FETTA CHAPTER 11

FETTA





CHAPTER 11



Zaune take saman carpet tana gyara kayanta, Tana jera su cikin wardrobe, Yana zaune saman gado ya barbaza takardu yana dubawa, Jefi jefi yana d’ago kai ya kalleta, Dukkan hankalinta na kan gyaran. +

Wayarsa tayi ringing, Yayi receiving, “Ku kula da kyau, Gani nan zuwa”, Shine abunda taji ya fad’a Ya kashe.

“Ke!”, Ta tsani kalmar tayi tamkar bata ji sa ba, ” Fatima”, Karon farko da ya kira sunan ta, sai taji sunan daban a bakin sa, ba kowa ke kiranta haka ba, “Na’am” Ta amsa murya a sanyaye, “Zo”, Ta mik’e taje gabansa, ” Tayani had’a takardun nan”, Ya fad’a yana mik’ewa ya shiga toilet,

Takardu ne masu yawa sosai, Ta shiga had’a su wuri d’aya.

Wanka yayi ya fito, Ya shirya, ya d’auki mukullin mota ya fice, D’akin ya game da k’amshin turaren sa, “Uhmm” Ta fad’a tana sauke ajiyar zuciya sakamakon k’amshin sa da ya daki hancin ta,

Sunayen mutane da wurare ne birjik a takardun, Ta tab’e baki tace “Kamar wani dan’ lek’en asiri”, Ta had’a su ta saka a drawer da taga yana ajiyewa.

 ” Dad please ka taimaka ya aureni, wallahi zan mutu”, Tasleem ta fad’a tana fashewa da kuka, ta dafe zuciyarta, A rud’e ya rik’ota “Sorry My daughter, ba zaki mutu ki barni ba”, Mahaifiyarta taja tsaki tace ” Alhaji wallahi kai ke biyewa yarinyar nan ace abunda take so za’a mata”, “Idan ban mata ba, wa kike so nayi ma ita kad’ai Allah ya bani”, Ta tab’e baki ta mik’e ta bar d’akin,

    Tasleem ta cigaba da tari tana dafe zuciya, Ya kwanto ta jikin shi, ” Bana so kina tada hankalin ki, ba dai Suraj ba”, Ta d’aga kanta sama, “Kin aure shi kin gama, meye amfanin dukiyata idan ba zanyi amfani da ita wurin samar miki farin ciki”, ” I Love You Daddy”, “Love you too My daughter, bana son damuwar ki”, Ta d’aga kai sama cike da shagwab’a.

    Alhaji Suleiman Tambari shine Mahaifin Tasleem, Matar sa d’aya Rakiya, Yana da tarin dukiya bana wasa ba, Kuma Dan’ siyasa ne, Senator ne, Tasleem kad’ai ce yar’sa ya d’auki son duniya ya d’aura mata, Duk abunda take so, shi yake mata.

    ” Ina jaririyar da aka kawo Yau?” Suraj ya tambaya, “Gata ranka ya dad’e”, Matron ta fad’a tana rissinawa, Ya karb’i yarinyar, Kyakkyawa da ita tasha lullub’i, Cike da tausayawa yace ” Waya kawota?”, “Wani mutumi ne ya tsinceta a bola”, ” Ban san sai yaushe mata zasu yi hankali, su daina cikin shege, suna haifar yara suna zubar dasu, Kinsha wahalar rainon ciki wata tara, kin haihu raino ne ba zaki iya ba, wasu na neman haihuwa, yayin da wasu ke zubarwa, Allah yasa mu dace”, Matron tace “Amin”, ” An rubuta details na komai akanta”, “Eh ranka ya dad’e”, ” OK, ina so a yanka rago a saka mata suna Halima”, Ta amsa da “OK Sir, Allah ya k’ara maka arzik’i ya sada ka da alkhairi, samun irin ka da wuya”, Ya amsa da ” Amin”, Ya mik’e yana zagaya orphanage d’in, Yana tambayar yaran matsalolin su, Duk jariran da aka kawo sabuwar haihuwa, Shi ke musu hud’uba, ya saka musu suna a yanka rago.

   
        Hajiya ta aiko tana kiran Fetta, Tazo wucewa, Feena ta saka k’afa, taci karo da k’afar saura kad’an ta fad’i, Tayi saurin rik’e kujera, “Bakya kallon gabanki ne”, Harara ta juyo ta watsa mata tayi gaba, bata da lokacin tsayawa sa’in sa da ita, Su’ad tace” Tabb kinga hararar da ta miki kuwa”, Feena tayi k’yafci tace “Zata san tayi da ya’ wallahi, jira kawai nake Ya Suraj ya auri Tasleem, ta raina kanta”, ” Nima shine burina, zaman gidan nan sai ya gagare ta”, “Wallahi da k’afar ta zata gudu”, Sukayi shewa.

     A d’aki ta sameta, Har k’asa ta duk’a ta gaishe ta, Ta amsa da sakin fuska, Leda ta jawo ta zazzage laces masu yawa, Tace ” Laces ne nasa Suraj ya kawo miki daga Lagos, ki rik’a siyarwa, bai kamata kina zama haka ba sana’a, kinga ba zaki rasa kud’in kashewa ba”,

STORY CONTINUES BELOW


      Cike da farin ciki da mamakin soyayyar da Hajiya ke mata tace “Nagode Allah ya saka da alkhairi amma ki barshi, wallahi ban rasa komai ba, a haka ma Alhamdulillah”, Ta b’ata rai tace ” Meyasa komai nace sai kice a’ah, baki d’aukeni mahaifiyar ki ba koh”, Ta girgiza kai, “Toh idan hakane kada ki k’ara musa mun, gasu nan ki d’auka zan had’aki da mutane, ki rik’a siyarwa”, ” Nag….”, “Kada kimun godiya, Mijinki zaki ma shi ya miki”, Tayi murmushi, Kowanne sai da Hajiya ta fad’a mata kud’insa, da yadda ya kamata ta siyar, Manyan laces ne masu tsada, Ta kwashe duka ta saka a leda, Ta d’auka ta nufi sashen ta.

     Ta kira Aliya ta sanar da ita, Tayi farin ciki, ta mata addu’ar farawa a sa’a, Tana kashe wayar Yasmeen ta shigo, ” Yanzu nake shirin kiran ki”, “Toh Gani nazo, daga school na biyo na kawo miki”, Leda ta mik’a mata tace ” Gashi akwai takarda a ciki bayanin yadda zakiyi amfani dashi”, “Nifah bana son kayan matan nan”, ” Su zasu taimaka miki wurin k’wato yancin ki”, Tayi murmushi burinta Suraj ya gane kuskuren sa,

     “Laces Hajiya ta bani na fara siyarwa”, ” Ina Suke?”, Ta nuna mata ledar, Ta bud’e tana cewa sun had’u, Ta d’auki guda d’aya, sauran tace zata nuna mata friends d’inta, Bata dad’e ba ta tafi.

    Fetta ta shiga kitchen had’a abincin dare, (Suraj baya wasa da girkin Fetta, abinci yake fara buk’ata idan ya dawo gida)

     Tuwon semo da miyar egushi tasha dry fish ta girka, ta had’a zob’o mai dad’i da yaji kayan had’i, Ta jera a dining table kamar ko da yaushe, Ta turare gidan da turaren wuta, Ta sake wanka ta shirya, Tasha maganin da Yasmeen ta kawo mata, A d’aki ta zauna tana tilawar Qur’ani.

      K’amshi mai sanyi da dad’i ya ziyarci k’ofofin hancin sa, Ya Lumshe ido yana jin wata natsuwa na ratsa shi, A duk lokacin da ya shigo gida yakan ji natsuwa, sab’anin wasu lokuta a baya, Ya k’arasa ciki,

     Ta kai ayar k’arshe ta rufe Qur’anin, Ba tare da ta d’ago ba, Tace “Sannu da zuwa”, ” Yawwa”, Ya furta yana kallon ta, tsaf da ita, D’akin ma tsaf babu wata k’azanta, Ta ajiye Qur’anin ma’ajiyar sa, Ta shiga toilet ta had’a masa ruwan wanka,

     Ya watsa ruwa, ya saka jallabiya da ta feshe ta da turaruka, Ya fito yaba ciki hakk’in sa, a ransa ya yaba dad’in girkin.

     Falo ya zauna ya kamo tashar NTA, Ya kalli news.

    Murya a sanyaye tace “Hajiya ta bani sak’o, Nagode Allah ya saka da alkhairi, Allah ya k’ara bud’i”

     Sosai yaji dad’in addu’o’in, Bilkisu duk kyautar da zai mata bata tab’a masa godiya, idan ta hannun Hajiya ne bata nuna mishi tasan yayi, Ko su Feena dake k’annen sa idan ya musu abu, highest suce Nagode,

      “Ameen”, Ya furta yana mik’ewa, D’aki ya shiga ya fito da kwalin waya, Saman cinyarta ya d’aura ” Zata taimaka miki kiyi promoting business d’inki”, D’aukar wayar tayi taje gabansa, “Ka barshi, wannan ma ta ishe ni”, ” Tana WhatsApp ne, bana son kilibibi tashi ki bani wuri”, Jiki a sanyaye ta mik’e, “Allah ya biya”, Bai amsata ba, ya cigaba da kallon sa,

     D’aki ta shiga, ta bud’e wayar, IPhone X Max, Baki ta bud’e sanin tsadarta, ” Ina ni ina wayar nan, ban ma iya operating d’inta ba”, “Yasmeen idan tazo ta koya miki”, Zuciyarta ta fad’a.

    Tana shirin bacci ya shigo d’akin, Ya saka ma k’ofa key, Hakan na nufin anan zata kwana,

” Kada ki k’ara kwana falo”, Ya fad’a ba tare da ya kalleta ba, Ya nufi gado ya kwanta, Ya jefo mata bargo,

   “Anya baka shiga hakk’inta kwana da take a k’asa”, Zuciyarsa ta fad’a mishi, ” Toh a gado d’aya zamu kwanta”, Yacewa Kansa, “Eh amma kana gefe tana gefe, kasa abu tsakiyar ku”,

    Bedside lamp ya kunna, ” Taso ki hau gado”, Da mamaki ta d’ago tace “Nan ma ya wadatar”, ” Bana son musu”, Ta mik’e, Bargon ya karb’a ya nannad’a yasa tsakiya, “Idan kika tsallako nan”, Ya nuna wurin sa, ” Zaki fuskanci hukunci”

     Extreme end na gadon ta kwanta, tana jin ta a takure, A haka bacci ya d’auke ta, Suraj shima bai d’auki lokacin ba yayi bacci.

     *5:45am*
  
    Bargo tuni sun wancakalar dashi gefe, Sun mannewa juna, Hannun shi rik’e da ita, itama nata rik’e dashi,

    Kiran sallar asuba, ya farkar dasu a tare, Idonsa cikin nata, Da sauri ya janye hannun sa yayi baya, itama ta janye nata tayi baya,

      “You! Meye tsallako dake nan, had jikina”, ” Kaine ka tsallako”, “Kar ki raina mun hankali”, ” Allah Kaine”, “In ganki a jikina kice nine”, ” Kaima ka rungume ni ai”, “Ke nine na rungumen ki”, ” Eh wallahi”, “Meye kai hannun ki jikina”, ” Kai ma meye kai naka”, Haka suka cigaba da musu kowane yana cewa bashi bane,

    Tsaki yayi yace “Wallahi sai kin karb’i hukunci”, ” Ni dai nasan bani bace Allah”, Ta fad’a tana tura baki kamar zata yi kuka, “Kika mun kuka, wallahi hukuncin ki ya k’aru”,

    Tayi shiru tana gunguni, Alwala yayi ya fice masallaci, Ta gabatar da sallar ta a gida.

        Jin motsin sa, Tayi saurin kwanciya kan sallaya, tana matsar k’walla da rik’e ciki,

      Kallo d’aya ya mata yasan pretending take ba wani ciwo, ” Ke tashi”, “Wash cikina”, ” Cikin ki ke ciwo koh?”, Ta gyad’a kai, “Tashi na baki magani”, Ta mik’e tana yatsina fuska, ” Hau gado ki kwanta, yanzu zan baki magani”, Bata gane manufar sa ba, ta haye gado,

     Jinsa kawai tayi a kanta, tayi saurin ture sa, “Wallahi yau bazan yarda ba”, ” Sai ki hana ni”, Kafin tayi wata magana, Ya had’e bakinsu wuri d’aya, Ya shiga sarrafata, Yau yaji ta daban, Ba zai iya fassara yanayin da yaji sa, Taji sa yana sumbatu, but bata rik’e mai yake cewa ba, Dan ba da wasa ya mata ba,

      Sumbatar ta yayi a goshi, Ya mik’e ya shiga toilet, Ya had’a ruwan zafi, D’aukarta yayi cak, tana wuntsila, “Ni ka saukeni wallahi, Dan’ iska”

     Toilet ya direta, Yana k’ok’arin cire kaya, Ta buga ihu sai da ya tsorata, “Wayyo Ku taimakeni, Bana so, Allah ba zanyi wanka tare da kai ba”, Ta shiga bubbuga k’afa, ” Ke!”, Ya dakata mata tsawa, Bata fasa ihu da buga k’afar ba,

   Dole ya fice yana dafe kai “Ya Allah!”, Ya furta, ” Yarinyar nan akwai rigima”,

     “Mugu kawai, Dan’ iska”, Ta fad’a tana murgad’a baki, ” Yasmeen kin cuce ni, bazan k’ara sha ba” 1

     Ta dad’e tana wanka, ta gama tak’i fitowa, Jin bata da niyyar fitowa, Yayi knocking yace “Ki fito, ko na sab’a miki kamanni”, ” Ka sab’a mun halitta ma”, “Ke ni kike fad’awa haka”, Ya buga k’ofar,

    ” Wayyo Allahna”, Ta tsorata a tunanin ta b’alla k’ofar zanyi, “Na baki minti d’aya ki fito”, Tasa kunnenta a k’ofar ko zata ji motsin sa, Jin shiru, ta bud’e, ta gansa tsaye bakin k’ofa, Da sauri ta koma, ya jawota, ta buga ihu, Ya toshe mata baki,

     ” Bana son ihu, yana sani ciwon kai”, Tayi gum, Ya saketa, ya shiga band’aki, Tabi bayansa da harara,

     “Ya Allah!, Hajiya ta had’a ni da aiki”, Ya fad’a, Ya shiga cikin jacuzzi, Ya lumshe ido, yana tunanin moment d’insu na yau.Har ta gama shiri tana gunguni abunda ya mata, Tana jin yana k’ok’arin bud’e k’ofa, Ta fice daga d’akin, +

   Shirin sa yayi hankali kwance, yana jin natsuwa a tare dashi.

    Ta kammala had’a breakfast tana jerawa a dining table, Ya fito yana rambad’a k’amshi, Direct dining area ya nufa, Tana shirin barin wurin,

   Yace “Dawo”, Ta tsaya kanta sunkuye k’asa, ” Zauna”, Ya nuna mata  kujerar dining table, Ta zauna ba musu “Me wannan yake nufi?”, Ta fad’a a ranta, “Serve me”, Plate ta jawo tayi serving d’insa, ta ajiye gabansa,

     ” Serve yourself”, Mamaki ya kamata “Sabon salo”, Ta fad’a a ranta, A fili tace ” Na k’oshi”, Wani shegen kallo ya watsa mata, “Me kika ci da kika k’oshi, bana son kilibibi salon ki rame mutane su zageni koh, Mama tace bana kula dake”,

     ” Shi damuwar sa mutane, komai yana yi dan ya burgesu ba Allah ba”, Tayi maganar ita kad’ai, “Zaki fara ci ko sai na baki huk’unci”, Da sauri ta jawo plate, tayi serving chips da miyar k’oda, ta fara ci ba dan tana jin ci ba,

    Baka jin komai sai motsin cutleries da suke amfani dashi, Ta cika baki da chips bata had’iye ba, tana so ta d’auki lokaci yadda zai rigata gamawa ya tashi, ta ajiye saura,

    Kallon ta yayi yace ” Na baki 5mins naga empty plate”, “Takura kawai”, Ta fad’a a ranta, ta had’iye na bakinta, Kad’an kad’an take d’iba tana ci,

     Ya cinye nashi, yasa tissue ya goge baki, Ya kalli wristwatch dake d’aure a hannun sa, 2mins ya rage a time da ya bata kuma ko rabi bata ci ba,

    ” Kinsan Allah 5mins ya cika baki cinye ba, zaki ga hukuncin da zan miki”, Kamar zatayi kuka tace “Allah bazan iya cinyewa ba, cikina kamar ya fashe”, Murmushi yayi wanda bata gane manufarsa ba Yace ” Na koya miki yadda zaki cinye”, Ta d’aga kai sama dan tasan babu wani koya mata da zai iya,

  Matso ya nuna mata kujerar kusa dashi, Ta taso ta dawo, Fork d’inta ya karb’a, Ya d’iba ya zuba a baki, Cike da murna zai taya ta ci, A ranta tace “Yau yan’ mutuncin na kansa”,

     ” Rufe ido ki bud’e baki”, Tayi kamar yadda yace, Na bakinsa ya juye mata cikin baki, Tayi saurin bud’e ido, Ya kafeta da wani shegen kallo, Ta sunkuyar da kai, ba zata iya jure kallon k’wayar idonsa, Tana k’ok’arin zubawar, yasa hannu ya rufe bakin, Ya d’ago kanta, Ya jefata da kallon gargad’i, Dan dole ta had’iye tana jin kamar ta fasa ihu, “Dan wulak’anci da k’azanta na bakinsa da ya sakawa yawu zai bata taci”

   Haka ya cigaba da sakawa a baki yana juye mata a bakin ta, Har plate ya zama empty, “Duk ranar da nace ki cinye abinci, baki cinye ba haka zan miki” Ya fad’a yana mik’ewa, Ya fice ana jiransa, He is late ma, He suppose to be there by 9;00 and it’s already 9;50am,

     Idonta cike da k’walla, Cikinta kamar zai fashe, “Dan mugunta kasa mutum overload, kuma na bakin ka”, Hawayen da take rik’o suka zubu, ” Ni wallahi na gaji da zama da kai, ka sakeni na koma gidan mu”

     “Waye zai sake ki?” Taji muryar Yasmeen kamar daga sama(Dama jiya ta mata text tana son ganin ta)

     “Shi mana, Allah mugunta yake mun, ga ikon masifa, Ni ya takura ni wallahi”, Ta fad’a tana k’ara had’e rai tana matsar k’walla, “Me ya miki?” Yasmeen ta tambaya cike da damuwa, “Abinci ya rik’a sawa a bakinsa yana juye mun a bakina fah, wai dan ban cinye ba, kiji mugunta da k’azanta”

STORY CONTINUES BELOW


    Yasmeen ta fashe da dariya tace “Inji soyayya dai, Wallahi Fetta dad’i ne ya miki yawa, abun kiyi farin ciki ne Suraj na son ki”,

    Harara ta watsa mata tace ” Kinsan me kike fad’awa kuwa”, Yasmeen tayi nodding kai tace “K’warai kuwa, wallahi Suraj ya fara son ki, me zai sa ya damu da cin abincin ki”, ” Mutane da Hajiya ne baya so suga na rame”, “Ya fad’a ne kawai, so ne kad’ai zai kawo ya baki abinci mouth to mouth”, ” Yasmeen kin cika shirme, ni bara na d’auko waya ki koya mun yadda zanyi operating ” Ta fad’a tana mik’ewa,

    “Inyee yar gatan Suraj, Uwargida kuma Amaryar Suraj, daga ke mun rufe k’ofa”, Tsaki tayi tace ” Ni koya mun please”, Ta kunna wayar tana nuna mata yadda zata yi.

       “Nace kaje ka duba Su’ad ko Safeena wacce ta maka a had’aku aure kayi kunnen uwar shegu” Matar Kawo Lamid’o ta fad’a, Bello yace “Gwaggo Dan Allah ki bar zancen nan, Wallahi Karima nake son ko dan jihadi da zumunci ki barni na aure ta”, Dak’uwa ta masa tace ” Ungo nan dan uban ka, ni zaka jawa abun fad’a a gari, karuwar zaka aura, wacce iyayenta basu san mutunci ba, toh wallahi baka isa ba, kuma a yau nake so kaje gidan Hajiya Tumba ka zab’a cikin yaranta ko na d’aga maka nono”, Kamar zai fasa ihu yace “Toh Gwaggo”, ” Tashi ka bani wuri, daga gani ba banza ba, ko bori suka hau bazan yarda ka aure ta ba”

      Duk kud’insu baya sha’awar auren su saboda rashin tarbiyar su, tamkar ba Hajiya Tumba ta haife su ba, a da ba ruwansu, suna yin arzik’i suka fand’are, shiyasa wasu kud’in masifa ne, Daga Hajiya har Suraj basu san iskancin dasu Feena keyi a makaranta da gari ba, a gabansu yi suke tamkar salihai, nuna bambamci tsakanin talaka da mai kud’i ne basa b’oyewa gaban Hajiya, but harkar samari sam basa nuna mata.

      “SURAJ SA’ID Matashi mai zamanin shi, mai ji da naira da k’uruciya”, Cewar Alhaji Suleiman Tambari yana murmushi mai ma’anoni, ” Honourable masu fad’a aji a garin nan”, Suraj ya fad’a shima yana murmushi, Alhaji Tambari (Kamar yadda aka fi sanin sa), Ya d’auki glass cup na lemo yayi sip d’aya ya ajiye,

     “Meke tafe da kai, nasan zuwan ka akwai dalili mai k’arfi?”, Alhaji Tambari yayi nodding kai yace ” K’warai kuwa”, Ya nisa yace “Duba da yadda kake gudanar da business d’inka successfully ina so muyi wani business tare, ribar sai mu raba”, ” Ban fahimta kuma wane iri?”, “Suraj you are very hardworking, ina neman Matashi kamar ka, da zamuyi business tare, kwangila aka bani na gyara gidan marayu guda 20 naga kai ya dace na saka besides kasan kan orphanage”,

   Suraj ya sauke ajiyar zuciya yasan idan ya amince ba k’aramin kud’i zai samu ba, kuma shi a kullum burinsa ya mallaki kud’i masu tarin yawa, 

     ” Alhaji Tambari nagode da wannan tayi, kuma na amince”, Yayi murmushi yace “But kasan sha’ani na kwangila zaka saka kud’in ka, daga baya su fito hadda riba”, Suraj ya jinjina kai, ” Yaushe kake tunanin zaka fara?”, “Anytime from now”, ” OK sai naji ka”, Ya mik’e ya masa rakiya, Ya dawo yana nazarin kwangilar. 1

     “Yaro yaro ne, na maka gada kana gaf da rufzawa, bana wasa idan akan Tasleem ne, kome ye zanyi dan samar mata farin ciki”, Cewar Alhaji Tambari, Yaja kan motar sa zuwa gida, Shi kad’ai yazo baya so kowa ya fahimci wani abu.

  
      Yasmeen ta bud’ewa Fetta WhatsApp ta saka ta a groups na k’aruwa na aure da girke-girke, da business, Tayi introducing Fetta wurin yan’ group d’in, Dama group ne kowa yasan kowa, Yan’ gayu masu ji da naira ne a ciki, babu hayaniya da k’ananun maganganu, suna mutunta junan su, Dama masu kud’i ba’a cika samun su da anyi ance kowa harkar gaban sa yake, Ta d’auki laces ta tura group, a take aka siye duka, akace ta tura account number, Bata dashi Yasmeen ta tura nata, wasu kuma zasu zo gida su bada kud’i su karb’a, Fetta taji dad’i sosai, WhatsApp d’in ya deb’e mata kewa.

     ” Ashe da gaske yake da yace wayar zata taimaka mata tayi promoting business d’inta”, Ta fad’awa kanta, a zuciyarta tayi appreciating coz ya taimaka mata.

    Shigowar sa ya katse mata tunani, “Sannu da Zuwa”, ” Yawwa”, Ya amsa, 
“Zo kimun tausa”, ” Yau kuma”, Ta fad’a a ranta, kwana biyu ba’a yi ba, Tausar ta dawo dashi gida, Yana zaune gidan gonar sa, yaji yana buk’ata.

       Ya mik’e k’afa, Ta shiga yi masa yana lumshe ido, K’amshin turaren ta na jefa sa a wani yanayi, A kasalance yace “Which perfume kike using?”, Da mamakin tambayar, Ta d’ago kai ta kallesa, ya zuba mata mayun idonsa masu rikita mata lissafi, Ta kawar da kai gefe tace ” Suna da yawa”, Bai sake cewa komai ba, Ya mayar da idonsa ya rufe,

    Ta cigaba da yi masa, Sai da ta fara gajiya, Ta koma yi a hankali, Ya bud’e idonsa ya zuba a kanta, “Kin gaji ne?”, Ta d’aga kai, “Ba ki da baki ne”, ” Eh na gaji”, Ta fad’a a sanyaye, Da hannu ya mata alama ta tafi, Tayi tamkar bata gane nufin sa ba, Yasan ta gane itama so take ya fad’a da baki,

     Da hannu ya sake mata alama, Ta basar, Fisgota yayi ta fad’o jikinsa, Yasa hannu ya zagaye ta, K’irjinta ya manne da nashi, Tana k’ok’arin tashi ya sake matse ta, “Ko ba haka kike so ba”, Ya fad’a yana kallon k’wayar idonta, Kanta ta shiga girgizawa alamar a’ah, Lips d’inta na k’asa ya d’an tsotsa ya saki, Tuni idonta suka cika da k’walla,

       ” Kika bari suka zubo, zaki karb’i hukunci”, Tayi saurin mayar dasu,

     Sai da ya jagalgalata, yana neman wuce wuri, Ta saki kuka, Yatsa ya d’aura saman lips d’inta alamun tayi shiru, Ta sake b’are baki,

     Aikuwa ya cigaba da aiwatar mata da sak’onni, Ta cije sa a baki, Murmushi yayi yace “Ni kika ciza”, Tana sharar k’walla tace ” Ni ban cije ka ba”, “Dole ki karb’i hukunci”, Kayansa ya shiga cirewa, Ta saki kuka, ” Wallahi ko ki kama mun bakin ki, ko nayi round goma”, Ta gumtse bakin,

    Bai barta ba sai da ya fanshe sadakin shi, ya mata hukunci (Ta bakinsa)😂😂

      Ya shige toilet, Ya barta tana fad’in “Dan’ iska jarababbe”, Anya ba zata rok’i Hajiya ta bud’e d’ayan d’akin su raba makwanci, ta gaji da jarabar sa.

        ” Meyasa a duk lokacin da body contact ya had’aku da yarinyar nan, kake kasa controlling kan ka?, Ya tambayi kansa, “Meye sirrin dake tattare da yarinyar nan, anya banza ta barka?”, Wata zuciyar tace ” Amma kuma bata so, da tana da masaniya bara tak’i so ba”, Haka yayi tama kansa tambayoyin da babu mai bashi amsa.

      “Bello yau Kaine a gidan namu”, Hajiya ta fad’awa tana saukowa daga stairs, Ya duk’a har k’asa ya gaisheta, Ta amsa, Tana k’arasuwa falon, ta zauna a kujera, tana tambayar sa mutanen gida, Ya amsa kowa lafiya, Su’ad ta shigo tana yanga, ” Ya Bello sannu”, “Yawwa Su’ad Ya makaranta?”, ” Lafiya”, “Kawo masa ruwa”, Cewar Hajiya,

       Su’ad da Feena na sakar masa fuska, saboda yana da rufin asirin shi daidai gwargado, yana kama kansa, baya son raini, basu cika ganinsa gidan ba.

    Bello bashi da wani zab’i da ya wuce yabi umarnin Mahaifiyarsa, zai gwada Su’ad, Ya cigaba da addu’a idan alkhairi ne Allah ya tabbatar, idan babu alkhairi Allah yasa su rabu cikin sauk’i ba tare da mahaifiyar sa taga laifinsa,

    Tray na ruwa ta ajiye gaban sa, ” Ina son magana dake”, Yayi maganar ta yadda ita kad’ai taji, Nodding kai ta masa, Ruwa kad’ai yasha, Yace “Zai wuce”, Hajiya tace ” Da wuri haka, ka gaida mutum gidan”, “Zasu ji”, Ta koma ciki,

    Ya fita waje, Su’ad tabi bayansa,

    ” Su’ad ina ganin me zai hana mu k’ara k’arfafa zumuncin mu”, “Ban gane me kake nufi ba”, ” Mu had’a hankulanmu mu zama a k’ark’ashin inuwa d’aya”, “Kaga Ya Bello ina ganin mutuncin ka, kada ka bari ya zube, kada ka k’ara zuwar mun da irin zancen nan, ina kai ina aurena, ruwa ai ba sa’an kwando bane”, Tana fad’ar haka ta wuce cikin gida.

   Ko kad’an bai ji haushin furucinta ba, Yasan hakan ne alkhairi, Ya Shiga mota ya wuce.

    ” Sister wai kinsan Ya Bello dan ya raina ni aurena yake son yi”, Feena tace “What yasha k’waya”, ” Hmm samun wuri, yaga ana sakar masa fuska”, “Ke share banza, yau na had’u da wani guy kinga kud’insa”, ” Kice munyi new catch”, Feena tace “K’warai”, Su’ad tace ” Nifah burina na auri mai kud’i sam bana son wahala”, “Nima wallahi sister”, ” Shiyasa nake son Adnan kinga gidansu, da motocin da yake hoto, ya had’u wallahi”, Haka suka cigaba ta tattauna kud’in samarin su.Aunty Jummai da Bilkisu zaune gaban Malamin tsibbu, Yayi zane a k’asa, Ya shafa ya buga, Ya d’ago ya kallesu, Yace “Akwai rikici babban dake tinkaro rayuwar ku”, Aunty Jummai ta zaro ido tace ” Rikici Mallam”, “K’warai kuwa, sai dai bansan yaushe bane amma yana zuwa”, ” Meye abun yi?”, “Toh zaki bada a yanka Akuya ayi sadaka dan neman kariya”, ” Toh babu matsala”, “Ya zancen shi yaron da matarsa, da komawar Bilkisu”, Yayi yan zane ya nisa yace ” Shima akwai rikicin dake tunkaro rayuwar sa, tsakaninsa da Matarsa zasu rabu”, “Malam taya?”, ” Za’a miki aiki, ma’ana ayi farrak’u tsakaninsu yaji ya tsaneta itama taji ta tsane sa”, “Yawwa hakan yayi” +

Ya mata lissafi gaba d’aya zata biya dubu talatin, Ta bud’e jaka ta zaro ta bashi, Kud’in adashen ta ne data karb’a dubu hamsin ta bashi a ciki, Yace ta dawo bayan kwana biyu ta karb’a, Sukayi sallama, Ta tasa Bilkisu suka tafi.

A k’ofar gida taci karo da Sahabi yana zaune kan dakali yana zuk’ar sigari,

“Hajiya barka da zuwa”, Ya fad’a yana busu sigari har ta hanci, ” Lafiya dai Sahabi”, “Alk’awarin da kika mun nazo ki cika”, ” Wane alk’awari aikin da kayi ai bai yi ba”, “Babu ruwana da yayi ko baiyi ba, naje gidan kuma nayi yadda kika buk’ata, naji dumus”, Ya fad’a yana mik’a mata hannu, ” Kaga Sahabi bazan k’ara maka ko naira ba, dan bani dasu”, Yayi wata dariya yace “Jar uba, ai kinyi k’arya wallahi”

Tsaki tayi zata shige cikin gida ya fisgo hijabinta, Bilkisu tasa hannu ta bige tace “Ashe baka da hankali, baka da mutunci”, Ya nuna ta da yatsa ” Ke kama mun bakin ki, uwarki ce sa’ar yi na, zan sab’a miki kamanni wallahi”, Zata sake magana Aunty Jummai ta hana ta tace ta shiga gida, Ta shige ba dan rai yaso ba,

Ta sassauto da murya tace “Wane ne zan cika maka”, ” Dubu goma”, “Kayi hak’uri na baka biyar”, Ya juya k’eya yace ” Goma zaki bani, ko kiga rashin mutunci da tashin hankali wallahi”, “A’ah abun bai kai can ba”, Ta bud’e jaka ta zaro 10k ta bashi, Ya karb’e ya wuce.

” Ohh ni na shiga uku, adashen da na karb’a da dubu goma na tashi” Ta fad’a rai a jagule, (Dama duk mai mugun abu da yawon malamai baya ajiye komai).

Abincin rana jollof rice da pepper chicken, A tare yace ta zauna suci, Abincin sa yake ci hankali kwance yana jin dad’in sa, Tana ci a takure, Ta k’oshi but ba damar ajiyewa sai ta cinye, “Mutum da cikinsa ana mishi iko”, Tayi maganar k’asa k’asa, Charaf a kunnen sa, Ya d’ago ya kalle ta,

” Me kika ce?”, “Ba da kai nake ba”, Ta fad’a tana d’ibar abinci, ” Naji kince ba zai ishe ki”, “A’ah ba haka nace ba wallahi”,

Foodflask ya bud’e, Ya cika serving spoon ya k’ara a plate d’inta, Ta zaro ido tace ” Nifah ba haka nace ba”, Ya d’age kafad’a yace “Naga empty plate, ko ki karb’i hukunci”, Idonta ya cika da k’walla, Ta cigaba da ci cike da takaicin sa, ” Ke da cikin ki ana miki iko, ki nuna masa bashi da iko akan cikin ki”, Zuciyarta ta fad’a mata,

“Ni fah gaskiya na k’oshi”, Ta fad’a cikin dakewa, Ya d’ago kai ya zuba mata mayun idonsa, Kanta sunkuye k’asa tana kallon plate dake gabanta, tana juya spoon, ” D’ago ki kalleni”, Ba musu ta d’ago, idonta cikin nashi, Wani kallo ya jefa mata da ta kasa fassara shi, Ya cije lips,

“Kin k’oshi koh?”, “Eh”, ” Tashi ki tafi, but ki shirya karb’ar hukunci anjima”, “Zanga yadda zan karb’i hukunci, zaka sha mamakina yau”, Ta fad’awa kanta tana mik’ewa, Yabi bayanta da kallon yarinya zaki gane.

Bai k’ara bi ta kanta ba, Ya fice zuwa gidan gonar sa, Office d’insa ya nufa, Yaronsa ya biyo bayansa, Ya kawo masa wani envelope, Yace ” Wani ya kawo yace a bashi”,

STORY CONTINUES BELOW


Ya bud’e ya duba, Alhaji Tambari ne ya aiko da bayanan ayyukan da za’a yi, Ya karanta komai, Yayi estimate kud’insa da zai saka 500million, idan kud’in zasu fito 850million, zai samu ribar 350m, Yayi murmushi mai cika da farin ciki, “Thank You Alhaji Tambari”, Ya furta a fili,

Fetta ta had’a kudad’en laces 270k, Wanda zasu karb’a a gida, sunzo sun karb’a sun bayar da kud’i, Masu turowa ta account sun turo, Yasmeen ta bata kud’in.

Sashen Hajiya ta nufa, Ta sameta ita kad’ai a falo cikin shiga ta alfarma, duk da bata da miji bata fasa gayu ba,

Ta duk’a har k’asa ta gaisheta, Ta amsa, ” Fetta kina lafiya?”, “Lafiya lau”, ” Ina mijin naki?”, “Ya fita”, ” Allah ya bada nasara, ya cigaba da baku zaman lafiya”, Ta amsa da “Amin”, Kar ta zargi wani abu,

” Kud’in laces ne na kawo miki an siya duka”, “Har kin siyar kin karb’i kud’i” Ta fad’a cike da mamaki, “Eh gasu”, Ta mik’a mata, ” A’ah rik’e abun ki naki ne, kina da sa’a Fetta, kin fara a nasara, Allah ya cigaba da shige miki gaba”, “Amin”, ” Ki cire ribar, uwar kud’in kiba Suraj ya siyo miki wasu a Lagos, idan tare zaku tafi, sai ya nuna miki wurin ki siya da kanki”, “Toh Hajiya”, Ta fad’a ba dan son ranta ba, Sam bata son mishi magana, Sun d’an tab’a hira ta koma sashen ta.

*12:30am*

Lokacin ya shigo gida, Fetta tayi nisa a duniyar bacci, Da spare key ya fita, Ya bud’e ya shiga,

Kan gado ya sameta, Tana bacci hankali kwance, ta wancakalar da bargon data lullub’e gefe, Yabi jikinta da kallo, Rigar bacci ce a jikinta, mai shara shara, tana showing jikinta, ya sauke idonsa kan dukiyar fulaninta, tsigar jikinsa ta tashi, Ya kalli fuskarta, tayi fayau, lips d’inta pink tamkar ta shafa musu janbaki, Ya kawar da kansa gefe, ya sauke ajiyar zuciya tamkar mayunwaci.

Wanka yayi, Ya shirya cikin pyjamas, Ya fesa perfs, yabi lafiyar gado, Zuciya da gangar jikinsa ke mitsinar sa, siffofin jikinta na masa yawo a ido, K’ok’arin controlling kansa yake ya kasa, Ya mirgina zai jawota jikinsa, Yayi saurin k’ame hannun sa, ” Idan ta farka ta ganka, zata raina ka”, Yacewa kansa,

Wata zuciyar tace “Ka manta kace zaka bata hukunci”, Da tunanin hakan ya jawota jikinsa, laushin fatar ta ya saka shi, Sauke sanyayyar ajiyar zuciya da k’ara jefa sa wani yanayi, Tuni ya shiga aikata mata sak’onni,

Tamkar a mafarki taji sa, Ta bud’e ido ta zube su kan fuskarsa da idonsa ke lumshe, Kasa aiwatar da wani abu tayi da zai hana sa, Ta sallama, Ya darjeta son ranshi, Bayan ya dawo hayyacin sa Yace ” Kin karb’i hukunci, gobe ki k’ara rashin cin abinci”

Dariya yaso ya bata, ta gano lagon sa, Yana wayon darjeta yace wai hukunci, “Muje ki cud’a mun baya”, Make kafad’a tayi tace ” Ban iya ba”, Ya ganta tamkar k’aramar yarinya, Yayi smiling ya shige toilet,

Kusan Minti 15 ya d’auka, ya fito, Ta shiga tayi wanka, Ko da ta fito, Ya koma bacci, dama bacci ne sosai a idonsa but dan jaraba sai da yayi, Tayi shirinta, Ta kwanta k’arshen gado ta kwanta,

Da asuba manne da juna ta farka ta gansu, Ta raba jikinsu, tana shirin mik’ewa ya tashi, Ba wanda yabi ta kan wani, Kowa ya shiga sabgarsa.

*11:00am*

Tana zaune falo tana kallo, Ya fito yana waya, Zama yayi kan kujera,

“Alhaji Tambari ya bani wata kwangila, zan saka 500million na samu ribar 350million”, Taji ya fad’a, bata ji abunda d’ayan yace ba, ” On my way, idan nazo zamu k’ara tattaunawa”,

“Goge mun k’afata”, Ya fad’a, ” Mutumin nan da tsirfa yake”, Tacewa kanta, Ta had’a ruwan d’umi, ta zuba wani gel na wanke k’afa da ta gani a toilet,

Zama tayi ta kama k’afar ta wanke tass, Ya zuba mata ido yana nazarinta, bata san yana yi ba, Ta gama ta d’auko man k’afa, ta fashe mishi, K’afar ta shiga k’yalli, Shi kansa yaga kyan k’afarshi, Bai mata godiya ba, but daga yanayin fuskar sa zai tabbatar maka yaji dad’i.

STORY CONTINUES BELOW


Ya saka takalmin sa, Ya fice tabi bayansa da kallo har ya b’acewa ganinta, Ta maida kallon ta kan TV, tana sauke ajiyar zuciya.

“Ni Jummai tayi wa Sharri, Suraj ya wulak’anta ni” Yelwa ta fad’a tana jijjiga kai, “Haka zaki barta taci bulus”, Cewar K’anwarta Asabe, ” Yelwa ake wa abu ta k’yale, ai wallahi ta d’ebo ruwan dafa kanta, rikicin dake tunkaro rayuwar ta ba k’arami bane”, “Wallahi ki tada mata hankali, ki hana ta zaman lafiya”, ” Hmm”, Ta fad’a tayi k’yafci.

Suraj ya fito cikin shiri, Da jaka briefcase, tafiyar gaggawa ta same sa zuwa Lagos, A falo ya sameta,

“Zan yi tafiya, ki kula”, (Ki kula da kanki ne yake jin nauyin fad’a, hoo Suraj), Ya ajiye mata kud’i masu yawa gabanta ” Incase zaki buk’aci wani abu”, “Da ka barsu bana buk’atar komai nagode”, Ya mata banza, yana shirin fita ya jiyo muryata ” Lagos zaka?”

Ya juyo yana kallon ta yace “Eh meye?”, ” Dama kud’in laces zan baka, ka siyo mun”, Juyowa yayi ya fice ba tare da ya bata amsa ba,

“Mutum sai girman kan tsiya, meye dan na baka ka siyo mun”, Ta fad’a cike da takaicin halin sa, ” Sai naba Yasmeen ta bayar a siyo mun, bazan bari Hajiya tasan yadda muka yi ba”, Taji dad’in fara sana’ar, kuma bata so Hajiya ta fuskanci wani abu, da ta bari.

Suraj yayi sallama da Hajiya, ta masa maganar Fetta yace ba dad’ewa zai yi ba.

“Taso muje sashen bararojin can mu d’an karta mata rashin mutunci”, Cewar Su’ad, Tasleem tace ” Ina tsoron mutumina”, Feena tace “Yayi tafiya, a haka za’a yi soyayyar ana tsoro”, Tasleem tayi dariya tace ” Bana so yaga rashin mutunci na”, Su’ad tace “Kina da gaskiya”,

Da k’arfi suka turo k’ofar falon, Fetta kallo d’aya ta musu ta kawar da kai gefe, tana cigaba ta danna wayarta,

“IPhone X max nake gani a hannun ta”, Feena tayi maganar k’asa k’asa, Su’ad tace ” Itace wallahi, Ta samu gindin zama fah”

“An nad’e k’afa tamkar gidan uban Mutum, kici rabon ki kafin ki koma inda kika fito”, Su’ad ta fad’a, Wani matsiyacin kallo Fetta ta watsa mata tace ” Dukkan ku albarka d’aya kuke ci, da wallahi hanyar da nake ba zaku kalla ba, na zame muku ciwon ido babu yadda zakuyi dani”

Tasleem tazo gabanta ta tsaya tace “Akwai yadda zamuyi dake, ke mara asali, mara gata har wani k’ima ne dake, kinsan baki dace da Ya Suraj ba, Ubanki kafin ya rasu fah mai gadi ne, matsiyaci”

“Ke! Ki gyara kalamanki, bana d’aukar a zagi mahaifina ko da na raye, balle yanzu da yake kwance cikin k’asa”, ” Idan an zaga me zaki iya”, Cewar Su’ad, “Na ba Mutum ruwan mamaki”, Ta fad’a fuska ba alamar wasa, Sun sha jinin jikinsu da yanayin ta,

Tasleem ta rank’wafo da kanta saitin Fetta, ” Alhaji Tambari shine mahaifina nasan kina jin sunan sa, Yar’ Alhaji Tambari da yar’ Maigadi waye zai yi nasara wurin mallakar Ya Suraj”, Fetta ta d’an tureta tace “Kinyi kuskure kud’i basa siyan soyayya”, Tasleem tayi shu’umin murmushi tace ” Zaki ga yadda kud’i zasu siya mun soyayyar Ya Suraj, Alhaji Tambari baya wasa akan yar’sa zai iya komai akan farin cikin ta, ke muga wanda ya tsaya miki”, “Allah”, Ta fad’a zuciya a raunane, ta fama mata rashin mahaifinta.

Dariya tayi tace ” We shall see”, Ta fice su Feena suka bi bayanta.

Suraj yana isa ya nufi company motocin sa, bayan ya gama ayyukan sa, Ya nufi gida, He is expecting yaji k’amshin turaren wuta kamar yadda ya saba ji, ya manta Lagos yake,

Ya shiga gidan mai k’amshin turaren sa, Dining table wayam babu abinci, unlike Kano da zai tarar da abinci ready, (Neighbour d’insa Yoruba ta daina kawo masa, tunda taji labarin auren sa), Gidan yaji sa so dull, tamkar wani abu is missing ( Nace mata, mace ta gari itace gida)

Yoghurt da ya shigo dashi Yasha ya kwanta, Da k’yar yayi bacci cikinsa na mishi kukan yunwa.

Fetta bacci ya k’auracewa idon ta, kewar Mahaifinta ta dabaibaiyeta, Tayi hawaye na rashin sa da addu’ar sa mishi rahama ubangiji da Mahafiyarta da sauran al’ummar musulmai da suka rigamu gidan gaskiya.

Maganar Tasleem tana mata yawo a kai, Ta tuna maganar Suraj akan Alhaji Tambari, Ta auna maganganun su “Alhaji Tambari ya bashi kwangila zai saka 500million, Tasleem tace zata ga yadda kud’i zai siya mata soyayyar Suraj, Mahaifinta zai iya komai dan samar mata farin ciki,

” Tabbas wani shirin Alhaji Tambari keyi akan Suraj dan farin cikin yar’sa”, Ta fad’awa kanta, “Ina ruwanki can masa”, ” Saboda Hajiya da dukiyar sa ta dogara”, Zuciyarta ta fad’a mata, tare da k’ara ingiza ta kan son taimaka mishi.

“Taya zaki taimaka mishi?, Wane evidence kike dashi?, Ya zaki gano ainihin shirin su?” Ta jefowa kanta tambayoyin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *