ABDULKADIR CHAPTER 6

ABDULKADIR





CHAPTER 6





Tun da ta kwanta tunanin abinda yaci takeyi, ko kadan zuciyarta taki samun nutsuwa, ita kanta Amatullah ce ta dafa musu taliya, da bata zuba musu tare ba, tana da tabbacin babu abinda zata saka a cikinta. Dan ta nemi yunwar data kwaso tun daga makaranta ta rasa, duk da tasan ba lallai ya amsata ba, bai hanata daukar waya ta bude manhajar sada zumuntarta na whatsapp ba. Sunan shine a sama dan shine mutum na karshe da tayi magana dashi. +

‘Me kaci?’

Ta tambaya, tana dorawa da

‘In dafa maka indomie? Ko zaka sha Tea?’

Amatullah dake kusa da ita ta gyara kwanciyar ta tana fadin

“Adda Wahee… Ki rage hasken wayarki mana”

Hannu takai tana rage hasken wayar hadi da fadin

“Yi hakuri…”

Bargo kawai Amatullah taja tana rufe jikinta har kai batare da tace komai ba. Hakan ya ba Waheedah damar mayar da hankalinta gabaki daya kan wayar, dan ba surutun take so ba daman.

‘Shine baka fadamun zaka zo ba ko?’

Ta sake rubutawa tana tura mishi, da tasan zaizo din da ta dafa mishi wani abu, lumshe idanuwanta tayi tanajin da dare bai farayi ba ita kam ko indomie ce data dafa takai mishi, a kasan zuciyarta take addu’ar karya zauna da yunwa. Alamar shigowar saqo da taji yasata ware idanuwanta kan screen din wayar da wani irin bugun zuciyar da bazai misaltu ba

‘Waheedah…’

Lumshe idanuwanta tayi data karanta sunan nata da muryarshi, tana bude idanuwan da murmushi a fuskarta

‘Waheedah…’

Taga ya sake rubutowa, saida ta goge hannunta jikin wandon kayan baccin da take sanye dasu saboda zufar da taji ya mata, tukunna ta iya amsa shi da

‘Hamma’

Rubutu taga yayi, babu shiri ta tashi zaune, da ita kadaice a dakin tsaf zata yi dan ihun murna ko ya yake, yanzun ma gudun tashin Amatullah daga barcine kawai ya hanata yin hakan, amman kanta har wani lilo yake, kamar tana saman gajimare haka take jinta, kafin ta karanta saqon shi daya shigo da wani yare daban da ya saka komai yi mata tsaye cik

‘Kina so na?’ 1

Karantawa takeyi tana kara maimaitawa cike da son fahimtar kalmamomin da take jin kamar ba’a yaren da take fahimta yayi su ba, bai bari ta gama fahimtar su ba ya kara mata da

‘Ba so na yan uwa ba Waheedah… So na aure. Kina so na?’

Wayar ta ajiye jin kamar ta dauki wani irin dumi da yake barazar qona mata hannuwa, sauka tayi daga kan gadon, fankar dake cikin dakin takejin ta mata kadan, zafi takeji bana zazzabi ba, zafi take ji daya girmi ta dora shi akan tsantar girgiza da mamaki. Littafin Amatullah da tayi assignment tagani a ajiye, da sauri ta dauka tana fifita fuskarta da duk wani waje a jikinta da zata iya. Zuciyarta kanta ta nutsu wani waje a cikin kirjinta dan taji abinda basu taba mafarkin ji ba su dukansu. Sakon da taji ya sake shigowa ya sata dauki wayar saidai ta kasa zama sam

‘Ki amsani, zan kirga daya zuwa goma. Karki amsa sai kina da tabbaci, idan bakida shi karki amsa, nida ke zamuyi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake hadamu ba har abada’

Gefen gadon ta zauna tana mayar da numfashi a hankali, ta runtsa idanuwanta ta budesu kan saqonnin nashi yafi sau ashirin, so take ta tabbatar ba mafarki takeyi ba. Ba kuma tunaninta yake hasaso mata abinda zuciyarta take burin ji ba, amman duk sanda zata bude sakon AbdulKadir din yake sake mata sallama.

‘Daya…’
‘Biyu…’
‘Uku…’ 1

Ta karanta kafin zuciyarta ta fara mata ihu tana sanar da ita yanda take musu wasa da dama kwara daya tal da suka samu a wajen AbdulKadir din. Tasan shi, kamar yanda ya fada ne, idan harya gama kirga goman da yace maganar ba zata sake hadasu ba har abada. Sai dai yanzun ma batasan yanda akai maganar ta hadasun ba, ko a mafarki bata taba tunanin hakan zata faru da ita ba

STORY CONTINUES BELOW


‘Hamma… Hamma kace wani abu, ka gayamun ba mafarki nake ba, kabani wani tabbacin banda wannan…’

Ta rubuta, sai ta tsinci kanta da gogewa

‘Hudu…’
‘Biyar…’
‘Shidda…’

Kai take girgiza mishi tana soma rubuta

“Ina sonka, bansan ko tun yaushe nake sonka ba, ina sonka fiye da yanda zan taba fada maka Hamma AbdulKadir, tare dakai zuciyata ta fara bude idanuwa, kai zuciyata ta fara dokawa…’ 4

Batasan meyasa ta sake gogewa ba, kalamai take nema, amman ta rasa, har lokacin jin komai take kamar a mafarki, kamar tana tura mishi amsar zata farka

‘Bakwai’

Kai ta sake girgiza wannan karin a fili tace

“Ka tsaya Hamma, dan Allah ka tsaya…”

Idanuwanta ta lumshe tana sake budesu kan wayar tata

‘Takwas…”

Wani irin yanayi ne ya bayyana kan fuskarta, muryarta a karye tace

“Hamma mana, dan Allah ka tsaya…”

Nutsuwarta take son tattarowa ko da abinda yake faruwa zai kasance mafarki, bataso ta manta komai, sakkonin nashi ta sake karantawa tana lumshe idanuwanta ta adana su wajen da tasan ba zasu taba bace mata ba koda ta farka tukunna ta bude idanuwan nata.

‘Tara…’

Ta karanta

“Bansan yazan ci gaba da rayuwa bayan abin nan ba Hamma, idan mafarkine ka tabani ta fannin da banajin zan koma dai-dai wannan karin… Ka fifitamun wutar burina ka dawomun da komai baya…”

Ta karasa maganar da wani irin sanyin murya, sosai take jin in har mafarki take a gefen soyayyarshi da take wahalar da ita, burin samun shi zai zauna, zata dinga kallon shi tana jiran ya sama mata wajen zama a rayuwarshi ko da bata samu a zuciyarshi ba.

‘Ina son ka, ina son ka da aure Hamma AbdulKadir’

Ta tura mishi tana jiran taji ta farka daga baccin da take, alama tagani na cewar ya karanta sakon, kafin taga ya sauka daga kan WhatsApp din, wani irin numfashi da batasan tana rike dashi ba ta saki, itama kashe data din tayi ta ajiye wayar hadi da mikewa. Bandaki ta shiga ta tara ruwa tana wanke fuskarta, har lokacin numfashi take mayarwa kamar wadda tayi gudu. Zuwa yanzun bata da kalaman da zata fassara abinda takeji. Takai mintina goma tsaye a bandakin ta dafe sink, amman idan ka tambayeta ba zatace ga asalin abinda take ji ko take tunani ba.

Alwala ta daura ta fito daga bandakin, doguwar hijab din da take sallah da ita ta dauko ta saka jikinta. Dardumar da tayi sallar isha’i tana shimfide bata nade ba, kai tahau ta fara jero salloli tana rokon tabbatar alkhairi a koma menene yake shirin faruwa tsakaninta da AbdulKadir din, dan tun daga yanda take son shi tasan abin yafi karfinta, yanzun ma ba zata iya ba, ba kuma zata bata darenta tana tunanin abinda baya karkashin ikonta ba, gara ta bude ma Allah zuciyarta, sosai kuma ta samu nutsuwar da take jin ta kwace mata, akan dardumar bacci mai nutsuwa ya dauketa.

*

Tana da darasin safe, gashi ta tashi da wani irin sanyin jiki, har iskar da take shaqa daban take jinta yau din, bata sake shiga wani yanayi ba saida taci karo da sakon Abba 4

‘Aslm. Waheedah ki sameni kafin ki wuce makaranta’

Haka kawai taji zuciyarta na mata rawa, duk da ba yau bane ranar farko da Abban yakan mata irin sakon ko idan zasuyi magana ko kuma zai bata wani abin. Yau dinne dai takejin kiran kamar zai zamana daban. Sanda tagama shiryawa saida ta biya dakin Mami tai mata sallama tukunna ta fita zuwa bangaren Abba. A bakin kofa ta tsaya ta kwankwasa, saida taji yai magana tukunna ta tura dakin da sallama tana shiga. Waje ta samu kan kafet din ta zauna dan shima anan yake zaune ya miqe kafafuwan shi.

STORY CONTINUES BELOW


“Ina kwana Abba…”

Ta gaishe dashi cikin sanyin muryarta

“Waheedah…”

Ya kira yana dorawa da

“Kin tashi lafiya? Ya makarantar?”

Hijab dinta da taji ta danne ta dan daga tana gyara zamanta sosai

“Alhamdulillah…”

Wani numfashi Abba yaja yana kallon yanda take komai nata cikin sanyi. Da tunaninta ya kwana a ranshi, har zuwa safiyar ranar yana jinjina ma kaddarar data hadata da AbdulKadir, dan ko a tunaninshi ya kasa dai-daita dacewarsu. Idan zabi za’a bashi na ya aurar da ita cikin yaranshi, yanajin Yazid kadai zai iya aura ma ita hankalin shi a kwance, yana da tabbaci akan Yazid zai riketa da amana, dan bazaice ga rana daya da yaji anyi wata hayaniya dashi ba tun yarintar shi. Muryarshi dauke da nauyin da yake jin dukkan jikin shi yai mishi ya soma magana

“AbdulKadir ya sameni jiya. Nasan halin shi, nasan bazai sameni batare da amincewarki ba, amman ina so in tabbatar daga bakinki Waheedah, amana ceke a wajena kamar yanda suma suke amana, banma kowa maganar ba tukunna, ki fadamun idan kin amince da auren shi…”

Kanta a kasa yake tunda ya fara magana, bata taba tsintar kanta cikin kunya irin wadda takeji ba, wasu zasuce kamar kasa ta tsage su shige, a irin kunyar da take ciki ba tajin zata iya jiran kasar ta tsage, ita take so ta narke ta sulale tabi kasar ta shige cikinta. Ga zuciyarta da take wata irin dokawa kamar zata fito daga kirjinta

“Kimun magana Waheedah, karkiji nauyina, idan har baki amince dashi ba yazo ya sameni ki fadamun, wallahi indai ina numfashi babu wanda zai miki dole akan komai na rayuwa…”

Shirun ta sakeyi tana kara sadda kanta kasa, numfashi Abba ya sauke

“Aure ba abu bane da akanyi dan kowa nayi, ba kuma abu bane da ake fatan idan anyi a fito, aure abune da ake fatan idan har anyi ya zamana har muddin rai, shisa ba’a son gaggawa a cikin duk wani abu daya shafe shi, ba’a kuma son tursasawa, da fahimtar juna ma dole sai an hada da hakuri a zamantakewar da za’a tashi a kwana karkashin inuwa daya. Kimun magana Waheedah, bazan samu nutsuwa akan maganar nan ba…” 1

Kanta da takejin yaima siririn wuyanta nauyi naban mamaki yau ta samu ta motsa tana dagashi a hankali, da ace nutsuwar Abba bata kanta da bazai ga daga kan ba

“Kin amince da auren shi?”

Abba ya tambaya yana son tabbatar wa, kan ta sake daga mishi a hankali. Wani numfashin ya sauke, yana jinjina ma karfin kaddara da take zuwa karkashin ikon Allah. Kai ya jinjina

“To Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi…”

Kafafuwanta Waheedah ta tattara, har lokacin ta kasa dago fuskarta, jikinta gabaki daya ya dauki dumi da kunyar Abba da takeji, mikewa tayi dakyar tana juyawa cikin sauri da nufin barin dakin

“Kizo ki karbi kudin makaranta…”

Abba ya fadi yana saka hannu a aljihun shi, amman kamar maganarshi ta kara tunzurata, da gudu ta fice daga dakin tana ja mishi kofar. Murmushi Abba yake

“Oh Allah mai iko…”

Ya fadi, ya jima wani abu bai bashi mamaki ba irin na daren jiya zuwa safiyar yau. Da gaske AbdulKadir da Waheedah sukeyi, yanda yake jinshi zai kwana biyu yana jinjina al’amarin. Wayarshi ya dauka ya kira Mami dan ya sanar da ita kafin ya samu dangin Baban Waheedah din da maganar, duk da sun jima da nuna mishi yana da damar yanke hukunci akan rayuwar Waheedah din bazai hanashi nuna musu godiya da halaccin da sukai mishi ba, zai samesu da maganar duk da yasan ba zasuki kowa yake son hadata dashi ba, balle kuma idan sunji jinin shi ne.

STORY CONTINUES BELOW


*

“Ina zaki je?” 1

Muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta, tana sakata gyara zaman jakar dake kafadarta tukunna ta juya tana sauke idanuwanta akan shi. Jikin shi sanye da riga fara kal, sai wandon sojoji gajere da silipas din wanka a Kafafuwan shi.

“Hamma…”

Ta kira da wani yanayi a muryarta, wani irin son shi taji ya taso mata har yana ma numfashinta barazana. Tasan ya kamata ta sauke idanuwanta daga kanshi, ta daina kallon shi, amman zuciyarta ce da iko kan idanuwanta wannan karin, ta kuma nuna mata bata gaji da kallon shi ba. Shima idanuwan shi ya kankance akanta da dakyar take ganin kwayar cikin su, fuskarshi a kumbure take har idanuwan da alamar rashin wadataccen bacci.

“Ina zaki je?”

Ya maimaita tambayar yana kallonta, tsaye yake ya hango hijabinta da yake share harabar gidan, blue ne mai hasken da yai mishi kyau sosai. Badan baya ganin masu saka hijab ba, amman kowa zai gani da hijab itace mace ta farko da take zuwa mishi a rai, kuma bai taba ganin wanda hijab yake ma kyau kamarta ba, zai rantse yanayin tafiyarta a cikin hijabanta daban yake. Kamar hijab din na bata wani asirtaccen confidence da idanuwa basa iya gani, sai yaga kamar ba Waheedah mai sanyin halin nan ba, kwarjininta daban yake mishi in tana cikin hijabanta. 1

Idanuwanta take raba mishi, wannan karin cike da wani yanayi da ya saka jikinshi daukar dumi, kalar hijabin ta kara mata farin da yasa shi furta

“Wanne irin mai kike shafawa?”

Da mamaki bayyane a fuskarta tace

“Vaseline…”

Kankance mata idanuwa ya karayi

“Yana kara haske?”

Dariya tayi tana girgiza mishi kai

“Hamma Vaseline fa”

Kafadunshi yadan daga mata, bazai sani ba, tunda haske take kara mishi a duk ganin dazai mata.

“Ina zaki je?”

Ya sake tambaya a karo na uku. Da murmushi a fuskarta har lokacin tace

“Makaranta…”

Ta dauka wani abu zai canza tsakaninsu da maganar auren, amman bataji komai ba ita kam, banda soyayyar shi da duk lokacin da zata dauka babu wani waje a jikinta daya rage wanda baya dokawa da soyayyarshi, sai ta sake jinshi a wani wajen da batasan yana motsi ba. Babu abinda ya canza, shidinne dai, Hammanta, Sadaukinta, ko babu maganar auren batajin akwai inda zatakai soyayyar shi.

“Da sassafen nan? Waye zai kaiki?”

AbdulKadir ya fadi yana katse mata tunanin da takeyi

“Ina da class, nama makara, napep zan hau…”

Kai ya fara girgiza mata yana sata dorawa da

“Ina zuwa Hamma, ba kullum ake kaini ba”

Kan AbdulKadir yake girgizawa har lokacin, yaushe Waheedah din tai girman da zataje makaranta, ta tafi ita kadai bai zauna mishi ba sam

“Na iya zuwa Allah”

Ta fadi ganin shakkun dake cikin idanuwan shi

“Ki jirani ina zuwa…”

Cewar AbdulKadir din yana juyawa da sauri. Binshi tayi da kallo harya shige bangarensu, idanuwanta akan kofar tana jiran fitowarshi da dukkan zuciyarta. Baifi mintina biyar ba taga ya fito yana takowa zuwa inda take, tari tadanyi da yanda zuciyarta ta matse cikin kirjinta kamar akanta yake tafiyar.

“Muje…”

Yai maganar yana yin gaba, tabishi a baya har wajen motar Yassar, mukullin yasa yana bude kofar, ita kuma ta zagaya, saida ya zaro wayarshi daga aljihun bayan wandon tukunna ya shiga ya zauna, hannu ya mika ya bude ma Waheedah dayar kofar ta shigo itama. Wayarshi ya dora kan cinyarta kamar babu inda zai iya ajiyewa a cikin motar gabaki daya. Daukar wayar tayi ta rike a hannunta, tanajin shi ya tayar da motar yana jansu suka fice daga gidan.

STORY CONTINUES BELOW


“BUK, old site…”

Tace mishi

“Nace miki bansani ba?”

Kai ta girgiza mishi

“Me yasa kike fadamun to?”

Ya sake maganar yana dan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuqin da yakeyi. Har malamansu gabaki daya yasani, bazai ce ga course din da take dashi ba a ranar, amman idan ya duba wayarshi zai iya fada mata, a cikin labaranta gabaki daya yasan hakan, me yasa take tunanin bai rike ba? Dan bai amsa ba baya nufin bai karanta ba, baya nufin hankalin shi baya kai. Shiru tayi bata amsa shi ba, tunda tasan halin shi.

“Bakici abinci ba…bakici komai ba kika fito”

Yai maganar kamar tunanin ya fado mishi. Girkin Mama ne har ranar, da yunwa ya tashi ya kuma je bangarenta bata gama ba, lokacin daya shiga ma ake fere doya. Ko da yayi maganar da alamar tambaya ne, Waheedah batajin zata amsa shi, bazai sauke mata fadanshi da sassafe ba.

“Kinsan yanda abincin safe yake da muhimmanci?”

Murmushi taji ya kwace mata, ba abincin safe bane kadai yake da muhimmanci a wajen AbdulKadir, duka abinci nada muhimmanci dan baya wasa da cikinshi ko kadan. Wani shago ya hango hakan yasa shi tsayawa, batare dayace mata komai ba ya fice daga motar. Wayarshi dake hannunta ta latsa dan taga ko karfe nawa, zuciyarta nayo tsalle zuwa makoshinta ganin hoton dake kan wayar. Hannuwanta ne babu tantama, da kunshinta da bata manta ranar daya dauka ba.

“Hamma…”

Ta fadi da wani irin yanayi a muryarta tana shafa screen din wayar. Dai-dai lokacin da AbdulKadir ya bude motar ya shigo yana dora mata leda akan jikinta da kashedin

“Karki sake fitowa bakici wani abu ba”

Bata abinci takeyi ba, kallon shi take tanajin wani irin yanayi da bazai fassaru ba, har suka karasa makarantar babu wanda ya sake cewa wani abu. Har department dinsu ya kaita yana zaune cikin motar saida yaga ta shiga aji tukunna ya sauke numfashin da baisan yana rike dashi ba, kafin yai wata irin hamma, ba wani bacci ya samu ba jiya, yana kwance yana tunanin yanda akai rayuwa ta kawo shi inda yake yanzun. Sai dai zuwa safiyar yau komai ya mishi dai-dai. Tana son shi, zai aureta, ya rigada ya gama duk wani tunani da zaiyi akan hakan. Yanzun yaga garin da aka kaishi ne abinda yake ranshi, sai yai magana da Hajja dan yaji ko nawa ne zai tara. Juya motar yayi yana nufar gida.

*

Sallar azahar ya dawo, yana kwance a daki yaji an turo kofar kamar za’a karyata

“AbdulKadir me kayi?”

Yaji muryar Yassar din ranshi da alamun a bace yake. Sai dai a iya tunanin AbdulKadir din baisan ya mishi wani abu da zai bata mishi rai ba. A nutse ya tashi daga kwanciyar shi ya zauna yana dakuna ma Yassar din fuskarshi cike da rashin fahimta.

“Kajini ai, me kayi?”

Yassar ya sake fadi yanajin yanda yake gab da kwashe AbdulKadir din da mari. Aiki ya fita, yau da wuri yake tashi, yana dawowa yakejin ana maganar auren AbdulKadir din da Waheedah cikin wata shidda tare za’a hada da nasu Yazid. Maganar yake ji kamar wasa, saida ya tambayi Mama tace mishi da gaske ne, Abba da kanshi ya fada musu. Yasan halin AbdulKadir zai iya cewa fiye da kowa a gidan, yasan yanda yake son kanshi fiye da tunani, amman bai dauka yakai haka ba. Bai dauka yakai yai amfani da soyayyar da Waheedah din take mishi ta wannan fannin ba.

“Kaimun magana yanda zan gane Hamma…”

AbdulKadir ya fadi a kasalance, bacci yakeji, kuma da niyyar yin baccin ya kwanta

“Waheedah… Me kayi AbdulKadir…”

Dan dafe kai AbdulKadir yayi yana fadin

“Oh… Aurenta zanyi…”

STORY CONTINUES BELOW


Numfashi Yassar yaja ta baki yana fitar dashi ta hancin shi

“Baka son ta AbdulKadir, me kayi haka?”

Kafadu AbdulKadir din yadan daga mishi

“Tana sona…” 1

Wata dariya Yassar yayi batare da yasani bama

“Wai ma meya faru ka sameni kanata hure-huren hanci kamar dragon… Ba jiya kake mun maganar yanda take sona ba?”

Kai Yassar ya dafe yana sauke numfashi, sosai yakejin yanda ya kusa kwada ma AbdulKadir mari

“Da nace tana sonka bance kaje kace zaka aureta baka shirya ba”

Gyara zaman shi AbdulKadir din yayi

“Eh haka Abba yace ba’a aure babu shiri, shisa ba za’ayi nan da sati biyu ba, tare da nasu Hamma Mubarak za’a hada, wai za’ayi su lefe… Zanje inma Hajja maganar ma… Zan tara kudin in shaa Allah, albashina da dan yawa… Zai isa idan na tara…”

Ciwon kai Yassar yaji ya saukar mishi, abinda yake nufi daban, abinda AbdulKadir yake fahimta daban, ba shiri na hidimar aure yake mishi magana ba, shiri na zaman aure da yake bukatar fiye da soyayya. 1

“AbdulKadir… Baka son ta”

Dakuna fuska AbdulKadir yayi

“Tana sona Hamma.. Me yasa bazai ishe mu ba?”

Ya karasa maganar yanajin ranshi ya soma baci, baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga maimaita mishi magana daya kamar itace abu mai muhimmanci a maganar auren, ya tambayi Waheedah tace tana son shi da aure, shima kuma a shirye yake yai zaman aure da ita, bai kuma san meye yafi wannan muhimmanci ba.

“Bacci nake ji… Dan Allah kabarni nikam. Na rigada nagama magana da Abba, auren nan zai faru… Maganganun duk da muke din nan basu da wani muhimmanci tunda ba zasu canza komai ba”

AbdulKadir yai maganar yana komawa ya kwanta hadi dajan mayafi ya rufe jikin shi. Kai Yassar yake girgiza mishi yana dana sanin furta mishi cewar Waheedah nasan shi, har ga Allah bai taba tunanin ba soyayya suke ba, da yasani da bazai taba tayar ma fa AbdulKadir da maganar ba, amman lokaci ya kure. Kamar yanda AbdulKadir din ya fadane, maganganun shi ba zasu canza komai ba.

“Dan Allah karka cutar da ita, karkai amfani da soyayyar da take maka ka cutar da ita AbdulKadir, marainiyace, karka cutar da ita…” 2

Yassar yai maganar da wani irin yanayi a muryarshi, a kasan zuciyarshi yana addu’ar kar AbdulKadir din ya taba dana sanin auren Waheedah din, dan yanajin ya yanke hukuncin aurenta cikin gaggawa, ko da ya shirya zaman aure da ita, yayi gaggawa yagane hakan a jiya kawai. A wani bangaren yana fatan akwai wani bangare a kirjin AbdulKadir din da yake dokama Waheedah batare daya sani ba.

“Ka jamun kofar inka fita”

AbdulKadir ya amsa kamar baiji maganganun da Yassar din yayi ba.

“Allah ya tabbatar da alkhairi…”

Cewar Yassar yana ficewa yajama AbdulKadir din kofa, idanuwan shi ya lumshe, dan bashi Yassar zai saka tunani ba, bacci mai karfi ya dauke shi.

*

Ba zatace ga yanda satika biyu suka wuce mata ba, tasan dai a cikinsu abubuwa da dama sun faru, harda maganar da Mami tai mata kan auren AbdulKadir din itama kamar Abba tana son karin tabbaci ne. Data samu din kuma addu’a tai musu

“Allah yasa alkhairin juna ne ku, Allah yasa muku albarka a tafiyar dake gabanku Waheedah, Allah ya yafe ma mahaifinka ta kyautata makwancin shi”

Ko ita kadai ta zauna addu’ar Mami kan sanyaya wajejen da batasan suna mata zafi ba. Tun yan gidan na mamakin maganar auren suma har sun daina, dan Zahra ma saida tace mata

STORY CONTINUES BELOW


“Lallai ma, ki rasa wa zaki aura a duniyar nan sai Hamma AbdulKadir? Ya gama zaneki ya lallabo kuma zaki aure shi…Tafdin…”

Dariya kawai takanyi, Mubarak ma da yakai ta makaranta a cikin satikan saida yai zancen

“Zuciyarki bata kyauta miki ba Waheedah… Ta rasa wa zata janyo muku sai masifaffen nan. A kafa aka dauramun AbdulKadir saina tsinke nayi takaina…” 1

Shima dariyar tai mishi a kunyace. Ba zasu taba fahimtar yanda take son AbdulKadir din ba, ita kanta ba zatacr ga yawan soyayyar da take mishi ba, halayenshi kaf babu wanda ya taba damunta balle ya daga mata hankali, fadanshi kan tsaya mata a rai duk idan yai matashi wasu lokuttan, tana kuma tsoron fadan nashi, sai dai bai taba zama dalilin da zai hanata tunkararshi da kowacce irin magana ba, kuma bai taba sa taji soyayyarshi ta yi ko alamar dishewa ba. Tana son shi da duk wani abu da yake tattare dashi.

Kwata-kwata tun satin farko take neman wayar Nuriyya bata samu ba, sau biyu ta biya ta makarantarsu bata samunta, sai a sati na biyune ta sameta a waya ashe batajin dadine, har gida taje ta dubata take kuma fada mata sa ranarta da AbdulKadir, tayi mamakin da

‘Allah yasa alkhairi’

Kawai Nuriyya ta furta, saidai Waheedah tai mata uzurin cewar dan batada lafiya ne, tadai gyara mata gidan da yai kamar yayi wata baiga tsintsiya ba, ga tarin wanke wanke, kusan duk wani abu da yake kitchen din bashida kyau. Ko ina ta gyara mata tsaf, har girki tai mata tukunna sukai sallama tabar gidan. A satin kuma saida ta koma dubata har sau biyu, zancen bikinta dai bai sake hadasu ba, zatai karya wannan karin in tace ranta bai mata wani iri ba. Ta dai sake mata uzuri da rashin jin dadin auren Anas da takeyi har lokacin, hankalinta baiyi kwanciyar da zatai rawar kafa kan nata auren ba. 2

Ranar lahadi ce, ba makaranta ke akwai ba, takanje islamiyya a ranakun hutun karshen mako, amman ranar AbdulKadir zai wuce, an tura shi Minna. Yace mata ba dawowa zaiba sai bikinsu, bazai tafi bata ganshi ba, text dinshi tagani a wayarta

‘Ina wajen motar Hamma Yassar’

Mikewa tayi zuciyarta na dokawa kamar zata fito waje. Hijab dinta ta dauka ta saka, tukunna ta dauki ledar dake ajiye kan gadon, addu’a take kartaci karo da Mami a falon dan batasan kalar kunyar da zataji ba. Ita da AbdulKadir din ba wani lokaci suke samu su kadai ba tun bayan maganar, yanzun takan samu ya amsata dai-dai a WhatsApp, wani lokacin kuma yana kira, duk da hirar ita zatai mishi, ko in tana mishi a WhatsApp zai kirata yace bacci yake ji ta karasa mishi labarin zai gani da safe. 4

Wasu lokuttan kuma in tana makaranta yace karta taho ta jira shi zaije ya daukota. Banda wannan babu abinda zatace ya canja, in sun hadu zata gaishe shi kamar da, zai satai mishi abu kamar yanda yakan satai mishi a baya. Allah ya amshi addu’arta bata samu Mami a falon ba, kamar marar gaskiya haka ta fice da saurinta. Wajen harabar motocin ta same shi ya jingina bayanshi da motar, jikinshi sanye da rigar saqi ta sanyi marar nauyi, dogon hannune amman yaja hannuwan rigar sosai, sun tattare daga wajen damtsen shi.

Kallon shi tayi tana daukar hotunan shi cikin kanta dan ya mata kyau sosai da sosai.

“Tafiya zanyi Waheedah…”

Ya fadi lokacin da ta karasa ta tsaya a gefen shi, kai ta jinjina mishi, tana sane da tafiyar kamar tare zasuyita, dan tanajin yanda zai tafi da fiye da zuciyarta, harda kadan daga cikin ruhinta. Ledar dake hannunta ta mika mishi ya karba yana rikewa

“Ka kula da kanka Hamma… Banda kin shan magani dan Allah…in bakajin dadi kaje a duba ka kaji?” 2

Ta karasa maganar tana kallon shi, tasan yana kula da kanshi takowanne fanni banda lafiyar shi, saboda bayason magani, bata taba ganin mutumin da bayason magani irin shi ba.

“Kibarni ba yaro bane ni…”

Yai maganar yana tsareta da kananun idanuwan shi, ita kadai take tsira shi da maganganu haka, take mishi kamar yaro batare data nuna alamar ta raina shi ba. Yanda take nuna tsoron shi yakan ga hakan har cikin idanuwan ta, amman baya hanata fada mishi duk abinda tayi niyya. Ledar dake hannun shi ya bude dan bazai iya jira saiya karasa daki ba, inya karasa dinma jakarshi zai dauka Yassar yakai shi tasha.

“Ba anan zaka bude ba Hamma…”

Waheedah tai maganar da murmushi a fuskarta

“Saboda me?”

Ya tambaya yana saka hannun shi cikin ledar

“Saboda haka kowa yakeyi”

Agogo yaji cikin ledar ya dauko yana fitowa dashi hadi da fadin

“Ni ba kowa bane ba”

Ya karasa maganar yana mika mata agogon ta karba, hannun shi ya miqa mata, akwai wani agogon a daure, na sojojine ma, kwance mishi agogon tayi ta daura mishi wanda ta siya din, dubawa yayi yana jinjina kai, nashi agogon ta mika mishi tana jin zuciyarta ta matse waje daya.

“Ki ajiyemun, idan na dawo zan karba…”

Ya fadi, yanayinta yasa shi son yabar mata wani abu, agogon ne kawai abinda yake dashi a yanzun. Koda bata bashi wani ba yai niyyar cirewa ya daura mata, ganin tayi tsaye tana kallon agogon kamar ya bata wani bangare na zuciyarshi yasa shi karbar agogon daga hannunta, dago idanuwanta tayi tana ware su kan fuskarta. Bai manta kashedin Yazid na cewar ba muharramar shi bace, ya daina tabata, kawai yayi watsi da kashedin ne ya kamo hannunta yana zagaya agogon a jiki hadi da daurawa. Dariya yayi har hakoran shi suka fito, ta jima bataga hakoran shi haka ba inba magana yake ba.

“Wahee…”

Ya fadi yana sa tsikar jikinta miqewa

“Wanne irin hannune wannan?” 1

Yai maganar da dariya a muryarshi ganin agogon na yawo, kwancewa yayi yana saka shi cikin tafin hannunta ta dumtse

“Ki kula da kanki Waheedah…”

Kai kawai ta iya jinjima mishi, kafafuwanta kamar an kwance abubuwan da suke daure dasu saboda sanyin da taji sun mata. Numfashi AbdulKadir ya sauke har lokacin yana rike da hannunta da yakejin shi dan karami a cikin nashi, tsintar kanshi yai da fadin

“Kice ma duk wanda zai kulaki a makaranta mijin da zaki aura soja ne. Ki fada musu Second Lieutenant A. Bugaje ne, yana da kishi fiye da tunani” 2

Murmushi mai sauti taji ya kwace mata, duk da idanuwanta cike suke taf da hawaye, kewar shi ta fara danneta tun yana tsaye a gabanta. Batasan hawayenta sun zubo ba saida taji yatsun dayan hannunshi ya share kuncinta.

“Ba’a san matar soja da rauni ba”

Ya fadi yana mata murmushi, zuciyarshi yake jin tayi wani shiru, hawayenta sun tsaya mishi a makoshi, da gaske Yassar yake, tana son shi, a fuskarta yake karantar hakan, yana mamakin yanda ya dauke shi tsayin lokaci baiga hakan ba. Har a kasusuwan shi yake jin aurenta ne zabi mafi girma da ya tabayi a rayuwar shi. 2

“Matar Sadauki”

Tai maganar tana saka idanuwanta cikin nashi. Kai ya jinjina mata yana maimaita

“Matar Sadauki…”

Sunan na zauna mishi a duka jikin shi, wannan karin ita tai dariya. Zatai kewar shi tasani, amman ya bata abinda zai riketa harya dawo. 1

“Allah ya tsare maka hanya ya sauke ka lafiya”

Amsawa yayi da

“Amin…”

Yana dumtsa hannunta dake cikin nashi kafin ya saki, muryarshi can kasan makoshi yace

“Zan kiraki…”

Kai ta daga mishi, tukunna ya juya, agogon shi dake hannunta ta dumtsa tana sauke numfashi mai nauyin gaske, idanuwanta akan shi harya bace ma ganinta…!!!Tunda aka fara kamun hankalinta nakan wayarta da Amatullah ta baro mata a gida. Mutuwa tayi, hakan ya sakata bata dan tasa mata a caji. Ba tunanin gidan da yake shakare da mutane ko za’a sace mata waya takeyi ba. Amatullah ta tabbatar mata da ta rufe dakin da mukulli ta kuma taho dashi. A’a, duk inda karfe bakwai tayi tasan AbdulKadir zai kirata, a watannin shiddan nan da suka wuce mata kamar kiftawar idanuwa, karfe bakwai ya zama lokacin wayarsu. Duk da tun jiya take baza idanuwa taga ta inda zai bullo, amman shiru, kuma ko da ya kirata jiya saita tsinci kanta da jin nauyin tambayarshi yaushe zaizo din. +

Gashi kamun babu maza, matane kawai, batai tunanin zai kaisu har lokacin ba, satin bikin ma jinshi takeyi kamar a mafarki. Itace za’ai bikinta wai. Tunda satin bikin ya kama take baza ido taga ta inda Nuriyya zata bullo, amman sai text tayi mata cewar an kwantar da ita asibiti saboda haka ba zata samu damar zuwa ba. Ta kikkirata yafi a kirga tana mata ya jiki, sosai taso zuwa har asibitin dan ta dubata amman bata samu dama ba. Ta dauka taji jiki lokacin bikin Nuriyya din, sai yanzun ne tasan yanda ake jin jiki da nata bikin yazo, abinci ma duk yinin ranar bata samu ta saka shi a cikinta ba. Har wani haske take gani yana gilmawa ta cikin idanuwanta duk idan ta mike saboda yunwar da take ji. 1

Jiya da sukai waya da AbdulKadir yayi mata fadanshi kaman zai ari baki da tace mishi bataci komai ba, kanta na mata ciwo. Yanzun ma tana jin alamar ciwon kai na barazar yi mata sallama, cikinta da taji yayi karar yunwa ta dafe tana gyara zamanta kan kujerar da take zaune.

“Ni fa nagaji wallahi, bakiji yunwar da nakeji ba”

Cewar Zahra da take zaune kusa da ita, tayi matuqar kyau cikin alkyabbar da ta dora kan kayan jikinta da iri dayace data Waheedah din

“Nifa duk yau babu abinda yaje cikina banda ruwan shayi da safe”

Juyowa Zahra tayi tana kallon Waheedah da tambayar

“Kina aikin me?”

Langabar dakai tayi, Zahra din naganin tayi mata wani irin kyau da kwalliyar da akai mata marar hayaniya. Jambakin ya zauna kan labbanta kaman dasu aka halicce shi

“Babu wanda yabani abinci fa… Anty Hafsah ce ta tambaya ko naci, to tace bari ta kawomun kuma ta shiga wata hidimar inajin ta manta…”

Tabe baki Zahra

“Zubawa nayi na shige daki na zauna naci abuna…ulcer ba zata kamani ranar bikina ba” 1

Dariya Waheedah tayi sosai tana sa Zahra din yin dariya itama. Haka sukaci gaba da hira da take tsayawa iya kunnuwansu.

*

Tsaye yake bakin wajen, jikin shi sanye da shadda ruwan toka mai cizawa sai hula da tayi matukar dacewa da shaddar jikin nashi. Ya kankance ma Anty Ramatu kanwar Hajja idanuwan shi da suke cike da rikici 1

“Bansan sau nawa zan gaya maka babu maza ba AbdulKadir, duk da yawancin mutanen da suke wajen yan uwane…me ma kazoyi wajen kamu?”

Ta sake mishi tambayar, dan itama wata makociyarsu da tazo matane zata tafi, ta rakota bakin kofar wajen ta samu AbdulKadir din ya cakumo rigar daya daga cikin masu gadin wajen yana shirin hadashi da bango saboda yace mishi maza basa shiga.

“Me zanyi a wajen kamu. Waheedah zaki kiramun ko ki matsa in shiga in kirata da kaina” 4

Kai Anty Ramatu ta girgiza mishi

“Muma yanzun zamu taho… Addu’a kawai za’ayi… Ka wuce gida gamu nan”

Kallon da AbdulKadir yake mata ya fara tabbatar mata da cewar babu inda zashi kafin ya bude baki yana tabbatar mata ta hanyar fadin

“Ki kiramun Waheedah…”

Yanajin hakurin shi na gab da karewa, bayason fadin wata magana da zatace ya mata rashin kunya. Tun karfe wajen biyar ya iso garin Kano, kiran wayarta yayi yajita a kashe. Duk da yana hanya ma bai hanashi bude WhatsApp dinshi ko zaiga sakonta ba, amman shiru, yinin ranar ko dan text bai samu ba. Kiris ya kira Yassar ya rokeshi yake ya duba mishi ko tana lafiya, ko ciwon kan ne ya hanata bude wayar. Da damuwarta ya sauka garin Kano. Ake fada mishi suna wajen kamu. Ya jira har lokacin daya saba kiranta dan yana da tabbacin ko da bai kirata ba ita zata kirashi, amman wayarta a kashe. 2

STORY CONTINUES BELOW


Bayason ya zauna yana wani tunani, dan ba abokin yinshi bane, shisa yasa daya daga cikin sababbin kayanshi da Yassar ya nuna mishi, yaso su fita amman yaki, baibi takanshi ba suka wuce koma ina ne zasu din, dan shi bai tambaya ba, bayason hayaniyar. Waheedah yake jin gani yaji dalilin da yasaka rufe waya bayan tasan zai kirata. Amman Anty Ramatu nason bata mishi rai. Bada ita yakejin yin fada ba, da Waheedah ne. Yana kallonta ta jinjina mishi kai

“To kayi hakuri dan Allah ka jira, ayi addu’ar inajin ma an fara saimu fito gabaki daya…”

Ganin har lokacin idanuwan shi na kafe a kanta yasa ta kara fadin

“Kaji… Yanzun zamu fito” 3

Kai ya jinjina ma Anty Ramatun a hankali yana juyawa ya koma jikin wata mota ya tsaya saitin kofar wajen. Dan shi a motar Yassar yazo tunda bashida tashi har lokacin. Kuma baiyi parking dinta a kurkusa ba, kasancewar akwai motoci da yawa a wajen. Baifi mintina goma a wajen ba ya fara ganin mutane na firfitowa, hakan yasaka shi raba bayanshi da jikin motar da yake jingine yana tsayawa tare da duba Waheedah da idanuwanshi a cikin taron mutanen. Anty Ramatu ya hango rike da hannunta, duk da baya ganin fuskarta da take sadde a kasa, ga hular alkyabbar jikinta ta kara boye mishi fuskarta.

Yana ganin yanayin tafiyarta, har suka karaso inda yake din

“Gata nan mintina biyar, kuyi maganar da zakuyi tafiya zamuyi”

Dakuna ma Anty Ramatu fuska yayi

“Zan taho da ita gida. Nazo da mota”

Kai ta girgiza ma AbdulKadir din, bada ita za’ayi wannan rashin hankalin ba

“Kuyi maganar ku, ko kabari muje gida sai kayi maganar a nutse. Amman yanda mukazo tare haka zamu koma tare da ita” 2

Ta karasa maganar tana sauke numfashi. Cikin bacin rai yake kallon Anty Ramatu

“Meyasa ba zamu tafi gida tare da ita ba?”

Kallon shi take itama

“Haka kawai…”

Kai AbdulKadir ya jinjina, koda zaiji maganar da aka fada mishi yana son ayita da hujjar da zata gamsar dashi, kaf gidansu Yassar ne kawai yakan sakashi yin abu wasu lokuttan batare da ya bashi kwakwaran dalili ba kuma yayi. Amman ko Abba yana fada mishi dalili, da Anty Ramatu tabashi wani dalili mai karfi zai iya juyawa ya tafi in yaso saisu hadu a gida. Amman haka kawai ba zata fara gaya mishi abinda zaiyi ba. Hannun shi ya mika da nufin kamo na Waheedah yajata subar wajen, Anty Ramatu ta tare da fadin

“Ai ba’a daura ba tukunna, Malam AbdulKadir…” 4

Bude baki yayi zai gaya mata maganar da take yawo cikin kanshi Anty Talatu ta karaso wajen tana riganshi da fadin

“Hajiya Ramatu ke aketa nema. Ashe kina nan… AbdulKadir…”

Anty Talatu ta karasa maganar tana maida hankalinta kan AbdulKadir da har lokacin Anty Ramatu yake kallo

“Ai kamun namu babu maza…”

Kallonta Anty Ramatu tayi

“Na fada mishi fa, wai yanzun tare yake so su koma gida da Waheedah…. Nace yaje zamu taho gidan…”

Murmushi Anty Talatu tayi, dan ita tasan halin shi sarai, Anty Ramatun ma da alamu ba sosai suke haduwa da AbdulKadir din ba

“Ki fada mata da Waheedah zan koma gida… Banaso inyi magana tace na mata rashin kunya”

AbdulKadir ya fadi yana kallon Anty Talatu. Kai kawai ta jinjina mishi tana fadin

“Allah ya tsare…muma gidan mukayo”

STORY CONTINUES BELOW


Ta karasa maganar tana janyo hannun Anty Ramatu da take kallon AbdulKadir daya kankance mata idanuwanshi cike da rashin kunya.

“Hannunta fa zai rike Hajiya Talatu. Kina ganin babu wata matsala su tafi gida su kadai… Yaron yanzun basuda kunya wallahi” 1

Wannan karin dariya Anty Talatu tayi

“AbdulKadir ne Hajiya Ramatu… Babu abinda zai faru… Idan basu tafi taren bane matsala…” 3

Kai kawai Anty Ramatu ta jinjina, amman duk da haka bataso tafiyar AbdulKadir da Waheedah din ba, musamman data juya taga ya rike hannun Waheedah din tana bin bayanshi. Wannan tabe-taben rashin kunyar ko kadan ba sonshi takeyi ba. Idan yai hakuri gobe dai-dai lokacin ta rigada ta zama mallakin shi duk rikon dazai mata ladan hakan zai samu ba yanzun da babu komai cikin hakan sai tarin zunubi ba. 3

*

Bai tsaya da ita ko ina ba sai gaban motar, har lokacin baiga fuskarta ba, kanta a kasa yake, banda dokawa babu abinda zuciyarta take mata. AbdulKadir ya gama sakata a kunya, batasan ya zata fara hada idanuwa dasu Anty Ramatu ba yanzun, sosai taji dadin zuwan Anty Talatu wajen dan a kasan zuciyarta take jin yanda AbdulKadir yake gab da tsulama Anty Ramatun rashin kunya. Tana nan tsaye kanta a kasa harya bude mata murfin motar, alkyabbar jikinta ta tattara tukunna ta shiga, zama tayi ta rufe murfin motar tana wasa da yatsun hannunta da ta ajiye kan kafafuwanta.

Bai mata magana ba shima, motar yaja suna kama hanyar gida. Zai iya rantsewa da duk wani abu na jikinshi harta gashin dake bayan wuyanshi yana sane da zamanta a gefen shi. Fuskarta yake son gani ko yayane, amman hular alkyabbarta ta kare mishi. Ko kunshinta baigani ba sosai, ta turo mishi hotunan da tace ana mata, amman da aka gama baigani ba, yaita jira ko zata tura mishi amman shiru, sai bai tambayeta ba tunda zaizo yagani da kanshi. A nutse yake tukin har suka karasa gida sannan ya samu waje cikin harabar gidan yayi parking.

Fitilar dake cikin motar ya kunna haske na gauraye su. Gyara zaman shi yayi yana kai hannu yaja hular alkyabbarta yana sauketa daga saman kan nata. Hakan yasa Waheedah da tayi zurfi cikin tunanin da ba zatace gashi ba ta juyo tana sauke mishi manyan idanuwanta da kwalliyar da akai musu ta saka su kara girma. Wani irin numfashi AbdulKadir ya tsinci kanshi da ja yana furzawarwa hadi da yawata idanuwan shi akan fuskarta da tayi mishi kamar ba tata ba. A hankali yake jin bugun zuciyarshi na karuwa musamman data motsa labbanta da yake komai dan ganin baisaka yatsan shi akai yaji ko janbakinta nada maikon da yake gani marar walqiya ko kuma idanuwan shine suke haska mishi hakan.

“Hamma…”

Ta kira cikin sanyin muryarta da yaji ya saukar mishi da wata kasala taban mamaki.

“Me yasa kika kashe wayarki? Kinsan zan kira meyasa kika kashe?”

Maganar tashi ta fito a matsayin tsegumi maimakon fadan da yayi niyya, ta gama kashe mishi duk wani fada da yakeji, kanshi ya jingina jikin kujerar motar yana kar kankance mata idanuwanshi

“Banda chargy ne shisa, wayar mutuwa tayi…”

Waheedah ta fadi tana kallon yanda shaddar jikin shi tai matukar karbar kalar fatarshi.

“Kayan nan sun maka kyau”

Ta tsinci kanta da furtawa tana sakashi dakuna mata fuska

“Nama kayan kyau dai…” 7

Dariya tayi da ta saka shi runtsa idanuwanshi yana budesu akanta, wani irin kyau tai mishi da bai taba sanin tana dashi ba. Kamar kullum ya dinga ganin fuskarta dauke da kwalliya haka. Har shigar mishi ido da haskenta yakeyi yau ya nema ya rasa, farin nata yaji yayi mishi dai-dai.

“Kinyi sallah?”

Ya bukata yana kallonta har lokacin, kai ta girgiza mishi tana tuna mishi da yanda ita kadaice a fadin rayuwarshi da take amsa mishi magana batare data bude bakinta ba, kuma ya karbi amsar. Ita tunda aka fara hidimar bikin a dai-danta take. Ko zata samu tsarki sai zuwa washegari.

STORY CONTINUES BELOW


“Zaki je kiyi saiki dawo? Lokaci na tafiya”

AbdulKadir ya sake fadi, dan sallah na daya daga cikin abubuwan da baya wasa dasu a rayuwar shi, bakuma yabari duk wani makusancin shi yayi wasa da ita. Sai dai ga mamakin shi kai ta sake girgiza mishi, tana saka shi fadin 3

“Me yasa?”

Cike da wata irin kunya da rabon da tajita a tsakaninsu ta manta ranar ta sauke idanuwanta daga cikin nashi tana fadin

“Hamma mana…”

Dan ware idanuwanshi yayi cike da fahimta, da murmushi a fuskarshi yace

“Oh…okay… Nagane. Duk yau me kikaci?”

Ganin ta sake sadda kanta kasa yasa shi fadin

“Yau ma bakici komai ba Waheedah? Jiya bance kici wani abu ba? Meyasa bakici ba? Saboda kin rainani ko? Ban isa in sakaki abu kiyi ba…”

Dagowa tayi ta kalli fuskarshi da take dauke da yanda rashin yake a bace

“Hamma…”

Ta kira cikin sanyin murya tanaso ya fahimci badan ta raina shi yasa bataci abinci ba, ba kuma dan bataji yunwa bane ba, anata hidima ita basu bata abincin bane shisa, amman tasan halin shi, idan tace ba’a bata abinci bane shisa bataci ba fadan karuwa zaiyi.

“Ki jirani ina zuwa…”

Yai maganar yana bude murfin motar ya fice. Gyara zamanta tayi sosai, tasan anacan ana nemanta watakila, ba zata iya rikicin AbdulKadir ba da tace mishi zata shiga cikin gidan dan kar a nemeta. Tana wannan tunanin AbdulKadir din ya dawo ya bude motar yana shigowa, robar take away da abinci a ciki ya dora akan cinyarta yana gyara zamanshi cikin motar ya rufo murfin, robar ruwan a jikinshi ya ajiyeta yana daukar robar dake jikin Waheedah ya bude ya saka mata cokalin da bata kula yana hannun shiba a ciki, kamshin fried rice din da tasha kayan hadi da nama ta daki hancinta tana kara mata yunwar da takeji.

Batare da tunanin komai ba tasa cokalin ta dibo abincin takai bakinta ta tauna, Lumshe idanuwa tayi dan ya mata dadi na fitar hankali, batasan ko hakan nada alaka da yunwar da takeji ba, hadiyewa tayi tana kara dibowa, yanda take cin abincin da sauri yasa AbdulKadir fadin

“Slow down, karki kware Waheedah…”

Kai ta girgiza mishi, tana hadiye abincin da yake bakinta

“Hamma yunwa nakeji sosai, banci komai bafa duk yau… Bazan kware ba”

Ta karasa maganar tana kai wani cokalin a bakinta. Sosai taci abincin dan kadan ta rage da taji ta koshi har cikin makoshinta. Ruwan AbdulKadir ya kwance yana mika mata, ta karba kuwa tana kaiwa bakinta. Yabi kunshin da yake hannunta da kallo. Ruwan data sauke ya karba yana sha shima, makoshin shi ya bushe batare da dalili ba tunda ba kishi yakeji ba. Numfashi Waheedah ta sauke wata nutsuwa na saukar mata, cokalin ta gyarama zama cikin robar ta rufe, tana jin yanda AbdulKadir yake binta da idanuwa, kafin yasa hannu ya dauki robar abincin yana dorawa gaban motar ya ajiye. Gyara zaman shi AbdulKadir yayi yana jingina da kujerar motar sosai ya lumshe idanuwan shi. 1

“Hamma…”

Waheedah ta kira ganin kamar shirin bacci AbdulKadir din yakeyi a cikin motar.

“Karki dameni da surutu Waheedah, hutawa zanyi” 6

Ya fadi batare daya bude idanuwan shi ba, gabaki daya bayajin karfi a jikinshi, saida yai sallar isha’i kafin ya karasa wajen kamun, amman bayajin shiga cikin gida ya kwanta a daki. Anan cikin motar inda take yake son hutawa, kokawa yake da abinda keson dora koda kanshine a jikinta yayi bacci, ba sai yayi tsayi ba, awa daya ma ya isheshi. Ba sosai yake samun bacci ba tunda ya tafi, yanzun ganinta yasa duk wata gajiya da yake rike da ita saukar mishi. Ita kadaice a rayuwarshi yake iya nunama kasawarshi ko gajiyarwar shi.

STORY CONTINUES BELOW


“Za’a nemeni Hamma…”

Waheedah tai maganar kamar zatai kuka, tana saka shi bude idanuwanshi ya duba agogon da tun wanda ta sai mishine

“Karfe takwas da rabi, tara da rabi saiki tafi”

Duk da yayi maganar babu wajen musu bai hanata fadin

“Hamma tara da rabi”

Idanuwan shi ya sauke cikin nata

“Musu zamuyi dake?”

Ya bukata yana sata girgiza mishi kai.

“Good…”

Ya fadi ya gyara zaman shi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi.

“Ki zauna sosai”

Yai maganar batare daya bude idanuwan shi ba. Ita kam bataga ta zama sosai ba, awa daya AbdulKadir yake son tayi a zaune cikin motar, badan batason zama dashi ba, har ranta awa dayama yai mata kadan tare dashi, amman za’a nemeta tasani, da ba’a hidima ba zata damu ba.

“Inajin sautin tunaninki har nan Waheedah…babu inda zakije kuma” 4

Shagwabe mishi fuska tayi duk da idanuwanshi a lumshe suke.

“To inje in dauko wayata?”

Ta bukata, ko wayar ta latsa kafin awa daya ta cika, zatafi mata sauri, hannu yasa a aljihunshi yana zaro wayarshi ya mika mata, hannu tasa ta karba ganin idanuwan shi a lumshe suke.

“Waheedah”

Ya fadi yana sauke numfashi. Cike da rashin fahimtar kiran sunanta da yayi take kallon shi, kamar yaji hakan yasa shi fadin

“Password din Waheedah” 7

Zuciyarta taji ta kumbura ta cika fam, sunanta ne mukullin sirrin wayarshi, dannawa tayi kuwa taga wayar ta bude, murmushi tayi tana gyara zamanta, takasa daina murmushi, abinda batasani ba shine kowanne abu nashi da yake bukatar mukullan sirri sunanta ne, hotunan shi ta shiga tana dubawa, duk wanda tagani saita shiga WhatsApp dinta ta turawa kanta shi. Batasan awa daya ta cika ba, batama san ya bude idanuwan shi ba, saida taji ya fisge wayar daga hannunta yana fadin

“Me kike mun da waya…”

Yana dubawa, hotunanshi yagani ta tura ma kanta ta WhatsApp, yana da tabbacin gabaki daya hotunanshi ne da suke cikin wayar. Kai kawai ya girgiza, da tace yabar mata wayar ma taje ta tura ba saita karar mishi da data ba. Mukullin motar ya zare yana zagayawa ya bude mata, fitowa tayi. Hamma yayi saboda bacci yakeji sosai

“Saida safe…”

Yace mata yana murza idanuwanshi cikin yanayin da yai mata kyau. Ganin ta tsaya tana kallon shi yasa shi fadin

“Ko in rakaki?”

Da sauri ta girgiza mishi kai. Zata lallaba ta shiga bangaren Anty, inta dan jima anan saita koma gida, ba saiya rakata kowa yasan tare suke ba. Juyawa ma tayi ko saida safe batai mishi ba, kafin rikicin shi ya yanke mishi hukuncin rakata. 2

*

Washegari hidimar tafi hade musu, tun karfe bakwai aka gama musu kwalliya ita da Zahra, wata doguwar rigace ruwan kwai, wuyan rigar dogone irin wanda ake kira high-neck a turance, sosai ta karbi su duka biyun, daga daurin dankwalayensu zuwa yanayin lullubinsu zaka gane amare ne ko baka kalli kunshin dake hannuwansu ba. A harabar gidan aka fito dasu dan ayi hotuna. AbdulKadir yafi duka mazan dake wajen tsayi, shima yana sanye da shadda fara kal da babban rigarta kamar sauran angwayen. Abin gwanin ban sha’awa, sosai akai musu hotuna, angwayen da amarensu su kadai, su duka gabaki daya, sai kuma da sauran mutane da abokan arziqi.

STORY CONTINUES BELOW


Kasancewar daurin auren na karfe takwas ne, Zahra kanta ba a Kano zata zauna ba, Katsina ne, ga Yazid da matarshi shima. Dan haka aka saka bikin da safe don ana dawowa za’a tafi da amaren. Suna gama daukar hotunan, babban masallacin dake nan kofar ruwa inda za’a daura auren suka dunguma suka nufa su dukkansu da abokan su. Ran AbdulKadir a bace yake, tun da safe daya samu Hajja da tambayar

“Wai da gaske za’a kai Waheedah ne itama?”

Cikin rashin fahimta Hajja tace

“Bangane za’a kai Waheedah ba”

Dakuna mata fuska yayi

“Ina nufin rakiya… Yanda za’a raka Zahra har katsina, itama za’a rakata har Minna?”

Kai Hajja ta jinjina sai lokacin ta fahimci abinda yake fada

“Eh, Hajiya Talatu, Hajiya Aisha, Dadda, Da waye naji suna maganar, su bakwai daine zasu rakata, saboda sauran zasu raka Zahra”

Girgizama Hajja kai yakeyi tunda ta fara magana, shi bayason wannan al’adar, a tsarin shi koda na wani gari bane yazo da mota ya dauki matarshi su tafi, su Anty Talatun da take magana su sukaje sukai jeren kaya har Minna din tun satin bikin. Hakan ma ya isa, Allah ya amfana ba sai sun raka mishi mata ba, bayason wannan al’adar ko kadan

“Kice musu su zauna abinsu Hajja, nida ita kawai zamu tafi da na dawo daurin auren…” 2

Kallon shi Hajja take kamar bashida hankali

“Bangane me kake son cewa ba”

Numfasawa yayi

“Wani rakiyar amarya nake magana… Ni banaso… Su zauna” 1

Wata dariyar takaici mai sauti da bata da alaka da nishadi Hajja tayi, tana sa AbdulKadir fadin

“Koni in gaya musu suyi zamansu?” 3

Cike da takaicin da ta kwana biyu bataji irin shi ba take kallon AbdulKadir din

“Wallahi idan baka bacemun daga nan ba saina kwasheka da mari…”

Kallonta AbdulKadir din yakeyi shima

“Mari fa Hajja…me nayi ni? Me nayi?” 3

Yake tambaya yana son sanin dalilin da Hajja zatace zata mare shi dan ya fadi ra’ayin shi, yaga kirkine shi su Anty Talatun zasuyiwa, kuma yace bayaso ba sai ayi abinda yace ba tunda matar tashi ce.

“Saina marekan zaka barmun daki ko?”

Dakuna fuska yayi

“Ai bansan me nayi bane ba… In fada musu zan dauki matata ko zaki fada musu” 1

Numfashi Hajja ta sauke, idan ta biyema AbdulKadir ba mari ba kawai, rufeshi da duka zatayi. Batasan ranar da zaiyi hankali ba, har ranta taji dadin hadin auren shi da Waheedah, ko bakomai tana fatan hankali da nutsuwar yarinya su tausasa halayyar AbdulKadir din, har dadi takeji ganin tunda aka fara hidimar bikin babu wanda yai kuka da shi, babu wanda yace yayi mishi rashin kunya. Amman yanzun yana son jama kanshi zagi da bakin mutane. 2

“Al’adace hakan, ba kuma za’a canzata daga kanka ba, daga nan har Minna zakace abarka ku tafi ku kadai saboda kai baka da hankali…”

Hajja take maganar cikin fada

“Hajja…”

AbdulKadir ya kira tana katse shi da

“Wallahi idan baka bacemun dagani ba sai ranka yayi mugun baci… Kuma inji ka sami wani da maganar nan dan Allah… Yau ka nunamun ban isa dakai ba AbdulKadir kai musu maganar nan…”

Hajja ta karasa tana mikewa taci gaba da hada kayanta da takeyi lokacin daya shiga dakin. Tunda ya fita ranshi a bace yake harya karasa shiryawa suka fito suna hotunan nan sama-sama yake jinshi, addu’a yake kar wanda ya tabo shi ballantana ya sauke mishi bacin ran da yake ji. Ko da ake musu hotuna da Waheedah, yana jinta tai magana dai-dai kunnen shi

STORY CONTINUES BELOW


“Waya tabamun kai Sadauki?” 13

Taso tasa murmushi ya kwace mishi, tun randa ta fara furta mishi sadaukin nan yaji sunan ya mishi dadi sosai. Sai dai hakan baisa bacin ran ya tafi ba, ko amsa ma bata samu ba har suka bar wajen. Da bacin ran ya karasa masallacin, haka har aka gama daurin auren aka fito daga masallacin, a kasan ranshi yakejin wata irin nutsuwa taban mamakin da igiyar data kulle tsakanin shi da Waheedah. Nanma saida aka tsaya bata lokaci wajen daukar wasu hotunan, danma Abba yace musu a tafi gida, akwai tafiya a gabansu.

*

Babbar rigarshi ya cire dan jinshi yake a takure yana sake kayan, duk da wata shaddar ya sake sakawa, amman bayajin nauyinta kamar wanda ya cire, ninke su yakeyi yaji Yassar ya shigo dakin da sallamar da ya amsa yana ci gaba da linke kayan da yakeyi.

“Kayi sauri, an fara shirye-shiryen tafiya…”

Kai kawai AbdulKadir din ya dagama Yassar yana saka shi fadin

“AbdulKadir…”

Bai amsa ba tunda kunnuwa ne suke jin magana

“AbdulKadir…”

Ya sake kira, kananun idanuwanshi ya sauke kan fuskar Yassar

“Kunnuwane suke ji Hamma… Kasan ina jinka ai”

Numfasawa Yassar yayi

“Zaka dauki yar mutane zuwa wani gari, AbdulKadir ba’a aura maka ita dan an gaji da ita ba, ba kuma a aura maka ita dan an gaji da kula da ita ba. Rokonka nake karka kuntata mata, karka cutar da ita…” 4

Idanuwan shi AbdulKadir ya kankance

“Dan ba’a jarabawar samun limanci da nace ka yanki form Hamma…” 3

Kai Yassar yake girgiza da murmushi a fuskar shi

“Dan ubanka ba maganar wasa nake dakai ba, nasiha nake maka”

Ware mishi idanuwa AbdulKadir yayi

“Abinda yasa nace limanci zai maka kyau kenan” 3

Dafe kai Yassar yayi, baisan ranar da AbdulKadir zai fara daukar abubuwa da muhimmanci ba, ganin babu alamar zai saurare shi yasa shi mikewa yana fadin 1

“Abba na kira…”

Dakuna fuska AbdulKadir yayi

“Dan Allah Hamma kace ba wata nasihar za’aimun ba… Wai ita Waheedah ba za’ai mata bane ba? Nima ai aurena aka bata, me yasa ni kadai za’a dinga yiwa…. Itama kaje kace ta riqeni amana, karta cutar dani…” 10

Kofar Yassar ya bude kamar baiji abinda AbdulKadir din yace ba

“Hamma magana nake kana tafiya…”

Ficewa yayi yana jan kofar, fuska ya kara dakunawa yana dibar kayan ya tura cikin karamar jakar daya shirya duk kayanshi da zai iya dauka a ciki, yawanci kananun kayane, manyan fiye da rabi anan gida yabarsu. Jakar ya bari kan gado yana fita daga dakin zuwa bangaren Abba yana shiga da sallama, babu kowa sai Waheedah da take zaune a gaban Abba, ta sake rigar dazun, bai gama ganinta ba sosai cikin rigar ta sake, yanzun bayama iya ganin fuskarta dan lafayane a jikinta anja shi an rufe fuskarta gabaki daya, yanayin yanda kafadunta suke rawa yasa shi gane kuka takeyi. 1

Gefenta ya zauna yana fadin

“Abba gani…Hamma yace kana kirana”

Kai Abba ya jinjina yana kallon yaran nashi, yanajin kaunar su fal cikin ranshi, yana kuma mamaki har lokacin yanda kaddarar rayuwa ta kawosu inda suke yanzun. Cikin ranshi yake ma Allah godiya yana karawa da musu fatan zaman lafiya da rayuwar aure mai inganci. 1

STORY CONTINUES BELOW


“Idan da wani yace mun zaku zo nan a rayuwar ku ko na yarda zan jinjina lamarin…” 1

Abba ya fara magana yana dorawa da

“Ko da kukejin ana kiran hakuri a zaman aure, badan yana jigon auren bane gabaki daya, sai dan yana taka muhimmiyar rawa a zamantakewa ta yau da kullum. Abu daya zan fada muku, karku bani kunya, ku dukanku karku bani kunya. Matsalar aurenku kuyi kokarin ganin kun shawo kanta da kanku, sirri na daya daga cikin abubuwan da suke da muhimmanci a aure… Ku rike sirrin junanku kamar fitar dashi zai iya zame muku matsala. 1

Dan nace hakan kuma ba ina nufin ya baku damar da zaku cutar da junanku dan zaku rike a matsayin sirri ba. A duk lokacin da hakan ya faru, kuke ganin ba zaku iya ba ku daga waya ku kirani, shine kawai mutuntakar da zakuyi mun, ku sanar dani kafin yanke hukunci mai girma…”

Su dukansu sunyi shiru suna sauraren Abba, Waheedah daman tunda aka rakata wajen Mami take kuka, har aka kawota wajen Abba, yanzun ma kukan takeyi sosai. AbdulKadir kanshi Abba yasa jikinshi yin sanyi, tabbas aure abune mai girman gaske, bazai tuna ranar karshe da Abba ya zaunar dashi yana mishi nasiha har yanajin kaunar shi a tare da kalaman shi ba sai yau.

“Allah yai muku albarka a zamantakewar ku, Allah ya tabbatar muku da dukkan alkhairi…” 2

Abba ya karasa da wani yanayi mai nauyi a muryarshi, har a kasan ranshi ya fara jin kewar yaran nashi.

“Mungode Abba…”

AbdulKadir ya fadi yana mikewa, amman Waheedah ta kasa mikewa, magana zai mata Anty ta shigo, bata ce mishi komai ba tazo ta kama Waheedah tana janta suka fice daga dakin. Kukan da take yai mishi tsaye a makoshi. Bin bayansu yayi yana wucewa bangarensu dan ya dauki jakarshi, yasan zai kwana biyu bai shigo Kano ba, makarantar Waheedah ma transfer akai mata zuwa Minna din, badan Abba yasan mutane ba da hakan yai musu matuqar wahala. Kuma yanda yakeji bazai iya barinta a Kano ba, inda duk yasa kafa nan zata mayar da tata. Saidai ta hakura da makarantar.

MINNA

Gajiya takeji har a kasusuwan ta, wannan ne karo na farko a rayuwarta da ta taba zuwa wani waje daya wuce kauyen bugaje. Jitai kamar zasu je karshen duniya, kamar tafiyar kwanaki ce a maimakon ta yini daya. Sosai ta gode ma Anty Aisha data hada mata ruwa mai zafi tace taje tai wanka. Sosai tadanji dadin jikinta, wasu kayan ta samu an dauko mata, doguwar rigace ta atamfa sabuwa fil, dauka tayi ta saka tukunna ta dauki hijabin da tagani dan gabatar da sallar magriba tabi data isha’i tunda ta samu tsarki.

Hakan kuwa tayi, lokacin data idar an kawo musu abinci kala-kala a take-away da alama siyowa akayi. Guda daya aka ajiye mata a gabanta, ta cire hijabin ta dora kan gadon da yake dakin kenan tana shirin bude robar abincin dake gabanta da batajin yunwar cin shi ko kadan saboda kewar gida da takeyi ga kuma gajiya, aka kwankwasa dakin.

“Waye? Shigo…”

Anty Talatu ta amsa, AbdulKadir ya shigo da sallama, a bakin kofar yai tsaye yana fadin

“Anty sannunku da hidima… Waheedah dan zo” 3

Wata irin kunya taji ta rufeta ganin gabaki daya su Anty ne a wajen, harda danginta na wajen uba guda biyu.

“Ki tashi kije mana”

Anty Aisha ta fadi, kafafuwanta da matukar nauyi taja su tana mikewa, mayafinta da aka fito dashi shima sabo ta dauka, sai lokacin AbdulKadir ya mayar da kanshi yana fita daga dakin, kafafuwanta babu karfi ta wuce tana fita daga dakin, ji takeyi kamar idanuwansu nakanta duk da tana jin suka cigaba da hirarsu kafin taja musu kofar. Kamar hakan AbdulKadir yake jira ya kama hannunta yana fara janta

“Ina zamuje?”

Ta tambaya, juyowa yayi yana kafeta da idanuwanshi da suka sakata yin shiru, saida taga suna shirin nufar hanyar da zata fita dasu daga gidan tukunna tace

STORY CONTINUES BELOW


“Takalmana Hamma…”

Hannunta ya saki yana kallon kafafuwanta, hanyar bedroom din da suka baro ya nufa, tsinin takalmanta yasa shi gane sune ya kwaso mata yana dawowa ya ajiye mata su, sakawa tayi ya sake kama hannunta suna fita. Sai lokacin take karewa barikin sojojin kallo, saidai saurin da AbdulKadir yakeyi ya sata maida hankalin ta kanshi tana binshi kamar wadda aka jona ma battery. Tafiya sukayi har bakin kofar wajen tana mamakin ganin motar Yassar, dan batasan dasu da abokan AbdulKadir din akazo rakoshi ba, hotel suka kama, sun dauka rashin son hayaniya yasa AbdulKadir kama nashi dakin daban, kuma nesa da nasu, tunda gidan nashi daki biyune kuma su Anty anan zasu kwana suma.

Saida yace ma Hajja a gaya musu karsuzo, kowa yai zaman shi ta balbale shi da fada kamar yai mata laifi. Ga gidan nan suyita kwana, shikam da matarshi a hotel zasu kwana. Batace mishi komai ba har suka shiga motar yaja su, a gajiye take jinta. 5

“Hamma nagaji wallahi, jikina ciwo yake…”

Ta fadi ganin har lokacin basu kai inda zasu kai ba

“Mun kusa…”

Ya fadi yana shan kwanar da zata kaishi hotel din, shiga ciki yayi ya samu waje yai parking din motar. Tukunna ya bude mata ta fito, a gajiyar da takeji bin AbdulKadir da yake rike da hannunta tayi duk inda yayi da ita, har suka karasa bakin wani daki ya bude yana jan hannunta suka shiga ya mayar da kofar ya rufe. Hannun nata ya sake kamawa yajata kan gadon ya zaunar da ita, takalmanta ta cire tana kare ma dakin kallo, tana mamakin yanda batajin tsoro ko dar a zuciyarta, sanin AbdulKadir din bazai tabayin abinda zai cutar da ita ba. 1

Abinci taga ya dauko yana fadin

“Sakko muci…”

Kai ta girgiza mishi a hankali

“Jikina namun ciwo…”

Gira ya daga mata

“Shine ba zakici abinci ba? Sauko kafin ranki ya baci”

Turo labbanta da har lokacin da sauran janbakin kwalliyar data wanke a jiki tayi tana saukowa, hannu yasa yana zare mayafin da taki cirewa ya ajiye shi a gefe batare dayace mata komai ba. Itama batai magana ba ta dauki cokalin tana sakawa cikin abincin, tare sukaci, turawa kawai tayi, tagode ma Allah da bai mata magana ba. Mikewa taga yayi ya shiga bandakin dake cikin dakin, karar ruwa ya tabbatar mata da wanka yakeyi, ya jima kafin ya fito. Tanajin wayarshi na kara, bata ko motsa daga inda take ba ballantana tai kokarin daga wayar.

Harya fito daure da towel a kugun shi dayasata dauke idanuwanta daga kanshi, wayar ya karaso ya dauka. Anty Talatu ce, hidimar bikin yasaka shi samun lambarta. Dagawa yayi yana fadin 1

“Hello…”

Daga dayan bangaren yaji tace

“Ina kukaje AbdulKadir? Kasan dai kowa ya kwaso gajiya ko? Kwanciya zamuyi ka dawo da ita haka”

Kankance idanuwan shi yayi

“Kuyi kwanciyarku kawai, zamu kwana a hotel” 5

Ya fadi

“Hotel?”

Anty Talatu ta maimaita da matuqar mamaki a muryarta

“Hotel fa AbdulKadir…”

Dakuna fuska yayi yana fadin

“Saida safe”

Ya kashe wayar tashi gabaki daya. In ba zasu kwanta ba su nemi motar Kano su juya a daren. Bayason wani dogon surutu shisa ya kashe wayar gabaki daya. Towel din ya kwance yana barin gajeran wandon dake jikinshi ya koma bandaki ya ajiye. Kan gadon ya karasa yana shirin kwanciya kenan yaji ana kwankwasa mishi daki, tashi yayi yaje ya bude kofar yana tsayawa a bakinta ganin Yassar na sauke waya daga kunnen shi

“Daukota kayi ka kawo nan? Saurin me kake AbdulKadir?”

Dakuna ma Yassar fuska yayi

“Ina da ikon dauko matata in kaita duk inda yaimun” 1

Ya ba Yassar din daya dafe kai amsa

“AbdulKadir… Oh Allah na, ka tashi ka mayar da ita… Meyasa zaka daukota? Kasan surutun da zaka jama Hajja kuwa? Me yasa baka da kunya ne”

Hamma AbdulKadir yayi dan bacci ne a idanun shi

“Wallahi bazan mayar da ita ba, ai nace ma Hajja karsu zo, kar suzo saboda za’a takurani, za’a shiga rayuwata, bata fada musu ba. Ni kabarni…” 13

Baki a bude Yassar yake kallon shi kafin yace

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Kallon shi AbdulKadir yakeyi

“Ka daina yi kamar anyi mutuwa fa… Ba zaisa in mayar da ita ba. Da ka wuce ka kwanta zaifi maka alkhairi…” 8

Ya karasa maganar yana rufe kofar a fuskar Yassar da yake tsaye. Cikin dakin ya shigo inda ya samu Waheedah a zaune tanajin duk wata kunyar duniya ta tattarar mata waje daya, batajin zata iya komawa gidan nan ta hada idanuwa dasu Anty. Amman batasan ya zatayi da AbdulKadir bane ba. Yanzun ma hannunta ya kama yana mikarwa ya dora kan gadon. Hawa yayi shima yana kai hannu ya kashe musu kwan dakin, kwanciya yayi yana jan Waheedah ya kwantar da ita kan kirjin shi yanajin wata irin nutsuwa na saukar mishi.

Yanda yakejin bugun zuciyarta a kirjinshi yasa murmushi kwace mishi

“Baki da hankali Waheedah… Kiyi bacci nima bacci zanyi…” 12

Yai maganar yana kara gyara mata kwanciya a jikin shi, da gaske yake mata baccin zasuyi. Bayajin yin bacci shi kadai ne shisa yaje ya dauko ta, addu’a yayi tana jinshi ya tofa musu, amman ta kasa koda runtsa idanuwanta ne balle bacci ya dauketa, saida taji numfashin shi ya canza alamar bacci yake da gaske tukunna ta sauke wata irin ajiyar zuciya da batasan tana rike da ita ba. Hannunta daya ta dora kan kirjinshi tana gyara kwanciyar ta, tana godema Allah daya nuna mata zama matar shi. 3

Kanta ta gyara kan kirjinshi, bugun zuciyar shi na nutsar da wani abu a cikin nata kirjin har baccin gajiya yai gaba da ita…!Waheedah…” 5

AbdulKadir ya sake kira a karo na hudu, fuskar shi dauke da murmushi, baisan kalar gajiyar da tayi ba, sallar asuba ma daya tasheta kallon shi ta dingayi kamar ya kwace mata wani abu, daya jasu sallar suka idar, yana kallonta taja jiki takoma kan gado, ko hijab bata cire ba. Yanzun ma hannun shi da yake kan kafadarta take turewa tana shagwabe mishi fuska

“Me zanyi?”

Ta tambaya muryarta cike da bacci, har lokacin idanuwanta a rufe suke, murmushi yayi har hakoranshi suka fito. Gyara zaman shi yayi gefenta yana saka hannuwan shi duka biyun ya dagota hadi da girgizata

“Ki tashi Waheedah…. Hamma zai kasheni inya dawo bamu shirya ba, idan mukaje gida sai kiyi baccin…” 1

A hankali take bude idanuwan ta, tanajin kanta kamar an dora buhun siminti, duk wata gaba da take jikinta ciwo take mata, bata taba gajiya irin wadda tai daga satin bikin zuwa wayewar garin ranar ba. Kallon fuskar AbdulKadir da yake mata dariya tayi, tana tunanin inda take kafin komai ya dawo mata.

“Hamma…”

Ta kira tanajin kunyar duniya ta tattaru ta rufe ta. Dariya yayi

“Ki tashi ki watsa ruwa mu tafi…”

Kai ta daga mishi tana bin hannuwan shi da suke rike da ita da kallo, hakan yasa AbdulKadir sakinta, ta dayan bangaren ta ja jikinta ta sauka, kanta a kasa ta wuce shi zuwa bandakin tana rufo kofar, wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta sauke. Ruwa ta watsa tana mayar da gabaki daya kayan da ta shiga dasu, tukunna ta fito. AbdulKadir na zaune inda tabarshi yana danna wayar shi, sai lokacin ta tuno da tata wayar tana gida cikin jaka. Hakan kuma na tuna mata da su Anty Talatu da suka bari da yanda zata fara hada ido dasu yanzun.

“Hamma…”

Ta kira cikin tashin hankali, dago da idanuwan shi yayi yana kankance su akanta

“Ina zamuje?”

Ta bukata, da mamaki yake kallonta

“Gida…”

Ya amsa a taqaice, kai ta girgiza mishi, tana sashi daga mata gira cikin alamar tambaya

“Su Anty na nan, ban san me zance musu ba…”

Bude baki yai da niyyar amsata, kwankwasa kofar da akayi ya hanashi.

“Wallahi badan Waheedah ba da tuni mun tafi…yanzun ma bazan sake magana ba…”

Yassar ya fadi daga wajen dakin, da alamun ranshi a bace yake, mikewa yayi yana daukar hijab din Waheedah ya karasa inda take tsaye, juya hijab din yayi zuwa dai-dai tukunna ya juyo da wajen kan yana saka mata, damtsen hannunta daya ya rike yana jinshi kamar kara a cikin hannun shi, gyara mata zaman hijab din yayi sosai, ya juya ya koma ya dauko dankwalin kayan nata, hannunta ya sake kamowa ya saka a ciki, kallon shi kawai takeyi

“Sadauki su Anty na nan…. Dan Allah… Bansan me zance musu ba”

Waheedah take fadi muryarta a karye, ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, wayarshi da wallet ya dauka ya saka a aljihu, yazo ta gabanta ya wuce, saida ya zira takalman shi tukunna ya dauko mata nata yana ajiyewa a gabanta.

“Hamma…”

Idanuwanshi ya kankance mata

“Ki zabi abinda zaki cemun guda daya…” 1

Da sauri ta amsa shi

“Sadauki…”

Kai ya jinjina mata yana dorawa da

“Kisa takalmanki, idan Hamma yaimun fada raina zai baci, naki zai baci kema saboda na shirya tun dazun ke kike batamun lokaci” 1

Takalman ta saka, idanuwanta na cika da hawayen da batasan dalilinsu ba. Gaba AbdulKadir yayi tana bin bayanshi suka fita daga dakin, tsaye tayi ya kulle kofar, kanta a kasa yake, koda ya kama hannunta binshi kawai takeyi, inda duk ya cire kafarshi nan takw saka tata, daya tsaya bada mukulli ma a reception, tsayawa tayi batare data amsa gaisuwar da matar tayi mata ba, asalima ko dagowa batai ba balle taga kalarta, tana tunanin da idanuwan da zata kalli su Anty Talatu ne.

STORY CONTINUES BELOW


Har bakin motar Yassar suka karasa, yana tsaye daga waje, addu’a Waheedah takeyi kar Yassar yai mata magana, shima ganin kanta a kasa yasa shi kin ce mara komai, Allah ya hadata da wani irin miji da sukai hannun riga shida kunya. Shi kanshi Yassar din tayata jin kunyar abinda AbdulKadir yakeyi. Wata irin harara Yassar ya watsa ma AbdulKadir yana f

“Wallahi da ka kara minti biyar da saidai ku nemi abin hawa…”

Dakuna fuska AbdulKadir yayi yana amsawa da

“Na tashi lafiya Hamma, thank you, fatan kaima ka tashi lafiya?” 5

Wata hararar Yassar ya watsa mishi dan yasan gatse yai mishi, zagayawa yayi ya bude motar ya shiga. Saida AbdulKadir ya bude ma Waheedah bayan motar ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe sannan ya shiga gaban, Yassar yaja motar yana fita daga hotel din zuwa hanyar da yake tunanin zata mayar dashi barikin su AbdulKadir din, yana addu’a ya gane hanyar ba sai yayi magana da AbdulKadir ba.

*

Bayan AbdulKadir take bi har cikin gidan, kanta a kasa cike da wata irin kunya da bata taba tsintar kanta ciki ba. Jikinta taji ya soma bari jin AbdulKadir yayi Sallama, kuma Anty Talatu ta amsa mishi muryata dauke da wani irin yanayi

“Anty. Sannunku da gida… Ya gajiya?”

Kallon shi Anty Talatu takeyi, murmushin takaici mai sauti na kwace mata, ba tun yanzun tasan AbdulKadir bashida kunya ba, tun randa tazo gidan akace ya mayar da ita, tai mishi fada kan ya zagi wani saurayi daya kusan bigewa ya gaya mata maganganu, tace ya tsaya ya sauketa, ya kuma yi parking gefe yana jira ta fita. Amman jiya ne ta tabbatar da gaske bashida kunya. Yanzun ma yanda yake hada idanuwa da ita ya kara tabbatar mata da hakan

“Waheedah ina son magana dake kafin mu wuce”

Anty Talatu ta fadi, tana saka Waheedah dago da manyan idanuwanta tana kallonta cike da tsoro, tukunna ta kalli AbdulKadir da yake gefenta, dan daga mata kafadu yayi, yana kallon Anty Talatu data juya

“Anty gaisheki fa nayi, baki amsani ba kika wuce” 1

AbdulKadir yace cike da takaici, dan ba kullum yake bata gaisuwar shi ba, yau ma dan yana cikin nishadi ne shisa ya gaisheta, amman ta wuce bata amsa ba kamar ya mata wani abu. Ko juyowa batai ba, hakan yasa shi kankance idanuwan shi, yanajin yanda ranshi yake gab da baci. Cikin sanyin jiki Waheedah ta wuce ta bayan AbdulKadir zuwa dakin da Anty ta shiga. A tsaye ta sameta, daga bakin kofa ta tsaya tana jin idanuwanta sun fara tara hawaye, batason fada, ko kadan batason tayima kowa laifi a rayuwarta. Hankalinta gabaki daya a tashe yake.

“Waheedah idan kika biyema soyayyar namiji zaki sha wahala wallahi, bance karki bi mijinki ba, amman ba’a kowanne yanayi ba, yanzun ke mutuncinki ne ace darenki na farko a gidan miji kin dauki kafa kin bishi hotel?” 2

Kai Waheedah ta girgiza, hawayen da suke cike da idanuwanta suna zubowa, ci gaba da magana Anty zatayi aka turo kofar. Idanuwan shi AbdulKadir ya sauke kan Anty, ranshi ya gama baci.

“Ki fadamun Hadith daya ko aya data ce kar matata tabini hotel…” 4

Ya karasa maganar yana cigaba da kallonta, shisa bayason mutane, saboda irin wannan ra’ayoyin nasu ya sha banban da nashi, idan kuma ana maganar ranshi zai iya baci, baisan matsalar hausawan mu da hotel ba, yawancin su suna tunanin babu wanda yake ziyartar wajen sai mazinata, basa tuna cewa akwai matafiya da halin kwana ya kama a hanya suka tsaya, akwai wanda aiki ko kasuwancin yan kwanaki yakai shi, bashida zabin daya wuce kama hotel din dan ya zame mishi masauki. 1

Ranshi na kara baci da amfi ma duk macen da za’a gani a hotel kallon marar tarbiyya, musamman idan aka gansu tare da namijin da zai iya zamowa Yayanta ne tafiyar ta kamasu, dakunan da zasu kwana mabanbanta ne, ko kuma mijinta ne, kowa zaka gani a hotel yana da dalilin shi na zuwa wajen, ba kuma duka dalilan bane suke zama na banza.

STORY CONTINUES BELOW


“Kar kaimun rashin kunya AbdulKadir…”

Anty Talatu tayi maganar ranta a bace

“Saboda na nemi ki bani hujja kan dalilin da yasa rashin mutuncine kwanan da mukai a hotel?”

Mikewa Anty Talatu tayi daga zaman da take bakin gadon tana fadin

“Allah ya shirya ya bada zaman lafiya”

AbdulKadir din ya amsata da

“Amin…”

Yana matsa mata ta rabashi dan ta wuce, kafin ta fita ya dora da

“Mungode Allah ya saka da alkhairi ya mayar daku gida lafiya” 1

Bata amsa shiba ta fice daga dakin, ya mayar da kofar ya kulle a bayanta, yana mayar da hankalin shi kan Waheedah da take faman hawaye. Kuka baya damun shi sam, yasha zane Zahra ya zauna ya jirata ta gama kukan da zatayi suyi magana, kuka marar dalili ne bayaso, amman wannan da Waheedah takeyi har kasan zuciyarshi yake jinshi.

“Banaso Waheedah, banason kuka marar dalili”

Kallon shi tayi, wasu hawayen na kara zubo mata, tsoro takeji kar Anty Talatu ta fadama Mami ta mata wani abu, Mami zatai mata fada tasani

“Karta fadama Mami”

Dariya AbdulKadir yayi yana girgiza mata kai

“Baki da hankali ke kam…” 3

Ya karasa maganar yana kama hannun kofar

“Bari inyi sallama dasu Hamma…”

Kai ta daga mishi tana sa hannu ta goge fuskarta, yana fita ta karasa gefen gadon ta zauna. Har lokacin hankalinta yaki kwanciya, ko kadan batason tashin hankali.

**

PRESENT DAY

Kwankwasa kofar da taji anyi ya katse mata tunanin da take, sallama Hauwa tayi da Waheedah ta amsa mata cikin sanyin murya, turo kofar tayi tana fadin

“Na dauka kinyi bacci, Yassar nason magana dake daman”

Kai Waheedah ta girgiza mata, tana dafa gado ta mike, juyawa Hauwa tayi, tabi bayanta, a bakin kofar ta samu Yassar din a tsaye

“Waheedah yanzun Anty ta kirani, tace za’a mayar dake asibiti ashe…”

Numfashi Waheedah ta sauke

“Dan Allah Hamma kubarni da asibitin nan, hutawa suke so inyi kuma zan huta…”

Kallonta Yassar yake, a yanayin da yake ganinta bayaso ya takura mata, amman kuma lafiyarta nada muhimmanci

“Da gaske zan huta… Allah kuwa, idan naji banajin dadi sosai saimu koma”

Tayi maganar cikin son tabbatar mishi, a hankali ya jinjina mata kai

“Dan Allah koya kikeji kiyi magana mu koma, nasan ba shiri kuke da AbdulKadir a yanzun ba, amman zai kasheni idan wani abu ya sameki karkashin kulawata”

Murmushin karfin hali tayi tana rasa abinda zatace mishi.

“Allah ya sauqaqa”

Yassar yai maganar cikin sanyin murya, saida ta amsa shi da

“Amin…”

Tukunna ta juya ta shiga dakin tana turo kofar, data bude da sauri tana fadin

“Hamma wayata… Tana can, sai kayan su Ikram…”

Kai Yassar ya jinjina mata, ta sake mayar da kofar ta rufe. Shikam hanyar da zata fita dashi daga gidan ya nufa yana ce ma Hauwa

“Bari in dawo ba dadewa zanyi ba…”

STORY CONTINUES BELOW


Cike da damuwa take kallon shi

“Bakaci abinci ba har yanzun…”

Murmushi yai mata

“Zanci da na dawo… Kici ke dai…”

Kai ta girgiza mishi

“Nidai zan jiraka… Karka dade kaji?”

Numfashi ya sauke yana jinjina mata kai ya wuce, har wajen motar shi ya karasa ya shiga yana nufar gidan AbdulKadir.

*

A harabar gidan yayi parking din motar shi, batare daya fito daga ciki ba ya kira wayar AbdulKadir din ya fada mishi yana cikin gidan. Ko mintina biyar ba aiba saiga AbdulKadir din ya fito. Da murmushi a fuskar shi yake takawa zuwa wajen motar dan a zaton shi Waheedah Yassar ya dawo mishi da ita, yasani daman, a jikin shi yakeji Waheedah ba zata iya kwana wani waje yana gari ba, bata taba ba, ba kuma zata fara ba yau. Yana karasawa wajen motar ya kama murfin bayan yana kikiniyar budewa, kasancewar gilasan baqaqe ne baka ganin waye a ciki daga waje. 1

Qasa da gilashin gefen shi Yassar yayi, ya ziro kai yana fadin

“Ka maida hankali ka karyamun murfin mota AbdulKadir…”

Sakin kofar yayi yana matsowa saitin Yassar din

“Tana ina?”

Cike da rashin fahimta Yassar yace

“Ita wa?”

Dakuna mishi fuska AbdulKadir yayi, yanayin da yasa Yassar din jan karamin tsaki

“Malam ka wuce ka dauko mun kayanta dana yara, sai wayarta tace tana nan in hado mata dasu”

Lokaci daya murnar da AbdulKadir din yakeyi ta bace, wani tuquqin bacin rai na maye gurbinta, ga yunwar dake cinshi na kara taimakawa wajen rura mishi bacin ran.

“Kace mata tazo ta diba da kanta”

Bude motar Yassar yayi ya fito, shima nashi ran yake ji a bace

“Kalleni…” 2

Ya fadi yana dorawa da

“Ka kalleni dan ubanka. Nayi maka kama da abokin wasan ka? Ko na maka kama da dan aike… Karka kara batamun rai fiye da yanda yake a bace…”

Juyawa AbdulKadir yayi yana nufar hanyar gidan, Yassar bazai kara bata mishi rai ba, Waheedah ta gama hada mishi zafi. Bin bayan shi Yassar din yayi yana tsayawa cikin falon, dai-dai fitowar Nuriyya da wandone a jikinta ko cinyoyinta bai rufe ba tana fadin

“Masoyi…” 6

Da sauri tayi baya babu shiri ganin Yassar din, AbdulKadir ko inda take ma bai kalla ba ya wuce hanyar da zata kaishi dakin baccin Waheedah din. Batama yi tunanin sako abaya ta dawo ta gaishe da Yassar din ba, tasan ya tsaneta kamar sauran yan uwan AbdulKadir din, gara kannen shi suna gaishe da ita ciki-ciki. Amman ko wacce irin gaisuwa taima Yassar din yakan amsata ne da

‘Sannunki’ 1

Ya mayar da girar kasa da ta sama ya hade. Yanzun dinma ganinta ya kara bata mishi rai, ko lokacin da take kawance da Waheedah batai mishi ba sam, yanzun tsanar dayai mata ta kara linkuwa, yakan so ko yayane ya dinga mata fara’a saboda AbdulKadir din, amman ya kasa. Yakai mintina goma a tsaye a wajen kafin AbdulKadir din ya fito da wata yar jaka da kaya a ciki, kan kujera ya ajiye yana dora mishi wayar Waheedah da charger a kai ya juya batare da yace komai ba. Shima dauka yai ya fice daga gidan.

Bangaren Nuriyya inda yabar tashi wayar ya nufa yana daukar ta ya rike tukunna ya samy waje ya zauna kan kujera, kirga mintunan da yake tunanin zasu kai Yassar din gida, gara yakai ma Waheedah wayar, saiya kirata ko zai samu ta fada mishi dalilin da yasa take son tarwatsa mishi zaman lafiya haka. Nuriyya ce ta fito daga bedroom dinta, dan taji motsin shi, tasan Yassar ya tafi. Kan kujerar ta karasa ta zauna tana jingina jikinta dashi, hannun shi ya zagaya yana rikota, sauqi yake nema koya yake, so yake ta dauke mishi hankali daga tunanin da yake dan bayaso. 4

STORY CONTINUES BELOW


Gefen fuskarta ya sumbata, ta sake narke mishi 1

“Jikina namun ciwo…”

Muryar shi can kasan makoshi yace

“Me kikayi?”

Sake kwanciya tayi a jikinshi, hanyar da zata gujema yin girki take nema 2

“Me zamu ci da dare? Ko musha Tea?”

Tun kafin ta karasa kalmar Tea din yake girgiza mata kai, ana zaune lafiya bazai sha shayi ya kwanta ba, yunwar da yakeji ma tafi karfin shayi.

“Wani abu dai banda shayi”

Shagwabe fuska tayi tana sauke muryarta cike da kissa

“Kamar me? Ka zabi wani abu mai sauqi”

Dakuna fuska AbdulKadir yayi, yanayin na mishi baqunta, shifa sam bai saba fadar abinda zaici ba, dafawa Waheedah takeyi ta kawo mishi

“Ki dafa komai ma, ni ban saba zabar abincin ba, kome kika bani zanci, amman banda shayi”

Numfashi taja tana saukewa

“Ko mu fita muci a waje?”

Kallonta yayi yana kankance mata idanuwan shi

“Saboda me?”

Ya bukata yana jiran jin dalilin da zaisa su fita waje suci abinci. Haka kawai tunani ya watsa shi washegarin auren su da Waheedah.

* 1

“Me zakici in siyo mana?”

Ya bukata bayan tafiyar su Anty, yana kallon yanda take dakuna mishi fuska tana tambayar shi

“Muna da abinci a kitchen, me yasa zaka siyo?”

Kafadu yadan daga mata

“Sai an dafa…”

Ya amsa a taqaice

“Nasani, amman akwai”

Kai ya girgiza

“Amarya bata girki”

Murmushi tai mishi tana mikewa ta nufi kitchen din, binta yayi. Tare sukaita bude-buden abubuwa a kitchen din harta gama dauko wanda take bukata, da wani gari daya gani kamar yaji, sai dai yafi yaji ja yaga ta jiqa a ruwa, sai tumatir na leda, macaroni tayi musu jalof da sauran kajin da aka kawo musu da su Anty basu cinye ba suka saka mata a fridge. Sosai yaci abincin dan ya mishi dadi. 3

*

“Masoyi…”

Nuriyya ta fadi tana riko hannun shi, ganin yayi shiru kamar yana tunani

“Ki soya mana ko dankali saiki mana sauce”

Ya fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi, ranta taji ya baci saboda zaman fere dankalin da zatayi

“Banda dankali fa, sai dai in siyowa zakayi”

Kai ya girgiza mata, bayajin fita sam

“Ki duba kitchen din Wahee… Tana dashi”

Mikewa tayi tana nufar bangaren Waheedah din da tunanin yaushe zata dawo gidan. Dan ita ba zata iya wannan bautar ba sam-sam, rabonta da wani girki harta manta. Gashi ta kula da AbdulKadir din nada mugun cin abinci, kuma tana da tabbacin Waheedah ta lalata shi haka. Kwando ta samu ta kwashi dankalin da take tunanin zai ishe su ta koma nata bangaren. Ta wuce AbdulKadir zaune inda ta same shi, wayar Waheedah ya kira a kashe, hakan yasa shi ajiye tashi yana jin ranshi a jagule. 15

“Masoyi ba zaka zo ka tayani ba? Da yawa fa dankalin…”

Nuriyya ta fadi daga bakin kofar kitchen din kamar zata fashe da kuka, gashi bata iya saka peeler ba, dole sai dai da wuqa. 1

STORY CONTINUES BELOW


“Ban iya ferewa ba nikam”

Yai maganar da iya gaskiyar shi, yakan dami Waheedah da zai tayata aiki in tanayi, amman banda Maggi bata bashi komai, sau daya ta bashi yankan albasa, yajin daya cika mishi ido yasa har ya yanke hannu, bata kara ba, da yayi magana zatace ya rufa mata asiri, kafin azo a kamata taba soja aiki ya yanke hannu. Sai dai yakan miqo mata su cokali ko kwano. Jin Nuriyya bata kara mishi magana ba yasa shi zamewa ya kwanta kan kujerar, ya dora hannun shi saman goshin shi yana lumshe idanuwan shi. 2

Baifi minti biyar ba ya bude idanuwan shi, sai dai me, yanda tunanin Waheedah ya addabeshi da ya rufe idanuwan hakan ma daya bude su. Tashi zaune yayi, tunani bakon abune a tare dashi, babu abinda ya isa ya saka shi tunani haka, Waheedah tasani, bazai iya kwana baisan matsayar matsalarsu ba. Wayar shi ya dauka ya wuce ya dauko mukullin mota tukunna ya dawo yana fadin

“Nuriyya bari in dubo Waheedah, zanyi sallah a hanya…”

Kai ta daga mishi daya saka shi dakuna mata fuska, babu shiri tace

“Tam a dawo lafiya, kayi mata sannu”

Nashi kan ya jinjina mata, ita bata isa tai mishi ba, tana kuma lura da Waheedah na amsa shi da kai baya ce mata komai, amman ranar farko data kwatanta magana yai mata, data gwada yi mishi shiru ma saida ya sauke mata masifarshi har kuka tayi ranar. Akwai abubuwa da yawa da take lura Waheedah kawai take yinsu yana dauka, hakan kuma na mata quna har kasan ranta. Tana jin takun tafiyar shi har ya bace mata. 7

*

Kamar yanda ya fada, a hanys ya tsaya yai sallar magriba, sannan ya karasa gidan Yassar. Ya gwada kiran wayar Waheedah bai samu ba, hakan yasa shi shiga gidan kanshi tsaye hadi dayin sallama. Hauwa ta amsa mishi suna gaisawa, AbdulKadir din ya dora da

“Waheedah fa?”

Dan jim tayi na minti daya, batasan me yake faruwa ba, ba kuma tason shiga koma menene, idan akwai abinda zama da Yassar ya koya mata bai wuce kin shiga abinda babu ruwanta a ciki ba. Dan haka ta nuna mishi hanyar dakin da Waheedah din take ciki, tana ci gaba da hidimar da takeyi ta fito musu da abincin dare. Sauri AbdulKadir yakeyi yana godema Allah da baiga Yassar ba, dan zai iya cewa bazai ga Waheedah din ba. Dakin ya tura ko sallama baiyi ba yana mayarwa ya rufe.

Tsaye yaganta ta goya Ikram tana jijjigata, kallon mamaki take mishi, dan ta dauka ma Fajr ne ya shigo mata daki babu sallama haka, juyowa tayi tai mishi fada taga AbdulKadir a tsaye. Lumshe idanuwanta tayi ta bude su akan shi tana jiran soyayyar shi da takanji ta taso mata duk lokacin da zai bayyana a gabanta, amman shiru, babu abinda takeji banda son kara yin nisa dashi. 10

“Waheedah…”

Ya kira muryar shi na fitowa a karye da ganin nisan da tayi mishi cikin idanuwanta duk da tana tsaye a gaban shi

“Ba zan iya bacci bansan me kike so dani ba…”

Murmushi tayi, kallon ta yake, da gaske murmushi tayi, shi kam ko kadan baiga abin nishadi a yanayin da suke ciki ba

“Da wanne yare kake so in fada maka? Na maka da Hausa, in maka da turanci ko da larabci? Su kadai nasan kana fahimta… Sakina nake so kayi Sadauki, ka fadamun idan akwai abu mai wahala cikin gane hakan”

Tabbas ranar tazo mishi da abubuwa naban mamaki, Waheedah yake kallo yana son ganin ko da gaske matar shi ce a gabanshi, da gaske Waheedahr shi ce da ko murya bata taba daga mishi ba, balle ta tsaya idanuwanta cikin nashi tana gaya mishi magana irin hakan. Ji yake kamar an watsa mishi ruwan sanyi an kunna mishi AC. Jikin shi ba la’asar kawai yai ba, isha’i yayi makararriya. 1

“Waheedah?”

Ya iya furtawa yana kallonta, ganin taki sauke idanuwanta, kuma bata da alamar amsa shi yasaka shi fadin

STORY CONTINUES BELOW


“Nine fa, Waheedah ni ne?” 7

Kai ta jinjina

“Naganka ai… Kaga na nuna alamar bakai bane?”

Wannan karin dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi

“Yaushe kika koyi rashin kunya?” 1

Maganar da yai zaton cikin kanshi yayi ta fito fili, sautin muryar shi na dukan kunnen shi da wani yanayi. Kafadu tadan daga mishi

“Zama da madaukin kanwa…” 7

Waheedah ta fadi tana zama gefen gadon

“Me kike nufi?”

Cewar AbdulKadir cikin bacin rai, kallon shi tayi wannan karin tana ganin yanda yake gab da birkice mata.

“Karka tasar mun da yarinya, Sadauki bazan iya hayaniya ba, dan Allah inba takarda zaka bani ba ka fita…sanda ka shirya bani kasan inda nake”

Kai kawai ya iya jinjinawa, yana juyawa ya bude kofar ya fice daga dakin, a falo ya samu Yassar da alama lokacin ya shigo

“AbdulKadir…”

Ya kira cike da mamaki, ko inda yake AbdulKadir bai kalla ba, hanyar da zata fitar dashi daga dakin kawai yake nema, saboda yanajin yanda wani agogo yake harbawa cikin kanshi yana mishi kashedin saura kiris ya cika, bayaso lokacin da koma meye ya dibar mishi ya cika a cikin mutane, kar a samu matsala. Rabon da ranshi ya baci irin haka harya manta, dan har wani duhu-duhu yake gani. Ganin hakan yasa Yassar kara kiran shi

“AbdulKadir…”

Gani yai ya fice daga dakin, babu shiri Yassar yabi bayanshi, ko takalma bai tsaya ya saka ba. Kafadar shi ya dafa yana juyo dashi

“Magana nake maka”

Ya fadi yana yawata idanuwan shi kan fuskar AbdulKadir din, bakuma yason abinda yake gani shimfide akai.

“A haka zaka shiga mota kai tuqi? Saboda baka da hankali”

Numfashi AbdulKadir ya sauke yana jan hancin shi da yake ji kamar yaji-yaji a ciki, muryar shi can kasan makoshi yace 1

“Me yasa igiyar aure ta shiga tsakanina da Waheedah? Hamma me yasa?”

Runtsa idanuwa Yassar yayi, cikin alamar rarrashi ya ce

“AbdulKadir…”

Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi yana jin kaman zai kama da wuta da yanda jikin shi ya dauki dumi saboda bacin rai.

“Na mareta da safe, bansan ya akai ba Hamma, wallahi ban sani ba, amman cikin idona ta kalla tai mun rashin kunya… Yanzun ta kara… Bansan meya faru ba, bansan me nai mata haka ba….amman a karo na farko inajin igiyar auren da ta hadamu batai mun adalci ba. Da ta bani damar da zan daketa yanda raina yake so da ta dawo hayyacin ta ta fadamun me nai mata sai in san yanda zanyi in gyara…” 7

Dafe kai Yassar yayi, baisan abinda ya kamata yayi ba, a yini daya yana ganin AbdulKadir din na shirin susucewa, baisan me zai faru in aka dauki kwanaki a haka ba, tsintar kanshi yayi da musu addu’ar samun maslaha su duka biyun, dan sun saka shi a tsakiya ta yanda bazai iya zaben bangare ba. Motar shi AbdulKadir ya bude tukunna ya sake juyowa

“Ka fada mata, wallahi bata isa ba…wallahi bata isa ta birkitamun lissafi ina zaune lafiya ba…idan rigima take so Hamma ka fada mata AbdulKadir ne…taga wajen kwanana shisa ta rainani haka…” 1

Da idanuwa yake bin AbdulKadir din da kallo, murmushin da baisan ta inda ya taho ba yana shirin kwace mishi. AbdulKadir na kiran Waheedah bata isa ta birkita mishi tunani ba, amman hauka yake tuburan, tsaye yayi saida yaga yanda AbdulKadir din ya birka mota kamar zai takashi tukunna ya matsa da sauri. Numfashi Yassar ya sauke, yana hango AbdulKadir din ya ziro kai ta window din motar ya kalli maigadin da bai bude mishi kofa da wuri ba, da sauri Yassar ya taka ya karasa kafin ya jibgi yaron mutane a banza. 1

“Dan kanwar uwarka bakaji karar mota bane halan?” 8

AbdulKadir din ya tambaya yana kallon yaron da yake a tsorace, da hannu Yassar yai mishi alamar ya matsa, da kanshi ya bude ma AbdulKadir din mota yana fadin

“Allah ya tsare Samarin Hajja…”

Tsaki AbdulKadir yaja 1

“Idan na zageka a fili yanzun zakace na maka rashin kunya” 9

Wata irin dariya ta kubce ma Yassar din, har AbdulKadir din ya figi mota, Yassar na tsaye ya rike gate din yana kwasar dariya, dakyar ya samu ya shiga cikin gida, har lokacin da murmushi a fuskar shi, a rayuwar shi bai taba hango abinda zai saka AbdulKadir susucewa a yini daya haka ba, har Waheedah din da kanta kuwa…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *