ABU-MALEEK CHAPTER 5 BY Nimcyluv
Www.bankinhausanovels.com.ng
Cafkar gashin kanta, sabida tsananin zafin daya ratsa jijiyoyin kan Julde ya sanya bata san lokacin data saki wani gigitaccen ihu tare da fasa ƙara da dukkan ƙarfinta,
Wanda hakan ya ƙara haddasa juyewar blue ɗin Idanunta wanda suka gama rinewa da jaaa sabida azabar da tayi mata yawa.
Baya Arɗo yayi cikin matuƙar jin daɗi da kuma farin cikin yau ya kama ɓarauniyar da take shiga cikin garken shanun har take samun damar tatse masa madarar shanunsa,
Zabura yay cikin son dukiyarsa da kuma son bawa dukiyar tasa kariya yace.
“Billahi Yaron nan ya kashe mu, madarar shanu ƙwarya biyu, dole ai masa hukuncin da yafi wannan, dole sai kayi mana kiwon shanu na mako biyu”
Da Zallar mamaki Lamiɗo ya tari numfashin Arɗo yace.
“Tayaya ne wannan ƙaramin yaron zai iya kiwon Nagge wajan guda 100?”
Murmushi Arɗo yayi yana mai jinjina kansa domin shi kaɗai yasan dalilin daya sanya yace haka,
Ba tare daya bada waccen amsar ba cikin bada umarni ya ƙara cewa.
“Cire sumar nan yanzu wannan kuma shi ne hukumcin ɓarawon madarar shanu, barin irin wannan a Rugar Mahinjo babban hatsari ne, domin cigaban faruwar hakan zai iya kawo daƙoshewar tattalin arziƙin Fulani makiyaya, kunfi kowa sanin cewa wannan shanun sune arziƙin dukkan wani ɗan Rugar Mahinjo,
Da kuma madarar shanun muke samun kuɗaɗan kula da wasu dukkan Nagge da suke ƙarƙashin kulawar mu”
Cike da fahimta kowa na wajan yay na’am da maganar Arɗo, domin yay amfani da abu mafi suyiwa a zuciyar fulanin wato shanunsu,
Babu wani abu dake baƙanta ran Fulani makiyaya irin nakastuwar shanunsu.
Lamiɗo ya jinjina kai tare da murmusawa, shi kaɗai shima yasan dalilin daya sanya Arɗo faɗin hakan,
Da ƙarfi kuma ya ƙara jan sumar kan Julde wacce har yanzu ya kasa kama ƙarshen sumar sabida tsayin da gashin yake dashi,
Ganin yadda Julde take ihu tare da ƙoƙarin fisgewa zata gudu yasa Arɗon Rugar Mahinjo faɗin.
“Ɗaure shi, maza kawo igiya a ɗaure wannan mugun irin”
Julde numfashinta ne ya kusa ɗaukewa sabida sabon tashin hankali,
Ita burinta a yanzu ta koma wajan Yakumbonta bata san halin da yunwa ta sanya ta a halin yanzu ba,
Da rarrafe taja Jikinta ta shiga lalubar inda take jiyo muryar Arɗo, duk da cewa bata gani amma tana iya bin sautin Muryar mutum ta isa inda yake.
Tana zuwa wajan Arɗo ta rirriƙesa tare rushewar da wani irin raunataccen kuka mai tarwatsa zuciyar dukkan wani mai imani da kuma tausayi,
Kuka take wanda yake nuni da irin hali ƙunci da kuma takurar da take ciki,
Kuka take da dukkan ƙarfinta zuciyarta, kuka ne wanda yake nunawa duk wani Mutumin dake wajan irin halin yunwa da kuma ƙishin da suke ciki ita da Yakumbo,
Kuka ne wanda yake nuni da halin ƙazantar da suke ciki domin rabonta da wanka a rayuwa harta manta,
Balle ai maganar gyaran jiki duk da cewa da fulanin daji irin su ba’a san so da haka ba.
Cikin muryar da kuka ya gama cin ƙarfinta tace.
“Kayi mini rai Arɗo, ka taimaki rayuka biyun da basu da wani mataimaki sai Allah, dan Allah kada ki cire min sumar kai ma, za’a min dariya kuma zan zama abin kallo da ƙyamata wajan mutanan Mahinjo,
Kaimin dukkan wani hukunci amma ka janye maganar cire min sumar kai, Ni macace ne, kada kuyi abinda zaku mai dani ta namiji,
Ban taɓa sata ba, yanzu halin yunwar da muke ciki ne yasa Ni fitowa neman abinda zan bawa Yakumbo,
Dan Allah Arɗo ki taimaka kada yunwa ta kashe shi, kada yunwa ya kashe Yakumbo, ka bani madarar ko kaɗan ne na bashi yasha”
Zame ƙafafuwansa Arɗo yayi yana ƙara kallon ƙyakkyawar fuskar Julde wacce take masa kama da wata halitta,
Kallon JULDEN kuma na ƙara ta fasa zuciyarsa, yana san yashi tuno da wani shuɗɗaɗan tarihi wanda tuno sa a yanzu dai-dai yake da bugawa zuciyarsa,
Cikin ɓacin rai yasa ƙafa tare da hankaɗe Julde wacce ta kasance bera a Rugar Mahinjo bata da kowa sai Yakumbo da Madibbo,
Da sauri kuma Lamiɗo yazo ya fisgi gashin kanta ya fara janta jikin wata bukka,
Gaba ɗaya mutanan Mahinjo suka mara masa baya domin suma a lokacin cike zuciyoyinsu suke da tsanar Julde wacce take shirin ganin bayan tattalin arziƙin su,.
Wani tsuhu kowa tuni ya koma gefe ya kuka wiwi, sabida a jikin shanuwarsa Julde ta tatsi nono, gashin Naggen tana da ɗauke da tsohun ciki wannan dalili ya ƙara tayarwa da tsohun hankali a tunaninsa shike nan Julde ta kashe masa abinda yake cikin shanuwarsa.
Cikin rashin Imani haɗi da rashin tausayi, Lamiɗo ya fara zubawa Julde ruwa mai sanyin a tsakiyar kanta tare da ɗaukan wani abu mai kama da sabulu ya shiga goga mata akai,
Cikin rashin Sa’a sabulun ya fara shiga cikin nakasassun Idanunta,
Wani kalar ihu da kurnani Julde ta fara wanda sabida tsabar kuka ko muryarta ba’a ji.
Wata duguwar aska Lamiɗo ya ɗauka sabu tass da ita sai sheƙi take, ya kafa askar a gaban ƙwantaccen sumar dake gaban goshinta, tunda ya ɗura askar bai dire ba sai daya zabtare gaba ɗaya rabin sumar kan.
*ABU_MALEEK IS NOT FREE BOOK, IT’S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616, ƳAN NIGER SUYI MAGANA TA WANNAN NUMBER 84506476*
A can cikin Bukkar su Julde kowa, Yakumbo wani kalar numfashi take,
Gaba ɗaya ta galabaita takai munzalin da idan Numfashin ya fita baya dawowa, a hankali ta buɗe bakinta ta shiga kiran sunan Julde tana faɗin.
“Hai kizo nan, kizo na faɗa maki wata magana kafin Ubangiji ya ɗauki raina, Julde!! Julde!! Julde!!!….” Kafin ta ƙara cewa komai numfashinta ya fara fisga ta shiga miƙewa domin babu komai Cikinta rabon da suci abinci ita da Julde har sun manta sabida zafin talaucin da suke ciki.
Shin su ba ƴan garin bane? Ko kuma dai basu da kiwo ko guda ɗaya ne wanda za suyi taƙama dashi suma a matsayin su na Fulani makiyaya?
Ko kuma dai akwai wani dalili daya sanya su cikin wannan halin?
Tabbas ruwa baya tsami banza..
Salati Yakumbo ta fara kumfa na fita ta cikin bakinta hannunta riƙe da wani abu wanda take sakinsa, a dai-dai lokacin da Lamiɗo ya gama yiwa Julde aski tass ya zamana ko jaririn da aka haifa yau ya fita sumar kai nesa ba kusa ba,
A kuma dai-dai lokacin ne Ubangiji ya amshi ran Yakumbon Julde, wanda ta tafi lahira ne cike da burin faɗawa Julde wata muhimmiyar magana Amma Ubangiji ya fita sanin komai dake cikin wannan duniyar mai cike da ruɗani da kuma tashin hankali,
A kuma wannan lokacin ne Madibbo yake can cikin daji yana haƙa rami da kuma ɓoye wani muhimmin abu, hakan ta sanya bai san abinda yake faruwa cikin Rugar Mahinjo ba.
A can Madrid kowa yau ya kasance weekend, wato ranar daya kasance hutu ga dukkan wasu ma’aikatan gwamnati,
11 dai-dai na safiyar lahadi wato Sunday, A.m ya shiga buɗe nauyayyen idanunsa wanda suke cike da tarin bacci da kuma gajiya,
Tunda ya buɗe idanunsa yaga duhu daga cikin bedroom ɗin sabida kashe hasken ɗakin da yay ya maida idanunsa ya rufe,
A hankali kuma cike da tarin gajiya da kuma ciwon da kansa yake masa a ƴan kwanakin nan,
Ya sanya hannunsa tare da ɗurawa a tsakiyar goshinsa yana murzawa a hankali sabida zufar da yaji tana tsastsafo masa,
A wannan lokacin tunani ne yake ta ziyartar ƙwaƙwalwarsa,
Wanda Yawan tunanin yake ƙara haddasa juyewar tunaninsa a koda yaushe,
Abunka da mara cikakken lafiya, wanda hankali irin na sauran mutana ne bai gama ratsa shi ba.
Tunanin Mami, da kuma kuma matar data zame masa tamkar uwa yake a wannan lokacin yake, yaya suke? Meke faruwa dasu babu abinda ya sani,
Sosai yake son zuwa gare su koda ace bazai zauna tare dasu ba,
Wata lafiyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke yana mai ganganro da hannunsa zuwa tsakiyar ƙirjinsa wanda yake ɗauke da kwantacciyar suma,
Mai kyau da tsari,
Fuskarsa, bugawar zuciyarsa ce ta tsananta da sauri ya sanya hannunsa a saitin ƙirjinsa yan kwaɓe fuska tare da marai-raice wa, kamar ƙaramin yaro,
Cike da tsoro ya ƙara buɗe idanunsa ya shiga rarraba su a cikin tafkeken bedroom ɗin nasa,
A sanyaye ya buɗe ƙyakƙyawan laɓɓansa wanda suke fresh so pink damn cute and softness, cikin can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Ya Rabbi! How can that be possible?,
Mene yasa ya kejin tsoro da kuma fargaba ne?”
Ya shiga yiwa kansa tambayar can kuma yasa hannu ya ɗan matse kansa a fili cikin slow voice ɗin nan nasa mai narkar da zuciya cike da tarin shagwaɓa yace.
“You’re mad Abu_maleek” zare ido yay sosai tare da pouting kansa da finger yace.
“What? Mad me? No!!! No!!! I’m not ni ba mahaukaci ba and never na zama mahaukaci”
Ya ƙare magana tana tsotsar laɓɓansa,
Ɗan juyawa yay kaɗan yana lumshe idanunsa sabida motsin da yaji a gefensa ana yaye duvet ɗin jikinsa, Sweet ce take yaye masa duvet ɗin, farar mage ƙyakƙyawa gata ƙatuwar gaske rainon madara,
Ganinta yasa ya ɗan yi Murmushi har sai da dimples ɗinsa ya luma tare da bayyanar teeths gave ɗinsa kana ya sanya hannunsa ya ɗauke ta cak yana shafa kanta yace.
“Mrng sweet, how was your night?”
Ya tambaye ta yana kissing goshinta, tare da rungome ta sosai ya shiga sauke ajjiyar zuciya, domin bashi da wani wanda zai magana dashi ta fahimta har ya fahimci maganar tasa a tunaninsa sama da magensa,
Yana sonta sosai, domin idan bata da lafiya sam bashi da walwala,
Kowa yana amsa sunan sa dana mahaifinsa amma shi madadin haka sai ake kiransa da sunan wani can daban, sunan da bai san lokacin daya fara ba shi dai ya riski kansa a ciki ne.
Ware idanunsa yay yana ya mutsa fuska yace.
“O’ohhh yunwa sweet lemme freshen up”
Ya faɗa yana sakinta da sauri ta sauka daga jikinsa kai tsaye shima ya miƙe sai lokacin ƙyakkyawar halittar jikinsa ta ƙara bayyana kana ganin Abu_maleek kansa cewa give of Allah bawai haka kawai ya kasance a duniya ba,
Akwai tarin ƙaddarori a tare da shi.
Kai tsaye bathroom ya shige yana zuwa ya sakarwa kansa shower, duk da cewa yau gashin akwai sanyi sosai ga snow da take ta zuba.
Ruwan shower na sauka a jikinsa yana sakin ajjiyar zuciya yana gamawa yay brush kana ya nufi mirror’n dake bathroom ɗin gigice kuma yay baya da sauri sabida idanunsa da suka sauka akan.
*ABU_MALEEK NA KUƊI NE, IT’S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 ƳAN NIGER SUYI MAGANA TA WANNAN NUMBER 84506476*