ABDULKADIR CHAPTER 4

ABDULKADIR




CHAPTER 4




Sai da yai wanka tukunna ya dauro alwalar sallar Asuba, yana kuma dawowa daga masallaci jakarshi ya hada tukunna ya kwanta. Sai lokacin ya kunna wayar shi tunda yazo Kano. Babban Yaya, Muhsin ne ya basu, dan shi harkar da yakeyi kenan, tun yana yaron shago da yake ubangidan nashi bamai baqin ciki bane, Muhsin din kuma akwai ladabi da kwantar dakai, kudaden duk da yake samu saiya tattara in za’a china saro kayayyaki saiya hada da nashi a dan saro mishi abubuwa. A haka har Allah ya saka mishi albarka, duk da ya kammala karatun shi bangaren computer science, bai nemi wani aikin ba, da sana’ar ya dogara, sai babban café daya bude a wajen rijiyar lemo da shima yana kawo mishi rufin asiri. 1

Shima wayar hannun nashi blackberry din ce, danne-danne yake, yana ma rasa abinda zaiyi da wayar, lokutta da dama hakan yakan faru tunda aka bashi wayar, idan ya gaisa dasu Hajja shikenan, kashewa yake, tana iya kwana biyu a kashe. Yazid ne ya turo dakin da sallamar da Abdulkadir din ya amsa mishi

“Ni banga amfanin wayarka ba”

Yazid ya fadi yana zama gefen gadon da Abdulkadir din yake zaune ya miqe kafar shi akai

“Ina amfani da ita mana…”

Kai Yazid ya girgiza cikin rashin yarda

“Kai dan BBM din nan da kowa yake yi ma bakayi”

Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi 1

“Meye BBM din wai? Nawaf ma ya isheni da maganar kwanaki”

Dariya Yazid yayi

“Kafar sada zumunta ce, amman wayar blackberry ce kadai take dashi. Idan kayi register zasu baka wasu lambobi hade da haruffa, to sune zasu zama kamar…”

Hannu Abdulkadir din ya dagama Yazid, alamar baya bukatar karasa ji hadi da cewa

“Bani da ra’ayi…” 2

Yassar da yake wanka ne ya fito daga bandakij dan yanajin duk hirar da suke

“Ai idan kana son magana da Abdulkadir sai dai kai mishi text kawai, ko ka tura mishi saqo ta email dinshi. Idan ba zaka iya jira ya kunna wayar shi kuyi magana ba”

Yassar ya karasa yana daukar mai dake ajiye a gefen Abdulkadir din ya kwance ya dangwala yana soma shafama hannuwan shi.

“Matar yaron nan tana da aiki” 4

Yazid ya fadi yana sa Abdulkadir din watsa mishi harara da kananun idanuwan shi

“Bafa naso Hamma, duka shekara baifi shekara hudu kabani ba” 2

Kai Yazid ya girgiza mishi

“Banma baka ko daya ba, yaro sai shegen son girma…”

Turo labba Abdulkadir yayi

“Kayi na girman ka Hamma, kar kai na ukku” 3

Mikewa Yazid din yayi

“Sallama nazo muyi, rasa kunya…” 1

Daquna fuska Abdulkadir ya sakeyi

“Wanne irin sallama sai kace wanda za akai kabari? Ina ce makaranta zan koma ba wani wajen ba” 2

Numfashi Yassar ya sauke, Yazid na girgiza kai

“Ba za’a taba maka abin arziqi ba kai kam. Allah ya tsare hanya, a kula, banda rashin kunya” 1

Idanuwa kawai Abdulkadir ya kankance mishi, baice komai ba harya fice daga dakin. Hankalin shi ya mayar kan Yassar

“Wai shafa mai ne haka tun dazun. Ka shiga uku kaikam, sai kace mace”

Murfin man Yassar ya jefa mishi yana fadin

“Fita daga dakin nan dan ubanka…”

Dariya Abdulkadir yayi

STORY CONTINUES BELOW


“Ba inda zanje, ni da dakina”

Ganin Yassar na ajiye robar man dake hannun shi yasa Abdulkadir din mikewa babu shiri, ya fice daga dakin yana dariya. Daman yana da niyyar zuwa ya gaisa da Hajja kuma yai mata sallama, tunda inya koma baisan lokacin da zai sake dawowa ba kuma, sai dai ta waya. Da sallama ya shiga dakin Hajja, yana samun wasu cikin dangin Abba da suma duk ranar zasu tattafi, yawancin su baya tunanin a garin Kano suke da zama, bai tabbatar ba, saboda ko taron dangi da akanyi duk karshen shekara zai iya qirga guda nawa ya taba zuwa, suma idan Yassar ya jashi.

“Sannun ku”

Ya fadi yana soma wucewa cikin dakin sosai, kamun wata mata da yasan yar uwar Abba ce, amman bazai tuna ya alaqar take ba, ko abokiyar wasan shi bai sani ba, tace 1

“Abdulkadir baka iya gaishe da mutane ba?” 2

Juyawa yayi yana kare mata kallo, kafin ya amsa da

“Sannun kun da nace bai miki ba?” 7

Daya daga cikin matan ta watsa mishi daquwa tana fadin

“Karbi wannan Abdulkadir, marar kunyar banza. Yayar gyatumin naka kake mayarwa magana haka” 5

Kankance idanuwa Abdulkadir yayi yana fara bude baki ya tambayeta meta hada da Abban nasu da zatai mishi zagin yara, Hajja ta katse shi da fadin 2

“Abdulkadir…”

Juyawa yayi ya kalli Hajja, ranshi ya gama baci

“Me yasa zatai mun zagin yara Hajja? Wacce gaisuwa suke so in musu? Bayan ta musulunci daya wajaba akaina har sannu na musu” 3

Runtsa idanuwa Hajja tayi, tana gujema Abdulkadir bakin mutane 2

“Abdulkadir…”

Ta sake fadi, wannan karin ranta a bace, da gajiya da halayenshi, ba zatace batayi kewarshi a shekarun nan ba, amman bakinta ya huta kwana biyu. Kuma babu wanda yazo gidan yagan shi ballantana wani abu ya hadasu har yai musu rashin kunya. Juyawa Abdulkadir din yayi yana ficewa daga dakin. Hajja tabi bayan shi, sauri ta kara tana wuce shi, ganin ta nufi sashin Abba yasa ran Abdulkadir din kara baci, yasan kararshi zata kai wajen Abba, shi ba karamin yaro ba. 1

Bayanta yabi har dakin Abban data shiga da sallama, yana zaune akan kafet da alama karyawa yagama yi. Hajja najin shi yana biye da ita, dan haka bata tsaya bata lokaci ba tace

“nagaji da halin yaron nan Alhaji. Yanzun su Hajiya Salamatu ya samu a falo yai musu rashin kunya…” 2

Numfashi Abba yaja ya fitar yana kallon Abdulkadir din da yake tsaye. Hakan yasa shi fadin

“Ni ba rashin kunya nai musu ba Abba” 1

Juyawa Hajja tai tana kallon shi

“Na maka ta kudin ka, kasan tambarin gidan muce” 5

Kai Abdulkadir ya sauke kasa, shisa daya tafi ya shekara biyu baizo gidan ba, sai angan shine za’a saka shi a gaba ana mai fada kamar karamin yaro. Juyawa Hajja tayi tana ficewa daga dakin 3

“Ni ban musu rashin kunya ba Abba. Nayi sallama fa, har sannu nayi musu. Shine zasuyi mun surutu ban gaishe dasu ba”

Numfashin dai Abba ya sauke da maganganun Abdulkadir din, addu’a itace abinda yake bin yaron da ita, dan idan yace zai saka bacin rai da halayenshi matsala za’a samu. Tunda haka Allah yayi shi da baudadden hali, idan zagin shi akai, ko akai mishi fada ba amfani yake ba, dukan ma ko sanda ake mishi baji yake ba. Addu’a ita kadai ce abinda zai tausasa zuciyar Abdulkadir. Hakan yake yawan kwatantama Hajiya Safiyya.

“Ka kyauta ai. Inace tun jiya da daddare kaimun sallama cewar yau da sassafe zaka wuce”

Abba ya fadi, kallon shi Abdulkadir yayi yanajin wani sabon bacin rai, dan yaga alama, Abban nason nuna harya gaji dashi.

STORY CONTINUES BELOW


“Yanzun ma sallama naje in mata…”

Kai Abba ya jinjina

“Allah ya tsare ya kaiku lafiya. A dinga tausar zuciya dai”

Sai da ya amsa da Amin tukunna ya fice daga dakin. Sosai ranshi a bace yake, amman bazai tafi baima Hajja sallama ba. Dakin ya sake komawa, yana buga kafafunshi cikin son sanar dasu Hajiya Salamatu baiyi niyyar gaishe su ba, babu kuma wanda ya isa yasa shi yin hakan, ba kuma yanda zasuyi dashi tunda ba haihuwarshi sukai ba. Dakin Hajja ya fara shiga ya samu bata nan, fitowa yayi yana nufar kitchen. Acan kuwa ya sameta tana hada shayi

“Hajja…”

Ya kira, inda yake bata kalla ba, aikin da takeyi taci gaba, dan sosai ya bata mata rai.

“Hajja mana… Banaso fa…” 4

Abdulkadir ya sake fadi, ganin bata da shirin kulashi yasa shi kama hannunta

“Zan watsa maka ruwan shayi idan baka bace mun dagani ba”

Wani guntun murmushi ya kwace ma Abdulkadir din

“Nine fa Hajja…”

Harara ta watsa mishi, yanayin yanda ya kankance mata idanuwan shi nasa murmushin da batayi niyya ba kwace mata, tana son yaranta fiye da yanda zata iya fadi, amman Abdulkadir daban take jin shi, tun yana karami jin shi take har ranta, ko dukan shi tayi tana da tabbacin yanda hakan yake mata zafi a zuciya yafi yanda yake mishi a jiki. Wasu yaran kan zama karfin ka, Abdulkadir rauninta ne.

“Hajja hanya zan hau, bana so in tafi kina mun fushi, bayan banyi komai ba”

Duka Hajja takai kishi a kafada tana yarfe yatsunta da suka amsa, dariya Abdulkadir yayi yana kama hannun nata data fisge tana hararshi, yasan ta huce dan yana ganin murmushi a idanuwanta

“Saura aita kiran wayarka a kashe”

Yar dariya Abdulkadir yayi

“Zan kunna in shaa Allah”

Kai Hajja ta jinjina mishi

“Dan Allah ka kula…kaga girma kake, banda rashin kunya” 2

Daquna mata fuska Abdulkadir yayi

“Nifa bana rashin kunya”

Rausayar dakai Hajja tayi

“Hmm…”

Kawai ta iya fadi, Abdulkadir din yai mata murmushi yana dorawa da

“Sai munyi waya…”

Kai ta jinjina mishi

“Allah ya tsare ya bada sa’a…”

“Amin. Zahra fa? Hamma Mubarak ma ni sau daya nagan shi tun da nazo”

Kofin shayi Hajja ta dauka tukunna tace

“Kasan wannan hidimarshi tafi karfin shi, nima da muke kwana gida daya, sai in yini ban saka shi a ido ba. Zahra kuma tana bangaren Hajiya Halima nake ji…”

Kai Abdulkadir ya daga mata kawai, saida ya samu plate ya zuba soyayyar doya da kwai da tayi, ya dauki shayin da ta hada mishi, tukunna ya sake yi mata sallama yana ficewa daga dakin ya nufi bangaren su.

*

Tare suka fito da Yassar, jakar Abdulkadir din riqe a hannun shi, sai wallet dinshi a dayan hannun, gaban mota ya bude yana jefa jakar tashi kujerar baya ta gaban. Ya fito da jikin shi kenan daga motar yaji ance

“Hamma…”

Sanyin muryarta yasa shi sanin itace tun kafin ya juya yana sauke kananun idanuwan shi akan Waheedah da take tsaye, jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa, ta saka farar hular sanyi saman kanta, sai yaga fuskarta tai mishi fayau. Kallon shi Waheedah take tana jin zuciyarta dake dokawa ta matse waje daya a kirjinta. Yanayine da bata da kalaman da zatayi amfani dasu wajen fassara shi, bata taba jin kewar wani a rayuwarta yanda take jin kewar shi tun kafin ya tafi din ba. Gaishe shi ya kamata ace tayi tasani 1

STORY CONTINUES BELOW


“Tafiya zakai?”

Ta bukata, bata bari ya amsa ba tace

“Hamma bakai mun sallama ba, tafiya zakai bakai mun sallama ba…” 5

Ta karasa maganar muryarta na karyewa tana jin hawayen da suke tahowa daga zuciyarta sun cika mata idanuwa taf. Kallonta Abdulkadir yakeyi, banda Hajja da Abba, babu wanda yaima sallama a gidan. Su kadaine yake jin ya zama dole yai musu sallama idan zai tafi, wanda yagani yanzun dazai fito dai sunyi sallama, baisan meye a yanayinta da yake son saka shi jin kamar bai kyauta ba da bai mata sallama ba. Tsintar kan shi yayi da fadin

“Zan zo hutun sallah…”

Saida ta ware mishi manyan idanuwanta tukunna maganganun dayai suka zauna mishi

“Da gaske zaka zo? Dan Allah kazo Hamma, kaji… Kazo dan Allah” 2

Kai Abdulkadir din yadan daga mata, yana ciza fatar bakin shi daga ciki, baisan meyasa yace mata zaizo din ba, amman hawayen da yake gani cike da idanuwanta ne bayason su zubo. Murmushi tai mishi da yasa fuskarta qara mishi haske. Su duka biyun basu kula da Yassar ba harya wuce ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya zauna yana jiran Abdulkadir din.

“Sai na dawo…”

Abdulkadir din ya furta muryar shi can kasan makoshi. Wani irin yanayi kalmomin nashi suka jefata, ji take kamar zai tafi da wani bangare na zuciyar ta, lokaci daya ta nemi tsallen da zuciyarta take mata najin zaizo hutun sallah ta rasa. Sai kewar shi da ta kara danneta

“Kamar karka tafi” 3

Ta furta muryarta a karye, tana saka shi runtsa idanuwan shi ya bude su hadi da kankance su akanta. Hannun shi daya yasa ya laluba aljihun shi duka biyun, da alama baiji abinda yake nema ba, juyawa yayi sai lokacin yaga Yassar, kanshi ya zira ta jikin murfin motar yana fadin

“Dan bani biro…”

Cike da mamaki Yassar yace

“Biro kuma?”

Daquna fuska Abdulkadir yayi

“Idan zaka bani kabani kawai Hamma, meye namun tambaya kamar na maka wani yare?” 2

Kallon shi Yassar yayi

“Bazan bayar ba to”

Da alamun gajiya Abdulkadir yace

“Hamma mana… Kabani nikam”

Kallon shi Yassar ya sakeyi, baisan me zai da biro ba, amman saboda Waheedah da take tsaye yasa shi dudduba cikin motar, yako samo wani baqi ya miqama Abdulkadir din, karba yayi yana takawa inda Waheedah take tsaye. Bashida takarda, bashida kuma lokacin zuwa nemo wata. Hannunta ya kamo, yana share yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike da mamaki, zuciyarta nayin wani irin tsalle ta dawo cikin hannun nata daya riqe, bin shi tayi da kallo tana mamakin yanda akai baya kyarma, dan tana jin yana kyarmar daga ciki. Rubutu Abdulkadir din yai mata a hannun tukunna ya saki yana juyawa batare daya ce komai ba.

Kallo Waheedah tabi shi dashi harya shiga mota yaja murfin ya rufe, da ido ta rakasu har gate suka fice, ko sau daya Abdulkadir din bai juyo ba balle tayi tunanin ko hannu zai dan daga mata cikin alamar bankwana, jikinta take jin kamar an mata allurar rashin kuzari, saida taga mai gadi yaja gate din gidan ya rufe tukunna ta dago hannunta da take jin har zufa-zufa yake ta bude tafin hannun tana juyo dashi saboda taga meya rubuta. Lambar wayar shi ce da adireshin shi na email, dayan hannunta tasa tana shafar rubutun hadi dayin yar dariya, sosai Abdulkadir yana da kokari ko da suke islamiyya da boko, a ajinsu kaf babu wanda yake kamo shi, amman baida rubutu me kyau, zaka rantse dan firamare ne yayi duk idan kagani.

Hannunta ta sake dubawa tana kallon lambobin hadi da rufe idanuwanta ta karanta su cikin kanta inda suka samu wajen zama daram. Adireshin email din ta duba ‘Abugaje@yahoo.com’ ta hada da lambar wayar tana samar musu waje me kyau ta adana, hannun dake da rubutun ta daga tana dorawa a kirjinta inda zuciyarta take dokawa da wata irin nutsuwa tukunna ta juya tana nufar bangaren su, tana jin tafiyar da take kamar akan gajimare. 1

STORY CONTINUES BELOW


*

Idanuwan shi kofar gidansu Nuriyya ya sauka suna fita, saiya tsinci kan shi da sauke wani numfashi da baisan yana rike dashi ba, bazai ce ga asalin abinda yake ji ba, amman idan da Nuriyya zata kasance tsaye a kofar gidan hakan zai mishi dadi, gyara zama yayi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi, numfashi ya sake ja, kafin ya fitar dashi Yassar yace 1

“Meke damunka?”

Idanuwan shi ya bude yana juya kanshi bangaren Yassar din daya dan juyo ya kalle shi yana sake mayar da hankalin shi kan tuqin da yake

“Kai ido kaman an saka ma sakwara dan yatsa, kaita qara kankance su…” 8

Dakuna mishi fuska Abdulkadir yayi

“Kana cewa Ma shaa Allah Hamma, kyawun idanuna yasa kuka cinye mun tun ina karami…” 1

Dariya Yassar yayi

“Banza. To har kai shekara wajen hudu in za’ai hoto idanuwanka basa fitowa” 8

Murmushi Abdulkadir yayi yana fadin

“Allah ya yafe maka…”

Dariya Yassar ya sake yi, muryar shi wannan karin babu alamun wasa yace

“Da gaske, me yake damun ka?”

Dan daga kafadu Abdulkadir din yayi, baisan me yake damun shi ba shi kanshi, kawai dai wani sanyin jiki yake ji naban mamaki, kuma ba zai cema Yassar yaso yaga Nuriyya a tsaye a kofar gidan ba, saboda bashida dalilin da zaiji hakan, bai kuma san abinda yasa yake jin hakan ba. Shiru Yassar yayi, dan ta gefen idon shi yaga Abdulkadir din ya daga mishi kafadu, ya kuma san ba sake wata magana zaiyi ba, idan wani abin ma yana damun shi sai yaga dama zai fada mishi.

“Kardai kabari koma menene ya dameka”

Yassar yace, wallet din shi Abdulkadir din yake wasa da ita, maballin yake ballewa yana mayarwa, kafin ya sauke idanuwan shi akan wallet din lokacin daya balle maballin, karamin hoto yagani a jiki, bayan shi a juye, daquna fuska yayi, a hankali yake furta

“Ba duka na bata ba?”

Dan kallon shi Yassar yayi

“Magana kake?”

Dagowa Abdulkadir yayi yana girgiza ma Yassar kai, kafin yasa dan yatsan shi ya zaro hoton yana juya shi, daquna fuska ya sakeyi ganin hoton Waheedah, kafin dariyar da baisan daga inda ta fito ba ta kwace mishi. Yana da tabbacin ko gawayi aka shafama Waheedah a fuska sai idanuwanta sun nuna alamun farinta, yanda akai ta kubcema zama zabiya abin jinjina ma Ikon Allah ne. Juya hoton yayi yasaka shi dai-dai a cikin wallet din, haka kawai ya tsinci kanshi da saka dan yatsa ya shafi fuskarta dake jikin hoton, kamar zaiga tsoron shi ya cika manyan idanuwanta. 1

Jiyai an fisge wallet din, da sauri ya bita da shirin kamowa, Yassar ya mayar da ita dayan bangaren yana daga cinyar shi ya saka wallet din

“Tuqi nake Abdulkadir…”

Harararshi Abdulkadir yayi

“Hamma bana so, bana so, kabani wallet dina”

Murmushi Yassar yake yi

“Meye kake shafawa da dan yatsa? Dariyar me kake kuma?”

Kankance idanuwa Abdulkadir yayi

“Ina ruwanka? Karka bude, kabani wallet dina…”

Gudun motar Yassar ya rage yana zaro wallet din daga karkashin cinyar shi ya bude, dan kallo yayi tukunna ya mayar da idanuwan shi kan titi, wannan karin shi ya daquna fuskar shi da take dauke da bayanannen mamaki ganin hoton Waheedah din

“Kabani Hamma, ni banason irin wannan. Ai zubda girma ne kana daukar abin kaninka. Ba saika ja in rainaka ba” 4

Abdulkadir din yake fadi yana miqa jikin shi ya fisge wallet din daga hannun Yassar ya balleta yana dan daga jikin shi ya saka a aljihu. Kallon shi Yassar yayi yana rasa abinda zai fada, sosai mamaki yakeyi.

STORY CONTINUES BELOW


“Karka fara abinda ba zaka iya karasawa ba Abdulkadir, karka fara” 1

Yassar yace da wani yanayi a muryar shi da yasa Abdulkadir din kallon shi cike da rudani

“Kar in fara me?”

Wannan karin sosai Yassar ya rage gudun motar, yana jin wanda suke bayan shi suna danna mishi hon, alamun idan shi baida gurin zuwa su suna dashi, amman bai damu dasu ba, Abdulkadir ya kalla sosai yana son karantar gaskiyar abinda yake tunanin, amman banda confusion babu abinda yake fuskar Abdulkadir din. Murmushi Yassar yayi yana girgiza mishi kai. Idan soyayya ce take shirin qulluwa a tsakanin Abdulkadir din da Waheedah bazai kara mata gudu ba tun kafin Abdulkadir din ya fahimci akwaita. 1

“Ni banaso a fara mun maganar da bangane ba, kasani kuma”

Gudun motar Yassar ya kara, tukunna ya amsa Abdulkadir din da

“A shaqeni a fito da sauran mana” 1

Wani kallo Abdulkadir din yai mishi, tukunna yakai hannu yana kunna radio din cikin motar, maganar yake qurewa da yasa Yassar bugar mishi hannun daya janye babu shiri, maganar ya rage yana fadin

“Ka qarata sai naci ubanka wallahi, ba zaka cika mun kunne ba”

Daquna fuska Abdulkadir din yayi kasa-kasa yace 2

“Matsala kake da ita Hamma”

Murmushi Yassar yayi

“Idan ma zagine bazan zagu a fili ba, kuma bazan daku ba…” 1

Gyara zaman shi Abdulkadir din yayi cikin kujerar, yana jingina kanshi da jikin kujerar. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na tasowa daga inda ya samu wajen zama cikin kan shi yana bayyana a bayan idanuwan shi cikin yanayin daya sashi bude idon shi babu shiri, kallon hanya yaci gaba dayi zuciyar shi ta mishi nauyi naban mamaki. 1

*

A kasan zuciyarta take jin wani irin fili da tafiyar Abdulkadir tabar mata, zata rantse da Allah akwai wani bangare nata da ya tafi dashi, sai dai ba zata iya dora dan yatsa akan bangaren ba, da duk kwanakin da yake karawa da yanda take jin filin na qara mata girma. Yanzun ma hakan take ji, komai baya mata dadi, har littafin da ta fara karantawa na Biebee Isa (ke Alheri ce) tana kwasar dariyar Nenne da dinkum dinta, yau ta kasa karasawa. Sosai take jin kewar shi na danne ta. Ga ranar Alhamis ce babu islamiyya balle taje ta rage zafi. Nuriyya kuma bata nan, taje wajen dangin mamanta sada zumunci.

Kujera ta dauko ta saka a harabar gidan ta zauna, tunanin ya hadar mata biyu. Gana Abdulkadir, gana Nuriyya da takeyi, dan ta jima tana mata maganar tsoron faduwa jarabawar aji shidda, kasancewar makarantar gwamnatin ba wani tabbacin kirki gareta ba, duk da Nuriyya na da kokari, gashi tunda suka shiga aji hudu su biyun, banda darasin ingilishi da lissafi, babu abinda suke iya samu suyi ita da Nuriyyan, tunda ita Waheedah bangaren Art take, Nuriyyar kuma commerce, a cewarta tana son karantar bangaren kasuwanci dan tayi aiki da wani kamfani babba. Ita kuwa Waheedah turanci take son karanta, ta kuma koyar in ta samu hakan. 1

To satin aka fara biyan jarabawar aji shiddan ta Waec, batasan ta inda zata fara yima Abba maganar Nuriyyan ba, saboda batason dora mishi nauyi fiye da wanda yake kan shi, amman ta tambayo wata makaranta da babu nisa dasu, Green olive, kudin jarabawar kuma kadan zai cika a wanda zai biya mata ita kadai a Sheikh Bashir su zana anan Green Olive din ita da Nuriyya. Kamar daga sama taji an tafa hannuwa a saitin fuskarta daya katse mata tunanin datai zurfi a ciki, tana sauke idanuwanta kan fuskar Yazid dake mata murmushi har dimple din gefen fuskar shi ya bayyana. 1

Kaf dakin Hajja, har matan babu mai kyawun Yazid, ga sumar dake fuskar shi ta kara mishi wani kwarjini naban mamaki, abinka da wanda yake da haske fata 1

“Hamma Yazid…”

Waheedah ta fadi tana mayar mishi da murmushin da yake mata

“Tunanin me kike haka?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi a hankali, daga mata girar shi duka biyun Yazid yayi, alamar bai yarda ba. Inda kujerun robar suke ya karasa yana dauko guda daya ya dawo da ita ya kusa da Waheedah ya zauna.

“Bansan kanwar tawa da karya ba”

A kunyace Waheedah ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, sosai yake jin kominta har ranshi. Shi ba mutum bane maison hayaniyar duniya, shisa jininsu ya hadu da Waheedah din, sanyin halinta ya mishi.

“Kinsan zaki iya fadamun damuwarki ko?”

Ya bukata a tausashe, numfashi Waheedah ta sauke

“Da gaske babu komai Hamma”

Kai Yazid ya girgiza mata

“Aikam zamuyi fada yau”

Dan murmushi Waheedah tayi

“Ina son inma Abba magana ne, kuma ina jin nauyi”

Sake gyara zaman shi Yazid yayi

“To ni kimun maganar”

Dagowa fuskarta tayi tana kallon yanda ya bata gabaki daya hankalin shi, idan wani yagani zai rantse bashida wani abu mai muhimmanci daya wuce saurarenta.

“Ki fadamun Waheedah…”

Ya umarta cikin yanayin dayasa ta fadin

“Nuriyya ce daman, Waec din da aka fara registration, shine nake so ince ma Abba da kudin da zai biyamun a sheikh Bashir, in da hali ya cika saiya biya mana mu biyun muyi a Green Olive, nasu da sauki na tambayo”

Murmushin shi Yazid ya fadada, ya dauka matsalar tata mai girma ce, kaunar da take ma Nuriyya na tsaya mishi a rai, yana musu addu’ar dorewar zumuncin su, dan kamar yanda rayuwa bata da tabbaci hakama mutanen cikinta sukan kasance, yana tsoron aminantaka irin haka, yana tsoron yai kusanci da mutane su shiga jikin shi su cutar dashi, dan yasan yana da raunin zuciya, ba komai yake da karfin dauka ba. 3

“Su Green Olive din nawa ne?”

Ya tambaya, cikin sanyin murya tace

“Dubu talatin da uku”

Kai Yazid ya jinjina yana mikewa tsaye hadi da fadin

“Kiyi mata magana, ta shirya gobe in shaa Allah da na daukoku daga makaranta, kafin lokacin sallah yayi sai muje ni dake da ita Green Olive din muji ya abin zai kasance”

Da wani irin murmushi da yasa zuciyar shi kumbura ta cika kirjin shi taf Waheedah ta kalle shi

“Zakai ma Abban magana ne?”

Kai Yazid ya girgiza mata, sosai yake jinta a ranshi har jikin shi yakejin yana daukar dumi da halin da zuciyarshi take ciki a kanta

“Zan biya mata” 2

Ware idanuwa Waheedah tayi da mamaki, kafin ta dago hannuwanta duka biyu tana rufe bakinta data bude cikin mamaki, kafin ta sauke su, tana sake kallon shi, dariya Yazid yake sosai

“Ki fada mata yau dan ta zama cikin shiri, kina ji?”

Yai maganar yana juyawa, farin cikin dake fuskarta zai jima yana tare dashi.

“Hamma!”

Waheedah ta kira tana jin yanda yagama mata komai a yar karamar duniyarta, idanuwanta cike taf da hawayen farin ciki take kallon Yazid daya juyo

“Nagode da karamcinka… Nagode fiye da yanda zan iya fada da kalmar…” 1

Kai kawai Yazid ya jinjina mata yana juyawa, yanzun kam yanda yake jin zuciyar shi a cike ba iya kirjin shi ta tsaya ba, har ko ina na jikin shi yake jinta. Da gaske yana son Waheedah, yana mata son da yake tunanin dakyar ya iya hakura ta karasa aji shiddan nan bai furta mata ba. Sai dai yana duba kankantar Waheedah din, yana ganin kamar yayi wuri, amman har Abba da bikinsu Babangida saida yai mishi magana cewar me yake jira? Idan aikine yana dashi, yana da muhallin dazai zauna tunda Allah yai mishi budi dai-dai gwargwado Kasancewarshi Engineer yana kuma aiki da kamfanin gine-gine babba da yake nan garin Kano. 6

Bai fadama Abba cewar matar tashi a gida take ba, saboda yana son ya fara furta mata tukunna. Idan suka san wacece zasu daina mishi surutu kan aure, sosai yake jin lokacin da zata sani yayi. Da wannan tunanin a ranshi ya nufi bangaren su…!Mami ce data fito daga daki ta kalli Waheedah da take kwance, tana murmushi tace

“Ki tashi an kusan kiran sallah”

Hannun kujerar Waheedah ta kama tana miqewa dakyar, kanta take jin kamar baya liqe da jikinta saboda rashin nauyin da yai mata. Tunda aka fara azumi babu wanda ya bata wahala kamar na karshen nan, ita bata damu da duk wani aikin gida ba. Amman tana azumi ace ta fita sosai take wahala. Gashi a dakinsu kowa zai sha ruwa ranar tunda girkin Mami ne. Amatullah da zata tayasu wani abin wuni tayi gidan kitso, bata jima da shigowa gidan ba.

“Mami hanjina kamar an kwashe”

Waheedah ta fadi tana taba cikinta da yake a shafe. Dariya Mami tayi

“Idan wani yaji saiya dauka zakici wani abin kirki…”

Kai Waheedah ta jinjina tana fadin

“Haba ai yau yunwar da nakeji zan baku Mami”

Murmushi kawai Mami tayi tana shiga kitchen ta dauko robar dabinon data dauraye ta fito da ita tana dorawa kan hannun kujera. Kitchen din ta sake komawa tana dauko babban kwanon tangaran din da yankakkun kayan marmari ne a cikinsu ta ajiye tsakiyar dakin. Ta miqa hannu ta dauko robar dabinon daga kan hannun kujera, samarin gidan na soma shigowa da sallama, dai-dai lokacin da aka kira sallah. Wasu dabinon kawai suka dauka suna ficewa daga dakin dan tafiya masallaci, Mami ma daki ta shige dan gabatar da sallar Magrib. Dakyar Waheedah takai hannunta tana daukar kankana hadi dayin Bismillah tukunna ta saka a bakinta.

Zata rantse da Allah inuwar shi ta banbanta da ta kowa, shekara daya da kwanaki

“Assalamu alaikum…”

Muryarshi ta daki kunnuwan ta, tana sa tari kwace mata saboda ruwan kankana da yabi mata ta hanyar da bata shirya ba, zuciyarta da take wani irin dokawa bata taimaki yanayin da take ciki ba. Yace mata zaizo da sallah, tun satin take baza ido ta inda zai bullo amman shiru, kallo daya Abdulkadir yai mata yana ganin yanda take tari sosai, takawa yayi zuwa kitchen yana dibo ruwa a cup ya dawo ya mika mata. Karba Waheedah tayi tana shan ruwan hadi da sake yin tari, tukunna tayi gyaran murya. Maqoshinta kamar zai ciro take jin shi.

A hankali ta dago tana kallon Abdulkadir din da yake tsaye yana kallon ta, ta dauka akwai shekarun da mutum yake kaiwa ya daina kara tsayi ko girma, amman banda Abdulkadir din. Zata rantse yafi lokacin dayazo tsayi da girma. Kalar askin da yazo dashine wancen karin, jikinshi sanye da farar riga mai dogon hannu sai wando daya rufe gwiwar shi da kadan, baqi yana da igiyoyi daga jikin kafafuwan. Wani irin kyau yai mata har zuciyarta na matsewa waje daya. Hannu taga ya miqo mata, dube-dube take tana neman abinda zata bashi

“Kofin… Kiban kofin Waheedah…”

Abdulkadir ya fadi a gajiye, babu abinda ya canza a tattare da ita, sai girma da ta kara mishi. Kofin ta miqa mishi ya karba yana wucewa ya mayar kitchen, yana fitowa hanyar kofa ya nufa, sai lokacin Waheedah ta samu bakinta ya motsa saboda wani irin yanayi da take ji da bazai misaltu ba

“Baka dauki komai ba”

Dawowa yayi ya dauki kankana guda daya yasa a bakinshi tukunna ya fice daga dakin. Cikin sanyin jiki Waheedah ta miqe daga falon, har wani zazzabi-zazzabi take ji yana shirin kamata, yanayi ne da kusanci da Abdulkadir ne kadai yake haifar mata dashi. Gama aji shidda, cin nasara a duk matakin da daliban da suke son samun gurbin karatu a jami’ar Bayero suke bukata baisa Abdulkadir yabar zuciyarta ko na minti daya ba. Bataji dadi ba da Nuriyya bata samu gurbin karatu a Bayero ba itama, sai nan Poly Abba yai mata cuku-cuku ta samu Business administration, kuma karfin karatun tun daga kan kudin makaranta da komai shiya fadama mahaifin Nuriyyan zai biya, hakan ba karamin zumunci ya kara tsakanin gidajen nasu ba. Su dukan su sai bayan sallar zasu fara registration. 2

STORY CONTINUES BELOW


Zuwa yanzun tasan cewar son Abdulkadir din take, wani irin so take mishi da rashin algus din da yake ciki har mamaki yake bata. Son Abdulkadir take irin soyayyar da ta ginu domin Allah, soyayyar da babu wani tsammani a cikinta, soyayyar da take jin ko ta samu kwatankwacinta ko akasin hakan duk ba matsala bane ba, zuciyarta abu daya take gane mata, shine son Abdulkadir. Nuriyya kadai ta furta ma data kalleta sau daya tana ci gaba da abinda take a lokacin, bata sake mata maganar ba, itama kuma Nuriyyar bata tayar mata da zancen ba. Hakan yasa Waheedah dauka ko Nuriyya tana tunanin wasa take mata. 1

Dakyar ta iya wucewa dakin su, inda ta samu Amatullah na sallah. Bandaki ta wuce itama ta gabatar da alwala, dakyar tayi gefe da tunanin Abdulkadir ta gabatar da sallar Magriba. Ko da ta fita falo duk suna nan, an cika falon ko ina tarkace ne ana hidimar shan ruwa. Kan kujera Waheedah ta zauna, Yazid na tashi daga inda yake ya koma kusa da ita, hannun shi riqe da kofin shayi

“Na dauka ai ba zaki fito ba”

Ya fadi yana kallon Waheedah, da tunda Mami ta aike su cefane da yamma take fada mishi yanda azumin yake wuju-wuju da ita. Murmushinta tai mishi da yake jin yana nutsar da wani abu da baisan a tashe yake ba cikin kirjin shi. Duk idan tai mishi murmushi haka yakan ji kamar ya bude bakin shi ya furta mata yanda ya gama tsara gabaki daya rayuwarshi da ita, amman ya rasa abinda yake danne shi, gani yake kamar har yanzun da sauran yarinta a tattare da Waheedah din, hakan kuma nada alaqa da tazarar shekarun da yake tsakanin su. 7

Waheedah tasan ya kamata taci wani abu, amman idanuwanta kafe suke kan kofa tana jiran shigowar Abdulkadir

‘Dan Allah Hamma baka shigo ina sallah ka sake ficewa ba. Dan Allah karkai mun haka, bamu gaisa ba, ban gaisheka ba’

Take fadi cikin zuciyarta. Yazid fuskarta yake kallo yana tunanin abinda yasa ta nutsuwa haka

“Waheedah…”

Ya kira a hankali yana sata raba idanuwanta daga kan kofar tana sauke su akan shi

“Kici wani abu… Tun dazun kike kiran yunwa”

Batare da tace komai ba ta miqe tana nufar kitchen. Akwai wake da shinkafar da Mami tayi musu jiya, jallof ce tasha busashen kifi da nama, sosai tayi mata dadi shisa data rage ta kwashe ta saka a fridge. Daukowa tayi tana saka robar a microwave ta kunna dan ta dumama. Tsaye tai a kitchen din har saida ta fara jin kamshin abincin alamar yayi, ta fito da robar kenan taji muryar Abdulkadir

“Menene kike dafawa? Ina ci…”

Juyowa tayi da murmushi a fuskarta, tana jin kusancin shi fiye da tazarar dake tsakanin su, tana jin shi har kasan zuciyarta.

“Hamma…”

Kananun idanuwan shi ya kankance mata 2

“Yaushe kazo? Ashe zaka zo”

Numfashi Abdulkadir ya sauke yana amsa ta da

“Banyi niyyar zuwa gida ba yanzun. Ba yanzun naso zuwa ba”

Cike da rashin fahimta Waheedah take kallon shi, idanuwan shi daya sauke cikin nata na saka wani abu tsirga mata har tsakiyar kanta

“Hamma…”

Ta furta muryarta can kasan makoshi, kai Abdulkadir ya dan daga mata, da gaske yake har zuciyarshi, baiyi niyyar zuwa gida ba sam, saboda tunda ya tafi Nuriyya na manne a wani waje tare dashi, duk kokarin dayai na ganin ya cirota daga duk inda take maqale dashi ya kasa. Bakon abune a gurin shi, tun tasowar shi abinda duk yasa ranshi sai yayi shi yakeyi, ko da su Hajja zasu karya shine kuwa. Shisa kasa cire Nuriyyan yake bata mishi rai. Suna shawowa kwanar gida shi da Yassar da yaje ya dauko shi komai na sake danne shi. Saima daya fito daga mota yana sauke idanuwan shi kofar gidansu, da zuciyarshi a makoshi saboda dokawar da take ya shiga gida. 4

STORY CONTINUES BELOW


Har yanzu kuma ranshi a bace yake jin shi, saboda bayason fara tunanin abinda mannewar da Nuriyya tai mishi yake nufi, sam bayaso, babu abinda hakan zai haifar mishi banda raini. Yana ganin yanda waje kadan Nuriyya take jira ta samu ta raina shi, ba sai an fada mishi ba, a yanayinta da fuskarta ya karanci akwai wannan halayyar a tare da ita. Shikam a duniya raini ne babban abinda bayaso, ko wanda suke da tazarar shekaru a tsakanin su bayaso su raina shi, shisa yake bala’in rike girman shi. Watan shi biyu da komawa Kaduna yaji yanda kwata-kwata bayason komawa Kano. 1

Koda zai koma din banan kusa ba, a qalla ya kara daukar wasu shekara biyun tukunna, wataqila hoton Nuriyya ya disashe mishi daga cikin kai. Amman duk idan ya kwanta ya rufe idanuwanshi baya ganin komai sai fuskar Waheedah da alkawarin da yai mata na cewar zai zo hutun sallah.

‘Da gaske zaka zo? Dan Allah kazo Hamma, kaji… Kazo dan Allah’

Shine abinda yake mishi yawo duk lokacin dayai tunanin kin zuwa hutun sallar, ran shi a bace yake, baisan wazai dorama ba, shisa ya zabi ya raba bacin ran da ita, tunda itace dalilin sakashi dauko kafafuwan shi daga Kaduna zuwa Kano.

“Ke kika sa nazo…alkawarin danai miki yasa ni zuwa. Jibi zan koma”

Yai maganar, kallon da yake mata nasaka tajin wani radadi a kirjinta da ba zatace ga daga inda yake fito ba. Kallon ta yake yana dora mata laifin zuwan dayayi, duk da hakan bai hana zuciyarta jin dadin zuwan nashi ba, koba komai tagan shi. Amman ita bata ce yai mata alkawarin zaizo ba, batasan me yasa yake kallonta ba.

“Ki bani abinci nikam”

Abdulkadir yace yana dauke idanuwan shi daga kanta, bayason ganin yanda take kallon shi kamar tana son sanin dalilin dayasa yake dora laifin zuwan shi akanta. Bayan ita ce dalilin da yasa shi zuwan tun daga farko, da bata kalle shi da idanuwanta din nan ba, da bata kalle shi da farar fuskarta tasa shi alkawarin da yake dana sani ba, babu abinda zai kawo shi Kano. Sai dai bacin ran da yake ciki bashi da alaqa da abinci. Bai taba fushi da abincin ba, cikin shi daban, abinda yake faruwa dashi daban. Plate Waheedah ta dauko ta dauraye, gabaki daya wake da shinkafar ta juye mishi, tana kallon shi ya dauko cokali kafin ta gama zubawa.

Mika mishi plate din tayi ya karba, yana shirin juyawa tayi saurin fadin

“Hamma…”

Sai dai sauran kalaman sun maqale mata, batama san me take shirin ce mishi ba, gashi ya kafeta da kananun idanuwan shi da suke rikita mata lissafi, kanta ta sauke kasa tana kallon kafafuwanta. Yakai mintina biyu a tsaye, ganin batada shirin magana yasa shi juyawa. Mami daya gani a falon zaune ya kalla da fadin

“Sannu da shan ruwa”

Da fara’a ta amsa shi tana dorawa da

“Abdulkadir. Saukar yaushe?”

Duk yanda yaso yayi murmushi ya kasa, ranshi a bace yake har lokacin, a gajiye yace

“Dazun…”

Kai Mami ta jinjina sanin halin Abdulkadir, wucewa yai abin shi, har ya kusa kofa yaji Yazid na tambayar

“Yaushe kuka karaso?”

Juyowa yayi yana kankance ido yace

“Meka sa a kunnen ka?”

Kai Yazid din ya girgiza mishi

“Bansa komai ba”

Ya amsa cike da rashin fahimtar tambayar Abdulkadir din

“Me yasa kake tambayata abinda na amsa yanzun to? Salon in magana kace na maka rashin kunya?”

Murmushi Mami tayi tana mishi addu’ar shiriya a ranta kafin ta mike tabar wajen. Ba za’ayi koma menene a gabanta ba. Hannuwa Yazid ya daga cikin nuna alamun saduda

STORY CONTINUES BELOW


“Allah ya baka hakuri…”

Juyawa Abdulkadir din yayi da shirin ficewa daga dakin, yaga Nabila tsaye a bakin kofa, taga alamar ranshi a bace yake, shisa tai tsaye dan kar ya sauke tambotsan akanta

“Ubanki kike a bakin kofa?” 2

Ya tambaya yana watsa mata harara, juyawa tayi da niyyar komawa inda ta fito, wani dogon tsaki Abdulkadir din yaja ya fice daga dakin yana nufar bangaren su. Nuriyya na manne dashi ya rasa yanda zai ya cirota, haushin kowa yake ji, komai yaci karo dashi qara bata mishi rai yake. Kofar dakinsu yagani adan bude, dubawa yayi yaga takalmine ya tokareta. Tsugunnawa yayi, plate dinshi a hannu daya, yasa dayan hannun ya dauko takalmin yana juyawa yai cilli dashi, kiris ya make Yasir da yake tahowa

“Anzo an ajiye wani banzan takalmi salon sauro ya cika mana daki” 1

Yake fadi shi kadai yana sauke numfashi. Karasowa Yasir yayi yana kallon ikon Allah

“Kai kuma kaida wa? Kake ta huci kamar kububuwa”

Batare da Abdulkadir ya juyo ba yace

“Ban sani ba…”

Ya wuce yana shigewa cikin dakin. Yasir baisan meyasa yanayin Abdulkadir din ya bashi dariya ba, dariya yake sosai a bakin kofar daya kasa karasa shiga ma. Har cikin ranshi Abdulkadir yake jin dariyar Yasir din, kofar dakinshi ya tura yana shiga hadi da rufeta da karfin gaske. Idan harya koma yaima Yasir magana fada zasuyi, yanda yake jin ranshi a bace, kan wanda zai huce yake nema. Abincin yacinye tas yasha ruwa, ganin idan ya zauna tunanin da baya buqata zai danne shi, fitowa yai ya tafi masallaci abinshi.

*

Kirjinta take ji kamar an dora dutse, tana isha’i ta wuce daki ta kwanta abinta, daya daga cikin hoton Abdulkadir din da yake cikin qaramin pillow dinta ta saka hannu ta zaro tana dubawa, shigowar Amatullah dakin yasata saurin mayar da hoton inda ta dauko shi. Waje Amatullah ta samu gefen gadon ta zauna tana ajiye robar dake hannunta a kasa tana fadin

“Hajiya Adda ai saikin sauko kasa ko?”

Cikin rashin fahimta Waheedah tace

“In sauko kasa in miki me?”

Ware idanuwa Amatullah tayi

“Lallai Adda Wahee… Kunshin fa”

Numfashi Waheedah ta sauke, sam ta manta da wani maganar kunshi, kitso daman Nuriyya tai mata, guda goma tace ma. Nuriyya bata saurareta ba tayi mata qanana duk da kan bawani gashin kirki yake dashi ba. Ba zata iya bin layin wani baqin qunshi ba, amman Amatullah ta iya jan lalle kala-kala, duka yan gidan ita tai musu.

“Ni na manta da wani kunshi. Dakin barni Amatu, jikina ciwo yake mun”

Tunda ta fara magana Amatullah ke girgiza mata kai

“Wallahi baki isa ba Adda, tunda ba takaba kike ba. Lallena dana kwaba fa? Waye zai amfani dashi. Bama zai yiwu bane ba, har Mami tayi jan lalle….ni wallahi da ina da farin ki da anga lalle”

Yar dariya Waheedah tayi, Amatullah din ba baqa bace, amman kuma ba zaka kirata fara ba, tana da hasken fata irin na yawancin yaran gidan Bugaje din.

“Kifa sauko…”

A kasalance Waheedah din ta sauko daga kan gadon. Tasan halin Amatullah idan ba’ayi kunshin ba fushi zata dauka da ita. Tsegumi kam sai kanta ya fara juyawa, gara tayi ta huta. Hira suke tabawa ita da Amatullah din har ta gama saka mata lallen a duka kafafuwa da hannuwanta, ita ta taimaka mata tahau kan gado ta kwanta, gabaki daya duniyar take ji ta tattaru a hannuwanta da kafafuwanta da suke a daure da ledoji. Ita kam bataga komai a cikin kunshi banda wahala ba. Batajin zata iya bacci da wannan ledojin a jikinta, da wannan tunanin bacci ya dauketa cike da mafarkin Abdulkadir.

STORY CONTINUES BELOW


*

Washegari kasancewar safiyar sallah, yanayin garin kanshi yayi sanyin da safiyar sallah ce kadai kan haifar. Tunda suka tashi suke hidimar su, Waheedah bata ga kunshin taba sosai saida gari ya fara wayewa tunda babu wutar lantarki. Kyau yai mata sosai, gashi ya kama har wani ruwan kasa-kasa mai cizawa yake. Da gudu ta taho tana rungume Amatullah da take tsaye ta baya

“Kinsan ina son ki ba?”

Ta fadi, Amatullah din na tureta

“Soyayya da sokamun kasusuwa?” 2

Dariya Waheedah tayi tana sake komawa ta riqe Amatullah din dake kiciniyar kwacewa gam

“Adda Wahee mana”

Amatullah ta fadi tana samu ta ture Waheedah din, da murmushi a fuskarta, Mami ce ta fito ta gansu

“Mami kalli kunshina”

Cewar Waheedah tana daga ma Mami hannuwanta, jinjina kai Mami tayi

“Ma shaa Allah. Yayi kyau sosai kuwa, yanzun kika zama yan mata”

Shagwabe fuska Waheedah tayi

“Me kike nufi Mami?”

Amatullah ta karbe zancen da amsa ta

“Kinfi kowa sanin me take nufi”

Numfashi Mami ta sauke

“Nikam ku matsamun ina da aikin yi”

Matsawar sukai ta wuce, suna rufa mata baya zuwa kitchen din. Wanke-wanke sukayi ita da Amatullah din. Sun gama kenan, Amatullah ta fice daga kitchen din, Nuriyya tai sallamar da Mami ta amsa mata tana dorawa da

“Nuriyya idonki kenan?”

Dariya Nuriyya tayi, dan kwana biyu bata shigo gidan ba, itama sunata hidimar sallah

“Wallahi Mami inata kitso ne fa. Ina kwana”

Murmushi Mami tayi

“Lafiya kalau, ya kowa da kowa?”

Da murmushi a fuskar Nuriyya take amsa Mami data fice daga kitchen din bayan sun gama gaisawa. Hijab dinta Nuriyya ta cire tana dorawa kan window din kitchen din, yanayin da yasa Waheedah kallon ta

“Naga kin cire hijab”

Kai Nuriyya ta jinjina

“Bazan cire in sha iska ba?”

Yar dariya Waheedah tayi, idan wani yaga Nuriyya ta cire hijabin zaiyi zaton aiki zata tayata, ita da yake tasan hali bata saka a rai ba, dan Allah ya zubama Nuriyya qwiya, ko aikin gida aka sakata sai ta zuba ha’inci a ciki, wani lokaci Maman su na kallonta zata tsallaketa tayi aikinta, a cewarta ko wanke-wanken Nuriyya ba fita suke ba, haka zakaga maiqo cikin kofuna.

“Ke jiya Anas yazo da daddare, saima bayan isha’i tukunna”

Nuriyya ta fadi wani tattausan murmushi na bayyana a fuskarta da yake nuna alamun Anas din ba karamar hidimta mata yayi ba. Sun hadu ne lokacin da suka kai mishi dinkin uniform din Nuriyya na Green Olive, Yazid ne ya hadasu dashi a cewar shi yakan mishi dinki wasu lokuttan, basu da nisa dashi sosai tunda suna kofar ruwa ne, shikuma yana Kurna babban layi ta wajen yan doya. Kusan tun lokacin ya manne ma Nuriyya, da yake ana barinta fita zance, sukam gidansu saika gama sakandire tukunna. Anas ya gama diploma dinshi a yanda Nuriyya take fadama Waheedah, sai dai baici gaba ba, shine babba a gidansu, kuma Allah yaima mahaifinshi rasuwa, hakan yasa yai tsaye kan sana’arshi ta dinki da take kawo mishi rufin asiri dai-dai gwargwado. 1

Dan a cikin sana’ar yake ma kanshi da mahafiyarshi harma da yan uwanshi duk wata hidima, duk a yanda Nuriyya take sanar da ita, yana da gidanshi na gado mai daki falle-falle guda biyu, sai bandaki da kitchen, dan in yanzun Nuriyya ta bashi dama a shirye yake daya turo a tsayar da magana. Abinda baisani ba shine ko kadan Nuriyya bata jinshi a ranta, duk da Anas bashida wata makusa a matsayinshi na matashi, yana da kyau na misali da cikar zarrah, ga nutsuwa da kamala shimfide a fuskar shi. Ko kadan Anas ba tsarin aurenta bane ba, bashi bane mijin da take buri.

STORY CONTINUES BELOW


Tana kulashi ne saboda hidimar da yake mata, hannun shi a bude yake, ko yaushe cikin mata hidima yake, sau biyu yakanzo a sati, duk zuwan da zaiyi da kalar kayan ciye-ciyen da zai kawo mata. Da sallar nan kaya yai mata kala uku, mayafi harda jaka da takalmi, shi yai mata dinkunan, ya kuma kawo dubu biyu ya bata tayi kitso da kunshi. Sosai Waheedah take son Nuriyya da Anas din saboda yanda yake da nutsuwa da kuma son Nuriyyan da take gani a tattare da yanayin shi.

“Turarenki yana gida…”

Nuriyya ta sake fadi tana yar dariya. Tana kara jin dadin yanda haduwa da Anas take bata damar yima Waheedah kyauta irin haka.

“Dan Allah fa… Turare ya kawo miki?”

Waheedah ta tambaya cike da jin dadi itama, kai Nuriyya ta daga mata

“Har guda uku ma”

Dan bude baki Waheedah tayi

“Aikam baki isa ba saina zaba… Mai kamshin cikin nake so”

Yar dariya Nuriyya tayi

“Banza in munje gidan duk wanda kike so saiki ta dauka. Ina da wasu ai”

Karasa share kitchen din Waheedah tayi suna hirar Anas din da Nuriyya

“A fara poly Anas ya turo musha biki”

Hade fuska Nuriyya tai waje daya

“A’a kin manta, uwar biki zaku sha”

Dariya Waheedah takeyi

“Ki daina mun wannan wasan, nace miki ina son shine?”

Kai Waheedah take girgiza mata

“A’a amman kina karbe mishi kaya ai, wallahi Nuriyya kar Allah ya kamaki”

Tsaki Nuriyya taja tana daukar hijab dinta daga kan kofa tana sa Waheedah tambayar ta

“Ina zakije?”

Ko kulata Nuriyya batai ba, ta saka hijab dinta, dan ta gama bata mata rai, wato fatan ta auri Anas take mata, dan karta huta. Ko a hanya aka ganta ansan batai kalar auren tela ba, diplomar da yake da ita ya fada mata bashida niyyar cigaba, tunda yana da tsayayyar sana’a, ita kam sai wanda yake zuwa office, babu abinda zatai da tela.

“Hamma yazo…”

Waheedah ta fadi cikin sanyin muryar da yasa zuciyar Nuriyya wani irin dokawa, da sauri ta juyo

“Haba dai…”

Kai Waheedah ta girgiza mata

“A’a ki tafi, ba tafiya zakiyi ba?”

Dan murmushi Nuriyya ta dora kan fuskarta

“Dallah ai kece kike son batamun rai. Ban labari yaushe Hamma din yazo?”

Wannan karin wani tsadadden murmushine ya bayyana kan fuskar Waheedah

“Allah Nuriyya ina son shi fa…”

Wani zafi Nuriyya taji kirjinta ya dauka, ta fada mata kwanaki, bata kulata bane, saboda tayi kamar sai lokacin tasan tana son Abdulkadir, batasan meyasa take maimaita mata ba yanzun

‘In shaa Allah ba zaki taba samun shi ba’

Nuriyya ta fadi a cikin ranta, a fili kuma tabe baki tayi tace

“Kina da hankali kuwa?”

Narai-narai Waheedah tayi da idanuwa, ita kanta tasan batada hankali, ta kuma san ta rungumowa kanta dala ba gammo

“Bansan yazan ba Nuriyya. Nasan banda hankali, shisama ban taba tunanin samun shi ba, kawai dai nasan ina son shi”

Ta karasa maganar muryarta cike da rauni

STORY CONTINUES BELOW


“Yafi miki alkhairi…”

Nuriyya ta fadi a taqaice tana dorawa da

“Bari inje gida… Zan dawo anjima”

Dan batasan Abdulkadir ya dawoba da ba zata shigo gidan haka ba, sauri zatayi taje gida tai wanka ta tsara kwalliya tukunna ta dawo, batasan me yasa ba, haka kawai taji bataso yaganta batare da tayi kwalliya ba. Kai kawai Waheedah ta iya daga mata dan batajin zata iya wata magana, tunanin Abdulkadir ya cika zuciyarta fal.

*

Yassar na kula da yanayin Abdulkadir din tun jiya da yaje dauko shi, dayake sunyi waya a bakin gate ya same shi tsaye da jakar shi, batare da yace ma Yassar din komai ba ya zagaya ya shiga mota. Hannu ya saka ya kunna radio din motar cikin nuna ma Yassar din alamar bayason yin magana. Haka daren jiya duk wanda yazo dan su gaisa da masifa Abdulkadir din yake amsa su, kamar sannu da zuwan nasu na kara mishi bacin ran da Yassar ya kula yazo dashi. To yau ma da alama da yanayin ya tashi, shisa tun asuba bai koma dakin nashi ba, duk da zai karya idan yace abin bai dame shi ba.

Maballan kayansu da tela bai saka musu ba Yassar din yake sassaka musu a jikin riguna, daga shi sai Aminu a falon, dan duk yawanci sun faffara shiga wanka. Abdulkadir ne ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando

“Ina kwana Hamma…”

Aminu ya gaishe dashi sanin halin shi, shiru Abdulkadir din yayi, hakan yasa Aminu sake gaishe dashi dan a zaton shi ko baiji bane, daquna fuska Abdulkadir yayi

“Karka dameni Aminu, meyasa zaka fara gaisheni tunda sassafe” 3

Numfashi Aminu ya sauke yana jinjina kanshi kawai, da idanuwa Yassar yai mishi alama da yabar falon, bai musu ba ya miqe ya nufi dakinsu, saida ya shiga ya turo kofar tukunna Yassar da bai dago daga maballin da yake sakawa ba yace

“Me yake damunka?”

Zagayawa Abdulkadir yayi ya zauna inda Aminu ya tashi, bayason yin magana, bayaso ai mishi magana, komai baya mishi dadi

“Da kai nake, me yake damunka?”

Yassar ya sake tambaya wannan karin yana sauke idanuwanshi kan fuskar Abdulkadir da babu alamar walwala a tare da ita

“Karka dameni Hamma, dan Allah. Gidane ban niyyar zuwa ba”

Rigar dake hannun shi Yassar ya ajiye yana mayar da hankalin shi kan Abdulkadir din

“Ubanwa yace ka daga waya ka kirani inzo in daukeka to? Idan kasan bakai niyyar zuwa ba saikai zamanka…meyasa zaka zo kana ma mutane bakin rai, ubanka akai maka?”

Yassar yake fadi dan shima ranshi ya fara baci, hakan Abdulkadir ya kula dashi yasa shi fara shirin mikewa dan yabar wajen

“Wallahi idan ka tashi ranka saiya baci, ka zauna ban gama maganar da nake ba…”

Komawa Abdulkadir yayi ya zauna, karshen abinda zaiso a yanayin da yake ciki shine bacin ran Yassar din, yana da zuciya yasani, abinda yake bata mishi rai a kusa yake, amman yana sauka da wuri, wasu lokuttan idan yai duka ko yai fada shikenan. Amman na Yassar daban ne, yakan jima ranshi bai baci ba, amman idan ya baci duka gidan sai hankalin kowa ya tashi

“Meke damunka? Bazan sake maimaitawa ba”

Numfashi Abdulkadir ya sauke yana rasa amsar dazai ba Yassar din, bashida wata kwakkwarar amsa, me zaice mishi? Ranshi a bace yake saboda zuciyarshi nason ja mishi abinda su dukansu bazai musu dadi ba? Ko kuma fada mishi zaiyi yanda yake ta kokarin ciro Nuriyya daga duk inda take a cikin jikinshi kafin ta zame mishi matsala amman ya kasa? Wanne daga ciki zai fada mishi da bazai mishi kallon marar hankali ba, ko zai fada mishi yanda Waheedah ta saka shi zuwa gida bai niyya ba, yanda alkawarin dayai mata yai mishi tsaye a wuya saida ya janyoshi garin kano. Amsar da tafi mishi sauki yaba ma Yassar din

“Bansani ba, komai bayamun dadi”

Numfashi Yassar ya sauke, yanayin da Abdulkadir din yai maganar na saka bacin ran da yake ji soma dishewa.

“Kayita istigfar, tana yaye damuwa”

Kai Abdulkadir ya jinjina mishi yana mikewa tsaye

“Bari inyi wanka… Kayana fa? An dinkamun?”

Dan kallon shi Yassar yayi

“Da bikin su Hamma ai masifa kaimun, na maka dinkin da bai maka ba….”

Daquna fuska Abdulkadir yayi

“Da wanne kayan zanje sallar idi?”

Dan daga mishi kafadu Yassar yayi

“Bakazo da kaya ba?”

Idanuwa ya kankance ma Yassar

“Gajerun wanduna ne fa…”

Maballan shi Yassar yaci gaba da sakawa, ganin AbdulKadir din na tsaye har lokacin yasa shi fadin

“Kamun tsaye a kai”

Da mamaki Abdulkadir yace

“Hamma da gaske baka dinka mun ba?”

Wani kallo Yassar ya watsa mishi daya tabbatar mishi da gaske yai maganar. Kuma da gangan yaki dinka ma Abdulkadir din kaya, saboda rashin kunyar dayai mishi wancen karin, har cayai shi bazai saka wasu manyan kaya ba. Ya fadama kanshi bazai sake dagama Abdulkadir din hannu ba, tunda ba yaro bane yanzun, amman hakan baya nufin bazai nuna mishi kuskuren shi ba. Yana jin Abdulkadir din ya wuce, danko dagowa baiyi ba, ya saka daya daga cikin nashi kayan, idan zasuyi mishi kenan, dan yaga ya kara budewa…!Da kayan shi rungume a kirji ya shiga dakin hadi dayin sallama, bai samu kowa a falon ba sai Yassar daya amsa mishi sallamar yana kuma binshi da kallo yana fadin 1

“Meye a jikin kayan daka rungumosu kamar sabon jariri?”

Murmushin shi Yazid ya kara fadadawa, Waheedah ta goge mishi kayan, akwai kalar kamshin da ya kula tana yi duk idan ta gifta shi a cikin gida, idan zata fitane kawai bayajin yana kamshin, sosai kuma yake jinjina ma kokarinta na wajen ganin ta gujema abubuwan da addini ya haramta mata da mata kan dauka kananun zunubi a zamanin da ake ciki. Haka kawai yau da ita ya tashi manne a ranshi fiye da kowanne lokaci, shisa yakai mata kayan yace ta danne mishi ta kuma shafa mishi turare. Tunda ya amso yake jin kayan har kasan zuciyar shi. 2

“Hamma…”

Yassar ya fadi ganin yanda murmushin Yazid din yake kara fadada da duk dakika.

“Karka dameni Yassar”

Yar dariya Yassar yayi, harda shi cikin yan gidan wajen yima Yazid surutun kin nemo matar aure, amman yanayin da yake nunawa yanzun kamar na sabon kamu a soyayya

“Anya Hamma? Baka kamu ba kuwa?”

Dakuwa Yazid din yai mishi, yana tsintar kanshi da jin wata irin kunyar kanin nashi da ta bashi mamaki. Sosai Yassar yake dariya yanzun kam

“Yaa Rabb… Hamma da gaske soyayya kake? Wace mai sa”ar ce?” 1

Ya karasa tambayar da farin ciki nannade a muryarshi, a kasan ranshi harya fara addu’a da fatan ta gari ce, akance ba’a shaidar mutum, amman zai tashi tsaye yai shaidar dan uwan shi, duk a cikin gidan Yazid ne kawai zai bada shaida akan shi batare da wani shakku ba, ya yarda da nagartar shi dari bisa dari. Yana da tabbacin matar da duk zata kasance karkashin kulawar shi ba zata taba samun dalilin yin koke ba. Yazid mutum ne mai hakuri da kauda kai akan al’amuran duniya. 3

“Wacece Hamma? Kaji? Dan Allah wacece?”

Yassar ya sake jero mishi tambayoyin yana saka shi sauke numfashi mai nauyi. Bai taba fadama kowa sirrin da yake zuciyarshi ba, har ita Waheedah din da sirrin ya shafa, amman yau yana jin ya fada ma wani, yana kuma jin son raba sirrin da wani, watakila ya samu karfin gwiwar fadama Waheedah din itama. Ya kuma san Yassar na da sirri ba kadan ba, idan bashi yace ya fadama wasu ba, maganar ba zata taba wuce tsakaninsu ba. Cikin sanyin murya Yazid yace

“Bata sani ba har yanzun ai”

Dan ware idanuwa Yassar yayi

“Jiran me kake to? Meyasa baka fada mata ba?”

Kafadun shi duka biyun Yazid yadan daga cikin yanayin dake fassara shima baisan dalili ba

“Ina ganin kamar tayi yarinta ne, hakan nake fadama kaina saboda banason tabbatar da na rasa karfin gwiwa ne”

Fuskar Yassar dauke da murmushin fahimta yace

“Ba’a yarinta da sanin ‘So’ Hamma, saboda abune mai wahalar sha’ani…”

Kai Yazid ya iya jinjina ma Yassar din, yanajin jikin shi yayi wani irin sanyi, da gaskene ya kamata Waheedah tasan yanda yagama tsara musu sauran rayuwar shi idan yana da rabon gani, bai taba hango komai na rayuwar aure da wata idan ba ita ba. Ko a titi yaga budurwa da saurayi, ita ce take fado mishi a rai. Idan kallo yake yaga wani abu daya burgeshi, da ita yake hasaso aiwatar dashi. Yana mata kyauta lokaci zuwa lokaci, amman yana jin tamkar ya janyo ranar dazai kashe mata duka kudin da suke cikin aljihun shi, ranar da zai siyo duk rigar daya gani yake tunanin zatai mata kyau ya kawo ta saka mishi yagani. 1

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskarta na mishi yawo a cikin kwanyar shi, wucewa yayi da niyyar shiga daki ya sake kaya, Yassar dakatar dashi da fadin

STORY CONTINUES BELOW


“Ka fadamun sunanta idan ban santa ba”

Saida ya murza hannun kofar dakinsu tukunna yace

“Waheedah… Waheedah ce Yassar”

Wani dum Yassar yaji cikin kanshi, kafin hanjin cikin shi su hautsina suna saka shi mikewa babu shiri ya rufa ma Yazid din baya. Yanda ya tura dakin na saka Yazid din tsorata, wani irin yanayi yake gani a fuskar Yassar daya saka zuciyarshi soma dokawa yana fadin

“Yassar?”

Cike da shakku da alamar tambaya, kai Yassar yake girgiza ma Yazid din yana son ya tabbatar mishi ba Waheedah bace yake so, yana son ya gaya mishi bai hada soyayya da Abdulkadir ba, kallon Yazid din yake da idanuwan shi yana rokon shi da cewar zuciyar shi batai mishi haka ba.

“Yassar…”

Yazid ya sake kira wannan karin muryar shi na rawa cike da tsoro, ko kadan bayason abinda tunanin shi yake shirin hasaso mishi, hannu yadan daga ma Yassar din yana saukewa, kafafuwan shi har rawa yake jin sunayi dan shi mutum ne mai raunanniyar zuciya. Gadon da yake dakin ya laluba ya zauna a gefe, yanajin yanda zuciyarshi ke dokawa har cikin kunnnuwan shi. Yanayin shi kawai da Yassar yake gani na kara tabbatar mishi da yanda ya dade da soyayyar Waheedah adane a cikin kirjin shi batare da kowa yasani ba. Wani abu Yassar din yaji yana danne shi, yanda akai bai kula ba na bashi mamaki, dan shi mutum ne mai kula da al’amuran yan uwan shi. Cikin wani yanayi yace

“Hamma…”

Yana tsintar bakin shi da yi mishi nauyi wajen karasa maganar da yake sonyi. Halin da Yazid din zai shiga yake tunani. Amman ko jiya da yana neman canji, bayan Abdulkadir din yazo ya dauki wallet din shi ya bude hoton Waheedah na jiki a manne, ya kuma ga ya sake wallet din, amman hoton na manne. Yasan kanin shi, yasan kanin shi fiye da kowa a gidan. Idan har ya cire hoton Waheedah daga dayar wallet din ya mayar a sabuwa tana da muhimmanci a wajen shi, idan har zai ajiye hoton daga farko to yana da tabbacin wani abu na faruwa a tsakaninsu. Idan har zai iya bazai bari su hada yarinya daya da Yazid ba, yana numfashi bazai taba bari wannan rikicin ya faru ba.

“Dan Allah Yassar kace wani abu, a tsorace nake wallah”

Yazid din yace yana sa wani abu tsagewa biyu a kirjin Yassar din, da yake tsaye yana tattaro duk wani karfin halin dazai iya

“Ba Waheedah ba Hamma, kowacce yarinya banda ita”

Kai Yazid din yake girgiza mishi yana jin iskar dake dakin na fara yi mishi kadan, cikin sabon tashin hankali yace

“Yassar…”

Da sauri Yassar din ya girgiza mishi kai, ganin yanayin da yake fuskar shi, ya tabbatar Yazid na tunanin shine yake son Waheedah

“Bani bane, Hamma bani bane ba”

Kan shi Yazid yadan dafe da ya fara ciwo, yanajin alamar zazzabi nason rufe shi

“Abdulkadir ne, ba zance soyayya suke ba kai tsaye, amman hoton tane a jikin wallet din shi shekara daya kenan…”

Wannan karin da duk hannayen shi Yazid ya dafe kan shi yana wani irin sauke numfashi kamar wanda yasha gudu. Zazzabin da yake ji na saukar mishi gabaki daya. Dago fuskar shi yayi yana saka hannu ya dauki hular shi dake ajiye akan gadon ya soma fifita dashi, dan sosai iskar dakin ta mishi kadan har bayajin tana kai mishi inda ya kamata ballantana ya iya tunanin wani abu. Shi kanshi Yassar din wani irin nauyi yake ji yana danne shi da bazai ce ga daga inda yake tasowa ba, amman Yazid din ya kamata yasan abinda yasani shima. 1

“Koni ba kullum nake kallon fuskar Abdulkadir in fada mishi magana ba, badon ina tsoron shi ba, sai dan ina gudun ya fada mun maganar da zan dake shi saina karya shi.

STORY CONTINUES BELOW


Ina kula dasu Hamma, cikin ido Waheedah take kallon shi tai mishi magana…”

Sosai Yazid yake fifita fuskar shi, muryar shi can kasan makoshi yace

“Kadan bani waje…”

Cike da wani irin yanayi Yassar yake kallon shi

“Hamma…”

Kai Yazid ya girgiza mishi, zuciyarshi yake ji ta kumbura ta cika kirjin shi taf, bayason ta tarwatse a gaban Yassar, bayason ta tarwatse a gaban kowa 5

“Dan Allah Yassar… Bana son in breaking a gabanka… Abin zaimun yawa…” 1

Numfashi Yassar din ya sauke yana kallon Yazid sosai, cike da son tabbatar da koma meye zai biyo baya, koya Yazid din zai karye, zai iya komawa dai-dai. Kamar Yazid yasan me Yassar din yake tunani yadan tattaro sauran karfin da yake ji yana mishi murmushi hadi da jinjina mishi ka cike da son tabbatar mishi cewar wannan abin bazai kashe shi ba, tukunna Yassar ya juya ya fita daga dakin. Kofar na rufewa Yazid ya kwanta kan gadon yana dunkule jikin shi. Wani irin ciwo yake ji da bai taba tunanin akwai kalar shi ba. 1

Numfashin shi har tsai-tsayawa yake da yanda kirjin shi yake zafi, yana jin yanda da duk dakika wani abu a zuciyar shi yana karyewa hadi da faduwa a cikin kirjin shi da wani irin ciwo da bashida kalaman dazai dora shi. Baisan tunanin me ya kamata yayi ba, asalima tunani daya yake cike da kan shi da zuciyar shi dake karyewa.

‘Bazai hada soyayya da kanin shi ba’ 1

Ko rana aka saka mishi da Waheedah yagane Abdulkadir din najin ta a zuciyar shi fiye da matsayin kanwa zai hakura yabar mishi, idan ma Allah bai nufa zai aureta ba, su biyun zasu hakura ta samu wani. Amman soyayyarta zata kashe shi kafin ya hadata waje daya data kanin shi. Yanzun yake kara godema Allah da bai furta mata ba, yana kuma tabbatar da wannan ne dalilin daya rike shi harya kasa furta mata. Yafi minti goma a kwance yana son ciwon da yake ji ya lafa mishi ya tashi ya saka kayan shi dan masallacin idi zasu tafi su duka gidan.

*

Tana fitowa wanka, mai ta shafa ta zura doguwar rigar sabuwar atamfarta, dankwalin ta daura yanda zata iya dora hijab akai batare daya dameta ba. Fuskarta ta duba a mudubi, atamfar yellow ce da ja, tayi matukar karbar hasken fatarta, maikon fuskarta taga kamar yai yawa. Farar hodar da take shafawa ta dauka ta zazzaga a jikin soson hodar Amatullah dan ba zata tuna ko tana da soson hoda ko bata dashi bama. Murzawa tayi a fuskarta ta ajiye tana sake dubawa. Kayan kwalliyar da banda farar hodar da wasu cikin turarukan dukan su sauran na Amatullah ne take dubawa.

Rasa wani abu da zata dauka tayi amfani dashi tai. Ko a gida zata zauna bata tunanin zatayi wata kwalliya fiye da wadda take fuskarta, ballantana fita zasuyi, su dukan su suke zuwa masallacin idi a gabatar da sunnar da take cikin zuwa sallar idi. Fuskar mace kan shiga cikin al’aura, wato abinda ya kamata ya zama a rufe duk lokacin da ta tsara mata kwalliya, sharadin saka niqab ya fada akanta koda batada kyawun dazai karya alwalar maza. Tana yawan tunasar da Amatullah da Nuriyya, amman biris suke da ita, wasu lokuttan ma Nuriyya kan ce mata ita ta cika tsawwala lamurran addini.

Sai dai tasan zunuban da yawancin mutane kan dauka kanana, sune suke taruwa a hankali har suyi girman da mutum bazai iya dauka ba. kwalli ta hango ta dauka ta sakama idonta, tana ganin yanda fuskarta ta sake fitowa. Da gaskiyar Mami, kwalli na mata kyau. Mikewa tayi ta dauki turare ta tuna fita zatayi, ta mayar ta ajiye. Hijab dinta da take a linke ta dauka ta warware tana sakawa a jikinta. Doguwa ce har kasa, sai dai babu hannu a jiki, tana kuma sane ta dauko dan kunshin da yake hannuwanta.

Kafafunta ma safa ta saka musu, batai kunshi dan mazan da ba muharramanta ba, tayine dan kwalliya. Dogayen takalmanta da suke ajiye ta saka. Amatullah kan mata tsiya cewar tana saka dogayen takalma ne dan bata da nauyin da zata dinga gurdewa. Dariya kawai Waheedah kan yi, ta riga ta sabane da dogayen takalman tun yarinta, gashi kuma hijabanta wani lokaci suna dan jan kasa, idan ta saka dogayen takalman sai taga sunfi kyau. Bata ga Mami a gidan ba, har dakinta ta leqa bayan ta fito, tana da tabbacin suna bangaren Hajja danyin hidimar bikin sallar da suke haduwa su duka hudun suyi.

STORY CONTINUES BELOW


Dan haka ta fice daga gidan itama, yau dai ta shirya da wuri, badan gugar da taima Yazid bama da tuni ta jima da shiryawa. Babu mai mata mita ta cika sanyin jiki. Takawa tayi har inda ake ajiye motocin gidan tana samun guda daya ta tsaya a jikinta, saitin da zata iya hango bangaren su Abdulkadir, dan shi take so tagani tunda ta tashi. Tafi minti biyar a tsaye kafin ta hango shi ya fito, jikin shi sanye da farin yadi da hula rike a hannun shi cikin yanayin da yasa bugun zuciyarta karuwa. Dago kai taga yayi yana tsayar dashi akanta. Bata hango idanuwan shi daga inda take, murmushi ya kwace mata.

Sosai take murmushi da yanda mazaunin idon AbdulKadir din kawai take iya hangowa daga inda yake. Hakan yasata sauke kallonta daga kan shi, zata rantse idanuwanta kawai ta sauke tana kallon takalmanta, ta sake dago su taga Abdulkadir din tsaye a gabanta yana kankance mata idanuwan shi, zuciyarta taji cikin makoshinta inda tai tsaye tana ci gaba da dokawa.

“Murmushin me kike?”

Ya tambaya yana tsare ta da idanuwa, dan shi baiga abin nishadi a safiyar ranar ba, kan shi ciwo yake. Gashi komai baya mishi dadi, kai ta girgiza mishi tana saka shi fadin

“Taqabbal Allaahu minna wa minkum”

Ya dora da

“Ba’aimun dinkin sallah ba” 4

Cikin yanayin da ya saka wani murmushin kwace mata, dan yanda yai maganar kamar karamin yaron da akaima gagarumin laifi ya sakata jin tamkar tana kan lilo. Komai nashi ya mata, komai a tattare dashi. Amsa gaisuwar sallar da yai mata tayi a hankali har lokacin tana murmushi

“Ba abin murmushi bane ba, kayan Hamma Yassar na saka, basumin dinkin sallah ba, kowa an mishi banda ni” 2

Abdulkadir din ya fadi yana rasa dalilin da yasa yake gaya mata. Kawai ya tsinci kanshi da son gaya mata ba’ai mishi dinkin sallar ba, yana kuma jin son gaya mata duniyar ma bata mishi dadi, baisan ta inda zai fara ba. Idan tana kusa dashi yakan tsinci kanshi dayin abubuwan da baisan dalilinsu ba. Abu daya yake gani a fuskarta, zai iya yin komai a gabanta, ba zata taba raina shi ba, bai taba ganin hakan a fuskar kowa ba sai tata, ko Yassar bakomai yake iyayi a gaban shi ba, a hakan ma ya raina shi dan yana ganin ya bashi wasu yan shekaru, shisa yake kokarin ganin ya kama girmanshi a gaban Yassar din. 2

Dayan hannun shi ya dago ya bude mata shi, links ne a cikin tafin hannun nashi. Hakan yasata tattaro hijab din jikinta ta fito da hannayenta da Abdulkadir din yabi da kallo, zuciyarshi na fada mishi bai taba ganin hannuwa masu kyau irinsu ba. Links din ta saka hannu ta dauka, Abdulkadir na rike hannun nata

“Kunshi kikayi”

Maganar ta fito daga kasan makoshin shi lokacin da ya dago dayan hannun shi yana kamo dayan hannun nata dashi hadi da duba kunshin nata da yakejin na kwance wasu kusoshi cikin kanshi. Wani irin yanayi yake ji da bazai fadu ba. Motsi yaji a bayan shi, amman bai juya ba, asalima bayason ya dauke idanuwan shi daga hannuwan Waheedah din, a karo na farko da ko kadan tunanin hasken fatarta baizo mishi ba, baya ganin komai sai jan lallen dayai wata irin fitowa a hannunta. 1

Tun daga nesa Yazid ya hango su, yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje, dan zazzabi ne a jikin shi ruf, dakyar ya iya fitowar ma, baisan kafafuwan shi sun motsa ba lokacin dayaga Abdulkadir din ya rike hannun Waheedah sai da yagan shi tsaye a bayan shi, amman daga Waheedah din har Abdulkadir sunyi kamar basu san yana wajen ba. Musamman Waheedah da yake ganin tsayuwar duniyarta akan Abdulkadir din ta cikin idanuwanta, tana saka shi tuna duka lokuttan da yake ganin hakan a idanuwanta idan Abdulkadir na wajen, yana sakashi tunanin kalar sakarcin shi wajen kasa fahimtar abinda yake faruwa a tsakaninta da AbdulKadir din, dan yana tunanin tayi yarinta ta fahimci wani So ballantana harta fada cikin shi.

“Waheedah…”

Yazid din ya kira yana saka zame hannuwanta daga cikin na Abdulkadir tadan kalli bayan shi inda Yazid yake tsaye 2

STORY CONTINUES BELOW


“Hamma…”

Ta fadi tana saka Abdulkadir din juyawa ya kalli Yazid din shima

“Taqabbal Allaahu minna wa minkum”

Abdulkadir ya fadi yana mikama Yazid din hannu, karba yayi ya amsa yana kuma yi musu murnar sallah a bisa tsarin addinin musulunci tukunna ya zagaya ta bayan motar ya tsaya, dan kirjinshi yake ji kamar zai bude. Juyawa Abdulkadir yayi yana mikama Waheedah hannuwan shi. Dai-dai lokacin da Yazid din ya juyo yana kallon su, links din Waheedah ta daura mishi, idanuwan shi nakan hannayenta da yake jin kamar ya yanke ya koma Kaduna dasu, ya manna a jikin bangon dakin shi, duk lokacin dayai ra’ayi ya juya ya kalla. Hakan dayai tunani ya saka shi laluba aljihun shi ya zaro wayarshi daga ciki.

Waheedah na kallon shi, zuciyarta kamar zata fito waje. Tana kuma kallon shi yana danna wayar, kafin ya kamo hannunta yana mikar dashi, ya kuma kamo dayan ya dora a kan dayan cikin yanayin yanda yake son yagan su, ita kam a gabanshi takan koma kamar yar tsana mai batir da remote, remote din kuma yana hannun Abdulkadir, yanda duk yake so tayi hakan yake juyata. Idanuwanta tsaye yake kan fuskar shi, tana jin yanda yake rike da yan yatsunta, kafin ya saki yana duba wayarshi hadi da dan daga mata kai cikin yanayin da yasata sauke hannuwanta tana murza su cikin hijab, har lokacin tana jin nashi hannuwan manne a jiki. 2

Kanshi Abdulkadir yadan dafe daga gefe yana runtsa idanuwa, tukunna ya bude su akan Waheedah yana fadin

“Kaina na ciwo…”

Bata ce mishi komai ba yaga ta juya da sauri, yana bin takalman kafarta da kallo, ko tunanin ta fadi cikin dogayen takalman nan batayi. Yana kuma kula da yanda kusan duka takalmanta dogayene. Bayan shi ya jingina da motar yana duba hoton hannuwanta a cikin wayar tashi, blackberry badai camera ba, sosai hoton ya dauku, shiya mayar kan wallpaper din shi daman hoton wani lallen ne, wannan dai yafi mishi kyau. Baisan lokacin da yasa hannu ya shafi screen din wayar ba, yana karama Yazid zazzabin da yake ji. Dan yana kallon duk abinda yake faruwa, bai daisan haka zai mishi zafi na gaske ba. 1

“Abdulkadir…”

Ya kira a hankali yana saka Abdulkadir din juyawa ta bangaren da yake ya kalle shi

“Karka sake rike Waheedah, akwai haramci a hakan, kasani ba saina fada maka ba, ba muharramarka bace ba” 2

Dakuna fuska Abdulkadir din yayi

“Kunshi tayi Hamma…” 3

Ya fadi kamar hakan zai zama dalilin da zaisa ya rike hannuwanta

“Na dai fada maka, ranka zai mugun baci idan na sake gani”

Yazid ya fadi cikin yanayin da AbdulKadir din bai taba gani a tare dashi ba. Hakan yasaka shi daga kai a hankali kawai tukunna ya juya yana hada bayanshi da motar wajen. Ranshi bai baci ba yau, bashida wannan wajen, kunshin Waheedah ya dauke mishi wannan yau kam, bashida lokacin fada da Yazid din, duk da ya tsoma mishi baki cikin lamurran da baiga ta inda ya shafe shi ba. Waheedah ce ta dawo da robar ruwa a hannunta, dayan hannun a dumtse, tana sake goge mishi komai da yake cikin kan shi. Robar ruwan ta mika mishi, ya karba, idanuwan shi kafe kan hannuwanta, dan yaji suna danna mishi tunanin Nuriyya inda yake son boye shi dan karya sake dawo mishi.

Dayan hannun Waheedah ta ware mishi yana ganin Panadol guda biyu, kai yake girgiza mata, a duniya babu abinda ya tsana irin magani, ko rashin lafiya yake bayasha. Yassar ya taba tura mishi cikin ayaba yana ce mishi ko itace yaci zaiji karfin jikin shi, kawai yana gutsura ya tauna magani a ciki, kuma ya tsare shi da saiya hadiye, har amai yayi.

“Bazan sha wani panadol ba”

Ya fadi yana kankance mata idanuwa. Kallon shi Waheedah takeyi

“Kanka na ciwo fa Hamma…”

STORY CONTINUES BELOW


Dakuna mata fuska Abdulkadir yayi

“Nifa bazan sha wani magani ba”

Yazid Waheedah ta kalla da yake tsaye yana kallon su, shima Panadol din yake bukata, ji yake kamar yai ihu ko zata ga yana bukata fiye da AbdulKadir din ta bashi

“Hamma kai mishi magana. Kan shi yana ciwo wai bazai sha magani ba”

Kallonta Abdulkadir yayi yana tunanin idan Zainab ce da yanzun ya kwada mata marin da bakinta bazai sake gigin kai karar shi ba, amman Waheedah ce, batayi hakan dan ta raina shi ba, yana ganin damuwa tattare da muryarta. 1

“Ki kyale shi tunda bazai sha ba”

Yazid ya fadi, yana kuma jin tun maganar ta fito daga zuciyar shi dake wani irin ciwo. 1

“Hamma…”

Waheedah ta kira cikin sanyin muryarta da yasaka Yazid din juyawa yana dana sanin fitowar da yayi. Bazai yiwu yanajin azababben kishin Abdulkadir ba, AbdulKadir ne, kanin shi, dan uwan shi ciki daya. Amman zuciyarshi batasan wannan ba, kishi yakeji har idanuwan shi na lumshewa 1

“Me yake faruwa ne?”

Yassar daya karaso wajen ya tambaya

“Bakomai…”

Abdulkadir ya fadi a lokacin da Waheedah tace

“Kanshi ne yake ciwo kuma wai bazai sha magani ba, har na ballo kuma”

Kallonta Abdulkadir yayi ciwon kan da yake ji na karuwa

“Bazan sha ba, ni babu maganin dazan sha. Nace ki ballo mun?”

Yake fadi cike da masifar shi

“Karbi maganin nan kafin inci ubanka, tunda ta ballo sai kasha wallahi. Kaji na rantse” 5

Hannu Abdulkadir ya mikama Waheedah da take murmushi tana sakashi kankance ido cikin son watsa mata harara.

“Mincika…” 3

Yassar ya fadi yana kwashewa da dariya hadi da dorawa da

“Anya ba’aima Hajja musayarka a asibiti ba? Abdulkadir wanne irin idone wannan?” 2

Maganin Abdulkadir ya saka a bakin shi ya bude robar ruwan ya hadiye tukunna ya watsama Waheedah da Yassar din harara, yana saka Yassar sake kwashewa da dariya, mukullin motar shi ya saka a jiki ya bude. Bayan motar Abdulkadir ya bude ya shiga, yana dakuna fuska, tsakanin shi da Allah fushi yake an sakashi shan magani. Yazid ma bayan ya bude ya shiga ta bangaren shi. Hakan yasa Waheedah bude gaban motar zata shiga, hango Nuriyya tayi ta shigo gidan, dan tare da ita sukan tafi tunda Babansu bazai taba jerawa ya tafi idi da ita ba. 1

Irin atamfar jikin Waheedah ce ta saka itama, dan tare Abba yai musu da duka sauran matan gidan. Hijab ce dako gwiwarta bata kai ba, daga inda Waheedah take tana hango kwalliyar da take fuskar Nuriyya, musamman jambakinta. Tana kuma hango yanda kugunta ya fito cikin skirt din da take sanye dashi, dan ita riga da skirt tayi. Kai kawai Waheedah ta girgiza dan in tai mata magana kan cewa hijab din tayi karama fada zasuyi da safen nan. Daman sunyi wani kan Anas. Karasowa Nuriyyar tayi

“Wallahi na dauka kun tafi, inata sauri”

Kai Waheedah ta girgiza mata

“Yanzun dai zamu tafi. Na dauka ba zakije ba”

Hararata Nuriyya tayi, tana ganin ta mata wani irin kyau naban mamaki. Dariya Waheedah tayi ta bude gaban motar ta shiga. Zagayo Nuriyya tayi ta bude bayan motar ta bangaren Abdulkadir da tunda yaji muryarta ya runtsa idanuwan shi yana budesu da wani irin bugawa da zuciyarshi tayi. Har addu’a yayi karya ganta harya tafi, yanzun ma kokarin kin juyawa yake yaji ta bude kofar, baisan lokacin daya juya ba, yana nasarar sauke idanuwan shi cikin nata. Janbakin ta na saka wani abu cikin kanshi yamutsawa. Tsarin kwalliyar da take fuskarta na samun wajen zama cikin kanshi.

Kallon shi Nuriyya tayi, bugun zuciyarta nayin dai-dai da nashi. Yayi mata wani irin kyau cikin farin yadin shi, ga wani irin kamshi da yake, yau kam sosai take jin kasancewarta sallah. Murmushi tayi tana zama cikin motar ta rufe murfin tukunna tace

“Ina kwananku”

Yassar ne ya amsa yana dorawa da

“Nuriyya anyi sallah lafiya?”

Amsa shi tayi, turarenta na cika hancin Abdulkadir din, yana saka shi sauke numfashi a wahalce da yanayin da yakeji. Dan matsawa ya sakeyi jin yanda tayi kusa dashi da yawa, amman hakan bai rage mishi komai ba, saima hannunta daya kalla da take gyara hijabinta dashi, itama kunshine, ja da baqin lalle daya saka shi runtse idanuwan shi yana kirga daya zuwa hamsin, har yaji Yassar ya tayar da motar ya juyata suna ficewa daga gidan. 6

Idanuwan shi ya bude yana gyara zaman hannun shi daya dauke babu shiri jin ya taba na Nuriyya, ta gefen idanuwan shi yaga ta kalle shi da idanuwanta da taja da eyeliner suna kara fitowa. Wani abu Abdulkadir yake ji tun daga dan yatsan kafarshi zuwa tsakiyar kanshi da kusancin da Nuriyya tayi dashi. Ita kam yau ranta kal ta zauna kusa da Abdulkadir, ta kuma lura da a takure yake, zataji dadi idan ya zamana itace tai affecting dinshi haka, yana nufin koyayane ya damu da zamanta. Inda idanuwan shi suke kallo take nema kafin ta kula da hannunta ne, dayan hannu ta zaro tana ci gaba da wasa da yatsunta. 4

Abdulkadir na kula da yanda har cikin tafukan hannuwanta itama kunshine, sai dai nata da ratsin baqi, na Waheedah kuma gabaki daya jan lalle ne. Dakyar ya raba idanuwan shi da hannayenta. Dan yana gab da rike su, ita kanta ji yake kamar yasa dan yatsa ya dangwali jambakin da yake lebenta yaji yana da maiqo ko idanuwan shine kawai suke gane mishi har kyalli yake. Da gaske zuciyar shi raini take neman ja mishi, yana da wannan tabbacin yanzun. 3

‘Kar muyi haka dake, dan Allah, terma four na shiga. Ba yanzun zan settling ba, saina gama NDA na fito, an posting dina wajen da zanyi aiki na nutsu tukunna’ 2

Abdulkadir yake magana da zuciyar shi yana rokonta data saurare shi, bashida wajen soyayya yanzun. Baya komai a rayuwarshi babu tsari. Wannan ne karo na farko da hakan ya kwace mishi akan Nuriyya, shisa yake jin komai ya cunkushe mishi, komai baya mishi dadi dan baisan yanda zai da ita ba. Ya rasa yanda zai da ita. Kokawa yake da kan shi da zuciyarshi akanta, yanzun kasancewarta kusa dashi yasa shi jin komai ya kara kwacewa daga hannun shi. Motar yaji Yassar ya tsayar alamar sun karaso. Kokarin bude kofar Nuriyya take amman ta kasa

“Hamma na kasa, kofar taki budewa”

Nuriyya ta fadi tana kallon shi cike da wani irin rauni da yake ji har bayan zuciyarshi. Baisan lokacin dayakai hannu ya bude mata kofar ba.

“Nagode…”

Ta fadi tana ficewa, idanuwan shi ya runtsa ya bude su, yana dan dafe kanshi da yake kara sarawa

“Yazan yi ne wai?” 1

Yai tambayar yana dukan jikin motar kamar ita tai mishi laifi…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *