ABDULKADIR CHAPTER 10

ABDULKADIR





CHAPTER 10



Cikin baccin da baisan lokacin daya dauke shi ba yaji wayar shi na ruri, idanuwan shi a rufe ya lalubota, har kiran ya yanke, numfashi ya sauke yana dora wayar a kirjin shi hadi da gyara kwanciya. Wani rurin yaji wayar ta sake dauka, dakyar ya bude idanuwan shi yana ganin Nuriyya ce, dagawa yayi ya kara a kunne batare da yace komai ba

“Masoyi…” 10

Ta kira ta dayan bangaren, shirun AbdulKadir ya sakeyi, sosai ta bata mishi rai, Waheedah ce a tunanin shi da komai shisa baiyi lokacinta ba har yanzun

“Hello…”

Ta sake fadi, muryar shi can kasan makoshi cike da bacci yace

“Ina jin ki”

Ya lumshe idanuwan shi da suke mishi yaji saboda bacci

“Naga baka dawo ba har yanzun… Dan Allah kayi hakuri…”

Ta karasa maganar muryar ta na karyewa

“Ina gida ni tun dazun”

Cewar AbdulKadir din yana ganin rashin hankalin Nuriyya da zatayi tunanin dan ta bata mishi rai zai tafi wani wajen, a lokaci daya kuma yana ganin yanda har yanzun bata san wa take aure ba, jin tayi shiru yasa shi fadin

“Kiyi bacci, sai da safe”

Kafin tace wani abu ya kashe wayar shi. Bai taba zaton akwai ranar da matar shi zata bata mishi rai harya raba shimfida da ita ba, duk fadan da zaiyi da Waheedah in dai suna gida daya a jikin shi take bacci, ko baya mata magana kuwa. Numfashi yaja yana sauke shi, kirjin shi zafi yake sosai, tunanin Waheedah din yanzun ya kara taso mishi da wata irin kewarta. Wayar shi ya duba yana ganin karfe sha daya na dare, karamin tsaki yaja, dare ma baiyi ba sosai, ga baccin gabaki daya yabar idanuwan shi.

Lambar Waheedah ya kira a kashe

“Dan Allah ki kunna wayarki, ba sai kin daga ba Wahee, ko ringing din naji a kunne na zan dan samu nutsuwa” 24

AbdulKadir ya fadi yana sake gwada kiran wayar, a kashen dai ya sake ji, tashi zaune yayi ya jingina bayan shi da jikin gadon. Dayan pillow din ya dauka yana dora shi kan cinyar shi. Bude wajen text yayi yana rasa abinda zaice mata, ko da can kalaman shi taqaitattu ne, balle yanzun kuma. Fasa tura mata yayi yana scrolling can sama, tsofin sakunanta ya dinga karantawa, duk yawan da suke dashi sai yaga sun kare mishi da wuri, WhatsApp ya koma yana jin dadin yanda baya goge chat, dan lokutta da dama ita take goge mishi in ta dauki wayar, sai tace yana cika waje.

Danma ya hanata goge mishi nasu, tunda idan yana wajen da babu network su din yake karantawa suna rage mishi kewarta. Lokacin da yabi duk wani text dinsu ya gama karantawa karfe biyu saura. Duniyar yakeji ta mishi wani irin fadi, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi, da yanajin nutsuwa sallah zaiyi har gari ya waye, amman bashida wannan nutsuwar. Saukowa yayi daga kan gadon yana fita daga dakin zuwa bangaren Nuriyya. Bacci ya samu tanayi hankalinta a kwance, shi yace tayi bacci da kan shi, baisan me yasa baccin ya bata mishi rai ba

‘Kin batamun rai, bana tare dake shine kikayi bacci kika barni’

AbdulKadir ya fadi a ran shi yana girgiza kai, bandaki ya wuce ya watsa ruwa. A rayuwar shi baya hada wani da wani, hakan na cikin abinda bayaso sam, ko fada Hajja take mishi ran shi yana baci yaji tana kwatanta shi da wani. A wajen shi Allah ya halicci mutane daban-daban mabanbanta halaye da ra’ayoyi, har kamanni ma, wanda Allah ya halitta yan biyu sukazo da kamanni daya, suka kwanta a ciki daya ma saika sami halayensu daban. 3

Sai gashi yanzun daya fito ya tsinci kan shi da hada halin Nuriyya da na Waheedah a waje daya yana aunawa, Waheedah ba zata taba bacci tabarshi ba, ko da shi ya bata mata rai, a yanda zata dinga kallon shi da idanuwanta kawai zaka gane babu nutsuwa a tattare da ita.

STORY CONTINUES BELOW


‘Na baka hakuri fa Sadauki, kai mun magana dan Allah, wallahi a takure nake jina, ni banason yin fada da kai’

Kalamanta suka dawo mishi

‘Hamma har yanzu fushi kake mun? Babba da hakuri aka san shi’ 1

Takance, duk idan tayi amfani da Hamma to ya kwana yana mata fushi, ko tana son tambayar shi unguwa, zatace shifa Yayanta ne. Murmushi yaji ya kwace mishi, kafin kirjin shi ya sake amsawa kamar zai bude, har zazzabin rashinta a kusa dashi yake ji. Sai da ya sake komawa bangarenta ya sakko gajeran wando da singlet tukunna ya dawo dakin Nuriyya din, baccin da take zai hana mata, tunda shi ya kasa, kuma bayajin tunanin Waheedah zai barshi ya samu. 1

*

Da safe dakyar Nuriyya ta tashi sallar asuba, tana ta turo baki saboda baccin dake idanuwanta, bata kwanta da wuri ba, idan tace dan bai dawo bane karya take, kallo takeyi a system dinta suka dauke wuta, bata tuna dashi ba sai da chargyn system din ya kare, kudine ta riga ta kashe, fada ne zaiyi ya gama. Ita ko kadan batama hango zai mata fada akan dubu arba’in ba, yanda take ganin kudin shi, yafi karfin dubu arba’in, idan nashi ran ya baci itama natan a bace yake.

Data kirama yace tayi bacci tana kashe wayar guntun tsaki taja ta ajiye ta kwanta, daman ko baice ba baccinta zatayi. Dan tunda harya dawo daga ko ina Major ya kaishi bai mata fada ba wani abu ya nutsu a ranta. Batajin akwai wani babban abu da zatayi mishi kuma da zai kai wannan, iya kacin shi fada, duk da fadan na tsaya mata a rai, in yayi yagama shikenan. Ta kula bashida riko, da wahala ya kwana yana fushi kan abu daya. Tana idar da sallah ta janyo wayarta, chajin taga saura goma, dan ta manta ta saka sanda aka kawo wuta. Haka kawai tunanin azumi da saura kwana biyu ya diro mata, wayar AbdulKadir din da take kan drawer din gado ta janyo, ta saka sunan Waheedah a cike taga bai bude ba.

Tasan dai duk password din shi baya wuce sunanta, dan waccen wayar daya sake haka password din yake, har wani daci-daci take ji duk idan ta dauki wayar shi, shisa yanzun taji zuciyarta tayi wani tsalle da tunanin ko sunanta ya saka, jikinta har bari yake lokacin da ta saka sunanta, sai taga wayar bata bude ba, kamar daga sama taji sallamar shi yana dorawa da

“Me kike mun da waya?”

A dan tsorace ta daga kai tana sauke idanuwanta cikin nashi daya kankance mata

“Bakomai, zan duba abune, nama kasa budewa kuma”

Gira daya AbdulKadir ya daga mata dan baiga abinda ta ajiye a wayar shi da zata duba ba, hakan ta kula dashi yasa ta dora da fadin

“Hotuna zan kalla fa, wayata babu chaji, ban saka ba na manta”

Karasawa AbdulKadir yayi yana hawa gadon

“Ko gaisheni bakiyi ba kike son cinyemun chajin waya”

Murmushi Nuriyya tayi mishi tana matsawa sosai ta kama hannun shi

“Ina kwana”

Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi

“Waheena” 8

Ya fadi yana zare hannun shi daga cikin nata yaja kafafuwan shi ya hau dasu kan gadon, cike da rashin fahimta

“Password din”

Ya fadi yana kwanciya ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya tabi shi da kallo yanda yake shirin komawa bacci kamar bai fada mata abinda taji dacin shi ya taso daga kasan zuciyarta zuwa makoshinta ba. Har wani hucin bacin rai takeji kamar kububuwa, AbdulKadir kuwa baccin shi ya koma, yana barin Nuriyya nan zaune ranta in yai dubu a bace yake. Dan kamar ba zata bude wayar ba, kafin ta yanke hukuncin Waheedah ba zata hanata latsa wayar AbdulKadir din ba, tunda yanda takejin mijinta ne itama haka takeji. Kuma tana so ta shiga messages din shi harna whatsapp taga ko yaushe Waheedah zata dawo. 3

STORY CONTINUES BELOW


Wani malolon takaici ya sake taso mata, ganin saita kara saka wani password din tukunna zata iya gani, gashi lambobine wannan karin, hakura tayi tana shiga wajen kira taga ko yayi magana da Waheedah.

‘Matar Sadauki’

Sunan farko data fara cin karo dashi a jerin wajen kiran wayar AbdulKadir yaso wanke mata bacin ran da takeji, kafin ta kula da kiran fita yayi ba shigowa ba, tana kuma ganin

‘Nuri’

Daga kasa, wannan karin wani irin tsakine ya kwace mata, fita tayi tana kara kula da wallpaper din AbdulKadir din, hoton Fajr ne daya sata jin son samun nata yaron taso mata yana zuwa mata wuya, ba sosai takanyi tunanin samun ciki ba, amman duk idan taga giccin Fajr tanajin kamar ace yaron nata ne. Kulle wayar tayi zata ajiye taga hoton dake fitowa idan an kulle waya kunshine, daga yatsun ta gane hannun Waheedah ne. A gefen AbdulKadir ta ajiye wayar tana addu’ar ya mirgino ya dora mata nauyi screen din ya samu matsala ko zai rage mata takaicin da take ciki. 9

Mikewa tayi ta cire hijabinta, kan gadon tahau daga can karshe ta kwanta, banda tafasa babu abinda ranta yake, kafin ta matso tana kwanciya jikin AbdulKadir din da Waheedah takeyi kamar nata ne ita kadai, sai dai duk yanda bacci bai wadaceta ba, ta kasa samun shi, data rufe ido hoton hannun Waheedah ke mata yawo da sunanta da take da tabbacin ita tayi saving din lamba dinta a haka a wayar AbdulKadir din, saboda rashin aji, ita ba zatai haka ba da ta dauki wayar AbdulKadir din tana sake nata sunan zuwa

‘Matar Masoyi’ 20

Da tunani barkatai a ranta, dukkan su suna hadewa sukai mata wani irin zafi lokaci yake ta tafiya, wutar da aka kawo yasata sakkowa daga kan gadon. Chaji ta fara sakawa tukunna ta shiga wanka ta fito, gaban mudubi ta zauna ta tsara kwalliya sosai a fuskarta, bum short ta saka da wata karamar riga, tana samun hula ta saka a kanta. Tayi kyau das da ita, yunwa ta fara addabarta, kitchen ta wuce ta dafa ruwan zafi a kettle tana hada shayi mai kaurin gaske ta duba biscuit ta dauko, shima ya kusan kare mata, gashi babu wasu kudi a hannunta, zatai ma AbdulKadir maganar kudi idan an kwana biyu, tasan bazai hanata ba. A kitchen din ta tsaya ta fara shan shayin dan yunwa take ji sosai. 1

Takun tafiyar AbdulKadir din taji, kafin ya rungumeta ta baya

“Yunwa nakeji Nuriyya”

Yatsine fuska tayi dan tasan baya ganinta, muryarta ciki-ciki tace

“Me zan baka Masoyi? Nima yunwar ce ta tasheni… In hada maka shayi?”

Sake matseta AbdulKadir yayi yana sauke numfashi

“Shayi da me?”

Ya tambaya

“Da biscuit” 1

Nuriyya ta amsa, tana sa AbdulKadir din sakinta ya kama hannunta yana juyo da ita, ta mishi wani irin kyau mai ban mamaki 1

“Ni zaki ba shayi da biscuit Nuriyya? Na miki kama da Fajr” 1

Shagwabe fuska tayi

“Bansan me zan baka ba wallahi, me kake son ci?”

Kafadu AbdulKadir yadan daga mata, shima baisani ba, Waheedah bata tambayar shi abinda zaici, bashi kawai takeyi

“Ni dai bazan ci biscuit ba, bari inyi wanka. Kimun koma menene”

Ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga kitchen din, kamar hakan Nuriyya take jira tayi wani irin juyi tana buga kafarta a kasa, ko kadan wannan wahalar ce ba zata iya ba sam, a gidansu ma ba girki take ba, can da babu kudi, gidan Anas ma sai ranar da tayi ra’ayi tunda in bai bata kudi ba, inya ajiye dauka take, duk bala’in da zasuyi, ko kudin waye. Daya daina ajiyewa kayan abincin shi take diba ta siyar, akwai gidajen da ake abincin siyarwa kala-kala a unguwar, wani lokacin ma danyen take kai musu, sai a dinga aiko mata dafaffe har kudinta ya kare. Ranta a bala’in bace ta karasa shanye shayin nata, kitchen din Waheedah ta wuce tana dauko duka kwalin indomie din da ko rabi ba’ayi amfani dashi ba. 7

STORY CONTINUES BELOW


Batasan abinda zata dafa mishi ba banda indomie din, in zaici yaci, in ba zaici ba kam batasan ya zatayi dashi ba ita. Wannan wahalar ko kadan jikinta ba zai dauka ba, tasan Waheedah zata dawo babu dadewa, tunda mayyar AbdulKadir din ce bata iya nisa dashi. Tana ta kwashema Waheedah albarka a ranta tana dora indomie din, ta duba, albasa ma bata da ita sai da ta sake komawa kitchen din Waheedah ta dauko ta dawo. Lokacin da AbdulKadir ya fito harta karasa ta kashe gas din, ta samu plate tana juye mishi ta saka cokali mai yan yatsu a ciki. Ta dauka zaiyi magana, baice komai ba ya saka cokalin ya fara ci, kitchen ta koma dan tayi wanke-wanke, a kasan ranta takejin yanda harta fara gajiya da zaman gidan. 14

*

Mami da kanta tace mata takoma gidan Yassar ta huta abinta, babu wanda zai dameta a can din, dan tunda yan gidan suka ga tana nan sai hirar ta dawo bangaren Mamin. Ita kanta Waheedah din tana bukatar shirun, tasan in tana nan gidan ba zata same shi ba, duk da sosai taji nauyin da kirjinta yayi ya mata sauki, musamman da aka hadu anata hira, sun rage mata kadaicin data jima tana fama dashi. Sun kuma rage mata zafin zuciyar da take tare dashi, sai gab da Magriba Yassar yazo ya dauketa daya dawo daga wajen aiki ya biyo.

Fajr ma bata ganshi ba, bata kuma bi ta kanshi ba, tunda ba bakon waje yake ba, ballantana yana wajen Hajja inda babu wanda ya isa ko murya ya daga mishi ai bazai nemeta ba. Da suka koma tadan samu taci abinci dakinta ta koma, tana sallar isha’i ta haye gado taci gaba da kallon film din daya rage mata tunani ba kadan ba. Har saida taji dakyar take bude idanuwanta sannan ta hakura ta kwanta. Badan taji kiran sallah ba, kawai sabo da tashin asuba dinne yasa tun kafin lokacinta ya karasa harta tashi. Tana gabatar da sallah Ikram ta dauka tabata tasha sukayi kwanciyarsu suna komawa bacci.

Sanda ta tashi goma tayi, wanka ta shiga, ta fito ta dauki Ikram dan tayi mata itama, da kuka aka gama wankan, daman in dai kana son jin kukanta to wanka ko yunwa, kafin wani lokaci harta shirya kanta cikin riga da zani na atamfa da dinkin ya zauna mata sosai, kwalliya tayi tana saka jambaki a labbanta, Ikram ta shirya tsaf tana kallon yanda kamanninta da AbdulKadir suke kara fitowa

“Ikram ki rufamun asiri mana, dan Allah banda idanuwan” 25

Waheedah ta fadi tana gyarama Ikram din riga da ta dauka wasa take mata ta dashe mata baki tana dariya, itama dariyar ta tsinci kanta dayi

“Dariya kike ko? Da gaske banda idanuwan…”

Waheedah take fadi tana jijjiga Ikram dake dariya sosai

“Kuma karkiyi irin rigimar shi, macece ke wahala zaki sha”

AbdulKadir da tun daga bakin kofa yakejin dariyar su, hakan yasa shi murza hannun kofar yana shigowa ya tsaya yana kare musu kallo da murmushin daya manta rabon da yayi shi a fuskar shi yace

“Ki daina hure ma yarinyata kunne…Fajr da ya biyo rigimarki me nace?”

Juyawa Waheedah tayi fuskarta dauke da mamakin ganin AbdulKadir din, duk da ya saba shigowa waje bataji shi ba sai dai ta ganshi, kare mishi kallo tayi ya saka gajeran wando iya gwiwarshi na sojoji sai farar riga a jikin shi, kamshin turarukanta yakeyi. Fuskar shi har lokacin da kumburi, kare mishi kallo tayi kafin ta dauke idanuwanta daga kan shi tana janye Ikram ta matsar da ita tsakiyar gadon ita tana zama a bakin gadon, ta dora hannuwan ta daga gefe da gefe. A hankali AbdulKadir yake takawa zuwa inda take, tsintar kan shi yayi da tsugunnawa saboda Waheedah ta sunkuyar da kanta. 5

Hannun shi yakai yana dago da habarta, agogon dake daure da hannun shi tabi da kallo, shine kyauta ta farko data shiga tsakaninta da shi, duk tarin agogunan shi, wannan din shi yafi daurawa fiye da ko yaushe, lokutta da yawa wanka da alwala duk dashi yakeyi, fatar duk ta koke, in tai mishi magana sai yace agogon na da muhimmanci a wajen shi, har wani ta siya mishi, amman dai yafi son wannan din. Bama aiki yake ba, batasan me yasa yake yawo da shi ba. AbdulKadir idanuwanta yake son gani, so yake yaga ko da giccin tarin soyayyar da take mishi ne.

STORY CONTINUES BELOW


“Wahee…”

Ya kira yana wani irin sauke murya cikin yanayin da baisan zuciyar shi zata taba iya jin shi ba balle ta fito dashi, idanuwan nata kuwa ta saka cikin na shi, maganganun Mami na dawo mata suna saka wani abu da batasan yana kulle a kirjinta ba budewa. Komai takeji yana dawo mata kamar a lokacin yake faruwa, tana jin wasu irin hawaye da suke fitowa daga wani waje a zuciyarta daya jima yana ciwo kafin su fara zuba kamar an bude su, dumin su ya fara ji a jikin hannun shi da yake kan habarta kafin ta sake sunkuyar da kanta. Da sauri AbdulKadir ya tashi ya zauna gefenta yana kama hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi

“Waheedah…”

Ya kira yanajin yanda kukanta ya karasa birkita mishi tunani, wani irin dana sani yana saukar mishi kamar ruwan sama, ba ita ba, yanajin zai jima a rayuwar shi bai dagawa wani hannu ba a yanayin da yakejin shi. Hannu yasa yana kamo fuskarta ta ture shi tana saka nata hannun ta goge hawayen da sunqi daina zubowa, hannu AbdulKadir ya sake kaiwa, kafin ya taba fuskarta ta sake ture shi

“Ka kyaleni….kabar ni”

Ta fadi cike da kashedin da AbdulKadir bai taba tunanin tana da zuciyar fito da shi ba, dan sanyin halinta yayi yawa, wani kuka na sake kwace mata. Gyara zaman shi yayi yana kokarin saka hannuwan shi duka biyun wannan karin, ture su ta sakeyi da dukkan karfinta tana mikewa, wani irin kallo take mishi da yasa shi jin kamar an watsa mishi ruwan kankara

“Ka kyaleni, kaje ka taba fuskar Nuriyya” 8

Da mamaki AbdulKadir yake kallonta, kafin shima ya mike yana son hade space din dake tsakanin su, baisan abinda ya kamata yace mata ba, kuma lallashinta yake sonyi, taki bari ya tabata, gabaki daya komai ya cunkushe mishi

“Dan Allah kiyi hakuri Waheedah…” 1

Ya fadi yanajin shima gab yake da nemo kuka duk inda yake, kilan in ya taga hawaye a fuskar shi sai tagane abinda nata hawayen yake mishi, takawa ya sakeyi, ta dago hannuwanta tana kokarin ture shi, kama hannuwan nata yayi yana sa karfi ya rike su

“Karyewa kike son yi shisa zaki tureni ko?” 1

Kiciniyar kwacewa takeyi zuciyarta na wata irin tafarfasa

“Nace kiyi hakuri…Dan Allah kiyi hakuri, ba zan kara ba wallahi” 2

AbdulKadir ya karasa maganar muryar shi na karyewa, har lokacin yana rike da hannuwan Waheedah da take kallon shi kamar tana shirin rufe shi da duka, ga hawayen da bayaso sunki daina zubar mata

“I’m sorry” 1

Ya fadi da harshen turanci yana dorawa da fadi cikin harshen larabci

“Ana Asif…” 2

Sosai yake kallonta, tunda yake baisan yanda hakuri yake fitowa daga zuciya ba sai yanzun da yake a gabanta, hannunta daya ya dago ya dora shi a kan kirjin shi inda zuciyar shi ke dokawa kamar zata fito waje saboda tashin hankali

“Su kadai ne yarukan da nake ganewa, idan akwai wani kalar hakurin ki fadamun….nace bazan kara ba, idan akwai abinda nayi miki banda mari ki fadamun duk sai in hada in baki hakuri” 5

AbdulKadir yake fadi yanajin a wannan gabar kome take so shidin zaiyi indai zata hakura ba zata kara furta mishi kalmar ya saukake mata auren shi ba, hannuwanta take kiciniyar kwacewa, sakar mata yayi, yana kallo tasa ka bayan hannu ta goge fuskarta da har ta kara ja saboda kukan da takeyi

“Kinga fuskar ki harta kumbura, kiyi hakuri kar kanki yayi ciwo Wahee…”

Kallon shi take, tanajin wani tuquqin kishi naban mamaki yana taso mata

“Bakayi tunanin kaina zai ciwo ba ka kara aure ban sani ba?” 3

Maganar ta dirar mishi cikin kunnuwa tana daukar wasu dakika kafin ta karasa cikin kan shi tana rarrabuwa zuwa inda zai fahimta

STORY CONTINUES BELOW


“Da kayi auren ka ban sani ba kamar na isa in hanaka, sai ka zabi ka dauki wata daya kafin ka gayamun ta text…Text”

Waheedah ta maimaita maganar cikin gunjin kukan da yaji ya samu wajen zama a zuciyar shi yana daskarar dashi tsaye a wajen, wannan karin ita ta taka tana hade space din dake tsakanin su, cikin fuska take kallon shi

“Bakayi tunanin abinda zanji ba ko Sadauki? Banda darajar da zan san ka yanke hukuncin da ba rayuwarka kawai zai canja ba harda tawa…. Bai isheka ba sai da ka sake nuna mun duk abinda zanji a kai ba matsalarka bane, ka fadamun ka kara aure ta text!” 2

Wannan karin da hargowa ta karasa maganar tana ture AbdulKadir din duk da ko motsi ya kasayi, tsaye yake kamar bishiyar da ta samu dashe mai kyau, kalamanta yake ji na saukar mishi da wani irin yanayi da bashida kalaman dora su, kuka Waheedah takeyi mai sauti, zuciyarta na ciwo kamar zata rabu da kirjinta, numfashi take ja tana fitar dashi a wahalce, sai dai kalaman takeji na tunkudedeniya da juna wajen fito mata, tagaji da rike su, tagaji da rike komai

“Da ka fadamun ta text, ko kadan hankalin ka bai baka ka fadamun kawata ka aura ba ko? Saboda kai ne, AbdulKadir da babu wanda ya isa, darajar kowa a kasan taka take shisa baka fadamun ba sai da ka dauko ta ka kawomun ita cikin gida na….Kawata Sadauki… Kawata ka aura, idan kaso ka kasheni zaka iya…”

Waheedah take fadi numfashin ta har barazanar tsayawa yake saboda kukan da take tana kuma magana a lokaci daya, amman ta kasa shiru, AbdulKadir din take turewa ko motsi ya kasayi

“Bakayi tunanin ya zanji ba ko? Shisa duk matan Kano….matan duk da suke Kano. Me yasa sai ita? Me yasa zaka sa in raba komai naka da ita?” 12

Ta karasa maganar wannan karin kamar wadda ta sami tabin hankali, jikinta ko ina bari yake da kukan da take, hannun AbdulKadir din guda daya ta kamo da duka nata biyun tana dorawa akan kirjinta

“Kaji?”

Ta tambayeshi wasu sabbin hawayen na wanke mata fuska tana sake ware hannun shi akan kirjinta inda zuciyarta ke mata ciwo kamar zata fado, wannan karin muryarta da rauni ta fito tana kuma sauka can kasa

“Tun bansan menene so ba zuciyata take doka maka, baka bani dalili ba, ban taba bukatar wani dalili na son ka ba, saboda kaunar ka bata bani wannan zabin ba, dan ban taba fada maka ba shisa bakayi tunanin ina kishin ka ba?”

Waheedah ta fadi tana sauke hannun shi daga kirjinta tana saka yatsunta cikin nashi ta dumtsa

“Duk yanda zuciyata take fadamun yanda take son ka kasance nawa ni kadai, kullum sai na fada mata kai ba nawa bane ni kadai, addini baice ka zama nawa ni kadai ba, nasani Sadauki…dan Allah me yasa ka hadani kishi da ita? Me yasa ita? Kawata ce Sadauki? Ka manta kamar Amatu nakejin Nuriyya?”

Hannun shi AbdulKadir ya zame daga cikin nata yana matsawa da baya taku biyu, kafin ya juya ya sake wani taku biyun, tsugunnawa yayi yana neman iskar da yakeji ta mishi kadan kamar mai asthma haka numfashin shi yake barazana, mikewa yayi har lokacin iska yake nema tukunna ya tantance asalin abinda yakeji, abinda kalamanta suke mishi, bin shi Waheedah tayi tana sake kamo hannun shi, tana jin dumin hawayenta wani na tunkudo wani kafin tace mishi 4

“Ina zaka je?”

Kai AbdulKadir ya girgiza mata yana son samun wadatacciyar iskar da zai iya fito da sauti kowanne irine, zuciyar shi yakeji kamar an sa hannu a kirjin shi an matse ta ana rabata da duk wani jini da yake jikinta 1

“Baka duba cewar na dauki ido na kyaleka ba, sai ka dinga zuwa mun da ita kamar kana son nuna mun kawata ce ka aura, saboda ka isa, babu kuma yanda zanyi da hakan” 3

Waheedah ta fadi da wani irin nisantaccen yanayi a fuskar ta, kai AbdulKadir ya sake girgiza mata yana so tayi shiru ko numfashin shi zai dai-daita kan shi ya rage zafin daya dauka, nata kan take girgiza mishi idanuwanta har wani yaji-yaji suke mata, tana hadawa da jijjigawa kamar yana bacci tana so ta tashe shi

“A gabana kake rike ta, tana kwanciya a jikin ka….kana so ka kasheni tana tayaka… Zuciyata na mun ciwo… Sosai zuciyata take mun ciwo… Bazan iya zama da kai ba, zaka kasheni…” 8

Cewar Waheedah, kafin a gajiye ta karasa da

“Ba soyayyar ka bace farko na, ba zata samo karshe na ba!” 11

Hannun shi daya AbdulKadir ya dago yana kama na Waheedah ya cire daga jikin dayan nashi yana dafe fuskar shi da tafukan shi, hadi da jan wani irin numfashi a wahalce, ba zai tuna ranar karshe da wani abu ya same shi yasa shi jin yana son ya ruga wajen Hajja ba sai yanzun. So yake ya ruga wajen ta kamar yaro dan shekara uku da aka kwacewa abin wasan shi, wata kila idan ya ruga Hajja ta saka hannu ta tarbe shi in zata iya ta daga shi ta rike shi a jikinta hawaye su zubar mishi ya samu saukin abinda yake ji. A filin duniya, a shekarun shi da Allah ya bashi aron su daga ranar farko zuwa yanzun da yake tsaya baiyi tunanin akwai tashin hankali kalar wanda yake ciki ba.

Tun kafin ya auri Waheedah duk idan ya kalleta akwai raunin da yake tare da ita da yake saka shi jin son yi mata rumfa ya kareta daga duk wani abu da yake a karkashin ikon iyawar shi, lokacin da igiyar aure ta daure su karkashin inuwa daya, bai fito daga masallacin da hakan ta faru ba sai da alkawurra masu tarin yawa, cikin su harda kokarin ganin wani abu bai cutar da ita ba, in har yana da ikon hakan. Sai dai a tsayin zaman su duk yanda yaso kareta daga hakan, baiyi tunanin kareta daga kan shi ba, baiyi tunanin shi zai iya cutar da ita fiye da kowa ba. Da za’a tambaye shi mutane uku da zasuyi komai saboda shi, mutane uku da zasu sadaukar da komai dan farin cikin shi, Waheedah zata zamo ta ukku bayan Hajja da Abba.

Da gaske ne ba zai ce ya bude zuciyar shi da soyayyarta ba, kafin ranar da Yassar yai mishi zancen ta, bai taba ko a mafarki hango aurenta ba. Amman tun kafin hakan ita din bangare ce ta rayuwar shi, ko da bai aureta ba yana da tabbacin labarin rayuwar shi ba zai cika batare da ta fito a shafuka da yawa ba. Daga ranar daya aure ta yasan cewa ba ita ya fara so ba, amman ita din ce duk wani abu da yake bukata. Baya tunani mai tsayi a kan kowanne bangare na rayuwar shi, shisa bai taba tunanin hukuncin daya dauka shi kadai ya shafa, shi kadai zai taba harda ita ba, kuskuren farko da yaji yayi a rayuwar shi. Yake kuma jin shi har cikin kasusuwan shi shine manta duniyar shi gauraye take da tata, manta cewar duk wani mataki da zai taka ko ya taka shi tare da Waheedah ne, abinda duk ya taba shi zai taba ta itama, kamar yanda yake jin duk abinda ya tabata shi ya taba. Shisa yanzun ciwon da takeji ya lullube shi ruf…! Tsugunnawa yayi yana fitar da numfashi a wahale, cikin shi ke ciwo saboda hanjin shi da yakeji sun tattaru sun kulle a gefe daya. Ko ina na jikin shi ciwo yake, har wajajen da bai taba sanin zasuyi mishi ciwo batare da zubar jini ba. Waheedah na tsaye tana kallon shi, yanda yakeyi kamar shi yayi watanni da ciwon da tayi fama da shi, a karo na farko halin da yake ciki bai taba zuciyarta ba, tana jin dadin yanda yake jin kadan cikin quncin da zuciyarta take fama dashi 1

“Kirjin ka kamar zai bude ko Sadauki?” 4

Ta bukata cikin wani irin sanyi murya da yasa AbdulKadir daga idanuwan shi da har sun canza launi yana kallon ta, rausayar da kai tayi

“Haka nake ji duk idan naganka tare da Nuriyya…” 6

Mikewa AbdulKadir yayi yana karasa inda Waheedah take, hannuwan shi yasa ya kama kafadunta yana dan dannawa cikin alamun ta zauna, batayi mishi musu ba tayi kasa tana zama kan kafet din dakin, shima zaman yayi a gefenta, dan dakin ya fara jujjuya mishi da jirin tashin hankali. Idan taci gaba da magana baisan inda zai saka rayuwar shi ba, ya bude bakin shi ya kai sau biyar amman ya kasa furta komai. Sai da yaja numfashi yana fitar dashi, kafin ya iya cewa

“Waheedah…”

Kalmar na fitowa daga wani sashi na zuciyar shi da yau dinne ranar farko daya san da zaman shi, runtsa idanuwan shi yayi yana bude su, cikin kan shi yake ji babu komai, baisan ko yanajin alamun kwakwalwa ba a baya, amman a yanzun bayajin komai sai kokon kan, balle yayi tunanin kwakwalwar shi zata taimaka mishi da wasu kalamai, amman kirjin shi ciwo yake kamar zai bude, da gaskiyar zancen Waheedah, bai gane yanda zai fassara abinda yakeji ba sai da ta fada, kan shi babu komai, amman zuciyar shi cike take fam da yanayoyi daban-daban, bude bakin shi yayi yana barin zuciyar shi ta mulki abin zai fito daga bakin shi

“Ina da son kai, ban taba sanin ina da son kai ba sai yau, kina da rashin adalci…” 1

AbdulKadir ya karasa maganar cikin muryar da ta dira kunnuwanshi kamar ta wanda yasha gudu, yana saka kwayar idanuwan shi cikin na Waheedah da take ware mishi nata cike da maiqon hawaye, kai ya daga mata a hankali

“Me yasa baki fadamun ba? Me yasa baki fadamun ba Wahee? Kince kina sona, ni nagani kina sona, me yasa kika boyemun?”

Kai Waheedah take girgiza mishi, idanuwan ta na tsiyayo wasu hawaye masu dumi, ba zai mata haka ba, ba zata bar shi ya dora mata laifin da bata da shi ba

“Me yasa ka boyemun za kai aure? Ka boyemun kayi aure har wata daya? Ka boyemun Kawata ka aura sai da ka shigomun da ita cikin gida?” 7

Jinjina kai AbdulKadir yayi, kalamanta duka suna dirar mishi kamar zubar ruwan gishiri a sabbin ciwukan da kalamanta na baya sukai mishi, yasan tana da muhimmancin a rayuwar shi fiye da yanda zai misalta da kalamai, bai dai san a tattare da muhimmanci akwai iko akan abubuwa da yawa da suka shafe shi ba, ciki harda zaman lafiyar shi, kwanciyar hankalin shi, nutsuwar shi gabaki dayan ta

“Hakane…”

AbdulKadir ya iya furtawa yana kallonta da wani nisantaccen yanayi, muryar shi yakeji na fitowa da wani sauti da baida fasali

“Ba uzurin da ya sani yin abinda nayi nake so in baki a kurarren lokaci irin yanzun ba…”

Ya fadi yana maida numfashi kafin yace

“Banda komai, ko kalaman ban hakuri bani dasu, wallahi banda kalaman baki hakuri” 1

Dan har zuciyar shi yakejin hakuri yayi kadan ya wanke girman laifin da yayi mata

“Shisa zan baki wani abu daban, zan baki dukkan gaskiyata, ban san zanyi aure ba, lokaci daya tunanin ya zo mun…”

Kai Waheedah take girgiza mishi, bata son ji, bata son jin yanda yayi aure, tunda ya rigada yayi, shima kan yake girgiza mata

STORY CONTINUES BELOW


“Za kijini, ba zaki yanke mun hukunci gabaki daya ba, kimun adalcin da ban miki ba dan Allah, na rokeki”

Cikin rawar murya data fito cike da sautin kuka Waheedah take girgiza mishi kai

“Son kai Sadauki, son kai ne wannan”

Kafada yadan daga mata, ita hawayenta sun zuba, ance kana samun sauki duk idan ka zubar da su, shi bai samu wannan zabin ba

“Nasani, halina ne daman…”

Cewar AbdulKadir din yana dorawa da

“Da sanin zanyi auren da auren duka a kwana biyu ya faru, na samu awanni 48 da zan dauki mintina talatin in fada miki zanyi auren, banyi ba, kuskurena ne wannan da zai zauna dani har karshen rayuwata…”

Hannunta ya kamo yana hada yatsunsu waje daya, yanajin yanda ta dumtse nashi cike da neman alfarmar da ba zai iya mata ba, idan bai fada mata na shi bangaren ba, yana da tabbacin kirjin shi budewa zaiyi

“Amman ni ne, bana tunani, ban fara tunani ba sai bayan nayi auren, na kasa fada miki, banji maganar su Hajja da suka fadamun akwai rashin kyautawa a abinda nayi ba saboda ina ganin addini ya halarta mun, banyi tunanin ke yanda zakiji ba har lokacin, nayi tunanin ban kyauta ba da ban fada miki ba, kin san me yasa?”

Kai ta girgiza mishi a hankali, akwai yanayin da yake tattare da muryar shi da bai hana gwiwoyinta yin sanyi ba duk da a zaune take

“Saboda ban saba boye miki abu ba, lokacin ya kamata in san ban kyauta ba…”

Wannan karin ajiyar zuciya mai nauyin gaske ya sauke

“Ina miki maganar Nuriyya ne saboda kece, badan na raina ki ba Wahee, ba dan in nuna miki na isa ba, Wallahi babu ko daya a ciki, ki yarda dani…”

Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, kafin ya ci gaba da fadin

“Ina fada miki ne saboda ke ce”

Ya sake maimaitawa kamar ‘Ke ce’ din ta isa ta fassara mata abinda yake nufi, shi kuma kalaman da zaiyi amfani dasu dan ta fahimta yake nema

“Tun ban san zan aureki ba kike sanin abubuwa a kaina da ba kowa ne yake sani ba, saboda ke ce, ke kadai kikejin maganata idan raina yana bace, saboda ke ce, su Hajja na so na, amman basa son da yawa cikin halayena, suna magana a kai, baki taba ba, kina so na da komai nawa, shisa nabari kika sanni yanda kowa bai sanni ba” 2

Idanuwanta Waheedah ta runtsa tana kokarin hadiye yawu ko zai wuce mata da abinda take jin ya tsaya mata a kirji, shagwabe mata fuska AbdulKadir yayi cikin yanayin da bata taba gani ba, sai da taji zuciyarta ta doka da tunanin ko kuka zaiyi

“Ban miki maganarta dan in sosa ranki ba, na miki maganarta saboda komai nawa ina fada miki, banyi tunanin kishin da zakiji ba, saboda ina son kai na da yawa, wannan ma kuskurena ne… Auren kawar ki” 1

AbdulKadir ya karashe maganar yana runtsa ido kamar kalaman nashi sun raunani shi, kafin ya bude su yana ci gaba da fadin

“Wahee ina so ince ki yafe mun, amman ina jin hakan ma zai kara zama rashin adalci…”

Kai ta daga mishi tana tabbatar mishi da ta yarda da kalaman shi, hawayen da suka zubo mata na kara tafasa shi, numfashi ya sauke yana dago hannun su da yake hade yakai kan goshin shi, ya lumshe idanuwan shi yana kara sauke numfashi mai nauyi, duniyar ta mishi tsaye waje daya, yakai mintina biyu a haka, kafin ya iya dago da kan shi

“Son kai halina ne, shisa zan fada miki ba zan iya rabuwa da ke ba….Wallahi ba zan iya ba, da tunanin aikina zaiyi sanadiyyar mutuwata nake kwana nake tashi kullum, cikin sati daya kin nuna mun kinfi aikina wannan hadarin, Wahee zaki kasheni in kika barni….” 6

STORY CONTINUES BELOW


AbdulKadir yake fadi a susuce, babu komai cikin kan shi har lokacin, ba lallai bane kalaman da yake fadi suna da wata ma’ana tunda bayajin taimakon kwakwalwar shi a fitarsu, zuciyar shi ce kawai take haukanta

“Idan lokaci kike bukata zan baki… Komin tsayin lokacin da kike so ki huce zan baki…” 1

Kallon shi Waheedah take tana girgiza mishi kai cikin rashin yarda da cewar zai bata duk lokacin da take so, shi kuma yana fahimtar hakan da cewa tana nufin bata yarda ba, ya saukake mata auren shi, hakan yasa shi kara rikicewa da fadin

“Ba zan dinga zuwa ba, ba zan dame ki ba, duk lokacin da kike bukata…”

Dayan hannunta tasa tana goge fuskarta, taja hancinta da takeji yana mata radadi kamar ta shaqi barkono

“Shekara daya…”

Ta furta cikin dakusasshiyar murya, wannan karin dokawar da yaji zuciyar shi tayi da a kasar wajene ya tabbatar likitoci zasuji mishi tsoro bugun zuciya na farat daya

“Shekara biyu”

Waheedah ta sake fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarta

“Uku… Hudu… Biyar….”

Taci gaba, ba iska kadai yakeji ta mishi kadan ba, hasken dakin yaga yana raguwa, ga zuciyar shi da take cigaba da dokawa tana mishi barazanar tsayawa, hannun Waheedah ya saki yana dafa gadon dake kusa da shi ya mike dakyar. Batace mishi komai ba, asalima da idanuwa take bin shi harya fice daga dakin, baiko ja mata kofar ba, bai taba ganin nisan daga cikin gidan Yassar ba zuwa harabar gidan inda ya ajiye motar shi. Wannan tashin hankalin bakon abune a wajen shi, kamar yanda tunanin da yai mishi daurin goro yake bako a wajen shi. 1

Dakyar yakai wajen motar shi, dishi-dishi yake gani lokacin daya bude ya shiga, bakomai na cikin tuqi yake iya tunawa ba, ya taka motar ne ta baya ya fita daga gidan, yana jin yanda ya daki gefen gate din dako gama budewa maigadin baiyi ba, haka yahau titi yana nufar hanyar gida, a ran shi yake karanto duk wani sunan Allah da yazo mishi, cike da yabo saboda yanda yake jinjina ikon Allah, yasan ba hankalin shi ya kai shi gida ba.

Lokacin da yayi parking din motar cikin gidan lumshe idanuwan shi yayi yana girgiza kan shi, ya sake bude su yana ganin duhun da yake son lullube mishi su ruf, dakyar ya fito daga cikin motar yana wani irin mayar da numfashi. Dishi-dishi yake gani duk yanda yake kara ware idanuwan shi, ga jiri da yakeji yana dibar shi. Ganin kamar Khalid yake hangowa yasaka shi kara ware idanuwan shi sosai, amman sai yake ganin Khalid din na rabe mishi gida wajen hudu. Da hannu yai ma yaron alama da yazo, yana sake runtsa idanuwan shi, can sama-sama yaji muryar Khalid din na fadin

“Hamma…Hamma lafiyar ka kuwa?”

Ko kai AbdulKadir ya kasa girgiza mishi, dan iskar wajen ta sake mishi kadan, Khalid kuwa a karo na farko da ya kai hannu yana kama na AbdulKadir din da tsoro daban, dan yanda yakeyi kokawa da numfashin shi kamar mai asthma

“Hamma…”

Khalid ya kira cike da tsoro, kafin AbdulKadir din ya lumshe idanuwan shi yana wata irin faduwa da ta saka Khalid sakin wani ihu daya fito daga kirjin shi da yake cike fal da tsoro

“Hamma AbdulKadir!”

Yake fadi yana tsugunnawa hadi da girgiza AbdulKadir din da baisan a wacce duniya yake ba, da gudu Khalid ya tashi yana nufar bangaren Mami da shine yafi kusa dashi, a falo yake kiran

“Mami, Hamma…. Hamma Mami”

Cikin tashin hankali Mami ta kama Khalid din, zatace a yaran gidan yana daga cikin wanda basu da hayaniya, baya shiga harkar kowa, daga gaisuwa sai kayi da gaske zaka sake jin maganar shi, duk cikin yaran Mama yafi kowa fita daban, bata taba ganin shi a hargitse ba, shisa lokaci daya hankalin ta ya tashi

STORY CONTINUES BELOW


“Wanne Hamman? Me ya faru Khalid?”

Ya kasa magana, da hannu kawai yake nuna mata alamar waje, bin bayan shi kawai tayi, daga nesa ta hango AbdulKadir din, da gudu ta karasa, cikin bayanannen tashin hankali tace

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…. AbdulKadir… Khalid kira Hajiya Safiyya…”

Juyawa yaran yayi zuwa bangaren Hajja da ko mintina biyu ba’a cika ba ta karaso wajen tana tsugunnawa ta kama AbdulKadir din ta dago shi jikinta tana kasa yarda yaronta ne a kwance kamar gawa

“AbdulKadir…”

Ta kira tana dora hannunta a kan kirjin shi, bugun zuciyarshi shi a cikin tafin hannunta na nutsar da wasu bangarori a tare da ita da batasan a tashe suke ba sai lokacin, wani irin numfashi take saukewa, Mami da take tsaye cikin tashin hankali itama tace

“Mu tafi asibiti…”

Kai Hajja take girgiza mata, su biyun duka tana da tabbacin ba zasu iya daga AbdulKadir din ba, balle su saka shi a mota

“Ki kiramun Yassar”

Hajja ta fadi, badan babu wasu manyan yaran gidan da in aka kirasu zasu zo ba, sai dai duk wani abu da ya shafi AbdulKadir din Yassar ne yake fara sani, wani lokaci yana ma rigan su sani, kuma shine mutum na farko da ya fara zuwa ma Hajja a kai. Har Mami tabar wajen ta kuma sake dawowa Hajja na zaune rike da AbdulKadir, zata kirga lokuttan da taga bashida lafiya a tsayin rayuwar shi, rashin lafiya dai wadda zata kwantar dashi. Shisa yanzun bata ma san asalin abinda take ji ba, lokacin take gani baya mata sauri duk da ba agogo bane a gabanta, sai taga kamar tayi awanni zaune a wajen kafin motar Yassar ta shigo cikin gidan.

Ko kasheta baiyi ba ya fito, kallo daya za kai mishi kasan a hargitse yake, baiko bi ta kan su Hajja ba ya tsugunna yana dago AbdulKadir din hadi da girgiza shi

“AbdulKadir ba za kai mun haka ba fa”

Yassar yake fadi muryar shi dauke da wani yanayi na karaya da tsantsar tashin hankali, baya tunanin ko su Hajja suna shiga tashin hankalin da yake shiga duk lokacin da aikin AbdulKadir zai kai shi wani waje mai hatsari, yana da Yasir, amman a duniya ji yake idan ya rasa AbdulKadir yayi rashin da har nashi numfashin ya tsaya ba zai taba komawa dai-dai ba. Su Hajja nada wasu yaran, shi kam ji yake bashi da wani dan uwan, shisa yanzun ma yake da tabbacin basa cikin tashin hankalin da yake ciki. A kafadar shi ya saka AbdulKadir din yana mikewa da shi, bayan motar shi ya bude ya saka shi a ciki, ya rufe murfin. 2

Harya zagaya bangaren direba ya shiga yana jin nauyin AbdulKadir din a tare dashi, baibi ta kansu Hajja ba, baima kula da ta shigo motar ba, ja kawai yayi yana nufar hanyar da zata kaishi wani asibitin kudi da yake yan albasa na rijiyar lemo, dan abokin shi yana aiki a wajen shisa har yasan da asibitin, tunda a cikin lungu yake. Gudu yake yanajin kamar yabi takan motocin da suke gaban shi saboda saurin da yakeyi, a haka suka karasa asibitin, a kafadar shi ya sake daukar AbdulKadir yana shiga asibitin da gudu, wasu nurses na hango su suka taho dan su taimaka musu, ko ba mata bane Yassar bayajin zai mika musu AbdulKadir, wani daki suka nuna mishi, ya nufa da AbdulKadir ya shimfide shi kan gadon dakin, ana kiran likitan daya shigo a rikice shima. 1

Ya gane Yassar din, dan yana zuwa wajen Dr Isa sosai

“Kadan fita…”

Yace mishi, yanda Yassar ya daga ido ya kalle shi cikin yanayin dake fassara ‘Wasa kake amman ko?’ yasa likitan mayar da hankalin shi kan AbdulKadir da ko motsi bayayi har lokacin, bugun zuciyar AbdulKadir din na tabbatar mishi da a sume yake. Duk wata allura da akai mishi da ruwan da suka daura mishi a kan idon Yassar akayi shi. Da suka gama ma, baibi ta kan su ba, likitan ma da yayi mishi magana yaga alamar hankalin shi ba’a kan su yake ba, shisa ya fita yana samun Hajja dake tsaye bakin kofar, ko takalma babu a kafarta, Hijab din jikinta ma sallar azahar zatayi da a haka zata fito, ita sukai ma tambayoyin da suke bukata wajen bude ma AbdulKadir din kati, lokacin Dr Isa ya fito wajen, Dr Aminu na kallon shi da fadin

STORY CONTINUES BELOW


“Mahaifiyar Yassar ce abokin ka, sun kawo marar lafiya ne”

Gaishe da Hajja, Dr Isa yayi yana mata kallon sani daman tunda ya zo wajen, amman shi yasan ba Mama bace ba, sai dai ko cikin matan Baban Yassar din. Mai jiki yake tambayarta, yana cewa taje kawai zai karasa sauran, har kudin bude katin shi ya biya. Tukunna ya karasa dakin da AbdulKadir din yake suna gaisawa da Yassar daya dora da

“Me ya same shi wai?”

Dan sai lokacin yaji ya samu natsuwar bukatar hakan, Hajja likitan yadan kalla da take zaune kan farar kujerar roba, tana share kwallar da taji ta tarar mata a gefen idanuwanta

“Kayi mun magana Isa, dole zata sani tunda Maman shi ce”

Kai Dr Isa ya jinjina dan yayi magana da Dr Aminu shisa yace

“Jinin shine ya hau sosai, Allah ya rufa asiri daya samu matsala, dan Allah a gujema daga mishi hankali. Idan ya kara faduwa haka zai iya samun matsala sosai…” 1

Wani abu Yassar yaji ya kulle a cikin shi

“Hawan jini?”

Ya maimaita cike da shakku a muryar shi, yana ganin kai da Dr Isa ya daga mishi

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…oh Allah na”

Cewar Yassar da yakejin wata sabuwar damuwa ta lullube shi, ganin halin daya shiga yasa Dr Isa yi mishi sallama hadi da yiwa AbdulKadir din fatan samun sauki. Yassar din idanuwan shi ya tsayar kan AbdulKadir da sai lokacin ya motsa yana saka Hajja fadin

“AbdulKadir…”

Fuskar shi ya dakuna batare daya bude ido ba yace

“Wahee…”

Kunne daga Hajja har Yassar din suka kasa, can kasan makoshi AbdulKadir yake ci gaba da sambatun da baisan yanayi bama

“Waheedah kiyi hakuri… Bazan iya ba, Wallahi ba zan iya ba”

Numfashi Hajja ta ja tana fitar dashi, idanuwanta na cikowa da hawayen tausayin dan nata, sosai maza suke tunanin suna da iko akan mace, saboda musulunci da al’ada sun saka matan a karkashin su, sai dai yawa cikin mazan sun ma abin juyayyar fahimta, musulunci bai saka mace a kasan namiji saboda ta kasance mai rauni ba kawai, sai dan wani karfin zuciya da Allah ya dasa mata da bakowane yake fahimta ba, mace na da juriyar daukar laulayin ciki da yafi kowanne yanayi wuyar sha’ani, tana da juriyar naquda da duk wani kashi da yake bayanta sai ya motsa, a lokaci daya kuma tana da juriyar daukar hakuri da kaddarar wahalar da namiji. 4

Mace zata iya hakurin shekaru da bakin cikin da namiji ba lallai ko a fuskarta a fahimci hakan ba, amman rana daya zata ware ta kwatanta rama kadan cikin wulakancin, harshen da namiji sai yayi tashin da duk wani makusancin shi zai fahimci yana cikin yanayin damuwa, karshe sai yaba mutane tausayi saboda ya kasa jurewa har a juyar da al’amarin ana ganin ita macen tayi hakuri, cikin masu mata rashin adalcin harda yan uwanta mata, su da ya kamata su fahimci halin da take ciki fiye da kowa. Shisa Hajja take ganin a duniya babu babban munafuncin da mata suke yaudarar kan su da shi sai fadin 2

‘Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne’ 6

Dan yanzun da take zaune a gaban AbdulKadir take kara karyata zancen, badan bataji zafin abinda yaiwa Waheedah ba, ta kwatanta kanta da Waheedah ta kuma san ko kusa ba zata dauki abinda Waheedah ta dauka ba, idan bata mutu ba, auren nata zai mutu. Har kasan ranta kuma take jin da Waheedah din Zahra ce da wahalar gaske idan bataje ta dauko ‘yarta ba. Amman ba Zahra bace, Waheedah ce, kuma a wannan gabar danta take ji fiye da ita, ciwon ‘ya mace kan zama na ‘ya mace ne kawai idan akwai samun riba a cikin al’amarin, shisa munafunci ne kawai a fadin hakan. 1

Waheedah take so tayi hakuri ta yafe ma AbdulKadir, dan kuwa ba zata jure ganin danta a cikin wannan halin ba, hakan yasa ta fadin 1

“Yassar zaka dan zauna da shi inje in dawo?”

STORY CONTINUES BELOW


Kai Yassar ya jinjina mata, ya sanar a wajen aikin shi, babu inda zai iya zuwa in ba gani yayi AbdulKadir din yaji sauki ba. Tun farko abinda yake mishi gudu kenan, amman AbdulKadir bayajin magana, taurin kan shi sai Allah, abinda zuciyar shi ta gaya mishi dai-dai ne shi yake aikatawa, bai taba zaton zai kwatanta ba Waheedah hakuri ba sai yanzun, yana kuma jin son kai da rashin son gaskiyar da yake cikin hakan, bai damu bane kawai. 1

“Kabani mukullin motar ka”

Babu musu Yassar ya dauka ya mika mata, karba Hajja tayi tana mikewa. Yassar yabita da kallo ganin babu takalma a kafarta, baice komai ba, ya koma inda ta tashi yana zama ya saka idanuwan shi a kan AbdulKadir da duk motsin da zaiyi sunan Waheedah ne a bakin shi, Yassar na jinjina ma kaddarar su, ya dauka yasan zafin so a kan Hauwa, yanzun AbdulKadir da Waheedah ke nuna mishi bakomai suka sani ba a soyayya, dan tasu kalarta daban ce. 3

*

Rabonta da gidan Yassar tun lokacin da matar shi tayi bari, da yake yarinyar ta sha wahala sosai. Bata kuma zata zatazo gidan batare da wani dalili da zai kasance ya shafi Yassar din ko Hauwa ba, bata taba tunanin dalilin AbdulKadir zaisa tazo gidan Yassar din ba, a kofar gida tayi parking din motar, tunda tasan inta gama abinda takeyi sake fita zatayi, bataga wahalar saita shigo da motar ba. Tsakuwoyin da ta taka na tuna mata cewar babu takalma a kafarta, haka ta shiga cikin gidan, maigadin kan shi kallon ta yake dan yana da tabbacin ba lafiya ba.

Har cikin gidan ta shiga, taci karo da Waheedah da take fita daga kitchen din, itama Ikram zata wankema jiki ta sake mata pampers taji ruwan da sanyi, tausayi yarinyar ta bata shisa ta dafa, tana sake mata kuma bacci ta koma, shine ta fito ta kawo kettle din taci karo da Hajja, sai da zuciyarta ta doka, musamman yanayin Hajja din

“Hajja…”

Waheedah ta kira cike da shakku da alamar tambaya, inda take Hajja ta karasa

“Alfarma na zo roka Waheedah”

Hawaye Waheedah taji sun cika mata idanuwan da suke a kumbure suna zubowa a hankali

“Nasan zaki ce na so kai na, zaki ce na duba bukatar ‘dana sama da taki, amman banda wani zabi… Wallahi yanzun ma yana asibiti, faduwa yayi Waheedah”

Hajja ta karasa maganar muryarta na karyewa, wasu hawayen Waheedah taji sun kara zubo mata, muryarta a sarqe cike da kuka tace

“Hajja nima naje asibitin gado zasu bani”

Kai Hajja ta jinjina mata

“Nasani, kiyi hakuri, dan Allah kiyi hakuri, ki duba yanda ya koma cikin sati daya… Kina tunanin zai iya rabuwa dake? Bakomai yake raunana AbdulKadir ba, banma taba ganin abinda ya saka shi shiga yanayi haka ba… Shisa na zo in baki hakuri, koma menene yai miki dan Allah kiyi hakuri”

Hannu Waheedah tasa tana goge fuskarta, amman wasu hawayen ke zuba, itakam hakurin ne bataso su bata, saboda zuciyarta harta fara karyewa, musamman da Hajja ta dafa kafadarta fuskarta cike da roko tana fadin

“Ki yafe mishi dan girman Allah, ki duba rokona Waheedah…”

Kuka Waheedah takeyi, hakan yasa Hajja ta riketa a jikinta, kaddarar yaran na tsaya mata, ita kanta Waheedah din a idanuwanta zaka ga rauni, AbdulKadir dinne ya tabata sosai, amman rabuwa dashine karshen abinda take bukata. Cikin kuka tace

“Hajja bansan ya zanyi ba… Ban sani ba nikam”

Riketa Hajja tayi sosai

“Hakuri zakiyi, kiyi hakuri… In yayi abinda ya nuna miki ke din bakida muhimmanci halin daya shiga yanzun ya isa ya karya shi… Ke dince rayuwar shi Wallahi…” 13

Kai Waheedah ta girgiza tana kin yarda da kalaman Hajja, wani kishi naban mamaki na turnuqe zuciyarta, da itace rayuwar shi da bai hadata kishi da Nuriyya ba, da itace rayuwar shi da bai ci mutuncinta ya auri aminiyarta ba. Dagowa tayi daga jikin Hajja tana saka hannuwanta duka ta share hawayenta

“Waheedah…”

Hajja ta fadi tana rasa da kalaman da zatayi amfani dasu dan rikici take gani shimfide a idanuwan Waheedah din, da gaskiyar mutane ka guji bacin ran mai hakuri

“Jinin shi ya hau”

Hajja tace tana saka Waheedah rausayar da kai, cikin sanyin murya tace

“Nima hawan jinin nake fama da shi Hajja” 5

Hawaye na zubar mata, duk idan tayi zaton hawayenta sun kare sai wani abin ya sake faruwa da zasuci gaba da zuba kamar an bude fanfo, numfashi Hajja taja tana fitar dashi kafin tace

“Shikenan Waheedah, Allah ya zaba muku abinda yafi alkhairi” 1

Ta juya tana ficewa daga gidan. Daki Waheedah ta koma ta dauki wayarta, kuka take har bata ganin abinda ke rubuce a screen din wayar sosai, saida ta goge fuskarta tukunna ta lalubo lambar Abba ta kira, bugun farko ya daga da fadin

“Waheedah…”

Wani irin kuka ta rushe dashi da yasa Abba cewa

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Waheedah me ya faru? Menene? Me akai miki?”

Ta dayan bangaren, kana jin tashin hankalin dake cikin muryar shi, numfashi take fitarwa kamar zata shide saboda kukan da takeyi

“Ab….Abba…”

Ta iya fadi dakyar tan dorawa da

“Kowa nata bani hakuri… Abba har Hajja hakuri take bani, zuciyata ciwo take mun Wallahi… Dana tuna zuciyata ciwo take mun… Ab…Abba bansan ya zanyi ba”

Tanajin ya sauke numfashi, cikin taushin murya mai cike da lallashi yace

“Kiyi duk abinda zuciyarki zata nutsu da shi, karki bari hakurin da suke baki ya saki yin zabin da zaki cutu, karkuma ki bari fushinki yasa kiyi zabin da ba zakiyi dana sani” 3

Kai Waheedah take jinjinawa tana goge fuskarta da bayan hannunta

“Kina jina?”

Abba ya fadi yana sa ta sake jinjina mishi kai

“Zan zo in dubaki anjima, ki samu ruwa ki sha, ki daina kuka kinji Waheedah? Komai zaiyi dai-dai”

Kai ta jinjina tana kara goge fuskarta, batace komai ba ta sauke wayar daga kunnenta, bata samu damar sanin mahaifinta ba, amman Abba ya bata kauna da kusancin da ko mahaifinta jinin shi dake yawo a jikinta ne kawai zai nunawa Abba. Abu biyu ta sani, zuciyarta na mata ciwo na gaske na biyun a fili ta fade shi

“Kin yi kadan in bar miki mijina Nuriyya… Nabar miki abubuwa da yawa a rayuwata, ban da shi, banda Sadauki na…” 87

Ta goge hawayen da suka zubo daga zuciyarta tana jin wani irin karfin gwiwa da bata taba jin irin shi ba…!Kunshin hannunta da yake rike cikin na farin matashin saurayin ya fara bi da kallo, kirjin shi na zafi kamar zai bude, kafin yaga saurayin ya mika kai saitin kunnen Waheedah yana rada mata wata magana da tasa tayin dariyar nan tata da take kashe mishi jiki. Baisan ya karasa wajen ba saboda wani irin kishi daya turnuqe shi har duhu-duhu yake gani, tsakanin su ya shiga yana huci kamar kububuwa. 2

“Lafiya?”

Saurayin ya fada yana kallon AbdulKadir din kamar yaga mahaukaci.

“Lafiya kake tambayata? Bakasan matata bace dan ubanka?”

Dariya saurayin yayi data kara bata ma AbdulKadir din rai

“Ka saketa din, na aura kana fadamun matar…”

Bai karasa maganar ba AbdulKadir din yakai mishi wani irin naushi a baki

*

Duka Yassar yakai ma AbdulKadir din da saura kadan ya gabje mishi hanci, duk da haka ya same shi kadan a gefen mummuqe, wani dukan ya kara jibga mishi yana fadin 12

“Tashi…. Ka warke shisa zaka kwantar dani ba…” 3

Mikewa AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da yake sarawa, a zuciyar shi yake karanto

‘Inalillahi wa ina ilaihi raji’un’

Yana neman tsari daga muguwar kaddara, tari ya sarke shi da yasa Yassar din mika hannu ya dauko robar ruwan da take gefe ya mika ma AbdulKadir din, da sauri ya karba yana sha. Kishine yake turnuqe shi har lokacin, kowanne mahaukaci ne yake tunanin zai saki Waheedah ya aura yana fatan yazo da bargo da filo, dan zaici gaba da kwana a wajen ne, in yagaji ya kara gaba. Karin ruwan da yake daure a hannun shi ya kalla yana son tuna lokacin da suka zo asibiti

“Karka kara tsoratani haka AbdulKadir, idan kana so in goyi bayanka ka zamana mai gaskiya, karka kara tsoratani haka”

Yassar ya fadi muryar shi can kasan makoshi, yanajin yanda har lokacin zuciyar shi bata daina rawa ba. Ganin AbdulKadir din a kwance ya tsorata shi fiye da tunani, ya tuna mishi duk wani dalili da yasa bayason uniform din shi, a lokaci daya kuma ya tuna mishi da soja ko ba soja ba, mutuwa babu ruwanta, ba zabe take yi ba, kowa nata ne, lokaci kawai take jira ta cika aikin ta.

“Ashe kana so na” 9

Cewar AbdulKadir da murmushi a fuskar shi duk da kirjin shi da yake ciwo, hararshi Yassar yayi da yasa ya karayin dariya, sautinta na dirar mishi a kunne da wani irin yanayi

“Zuciyata namun ciwo Hamma”

AbdulKadir ya fadi yana dorawa da

“Kaman zata fito daga kirjina haka nake ji…amman Waheedah tace mun haka ta dinga ji harna wata takwas, Hamma ta ina zan fara bata hakuri? Ta ina? Yau kawai na fara jin hakan amman inajin kamar lokacin mutuwa yazo gab… Wanne irin karfin hali gare ta?” 3

Kallon shi Yassar yake, yana jin kuncin dake tattare da muryar kanin na shi da yake tabashi sosai da sosai

“Kayi kuskure AbdulKadir… Bance maka nayi dana sanin zama sanadin daka auri Waheedah dan bana son zaman ku ba… A karo na farko kasa naji dana sani nabar Hamma Yazid ya aure ta”

Da mamaki AbdulKadir yake kallon Yassar din yana jin maganganun shi sun dirar mishi kamar saukar ruwan da babu hadari

“Hamma Yazid?”

Ya maimaita cike da alamar tambaya, kai Yassar ya jinjina mata

“Yana son ta, ya sota a lokacin, ni na fada mishi kuna soyayya saiya hakura… Shisa yai nisa da Kano…”

STORY CONTINUES BELOW


Wannan karin ruwan da yake hannun shi AbdulKadir ya fisge duk yanda Yassar din ya kira sunan shi, kafafuwan shi ya sakko daga kan gadon yana jin shi wani sama-sama. Yazid ya so Waheedah? Ko kadan kwakwalwar shi ta kasa yardar mishi da maganar, muryar shi can nesa cike da tuquqin kishi yace 2

“Me yasa ta aure ni to? Tunda yana son ta”

Ya karasa maganar yana kallon Yassar din kamar zai rufe shi da duka, numfashi Yassar ya sauke

“Ka taba ganin son wani a idanuwan ta? Bai taba fada mata ba, bata taba son shi ba, kishin banza da wofi zaka nuna yanzun? Kana kishinta amman baka iya kula da damuwar ta ba” 2

Runtsa idanuwa AbdulKadir yayi yanajin kamar Yassar ya watsa mishi ruwan zafi, kafin ya bude su a kan shi da fadin

“Karka karamun ciwon da nakeji”

Kujerar shi Yassar yaja yana matsawa gab da AbdulKadir din sosai

“Ba Hamma Yazid ya so Waheedah zaka duba ba AbdulKadir, ka duba yanda ya zabi farin cikin ka a kan nashi, ka duba yanda mu duka muke a shirye da dora farin cikin ka akan namu, ka fara yarda da fadanmu ba nuna isa bane a kanka, fadan mu na tare da yanda muke son ka”

Wannan karin kamar AbdulKadir din zaiyi kuka yake kallon Yassar, idanuwan shi sun kara kankancewa

“Sau nawa abinda nayi yai hurting din ku? Rashin tunani da rashin duba abinda halayena suke yiwa na kusa dani, Hamma sau nawa?”

Dan murmushi Yassar yayi

“Ba zai lissafu ba”

Ya amsa a taqaice yana sa AbdulKadir din runtsa idanuwan shi yana bude su, zuciyar shi na wani irin ciwo

“Harda su Hajja ko? Halayena na taba su suma” 3

Kai Yassar ya daga ma AbdulKadir din da dan murmushin karfin hali a fuskar shi

“Ta ina zan fara? Taya zan fara baku hakuri Hamma? Ban taba tunanin nan ba, ban taba tunanin dan nayi abinda ni ya shafa zai taba mutanen da nafi kusanci da su ba, mutanen da nake kauna da dukkan zuciyata” 1

Numfashi Yassar ya sauke

“Ka fara da sauraren shawarwarin mu, ko da baka dauka ba, ka nuna mana yanda muka isa ka saurara”

Kai AbdulKadir yake jinjina, kome suke so shikam zaiyi, tunanin yana cutar dasu ba karamin karyar mishi da zuciya yake ba 3

“Ka bude bakin ka kaba Waheedah hakuri, tana son ka, shisa kishinka yai mata yawa…”

Kai AbdulKadir din ya sake jinjina, muryar shi a karye yace

“Bansan ya akai kuke so na ba har yanzun Hamma, bana tunanin idan nine a matsayin ku zan manta duk abubuwan nan inci gaba da zama daku”

Wannan karin murmushin Yassar daga zuciyar shi ya fito

“Ba zabi aka bamu ba kafin ka kasance dan uwan mu, akwai alakar da bata baka wannan zabin, haka kaunar da muke maka, ba muna tare da kai dan mun manta abubuwan da kayi da bamu so ba, muna tare da kai saboda mun yafe maka hakan tun kafin kagane kuskure ne ka roke mu” 1

Hannu AbdulKadir din yakai yanajin kamar maiqo a gefe-gefen idanuwan shi, yasa yatsun shi yana dangwalowa, Yassar din naci gaba da fadin

“A kasan duk rashin kunyar ka, dan uwane kai da ko an bani zabi bazan taba daukar irin shi ba, kana da halaye da bana so, halayen da zanso ka sake su, amman shine cikar dan adam din, duk idan zamu fadama kan mu gaskiya akwai halayen da muke dasu da muke son canzawa saboda ba masu kyau bane ba” 1

Ya dauka zuciyar shi tagama karyewa da maganganun Waheedah, sai yanzun da yakejin hawayen daya dauka sunyi bankwana dashi cike taf da idanuwan shi, kaunar Yassar din na taba shi tana karya sauran abinda ya rage a zuciyar shi, ko yau rayuwa ta kare mishi yana da tabbacin kaunar su zata cigaba da samun shi a kabarin shi, saboda addu’o’in su ba zasu taba yankewa ba. Baisan ya mike daga kan gadon ba saida yaji Yassar yasa hannu yana ture shi ya mayar dashi ya zaunar

STORY CONTINUES BELOW


“Rungumeni za kai dan ubanka? Meye haka? A india muke ko America? Bana son iskancin banza da wofi fa” 36

Dariya AbdulKadir yake sosai yana goge idanuwan shi da yakeji cike da hawaye

“Nagode Hamma”

Ya fadi da dukkan zuciyar shi, kai Yassar ya daga mishi, AbdulKadir din na dorawa da

“Kai musu magana su zo su sallameni, ni bazan kwana anan ba”

Kallon shi Yassar yayi

“Faduwa fa kayi AbdulKadir…”

Kafadun shi duka biyun ya maqale ma Yassar

“Wallahi Hamma bazan kwana ba, in basu sallameni ba zan tafi da kaina”

Kai kawai Yassar ya girgiza hadi da sauke numfashi ya mike, mai hali akace baya taba canzawa, akwai halayyar AbdulKadir din da a jinin shi take, bazai iya canza ta ba, taurin kai na cikin wannan

“Kai kam ko Sheikh Mufti aka saka a ruwa aka girgiza aka baka kasha kayi wanka ba zaka canza hali ba Wallahi” 4

Dakuna mishi fuska AbdulKadir din yayi yana hade girar sama da ta kasa, babu wanda zai saka shi zama a asibiti, banda zazzabi bayajin komai, sai ciwon kai sama-sama, kirjin shi da yakeyi kamar zai bude ba asibiti yake bukata ba, Waheedah yake bukata, in ya riketa a jikin shi zai samu saukin duk wannan abubuwan da yake ji. Da ido yabi Yassar din harya fice daga dakin, kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin tunanin Waheedah daya baibaye shi.

*

Ruwa ta watsa bayan tafiyar Hajja, ta sake kaya. Wata nutsuwa take ji data kwana biyu bataji irin ta ba, WhatsApp dinta ta bude tana shiga sakon da Hauwa ta turo mata na littafin Farin Wata na Zahra Tabi’u. 4

‘An saka mata sunan mace ba dan ana tunanin ita din cikakkiyar mace bace’

Ta karanta layin farko, maganganun na saka ta tunani barkatai, tun daga kan maitafiya take son marubuciyar, saboda tana tabo labaran da bako yaushe ake tabo su ba a cikin duniyar rubutu, tallar kawai ta ja hankalinta sosai. Dari uku batai mata tsada ba, account number din ta dauka tana tura kudin kafin ta dauki lambar marubuciyar 08065156303 dan ta tura mata shaidar biya. Tana karasawa ta mike, tana tunanin shiga kasuwane dan tayi siyayyar azumi tunda yau dinne ake sa ran fara duban fitowar watan, duk da anata gardama kan hakan kamar ko da yaushe. 5

Abin na daurema Waheedah kai, yanda ake shafe watanni goma cir ana tafiya kai a hade, sai ance watan Ramadan ya gabato sai a fara rikici kan lissafi, yanda aka saki sunnah da Manzo SAW ya doramu a kai na tsoratar da ita, shisa abubuwa sukai mana yawa, wahalhalun mu suka yawaita. Shagon da takanyi siyayyarta guda dayane, dan sun saba sosai, lokutta da dama duk abinda take so ma list takeyi saita tura musu text, wanda sai an shiga kasuwa cikin yaran shagon ake sakawa yaje ya siyo mata, kafin ta shiga duk sun hada mata kayayyakinta, kudin kawa za tayi musu transfer, sai a nemo mata mai napep a saka mata kayan a baya. Wasu lokuttan kuma mai napep din da taje dashi ne bata sallama.

Yanzun ma komawa tayi ta zauna tana tunanin abubuwan da take bukata, list dinsu tayi gabaki dayan su, sai doya da dankali da ta saka na adadin da zasu siyo mata, daya daga cikin yaran shagon Tasi’u ta kira, bazai wuce shekaru sha tara ba, amman hankalin shi har mamaki yake bata, ga girmama mutane, tace ya duba whatsapp din shi ga kayyakin da za’a hada mata nan, yanzun zata shigo kasuwar, ya kuma taimaka inda yakan siyo mata doya da dankali ya siyo mata doya ta dubu biyu sai dankali na dubu uku. Tasan zata kwana biyu bata nema ba.

Kayan su ta hada a jakar da Yassar ya kawo musu. Ta kara gyara dakin tsaf tukunna ta saka Ikram a jakar goyanta, tasa hijab tana goya yarinyar ta gaba, ta dauki jakar da mukulli ta wuce, a falo suka ci karo da Hauwa, da mamakin ganin ta dawo da wuri a tattare da Waheedah tace

STORY CONTINUES BELOW


“Yau da wuri haka?”

Dariya Hauwa tayi

“Nagaji fa, gudowa nayi nace banda lafiya”

Murmushi Waheedah tayi, daman tayi niyyar karbar kayanta a kasuwa ta sauke a gida ta dawo, sai tayi musu sallama tukunna ta wuce. Cikin sanyin murya tace

“Ina son zuwa kasuwa ne, sai in biya gida in kai kayan nan”

Hauwa batasan lokacin data hade space din dake tsakanin su da Waheedah ta rungumeta ta gefe ba, saboda Ikram da take rike da ita, tukunna ta dago tace

“Inata kokari kar in miki magana Wallahi, inakuma kokari kar in wuce gidanki daga wajen aiki in jibgi Nuriyya ko zan huce haushina… In kika bar mata gidan harni kin cuceni, bata isa kibar mata gidanki ba wallahi”

Dariyar karfin hali Waheedah tayi, Yassar yasa ta sami kawa a tare da Hauwa.

“Nagode Hauwa”

Ta fadi a sanyaye, kai Hauwa ta jinjina mata

“Muje in kaiki, ba abinda zanyi sai kwanciya ko na zauna gidan daman”

Tare suka fita da Hauwa din, har kasuwa sukaje tare tana ta tsegumin yanda motarta take bukatar ganin bakanike saboda tana mata wata kara da Waheedah bataji ba, tunda ba sanin kan mota tayi ba. Da suka dauki kayan gidan Waheedah din suka wuce ta kai, bataga Nuriyya ba, bata kuma damu da hakan ba, har bedroom dinta ta wuce ta ajiye jakar kayansu, ta dauki mukullan data manta ranar karshe da tayi amfani dasu, ta kulle dakin baccin nata da sauran dakunan da suke bangarenta, dawowa tayi ta rufe kitchen dinta ma, dan siyayyar duk da tayi a tsakiyar kitchen din ta ajiye su, inta dawo ta shirya komai. Suka sake ficewa da Hauwa din.

Saloon tace zataje ta wanke kai, tare sukaje, itama Waheedah kan aka wanke mata akayi mata kitso, yanda suka dameta da a saka mata bakin lalle akan jan da yake hannunta zaiyi kyau, harda Hauwa din yasa ta bari, da yake babban saloon ne, har su gyaran jiki anayi. Lokacin da suka gama, wani yawon Hauwa ta sake janta, wai zata kai dinki. Gidansu Waheedah tace ta sauketa, lokacin gab da magriba, dan anan Hauwa tayi magriba tana ta sauri 7

“Yau zan sha fada nasani Wallahi”

Hauwa ta fadi hankalinta a tashe, bakomai Yassar yake magana a kai ba, amman Allah yai mata son yawo, shikuma ya tsani taje unguwa tayo dare, tasani kawai taurin kaine irin na mata, dariya Waheedah ta dinga mata, har bakin mota ta rakata tukunna ta koma ciki tana samun Mami a dakinta, gefen gado ta zauna tana fadin

“Mami zan koma”

Numfashi mai nauyi Mami ta sauke

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, karkiyi wasa da addu’a, kinsan in kina da matsala waya kawai zaki dauka ki kirani ko?”

Kai Waheedah ta jinjina mata, addu’o’inta Mami ta sakeyi musu tana kara binta da nasiha mai ratsa jiki, tukunna ta dauki Hijab dinta tana barin Ikram ta wuce bangaren Abba, shisa ta kirashi kar yaje gidan Yassar zata taho gida itama. Da sallama ta tura kofar tana shiga falon Abban da murmushin dake fuskar shi ya nutsa wani abu a zuciyarta

“Abba…”

Waheedah ta fadi cike da farin ciki, bata taba tunanin zata kaunaci wani da jinin shi baya yawo a jikinta da yawa haka ba, tana son Abba da dukkan zuciyarta. Babu jinin shi a jikinta, amman kaunar shi na ciki ta gauraye, karasawa tayi ta zauna a gefen shi kan kafet bayan sun gaisa

“Kina lafiya ko?”

Abba ya bukata, yana jin dadin ganin murmushin da yake kan fuskarta

“Ina lafiya Abba…”

Numfashi mai nauyi Abba ya sauke

“Kin yi magana da AbdulKadir din?”

Kai ta jinjina ma Abba a kunyace, murmushi yayi ba saita fada mishi ba, yasan sun shirya da AbdulKadir din, tsakanin mata da miji daman ance sai Allah.

STORY CONTINUES BELOW


“Babu inda hakuri ya tashi a banza Waheedah, kar wani ya taba sa kiji hakurin ki yayi yawa. Karki bari halayen kowa ya canza naki masu kyau. Da yawan lokaci rashin kirkin mutane na gurbata na masu kirki….karki bari hakan ya faru dake kinji?” 1

Kai ta sake jinjina wa tana furta

“In shaa Allah”

Numfashi Abba ya sauke yana cigaba da fadin

“A lokaci daya kuma karki bari hakurin ki yaja miki raini, ko da zaki yafe in an miki kuskure ki nuna hakan, ba saikin yi da hayaniya ba, tunda ba halinki bane, kiyi a nutse, karki barshi a cikin ki zai cutar dake. Allah yai miki albarka, Allah ya shirya miki zuri’arki” 2

Da wani yanayi a muryarta tace

“Amin Abba, Allah ya bamu aron rayuwa mai tsayi tare da kai”

Da murmushi a fuskar shi ya amsa ta da

“Amin…”

Yana dorawa da

“Ba gidan ki zaki koma ba?”

Kai ta sake sunkuyar wa cike da kunyar shi data lullube ta, hakan yasa Abba fadin

“Kije ki shirya ki fito in kai ki” 1

Mikewa tayi dan ji take kamar zata nutse a wajen saboda kunya. Babu abinda zata dauka banda Ikram, Fajr na wajen Hajja, kunyar Hajja din takeji dan dazun batasan bakinta ya subuce ta mayar mata da magana ba. Duk gidan itace ta farko da ta sameta har gidanta bayan taji Nuriyya ta tare ta bata hakuri, ita ta fara nuna mata ko kadan bada son ranta akai auren AbdulKadir din da Nuriyya ba, duk da a lokacin ta nuna ma Hajjan babu komai, bata kwana uku bata kirata taji lafiyarta ba, matar bata nuna mata komai banda kauna ba. Sallama tayi da Mami tana goya Ikram, ta samu Abba harya fito ma yana motar shi a zaune. Budewa tayi ta shiga gaba ta zauna tana mayar da murfin ta rufe.

*

A kofar gida Abba yayi parking yana kiran wayar AbdulKadir din, da ya fito ko takalma babu a kafafuwan shi, kamar baiga Abba a tsaye ba yace

“Waheedah…”

Yana kasa boye farin cikin shi, kunya tasa Waheedah raba AbdulKadir din ta wuce cikin gidan da sauri. Sai lokacin AbdulKadir ya kalli Abba yana fadin 1

“Abba… Ina wuni”

Harar shi Abba yayi

“Sai yanzun kaganni?”

Dan sosa kai AbdulKadir yayi yana karasawa wajen motar Abban ya jingina, yanajin tsakuwoyin da yake takawa da suke tunasar dashi bai ko saka takalma ba.

“Ba yaro bane kai da zan zauna ina maka fada akan duk wani abu na rayuwa, ya kamata ace ka hutar dani haka AbdulKadir, kasan wasu abubuwan sun kamata ko basu kamata ba, bansan me kai mata ba wannan karin, ban kuma san inda ta sami karfin zuciyar yafe maka ba. Amman banajin ni zan yafe maka idan ka sake taba ta haka, Hajiya Safiyya tace mun Fajr ya fada mata ka ture Waheedah harta fadi, ya kuma yi kankanta ya shirya karyar da baigani ba haka”

Kan shi AbdulKadir ya sadda kasa yanajin maganganun Abban na shigar shi sosai

“Bansan inda ka sami tarbiyar dagama matar aurenka hannu ba, nikam badaga wajena ka dauka ba…”

Abba ya karashe maganar cikin sanyin murya kafin yace

“AbdulKadir…”

Yana saka AbdulKadir din dagowa ya kalli Abba

“Ranar da duk ka sake dagama yarinyata hannu, ka kalli fuskata ba wasa nake da kai ba, wallahi ka daki aurenka” 8

Rufe fuskar shi AbdulKadir yayi da hannuwan shi biyu yana budeta, kirjin shi na daukar dumi kamar ana gobara a cikin shi, muryar shi a karye yace

STORY CONTINUES BELOW


“Abba nima dan ka ne… Itama kace mata idan nayi mata abu ta dinga fadamun ina bata hakuri, kace mata ta daina bari a ranta babu kyau. Abba ka kalli yanda duk ka tsoratani”

Ya karasa yana goge zufar da take tsatssafo mishi a goshi, amman fuskar Abban babu wani alamar wasa, shikam yanzun kowa yagane raunin shi, rabuwa da Waheedah ne raunin shi, shisa suke son kashe shi duk su huta, yasan da yayi abu zasu dinga mishi barazanar rabashi da Waheedah din tunda sun san hankalin shi tashi zaiyi

“Itama in kirata kace mata a bakin aurena idan tana qullata ta” 32

Mota Abba ya bude ya shiga yana mayar da murfin ya wuce, ya yarda akwai mutanen da duk shekarun da zasuyi a duniya rashin hankali bazai taba barin su ba, ciki harda AbdulKadir. 8

“Kaji Abba…”

Baiko kalle shi ba, ya tayar da motar, murmushi AbdulKadir din yayi

“Nagode Abba… Zan kiyaye in shaa Allah, zan kiyaye”

Ya sake jaddadama Abban, kafin yaja motar shi ya wuce. Numfashi AbdulKadir ya sauke yana wucewa cikin gidan. Shima da magriba Yassar ya dawo dashi, dan asibitin kin sallamar shi sukayi sai da suka karasa mishi wani ruwan da allurar da ta sakashi bacci har kusan magribar, bai jima da dawowa ba, wanka kawai yayi tunda sunyi sallah a hanya. Har haushin Yassar yaji da yace

‘Matar ka bata da hankalin da zaka wuni baka koma gida ta nemeka ba ko?’ 8

Duk da gaskiya ce ya fada, Nuriyya din ko flashing batayi mishi ba, ya kuma ji haushi sosai, dan shi mutum ne mai bala’in son kulawa, shisa tunda ya dawo yake shashareta, ya kuma ga bata damu ba, hidimarta kawai takeyi, yayi alkawarin zai dafata a ruwan sanyi, dan bazai dauki wannan halin ko in kula din nata ba, inma ba da gangan takeyi ba, bangaren Waheedah ya shiga yana samun ta ta fito daga bandaki, da alama alwala tayi, bata ce mishi komai ba ta dauki hijab dinta, shima bandakin ya shiga ya daura alwala yana fita masallaci, zuciyar shi a nutse yake jinta har aka idar da sallah. Ko azkar bai tsaya yiba ya dawo gida, dan so yake yagan shi a kusa da ita.

Ita kam Waheedah zafi taji ya isheta ta sake watsa ruwa tana idar da sallah, doguwar riga ta saka ta material dinki bubu, yadin blue mai haske, ta dauki hula kalar shi mai cizawa ta saka a kanta, tana jin dadin wutar da suka dawo da ita, dan fitilar waya take ta amfani da ita a dakin, torchlight dinta babu caji a jiki. Duk da darene jambaki ta tsinci kanta da shafawa a labbanta, tana dan murza mai a hannuwanta, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi. Sanda AbdulKadir ya shigo ta sauke ikram kan katifarta, tana kara gyara gadon da yake a hargitse. Tsaye yayi a tsakiyar dakin, kamshin ta na saka shi lumshe ido, wata irin kewarta na dabaibaye shi.

Har inda take ya taka yana rungumeta ta baya ya sumbaci kuncinta, cikin kunnenta yace

“Ki yafemun Waheedah, dan Allah ki yafemun”

Tanajin yanda maganar ta fito daga zuciyar shi, zame jikinta tayi daga nashi, tana juyowa ta fuskance shi, fuskar shi take kallo sosai, tana saka hannuwanta ta rike kuncin shi, tanajin yanda sai da tadan daga kafafuwanta, girman shi harya daina bata mamaki, kallon shi tayi na wasu dakika kafin ta sauke hannunta batare da tace mishi komai ba, a shirunta yake karantar yafiya, duk yanda idanuwanta suke tabbatar mishi yana da sauran lokaci kafin ta sauka daga fushin da take, zaiyi komai, indai tana kusa dashi duk mai sauki ne.

Gadon ta karasa gyarawa, ta dauki Ikram dake ta bacci ta mayar da ita kan gadon tana ficewa daga dakin zuwa kitchen, tanajin AbdulKadir na biye da ita, mukulli tasa ta bude kitchen din tana turawa, tabar mukullin a jiki, tsugunnawa tayi tana bude kwalaye da ledojin siyayyarta, AbdulKadir na tsaye yanata binta da idanuwa kamar bai taba ganinta ba, ta mishi kyau sosai. Da ance mishi lokaci zaizo da zaiji shakkarta zai karyata, amman yanayin dake fuskarta yasa shi hakura da duk yanda yake son sumbatarta. Yanzun ma kasa hakura yayi ya tsugunna kamar zai tayata fiffito da kayayyakin da take ya kamo hannunta da yasha lalle yana dago shi ya sumbata.

STORY CONTINUES BELOW


Kallon shi Waheedah tayi tanajin yanda ko meye tasa ta lullube kaunar shi dashi yana soma budewa, hakan yasata zame hannunta daga cikin nashi

“Aiki nake Sadauki”

Ta fadi tana dauke idanuwanta daga kan shi, ta dauki ledojin maggi tana dorawa kan kantar kitchen din ta dauko robobinsu ta bude kowane tana juye shi a mazaunin shi. Baice mata komai ba, kayan ya tayata shiryawa, suna cikin aikin Nuriyya ta karaso wajen da murmushi a fuskarta, wutar da aka kawo yasa ta fitowa falon sai taji motsin yayi yawa shisa ta fito, sosai taji sanyi a ranta na ganin Waheedah din, taliya ce ta samu ta dafa fara, tanayin miyar da ko a ido batai mata kyau ba.

Tunanin abinda zasuyi suhoor dashi takeyi da yanda zata kaya musu washegari, ranta duk baya mata dadi, amman yanzun tasan indai girki ne ta kare, fadansu da ta hango ita da AbdulKadir kan hakan ya wuce. Sosai hankalinta ya kwanta 10

“Waheedah… Ashe kin dawo” 2

Ta fadi tana saka Waheedah din da AbdulKadir juyawa a tare, Waheedah najin wani abu ya taso mata daga dan yatsan kafarta zuwa tsakiyar kanta yana dawowa kirjinta ya tokare, AbdulKadir kuwa wani irin tsoro da baiyi tsammani ba yaji ya lullube shi, kar Nuriyya din tayi kokarin rike shi a gaban Waheedah, da sauri yazo ya rabata ya fice daga kitchen din yana wucewa bedroom din Waheedah ya turo kofar, jikin shi yakeji har bari yake mai, dan baisan ya zaiyi ba, a karo na farko a rayuwar shi da komai ya kwance mishi. 20

Waheedah kuwa wani kallo tayi ma Nuriyya din da yasa taji gwiwoyinta sunyi sanyi. Ba zatace tun zuwanta gidan suna hira da Waheedah din ba, ko kuma sunci gaba da zama kawaye, amman suna gaisawa kullum, kuma tana shigowa bangaren Waheedah din ta zauna a falo, har remote take dauka tayi kallo, musamman in tajiyo kamshin girki, data kula ko batazo ba tana bata abinci saita rage zuwa sai AbdulKadir na nan. Amman Waheedah daman ta daina fara’a a gabanta, sai dai bata mata irin wannan kallon, bata mata kowanne kallo ma. 2

“Sannun ki”

Waheedah ta fadi tana juyawa taci gaba da abinda takeyi, watakila ko dan batajin dadine, Nuriyyar tayi tunani, hakan yasa ta wuce ta koma bangarenta dan bata kula da sanda AbdulKadir ya fice ba. Tsaf Waheedah ta karasa gyara kitchen din tana share shi, fridge dinta ta bude taga an dibar mata robobin kayan miya, ta kuma san Nuriyya ce, daga yau kuma ta kare, can gidan kasa ta tsugunna, tana janyo kwami ta ciro roba fara mai murfi, dakyar ma ta fito da ita dan tayi kankara. Farfesun kayan cikine a ciki, tukunya ta dauko ta saka robar a sink tana sakar mata ruwa dan yadan saki. 1

Doya ta yanka da zata isheta iya cikinta, ta fere tana zuba dan mai a abin suya, ta soyata fararta, tana kwashewa a plate. Lokacin farfesun ya saki, iya wanda zai isheta ta diba ta zuba a tukunya tana mayar da sauran a fridge. Ta dora, da yake yasha kayan kamshi, kafin kace wani abu gidan ya budade da kamshin daya fito da AbdulKadir yazo kitchen din yana fadin 2

“Me kike dafa mana?” 3

Juyowa tayi tana kallon shi

“Daga dawowata zan karbi girki? Banda lafiya ko ka manta, sai jibi nikam”

Da mamaki AbdulKadir yake kallonta

“A’a ba abin tashin hankali bane ba, sai in koma gida, jibin in dawo” 11

Kai ya girgiza mata da sauri, shi bashida karfin fada koyin gaddama da ita. Duk da yaso jinta a jikin shi daren yau, kwana biyu bazai canza wani abu ba, sanin tana cikin gidan ya ishe shi, ran shi ya biya da abincin sosai, wata yunwa da baisan yanajin taba ta taso mishi. Dan waje ta samu ta juye farfesun a ciki, AbdulKadir din yakai hannu zai dauki guda daya ta doke hannun shi 1

“Ni ban dafa da kai ba Wallahi”

Tana janye kwanon ta ajiye gefe, kallonta yake, yayi mata laifi yasani, ya bata hakuri kuma

“Ba kyau horon yunwa” 1

Ya fadi can kasan makoshi, Waheedah nayin kamar bataji shi ba, duk abin ya mishi wani iri sosai dan bai saba ba, sau nawa take hakura da abu tabar mishi, amman yau itace take cewa tayi girki banda shi, zuciyar shi batai mishi dadi ba sam, tukunyar data bata take wankewa. Sai ga Nuriyya ta shigo kitchen din tana ta washe baki, dan tana sallar isha’i take jiyo kamshin, yawunta sai tsinkewa yake, kwana biyu bataci abu mai galmi-galmi ba. 14

“Kamshi duk ya cika gidan, me ake dafa mana ne” 29

Ta fadi kamar yanda ta saba, AbdulKadir na kallonta a karo na farko yaga kwadayi a fuskarta, baisan ko dan shima an hanashi bane yasa shi jin haushin kwadayin nata. Ga mamakinta ko inda take Waheedah bata kalla ba, asalima plate din doyar ta dauka da kwanon farfesun tana zuwa ta gabansu, 7

“Kudan fita zan rufe kitchen din” 22

Ta fadi tana ganin suka fita bakin kitchen din suna ta kallonta, sai da ta janyo kitchen din tasa mukulli ta rufe tukunna ta wuce da fadin 3

“Sai da safen ku” 7

Su biyun suna binta da kallo cike da mamaki

“Ina namu?” 48

Nuriyya ta fadi bayan Waheedah ta shige lungun da zai kaita dakin baccin ta, dakuna fuska AbdulKadir yayi 2

“Nima bata bani ba” 20

Ya amsa ranshi a jagule yana wucewa bangaren Nuriyya din, da duk da mamakin da take bai hanata jijjiga kitchen din ba taji da gaske a kulle yake, dan Waheedah bata taba rufe kitchen dinta ba. Tsaye tayi a wajen ta kasa yarda da abinda ya faru…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *