ABDULLKADIR CHAPTER 2

ABDULLKADIR





CHAPTER 2




Maballan rigar shi ta makaranta yake ballewa, yana saka hannu a aljihu ya ciro links dinshi, kasancewar rigar mai dogon hannu. Hajja ce ta fito daga daki tana kallon shi

“Dogo dan baban shi, sojan gidan Bugaje…”

Ta fadi da alamun zolaya, kayataccen murmushin da bako yaushe ake gani ba Abdulkadir yai mata. Yan gidan Bugaje suna da tsayi babu laifi daga mazan har matan, dan gajerun cikin gidan basu wuce su hudu ba, amman tsayin da Abdulkadir yake dashi har mamaki yake basu, duk manyan yayyen shi tsayinsu daya dashi, gashi lokacin banda ball da yake yi har motsa jiki yake zuwa, gidan kaf babu wanda baisan burin Abdulkadir shine zama soja ba. Tun yana da karancin shekaru yakan ce shi soja zai zama, tun suna daukar abin kuruciya harya fara tasawa yana cigaba da jaddada musu kaunar shi da aikin soja, ko a hanya yagan su sai yaje sun gaisa.

Ganin nasu baya mishi wahala tunda akwai barikin sojoji tanan kofar ruwa, ga abokan shi biyu Imran da Nawaf duka iyayen su sojojine, abinda ya kara danqon zumuntar su kenan da Abdulkadir.

“Hajja…”

Ya kira, sun gaisa daya dawo daga sallar asuba, shi bazai iya wannan wahalar ta sake sabuwar gaisuwa ba kuma. 4

“Har an shirya?”

Kai ya daga mata yana dorawa da

“Me kika dafa? Wai Mama koko fa tayi mana da safen nan…”

Dariya Hajja tayi, dan ita bata ma jima da tashi ba, ruwan shayi ta dora batajin ko tafasa yayi

“Sai dai in zaka sha shayi…ban jima da tashi ba nima…”

Daga ido yayi yana kallon agogon da yake dakin hadi da girgiza mata kai

“Naci wani abu idan na fita makaranta…”

Zahra ce ta shigo dakin tana saka Hijab dinta, bata kula da Abdulkadir da yake tsaye ba ta kuwa bangaje shi 1

“Subhanallah…”

Ta fadi tana jan hijab din ta saka ta dakyau, wani irin mari ya dauketa dashi da yasa Hajja karasawa tana riqo Zahra da ta fashe da kuka tana fadin 3

“Wallahi Hamma banganka ba…”

Kallon shi Hajja tayi

“Me yasa kake da saurin hannu ne haka Abdulkadir? Zata tureka ne idan taganka…”

Zame jikinta Zahra tayi daga rikon da Hajja tayi mata, kuka take sosai dan ta maru yanda ya kamata, Abdulkadir take kallo daya kafe idanuwan shi akanta yana qarasa saka link din dayan hannun rigar shi

“Ina kwana…”

Ta fadi muryarta can kasa, girar shi ya daga duka biyun

“Abdulkadir…”

Hajja ta kira, yi yayi kamar baiji me tace bama, hankalin shi na kan Zahra

“Ki saki ranki ki gaisheni, fada muke?” 5

Kai ta girgiza tana share hawayen ta, muryarta ta gyara tana sake fadin 9

“Ina kwana”

Murmushin gefen fuska yayi

“Kin tashi lafiya?” 1

Dakyar tace

“Lafiya kalau…”

Tukunna ta wuce daki, safa tazo ta dauka daman, dan girkin Mama ne duka suna dakinta zasu karya acan. Alhaji Ahmad Bugaje mutum ne tsayayye, ba zaka rasa rikici a gidanka ba koda mata daya ka ajiye, ballantana har hudu, sai dai suna kokarin duk wani rikici da zai faru a tsakanin su baya karasawa kunnuwan shi sai dole. Duk abinsu suna shakkar bacin ran shi, shisa aka samu wadataccen hadin kai a tsakanin yaran, dan suna son junansu sosai. Ko a makaranta babu wanda yake taba daya daga ciki, su dukan su zaka gani a saman kanka kaman kudan zuma. Girki a hade sukeyi, sai dai ko in kanason dafa wani dan abin ka dafa a dakinka. Amman duk mai girki zaiyi da duka yaran gidan a dakinshi zasuje suci abinci daga safe har zuwa dare. 4

STORY CONTINUES BELOW


Zahra na barin wajen, Abdulkadir ya juyo, fuskar shi a daqune yake kallon Hajja

“Kina mun fada a gaban ta, kina so su rainani ne Hajja? Ya zata shigo daki fuskarta lillibe da hijab? Meyasa ba zata tsaya ta saka ba tukunna ta shigo? Shine zakimun fada a gabanta…” 15

Hararshi Hajja tayi tana fadin

“Kai yanzun me kakeyi?”

Sake daquna fuska yayi

“Nidai bana so…” 1

Yace yana sa hannu ya dauki jakar shi ya saqalota yana rataya hadi da juyawa ya fice daga dakin. Harabar gidan ya fita inda babbar motar da ake kaisu makaranta gabaki dayansu take, shekara daya dai ta rage mishi ya gama makarantar nan ya huta da saka uniform, duk da ba wasu shekaru ne dashi ba, yana cikin ta goma sha bakwai ne, amman tsayin shi yasa ana tunanin ya girmi shekarun shi. Bakin motar ya tsaya, yasa hannu a aljihu ya ciro agogon shi, bakwai da kwata 1

“Duk yaran da yasa nayi latti sai naci uban shi wallahi”

Ya fadi a fili yana daura agogon, duk da shi yake rike da muqamin mai horar da dalibai na makarantar bazai hana principal dinsu yarfa shi gaban yara idan ya makara ba, duk da zai huce a kansu bayaso dai, duk wani abu dazai ja a ci mishi mutunci a gaban yara a makarantar yana guje mishi. Danma ba daliban da suke kasan shi ba, har yan ajinsu shakkar Abdulkadir suke, banda Imran da Nawaf babu mai tinkarar inda yake kai tsaye, dan su kadaine abokan shi nahar wajen makaranta, daman abokai hudu kacal gare shi, sauran biyun Anwar da Tijjani, unguwar su daya, islamiyyar su ma daya, duk tare suka tashi.

Amatullah,Nusaiba, Nabila da Kabir ya hango suna karasowa wajen.

“Ke kaman Hamma Abdulkadir ne tsaye fa…”

Nabila ta fadi, tana saka Nusaiba kallon wajen a firgice

“Inalillahi… Karfe nawa?”

Nusaiba ta tambaya, duk da tsiran sati biyune tsakaninta da Abdulkadir din, ajinsu daya ma a makaranta, amman hakan baya hanashi jibgarta. Babu mai agogo a cikinsu balle ya amsata. Sa’adatu kuwa kallon Kabir tayi

“Kabir dan Allah ce duk su fito…”

Juyawa Kabir din yayi da gudu, su kuma suka karaso wajen suna gaishe dashi a tsorace, amsawa yayi, da sauri suka shiga motar suka sami waje suna zama, Zahra ce ta fito itama, fuskarta a kumbure da kukan da tayi, ga shatin yan yatsun shi nan kwance saman fuskarta, ko da ta shiga motar babu wanda ya tambayeta, duk sunsan bazai wuce Abdulkadir ba. Ba kullum yake binsu a tafi makaranta haka ba, ranakun duk da yahau machine yai gaba abinshi ransu wasai, motar kamar zasu tasheta da hira, in kuwa yana ciki ba zakaji bakin kowa ba.

Kabir bangaren Mama ya nufa, duk suna falon nata, wasu na daura takalma, wasu na saka safa

“Wallahi Commander ya fito…” 13

Ya fadi yana dariya, Commander shine sunan da suka laqaba ma Abdulkadir din, suke kuma kiran shi dashi a bayan idon shi. Basu jira karin bayani ba da gudu suka kwasa, wani takalmi daya a hannu suna fita. Kusan a tare suka karasa suna maida numfashi 2

“Wanne rashin hankali ne wannan?”

Abdulkadir din ya tambaya yana kare musu kallo

“Ina kwana Hamma…”

Suka fadi kusan su dukan su, madadin tambayar dayai musu, tsaki kawai yaja yana bude gaban motar ya shiga. Suma soma shiga sukayi, tukunna Waheedah ta karaso wajen, hijabinta a hannu ko sakawa bata samu tayi ba. Gabaki dayansu Sheikh Bashir sukeyi. A bangaren Waheedah banda sunanta daya banbanta da nasu ko ita da kanta da ba zata taba sanin ba Alhaji Ahmad bane mahaifinta, balle kuma yan makarantar su, da rana daya bai taba nuna mata cewar bata fito daga jikin shi ba, kuma a cikin gidan ma babu wanda ya taba daga mata kai akan zaman agolancin da takeyi. Sai kuma kalarta ta banbanta data su, fara ce har shiga ido takeyi, sukan tsokaneta da cewar da taku daya ta gujema zuwa duniya a zabiya, duk da suma akwai fararen a cikin su. 2

STORY CONTINUES BELOW


Zata iya cewa ta fara sanin labarinta ya canza ne a ranar, lokacin tana aji uku a sakandire, a gaban motar tagan shi a zaune, duk da gefen fuskarshi tagani saida zuciyarta tai wata irin dokawa da batada alaqa da tsoron shi da kusan su dukansu sukeyi. Yanayine da ba zatace ga lokacin daya fara ba, ko muryarshi taji sai zuciyarta ta fara doka mata irin hakan, dan zata rantse wasu lokuttan har wani gashi ne yake miqewa a bayan wuyanta. Jikinta da wani irin yanayi ta saka kafarta a cikin motar, dariya taga sunayi mata kasa-kasa, motar ta cika taf.

“Ku matsamun…”

Ta fadi cikin sanyin maganarta

“Babu waje fa”

Nabila ta amsa ta da murmushi a fuskarta, a raunane Waheedah ke kallon su, tana sauke idanuwanta kan Nazir da yake zaune a gefe, hararata yayi yana fadin

“Tab…”

Yazid da shine zai kaisu ya karaso wajen motar, cikin sanyin halinta ta gaishe dashi, ya zagaya ya bude gaban motar ya shiga yana mayarwa ya rufe

“Wai waye bai fito bane?”

Abdulkadir ya tambaya yana juyowa, Waheedah yagani tsaye

“Uban me kike da ba zaki shigo ba?”

Idanuwanta taji sun ciko da hawaye, ga zuciyarta naci gaba da dokawa da wani irin yanayi da bata da kalaman fassara shi

“Babu wajene anan din…”

Kabir ya amsa mata

“Baga waje anan ba?”

Abdulkadir ya fadi yana kallon su, hannu Nazir ya saka yaja murfin motar ya rufe, dan babu yanda za’ai ya koma gaba, bazai zauna waje daya da Abdulkadir ba. Karma yaga shine a gefe yace ya tashi ya koma, ita Waheedah da bata fito da wuri ba, ita zata zauna kusa dashi, tsaye tayi a wajen tana rasa yanda zatayi. Ba zama waje dayan dashi bane tashin hankalinta, luguden da zuciyarta takeyi duk idan ya wuce ta gabanta ma kawai, balle kuma ta zauna ga kugunta ga nashi tana jin kusancin shi. Tunda take shine namiji na farko da batasan meyasa take jin hakan akan shi ba. 4

Hannu Abdulkadir yasa ya bude murfin motar

“Idan bakina ya sake magana sai ranki ya baci”

Batasan lokacin da kafafuwan ta suka motsa zuwa gaban motar ba, tana ganin ya kara matsawa, shiga tayi jikinta a sanyaye, kafin ta zauna ta dora hijab dinta kan cinyar shi tana rufo murfin kofar tukunna ta zauna a takure, tasa hannu tana daukar hijab din nata

“Baki ga inda zaki ajiye ba sai a jikina?” 2

Kai ta girgiza mishi, karamin tsaki yaja yana gyara zama, farinta yake ji yana shigar mishi idanuwa, a dakinsu shida Babban Yayan su Muhsin ne baqaqe, shi yadanfi Muhsin hasken fata ma, amman farin Waheedah na mishi wani iri, duk inya ganta tana kara saka shi yanajin yanda babu abinda zai hada mishi hanya da auren farar mace, ko kadan basa burgeshi. Hijab din ta dayasha guga ta warware tana shirin fara sakawa

“Idan kika bigeni sai na mareki Waheedah, bansan iskancin dazaisa ba zaku saka hijab tun daga gida ba…” 2

Yazid dake tuqi ya girgiza kanshi yana murmushi

“Wallahi ka cika shegiyar masifa…”

A hasale Abdulkadir yace

“Hamma banaso…”

Waheedah kuwa hannuwanta ta sauke tana rike da Hijab din, numfashin kirkima ba sosai take yinshi ba, kar yaji iskar ta mishi yawa a kusa dashi ya sauke mata wata masifar tashi da bata karewa. A haka suka karasa makarantar babu wanda yake ko motsin kirki. 2

**

Kitchen din Mama ta shiga, tana bude katuwar kular data zuba abincin a ciki taga ko rabi ba’a diba ba. Jinjina kai tayi

STORY CONTINUES BELOW


“Kunma kanki Wallahi, gaba takaini”

Ta fadi tana dauko wasu manyan robobi masu murfi guda uku ta soma rage dafadukar shinkafar a ciki. Daman bayan sun tafi makaranta, tunanin abinda zata dafa takeyi, tana bude fridge taga bata da cefane, dubu uku Abba ya bata kafin ya fita, zubin adashi zatayi da dubu biyu, akwai bikin da zasuje na bangaren kishiyar Ummanta, dole a kece raini a nuna banbanci, dan ba tun yau take ma bikin tanadi na gaske ba. Sauran guntayen miya da tagani, wasu ma Allah kadai yasan tun yaushe suke ta dauko ta hade su waje daya ta sheqa ruwa ta kara mai da niqaqqen yaji a ciki, taga wani tsohon crayfish ta watsa a ciki, ko tsincewa bata tsaya tayi ba, tasan baci zatai ba, tai musu dafadukar shinkafa. 2

Da daddare tuwo zata tuqa, tana da sauran miyar kubewar da suka bar mata wancen girkin nata, ita zata juye ta karama ruwa ta kara kada wata kubewar ta tasheta, dan ita bata zubar da abinci, yanda suka barshi basuci ba, in wani girkin nata ya zagayo shi zataima kwaskwarima suzo su diba. Dubu dayan zata aiki salim yayo mata cefane kona dari ne naman dari biyu tayi yar miya ta dafama Alhaji Ahmad taliya, damam hakan takanyi, dan idan yasan kalar abincin da take dafama yaran tashin hankali zai mata marar misaltuwa. Shinkafar take kwashewa tana fadin

“Haba yara, wannan shinkafar ruwan jakara ce, in kunqi ci yau, kunci gobe” 4

Abdulkadir ya shigo, ya dan tsoratata dan ganin shi kawai tayi

“Kai dan ubanka baka iya sallama bane?”

Kallonta yayi rai a bace

“Karki sake zagina gaskiya tunda nayi sallama tun daga falo, ba laifina bane in bakiji ba” 5

Baki a sake Mama take kallon shi, rashin kunyarshi karuwa take duk rana

“Zaka rama zagin ne Abdulkadir?”

Rabata yayi yana dauko plate, ko Hajja inta zage shi ji yake kamar ta watsa mishi ruwan zafi, dan gani yake a shekarun shi ya girmi zagi, in yara sukaji ai saisu raina shi. Balle kuma Mama da baiga dalilin da take dashi na zagin shi ba. Wani ludayin ya dauko yana shirin sakawa cikin kular abincin da ko kadan yanayin shi bai kwanta mishi ba 1

“Karka batamun wani ludayin, ga wani nan…”

Ta fadi tana miqa mishi, karba yayi ya saka a ciki yana jujjuya abinci

“Meye wannan baqi-baqi a ciki?”

Ya tambaya yana daquna fuska

“Abin crayfish ne…”

Kallonta Abdulkadir yayi

“Crayfish kuma? Meye yasa za’a saka mana a abinci…me yasa ba za’ai mana da nama ba” 3

Shisa taki fitowa tun dazun, ta dauka duk sun gama dibar abinda zasu diba tunda taga lokacin tafiya islamiyyar su ya kusa, duk a cikin yaran gidan shi kadai yake tsareta da tambaya kan abinda ta dafa musu, bamai mata wannan fitsarar sai Abdulkadir, har bataso yaganta ranar girkinta, tana kuma shakkar yaje ya samu Abba da maganar dan tasan tsaf zai iya. Dan murmushi tayi

“To ai ana sakawa, yama fi nama zaqi…” 4

Ta fadi a fili a ranta tana

‘Dan iska yaro mai baqin hali irin na uwar shi’

Cigaba da jagula abincin yake da ludayi, ranshi yake jin yana kara baci, duk kwana biyun da zatayi a jigashe suke yinshi, har yaranta, saboda kalar abincin da take dafa musu.

“Nikam gaskiya bazanci wannan jagwalgwalon ba” 2

Ya fadi yana ajiye plate din daya dauka yabar mata ludayin cikin kular ta juya ya fice daga dakin

“Karkaci dan ubanka, in girkina ya zagayo ita din zaka sake dawowa ka samu, shegen iyayin banza da wofi. Yaro ga rashin kunya malam…”

Mama take cewa tana kwashe sauran shinkafar a robobin ta rufe su ta saka a fridge, harta koma daki bata daina kwashe ma Abdulkadir albarka ba. Shikam bangaren su ya koma yana samun Zahra ta dauko uniform din islamiyar ta a hannu

STORY CONTINUES BELOW


“Sannu Hamma”

Tace mishi, dan baka isa ku hadu ka wuce bakai ma koda sannu bane ba. 4

“Zahra ki dafamun ko taliya” 2

Ware mishi idanuwa tayi

“Hamma guga zanyi… Lokacin islamiyya kuma ya kusa, dan Allah kayi hakuri” 2

Ta karasa maganar idanuwanta na cikowa da hawaye. Agogo ya kalla, uku da rabi harda wasu yan mintina akai

“Tsayuwar me kike? Da yanzun kin kai kitchen, kiyi sauri, wallahi kikai latti ubanki zanci” 2

Uniform din ta ajiye akan kujera tana nufar kitchen, tasan da gaske yake, zai iya yana gama cin abincin shi ya fita Islamiyyar, tana da tabbacin zai iya riganta zuwa, kuma babu abinda zai hanashi dukan ta, fiye dana kowa ma, dan in ya tare latti su gefe yake sawa su ware, in yaima sauran bulala biyar-biyar nasu sai yakai goma. Wani lokacin zata rantse da Allah yanayin murmushin shi yakan canza duk idan ya kama wani ya zane, kamar akwai nishadi na musamman da duka yake samar mishi. Lokutta da dama ko fada Hajja tai mishi akan su yake huce wa, motsi ma in kayi bai mishi ba zai iya ja maka duka.

Sai dai yana da wani hali daya, babu wanda ya isa ya dake su a waje, babu malamin da baisan rikicin Abdulkadir ba duk Islamiyyar, tun baikai haka ba, hannunsu yake kamawa har inda malamin da ya dake sun yake ya tambayi dalilin da zaisa yai musu kalar dukan dayai musun, tun ana bashi suspension, har suka gaji da halin shi suka kyaleshi, su da kansu basa son a dake su ya sani, basama fara zuwa suyi labarin inda zaiji. Kan kujera ya samu waje ya zauna yana jiran Zahra ta dafa mishi taliyar ta kawo. 7

*

Yau bata jira kowa a gidan ba, dan ranta kal take jin shi, tunda Mami ta siyo musu sabon takalmin makaranta ita da Amatullah, ta tambayeta ko zata iya bama Nuriyya wancen natan, dan kafar su daya. Kai kawai Mamin ta daga mata, dan tasan ko ta hanata ma a sace zata dauka ta bata. Da takalman da atamfar da wata yar uwar su Mami ta bata, taqi rabawa da Amatullah ta roki Ammi din ta kara siya musu wani yadi aka dinka musu doguwar riga ita da Nuriyya, duka ta hado ta saka a leda tana shiga gidansu Nuriyya da yake liqe jikin nasu, ba wani babban gida bane, daki ukune a cikin gidan, Nuriyya ce babba a gidansu, kuma yarinya kwalli a wajen mahaifiyarta da Allah yai ma rasuwa wajen haihuwarta din, tana da kannai guda hudu yanzun haka da matar babanta ta haifa dashi, ga cikin na biyar a jikinta. 4

Zakai karya idan kace Mama kamar yanda su Nuriyya suke kiran matar baban nata Maryama tana musguna mata, da zuciya daya matar take rike da ita, wanda abune mai wahalar samu a wannan zamanin, yanda mata suke musguna ma yaran mijin su da zaman kishi sam bai ma hadasu da iyayen yaran ba abune mai matuqar muni daya zama ruwan dare. Sai dai Baban Nuriyya talakane sosai, dan sana’ar kanikanci yake a wani gareji, da kuma kacokan din sana’ar suka dangana, danma mutum ne da yake tsaye kan iyalan shi da dukkan karfin shi.

Waheedah zata iya cewa ta tashine taga Nuriyya a rayuwarta, dan a lissafi da akayi, wata daya Nuriyyan ta bata, kawancen su abune da zai baka mamaki, dan tunda karancin shekarun Waheedah ko abu aka bata saita tambaya ina na Nuriyya din, tun Mami na hanata shiga gidan su Nuriyya dan ita macece da batason tashin hankali a rayuwarta, harta hakura da taga kawancen na yarta da Nuriyya abune da kaddara ta hada. Yanzun ma sallama ta rangada tana gaishe da Mama data amsa tana dorawa da

“Hassanar taki na ciki…”

Dariya kawai Waheedah tayi tana wucewa ta nufi dakin su Nuriyyan. Abba shiya fara musu tsokanar nan ita da Nuriyya gashi kowa ya dauka, duk idan ya siyo mata abu zai bata wani irin shi yace na Hassanarta ne, dan shaquwarsu zaka rantse yan biyune, duk da kamannin su da halayensu ya bambanta, Waheedah fara ce sosai, kuma siririya ce ta gaske, tana da kyau da in zaka tsaya ka kalleta sosai zakaga bashi da alaka da hasken fatarta, sannan komai nata da sanyi takeyin shi, gashi babu wanda zaice ya taba ganin bacin ranta balle kuma fada, shisa tasu tazo daya da Nuriyya din, ita kadai take iya hakuri da halinta. Sannan Waheedah zata iya sati fuskarta bata ga ko hoda ba, dan ma farace, ba zatace bakinta ya taba ganin jambaki ba, kwalliya kwata-kwata ba abu bane da yake gabanta, indai ta saka kaya masu kyau tadan goga turare mai sauqin kamshi, shikenan.

STORY CONTINUES BELOW


Nuriyya na da fada sosai, ba zaka daga mata dan yatsa ka sauke batare data lankwasa shi ba, ba fara bace, zaka iya saka hasken fatarta a mutanen da ake ma laqabi da masu kalar cakuleti. Kusan kyawun mahaifiyarta ta biyo, dan kowanne irin kaya Nuriyya tasa saikaga sun amshi jikinta, tana da matsakaicin tsayin da mutane da yawa zasu iya kiranta gajera, amman a dire take, tun da yan shekarun tan nan zaka fahimci Allah ya halicci mace a wajen, cikar lokaci kawai take jira ta karasa fitowa. Gashi fuskar nan tana daukar kwalliyar dake kara fito da ita, da wahala ka kalli Nuriyya baka sake kallonta ba. Itama aji ukku take a sakandiren gwamnati ta mata dake nan cikin barikin sojoji, sannan islamiyarsu daya da Waheedah.

“Kardai kice baki shirya ba…”

Waheedah ta fadi ganin Nuriyyan a kwance kan katifar dake tsakar dakin, bayan tayi sallama tana daga labulen, takalman kafarta ta zare a bakin kofa tana shiga dakin sosai. Sai lokacin Nuriyya ta tashi tana fadin

“Nayi wanka, har alwalar la’asar nayi, uniform fa zan tashi in saka…”

Gefen katifa Waheedah ta zauna tana ajiye jakar makarantarta da ledar kayan data kawoma Nuriyya din hadi dabin farantin daya ke ajiye a gefen katifar

“Kai dan Allah Nuriyya, me kuka dafa mai manja baki kawomun ba?”

Waheedah ta bukata dan ita duk abincin mai manja baya wuce ta, ga yan gidan nasu basu cika son manja ba, ko alala sai ace da farin mai za’ayi aci da sauce, itakam tana son abinci mai manja, kallon ta Nuriyya tayi

“Gero da wake ne…” 2

Bakinta Waheedah taji yana tara yawun kwadayi, dan inba gidansu Nuriyya ba bata taba ganin inda aka dafa gero da wake ba, sai kuwa in sunje Bugaje ne da Abba, akan kawo musu, bamai ci sai ita.

“Zakici ne in zubo miki?”

Nuriyya ta tambaya a daqile, wani lokaci irin rainin wayan nan na Waheedah yana sata jin wani maqaqi a makoshin ta, ta tabbatar abincine mai rai da lafiya aka dafama su Waheedah a nasu gidan, da wahalar gaske in babu naman kaji, amman tana nuna mata kamar su wanda suka dafa din yafi nasu, badan batason mahaifinta ba, tana jin shi har ranta, amman idan akai mata tayin musayar rayuwa da Waheedah da gudu zata amsa, kodan ta dinga zuwa makarantar kudi tana turanci kamar yanda taji sunayi, duk da itama nacin ta yasa tana da kokari naban mamaki, kuma tana kwaba turancin duk yanda yazo mata, Waheedah na gyara mata sosai. 9

“Kema kinsan zanci ai”

Waheedah ta fadi, daman ba wani abin kirki Waheedah din taci ba, girkin Mama sai godiyar Allah. Mikewa Nuriyya tayi tana nufar karamin kitchen dinsu ta samu faranti ta zubo mata gero da waken ta zuba mata manja da yaji a gefe ta dauki cokali ta saka mata a ciki, dakin ta koma ta ajiye mata plate din a gabanta 1

“Allah dai yai miki albarka yarinyar nan”

Harararta kawai Nuriyya tayi, ledar dake gefenta Waheedah ta dauka tana miqa ma Nuriyyan da fadin

“Anty Asabe taban atamfa kwanaki, sai Mami ta bayar akai mana doguwar riga nida ke”

Da sauri Nuriyya ta karbi kayan da murmushi a fuskarta tana kasa tsayawa ta kwance ledar, yagawa tayi tana fito da doguwar rigar da dinkin yai matuqar burgeta, kasan rigar ta tsugunna ta tattaro sai lokacin ta kula da takalman da suka fado, kafa daya ta dago, badan tasan Waheedah da takalman ba, zata ce sabone yanda ta wanke shi fes dashi.

“Ke banza harda takalmi kika hado dashi”

Kai Waheedah ta daga mata, dan ta cika bakinta da abinci, saida ta fara hadiye wani daga ciki tukunna tace

“Nakine… Mami ta siyo mana sabo”

Ta karasa maganar tana kara kai wani cokalin bakinta. Takalmin Nuriyya ta mayar ta ajiye kan katifa tana jin wani irin abu a kasan ranta da ta kasa fassara shi. Bawai batai murna da kyautar bane ba, tana tunanin har lokacin da zatakai tana saka kwancen abubuwan Waheedah, tana da wani irin buri a rayuwarta, tana son taga ranar da zatazo ace itace take da damar yima Waheedah irin hidimar da takeyi da ita, ba zataki ace idan damar tazo Waheedah bace a kasanta, hakan zai mata dadi ba kadan ba. 22

Idan bata samu damar yin karatu ta zama wani abu ba, ba zata taba auren marar hali ba, zata auri mai kudi, irin mijin da takanji a cikin litattafan hausar da bata jima da soma karanta su ba.

“Kisa uniform dan Allah Nuriyya…”

Waheedah ta fadi dan ta kusa cinye abincinta, kayan ta linke ta ajiye su a gefe tana dauko uniform dinta da su kansu tsofin na Waheedah ne ta bata bayan an dinka mata sabo, abinda takeji kasan ranta girma yake karawa, batun yanzun ta jima tana jin yanayin ba, yana kara girma ne duk lokacin da zataga Waheedah da sabon abu, ko kuma Waheedah din ta bata abinda ta rigada tai amfani dashi. Kayan ta zira tana dauko doguwar hijab dinta ta saka, Waheedah ta rigata fita ta nufi randar ruwan su Nuriyyan da take ajiye a tsakar gida tasa cup
din dake sama ta dibi ruwa tasha.

“Nuriyya dan Allah kibar kwalliyar nan ki fito haka, wallahi zamuyi latti”

Daga can cikin dakin Nuriyya ta amsa da

“Dan Allah karki isheni, hoda kawai nake shafawa…”

Dan ana duka kan yawan kwalliya a islamiyar tasu, duk da haka saida ta kara wajen mintina goma bata fito ba. Sallama sukai da Mama, bayan Nuriyyan ta fito suka nufi hanyar kofa tare, suna fitowa kofar gida suna cin karo da Abdulkadir, wani irin dokawa da zuciyarta tayi saida ta riko hannun Nuriyya

“Ina wuni Hamma”

Nuriyya ta fadi a tsorace itama, prefect ne a makarantar, batun anan tasan shi farin sani ba, duk da inba a makarantar su ba, bai taba dukanta ba. Asalima ko gidan ta shiga gaisuwarta ma can kasan makoshi yake amsawa kamar ta mishi dole. Yanzun ma amsa ta yayi da

“Lafiya…”

Yana tsayar da idanuwan shi kan Waheedah da ko ina cikinta bari yake

“Ban hanaku tsayawa wani waje in kun fito islamiyya ba?” 1

Dagowa idanuwanta da suka tara hawaye tayi tana kallon shi, ko batai wani abuba ya kafeta da idanuwan shin nan masu kama dana yan Japan saboda kankantarsu ji take komai ta kwance mata batare da wani dalili ba.

“Ka…ka hanamu”

Ta fadi a daburce, kai ya jinjina yana wuce su, hannun juna suka kama ita da Nuriyya suna wucewa suma, wani irin sauri suke zumbudawa kamar zasu tashi sama, Waheedah nada tabbacin in ya rigasu isa makaranta zai kirki dalilin dazai mata dukan biyawa gidansu Nuriyya, ita kuma Nuriyya laifin Waheedah din tasan shi zai shafeta, juyawa Nuriyya tayi taga ko yana gab dasu, ta sauke idanuwanta cikin nashi da yasa wani irin yanayi tsirga mata daga dayan tsakiyar kafarta zuwa dan yatsan kafarta, kafin da sauri ta juya tana kiran duk wani sunan Allah dazai zo bakinta ko zuciyarta zata daina rage gudun da takeyi. Tana sake damke hannun Waheedah hadi da janta dan su kara sauri…!Da yawan lokutta idan aka tashe su daga makaranta sukan fi mintina sha biyar suna jira kafin azo a dauke su. Yazid yafi kawo su yazo ya dauke su, amman kowa in za’a tambaye shi zaice yafi son Mubarak yazo, dan duk gidan babu dan raha irin shi, kudin duk da yake aljihun shi kuma ranar akan su zai karar, duk abinda zasu nuna suna so sai an tsaya an siya. Yanzun basa komawa lokaci daya da Abdulkadir, saboda yana tsayawa extra lesson din da zai taimaka mishi wajen zana jarabawar aji shidda.

Yau din kuwa sa’a sukaci Mubarak ne yazo daukar su, kowa ka duba fuskar shi kar take

“Ina Commander din naku?” 5

Ya bukata yana sa Amatullah jan wani numfashi a tsorace

“Hamma…”

Suka kira kusan gabaki daya, dariya Mubarak yayi

“Bansan ya akai baiji sunan nan ba har yanzun” 3

Jinjina kai Zahra tayi, tana hasaso kalar drama din da za’ayi duk randa yaji suna kiran shi da Commander din nan. Mubarak ya rigada ya juya motar ya hango mai yalo a tsallaken titi

“Wazai siyo mana yalo?”

Ya bukata yana kallon Waheedah dake zaune a gaba, dan kafin ma ta ja kafarta cikin sanyin tafiyarta da mutane da yawa zasu iya kuskurewa da yanga sun gaggama shiga motar, gaba kadai ya rage. Jakarta ta ajiye tana cewa

“Kawo a siyo…. Wanne iri? Farin?”

Daga baya Nazir yace

“Nidai bana cin fari…”

Yana sa Mubarak juya ya harare shi

“Kaji mun yaron nan fa, nace zan siyo dakai ne?”

Yana zaro dari biyu ya miqama Waheedah

“Kowanne na dari…”

Motar ta bude ta sauko, baya tadan yi tana tsayawa daga bayan motar, abubuwan da take tsoro a rayuwarta basu da yawa, tsallaka titi na daya daga cikinsu, bataso tai magana ne su isheta da tsokanar su da bata karewa shisa ta karba, amman zuciyarta dukan uku-uku kawai take. Dakyar ta iya tsallaka hannu daya, tana tsaye a tsakiya, ganin motocin da mashina take suna wucewa da gudun da take tunanin ko suna da niyyar tashi sama ne. Banda zare idanuwa babu abinda takeyi, juyawa tayi dan ta tsallaka ta koma, amman abin ya gagara, data sani tace wani yaje, yanzun take jin gara tsokanar su da wannan tashin hankalin da take ciki.

Yana daga dayan bangaren shida Imran da Nawaf da suka jashi suna fitowa dashi, kasancewar basa fara extra lesson din sai biyu da rabi cif, ana nada rabin awar dan sallah da cin abinci.

“Lokaci yana tafiya, wanne iskanci ne wannan wai? Ku siyi kome zaku siya mu koma dan Allah”

Cewar Abdulkadir yana duba agogon dake manne a hannun shi. Imran ne ya kalle shi, dan Nawaf bai niyyar asarar bakin shi ba

“Karka daga mana hankali Malan, ka koma abinka mana”

Wani kallo Abdulkadir ya watsa ma Imran din

“Ai kuma karya kake, ku biyun, yanda kuka janyoni na fito haka zamu koma tare…”

Ya karashe maganar yana gyara tsayuwar shi, kamar ance ya daga idanuwan shi, ya kuwa sauke su kan Waheedah, duk da tana juyawa zuwa dayan bangaren hadi da bashi baya bai hanashi ganeta ba, akwai farare a makarantar sosai, harda yaran kwarori da suke makarantar, yana tunanin da kalar farin sune kawai zai iya kwatanta na Waheedah, yanzun ma yanda ya shigar mishi idone yagane itace, sai kuma yanayin sirantakar. Sake kankance kananun idanuwan shi yayi ganin ta sake juyowa ta fuskanto inda yake tsaye, da alama a rikice take. Apple din dake hannun shi ya juya yana tunanin abinda ya tsallako da ita titi.

STORY CONTINUES BELOW


Bai amsa Imran da yake tambayar shi ya sake shawarar tafiya babu su ne, dan abarba suka siya ana fere musu. Titin ya tsallaka yana takawa harya karasa inda take. Saboda a daburce Waheedah take ko kula batayi dashi ba

“Uban me ya tsallako dake?” 1

Muryar shi ta daki kunnuwanta tana tsoratata, baya tayi saboda yanda zuciyarta tai wani irin tsalle, da zafin nama Abdulkadir ya riko hannunta daya yana mata wata irin damqa kamar zai karyata, bakin shi da take ganin yana motsi ya tabbatar mata da ba magana kawai yakeyi ba, fadan shi yake mata da baya karewa, amman batajin shi, ta tsorata har cikin ranta, da bai riketa ba da labarin ya banbanta, tana jin yajata suna tsallakawa bangaren titin daya baro. Hannunta ya saki yana kai nashi hannun ya dan goge wani abu a goshin shi da yake jin ya taru.

Badan yanda zuciyar shi take dokawa ba daya dauke ta da mari 8

“Me zakiyi a tsallaken titi?”

Ya bukata yana kafeta da idanuwan shi da suka saukar mata da wata irin nutsuwa

“Ya… Yalo zan siya”

Numfashi Abdulkadir yaja yana saukewa, wani irin yanayi yakeji da bayason alaqanta shi da tsoron da yaji, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, sam bayason tuna yanda ta kusan fadawa titi 1

“Hamma Mubarak yace in siyo…”

Waheedah ta fadi a tsorace, ba tsoron titin data kusa fadawa ba, tsoron yanayin da take ganin Abdulkadir din a ciki, yanda ya dago da idanuwan shi yasata kai hannuwanta duka biyun tana rufe kuncinta dasu, wani irin dogon kallo yai mata yana kai hannun shi wajen fuskarta, matsawa tadanyi a tsorace tana rufe idanuwanta gam, cikin yanayi biyu zuciyarta take dokawa, yanda take cike da tsoron shi, da kuma yanda takanyi duk idan yana kusa da ita haka. Dari biyun da ke cikin hannunta yakai yan yatsun shi yana fisgewa hadi da nufar inda mai yalon yake, baisan me take tunanin zaiyi ba, dukanta ne karshen abinda yazo mishi. 2

Mai yalon ya mika ma kudin yana tsayawa

“Na nawa?”

Mai yalon ya tambaya

“Na duka…”

Kai ya jinjina ma Abdulkadir ya dauko leda hadi da sake fadin

“Wanne iri”

Wani irin kallo Abdulkadir ya watsa mishi, yalo duk ba yalo bane da zai tsare shi da tambayar banza

“Malan ka sakamun yalo, karka isheni da tambaya dan Allah…” 8

Ya karasa maganar da jan karamin tsaki, daya miko mishi ma a hasale ya karba, ranshi a bace yake jin shi. Waheedah na tsaye inda ya barta, ta sauke hannuwan ta daga kuncinta saboda bataji marin da tai tsammani ba. Batare da yace komai ba yasa dayan hannun shi ya damqi nata dashi yana janta batare da yace komai ba, hannun nashi tabi da kallo, wani irin yanayi na lullubeta, kafin ta kalli fuskar shi da take a nutse, yanda wani abu ke motsi a kuncin shi dake nuna alamar ciza hakoran shi yake ta cikin bakin shi tasan ranshi a bace yake. Yan gidan duka sukan ce kullum ma ran Abdulkadir a bace yake. 5

Tasan ba dariya yakanyi ba, in kuwa yayi takan ga baquntar yanayin akan fuskar shi, amman ita tana gane idan ranshi a bace yake ko ba’a bace yake ba, batasan ya akai take ganewa ba, tunda ta taba gwada yi musu bayani sau daya suka sakata a gaba da dariya bata sake kwatantawa ba. Fuskar shi take kallo tana binshi duk inda ya jata, batasan sun tsallaka duka titin biyu ba saida ya saka ledar yalon a hannunta yana sakin hannun tukunna.

“Idan na sake ganin ko da wasa kin nufo kusa da titi saina zane jikin ki Waheedah, Allah saina zane ki, kina jina ko?” 1

Kai ta daga mishi a hankali, bai jira amsarta ba, duk cikinsu ita kadaice baya damuwa da saita mishi magana da bakinta, inta ware mishi idanuwanta haka tana kallon shi da farar fuskarta yasan ko kasheta zaiyi ba iya magana zatai ba. Dan haka ya juya yana zagaya wa inda Mubarak ya fito daga motar ya tare mai yoghurt yana zaba yana sakawa a mota

STORY CONTINUES BELOW


“Hamma idan kasan zaka siyi wani abu tsallaken titi ka daina aiken yara, in ba zaka tsallaka da kanka ba ka hakura” 7

Dago kai Mubarak yayi yana kallon Abdulkadir din da in zasu gwada tsayi a kafadar shi kan shi zai tsaya. Duk da ba wani nisa bane a tsakanin su ta bangaren shekaru, amman ya girmi Abdulkadir din, yanda yai tsaye yana bashi umarni yasa shi yin dariya da fadin

“To Abba…” 12

Cikin ido Abdulkadir ya kalle shi

“Da gaske nake, karka sake aiken su tsallaka titi, bana so…” 13

Kai Mubarak ya daga mishi, dan bazai iya masifar Abdulkadir din ba, juyawa yake da shirin tafiya, Mubarak yace

“Kazo ka dauki yoghurt”

“Bana sha…”

Kallon shi Mubarak yayi

“Daga abin arziqi?”

Daquna fuska Abdulkadir yayi

“Nima bance wani abu ba, bana sha kawai nace”

Hannu Mubarak ya daga mishi

“Naji, sai anjima, jeka abinka”

Tafiyar kuwa yayi yana nufar hanyar da zata mayar dashi cikin makarantar. Waheedah kuwa dakyar ta iya jan kafafuwanta ta shiga cikin motar. Kan sit din da Mubarak ya tashi ta dora mishi ledar yalon, hannunta take murzawa inda take jin na Abdulkadir har lokacin, zuciyarta na mata wani irin yanayi da ta kasa fahimta. Har Mubarak ya shigo ya bama kowa yoghurt din shi, tata karba tayi tana zage aljihun jaka ta jefa a ciki, haka yalon ma, dan ji take sun takura yanayin ta, kanta ta jingina da jikin motar tana lumshe ido, kafin ta daina jin hayaniyar da suke a cikin motar dan ta bace cikin duniyar tunani.

Jikinta gabaki daya a sanyaye take jin shi, banda yanayin fuskar Abdulkadir din lokacin daya rikota babu abinda take hasasowa, so take taji ta a kwance a daki, ta janyo bargo ta rufe jikinta gabaki daya har hakanta, ba zataki bacci ya dauketa cike da tunanin shi ba, dan a dakine kawai take da tabbacin babu wanda zai uzzura mata balle ya katse mata tunanin ta. 13

“Waheedah…”

Taji an kira ana tabota, juyawa tayi fuskarta babu walwala

“Dallah anata miki magana, mu kwance kai yau, kinga alhamis babu islamiya, gobe in Allah ya kaimu sai muje kitso gabaki dayan mu…”

Da sanyin murya tace amsa Zahra da

“Kuje kitson ku, Nuriyya zatai mun”

Hararta Zahra tayi

“To mai Nuriyya data iya kitso, sai kita zuwa ai”

Tana kallon Amatullah ta tabe baki, juyawa tayi ta gyara zamanta tana kyalesu, batasan me Nuriyya ta tsare musu da basa sonta har haka ba, ko wani abin ake in tace da Nuriyya zatayi takan ga kiyayya shimfide a fuskarsu, musamman Amatullah da takance tama fi son Nuriyya akan ta, bata raba duk wani lokacin da ta samu tare da ita saida Nuriyya, zata iya cewa dukka yan uwan nata kan yi mata wannan mitar, kamar suna kishi da Nuriyya din, dariya takan yi musu kawai, yau kam ko dariyar basu samu ba, dan tunanin Abdulkadir ya addabeta fiye da kowanne lokaci, dashi manne a kasan zuciyarta kuma suka karasa gida. 4

**

Bai shigo gidan ba sai gab da Magriba, bangaren su ya wuce yana tura kofar dakin da sallama ya shiga, kafafuwan shi da jikin shi cikin shigar kayan ball. Bangaren da gabaki daya mazan gidan suke daban yake, daka shiga falo zaka samu da kujeru a ciki, sai kofofin dakuna a zagaye, dakin bacci hudune a cikin wajen manya-manya, sai karamin nashi da yake tunanin anyi shi na baki. Da shi da Mubarak suke kwana, kafin ya tattara yana bar mishi dakin, bai damu da kwana shi kadai ba, asalima hakan na mishi dadi, da dakin ya kasance nashi ne shi kadai, amman baisan dalilin da yasa kowa yake gudun hada daki dashi ba, abin na bata mishi rai wani lokacin, ko kujera mai zaman mutum biyu ya zauna da wahala kaga wani ya zauna kusa dashi. 10

STORY CONTINUES BELOW


Kusan su hudu yagani a falon suna kallo, baibi takan su ba, kitchen ya fara wucewa ya bude fridge din da yake kitchen din ya dauki ruwa, ba wani amfani suke da kitchen din ba, banda kwanonin da in suka shiga cikin gidan sukan zo su jibge, sai ya gaji da ganin su yake sa wani ya kwashe ya mayar cikin gidan. Dakin shi ya wuce yana cire kayan jikin shi ya shiga bandaki, ruwa ya watsa cikin hanzari dan yasan ana gab da kiran sallah ya dauro alwala ya fito, kananun kaya ya saka, dan Hajja harta gane shi, in ya saka manyan kaya to sallar juma’a zashi, kayan duk da za’a dinka musu manya da sallah, yana dawowa idi yake zare su daga jikin shi.

Fitowa yayi yana jin ana kiran sallah, har yakai kofa ya juyo yaga su Yasir a zaune.

“Kuna ji ana kiran sallah, kuna kara gyara zama” 1

Yassar ne ya dago daga cikin kujera yana kallon Abdulkadir din

“Ka wuce abinka kai dai…”

“Badai kyau wallahi”

Cewar Abdulkadir din, dan yagane Yassar ne a yanayin shi, kusan duk gidan zai iya kwantanta zafin ranshi dana Yassar ne, baya tunanin ko Mama tana iya banbance su in bada hakan ba, kamannin su ya baci, gashi ya rasa jarabar da tasa komai iri daya sukeyi, har askin kansu, in suna tare ka kira daya su dukan su suke juyowa. Da zafin ransu ne kawai ake ganewa.

“Karka bari in taso Abdulkadir…”

Yassar ya fada, amman ko motsi Abdulkadir baiyi ba

“Hamma Yasir kaima biye mishi zakayi? Dan kun fito a yan biyu bazai sa a rufeku a kabari daya bafa, wallahi jibgar banza zaka sha…” 4

Mikewa Yassar din yayi yana fara takawa inda Abdulkadir din dayake dariya yake tsaye, sai dai kafin ya karasa harya bude kofar ya fice da gudu 4

“Dan banzan yaro marar kunya, daka tsaya ai”

Yassar ya fadi, yana sa Yasir yin dariya

“Banda kai a gidan nan, banga wanda Abdulkadir yake wasa dashi haka ba”

Mubarak ne ya jinjina kai yana miqewa

“Halin sune yazo daya shisa, yaron can ko tsokanar shi na gwada yi zaice mun bayaso, zansa yara suji su raina shi”

Dariya kawai Yassar yayi yana wucewa yabar su anan, banda Yasir da suka fito rana daya, bayajin akwai wanda yake ji har kasan ranshi a gidan kaman Abdulkadir, duk da kusancin su baya hana yai mishi rashin kunya sosai, amman kuma shi kadai yake daga ma Abdulkadir hannu ya sauke batare da Abdulkadir din ya gwada ramawa ba, sai dai ya sake fadar maganganu ya wuce, ko rikici akeyi dashi, Yassar din ake kira dan shi kadai yake iya raba rikicin Abdulkadir. Alwala duk sukayi suna fita masallaci tare. 2

*

Abdulkadir bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha’i, bai samu kowa a falon ba sai Yassar da yake cin abinci, kamshin da wake da shinkafar da ya hango yaji busashen kifi yake yasa shi sanin girkin Mami ne, dan duk ranar baici abinci a gidan ba, da safe ya rigasu fita makaranta dan shi yake da duty, acan ya siyi abinda ya sakama cikin shi, daya dawo kuma sunje gidansu Imran, acan sukaci abinci rana. Cikin shi yaji ya murda da yunwa, ya karasa yana zama kusa da Yassar din, hannu yakai zai dauki cokalin Yassar ya doke hannun shi

“Tashi ka zubo naka”

Daquna mishi fuska Abdulkadir yayi

“Hamma mana…”

Abincin Yassar ya kara diba ya cika bakin shi yana fadin

“Zanci ubanka wallahi”

Sake daquna fuska Abdulkadir yayi

“Saika dinga zagina, ko a gaban yara saika zageni, salon kasa yara su rainani. Ni kam bana so kana mun irin haka” 2

Hannu Yassar yasa yana kai mishi duka saboda bakin shi da yake cike da abinci, miqewa Abdulkadir yayi, duk gidan babu wanda yake mishi irin wannan cin mutunci sai Yassar, ya rasa kuma menene tattare da Yassar din da yakan sashi daga mishi kafa tunda ba tsoron shi yake ba, baya tunanin idan fada ya hadasu Yassar zai iya dibar wani abu a jikin shi, amman saiya barshi yana ci mishi mutunci haka, ko Abba bai taba dukan shi ba, balle kuma Hajja, Yassar ne mutum na farko a duniyar shi daya fara dauke shi da mari bai iya ramawa ba, lokacin da fada ya kaure tsakanin shi da Babban Yaya, kan ya mare shi ya rama. 9

STORY CONTINUES BELOW


Amman da Yassar din ya kafe shi da idanuwa tsintar kanshi yai da barin wajen, yana mishi kwarjini naban mamaki. Yanzun ma kallon da yake mishi yasa shi fita daga dakin. Kanshi tsaye bangaren Mami ya wuce yana shiga har tsakiyar falon tukunna yai sallama, Mami din data fito daga kitchen ta amsa shi

“Ina wuni”

Ya furta a hankali, duk cikin matan Abba yafi ganin girmanta, ita kadaice bata taba shiga harkar shi ba, asalima banda gaisuwa babu abinda yake hadasu, yanzun ma wucewa tayi hidimar gabanta, shi kuma ya taka yana karasawa har kitchen din, inda yaga Waheedah a tsaye, juyowa tayi tana kallon shi, kafin a dan daburce tace

“Hamma…”

Ludayin da yake hannunta ya karba, jajayen kayane a jikinta daya kara fito da farin ta yana saka shi daquna fuska

‘In shaa Allah babu abinda zai hadani hanya da farar mace’ 5

Ya fadi a kasan ranshi, plate ya dauko batare daya kulata ba, yana kallo ta matsa tana hade bayanta da kantar kitchen din, abincin da yake tunanin zai iya cinyewa ya zuba

“Ina miya?”

Ya tambaya yana kin kallonta dan farinta na shigar mishi ido, da hannu ta nuna mishi tana sake matsawa dan zuciyarta dokawa take sosai, da tunanin shi manne ta yini, har fita tayi harabar gidan ko zata ganshi batare da tasan dalilin hakan ba, ta gaji da leqe-leqenta ta dawo cikin gida, ko sallar isha’i sai yanzun ne tayi alwalarta, a falo ta zauna tana jiran ko zata ga ya shigo dibar abinci, sai yanzun da yake tana da rabon tagan shi din. Cokali yasa hannu ya dauka hadi da wani plate din daya dora kan abincin ya rufe yana ficewa batare daya sake kallon inda take ba. Bangaren su ya koma, abincin ya fara ajiyewa tukunna yaje ya dauko ruwa ya dawo ya zauna. Daga shi sai Yasir da Yassar, Ahmad da suke kira da Babangida, sai Mubarak a falon. 2

Film din da lokacin ake rubuta sunaye alamun farawa ya tsayar da idanuwan shi akai.

‘Paheli’

Ya karanta sunan film din da tun daga kidan daman yagane indiya ne. Abinci yake ci yana nutsar da hankalin shi kan film din, dan sosai yake jin dadin shi, kafin yaji an harbar mishi baya da kafa, ya kuma san Yassar ne

“Sojan gobe ne yake kallon soyayya haka?”

Yassar yai maganar yana dariya

“Babu abinda zai hana insa a rufemun kai ko kwana biyune, saboda babu wanda ya rainani a gidan nan kamar ka”

Dariya Yassar ya sake yi

“Lallai ma yaron nan. Ka zama sojan tukunna”

Juyawa Abdulkadir yayi yana kankance mishi idanuwa

“Na kusan applying NDA ai, in shaa Allah. Kuma wayaki soyayya?”

Wannan karin Babangida ne yace

“Tambaye su dai, kaman suma ba kallon suke ba”

Murmushin gefen fuska Abdulkadir yayi

“Allah Hamma bazan auri matar da bana so ba, ina da buri mai yawa kan matata”

Dariya sukayi gabaki daya

“Hmm, tadai shiga uku da masifarka, aikai mai zama dakai tana da aiki wallahi” 3

Mubarak ya fadi

“Shisa nace zan auri wadda nake so…” 3

Murmushi Yasir yayi mai sauti

“Yaron da ko tafasa baiyi ba yana maganar soyayya da mata. Allah ya shirya”

Daquna fuska Abdulkadir yayi

“A’a Hamma…a’a wallahi, naji kamar kana so kace mun yaro” 2

Ware idanuwa Yasir din yayi, bai gama mamakin Abdulkadir ba yaji ya dora da

STORY CONTINUES BELOW


“Kaima yanzun kake level 2, bawai ka girmeni bane can da yawa”

Yassar ne ya kara kai mishi duka da kafa, wannan karin yana kaucewa dan yagan shi

“Me nayi? Karya na fada? Nidai Hamma Yasir karka fara gwada kirana yaro wallahi, ko mu kadaine balle a gaban yara” 2

Abdulkadir ya karasa fadi yana kumbura fuska

“Me zai faru in nace maka yaron?”

Yasir ya tambaya

“Nidai ai kashedi nayi” 2

Ganin abin zai zama fada yasa Yassar cewa

“Ya isa haka… Abdulkadir tashi daga falon nan”

Kallon Yassar yake kamar ya mishi magana da wani yare daban dana Hausa

“Yes ka tashi naje, ka jini kuma”

Wata dariya mai sauti Abdulkadir yayi

“Bazan tashi bafa, dan kallo nake, sai dai shi ya tashi” 2

Ya karasa maganar yana nuna Yasir da dan yatsa, murmushi kawai Yasir yayi

“Ka kyale shi kawai Yassar”

“In bai kyaleni ba ya zaiyi dani daman?”

Dafe kai Yassar yayi yana sauke numfashi, su Babangida da Mubarak daman basu sake saka musu baki ba, asalima kallon su suka ci gaba dayi, dan babu wanda ya shirya rashin kunyar Abdulkadir din, ganin kowa yai shiru yasa Abdulkadir mayar da hankalin shi kan film din, duk da zuciyar shi da yakeji ta kawo wuya. A hankali yake jin soyayyar da ake gudanarwa a film din na nutsar mishi da wani abu a kasan zuciyar shi, kamar yanda ya fada ne yana da buri mai yawa akan matar shi, kuma auren soyayya zaiyi, bazai auri yarinyar da bayaji har kasan ranshi ba, dan da kadan soyayyar da yake ma kakin sojoji zata dara tata. 3

*

Kamar yanda Waheedah tace Nuriyya zatai mata kitso, hakan ya faru ranar juma’a, tana dawowa daga makaranta, kaya kawai ta sake ta fadama Mami zata shiga gidan su Nuriyya, Amatullah ma anan tabarta zatayi wanke-wanke ta shirya itama su fita kitson dasu Zahra. A dakin su Nuriyyan suka zauna dan yin kitson

“Karkimun manya fa”

Waheedah ta fadi, tana saka Nuriyya kwashewa da wata irin dariya

“Dame za’ayi kananun kitson to?”

Duka Waheedah takai mata

“Bana son iskanci, ai kinga dai gashina ya fara dawowa Allah”

Dariya Nuriyya ta sake kwashewa da ita, tana kallom gaban kan Waheedah din da duk ya giwgwiye, daman bawai tana da gashin kirkin bane, taje wata yar ajinsu ta fada mata tayi retouching da Petals yana saka bakin gashi, dan farin Waheedah yasa gashin ta jane, Petals din baisaka mata bakin gashi ba saima gaban daya kara kwashewa kamar an aske 3

“To zaki sake gwada Petals dinne?” 3

Nuriyya ta tambaya har lokacin tana dariya, ita kanta Waheedah murmushi take

“Allah zai kama mun ke, dan gashin nan da kike mun wulakanci sai kin tashi da safe ya kwakushe”

Duka Nuriyya takai mata, duk da ba za’a sakata a layin masu dogon gashi ba, Allah ya bata yalwarshi babu laifi, tana kuma bala’ij ji da gashin har ranta.

“Aniyarki ta biki”

Wannan karin Waheedah ce tayi dariya, hira suke sosai ana kitson, a haka har aka gama

“Ki tambaya Mami muje rijiyar lemo gobe in Allah ya kaimu” 1

Nuriyya ta fadi, gidan Antynta take son zuwa, kuma Naira Hamsin gareta, batajin zata isheta, in suka tafi da Waheedah din tasan zata biya kudin motar. In ta tambayeta ma ba zata hana ta ba, tambayar ce ba zata iya ba, wani abu na mata zafi a kasan zuciyarta da tunanin hakan. Kai Waheedah ta girgiza mata 4

“Da wahala Mami ta barni wallahi”

Dan duk yanda Mami ta yarda da kawancen su da Nuriyya, tasan bata son yawon da babu dalili, duk da in ana biki ko suna a bangaren su Nuriyyan takan barta taje wasu lokuttan, amman yanzun tasan babu wani dalili, fada ma zatai mata. Hannu ta saka cikin aljihun wandon Pakistan din da take sanye dashi ta zaro Naira dari, kudin makarantar da aka bata ne ranar, babu abinda ta siya dashi.

“Ki dai siya ma su Nana ko Guava ce”

Karba Nuriyya tayi cikin ranta tana fadin

‘Ashe su Nana’

A fili kuma batace komai ba, dan bakinta yakan yi nauyi da taima Waheedah godiya a irin yanayin nan, ita ma Waheedah bata taba damuwa ba, dan a ganinta sun zama yan uwan ita da Nuriyya, babu wannan a tsakanin su, mikewa Waheedah tayi tana kakkabe jikinta, hadi da durqusawa ta dauki hijab dinta 7

“Ki gaishe da Antyn dan Allah. Bari inje nasan su Amatullah basu dawo ba, in kamawa Mami girki”

Kai Nuriyya ta jinjina, tana jin son cin komeye zasu girka din, dan ta tabbatar zaiji nama. Mami bata kwauron nama a abincin ta 1

“Inkin dawo ki biyo, dambun shinkafa Mami zatai mana, in kuma baki biyo ba naba Aminu ya kawo miki”

Dacin da takan ji wasu lokuttan Nuriyya taji ya mata sallama a cikin makoshin ta, zatayi komai dan suyi musayar matsayi da Waheedah, da duk rana take sa tana kara jin yanayin. 5

“Wai aita magana kiyi shiru ki kyale mutane”

Numfashi Nuriyya ta sauke

“Ba kunne yake ji ba? Ai ina jinki ko?”

Kai kawai Waheedah ta jinjina tana saka Hijab dinta

“Allah dai ya shirya halinki”

Ta juya ta fice daga gidan, wanka Nuriyya ta shiga, da yake ba nawa gareta ba, nan da nan ta shirya, taci uwar kwalliya, wata doguwar riga da Abban su Waheedah din ya siyo musu lokacin dayaje Umrah ta saka tana nade kanta da mayafins rigar daya bala’in karbarta. Sallama tayi da Mama tana ficewa daga gidan, a kofar gidan su Waheedah taci karo da Abdulkadir dan nan ne hanyar da zata bi ta nufi titi, haka kawai zuciyarta tai wata irin dokawa, ba tun yanzun yake mata kyau ba, yakan yi mata kama da mazan da takan karanta a litattafan Hausa. 2

“Ina wuni Hamma?”

Ta furta a hankali, a karo na farko da Abdulkadir zaice ya tsaya ya kare mata kallo, baisan tana da kyau har haka ba, ga yanayin jambakin ta ya zauna a fuskarta, raini ne bayaso ko a wajen yan gidansu, shisa duk wasu tarkacen kawayen su Zahra baya damuwa da su, in sun gaishe shi ya amsa, in basu gaishe shi ba shikenan, sam bayason raini da rashin kunyar kananun yara.

“Lafiya…”

Ya amsa tukunna ta wuce, cikin gida ya koma, yana kudurta a ranshi kudin kayan kwalliya daban zai ware ma matar shi, dan ko wajen aiki ya koma yana son tuno fuskarta da kwalliyarta da yasan zasu rage mishi kewar ta da zaiyi. Burin shi akan matar shi mai girma ne, shi kanshi yasani, duk da burin shi na saka uniform ya girme shi nesa ba kusa ba, amman ya matsa mishi ya samu wajen zama daram a zuciyar shi.Akan ce kwanaki na gudu, bai taba yarda da hakan ba sai bayan sunan shi ya fita cikin jerin mutanen da suka samu gurbi a makarantar horar da sojoji ta NDA da take cikin garin Kaduna, bayan surutun da ake tayi ja cewar makarantar nada wahalar samu, sai kana da hanya. Zai karya idan yace Abba baisan mutane ba, ko cikin kawunnan shi baza’a rasa wanda yasan wani da zai taimaka mishi wajen samun makarantar ba, baidai nemi taimakon su bane kawai. Kuma da yake yana da rabo sai gashi Allah ya bashi. Ranar wani sama-sama yake jin shi, sosai ya yarda ranaku na gudu. +

Duka yaushe ya fara sakandire, gashi harya kammala yana shirin jefa takun farko a hanyar shi ta cikar burin shi. Ji yake kamar ya janyo lokacin tafiyar, yan gidan kansu sun fahimci nishadin da yake ciki, dan tunda suke basu taba ganin ya wuni da murmushi a fuskar shi ba, ko gaishe shi kayi ranar da murmushi yake amsawa. Idan ka tona ran kowa a gidan qal yake, musamman yaran da duk ya kasance akwai tazarar koda satika ce tsakanin shi da Abdulkadir, har tambaya sukayi akace musu akan shekara daya ma ba’azo gida ba, dan sai hutun sallah da ba koyaushe yake kaiwa sati biyu ba ballantana ma ya shige hakan. Ran su qal suke jinshi, zasu sakata su wala a gidan batare da tunanin Abdulkadir din ba. 4

Yanzun ma abinci suke ci a dakin Anty. Waheedah ta kalli Zahra tace

“Wai da gaske daga shekara sai shekara Hamma Abdulkadir zai dinga zuwa gida?”

Kai Zahra ta daga mata tana hadiye abincin data cika bakinta dashi.

“Haka naji Hajja da Hamma Yazid na maganar…”

Kai Waheedah ta jinjina tanajin wani abu yai mata tsaye a wuya batare da sanin dalili ba 2

“Kinsan duk yanda nake murnar tafiyar nan…Zanyi kewar shi fa”

Ta karasa maganar tana dan yin jim

“Babu wanda yake shan dukan Hamma Abdulkadir irinki duk gidan nan…kewar me zakiyi tashi? Jibgar da kike sha?”

Nabila tai maganar tana cakuda abincin ta, dariya Zahra tayi, dan batasan ya zatai ma Nabila bayani ta fahimce ta ba, da gaske ne babu wanda yake shan dukan Abdulkadir din duk gidan kamar ita, sai dai ko shigowa yayi bai ganta ba sai ya tambaya tana ina, idan abu ya shigo dashi ko bata nan sai yasa an ajiye mata, tana kula da ko aiki yake so ai mishi ita kadai yafi matsawa, da wahala rana ta fito ta koma bai taba lafiyarta ba, duk da hakan tana jin Yayan nata har kasan ranta. 2

Abincin suka ci gaba daci suna hira abinsu, Anty ta fito daga dakin baccin ta tana ganin yanda suka mayar mata da falo

“Lallai yaran nan, falo nane haka? Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ta karasa ganin shinkafar dake dankare kan kafet dinta

“Wallahi tas zaku sharemun daki…ko kwayar shinkafa banason gani”

Turo baki Nabila tayi dan Allah ya dora mata son jiki naban mamaki

“Anty su Hamma ne fa…”

Hararta Anty tayi

“Banga su Hamma ba, kuna gani…”

Waheedah kam murmushi tayi hadi da fadin

“Za’a share Anty… Damun gama. Har wanke-wanke ma duk zamuyi” 1

Tanajin zungurin da Zahra tai mata

“Naganki dan ubanki, wato tace wanke-wanke shine kike zungurinta ko?”

Cewar Antyn tana dorawa da

“Maquyatan banza da wofi, sai kace ba mata ba”

Ta juya ta koma dakinta, harara Nabila da Zahra suka zabga mata, Nabila na fadin

“Adda Wahee ke zakiyi wanke-wanken?”

Kai Waheedah ta daga musu tana ajiye cokalinta cikin abincin dan ta riga ta koshi tuntuni, hanyar kitchen din ta nufa tana ganin jibgin kwanonin wanke-wanken da ko kadan basu daga mata hankali ba, indai aikine da zatayi da jikinta baya mata wahala, duk da Mami kance ta cika yin abu da sanyin jiki. Saida ta fara share kitchen din tukunna ta fara wanke-wanken, tafiyar Abdulkadir tayi mata tsaye a makoshinta. Shekara daya na mata wani irin nisa naban mamaki, a wani bangaren kuma tana mata saurin zuwa, duka yaushe yagama jarabawar aji shidda harta fito, ita kanta aji biyar take shirin shiga yanzun hakan. 1

STORY CONTINUES BELOW


**

Ranar lahadin da saura kwana daya su koma makaranta, kuma yai dai-dai da litinin din da Abdulkadir din ma zai tafi Kaduna. Wani iri take jinta, dan haka tanayin wanka tagama abinda takeyi ta fito zata shiga gidan su Nuriyya ko hira suyi, ta fito harabar gidan taci karo da Abba.

“Abbah…”

Ta kira fuskarta dauke da fara’a cikin yanayin da ita kadai take kiran shi da hakan. Shima muryar shi dauke da fara’a yace

“Waheedah…”

Murmushinta ya kara fadada

“Ina kwana…”

Amsawa yayi yana dorawa da

“Har za’aje islamiyya ne da wuri haka?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi, kafin ta amsa yace

“Wajen Hassanarki zakije kenan”

Dariya Waheedah tayi

“Abba mana”

Jinjina kai yayi yana saka hannu a aljihu

“Aina sani….itama goben suke komawa makaranta ko?”

Kai Waheedah ta dan daga mishi, dubu uku ya zaro daga aljihunshi yana mikama Waheedah din

“Na manta ne wallahi, ki bata saita dinka sabon kayan makaranta itama, abin na raina tun randa na bayar da naku dinkin…” 3

Da fara’a a fuskar Waheedah ta karbi kudin

“Allah ya kara arziqi Abba… Angode sosai”

Murmushi kawai Abba yayi, hankalin yarinyar yasa yake jinta kamar daga cikin shi ta fito, ko kadan bayaso taji maraicin rashin mahaifinta, alkawari ya daukarwa mahaifiyarta na cewa zai riqeta, ko da mahaifinta na raye, nauyin alkawarin daya dauka zai cigaba da danne shi.

“A dawo lafiya. Allah ya tsare mana kai”

Waheedah ta fadi, Abban ya amsata, tsaye tayi saida taga ya shiga mota ya juyata ya fice daga gidan tukunna ta karasa takawa tana isa kofar gidan ta fice tana shiga gidan su Nuriyya din. Bata ma sameta a gidan ba, Mama ta aiketa, kudin da Abban ya bata ta mikawa Mama tana mata bayani, sosai Mama ta nuna jin dadinta hadi dayin godiya mai yawa, tukunna Waheedah ta koma gida. Bangaren su ta nufa ta shiga dakinsu ta kwanta. Bata da abinda zatayi, gashi sunqi kawo wuta balle tayi kallo ta rage zafi

Tunawa tayi da wani littafi da tafi wata shidda da karba wajen Nuriyya, amman bata karanta ba, dan har yanzun ita karance-karancen littafin Hausar nan basa kanta, saukowa tayi daga kan gado tana dauko tsohuwar jakar makarantarta, aikam tana saka hannu ta bincika ta janyo littafin, kan gado ta dora shi tana mayar da jakar tukunna ta koma tahau gadon ta kishingida tana daukar littafin. ABIN DA AKE GUDU na BATUL MAMMAN ta duba sunan littafin da marubuciyar, sosai takan ji Nuriyya na maganar marubuciyar da yanda tsarin rubutunta yake tafiya a nutse, dan takance bata da gwana a marubutan Hausa kamar matar. Shafin farko ta bude tana nutsawa cikin labarin ASMA’U. 10

*

Ko da suka dawo islamiyya so take kawai ta gama duk wata hidima da zatayi tai sallar isha’i ta koma daki ta karasa jin yanda za’a kare da labarin ASMA’U, da ta dauka Nuriyya zuzuta marubuciyar kawai takeyi, sai yanzun da labarin ya tabata fiye da tunani. Ga tarin darussan da iya tsayin rayuwarta bata taba hango faruwar su ba, tashin hankali abune da sai dai taji labarin shi a waje ko a fina-finai, sai kuma yanzun da take karanta shi a littafin BATUL MAMMAN. Kayan makarantar su duk ta hada ta goge. Dauka tayi tana nufar daki, taga Amatullah a kwance a kasa kan kafet. 1

Tunda zasu fita islamiyya take fadin cikinta na ciwo, har suka dawo, dan Waheedah ba zatace taga taci abinci ba

“Ki tashi ki fadama Mami ko magani sai ta baki… Ya zaka zauna ciwo na cinka”

STORY CONTINUES BELOW


Waheedah ta fadi tana ajiye uniform din a gefen gado, hadi da taba Amatullah din, zuciyarta tai wata irin dokawa ganin kamar bata motsi, tsugunnawa tayi tana kamota 4

“Amatu… Amatullah…”

Take fadi tana jijjigata, idanuwanta cike taf da hawaye, dakyar Amatullah ta daga idonta

“Adda Wahee cikina, cikina ciwo yake…”

Hannu Waheedah tasa tana share kwallar da take shirin zubo mata, muryarta a karye tace

“Bari in kira Mami…sannu”

Ta kara maganar tana zame Amatullah daga jikinta, ta fice daga dakin da sauri, koda taje wajen Mami dinma hannunta kawai ta kamo dan ta kasa magana, saboda kukan da take, dakin nasu Mami tabita hankali a tashe, a kafada ta sabe Amatullah din tana daukar hijab din Waheedah da tagani inda tai sallar Magrib tana nufar hanyar fita daga bangaren nasu, Waheedah na rufa mata baya. Bangaren Hajja ta nufa da Amatullah dan tasan Abban su bai isa dawowa ba.

“Subhanallah, me ya faru haka?”

Hajja ta tambaya, Mami na amsata da

“Cikinta ne yake ciwo…”

Hajja batace komai ba ta koma cikin dakin da hanzari, Hijab dinta ta dauko itama ta saka ta dauko mukullin motar ta tana fadin

“Muje… Bari in dubo cikin yaran nan, ko wani yana nan. Tafiya asibiti da namiji nada dadi, kodan zirga-zirga…” 2

Basu ma karasa bangaren nasu ba saiga Muhsin ya shigo gidan. Motar Hajja ta bude tana karbar Amatullah da take fitar da numfashin wahala ta sakata a bayan motar tana shiga. Ganin Waheedah dake kuka ta kama murfin motar yasa Mami fadin

“Ina zaki ke kuma? Wuce ki koma gida…”

Rau-rau ta sakeyi da ido, wani kallo Mami ta watsa mata dayasata sakin murfin motar, tana kallo suka rufe, gefe ta matsa, Muhsin din ya juya motar suka fice. Tsaye tayi a wajen tana share hawaye, hadi da sauke ajiyar zuciyar da take jin tana mata zafi. Ita kam da sun tafi da ita hankalinta zaifi kwanciya. A wajen ta zauna ko sauron dake gartsa mata cizo bataji, danma da haske, kasancewar an kunna musu gen. Bata san iya lokacin data dauka a wajen ba, ta hada kai da gwiwa, kuka kawai take sharba.

Abdulkadir ne yazo wucewa, dan ranar ya wuni ne dasu Nawaf tunda washegari da sassafe zai wuce, ajiyar numfashin ta ya soma ji, kafin ya tsaya yana dakuna fuska, sosai ya saurara yaji daga inda kukan yake fitowa, dube-dube ya shiga yi, yana hangota rakube wajen ajiye motocin, daga hannuwanta yagane itace

‘Me yarinyar nan take anan?’

Ya tambayi kanshi yana karasawa wajen, ta hade kanta da gwiwa da alama kuka takeyi.

“Waheedah…”

Ya kira, muryarshi na dukan dodon kunnenta da wani irin yanayi da yasata dagowa, fuskarta ta karayin ja, idanuwanta duk sun kumbura saboda kukan da takeyi, saiya tsinci kanshi da kasa yi mata fada. Muryarshi dauke da wani yanayi yace

“Menene? Waya dake ki?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi, wani rauni takejin yana kara danneta da ganin shi, hawayen ta na kara zubowa.

“Me kike anan to? Meya faru? Mutuwa akai?”

Abdulkadir ya tambaya, wannan karin da damuwa a muryarshi. Kan dai ta sake girgiza mishi

“Kimun magana Waheedah, kina son batamun raine kome?”

Ya karasa maganar a fadace, dakyar, muryarta can kasan makoshi tace

“Amatu…Amatullah ce bata da lafiya”

Numfashi ya sauke

“Shine kikazo nan kina kuka…ina Amatu din yanzun?”

STORY CONTINUES BELOW


Hannu tasa ta goge hawayen dake shimfide kan fuskarta tana jan hanci

“Sunje asibiti…”

Ta amsa muryarta na sake karyewa

“Me yasa basu tafi dake ba? Mtswww”

Abdulkadir ya karasa maganar da jan karamin tsaki. Kukan da take yana mishi wani iri 2

“Tashi daga nan”

Ya umarta, idanuwanta cike da hawaye take kallon shi

“Zan jira su dawone Hamma…”

Wani irin kallo yai mata yana fadin

“Zaki tashi ko saina watsa miki mari? Cikin sauron zaki zauna da yake baki da hankali ko?” 1

Mikewa Waheedah tayi babu shiri, tana ganinta yar mitsitsiya a gaban shi, duk da halin damuwar da take ciki bai hanata jin yanda zuciyarta take dokawa ba.

“Ki koma cikin gida. Idan naganki a wajen nan saina zaneki…”

Wasu sabbin hawayen taji sun zubo mata, duk da basu hanata kin bin umarnin shi ba, tsaye yayi a wajen yana kallonta harta sha kwana, dan dafe kanshi yayi, yana jin ranshi na baci babu dalili, bangaren su ya nufa, ko sallama baiyi ba ya wuce su Yassar da suke cikin abinci

“Ko shi da wa kuma?”

Yazid ya tambaya, Yasir ya amsa shi da

“Indai bakin ran Abdulkadir ya motsa ko babu dalili yin shi yake…”

Dariya sukayi, sai gashi ya fito, karamin tsaki yaja, dan baiga abinda zai basu dariya ba, ranshi yana baci suna dariya

“Ku komai na dariya ne”

Ya fadi yana kara jan tsaki

“Kai da uban wa?”

Yassar ya tambaya, bai samu amsa ba, Abdulkadir din yazo ya wuce yana yin ciki da kafafuwan Yazid da yace

“Ikon Allah…bani na kar zomon ba”

Shima bai samu amsa ba, Abdulkadir din ya fice daga dakin, yana doko musu kofar kamar zai karyata. Haka kawai ya tsinci kanshi da nufar bangaren su Waheedah dan bai yarda cewar ta koma ba, hangota yayi tsaye bakin kofa tana kai hannu tana goge fuskarta

“Yarinyar nan bata da hankali”

Ya furta a hankali, kukan da takeyi ma zai saka mata wani ciwon kan, ga sauro daya gama moreta a wajen da ta zauna. Da alama bata ganshi ba, dan saida ya kure mata tukunna ta ruga da gudu tana shirin komawa cikin dakin, Abdulkadir ya damqo hannunta

“Hamma dan Allah…”

Waheedah ta fadi idanuwanta kamar zasu fado, ga wani lugude da zuciyarta take mata

“Me nace?”

Kai ta girgiza mishi, hawaye na silalowa daga idanuwanta

“Me nace miki?”

Ya tambaya a tsawace

“Kar in fito… Haka kace kar in fito…”

Idanuwa Abdulkadir ya tsura mata, baiyi niyyar dukanta ba, haka kawai yaji yana son ganin ta tsorata haka.

“Wallahi Hamma kafata daya na cikin daki… Dayace kawai a waje… Wallahi” 12

Waheedah ta fadi, baisan dariya ta kubce mishi ba saida yaji sautinta cikin kunnen shi. Zahra na da wauta, bayajin kuma a cikin gidan akwai wanda yakai Nabila rawar kai, amman Waheedah cikin sanyi take nata rashin hankalin, dariya yake daya kwana biyu baiyi ba, ita kanta Waheedah din kallon shi take da mamaki, bawai baya dariya bane, amman dariya irin haka da sauti ba zata tuna ranar karshe da taga hakan ya faru dashi ba. Dayan hannunta tasa tana share hawayenta, dan karamin murmushi na kwace mata. 1

STORY CONTINUES BELOW


Hannunta Abdulkadir yaja zuwa cikin dakin, ya zaunar da ita kan kujera, da murmushi a fuskarshi ya nufi kitchen din, ruwa ya dibo a cup yazo ya kawo mata, karba tayi tana mamakin yanda batasan tana jin kishi haka ba, ta kusan shanye ruwan, ta ajiye kofin hadi da sauke numfashi, mikewa tayi

“Ina zakije?”

Abdulkadir da yake tsaye ta tambaya, muryarta a dishe tace

“Fuskata zan wanke”

Kai ya daga mata, ta zagaya ta bayan kujerar ta wuce, dan gani take inta wuce ta gaban shi zaiji yanda zuciyarta take dokawa. Kofin ruwan ya dauke yana mayarwa kitchen ya fito ya koma kan hannun kujerar dake kusa da kofa ya zauna. Fitowa Waheedah tayi, yabi fuskarta da ta kara mishi ja saboda kukan da tayi, yana tunanin kartai ciwon ido da yanda yaga idanuwan sun kumbura. Wajen data tashi ta koma tana zama, wasa take da hannuwanta, ko zuciyarta zata rage gudun da take, lokaci zuwa lokaci takan dan dago ta saci kallon Abdulkadir din da yake zaune, kananun idanuwan shi na kafe a kanta, duk da alamun shi sun nuna yayi nisa a duniyar tunani.

Hakan ne a bangaren Abdulkadir din, in da zaka tabashi ka tambayeshi tunanin da yakeyi baisani ba, balle kuma azo dalilin daya sashi yake zaune a wajen, kukan da yaga tanayine ya dame shi, shisa ya dawo kota sake fitowa, yanzun din ma yana zaune ne karya tafi ta sake fita, yana kuma so yaga dawowar su Mami din ya duba jikin Amatullah, dalilan duka sun zauna mishi, dan baya tunanin akwai wani dalili baya hakan, numfashi yaja a hankali yana fitarwa, yana jinjina ikon Allah akan Waheedah din, yanda ta kubcewa fitowa a zabaya abin al’ajabine, hannuwanta da take wasa dasu ya tsayar da idanuwan shi akai, har faratan yatsunta farare ne. 1

‘Wannan wanne irin haske ne?’ 5

Ya tambayi kan shi yana sake sauke numfashin dayasa Waheedah kallon shi, duk cikin yayyen nasu shine basa hira dashi, bakama ga wannan fuskar ba, inba gaisuwa ba, saidai in shi da kanshi ya tambayeka abu zaka amsa, amman hira kam bayayi dasu, wani irin gudu taji zuciyarta ta kara, sautin na bugawa har cikin kunnuwanta, da labbanta da ta dagasu dakyar tana fadin

“Gobe In Allah ya kaimu zaka tafi ko?”

Da mamaki Abdulkadir din ya kalleta, yana dan daquna fuskar shi hadi da jinjina mata kai, wani abu Waheedah ta hadiye da takejin shi tsaye a makoshinta, batasan ya akai take son tambayar shi ba

“Hamma sai kayi shekara baka dawo ba ko?”

Kai ya sake jinjina mata, kamar bazaiyi magana ba kafin yace

“Menene? Ba murna kuke zan tafi ba”

Wannan karin ita ta girgiza mishi kai, tana kallo ya sake kankance mata idanuwan shi kafin yace

“Karya ne…”

Yana sakata yin karamin murmushi

“Ki ban ruwa in sha Waheedah…”

Abdulkadir ya fadi yana kara gyara zaman shi akan kujerar, mikewa Waheedah tayi tana zuwa kitchen ta dibo ruwan ta kawo mishi, karba yayi yana shanyewa tas ya mika mata kofin data mayar kitchen, ta kai mintina uku a ciki tsaye batare datasan tunanin me takeyi ba. Kafin ta fito tana komawa kan kujerar ta zauna, wannan karin tana kwantar da kanta a jikin hannun kujerar, agogon dake daure a hannun shi ya duba yana mamakin gudun da lokaci yayi dan har tara da rabi ta gota.

“Kinci abinci?”

Ya tsinci kanshi da tambayarta, dan yanda ta langabar dakai a jikin hannun kujerar yasa shi tunanin ko yunwa take ji, shi kanshi baici abincin ba. A hankali Waheeda ta daga mishi kai, gyara zaman shi ya kara yi kan hannun kujerar. Lumshe idanuwanta Waheedah tayi, batasan iya lokacin da suka dauka a haka ba, balle tasan bacci ya dauketa, cikin bacci taji muryar Abdulkadir din na fadin

STORY CONTINUES BELOW


“Ya jikin nata yanzun?”

A hankali ta bude idanuwanta tana kallon Mami, da sauri ta mike tana murza fuskarta

“Mami… Ina Amatullah din”

Kallon ta Mami tayi

“Suna asibitin ita da Hajja, bacci takeyi, da sauqi ma sosai, zasu dawo da safe in shaa Allah…”

Numfashi Waheedah ta sauke, Abdulkadir da yake tsaye ya kalli Mami yana fadin

“Me yasa baku tafi da ita ba?”

Ware idanuwa Mami tayi tana kallon Abdulkadir din

“Asibitin sai munyi gayya Abdulkadir?”

Dakuna fuska yayi

“Da kun tafi da ita ai, ta zauna tanata kuka a waje”

Kallon ta Mami tayi, tana sakata sadda kanta kasa, sai yanzun take jin kunya ta lullubeta

“Harabar motoci Mami, ga sauro a wajen…nikam da kun tafi da ita”

Ya sake maimaitawa, yana kokarin tausasa harshen shi saboda Mami ce, dan murmushi Mami tayi, tasan halin yaron sarai, ta kuma san kokari yake kar maganar da yake tayi kamar yana mata fada ne.

“Ai mun dawo yanzun”

Mami ta fasi da murmushi a fuskarta. Kai Abdulkadir ya jinjina mata

“Sai da safen ku. Allah ya kara sauqi”

Yai maganar yana ficewa daga dakin kafin yace komai, kamar hakan Waheedah take jira ta karaso tana kwantar da kanta a jikin Mami data tureta tana fadin

“Ke yanzun meye na kuka? Ke da zakiyi mata addu’a? Ke komai na kuka ne?”

Dariya Waheedah din tayi tana jin hankalinta ya kwanta, bin Mamin tayi suna hira, kafin tai mata sallama ta wuce dakin su. Sai taji dakin yai mata shiru, musamman data kwanta, da yanzun Amatullah din tana mata tsegumin juye-jujen da take inta yi bacci, dan da yawan lokutta tana cikin bacci zataji Amatullah ta dala mata duka, ta kwashe kafafuwanta data jibga mata ta warbar gefe tana fadin

“Adda Wahee ki kasheni saiki huta”

Dariya tayi ita kadai, mikewa tayi ta kashe wutar dakin, tana daukar yar karamar fitila mai batir ta maqala a cikin hular dake saman kanta, tukunna ta kwanta tana janyo littafin ta dan taci gaba da karantawa. Idanuwanta da taji har zafi suke mata yasata lanqwasa shafin data tsaya din, tayi addu’ar bacci tana rufe idanuwanta, soyayyar Asma’u da Jikamshi na mata tsaye, soyayyar tasu na sata tunani kala-kala, kafin bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkin su. 1

*

Bangarensu ya nufa ya shiga kitchen tunda girkin Hajja ne ranar, tuwon shinkafa ne tayi da miyar taushe data sha albasa mai lawashi sai kamshi take. Yanajin dadin girkin Anty da Mami, amman abincin Hajja daban yake jin shi, a wajen shi duk wani abinci da zaici bayan na Hajja zai biyo, baisan ko kaunar da ke tsakanin su bace ta rufe mishi ido. Anan kitchen din ya tsaya yana dora abincin kan kantar kitchen din, hannun shi ya dauraye jikin famfon dake gurbin wanke-wanke. A tsayen yaci abincin. 3

‘Kaga zaka tafi wani gari da babu idanuwan mu akan ka, dan Allah ka rike addininka, karkai wasa da sallah, in har kana yinta cikin lokaci, kana kokarin yinta yanda ya kamata zata kare maka aikata abubuwan dabai kamata ba. Kuma ka rage zafin zuciya, dan Allah Abdulkadir ka dinga sakama ranka salama’

Nasihar da Abba yai mishi ta dawo mishi, kai yadan jinjina yana karasa cinye abincin ya wanke hannun shi ya fice daga dakin. Bangaren su ya koma, babu kowa a falon sai Yassar daya kalle shi cike da mamaki

“Daga ina kake haka kaikuma?”

Saida ya zauna tukunna ya daquna ma Yassar din fuska

“Hamma kana tsareni da tambaya kamar yaro”

Dariya Yassar yayi

“Nakai shekarun dazan fita in dawo sanda naga dama” 4

Dare yayi, dan sha daya harda rabi, gashi bayajin yana da karfin biyewa rashin kunyar Abdulkadir din da zuwa yanzun inda sabo ya kamata ace ya saba, in wani yaiwa a waje su Hajja yake jama zagi, mutane naganin bai samu wadatacciyar tarbiya ba. Abin nama Yassar takaici, mutane nabashi mamaki, yanda sukan dora laifin yara akan iyayensu batare da kwakwwarar shaidar cewa laifin na iyayen bane na ci mishi rai. A ganin shi burin kowanne iyaye dansu ya zamo nagartacce, ya zamo abinda zasuyi alfahari dashi. 2

Baice wasu lokuttan ba’a samun baraka daga bangaren iyayen ba, baice ba’a samun sakacin iyaye a kan tarbiyar yaransu ba, amman hakan baya nufin duk wani abu da yaro zaiyi saiya zamana laifin iyayen shine, kowanne dan Adam yana da zabi a rayuwa, cikin zabin harda fatali da tarbiyar da iyaye kan dora yaransu akai, a bangaren Abdulkadir din kusan zaice hakane, tun yana da karancin shekaru yake da wata irin zuciya, da ko laifi yayi in zaka kasheshi da duka bazai ko motsa ba ballantana yai tunanin gudu, ko wani yazo ya da nufin janye shi zai nuna bayaso.

Yana tuna lokuttan da Hajja ke dukan shi akan abubuwa da dama, kafin Abba yace tana binshi da addu’ar shiriya tunda dukan baya aiki, ga bakin shi bazai shiru ba, inka fadi daya saiya fadi goma, musamman in yana ganin akan gaskiyar shine, komin girmanka baka wuce Abdulkadir ya datsa maka maganar duk da tazo kan shi ba. Kallon shi Yassar yayi yana fadin

“Dan Allah ka kula da kanka, banda fada da mutane, banda rashin kunya…”

Murmushi Abdulkadir din yayi yana sa Yassar tashi daga kishingidar da yayi a jikin kujerar yana gyara zaman shi sosai

“Nasan fada dai sai kayi, dan Allah banda fadan da babu dalili”

Kankance mishi idanuwa Abdulkadir yayi

“Nasiha kake mun?” 1

Duka Yassar yakai mishi da yasa shi ture Yassar din yana fadin

“Cin zali babu kyau”

Hadi da mikewa dan kan shi yakeji ya mishi nauyi

“Idan nabar gidan saika nemi wanda zakaci zali”

Ya karasa maganar yana wucewa hadi da turo kofar dakin shi, murmushi Yassar din yayi yana komawa kan kujerar ya kwanta yana sauke numfashi. Addu’ar Allah ya tsare da ta neman saukin zafin rai yake nemawa Abdulkadir din, da damuwar yanda kanin nashi zai rayuwa shi kadai a wani gari batare da kulawar wani nashi a kusa ba…!!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *