ganin haka mahaifina har la’antata yaso yi amma mahaifin Mahmud ya hana shi sai yace matu’kar na aikata wani abu da be kamata ba toh be yafemin ba.
STORY CONTINUES BELOW
Wannan kalmar batasa na yi wa kaina fa’da ba, mahaifiyata matayi ‘ko’karin jan hankalina amma na nuna mata bata isa ba dole itama tazuba min idanu ta ‘kyale ni.
Ko bayan auren nayi ta neman hanyan dazan rabasu amma narasa yadda zanyi, ni kaina bansan me yasa na tsani auren ba, bansani ba ashe shai’dan ke ingizani, dan Fateema bata ta6a 6ata raina ko sau ‘daya ba amma duk da haka banji amincewar barinta ta zauna amatsayin matar ‘dana ba.
Hakan nema yasa da ‘kawata ta nemi ha’din kanta izuwa aikata alfasha nice na tsaya tsayin daka wajen ganin faruwar hakan, akan haka Mahmud yazo yau ‘din nan dasafe yana kuka Khadija, yana hawaye yake ro’kona akan meyasa nayi haka, meyasa zan bada irin wannan gudummuwar wa rayuwarsa, banji komai araina ba face ‘karin haushin matarsa araina hakan yasa nafa’da masa maganganu son raina wanda be kamata ni in fa’da masaba amatsayina na mahaifiyarsa,
Kinsan me yace min ?
“Cewa yayi zai ‘dauke matarsa su bar min garin yace inyafe masa in Abbahn sama yadawo ince ya yafe masa laifukan daya masa daga nan yatafi yana share hawaye, ashe ‘karshen Mahmud kenan, ‘karshen rayuwarsa kenan, ban masa adalci ba koka’dan amma duk da haka yace ya yafemin yace in yi masa addu’ah kawai Mahmud yatafi ya barni da ba’kin cikin rasashi da muguwar dana sanin da bazata ta6a amfanata da komai ba, kaicona nikam wallahi dana kasance me tsananin son kaina, inama zaka dawo Mahmud mu sake rayuwa dakai da sai na so ka na sada ka da ‘yan uwanka na kula da kai yanda se ka zama abin kwatance zan zame maka uwa yanda kowa sai ya yi sha’awar rayuwarka, da kai kanka sai kayi alafahari da kasancewata uwa agareka, amma babu dama, ni da kai na nasan ni ba uwa tagari bace, ban kasance acikinsu ba face masu cika rayuwar ‘ya’yansu da ‘kunci, wahala da azaba gashi ni da kaina nayi sanadin rayuwarka.. inasonka yarona, inason ka Mahmud bansan me ya ‘dauke hankalina na manta cewa kai ‘din amana ne agurina ba, amanarka Allah ya bani gashi sanadina kabar duniya da tarin ba’kin ciki azuciyarka, Allah kaji’kan yarona kayi masa rahama, Allah ka hasakaka kabarinsa kasa shi ‘din me rabone”
Ta ‘karashe da kuka me ciwo tana dafe ‘kirjinta, kusan dukkan wa’danda ke cikin ‘dakin sai da suka zubda hawaye tsaban yanda Anty tacika zuciyoyinsu da tausayi.
Cikin kukan tace
“Khadija dan Allah ku yafemin, tun da sauran rayuwata, Mahmud ya tafi ya barni batare da yabani damar da zan ro’ki yafiyar sa ba wanda inajin ciwon hakan har azuciyata nasan wannan nawin baze ta6a barina in rayu cikin salama ba, Khadija idan ke ma kika ‘ki ki yafeni bansan ya ‘karshen rayuwata zata kasance ba, na tabbata nayi babban hasara dana ‘dauki tsana mafi girma na shinfi’da atsakaninmu, gashi nan shine sanadin komai nice nayi hasara arayuwata gaba ‘daya, Fateemah ki yafemin kinji dan Allah ku yafe min ko Allah ze ji tausayina “
Mummy kuka take tayi harda sheshsheka har maganar ma kasayi tayi gaba ‘daya jikinta yayi sanyi da al’amarin Anty duk da yake dama ita bata wani ri’keta da haushi azuciya ba, kullum addu’ah take faman yi akan Allah ya shiryata yasa tagane cewa ita ‘din bata nufinta da komai, tagane cewa ‘dan uwa ba abin yarwa bane, amma hakan be samu ba har se da rai yabi al’amarin kafin nan, yanzu kam se fatan Allah ya jikan Mahmud yasa aljannah itace makomarsa muma Allah yasa mucika da imani Allah yasa kalmar shahada itace ‘karshen kalmarmu.
(Ameen).
Kafin Mummy ta bu’di baki tayi magana sukaji anyi sallama ashe har anfito daga masallaci, anzo fita da gawa, cikin masu shigowan harda Abbas aka shigo.
Anan ne kam koke-koke ya ‘karu dan Anty da Teemah kukansu nin kuwa yayi fiye dana baya, banda su Ummah ma da sauran mutane suma sai share hawaye sukeyi.
Anty kam ri’ke shi tayi tana sake zubda hawaye tare da dana sanin abubuwan duk data aikata abaya.
Abbas ne yace su ‘dauka su tafi kawai kukan bashi da anfani tunda ba addu’ah zasuyi masa ba.
Haka suka ‘dauke shi suka fita dashi zuwa waje.
Teemah kam cak kukanta ya tsaya tabisu kawai da idanu har ta daina hangosu, babu wanda ya lura da ita sai Ummah, itace tazo ta mi’kar da ita tsaye sannan suka koma gefe suka zauna taringa yimata nasiha tare da bata baki har ta nutsu.
Agurin Abbah aka ajiyeshi yayi masa addu’ah sosai hakama Alhaji Muhammad (kakansa mahaifin Anty).
Daga nan akayi masa sallah aka sada shi da makwancinsa na gaskiya.
Abbas kam suna dawowa daga ma’kabarta be wani da’de ba bayan yasamu ya isar da ta’aziyarsa ga su Abbah kawai ya wuche abinsa, dan baze iya shiga cikin gida gurin matan ba a wannan lokacin, bayaga haka ma shi sam ya tsani ganin fuskar Anty ayanzun.
Yana komawa kuwa ya tarar komai ya kammala sai kawai suka ‘dau hanya.
Niyyarsa idan yakoma ‘din ze nemi pass ne sai yasake dawowa gurin rasuwar amma kuma koda suka koma sai suka tarar da wani mummunan hari da aka kawo, an kashe dayawan sojojinsu aranar, ka’dan ne suka samu rauni inda ‘kalilan daga cikinsu kuma suka tsira da rayukansu da ‘kyar.
Washegari sauran ‘yan uwan su dake ‘kauye suma suka iso da ‘yan uwan Anty inda so rin’ka tunawa da alkhairin da Mahmud ya musu kwanaki ka’dan da suka gabata, suna jinjina halin rayuwa ha’ki’ka rai ba’a bakin komai yake ba.
*****
Abin ya matu’kar ‘kona ransa yanda ‘yan ta’addan ke faman wasa da rayukan mutane batare da damuwar komai ba, sun maida rayukan al’ummah tamkar ran kiyashi, son ransu suke 6arna agurare batare da damuwar komai ba, haushin hakan yasa ya manta da batun mutuwar Mahmud kawai yafara tunanin neman mafita.
*BAYAN SATI ‘DAYA* .
Kafin a’karo musu wasu sojoji Abbas da kansa yayi shiri sosai jin inda ma6oyar ‘yan ta’addan yake acikin garin daga wani majiyar sirri sai ya yi shirinsa sosai musamman dayake akwai kayan aiki agurinsu sai sukayi amfani dasu tare da taimakon wa’dan da suka rage daga cikin battalion ‘dinsa suka tunkari wajen da harin ko ta kwana.
Yariga yasawa ransa cewa ze yi ya’ki dasu da dukkan ‘karfinsa da zuciyarsa hakan yasa be ji ko ‘dar ba ya tunkare su da zuciya ‘daya Allah kawai ya mi’kawa dogoransa, abu ‘dayane dama abin tsoron shine mutuwa shikuwa be dame sa ba, yasan ko mutuwa yayi awanan halin Allah yasani, bashi da alhakin kowa dan haka no retreat no surrender.
Basu fi su goma ba, ha’di da armourtank guda biyu suka tunkari sansanin.
Allah cikin ikonsa kuwa gaba ‘daya suka tada gurin suka ‘kona komai, kafin hakan sai da yayi ko’kari wajen ganin ya kama director ‘din su dake gurin araye, sai de kuma shima Abbas ‘din an kashe kusan bakwai daga cikin sojojin nasa befi su biyar bane suka tsira da rayukansu.
Wannan abin da Abbas yayi ba ‘karamin girma ya ‘karawa hukumarsu ba, dan kuwa aganinsu yayi abinda bakowa ne ze iya yi ba sosai sukayi farin ciki tare da alfahari dashi, hakan yasa duk su biyar ‘din da suka rage aka yi musu albishir na ‘karinum girma.
Hutu aka basu na tsawon wata ‘daya dan su koma ga iyayensu da matayensu.
Abbas ma porthacourt ya koma ya ‘dan huta tukunna sai da yayi kwana biyu kafin yakoma Abuja.
Daddyn Abuja yaji labarin abinda sojoji suka aikata a Borno akafan ya’da labarai amma be ta6a zaton ‘dansa Abbas bane ya jagoranci abin har se da Abbas ya dawo gida yake sanar dasu ‘karin girman da za’a yi masa.
Mamaki sosai Daddyn Abuja yayi har yake tambayarsa dama haka akeyine, daga shigan mutun sai ‘karin girma yabiyo baya.
Anan Abbas yayi masa bayani atakaice akan abinda yafaru, ai kuwa anan Daddyn Abuja yafara masa masifa akan abinda ya aikata ‘din yake cewa yanzu badan Allah yarufa asiri ba inda sun kashe shi awurin fa, yace shi sam baya son rigima da tashin hankali yace shiyasa tun farko ni hankalina be wani kwanta da wannan aikin ba in ban dama Yayah Kabiru ya sa baki da wallahi bazaka yi wannan aikin ba ballantana har kaje kana rigima irin wannan, ‘karin girman banza da wofi salon cuta, aidan sunga kana bada rayuwarka ne shiyasa inda bakayi hakan ba da bawani girma da sazu ‘kara maka”
Shiru Abbas yayi yana sauraronsa sai da yaji yayi shiru kafin ya fara bashi
ha’kuri amma kamar ‘kara zugashi yakeyi sai sake 6allewa yakeyi yana bu’de sabon salon masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, shi tsakaninsa da Allah yaji haushin
abinda yafarun.
Abbas dayaga haka sai yayi shiru kawai yaci gaba da sauraransa.
Allah sai ya taimaki shi ya kawo masa Daddy Babba dayake shi be baro wajen ta’aziyar Mahmud ba sai yau kasancewar Abbah babban abokinsa ne dole ya kasance dashi a kowani irin hali.
Yana shigowa kuwa yaji me suke tattaunawa akai sai da yaji Daddyn ya kasa fahimtar Abbas ne kafin ya jefo nashi da fa’din
” _haba Hassan, ya zakayi haka kuma? dama ya shiga aikin ne dan ya zauna yaga ana abinda bashine ba_ _ya kuma sar’ke hannuwa yana kallo?_
” _Ai kamata yayi ka ‘kara masa ‘karfin gwiwa tare da godewa mahallici daya sanya ya tsira da ransa, bawai kasashi agaba da bambami irin haka ba, da wanne zaiji?_ “
Shiru Daddyn Abuja yayi ya kauda kai gefe, hakan yasa Daddyn Teemah ‘karasowa ya zauna shima.
Dan ya fahimci ran ‘kanin nasa a matu’kar 6ace yake tunda har ya nuna halin ko in kula da zuwansa.
Da ‘kyar yasamu yashawo kansa ya sassauto.
Amma be wani saki jiki sosai ba, duk lokacin dayaga Abbas ‘din sai kawai ya tuna da abubuwan da yayi taji a labarai sai yaji ransa ya 6acida hakan.
Kusan kwana uku da dawowar Abbas amma maganar bata wuce ba, su daddy suka koma Dubai da Mummy sai daga baya da ya samu Daddyn nasa yayi wata tafiya kafin yasamu ya ‘dan sake a Abujan.
Sai da su Mummy sukayi kwana biyar da tafiya kafin yasamu suka zauna da su Ummah har suka ‘dan tattauna akan rasuwar Mahmud wanda dukkansu abin ya ta6a rayukansu ciki harda Hannah ma da ita bataje ba kuma ma bawani sabo tayi dashi ba, amma yanda Ummah ta ke basu labarin yasa duk takejin tamkar tana gurin akayi komai, dataji batun saka Teemah ta aikata lesbian da Anty taso yi da wata mata wacce bama musulma ba ce yasa tunanin Hannah yayi saurin kawo mata cewa waccen matar ne data ganta ranar da suka kai Teemah gidan uwar mijinta dan taga yanda matar take kallon Teemah alokacin tamkar zata cinyeta ‘danye bata ta6a raba ‘dayan biyu itace.
STORY CONTINUES BELOW
Hannah ce ta tambaye Ummahn tace da ita ” _toh meyasa kuma aka baro Teemah acan bayan duk faruwar wa’dannan_ _abubuwan, basa jin tsoron abinda ze biyo baya ne_ ?
sai Ummah tace
” _Antyn yanzu tana bata tausayi ne sosai kuma ita ta ro’ki abar mata Teemahn saboda_ _ka’daici_ “
Ummah tace itama bata amince ba da farko ‘ki tayi dan taga yanda yanayin Teemahn yake har yanzu bata saki ranta ta sosai ba, taso a ‘dan nesantata da garin ko zata samu ta warware da wuri, amma se Mummy tayi saurin amincewa da batun Antyn.
Ummah tace
” _koda muka ke6e ma naso in tuhumi Khadija akan_ _meyasa tayi haka amma sai ta nuna min bakomai ai yanzu Anty tayi_ _nadama ta gane kuskurenta, mutuwar Mahmud ya kasance aya ne agareta me girma, dan haka abar mata Teemahn kawai wai_ _Antyn tausayi take bata sosai itama yanzun_ “
Ta6e baki Hannah tayi ta ‘dauki wayarta taci gaba da latsawa tamkar bata damu ba amma Allah ne ka’dai yasan yanda taji haushin hakan azuciyarta, abar yarinya ma da abinda ya dameta za’a wani ‘kara barinta agurin muguwar matar nan, itama Teemah ai abin tausayi ce ba wata Anty ka’dai ba, ji take da ‘ace tana da iko da sai ta je ta ‘dauko ‘yar uwarta zuwa gida , yayinda Abbas ya kauda kansa gefe sam yaji nutsuwarsa ta kau, shi ai be ta6a tunanin an baro yarinyar acan ba, taya ma za’ayi ace tana can gurin matar da ta fi tsananta aduniya se kace tarasa ‘yan uwa ko kuma tarasa inda zata zauna , wannan ai rashin gata ne akayi mata, sam ya tsani matar nan har zuciyarsa, halinta sam be masa ba, yanzu kuwa dayaji komai kaf sai yakejin ma gaba ‘daya itace abu mafi girma dayafi tsana arayuwarsa, tausayin banza tausayin wofi
shi be abin tausayi awurinta ba sam.
Be ce da Ummah komai ba kawai ya tashi yana wani ha’da goshi yakoma ‘dakinsa.
Ummah da idanu kawai ta rakashi dan ta fahimci ba’a saiti yake ba.
*****
Yanzu komai ya dawowa Anty sabo fil, ibada kawai tasa agaba tana neman gafarar mahallici tare da yiwa marigayi Mahmud addu’an neman dacewa, kusan kullum sai ta zubda hawaye musamman idan ta dubi Teemah sai taji dama ta bari sun yi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali sun haifa mata jikoki masu kyau kamar su, da ma bata shigo da su Munnira cikin rayuwarta ba, tasan da yanzu komai be faru ba,
lallai gaskiya ne da’ake cewa tsalle ‘daya tak zakayi kafa’da rami amma fita daga ciki kuwa sai kayi dagaske, yanzu gashi nan ita gari ya waya dan kowa na zaune da ‘ya’yansa cikin so da ‘kauna ita kuwa babu nata, tsanan data yiwa Khadija na ba gaira ba dalili gashi ita abin ya cutar, awannan lamarin bata tashi da komai ba face hasara me girma, ko Anty Chiddy da take aminiyar tama gashi tun rasuwar Mahmud ‘din har yau sau ‘daya tak taganta agidan, bata ‘kara zuwa ba, ha’ki’ka masoya nada wahalar samu wani lokacin ma’kiya kuwa ko’ina suna nan birjik akewaye dakai, gashi ita masoyanta ma na kusa da ita amma ta rintse idanu ta ringa hango ma’kiyanta dake nesa da ita ‘karfi da yaji ta matso dasu kusa da ita, bata sani ba ashe kanta zata cutar, gashi nan Khadija data nunawa tsana muraran itace ta bar mata ‘yar cikinta amatsayin sanyin idaniya dan ta rin’ka ‘debe mata kewa batare da ta yi musu ko da ka’dan ba, yau da ace burin Anty Chiddy ya cika akan Fateemah tayi lalata da ita da bata san ya zatayi da abin kunya ba, tasan ita kanta da se ta tsani kanta da rayuwarta, Alhamdulillah ma da abubuwa suka ‘dan yi sau’ki Allah ya tsare Fateema ya bata kariya.
Abbah kansa yanzu baya kula ta ko da ya shigo sede su gaisa da Fateemah ya ‘dan jata da hira da tambayarta damuwarta sannLnan ya yi mata nasiha daga nan ya tafi abinsa ko kallon inda Anty takeyi ma bayayi.
Da farko tana damuwa da hakan amma ganin dagaske yakeyi yasa itama ta ha’kura ta daina damuwa tasawa ranta cewa girban sharrinta kawai takeyi adun’kule, tariga kuma ta kar6i duk wani ‘kalubale da zai zo mata ko da kuwa Abbah zai ce ne yasake ta bazata damu ba in kuwa yankan naman jikinta zai rin’kayi kullum shima bazata yi musu ba, dan tasan ka’dan kenan daga cikin abinda Allah ze mata dan ba ‘karamin amanar amintattun bayinsa taci ba.
STORY CONTINUES BELOW
Abbah kullum idan ze dawo sai ya kawo mata wani abu naci sha kona sawa sannan yayi ta mata hira har se yaga ta ‘dan saki jiki kafin ya barta, shi kanshi ma bawai mutuwar bata dameshi bane a’a sosai yake jin kewar ‘dansa amma baya nuna damuwarsa afili, sai ko in yana ‘dakinsa shi ka’dai kafin nan yake tunani tare da yi masa addu’ah sosai, amma kana ganinsa kasan mutuwar ta bigeshi, musamman idan kayi duba da irin ramar da yayi, tausayin Teemahn yake ji ayanzun ganin cewa wannan lamarin ya sameta ne tun a ‘kananun shekarunta, tana yarinya ‘karama da ita shiyasa ma kullum yake ‘ko’kari wajen ganin ya faranta mata.
Anty kuwa kawai dubanta yakeyi baze iya koda maimaita abinda yafaru abaya da ita, be ta6a sanin haukarta takai hakaba, shi dai baze rabu da ita ba saboda darajar mahaifinta amma bayajin ze ‘kara yadda da ita har ‘karshen rayuwarsa, tsana me girma yake yi mata wanda baya jin akwai ranar da hakan ze bar ransa.
Teemah har karatu take ‘karawa Anty ka’dan dan gaba ‘daya ta mantasu duk da ta yi karatun abaya amma rashin kulawa yasa yanzu ko izu biyu bazata iya kawowa da kanta ba, hakan yasa tace Teemahn tana yi mata ko zatana tunawa dasu.
Tanajin da’din hakan kuwa dan kuwa sosai take ‘karajin kusancin ta ga mahallici, sai de lokuta da dama sukan bar karatun ne saboda kukan da Anty takeyi musamman idan ta tuna baya ta tuna da ‘ko’karin da mahaifinsu yayi tayi akansu amma duk ta watsar, shima yau gashi da fushinta ya yabar Lagos beko tsaya ya saurareta ba, tasan yanzu kusan kowa ya tsaneta tunda gashi iyayenta ma basu saurareta ba, saboda mummunan halayenta.
Anan ne Teemah sai tayi ta bata ha’kuri tana mata nasiha hartayi shiru, gaba ‘daya damuwar Anty sai ta nunka na Teemah harma wani lokaci manta nata takeyi sai de Anty.
Itama yanzu sosai Antyn take bata tausayi ganin yanda gaba ‘daya take damun kanta alokuta da dama.
Gashi Abbah ma sai ya daina shigowa sai de ya ‘kira Teemahn zuwa ‘dakinsa suyi hirarsu ya bata duk abinda zai bata sannan ya sallameta, sau tari sai bayan ta fita damuwarsa ke ‘kara yawaita addu’arsa kullum agareta shine Allah ubangiji ya bata miji nagari wanda zai so ta ya kuma kula da rayuwarta.
Haka rayuwar Abbah ayanzu sam Anty kwatakwata ta daina ganinsa ma.
Ganin kamar abin ze mata yawa ne yasa Teemah ta ‘dan fara yiwa Abbah magana akan ya yafewa Anty kar damuwan yayi mata yawa tunda yanzu ta tuba tace ya yafe mata shima, Allah ma yafe mana yakeyi idan mukayi masa laifi meyasa mu bazamu yafi junanmu ba.
Da ‘kyar da su’din goshi Teemah tasamu kyakkyawar kalmah daga gurin Abbahn dan kusan kwana uku sukayi akan maganar kafin yace zai yafe mata amma sai in ya ga cewa tuban gaskiya tayi sannan yace hakan ma darajar Fateemahn zataci in ba dan haka ba da beyi niyyan sake waiwayanta ba.
Sosai Teemah taji da’di harma takasa ri’kewa sai da ta gayawa Antyn abinda Abbah ya fa’da, Anty tana jin haka kuwa ta rarumo Teemah ta rungumeta tana mata godiya tare da sanya mata albarka .
Duk wani kulawa da ya kamata uwa tayiwa ‘yarta Anty nayiwa Teemah shi inka gani sai kayi zaton tun tasowarta tare suke da ita, gata babu irin wanda Anty bata mata shi komai takeyi hankalinta nakan Teemahn motsi ka’dan tayi kuwa sai ta ji dalili ita kanta Fateemah wani lokaci murmushi kawai takeyi da canjuwar Anty.
Anty tariga ta yanke shawarar Teemah agidanta zata yi duk watannin takabanta dan haka tasaki jiki sosai ta rungumi rayuwarta dana Teemahn tare da kiyaye duk wani abu da ze sa Abbah ya zargeta daga wani abu.
Kwanan Abbas shida agida amma sam zuciyarsa ta gagara saduda da barin Teemah da akayi a Lagos, gani yake kamar ‘kara salwantar da rayuwarta ne akeso ayi abanza.
Gashi shi ba ze iya ‘kara tunkarar Ummah da batun ba kawai abin nacinsa ne azuci, wani lokaci ko dadare kasa bacci yakeyi, sai ya ringa tuno da mafarkin da yayi kwanaki, idan ya fasa mafarkin nasa sai yaga kamar azahiri abin ke faruwa, tunda kam gashi Mahmud yatafi yabarsu, toh in hakane kuwa meyasa za’a bar Teemah wajen Anty data so ta lalata mata rayuwa abanza.
STORY CONTINUES BELOW
Haushin wannan al’amarin yasashi ya kasa zama a Abuja, rana tsaka kawai ya fito da shiri yace zai tafi Porthacourt, dayake ma saura kwana bakwai za’a yi musu ‘karin girman su shiyasa ma Ummah bata yi wani tsokaci game da tafiyar ba tunaninta ko wani abin zeje yayi kafin ranar dan haka kawai sai ta bishi da addu’an Allah ya kiyaye ya bada sa’a.
Koda ya isa can ma bawani abu yakeyi ba dayake yana hutu bashi da aiki, tunanin nan dai ne yakasa barinsa, kusan kwanansa biyu amma still be samu nutsuwa ba, cikin hakane ya tuno da amanar da Mahmud yabashi kafin rasuwarsa, take kuwa yaji wani ‘kwarin gwiwa ya shige shi.
Be bari yasake kwana a rivers state ba sai daya ganshi a Lagos.
Wani ha’da’d’den hotel ya nema ya sau’ke gajiyarsa dayake shigan yamma yayi washe gari misalin ‘karfe sha ‘daya yayiwa gidan dirar mikiya.
Abbah na shirin fita sai kawai ya ganshi ya shigo daga ba’kin gate, dayake da taxi yazo so tun a wajen gate aka sau’keshi.
Fuskarsa ba yabo ba fallasa bazaka ce ga asalin yanayinsa ba, amma shikam zuwansa ayanzun gaba ‘daya ya tuno masa da Mahmud komai yadawo masa sabo fil.
Abbah kam ba ‘karamin farin ciki yayi ba da zuwan Abbas ‘din dan yasan albarkacin Mahmud yaci bayaga haka yasan da baze ta6a waiwayar inda suke ba, yana godiya ga Allah sosai daya kasance abokan marigayi ‘dansa Mahmud duk mutanen kirki ne hakan ma na ‘daya daga cikin alamomin nagartar mutun, dan jiya Umar da iyalansa gaba ‘daya suma suka zo gaishe su, daga rasuwar Mahmud zuwa yau yasamu kar6ar ba’ki da dama ta sanadin Mahmud ‘din, su jafar, da wasu friends ‘din sama sun zo sun gaisheshi sosai hakan yake sashi farin ciki ko bakomai yasan cewa ‘dan sa yayi mu’amala ne da mutane masu kyawawanan halaye.
Kar6a me kyau aka yiwa Abbas agidan dan Abbah be samu nutsuwa ba sai da yaga an wadata shi da komai da komai, musamman dayaji cewa ya kwana a hotel ne acikin gari so yasan dole zai bu’kaci wani abin zuwa yanzu.
Shikuwa Abbas sam duk ba wannan bane agabansa damuwarsa tasha bambam, aikuwa ko ruwa be shaba batare da jan wani dogon lokaci ba ya bayyanawa Abbah abinda yakawo shi.
Abbah yayi mamaki sosai amma yace meyasa baze barta anan ‘din ba, koda watanninta ne ta ‘karasa.
Sai yace
” _Hankalina yakasa nutsuwa ne Abbah, amanarta Mahmud ya bar min hakan yasa rashin ganin irin rayuwar data keyi yake ‘daga min hankali, kayi ha’kuri Abbah ba wai na raina kulan datake samu anan ‘din_ _bane kawai de inaga can ‘din zaifi kaga bazatana tunani ba tunda ga Hannah nan suna tare kuma zanfi kulawa da amanarta dana kar6a idan tana kusa dani_ “
Abbah beyi masa musu ba take ya amince masa, sai de yasan ba wannan dalilin bane yakawo Abbas ‘daukan Fateemah ba, ta iya yiyuwa tarbiyar gidan nashi ne be yadda dashi ba ko kuma wani abu daban amma ba de wanda ya fa’da ba, duk da haka bega lafinsa ba, dan yasan koma menene yafaru bakowa bane yaja hakan face matarsa, shiyasa duk abinda zakayi ka kula kayi shi akan dai-dai in kasan farkon abu toh ganin ‘karshensa ne damuwa.
Fateemah kam bazeyi ba’kin ciki da tafiyarta ba duk da ransa be so hakan ba amma idan zata fi samun farin ciki acan ‘din falillahil hamdu, shi bashi da haufi akan hakan, duk da ze so taci gaba da zama awurinshi amma tunda hakan baze samu ba bakomai yasan wannan ka’dan kenan daga halin rayuwa, sede ze yi ta binta da kykykyawar addu’ar dacewa har ‘karshen rayuwarta.
Atake ya ‘daga wayarsa ya ‘kirata yace tazo, itama tayi mamaki dan basu jima da rabuwa ba yace mata ze fita sai kuma gashi taji wai akawo masa kayan tarar ba’ko and now kuma wai ita taje.
Hijabinta ta nema tasaka akanta, dama kullum ahaka take zuwa gurin Abbahn bata ta6a zuwa inda yake batare da hijabi ba.
Amma yanzun kam tunda ta tunkari ‘kofar Abbahn ta rin’ka jin zuciyarta na dokawa, haka de ta daure tashiga da sallamarta.
STORY CONTINUES BELOW
Tana shiga kuwa idanunta ya sar’ke cikin na Yayanta Abbas.
Ahankali ta ‘karasa ta zauna nesa ka’dan da su, tace ” _gani Abbah_ “
Yana murmushi yace ” _baki ga yayanki bane, naji baki gaishe shi ba_ .”
‘Daga idanu tayi ta kalleshi sai taga yawani kauda idanu tamkar ma be san da zuwanta ‘dakin ba.
Sai itama tayi ‘kasa da nata idanun tace
” _Ina kwana Yayah_ ?
Yace
” _lafiya ‘kalau_ “
Kamar ba ze sake magana ba sai can yace
” _ya ‘karin ha’kuri_ “
Can ‘kasan ma’koshi yayi maganar albarkacin Abbah ne ma yasa yayi tambayar badan haka ba ze tambayeta ba.
Itama ahankali ta amsa da fa’din
” _Alhamdulillah_ “.
Murtarta na ‘dan rawa Kamar zatayi kuka, hakan yasa ya ‘dago ya kalleta da kyau jin yanayin muryarta.
Aikuwa sai yaga tana share hawaye, tsayawa yayi kallanta da mamaki wato har yanzu bata daina kuka ba kenan da rasuwar shiyasa ma yaga tayi fayau da yawa duk ta rame kamar ba ita ba, aransa yace ” _toh ki bishi mana tunda kin fi kowa damuwa da rashinsa._ “
Abbah ne yayi mata bayanin abinda yakawo Abbas ‘din inda ya ‘karashe da lallashi ganin cewa tunkan yafara magana ma harta fara kuka yasan be wuci tambayar da Abbas yayi mata bane yasata kuka, dan kusan kullum haka takeyi indai za’a ambaci abinda ya danganci Mahmud toh sai tayi kuka koda kuwa gaisuwa ce shima Abbahn hakan datakeyi na damunsa shiyasa ma gara ya barta ta koma Abujan ko zata ‘dan samu sassauci ta ‘dan manta wasu abubuwa.
Abbas kam haushin kukan nata yakeyi jiyake kamar ya maketa idan yaga tana share hawayen, dan haka sai yayi ‘kasa da kansa yayi shiru yana sauraren yanda Abbahn ke bata baki.
Yanzu kimanin kwana ashirin kenan da rasuwar Mahmud amma ace har yanzu yarinyar nan bata bar kuka ba yaushe kenan zata daina?
Abbas ne yake wannan tunanin aransa.
Abbah kam sallaman ta yayi yace taje ta shirya yanzu zasu wuche dashi.
Tashi tayi salaf-salaf ta fita ahaka ta isa har gurin Anty, ita yanzu duk ba wannan bane matsalarta, ko ina ma tana so ta zauna dan zuwa yanzu tayi sabo sosai da Anty yanda bata jin koka’dan zataji da’din rabuwa da ita, sannan zata so zama a Abuja musamman ma tare da Hannah, saboda ita ma tana sonta kuma ‘yar uwa ce ita mai damuwa da damuwar waninta, amma duk wannan bashi ze hanata son zama da Mummyn ba, gurin mummy take son zuwa, sai de ga dukkan alamu mummy ta sallamata ne, tun da akayi mata aure da Yah Mahmud Mummy take gudunta, gashi yanzu ma da mijinta ya rasu take bu’katan ‘kirjin lallashi mummy ta tsallake ta tatafi ta barta.
Anty kawai ganinta tayi tana kuka da sauri ta kamo hannun ta tana tambayarta me akayi mata me ya faru?
Kuka tacigaba dayi da ‘kyar tasamu ta bu’di baki tafa’di abinda Abbah ya sanar da ita.
Anty bata hanata ba, kamar yanda bata nuna damuwa da hakan ba, da kanta ta lallasheta hartayi shiru sannan ta ha’da mata kayanta gaba ‘daya da kanta, harma tace ko akwai abinda zata ‘dauka acan gidan nasu,
Teeemah da wuri tace ” _a’a_ ” dan ita koka’dan bata son gidan yanzu tsoro yake bata, bata son duk wani abu da zai dangantata da zuwa gidan ayanzu bazama ta iya zuwa ciki ba tanajin ita da wannan gidan har abada.
Haka Anty ta gama shirya mata komai kuma tanayi tana bata baki tare da janta da hira, dan kawai taga Teemah tasaki ranta har tace mata bazata da’de ba zata je ta dubo ta dakanta har Abujan.
Duk iya dauriyar da Anty taso tayi amma kasawa tayi musamman da suka yi musu rakiya zuwa inda zasu hau mota bayan ansaka kayan Teemah a boot taga Teemah nayi musu sallama tana share hawaye take itama sai hawayenta ya gangaro, dama ri’ke nata kukan taketa faman yi tun ‘dazu dan kar ta ‘dagawa Fateema hankali amma yanzu kam dataga ehh dagaske Fateemah zata tafi ta barta sai kawai takasa ri’kewa, tasan yanzu ne zatafi jin mutuwar Mahmud, idan Fateema ta barta shine zata san tayi rashi babbah domin ka’daici ne gadan-gadan ya tunkaro ta.
Ga wani son yarinyar daya bi yacika mata zuciya jitake tamkar Khadija ma bata kaita son ta ba, sai gashi kuma Abbas na ‘ko’karin rabasu, sai dai tasan bakomai yajawo hakan ba face banzan halinta, data kasance me son kanta fiye da komai, da ace ta kasance uwa tagari tasan da babu wanda ze yi shayin rayuwar waninsa tare da ita, kuma tana da tabbacin wannan dalilin ne yasa Abbas zuwa musamman dan ya koma da ‘yar uwarsa Abuja.
Kuka takeyi Teemah ma nayi haka suka rabu, Abbah kam daure ransa yayi yayi musu bankwana, rayuwa kenan, babu abinda baya faruwa idan kana raye zakaga abubuwa da dama najin da’di da rashinsa, duk akwai sai fatan Allah yasa mu dace [AM££N].
Tun a mota kukan da takeyi ya ishesa sosai kukan ke sosa ransa amma ya ‘kyaleta ganin suna tare da driver in badan haka ba da shi ka’dai yasan abinda ze mata.
Duk da haka sai da ya ringa sakin tsaki akai-akai kafin su isa kuwa yayi tsakin sau ba adadi har se data fahimci cewa da ita yakeyi tukunna.
Suna sau’ka kuwa bayan wucewar drivern ya watsa mata kallo yace
” _Idan kika kuskura kika min kuka acikin mutane ni da kene, angaya miki ke ka’dai akayiwa mutuwan ne_ ?
Lokacin ma hawaye kawai take sharewa, daya kasa tsayuwa mata, ahaka ta ‘daga idanun nata dake cike taf da hawayen ta kalleshi.
” _Wipe all those tears kafin in sa6a miki, banson kukan nan ni_ “
+
Yanda yayi maganar atsare dole yasa ta goge hawayen nata ta ringa ajiyan zuciya kawai ahankali.
Hotel ‘din da ya kwana anan suka koma yace tajira shira shi yaje ya nema musu flight ‘din zuwa Abuja sannan yadawo.
Ummah na zaune a parlour tana kallon wani Hausa Movie kawai taji muryar Abbas nayi mata sallama kamar daga sama.
A mamakance ta amsa sallamar tare da maida dukkan hankalinta gareshi.
Fuskan nan atamke ya ‘karaso ciki Ummah da mamaki take dubansa ganinsa ayau ‘din bayan be da’de da tafiya ba, baya ga haka ma tasan yana da uzuri acan, mamakinta ne ya ‘karu ganin Teemah ta shigo da sallamar ta itama kanta a’kasa ta ‘karaso wajen Ummahn.
” _Ah’ah, Teemah kune tafe_ ?
_Keda waye haka_ ?
Ummahn ta tambaya tana me waro idanu ko zata ga abokin tafiyan Teemahn tare da kamota ta zaunar da ita kusa da jikinta.
Abbas kam ‘dauke kai yayi tamkar be san da zancen ba dayaga hakan ma be masa ba sai kawai ya mi’ke ya wuce ciki.
” _Keda waye kuka zo ne Teemah naga shiru har yanzu banga kowa ba_ ?
Ummah ta sake tambayar Teemahn akaro na biyu.
” _Ni da Yayah ne muka_ _zo_ ?
Teemah ta bata amsa ahankali.
Da wuri Ummah tace mata
” _wani Yayahn kenan_ ?
Sai tace
” _Yayah Abbas_ “
” _Abbas dai_ ?
Ummah ta sake tambaya da mamaki.
Kai Teemah ta ‘daga mata alamar _ehhh_ .
” _Toh garin yayah haka ta faru_ ?
_a ina kuka ha’du_ ?
_Ko ke kika ce masa zaki zo nan ‘din, ina_ _ita Antyn_ _naki_ ?
Shiru Teemah tayi dan bata san wanne daga cikin tambayoyin Ummahn zata fara amsawa ba.
Ganin haka yasa Ummah kam ta fassara shirun da abinda hasashen ta ya bata.
Kafin tayi magana sai ga akwati an shigo da shi wanda kallo ‘daya tayi masa ta fahimci cewa na Teemah ne.
Jinjina kai tayi tace
” _lallai yaron nan wato sai da yaje ya taho dake ko,_ _ai dama tun ranar da_ _yaji labarin kina can_ _naga sai wani huhhura hanci_ _yakeyi yana kauda kai gefe ashe shirin da yayi aransa_ _daban_ .
_Zai zo ai yasame ni neh sai naji dalilin_ _hakan_ “
Kallonta ta dawo dashi kan Teemah tace ” _maza shiga ciki ki watsa ruwa ki huta kinji Fateemah_ “
Duk wannan dramar Teemah bata ga Hannah ba tun zuwanta Ummah ce tayi mata kwatancen inda ‘dakin Hannah yake tace mata Hannahn na ciki.
Koda taje ‘dakin ma bata ganta a’dakin ba motsin ruwa data jiyo abayi ne yasa ta gane cewa tana bathroom, cigaba da tsayuwa tayi kamar me jiran abata umarni, bakomai take tunawa ba kuwa sai Mahmud tare da tausayin Anty dayayi matu’kar tasiri a zuciyarta.
STORY CONTINUES BELOW
Tana tsayen har Hannah tafito daga bayin tagama firgita da ganinta dan bata ta6a zaton ganinta awannan lokacin ba, har kuwa tazo ta fahimci cewa itan ce dagaske ita Teemah bata ma san ta fito ba, sai da Hannah ta taho ta dafa kafa’dar ta tare da ‘kiran sunanta kafin tayi firgigi ta dawo hankalinta.
Ai kuwa tana ganin Hannah ta sanya kuka tare da rungumarta zuwa jikinta sannan tacigaba da kukanta.
Hannah kam shiru tayi tama kasa magana dan mamakin zuwan Teemahn tare da farin cikin ganinta duk su suka cika mata zuciya ayanzun.
Sai da taga kukan Teemahn bana ‘kare bane kafin tafara bata ha’kuri tana bata baki da ‘kyar ta sarara da kukan wanda hakanne yabawa Hannah damar tam
bayarta tace ” _ke dawa kika zo ne Teemah kinsan kuwa yanda naji haushin zamanki acan ai wallahi dama niyyata in je in zuga daddy ko kuma Yayah a’dauko ki haka kawai sai awani barki agurin muguwar matar nan, ni ai kin min dai-dai da kika taho wallahi_ , _Allah yasa bazaki sake_ _komawa ba_ “
Cikin rawar murya Teemah tace
” _Anty tana bani tausayi sosai_ _Hannah nasan zata shiga damuwa sosai dana barta_ “
Fa’din Teemah tana me cigaba da zizaro hawayenta.
Hannah kam kwafa tayi tana kallon Teemah sai daga baya tace ” _ke wallahi wani lokaci rasa inda wayoki_ _yake tafiya nakeyi, ina ruwanki da ita? tausayinta na banza da wofi, ita ta_ _tausaya miki ne lokacin da take neman cin mutuncin ki duk da kina matsayin_ _matar ‘danta kuma ‘ya agurin mijinta? Sai yanzu ne data ga babu ‘dan shine zata wani kalallame_ _ki dan ki zauna tare da ita tasamu hanyar_ _sake cutar da ke_ _cikin sau’ki ko_ ?
Teemah cewa tayi
” _Hannah ba haka bane fah, Allah Anty ta canja yanzun ba kamar da take ba_ “
Hannah tace ” _ni ya isheni haka da_ _Allah bari kiga nayi sallah lokaci na ‘kurewa kema jeki yi alwala, ni yau_ _farin ciki ma_ _inajin baze_ _barni na samu bacci_ _ba_ “
Agurin cin abinci suka ha’du dukkansu Abbas kam sai wani shan ‘kamshi yakeyi kamar besan me ya aikata ba nan kuwa duk yana hakan ne dan kar Ummah ta samu daman yi masa fa’da akan maganar .
Hannah ce ” _tace Yayah bakaga Teemah bane_ ‘ _dazunnan fah tazo itama bata jima ba_ “
Tunanin ta wai ko Teemah tariga shi isowa ne shiyasa ta fa’di haka dayake bata san lokacin daya zo ba.
‘Dago kai yayi ya sauke shi akan Teemah yaga yanda ta ke kallon abincin tana wasa da spoon aciki sai ya maida kansa ‘kasa asaman la66ansa yace da Hannah
” _na ganta mana!_ “
Ummah ce tace
” _Hannah ai shi tun kafin ki ganta shi yariga yaganta_ “
Hannah kam waro idanu tayi da mamaki tace ” _haba dai, Ummah a ina toh suka ha’du tun ‘dazu fah muna_ _’daki_ ?
Atakaice Ummah tace mata
” _shine dakansa ya_ _kawota_ “
Hannah kam kallonta ta miyar kan Abbas ‘din da fara’arta tace ” _wallahi Yayah ka kyauta kamar kasan meke cikin raina, ni dama_ …. “
” _Stop talking and eat your food Hannah later then kyayi surutun, okay_ “
Cin abincin tafara cikin farin ciki tanayi tana murmushi dan ita yanzu komai normal ne a6angarenta bata da damuwar komai tunda kam ga Teemah agefenta zaune.
Cikin hakan ta waiwaya 6angaren Teemah sai taga ba ta cin ma abincin ita kam.
Zungurinta tayi da kafarta, data ‘dago ta kalle ta sai ta mata nuni da abincin Teemah ma sai ta fara kaiwa kamar gaske.
Ummah ma ta lura da hakan amma bata nuna ba dan zatonta ko idanun mutane ne yayi mata yawa shiyasa takasa ci, sai ta bari akan idan sun gama zatace da Hannah ta ‘diba mata zuwa ‘daki wata’kila can zatafi sakewa.
STORY CONTINUES BELOW
Abbas kam da hanzari yake cin nashi abincin ‘ko ‘karinsa yayi ya tashi ya bar gurin dan yasan Ummah dole ne sai ta tuhume shi shikuwa be san ma me zece da ita ba.
Ummah ma duk tana lura dashi sai ta ‘kyaleshi kawai tana jiran su Hannah su tashi dan bata son yimasa surutu agaban ‘kanwarshi sam shima kuma yasan hakan shiyasa yake hanzari yayi ya rigasu barin table ‘din.
Yagama kenan yana niyyan tashi sai yaga Hannah ta rigashi mi’kewa tana shirin yin magana sai Ummah tari bakinta da fa’din ” _’Dauka wa Fateemah abincinta naga bata ci ba sam may be a’dakin zata fi sakin jiki taci_ “
” _ah’ ah nifa nama koshi Ummah basai_ _ta ‘diba min_ _ba_ !
Cewar Teemah tana ‘ko’karin mi’kewa itama.
Wani kallo da Abbas ya watsa mata yasa take tayi kasa da ‘kanta ‘kirjinta na harbawa.
Ummah cewa tayi ” _ah’ah Fateemah ni banga wani abin kirki da kika ci_ _anan ba_ ,
” _Hannah maza ‘diba mata ko ka’dan ma tasamu taci zama_ _da yunwa ai bashida da’di koka’dan_ ,
_dubi fah yanda duk kika ‘kare abanza_ “
Hannu Hannah tasa ta harha’da mata komai sannan tace da ita
” _tashi muje_ “
Shima mi’kewa yayi daniyar barin gurin sai kuma Ummah tace masa
” _zauna Abbas_ “
Dayake yana kusa da ita shiyasa shi ka’dai yaji maganar da Ummahn tayi.
A’darare ya koma ya zauna yana me shafo kansa da hannunsa ‘daya.
Sai da su Hannah suka shige ciki kafin nan Ummah tace masa
” _sannu ko_ “
Kallon ” _me nayi_ ” ya yiwa Ummahn yana murmushi
” _Haba Muhammad yazakayi haka dan Allah bayan da kai rannan mukayi_ _magana akan yarinyar nan, shine kuma ka san’di jiki ka koma ka taho da_ _ita_ ?
” _Kai ko kunya ma bakaji ba, ka duba halin da matar nan take ciki amma sai_ _ka yi wannan rashin mutuncin, itace fah da kanta ta nemi_ _abar mata yarinyar nan_ _agurinta harta gama watannin takabarta kuma aka amince mata_ _sai daga baya kuma_ _haka yafaru kai kana ganin zata_ _ji da’di_ _ne_ ?
Ta ‘karashe maganar tana kallonsa.
” _’kyale ta kawai Ummah yariga ya_ _wuce ai yanzu tunda gashi mun_ _taho_ “
Ya bata amsa yana me duba agogon hannunsa.
Shi koka’dan bega rashin kyautawar sa ba a wannan lamari dama me yasa za’a barta acan ‘din in ba ahanata mantawa da mutuwar ba.
Ummah kam kwafa tayi tana dubansa jin irin amsar daya bata sai tace masa
” _Toh na barta tunda haka kace, amma shikuwa kawun nata fah, miye laifinsa acikin_ _lamarin ko kuma shi ‘din kana ganin zaiji da’dine ace rana tsaka_ _kawai ka dira masa ka wani ce zaka tafi da ita bayan sun saki ransu cewa_ _zata zauna tare dasu, kuma ai baka ji ra’ayin yarinyar ba akan haka baka_ _sani ba ma ko can ‘din yafi mata fiye_ _da nan_ …”
” _i don’t care Ummah, shi ‘din lokacin da_ _abubuwan sukayi ta faruwa yana ina?, da ace an samu_ _nasarar cutar da ita Ummah da ya za’ayi, nifah banga abin damuwa_ _anan ba dan tausayi ina jin tausayinsa mana amma gaskiya_ _bazan sake barin yarinyar nan ta zauna tare da muguwar matar nan ba, domin_ _amanar ta aka barmin, koma menene zatayi tayishi tagama anan babu inda_ _zataje_ “
” _Muhammad_ !!
Ummah tafa’da tana kallonsa.
Juya kai yayi ya tare ta da fa’din
” _bazaki gane bane Ummah, wallahi na_ _tsani matar nan, ki fahimce dan_ _Allah Ummah, wani lokaci fah jinake kamar inje_ _in sa akamamin ita nayi ta dukanta har se_ _ta suma……amma bazan iya ba, bazan mata haka ba_ _saboda darajar_ _Mahmud_ , _albarkacin ‘dan data haifa take ci_ _awurina da kuma Abbah in badan_ _haka ba da ni ka’dai nasan me zan_ _mata…. kiyi ha’kuri Ummah amma gaskiya yarinyar nan bazata_ _koma ba koda kuwa me ze_ _faru_ “
STORY CONTINUES BELOW
Ummah kam shiru tayi tana kallonsa yanda yasata agaba da masifa, amma bata wani yi mamaki ba dan tasan abinda ke cikin ransa yake fa’da mata and kuma tasan iya gaskiyarsa kenan dan haka tayi shiru tana sauraransa.
Yana gama maganar ya tashi ya wuche zuwa ‘dakinsa da ido kawai Ummah tarakashi har ya shige ta daina kallonsa sannan ta dawo da idanunta gabanta.
Koda ya koma ciki ma tunani ne duk yabi ya ishe shi, sosai yake jin haushin Anty tare da Allah wadai da halinta, at d same time yana tausayawa Fateemah, cikin haka ya tuno da abinda yafaru ‘dazu a wajen dinning, yasan halinta sarai tana dai-dai ‘dinta ma bata bawa abinci daraja ba balle kuma ance tana cikin damuwa ai se ahankali.
Shiyasa ma yaga duk ta rame ta lalace.
Wayarsa ya ‘dago ya ‘kira layin Hannah.
Hannah na ‘ko’karin shiga wanka taji ‘karar wayanta, zuwa tayi ta ‘daga tare da yin sallama.
Ciki-ciki ya amsa mata tare da fa’din ” _Hannah me kikeyi_ _ne pls_ ?
Sai da ta ‘daga idanu sama ta kuma juya su kafin tace ” _wanka zan_ _shiga Yayah_ “!
yace
” _Okay, akwai abinci_ _agurinku_ _ko_ ?
” _Ehh sai na Teemah ne wanda bata ci ba_ “
cewa yayi
” _Yauwa ki bata ta_ _kawo min_ _yanzu_ “
Hannah da mamaki tace
” _Toh, amma Yayah baka ci abinci ‘dazu_ _ba_ ?
Be bata amsar tambayarta ba kawai sai yace da ita
” _hope kinji me nace_ _ko_ ?
Da sauri ta bashi amsa da fadin
” _Umm naji_ “
Be sake magana ba ya yanke ‘kiran kawai.
Bin wayar Hannah tayi da kallo sannan ta ‘karaso wurin Teemah tace ” _Yayah yace wai ki kai masa abinci inajin tsutsar ciki ke damunsa, ‘dazun nan fah yaci abinci_ _amma kiji wai a’kara kai masa wani_ “
Teemah tuni tayi kicin-kicin da fuska kamar zatayi kuka tace ” _Hannah ni kuma zankai masa dan Allah_ ?
” _nima haka yace min ko baki ji ba sanda nace masa_ _wanka zanshiga, ki daure ki kai masa yanzu zaki dawo ai_ “
Hannah tana maganar tana ‘ko’karin ‘dauko mata plate ‘din abincin.
” _ungo ki kai masa_ “
Kar6a Teemah tayi ta kama hanyar fita.
” _’Bangaren yamma zakiyi ‘kofarsa ce ka’dai zaki fara gani agabanki_ “
cewar Hannah dake tsayen abayan Teemah.
Teemah kam fita tayi ko waiwayowa batayi ba ta fice daga ‘dakin
tana jan ‘kafa kamar bazata ba, tariga tasan halinsa sarai bawani abincin da ze sake ci tunda baya cin abinci sau biyu lokaci ‘daya ‘kilan kawai wani abin ne yasa shi cewa takawo masa.
Da sallamarta ta shiga ‘dakin nasa taje ta ajiye abincin akan ‘dan ‘karamin dinning ‘din dake ‘dakin nasa me kujeru biyu kacal.
Tana shirin juyawa ta tsinkayi muryarsa yana fa’din ” _kawo min_ _nan_ “
Komawa tayi ta ‘dauko sannan ta kawo masa tana ajiyewa shikuma yana mi’kewa yake fa’din ” _zauna kici ina zuwa yanzun_ _nan_ “
Hawaye kawai taji ya gangaro mata, kamar tasa hannu aka tayi ihu dan takaici, dama tasan bacin abincin zaiyi ba, da ta san cewa ita ze sa taci ma da bazata zo ba.
Kusan mintina biyu tana zaune da abincin agabanta, tana share hawaye, dataga ba yanda zatayi kawai sai ta bu’de tafara ci ahankali sanin halinsa datayi akan hakan, dan tunda yace taci toh matu’kar bataci ba baze ta6a barinta ta tafi ba, dan haka sai ta ringa ci ahankali take turawa bakinta harta jita dam, daga nan ta tsaya da cokalin ahannunta, tana jiran fitowarsa.
Ashe watsa ruwa yaje yayi sai da ya shirya kafin ya dawo parlourn cikin kayan baccinsa me birgewa jikinsa na tashin sayayyan ‘kamshi.
Zuwa yayi ya zauna tare da ha’de hannayensa wuri guda yasata agaba yace mata ” _ya dai_ ?
” _Na’koshi ne Yayah_ “
Muryarta na rawa tayi maganar.
Baya yayi ya jinginu da jikin kujera dan yaga ba laifi ta ‘danci ka’dan sai yace ” _U can leave, amma fah ki kiyaye kina cin abinci akan lokaci dan duk ranar dana_ _dawo na ga baki canja ba wallahi zan sa6a miki ne, bana son yawan_ _kukan nan da damuwa kuma, ko shi Mahmud ‘din ce miki yayi ki dinga yi_ _masa kuka idan_ _ya rasu_ ?
Da kai ta bashi amsa alamar ” _ah’ah_ “
Sai kawai yaci gaba da da fa’din
” _Ya kamata kisani Mahmud is now no more, baze ta6a dawowa ba, is better ki nutsu ki san_ _abinda ya dace ba ki ringa damun mutane da kuka da damuwa_ _ba, zan bawa Abbah_ _ha’kuri akan tahowarki dan nasan beji da’din hakan ba, sannan_ _idan nadawo naga kin saki jiki ni da kaina zan kaiki Lagos ‘din ki dubo_ _su har wurin Mummy ma duk zan kaiki amma sai naga kina jin_ _magana tukunna……_ _clear_ “
Ta gya’da kanta tare da furta ” _yes_” ahankali.
” _Toh gudnight_ “
Daga nan be sake kallon inda take ba ya maida idanunsa kan television.
Tashi tayi ta fita zuciyarta fal farin ciki, musamman dataji yace zai kaita gurin Mummyn ta, ai gaba ‘daya sai ta manta da komai.
Hannah ma sai da ta fahimci farin cikin dake kan fuskar Teemahn data tambayeta kuwa take ta sanar da ita yanda sukayi da Abbas ‘din.
Murmushi kawai Hannah tayi tare da jinjina masa aranta tasan yana yin duk hakan ne dan yaga ‘kuncin Teemahn yaragu.
Wani lokaci takan ga kamar Teemahn na da sa’ansa domin Yayah yakanyi mata abinda bakowa ke samun hakan daga gareshi ba, bata san dalilin sa ba amma tana jinjinawa dangatar dake tsakaninsu.
*****
Washegari ‘karfe bakwai ya bar gidan yayi tafiyarsa ya koma Rivers state, Umman ce ka’dai tasan da fitarshi itan ma atsatstsaye yazo yayi mata sallama yafice.
Tasan halinsa sarai yanzun yana hakan ne dan kar tasake yi masa magana akan Fateemah shiyasa yayi hakan ita kuwa yanzu ta riga ta saduda barinsa zatayi taga iya gudun ruwansa tunda kam yace Fateemahn amanar sa ce ita, toh nata kallo ne.
Kwanan Fateemah biyu agidan sannan ta ‘dan saki jikinta, Daddyn Abuja ma daya dawo sosai yayi farin ciki da zuwanta dan ko shima bawani da’di yaji da barinta da akayi acan ba kawai de yayi shiru ne saboda al’amarin ahannun matan yake, yanzu kuwa da ya ganta ya kuma ji labarin cewa Abbas ne ya kawo ta ai shikenan gaba ‘daya sai ya manta ma da haushin Abbas ‘din daya keji ya ringa sa masa albarka.
+
‘Ko’kari sosai Hannah keyi wajen ganin ta mantar da Teemahn damuwar da take ciki, saboda bata barinta zama shiru sai de in tatafi makaranta wanda makarantar ma dan ya zama dole ne shiyasa lokuta takance da ita badan tana zaman ‘dakin rasuwar mijinta bama da se ta ringa rakata makarantar ai.
Teemah kam baki take ta6ewa ta yi shiru, dama yanzu gaba ‘daya ta canja wannan rashin jin duk babu shi ta dawo wata salihar ‘karfi da yaji, wani lokaci idan tana abu se kaga kamar ba ita ba.
Haka abinci ma yanzu bata ci da wasa 3square meal ‘din nan duk basa wuceta takanyi ‘ko’kari taci a’kalla kamar spoon goma koma fi akowani lokacin cin abinci, Ummah sosai take jin da’din canjawar tata musamman data ga yanzu tasaki jiki har tana cin abinci batare da an takurata ba.
Damuwar ma duk ta rage shi yanzu ta barwa zuciyarta, addu’ah kawai take masa akowani lokaci musamman idan tayi sallah toh sosai take 6ata lokaci waken yi masa addu’ah wanda a lokacin ne tafiya yin kuka sai de ko Hannah bata bari ta fahimci yanayin data ke shiga.
Tana waya dasu mummy da Anty akai-akai, inda mummy kanta da taji cewar Teemah ta dawo Abuja sai da ta sau’ke ajiyan zuciya da can ‘din ma kawai ta daure ranta ne tare da yiwa Anty kawaici, amma tunda ta koma Dubai sai taji zuciyarta ya kasa nutsuwa sai take ganin kamar Antyn zata iya sake cutar da Fateemah tunda tana gabanta.
Anty kuwa bayan tafiyar Teemah da kwana biyu sai taji damuwarta ta dawo mata sabo fil, tunaninta ya yawaita akoda yaushe bata da aiki sai zubda ‘kwalla, gashi babu wanda ke zuwa gurinta ayanzun, Abbah ma ‘kara nisanta kansa yayi da ita, dan tun tafiyar Teemah sau ‘daya kawai ta ganshi, wannan ‘dinma ta window ne lokacin shigowar sa gida kenan jin dirin mota yasa ta le’ka sai taganshi.
Ganin sa ‘din kuma sai ya ‘kara kashe mata zuciyar dan gaba ‘daya Abbah ya lalace wani rama taga yayi na masifa, tausayinsa har se da ya sata sakin hawaye, tasan koma menene yafaru laifinta ne, mutuwa ba a hannunta yake ba, amma tasan son zuciyarta shine sanadin komai.
Komawa tayi ta jinginu da jikin window ta lumshe idanu yayinda hawaye suka ci gaba da gangarowa ta ‘kasan idanun suna sau’ka saman kuncinta, samata ‘daga kanta tace
” _Allah na tuba ka yafe min, ka yafe min kura kuraina, ya ubangiji Allah ka sanyaya zu’katan duk wa’danda na_ ‘ _kuntatawa, Ya Allah kaji’kan Mahmud ka haskaka masa ‘kabarin sa_ “
Washe gari da sassafe tayiwa ‘dakin Abbah tsinke, sallamrta ka’dai ya amsa saboda darajar da sallama ke da shi ga dukkan wani musulmi, daga nan yaci gaba da shirinsa be ko kalli inda take ba, kallo ‘daya Anty tayi masa ta fahimci cewa shirin tafiya yakeyi dan haka sai ta zauna agefen gado ahankali tace ” barka da warhaka Alhaji fatan antshi lafiya”
STORY CONTINUES BELOW
Da ” lafiya ‘kalau”
Kawai ya amsa ta atakaice.
Anty ma sai tayi shiru bata ‘kara magana ba kawai ta rin’ka binsa da idanu.
Ganin kamar bashi da niyyar sake kulata sai tace dashi
” _Alhaji dan Allah kayi ha’kuri ka yafemin laifukana, ka daina fushi dani,_ _wallahi nayi dana sanin duk abubuwan dana aikata abaya, ni kaina inajin tsanar kaina akan haka_ , _bansan ya zanyi in goge laifina awurin mahallicina ba amma nasan idan kun yafeni wata’kila_ _Allah zaiji tausayina ya min afuwa_ “
_Nasan ban yi mana adalci ba koka’dan, ban kyauta wa rayuwar mu ba gaba ‘daya tunda_ _gashi son kaina yasa har nayi sanadin da ‘dana yarasa_ _rayuwarsa……_
Kuka ne ya kubce mata tayi na kusan mintina biyu sannan taci gaba da fa’din
” _Mahmud yace kayafe masa Alhaji, yace in ro’ka masa yafiya awurinka akan duk laifukan_ _daya maka arayuwarsa……_
Sai ta sake sakin kuka gwanin tausayi.
Abbah ma dakansa sai da ya share hawaye da jin abinda Anty take fa’di tunanin yaronsa da tausayin kansa ya ‘kara kamashi, ‘dansa ‘kwaya tal da Allah ya bashi gashi be samu damar bashi farin cikin daya dace ba har ya bar duniya, yau gashi babu shi, Mahmud ya tafi, sai de yasan Allahn daya kar6e shi yafishi son shine, yasan kuma Allah baya ta6a barin wani dan wani yaji da’di, sai fatan Allah yayiwa Mahmud Ubangiji ya sada shi da dukkan rahamarsa.
Yana goge hawayen fuskarsa ya ‘dauki ‘yar ‘karamar jakar kayansa daya gama shiryawa tare da ‘daukan wayoyinsa ya nufi hanyar fita.
Ganin Abbah na shirin fita batare da taji kalma ‘daya me kyau daga bakinsa ba yasata ta mi’ke da hanzari tace
” _Alhaji ko bazaka min magana ba dan Allah kayi min izini in tafi kano_ “
” _Allah ya kiyaye_ _hanya_ “
ya fa’da tare da ficewa abinsa daga ‘dakin.
Anty kam kuka tasanya har tana ‘dan bubbuga kanta da hannunta, nadama da takaici ne duk suka ha’du sukayi mata yawa, duk da tana farin ciki da barinta da Abbah yayi amma kuma halin dayake cikin ya matu’kar tsaya mata arai, tasan dama ba ze ta6a hanata zuwa kano ba, baze ta6a shiga tsakaninta da ahalinta ba, shi akullum ma burinsa taringa ziyartar su tare da mutunta familynta sa6anin nata halin.
Zata je ta nemi gafarar iyayenta ta gyara dukkan kurakuranta na baya, ta faranta musu a matsayinta na ‘ya agare su.
Ko zata samu su yafe mata laifukanta garesu.
*****
Daddy musamman ya baro Dubai yataho domin ya amsa gayyatar Abbas inda suka je shi da Daddyn Abuja suka halacci taron ‘karin girmansa inda daga ranar ya amsa matsayinsa na *CAPTAIN* .
Tun acan Daddynsa yafara wa Yayan sa magana akan Abbas ‘din, complain ya shigar akan cewa wai yayi-yayi dashi ya yi aure amma ya’ki, shi kuma duk wannan abubuwan ba farin ciki suke saka shi ba, dan ko wani irin matsayi mutun yakai aduniya matu’kar bashi da iyali toh darajarsa ragaggiya ce, gara tun wuri kayi wa ‘danka magana yafito da mata inbahaka ba wallahi da kaina zan za6a masa mata idan nagaji da magana.
Murmushi Daddy yayi sannan yace
“Haba Hassan kabarshi mana yasamu nutsuwa, yaushe ma yasamu ya zauna da har za’a fara yi masa maganar aure, shi auren de lokacine idan lokacin yayi kuwa ba se ka tsaya 6ata bakinka ba, da kansa zakaga ya furta, dan Allah ka sarara masa Al-Hassan ka raba masa hankali”
Kauda kai Daddyn Abuja yayi wanda Daddy yafahimci cewa maganar tasa bata wani shiga ransa ba amma de yasan Hassan ‘din ba ze taka maganar sa ba tunda ya furta, dan Hassan na matu’kar bashi girmansa sosai.
Daddy daga can ya wuche ko Abuja be dawo ba, saboda baya son ha’duwa da Teemah a dai-dai wannan lokacin dan uasan rigimarta yawa ne da ita.
Abbas kam tare suka dawo gida shida Daddynsa, dan har yanzu acikin hutunsa yake be gama ba.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da yazo gida kafin su Ummah suka shirya wata ‘kwarya-‘kwaryar walimah acikin gida na tayashi murna, yaji da’di sosai da hakan barin ma daya ga Fateemah ta ‘dan saki ranta yanzun bakamar da ba, gashi ta ‘dan yi kyan gani duk da hijab ta zun6ula har ‘kasa amma hakan be hanashi fahimtar canjawarta ba.
Ahankali ya ‘kara fahimtar rungumar ‘kaddara da tayi saboda ko a dinning yaga yanzu tana ‘ dan sake wa taci abinci harma ayi hira da ita, duk da murmusho yafi yawa anata fuskar amma sometimes takan jefa nata ka’dan.
Idan Hannah na makaranta kuwa sau tari da Ummah zaka same ta tmsuna ta’di abinsu, ko kuma ta yi kwanciyarta akan cinyar Ummahn tana shagwa6arta wani lokaci har bacci takeyi agurinta.
*Bayan sati ‘daya……*
Teemah ha’kurin ta yafara gazawa ganin har yanzu Yayah Abbas be sake mata maganar tafiyan ba, kuma xe mata yayi idan yadawo zai kata, tayi ‘ko’karin kiyaye duk wani abu da tasan ze sa shi canja ra’ayi amma shiru bata ji yace komai ba.
Bata san me zata ce dashi ba dan haka sai ta fara bawa Ummah labari ka’dan-ka’dan, sai tace da Ummahn ” _Yayah fah uace zamu je wurin Mummy da Anty in gaishesu amma kuma naji be sake_ _maganan ba_ “
” _Antyn naki ba kince tana kano ba_ ?
Ummah ta tambaya tana kallonta.
Sai tace
” _Ehh tatafi kano, ai shi ne yace zamu_ _wajenta_ “
“Toh inaga be shirya tafiyan bane tukunna, amma nasan tunda har ya fa’da toh babu shakka zai kaiki ‘din, zai fison idan kin warawre gaba ‘daya”
Cikin shagwa6a tace “Ummah nafa riga warware gaba ‘daya”
” _Toh ni Fateemah ni miye nawa, ba fa dani kukayi_ _shawaran ku ba_ “
Kwa6a fuska tayi kamar zata yi kuka gani hakan yasa Ummah ta janyo ta zuwa jikinta ta kwanatar.
” _Haba Fateemah, kiyi ha’kuri mana ki ‘dan ‘kara bashi lokaci kinji_ “
Ummah ma biye ta ringayi da lallami har zancen ya kau.
Ita kam ma ai jinta take yi kawai, dan ko Abbas ya ‘dago zancen tafiyar toh ita ba yadda zatayi ba.
Yawon ai ya isa hakan gara ta zauna wuri ‘daya ta iddasa zaman takabarta inyaso daga ko ina ne ma taje.
Teemah kam ha’kurinta ‘karewa yayi, kwana biyar bayan maganar da sukayi da Ummah sai taje dakanta tasame shi.
Duk yanda take ganin ta canja Abbas cewa yayi be ga hakan ba shi har yanzu dan haka tafiya ba yanzu ba.
Ranar kam kuka tasha da dare dan haushi, tana cikin kukan ne Anty ta ‘kirata awayarta tana ‘dauka kuwa tasake mata kuka, take Anty ta rikice ta fara tambayarta abinda ya faru, me aka mata?
cikin kukan tayi mata bayanin komai, Anty kam murmushi tayi dan take ta fahimci wayo kawai Abbas yamata dan ta saki ranta ta sake da kowa, amma duk da haka sai tace da ita
” _har kin sa na ji wani iri ma, ai inajin Abbas ‘din yama fiki gaskiya, amma de kiyi ha’kuri kinji, ki bari idan na koma Lagos ‘din nasan zai kawo ki tunda shi yafa’di haka, ai yawo banaki bane yanzu Fateemah, akwai sauran lokaci kinji inna samu lokaci ma zanzo na duba ki a Abujan kinji_ ?
Baki ta tura gaba ciki muryar shagwa6arta tace
” _Dan Allah Anty kizo toh, ni nagaji da zaman ne Anty, bafah na zuwa ko’ina ko shopping Hannah ce_ _ka’dai take zuwa, ni Ummah bata_ _barina in bita kuma idan ta dawo sai ta ta min dariya_ “
Murmushi Anty tayi daga 6angarenta, tana mamakin yarintar Teemah ita kam, ashe yarinya ce ‘ karama sosai har yanzu, tasan koda tace zata mata bayani ma ‘kila ba gane manufarta zatayi ba, dan haka sai ta bar wancan tunanin kawai tace
” _Ayyah very sorry kinji, soon kema zaki fita ai yanzun be kamata kina yawo bane shiyasa amma in lokaci yayi nasan babu me hanaki fita_ “
STORY CONTINUES BELOW
Sosai Anty tayi ta rarrashinta har ta ha’kura tayi shiru.
Ganin ta nutsu yasa har Anty ta bata labarin kaf yanda suka yi da mahaifanta bata 6oye mata komai ba, yanda tasha gwagwarmaya kafin ya amince da ita, da ‘kyar ya furta mata kalmar yafiya dan shi tsakaninsa da Allah ya tsani ganinta arayuwarsa ma.
Teemah ta tausaya mata da jin labarin, inda tasake bata ‘kwarin gwiwa sosai kamar ba ita bace me zuba shagwa6a ba ‘dazu.
Anty najin da’din kasancewa da ita dan ko ba komai takan ‘de be mata kewa, gashi tana ‘ko’karin bata shawarwari masu kyau duk da take yarinya ‘karama amma akwai ta da ilimi, bayan sata ahanya data tayi lokacin suna Lagos, Anty tamkar sa’arta ta maida ita dan duk shawaranta da ita takeyi yanzu, in abune ma ya dameta Teemah take sanarwa su jajanta tare sosai take janta ajiki tana jinta tamkar 6arin zuciyarta ce.
Sau tari Anty na addu’ar Allah yasa Fateemah nada cikin Mahmud saboda zata so ace tasamu jika daga ita, amma lokaci guda take kauda wannan tunanin idan ta tuno kato6arar da Munnira ta aikata, musu sai dai akullun bata cire rai idan son jikan yacika mata zuciya sai kuma taji kamar batun Munniran ‘karyane babu wani barrier da ta yi atsakaninsu ,alokacinn ne take ‘karyata Munnira da kuma aikin bokayen sai taji kamar tunanin ta gaskiya ne, Fateemah nada cikin Mahmud ajikinta.
Har kwatanta ranar da za’a ce maganar ta tabbata takeyi tana misalta irin farin cikin da zataji, takance da kuwa anga zallar so dazata nunawa jikan nata, bata jin akwai abinda zata so fiye dashi aduk fa’din rayuwarta kuwa.
Lokacin da sukayi sallama da Anty Fateemah ma shiru tayi tana tunani, abin na damun ta sosai, yanda akabi aka tsare ta agida kamar munafuka, turare wannan Ummah hanata amfani tayi da shi, duk kuwa da yanda Teemah ke da jarabar turare amma hanata akayi amfani da masu ‘karfi, sai da taga Teemah na shirin yi mata kuka kafin da ‘kyar ta barta take amfani da wani me sanyin ‘kamshi sam bashida ‘karfi, wani lokaci idan tasaka shi ajikinta mintina biyar bayayi ajikinta sai taji babu ‘kamshin duk ya gushe, sannan bata kwalliya kullum tana nan sai fama da waya a’daki.
Islamiya wannan idan suka ce zasuje tare da Hannah Ummah hanata takeyi, akwai ranar dama ta san’di jiki suka fita ta ‘kofar kitchen har suna murna amma cikin rashin sa’a sai ga Yayah agabansu take kuwa ya maida ta gida yace maza ta koma babu inda zata je.
Ranar kam tasha kuka, wani lokaci gani take kamar ita ka’dai aka tsana agidan shiyasa akeyi mata haka, yayinda kuma taga ake riritata tare da girmama bu’katunta fiye da Hannah sai kuma ta ‘karyata zancenta na farko, sam tarasa dalilin hakan gaba ‘daya ta gaji.
Dai-dai lokacin da tacika sati uku cif da zuwa gidan adai-dai lokacin Yayah Abbas ya koma bakin aikinsa wanda yayi dai-dai da wata biyu da kwana uku da rasuwar Mahmud.
Zuwa lokacin kam Teemah ta saduda ta daina damuwa, ri’ke ‘kuncinta kawai tayi azuciya.
Abbas ‘din ma dayake bazama sosai yayi agidan ba, ita dai tasan yaje Gombe inda daganan taji labari abakin Ummah cewa ya wuche Dubai daga can.
So rashin zaman nasa yasa bata fiya ganinsa ba, amma duk da haka ‘ko’kari sosai ko da bayanan amma yana kula dasu yana yawan turawa Hannah ku’di yace suyi amfani dashi, wai shi duk a’ko’karinsa naganain ya kula da amanar marigayi da ya kar6a, Hannah kam murna ta ke yi aduk lokacin da taga alert awayan ta takance ” _albarkacin ki fah nake ci Teemah, da Yayah baya son bani ku’di ko na tambaya baya bani sai yaji ‘kwa’kwkwaran dalili kafin nan yabani, kuma Daddy ma baya bani idan na tambaya sai ya wani ce in tambayi_ _Yayah na yabani kuma fah yasan dramar da muke sha dashi, amma duk da haka gurinsa yake turani, shi wai adole_ _be so_ _insaba da kashemanyan ku’da’de sai kuma_ _yanzu naga ba’a tambaya bama bayarwa yake yi_ “
Ta6e baki Teemah kwaia tayi dan ita bata da matsala da wannan.
Abinda ke damunta ma ya isheta, dan haushi ranar kam har kuka tayi musamman da ta tuno da Mummy, da ance aure toh yanzu kuma fah tunda babu auren memiye kuma dalilin tsareta,
bata ja tsawon lokaci ba ta bawa kanta ha’kuri, wani lokaci harda laifin mummy take gani, tasan ai itace ta shareta da bata manta da ita ba da duk haka be faru ba.
Daddy kam ba’a ma maganarsa dan shi samun layinsa bata fiye yi ba dayake yana yawan tafiye tafiye shiyasa bashi da takamammiyar number da zata sameshi akai
.
Ko bayan tafiyar Abbas ma bata damu ba dan zuwa yanzun babu ba’konta cikin duk rayuwarta komai tasaba dashi, zaman gida da sauransu, ita kanta ma yanzu tana jin da’din rayuwarta mafi yawan damuwarta ya kau, Anty ma har yanzu tana kano bata koma Lagos ba kuma cikin sabo da sha ‘kuwarsu babu abinda ya ragu sai ma ‘karuwa.
Ahaka da da’di ba da’di har Mahmud yacika wata hu’du da rasuwa, inda duk mutanen zuwa yanzu alhinin rashin sa ya ragu azu’katansu addu’a kawai suke binsa dashi.
Alhaji Muhammad kuma sosai yagaji da zaman Anty agida koda yayi mata magana kuwa sai tace Abbah ne yace tazo gida, tafa’di hakane kuma dan bata so mahaifin nata yaringa damunta da batun komawa.
Shikuwa da be san manufarta ba suna rabuwa da ita sai ya tuntu6i Abbah awaya yace masa ” _Yusuf wai meke faruwane, naga tsawon wata biyu kenan harda_ _kwanaki Maryam nagida, bamu ta6a tattauna dalilin zaman ba, naga_ _kuma ko ka ‘kirani baka kawo maganar ince dai lafiya ko?_
Abbah cewa
” _Lafiya ‘kalau Alhaji ina nan ma zuwa kwanan nan insha Allahu nima_ “
” _Toh Allah ya kawoka lafiya, gara de ayi abinda ya dace ina ganin zai fi_ _ko_ “
Cewar Alhaji Muhammad yana me shafa gemunsa.
Abbah sai ya tabbatar masa da cewa
” _insha Allah komai zai tafi dai dai bisa dacewa_ “