SAMU CHAPTER 5


SAMU





CHAPTER 5





Washe gari da safe,abun farin ciki ne ya same zuwairah, ganin kiran karime ya sa ta bulbukan farin ciki a kan fuskan ta sai barin jiki take tun kafin ta kai kunne..

Nan ta dauka tace Alhamdullh, karime?
Dan shiru ne ya biyo baya kafin karimen ta amsa

Sai dai taji wani dum da yanayin karimen”
zuwairah kina ina ne?

Tace karime lpya kuwa gani nan a gida!

..tace to ina zuwa daga nan ta katse wayar..

Kasa zama zuwairah tayi
Duk dama Yanzun ta tashi a bacci so ko sallah bata yi bare wanka ko brush tana tsaye tana zirga zirgan jiran shigowar karime…

After 25minutes aka buga kofa da gudu ta taho falour lakatar lakatr ta bude kofa
da tsananin shauki suke kallon juna, amma sai suka kasa rungume juna sabida yanayin da kowacce ta sauya.

karime na mamakin yadda gidan jabir ya dawo datti makamalan bakamar yadda ta saba zuwa ta gani ba, ita kuma zuwairah na mamakin ganin yadda karimen ta ta dada mokadewa ta dawo kamar mai tallen sigari da goro..

Kawata lpya kuwa ta jawo hannun ta ciki,

Kafime tace”Ina masu gidan?
Ina nufin ke kadai ne haka.?.

Eh ni kadai ne karime har kin mance samha ta je wankan gida?mmmmm daga ina haka
Ai nayi ta neman layin ki kamar nayi hauka baya shiga..

” ajiyan zuciya tayi Cikin jimami tace bari kawai ke dai ki bani abinci na ci,

Tace tabbb kinsan wannan mai wuya ne anan kam gaskiya nifa tunda matar sa ta je wankan gida ban sake daura komai ba don bazan kashe kaina ba..

Karime dai na kan kallon ko ina tace ni ki san nayi yunwa nake ji…
Tace to in kin iya sai muje ai
Ba musu suka shige kitchen nan ma dauriya kawai tayi ta dafa abincin duk dama halin su daya amma sosai take shan mamakin kazantar zuwairah shinkafa da mai da yaji suka daura daga nan ta zauna suka ci..

Karime Bata samu daman magana ba sai da taji dumi aciikin ta hawaye ne suka soma saukowa..

Hankalin zuwairah ya tashi sosai don dama tayi ta tambayar ta meke faruwa bata ce komi ba

gashi tunda ta zauna zuwairah ta ke sharo mata abunda ya wakana tass tasss ba ragi

Yanzu ne tace hmmmm zuwairah kenan” kina cin duniyar ki ashe har yanzu,uhm uhm ke nikam naga duniya lallai rayuwan nan bata da tabbas

A tsorace tace wai meya faru ne karime..

Bata kula ba tace
Wato ke har yanzu baki dena kazantar nan naki bane zuwairah?

Ta dan murguda baki tace kin fara kenan ko karime..tace am seriious na dauka ko danki samu gida zaki dan rage wasu abun ki waye amma jibi muhallin ki kamar gidan mahaukaciya anan a gidan nan ba inda yakai dakin ki wari fa..

A fusace zuwairah tace ua isa, ta bi ta daure fuska..wai meye haka daga zuwa zaki fara soka min maganan ni bana son iskan ci msww…

Karime ta dan fashe da dariyar takaici mai ban mamaki tace ai bani da lokaci ne zuwairah
Gwara na soma gaya miki abunda nake tafe da shi tun kafin lokaci ya kure mun..

Ki sauya halin ki zuwairah a duk dama ke kadai ce agidan kin kasa yin komai sai bin gado?,to wallhy wannan rayuwar taki ba mai bullewa bane,

Kinsan me ya faru dani kuwa? …anan ta bata labarin bakin hakin data shiga a hannun mijin ta malamin zaure…
Shi babu wani maganin ko kisisnan mata da bai sani ba don har shi dakan sa yake bda taimako….sannan ya kafe ta akan kishiyoyi wanda suka koya mata da maganin matan ma sai ta rike Allah da tarbiyan ta kafim tayi zaman aure

STORY CONTINUES BELOW

..sosai suka wajiga ta suka nuna mata halayen da ko a mafarki bata son asake nuna mata irin su
Wannan ma bai dame ta ba, yanzu ance bazata iya daukar ciki ba sabida mahaifan ta ya kamo da ciwo sanadiyar dure duren magani..

Karime Ta dan ware kafan ta kadan wani guntsurarren wari ne ya taso wanda ya gautsina musu ciki baki dayan su..

Tuni zuwairah ta mike tana kakarin amai..
Gaban karime kamar famin shadda har wani baki baki yayi yana fidda diwa mai shegen wari…

Amma da shike ta saduda da sha tana kuma karban magani ya zamo sa sai ta bude ake jin gumi..

Tuni hankalin zuwairah ya tashi sai ma ta kasa zama kusa da karime baki na bari tace
kan uban chan in gindi na ya dawo haka ai na mutu..

To ke Wani magani kikayi ta sha haka karime?.tace zuwairah ba wani maganin da na sha wanda baki sha ba kema nazo nan ne na sanar dake tun wuri kije aduba lpyar ki kafin ki naki ya dagargaje irin nawa..

Nayi ta dura abu ba kakkauwatawa Gashi ni ban samu na tara komai ba ga miji ya kora ni sabida dama amfani na kenan sex..

“Tabbbb kamar ya amfanin ki kenan?
Amma lokacin da yake jin dadin ki ai bai kawo amfanin ki bakenan ko..

Tace ki bar maganan na nikam zuwairah ni na san me nake ciki..

Ni dai Zuwairah na rike ki da girman Allah ki sauya rayuwar ki kafin lokacin ya kure miki

Zuwairah “Tace tabbbbbb……

Akan dan wannan abun,?toh Nikam banga ta wani sauyawa ba karime kknajin abinda na gaya miki jabir fa ya lalace yanzu wulakanci yake min gaskiya sai na saita shi kafin koma miye ya biyo baya ….

A fusace karime ta dakatar da ita zashe kuwa kin da aiki …wai To ya baza’a miki waknci ba zuwairah ki dube ki fa hammata duk wari baki kamar shadda,
Atlest ki bar wannan shegen son jikin naki mana ki tsaftace kanki

Wuf ta mike tsaye”Ah”a dakata ba wanin nan , da chan ma haka nake amma bai ta shi mun tsiwa ba sai yanzu Kawai in zaki taimaka min ki taimaka min, dama tunda na rasa maganin da kike kawo mun na soma ganin hau hau a al’amura na…

“Hmmmm zuwairah kenan…
to bari kiji gwara ma ki sake ranki ki ajiye maganan magani ki fara gyara halayen ki tukuna dama chan bangaya miki bane,..wallhy wata mata ce ta kaini wajen wani mutum shima wai bada maganin yake..
Shine na siya miki maganin da kuke using da wannan jinin al’adan naki daga baya nake jin ashe asiri yaje yumi da aljanu’….

Wai muddin miji ya hada ido dake bazai iya tabuka komai ba sai yanda kika ga daman yi da shi.

Ke banza kin dauka ko maganin mata ne zallah ko?toh Sannu mai gindin zinare
Wallhy ki shiga hankalin ki zai iya kasancewa jabir yana jin dadin kin amma ki sani mallakar sa da ki kayi fa asiri ne..kuma inaga karyewa yayi,

Hannu zuwairah ta daura akai ta budu ido tace na shiga uku zuwairah asiri ?
Tace kwarai kuwa..

Yanzu kuma gaskiya bazan sake tsoka kai na a wannan halin ma don naji ajiki na nagaji da wannan harkan..

Ta mike tsaye tace shawara ta gareki ki sauya halayen ki

Ki sauya ko dan tsaftan nan kina yi sabida kija mutuncin ki a idon sa  haba zuwairah??..wallhy idan jabir ya gama gano siffar ki fa zaki ci ubanki anan gidan..dakan ki zaki kwashe kayan ki bashi waje ah toh..

Tana shiru chan ta ce “A ganin ki ba?
Ni nasan jabir 
Wallhy kawai wani abun ke ruda sa kuma zai dawo dai dai..

Kema ki tsaya kiga na sami kudin.
Kinga sauki ma ya samo kawai bani nunber malamin zanje ya bani tunda ke kin saduda
gaskiya bazan iya komai ba..don ban iya ba..

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi kawai karime tayi ta buga shewa tace iska zai wahakar da mai kayan kara..
Anan ta dauko abu ta rubuce mata nunber malam mai mallaka..

Tace Allah ya baki sa’a zuwairah ni na tafi,.

Ko sai anjima bata fada ba ta soma zagin ta..
munafuka kawai don nata gindin ya rube duniya ya juya mata baya tana so ta durgushe nawa mu dawo daya..

Jabir kam kamar na  mallake sa daa asiri ko babu asiiri ba abunda ya dame ni..

Daga nan ta koma daki ta shiga nazari
Kawai sai ta tashi ta shiga kimtsa wajen ta shirya ko ina da kyar da bala’i kamar zata yi amai awasu abubuwan ma dan dole ta kyakem.

Itama tayi wanka ta dan tsafatace wajen…

Ta zauna rigijin tace to yau na sauya Ai zanga karyan nasa,in ma wasu ke juya masa kwakwalwa akai na duk zan gani…

Cikin ranta ta na kawo tunanin ko abokai ne suke zuga shi, ta dan girgiza kai ta kuma cewa tabb
Toh walllhy ba a haka dani uwar mutum zanci idan na na sami kudin nan kaf sai na raba shi da yan iskan nan shegu masu dogon baki..

Shikam Sai 9.30 ya dawo already ya ci abincin sa awaje ya kammala komai yana tahowa dakin sa ya wuce straight ko noticing din gyaran nata bai yi ba,duk dama banbancin kadan ne cos dama ba iyawan tayi ba

Tana jin motsin sa ta fito, ta shigo dakin sa sai dai bata iya da’a ba, a tsaye ta tsaya ringim a kansa tace har ka dawo ne jabir..

Yayi shiru kamar baiji ba … Wani tunanin ta yi aranta a take sai
Ta tsuguna,tace” desire magana fa nake da kai

Ya dago fuskan sa a dan daure yace tashi kije ki jira ni a dakin ki ina zuwa…

Ganin ya dada tamke fuska ya sa ta tashi ta fita…

Bayan kamar minti 30 ya shigo ya same ta a dakin ba laifi babu wani kaya a kasa ko a cunkushe..

Bai wani bata lokaci ba  ya afka mata suka samu gamsuwar junan su…

Ba yadda bata yi da shi ya amsa ta ba amma gum ya kame bakin sa har ya sauka akan ta nishi kawai yake saukewa

Bawai baya jin ta bane har yanzun kawai rashin da’ar ta yake ganin bazai dauka ba, Don kuwa tunda tayi barin ciki jinin ya wuce mata komai ya since daga asirin mallakan da ta masa shiyasa ma da yayi tafiyan nan kwana biyu sai yaji ya dawo cikin hankalin sa wasu tunanin anan suke shigo masa

Washe gari data ga ba samun kansa zatayi ba sai ta tayi nasha nasha ta na kwakwalo amai tana nishi…

She tot ko na dan lokaci zai yaba kokarin datayi ta kimtsa kanta amma baiyi hakan ba kwata kwata sai taga bata da wani amfani yanzu in ba akan gadon sa ba..

Sai data ji motsin sa daf falo sai ta kara kakarin tana wyyo wayyo Allah
Anan ne a shigo ya same ta tayi nasoo akasa tana kifi kifi da ido..

Daga tsaye ya dube ta fuska ba yabo ba fallasa yace lpya? Dama baki da lpya ne zuwairah?

Cikin dan karamin nishi da sanyin jiki tace , ai baka damu ba yanzu ina kuwa zaka san halin da nake ciki..

Zai yi magana ta dan daddafe ta mike sigar kuka da tsananin jin takaicin abun
…tace jabir ka fada min gaskiya wa yake shiga tsakani na da kai, ? Ni ka fada min sabida abubuwan naka sun wuce misali in so na me bakayi ka sawwaka min mana, yace stop it, ke ma ai kinsan abunda kike yi,  tace “eh na sani
kace kazanta amma na dau gyara yau still baka canza  ba, hakan yana nufin ba shi bane akwai munfrcin da ake kulla min a wajen ka kuma Allah ya isa tsakani na da munafukai duk wanda yake so ya raba ni da kai ba zai ci nasara ba…

Tasan zai amsa sai tayi saurin zubewa kasa ta shiga kakalo amai da baya ma fitowa sai ruwan yawu datake fetsowa..

Ya dan duka ya riko ta yace wai meke damun ki ne?
Toh dauko mayafin ki kije asibiti…

STORY CONTINUES BELOW

Batayi musu ba ta tashi ta kimtsa ya dau ki 5k ya bata sannan ta fice..

Shima office yaje ya cigaba da abubuwan da ke gaban sa,.

Yana tafiya ta dawo, 
Ta cigaba da kulle kullen ta

Chan da yamma ya tashi amma bai kuma dawowa ba ya je chan wajen sabon ginin sa  dayake kerawa babu wanda ya sani daga matan nasa..

Sai dare ya sake dawo wa anan tazo ta ke kawo masa maganan tayi barin ciki,alhalin karya take duk shirin da ta hada ne don ta sami kudi

Tace Kuma ina bukatan kudin wanke ciki kamar yadda doc ya fada…

Baiyi musu ba ya jimanta ya kuma tambaye ta amount…nan farin ciki ya balbale ta a ranta , jin zata sami kudin da zata koma wajen malam mai mallaka..budar bakin ta tace, duka duka dai dubu 150k ne.

Yace what? A wani asibiti kenan..

Toh ni bani da shi,kai kima bari kawai ni zan kaiki wani asibiti gobe aikin su nada kyau…

Nan take taji ranta ya baci, dama daurewa take yi taga ko zata karbe ta wannan salon amma sosai take ganin kamar jabir zai raina mata hankali…

Tuni ta shigo da tsegeran cin ta, 
Tace akan me?yanzu kudin jinyan nawa ne zaka ce babu Kai dai kace bazaka bani ba kawai..

Yace eh,bazan bayar ba.. wateva, kije ki jira goben ni bani da150k,..haba da Allah ai ko operation albarka kar ki maida ni shasha sha..

Tana shiru can ta kuma a shsance murya tace,jabir dan Allah ni ka bani kawai zanyi komai da kai na..!
Dama so nake idan nayi wankin cikin sai na siya maganin mata, kasan in ban kula da nan ba bazamu ji dadi ba..

Yace,nace banda shi..kije kawai gobe zamu je asibiti… Ya daure fuska

Tsaki ta ja tana kallon sa da mugayen ido daga bisani ta tabe baki tayi waje…

A hakan ma ko bacci bata iya yi ba ,gashi tunda ta gaya ta yi bari zai bai zo dakin ta yau ba..

Hakan ya sa ta zauna tayi dogon tunani taga ba abunda ya rage mata illah ta debi gudun ko da ta sata ne.

Da asubah tana jin  ya wuce masallaci ta shiga room dinsa.

Straight inda yake ajiye kudi taje sai dai sholl babu ko sisi sai ma transaction slip na kudi dayawa anan ya zuba wasu yayi using wasu baiyi ba

Ba lokacin tsayawa karantawa don haka kawai sai ta  kawo tunanin ko ya daina ajiyewa kudi ne a gida sai a banki?

Nan ta jawo wayar sa ta bude messges ta soma dubawa 
Anan ne ta ke sanin ma na haihu, kuma take ganin tex mesges dinsa da kudaden da ya tura min dan kwanaki Akalla dani da yaro na munci almost 360k daga wajen sa..

“Fushi ya sa ta jefar da wayar akan gado tayi waje..anan ma zirga zirga kawai take ji da wani sabon shaukin jin dole ne ma ta mallake jabir ko da tsiya ne..

Bayan ya dawo daya gama kimtsawa ya buga mata kofa akan tafi zai kaita asibiti,

Anan ta soma masa borin da bai da kai baida wutsiya cewar ta ai yanzu ta gane mai shiga tsakanin su,ai tunda ta zo gidan sa bai taba bata kudin da yakai rabin wanda yake turamin ba..
Acewar ta baida adalci..

Ire iren abubuwan da yake dada sa shi yaji tafita masa akai kenan
..amma sam yau din baida niyyar masifa sai ya kyale ta anan ya fice…

A office ne da yayi bako daga lagos wani baban abokin sa suleiman..
Tun secdnry schl suke tare,kuma sun san juna sosai sai dai hardly suke sharing matsalolin su musamman na gida..

Dama umar da usman ke yawan magana akan nasu har suke jan shi shima ya tofa,…

Yau sai ya sha mamakin tambayar da Suleiman din ya masa yace masa ,”jabir anya kuwa lpyar ka kuwa?tun dazu nake ganin kana katse wayar matar ka i hope dai ba wani abu bane kasan mata fa sai da hakuri zama da su…

STORY CONTINUES BELOW

Abun zuwairah na mugun damun sa amma ya kasa sanin ta ina zaiyi bayani sai yace ma suleiman kawai ‘ya shiga confusion ne matar sa na gida tana ganin kamar baiya adalci amma a ganin sa yafi rashin adalci ma uwar gidan sa sai dai ita bata fada masa hakan shiyasa ma yanzu kansa ya kulle..

Suleiman yace” indai haka ne kai kafi kowa sanin yadda zaka warware matsalan ka ba sai an baka shawara ba..
Wanda kasan kana mata acikin su ka daure ka nemi gafarar ta ku sasan ta ita kuma wanda kasan baka mata sai ka fahimtar da ita sosai ta gane hakan…

U have to be a man duk abun daga zuciya ne ka nitsu..

Yace, toh suleimam bakomai insha Allah zan yi tunani..

He just didnt think that har zai sami shawara mai inganci batare da fadan komai in details ba..
Har suka rabu da suleiman yana nazarin yadda zai dena jin nauyin samha ya budi baki ayi ta ta kare..

Yasan zuwairah kam lokacin sa take bukata ya qudira sosai aransa zai nuna mata shi miji ne wajen ta ba abun wasa ba….

Haka ya dena kula su kwana biyu bayi shiga harkan ko daya daga cikin su ..ya dai nemi nitsuwa makan sa yana tunanin yadda zai tallafi familyn sa har ya fara rayuwa mai inganci

ya san saura sati biyu zuwa uku na dawo daga wankan gida so he have to move fast..

Duk wannan lokacin Zuwairah sam bata cikin hankalin ta gashi , abubuwan sai dada tsami suke mata
Yau tayi kwana uku chur ba abunda ya shiga tsakanin ta da shi kuma yana gidan sai ta gwammaci da ma batayi masa karyan nan ba..

Sai dakanta ya soma neman kuncewa tsaban tunanin yadda zata samu kudin da zata siya magungun ta..

Kawai sai ta yanke shawarar sata, 
dakin sa ta sake shiga ta sake dube dube, agogon sa da wani  chain bracelets sabo ta kwashe guda hudu ta kai ta boye a dakin ta..

Yana dawowa daga sallah, bai kula ba har ya shirya zai fita aiki..

Da mamakin sa saiga ta nan ta fito, ba gaisuwa ba komai tace masa zata fice gidan kawar ta anjima..

Harara ya watsa mata tukun na yace bazata je ko ena ba..

Sannnan in ta sa ka fa ta fita a bakin auren ta..ko sauraron ta bayi ba ya fice..

Ta so ace ta fitan kawai in ya so in ta cika burin ta na siyar da abubuwan da ta kwaso sai tayi shirin sanin yadda zata hadu da malam mallaka..

Gashi wayar sa baya shiga gani take kamar karime wrong number ta bata amma ta kudira aranta sai ta nemo sa..

Ba yadda ta iya sai ta kira maman abdul ta tambye ta ko zata sami me sayan abubuwan,?

Bata dai bata amsa ba amma sai tace zata mata tallah da karfe 12 na rana zata zo ta karba..

Nan ta baza su akan gadon ta tana lissafin ko wanne kudin da zai ci a kasuwa Tun daga lokacin take jiran ko za’a bata iya yi ta dau kusan awa 3 tana zaune tana sake sake aranta
Tana cikiin haka
Kashi ne ya matse ta, ta shige toilet agurguje

Cikin rashin sa”a, sai dawowa tayi taga babu komai akan wajen da ta ajiye ..

Hankalin ta inyayi dubu ya tashi tayi ta dube dube bata gansu ba, gashi dai yanzu 11 ne jabir  baima sa lahadin dawowa ba bare ta ce shine…

A girguje tayo hanyar waje ta duba ko barawo ne ya shigo tana bude kofa suka hada ido da shi yana tsaye alaman shima wucewa zaiyi,

Wani garas ta ji a kanta, haka kawai jikin ta ya bata ya kamo ta,

Hakan kuwa akayi dama ya zo ne ya tabbatar da ko ta fice ko ba ta fice ba,, a lokacin ne ta soma sanin ita din ba komai bace,sai da yayi mata lilis yace bazai dauki kazan ta sannan ya dawo ya dauki sata ba,

Daga lokaci ya kuma kafa mata doka kar ta sake shigo masa daki akaro na uku kuma ko tsinke ya bata dakin sa daga yanzu sai ta biya shi ko ita ce ko ba ita bace…

“taci kuka ranar Haka duniya ta murde mata ta rasa abunyi,
Washe gari da faruwan haka, gaba daya sai  ya kasa samun sukuni gani yake don ya hana ta kudin wanke ciki ya sa ta sata ai da zuwairah bata dauke dauke,kawai sai ya dauki 30k ya ajiye mata don ya mata adalci..

Gashi yanzu ya mugun sama mata ido y Tsaban bata da wani mafita  sai ta kudira kawai gwara tayi ta siyan maganin mata tana sha tana dada zaki harta samu ta sake zumma zuciyan sa kan ta Kafin ta samu kudin siyan na mallakan.

A dan wannan lokacin zaman sa da zuwairah, ya sa ya fahimci abubuwa da yawa..

Wato Lokacin da Allah zai azirta ka da mace na gari mai tattali da biyayya da sanin ya kamata a lokacin kai kuma kake jin a duniyan nan  kai kadai ne  kuma ka isa ne.. So you  just take her for granted.

Sannan ya gano cewa , ba ma abokai ba kawai har mutanen da kake tare da su wasu zasu baka shawara ne yadda ransu yake so bawai don su magance maka matsalan ka ba,sabida most of them basu ma san ya kake zama da iyalan ka ba sai dai suyi harshashe suyi judging yadda su suke zama da nasu iyalin..

Kai kana nan baka sani ba hala ba ka fisu ma nesa ba kusa ba wajen kyautatawa da iya bi da  tsarin zaman takewa..

Abu daya ne dan adam bai gane ba har yanzu,
Yawanci maza dake zama suce sun iya kaza ko matan su basu kaza …99.9 %dinsu karya suke yi,..

so kawai suke ka dulmuya ku dawo dai dai Saboda su baza su iya ba kai kuma ka iya, da su sauke kai su tambaye ka shawara ko taimako sun fi so suga kana tagumi suma sun jera da kai suna yi..

Most of them sum fika damuwa amma bazaka taba ganin sun damu awaje ba amma su suka san halin da suke ciki a gidan su.. 1

You must be carefull with  duk aboki ko abokiyar da take fitowa karara tana buga kirji tana bare deden  ta iya da gidan ta ko mijin ta ko namijin da zaice a gidan sa shine kaza shine kaza …

always see for your self ance wai masu mulki da saurata ba sai sun fada baa na ganin su dole za basu girman su….

Shikan sa jabir ya gani, tunda ya soma shiga tarkon zuwairah ,har yau babu wanda ya taba ce masa ga shawara ko meke damun ka?
Kowa sai dai ya zuba masa ido..

Abunda ya bashi mamaki bai wuce a office da ake gulman sa ba cewa ya auro dai dai da shi kuma har da umar da oga yisuf aciki.. Shiyasa a yanzu ma ya dena zaman  majalisan su ya dawo kawai ayi frndship kawai a zauna lpya

A washe garin ranar ne ya shirya zai je shi kaduna .
Saboda samun tataunwa da ni akan matsalan da muka fuskan ta abaya..
   
Ga kudi yanzu kam Allah ya dada masa budi, ..

Yanzun bai da wani buri illa ya samu kwanciyar hankali kamar ko wani magidan ci.

A ranar juma’a da safe ya bar kano ya kamo hanyar kaduna.Nikam tunda da seif yayi bacci, nake kwance ina tuna abubuwan da su anty hanifa da mumy ke gaya min..” +

Fargaba ne tam araina amma abu ne wanda ko ni nan na san ya zama min dole na aikata su ,
Gashi tun da anty hanifa ta tafi Mumy salamtu ta yi min fada akan jajircewa da hakuri in har mallakan mijin na ke nema..

Ta kuma gaya min ba gamsar da miji ba shi kadai bane hanyar mallaka ah ‘a , mumy tace, shi Aure da nake gani ya na da pillars kwarara wanda suke rike da shi,masu nauyin su daga ciki shine hakuri, shi sex din, da kuma tattali….but most of all namiji yafi daukar mace mai biyayya da respect a zuciyan sa 
saboda ita ce kadai mai ikon mallake sa har abada Ba maganin boka ko sex ba.. 1

Tace min “Da jikin naki mai dadin amma idan baki da da’a, da tarbiya watan wata rana zaki gane ke ba komai bane a wajen sa sai engine kashe wutar gaban sa..

Sannan tace”shi kazan ta yana kashe ma namiji karfin shawa’ar sa kamar yadda qamshi da tsafta ke daga wa, inda chan kina ganin tsaban dadin jikiin ki bazai bari ya daga miki murya ba,to kijira a kwana a tashi kazantar ki zai kore sa karfi da yaji kuwa zaki ga yadda zai guje miki.. 
abu mafi muni da kazanta shine “tsana” yake cusa ma mutum aransa game da ke sai miji yana jin ya tsane ki altho wasu bazai hana su kwana da ke din ba.. 2

Amma Ranar da ya cika sai dai kawai kiga miji m
Na hantarar ki yana bata rai dake haka kawai baya ma son ki zo inda yake bare companyn ki a tare da shi…

Mumy tace
Shi kuma biyayya kuma ba off head ake yin sa ba garan gatsau,..dole mace ta zama mai nazari da basira da kuma lissafi wajen sa kafar ta  ..

Hakan kuma baiya samuwa sai kin kwantar da hankalin ki kin nitsu kin tara hankalin ki waje daya..

Anan ma ta kawo min magana mai muhimmnci”tace shi nitsuwa baya samun matar da bata ibada ko da ace sallah akan kari ne, ko macen da ta dauki addu’a ma kanta da iyalan Ta a banza ,

sai kiga a yi wata agidan mace babu kira’a ko karatun Qur’ani,toh idan ma ace har baki samu ilimin addini ko islamiya agidan ku ba sai ki yi kokari ki shiga agidan miji ko shi dakan sa in ya samu lokaci yana koyar miki,

nitsuwa ma dan adam baiya samuwa a zuciya sai ya cika addinin sa dam dam yadda ya kamata…ta kuma ce min kar ma mance da dan sallahr daren nan da azumin lada kai har ma sadaqa da taimakon yan uwa da dangi a duk lokacin da na samu wadata da sarari…. 1

Tace”Biyayya wa namiji cikin fasaha ake sa shi,bawai zaki fito karara kina nuna masa eh ena maka biyayya ba ne ki kyale sa shi da kansa ya gane haka,don wasu matan ma idan hakurin su ya gaza sai suyii gori akan ai ina maka biyayya baka gani, Hakan ya nuna ba don Allah kike yi ba Babu kyutatawar niyyya akan neman aljannar ki..

A matsayin ki na mace ki sabar ma kanki salo na masa godiya da sama miki abinci da muhalli da sutura abu ne mai girma, 2

sannan ki tuna fa mijin ki shima yana da na shi damuwar da kuma farin cikin sai ki dinga tunawa da shi a duk lokacin da zaki yanke wani hukunci.

idan ya nuna bacin rai akan dan wani qaramin abu da kikayi masa ko ma aka masa a waje sai ki bashi hakuri bakiyi musu da shi ko kiyi masa fada ba , 1

Kar kuma daga shigowar sa ko zama baiyi ba ki soma kawo masa matsaloli  da complains atleast ki dan barshi ya nitsu kafin ki kawo maganar ki zai fi saurara, 1

namiji baya son mace kamar maza misali ko da tambayar sa zaki yi ajere ajere muddin kinsa shi cikin fahima zaki samu biyan bukata a saukake ba sai da maganin mallaka  ba ko sex. 1

STORY CONTINUES BELOW

Duk abunda mummy ta lisaafo min kenan atakaice Kuma tayi min gargadi da tuni nayi shi don Allah ba don komai acewar ta ba insha Allah zan ci riba..

Ni yanzu Tunani na shine ,yadda zan koma gidan jabir, haka kawai nake jin wani iri araina, gani nake kamar bazan iya ba Duk da hakan daga zuciya ta ce
Amma karfin gwiwa  kam na samu..
Im all groomed up har dilka da sauran gyaran jiki ina samu, na murmure nayi bul bul fata na na sheki adan kankanin lokaci na haska..

Gashi mumy bata mancewa wajen bani abinci da abubuwan da suka tanada min na gyaran hq na sabida haihuwan da nayi..

Tuni ta sa aka rubuce min suratul yusuf, suratul maryam da suratll rahma aka wanke min su da ruwan kankana ta sa nayi bisamillahh na shanye su tassss..wannnan hadin tun ina budurwa aka mana sabida shikan sa ma kariya ne daga wulaknci da juya baya daga da namiji ko da kuwa asiri akai masa bazai taba mancewa da ke ba. 6

Shi mumy take wa lakanin mallaka. 1

Sannan ta sa aka dafo min kazar gida da nonon raqumi aka yi mata barbaden ridi shima na cinye..
Tace to ko wannnan ma ya isa ya iya min da duk wani dawainiyar miji n amma duk da haka ta hada ni da wasu tarkacen.

Ajiyan zuciya nayi na jawo ledojin da ta zuba min  hadin dakakken
Garin furen zogale,zanjabil habba da garin raihan tace na dinga deban karamin cokali ina hadawa da zuma safe da yamma  ina sha..sai  man tafarnuwa
Dear musk
auduga
Tace ki hada deer musk cikin cokalin shayi man tafarnuwa cokali biyu ki gauraya kisa auduga ki dangwala kiyi inserting a hq awa uku ki cire amma tace once in a while ba kullum ba
Sai  kankana 
Zuma
Madara
Kinsan kankana uwar ruwa ce sai ki matse ruwan ta ki tace ki juye madarar ruwa a ciki kisa zuma ckl biyu 
sai
aya
Dabino
Gyadar mata
Gyada mei gishiri
Minannas
Sugar
Kanunfari
Yougurt ko nono
Ki hadasu ki daka ki rika diban cokali biyu kinasha da yugurt ko nono 
saiwar kankana
Saiwar zogale
Kanunfari
Mazarkwaila
Tace Ki sami saiwowin ki tafasa ki tace ki maida ruwan inya dahu ki sauke kisha sau uku a rana.
Sai  ruwan rake
Da Ruwan kankana
Tace Ki matse ki rika sha sau uku a rana yadda kikasha kinajin dadi hka shima zai ji ki
Sai kuma aya
dabino
Mazarkwaila
Farin dankalin hausa
gyada
Tace Ki gyara dankalin ki ki yanka ki shanya ya bushe ki zuba kayan kamshi ki dakashi ki daka dabino da mazarkwaila ki soya gyadar ki sama sama ki turmushe ta ki daka su duk ki daka ayanki ki hadasu guri daya ki rikasha da madara peak
Sai hadin Gwanda
Kankana
Zogale
Abarba
Citta
lemun tsami
Tace Ki hada ki markada ki tace kisa lemun tsami kadan da zuma kisha
Sai na kanun fari
Zuma
Garin ridi
Nonon shanu mara tsami
Ki dafa kanunfari ya dahu kisami garin ridi da nono ki hada ki gauraya kisa a frigde ki sha idan yayi sanyi ki maimaita duk sati ba ruwanki da rashin ruwa kuma
Sai ki sami minannas kadan da kanunfari ki dakasu kidora ruwa a wuta kisa citta da hadin ki tafasa kisa sugar da lipton tace kusha keda shi.
gyadar mata 
Dan bashanana
Yayan kankana
Yayan zogale
Minannas
Farar biya rana
Idon zakara
Asuwakin mata
Mazarkwaila
kidakasu luguf kina diba kinasha da madara peak 
Sai zogale
Zuma
nonon shanu
Ki shanya zogale ba a rana ba idanya bushe ki daka ki tankade ki debi ckl daya ki zuba nono da zuma kisha

lemon zaki
Madara peak
Zuma
Ki matse ruwan lemun kizuba madarar da suma kisa a fridge yayi sanyi kii sha

kwakwa
dabino
Madara
Ki markada kwakwa da dabino ki zuba madara peak ta ruwa kirika sha
Duk wayannan na rubuce su a dan joter wasu na na haddace su kawai akaina..

Duk Su mumy da anty hanifa sun gama min komai su mummy na ba su ma sani ba..

Ranar da jabir ya soma zuwa gidan namu, a lokacin mumy salamatu ta soma nunawa karara abunda ke damun ta arai,

sabida daga ganin sa sai
mumy na ta soma declaring kawai tunda ya zo na shirya na bi shi ba sauran jira,

Tace ai kwana kadan ya rage nagama hutun naje kawai na kara sa agaban sa,

ranar da kyar na sha sai da kowa ya sa baki akan abari na karasa sati guda na gama kimtsawa

Shikuwa jabir Tun daga ranar ya samu saran zuwa gidan mu sao iban rawar kafa yake da zumudi musamman ma da ya ga yanzu na sauya gaba daya nayi kyau na kara cikowa har ma fiye da yadda ya auro ni ina budurwa,

sai dai yayi yayi na saurare shi muyi magana amma sam sai ma dauke masa wuta idan ya zo haka zai kara ci zaman sa shi da dan sa har ya kama hanya ya tafi ban leko ba,

wani bin ma bana zuwa kai masa seif din sai da na ba ma mummy sukara ta chan har ya kara da wuta..

Ita kam mumy na kullum a fushi take dani a duk lokacin da ya fice sai ta ce Allah sarki, yaron nan sai bin samha yake mutum da matar sa amma sai a ajiye masa ita ni sam wannnan abun baiyi ba

sai Ana saura kwana biyu tal mu dawo gida kano da jabir, kafi nan ma har ma yaje kanon sau biyu a kwanakin ya dawo

Da daddare ya zo gidan mu ya aika na same shi a palour.. Amma banzo ba sai da na tabbata yana dab da tafiya don lokaci ya tafi sosai kafin na tashi

Daurewa nayi as usual,amma duk bana jin dadi a raina haka kawai in na tuno da rayuwar da nayi a gidan sa ai naji bana jin  zan iya komai

Na taho na zauna sannan na dube shi a ladabce na gaishe sa..shiru yayi yana kallo na na dan lokaci sannna yayi gyaran murya
Bai wani bata lokaci ba Yace samha pls lets talk about this mana,wai meya sa kike gudu na ne?, yanzu ma har baki daga waya na in na zo gidan nan kuma bazaki zo mu gaisa ba?

Ina shiru ban ce komai ba ,,yace “tun zuwa na nake gaya miki ina so muyi magana da ke kafin mu kuma kano ko?
Still ina shiru, abun ya dada damun sa ya kawo hannu zai taba ni ma dan kauce
Na fashe da kuka a hankali “nace ni kam gaskiya bazan koma ba ai naga babu wani abun da zamu ce ma.

a take murya na ya hau rawa na soma jan masa shessheka a hankali mai shiga zuciya….ni kaina bansan meyasa na kawo wannan salon ba.

Ba shiri naga ya saukake murya abun bai masa ba ma ya sauko kusa da inda nake “yace samha meyasa bazaki koma ba?

Nayi shiru na kuma matsawa nisa da shi ,

a dame yace Ko dan  abubuwan da suka faru ne samha,?ban amsa ba a yce “pls listen to me shiyasa ma nake so nayi miki maganan dake dan Allah ki yi hakuri ki yafe min samha, samha im sorry i will do anything to make you happy wallhy nasna na dau alhakin ki,

Ya dada langwasa murya ” yana duba ni kalar tausayi …”Nasan kinyi hakuri da ni duk dam baki son ki nuna min hakan anymore, but im assuring you na gyara halaye na, just give a chance kinji?

Na mike tsaye  abuna ..”nace ni dai wallhy bazan iya ba,dan Allah ka taimaka min  kayi tafiyar ka ni gaskiya anan zan zauna bana son chan din kayi zamar ka da matar ka zan zauna anan yafi min dadi da kwanciyar hankali…

Zai yi magana na dakatar da shi cikin dan karamin kuka nace dan Allah fa nace jabir, shin bazaka iya min wannna alfarman bane?
Ai ba cewa nayi ka sake ni nace ni bazan je kano gidan ka bane,ni a gidan mu zan zauna …

Hankalin sa sosai ya tashi, ya rasa akan meye guda nake bori  sabida naki na fito fili na baje maganam dake zuciyan mu duka ..
Ga hawaye sharbe sarbe a fuskata ina jan shesaheka…

Jin alaman shigowar abba site din ya sa dan dole ya yi shiru ya kasa fadan maganan da zai gaya min…ya matso daff da ni kalar tausayi, yace kinga dare yayi min anan sosai ni zan tafi, sai ya ce to sai na zo goben ko?

samha dan Allah ki cire wannan maganan a ranki wallhy nayi nadaman abunda nayi miki ki yafe min kinji?

Na daure fuska na yam na tsime kamar ba da ni yake ba,kuma bance komai ba, har ya sulale ya fice..

Share hawaye na nayi na kama hanya na koma daki ko ajiki na…

Don Sosai na kudira araina bazan taba komawa hannun sa cikin sauki ba sai na chaguda masa tunani, duk dama nasan dole ne zan koma tare da jabir ko naki ko naso…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *