ABDULKADIR CHAPTER 8

ABDULKADIR




CHAPTER 8




Har ya shiga gida ran shi a bace yake jin shi. Yana jin Waheedah tun da ta amsa mishi sallama tai mishi sannu da zuwa tana bin shi da ido. Yasan ta fahimci ran shi a bace yake. Kitchen ta shiga ta samu babban plate ta zuba musu abinci a ciki, manja ta zuba musu ta saka cokulla guda biyu a cikin abincin, maggi ta dauka da robar yaji ta fita falon. AbdulKadir na zaune inda tabar shi akan kujera, so take ta tambaye shi waya bata mishi rai, amman batajin dadin jikinta, ba tajin zata iya da fadan shi da daren, shisa tayi shiru. A kasa ta ajiye abinci da robar yajin ta dora maggin a sama. +

Kitchen ta koma ta dauko wani plate din da kofuna guda biyu, ta bude fridge ta dauko pure water guda biyu, sai robar da cittarta take a ciki, in dai an kawo ruwan roba gidan AbdulKadir ne yazo ya fita ya siyo shi, barnar kudin nan bada ita akeyinta ba, akwai gidan ruwa a unguwarsu, maigadi take ba ya siyo mata leda goma ta zuba a fridge din, sai ta kwana biyu bata nemi ruwa ba. Danma Fajr na mata barnar shi, idan yagan shi a roba kuma bakinta baya hutawa da surutu, babu qishin da yake ji, zai dauko ne kawai dan yasata magana. 3

A kasa ta samu AbdulKadir ya sakko, itama ta ajiye ruwan ta samu waje ta zauna. Maggin ta barbada ta bude robar yaji ta zuba, duka ta cakuda, tasan AbdulKadir zai tsaya kallonta sai ta cakuda inda zataci suci wajen tare, ko ta cakuda mishi na gaban shi, in sunje gidan su har mamakin yanda yake komai da kan shi take, amman da sun dawo yaga su kadai ne zai shagwabe mata. Badan batason hakan ba, wani lokaci abin kanyi mata yawa, gashi, ga Fajr. Abincin suke ci, bakajin komai na tashi a dakin sai karar cokulla. Sun gama kenan ta zuba mishi ruwa ta mika mishi kofin sukaji sallamar Yassar.

Ita ta amsa mishi sallamar tana kallon yanayin shi ko zata fahimci dalilin zuwan shi da dare haka. Murmushi yai mata yana amsa gaisuwar ta hadi da dorawa da

“Duk suna lafiya. Ya jikin ki?”

Sunkuyar da kanta tayi kasa a kunyace, tana amsawa can kasan makoshi, idanuwa Yassar ya sauke kan AbdulKadir, hakan da Waheedah ta kula da shi yasa ta mikewa ta dibi kwanonin ta wuce kitchen, acan tasha ruwa tukunna ta fito tana ma Yassar sallama ta wuce daki. Kowa ya batama AbdulKadir din rai tasan bazai wuce a gida bane, tunda taga Yassar yazo. Shisa tabasu waje, in AbdulKadir yana so taji da kanshi zai fada mata, ita kam kaya zata sake ta kwanta abinta.

Yassar mikewa yayi, baisan yanda akayi ya iya dora murmushi a fuskar shi ba, bayan abinda yake so yayi daya shigo shine wanke fuskar AbdulKadir din da mari. Abinci zaici Abba ya kirashi rai a bace yake fada mishi abinda AbdulKadir din yake shirin yi da ko a mugun mafarki Yassar bai taba hango faruwar lamarin ba. 2

“Magana nake son yi da kai”

Kallon shi AbdulKadir yayi yana kankance idanuwan shi, ran shi ya kara baci, Abba kiran Yassar yayi ya fada mishi kenan, kuma baiga dalilin yin hakan ba, tunda zai fadama Yassar din da kan shi, magana ce da ba boyuwa zatayi ba, dan baiga abinda zaisa shi ya fasa ba, ya rigada ya furta. 2

“Ina jin ka ai”

Ya amsa, mikewa Yassar yayi, idan AbdulKadir bashida hankali, shi yana dashi, da alama Waheedah bata sani ba, ba zaiso ta faraji daga bakin shi ba.

“A waje zamuyi magana ba anan ba”

Cewar Yassar yana ficewa daga dakin, tashi AbdulKadir yayi yabi bayan shi har wajen motar shi, suka tsaya. Sun kai mintina biyu Yassar nason hadiye abinda yakeji yana taso mishi ko zai samu nutsuwar yima AbdulKadir din magana batare daya dura mishi ashar ba.

“Abba ya kirani….”

Shiru AbdulKadir din yayi, yana jira Yassar ya fada mishi wani abu da bai sani ba, wannan tsohon zance ne tunda gashi tsaye a gefen shi yana huci kamar sabon biredi. 2

STORY CONTINUES BELOW


“Ka ce mun wasa kake AbdulKadir, dan wallahi na kasa wrapping din kaina akan maganar nan”

Kallon shi AbdulKadir yayi

“Yaushe Abba ya zama abokin wasana? Meye wahala a fahimtar maganganun da nayi? Auren da zan kara ne yake maka wahalar fahimta?”

Numfashi Yassar yake ja yana fitarwa a hankali, da alama idan bai kai zuciyarshi nesa ba, mota zai koma yajata ya take AbdulKadir din duk su huta. 6

“Bansan me kake so ince maka ba Hamma… Bansan me yasa kazo kana kallona kamar akwai haramci a cikin abinda nake so inyi ba” 1

AbdulKadir yake fadi ranshi inyai dubu kowanne a bace yake, tun a hanya yake jin maganganun daya fadama Abba suna dawo mishi, abin na mishi kamar mafarki, yana kasa yarda da abinda yake shirin faruwa din. Amman zuwan Yassar ya kara tabbatar mishi da cewa auren zaiyi babu fashi. Dan baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga mishi kallon da yake mishi ba. Kai Yassar yake girgizawa, muryarshi a gajiye yace

“Bani da matsala da auren ka, wadda zaka aura din ce damuwata, me yasa sai ita? Kawarta ce AbdulKadir…”

Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi

“Sai me ya faru dan kawarta ce? Haramun ne in auri kawar ta?” 15

Dafe kai Yassar yayi da yakejin wani irin ciwon kai ya dirar mishi. Ga zuciyar shi dake zafi, in har yanajin haka da abinda AbdulKadir yake shirinyi, baisan ya Waheedah zataji ba

“Ka daina yin kaman mai asthma Hamma, bazai sa in fasa auren nan ba. Bansan me yasa Abba zai fada maka ba, tunda ai zan gaya maka da kaina daman” 5

Da hannuwa biyu wannan karin Yassar ya tallafe fuskar shi. Da ance mishi akwai ranar da zata zo da zaiji bayason ganin AbdulKadir zai karyata, amman abinda yake ji yanzun, maganganun AbdulKadir din ko kadan bayason gani. Dashi ake jinjina maganar matan da suke cakawa mazajen su wuka duk idan hakan ya faru, AbdulKadir yasa shi fahimtar kadan daga cikin dalilin da maza suke ba matansu har shaidan yai galaba akan su, su hau dokin zuciya su aikata abinda zaisa ka su dana sani daga doron duniyar har lahira. 2

Idan akwai mazaje dari irin AbdulKadir, yana da tabbas lahirar mata da yawa zata raunana, zasu zama barazana da kwanciyar kabarin mata da dama. Fuskar shi Yassar ya bude yana jan wani irin numfashi ya fitar dashi rai a bace

“Babban kuskuren rayuwar Waheedah shine amince ma auren ka” 11

Wannan karin AbdulKadir ne yaja wani irin numfashi, kai yake girgizawa

“Baka fadamun maganar nan ba Hamma, ka janye kalamanka…” 7

Mukullin shi Yassar yake lalubawa cikin aljihu, ya kuwa yi nasarar ciro shi yasa a jikin murfin mota ya bude. AbdulKadir ya mayar da murfin yana rufewa, ya kuma rike hannun kofar gam. Muryarshi can kasan makoshi yake cewa

“Hamma ka janye kalaman ka, dan Allah ka janye ko zasu rage mun zafin da sukeyi…”

Tsaki Yassar yaja

“Ka matsamun daga jikin mota kafin in kwada maka mari AbdulKadir…. Wallahi yanda nake ji komai zai iya faruwa…” 3

Kallon shi AbdulKadir din yakeyi, a tsayin rayuwar shi yaune rana ta farko da Yassar ya fada mishi maganganun da yakejin ciwon su har cikin kasusuwan shi, akan maganar abinda addini ya halarta mishi ta kowacce fuska. Yasha ganin ya ta mutu, kanwarta ta auri mijin, baisan me yasa nashi zai banbanta ba. 3

“Me yasa zaka fadamun haka? Hamma me yasa? Saboda nace zan auri Nuriyya? Dan zanyi abinda Allah bai haramtamun ba…ya tana mutuwa, mijin ko bai nuna yana son kanwar ba a bashi, me yasa nawa zaiyi maka zafi haka?”

Ture shi Yassar yayi yana fadin

“Mahaukaci ne kai wai? Dan ubanka allurar sojojin kai ka miqa musu suka caka maka ita? Addini bai haramta maka auren Nuriyya ba, amman al’ada ta haramta maka shi, kunya ta haramta maka, ko mutuwa Waheedah tayi ka nuna kana son auren ta, akwai mutane da yawa da zasu ga rashin kyautawar haka… Ka matsamun AbdulKadir, ka matsamun in wuce…mahaukacin banza marar tunani” 17

STORY CONTINUES BELOW


Yassar ya karashe yana kara sa hannu ya ture AbdulKadir din, ya bude motar shi ya tayar. AbdulKadir nabin shi da kallo harya fice daga gidan. Bai ce mishi komai ba, saboda yaga alama Yassar din marin shi zaiyi idan ya sake magana, a karo na farko kuma da yasan inya mare shi ramawa zaiyi, dan shima ran nashi ya gama baci. Yafi mintina goma a tsaye a wajen, kafin ya iya wucewa ya shiga gida. Kai tsaye daki ya shiga yana wucewa bandaki ya sakarwa kanshi ruwan sanyi ko zai samu sauqin abinda yakeji.

Daga shi sai towel ya fito, ya samu gajeran wando ya saka, Waheedah har tayi bacci ya hau kan gadon yana matsawa gab da ita. A hankali yake girgizata

“Wahee…. Waheedah…”

Bude idanuwanta tayi cike da bacci tana jin fitilar dakin dake kunne ta shigar mata idanuwa yana sa ta mayar dasu ta rufe babu shiri.

“Ki tashi Waheedah…. Kinji… Kimun hira” 20

AbdulKadir ya karashe yana kara girgiza ta, bude idanuwan ta tayi tana kallon fuskar shi

“Banajin dadi Sadauki… Dan Allah kabarni inyi bacci”

Kai ya girgiza mata, ita batajin dadine, shi zuciyar shi zafi take mishi kamar kirjin shi zai bude, hannunta ya kamo ya dora kan kirjin shi inda yakeji yana mishi ciwo na gaske

“Wahee raina a bace yake, zuciyata zafi take mun wallahi, Hamma ya batamun rai” 11

Yanda ya karashe maganar yasa ta mikewa, sosai take kallon shi, idanuwan shi harsun canza launi saboda bacin rai, tashi zaune tayi tana jingina bayanta da gadon, zazzabine ruf a jikinta, tashin da AbdulKadir din yai mata yasa har amai takeji. Ganin ta tashi yasa shi barin pillown shi yana komawa kan cinyoyinta ya kwanta, ya kama hannunta ya dora kan fuskar shi yana neman sauqi koya yake. 4

“Kayi hakuri dan Allah… Kome zai fada maka nasan baya nufin kalaman, bacin rai ne kawai… Daya huce shikenan, kayi hakuri” 2

Ta fadi a tausashe, kara naniqe mata yayi, ba zata iya hana shi ba, duk da zazzabin da take ji, yanayin shi ya gama raunana tata zuciyar, indai zata sama mishi sauki koya yake zata kokarta. Biye mishi tayi, bata samu yayi bacci ba sai wajen karfe biyun dare. A daddafe ta shiga bandaki tana dubawa ko da ruwan zafi dan basu bar wutar ta zauna ba. Dakyar ta iya watsa ruwa, ga wata yunwa da take wujijjigata, kitchen ta wuce ta duba sauran abincin da yake tukunya, ba zata iya cin shi da sanyi ba, dan haka ta dora tayi warming. 1

Ta dauko plate kenan ta fara zubawa taji takun AbdulKadir din, kafin ta juya ya rungumeta ta baya, muryarshi cike da bacci yace

“Shine kike barni ko?”

Numfashi ta sauke

“Yunwa nakeji…ka koma ka kwanta, da naci abinci zan dawo…”

Tanajin shi yana girgiza mata kai, ko daya farka baiji ta a kusa dashi ba ranshine yaji yana shirin kara baci. Ya duba bandaki bai ganta ba, shisa ya fito nemanta. 2

“Sadauki dan Allah… Karka karyani”

Magana yai mata data tsaya iya kunnenta, ta ture shi tana dariya. Abincin ta zuba, falo ta koma yabita ya zauna a gefenta. Wani lokaci har bataso a bato mishi rai, in kuwa ya faru gara ta tambayeshi ya sauke mata fadan shi da ya shiga yanayin nan da ko bandaki ta shiga tabar shi saiya bita. A kanta abin yake karewa, yanzun din kuma yaki fahimtar ba ita kadai bace itama, ko karfin kirki bata dashi. Yabarta taci abincin a nutse yaki, sai murza ido yake yana hamma, gashi rabin jikin shi a kanta yake. Samu tayi tagama suka wuce suke kwanta. 8

*

Tunda ya dawo sallar asuba yaga sakon Hajja

‘Ka zo ina neman ka’

Wayar ya kashe gabaki daya. Zai je inya tashi, saiya gama baccin safen shi amman. Waheedah kuwa dankalin Hausa taji tana marmari, tana dashi dan haka ta fere bayan ta idar da sallah, ta yayyanka ta zuba a karamar roba ta saka ruwa. AbdulKadir na dawowa Masallaci yaga tana karatun Qur’ani ya samu waje ya zauna a gefen gado, tana idarwa ta ajiye ta cire hijab din ta wuce kitchen yabi bayanta.

STORY CONTINUES BELOW


“Yanzun Waheedah sai kin soya dankalin zamu kwanta? Bacci fa nake ji” 13

AbdulKadir da yake tsaye yace ma Waheedah da take share wajen da ta bata. Indai bacci ne ta fishi bukata, tunda bai bari ta samu na kirki ba, yama fita samun baccin, batace mishi komai ba.

“Ke kadai nake ma magana kijini kuma kiyi shiru”

Abin kwashe shara ta saka cikin dustbin, ta wanke hannunta tukunna ta kalle shi da fadin

“Yi hakuri… Muje”

Kankance mata idanuwanshi yayi da suke cike da rikicin da bata da karfin biye mishi. Kwanciyar sukai, sanda ta tashi karfe goma, ruwa ta watsa ta saka doguwar riga ta material da farar hula tukunna ta wuce kitchen tana dora mai dan ta fara soya dankalin. Idan AbdulKadir ya tashi zai fara mata maganar abinci ne tasani, kuma tashin zaiyi, dan daya laluba yaji bata kusa dashi tashi zaiyi. 2

Tana sauke kaskon farko AbdulKadir din na fitowa daga shi sai towel

“Baki dauko mun kayan da zan saka ba” 1

Ya fadi, in tace yaje ya dauko da kan shi dogon surutu zasuyi, kuma karshe ita zata dauko mishi, sauran dankalin ta juye ta wuce daki ta dauko mishi farar riga marar nauyi da wani three quarter mai igigoyi daga kasan, sai singlet da boxers, turare ta fesa mishi a jiki tana ajiye mishi kan gadon. Murmushi yayi mata yana sa hannu ya taba fuskarta

“Ya kuka tashi? Ya jikin ki?” 1

Murmushi Waheedah tayi

“Baka tambayi jikina ba sai da kagama sani aiki ko?”

Yar dariya yayi, ta gaishe shi da asuba, ya tabata yaji babu zazzabin, bai dai tambaya bane sai yanzun. Ganin yayi shiru yasa ta fadin

“Mun tashi lafiya. Kasa kaya, kar dankalina ya kone…”

Kafin ya amsa ta juya da sauri ta fice daga dakin. Albasa ta yanka dan tana so, ta zuba a cikin wancen data kwashe, na biyun bai karasa ba har AbdulKadir ya fito, falo ya wuce ya zauna yana jiranta, tana gamawa ta hada mishi shayi ta zubo dankalin ta fito. Ci sukayi suna hira, suna gamawa yace mata zaije gida. Rakashi tayi har kofa tukunna ta dawo ta hada wanke-wanke tayi, ta goge kitchen din tukunna ta koma dakin su ta gyara gadon, batajin zata iya share shi tunda ba dauda yayi ba, kuma batama jin dadin jikinta. Komawa tayi ta kwanta tana tunanin abinda zasuci da rana.

*

Gida ya shiga, bai samu Hajja a falo ba, ya wuce dakinta yana kwankwasawa, ya tura bayan ta amsa hadi dayin sallama. A zaune ya sameta kan gado ta mike kafafuwanta ta saka glass din karatu da littafin ‘Tarihin Annabi Kamalalle’ a hannunta tana karantawa.

“Hajja…”

Ya fadi cikin sigar gaisuwa, littafin ta ajiye tana cire gilashinta shima ta ajiye shi a gefe. A nutse take kallon AbdulKadir

“Menene matsalarka? AbdulKadir yau kam ka gayamun menene matsalar ka”

Da mamaki a fuskar shi yake kallon Hajja yana girgiza mata kai

“Bani da matsalar komai Hajja”

Numfashi ta sauke

“Kawai wulakanci ne kenan ko? So kake kaja mana abin magana shisa kake so ka auri Nuriyya… Itama Nuriyyar dan ubanta idan tana da kunya ai ko mutuwa Waheedah tayi idan kazo mata da wannan maganar za ta dubi amintakar dake tsakanin su taki amincewa. Amman naga alama yanda kasa kafa ka shure duk wata kunya da ake halittar dan adam da ita haka itama tayi fatali da tata”

Gefen Hajja AbdulKadir ya zauna yana fadin

“Hajja akan maganar ne kema kike so ki bata ranki? Me yasa bazan aureta ba bayan addini ya halarta mun, me yasa kuke son haramtamun abinda Allah bai….”

STORY CONTINUES BELOW


Kara yaji cikin kunnen shi na haggu da ya katse mishi maganar da yake shirinyi, kafin daga baya ya fuskanci abinda ya faru. Hannun shi yasa yana taba kuncin shi cike da tsantsar mamaki. 1

“Hajja… Marina kikayi Hajja… Mari Hajja” 1

Kai ta jinjina mishi tana fadin

“Ina gab da kara maka wani in baka bacemun dagani ba wallahi. Tunda kai bakasan abinda ke maka ciwo ba, abinda duk kaga dama shi kake son yi…. Aure ko? Auren cin amana, ayi lafiya AbdulKadir, wallahi ba baki nai maka ba, alhakin Waheedah bazai barku ba” 9

Hajja ta karasa maganar tana kokarin tarbe hawayen da takejin sun cika idanuwanta dan takaici, rokar mishi yafiyar Allah take da yanda ya bata mata rai kar wani abin ya same shi. Mikewar yayi kuwa, baya niyyar bata hakuri koya ce mata ya fasa auren. Muryar shi can kasan makoshi yace 7

“In kin huce kimun addu’a Hajja…” 14

Ya wuce yana fita daga dakin, yaja mata kofar a hankali, yanajin yanda ita kadaice zata mishi abinda tai mishi din. Duk da ran shi yakai koluluwa a baci. Daga jiya zuwa yau, abinda Abba yai mishi, Yassar, yanzun kuma ita. Kamar tunzura shi sukeyi da son yin auren, dan yanajin bashi bane mutum na farko da addini ya halarta ma abu al’ada ta haramta mishi. Zai dai zama cikin mutane kalilan da ba zasu taba barin al’ada tayi nasara akan su ba. 2

Yana fita daga gidan, machine ya tare yahau zuwa zoo road, rabon shi da gidan kanin Abba, Alhaji Ali da suke kira da Kawu Ali, harya manta. Amman shi kadai ne mutumin da yake da yakinin zai tsaya mishi kan maganar, dan a gidan su Abba kaf shine yake dan boko na gaske, kuma mutumin da ko a yaran shi zaka fuskanci wayewar da suke tafiyar da rayuwar su a kai. Duk da a baya AbdulKadir din kanyi tir da kalar tarbiyar tasu, yau dai Kawu Ali zai mishi ranar da bai zata ba.

Da yake ranar lahadi ce, babu aiki, ya kuwa yi nasarar samun Kawu Ali a gida. Fada mishi abinda yake faruwa yayi, sosai Kawu Ali ya jinjina maganar

“Shima Alhaji yana da matsala wallahi, yanzun da kuzo kuna abinda bai kamata ba ai gara ayi auren. Kayi hankali da kazo ka sameni da maganar, kaje abinka, zan kira shi muyi magana in shaa Allah”

Dan jim AbdulKadir yayi kafin yace

“Gobe in shaa Allah zan wuce ne Kawu, nafi so a gama maganar kafin in tafi”

Kai Kawu Ali ya jinjina yana fadin

“Bari in kira shi yanzun inji idan bai fita ba, sai muje gidan”

Gyara zama AbdulKadir din yayi, yana sauraren Kawu Ali ya kira Abba, bayajin me Abban yake cewa. Amman da alama baya gida, Kawu Ali na sauke wayar ya kalli AbdulKadir

“Sai da dare, ya fita. Amman karka damu in shaa Allah komai zaiyi dai-dai”

Godiya AbdulKadir yaima Kawu Ali tukunna ya wuce, gida ya nufa, a kitchen ya samu Waheedah tana ta aikin da baisan na menene ba, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera. Babu abinda yake so sai yaga an daura auren ya gama da wannan matsalar, ganin tunani zai mishi yawa inya kwanta yasa shi tashi yabi Waheedah kitchen din

“Me kike dafa mana?”

Kallon shi tayi tace

“Dambun shinkafa”

Murmushin da yai mata yasa taji gabaki daya wahalar dambun ta bace mata 1

“Ina son shi sosai”

“Nasani… Harda zobo na dafa mana, shi zan hada yanzun”

Murmushin AbdulKadir ya sake yi mata, a cikin gidan su ya baro marin da Hajja tai mishi, dan bazai saka abin a ranshi ba. Abu daya da kowa bai sani ba shine yana da Waheedah, babu wani abu da zai bata mishi rai fiye da rana daya. Zatayi wani abin da zaishi ranshi kal, kamar yanzun din ma, gashi duk da hasken da yake ganin ta kara, ta mishi kyau cikin riga da skirt dinta, dankwalin ta daura shi simple, da jan jambaki a labbanta da tunda ta kula yana so take sakawa, dan ita kwalliya ba damunta tayi ba. 1

STORY CONTINUES BELOW


Ganin yana matsowa cikin kokarin hade space din sake tsakanin su yasa ta nuna shi da ludayin hannun ta tana matsawa baya

“Sadauki aiki nake wallahi, dan Allah kaje kayi zamanka, zobo zan hada kaga…. Kaji”

Dariya AbdulKadir yayi yana ja ya tsaya, har saida ta karasa wajen kantar kitchen din, tukunna ya taka yana taba fuskarta zuwa wuyanta

“Ni zanji ko da zazzabi a jikinki ne kawai…”

Murmushi tayi, tasan halin shi sarai. Shiya miko mata robar sukari ta hada zobon da zallar shine yasha kayan kamshi, sai flavor din abarba da tadan diga na ruwa. Da dumin shi haka AbdulKadir yace mata shi yana sha. Dole ta zuba mishi tukunna ya fitar mata daga kitchen din yana komawa falo, taci gaba da aikinta.

*

Kafin isha’i Kawu Ali ya kirashi da su hadu a gida. Dan haka yana fitowa daga masallaci yahau machine ya wuce. Dakin Abba ya nufa, zuciyar shi a dake yake jinta. Dan ya gama yanke hukuncin duk abinda zasu fada bazai canza ra’ayin shi ba. Da sallama ya shiga dakin Abban yana samun shi zaune da Kawu Ali. Wani irin kallo Abba yabi shi dashi da yake jin yana neman sanyaya mishi jiki.

Yana zama kuwa kamar jiran shi Abba yake

“Ni ban isa ba ko AbdulKadir? Ban isa da kai ba kake son nuna mun, kuma nagani. Allah yai maka albarka ya kuma shiryeka…. Aure ayi lafiya amman wallahi babu hannuna a maganar”

Numfashi Kawu Ali ya sauke, ya bude baki zaiyi magana Abba ya katse shi da fadin

“Ku biyun tashi zakuyi kubani waje, kai boko ta hanaka ganin aibun abinda zaiyi, shikuma taurin kai ko? Allah ya bada zaman lafiya, sai kuje kuyi duk abinda kuke so, bana son jin kowacce irin magana indai kan auren nan ne…” 2

Ganin sun zauna yasa Abba mikewa ya shige bedroom din shi yana barinsu. AbdulKadir kan shi a kasa yake, tunda yake da Abba bai taba ganin ranshi ya baci haka ba. Shi kan shi Kawun jikin shi a sanyaye yake jin shi.

“Abbanka yace yarinyar nan makota take, kuma bazawara ce, abin bazaiyi wahala ba….da Babanta yana nan ma sai mu fara magana”

Mikewa AbdulKadir yayi yanajin shi kamar yana yawo a gajimare, komai yake jin yai mishi wani irin shiru.

“Sai mu duba mugani”

Ya fadi, muryar shi na dawowa kunnuwan shi da wani irin yanayi. Tare da Kawu suka fita har kofar gidan su Nuriyya, sallama sukayi da Babanta, ya kuwa fito, yagane AbdulKadir din, amman yayi mamakin ganin su a kofar gidan. Gaishe dashi AbdulKadir yayi yanajin Kawu Ali na mishi bayanin komai. Sosai Baba ya nutsu yana sauraren su. Duk yanda yake son sakama Nuriyya ido, zai karya idan yace matsalar yarinyar bata damun shi tana kuma bata mishi rai. 1

Alhaji Ahmad mutum ne da yake gani da matuqar mutunci, kuma yana taimaka mishi sosai da sosai. Ba zaiso Nuriyya ta zama sanadin da wannan zumuncin da suka shafe shekaru suna ginawa ya zube ba. A nutse yace ma kawu Ali

“Ku bani mintina biyar in dawo”

Cikin gida ya shiga ya sa aka kira mishi Nuriyyar, muryarshi babu alamun wasa yace

“AbdulKadir ne yaron Alhaji Ahmad da Kawun shi suka zo kan maganar auren ki”

Dagowa tayi ta kalli Baba tanajin ta kamar a mafarki, text din karshe da AbdulKadir yayi mata shine

‘Karki kirani, ki jirani zanma Abba magana’

Bata kirashi din ba kuwa, da zullumi ta kwana fal ranta, ko abinci sai dazun da magriba ta tura shi badan tana gane kanshi ba, haka kawai zuciyarta rawa take mata. Gani take ko sama da kasa zasu hade ba za’a bari AbdulKadir ya aureta ba, yanzun kuma da Baba yazo mata da maganar sai take ganin kamar mafarki take.

“Kinga abinda kikai mana aurenki na farko, badan bana miki addu’a ba, amman wallahi ban taba tunanin zaki sami namijin da yake da masuyi mishi fada bayan yayi bincike yaji abinda ya fito dake daga gidan mijinki su barshi ya aure ki. Idan za’ayi magana ta gaskiya ni bazan bari dana ya aureki ba. Zuwa nayi in tambayeki dan idan kika kaso wannan auren ki nemi inda zaki wuce daga gidan mijin, wallahi Nuriyya ba zanyi kaffara ba, kika kaso auren nan ba zaki zauna mun a gida ba” 4

Kai ta daga mishi, haka kawai idanuwanta na cika da hawaye. Juyawa Baba yayi ya koma kofar gidan ya samu su AbdulKadir yana fadin

“Idan yanzun kun shirya ma ana iya daura aure tunda ba budurwa bace” 2

Ware idanuwa AbdulKadir yayi, yana da inda zai ajiye Nuriyya, yana da kudin Sadaki da zai bayar, amman akwai su lefe da sauran kananun abubuwa, duk da an tayashi bikin Waheedah bazai manta kalar kudaden daya tara ba.

“Baba akwai su lefe”

Dariya Kawu yayi yana cewa

“Kayya AbdulKadir… Ai ta taba wani auren, za’a iya daurawa yanzun, duk da gaggawa na daga shaidan, amman auren za’a iya daurawa sai kuyi maganar lokacin tarewa da sauran abubuwa”

Kai AbdulKadir ya daga yana fadin

“Babu kudi a jikina, sai dai inje banki in dawo yanzun”

Jinshi yake kamar a mafarki, kai Kawu Ali ya girgiza mishi yana fadin akwai kudi a wajen shi. Mota suka koma Kawu Ali ya kirgo dubu hamsin suka sake fita, masallaci sukaje akayiwa Liman magana, da wasu manyan mutane da suke zaune a majalissa nan gefen masallacin. Cikin kasa da mintina talatin aka daura auren aka gama komai. Kawu Ali da kanshi ya sauke AbdulKadir har gida dan yace mishi bada mota yazo ba. 6

Ya shiga cikin gidan, ya dora hannun shi kan handle din kofa, amman ya kasa murzawa, komai daya faru yakeji yana danne shi, kamar wani mafarkine yakeyi sai yanzun ya farka ya samu mafarkin da gaske ne. Aure yayi, Nuriyya ya aura, ba wannan bane damuwar shi, bai fadama Waheedah ba, bai kuma san ta inda zai fara fada mata ba…!!!Yakanji mutane na fadin gwiwoyin su sunyi sanyi, akwai lokutta da yawa da zaice ya taba jin irin yanayin, baisan asalin yanda yake ba sai yanzun da yake a bakin kofar gidan shi amman ya kasa shiga. 2

“Oh Allah na”

Ya tsinci kan shi da fadi ganin da gaske shine a tsaye bakin kofar gidan shi ya kasa shiga. Lumshe idanuwan shi yayi yana bude su hadi da sauke numfashi, duk wani sauran karfi da yake jin ya rage mishi ya tattaro ya murda hannun kofar dashi. Kafafuwan shi da yakeji kamar itace saboda nauyin da sukai mishi yaja yana shiga cikin gidan dayin sallamar da ta tsaya cikin makoshin shi. Gyaran murya yayi yana sake yin sallama, amman duk da haka a hankali yaji muryar shi ta fito. 2

Dakyar yaja kafafuwan shi zuwa bedroom din su, ko sallama sai bayan ya tura ya shiga yayi ta. Amsawa Waheedah tayi, tana jera kaya a wardrobe din dakin da take cikin bango.

“Takalma Sadauki… Saboda kai bana sallah a tsakar daki saina saka darduma, ko ina shigarmun kake da takalma…”

Nan inda yake ya tsaya ya kwance igiyar takalman da suke kafarshi yana zame su tukunna ya karasa cikin dakin ya zauna kan gado.

“Sannu da aiki…” 3

Ya furta da wani irin sanyin murya da yasata barin abinda takeyi ta juyo tana kallon shi.

“Sadauki?”

Waheedah ta kira cike da alamun tambaya, dan yanayin shi gabaki daya ya bata tsoro, ganin bai dago ba, asalima sake sukunyar da kan shi yayi, yasa ta rufe wardrobe din tana karasawa ta zauna kusa dashi. Kafadar shi ta dafa tana fadin

“Lafiya? Me ya faru? Menene? Wani bashida lafiya a gida?”

Kai AbdulKadir yake girgizawa da duk tambayarta, amman ya kasa dagowa ya sauke idanuwan shi cikin nata. A karo na farko da yake tir da gaggawa kan al’amura batare da tunani ba. Saboda bai taba tunanin zaiji abinda yakeji din ba yanzun, ya rasa karfin gwiwar fuskantar Waheedah ya fada mata yayi aure, an daura mishi aure, matsalar shi ba gaya mata da wa aka daura mishi auren bace a yanzun, ta inda ma zai fara mata maganar auren. 6

Kan shi ya dora a kafadarta yana sauke wani irin numfashi

“Waheedah….”

Ya fadi cikin wani irin yanayi, hannunta ya kamo ya rike yana rasa kalaman da zaiyi amfani dasu. Da Hajja bata mishi fushi sai ya kirata tazo ta taimaka mishi ta fadama Waheedah din, ko Yassar ma, wani dai ya fara fada mata dan shikam har wani zazzabin tashin hankali yakeji ya fara rufar mishi. 15

“Kana bani tsoro Sadauki… Na kasa yarda komai lafiya” 4

Waheedah tace tana dumtsa hannun shi da yake cikin nata. Idanuwan shi ya lumshe da maganganunta yanajin komai yai mishi tsaye cik. Waheedah ce, Waheedahr shi. Ta ina zai fara fada mata ya kara aure batare da saninta ba, sai yanzun tunanin ita ya kamata ta fara sani kafin kowa yazo mishi. Dagowa yayi daga jikinta ya ja Kafafuwan shi kan gadon yana lankwashe su. Numfashi ta sauke, tunda ya shigo gidan sai yanzun ya hada idanuwa da ita, duk da akwai wani abu da take gani tattare da yanayin fuskar shi da yasa zuciyarta yin rawa.

Fuskarta ya tallafa cikin hannuwan shi yana fadin

“Karki barni Waheedah, ki tabbatar mun da ba zaki barni ba” 14

Nata hannuwan ta dora kan nashi dake fuskarta

“Dan Allah ka gayamun me yake faruwa”

Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye dan gabaki daya ya tsoratata

STORY CONTINUES BELOW


“Wani waje mai hatsari zasu sake turamun kai ko? Ka fadamun dan Allah…” 2

Cewar Waheedah muryarta na karyewa. Wannan na cikin bangaren da tafi tsana a aikin shi, in duk aka turasu wajen da ake hatsaniya, tare da kwanciyar hankalinta yake tafiya, wayar duk da zataji sai gabanta yai wata irin faduwa, idan tayi sati daya bataji shi ba, ko baccin kirki batayi. Tana da tabbacin matan sojoji tare suke raba duk wani tashin hankali dake cikin aikin mazajen su. Mata da yawa nason auren sojoji, ita AbdulKadir take so, in da tana da yanda zatayi da baizo mata a soja ba. Tashin hankalin dake cikin aikin shi yana da yawa. 3

Kai ya girgiza mata, muryarshi can kasan makoshi yace

“Babu inda aka turani, kawai ina son jin ba zaki barni ba” 1

Murmushin karfin hali tayi badan zuciyarta ta nutsu ba, amman shi dinma bata ganin nutsuwa a tattare dashi, bata so ya koma wajen aiki a haka.

“Ka taba ganin mata tabar mijinta? Ina zanje nikam…ina tare da kai daga yanzun har sauran kwanakin da Allah ya aramun” 3

Numfashi AbdulKadir ya sauke yana barin kalamanta na samun wajen zama a kasan zuciyarshi. Yakai mintina biyu tukunna ya saki fuskarta yana mikewa, bandaki ya shiga ya watsa ruwa, amman ko kadan baiji wani sauki ba, hankalin shi yakeji yaki kwanciya, ga wani bangare na zuciyarshi da yake azalzalar shi ya fadama Waheedah din kawai ya huta, amman ya kasa samun karfin gwiwar fada mata, baisan ta inda zai fara ba.

Kwanciya sukayi, Waheedah na jikin shi, ko kadan bacci ya kaurace ma idanuwan shi, ya rasa abinda yake mishi dadi a duniya, karfe hudu ya mike ya karayin wanka, shiya hada kayanshi, ya rasa karfin zuciyar tashin Waheedah din, kai kawon da yakeyi da motsin shi da yai yawa shiya tasheta. Fuskarta kawai ta wanke tayi brush ta wuce kitchen tana fara fere dankalin turawa, iya wanda AbdulKadir din zaici ta soya. Kafin biyar harta gama komai yaci, tana kula da yanda yake komai da wani irin sanyi da yake taba mata zuciya.

Kafin asuba yake fita daman, Yassar ne yake zuwa yana sauke shi tasha. Amman yau kwata-kwatsa AbdulKadir din bai tsammaci zai zo ba, har saida yaji karar shigowar mota tukunna. Jakarshi ya rataya Waheedah na rakashi har bakin kofa, ta kasa sabawa har yanzun, duk randa zai tafi sai tayi kuka. Yanzun ma idanuwan ta cike suke da hawaye, muryarta na rawa tace

“Allah ya tsare mun kai a duk inda zaka shiga. Ka kula da kanka dan Allah…”

Kai AbdulKadir din ya daga mata yana rungumeta a jikin shi, saman kanta ya sumbata da gefen fuskarta, tukunna ya dago ta daga jikin shi

“Zanyi kokari in dawo wata na gaba in shaa Allah. Ki kulamun da kanku…”

Sake rungumeshi tayi tanajin kamar karya tafi. Dakyar ta iya raba jikinta da nashi, tana sa hannunta ta share kwallar data tarar mata. Shi kanshi yanajin barin nata, da son samun shine duk inda zaije da ita zai tafi. Amman ya fahimce ta data fada mishi Fajr na bukatar samun ilimin addini mai inganci, zaman Lagos ba nata bane da yara, tafiso ta natsu waje daya. Shisa ma ya dawo da ita Kanon, tunda shima wani lokaci aiki na dauke shi watanni, duk inda yakaita in hakan ya faru ita kadai zata zauna. Gara a gida inda yasan tana zagaye da yan uwa.

Sai da ya sake sumbatarta tukunna ya fice daga gidan yanajin yau ba wani bangaren shi ya bari ba, harda wani irin nauyi mai girman gaske da rashin gaya mata maganar auren shi, tunda ta tashi yake motsa bakin shi, kalamai ne sukaqi fitowa. Abba ya kamata ya tambaya ta inda zai fara tunda shi yayi hakan har sau uku. Zaifi kowa sanin kalaman daya dace yayi amfani dasu, amman Abba fushi yake mishi, tunda bai kirashi yau ya mishi Allah ya tsare ba. 9

Wajen motar Yassar din ya karasa ya bude ya shiga yana fadin

“Hamma ina kwana…”

Inda yake Yassar bai kalla ba yaja motar yana fita daga gidan. Numfashi AbdulKadir ya sauke

STORY CONTINUES BELOW


“Kai ma fushin kakeyi kenan har yau… Ni banyi fushi na Hamma kaine kakeyi… Ok” 4

AbdulKadir ya karasa maganar yana sauke wani numfashin

“Da Kawu Ali mukaje jiya… An daura auren tun jiya… Ban fadama Waheedah ba, Hamma na kasa fada mata, tunanin bai zo mun ba sam sai bayan an daura auren. Ya kamata in fada mata…”

Katse shi Yassar yayi da cewa

“Wallahi, Wallahi idan kaci gaba da magana zan saukeka ka nemi abinda zai kaika tasha ko ka taka da kafa bai dameni ba. Allah kadai yasan yanda nakai zuciyata nesa na fito… Kayi abinda kake so, wannan matsalarka ce, tun jiya ka rigada ka nuna mun banda matsala da aurenka. Kabar shi a haka kawai, bana son jin duk wani abu daya shafi tsakanin ka da Nuriyya, yanzun, anjima, gobe, kai har iya zaman rayuwar aurenku idan kana son zaman lafiya dani ba zaka kawomun zancen ta ba” 1

Muryar Yassar din ta tabbatar ma da AbdulKadir yana nufin dukkan kalaman daya fada, daga zuciyarshi yai maganar. A karo na farko da yaji bayason kure hakurin Yassar din. Shiru yayi, yana kara jin komai ya hade mishi waje daya. Wayarshi ya laluba yana ganin text din Nuriyya. Mayar da ita yayi ya ajiye, itama baisan me zaice mata din ba, baisan me zaicewa kowa ba. A bakin tashar unguwa uku Yassar ya sauke AbdulKadir din yana fadin

“Allah ya tsare…”

Yaja motar shi ya wuce, da gaske fushi Yassar yake mishi, dan yakan samu waje yai parking, baya tafiya sai yaga AbdulKadir din ya shiga mota suna shirin tashi tukunna. Wani irin numfashi AbdulKadir yaja yana fitar dashi a wahalce, zai karya idan yace ranshi bai sosu ba, amman Waheedah ta danne duk wani abu da yakeji yau. Zai bi takan sauran al’amura idan ya samu hanyar fada mata ya kara aure. 2

*

Inda Baba ya fita yabarta, nan ya dawo ya sameta, badan bataso ta tashin ba, sai dan tanajin tsoron tashi ta farka daga mafarkin da takeyi na cewar AbdulKadir yazo neman aurenta wajen Baba. Magana ce da takejin ta kamar almara. Sallamar da Baba yayi yana kiran Mama ya katse mata tunanin da takeyi, duk da hakan baisa ta daina jinta kamar a mafarki ba. Mama ta fito tana kallon Baba da farin cikin dake fuskar shi.

“Auren Nuriyya aka daura yanzun a masallaci”

Cike da mamaki Mama take kallon Baba, tasan kullum zancen shi baya wuce na Nuriyyar duk sanda zasu kebe, amman bai mata zancen ya samo mata miji ko kuma akwai wanda ya same shi da maganar aurenta ba.

“Ban fahimta ba, aure fa kace Baban Nuriyya…”

Kai Baba ya jinjina mata

“Fitar da nayi dazun da maganar suka zo, to a shirye suke ashe”

Har lokacin da mamaki a fuskar Mama tace

“Duk da a shirye suke, kuma ba auren farko bane abin da mamaki, badan baya faruwa ba har a auren budurwar, amman gaggawa na daga shaidan fa, wanene yaron? A musulunce ya kamata ayi bincike kafin a daura” 2

Murmushi Baba yayi

“Nasani, nima nayi tunanin, amman ganin dan gidan Alhaji Ahmad ne shisa ma banki ba”

Da wani sabon mamakin karara a fuskar Mama take kallon Baba

“Dan gidan Alhaji Ahmad kuma? Wanne daga ciki?”

Gyaran murya Baba yayi tukunna yace

“AbdulKadir”

Wannan karin da tashin hankali bayananne Mama take kallon shi, cike da yanayin da yasa yaji gabanshi ya fadi

“Lafiya kuwa? Me ya faru?” 3

Kai Mama take girgizawa

“AbdulKadir naji kace, AbdulKadir dan gidan Alhaji Ahmad”

STORY CONTINUES BELOW


Da sauri Baba yake jinjina mata kai.

“Eh shi nace”

Bango Mama ta laluba tana samun kujera ta katako ta zauna akai tana wani irin mayar da numfashi hadi da fadin

“Nuriyya me kikayi? Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Sosai Baba yake kallon Mama

“Kimun bayani yanda zan gane… Me yake faruwa wai”

Kai Mama ta daga tana kallon Baba da idanuwan da suke cike da hawaye, ko da fada mishi tayi ba lallai bane ya fahimta, abune da ‘ya mace kawai zata fahimci ciwon shi, dan ita zuciyarta wani irin zugi take mata, batajin zata dauki abinda akai ma Waheedah din, batasan hawayen ta sun zubo ba sai da taji su kan kuncinta, muryarta na sarqewa tace

“AbdulKadir dinne baka sani ba? Baban Nuriyya AbdulKadir dinne baka gane ba kafin ka biyewa son zuciyar ‘yarka ka wakilci daurin auren nan ko me?” 1

Kafafuwan shi Baba yaji sunyi sanyi, tsugunnawa yayi, yasan matarshi farin sani, a tsayin zamansu, abinda zai sakata zubar kwalla babba ne.

“Maryama na kasa fahimtar ki, kimun magana yanda zan gane, kaina ya daure”

Wani irin kallo Mama take mishi da duk ya kara dagula mishi lissafi

“Kasan yana da aure ko?”

Kai Baba ya jinjina yana kallonta cikin kaguwa da jin sauran zancen

“Kana so kace mun baka san wacece matar shi ba”

Kai Baba yake girgiza mata, zai iya tuna lokacin da akai auren AbdulKadir din, su uku ne ko fiye da haka aka daurama aure ranar in zai tuna, dan a makare yaje, ko cikin masallacin bai samu shiga ba saboda cikowar mutane, ya tsayane har Alhaji Ahmad ya fito yai mishi Allah yasa alkhairi ya wuce. Wani irin daci Mama takeji har kasan zuciyarta, bata shiga harkar Nuriyya ne saboda batason rainin yarinyar, shisa a lokutta da dama take binta da ido, tasan tana da halaye marassa kyau, amman bata taba zaton ko zata nunawa kowa zai fada kan Waheedah ba.

“Amman kasan Waheedah ai” 1

Kan dai Baba ya sake daga mata

“Ya zakice nasan Waheedah… Waheedah fa”

Baba ya maimaita, yarinyar da aminiyar ‘yar shi ce, kaunar dake tsakaninta da Nuriyyar ta kara karfin zumunci shi da Alhaji Ahmad din har yake samun alkhairai da dama daga shi har ‘yar tashi. Hankali da nutsuwar yarinyar yasa duk shekarun shi yana ganin girmanta ba kadan ba. Kuma ko da Nuriyya tayi aure duk idan Waheedah tazo gida saita biyo ta gaishe dasu ko baya nan, yakan dawo ya samu sakon abin alkhairin da ta kawo musu.

“Hmm…”

Mama ta fadi zuciyarta kamar zata baro kirjinta, sai da ta hadiye wani abu dayai mata tsaye a makoshi tukunna tace

“Mijinta ne ka aura ma ‘yarka” 2

Cikin tashin hankali Baba yake kallon Mama, yana son tace mishi abinda yaji ba gaskiya bane ba. Yasan Nuriyya daya daga cikin yaran Alhaji Ahmad ta aura, amman harga Allah bazai ce wanne bane a cikinsu, kuma bai taba kawo ma ranshi AbdulKadir din bane ba, tunda da kan shi yazo neman auren Nuriyyar, kuma itama Nuriyyar tasani, ko a mugun mafarki kuma bai hango cewar zasu hadu su biyun suyi wannan cin amanar da addini bai haramta ba, amman kunya da kara ta haramtashi ta kowacce fuska. 1

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Baba yake fadi yana maimaitawa, idan hankalin shi yayi dubu gabaki daya yagama tashi. Ya rasa abinda zaice, mikewa Mama tayi tana kara share kwalla kafin tace

“Bansan abinda kikayi ba Nuriyya, bansan da idon da zaki kalli Waheedah a matsayin kishiya bayan duk halarcin da taimiki da zumuncin dake tsakanin ku ba, wallahi bansani ba. Nikam nasan bazan iya kallon idanuwan yarinyar nan ba…. Duk da ina son tasan bada sa hannuna kikai mata wannan cin amanar ba”

STORY CONTINUES BELOW


Mama ta karashe maganar tana barin wajen, Baba kuwa har lokacin ya kasa magana, hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro sadakin Nuriyya da tunda aka fara maganar kanta yake a kasa, hawaye kawai suke zubar mata badan zata iya cewa ga asalin dalilin zubar tasu ba. Duk da ta daina jin duk wata magana da ta biyo bayan an daura aurenta da AbdulKadir, sai yanzun da tabi kudin da Baba ya ajiye mata da kallo.

“Wallahi da nasan mijin Waheedah ne sai dai ku nemi wanda zai daura muku auren nan Nuriyya… Bansan me kikayi ba, daga ke har shi, ban kuma san dalilinku nayin abinda kukayi ba. Amman in kunyi da son zuciya amana ba zata taba barinku ba…” 10

Baba ya fadi yana tashi shima. Dakin shi ya wuce yana jinjina al’amarin da kuma daukar da Waheedah zatayi musu ta mutanen da basu san darajar zaman tare da girman alkhairi ba, kuma bazai ga laifinta ba. Da gaske ne gaggawa a komai daga shaidan take, yanda ya kaqu ya rabu da Nuriyya yasa shi amincewa auren batare da tunanin komai ba. A karo na farko da yabi son zuciyarshi gashi tun ba’a je ko ina ba ya fara dana sani. Nuriyya kuwa kudin ta dauka tana komawa daki ta kwanta, har lokacin bata daina jinta kamar a mafarki ba.

Wayarta ta dauko, duk da tana shakkar ta kira AbdulKadir din, text ta tura mishi

‘Nagode Masoyi, duk da na kasa yarda na zaka matarka, wallahi ina jina kamar a mafarki’ 2

Sai da taga sakon ya shiga tukunna ta sauke wayar kan kirjinta tana jin wani irin nishadi da bata tabaji ba a rayuwarta yana lullubeta, kafin bacci ya kwasheta cike da mafarkin rayuwar da zatayi a matsayin matar AbdulKadir. 2

*

Komai bai sake hade mishi waje daya ba sai bayan komawar shi Lagos. Duk wani wanda yake sama dashi a gidansu saida ya kira yai mishi tas kan maganar auren, gabaki daya babu wanda ko Allah yasa alkhairi yai mishi, ya manta rabon da yayi kwanaki da bacin rai haka. Har kannen nashi ma Zahra sai da tayi mishi text

‘Hamma baka kyauta mana ba, zaka zageni nasani, amman bai dameni ba wallahi. Abinda kayi baka kyauta ba’

Ya kuwa kira din ya sauke mata masifa kamar zai cinyeta, kukan ta daya ishe shine yasa shi kashe wayar shi, daman wanda zai huce akan shi yake nema. Gabaki daya ya rasa yanda zaiyi ko inda zai saka ranshi yaji sanyi, ga Waheedah duk waya ko video call din da zasuyi sai yaga ta kara mishi wani irin kwarjini da ko maganar kirki sai yayi da gaske yake iya hadata balle har yai mata zancen auren. Nuriyya ma kullum suna waya a gajarce, a satika biyun da yayi a Lagos doguwar waya daya sukayi, shima bayan ya kira Anty Talatu da tunda yake a rayuwarshi bai taba tunanin akwai ranar da zai bukaci wani abu daga wajenta ba.

Amman babu yanda zaiyi, babu wanda zai tambaya tunda duka yan gidansu basa magana dashi dan ya kara aure, itace ta fara zuwa kan shi. Ko ita din ma mamakine bayyane a muryarta da ta daga wayar, suka gaisa tana dorawa da

“Lafiya dai ko AbdulKadir? Kowa lafiyar shi kalau?”

Kai ya daga kamar tana ganin shi

“Lafiya kalau Anty, zan tambayeki ne daman”

Yanajin sauke numfashin da tayi kafin ya dora da

“Idan ka auri bazawara zakayi akwatuna duka ko?”

Dariya Anty tayi daga dayan bangaren

“In kana da halin hakan, ai kyautatawa ce, amman bakowa yakeyi ba gaskiya. Zaka iya magana da ita kaji, wasu sunfi son a basu kudin ma akan a sai musu kayan, kai ma kuma zaifi maka sauqi”

Jinjina kai AbdulKadir yayi, dan bai fahimci maganar Kawu Ali kan lefen ba, ita kuma Nuriyya batayi mishi zancen ba. Shisa ya kira Antyn dan yaji in sai yayine sai yasan yanda zaiyi

“Kaman nawa zai isa”

Ya tambaya

“Gaskiya bazance ba, daga dubu dari in kana da hali har dari biyu ma, ko kasa da hakan. Iya aljihunka iya abinda zaka yi”

STORY CONTINUES BELOW


Shiru AbdulKadir yayi

“Idan nace banda dubu dari biyu nayi karya, amman akwai hidindimu a gabana nikam, matata nada ciki”

Yar dariya Anty tayi

“Bakayi tunanin akwai wata hidima a gabanka ba kake shirin kara aure, na dauka halin naku na mazane ya motsa ai, aljihunka kaji a cike da kudin da bakasan yanda zakayi dashi ba sai karin aure…”

Dan murmushi AbdulKadir yayi

“Nasan ba zamu gama wayar nan lafiya ba Anty… Dole sai kin fadamun maganar da zanji daman ban kira ba” 1

Dariya Anty tayi sosai

“Allah ya shirya mana halinka AbdulKadir…”

Sallama yai mata hadi da godiya kafin ya kashe wayar. Da gaske yake da yace mata hidima ce a gabanshi, akwai kudaden da yake ajiye da sai dolece take sakawa ya tabasu, yana ajiyewa ne saboda tsaron lalura. Dan sai da aka haifi Fajr tukunna yasan kula da yara ba abu bane me sauqi. Saima daya fara haqora, ga kyanda. Shisa baya wasa da ajiye kudi dan irin lalura haka. Yanzun kuma Waheedah nada wani cikin, yana son ta samu duk kulawar da take bukata, asibiti me kyau da baifi karfin shi ba. Sannan ga kayan babies da itama kayan da zai mata da sauran hidindimu. Amman auren ma shiya yanke hukuncin yin shi. Dole ne yayi abinda ya dace.

Akan maganar kudin kayan ne sukai doguwar waya da Nuriyya. Ya karbi account number dinta ya tura mata, ta mishi maganar tarewa yace mata saiya koma nan da sati biyu sai suyi maganar. Badan bashida wajen da zai ajiyeta ba, sai dan har zuwa lokacin bai fadama Waheedah ba. Duk wayar da zasuyi sai yaji zuciyarshi ta doka, hankalin shi baya kwanciya sai yaji tana mishi hira, gani yake kamar wani daga cikin yan gidansu zai sameta ya fada mata. Duk da zaiso hakan, zasu hutar dashi, amman kuma dukkan zuciyarshi na fada mishi zai kyautu ya fada mata da kan shi. In da zai samu kwarin gwiwar yin hakan. 3

Idan yace ga yanda watan ya wuce mishi da sauri haka yayi karya. Bai taba ganin gudun kwanaki ba sai da yagan shi yana hada abinda yake bukata a yar jakar shi da yammacin juma’a, dan ranar zaibi motar dare ya isa Kano da safiyar asabar. Yasan yau dinne ranar karshe da yake da ita da zai fadama Waheedah ya kara aure, idan bata sani yau ba sai yaje gida gobe tukunna, ba kuma yajin zai iya kallon idanuwanta ya fada mata. Bashi da wannan karfin halin, yanzun kuma yake sanin hakan.

Gefen gadon dakin yake zaune, ya mika hannu ya dauko wayar shi. Lambar Waheedah ya lalubo, basu dade da gama magana ba, ita tasa shi ya tashi ya hada kayan shi, tace karya taho da yunwa, yaci wani abu. Amman abinci ne karshen abinda yake ranshi. Sake kira yayi, ta daga da fadin

“Sadauki… Harka shirya kayan?”

Kai ya daga mata batare da yace komai ba, dan a rayuwarshi ita kadaice take fahimtar shirun shi, da yayi magana da baiyi ba Waheedah takan fahimta, abin ya daina bashi mamaki.

“Menene? Shirun nan naka yana mun yawa kwana biyu. Wani abu yana damunka amman kaqi fadamun ko?”

Numfashi ya tsinci kanshi da saukewa da baisan yana rike dashi ba. Muryarshi na rawa yace

“Magana nake so in fada miki, ba tun yau ba, tun ana gobe zan taho, bansan ta ina zan fara bane Wahee…a karo na farko da bansan yazan miki magana ba, ina nufin kece, komai fada miki nake batare da tunani ba, na kasa yanzun…. Ina so in fada miki har raina amman na kasa”

Ya karashe yanajin wani irin tashin hankali da bai taba tunani ba

“Nice kaman yanda kace… Akwai wani abu da zaka boyemun? Ka fadamun dan Allah… Menene?”

Kai AbdulKadir yake girgizawa, yanayin muryarta ya kara sakawa yaji komai ya kwance mishi

“Bansan ya zan fara ba”

Shiru tadanyi na wasu dakika kafin tace

“Sadauki kana tsoratani, cikine a jikina ko ka manta? Ka fadamun dan Allah”

Wannan karin hannu yasa yana dafe kan shi, bugun zuciyarshi na karuwa, sauke wayar yayi daga kunnen shi yana kashewa. Kafin ya rasa kwarin gwiwar da yakeji ya bude shafin tura saqo ya fara rubutu

‘Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan yazan fada miki ba’ 11

Ya tura yana jin kamar yabishi ya kamo, sai dai kamar auren shine, ya riga da ya faru, babu damar komawa baya ya canza komai, sakon ya riga ya shiga dan ya nuna mishi alama Waheedah ta samu, zufa yakeji a duk wata kafa ta jikin shi yana jiran ganin sakonta. Da hasken wayar ya dauke sai ya sake tabawa, bai san ya dauki mintina talatin yana jiran sakonta ba saida ya duba lokaci. 2

‘Dan Allah kice wani abu Waheedah, ki ce wani abu’

Nan ma saida ya kara mintina goma yana zufar da duk iskar fankar dake dakin bata kai mishi kafin yaga wayar shi ta kawo haske. Jikin shi babu inda baya rawa ya daga yana dubawa.

‘Ran daren da zaka tafi? Wata daya daya wuce kenan ko?’

Da sauri ya fara bata amsa

‘Da gaske Wahee, ki yarda dani tun ranar naso in fada miki, tun ranar’ 1

Wannan karin bata dauki lokaci ba ta turo mishi

‘Karka damu. Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, bari inyi alwala naji an fara kiran Magriba’ 20

Wata irin ajiyar zuciya AbdulKadir din ya sauke, kafin ya sake ganin text dinta

‘Allah ya tsare ya kawo mana kai lafiya, ka daici abinci karka manta. Zan sa chargy an kawo wuta, saura 2%’ 3

Da murmushi a fuskarshi yace

‘Nagode, Nagode sosai. In shaa Allah. Ki kulamun da ku. Zan kiraki dana shiga mota’ 4

Ya sa ran amsa koya take, dayaga bata turo komai ba ya mike yana hakura. Wanka ya shiga yayi ya fito ya sake kayan jikin shi tukunna ya fita masallaci. Saida ya biya ya siya abinci yaci, hankalin shi yakeji ya kwanta sosai. Yasan daman idan kowa bai fahimce shi ba, Waheedah zata fahimce shi, shisa take da matsayin da babu wanda yake dashi a rayuwar shi. Yana dawowa jakar shi ya dauka yayi addu’a a bakin kofa kafin ya fita ya kulle gidan yana takawa zuwa gate da zai samu yaje inda zai hau machine zuwa tasha…!Wayar tasa a chargy kamar yanda ta fada mishi, sai dai ta kasa dagowa daga tsugunnan da tayi. Wayar take kallo tana gane asalin ma’anar ‘Yawo kan gajimare’. Duk da ba zatace ga ranar da wuyanta ya gajiya da daukar nauyin kanta ba, yau kan jinshi take kamar baya jikin ta, gashi yana mata tamkar iska ta cika shi tana fita ta hancinta da kunnuwanta har ma da idanuwanta. Kafin kan nata yai wata irin sarawa cike da fahimtar ma’anar 10

‘Aure nayi ana gobe zan dawo Waheedah, bansan ya zan fada miki ba’

Da kuma abinda hakan yake nufi a rayuwarta, numfashinta takeji yana barazanar kin wuce kirjinta yakai inda zai ba zuciyarta damar cigaba da dokawa yanda ya kamata. Wani irin numfashi take ja a wahalce, a karo na farko a rayuwarta da tashin hankalin da takeji yafi karfin hawayenta. 12

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un”

Ta samu furtawa tana zama sosai kafin taja kafafuwanta ta dora kanta a sama ko zataji saukin zafin da zuciyarta take mata, lokacin da ta fara laulayi jinta take a wata duniya ta daban, duniyar da wanda ya taba shiga halin da ta tsinci kanta ne kawai zai fahimta, bata san akwai duniyar da zata shiga tafi waccen wahalar sha’ani ba sai yanzun. Ciwo take ji daya wuce fatarta da jininta zuwa cikin kasusuwan jikinta. Idan tace ga asalin abinda ya fi mata ciwo karya take. 3

Auren da yayi da batada darajar da zata sani kafin a daura shi, kallon idanuwanta bayan an daura din dayi mata murmushi kamar babu wani abu mai muhimmanci da yake tunanin ya kamata ya sanar da ita, ko kuma zabar ya fada mata abinda ya canza rayuwarta da ta tashi ta sakon waya. 1

“Banda daraja har haka a idanuwanka Sadauki? Ban nuna maka farin cikin ka na da muhimmanci a wajena bane da zai isa in baka goyon baya akan kowanne irin al’amari ba?” 3

Waheedah take maganar kamar zararriya, dan batasan a fili takeyin ta ba, ta dai san daga wani bangare na zuciyarta mai ciwon gaske maganganun suke fitowa. Bata san iya lokacin da ta dauka a zaune tana kallon bango batare da tasan asalin abinda take tunani ba, banda wani irin ciwo da bata tunanin akwai abinda yake da maganin shi batajin komai. Kamar a wata duniya da ta jima da bari take jin wayarta na ruri, dakyar ta iya raba idanuwanta daga bangon da take kallo tana sauke su akan wayar 1

‘Sadauki’

Ta gani rubuce a jiki

“Me kake so dani Sadauki?” 2

Ta tambaya tana kallon wayar harta yanke, wani sabon kiran ya sake shigowa. Hannu ta mika ta zare wayar daga chargy tana dannawa ta amsa kiran hadi da karawa a kunnenta da wani irin sanyin murya tace

“Hello…”

Tana mike kafafuwanta da sukai mata sanyi, ga abinda ke cikinta da taji ya dunqule waje daya kamar yana tayata daukar ciwon da takeji, hakan nasata fahimtar wani irin ciwon mara da batasan tun yaushe ya fara mata ba.

“Kin fara bacci ne?” 2

Kai ta girgiza mishi a hankali, a karo na farko da taji muryarshi na kara mata ciwo, taji da magana dashi gara mata kallon bangon da takeyi, shi baya kara mata ciwo, amman muryar AbdulKadir din kamar gishiri a sababbin ciwukan da yaji mata takejinta. 1

“Na sa chargy ne”

Dan jim yayi ta dayan bangaren kafin yace

“Inata kira tun dazun babu network”

Sama-sama take jinta, komai na mata wani iri

“Har kun taho?”

Ta tsinci kanta da tambaya

“Tun dazun, amman cunkoso har yanzun muna cikin Lagos”

Kai ta jinjina mishi

“Allah ya tsare maka hanya ya kawo ka lafiya”

STORY CONTINUES BELOW


Amsawa yayi da

“Amin…”

Yana dorawa da

“Ki kula da kanku” 1

Ita ta jinjina kan tana kasa cewa komai ta sauke wayar daga kunnenta, chargyn ta mayar, dakyar ta iya mikewa, wani irin jiri daya dibeta yasa ta koma tana kiran sunan Allah duk wanda ya zo bakinta. Numfashi take fitarwa a wahalshe, ciwo take ji da bazai misaltu ba, tafi awa daya a zaune kafin ta iya mikewa, Fajr ma bata iya ta matsar dashi gefe ba, ita taja jiki kan katifar ta kwanta gefen shi. Ko sallar isha’i batayi ba, amman ciwon da takeji ba zata iya zuwa bandaki har ta iyayin alwala ba. Daga kwancen ma jiri take ji. Bata san dare yayi ba sai lokacin da ta samu ta sauko daga gadon ta dauki wayar ta taga karfe daya. Ajiyewa tayi har lokacin jiri takeji. 2

Ga ciwon marar da takeji ya tsanantar mata, ga wasu ciwukan daban da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, amman mararta da zuciyarta su tafi ji. Bango ta dinga bi har takai bandaki, dakyar ta iya daura alwala ta fito. Daga zaune tayi sallah dan ba zata iya tsayuwar ba, azkar ta gabatar na bayan sallah, tana kwanciya anan kan kafet din dan ko addu’a bata iyayi ba. Sunayen Allah duk wanda yazo bakinta fadin shi takeyi ko zata samu saukin azabar da takeji. Akan kunnenta akai kiran sallah na farko, har aka sakeyin wani aka shiga masallaci tukunna ta iya raba jikinta da kafet din. Alwala ta sake zuwa tayi dan batajin ta cikin yanayin da zata tabbatar tana da alwalar. 1

Ta shiga wata duniya mai wahalar misaltawa. Sallah ta dawo tayi, tana sake komawa ta kwanta kan kafet din. Sai yanzun takejin dama ta kira Yassar jiya ya dauki Fajr, dan ko wanka ba zata iya mishi ba, ballantana abinda zata bashi yaci. Wajen shidda na safe ko motsin kirki bata iyayi, ga wani irin zazzabi mai zafin gaske daya lullubeta. A haka AbdulKadir ya shigo ya sameta, dan shi ya dauka bacci takeyi da yaita sallama yaji shiru.

“Waheedah…”

Ya kira yanajin gabanshi yayi wata irin faduwa, da sauri ya karasa yana tsugunnawa ya dagota, jikinta da yaji kamar garwashin wuta yasa shi fadin

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Yana dorawa da

“Baki da lafiya? Tun yaushe Wahee? Me yasa baki fadamun ba?” 6

Dakyar ta iya bude idanuwanta ta kalle shi, da gaske kara mata ciwo yakeyi, daga muryarshi har tabatan da yakeyi. Tana ji ya zameta daga jikin shi yaje ya tashi Fajr daya shagwabe fuskarshi cike da bacci zaiyi kuka, ganin AbdulKadir din yasa yaron wartsakewa dukkan shi

“Paapi”

Ya fadi yana riko AbdulKadir din daya kamashi ya sauko dashi daga kan gadon

“Fajr tashi, Omman ka zamu kai asibiti”

AbdulKadir ya karasa maganar yana yin bandaki da Fajr, fuska ya wanke mishi yaga abin bazaiyi ba. Da kanshi yai ma yaron wanka ya goge mishi jiki da towel, kaya yazo ya dauko mishi yanajin dadin yanda komai yake a shirye, baisha wata wahala ba. Yana gama saka ma Fajr kaya da yake ta mishi surutun da hankalin shi baya kai, yaga Waheedah taja jiki dakyar ta mike. Muryarta na rawa tace mishi

“Nikam kabarni da zuwa asibitin nan”

Ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, Fajr ya zaunar kusa da ita, ya koma ya dauko wayarshi dake cikin jaka. Yassar ya kira, sai da ta kusa yankewa tukunna ya daga batare da yace komai ba, jin hakan yasa AbdulKadir fadin

“Hamma banzo da mota ba, Waheedah bata da lafiya kuma…”

Da sauri Yassar din yace

“Subhanallahi, ina zuwa yanzun”

Ya kashe kiran daga can bangaren shi, yana saka AbdulKadir din bata rai, bayaso a kashe mishi waya a kunne, ko kadan abin na bata mishi rai, ya kuma rasa dalili. Wayar ya ajiye kan gado yana karasa ya kama hannuwan Waheedah duka biyun, batayi mishi musu ba. Kasa yai da muryarshi sosai saboda Fajr dake zaune a wajen 2

STORY CONTINUES BELOW


“In tayaki kiyi wanka?”

Kai ta girgiza mishi

“Zan iyayi… Ka rakani bandakin kawai”

Taimaka mata yayi har cikin bandakin, duk da hankalin shi bai kwanta daya barta ita kadai din ba, fitowa yayi yai tsaye bakin kofar bandakin, duk bayan wasu daqiqa saiya kira sunanta duk da yasan babu kyau tayi magana a bandakin. Badon Fajr ba shikam shiga zaiyi, karta fadi a ciki ya shiga uku. Saida yaga ta fito tukunna hankalin shi yadan kwanta, kama hannunta yayi yana janta zuwa gefen gado ta zauna. Da kan shi ya dauko mata doguwar riga da inners ya ajiye mata akan gado gefenta

“Sannu, Bari in hadama Fajr Tea”

Kai Waheedah ta daga mishi, ya kama hannun Fajr din suna wucewa kitchen. Flask ya fara jijjigawa yaji akwai ruwan zafi a ciki, ya samu kofi ya zuba madara da milo ya hada mishi rabi, ya saka sikari yana juyawa. Hannun yaron ya sake kamawa har falo ya zaunar dashi kan kafet yana ajiye mishi kofin shayin, Fajr na kama kofin yaga yana tiriri ya kalli AbdulKadir din

“Bamai zafi Omma take bani ba”

Kofin AbdulKadir ya dauka ya kurbi shayin, babu wani zafin da bazai iya sha ba

“Wanne irin shayine bamai zafi ba Fajr?”

Shagwabe fuska Fajr yayi

“Na Omma…”

Kai AbdulKadir ya jinjina yana ajiye kofin

“Bata da lafiya, sai kasha nawa yau”

Turo baki Fajr yayi

“Baka bani biscuit ba”

Runtsa idanuwa AbdulKadir din yayi, wajen matar shi yake son zuwa ya dubata, yaron yana da rikici, duk karancin shekarun shi baya hana AbdulKadir din zane shi. Kitchen ya koma ya dudduba, baiga inda Waheedah ta ajiye biscuit ba idan akwai kenan. Ya dawo yana fadin 1

“Ni banga biscuit ba”

Narai-narai Fajr yayi da idanuwa

“Kasan Allah idan kaimun rigima zaneka zanyi Fajr. Ka zauna kasha Tea din ka kana jina…” 1

Ya karasa yana juyawa ya koma wajen Waheedah, harta saka kaya, da alama tadanji kwarin jikinta da tayi wanka. Kusa da ita ya zauna yana taba wuyanta, da zazzabi har lokacin

“Shine jiya baki fadamun baki da lafiya ba?”

Idanuwanta ta ware mishi

“Zazzabi ne kawai, zai tafi”

Kai AbdulKadir ya girgiza

“Banaso… Karki karamun wannan, idan baki da lafiya ki fadamun ni dai” 6

Kai Waheedah ta jinjina mishi, ba zata iya doguwar magana ba, kirjinta yayi nauyi, mararta na ciwo har lokacin. Kiran Yassar yagani, hakan yasa bai daga ba ya mike yana ficewa daga dakin da falon gabaki daya. Fajr na ajiye kofin shayin ya bishi da gudu ko takaa babu a kafarshi, yana kara gudun shi ganin Yassar ne, cike da farin ciki yake fadin

“Uncle…”

Daga shi sama Yassar din yayi yana dariya

“Fajr…”

Ya kira yana rike shi a jikin shi sosai

“Zan bika ni”

Kai Yassar ya jinjina

“Tare zamu tafi aikam”

Tukunna ya kalli AbdulKadir da yake mishi murmushi, hade fuska Yassar yayi kamar bashi ya gama dariya ba

“Ya mai jiki?”

Ya tambaya, kai AbdulKadir ya jinjina

“Yanzun kai ma Fajr dariya kana magana muryarka lafiya kalau…”

STORY CONTINUES BELOW


Mukullin dake hannun shi Yassar ya mikama AbdulKadir din yana juyawa tare da Fajr din tunda yana da kaya a gidan. Kyaleshi AbdulKadir yayi ya koma cikin gida suna fitowa tare da Waheedah, da kanshi ya bude mata mota ta shiga ta zauna, ya rufe tukunna ya zagaya ta dayan bangaren, ya tayar da motar, yana ja suka fita daga gidan zuwa wani asibitin kudi na masu ciki da bashi da nisa sosai da gidan.

*

Har azahar suna asibitin, dan ruwa suka saka mata leda biyu. Har Hajja ya kira bata daga wayar ba. Sosai ran shi yaji bai mishi dadi ba, daman ya fada mata ne, sai a turo wani cikin yan gidan da zai tayasu aiki, Waheedah din ta huta. Amman zaiyi komai da zai iya, kuma yaga Waheedah din da sauki, duk da ance ta samu wadataccen hutu, kafin a sallamesu su tafi gida. Magunguna kala biyu ne kawai aka basu, duk zuwan da yake asibitin tare da ita, wannan ne karo na hudu magani sai dai yaga guda daya ko biyu, sam basa tila magunguna.

“Nikam kamar in dinga zuwa asibitin nan in bani da lafiya, sam basa bada magunguna masu yawa”

Ya fadi yana kwance takalman kafar shi, sai da Waheedah ta cire hijabinta tukunna ta kalli AbdulKadir din

“Asibitin masu cikin Sadauki?”

Dakuna mata fuska yayi

“Me yasa sai masu cikine kawai zasu je? Basa bada magani da yawa”

Kai Waheedah ta girgiza

“Dan na masu cikine shisa basa bayarwa da yawa, bakowanne magani ake sha ba in ana da ciki” 1

Kai ya jinjina mata yana fahimta, ita kuwa hannunta take murzawa inda akai mata karin ruwa tanajin yana mata ciwo. Har lokacin ba zatace ga asalin yanda takeji ba, kallon AbdulKadir din kawai takeyi duk inda yayi, kamar tana jira yace mata maganar da sukai daren jiya wasa ne, sai dai tasan akwai maganganun da badon ba’a wasa dasu ba, AbdulKadir dinne dai bazai taba mata wasa dasu ba. Idanuwanta ta lumshe taji yace

“Me zaki ci?”

Budesu tayi a kanshi a hankali

“Taliyar Hausa nake so, zan dafa idan na tashi. Kai me zakaci?”

Dan shiya kamata ta tambaya ma, daya kwaso tafiya, ko hutawa baiyi ba

“Nima ina ci, a ina kika ajiye in dafa mana?” 1

Tun kafin ya karasa take girgiza mishi kai, ita zata shaida dahuwar taliyar shi, narkewa ne kawai batayi ba, amman harshi kan shi bai iya yaci ba, daga ta tafi kitso, tayi miyarta take ce mishi taliya zata dafa, data dawo tunda babu wahala shine ya dafa, ta nadi uban ruwan da ta tabbatar bai tafasa ba ya zuba taliyar

‘Kinga dana dauko daya sai inji kamar ta dahu, amman naga batai fari ba kamar yanda kike dafawa’

AbdulKadir din ya fadi lokacin da ta shiga kitchen din ta samu taliyar kan wuta. Idan ya dafa taliyar hausa tabbas kunu zata koma. 1

“Nagode. Allah ya bada ladan niyya Sadauki. Zan dafa.. Kaje ka watsa ruwa ka kwanta. Baka huta ba”

Kai ya girgiza mata

“Zanyi wanka, nikam banajin bacci. Ke da baki da lafiya, ya za’ayi ki iya dafa taliya…naga yanda kikeyi. Zan dafa nikam… Bari in fito wanka”

Ya karasa maganar yana shigewa daki, bai jima ba ya fito, ya saka riga mai yankakken hannu da gajeran wando. Rigima ce cike da idanuwan shi, barnar taliyar da take bala’in ji da ita zai mata

“Akwai sauran doya, a dafa doya kawai”

Murmushi AbdulKadir yayi

“Baki yarda dani ba ko? To wallahi saina dafa…” 1

Ya fadi yana shiga kitchen din ya dauko tukunya. Mikewa Waheedah tayi tana bin bayan shi

“Sadauki dan Allah nidai kabar shi, zan iya. Kaga zazzabin ma ya sauka tun dazun”

STORY CONTINUES BELOW


Da gasken take tun kafin a cire ruwan farko da ta samu bacci zazzabin ya dauka, ciwon marar ma yai mata sauki. Kirjinta ne dai takejin kamar zai bude da wani irin ciwo.

“Gara ki dauko mun taliya kije ki zauna. Kuma ba wasa nake ba”

Taliyar ta dauko mishi, ta ajiye taja kujerar rubber da take ajiye a kitchen din in zata yanka wani abu tana jin qwiyar tsayuwa ta zauna.

“Ruwan sai ya tafasa”

Tace ma AbdulKadir din ganin duk mintina biyu saiya bude tukunya. Da taimakon ta ya dafa musu taliyar, tana da soyayyen manja da zafi baisa ya kwanta mata ba. A asibitin sukai sallah daman. Dan haka Waheedah taje ta kara watsa ruwa itama ta sake rigar jikinta da takejin tana mata warin asibiti har lokacin tukunna ta fito sukaci abinci. Yinin ranar babu inda ya fita sai masallaci, duk da tana iya kokarinta na ganin jikinsu bai hadu da juna ba, ko hannunta bataso ya rike sai taji ya kara mata ciwon da take ji a kirjinta. Abin har tsoro ya fara bata. Bai mata zancen auren ba, ita kuma tama kanta alkawarin in bai tayar mata da maganar ba, ba zatace mishi komai ba.

Inya tayar mata dinma maganar data fada mishi jiya ita zata maimaita mishi, bata da wasu kalaman banda wannan. Sai da daddare ya samu ya turama Nuriyya text

‘Ya kika wuni? Zan zo sai gobe in shaa Allah. Waheedah bata jin dadi. Zan kiraki goben, ki kula da kanki’ 4

Bai jira amsarta ba yasa chargy ya kwanta gefen Waheedah da duk idanuwanta data rufe bai hana shi kakume mata ba. Ta godema Allah da bai jima ba bacci ya dauke shi, amman koya ta motsa sai taji ya sake riketa kamar zai shige jikinta. Ta jima sosai saboda yanda kusancin da yayi da ita yake kara ma kirjinta ciwo, kafin barawon bacci ya saceta.

**

Washegari da karfinta ta tashi, babu abinda takejin yana mata ciwo banda zuciyarta. Doya ta dafa, Anty ta aiko mata da wani yaji mai dadi, lallaba shi takeyi karya kare, tata doyar ta diba dan da mai da yaji takejin ci. AbdulKadir ta soya mishi tashi. Tana gamawa ya fito shikuma suka ci karo a bakin kofar kitchen din

“Ni ban isa ba ko Waheedah? Bazan ce karkiyi abu kijini ba”

Kai ta girgiza mishi

“Yayi kyau, yanzun kuma karya nayi. Me nace miki dana dawo masallaci? Ko shara karkiyi… Amman ban isa ba shisa kika fito” 3

Numfashi Waheedah ta sauke, tasan zaiyi fada daman, amman ta kasa komawa bacci, aikin da ga fito tanayi yana rage mata tunani tunda babu wuta balle ko kallo tayi, ko da wutar ma batajin yin wani kallo ita.

“Kayi hakuri, ba wani aiki nayi ba, doya kawai na dafa na soya”

Yanda tai maganar yasa shi jin wani iri, karasawa yayi yana kama hannunta

“Dan kinga bana iya miki fada shisa kika daina jin maganata” 1

Murmushin karfin hali tayi tana ware mishi idanuwa

“Dan Allah karki karayin komai, ki huta, inkin ji sauki sai kiyi”

Kai ta daga mishi. Ya sumbaci gefen fuskarta, ya dago hannunta yana shafa inda yai ja da alamar hudar zaman allurar karin ruwan da akai mata.

“Sannu…”

Ya furta cike da kulawar da ta ragema kusancin da yayi da ita kara mata ciwon da takeji.

“Zaka karya yanzun?”

Kai ya daga mata, ta dora da

“Ina da zobo a fridge, ko zaka sha Tea?”

Da sauri ya girgiza mata kai

“Yaushe kikayi zobo?”

Hannunta ta zame daga cikin nashi tana bude fridge din ta dauko roba daya

STORY CONTINUES BELOW


“Tun shekaranjiya, da yawa nayi, Fajr duk yamun barnar shi”

Tare suka fita da kayyakin, AbdulKadir a kular ma yaci tashi doyar. Itama tayi mamakin wadda taci dan lokacin da suka zauna ko yunwar bataji. AbdulKadir din ya kwashe kayan tana zaune. Tanajin shi yana ta kwaramniya da kwanoni. Sai daya fito taga hannuwan shi duk ruwa

“Me kayi?”

Ta tambaya

“Wanke-wanke… Har gogewa nayi”

Murmushi tayi mishi da yake ganin kamar bai kai idanuwanta ba.

“Sannu da aiki…”

Amsawa yayi da

“Yawwa”

Yana dan nazarin yanayinta kafin ya wuce dakin. Wayar shi ya dauka ya kira Yassar, yau dinma sai da yayi tunanin ba zai dauka ba tukunna ya daga.

“Ina jin ka”

Numfashi AbdulKadir ya sauke

“Gaba babu kyau Hamma…Kuma yanzun mun girma mu ba yara bane, bai kamata muna irin wannan…” 1

Bai karasa ba saboda Yassar din ya kashe mishi waya a kunne, lumshe idanuwa AbdulKadir yayi yana budesu hadi da furzar da wani numfashi ran shi a bace, wayar Yassar din ya sake kira, wannan karin yana dagawa yace

“Wai meye?”

Numfashin AbdulKadir ya sake fitarwa, zai dauki girman yau, girman da Yassar din ya kasa dauka

“Motar ka daman, in ba zaka bukata ba, zanyi abu da ita”

Dan shiru Yassar yayi

“Me yasa baka zo da taka ba? Wanne abu zakayi?” 1

A ranshi AbdulKadir yayi niyya tun jiya, daya koma akwai abokan aikin shi da zasu taho Kano su biyu satin sama, zai basu motar su taho mishi da ita, yabarta a gida tunda sai yazo yake gane yafi bukatarta anan din fiye da can Lagos. Tunda inba wani dalili ba sunfi fita da motar aiki.

“Da gaske kana son sanin abinda zanyi da ita?”

Murya a dakile Yassar yace

“Inka gama ka dawomun da motata gaskiya”

Yana kashe wayar. A karo na biyu a rana daya daya kashema AbdulKadir din waya a kunne, inda wani ne a gidan ba Yassar ba, kome zaiyi da motar ya hakura, amman shi kan shi Yassar din yasan ba zaiyi zuciya ba. Shi kadai AbdulKadir yake tambaya abu, ya zageshi, kuma ya bashi abin ya karba. Shakuwar dake tsakanin su ta daban ce, Yasir ne suka kwanta a ciki daya a lokaci daya, amman zai iya rantsewa babu shaquwa mai karfi irin wannan a tsakanin su. Dan zai iya kwana biyu ma basu gaisa da Yasir din ba, musamman yanzun da shi yana Katsina, tunda aiki ya mayar dashi can ya samu yar Katsina ya aura.

Falo AbdulKadir ya dawo yana samun Waheedah a zaune inda yabarta. Zama yayi ya zame jikin shi ya kwanta yana dora kan shi a cinyarta. Jin yana gyara kwanciya yasa ta fadin 2

“Karka danne mun hancin yaro Sadauki”

Dariya AbdulKadir yayi

“Yarinya dai”

Shiru tayi ta kyale shi, cikin Fajr ma haka sukai ta wannan gardamar, sai ta haifi namiji. Kuma shi yace bayason sani a asibiti, wannan dinma yace mata ko an tambayesu zasuce basa son sani, sai ta haihu tukunna.

“Ina so in fita, amman banaso in barki ke kadai”

Hannunta ta dora kan fuskar shi, tana jin maganar shi can nesa, da wani yanayi a fuskar ta tace

“Ka fita abinka, naji sauki ai. Ka tahomun da kwakwa inka ganta” 1

Kai AbdulKadir ya jinjina mata

STORY CONTINUES BELOW


“Bacci zanyi yanzun. Sai azahar tukunna, kwakwa kawai?”

Ya karasa maganar yana juya kwanciyar shi, ta daga mishi kai. Baice komai ba ya lumshe idanuwan shi. Kanta Waheedah ta jingina jikin kujerar dake bayanta. Tunani take, amman ba zatace ga ko na menene ba, kawai tasan ta lula tsakiyar wata duniya da bata ganin falonta balle tayi tunanin karshenta.

*

Jikin shi ya mishi nauyi saboda baccin da yayi, dan sai da Waheedah ta tashe shi da aka kira sallah. Hamma kawai yake a mota, harya karasa kofar gidansu Nuriyya yayi parking, gida yake son shiga, amman bayaso su bata mishi rai, kan shi a cunkushe yake jin shi, bayason hada abubuwa da yawa waje daya, tunanin zai iya damun shi. A cikin motar yai zaman shi yana kiran wayar Nuriyya ya fada mata yana kofar gidan. A cikin motar ta same shi, tana zama da wani irin bugun zuciya naban mamaki.

Turarenta daya cika motar na mishi daban

“Ina wuni”

Ta gaishe dashi cike da kunyar da batasan tana da ita ba.

“Lafiya kalau. Ya kike?”

Kanta a kasa tana wasa da yatsunta da suka sha kunshin jan lallen da rashin aikinyi yasa ta daura shi shekaranjiya. Ta mishi maganar tarewa ne saboda zaman gidan ya isheta, kwata-kwata Mama bata hira da ita, gaisuwa ce kawai take hadasu, ko dariya take inta hangota zata daina, Baba ma inta gaishe shi dakyar yake amsawa. Gashi babu damar ta fita daga gidan ballantana ta sha iska. Yanzun ma maganar take sakeyi mishi, amman kunya ta hanata.

“Alhamdulillah”

Ta amsa, AbdulKadir din na tsintar kanshi da kamo hannunta yana wasa da yatsunta da suka sha kunshin da yai mishi kyau sosai. Sai yake ganin hannun ya mishi daban, ko a mafarki bai hango rike hannun wata macen da zata kira kanta da matar shi banda Waheedah ba. Komai bako yakejin ya dawo mishi, duk da hannun Nuriyya din a cikin nashi yasa wani abu tsirga mishi cikin kai yana yamutsa mishi tunani. 9

“Kin shirya ne?”

Da sauri ta dago kanta tana sauke idanuwanta cikin nashi tana kasa yarda da cewar shi din mijinta ne.

“Eh na shirya, amman ban fadama su Mama ba tukunna”

Kai AbdulKadir ya jinjina mata

“Ki fada musu to, saiki kirani inji yaushe… Gobe in shaa Allah zan wuce”

Shagwabe fuska Nuriyya tayi

“Gobe? Da wuri haka Masoyi? Jiya banganka ba”

Kallonta yake, sunan da take kiran nashi dashi na mishi banbarakwai a lokaci daya kuma yana saka mishi wani irin nishadi. Murmushi yayi da yasa gwiwoyin Nuriyya yin sanyi. Tasha ganin murmushin a fuskar shi, amman yaune karo na farko da yayi shi domin ita, wani shauqin kaunar shi taji yana fisgarta.

“In dauko wasu kayan ka tafar mun dasu?” 8

Nuriyya ta bukata da sauri tana dora dayan hannun nata saman nashi, tanajin dadin yanda take da damar yin hakan yanzun. Kai AbdulKadir ya daga mata, ya fada mata inda zata zauna akwai komai, kitchen ne kawai ba kaya. Ta siyi kayan kitchen sosai, kusan abinda tayi da kudin da ya bata kenan, daman akwai sauran kudin kayan dakinta wancen da ta siyar bayan ta fito daga gidan Anas. Da su da sadakinta ta hada ta siyi fridge. Yana gidan Asma’u kawarta, dan duk kayyakin ma ita ta dinga turama kudin tunda sana’arta kenan, siyar da kayan kitchen din. Ta kuma kawo mata komai da ta siya, fridge dinne da babu inda zata ajiye.

Hannun AbdulKadir ta saki tana fita daga motar cike da zumudin kayanta zasu isa gidan AbdulKadir din, itama kuma zata bi bayansu babu jimawa. Ganin ta fara fitowa da kaya yasa AbdulKadir fitowa daga motar ta bude mata boot, yana taimaka mata ta zuba wanda zasu shiga, wasu kuma a bayan motar. Tukunna sukai sallama, yana wucewa gida. Da niyyar inta kirashi ba ranar zata tare ba, saiya tura mata kudin abinci, daman wancen watan bayan tafiyar shi saida ya tura mata kudin abinci tunda tana karkashin kulawar shi, yasan hakan hakkinta ne.

STORY CONTINUES BELOW


A hanya yai la’asar tukunna ya wuce gida. A mota yabar kayan. Yana fara shiga gidan da sallama, a falo ya samu Waheedah, ta mishi wani irin kyau cikin jan lace din daya karbi fatarta, ga jambakin da yake so manne da labbanta tana saka komai kwance mishi.

“Wahee”

Ya tsinci kan shi da fadi maimakon amsa sannu da zuwan da tai mishi. Karasawa yayi ya zauna gefenta kan kujerar yana fuskantarta.

“Ya jikin ki”

Idanuwa ta ware mishi

“Naji sauki”

Numfashi AbdulKadir ya shaqa yanajin komai ya mishi dai-dai.

“Sannu”

Murmushi tayi mishi da yasa yakai hannu yana taba labbanta, yanda baya dangwalo janbakin ta yana bashi mamaki, muryarshi can kasan makoshi yace

“Idan babu matsala zata zauna a gidan nan, bangarena tunda bana amfani dashi” 2

AbdulKadir yai maganar yana sa tanajin kamar tana da zabin da bataga dalilin da zaisa ya bata shi ba, batako hango auren shi ba, gashi dashi yanzun, kamar yanda yake da iko da kan shi, haka yake da iko da gidan shi.

“Banda matsalar komai” 1

Ta fadi tanajin ta sama-sama, kamar gangar jikinta ce a zaune tare dashi. Ruhinta na tsaye a gefe yana kallon abubuwan da suke faruwa kamar bai shafe shi ba. Gyara zama AbdulKadir yayi yana kwantar da kanshi a kafadarta, ita din alkhairi ce a rayuwar shi fiye da yanda zata taba sani. Tasa yanajin saukin abinda ko a labarin da yakeji mai matuqar wahala ne. 1

“Nagode. Nagode da yanda kikasa komai yazo mun da sauki” 1

Batace komai ba, dan batasan me ya kamata tace ba, yakai mintina goma a zaune yayi luf a jikinta, kafin ya tashi.

“Sai ina?”

Ta tambaya

“Akwai kayanta a mota, zan shigo dasu”

Mikewa Waheedah tayi

“Baka fadamun yau zata zo ba, ba’a kara share wajen ba” 1

Dan daquna fuska AbdulKadir yayi

“Bansani ba nima, kayan ne dai kawai. Ba zakiyi shara baki da lafiya ba”

Kai ta girgiza mishi

“Amman a haka za’a saka mata kaya babu shara?” 5

Idanuwa AbdulKadir ya kankance mata, a halin da take ciki ba zata iya karawa da fadan shi ba. Shisa tayi shiru, wajen ta bishi har bakin mota, duk da ya hanata daukar komai. Tsaye tayi tana kallon shi yana kwasar kayan yana kaiwa, jinta take kamar a mafarkin da zata iya farkawa ko da yaushe. Harya gama kwashe kayan tas. Tukunna ya kama hannunta suka koma cikin gida. Harya zauna ya tuna da kwakwar daya siyo mata tana mota, ya sake fita ya dawo da ita a leda. Guda biyar duk sun bare mishi. Mika mata yayi

“Na dauka ka manta”

Kai ya girgiza mata, ya zauna, ita tana mikewa ta nufi kitchen. Guda daya ta wanke, ta saka sauran a fridge, wuka tasa ta huda ta tsiyaye ruwan tana shanyewa ta yanka kwakwar da tasan cikine kawai ya saka mata sha’awarta, dan sai dai in zatayi kunun aya tadan balla, amman ba damunta tayi ba, a cup ta zuba ta dauka tana komawa falo, wuta tagani

“Yaushe suka kawo?”

Ta tambayi AbdulKadir

“Yanzun fa, kina tashi”

Zama tayi, komai a kunne yake, remote din na hannun AbdulKadir yana yawon shiga tashoshi dashi.

“Wahee baki bani kwakwar ba…yau ba kina cin abu baki bani ba”

STORY CONTINUES BELOW


Murmushi tayi mai sauti, duk da batajin wani nishadi

“Yi hakuri… Wallahi na manta ne”

Langabar da kai yayi, bata saba mishi ba, kome takeci tana bashi, bai saba tambayar ta ba. Mika mishi kofin tayi, yasa hannu ya dauka. Kallo suke suna hira jefi jefi har aka kira magriba. Ita tayi daki, shikuma ya fita masallaci. Ya dawo ne ya samu text din Nuriyya

‘Masoyi duk sanda ka tashi kazo mu tafi, na fada musu, na gama hada sauran kayan kuma’ 2

Wayar ya mayar aljihun shi. Yana cewa Waheedah

“Yau zata zo”

Idanuwanta ta ware akan fuskarshi, kafin ta daga mishi kai a hankali, cike da wani yanayi a idanuwanta da yasaka shi karasawa inda take ya zauna, ya kama hannunta yana rikewa

“Wahee kimun magana dan Allah… Ki daina kallona haka… Kimun magana zaifi”

Murmushin karfin hali tayi

“Abinne yake mun bakunta, shine kawai”

Numfashi ya sauke yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, duk da bata saba mishi karya ba, haka kawai zuciyarshi ta kasa nutsuwa waje daya. Baice mata komai ba ya sumbaci hannunta yana mikewa.

“Saina dawo”

Kai Waheedah tadan daga mishi

“Allah ya tsare hanya”

Tana sake kwanciya cikin kujerar. AbdulKadir kuma ya fice daga gidan. Yana motane yake tunanin haka yaso bikin shi da Waheedah, yaje ya dauko matar shi su tafi, babu wannan al’adar na cewa sai an rakota, ya dauka duk sai anyi su Walima da kamu kamar auren shi da Waheedah. Anty Talatu ce take fada mishi, ko da za’ayi wani abin sai dai ko ita Nuriyya in zatai walima, kuma batace mishi zatayi din ba. Hakan yafi mishi, badan zai hanata in tasoyi ba, amman yana ganin daurin aurene kawai ya zama dole, kuma yake da muhimmanci, shi bayason duk wani abubuwa da bai zame mishi dole ba.

Sai dai abinda ya dinga mishi yawo bayan yaje ya dauko Nuriyyan a hanyarsu ta zuwa gida shine yanda Babanta bai bukaci yagan shi ba, ko ita Mama din ma, a tunanin ko za’ayi musu wata nasiha kamar yanda aka saka shi a gaba lokacin auren Waheedah. Sai yaga ta bude mota ta shiga batare da tace mishi iyayenta nason ganin shi ba. Wata zuciyarta sai take darsa mishi ko haka aure na biyu yake, tunda ana ganin babu wata kuruciya a tattare dasu biyun, kuma duk an rigada an fada musu abinda ya kamata a aurensu na farko. 14

*

A hanya ya tsaya dasu yai siyayyar abinda yake tunanin zasu bukata, saboda Nuriyya din, dan yasan Waheedah ba komai ta keci ba yanzun. Ya dai siya mata apple ko zataci, tunda yasan tana so sosai. Tukunna suka karasa gidan. Sai da Nuriyya ta ganta a cikin harabar gidan tukunna taji wata irin faduwar gaba da bata taba tunani ba. Da bata damu ba data fadama su Baba cewar AbdulKadir din yace zaizo su tafi. Su duka Allah ya kiyaye sukai mata batare da sun kara wasu kalaman a kai ba. Ita tana cikin nishadin da fushin da suke da itane karshen abinda yake ranta.

Amman yanzun tunanin fuskantar Waheedah ya dawo mata da komai sabo, wani irin tsoro takeji har kafafuwanta na mata rawa. Da AbdulKadir ya zagayo ya bude mata motar sai da ya mika mata hannun shi tukunna ta kama ta fito daga motar, ya mayar ya rufe, yana sakin hannunta ya bude bayan motar ya dauko dayan akwatinta yana soma jan shi zuwa cikin gidan. Da wani irin sanyin jiki na mamaki take bin bayan shi, tana kallo ya tura kofar yana shiga da cikin gidan da sallama. 1

Amsa shi Waheedah tayi tana mikewa, ta sake kaya zuwa wata atamfa da tafi dazun yin kyau, ga wani irin kwarjini da yaga ta mishi, gidan gabaki daya sai kamshin turarukanta yakeyi da yai mishi dadi.

“Sannu da zuwa…”

Ta fadi, tana ware idanuwanta ganin Nuriyya, harara ta watsa mata

“Sannu Nuriyya”

STORY CONTINUES BELOW


Ta fadi, dan rabon da ta sakata a idanuwanta harta manta, duk da suna chatting kuma suyi waya. Amman batace mata ta dawo ba, tunda ko shekaranjiya ta kirata sun gaisa. Ita kuwa Nuriyya wani irin ras kirjinta ya doka jin kalaman Waheedah din, da kuma harar datai mata. Maganar tata nasa AbdulKadir yaji nashi kirjin ya doka, cikin wani irin tashin hankali ya taka yana kama hannun Waheedah ya soma janta, juyawa tayi tace ma Nuriyya

“Ina zuwa…”

Kafin ta mayar da hankalinta kan AbdulKadir din cike da mamaki. Har bedroom dinsu, sannan ya saki hannunta tana kallon zufar da goshin shi yakeyi.

“Waheedah…”

Ya kira yana jin sauran kalaman sun makale mishi, kallon shi takeyi da irin zufar da yakeyi, kafin wani abu ya sara mata a tsakiyar kai. Lokacin da tayi ma Nuriyya magana taga ta matsa tana boyewa bayan AbdulKadir din har jikinta na taba nashi, batasan me yasa sai yanzun kwakwalwarta ta zabi tayi processing wannan yanayin ba. Numfashi take ja a hankali tana fitar dashi, a nutse takeyin hakan tana son iskar ta isa inda ya kamata. Kafin ta iya kallon AbdulKadir, muryarta na dukan dodon kunnenta da fadin

“Nuriyya…”

Tayi shiru tana sake jan wani numfashin ta tabbatar da kirjinta ba zai bude zuciyarta ta fito ba, tukunna taci gaba

“Nuriyya ka aura?!” 3

Kasa magana yayi, zufa yakeji tana tsatsafo mishi a duk wata kafa da zai iyaji, abin har mamaki yake bashi, tunda zazzabine ruf yaji ya rufe shi duk da zufar da yakeyi. 3

“Ma shaa Allah”

Waheedah ta fadi tana sake kallon shi da fadin

“Kabarta ita kadai” 1

Ya bude bakin shi yafi sau biyar yana mayarwa ya rufe kafin ya iya furta

“Waheedah…”

Dariya tayi da tasa shi sake kallonta

“Sadauki… Kaje…” 3

Badan yana son ya tafin ba, sai dan yana so ya fita daga dakin ko zai ji iska na ratsa shi. Fita yayi yana samun Nuriyya a tsaye bakin kofa kamar mai jiran kyat ta bude tayi ta kanta. Da gasken a tsorace take, dan tana da tabbacin AbdulKadir din ya janye Waheedah ne dan karta far mata. 1

“Muje..” 2

Ya fadi lokacin daya karasa yana kama akwatinta ya dauki sauran ledojin da baisan ya sake su ba, suka wuce har bangaren da zata iya kira nata yanzun. A falo ya ajiye akwatin ya nufi bedroom din tabi bayan shi, ledar ya ajiye yana shiga bandaki ya dauro alwala, itama yace taje tayi. Sallah yaja su sukayi ta godiya ga Allah, kafin AbdulKadir din ya mike ya dauko ledojin yana cire na Waheedah ya fice daga dakin ya nufi bagarenta, kwankwasawa yayi yana turawa.

A tsaye ya sameta tana dauko kayan bacci

“Sadauki…”

Ta fadi, ya karasa

“Apple na siyo miki”

Hannu ta mika ta karbi ledar

“Aikam ka kyauta, dan banajin cin komai” 2

Space din dake tsakanin su AbdulKadir ya hade yana zagaya hannuwan shi ya rungumeta a jikin shi. Zuwa yanzun ya kasa gane ko da gaske lafiyarta kalau ba, yasan Waheedahr shi daban take da duk wasu mata daya taba cin karo dasu. A kaf duniyar shi kuma Hajja ce kawai macen da Waheedah bataiwa nisa ba, duk da haka yanajin kamar ya kamata ta nuna mishi ranta ya baci, ko yaga kishi a idanuwanta, amman ya kasa ganin komai, yana kuma jin kamar tana boye mishi asalin abinda takeji ne. 6

Sosai ya riketa a jikin shi

“Allah ya bani ikon yi muku adalci” 3

Ya furta a hankali yana lumshe idanuwan shi, badan zuciyar shi bata dokawa Nuriyya ba, sai dan yanajin inda Waheedah take babu wanda ya taba hangowa balle harya zauna. Ita din daban ce a rayuwar shi. Hannuwanta Waheedah ta zagaya ta bayanshi tana sake shigewa jikin shi, ta lumshe idanuwanta da yanda takejin zuciyarta kamar da bulallukan tsokoki aka jerata, yanzun kuma rugujewa take ta ko ina, kurar ce take saka jikinta daukar wani irin dumi. A hankali ta zame jikinta daga nashi tana sauke idanuwanta cikin nashi, rankwafowa yayi ya sumbace ta.

“Sai da safe”

Ya fadi yana juyawa, bata iya ce mishi komai ba, harya fice daga dakin yana komawa ya samu Nuriyya da tunda ya fita takejin kamar ta bi bayan shi ya dawo saboda wani irin azababben kishi daya turnuqeta, gani tayi ya dade, zuciyarta har tafasa takeyi, kwana daya take dashi, yace mata gobe zai wuce, Waheedah ba zata bar mata shi ya dawo ba, zuwa yanzun kishi ya maye gurbin duk wani tsoro data shigo dashi gidan. Murmushi tayi tana ganin ya shigo, jikinta ya mutu ganin bai mayar mata da murmushin ba. 27

Karasawa yayi ya zauna gefenta yana kallonta, fuskar shi babu alamar wasa yace

“Bana son tashin hankali, bana son rigima badan ban iya ba, bansan yanda zan daina ba idan na fara. Nasan halin matata tun kafin in aureta, nasan abinda Waheedah zatayi da wanda ba zatayi ba tun kafin insan zan aureta, bansan halinki ko daya ba na aureki, idan har naji rigima a gidana daga wajenki hakan zai fara. 3

Ko baki girmama Waheedah ba idan baki shiga huruminta ba nasan ba zata taba biyema kome zakiyi ba. Zaman lafiyarta na da muhimmanci a wajena, idan har zamana dake zaiyi nisa zaki zauna da ita lafiya…”

Kai Nuriyya ta jinjina mishi a hankali, itama tasan halin Waheedah din, ba saiya jaddada mata ba, wanda duk yake tare da Waheedah yasan halinta, kuma ita bata shigo gidan dan ta nemi rigima da ita ba, duk da tanajin idan Waheedah tai mata ba zataki ramawa ba. Zadai tayi karya in tace idanuwanta basa mata yaji da shirin taruwar hawayen bakin cikin maganganun shi. Wani irin kishi takeji marar misaltuwa, zuciyarta na dan tsahirta mata da hannunta da AbdulKadir din ya kama.

*

Waheedah kuwa AbdulKadir na fita daga dakin ledar apple din ta bude ta dauki guda daya tana shiga bandaki ta wanko ta dawo kan gado ta zauna. Cinye shi tayi batare data gane dandanon shi ko dalilin da yasa takeci ba, kafin taja kafafuwanta zuwa kan gadon ta kwanta akan bayanta, jin kirjinta na shirin budewa yasa ta juya tana kwanciya kan gefen hannunta na dama. Wani abu takeji yana zubar mata, da sauri tasa hannu ta taba fuskarta, amman babu digon hawaye ko daya, kuka take amman daga ciki. 6

Ranar ne ya zame musu MAFARIN komai daya kawo su inda suke yanzun, ranar ne kuma Waheedah taji ta shiga wata duniya da tai nisa da zubar hawaye, duniyar data bata mukullin waccen data bari tana budewa tana zuba duk wani bacin rai da zai sameta ta rufe har zuwa yanzun…! 1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *