YAR MAKIYAYA
CHAPTER 1
*Belel* K’auye ne kamar ko wanne cike da ahali iri daban daban d’auke da dabi’u iri iri, sedai duk da banbancin da suke da shi akwai abu d’aya da sukayi tarayya a kai wanda shi ne zaman lafiya, kamar dai ko wanne gari walau birnin ko k’auyen akan samu ahali mabanbanta wad’anda basu jituwa ko dai saboda matsayi ko kuma muk’ami.
Mafi d’aukar hankali cikin k’auyen wasu ahali ne guda uku mabanbanta a matsayi da kuma yanayin tafiyar da rayuwa. Wannan labari ya fara ne daga zuciyar Wannan k’auyen wanda ya kasance shine mazaunin wani katafaren gidan sarauta mai cike da gargajiya da aladu, Masarautar da babu irin ta a wasu k’auyukan na k’etare.
Daga wani b’angare na k’auyen akwai wani ahali wanda ya kasance shi na daban ne, jagora a wannan k’aramin ahali ya kasance *makiyayi* ne mai kiwon dabbobi kamar yadda kiwon ya zama gado ne gare shi haka ma ga iyalan shi sedai duk da ana musu kallon masu zama cikin lumana an gaza gane cewa cikin ko wanne ahali akwai nasu b’oyayyen k’aramin sirrin sannan kuma kowanne zai kasance yana da nashi irin burin da yake son ya cika, walau na fansa ko dai na soyayya ko ma akasin hakan. Labarin ya fara ne da …………….
💗🌷 Y’AR MAKIYAYA💗🌷
Iskar bazara ke hurawa da k’arfin gaske hakan yayi sanadiyyar zubewar ganyayyaki daga rassan bishiyoyi dake cunkushe birjik. Waje ne kamar daji.
Gabas ta nufa da dabbobin yayinda rana ke b’ullo wa hakan yayi sanadiyyar sa idanuwan ta lumshe wa sannan Iskar tana k’ok’arin yaye mayafin da ta rufe kanta da shi, k’aran da ta jiyo daga bayan ta ne ya rikita ta gaba d’aya ta kasa motsa wa sai dabbobin ta wad’anda k’aran ya sa duk suka rikice suka kasa nutsuwa, ba na farko ba kenan da ta tab’a jin Wannan k’aran ,k’aran mota ne wad’anda ake amfani dashi a gidan sarkin garin kuma yana da su iri daban daban duk da yawanci takan ji k’aran ne bayan sati sati Idan Sarki ko wani daga iyalan sa zai fita.
Teet! Teet! Motar ta sake k’ara a karo na biyu. Daga gani wanda ke zaune gefen matuk’in ya kwankwad’i boko ya k’oshi domin shigar sa ma kad’ai ya isa yin bayani. Jaridar dake hannun sa ya rufe fuska a dak’ile yayi tsaki cike da hasala yace “Filthy humans! Duk inda bak’auye yake sai ya nuna halin sa especially wad’annan gidadawan makiyayan da su da dabbobin su sam basu da banbanci!”
Shiru driver yayi ya girgiza kai.
Tun da mahaifin shi ya fara magana
*Suraj* Bai ce komai ba illa sak’ale kanshi da yayi ta window yana kallon how desperate mai kiwon ya zama hakan yasa ya bud’e motar ya fito ya tinkari inda mai kiwon yake tsaye.
Dad ba shiri ya zare gilashin idanuwan shi ya ce “what the hell is he trying to do or has he gone insane?” Driver dai bai ce komai ba se Murmushi da yayi yayinda ya cigaba da kallon Suraj wanda bai fi saura taku shida tsakanin shi da mai kiwon ba.
A garin tirka tirka da dabbobin ke yi d’aya ya buge ta, kad’an ya rage takai k’asa bata ankara ba taji Mafi k’arfin rik’o ya tarbe ta wanda hakan yasa tayi k’ok’arin rik’e abunda ya rik’e ta tun k’arfin ta saboda tsoro kuwa duk ta k’ank’ame idanuwan ta.
Cikin dak’ik’ai uku zuciyar sa ta tsaya chak kamar daskararriyar k’ank’ara, jinin jikin shi ya daina gudana for a moment ya manta inda yake ya b’ata cikin wata duniyar ta daban.
Zagayayyen fuska gareta ma’abocin haske, gashin girar ta cikakku ne wanda tsabar yawa har sun had’e tana da hanci siriri madaidaici ga kuma kyawawan lab’b’a masu kama da kunnen furen rose, abu Mafi d’aukar hankali shine idanuwan ta bayan ta bud’e su wad’anda suka kasance Emerald green wanda abu ne Mafi wuya ka samu irin shi a irin wannan nahiyar in dai ba had’i da bature ko dai balarabe ba, abu na biyu Mafi Jan hankali shine gashin kanta da ya kasance ja, babu makawa akwai wani abu na musamman tattare da ita. Da k’arfin tsiya ta fisge kanta daga rik’on da Suraj yayi mata ta fara k’ok’arin kad’a kan dabbobin domin ta bada hanya. Tayi nisa sosai kafin ta juyo karo na farko ta sakar masa da tsadadden murmushi sannan ta cigaba.
Shafa kansa yayi yana Murmushi k’asa k’asa kuma yace “does that means thank you?”
K’iran da Dad yayi mishi ne ya sa shi komawa mota yana Murmushi.
A fusace Dad ya juyo ya dube shi kafin yace ” mesa kayi haka? Why did you help her?”
Baki sake Suraj yace “Dad she was desperate and out of idea ko dabbobin ma duk sun rud’e ai ban ga laifi a ciki ba don na taimaka mata.”
Dad ya dakatar da shi ta hanyar d’aga masa hannu sannan yace ” look! I don’t care if she’s desperate, all that matters is that ita talaka ce kuma Mafi k’azanta cikin talakawa she’s no match for us, you can’t even trust such peoples, tsakanin mu da su shine su mana bauta mu taka su yadda muke so su basu kasance komai a garemu ba face k’ask’antattu”
Idanuwan Suraj sun nuna bai ji dad’in kalaman mahaifin shi ba amma yasan Dad ba irin mutanen da za’a yi wa titsiye bane a sha’anin su ,don haka bai ce k’ala ba amma da ka ganshi kasan Lallai ranshi ya b’aci….
Isowar ta gida ta kora dabbobin zuwa garken su sannan ta ruga a guje tana dariya tayi cikin daji wanda ke gefe da gidan su kasancewar gidan su yana nesa daga sauran gidajen k’auyen. Bakin wani tafkeken kogi ta tsaya ta zame kayan jikin ta gami da afkawa cikin sassanyar ruwan tana ta watsa wa tana dariya.
“Laila! Laila!! Wata y’ar budurwa wanda bazata wuce sa’ar ta ba ta nufo inda take da gudu amma maimakon ta shiga ruwan zama tayi bakin ruwan tana kallon *Laila* wanda tayi zurfi cikin nata duniyar tunanin.
Tab’e baki yarinyar tayi kafin tace “wai kam kin yi hauka ne? Ke kad’ai se dariya kike yi? Ki fito ki raka ni”
Da sauri Laila ta fito tana dariya ta kama kafad’un k’awar ta tana jijjiga wa yayinda k’awar ta saki baki dalala tana kallon ta har saida ta gama kafin k’awar ta rik’e kunkumi tace
“Yanzu kam ina matuk’ar buk’atar k’arin bayani, domin gaba d’aya kin fita hayyacin ki sai kace wanda ta fad’a soyayya?”
Laila dake zaune tana jefa dutse cikin ruwa ta fisgo hannun k’awar nata har saida ta tsorita gami da zauna wa gefen ta babu shiri tace “Kin chanka daidai !!! Na fad’a soyayya ne *Zubaina*!! Zaro ido Zubaina tayi tace “haba de k’awa ta? Waye shi?”
Kallon ta Laila tayi gami da girgiza kai ta ce ” Nima ban sani ba amma de tabbas ko ma waye shi ya tafi da zuciya ta, ji nayi kamar in bi shi mu tafi tare na musamman ne shi .!”
Gyara zama Zubaina tayi hannayen ta cikin na Laila cike da zumud’i tace “fad’a min ya kamannin sa yake? Nasan kyakkyawa ne!”
Murmushi Laila tayi ta dubi Zubaina kafin tace “ba kyakkyawa ba in takaice miki shi mak’uran kyau ne, ma’abocin tsayi yadda kika san zaki mai gurnani haka yake da k’arfi k’amshin jikin shi kad’ai ya isa Jan hankali”.
Baki a sake Zubaina tace wad’annan suffofi haka se kace aljani? Yo ai naga ko Suleiman da ya kasance wanda ya kere bazan k’auyen nan a kyau bashi da wad’annan suffofi!” Tsaki *Laila* ta ja
“Mtsew ! Ana maganar gwarzon namiji ma’abocin kyau da tausayi me zai kawo maganar wancan tankwasasshen?” Tashi muje in raka ki kafin *Inna* ta neme ni”
A tare suka mik’e suka nufi cikin gari……..Duk Mun ji farkon had’uwar Suraj da Laila ,sun kasance mutane ne biyu mabanbanta a matsayi da yanayin rayuwa ,sannan mun ga tsananin k’iyayyar talauci da talaka dake shimfid’e a fuskar mahaifin Suraj, will the impossible happen?” There’s only one way to find out!. +
***** ***** *****
A tsanake motar ke tafiya Suraj kan shi na waje ya lumshe idanuwa yana feeling yadda iska ke kad’a wa cike da burge wa ,kukan tsuntsaye masu dad’in sauraro ke dukan kunnen shi, ita kad’ai yake gani ko da ya bud’e idanuwa, Murmushin ta, that smile that melts his heart! Ya kasa manta fuskar kuma baya fata ya manta ko daidai da na rana d’aya.
Duk wannan tunani da yake yi Dad banbami yake wai kawai don ya yi taimako a hanya kuma ma talaka.
Motar bata gama Tsayawa ba Suraj ya bud’e k’ofa yayi tsalle , jacket nashi a hannu ya ruga da gudu cikin katafaren gidan sarauta da ke fuskantar su baki kawai Dad ya sake kafin yace “all this while ina ta magana ko saurare na baya yi, dubi yanda yake behaving kamar wani bagidaje he can’t even act like a Prince.” Yana kai nan wani ya bud’e masa k’ofa gami da mishi iso, cike da fankama da k’asaita ya fito daga motar ba tare da ya amsa wa Mutumin ba ya kutsa kai sashen mai Martaba wanda ya kasance mahaifin shi kuma kakan Suraj.
Kasaitaccen falo, makeken gaske cike da kayan k’awa ,zaune ya hango shi cikin sutura ta sarauta ba tare da b’ata ko da second ba ya k’arisa gaban sa ya zube yana kwasar gaisuwa
”’Kafin mu cigaba zai fi kyau musan asalin tarihin Sarkin Belel, kasancewar shi kaka ga Suraj”’
Kowacce Masarauta burin ta bai wuce mai mulkin ta ya kasance adali kuma abin alfahari ga al’ummar ta, haka ne ya kasance a wannan K’auye, gari ne wanda ya tashi tun asali ba tare da sanin komai ba na rayuwa wanda ya wuce kiwo noma da Su watau kamun kifi zaman lafiya kuwa sun d’auke ta tamkar ibada Mutum d’aya ke fad’a a ji a garin nan kuma ba kowa bane illa wani tsohon dattijo Halliru Mammadou ya kasance abin kwatance har ma a makwabtan k’auyukan ganin kyawawan dabi’u da tausaya wa na k’asa da shi hakan yasa manyan gari suka zab’e shi a matsayin Sarkin su hakan ya janyo hatsaniya mai rikitar wa tsakanin Halliru da d’an uwansa *OMAR* wanda shi ma babban burinsa bai wuce ya zama mai mulkin Belel ba ,an sha gwagwarmaya kafin daga bisani Omar ya hau dokin zuciya ya bar gida tare da matar sa Ramatou Allah kad’ai ya san inda suka shige , tun *Halliru Mammadou* yana cikiya har ya gaji , bayan an nad’a shi sarkin Belel da Watanni uku Sarauniya Aminah ta haifi d’an ta na fari *Yerima Ahmadu* bayan shekaru biyar kafin ta sake haifo na biyu *Yerima Abdul-malik* ,
Su biyun a dabi’u da halaye sun banbanta , kamar Mahaifin shi mai martaba *Yerima Ahmadu* ya kasance mai son jama’a da taimakon talaka sedai *Abdul-malik* akasin hakan yake , a wajen shi talaka ba komai bane, kuma basu chanchanta a yarda da su ba. Da wannan dabi’u suka girma kuma Kasantuwar suna da mabanbanta halaye ba kasafai suke jituwa ba abu d’aya ke ci wa *Abdul-malik* tuwo a kwarya kuma ba komai bane illa yadda bashi da ikon fad’a a ji Idan har *Ahmadu* ya yanke hukunci Toh ya zauna.
A haka suka cigaba da rayuwa har Akayi bikin
*Ahmadu* da Maryama D’iyar sarkin Madagali. Shi kuwa *Abdul-malik* ya zab’i ya tafi ya k’aro ilimi na zamani, Sarki bai hana shi ba illa saka masa Albarka da yayi.
Shekaru biyar kenan da tafiyar *Abdul-malik* karatu a Cairo ya dawo tare da wata kyakkyawar balarabiya da sunan ita zai Aura, hakan ya jawo cecekuce tsakanin sa da iyayen shi Amma daga bisani suka amince. Saida ta shekara biyu tana shanye gori da zage zage na dangi kafin kwatsam ta sami ciki, bayan wasu Watanni ta haifi d’an ta son kowa k’in wanda ya rasa. Ran suna yaro yaci suna *Suraj*.
*Suraj* yana da shekaru uku *Abdul-malik* ya d’auki matar sa *Razia* suka koma Egypt domin ya samu kyakkyawan educational background amma duk wani Hutu a Belel suke yin sa Kasantuwar yayi alk’awari wa mai martaba duk wani holiday zasu dawo. Wannan karon *Suraj* ya kammala karatun sa ne baki d’aya inda ya karanci architecture a jam’iar New York wato (NY university ) dake K’asar Amurka.
*Suraj* ya kasance mai son jama’a akasin mahaifin shi Abdul-malik, shekarun sa ashirin da uku ne a duniya 23yrs gashi mai kwazo, ga kuma uwa uba kyau bashi da kyamar d’an Adam kamar mahaifin shi all credit goes to his mother Razia da ta tayar da shi da kulawa ta nuna mishi Cewar bashi da banbanci da talaka they all are humans.
”’Wannan kenan takaitaccen labarin Sarautar Belel da kuma asalin Suraj”’Yanzu de Mun ji takaitaccen tarihin Sarkin Belel, yadda d’an uwansa *Omar Mammadou* ya hau dokin zuciya ya bar gida sannan Mun ji yadda *Yerima Ahmadu da Yerima Abdul-malik* suka banbanta bisa halayen su yanzu kuma cigaban labari zai soma. +
***** ****** *****
K’asaitaccen falo,makeken gaske cike da kayan k’awa, zaune ya hango shi cikin sutura ta sarauta. Ba tare da b’ata koda second ba ya k’arisa gaban sa ya zube gami da kwasar gaisuwa.
Da taste of royalty Mai martaba ya d’ago kai ya dubi *Abdul-malik* ya ce “Naji labarin wannan karon baka taho da Mahaifiyar Surajo ba, ina fata ba wata matsala?” Sosa k’eya yayi kai a k’asa ya ce “Tana Cairo, y’ar uwarta babu lafiya shiyasa na barta a chan amma komai lafiya.” Kai mai Martaba ya jinjina kafin ya sake wata maganar Suraj ya shigo
“Grandpa!” Ya fad’a yana dariya mai martaba yana son Suraj matuk’a gashi kuma kaf cikin jikannun gidan shine k’arami Kasantuwar akwai yayin sa y’ay’an Yerima Ahmadu kawun sa wanda suka had’a da *Abubakar, Ameer, da Saeed* Ameer ne k’arami kuma miskili, akwai shi da had’a guri,da gulma, Saeed shine na tsakiya halinsa d’aya da K’anin baban sa watau Abdul-malik ya k’i jinin talaka da talauci. Abubakar kasancewar shi babba babu ruwan sa tamkar mahaifin sa Ahmadu.
Suraj yana k’arisa wa ya kwanta kansa a cinyar mai martaba tuni suka shiga hirar su mai ban sha’awa ta kaka da jika Abdul-malik kuwa ya gaji da zama dan haka ya mik’e yayi sallama da maimartaba ya fice.
Nan Suraj ya gyara zama yana bawa kakan shi labarin yadda tun shigowar su Belel Dad yake ta masifa wai don ya taimaki wata Yarinya, ko kad’an mai Martaba bai mamaki ba don yasan halin Abdul-malik. Haka suka cigaba da hirar su har lokacin cin abinci yayi suka ci sannan Suraj yayi sallama da Kakan shi ya shiga cikin gida, kai tsaye b’angaren uncle Ahmadu inda ya tarar da shi zaune kan doguwar kujera suna hira, da Murmushi ya k’arisa ciki ya duk’a gami da kwasar gaisuwa, cike da farin ciki suka amsa Uncle Ahmadu ya jawo shi jiki yace
“Sai yanzu hirar ta k’are da mai martaba kenan, very well! It’s good to have you here son, Yaya Ummin ka take ? Naji ance bata zo ba Wannan karon, hope all is well?”
Kai Suraj ya gyada sannan ya amsa da “eh lafiya lau kawai tana jinyar sistern ta ne shiyasa bata zo ba amma zata taho daga baya”. Kai kawai Uncle Ahmadu ya jinjina gami da fad’in “Allah ya bata lafiya” duk suka amsa da Ameen.
Ya dad’e sosai a nan ma kafin ya buk’aci a kaishi wajen y’an uwanshi Kasantuwar basu had’u ba tun zuwan sa, haka kuwa akayi wani security ya yi leading hanya inda suka bar side d’in Unclee zuwa wani dank’areren side daban , tafiyar akwai rata dan haka mota suka shiga zuwa side d’in inda maigadi ya bud’e musu k’ofa cike da girmama wa motar ta kutsa kai bata tsaya ba se bakin entrance da zai sada mutum da cikin first flat, bai ko rufe k’ofar motar ba ya tsaya gami da bud’e hannayen shi ya d’aga kai sama gami da rufe idanuwan shi yana mai shak’ar sassanyar Iskar dake busawa a tsanake kana yana sauraron dad’ad’an kukan tsuntsaye masu tsuma rai ,a nan fuskar ta ya fara dawo masa, ji yayi kamar ya tsaya a haka iya tsawon rayuwar sa.
Tun fitowar Suraj yake tsaye hannu nad’e a k’irji yana kallon sa, saida ya k’are masa kallo sannan ya juya da gudu ba tare da yayi magana ba ya koma cikin falo inda ya zube rigijib kan kujera hakan yasa wayar hannun Saeed ta zame ya d’ago a fusace cike da hasala yace
“God damn it Ameer! Kai daga gulma ta ci ka gaba d’aya se ka zama tamkar mahaukaci you can’t even behave like proper prince!”
Ameer ya kwashe da dariya harda rik’e ciki kafin ya had’a hannayen shi biyu yace “Sorry! Am so sorry wallahy wani abu ne ya ban dariya ka ma san wa na gani kuwa?”
Abubakar dake fitowa daga wani d’aki yana rik’e da k’aramar yarinya da bata fi three years ba yace
“kai daman kana rasa gulmar yi ne? Mutum bashi da aiki se gulma kai ba mace ba” yana kai nan ya haye kujera ya zauna gami da d’aura yarinyar kan cikin shi yana mata wasa. Saeed ya dubi Ameer dake tab’e baki yace “ina jin ka, da wacce ka zo kuma?”.
Gyara zama Ameer yayi sannan yace “Yau kam Mun yi babban bak’o”. Daga Abubakar har Saeed suka had’e baki wajen fad’in “Waye?”.
“Crazy prince mana! I mean Suraj, yana chan waje ya tsaya ya rungume iska ya rufe idanu se Murmushi yake am scared haukar sa tafi ta da.”
Murmushi kawai Saeed yayi Abubakar kuwa wasan sa yake da yarinyar tana ta kyalkyala dariya bai ma maida hankalin sa ga labaran da Ameer ke bayar wa ba.
A yanda yake tsayen wayar shi tayi ruri daga cikin aljihu hakan yayi distracting yanayin da ya shiga ,y’ar tsaki ya sakar kafin ya d’auko wayar yaga Oummin shi ce Razia dan haka ya k’i d’aga wa ya kutsa kai ciki….