SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 6

SILAR GIDAN AIKI





CHAPTER 6



Bayan Kwana biyu
Mubin Sake sabuwar wulakanci yake a cikin gidan nan, Be dawowa gida da wuri, ko magana akaimai se yaga dama yakeyi, Gaba daya hankalinshi yana wajen Nazeefa, Sonta Kara azabtar Dashi yakeyi, gashi Nazeefa ita sam ta tsaneshi, 2days dinnan da akai harya Dan chanza kamanni saboda ji yake idan be sama Nazeefa a matsayin matarsaba akwai matsala +

Alhaji Sada ne da matarsa suna zaune a falo suna hira akan yanda zasu bullo ma lamarin, Nazeefa ce ta fito sanye da hijab har kasa tazo ta gaishesu tace” zataje ta gaisar da kawarta, Alhaji Binta da kallo yayi Bece komai ba

Hajiya kuwa cewa tayi saikin dawo kuma karki dad’e ba tare da ta kalle inda takeba, Nazeefa tace” OK Nagode

Bayan ta fita Alhaji ya kalle matarsa yace” kinsan wani Abu kuwa? Ta girgiza Kai alamun aa, yace” when ever I look at this Girl sai naji gabana na mugun fadi haka kawai, Hajiya tace” Nima haka sai yasa bana sake Mata fuska, Dan kwata kwata tunda Son yace yanasonta naji na tsaneta, Alhaji yace” waaa Allah ya kyauta wannan ta zama sirikata, Suna cikin maganar ne Maman Haleema ta Kira

Hajiya jikinta na rawa ta amsa waya tasa a loudspeaker, Daga Chan bangeren tace” Hajiya ya naji shuru yanzu kusan 1 week da magana

Bakin Hajiya na rawa tace” yanzuma muke maganar da Alhaji, AI kema kinsan ba fashi Haleema Yar gidatace, tana Ina?

Haleema na kan cinyar uwarta tace” gatanan ta mik’a Mata wayar, Hajiya tace” daughter in law hope kina lafiya?

“Haleema cikin shagwaba tace” mummy Ina lafiya lau sedai I miss you inason ganinki? Hajiya Asmau tace karkidamu zamuzo da Alhaji ma, nan ta wani juya ido kamar tana gabansu tace” Ayyah, Allah yakaimu sannan sukai sallama suka kashe wayan

Bayan sungama ne Hajiya Hadiza mahaifiyar Haleema tai wani irin gud’a taima kanta kirari tace” Saini Hajiya Hadiza, munci dubu sai ceto, Abun da nakeso dole ayishi KO mutun yaga ba daidai ba, Sai ni dakalin Majina a hauni a zame nahau mutun na zauna daram, Haleemane takai hannunta kam bakin mamarta tace” Mum it OK plz,

H.Hadiza tace” my Only daughter wahalar da nasha Dole na jajirce Aci daular nan damu, Haleema tace” KO mum? Tace” ah ki tsaya kigani

Hajiya Hadiza irin Matan nan ne yan duniya Sosai, lungu sako na gari ba inda basu saniba

Haleema ne ta Ciro wayarta ta kira Mubin yana wajen aiki, se rejecting yakeyi, Kuka zata saka mamarta tace” Meye? Tace Uncle Mubin naketa Kira yana rejecting, Murmushi tayi tace” Zaizo hannu karki damu…..wannan kenan

Bangaren Mansur Turaki jiki Alhamdulillah, yana samun sauki Dan anasa ran zuwa gobe za’a sallamesu, Hankalin beloved parent dinshi ya kwanta

*****
Nazeefa fitowarta keda wuya sukaci Karo da Faeez, malama Nazeefa yace” sai Ina? Tace zanje gidan kawatace mundade bamu haduba, Yace” ayyah inaso inyi wani abune a gida dana rakaki, Nazeefa murnushi tayi tace” haba dai faeez bakomai, Nagode, Zata wuce faeez yace inaso muyi magana though maganar bame tsaho bane please n Please Nazeefa kita hakuri da yan gidanmu, kinsan wasu mutanan sai ahankali..

Murmushi tayi tace” Karka damu aikina ne Wata rana Sai Labari, feez yace hakane Allah ya baki miji nagari ma ki huta, ta rufe Fuskarta tace” Ameen nagode yace” bakomai

Tace Bari kaga nai Sauri naje Kar ace nadade, Yace hakane kuma saikin dawo, kama hanya da sauri tayi bata dadeba ta isa gidan kawarta

Kawarta suna shirin fita saiga Nazeefa kamar daga sama, Tace” kawana seyau? Nayi fushi

Nazeefa tace” kiyi hakuri bana samun Time ne, kinsan yanayin aikina, inasu mama? Tace suna ciki, Nazeefa ce taje ta gaisar da Maman kawarta, Sukace sannu baiwar Allah, har yanzu iyayanki basuzo ba? Nazeeefa cikin ladabi da biyayya ta daga Kai tace” Eh, matan gidan suka tausayawa Nazeefa Sosai, sukai Mata addu’a Allah ya bayyana iyayanta ya kuma kawo mata miji nagari…Tace Ameen

Kawarta tace zoki rakani Wlhi asibiti zamuje da aunty na zamuje Mu gaisar da yarinyar hajiyar datake ma aiki, Batada lafiya

Nazeefa tace OK muje kawata

Suna tafe suna hira har suka sama Napep din dazai karasa dasu hospital din, A cikin na pepep dinne Kawarta tace” ya bayanin school kinsamu Jami’ar kuwa? Nazeefa ta taba baki tace” hmm kina ganin zasu barnine lalla kuwa, Kawarta tace karki damu Zan baki wani addu’a kidingayi inshaa Allah, Allah zai daukaki akansu, Nazeefa tace aiko danaji dadi nan dai suketa hirar Samari Dama yan Mata aka hadu yawanci se an Dana…Lol basu dade ba suka Sauka a babban Asibitin *GIWA HOSPITAL*

Kallo daya zakaima asibitin kasan Yayan manya ake admitting a hospital din, Sake baki Nazeefa tayi Dan hospital ba karya ya hadu, aranta tace” Ayyah na ni watace karatun doctor zanyi nadinga temakawa yan uwana Mata, Koda suka shiga Tara tagani yan daidai shekaru sanye da kayan doctors da nurses abun yai bala’in burgeta aranta tace dama nine

Ward ward suka shiga Dan gaisar da sauran marasa lafiya

Wani ward suka gani private room a kulle, har kawarta tayi gaba Nazeefa ta bude ward din Ido hudu Nazeefa sukai da wani mutumi dake kwance a gadon dakin, Kallo cikin ido sukai sukai, M.Turaki kura mata ido yayi like he’s re-calling Something habaaaaa

Kankame bed din yayi jikinshi ya Fara rawa gashi ba kowa a dakin, Da karfi Yace Aljanna get out from here

Nazeefa Ma tana ganinshi Tace” Aljani ta fita hospital din a guje,

Kawarta tai gaba batasan wainar da ake toyawaba………..Nazeefa gudu takeyi bata tsaya ko inaba sai bakin gate, aranta tana cewa wani irin aljanine wannan? Kawartace ta juyu Dan ce mata ga room din da zamu shiga nan, taga wayam. She’s surprise ko ta shiga wani room ne tadan lallek’a but she couldn’t find her, Mamaki taji sosai then sai ta koma Bakin gate saiga Nazeefa Rik’e da kugu tana girgiza Kai, Kawartace tace” ya haka? Kizo Mu shiga mana +

Nazeefa ta girgiza Kai tace” just go bazan Iya shiga ba naga aljani, Kawartace ta dafa ta tace” meye haka? aljani a asibiti? Taya ya kika ganshi?

Nazeefa tace” room din da muka leka a nan naganshi, kawarta tace” please banason wasa ni ya akai banganshiba KO kin fini idone?

Nazeefa binta da kallo tayi tace” plz kawata kedai ki Shiga I’ll wait for you..Kawarta me Suna Amira bata matsa mataba Dan tasan halin Nazeefa idan ta kafe a Abu kome zakace bazata yardaba, Dan haka Amira ta shiga hospital din cike da Tinani……..

Bangaren Mansur Turaki kuwa, tunda suka hada ido jikinshi rawa yakeyi sosai hatta gadon da yake shaking yakeyi, Abokinshine Abdallah ya murda Kofar ya Shugo Kara tsurewa yayi jikinshi na rawa, Da sauri Abdallah yaje kusa dashi yana M.T meya faru

Kallonshi yayi idonshi yai ja bece komai ba, Abdallah ya girgiza shi yace” My Frnd menene please ko jikin ne

Dakyar ya Iya bude bakinshi yace” That aljanar nan? Abdallah yace eh meye faru? M.T Yace” ta..taaaa… Sai kuma yayi shuru yana kallon Abdallah

Abdallah tausayin Mansur yayi yace” ta mene? Kasa magana yayi saidai yai nuni da Kofa, Wai gawa Abdallah yayi yace kagantane?

Mansur cikin sleeping eyes dinshi ya daga Kai alamun eh

What Abdallah yace” you mean har nan ta biyoka? Ya daga Kai alamaun eh! Abdallah yace” are you sure kodai mutun ce? mansur Yace ah…ah…

Ba mutun bane Abokina aljanace Da farin hijab na ganta, Abdallah ne yace” OK please karka daga hankalinka har Su mummy Su fahimta akwai matsala, kaga idan kana cikin damuwa sunfi kowa dag’a hankalinsu gashi baba yace” sunada Meeting da president gobe kaga idan har yaga alamun jikinka ba sauki bazaijeba and zuwan meeting dinshi kaga zai kawo cigaban mutane da yawa

Mansur yace” to shikkenan amma dai zaka zauna dani kar ta K’ara zuwa KO?

Murmushu Abdallah yayi yana mamakin sauyawan Mansur, Danshi strong guy ne lalle kam ba karamin abun yaga niba daya chanza shi, Abdallah yace” inanan tare dakai aminina har Seka sama Sauki yace” OK Nagode Suna cikin Hirane Phone din Mansur turaki yai ringing, Suna yagani yai appearing da _Yar commissioner_ danna rejecting tayi, Kara Kira tayi ze sake dannawa kenan, Abdallah ya Rik’e hannunshi yace” pick please, girgiza Kai yayi alamun a’a, Yasan halin gogan nasa shima idan yace Abu bai chanzawa, Dan Haka Abdallah ne yai picking yace” ranki ya Dad’e! Cikin shagwaba da yanga tace” where is the owner of the phone kabashi mana!

Abdallah yace” he can’t talk yanzu haka yana asibiti beda lafia..What tace cikin rudewa! Yana wani asibitin please?

Kafin Abdallah yai magana, Mansur ya kwace wayan yasa a airplane mode, tsaki yayi yace I hate nonsense wallahi, Abdallah murmushi yayi yace haba Abokina meye laifin Yasmin? Girl dinfa nasonka sosai kuma ta hadu, intact kundace da juna fa!

Mansur yace” abokina ko sonta zai kashenine I can’t marry her she’s not my type, Abdallah yafi sanin halin abokinsa sarai sai yace” bece Komai ba Yace” Allah yai mana zabi na alheri, Yace Ameeen

Mansur Turaki yace ya Girl dinka fa? Munkusan shan biki ko? Abdallah yace” AI sekaji garau sannan ma za’a Fara komai nan dai suketa hirarsu, Kana ganinsu kasan aminan junane!

Nazeefa kuwa tsaye take a bakin gate samari sai parking sukeyi suna yi Mata magana amma KO kulasu batayi, gabanta in banda dukan uku uku ba abun da yakeyi, ji takeyi kamar wani abu zai sameta gaba daya ta kasa sukuni!

Amira ce ta Fito ta dafa ta tace” Me tsoron Aljani muje KO? Murmushi Nazeefa tayi tace OK let’s go…tafiya kadan suka sama Napep Suna tafe suna hira, Amira tace” Nazeefa wai waye gwanin Namu?

Tai kamar batajiba

Amira ta Kara furtawa for the 2nd time tace wai waye gwanin? Nazeefa tace ke kincika damu Wallahi ni ta wani gwani nake ko nai ido hudu da iyayena?

Amira tace Hakane Amira tace hakane, Allah ya kawo mana nagarin muma muji Dadi,

Nazeefa ce ta kalleta tace” ke ai kinji dadinki akwai mazan da zasuzo nemanki, nifa da ake guduna Yar aiki, yar aiki, Amira ta dafata tace” ai ba anan takeba Sai kiga kinfini samun miji, Nazeefa tace” Kawata kenan Allah ya kawo mana nagarin shine kawai Tace Amen

Ahaka Suna hira har suka Isa gidan Su Amira, koda ta shiga bata dadeba ta fito tayi gida
Ahaka Nazeefa da Amira suke hira har suka Isa gidan Su Amira, koda ta shiga bata dadeba ta fito tace gida zata cos Hajiya tace Mata karta dade, Amira ce ta rako ta har kofar gida sukai Sallama

Tana isa gida mubin ne ya kafeta da ido kamar zai cinyeta, yace” Ina kikaje? Ko kallon inda yake bataiba tace” naje gidan Frnd dinane, Hada rai yayi Dan wani bugu da kirjinshi yakeyi, aranshi yace” yanzu duk angama kalleta, Tsaki yayi yace i know what to do

******
Bayan Kwana biyu Mansur Turaki Alhamdulillah yaji sauk’i amma duk baccin da zaiyi ko na 30mins ne seyai mafarkin Aljanarsa (Nazeefa) wai gasunan cikin garden suna soyayya, Sunsa kaya iri daya, idan ya tashi yai ta smiling har rannan hajiyarshi ta tambayeshi lafiya kuwa? Sedai yace lafiya lau mum cos yana enjoying dream dinshi, Besan Mutun bane But yana rokan Allah ya Kara hadashi da ita cos yawan mafarkinta da yakeyi ahankali Sonta na Kara shigarsa……..

******
Bayan Wata daya

Mubin son Nazeefa se karuwa yakeyi, Dan shawarta yakeji sosai, Yasha kawo Mata hari, Amma baya samun sa’a cos tunda yasha furta Mata yana sonta ta’qi amincewa ya daura aniyar sai ya bata mata rayuwa kila ta soshi Dan a tinaninshi hakane way out!

Akwana a tashi ba wuya yau Wata daya da sati biyu da Hajiya Hadiza sukai maganar auran yaransu, amma Su hajiya suna neman Saba mata Dan haka tadau aniyar yau komun dare sai taje garin kaduna sedai duk bura uban da za’ai an Dade ba’ai ba

Misalin karfe 4.00Pm suka sauka a garin Kaduna, direct gidan Alhaji Sada ta wuce, Tana shiga Su hajiya suka hangota ta window, Innalillahi wa Inna ilahir rajiun suketa nanatawa

Lokacin Nazeefa kuwa ta tafi cefane kasuwa, Dawowa tayi taci Karo da mutane a tsakar gida

Haleema ce da uwarta hajiya Hadiza, gabantane yai mugun fadi Dan ta tsorata datagansu innalillahi wa Inna ilaihir rajiun tace a zuciyarta sannan ta kallesu, Sannu tace musu sannan ta shige falo, a tsaye taga Hajiya da Alhaji suna tattaunawa, Wani harara hajiya ta balla mata seda ta kusan fadi tai maza ta shige kitchen

Haleemace tace” Mum kinga yarinyar da mubin yakeso ko? Hajiya Hadiza Tai shewa tace” yar nan, Yaga jan fata ba doleba kuma kwalelensa,

Wai Ina mutanan gidan nan sukene? inji Hadiza, Hajiyane jikinka na rawa tace” Hajiya Hadiza ki Shugo mana, Hajiya Hadiza tace” yau ba zama nazo ba balle in Shugo dakin

Yau za’ayita ta kare, yau sena tara muku jama’a a unguwar nan kowa yasan ku waye tunda munyi magana daku kun maidani bansan meke nakeyiba, kun manta komai naku A tafin hannuna yake? Ni zaku maida Yar iska, Sannan tai wani Shu’umin dariya

Hajiya Asma’u da sauri tazo ta rufe Mata baki tace Dan Allah ki rufa mana asiri yanzu, munyimai magana yaqi amincewa, Hajiya Hadiza tace” aikin banza ni Ina ruwana, kunsan abunda Zan Iya ai

Tai kamar Zata fita, Da Alhaji da hajiya da gudu sukasha gabanta suna bata hakuri, akan duk abunda takeso yanzu shi za’ai

Ahankali tai magana tace” kun manta da boka gobe da nisa ne? Muje yai mana aiki akan mubin mana, If not rayuwarku sai kowa yaji Nidai ba ruwana

Nan take Alhaji ya amince, Hajiya kuma taqi amincewa, tace Sam akan soyayya bazata taba Kai d’anta wajen boka ba

Nan suka fara jayayya

Duk Abunda Akeyi Nazeefa na kitchen batasan wainar da ake toyawaba, balle su faeez da suke school

Hajiya Hadiza dataga mamansu mubin taqi amincewa tace” zanje gidan kanwata na kwana zuwa gobe Ku yanke shawara, If not Zakusha mamakina, Haleema na tsaye sai cin chigum takeyi ita ko a jikinta dukdai yanda za’ai ita ba damuwarta bane adai kwato Mata Mubin Dan she’s madly in love with him….

Tisa keyar Y’arta tayi sukabar gidan, Hajiya da Alhaji sune tsaye, Hajiya tace bazaiyuba, Dana bazai aura Yar aiki ba balle ya aura yar Tijararriyar Matar nan (Hadiza) Alhajine ya Kama hannunta sukai daki yana kwantar Mata da hankali

   Suna fita Hajiya Hadiza motar ta ta bude suka Shiga, Tana driving Haleema kuwa sai Chating takeyi

       Cikin darene Alhaji ya kasa sukuni, hajiya na bacci ya tada ita yace” ki tashi kinsan yau ne last day dinmu muka bari maganar nan yakai gobe kuwa Kinsan zamusha mamaki fa

Hajiyace ta bishi da ido kamar lebenta nason furta wani Abu kuma saita fasa, Alhaji yaci gaba da magana yace” kawai ki kabari mukaishi gun malami asasai Son Haleema if not Nigeria nan seta mana kadan, Kinsan Halin da muka shiga Shekarun baya KO?

Wani dogon nunfashi taja, tace” Alhaji gani nayi hakan baidace ba danmu fa na cikinmu zamukai wajen malami? Tsareta da ido yayi yace” nasani for now dole muyi inyaso daga baya sai muje a warware Sihiri kinga bata da bakin magana tunda ancika Mata burinta

Hajiya tadanshi Sanyi a zuciyarta tace” na Amince da hakan,  Sannan ya rungumeta sukai baccinsu

Safiya nayi suka kintsa suna jirar isowar Hajiya Hadiza, Aikuwa 8:00pm nayi dot saigata ta sun Shugo gidan da y’arta Haleema, da gadara suka shugo gidan

Hajiya Hadiza tace” kunsan ba zama nazo yiba Ina muka tsaya Sukace Hakanan zamuyi mun amince, Wani Shegen dariya tayi da seda yan hanjin Hajiya Asma’u ya kad’a aranta dai tace Hmmmm nima ba kwanwar lasa bace muje zuwa!

    Hajiya Hadiza ta kalla yarta tace” ki shiga Ki zauna zamu fita, Aranta dadi taji tace” OK Ma sai kundawo

  Hajiya da Alhaji da H.Hadiza suka Kama hanya Sai waken Boka…Allah ya kyauta

Mubin na kwance a daki, yana mafarkin Nazeefa besan ma drama din da akeyiba

Haleema kuwa Wani Sallama tayi direct dakin mubin ta wuce ta murda kofan daki but unfortunately is locked..lol

      Falo ta dawo, Ta zaune ta Fara kiran yar Aiki…Yar Aiki….Yar aiki….
Nazeefa najinta tai banza da ita kamar ba ita ake kiraba, Haleema taji haushi har kitchen ta biyota tace” Dan ubanki bakiji Ina kiranki bane Yar talakawa!  Abun ya batama Nazeefa rai tace” yes yar talakawan Kuma Dan uwanki ya manne mawa ba!

Haleema tace Wlhi baki isaba mubin na wane ni kadai tana magana tana buga kofar kitchen da karfi da sedayai sanadiyyar tashin mubin daga bacci

Ahankali mubin ya bude ido yaji hayaniya bude kofarshi Yayi ya fito ya labe duk cikinsu ba Wanda yasan ma ya fito

    Haleema ta Kara da cewa, Yar matsiyata kawai, se kinbar gidan nan indai aka auroni, Nazeefa tace aikin banza   akan mubin kike wannan haukar, to bari kiji da banason Mubin amma yanzu naji Ina son shi, Ina kaunarshi inason hada shimfida dashi kuma ya zamo uban yayana, Mubin jinin jikinane, inke Yar iskace Toni na fiki iskanci

Mubin na labe yaji wani farin ciki kamar zaiyi ihu, aranshi yace” anzo Wajen

Murna yayi sosai yaji wani farin ciki ya ziyarshi zuciyarshi, ji yai kamar ansamai ruwan sanyi Dan har murmushi yakeyi kamar wani maye yaga abinci😂

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *