ABDULKADIR
CHAPTER 9
A rayuwar shi bai taba sanin menene asalin ma’anar kalmar wulakanci ba sai da yaje NDA, kamar yanda ba zaice ga tun lokacin da yake son saka uniform din sojoji ba. Sai dai shi mutum ne da idan yasa abu a ranshi, wahala ko makamancin hakan baya hanashi cimma burin shi. Zai iya rantsewa a yan shekararsu babu wanda ya sha wahalar da yasha a NDA, daga horo zuwa jibga, akwai lokutta da dama a shekarar shi ta farko da baiyi tunanin zai gama NDA da ran shi ba. Saboda bai iya tauna magana kafin ya fadeta ba, kuma bai iyayin shiru idan yana tunanin akan gaskiyar shi yake. Abinda ya ja mishi tsana da kauna daga wajen manyan shi.
Zai iya cewa kwana biyar din da yayi bakomai bane akan irin wahalhalun da ya sha a baya. Abinda ya bambanta da sauran loluttan shine, bashi yayi laifin da kan shi ba, kuma yanzun da yake hanyar shi ta zuwa gida zai shiga gidan batare da yaga Waheedah ba, kuma yayi kwanakin biyar da tunaninta cunkushe a kan shi, ranakun da sukayi mishi wani irin tsayi naban mamaki. Sabon da yayi da rashin wanka na tsayin lokaci idan aiki ya kaisu wajajen da babu nutsuwar yin hakan bai hanashi jin wari da karnin jinin da yake ba. 6
Ko sallama baiyi ba lokacin daya shiga gida, bangaren Nuriyya ya wuce, dan haka ko kadan bata tsammaci shigowar shi ba. Ta dauka auren Anas shine babban tashin hankalin daya faru da rayuwarta, sai kwanaki biyar da suka wuce da ta dawo gida tana rasa inda zata saka rayuwar ta taji sanyi. Da zazzabi ta wuni, ta kuma tashi dashi ganin har an kwana daya AbdulKadir din bai dawo ba, tayi tunanin zuwa gidansu ta sanar dasu halin da ake ciki, amman ta rasa samun karfin gwiwar yin hakan. Wanda duk suke dan son ta a gidan su AbdulKadir din sanadin Waheedah ne daman, tun bayan auren ta da AbdulKadir babu wanda ya sake ko kallon inda take ballantana magana ta hadasu.
Ta gwada zuwa gidansu AbdulKadir din sau daya, tunda Hajja ta amsa mata gaisuwa bata sake ce mata komai ba, ta muzanta fiye da tunani ranar, dan har kuka tayi bayan ta fito, bata kuma sake marmarin komawa ba. Babban tashin hankalin da ta shiga shine tunanin abinda zai biyo baya da fitowar AbdulKadir din, ta kira lambar Waheedah bata san adadi ba, amman a kashe, dan tasan inta fada mata zata gayawa yan gidansu AbdulKadir din ayi wani abu a kai. Hankalinta in yayi dubu a tashe yake da taga kwanaki na tafiya babu alamar AbdulKadir din. 2
Yaune ta yanke hukuncin ko me su Hajja zasuyi mata zataje ta same su, dan in su basu kasheta ba, zullumi zai kasheta, ko abinci ta dan samu ta dafa, plate daya haka zata wuni tana jagalar shi. Tayi zuru-zuru ta fita hayyacin ta, ko hankalinta a kwance yake sai tayi kwana biyu bata share dakinta ba, shima idan AbdulKadir na gari ne sai tayi shara ta gyara gado. Daya tafi kuma tana hada sati dakinta baiga tsintsiya ba, yanzun kuwa a kwanaki biyar din nan ko wanke-wanke batayi ba, falon a hautsine yake da gwangwanin lemuka da robobin ruwa, dan tunda ta zo gidan shi rabon ta da shan pure water, inya bata kudi ruwan roba take zuwa ta siyo. 6
Ita kanta rabonta da wanka tun jiya, duniyar take ji ta hade mata waje daya. Yanzun da AbdulKadir din yake a gabanta, wata irin ajiyar zuciya take saukewa da bata san daga inda take fitowa ba, ta dauka hawayenta sun gama karewa, sai yanzun da taji idanuwanta sun ciko taf da hawaye. Bata taba tunanin bakin mutum zai iya kara baki ba sai yau, duk kumburin fuskar shi bai hana idanuwan shi yin zuru-zuru suna kara shigewa ciki ba. Gashi yayi wani irin dukun-dukun. Kallon ta kawai AbdulKadir yayi yana wucewa cikin dakin baccin su, kai tsaye bandaki ya wuce yana cire kayan da yasan sun rigada sun tashi aiki. 2
Bandakin yake gani yayi mishi kaca-kaca, ga kayan wanki saman injin wanki harda jiqaqqu, wanka yayi, ya saba jikin shi da sabulu yafi sau biyar amman duk da haka jin shi yake kamar akwai sauran dauda a jikin shi. Towel ya dauka yana goge jikin shi ya daura shi a kugun shi ya fito, idan yace ga asalin abinda yakeji karya yake, dan bayajin komai, zafin dukan da yake jikin shi, ko bacin rai, shiru komai yake mishi. A karo na farko da ko ganin Nuriyya din bai saka shi jin komai ba. Banda Waheedah babu abinda yake cikin kan shi. Takawa yayi yana fita daga dakin, a tsaye bakin kofa yaga Nuriyya tana kallon shi
STORY CONTINUES BELOW
“Masoyi…” 11
Ta fadi muryarta na rawa, fuskarta da bayanannen tsoro. Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta yana kara saka tsoro cika zuciyarta
“Dan Allah… Dan Allah kayi hakuri… Kaji… Bazan sake ba…. Dan Allah karka sakeni, kai mun komai karka sakeni, dan Allah…” 2
Numfashi nai nauyi AbdulKadir ya sauke, da gaske yake bayajin komai, ciki harda magana da ita, wucewa yayi da nufin karasawa bangaren Waheedah ya dauki kayan da zai saka. Bin bayan shi Nuriyya tayi tana kamo hannun shi, gabaki daya shirun shi ya kara rikitata 1
“Masoyi…”
Tsaye AbdulKadir yayi batare daya juyo ba, hannun shi yake kokarin zamewa daga cikin nata, ta sake kamashi tana matsawa ta zagaya ta fuskance shi, wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, tana saka shi tuna yanda ko kadan batasan shi ba, da ta kyale shi, ta nemi waje ta zauna, da bata tsaya a gaban shi tana mishi kukan da baiga dalilin shi ba. Numfashin ya sake saukewa 1
“Kaji… Dan Allah kayi hakuri…dan Allah… Wallahi ba zan sake ba”
Nuriyya take fadi kuka mai karfi na kwace mata, hannun shi AbdulKadir ya zare daga cikin nata, yana rabata ya wuce, jin takun tafiyarta yasa shi juyawa
“Bance kin mun wani abu ba, ban miki magana ba saboda bana son yin magana da kowa, ki kyaleni Nuriyya, ki kyaleni kafin mu samu matsala…”
AbdulKadir ya karashe maganar yana juyawa ya wuce, da idanuwa Nuriyya tabi shi, zatace yana da wata irin kula da ko a tunaninta ba tayi zaton zata samu a gidan aure ba, abinda duk ta nuna tana so yana kokarin yi mata, idan kudi ta tambayeshi yana bata, wani lokacin yana ce mata bashi da kudin da zai bata ta kashe, akwai hidimar da zaiyi. Sai dai akwai bangaren shi da takejin bata sani ba, sannan mutum ne shi mai wahalar sha’ani duk da ba sosai zaman su yake tsayi ba, inya dawo kwana biyune, ita daya, Waheedah daya, amman zatai karya idan tace bata takura da kwana dayan.
Bata cika tsawaita tunaninta akan abin bane kawai, amman AbdulKadir din da Waheedah kanyi magana ko da yaushe daban yake da ita wanda take gani. AbdulKadir din Waheedah namiji ne da ko a littafin hausa batajin akwai irin shi, dan mazan littafin hausa miskilai ne, AbdulKadir din Waheedah ba haka yake ba, AbdulKadir din Waheedah kan mata abu batare da ta tambaye shi ba, yana girmamata fiye da yanda take nunawa, dan Nuriyya da idanuwanta taga hakan. AbdulKadir din Waheedah bashi da wani hali marar kyau, ita shine mutumin da take so, mutumin da tayi tunanin ta aura. 13
Sai bayan auren da ta fara cin karo da kashedi a darenta na farko taji zuciyarta ta tsinke, sai kuma lokutta da dama da zaiyi tunanin tayi mishi abu tayi kokarin bayani ya rufeta da wani irin fada mai cin rai, kananun abubuwa masu tarin takaici da ba zaka gani daga nesa ba, ko kuma take tunanin AbdulKadir din Waheedah ba zai tabayi ba, sannan yana surutai cikin baccin shi, yana firgita sosai, ranar farko da hakan ta faru tsoron shi ta dingaji, musamman da tayi kokarin taba shi bayan ya farka ya hankadeta yana mata wani irin kashedi da har yau bata sake kokarin zuwa kusa dashi in yana surutan shi a bacci ba. 7
AbdulKadir na da matsalolin da take da tabbacin bata gama gani ba. Sai dai batasan ita kadai yake nunawa ba, ko harda Waheedah. Falonta ta koma ta zauna tana jin wasu hawaye masu dumi na zarya kan kuncinta. Ita dai yanzun koma me zaiyi indai bazai saketa ba da sauqi. 5
*
AbdulKadir yana sake kaya, dakin Nuriyya ya koma ya shiga bandaki yana daukar wandon daya cire ya zaro wayarshi da wallet, wayar da take a kashe ya kunna yana fitowa. Sakonni ne guda biyar suka shigo tana gama loading, budewa yayi, biyu daga MTN ne, daya bankin shine, yasan albashi ne, biyu kuma Yassar ne, ya shiga na farkon
‘Lafiyar ka kuwa? Wayarka a kashe. Duk da ba ina so ka zo ka dame ta bane, lafiyarka ko?’ 1
Fita yayi yana shiga dayan
STORY CONTINUES BELOW
‘Ka kashe wayarka ne, kayi shiru dan in daga hankalina in goyi bayanka ko AbdulKadir? Yayi maka kyau’ 4
Murmushi yadan yi duk da nishadi na daya daga cikin karshen abinda yakeji. Wallet din shi ya saka a aljihun shi. Ya samu waje gefen gadon yana zama, dan dayaga albashin shi bayaso su kwana baiyi hidindumun da zaiyi dasu ba. Waheedah ya fara turama kudin nata hidimar na wata kamar yanda ya saba, sannan ya tura ma Nuriyya ma, saiya tura wasu cikin account din shi na ajiyar kudin tsaron lalura. Ya turana Abba da Hajja. Kati ya tura ma sauran yan gidan kamar yanda ya saba duk watan duniya, ko yayane yakan tura musu. Wata natsuwa yaji ta daban daya sauke wannan nauyin. 9
Wancen watan daya fita ya karo musu kayan abinci, dan shi yake siyan su shinkafa da su taliya, sai mai. Kananun abubuwa ne yake basu kudin a hannunsu. Haka suke tsarin da Waheedah, Nuriyya ma data shigo bai canza ba. Duk da ita tana tambayar shi kudi, Waheedah kuma bazai tuna ranar karshe da ta tambayeshi kudi ba, inya dauka ya bata tana karba, in baibata ba bata taba tambayarshi. Na Nuriyyar baya damun shi sam, yakan yi mamakin abinda takeyi da kudi ne kawai wasu lokuttan.
Mikewa yayi ya saka wayar a aljihu, mukullin motar shi yagani ajiye akan drawer din kusa da gadon ta, ya dauka ya fito, ko inda take bai kalla ba ya taka yana ficewa daga gidan. Motar ya shiga ya tayar, kan shi tsaye gidan Yassar ya nufa, yana kallon yanda maigadin Yassar din ya kara sauri wajen bude gate din ganin motar tashi. Saurayine matashi, daga yanayin shi AbdulKadir din ya fuskanci yaron tsoron shi yakeji. Har cikin harabar gidan ya shiga da motar yanayin parking, tukunna ya taka yana karasawa cikin gidan. Sallama yake tayi baiji alamar akwai mutane ba. 1
Ranar aiki ce yasani, Yassar din zai yiwu yana wajen aiki, matar shi ma tana aiki a asibiti, bangaren accounting tunda abinda ta karanta kenan. Sai dai yasan Waheedah na nan, dan haka ya taka zuwa bangaren da ya sameta zuwan karshe da yayi. Kwankwasa dakin yayi tukunna ya tura hadi dayin sallama, kamshi na dukan hancin shi, duk da bana turarukanta bane ba, kamshin yai mishi dadi sosai. Wani irin tsalle zuciyar shi tayi naban mamaki ganin Waheedah a zaune, doguwar rigace ta atamfa a jikinta wani irin dinki da bazaice ga yanda yake ba, ta saka Ikram cikin jakar goyo ta goyata ta gaba tana tallabe da yarinyar da take bacci.
Kwalliya ce a fuskarta da ba koda yaushe takeyi ba, ta daura dankwalinta ya zauna das a saman kanta kamar a jiki akayi. Tana zaune gefen gado ta dora kafa daya kan daya, da plate din soyayyen dankali a gefenta da cokali mai yatsu a ciki, ta dora system din da yake zaton ta Yassar ce akan wani dan tebir tana kallo. Kafafuwanta yake kallo da suka sha zanen flower tayi wani irin ja mai duhu, kafin ya yawata da idanuwan shi yana tsayarwa kan hannunta daya dake tallafe da Ikram da shima yasha kunshin. 5
Kai ta dago tana kallon AbdulKadir din, zuciyarta na wata irin dokawa da wani sabon tashin hankalin da ta kwana biyar bataji shi ba, duk wani abu da su Yassar suka san zai dauke mata hankali ya rage mata tunani shi sukeyi mata. Har system din Hauwa dake cike da fina-finai daga American zuwa na indiya harda na korea da tafi so ta kawo mata, ta manta lokacin karshe data huta haka. Ji takeyi kamar tayi wata takwas rabonta da samun bacci mai nutsuwa, wata takwas rabon da ta zauna ta huta ma rayuwarta, rabon da tayi wani abu don kanta kawai. 6
Taji dadi da AbdulKadir din bai dameta ba, shisa ta kashe wayarta ta ajiye. Bashi kadai ba, har yan gidan su batason kowa yayi mata maganar, kuma kowa ya kyaleta. Yanzun ganin AbdulKadir din na mata barazana da dan kwanciyar hankalin da ta samu, dan jiya da akazo yiwa Hauwa kunshi itama yi mata akayi, jinta takeyi daban, kamar tabaro waccen Waheedahr a gidan AbdulKadir, yanzun kuma watace daban da batasan akwaita bama.
“Wahee…”
AbdulKadir ya kira da wani irin sanyin murya mai tattare da mamakin ganin hankalinta a kwance yake. Dan ganinta yasa komai dawo mishi, dukan da yasha a barikin sojoji da yake nan garin Kano, yunwar da yake tattare da ita ta kwanaki na rashin samun wadataccen abinci, rashin bacci, da duk wani rauni da baya iya nunawa a gaban kowa. Itama Waheedah kallon shi takeyi, tana kallon kumburin dake kasan idanuwan shi da tasan rashin bacci ne, da kuma wasu kumburin na alamun duka. A karo na farko a rayuwarta da taji halin da yake ciki bai dameta ba, ballantana harta tambaye shi ya akai ya shiga ciki. 22
STORY CONTINUES BELOW
Dauke idanuwanta tayi daga kan shi tana mayar da hankalinta kan kallon da takeyi, tana kai hannu ta dauki plate din dankalinta tana cigaba daci
“Waheedah…”
AbdulKadir din ya kira wannan karin cike da rashin yarda cewa ita din ce ta nuna mishi halin ko in kula, ita din ce ya shigo waje ta kalle shi taci gaba da wata hidimar kamar baya nan. Takawa yayi yana karasawa inda take ya zauna gefenta yana son ta sake ganin shi dinne 2
“Baki ganni bane?” 2
Ya tambaya yana kallon fuskarta da babu kowanne irin yanayi akai, dankalin data tauna ta hadiye tana tsayar da film dinta dan batason komai ya wuce ta. 4
“Naganka… Menene? Takardata ka kawomun?” 4
Wata irin dariya mai sauti AbdulKadir yaji ta subuce mishi, tabbas Waheedah na da aljanu, yana mamakin yanda akai basu taba tashi ba sai yanzun, film dinta ta dannama play tana mayar da hankalinta a kai. Hannuwan shi AbdulKadir ya saka fuskar shi a ciki yana fitar da wani irin numfashi, bashi da karfin yin ko hayaniyar kirki, duk wani kashi da yake jikin shi ciwo yake, yasan yanda ake dukan ma’aikata in na horo ne, sun san inda suke duka da zai shigeka batare daya ji maka ciwon da zai hanaka zuwa aiki washegari ba. Lokutta da dama ko fuskarka ba zata gwada alamun dukan da kaci ba.
Suna dukan inda uniform zai kare shatikan ko ciwukan. Sauke hannayen shi yayi yana rutsa idanuwan shi da yanda hakarkarin shi ya amsa, yasan ba karaya ko daya a jiki, amman wajen ya tara jini saboda dukan da yasha, bashi bane na farko, Waheedah kan sa towel da ruwa mai zafi ta gasa mishi ta bashi panadol ko da bayason sha. 2
“Kwanana biyar a barikin sojoji…” 4
AbdulKadir ya tsinci kanshi da fadi da wani irin sanyin murya, Waheedah batama ji shi ba, dan gabaki daya hankalinta ya tattaru kan kallon da takeyi, hannu AbdulKadir yakai yana rufe system, hakan yasa ta kalle shi 6
“Bana so, banma ga dalilin da zaka shigomun daki ka nemi dagamun hankali ba” 1
Murmushi AbdulKadir yayi
“Ina da duk wani dalili da zan shigo dakin nan, hankalina ba’a kwance yake ba, banga dalilin da zai sa naki ya kwanta ba Wahee, ke kika zabar mana wannan rayuwar…sannan ba dakinki bane wannan… Dakinki yana gidana” 7
Da kalar rigimar dake cikin idanuwan shi take kallon shi tana jin dai-dai take da duk wani abu daya shirya tarar ta dashi, gabaki daya yagama fita daga ranta, ko ganin shi batason yi, auren shi takeji kamar wata igiya data shake mata wuya tana hana mata yin numfashi a walwale, shisa take so ya datseta ya warware mata ko zata samu ta shaqi iska mai nutsuwa. 9
“Bani da daki a gidanka, bani da komai a gidan ka sai kayan da nake gab da zuwa in kwashe dan takardata zaka bani tunda babu inda aka taba aure dole” 3
Mikewa AbdulKadir yayi, ya dauka bashida karfin yin hayaniya, amman tunda can Waheedah tafi kowa damar bata mishi rai, bata amfani da wannan damar ne sai yanzun. 2
“Igiyar aurenki a hannuna take, yanzun kuma na fara rikon ta, kaya kuma Allah ya baki iko, kina jina? Allah ya baki iko dake da duk wanda yake da tsautsayin shigomun gida da nufin tayaki kwashe su… Aljanu ne kike dasu da bansani ba sai yanzun, to wallahi ko su ubansu yayi karya….ke da kanki ma kinyi karya kisani yin abinda banyi niyya ba” 6
Kallon shi Waheedah takeyi itama tana tsintar kanta da mikewa tsaye
“Ana dole ne? Nagaji… Nagaji da aurenka”
Cikin hargowa yace
“Ni bangaji ba, gajiyarki bata da wani muhimmanci” 6
Dariya Waheedah tayi tana jin duk wani kwanciyar hankali data samu a kwanakin nan na bace mata
STORY CONTINUES BELOW
“Abubuwa da yawa da suka shafeni basu da muhimmanci a wajenka daman, saboda haka banyi mamaki ba”
Cike da rashin fahimta AbdulKadir yake kallon ta
“Bangane abubuwa da suka shafeki ba suda muhimmanci a wajena ba”
Gyarama Ikram zama ta sakeyi a jikinta tana kara tallabeta
“Kwakwalwa ce a kanka duk da bako yaushe kake amfani da ita ba, sai kayi tunani ai” 28
Kallon ta AbdulKadir yakeyi, ya dauka ya gama shan mamakinta tunda ta iya bude baki ta nemi ya saketa, amman da duk wani gani da zai mata bayan haka da yanda take kara shayar dashi mamaki
“Zagina zakiyi Waheedah?” 2
Kai ta girgiza mishi, zagi ba dabi’arta bane tunda can, ko Fajr ma zata kirga lokuttan da ta zage shi balle shi AbdulKadir din
“Idan ba zagi ba, me maganganun ki suke nufi? Rashin kunya kike neman yimun da bansan lokacin da kika koyeta ba” 4
Yake karasa maganar da wani irin bacin rai marar misaltuwa
“Nifa ban zageka ba, rashin kunya kuma in dai koya nayi bai kamata kayi mamaki ba tunda nayi rayuwar aure da kai” 26
Da hannu yake nunata
“Gashi nan… Yanzun me kikayi.. Wani zagin ne wannan ai… Wallahi Waheedah ki kiyayeni, kina gwada hakurina… Kuma tashi zakiyi mu koma gida”
AbdulKadir yayi maganar yana son ture alamun da yakeji kamar na tsoro na son taso mishi, ga hankalin shi da yake a tashe kasan bacin ran da yake fama dashi, musamman da Waheedah tayi mishi wani irin kallo tana komawa ta zauna tare da fadin
“Saika daukeni ka dora saman kai ka mayar dani ai” 2
Kai AbdulKadir yake jinjina mata, inda take ya karasa, rashin hankali take nuna mishi karara, zai nuna mata duk abinda takeji dai-dai yake da ita. Belt din da yake kafadunta na jakar goyon yake kokarin ballewa, ta ture hannun shi
“Me kakeyi?”
Ta tambaya muryata cike da tsoro, hannuwanta AbdulKadir ya kama duka biyun yana saka karfi ya rike su, belt din ya kwance duk ihun da Waheedah take mishi, da hannu daya ya zame Ikram yana sauketa daga jikin Waheedah din
“Sadauki ka sakeni, dan Allah ka kyaleni, kaga Ikram na kuka”
Waheedah ta karasa tanajin idanuwanta sun ciko da hawaye duk yanda ta fadama kanta ta gama yi mishi kuka
“Ashe muryarki na sauka haka, harna manta saboda yanda kike dagamun ita a kwanakin nan”
Cewar AbdulKadir din yana kama hannuwanta da yake rike dasu ya dagota ya mikar tsaye, zuwa lokacin ta daina kiciniyar kwacewa, dagata yayi yana sabata a kafadar shi kamar ya dibi kayan wanki, yasa hannuwan shi yana mata rikon da tasan ko da wasa ba zata iya kwacewa ba, ikon Allah take saurare kawai tana tabbar da AbdulKadir na da tabin hankali, bata sani bane tuntuni sai yanzun. 3
“Wallahi ka saukeni, wannan kidnapping ne, shekara goma sha biyar zakayi a gidan yari” 2
Dariya AbdulKadir yayi, wannan karin tana fitowa daga bangaren zuciyarshi daya kwana biyu baiji ya buga mishi ba.
“Ka saukeni, bana son haka, ka saukeni…ko ka kaini ba zama zanyi ba Sadauki…na fada maka nagama aurenka”
Hanyar da zata fitar dashi daga dakin ya nufa yana bude kofar yaci karo da Yassar da ya miko hannu da alama yana shirin kwankwasa kofar ne koya bude. Dan tunda ta shigo gidan yakejin kamar maganganu shisa ya nufo bangaren Waheedah din, muryarta na tabbatar mishi da AbdulKadir na ciki. Yanayin maganganunta ne ya hanashi bankada kofar kar yaga abinda bai kamata ba, tunda yasan AbdulKadir ba hankali gare shi ba ballantana kunya. Sai dai baki a bude yake kallon AbdulKadir din 1
STORY CONTINUES BELOW
“Ka matsamun Hamma…”
Ya fadi yana gyara ma Waheedah zama a kafadar shi 1
“Me kakeyi AbdulKadir? Me kakeyi?”
Yassar yake tambaya yana kallon AbdulKadir din kamar a film, dan bai taba ganin abinda yakeyi a zahiri ba, cikin kuka Waheedah take fadin
“Hamma kace ya saukeni, dan Allah kayi mishi magana, ni bazan koma gidan shi ba…”
Muryar Yassar har lokacin da mamaki yace
“Ka sauketa AbdulKadir…. Ka sauketa tun kafin ranka ya baci”
Kankance idanuwa AbdulKadir yayi
“Ita tace in dauketa a kai in tafi da ita…” 3
Waheedah najin hawayen dake digar mata, ga kanta daya fara tara jini saboda yanayin yanda AbdulKadir din ya riketa
“Ni bance mai ba Hamma… Dan Allah kace ya saukeni”
Kokari Yassar yakeyi kar murmushi ya kwace mishi, idan AbdulKadir yaga alamar wasa koya take tattare da Yassar din bazai sauke Waheedah ba
“Ka sauketa nace maka AbdulKadir…”
Baisan ya akayi maganar Yassar din tayi tasiri akan shi ba. Sauketa yayi tana dafa kofar wajen jin zata fadi, tana tsayuwa sosai tasa hannu tana goge fuskarta, dankwalinta batasan ma lokacin daya fadi ba, ga wata irin matsananciyar kunyar Yassar din da ta kamata. Wani irin kallo ta watsa ma AbdulKadir din
“Aurenka ko na zobe ne sai ka rabu dani… Kuma wallahi saina fadama Abba” 1
Ta karashe maganar wasu hawayen takaici masu zafi na zubo mata. AbdulKadir kuwa Yassar ya kalla
“Kagani ko? Hamma kanajin irin rashin kunyar da take mun”
Hannu Yassar ya daga mishi
“Ka wuce ka tafi”
Kafada AbdulKadir ya makale
“Ni bangama magana da ita ba”
Kai Yassar ya girgiza yana sauke numfashi, so yake yabar wajen kafin dariya ta kwace mishi. 3
“Ka tabbata zakai mata magana kamar mai hankali?” 1
Kai AbdulKadir din ya daga mishi, saida Yassar din yadan tsaya tukunna ya juya. Kofar AbdulKadir ya tura yana mayar da hankalin shi kan Waheedah data dauki Ikram tana kokarin lallashin ta
“Babu ribar da zakici a fada dani Waheedah… Ki taho mu koma gida, na baki hakuri.. Kiyi hakuri dan Allah. Kizo mu koma… Kinga ni bana son yin fada dake” 4
Ya karasa maganar yana sauke muryarshi, amman a idanuwanta yake ganin yanda maganganun shi ko kadan basuyi tasiri ba, ci gaba yai da fadin
“Kinji Wahee… Kina ta dagamun hankali akan magana karama, Wallahi kwanana biyar a barikin sojojin garin nan, ki kalli fuskata, na manta rabona da wadataccen bacci balle abincin kirki…”
Yayi maganar yana kama rigar jikin shi ya daga mata, jinine yayi baqiqirin a gefen cikin shi da duka hakarkarin shi, tana kallo ya juya mata har bayan shi da nan ma jinin ne a kwance, kowanne irin duka akai mishi ba karami bane ba, zuciyarta takeji a bushe babu wani abu da take sonyi banda shakar numfashi batare da igiyar auren shi ta daure mata wuya ba. Sakin rigar shi AbdulKadir yayi 2
“Ban shigo da nufin yin fada dake ba, har kudin hidimar gida na tura miki dazun…” 2
Kalamai yake nema da zai lallasheta dasu, amman ya rasa, saboda basu taba fada ya wuce yini daya ba, koyace bata taba fada dashi ya wuce yini daya ba, tunda ba biye mishu takeyi ba, ita ta saba lallashin shi, shisa komai ya kwance mishi. Takawa yayi ya karasa yana kamo dayan hannunta da yake jikin Ikram yana sakata sake rike yarinyar sosai
“Kinga azumi ya kusa, saura kwanaki kadan, ana yafewa juna kafin azumi, bama kyau fada kafin azumi” 12
Cikin idanuwan shi Waheedah ta kalla
“Ka saukake mun kafin azumin…dan Allah Sadauki…kaji…ka sakeni in huta nima. Nagaji da auren ka” 3
Ta karasa maganar tana zame hannunta daga cikin nashi ta share kwallar data zubo mata. Wani irin numfashi AbdulKadir ya sauke yana juyawa ya fice daga dakin, bai tsaya ko ina ba sai cikin motar shi, tayar da ita yayi ya fita daga gidan Yassar, a gefen hanya yayi parking yana hade kan shi da abin tuqin motar. Kan shi ciwo yake da bashida alaka da yunwa ko rashin bacci. Wani irin tsoro yakeji da bai taba sanin akwai shi ba. Kalaman Waheedah ke mishi yawo da wani yanayi naban mamaki.
Batayi mishi maganar da hayaniya ba, asalima idanuwanta cike suke taf da hawaye, da neman alfarma, bata taba rokon wani abu a wajen shi ba, yaune yake ganin alamar tana rokon shi, kuma rokon farko daya shiga tsakanin su shine na ya rabata da auren shi, si take ya bude bakin shi ya furta mata kalaman da zasu warware igiyar da bai yarda an kullata tsakanin su ba saida nufin mutuwa ce kawai zata raba. Bai taba tunanin cewa zata roke shi wani abu da zai kasayi mata ba, kodan girman matsayinta a wajen shi, amman sai ta tambayeshi abinda yakejin duk duniya babu wanda ya isa ya sakashi yin shi. 6
Wani irin tsoro yakeji daya danne duk wani abu da yake damun shi. Lumshe idanuwan shi yayi yana hango yin rayuwa babu Waheedah, da sauri ya bude su yana dagowa daga jikin motar, dan jin shi yayi duniyar tai mishi wani irin girma, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi. Da aurenta yasan akwai abinda babu a rayuwar shi sai bayan ta shigota, daga randa igiyar aure ta hadasu zama a karkashin inuwa daya bai kara hasko wani lokaci a rayuwar shi da babu ita a ciki ba. Ko tunanin mutuwa yake bai taba hango zata riga shi ba, abu ne da tunanin shi ma baya hasaso mishi. 2
Film idan yana kallo indai za ai mutuwa, yafi son yaga mijinne ya mutu yabar matar, dan baisan yanda zaiyi da sauran rayuwar shi idan babu ita a ciki ba.
“Bazan iya sakinki ba Waheedah… Ko meye nai miki me zafi haka hakuri zakiyi ki dawo. Inke zaki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi… Bazan iya ba” 12
Ya karasa maganar yana dafa fuskarshi da duka hannuwan shi biyu. Yafi mintina talatin a cikin motar kafin ya tayar da ita yana nufar gida…!Tun daya tunkari kofar yake jin kauri ya cika mishi hanci, yana bude kofar ya saka kafafuwan shi cikin falon Waheedah yakejin kaurin na karuwa, bangaren Nuriyya ya karasa yana ganin hayakin dayake fitowa daga kitchen din ya turnuqe falon, gaban shi yaji yayi wata irin mummunar faduwa, da gudu ya shiga kitchen din, hayakin na shaqe mishi kafofin shige da ficen iska, yana soma tari, ta inda kaurin yake fitowa AbdulKadir ke nema. Kafin idanuwan shi sukai kan tukunyar da tayi wani irin baki. Hannu yakai yana kashe gas din ya fito daga kitchen din yana takawa zuwa dakin baccin Nuriyya. 3
Tunda AbdulKadir din ya fita, ta tashi tana dora ruwa ta zuba shinkafa a ciki dan ita ba tsayawa zatayi sai ruwan yayi zafi ba. Dawowa tayi ta dauki wayarta tana ganin text, dubawa tayi taga dubu arba’in, murmushi tayi hankalinta da yake a tashe taji ya kwanta. Daman ko da AbdulKadir din bai dawo ba ita ba tunanin abinda ya same shi ko abinda ake mishi ne a gabanta ba, tunanin abinda zai mata idan ya dawo shine matsalarta, tunda kuma ya tura mata kudi kamar yanda yakanyi duk wata, hakan na nuna alamar babu abinda zai faru. Ko fadama bai mata ba, shisa ta wuce dakin baccin. 5
Akwai wasu takalma da aka turo a group dinsu na mata da kawarta Safara’u ta sakata ciki, takalman sun mata kyau, har ta private Safara’u tai mata magana ko zata siya, sai dai ta kashe kudin hannunta tas, tayi niyyar ta nunama AbdulKadir din daman inya kwana biyu ya huta, sai ga Waheedah tazo tana asibiti ita kuma. Batasan cutar da har yanzun take damunta da bata warke bama, takalmin tace tana so dubu bakwai da dari biyar, ta tura kudin, saita turama Safara’u balance din atamfofin da ta dauka wancen watan dubu goma, ta kuma turama mai dinkinta shima dubu goma. Kafin wani lokaci dubu hudu ce ta rage mata a banki.
Kwanciya tayi kan gadon da yake a hargitse tana manta cewar ta dora wani girki tunda ba sabawa tayi ba. Hankalinta ya nutsu kan littafin DAN ADAM na Rufaida Omar da take karantawa, dan littafin saika nutsu zaka fahimce shi yanda ya kamata. Ranta kal take jin shi, ko kadan bataji shigowar AbdulKadir daya nutsar da hankalin shi kanta ba, ya dauka ma wani abinne ya sameta harta dora girki yai wannan kamun ko kaurin shi bataji ba.
“Nuriyya…”
AbdulKadir ya kira ranshi a matukar bace, da alama batama jishi ba, dan tayi rufda cikine da waya rike a hannunta
“Nuriyya!”
Ya sake kira da karfi wannan karin yana sakata juyowa a tsorace, ganin shine yasa ta tashi zaune tana ajiye wayar hadi da fadin
“Sannu da zuwa”
Da idanuwa AbdulKadir ya kafeta
“Bakida hankali ko? Baki da hankali zaki dora girki ki dawo daki ki zauna kina danna waya. Gobara kike son ki hadamun a gida Nuriyya?”
Gabanta ne yai wata irin mummunar faduwa tana mikewa tsaye
“Ina zakije?”
AbdulKadir ya bukata
“Wallahi na manta ne”
Ta amsa tana wani irin sauke murya da ya kara bata mishi rai
“Saboda girkin bashi bane a gabanki, ya zaki dora girki har yai wannan konewar kina fadamun kin manta”
Idanuwanta Nuriyya taji sun ciko da hawaye, ta manta ranar karshe da aka tusata gaba ana mata fada haka, daman shine in yana nan baya rasa abinda zatayi da zai mata fada.
“Masoyi mantuwa ce, kowa nayi kuma”
Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance a kanta, yanajin yanda ranshi yake kara baci, bazai dauki wata rashin kunyar bayan wadda Waheedah ta gama sauke mishi ba. Karasawa yayi ya kama hannunta yana fara janta zuwa hanyar da zata fita dasu daga dakin, binshi kawai Nuriyya take har kitchen din tana ganin hayakin da har lokacin bai gama fita ba 1
STORY CONTINUES BELOW
“Meye a hancinki? Danna waya yafi miki muhimmanci, ki kalli kitchen dinki, yaushe rabonki da shara Nuriyya? Wanke-wanke fa?”
Hannunta daya damka take murzawa da dayan, tana jin wani hawaye mai dumi ya zubo mata
“Karki mun kukan banza da bashida dalili wallahi…”
AbdulKadir din ya fada, dan bayason kukan banza. Rabata yayi ya wuce yana fita daga kitchen din, daki ya koma ya shiga bandaki, yana ganin yanda farin tiles din yai duqun-duqun, bangon har wani dallakin daudar da baisan ko tun ta yaushe bace ba, ga kayan wanki kaca-kaca. Tsintar kanshi yayi da kasa amfani da bandakin, ya fito yana ganin bedroom dinma a hargitse. Kai kawai ya girgiza yana tunanin kalar Nuriyya, inda zaman kallone ko danna waya babu wanda zai nuna mata. 5
Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga bandakin ya gama abinda zaiyi ya fito. Bangaren Nuriyyan ya koma ya zauna a falo yana dora kafafuwan shi kan kujera dan jin kasar da yake takawa kan kafet din. Yanajin kacafniyar kwanoninta a kitchen din. Da alama wanke-wanke take, aikam abinda takeyi kenan, ranta a bace yake, batasan yanda zata sake mishi maganar yar aiki ba, idan azumi yazo mata Waheedah bata dawo ba ta gama yawo tasani. Kugunta taji ya gaji lokacin data gama tana share kitchen din, fitowa tayi ta samu AbdulKadir din a zaune 3
“Yunwa nakeji nikam”
Ya fadi yana kallonta, dan zaman da yayi waje daya yasa yunwar taso mishi. Nuriyya kamar zatayi kuka tace
“Nikam me zan baka? Kaga abincin ne na dora ya kama, ko zaka yo mana takeaway?” 8
Kai ya girgiza mata, yanda yakeji bazai iya fita ba
“Ko indomie ki dafa mun, bazan iya fita ba Nuriyya”
Robobin lemukan ta karasa tsincewa dana ruwa tan komawa kitchen din, ranta inyai dubu ya gama baci. Ita har ranta batayi niyyar cin indomie ba, batama tunanin tana da indomie din, dubawa tayi, sauran data rage matace ta dafa jiya. Fitowa tayi tana kallon AbdulKadir din, muryarta can kasan makoshi tace
“Babu indomie”
Juyawa yayi yana kallonta da mamaki
“Baki siya bane wancen watan?”
Kai Nuriyya ta girgiza mishi, ita wancen watan kudin da ya batane gabaki daya ta tattara ta siyi zobon gwal karami, dubu biyu kawai ta cika. Babu abinda ta siya, ta dauka ma shi zai siyo musu. 8
“Ki duba kitchen din Waheedah”
AbdulKadir din ya fadi da alamar gajiya a muryarshi. Wucewa tayi ta dibo indomie din guda hudu ta dawo
“Masoyi”
Ta kira tana dorawa da
“Yaushe Waheedah zata dawo? Jikinne har yanzun?”
Kai AbdulKadir ya jinjina mata
“Zata dawo, tana gida….data kara warwarewa”
Wucewa Nuriyya tayi batare da tace mishi komai ba. Ranta ya kara baci ba kadan ba, ashe gida Waheedah ta wuce abinta saboda bakin hali. Nan da nan ta dafa indomie din, dan zatace duk a abinci ita kadai take dafawa babu wata matsala, a plate ta zubo musu ta saka cokula tana fitowa da ita ta ajiye, cokalin AbdulKadir ya dauka, duk yunwar da yakeji bata hanashi fadin 3
“Baki dafa mana kwai ba? Haka zamu ci?” 1
Batare da Nuriyya ta kalle shi ba tace
“Banda kwai ni”
Da alamar kosawa a muryarta, ta kula ba a iyama AbdulKadir din, ta samu waje ta zauna
“In zakiyi mana siyayyar azumi ki siyo mana, ina so ni fa”
STORY CONTINUES BELOW
Cewar AbdulKadir din yana fara dibo indomie din da tai mishi zafi yana jira ta huce, kallon shi Nuriyya take cike da rashin fahimta
“Bakai zaka siyo ba?”
Kai AbdulKadir ya girgiza mata
“Me yasa zan tura miki kudin idan ni zan siyo”
Hanjin cikinta Nuriyya taji sun tattaru sun kulle waje daya
“Wanne kudin?”
Ta tambaya cikin bayanannen tashin hankali, indomie din daya dibo yakai bakin shi ya tauna yana hadiye tukunna ya kalli Nuriyya
“Na tura miki dubu arba’in dazun, baki gani bane?”
Kai Nuriyya ta daga dan dakyar ta hadiye indomie din dake bakinta
“Na siyayya ne daman?”
Cikin rashin fahimta AbdulKadir yake kallonta kafin yace
“Nuriyya…”
Saboda yanayinta daya gani duk ta daburce, ya kirata ne yana tambayar ko lafiyarta, amman ita bata fahimce shi ba, ta dauka koya gane bata da gaskiya ne
“Wallahi bansan na siyayyar azumi bane Masoyi, nasan kana bani kyautar kudi” 5
Kallon nata AbdulKadir yakeyi, yana son fahimtar inda kalamanta suka dosa, kallon ne takejin yana kara rikitata
“Na siyi takalma a ciki, daman wancen watan akwai atamfofin dana dauka, shine na cika kudin…. Saina biya kudin dinki kuma” 2
Cokalin AbdulKadir ya ajiye cikin abincin yana kallon Nuriyya
“Bangane me kike cemun ba, kudin dana tura miki dazun dinne kika siyi su takalma da atamfofi?”
Kai Nuriyya ta daga mishi, cikin tashin hankali take fadin
“Dan Allah kayi hakuri, wallahi bansan na siyayya bane” 7
Kallonta AbdulKadir yake yana rasa abinda ya kamata yayi, ranshi da yake kokarin kwantarwa ne Nuriyya take ta batawa tunda ya shigo. Tsaye yake akan gidan shi, indai kayan sawa ne duk bayan wata biyu ko uku yake ba Waheedah kudi ko zata siya, itama Nuriyyar ya fara bayan watanta biyu da zuwa, to tana yawan tambayar shi kudi, ko zatayi ankon suna kona bikin kawayenta, ko zata siyi wani abin, shisa ya daina bata. Akwai kudin daya ware na siyayyar kayan sallar su daman.
“Kudin kayan abincinne kika siyi takalma dasu Nuriyya? Abinda duk nake miki bai isheki ba saikin tabamun wannan kudin?”
Kai Nuriyya ta girgiza mishi
“Baki da takalma? Baki da kayan sawa? Kin tambayeni kudin takalma na hanaki ne?”
AbdulKadir yake tambaya yana kallonta, kai kawai take girgiza mishi, mikewa AbdulKadir yayi abincin gabaki daya ya fita daga ranshi, itama Nuriyyar mikewa tayi tana dana sanin fada mishi, hannun shi zata kama yace
“In kika tabani saina mareki Nuriyya…” 6
Tsaye tayi tana zare idanuwanta da suke cike da rashin gaskiya
“Yau ya zama ranar karshe da zakimun amfani da kudin hidimar gida kan wani abu daban, wallahi ranki zai mugun baci tunda naga alama ke baki da hankali” 2
AbdulKadir ya karasa maganar ranshi a bace
“Dan Allah kayi hakuri”
Nuriyya ta fadi, wani irin kallo AbdulKadir din ya watsa mata, hakurin da take bashi ne yakejin yana kara bata mishi rai, wucewa yayi yana komawa bangaren Waheedah, dan idan yana ganin Nuriyya komai zai iya faruwa. Kan kujera ya kwanta yana lumshe idanuwan shi. Da Waheedah na nan ma koyayane zuciyarshi zatai sanyi, amman tayi tafiyarta saboda ta daina damuwa dashi, abinda yafi tsana fiye da komai ya tsinci kanshi tsundum a ciki, tunanin safiyar ranar da sukayi fada da ita. 3
STORY CONTINUES BELOW
*
Kwanan shi biyu da zuwa, yana kula da yanayinta tunda yazo. Shirunta ya mishi yawa, bai dai tambaya ba sai safiyar ranar tana kitchen tana soya musu fanke ya shiga yai tsaye yana jingina bayan shi da kantar kitchen din
“Wahee me yake damun ki?”
Ya tambaya, da wani nisantaccen yanayi a fuskarta ta girgiza mishi kai
“Lafiya ta kalau”
Ta fadi tana cigaba da aikinta, da idanuwa AbdulKadir din yake binta harta gama ta dauki kulolin tana wucewa falo. Har suka karya idanuwan shi na kanta, shirun nata tabashi yake har kasan zuciyarshi, ranar ta karbi girki, tunda hutu zaiyi kwanan shi biyu a wajen Nuriyya. Sake binta kitchen yayi ya samu tana wanke-wanke
“Shirunki yamun yawa”
Batare da ta kalle shi ba ta amsa a takaice
“Babu komai”
Kasa fita yayi daga kitchen din harta gama wanke-wanke tana goge kitchen din, ta dauki karamin towel na goge-goge ta sake fitowa falo, AbdulKadir din na binta. Tana jin shi, batada abinda zatace mishi, bata kuma jin yin surutun, yana tsaye Nuriyya ta fito tana fadin
“Masoyi…”
Goge-gogenta Waheedah ta cigaba dayi duk da zuciyarta da takejin kamar zata bude kirjinta ta fito, ta gefen idanuwanta taga Nuriyyar ta karaso ta kama hannun AbdulKadir din tana saka wani irin tukukin kishi taso mata. Batasan me suke cewa ba saboda zafin da kirjinta yakeyi ya dauke mata hankali daga kan su. Bayau ta fara gani ba, wani lokaci suna zaune a kujera Nuriyyar zata fito daga bangarenta tazo ta zauna gefen AbdulKadir din, ko ta kwantar da kanta a jikin shi, ko ta rike hannun shi, duk wani abu da jikinsu zai hadu a gaban Waheedah din ta kula shi takeyi. 6
Bata taba daga kai ta kalle su ba, ballantana tayi magana, tasan idan aka tsaya tambayarta kalar soyayyar da take yiwa AbdulKadir ba zata iya misaltata ba. Sai dai koda wasa batayi tunanin tana da zafin kishi ba sai da taga Nuriyya a kusa da shi. Bata kara sanin zafin kishinta ya girmama ba sai lokacin da AbdulKadir din ya fara mata hirar Nuriyya da batason ji, baya kuma kula da bata tanka mishi duk idan yanayi. Ko film take kallo in sun kalla da Nuriyya saiya fara bata labari har abinda Nuriyya din ta fada kan film din. 3
Babu abinda tagaji dashi sai yanda ran girkinta ko ba ranar girkinta ba sai dai tagansu a bangarenta zaune suna jira tagama girki suci, idan girkin Nuriyya dinne ma inta zuba musu tare suke ci mata abinci a falo. Bata taba jin tagaji dasu biyun ba irin wannan karin, daga Nuriyyar har shi AbdulKadir din daya kwaso mata ita ya ajiye mata a gida tagaji dasu, ko ganin su bata son yi. Ji take idan bata dan fita tasha iska koyaya ba komai zai iya faruwa. 18
Tanajin kamar daga randa Nuriyya ta shigo gidan wani abu mai kama da bomb ya kunnu a cikin jikinta, abinda ganin Nuriyyar da AbdulKadir ke karama gudun lokacin fashewa, yanzun tanajin yana gab da tarwatsewa kuma ba zaiyi kyau ba. Muryar AbdulKadir din taji yana fadin
“Wai zata fitane da, kuma ta fasa” 1
Dagowa Waheedah tayi tana kallon shi, kafin taji Fajr ya riko mata hannu
“Omma banga socks ba, nasa uniform din”
Kai ta jinjina mishi
“Zan duba idan na shiga daki Fajr”
Sakin hannunta yaron yayi yana komawa kan kujera inda ta kwantar da Ikram
“Karka tasar mun yarinya bangama aikina ba”
Tace mishi, hakan yasa shi matsawa gefe ya zauna. Hankalinta ta mayar kan AbdulKadir
“Zanje gida anjima…”
STORY CONTINUES BELOW
Tana kallon yanda yake girgiza mata kai tun kafin ta karasa maganar
“Zaki barni ni kadai… A’a kam, ba yau ba Wahee”
Cikin idanuwa ta kalle shi wannan karin
“Ni ina so inje, dan Allah kabarni”
Ta karasa maganar wani abu na mata tsaye a makoshi, kai AbdulKadir ya kara girgiza mata
“Karma mu fara jan maganar nan, ba zakije ba” 1
Hawaye taji sun cika mata idanuwa da take da tabbacin basu da alaka da hanata fita da yayi, kawai tagajine har cikin kasusuwan jikinta 1
“Gaskiya Sadauki sai naje… Ina so inje gida nikam”
Da bayanannen mamaki a fuskar shi AbdulKadir yake kallon ta, bata taba mishi magana da wannan yanayin ba, baya kuma son ta fara
“Ba zakije ba to”
Ya fadi yana kankance mata idanuwanshi, sai dai rikicin da yake cikin nata yafi nashi
“Zamu gani”
Ta fadi tana juyawa da nufin komawa kitchen ta wanke towel din da yake hannunta
“Me kika ce?”
AbdulKadir din ya tambaya ranshi a bace, juyowa tayi tana saka idanuwanta cikin nashi
“Kajini ai, ca nayi zamu gani”
Murmushi AbdulKadir yayi me sauti
“Zamu ga me?”
Ya tambaya, wuce shi Waheedah tayi ta ajiye towel din tana fitowa, bataso kome takeji ya tarwatse mata cikin gidan. Ta gaban AbdulKadir din tazo wucewa
“Bafa inda zakije Waheedah…kinjini ai”
Ikram ta gyarama kwanciya, ganin kamar zata fado tana cewa
“Sai kai tayi kuma”
Sosai AbdulKadir yake kallonta
“Rashin kunya zakimun Waheedah?”
Ya tambaya yanajin kanshi har dumi yake dauka saboda bacin rai, dagowa tayi tana matsowa kusa dashi
“Idan rashin kunya nai maka me zai faru?” 4
Mamakin da yakeji ne yake kokarin danne yanda ranshi yake tafasa, da za’a tambayeshi zaice babu rana daya da Waheedah zata iya daga mishi murya balle harta kalli cikin idanuwan shi tana fada mishi magana. Murmushin takaici ya sake kwace mishi, juyawa yayi da nufin yabar mata dakin, dan komai zai iya faruwa yaji tace 1
“Na dauka wani abin zakayi ai…”
Baisan me ya shiga kanta haka ba, har tambayarta yayi da yaga kamar wani abin yana damunta tace mishi bakomai
“Waheedah ki kiyayeni, Allah ki kiyayeni, karkice zaki fara mun rashin kunya. Gidane ba zakije ba, duk kwanan nan ma babu inda zakije, ba gida kawai ba ko ina ne ma”
Dariya Waheedah tayi da take nuna mishi shidin bai isa ba, tana kara bata mishi rai
“Lallai…”
Ta fadi tana sakeyin wata dariyar, runtsa idanuwan shi yayi yana budesu a kanta, ranshi in yayi dubu a bace yake, ya manta ranar karshe da wani abu ya bata mishi rai irin hakan, bayajin ma a duniyar shi gabaki daya akwai wanda ya isa ya bata mishi rai har haka, sai dai ita din.
“Ban isa ba kenan ko me kike son ce mun?”
Ganin kallon da take mishi ya tabbatar mishi da abinda take nufi kenan
“Waheedah…”
Ya fadi cike da kashedi
“Meye Sadauki? Nifa sai na fita, kaji na fada maka ma”
STORY CONTINUES BELOW
Juyawar yayi yana soma tafiya, gidan zai bar mata gabaki daya, idan ya daina jin bazai dauke ta da mari ba sai ya dawo yaji ta inda rashin kunyar nan da ba halinta bane take fitowa. Bin shi Waheedah tayi tana riko hannun shi, in bata fita ta shaki wata iska daban da ta gidan ba tanajin matsala zata samu, kirjinta zafi yake
“Kace mun inje ni dai, kaji… Dan Allah”
Hannun shi ya zame daga cikin nata
“Ki sakeni kafin in mareki”
Wannan karin mamakine karara fuskar ta
“Saboda zan fita shine zaka mareni? To ka mareni dan Allah… Ka mareni kaga in zai hanani fita”
Hannun shi AbdulKadir ya zame yana ci gaba da tafiya, sake riko shi tayi, ko kadan baisan ya akai hannun shi ya sauka kan fuskarta ba yana hadawa da tureta, ya manta yanda ko kadan bata da kwarin kirki, kafin ya rikota takai kasa kanta na buguwa da table din da yake ajiye a wajen, lokacin dayai kasa yana rikota har jini ya fara taruwa inda da alama ta fasa kanta ne. A rikice yake girgizata 4
“Waheedah…Waheedah…”
Tunda yake a duniya bai tunanin zaiga tashin hankali kalar wanda yake gani yanzun da take rike a hannun shi kamar bata numfashi ba. Baiyi tunanin akwai abinda zai gigita shi kamar wannan gigitar ba, sai yanzun da yakejin duniyar ta hade mishi waje daya. 2
*
Gyara kwanciya yayi yana sauke wani irin numfashi, kuskurene yayi da baisan ta inda zai fara gyarashi ba, na lokacin ya manta yanda Waheedah matarshi ba kanwarshi ba, da tana kanwar shi har lokacin zai dauketa ya kaita asibiti, in taji sauki suka dawo gida zaisa cable ya zani rashin kunyar da tai mishi, ya kuma zane wadda takejin zatayi mishi a gaba. Amman matarshi ce, baisan da wanne ido zai kalli Abba idan ta fada mishi ya mareta ba, dan a gaban shi Abba kan fadi duk namijin daya daga ma yarinyar shi hannu ya sani sai dai kaddara amman ya daki auren shi.
Sai dai ya bata hakuri, ya kamata ta hakura, ta sake bashi wata damar, kome zata ce mishi, duk rashin kunyar da zatayi mishi ba zaima kulata ba ballantana ya daga mata hannu. Tashi zaune AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da hannuwan shi biyun, komai yakeji ya hade mishi waje daya, baisan dame zaiji ba, ranshi dayake bace da Nuriyya da ko kadan bata kula hankalin shi ba’a kwance yake ba ta kara bata mishi rai, ko da Waheedah da ta hargitsa duk wani kwanciyar hankalin shi. 3
Yasan da baiyi rashin kunya lokacin da aka bashi damar yin bayanin karar shi da Major yakai ba, da wahala ma ya kwana, tunda bayani kawai zaiyi suce mishi yaja ma matar shi kunne, sai yaba Major hakuri, amman bazai iya wannan ba. Rashin kunya ya tsula har Major din ya sa mishi hannu, da sukayi detaining din shi kuma ya sake jibgar wani a cikin cell din. Shisa yai kwanakin da yayi, gashi sai yanzun yakejin ciwon da jikin shi yake mishi. 8
Waheedah ko wannan bata duba ba take kara kallon idanuwan shi tana cewa ya rabu da ita, shikam bashi da wannan zuciyar, hakuri zatayi ta yafe mishi ta dawo suyi zaman su. Dan shi bazai taba iya rabuwa da ita ba. Yanzun ma ji yake yanda ranshi yake a bace in bai ganta ba akwai matsala, wata irin kewarta yakeji tana danne shi kamar bai ganta awanni kadan da suka wuce ba, a gigice yakejin rayuwar shi da wata irin rashin nutsuwa da kusancin Waheedah kawai yake samar mishi. Tashi yayi yana laluba aljihun shi yaji mukullan motar shi suna ciki. Ficewa yayi daga gidan ya shiga mota, wajen Abba zashi, in Waheedah bata dawo gidan shi yajita a kusa dashi ba yau baisan yanda zaiyi da tunani ba. 2
*
Tsintar kan shi yayi da kasa nufar bangaren Abba kai tsaye, dan haka ya wuce wajen Hajja, a falo ya sameta zaune da remote a hannunta, Zainab da itace Autarta kuma tana aji daya a jami’a a yanzun tana zaune gefen Hajja din
“Hamma ina wuni”
Ta fadi bayan Hajja ta amsa sallamar AbdulKadir din, kai kawai yadan daga ma Zainab din data mike tabar musu falon. Inda ta tashi AbdulKadir ya koma ya zauna, yana dafe kan shi cikin hannuwan shi dan ya rasa abinda zaice. Kallon shi Hajja tayi, tunda ya shigo tagan shi a firgice, kamar ba AbdulKadir din ta ba, kamar ba sojan gidanta ba, cikin kwanaki bakwai gabaki daya ya fita hayyacin shi. Ba zatace auren soyayya sukai da Alhaji Ahmad ba, asalima baifi sau biyu tagan shi kafin a tsayar da maganar auren su ba.
Ba kuma kasafai take fahimtar soyayya irin ta yaran yanzun ba, amman akan AbdulKadir da Waheedah tasan cewa kaddarar data hadasu mai girma ce, dan ko ita sosai ta jinjina al’amarin sanin yanda Waheedah take da sanyin hali, shekarun da taga suna wucewa batare da matsala ko daya daga gidan AbdulKadir din ba ya nutsar da hankalinta, ta sake jinjina kaddarar zamansu lokacin da taji ya auri Nuriyya, duk idan taga Waheedah a gidan sai taita kallonta tana mamakin yanda ta shanye wannan cin amanar.
Dan ita kam tasan ba zata iya ba, da saninta ma a auren Alhaji Ahmad saida takai zuciya nesa, har gobe kishin sauran matan shi kan motsa mata ba kadan ba, shisa batason wani abu ya sami auren dan nata da Waheedah, babu macen da zata iya zama dashi tana da wannan tabbacin, Nuriyyar ma ba baki tai musu ba, babu inda auren zaije ko bana cin amana bane, saboda ta kula da yarinyar tana da ji dakai da son abin duniya.
“AbdulKadir…”
Hajja ta kira tana ganin ya dago fuska yana sauke mata kananun idanuwan shi
“Kaci abinci?”
Kai ya girgiza mata, yunwar ma ya nemeta ya rasa. Mikewa Hajja tayi, da sauri AbdulKadir din yace
“Hajja na rasa yanda zanyi…na bata hakuri Hajja… Bansan ya zanyi ba kuma. Wallahi bazan iya rabuwa da ita ba” 4
Numfashi Hajja ta sauke, tausayin shi na cika mata zuciya. Kitchen ta wuce ta zuba mishi shinkafa da miya da lettuce. Ta dawo tana mika mishi, karbar plate din yayi ya ajiye akan kafet
“Ba abinci ba Hajja… Matata…” 12
Numfashin Hajja ta sake saukewa
“Kaci abincin AbdulKadir… Zan roki Abbanku sai a bata hakuri kaji…”
Kallon Hajja yake
“Za’a bata hakuri da gaske? Abba yace ba zai saka baki ba fa… Hajja haka yace ya daina saka baki a lamurrana, dan Allah shima ki bashi hakuri… Nikam rayuwata na cikin wani yanayi” 3
Yanda ya karasa maganar takeji har cikin ranta, bata taba ganin dan nata yayi laushi haka ba, da bakin shi yake kiran a bama Abba hakuri yau, tura takai bango. Shisa take jinjina ma kokarin maza, zasu dauki shekaru suna musgunawa mace, ko a fuskarta da wahala a gane, amman rana daya idan ta ware ta rama sai kagani a fuskar shi namijin. Sai kaji an fara bata rashin gaskiya saboda halittarta da juriya aka santa. Yanzun wanda duk zaiga AbdulKadir din saiya tausaya mishi, da yawama zasu manta cewa koma me yake faruwa dashi yanzun laifin shine, wasu ma zasu ce me yasa Waheedah ba zata hakura ba tunda harya bude baki ya bata hakuri. 3
Amman yarinyar kawai tasan abinda ta hadiya tunda har take neman ya saukake mata
“Kaci abinci AbdulKadir, zan ma Abban naka magana”
Kai AbdulKadir ya jinjina mata, shi abincin ma yau ba damun shi yayi ba. Sai da Hajja ta sake dauko plate din ta mika mishi a hannun shi, cakudawa yayi gabaki dayan shi ya fara ci, taunawa yake yana hadiyewa da wani irin nisantaccen yanayi shimfide a fuskar shi…!A waya Hajja ta kira mishi Abba, amman ca yayi bayason ganin AbdulKadir din, idan sulhu yake nema yaje wajen Waheedah, shi kam ba zai saka musu baki ba. Da wani irin sanyin jiki AbdulKadir yabar gidan. Amman tsintar kan shi yayi da nufar hanyar gidan Yassar, ba zai iya zuwa gida ba, har a kasusuwan shi yakejin bukatar Waheedah a kusa dashi. Bai taba zaton zaiyi kewarta irin haka ba, ko watannin da yakan shafe batare da ita ba, inya tuna cewar tana gidan shi, tana jiran komawar shi kan nutsar da wani bangare na zuciyar shi. +
Amman yau yana gari daya da ita, da auren shi a kanta ace ta kwana bakwai bata cikin gidan shi, gidan su, abin yana ci mishi zuciya fiye da yanda zai iya fadi. Gidan Yassar ya karasa yana parking din motarshi, a jiki yabar mukullin yana fitowa, ya karasa bakin kofa yaci karo da Yassar din da yake girgiza kai 5
“AbdulKadir…”
Katse shi AbdulKadir yayi da fadin
“Hamma dan Allah, banajin tashin hankali, magana kawai zan mata, dan Allah karka cemun wani abu, na roke ka” 4
Da bayanannen mamaki Yassar yake kallon AbdulKadir, yasan kaf gidan su daga su Hajja sai shi AbdulKadir kan dagawa kafa lokutta da dama, amman Yassar yasan su Hajja kawai yake saukewa murya irin haka, ya kasa yarda da AbdulKadir ne a gabanshi yake rokon shi alfarma yau. Mutane kan ce in da ranka ka sha kallo, kallon yake sha yanzun. Rabashi AbdulKadir yayi yana wucewa cikin gidan, yaji dadi da baici karo da Hauwa ba har ya karasa dakin da Waheedah take ya kwankwasa tukunna ya murza hannun kofar yana shiga. 3
Ta sake kaya, rigar bacci ce a jikinta, doguwa har kasa. Kalar rigar bata dami AbdulKadir ba, idanuwan shi na kan fuskar Waheedah da take kallon shi da gajiya shimfide cikin idanuwanta, takawa yayi ya karasa gefen gadon yana kama hannuwanta ya dumtse cikin nashi
“Me yasa zaki karya alkawarin ki? Kince ba zaki barni ba, da bakin ki kin sha fadamun zaki kasance tare dani…. Wahee in ke zaki iya barina ni bazan iya barin ki ba…. Wallahi ba zan iya ba”
Kallon shi Waheedah take tunda ya fara magana, amman zuciyarta a bushe take ballantana kalaman shi suyi mata tasiri, a hankali ta tara abinda ya kawota inda take yanzun, batajin akwai kalaman da zasu canza ra’ayinta. Hakan AbdulKadir ya kula dashi, ya sake dumtse hannuwanta da ta fara zamewa daga cikin na shi. 4
“Waheedah ni ne fa, ki kalle ni, ni ne, ban aureki dan in rabu dake ba…”
Ya karasa maganar da wani nisantaccen yanayi a muryar shi, yana kasa yarda Waheedah ce take son barin shi. Yana tuna lokacin da aiki ya kaishi tsakiyar inda ake tarzomar yan boko haram a Maiduguri.
*
Ta dauka tashin hankalinta kan aikin shi ya fara tsagaitawa, sai da aikin ya daukar mata miji yayi Maiduguri da shi. Tana da cikin Fajr wata kusan bakwai. Ko yaushe wajen awo ca suke mata ta kwantar da hankalinta, amman tasan ita da kwanciyar hankali sunyi hannun riga har sai AbdulKadir ya dawo gida. Kasancewar in da suke babu network, duk Asabar yana samu ya fito ya kirata, idan bai kirata ba, wani idan ya fito cikin abokan aikin nashi zai turo mata da sakon AbdulKadir din. Yanda kwanaki kan wuce mata tsakanin Asabar zuwa wata Asabar din ba zatace ba.
Sai dai duk wani tashin hankali da take tunanin ta taba shiga, ko ta taba jin labari bai kai wanda take ciki a yanzun da satika uku suka wuce batare da labarin AbdulKadir ba, wata na hudu yake nema lokacin a Maiduguri, bai kuma taba wuce sati biyu bataji daga wajen shi ba. Ya fada mata idan sati hudu suka wuce bai kira ba, ko sakon cewar yana lafiya bai sameta ba, to wani abin ya faru dashi, tayi mishi addu’a. Kukanta bai tsananta ba sai da satika hudun suka cika babu labarin AbdulKadir, musamman da su Hajja suka fara kiranta suji ko AbdulKadir din ya kira, Anty ma ca tayi zata zo ta dauketa su koma gida, tunda ga cikin ya tsufa, ga kuma tashin hankali, sai dai ba zasu gane ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ba gida take son zuwa ba, mijinta take son sanin yana lafiya. Ba zata ce ga abinda take tunani ba, safiyar asabar din da AbdulKadir ya cika sati biyar bai kirata ba. Zata iya tuna sauka daga kan gado ta shiga bandaki, yanda tayi wanka bata sani ba, dan hankalinta yayi nisan da ba zata iya taro shi ba. Da kayan data shiga bandaki ta fito, hijab kawai ta dora a saman su, ta dauki jakarta tana zuba duka kudin data ciro na hidimar gida a ciki, ta saka wayarta da bata da wani amfani yanzun a wajenta ta dauki jakar, takalma ta karasa ta zira a kafafuwanta, batare data kula na wanka bane.
Lokaci zuwa lokaci take share kwallar dake bin fuskarta. Maiduguri zataje neman shi, batasan ina yake a Maiduguri din ba, amman zaifi mata zaman da zatayi cikin gida batare da sanin halin da yake ciki ba. Fita tayi daga gidan, tana tsaye tana kulle gidan da rashin nutsuwa yasa ta kasa saka mukullin a mazaunin shi harta rufe gidan, ga idanuwanta da suke cike taf da hawaye, a cikin kanta kawai ta kasa yarda tayi tunanin cewar wani abu ya sami AbdulKadir din. 8
“Wahee….”
Taji muryarshi cikin kanta, dan jim tayi na wasu dakika, kafin ta share wasu hawaye masu dumin gaske da suka zubo mata, jin muryarshi cikin kanta ba bakon abu bane ba, yau dinne tajita kurkusa sosai.
“Waheedah…”
Ta sake ji ya kira, juyawa tayi tana sauke idanuwanta akan AbdulKadir dayake tsaye, duka hannuwanta biyu ta saka wannan karin ta share hawayen fuskarta, tsaye yake cikin uniform harda hularsu ta sojoji, hana sallah a saman kan shi, hannun shi daya rike da jaka.
“Yanzun kuma gizo kake mun Sadauki?”
Ta furta wasu sababbin hawayen na sake zubo mata. Kai AbdulKadir ya girgiza mata, yana jin da akwai sauran hawaye tattare dashi babu abinda zai hanasu zuba, ya riga ya fitar da rai da sake ganinta, tashin hankalin da ya gani a watannin bai dauka zai fito da ran shi ba, inya fito da ran nashi ma bai dauka batare da wata nakasa ba. Duk da akwai tabbai na tsofin ciwuka da sababbin da ko warkewa basu gama yi ba, dan dinkine waje hudu a fuskar shi, akwai wasu guda uku cikin kan shi da hular da ya saka ta boye. Sai jikin hannuwan shi da cikin shi. Sai dai ganin Waheedah ya saka duk wani radadi da zugi da yakeji bace mishi. 1
“Waheedah”
Ya kira a karo na uku, yana kallon yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike taf da hawaye, kafin ta soma kokawa da numfashinta cikin yanayin da yasaka shi karasawa yana riko damtsen hannunta, amman har lokacin kokawa take da daidaiton numfashinta, da gaske AbdulKadir din ne a gabanta, ba gizo yake mata ba, jikinta ko ina bari yake, batasan ta yarda jakar da take hannunta ba, tana saka hannunta kan fuskar shi cike da son tabbatar ma kanta shine. 1
“Sadauki…”
Ta kira wani irin kuka me sauti na kwace mata, hannuwan shi AbdulKadir din ya zagaya yana riketa gam, batare da damuwa da yanda katon cikinta yake tokare shi yana hana mishi riketa yanda ya kamata. Kuka take da yasa ko ina na jikinta bari.
“Babu abinda ya sameni Waheedah…. Gani… Babu abinda ya sameni”
AbdulKadir yake fadi yana jijjigata, kukan da take yana taba zuciyarshi, sai da ya tabbatar jikinta ya daina bari tukunna ya dauki jakarta, har lokacin tana jikin shi, da dabara ya jasu yana bude kofar suka shiga cikin gidan, jakunkunan ya ajiye, yana kama hannun Waheedah da take sauke ajiyar zuciya ya zaunar da ita a kasa, yana kallon yanda sai da dabara ta samu ta zauna. Ruwa yaje ya zubo a kofi ya kawo yana bata, da sauri ta karba ta shanye tas tana mika mishi kofin, ajiyewa yayi a gefe ya zauna. Ko takalman kafarshi bai yunkurin cirewa ba, kanta Waheedah ta kwantar a jikin shi, ya kara matsawa yana riketa a jikin shi sosai.
Idanuwan shi ya lumshe yana jero duk wata addu’a ta godiya ga Allah daya dawo dashi gida lafiya, ya bashi damar rike matar shi a jikin shi haka. Dayan hannun shi ya dago ya dora kan cikinta, saida ya sumbaci kanta tukunna yace
STORY CONTINUES BELOW
“Ya kuke?”
Hannu Waheedah takai ta share wasu hawayen da tambayar AbdulKadir din ta fito dasu, muryarta a dishe saboda kukan da tasha ta amsa shi da fadin
“Ka tsorata mu, Sadauki ka tsoratani”
Sumbatarta ya sakeyi yana riketa gam a jikin shi. Cikin kuka tace
“Karka barni, dan Allah karka barni, bansan inda zan saka rayuwata ba, banma san ta inda zan farata babu kai a ciki ba”
Shiru yayi, baya yarda bakin shi ya bude da alkawarin da bashida ikon cikawa a tsakanin su, tunda rayuwar ba a hannun shi take ba, a lokacin cikin kan shi ya roki Allah ya bashi aron rayuwa mai tsayi a tare da ita. 1
“Ina zaki je da?”
Ya bukata cikin sanyin murya
“Maiduguri”
Waheedah ta amsa tana saka AbdulKadir din kallonta da murmushi a fuskar shi
“Bansan me zanyi bane ba…baka barni da zabi da yawa ba”
Kai AbdulKadir yake girgizawa, Waheedah da ko bindiga ya shigo da ita gidan inta sani sai dai bindigar ta kwana wani daki, su su kwana dakinsu daban. Itace zata bishi Maiduguri
“Baki da hankali ko? Ta ina zaki fara nemana?” 1
Kafadunta ta daga mishi, itama bata sani ba, binshi dinne abinda ya fara zuwa mata a kai
“Karki kara tunanin yin wannan kasadar”
Jin tayi shiru yasa AbdulKadir dagota daga jikin shi yana kallon cikin idanuwanta
“Da gaske nake Waheedah…”
AbdulKadir ya fadi yana dorawa da
“Bambanci kowacce rana na tare da yanda take kara kusantani dake” 2
Dan sanin cewa tana gida tana jiran shi ya ishe shi kwanciyar hankali
“Nutsuwar da take ragemun shine sanin kina lafiya, kina gida a kwance, kina lafiya, karki hargitsamun da tunanin ko kina shirin bina inda nake. Kullum maganarki kar in barki… Kin taba tunanin ke idan kika barni ya zanyi?”
Yanayin dake fuskar shi yasa idanuwanta sake cika da hawaye
“Babu inda zani, bazan barka ba, mutuwa ce kawai abinda zata saka in barka” 1
Ta tabbatar mishi tana saka shi jinjina mata kan shi kafin ya riketa a jikin shi.
*
Yanzun ma hannunta ya dago yana dorawa kan fuskar shi
“Kin ce babu inda zaki barni, me yasa kika bari na yarda da hakan bayan kinsan karya kike?” 4
Hannuwanta take zamewa daga cikin nashi, wannan karin bai hanata ba, wata irin gajiya yakeji har cikin zuciyar shi, numfashi ya sauke kirjin shi na wani irin ciwo. Cikin sanyin murya yace
“Fajr fa?”
So takeyi ta amsa shi, yanayin shi takejin kamar zaiyi tasiri a kanta, shisa ta zabi yin shiru. Dan ko kusa bata tunanin komawa gidan shi, tana jin shi ya mika hannu ya dauki Ikram dake bacci, rike yarinyar AbdulKadir yayi a jikin shi, ya nutsu yana kallon yanda take bacci batare da tunani ko damuwar wani abu ba, yanajin kamar suyi musayar matsayi da yarinyar, ya kai mintina biyar a zaune a wajen, kafin ya mayar da Ikram inda ya dauketa. Numfashi yaja yana sake fitar dashi, kafin ya mike, Waheedah yake kallo da taki dago fuskarta ballantana su hada idanuwa. 4
“Sai da safe Wahee, kiyi hakuri nikam, bazan iya fadan nan ba wallahi, dan Allah kiyi hakuri. Zan dawo gobe in shaa Allah, ki kula da ku” 7
AbdulKadir ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga dakin yana nufar hanyar da zata fitar dashi zuwa harabar gidan. Ko da ya shiga motar shi ya dade zaune a ciki, ya hade kan shi da abin tuqin yana rasa abinda ya kamata yayi, rayuwa bata taba gwada karfin halin shi ta irin wannan fannin ba, yanzun da hakan ya faru yake gane shi raggo ne na gaske, dan kam bayajin zai iya jurewa. Tuqi yake a karo na farko ba tare da nutsuwa ba, yanajin mutane na zagin shi, bata su yake ba, gida kawai yake son karasawa batare daya kashe wani ko wani ya kashe shi ba, daya gan shi cikin gida ma bazai ce ga yanda ya karasa ba. Mukullin a jiki yabar shi tunda ya shigo da motar, ya wuce cikin gida, kan shi tsaye ya nufi bagaren Waheedah, bedroom ya shiga ya kwanta yana lumshe idanuwan shi batare da yasan tunanin da yakeyi ba. 1
STORY CONTINUES BELOW
*
Yanda taga dare haka taga rana, da safe fuskarta a kumbure ta tashi da ita, saboda rashin bacci da kuma kukan da tasha. Dadinta daya, a satin su Fajr sukai hutun makaranta saboda gabatowar azumi. Ikram ta fara yima wanka ko da ta tashi, ta bata tasha da taga tayi bacci ta ajiyeta taje tai wanka itama. Saida ta fita suka gaisa da su Hauwa da suketa sauri da alama sun makara, tukunna ta koma daki, kusa da Ikram ta kwanta jin idanuwanta har yaji suke mata saboda rashin bacci. Ta lumshe idanuwanta taji Fajr a jikinta, hannu tasa tana dagashi
“Fajr ka kwanta a katifa…. Karka dameni dan Allah”
Kallonta yayi, da alama yanayin fuskarta yagani yasa shi zagayawa ta dayan bangaren ya hau gadon ya kwanta, juya kwanciya tayi ta fuskance su, tana kama hannun Ikram da kamar tajita, ta damqe dan yatsanta guda daya. Murmushi Waheedah tayi zuciyarta na cika fam da kaunar yarinyar, kullum sai ta dauka babu yanda za ayi taso yaranta fiye da son da take musu, sai suyi wani abin da zaisa zuciyarta cika fam da wata irin kaunar su. Bata san lokaci na tafiya ba, baccin kuma bai dauketa kamar yanda tayi tsammani ba.
Babu komai cikin kanta daya wuce su Fajr da take kallo sun nutsu suna bacci. Kwankwasa kofar da taji anayi ne yasata lumshe idanuwanta dan a tunanin ta AbdulKadir ne, muryar Anty taji
“Waheedah…”
Da sauri ta diro daga kan gadon tana zuwa ta bude kofar.
“Anty…”
Ta fadi cikin sigar gaisuwa tana dan matsawa Antyn ta shiga cikin dakin, mayar da kofar Waheedah tayi ta rufe tukunna ta karasa gefen gadon kusa da Anty ta zauna suna gaisawa sosai.
“Ya jikin ki?”
Dan rausayar da kai gefe Waheedah tayi
“Alhamdulillah… Naji sauki”
Kai Anty ta jinjina, tausayin Waheedah na cika zuciyarta. Duka cikin su babu wanda yasan da maganar auren AbdulKadir din, Nabila ce taje gidan ta dawo musu da labarin, ita Anty tafi awa daya a zaune jin Nuriyya ce AbdulKadir ya aura, kafin daga baya taje har bangaren Mami tana sauke takaicinta a can, dan ca tayiwa Mami lokacin suje su taho da Waheedah din tunda AbdulKadir bashida hali ballantana kunya, murmushi kawai Mami tayi duk da a idanuwanta zakaga tsantsar damuwar da take tattare da ita.
Kawaici irin na matar har mamaki yake ba Anty. Shisa take ganin girmanta ba kadan ba, dan da Waheedah yarta ce ikon Allah ne kawai zaisa ba zata kashe aurenta da na AbdulKadir ba, tunda farko ma bataga dalilin da zaisa ta dauki yarinya ta bashi ba, musamman mai sanyin hali irin na Waheedah. Numfashi Anty ta sauke
“Bansan me kikai ta bari a ranki har zuwa lokacin nan ba, ni bazan baki hakuri ba Waheedah, amman kije gida kiyi magana da Maminki, nasan kawaici ba zai barta furta komai ba, kije taga kina lafiya ba wai a waya ba”
Hannu Waheedah takai tana share hawayen da taji sun zubo mata. Cikin sanyin murya tace
“Idan gidan zaki koma bari mu wuce tare”
Kai Anty ta jinjina mata, ba gida zata koma ba, amman hidimarta zata jira, inta sauke Waheedah din saita sake fitowa. Hijab dinta ta dauko, sai jakar goyon Ikram din ta sakata a ciki tana goyata ta gaba ta tallabe, Fajr zata tasa Anty ta hanata, sabar yaron tayi a kafadarta, wayarta kawai Waheedah ta saka a jaka ta rike a hannu, mukullin da Hauwa ta bata na gidan guda daya, ko da zata fita ta dauka, sannan tabi bayan Anty. Kulle gidan tayin suka nufi motar Antyn, a cunkushe Waheedah takejin kanta da zuciyarta gabaki daya. Da tunani fal a kanta suka nufi gida.
Har suka karasa gida Waheedah batama sani ba, sai da taji Anty ta bude mata kofar motar ta bangarenta, saukowa tayi da Ikram tallabe a kirjinta. Fajr ya tashi bata ma sani ba, jakarta ta dauka tana ratayawa ta kama hannun shi, ko sallama bataiwa Anty ba ta wuce tana nufar bangaren su, Antyn ma mota ta koma ta fice daga gidan, zuciyarta cike da tunanin Waheedah din. Da sanyin jikinta ta karasa gida tana shiga da sallama, a falo ta samu Mami a zaune, Fajr kam bai bita ciki ba ya wuce bangaren Hajja, ita ma batabi ta kan shi ba. Sallama tayi tana cire takalmanta ta karasa, tunda Mami ta amsa ta taji idanuwan ta sun cika da hawaye.
STORY CONTINUES BELOW
Kan kujera ta zauna kusa da Mami tana sauko Ikram ta kwantar da ita a gefe, hijabinta ta cire, tana saka dan yatsa ta share kwallar da ta taru a gefen idanta, kallon ramar dake kasan idanuwanta Mami tayi, zatai karya idan tace bata kwana da yarinyar tana tashi da ita a rai, kwanakin nan yinsu kawai take badan suna mata dadi ba, duk da Yassar kullum da safe saiya kira ya hadata da Waheedah din sun gaisa, baccin kirki ma ba sosai take samun shi ba, haka takan raya daren da salloli tana yima Waheedahr addu’a.
“Waheedah…”
Mami ta kira tana rasa ta inda zata fara mata magana, maganar cewar bata taya Waheedah jin abinda Nuriyya tai mata ba baima taso ba, har kasan zuciyarta taji zafin abin, musamman ita da tafi kowa sanin yanda Waheedah ta dauki Nuriyyar, amman rayuwar haka take tafiya, wanda yafi kusa dakai shi yafi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki basu bane wanda zasu dauki abu su baka, mutanen kirki sune wanda zakuyi tarayya tare dasu basu cutar da kai ba. Auren da AbdulKadir din yayi bai saba addini ba, ya taka matakai da yawa na rashin kyautawa ne kawai a al’adance. 1
Taso yima Waheedah maganar sai tace mata
‘Babu komai Mami, ya rigada ya faru, ki mana addu’a Allah yasa hakan alkhairi ne’
Duk da tabar zancen, wani abu a kasan ranta saida ya fada mata Waheedah na boye kishin da tasan yana damunta ne, ta kuma jima tana tsoron rana irin wannan. Tana kallon yanda Waheedah take kai hannu tana share kwallar da take tarar mata lokaci zuwa lokaci, numfashi Mami ta sauke
“Waheedah…”
Ta sake kira a tausashe, wannan karin kamar hakan Waheedah take jira wani irin kuka mai sauti ya kwace mata, jikin Mami ta kwanta tana kukan da takeji yana fitowa daga kasan zuciyarta inda yake mata ciwo na gaske. Kuka take da bata tabayin irin shi ba a rayuwarta, kukan ranar da AbdulKadir ya fada mata ya kara aure ta text saboda bai darajata ba, kukan ranar da ya shigo mata da kawarta, Nuriyya da ta dauka yar uwa a matsayin kishiya, kuka take da duk ranar da Nuriyya ta rike AbdulKadir din a gabanta, kuka take daya kamata tayi shi watanni takwas da suka wuce, ta jima tana rike da shi a ranta, yanzun da ta fara bata san ya zata daina ba, muryarta a karye cikin wani irin kuka ta dago daga jikin Mami tana fadin 13
“Ma… Mami duk mata… Duk matan garin Kano da inda aiki yake kai shi… Mami baiga kowa ba sai Nuriyya….me yasa Nuriyya?” 4
Waheedah ta karasa maganar tana kai hannu ta dafe kirjinta da yake wani irin ciwo kamar zai tsage. Kishi takeji har wani duhu-duhu take gani. Riketa kawai Mami tayi, tasan kukan ma Rahma ne, amman har ranta take jin shi, duk karfin hali irin nata hawaye takeji cike taf da idanuwanta, yanzun tagane kishi ne yake cin ‘yar tata
“Kuma Nuriyya ta aure shi, ni bazan taba mata haka ba, bai haramta ba, amman bazan auri mijinta ba…me yasa zata auri nawa? Mijina Mami, Sadauki ta gani duk fadin Kano….” 10
Waheedah take fadi batare data sani ba, dan yanda take maganar tana wani irin kuka kasan ba a cikin hayyacinta take ba, sosai take kuka tana sambatun da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, riketa kawai Mami tayi tana jijjigata kamar karamar yarinya. A jikin Mamin tayi kuka har bacci ya dauketa, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, a hankali Mami ta zame Waheedah kan kujerar tana dauke mata Ikram. Bacci tayi har azahar, lokacin da ta tashi wani irin zazzabi ya rufe ta ruf, dakyar taja jiki ta wuce dakin Mami tayi alwala, sai da taba Ikram tasha dan duk hakurin yarinyar harta fara kuka, tukunna ta samu tayi sallah.
Duk yanda Mami ta lallabata kasa cin abinci tayi, shayi ta hada ta samu tasha rabin kofi, da idanuwa Mami take binta duk inda tayi, har saida ta gama jijjiga Ikram tayi bacci, Mami ta karbeta ta saka zani ta goyata. Waheedah din na zaune kan kujera, tanajin kamar ta shige ciki dan gujema magana da Mami din. Cikin sanyin murya Mami tace
“Na dauki ido na saka miki ne tun farko saboda nayi tunanin in har kina da matsala ina da kusancin da zaki sameni da ita. Bazance miki hakuri ba abu bane me kyau, duk da akan ce idan yayi yawa yana zama cuta. Babu inda hakuri yake yawa, a zamantakewa ta yau da kullum, ko a zamantakewa ta aure, musamman ma ta aure…”
Gyara zama Waheedah tayi, tanajin yanda hawaye suka cika mata idanuwa, magana Mami ta cigaba dayi
“Ba hakuri bane yake yawa ya zama cuta, rashin yafiya ne, akwai banbanci tsakanin ai maka abu ka hakura bakace komai ba, da ai maka abu ka hakura ka yafe. Yafiyar itace take saka duk yawan lokuttan da kai hakuri kake samun riba, idan har zaka hakura ba zakayi magana ba kabar abin a ranka bashida wani amfani, gara ka fito da shi kawai…” 3
Mami ta karasa maganar tana sake sauke muryarta da fadin
“AbdulKadir halin shine ya fito fili, shisa babu wanda ya tambayeshi me ya faru, babu ma wanda yai tunanin yaji nashi uzurin, kowa laifi ya dauka ya dora mishi. A karo na farko koya dace ko bai dace ba Waheedah, ko da za’a ce nayi son kai zan fadi raina ya sosu da auren Nuriyya da AbdulKadir yayi, bai taka addini ba, amman banji dadi ba ko kadan, saboda halin da zaki shiga nayi tunani”
Wannan karin Waheedah bata koyi kokarin share hawayen dake zubar mata ba, yanda muryar Mami take a karye kawai na kara taba zuciyarta, ita kanta Mamin kokarin tarbe hawayen da suke ta mata barazana take, yanayin Waheedah din na gwada karfin zuciyar ta fiye da yanda ta zata.
“Mutuwar aure tafi yin shi wahala, duk yanda ake ganin da kalamai kawai za’a yita. Ban taba ganin inda uwa taso mutuwar auren yarta ba Waheedah, ko ya kaddara ta rubuto hakan, ni shawara kawai zan baki a wannan matakin, bazanyi kokarin haramta miki abinda addini ya halarta miki ba, abu daya zance miki, kiyi magana da AbdulKadir…” 2
Kai Waheedah take girgiza ma Mami wasu sabbin hawayen na zubar mata, har ranta tagaji da auren shi, tanajin idan ta koma komai zai iya faruwa, ciki harda tarwatsewar zuciyarta, ba zata iya daukar wani ciwon bayan wanda taita dauka ba
“Wallahi Mami nagaji, nagaji har raina…”
Waheedah ta fadi cikin kuka, kai Mami ta jinjina mata
“Bance wani abu ba nima, kiyi magana da shi, magana ta fahimta, lokutta da dama aure kan samu tangarda ne saboda rashin tattauna matsala har a samu maslaha, kowa naganin laifin dan uwan shine, babu kuma wanda yake kokarin sauke girman kai ya saurari dayan har a gano bakin zaren, ki fada mishi matsalar ki, ki saurari uzurin shi” 12
Shiru Waheedah tayi tana share kwalla
“Kina jina?”
Mami ta fadi, kai kawai Waheedah ta iya daga mata, tana sake shigewa cikin kujera. Numfashi Mami ta sauke, komai baya mata dadi sam, kitchen ta wuce badan tana da wani abu mai muhimmanci da zatayi a ciki ba, sai dan inta ci gaba da kallon Waheedah din hawayen da take ta boyewa ne zasu zubo. Duk wannan kishin da yake nuqurqusarta, da gajiyar da take fadin tayi, zaka fahimci yanda rabuwa da AbdulKadir shine karshen abinda take son yi…!