ABDULKADIR CHAPTER 7

ABDULKADIR





CHAPTER 7





Tana kitchen din har aka kira sallar Magriba, bata mike ba saida ta karasa yanka dankalin tukunna, wanke shi tayi ta tace a kwando, tana ganin kamar yankan yayi girma, amman ta riga ta gaji, ko bata gaji bama ba zata sake tsayawa yankawa ba, ranta a bace take jin shi. Gas ta kunna ta dora kasko ta zuba mai a ciki, tunanin ta barbadama dankalin gishiri bai zo mata ba, man ma ko dumi baiyi ba, balle yayi zafi, ta dibi rabin dankalin ta zuba a ciki tukunna ta fice daga kitchen din. Dakinta ta wuce tana shigewa bandaki ta dauro alwala ta fito, sallah ta gabatar a nutse, bata tsaya addu’a ba ta tashi ta nufi kitchen din dan ganin halin da dankalin ta yake ciki.

Danqare ta same shi, kasancewar man da yasha yayi luntsum, haka ta cigaba da cakuda shi, duk ya kakkarye ya dame cikin man, yana kara jagula mata lissafi gabaki daya. Batajin a cikin abubuwan da mata sukeyi na zaman aure akwai wanda yakai girki bata lokaci da wahala. Bata taba tunanin suyar dankalin zatai mata wannan rashin mutuncin ba, barin shi tayi yadan karayi, tukunna ta kwashe, bata jira man ya tsane ba ta juye a wani kwano da ta dauko. Sauran dankalin ta zuba, tana komawa falo ta zauna. Da fitilar wayarta take ta amfani, kasancewar har lokacin basu dawo da wuta ba. Ga AbdulKadir ya jima, balle yazo ya kunna musu generator, ko kallo tayi ta rage zafi. 6

Shima sauran dankalin haka taita juya shi duk ya dagargaje mata, ta kwashe tana kallon yanda a ido ma baiyi kyawun gani ba. Gashi sai tayi wata sauce kuma. Badan tana tsoron fadan AbdulKadir din ba, kwai zata soya su hada dashi. Sauran kayan miyar da ta dauko kitchen din Waheedah ta fito dashi ta juye a tukunya tana dorawa kan gas. Tukunna ta dauko albasa ta fara yankawa, ga yajin albasar daya cika mata ido, ga kayan miyar daya fara kamawa, banda tsakinta bakajin komai na tashi a kitchen din, sai kuma kauri. Albasar ta zuba ciki, tukunna ta zuba mai wajen ludayi takwas, dan kusan na kaskon da tayi suyane ta kusa juyewa, cakudawa tayi, taga kamar ta mata yawa, ta fara saka ludayi tana rage man. 4

Ganin miyar na kara konewa yasa ta kashe gas din

“Wanne irin bala’i ne wannan?” 3

Tai maganar kamar zata saka kuka, tunawar da tayi bata saka maggi ba, guda takwas ta dibo ta bare, dandanqa shi tayi ta zuba a ciki tana cakudawa, sai taga kamar miyar ta kara baqi. Tabe baki tayi, dan kanta harya fara daukar alamar ciwo. Sanda ta fito daga kitchen din ana Isha’i, tana da alwalar ta, hakan yasa ta wuce daki, tana idarwa ta fara kiran lambar AbdulKadir, sau hudu tana kira bai daga ba. Na biyar dinne ta ji ringing din wayar a cikin gidan ta bangarenta. Hakan yasa ta fito tana dora murmushi a fuskarta 1

“Sannu da zuwa…”

Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata yana zama kan kujera, wayar shi ya ajiye a gefe.

“In zubo mana abinci?”

Da kai ya sake amsata, ta wuce kitchen din, plate ta samu ta juye dankalin a ciki, tana samun karamun wajen zuba miya ta zuba, ta hado ta fito, a kan kafet ta ajiye. Tana kallon AbdulKadir da gabaki daya hankalin shi ba’a kanta yake ba. Kafarshi ta taba, ya sauke wani numfashi mai nauyi. Waheedah ba zata saka shi kin cin abinci ba, bata isa ta daga mishi hankali yana zaune lafiya ba. 1

“Meye wannan Nuriyya?”

Ya bukata yana kallon dankalin da ya koma kamar dambu a cikin plate. Zuciyarta taji ta doka a cikin kirjinta, nan take idanuwanta suka ciko da hawaye. Ranshi AbdulKadir yaji ya kara baci, inda Waheedah ce ya shigo tana kallon shi zata gane halin da yake ciki, kuma kome zaice mata ba zata nuna ranta ya baci ba dan tasan nashi a bace yake, balle tayi shirin mishi kuka. 7

“Bana son Kukan banza da bashida dalili, tambayarki nayi, ki bani amsa, meye wannan?”

Hawayen take kokarin dannewa, amman sosai suke mata barazana. Muryarta can kasan makoshi tace

STORY CONTINUES BELOW


“Wallahi bansan ya akayi yai haka ba nima…”

Kai AbdulKadir ya jinjina, yasan ana samun akasi wajen girki, a ranakun da ranshi ba a bace yake ba, zai mata uzuri da cewar dan Adam baya wuce kuskure, amman yau haushin shi yake son hucewa akan kowa ya samu, ita kadai ce kuma a gaban shi.

“Hannu zan saka?”

Ya sake bukata yana kankance mata ido, kai ta girgiza mishi da sauri, tana mikewa ta wuce kitchen din, sai da ta matse kwallar da ta taru cikin idanuwanta, tukunna ta dauko cokula guda biyu ta dawo, mika mishi tayi ya karba, yana sakawa cikin miyar daya rasa gane wace iri ce, ga man da yake kwance a miyar zai iya ganin fuskar shi in ya leqa cikinta. 1

“Me yasa baki saka mana nama ba? Wacce irin miya ce wannan?”

AbdulKadir ya karasa tambayar yana jujjuya cokalin shi cikin miyar, kafin Nuriyya ta amsa ya sake fadin

“Ni sauce nace kiyi mana, ita Waheedah takeyi idan ta soya mana dankali”

Yau ne karo na farko da Nuriyya taji takaicin rashin iya girki a rayuwarta, dan shine karo na biyu a rana daya da AbdulKadir ya hada girkin ta dana Waheedah, kishin da takeji kuwa kirjinta har zafi yake mata. Shikuwa sunan Waheedah daya fadi yasa ranshi kara baci, babu shiri ya dibo miyar ya zuba akan dankalin daga gefe yana cakudashi kamar shinkafa ya dibo da cokalin yakai baki, yana jin kaurin daya cika mishi hanci daga cikin bakin nashi. Hadiyewa yayi batare daya tauna ba, dakyar ya iya cokali hudu, yunwar da yake tunanin yanaji ya nemeta ya rasa. Mikewa yayi kawai, Nuriyya na binshi da ido harya fice daga falon.

Tsoron kar yai mata fada yasa bata tambaye shi inda zaije ba. Ita kanta a dole takecin dankalin, sai da taji cikinta ya cika tukunna ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, ta dawo ta zauna, jin har lokacin AbdulKadir bai tashi generator yasa tayi tunanin ko ta kira wayar shi, sai taganta ajiye akan kujera. Salama ta sakama ranta taci gaba da danne-danne wayar da rashin abin kallo ya sakata. Dan ita ba ma’abociyar chatting bace ba, daman karatu ne, nan tafi kwarewa, to duk litattafan da take bi, ba’a dora sabon cigaba ba.

AbdulKadir kuwa waje ya fita yana samun waje kan matattakalar shiga gidan ya zauna. Yana kallon farin watan da ya haske harabar gidan, yana kuma daukar tunanin shi ya watsa satin su na biyu da tarewa a gidan shi da Waheedah.

*

Tunda sukaje gida ta samo fina-finai wajen Nabila, data gama aiki bata komai sai kallo, daya tambayeta wanne irin film ne tace mishi Korean, jiya daya farka yaganta tana kallo, da kan shi ya kashe system din, sai da ya zare mata ido da gaske tukunna ta hakura ta kwanta, da ta shagwabe fuska zatai mishi kuka. Yau ma aikin kallon takeyi da gab yake da haramta shi saiya bar gidan, tunda ta rage samun lokacin shi. Hidimar shi ya gama yi ya fita sallar isha’i. Fajr na dakin shi yana bacci, dan shi da anyi Magriba cikin shi ya dauka sai bacci, inba yanajin rigima ba.

A matattakalar shiga gidan ya sameta zaune, jikinta sanye da rigar sanyin shi da ba hannun bane kawai yai mata yawa, har da rigar gabaki daya, sai dai Waheedah ce, haka take mishi, sai dai yaga rigunan shi a jikinta, inyai magana zata ce kamshin turarukan shi take so, kuma gasu a ajiye. Yakan ce ta fesa ta ajiye mishi rigar shi, dariya takeyi kawai

“Kamshin ai ya hadu da naka….”

Shine amsarta lokutta da yawa. Murmushi kawai yakanyi, a duniyar shi gabaki daya, ita kadai take mishi abinda take so, ita kadai yake cewa tayi abu ta maqale mishi kafada alamar ba zatayi ba, kuma ya hakura, wani lokacin ma kai kawai zata girgiza, idanuwanta na cikowa da hawaye, sai yaji gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi.

“Me kike a waje?”

Ya bukata yana karasowa ya zauna kusa da ita. Hancinta da sanyi ya cika ta ja, tukunna ta amsa shi

STORY CONTINUES BELOW


“Wata nake kallo”

Murmushi ya kwace mishi mai sauti

“Wata?”

Ya maimaita cike da alamar tambaya, yana kallon ta, kai ta daga mishi. Gabaki daya film din da ta gama kallo ya tafi da imaninta, duk wani abu da akai a film din taji tana sonyi itama, balle kuma kalar soyayyar da aka zuba. Sai dai akwai haukan da ita kanta tasan ba zata fara tunkarar AbdulKadir da shi ba. Shisa ta fito ta kalli watan abinta.

“Me yasa zaki fito kallon wata?”

Ya kara tambaya har lokacin yana kallon ta, shagwabe fuska tayi

“Ba’a magana fa Sadauki, shiru akeyi a kalli kyan watan… Da yan….Subhanallah….”

Waheedah ta karashe tana mikewa babu shiri tana fara zazzage skirt din dake jikinta tana dorawa da

“Cinnaka… Hamma cinnaka wallahi…”

Skirt din take zazzagewa tana murza cinyarta da take da tabbacin cizon daya manna mata ya wuce biyu. AbdulKadir take kallo da yake dariya harda rike ciki

“Ba abin dariya bane, da gaske cinnaka ne…”

Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata saboda dariyar da yake, dakyar ya iya cewa

“Sannu… Mu karasa kallon watan…”

Kafin ya rufe baki ta fara girgiza mishi kai, tana murza cinyarta da azaba ta isheta

“Akwai dalilin da yasa bama yin wasu abubuwan a najeriya…”

Wata dariyar AbdulKadir yaji ta sake kubce mishi

“Mu koma daki…”

Waheedah ta fadi tana wucewa, yabi bayanta, kasa ta zauna kan kafet tana cigaba da murza cinyarta, AbdulKadir din ya zauna kusa da ita, hadi da riko hannunta, da murmushi a fuskar shi har lokacin, yanzun ya tabbatar da abinda tagani a film ne taso gwadawa, saboda bata da hankali

“Ki daina murzawa…”

Hannunta ta kwace, ya sake riko shi, yana saka karfi wannan karin, skirt din ya kama da dayan hannun shi ya daga sama, yana duba inda cinnakan ya cijeta, wajen haryayi burdi, abinka da farar fata, har yayi ja. Duk da tausayinta da yaji bai hana shi cewa

“Baki da hankali Waheedah…”

Shiru tadanyi, tana tunanin abinda tayi, kafin dariya ta kubce mata, tana saka AbdulKadir din jin wata sabuwar dariyar shima, dariya suke kamar babu wani abu da zai iya taba farin cikin su.

*

Yanzun ma dariyar yake yi da sautin ta ya dawo dashi hayyacin shi, yana saka wani abu matsewa a kirjin shi, dariyar na dishe mishi, kan shi ya dafe da hannuwa biyu

“Waheedah….Waheedah karki mun haka dan Allah… Ki rufamun asiri…” 1

Yake fadi shi kadai. Bai san iya lokacin daya dauka zaune a wajen ba, kafin sauron da yake ta girbar shi yasa shi mikewa ya koma cikin gidan, dakin Nuriyya ya wuce, ya sameta a kwance, da alamar tayi bacci, dan ta kunna fitilar wayarta ta dora akan drawer din gefen gadon. Kayan jikin shi ya rage ya wuce bandakin yana watsa ruwa. Fitowa yayi ya saka gajeran wando ya zagaya ta gefen gadon ya hau yana kwanciya. Baifi mintina goma ba yaja karamin tsaki ya sauko, wayar Nuriyya ya dauka ya haska har zuwa falon ya dauki tashi wayar.

Anan ya tsaya yana kiran lambar Waheedah, ta kuwa shiga, da alama ta kunna wayar, dagawa tayi, ya numfasa zai magana ta kashe wayar a kunnen shi, tana saka shi dawo da fuskar wayar ya kalla dan ya tabbatar da kashe mishi waya tayi a kunne. Wata irin dariya da bata da alaka da nishadi yayi, yana sake dannawa ya kirata, a kashe yaji wayar. Wata dariyar ya sake yi

STORY CONTINUES BELOW


“Zaman lafiya ne bakya so Waheedah, tashin hankali kike nema dani shisa kika kashemun waya a kunne”

Ya fadi yana wucewa daki ya koma ya kwanta, juyi kawai yake yana duba agogon wayar da yaga kamar baya tafiya dai-dai, dan yaqi yin sauri. Gari yake so ya waye, asuba a gidan Yassar zatai mishi, zaiji dalilin da zai sa ta kashe mishi waya a kunne, bayan tafi kowa sanin bayaso.

*

Bai samu bacci ba sai bayan sallar Asuba, dan yanda yaga rana haka yaga dare, da safen ma ciwon kai ne ya saka shi kwanciya. Tunda Waheedah na gidan Yassar babu inda zataje, in yayi baccin ya tashi sai yaje ya sauke mata. Ba zaice ga abinda yake faruwa ba, dan bacci yake daya kwana biyu bai samu irin shi ba, yaji kamar ana taba shi, wata irin damqa ya kaima hannun Nuriyya da yasata sakin ihu, idanuwan shi da suke cike da bacci ya sauke akan ta, tukunna ya saki hannunta da yake rike dashi.

“Masoyi da ka karyani…”

Ta fadi a shagwabe, kan shi yakeji kamar ana buga ganga a ciki saboda ciwon da yake yi

“Ki kira sunana in zaki tasheni daga bacci, karki tabani…”

Kai taje daga mishi tana murza hannunta

“Zan fita ne daman…”

Cike da rashin fahimta yake kallonta, hakan yasa ta dorawa da

“Nace maka zanje wankin kai, tun shekaranjiya…”

Kai ya jinjina mata, dan ya manta sunyi maganar, idanuwan shi ya fara lumshewa da alamun shirin komawa bacci tace

“Masoyi….”

Batare daya bude idanuwan nashi ba ya amsa ta da fadin

“Nuriyya ki duba wallet dina ki dauki kudi, dan Allah kibarni nikam”

Turo labbanta tayi tunda ba ganinta yake ba, ya bata kudi tun randa tai maganar, hakan dai ba zai hanata sake dauka ba, tunda ya manta.

“Daman in dauki motar ka tunda bacci kake, ko zaka fita?”

Ko kadan bayason dogon surutu, tsoro ya hana Waheedah koyon tuqi tun lokacin daya siyi mota, ba yanda baiyi daya koya mata ba, ya gaji ya kyaleta, Nuriyya kuwa da kanta ta nuna mishi tana son koya, ko sati biyu basu hada ba ta fara hawa babban titi, karambanin ta yana burgeshi lokutta da dama. Zai fita da motar shi, indai Nuriyya ce yasan zata bata lokaci kafin ta dawo, amman bayason yin surutun shisa yace mata

“Allah ya tsare, ki karamun mai… Karki dade kuma”

Murmushi tayi, sai da ta sumbaci fuskar shi tukunna ta zagaya gefen shi tana daukar wallet din shi da take ajiye kan gado, kudin ciki ta kirga taga dubu bakwai ne, duka ta kwashe tunda yace ta kara zuba mishi mai. Mayafinta ta dauka ta saka, tukunna ta dauki mukullin motar ta fice. Ranta kal take jin shi, zata fito a matar hamshaqin da take jinta, tun daga shigar jikinta, da leshi ne daya sha dinkin doguwar riga zuwa takalman kafarta da mayafinta, tasan ta wuce rainin kowa. Gata matar soja, wanda taga dama zata taka babu abinda zai faru. 5

Haka ta shiga gidan man da ta fara samu a hanya, sosai ta kosa saboda layin da yake gidan man a ranar kamar anayin wata hidimar, duk da watan azumi ya gabato, amman sauran wajen kwanaki takwas, ballantana ace siyayyar azumi ce ta saka garin cunkushewa, danne danne waya takeyi a cikin motar tana hade rai ita kadai, ta sauke gilasan motar daman yanda za’a fi hangota, tana kuma jin dadin yanda duk wanda ya kalleta saiya kara kallon ta. Man dubu uku ta zuba, ta ja motar kenan da nufin fita daga gidan man wayarta ta fara ruri, kawarta ce da sukayi FCE tare. Bata kashe motar ba ta tsaya amsa wayar, barkewa sukayi da labari, tana fada mata auren wata bazawarar kawar su da za’ayi da kuma kalar shagulgulan da suka tanada.

Honking taji an isheta dashi, taja karamin tsaki hadi da zuro kai ta window din motar, har lokacin bata sauke wayar daga kunnenta ba, a wulakance tace

STORY CONTINUES BELOW


“Idan sauri kakeyi, kayi juya ka fita ta inda ka shigo mana”

Shima mutumin da yake cikin motar shi qirar golf leqo da kai yayi

“Bangane in juya in fita ba, Hajiya bakiga layin da yake bayana bane? Ke ai yakamata kiyi gaba saiki amsa wayar… Wannan ai rashin tunani ne…”

Bude baki Nuriyya tayi tana kallon shi cike da mamakin kalaman shi da take dauka a matsayin tsantsar rainin hankali, tunda can ma ba hakuri gareta ba, dan ko matar babanta sai da tace ta dauka aure zai sa ta rage fada, amman hausawa kan ce mai hali baya barin halin shi.

“Asma zan kiraki, ina zuwa…”

Ta karasa tana sauke wayar daga kunnenta ta bude murfin motar ta fito, zuwa lokacin hankalin mutane da yawa ya fara dawowa kan su, musamman zagin da Nuriyya ta fara sirfawa mutumin, ganin kalar motar da ya fito daga ciki da kuma yadin jikin shi, sam bata kula da su biyu bane, dayan babban mutum ne, zai kai shekaru arba’in da biyar ko da doriya ma. Jikin shi sanye da shigar kananun kaya, rigar mai dogon hannu. Fuskar shi manne da farin gilashi.

“Hajiya daga cewa ki fita zaki fara zagin shi? Kanki daya kuwa”

A hasale Nuriyya ta mayar da hankalinta kan shi

“Ko zaka rama mishi ne?”

Jinjina kai mutumin yayi, yana rufe murfin motar ya zagaya a fusace, hakan yasa dayan abokin tafiyar tashi rike shi, da sauran mutane ma, harda ma’aikatan gidan man da suke ta ba Nuriyya hakuri ana so ta wuce ta tafi, amman ina, jinta take matar soja ce ita, sojan ma AbdulKadir, tana da tabbacin babu wanda ya isa ya tabata. Mutumin da ake rikewa kuwa fadi yake

“Alhaji Mannir ka sakeni in ci uban yarinyar nan…”

Kafin wani ya kula, hannun Nuriyya ya tashi sama ta kuwa yi nasarar zira shi tana dauke mutumin nan da marin da yasa wajen yin shiru na mintuna, kafin a taru a shiga tsakani. Huci kawai take tana girgije-girgije. Wasu mata da suma sukazo shan mai suka fito daga motar su suna kama Nuriyya din suka janyeta gefe, kuka ta fashe dashi tana fadin

“Dan sun gani mace shine zasuci mun mutunci, wallahi sai na kira mijina… Dan bazan yarda ba”

Daga gefe mutumin da har lokacin bai daina kokarin kwacewa ba yace

“Ki kira shi fa, dan yau ina son ganin uban da ya tsaya miki a fadin garin Kano da ketaren ta…”

Sosai mutane suke kokarin bashi hakuri, dan dayan abokin tafiyar daya kira da Alhaji Mannir ne ya samu ya fitar musu da motar su sukayi parking daga can gefe suka tsaya. Duk da mutane da suke basu hakurin cewar su tafi, kafin rigimar tayi nisa, tunda da alama Nuriyya din matar wani babban ce shisa taja rigimar. Ita kuwa Nuriyya AbdulKadir ta kira tana saka mishi kuka cewar wasu sunci mutuncinta a gidan mai. Sai da ta fada mishi sunan gidan man ta kuma ji yace mata ta jirashi, tukunna ta kashe wayar ta koma gefe tana matse hawaye.

Mutanen gurin kowa da abinda yake fada, wanda ba’a fara rigimar a gabansu ba suna tambayar me ya faru, da yawa da aka fara a gabansu kuma suna tir da hali irin na Nuriyya din, wasu ma tafiya sukayi, da yawa kuma sun ma sha man, amman suna tsaye dan ganin karshen rikicin. 3

*

Gajeran wando ya saka, ya dauki farar riga ya dora, wayar shi ya saka a aljihu ya dauki wallet din shi, dubawa yayi yaga babu kudi a ciki, bazai iya tsayawa ATM ba, ran shi in yai dubu a bace kowanne yake, tun jiya yake neman inda zai huce haushin da yakeji, bai samu ba. Sai yanzun da Nuriyya ta katse mishi baccin da yakeyi, ga yunwar da yake ji har hanjin shi kullewa yake. Fitowa yai ya wuce dakin Waheedah. Cikin jakunkunan ta ya dauko ya duba, dari biyar ya dauka a ciki yasaka a aljihu yana ficewa.

Mai babur ya tara zuwa gidan man, jikin shi har bari yakeyi daya karasa ya samu wanda zai jibga, ko canji bai tsaya karba ba, ya shiga cikin gidan man, inda take yake neman, kafin ya hango motar shi, da kuma Nuriyyar da take jingine a jiki. Har yayi hanyar ya hango kamar Major M. Alkali a tsaye jikin wata golf, sake dubawa yayi kuwa, shi dinne, dan sunyi aiki tare a Lagos. Mutum ne shi da matsayin shi da kakin shi bai taba sa ya wulakanta kowa ba, duk da yana da zafi in an tabashi, kuma yana cikin sojojin da AbdulKadir yasani da suka tsani wanda yake amfani da kakin shi yaci zarafin mutane. 3

Fasa karasawa yayi inda Nuriyya take, sai da ya karasa can wajen shi yana kai gaisuwa, amsawa yayi baima iya tambayar AbdulKadir din abinda yake a gidan man ba. Ganin kamar ran shi a bace yake yasa AbdulKadir din yi mishi sallama yana takawa ya karasa wajen Nuriyya da ta fara fifita fuskarta da mayafin jikinta tun daga lokacin da ta hango AbdulKadir din ya karasa ya sarawa mutumin da ta wanke da mari. Hawayen ne wani nabin wani yake saukar mata

“Ki daina kuka… Su waye? Waye ya tabaki?” 2

AbdulKadir yake tambaya, sai dai ta kasa amsa shi, kuka take kamar zata shide mishi, baki ya bude zai sake magana, kamar daga sama yaji muryar Major M. Alkali yana fadin

“Matarka ce ta wanke ni da mari kenan? Shine ta kiraka kazo kayi amfani da kakinka kaci mun mutunci…” 2

Cikin tashin hankali AbdulKadir ya juya yana kallon Major, kafin ya juyo ya kalli Nuriyya da ta ja mishi bala’in da baisan ta inda zai fara fita daga cikin shi ba.

“Nuriyya…”

Ya kira muryar shi dauke da wani yanayi. Kuka take tana girgiza mishi kai, dan ita kanta batasan kalar tashin hankalin da zai biyo baya ba kenan, da tasan soja ne, sojan ma da alama yaiwa mijinta fintinkau da bata fara tsayawa ba, tun sanda ake cewa ta tafi, da lokacin ta shiga motarta ta wuce.

“Muje ko…”

Major ya fadi yana kallon AbdulKadir. Shikuma ya kalli Nuriyya kafin yabi bayan Major din, da sauri Nuriyya take shirin bin bayansu, wani irin kallo AbdulKadir ya watsa mata daya saka ta jin gabaki daya kayan cikinta na yamutsawa, idanuwanta cike taf da sababbin hawaye take kallon su, har suka karasa wajen golf din su Major da ta raina har tayi musu dibar albarka, boot din motar taga ya bude, AbdulKadir ya shiga ya kwanta, ya kuma mayar da murfin ya rufe, suna shirin shiga su tafi. Ai bata san lokacin da ta kwasa da gudu tayi wajen su tana fadin 14

“Ina zaku kai shi? Ina zaka tafar mun da miji? Ka rufamun asiri, dan Allah kayi hakuri… Ka rama marinka ka kyalemun miji” 2

Wani irin kallo Major ya watsa mata

“Marin zai fita a jikin mijinki, karki damu” 4

Ya bude motar ya shiga, suka wuce suna barin Nuriyya nan tsaye ta dora hannunta saman kai tana fadin

“Na shiga uku na…”MAFARI +

Rigima ce ta saka shi biyo mota daga Lagos zuwa garin Kano, dan tashi motar in ba hutun karshen shekara zai zo ba, baya tahowa da ita, babu yanda Waheedah batayi dashi akan ya biyo jirgi ba, yace mata bashi da kudi, wata yayi nisa, ga hidimar gida da sauran hidindimun dake gaban shi. Saida tace mishi ya biya kawai, akwai kudi a hannun ta, Abba ya bata kyautar kudi, batayi amfani dasu ba, akwai kuma kudin da shima yake bata, duk bata siyi komai ba, amman yaki. Jikin shi babu inda baya ciwo, ga rashin wadataccen bacci tunda motar dare ya biyo, da safe ya iso garin Kano.

Tunda Waheedah ta hada mishi ruwan wanka ta tafiyarta kitchen taci gaba da aikin kifin da ta fito dashi dan ya huce tun da asuba, tunda yayi kankara a fridge. Sanda ya fito daga wanka, ta dauko mishi riga da wando marassa nauyi, sakawa yayi yana binta kitchen din. Bude-buden kulolin duk da yagani yakeyi, ko kallon shi Waheedah batayi ba, kifinta take gyarawa, tana jinshi ya karaso inda take, yana dora kanshi a kafadarta, ta baya. Ture shi tayi

“Sai na saka maka karnin kifi ko?”

Kankance mata idanuwanshi yayi

“Ni kike ta sharewa ko Wahee? Yunwa nakeji, ki bani abinci, tun jiya banci komai ba” 1

Kwandon da ta zuba kifin a ciki ta dauka ta dora cikin wani kwano, tana saka omo ta wanke hannuwanta da sink din wanke-wanken ma, tana son kifi, amman sosai karnin shi yake damunta, shisa duk abinda zatayi amfani dashi bata iya ajiyewa, saita wanke. Karamin towel ta dauka ta goge hannuwanta, sai lokacin ta kalli AbdulKadir sosai, daya biye mata, tun jiya da suna tare, yanzun idan ya tafi tana iya wata uku ko fiye da haka bata saka shi a idanuwanta ba, dan ma manhajar Imo data shigo, suna video call sosai, amman ba kamar dai yana kusa da ita ba.

“Duk lokacin dana samu na ganinka yana da muhimmanci a wajena, kamun asarar kwana daya saboda bakajin maganata”

Ta karasa tana hararshi, murmushi yayi yana fadin

“Kin san wa kika aura Wahee, kinsanni”

Kai ta jinjina mishi, ita kuwa ta san shi fiye da kowa da yake da kusanci dashi, wucewa tayi ta gaban shi tana fita daga kitchen din

“Da gaske yunwa nake ji, Allah banci komai ba”

Wannan karin ita tayi dariya, har mamakin yanda yake rayuwa a matsayin soja takeyi, da wajajen da ya shiga, da wanda tasan zai shiga anan gaba. In yana bata wasu labaran, takan tambayeshi ya yakeyi da abinci. Dan daga mata kafadu yakan yi

‘Tunanin ko zan sake ganinku, ko zan sake samun damar rike ki a jikina baya barina yin wani tunanin, Hajja kan zo mun a rai, amman tana da wasu yaran, rashina zai mata sauqi duk idan ta kalle su, bana son barinki, tunanin yanda zakiyi yana sani jure komai, ciki harda rashin abinci ko na tsayin kwanaki nawa’ 2

Ranar farko daya fada mata hakan, kasa magana tayi, sake shigewa jikin shi tayi, tana kokarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta, banda nemawa kanta sauqin mutuwa da kariya daga azabar kabari, ta manta ranar karshe da tayiwa kanta wata addu’a, dukkan sujjadarta cike take da neman Allah ya tsare mata mijinta. Matan sojoji ne kawai zasu iya fahimtar wannan fargabar da take ciki a duk ranar da baya kusa da ita, ko bata ji muryar shi ba, ko ta nemi wayarshi bata shiga. Zuwa yanzun zata iya cewa sai zazzabi yayi da gaske yake kwantar da ita, dan sunyi wani irin sabo na ban mamaki. 1

Wajen cin abincin ta, sai dai ta janye kujerun ta goge, ta kakkabe su, inba randa tayi baqi ba. AbdulKadir ba so yake takai mishi abinci can ba, yafi so ya zauna a kan kafet, harya saba mata itama, ko baya nan kan kafet take zama taci abincin ta. Yanzun ma ta riga ta fito da kulolin da flask din shayi. Saida ya zauna tukunna yace mata

“Ina yaro na?”

Numfashi ta sauke, tana zama itama

“Hamma Yassar ya dauke shi tun jiya”

STORY CONTINUES BELOW


Daquna mata fuska AbdulKadir yayi

“Kinsan zan zo…. Me yasa zaki bar shi ya tafi dashi? Ni zanje in dauko yaro na”

Bata ce mishi komai ba, dankalin da ta soya ta zuba mishi a plate, ta samu dan kwano data fito dashi ta zuba farfesun naman da dumamawa tayi da safen, dan tun jiya da rana tayi ta saka a fridge. Bata san yanda AbdulKadir yake so ta fara cewa Yassar karya tafi da Fajr ba. Wannan aikin sai shi, dan akwai dawowar da yayi yaje har gaban Hajja ya dauko yaran shi. Wani abin idan yayi sai dai ita taji kunya, shikam ko a jikin shi. Hira suke danyi sama-sama harya gama cin abincin ya miqe, tayata kwashe kwanonin yayi ya wanko hannun shi a kitchen din, ya fito yana fadin

“Zanje mu gaisa da Hajja… Sai in biya in dauko Fajr…ko zaki rakani?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi

“Aiki zanyi wallahi, dan Allah karkai mun rigima Sadauki, kaga kifi na gyara, aiki zanyi… Kaje ka dawo”

Waheedah ta karasa tana shagwabe mishi fuska, dan ya fara kankance mata idanuwanshi cike da rigima, zai iya cewa ta ajiye kifin suje su dawo.

“Shikenan tunda ba zaki rakani ba”

Langabe kai tayi

“Ba kin rakaka nayi ba, aiki zanyi. Anjima kadan zaka fara kira mun yunwa”

Murmushi yayi, dakinta ta wuce tana dauko wallet din shi da wayar shi da suke ajiye kan gadon ta, bude wallet din tayi taga da kudi a ciki, ta fito tana kawo mishi. Numfashi ya sauke, zai iya rantsewa daya gan shi a kusa da ita yake manta yanda zaiyi abubuwa da yawa. Da bata dauko mishi ba, ya manta wallet din da wayar basa jikin shi. Har bakin kofa ta raka shi, tukunna ta dawo ta shiga kitchen. 1

*

Da Mami kawai ya gaisa, dan bai samu Hajja ba, yarinyar kanwarta ta haihu, tunda safe ta tafi Aminu Kano. Tunanin ya kira wayarta bai zo mishi ba, da bai sha wahala ya fito ba, yayi kwanciyar shi yai bacci. Inya tashi sai yazo ya dauki Fajr din. Fitowa yayi daga gida, yana sakko kafarshi bakin kofa yana cin karo da ita, wani irin tsalle zuciyar shi tayi daga kirjin shi, kafin ta koma mazauninta tana ci gaba da wani irin dokawa da yakeji har cikin kunnuwan shi.

A duk tsayin shekarun nan, bai taba barin kan shi yayi tunaninta ba, saboda yasan matsayin hakan a addinin shi, ya kuma san darajar kan shi, fadin garin Kano zai musu kadan da duk namijin da yasan yana mishi tunanin Waheedah. Kuma ko ba komai, shi mutum ne da baya tunani akan abinda ya wuce. Nuriyya na daya daga cikin su, ganin karshe da yai mata yana NDA ne, kuma daga lokacin sai labarin aurenta ya samu. Bai sake sakata a idanuwan shi ba, tunaninta kuma bai sake fado mishi ba. Sai yanzun, duk shekarun nan kusan, basu nuna a jikinta ba, tana nan yanda yasan ta, sai dai wata irin wayewa da ta shigeta, da sauri ya sauke idanuwan shi yana neman yafiyar Allah a cikin zuciyar shi na tsayawa da kare mata kallo da yayi.

“Hamma…. Ina kwana”

Ta fadi, muryarta na sauka kunnuwan shi da wani irin yanayi da bai taba tunani ba. Idanuwan shi har lokacin suna kasa ya amsa ta

“Lafiya…”

A taqaice, kamar yanda yakanyi tun da can, ita kanta Nuriyya batayi tunanin ganin shi ba, watan aurenta shidda kenan da mutuwa, taje gidan Waheedah sosai a tsakanin, dan tunda ta gama iddarta take yawo sosai da sosai. Ba zatai karya ba, ganin kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki a duk lokacin da takan je gidanta yana tsaya mata a rai, shi yasa ma ta kusan wata daya yanzun bata taka gidan ba. Yanda Waheedah ta samu duk wani abu da take mafarkin samu na tsaya mata. Miji mai kudi, ga gidanta da ita kanta dinta, ga yaronta da takeji kamar ta sace saboda yanda yake mata kyau. Duk da bai kai hasken fatar Waheedah din ba, yaron yafi su dukan su kyau. 1

STORY CONTINUES BELOW


Ko a wayar Waheedah ta so ganin AbdulKadir din, ta ga yanda ya koma. Haka kawai ta tsinci kanta da son sani, amman bata samu damar hakan ba, Waheedah kuma ko da wasa batai mata zancen shi ba, bata ga fuskar da zata sakko mata da zancen ba ita kuma. Dan sosai Waheedah ta canza, ba wai ita Nuriyyar ta canzawa ba, ita dince gabaki daya ta canza. Dan duk wani sirrin aurenta da taso ji ta kasa, tana mata kyauta kamar da, su sha labarin duniya dai, amman hirar halin da aurenta yake ciki, ko wani sirrinta sam bata ji ko daya ba. Abin kuma ya tsaya mata. 3

AbdulKadir din take kallo, ya kara girma, dan sai ta ganta yar karama a gaban shi, ya aske gashin kan shi kasa sosai, sai ta ga idanuwan shi kamar sun kara kankancewa, akwai tabbai kanana a fuskar shi, sai wani babban tabo da alamun dinkine daga gefen habarshi zuwa wuyan shi, zuwa wani waje cikin rigar shi da take son ganin iya inda tabon ya tsaya. Shi kam bata ga alamar ya canza ba, dan yanda ya amsa mata gaisuwa, hakan yake amsa mata tunda can, a taqaice, cike da rashin kulawar da yake bata mata rai.

Gani tayi yana shirin wucewa, da sauri ta tsinci kanta da fadin

“Hamma…”

Juyowa AbdulKadir yayi yana kokarin kar su hada idanuwa, zuciyarta taji tana dokawa

“Aure na ya mutu, wata shidda da suka wuce, aurena ya mutu…” 4

Ta karashe, tana kallon yanda a hankali ya sauke idanuwan shi cikin nata. Wannan karin kallonta yake, kallonta yakeyi da canjin da kalamanta suka haifar mishi, kallon ta yakeyi yanajin yanda babu shamakin igiyar auren da yake tunanin ta haramta mishi hakan. Ba zaice ga abinda ya faru ba, yanajin wani hijabi da yake tsakanin su ya yaye, yanajin abinda yake tunanin ya binne a NDA na warwarewa.

“Me yasa?”

Ya bukata, cike da rashin fahimta Nuriyya tace

“Me yasa me?”

Saida AbdulKadir ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya, tukunna ya amsa ta

“Me yasa kika fadamun?”

Wannan karin tata zuciyar taji ta doka, ita kanta ba zata ce ga asalin dalilin da yasa ta fada mishi ba, kawai taji tana so yasani ne, bada tunanin komai ba.

“Ina so ka sani ne kawai”

Kai ya girgiza mata, ya rabata ya wuce yana jin yanda take bin shi da idanuwa, yana kuma jin yanda da duk takun da zaiyi da canjin da kalamanta sukai mishi. Machine ya tare zuwa gidan Yassar din. Har cikin gida ya shiga, ya samu Yassar ya fita shi da Fajr din, hakan yasa shi juyawa, ko zama baiyi ba, duk yanda Hauwa ta tabbatar mishi da cewar ba nisa Yassar din yayi ba. Gida kawai yake son ya tafi, wajen Waheedah ko zai daina jin abin da yake ji.

BAYAN KWANA BIYU

Baccin da bata samu a kwanaki biyun da AbdulKadir yazo bane take ramawa, dan dakyar ta kai Fajr makaranta, bata tashi ba sai da azahar, masallaci ma suna raka’ar karshe, a daddafe tayo alwala ta gabatar da sallah, jin yanda jikinta yai nauyi har lokacin yasa ta sake watsa ruwa, atamfa ta saka, riga da zani tana daura dankwalin a kanta, ko mai bata shafa ba, tunda AbdulKadir din baya nan, bataga wahalar da kanta da zatayi ba. Falo ta fito ta kunna kayan kallon ta ganin da wuta. Tunanin AbdulKadir din zai iya kiranta kowanne lokaci yasa ta tashi ta dauko wayarta daga daki.

Text ta tura mishi

‘Ya hanya? Allah ya tsare ya saukeku lafiya’

Ta ajiye wayar, duk da kallon da takeyi bai hanata tunanin wanke-wanken da yake jiranta a kitchen ba. Kwankwasa kofa taji anayi

“Shigo…”

Ta fadi, tana tuna cewar ta rufe kofar da mukulli, tashi tayi ta karasa ta bude, murmushi na kwace mata ganin Nuriyya.

STORY CONTINUES BELOW


“Sannu da rashin kirki”

Waheedah ta fadi tana mayar da kofar ta rufe, dariya Nuriyya tayi suna karasawa suka zauna.

“Ina ta so inzo Allah…. Ban samu lokaci bane ba”

Hararta Waheedah tayi

“Haka zaki ce daman, kingama sai kimun kitso, kan ya isheni wallahi”

Kai Nuriyya ta jinjina mata, suna gaisawa sosai, Nuriyyar ta dora da fadin

“Fajr ana makaranta?”

“Wallahi kam, tunda na kaishi na dawo na kwanta. Babu abinda nayi a gidan nan. Bari inyi wanke-wanke dai, me zakici? Akwai shayi, ko in tafasa mana taliya tunda ina da miya”

Dan jim Nuriyya tayi kafin tace

“Taliyar dai, bama yunwa nakeji ba, ki gama aikin ki a nutse…”

Kitchen Waheedah ta wuce tana barin Nuriyya a falon. Kwanciya tayi ta dauki remote tana canza tashar zuwa Arewa24, wani film din Hausa sukeyi ‘Bakin alkalami’. Shi ta nutsar da hankalinta tana kallo, kafin taji wayar Waheedah din na ihu kan kujerar, daga kitchen din Waheedah tace

“Nuriyya dan Allah taimaka mun da wayata, Sadauki ne ina jin…”

Mikewa Nuriyya tayi daga kujerar tana daukar wayar, aikam shi dinne, ga sunan nan a rubuce, haka kawai sai taji zuciyarta tana wata irin dokawa, lambar ta nutsar da hankalinta akai, komai na AbdulKadir daban ne, lambar kanta bamai wahala bace ba, hanyar kitchen din ta nufa da wayar, ta mikama Waheedah, da sauri ta dawo ta dauki tata wayar, gabanta ke wata irin faduwa lokacin da ta saka lambar AbdulKadir din a wayarta tana saving da ‘Hamma AbdulKadir’. Ta mayar da wayar cikin jakarta ta ajiye. Ta koma ta kwanta, amman yanda gabanta yake faduwa yasa kwata-kwata ta daina fahimtar film din. 13

Ko da Waheedah ta fito daga kitchen din ma sai take ganin kamar zata gane abinda tayi, har wata zufa takeji ta daban, duk da fankar dakin, dakyar ta iya yiwa Waheedah kitson, sukaci abinci, tana yin sallar la’asar tace wucewa zatayi. Tana kai Magriba ma wasu lokuttan, musamman in tazo Fajr na makaranta tunda wuni yake, hade makarantar tasu take da islamiyya. Sai tace sai ta gan shi zata wuce, amman yau din ba’a nutse take ba. Biscuit kala-kala da cake din da matar Yassar ta kawo mata lodi guda ta dibarwa Nuriyyan, ta bata dubu biyu, dan tasan zata kwana biyu bata dawo ba.

Yanayin kaddarar Nuriyyan na tsaya mata a rai, duk da bata tambayeta me ya faru ba, tasan da laifin Nuriyyar a mutuwar aurenta, amman Waheedah na cikin mutanen da basa yanke ma kowa hukunci batare da sanin asalin abinda ya faru ba. Tana mata fatan alkhairi a ko da yaushe, dan har yanzun bata da wata kawar da tafita, sai dai yan uwanta. Sukan kwana biyu basu hadu ba yanzun kuma, Amatu ma aure ya watsa ta Gombe. Dukkan su aure yayi nisa dasu, sai wani abin ya faru akan hadu gabaki daya. Sai dai waya ko da yaushe da sukanyi.

Anan falon tai zamanta, tana jiran lokacin dauko Fajr daga makaranta yayi taje ta taho dashi. Wani indiyan film ta nutsu tana kallo.

LAGOS

Wanka yayi, ya kwanta, daga shi sai singlet da gajeran wando, ya ja bargo ya rufe jikin shi, saboda ruwan da akeyi, garin yayi sanyi, kuma yana jin kwiyar tashi ya kashe fanka, lokaci irin wannan yakanyi kewar Waheedah kamar ba jiya suka rabu ba, da tana nan zata kashe mishi fanka, har bargon ma ita zata rufa mishi, ko bacci yake zata lullube shi, yanda ake take gane yanajin sanyi na bashi mamaki, amman Waheedah ce, takan gane yana bukatar abubuwa da yawa a lokutta dashi kan shi bai gane yana bukatar ba. 3

Hoton shi ya dauka yana rufe da bargon ya tura mata a whatsapp, yana shiga tana hawa ta bude, itama nata ta turo mishi da Fajr dake bacci a kusa da ita, tana rubuto

“Muna ta kewarka”

Daga kasan hoton, hira sukeyi sosai, dan in yana hira da ita baya ma fita daga kan chat din ballantana ya duba ko wani ya mishi magana, Waheedah ma ta koya mishi chatting, kuma da ita kadai yakanyi hira mai tsayi. Sai kannen shi in sun gaishe dashi yakan amsa, suma ba kullum ba. Message na iya kwana biyu bai ko bude ba. Badan yagaji da hira da Waheedah din ba, tunda kullum bata rasa labarin da zata bashi, yace mata ta kwanta, dan yasan zata tashi da sassafe ta shirya Fajr makaranta. Sai da yaga ta sauka, tukunna, bai kai da kashe data din shi ba kiranta ya shigo. Da murmushi ya daga ya kara wayar a kunnen shi

STORY CONTINUES BELOW


“Bakya jin magana ko? Bance ki ajiye wayar ki kwanta ba”

Yanajin dariyarta ta dayan bangaren

“Zan ji muryarka ne fa, yanzun zan kwanta”

Har lokacin da murmushi a fuskar shi

“Ke kadai nake sawa abu, sai kinga dama Waheedah, in fada miki magana kiyi kamar bakijini ba…”

Dariyar ta sakeyi

“Yanzun zan kwanta Allah. Sai da safe. Allah ya tsare mana kai”

Amsawa yayi da

“Amin. Ki kula da ku”

Tukunna ya kashe wayar, ya sauketa daga kunnen shi, yana duba lokaci, karfe sha daya har da rabi, saqo yagani a saman na Waheedah da shine karshe.

‘Hamma…’

Dubawa yayi da mamakin ko waye, ba zai wuce Zahra ba, dan itace sarkin sake lamba, kullum cikin yarda waya take. Budewa yayi yana ganin tana online, da sauri ya amsa

‘Na’am…”

Fara typing yayi da shirin tambayarta ko lafiya? In yaji lafiya ne sai ya sauke mata fada da tambayar abinda takeyi online da daren nan. Hannuwan shi yaji sun daina rubutun a yake ganin sakon da ya shigo

‘Nuriyya ce’

Daquna fuska yayi, sannan ya kankance idanuwan shi, badan baigane ta ba, sai dan mamakin dalilin da yasa take mishi magana da tsakiyar dare haka. Tun randa yaganta tana manne da ranshi kamar yanda takanyi tun lokacin da take budurwa, lokacin farko da zuciyar shi ta fara doka mata, ba bakon yanayi bane a wajen shi, shisa bai dame shi ba balle ya hana shi hidindimun shi.

‘Ok.’

Ya rubuta mata, yaja data din shi ya kashe, ya ajiye wayar a gefe ya gyara kwanciyar shi, addu’ar bacci yayi ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya manne da zuciyar shi, ba sai me zaice mata ba shisa ya kashe data din shi, baima san ko yana so yai hira da ita din ba. In ya riga ya gama waya da Waheedah baya son jin muryar kowa kuma, ko yin magana da wani. Dan ko Yassar ya kira shi yakan daga da fadin

‘Nafa yiwa Matata sallama Hamma, kana kirana kuma, na gama jin muryarta yanzun ina jin taka’

Yassar yakan amsa shi da

‘Wallahi da bani da aure, kai zaka sa dole in fara nema, sai kace kai kadai ne me mata a duniya’

Dariya kawai AbdulKadir zaiyi, amman har ranshi bayaso kowa yai mishi magana in yayi sallama da Waheedah. Baiqi ta zamo farko da karshen wadda zai wa magana a duk ranakun shi ba. Da wannan tunanin a ran shi bacci mai nutsuwa ya dauke shi.

*

Wayarta take kallo, ta tsammaci ya tambayeta inda ta samu lambar shi, tun jiya ta kasa samun sukuni, so takeyi ta kirashi, amman ta kasa samun karfin gwiwar yin hakan. Har ranta tana shakkar shi, kwarjinin da yake mata da, ganin shi da tayi ya ninku. Batasan me take tsammanin zai faru ba. Amman tana son mishi magana din, sai yanzun da ta kasa bacci, da tunanin shi fal ranta tukunna ta yanke hukuncin ta duba shi a whatsapp.

Hoton dake kan display picture din shi ya fara saka zuciyarta daukar wani irin zafi, hoton shine, sai hannun Waheedah da yake rike cikin nashi, yatsunsu lankwashe cikin na juna, AbdulKadir din ya dago hannuwan ya sumbata. Wani irin abu takeji, inda tana da karfin ikon sake hoton, ta cire hannun Waheedah ta saka nata a ciki, zatayi hakan, tun ranar farko da taje gidan Waheedah takejin son samun abinda duk take dashi. Dp din AbdulKadir ya saka shi cikin lissafin abinda take son samu iri daya da Waheedah.

‘Ok’

Din shi take ta kallo ta kasa yarda da cewar baima damu da ita din bace, balle harya tambayi inda ta samu lambarshi.

“Zan sa ka damu dani Hamma AbdulKadir… Wallahi nafi karfin wulakancin ka…” 1

Ta fadi a fili, kalaman na zauna mata, tanajin yanda take a shirye da tayi komai indai zata same shi, kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki, shigar alfarmar da takeyi da komai nata, take son samun irin shi. Kwanciya tayi tana lumshe idanuwanta, muryar Anas na dawo mata

‘Saki kike so ko Nuriyya? Tunda na aureki hankalina bai kwanta ba, ke kanki baki bari naki ya kwanta ba, balle kibari nawa ya kwanta, saboda kina hangen abin duniya. Ba baki na miki ba, amman wallahi ba zaki taba samun kwanciyar hankali ba, alhakina bazai barki samun wannan nutsuwar ba. Bawai zan sakeki dan kin isa bane, zan sakeki saboda ina bukatar samun kwanciyar hankali…’

Tashi zaune tayi tana girgiza kanta cike da son batar da tunanin Anas daga ranta, karya yake yace alhakin shi zai kamata. Ta yarda farkon auren su ta bashi wahala, bala’in yau daban na gobe da ban, inda take so tafiya take ko ya barta ko bai barta ba, abinci kuwa sai dai inya dawo ya dafa, har gyaran gidan shi yakeyi. Amman ta karfi da yaji Anas ya karbi mutuncinta, a cewar shi abin nata bana kare bane ba. Daga lokacin kuma tashin hankalinta ya fara itama, dan Anas daina raga mata yayi, saiya daina kawo abinci, duk idan ta fita batare daya barta ba, saita kwana ta yini da bakar yunwa, komin zagin da zatai mishi.

Hakkin shi inya tashi karba baya tausaya mata, karfi yake nuna mata. A haka ta samu shigar cikin farko, a shekarar auren su, lokacin ya fara nuna mata wani irin gata da soyayya, kome tace tana so sai yai mata, amman ba wannan bane a gabanta, da rana daya bata tabajin soyayyar Anas ba, kullum tsanar shi kuma gaba takeyi a zuciyarta. Kudin da ta dinga karba a wajen shi sanadin cikin, da su tayi amfani aka cire mata shi. Dan ba zata hada jini da Anas ba, balle yara su sakata zama dashi.

Idan ance mata zata shekara hudu da Anas zata karyata, ko shekara bata hango ba, ciki biyar ta zubar a gidan shi, na karshen ne yagane, kuma shine yai sanadin sakin da yai mata. Har gida yazo ya samu Baba ya bashi hakuri, ya kuma yi mishi bayanin duk abinda ya faru. Taga tashin hankalin da bata taba tunani ba, dan Baba ca yai saita koma ko ya tsine mata, kafin yaji saki Uku Anas din yai mata. Ko kadan Baba baiji dadin zancen ba, hausawa kan ce ka haifi yaro baka haifi halin shi ba. Haka Nuriyya ta zame mishi. 3

Badan yana duba abubuwa da yawa da korar Nuriyya daga gidan zai haifar mata da shi ba, da babu dalilin da zaisa taci gaba da zamar mishi a gida. Amman duniya ta nuna mishi ta zaba fiye da darajtasu da mijin aurenta, idanuwa su Baba ya dauka ya saka ma Nuriyya, yabarta da duniyar da yake da tabbaci zata gyara mata zama. Mama daman ba darajar kirki take dashi a idanuwan Nuriyyar ba tun da can, balle yanzun da take ganinta dai-dai da kowa. Ganin babu mai mata fada yasa take duk abinda taga dama. Kullum yawon gidajen kawayenta tun na FCE da yawancin su yan duniya ne na asali.

Maza kuwa kala-kala take tarawa a kofar gidan su. Yanzun ne takejin lokaci yayi da zata tsayar da hankalinta kan kudirinta. Dan duk a cikin masu zuwa mata da maganar aure bayan ta kare iddarta, talakawa ne, masu kudin da maganar banza sukan zo mata. Ita kuwa duk fitsararta bata kai nan ba, aure take son yi, soyayya bata gabanta, inda zata huta tayi abinda take so ne muradinta. Ta kuma hango hakan akan AbdulKadir. Komawa tayi ta kwanta, ta dauki wayar, duk da zuciyarta da take dokawa bai hanata tura mishi text ba

‘Naga ka sauka, har kayi bacci? Sai da safe Hamma. Allah ya tsare mana kai’

Ta saka wayar a caji ko da zasu kawo wuta cikin dare tukunna ta kwanta. Juye-juye take, bacci ya kaurace mata, tunani ne a ranta kala-kala…!
A watanni uku babu dabarar da take tunanin tana da ita da zatayi aiki akan AbdulKadir. Ga wata irin soyayyar shi da takeji kamar ana hura mata wuta. Inda ance ita Nuriyya zata ajiye yanda take ji da kanta ta dauki duniya ta fadama da namiji tana son shi zata karyata. Amman sai gata, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, harta bace kirgan lokuttan da ta furta ma AbdulKadir din kalmar so. A rana tana iya tura mai sakonnin text fiye da goma, tana tambayar lafiyar shi, ko yaci abinci, da sauran duk wani abu da take tunanin inta tambaye shi zai amsata. 2

Sai dai tun kafin ma tace mishi tana son shi din, tana iya tura mishi sakonni hamsin a whatsapp ya bude ya karanta yai banza ya kyaleta. Sakonnin ma da alama suna zuwa, amsa ce kawai bata samu, tana iya kiran shi sau goma a jere bai daga ba. Yanzun kuma ta tsagaita mishi da kiran wayar, tunda ya daga ya balbaleta da fadin 1

‘Ko matata sau biyu take kirana. Karki sake mun kiran yara Nuriyya. Bakisan bana so a dameni ba ko? Me yasa zaki dameni? Ranki zai mugun baci kika sake mun kiran yara. Idan ina son magana dake, kiran farko zan daga, idan bana kusa na zo nagani zan kiraki…’ 7

Ko amsarta bai jira ba ya kashe wayar. Kwana tayi tana kuka daren ranar. Komai sai da taji baya mata dadi. Tayi dana sanin sanayyar dake tsakaninta da Waheedah, sanayyar da tasa take kishinta, take son mallakar duk wani abu da take dashi, sanayyar da ta jefata cikin son mallakar AbdulKadir har yake mata wannan wulakancin. A tsayin watannin kwata-kwata bata taka kafarta gidan Waheedah din ba, sai dai su gaisa a waya, ko ta whatsapp wasu lokuttan, haka tace mata tana gidan kawunta dake Bebeji, taje tadan huta. 3

A watannin ko fita batayi, tana gida kullum, samarin ma sun fita daga ranta, tana dan daga kiransu ne wasu lokuttan saboda ta samu katin waya. Waheedah kuma kan turo mata na dubu daya da dari biyar duk wata, ta siyi data. Duk da tana jin lokaci zai zo da ba zata bukaci wannan taimakon daga wajen Waheedah din ba. Ta dai samu AbdulKadir din, satin daya gabata, har gayawa kanta tayi ta hakura dashi, tagaji da wulakancin da take kwasa, amman da safe saita tsinci kanta da tura mishi sako ta gaishe dashi.

Yau ma kamar ko da yaushe, yana online wajen karfe goma da rabi, dan ya saka hoton Fajr a status din shi, har ta bude ma tayi mishi magana

‘Fajr fa yafi ku kyau’ 1

Ko budewa baiyi ba. Wani radadi kirjinta yake dan tasan da Waheedah yake chatting, zuwa yanzun wani irin kishi take da ita naban mamaki. Batasan me AbdulKadir yagani a jikin Waheedah ba, akan ce kana kiba inka haihu, amman tana nan yanda take, kamar sillen kara, in zasu jera ita da Waheedah, babu abinda Waheedah take dashi da za nuna mata. Tana da kyau tasani, daga na fuska harna jiki, batasan abinda Waheedah din take dashi har haka ba. Ko me tayiwa AbdulKadir din harya aureta.

“Yanzun haka mayyar ita tace tana son shi”

Ta fadi a fili, zuciyarta kuma na saka mata, indai wannan hanyar Waheedah tabi, to itama gata akai, amman babu alamar nasara. Saqe-saqe take a zuciyarta. Kafin taji wayarta da ta saka a silent tana zuuuu alamar kira ya shigo. Karamin tsaki taja, dan batasan kowanne maye bane cikin dare, tana dubawa jikinta taji har kyarma yake, ga zuciyarta na wani irin dokawa, ganin sunan AbdulKadir din da tayi editing zuwa

‘Masoyi 💕’

Na fitowa kiri-kiri, tunda tace tana son shi ta sake sunan, haka kuma takan kira shi dashi a duk sakonninta, bai taba kiranta ba, ita dinma inta kira shi ba dagawa yake ba. Jikinta rawa yake sosai lokacin da ta kara wayar a kunnenta

“Masoyi…”

Ta tsinci kanta da fadi, muryarta a karye, tanajin shige da ficen numfashin shi ta cikin wayar, yafi mintina biyu baice komai ba, badan numfashin shi da takeji da shuu kamar alamun yana cikin mota ba, zata iya rantsewa ya kashe wayar. Kafin yace

“Sai da safe…”

Yana kashewa din batare da ta samu damar amsa shi ba, murmushi tayi tana sauke wayar ta rungume a kirjinta, wani irin nishadi takeji yana ratsata ta ko ina. Ko ba komai yau ya kirata da kanshi, hakan kawai nasara ne. Da tunanin shi fal ranta bacci ya kwasheta.

STORY CONTINUES BELOW


*

Bata gane cikin Fajr kamar sadakar shi aka bata ba sai yanzun da take dauke da cikinta na biyu, da tun a satika kadan da shigarshi ya soma wasan kura da rayuwarta. Daga zazzabi zuwa amai tun kafin asubahi. Duk wani labari da taji masu ciki na bayarwa lokacin da take da cikin Fajr ne ya hadu waje daya yake wujijjigata. Bata son jin kamshin duk wani abinci mai miya. Nabila ta kira ta kwashe mata duk wani kayan miya da yake cikin gidan ta tafi dashi. Abinci sai dai ta saka mai da yaji, man ma na ja, idan tasha bakin ruwa sai tayi kamar zata amayar da kayan cikinta. Citta ta gyara ta dandaqa da kanumfari ta saka a fridge, duk in zata sha ruwa sai ta dan tsiyaya a ciki dan ya canza launi.

Bata taba ganin tashin hankalin irin na watanni ukun nan ba, ga cikin harya fito mata, kamar mai yan biyu. Hankalin AbdulKadir yaki kwanciya, duk yanda take tabbatar mishi da lafiyarta kalau, laulayine kawai, kuma ance zai mata sauqi in cikin yadan kara girma. Amman duk wani dan lokaci da zai samu cikin kiranta yake. Har dariya takan mishi idan yana mata wasu tambayoyin

“Kanki na ciwo? Kina jin zazzabi, bani lamba daga 1 zuwa 10 ya kikeji?”

Wani lokacin har da fushin shi inta ce mishi ita lafiyar ta kalau, ya sha kiran Hajja inyaji muryarta can kasa yasa tazo, kunya yakan bata kamar ta nutse a kasa. Akwai randa suna cikin waya amai ya taso mata, ta ajiye wayar, ashe yanata magana, sai da tagama aman ta dawo hayyacinta ta kira shi.

“Wahee ban samu Hajja ba, na kira Abba amman, yace za’a turo wani”

Babu kalar salatin da batayi ba, balbaleta da fadan shi yayi, me yasa bazai kira Abba ba, ai ba abin kunya bane ba, su da zasuje da baby gidan harma su bashi. Meye dan yasan babyn na hanya. Shiru tayi harya gama ya kashe kiran, tayi murmushi kawai. Rigimar shi babu kalar da bata sani ba, akwai kalar da ta kasa sabawa da itane har yanzun kawai. Nabila tazo tayi mata su shara da mopping, anan ta kwana, da safe ma sai da ta soya mata dankali da kwai tasa a kula, ta dafa ruwan zafi, har taliyar Hausa da Waheedah din tace tana so a bayar ai mata saida Nabila ta dafa mata, tukunna ta wuce gida.

Da Fajr ta wuce, itama ta samu sauki. Tana da tabbacin dai AbdulKadir zaije ya dauko shi inya iso. Ta ga ma har goma da rabi, wayar shi take kira taji yana ina, in yabi motar dare da sassafe yake isowa. Taji sallamar shi, sanyi takeji saboda zazzabin da take ta fama dashi tunda dare, da ruwa mai zafi tayi wanka, amman duk da haka sanyi takeji. Wando ne a jikinta dogo, baqi, ta saka tshirt, ta dauki rigar sanyin AbdulKadir din ruwan toka mai hade da hula ta saka. Kalba ce manya a kanta da Nabila ta taimaka tayi mata, ko dankwali bata saka ba, hular rigar sanyi taja ta saka a kanta.

Kafin ya bude kofar ta sakko daga kan gadon, a tsakiyar dakin suka hadu tana rungume shi, ya zagaya hannuwan shi a bayanta ya lumshe idanuwan shi, kamshin turarukanta sun canza mishi

“Sannu da zuwa…”

Ta fadi tana sake makalewa a jikin shi, wata irin kewar shi take ji tana danneta duk da yana tsaye a gabanta, tana jin dumin shi a jikinta

“Turarenki ya canza mun”

AbdulKadir yace maimakon ya amsa mata sannun da tayi mishi. Murmushi tayi, batasan kalar sabon da yayi da komai nata ba, da kuma kalar kula da yakeyi, ko a whatsapp suke chatting in yaga tana amsa shi kayi dai-dai sai ya fara tambaya me yai mata bata mishi hira. Bayaso yaga canji a tare da ita kowanne iri ne. Murmushi tayi

“Akwai kamshin da bana so a wancen, shisa…”

Dagota yayi daga jikin shi yana saka dayan hannun shi ya taba kuncinta dashi zuwa wuyanta.

“Zazzabi kike ko? Ina hijab dinki muje asibiti”

Kai take girgiza mishi tun kafin ya karasa maganar

STORY CONTINUES BELOW


“Nasha paracetamol ai, zai tafi, yana mun haka wani lokacin”

Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi

“Waheedah…”

Ya kira cike da alamar tambaya da rashin yarda da ita, yana kara taba jikinta, dariya tayi tana kama hannun shi ta sauke daga wuyanta

“Da gaske”

Numfashi yaja yana fitarwa

“Nikam cikin Fajr ba haka yayi bafa, baki sha wahala da yawa ba…” 1

Sanin halin shi yasa ta canza maganar da fadin

“Abinci ko zaka fara watsa ruwa?”

Dan jim yayi, dan yanajin yunwa sosai. Amman yafi so yaci a nutse, jakar daya dawo da itama a falo kan kujera ya ajiye. Tare suka shiga bandakin, ya korota karta taba ruwa tunda yaganta da rigar sanyi, ta mishi wani irin fayau, kamar cikin yasa ta kara haske sosai. Wanka yayi ya fito, kaya ma shiya dauko da kan shi, dan tana gefen gado ta zauna. Tare suka fita zuwa kitchen din, ya dauko mata kula da plate. Shayin shiya hada a kitchen ya fito dashi, ita ta zuba taliyarta da manja, tunda babu abinda ta iya sakama cikinta.

Zama sukayi, AbdulKadir ya dan fara shan shayin da yake tunanin kamar ya mishi yawa ma, gashi sukarin baiji ba, Waheedah ita data zuba inya sha sai yaji yayi dai-dai.

“Shayin salaf…”

Ya fadi yana kara kurba

“Baka zuba sukari ba?”

Kankance mata idanuwa yayi

“Na zuba”

Taliyarta take cakudawa

“Kaje ka kara…”

Kafada ya makale mata, dan a gajiye yakejin shi, kuma zaman ya mishi dadi. Tashi tayi yaba binta da ido, ta dauko kwalin sikarin ta ajiye a gaban shi, kallonta ya sakeyi

“Guda nawa zan saka”

Dayan hannunta da babu manja ta saka ta dibi guda uku ta jefa mishi a kofin ta cakuda, dan gara mata Fajr da tabarar AbdulKadir lokutta da dama, sai da ya dauka ya kurba, tace mishi

“Yayi?”

Kai ya jinjina mata yana soma cin dankalin

“Ni baki bani taliyar ba Waheedah…”

Ta bakinta ta hadiye tukunna ta amsa shi

“Sadauki taliyar hausa ce… Kwanaki dana dafa cakayi mun wacce irin taliya ce wannan?”

Shayin shi ya sake kurba

“Amman bance banaci ba ai, kuma wannan ba irin waccen bace, da manja fa, inata kallon ki tun dazun, baki bani ba. Kuma raina ya biya…” 1

Murmushi tayi, ta tsame hannunta daga taliyar tana mika mishi kwanon, ita kenan Nabila ta dafa mata, dan bata dauka zaici ba, mikewa tayi ta wanko hannunta a kitchen ta dawo. Ta same shi ya cinye taliyar yana fadin

“Ki kara dafa mana anjima…. Irin wannan”

Kai ta jinjina mishi kawai, shiya kwashe kwanonin ya dawo.

“Bacci nake ji”

Ya karasa maganar yana mika mata hannun shi, ta kama tana mikewa. Ta riga tasan ko batajin bacci saita kwanta, rigimar AbdulKadir bata karewa, ko da Fajr na jariri haka ta dinga fama dasu biyun. Sai dai ta saka Fajr daga gefenta, AbdulKadir na bayanta. Dakinta suka wuce, duk da yana da nashi bangaren da bata ga amfanin shi ba, sai ta kwana hudu ma bata taka sashin ba, takan shiga ta share inyai kura, haka ya siyi gidan bangare biyu, dayan bangaren bai kai nan inda take girma ba, amman da falo da bedroom da bandaki, harda kitchen. Nata kuma bedroom biyune, kitchen harda store, kuma akwai bandakin baki daban ta cikin falon nata. 2

STORY CONTINUES BELOW


Har kujeru da komai AbdulKadir ya zuba a dayan bangaren, kitchen dinne kawai babu komai, wasu lokuttan in yana nan, takan ja shi su shiga, su zauna, kafin aljanu su samu wajen labewa. Ko minti sha biyar ba suyi da kwanciya ba, bacci ya dauke shi, itama gyara kwanciyar ta tayi tana rufe nata idanuwan tana jiran bacci yai gaba da ita.

*

Bacci suka wuni yi, da sukai azahar ma komawa sukai har la’asar, garama AbdulKadir ace ramuwar bacci yake. Ita kam cikinne yake sakata wani irin bacci kamar kaza. Taliyar ta dafa musu suka ci. Suka zauna suna kallon wani indiyan film, gabaki daya AbdulKadir ya langabe mata, duk da zazzabin da take ji ya sauka, jikinta babu karfin kirki. Amman ya tattara kafafuwan shi ya dora kan kujerar dan ya kwanta a jikinta. 1

“Ka karyani Sadauki… Sai ka huta kaga”

Waheedah ta fadi jin yanda ya sake naniqe mata. Sake gyarawa yayi bai kulata ba, tunanin da bashi da daliline bayason yi. Nuriyya kuma ta addabi rayuwar shi, tunda ya shigo gidan ya kashe wayarshi ya ajiye. Yasan yana kunnawa zaici karo da sakkoninta. Baisan me take so dashi ba, bayan bata jira shi ba, aure tayi abinta ta kyale shi, tunda batasan tana son shi ba sai yanzun. Shisa bata samun amsar shi, bacin ran dayai tunanin ya binne a NDA ne ta taso mishi dashi gabaki daya. Bakuma yaso ana taso mishi da abinda ya rigada ta wuce shisa.

Kusancin nan da Waheedah yasa yaji sanyi-sanyi. Tunda ya shigo ya dora idanuwanshi akanta cikin rigar shi da tayi mata yawa yaji komai ya kwance mishi. Nuriyya na manne cikin kan shi, amman Waheedah ta saka shi jin nutsuwar da ita kadai take saka shi samu. Saboda haka bazai kulata ba, ta saba cewa zai karyata daman, ko hannunta ya riko sai ta fara cewa zai karyata. Ko shi farkon auren su lallabata yake kamar yana tsoron da gasken zai karyata. Amman zai iya rantsewa daman can Waheedah din dan shi akayita.

“Matar kowa daga kashin hakarkari ake cirota, na sha taba nawa hakarkarin Waheedah, kasusuwan nada kauri, ki kalleki dan Allah…” 4

Ya taba ce mata, lokacin daya kamo damtsen hannunta yaji shi kamar babu tsoka a jiki, tayi dariya kamar me ranar, amman fuskar AbdulKadir din ko alamar murmushi babu, dan daga zuciyarshi yai maganar. Har saka mata ido yayi kan abinci, amman tanaci lafiya kalau, kawai jikin ‘yan matan kenan. Yanzun daya gane ba zai karyata ba, shikenan kuma. Inma ta fada sai dai yayi dariya kawai. Ture shi Waheedah tayi tana mikewa ta nufi kitchen ganin biyar hartayi. Wake ta dibo ta dawo tana zama kan kafet hadi da fadin

“Ta so ka tayani tsince wake…”

Kafada ya maqale yana sake kwanciya cikin kujera

“Ni kibarni… Nagaji. Jikina ciwo yake mun”

Murmushi tayi, neman tsokana ne yasa ta cewa ya tayata din daman.

“Ko zakaje kaci abinci a wajen Hajja?”

Cike da rashin fahimta yake kallonta yana jiran karin bayani kan dalilin da zaisa yaje gida cin abinci bayan ga gidan shi, ganin tayi shiru yasa shi fadin

“Saboda ban tsince wake ba shisa ba zaki bani abinci ba?”

Dariya Waheedah takeyi tana girgiza mishi kai

“Abincina yanzun da mai da yaji ne, ko kana so kaci da miya, ko kamshin nama banaso… Shisa nace ko zakaje can”

Kai ya girgiza mata

“Kome kika bani kinsan zanci ai, zanci da mai din nima”

Shiru tayi batace komai ba, tasan halin shi da abinci ne, shisa tace ko yaje wajen Hajja din yaji, har ranta hakan ba komai bane ba, indai zaici abinda yake so ya wadatar da ita. Amman AbdulKadir ne, ko yana so din ba zaije ba, gani zaiyi tunda shine sanadin kin cin miyar tata, sai suci kome ya samu a tare. Kallon suka ci gaba dayi, ta karasa tsintar waken taje ta wanke ta dora. Da zai fita da magriba binshi tayi ta kulle kofar daga ciki, duk da akwai maigadi a bakin kofa. Dan yace mata zaije gida ya gaishe dasu Abba. Tasan kuma zai iya kai karfe tara bai dawo ba, dan har wajen Yassar saiya biya.

STORY CONTINUES BELOW


*

Gidan Yassar din kuwa ya fara biyawa. Kowa a gidan na mishi mitar baya zuwa a gaisa. Banda Yassar babu wanda yake ganin shi, baya kulasu, ko Hajja ta mishi fada fushi yake mata. In gaisuwa ce sunayi a waya, kuma sukan hadu a gida, idan anyi wani abu na rashin lafiya in yazo ta fada mishi yakanje ya duba su. Baiga dalilin da zaisa a takura mishi da cewar sai yaje gidajen su ba, kuma da karamar sallah duk ana haduwa har wanda suke nesa ma suna zuwa. 1

A masallacin unguwar su Yassar yai isha’i, tukunna yahau babur zuwa kofar ruwa. A hanya ya kunna wayar shi yana jin sakonni nata shigowa ya kuma san Nuriyya ce. Jinta yake a wuyan shi, a rayuwar shi bayason abinda duk zai saka shi tunani, kuma ba zaima kanshi karya akan abinda yakeji a kanta ba. Kofar gidansu babur din ya ajiye shi, ya sallame shi, yana saka canjin a wallet zai mayar aljihu ya hango Nuriyya tsaye ita da wani a bakin motar shi. Ko babu fitilar kofar gidan su AbdulKadir din da ta haska mishi ita, yana da tabbacin zai gane ita din ce.

Wani irin tuquqin kishi da yajine idanuwan shi har lumshewa suke ne abinda bai tsammata ba. Baisan kafafuwan shi na takawa ba sai da yagan shi tsaye a gabanta. Ita kanta ta girgiza dan bata tsammaci ganin shi ba, tun da safe take kiran wayarshi a kashe, ga sakonnin duk da ta tura basu nuna alamar sun shiga ba, ya kirata jiya da dare ya dorata kan tsanin buri, da safen nan ya girgizata ta fado. Har kuka tayi, tunanin shine yai mata yawa shisa ma ta fito zancen ko bakomai zata rage dare, inta koma ta sake kiran shi in bata samu ba ta hakura ta gwada kwanciya ko bacci zai saceta, shine tunaninta lokacin data fito

“Masoyi…”

Ta fadi murmushi na kwace mata, kallo daya AbdulKadir yai ma yaron da yake tsaye ya zagaya ya shiga motar shi yajata yana barin wajen.

“Me kike tsaye da wancan yaron Nuriyya?”

Ya bukata ranshi a matukar bace, saboda baiga dalilin da zaisa ta addabi rayuwar shi idan tasan zata dinga kula wannan yaran ba, baisan me yasa zata ce tana son shi ta fito tana kula kananun yara ba. Kafin ta bashi amsa ya dora da

“Me kike so da ni? Me yasa zaki dameni kuma ki fito kina kula wannan yaron? Da wannan yaron zaki hadamun soyayya Nuriyya? Raini kike son ja mun?” 6

Kai take girgiza mishi, gabaki daya yanayin shi ya tsoratata, muryarta a karye tace

“Ka aureni, ka aureni….in baka son ganina da kananan yara ka aureni”

Murmushi AbdulKadir yayi mai sauti da ko kadan bashida alaka da nishadi, tana maganar aure kamar abune mai sauqi, shisa ta zabi tayi auren tabarshi tun daga farko. Magana zaiyi yaga ta matsa da sauri tana boyewa a inuwar shi. Hakan yasa shi juyawa ya kalli inda idanuwanta suka bari, baisan waye ya shiga gidan su ba, amman bazai wuce wani cikin kannen shi ba. Hankalin shi ya mayar kanta

“Me kike boyewa?”

Idanuwanta cike taf da hawayen da batasan ta inda suka taso ba ta tsinci kanta da fadin

“Naziru ne ya wuce…”

Lokacin da tace tana son shi, bata hango girman hakan ba, asalima idanuwanta a rufe suke da tunanin samun shi, ta manta alakar da take tsakaninta da Waheedah da zata iya saka auren shi ya zame mata abu mai matuqar wahala.

“Me yasa zaki boye?”

AbdulKadir ya sake tambaya, Nazirun ba bakonta bane, baiga dalilin da zaisa ta boye ba.

“Zai ganmu a tsaye”

Ta amsa a sanyaye, tana saka hannu ta share kwallar data taru a gefen idanuwanta, wata irin soyayyar AbdulKadir din na dafa ruhinta

“Me yasa kika ce kina sona idan kananun abubuwa irin wannan zasu dameki?”

Idanuwanta ta sauke cikin nashi tana rasa abinda zata ce mishi, numfashi AbdulKadir ya sauke, gabaki daya kanshi yayi nauyi, bayaso abu ya dame shi, yaga alama kuma Nuriyya zata dame shi

STORY CONTINUES BELOW


“Kina sona da gaske?” 1

Kai ta daga mishi, inta ce kalamai zatayi amfani dasu ba zasu isheta ba, kalar son da take mishi har mamaki yake bata. Kai ya jinjina mata

“Zai zo karshe in na sake ganinki tsaye da wani, bana so, raina zai baci idan naganki da wani”

Kan ta sake daga mishi

“Bana so ana mun magana da kai, ki bude bakinki insan kin fahimci abinda nake fadi”

Wani abu dayai mata tsaye a wuya ta hadiye tana kallon fuskar AbdulKadir din

“Ba zaka sake ganina da kowa ba”
.
Wannan karin shiya jinjina mata kai, ya juya yana barinta a tsaye a wajen, sai da taga ya shiga gida tukunna itama ta wuce, zuciyarta na wata irin dokawa taban mamaki. AbdulKadir kuwa wani irin yanayi yakeji da bai taba tunanin zaiji ba, cikin gida ya shiga yana wucewa bangarensu. A daki ya samu Hajja da ko gaisheta baiyi ba, sallamar da yayi ma bai jira ta amsa shi ba yace

“Hajja ina Abba?”

Cike da mamaki take kallon AbdulKadir din

“Lafiya? Me ya faru?”

Kai AbdulKadir ya girgiza mata

“Lafiya kalau Hajja, ina son magana dashi ne, yana ina?”

Ita ba girkinta bane ba, Mami ke da girki, dan haka tace ma AbdulKadir din

“Yana bangaren shi…”

Kai ya jinjina mata ya fice zuwa bangaren Abba, da sallama ta shiga, ya samu Mami tana hada kwanonin abincin da alama Abba ya gama ci.

“AbdulKadir…. An iso kenan”

Abba ya fadi da fara’a a fuskar shi. Murmushi AbdulKadir din yayi shima yana gaishe da Mami da ta amsa shi cike da fara’a, kunya irin tata bata iya tambayarshi ya Waheedah ba, ta fice daga dakin tana barinsu. Kan hannun kujera AbdulKadir ya zauna

“Abba…”

Ya kira yana dorawa da

“Ina wuni”

Gyara zama Abba ya sakeyi kan kafet din

“Lafiya kalau, ya aikin? Ka samu kowa lafiya dai ko?”

Kai AbdulKadir ya jinjina yana tsintar kanshi da daburcewa a karo na farko a rayuwar shi

“Abba.. Daman zanyi magana dakai ne… Zamuyi magana…”

Ya rasa kalaman daya kamata yayi amfani dasu. Cike da kulawa Abba yace

“Allah yasa lafiya”

Numfashi AbdulKadir ya fitar da baisan yana rike da shi ba, sakkowa yai daga kan kujerar yana zama a kasa a gaban Abba din, muryarshi can kasan makoshi yace

“Aure zanyi Abba…” 7

Maganar Abba yaji kamar daga sama, yanda yajita yafi yanda maganar auren AbdulKadir din daga farko ta dirar mishi.

“Aure AbdulKadir?”

Abba ya tambaya cike da shakku, duk da matan shi hudu, hakan bai hanashi jinjina maganar AbdulKadir din ba, dan yasan yan zamanin su da zamanin su AbdulKadir din akwai banbanci, adalci nama yaran yanzun wahala, kuma da yawa sukanyi auren ne badan ra’ayin hakan ba, sukanyi ne saboda dalilai da kala-kala, da yawa dan suna samun matsala da matan su na gidane. Maimakon su tsaya su fuskanci matsalar su shawo kanta, sai a dinga basu shawarar su kara aure, kamar hakan zai zama sanadin batan matsalar da suke fama da ita.

Wasu kanyi dan su huce haushin wani abin da matarsu ta gida tayi ko take musu, wanda duk dalilai ne da basu kamata a dubasu wajen karin aure ba, shisa ga sunan, yara kanana suna fama da mata biyu da basu san yanda zasuyi dasu ba, tunda ta farkon ma tana neman fin karfinsu. Bayaso AbdulKadir ya kasance cikin mazan da zasu duba wannan dalilin wajen kara aure. Duk a cikin yaran shi babu wanda yake da mata biyu, a matan dai akwai wanda suke da abokan zama. Jin AbdulKadir din yayi shiru yasa shi dora tambayar tashi da

“Me yasa kake son kara aure? Kuna samun wata matsala da Waheedah ne?” 1

Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi da sauri, bazai ce a zamansu da Waheedah basu taba samun matsala ba, amman inzai fadi gaskiya yafi bata mata rai fiye da yanda take bata mishi rai, dan ko abu yai mata bata taba daga mishi murya ba, in tai mishi maganar ya balbaleta da fadan shi sai dai ta bashi hakuri ta wuce daki, da duk idan ya bita kuka yake samun tanayi. Waheedah macece da yasan maza da yawa zasu so samun irinta, bata taba bashi wani dalili na dana sanin aurenta ba, asalima hukuncin aurenta na daya daga cikin abubuwa mafi girma na alkhairi daya sami rayuwar shi.

“Kawai ina son kara auren ne, babu wani dalili bayan haka Abba…” 2

AbdulKadir ya karasa maganar da yakeji tana fitowa daga zuciyar shi. Kai Abba ya jinjina,haka kawai yakejin maganar ta kasa zauna mishi. Har ga Allah duk lokacin da zai ga Waheedah a gidan sai yaji gabanshi ya fadi, dan yana tunanin ko AbdulKadir din yayi mata wani abu, amman har gashi aurensu na dosarma shekaru biyar ko a fuskar yarinyar bai taba ganin damuwa ba. Yafi kowa murna, dan baiyi tunanin akwai macen da zatai hakuri da baudadden halin AbdulKadir na tsayin lokacin ba. Shisa yaji auren bai zauna mishi ba, yana jin yaron har kasan zuciyarshi, bayason yana zaune lafiya ya jajibo abinda zai zame mishi matsala. Numfashi mai nauyi Abba ya sauke

“Kayi tunani akan maganar nan dai AbdulKadir, aure ba abu bane da zaka tashi kaji kana sonyi, yana bukatar natsuwa a cikin shi” 1

Kai AbdulKadir yake girgizawa, bayason abu ya dame shi, gudun tunanin ne yasa shi yanke hukuncin yin auren. Baiga dalilin da Abba zaice mishi ya kara yin wani nazari ba

“Nagama duk tunanin da zanyi… Auren kawai nake sonyi, shisa nazo na fada maka”

Shiru Abba yayi kafin yace

“Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, yar gidan wacece? Wacce unguwa take? In yaso sai kayi mata magana su saka mana rana, ni da Alhaji Hamisu da Alhaji Hadi sai muje ayi magana”

Goshin shi AbdulKadir ya tana yana share zufar da yaji alamar tana tarar mishi. Bai taba tunanin muryarshi zatayi saukar da tayi yanzun da yake furta 1

“Nuriyya ce Abba?”

Kallon shi Abba yayi yana jiran ya tabbatar mishi da rashin hankalin da Hajja kance yana tattare dashi. Wani abu da yaji ya tokare mishi wuya AbdulKadir yake hadiyewa, ko kadan bayason kallon da Abba yake mishi

“Abba ita Nuriyyar…Dan Allah karkace wani abu…ita nake so in aura”

Abba bai taba tunanin akwai ranar da zai so wanke fuskar AbdulKadir da mari haka ba, da auren shi harda yaro.

“Ban taba yarda da baka da hankali ba sai yau AbdulKadir, wallahi yau ka tabbatar mun da cewar baka da hanlali. Nuriyya kake magana, kawar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita kazo kana fadamun kana so ka aura” 3

Kallon Abba AbdulKadir din yake yana rokon shi daya fahimce shi, yasan lokutta da daman mutane na barin abinda addini ya halarta musu dan al’ada na ganin hakan bai kamata ba, kuma tun da ya fara tako kafarshi da niyyar furta maganar auren Nuriyya yasan zai fuskanci wannan matsalar, amman shi mutum ne da surutu irin wannan basa damun shi sam, bayajin akwai wani abu da addini zai halarta mishi kunya ta hanashi yi.

“Bafa haramun bane Abba” 5

AbdulKadir din ya fadi yanajin yanda ranshi ya soma baci, Hajja ce ya tsammaci zatai mishi wannan maganar ba Abba ba, tunda shi namiji me zai fahimta.

“Idan baka fitar mun daga daki ba, wallahi saina wanke ka da mari, marar kunyar banza da wofi…”

Mikewa AbdulKadir yayi yana fadin

“Babu abinda nayi da ba dai-dai ba Abba, nikam zan aureta…” 5

Dafe kai Abba yayi, yanajin zagin da bai taba tunani ba na mishi yawo a cikin kai, da yana da tsohon hawan jini bacin ran da yake ciki yanzun zai taso mishi dashi. Yanajin AbdulKadir din na sake cewa

“Zan mata magana sai a ta fadi ranar da zakuje din” 4

Kafin yaja mishi kofar yana ficewa daga dakin…!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *