HEEDAYA CHAPTER 9 BY By Khaleesat Haiydar
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan isha Shuraim ya shigo parlon kaka da sallama, kaka dake xaune ta sa tv gaba wai tana kallo tace “Ni ai na
xata ka wuce, ka ma ci abinci kuwa ko basu ga daman baka ba?” Ya xauna saman kujera yace “Bana gidan, yanxu na
dawo, ina su Khadijah?” Kaka tace “Waye kuma su Khadijah, tun karfe shidda suka wuce kamar ana tsungulinsu ai,
kuma uwar ce ta koya masu idan sun xo kar su dade, wannan yarinya Deedayah kadai ce kwance tana bacci a daki,
to ni bata fiye min su ba ma Allah na tuba…” Bai tanka ta ba, bayan wani lkci yace “Toh ki taso ta xa mu wuce…” Kaka ta juyo da sauri tace “In taso ta kuma, nan din da can gidan naku ba daya bane xan taso ta? ko kuma me xata
maku idan ta je can gidan ban da wahalar da ita da ku ke” Yace “Abba bai ce in bar ta a nan ba” Kaka tace “To dama
ya xai ce a bar ta a nan in cinyeta ga ni mayya, sai ka shiga ka daukota ku wuce ku bani waje, idan haka ne ma kar a
sake kawo min ita ko nace a kawota, baka ga ba har kitso sai da nayi mata na wanke nata hijabi da ta 6ata da lemon
da wnn mutumi Sudess ya bata shi kuma wahalalle, ita kuma wnn sabuwar matar ta rantse baxata daina sa mata
kayan shegu ba, har nace xan bada kudi a siyo atamfa ko ‘yan dubu dubu a dinka mata, to ba ruwana na fasa….”
Mikewa Shuraim yyi ya shiga cikin dakin, kwance ya tadda Heedayah tsakiyar gadon Kaka tana bacci manyan
kalaban da kaka tayi mata ya rufe fuskarta, ya karasa bakin gadon yana kallonta kafarta ya buge amma bata ko
motsa ba, ya sake buge kafar ta juyo ta bude idanuwanta da suka kumbura a hankali, kana ganinta kasan ta ci kuka,
yace “Sakko kar in wuce in bar ki” Jin muryarsa ta fara sakkowa tana lalube lalube ta mike tsaye, kama hannunta yyi
tana bin sa kamar xata fadi suka fita dakin, ya dau makullin motarsa saman kujera yace “Sai da safe” Kaka tayi
masa banxa ita a dole an tafi da Heedayah, dai dai bakin kofa ya ji an wurgo masa abu a kai ya juya ya ga Hijab din
Heedayah ta jefo masa, ya rike Hijab din yyi ficewarsa ya kulle mata kofarta…. A kusa da motarsa ya sake hannun
Heedayah bayan ya bude motar, ita dai tana tsaye sai bin inda taji motsi take da ido, yace “Baxa ki shiga ba sai na
wuce na bar ki?” Kamar xata yi kuka tace “Toh ai bana gani, Kar ka wuce don Allah” yace “Xa ki kwana a nan kuwa
idan ni xan saka ki cikin motar” da sauri ta fara ta6a motar tace “Aa plsss” Ta laluba jin motar a bude ta shiga, kulle
motar yyi ya xaga xai shiga side din driver sai ga Sudais, ya jira har ya karaso, Sudais yace “What about Heedayah?”
Ba tare da Shuraim ya kallesa ba yace “Tana wajen kaka, sai da safe” Sudais yace “Ohk a nan xata kwana?” Shuraim
yace “Ehh” Sudais yace “Alright, sai da safe” Shuraim yace “Allah ya kai mu” daga haka ya shiga motarsa yayi
reverse, Sudais ya koma ciki. Shuraim na isa gida yyi parking a parking space ya fito ya bude back seat, kwance ya
ganta ta koma baccin, bude gate da aka yi yasa ya juya yaga Abba ne ya shigo gate din from mosque, Tashinta ya
shiga yi yace “Sakko mu shiga ciki we are home” Bai jira tace komai ba ya sauko da ita ya kama hannunta ya nufi
entrance din shiga gidan walking calmly… Mami na kallon Heedayah dake xaune saman kujera tace “Toh shine kike
kuka Heedayah?” Cikin rawar murya tace “Da xafi ta min, kaina yana ta ciwo yanxu” Mami tace “To yi hakuri xai
daina my dear….” Abba ya bude kofar parlon Mami ya shigo, Mami na kallonsa tace “Welcome…” Yace “Thank you,
sai yanxu suka dawo” tace “Ehh gashi kaka tayi mata kitso ma” Abba na kallon idon Heedayah yace “What
happened to her eyes?” Mami tayi dariya tace “Kukan kitso mana” Heedayah ta fara shessheka tace “Abba xafi yake
min” Abba yace “Xafi kuma?” Ta gyada masa kai, yace “Toh a kwance” Mami tace “A kwance? nan da gobe fa xai
daina xafin” Abba yace “No a kwance gaskiya, wnn kitson ai an dauresa da yawa, Kar ya ja mata matsala, till date
Rabi’ah bata kitso a gidan nan sbda irin haka” Mami tace “Ikon Allah….” Abba ya fita don daukan wayarsa dake ring,
Mami na kallon Heedayah tace “Toh baxa a kwance ba mu je ki kwanta, kin dai ci abinci Koh?” A hankali Heedayah
ta gyada mata kai, Mami ta kama hannunta ta wuce da ita bedroom, ko da ta fito a parlonta ta tadda su Khadijah da
Rabi’ah a xaune kana ganinsu kasan Abba ne ya saka su shigowa, duk suka gaisheta, ta amsa tace “Kun debi abinci a
kitchen?” Khadija tace “Uhn mun ci” Ranan dai duk a bangaren Mami suka kwana. Da Asuba Shuraim na dawowa
masallaci ya tafi part din Mami, a hankali ya kwankwasa kofar, Rabi’ah ta bude, tace “Yaya ina kwana?” Yace
“Lafiya, ina wannan yarinyar take?” Ta d’an turo baki tace “The blind girl? Tana can daki” yace “Fito min da ita”
juyawa tayi ta koma, Mami na kallon Rabi’ah tace “Waye?” Rabi’ah tace “Ya Shuraim, yace wai in taho da ita” Mami
tace “Bata jin dadi sai gobe” Rabi’ah ta juya ta koma ta gaya ma Shuraim, wani ajiyar xuciya ya sauke ya juya ya
wuce part dinsa…. Da safe misalin karfe goma sha daya Abba na xaune parlonsa da Junaid, kasancewar ranan lahadi
ce, Abba ya mika ma Junaid takardun hannunsa ya amsa yana dubawa, Abba yace “Asibitin Mecca aka yi duka wnn”
Junaid na ci gaba da duba takardun gaba daya yace “A kano kenan” Abba yace “Yess” Junaid yace “Ohk….” Shuraim
ne ya shigo parlon da sallama ya kulle kofar, tun da ya shiga dakinsa da asuba sai a lkcn ya fito, ya xauna nan kasa
ya gaida Abba, sannan suka gaisa da Junaid, Abba na kallon Junaid da duk hankalinsa na kan takardun yace “So xan
baka kudi ka siyo eye drops da aka yi prescribing before the operation….” Junaid yace “Amma ba yanxu aka sa xa
ayi operation din ba Abba” Abba yace “Yess ba yanxu ba amma lkcn xai xo in sha Allah” Ta gefen ido Shuraim ya
kalli Junaid ya dauke kai, Junaid yace “Toh Allah ya kai mu” Abba yace “Yanxu pharmacy din da xa a samu
maganin xaka duba, sai ka min texting din Price with ur details” Junaid ya d’an yi murmushi ya mike yace “In sha
Allah Abba, xan wuce sai anjima” Abba yace “Allah ya kai mu…” Sallama yyi ma Shuraim sannan ya fita, Heedayah
na kitchen tare da Mami dake gaya ma maid din gidan what to cook for lunch, ko da wasa bata yrda ta bar Heedayah
tare da su Rabi’ah kawai ba, jin an bude kofar Abba ta fito daga kitchen Junaid yace “Xan tafi Mami sai anjima”
Heedayah dake makale da Mami jin muryarsa da sauri tace “Mami xan bi sa plss” Junaid na kallonta yace “Baxa a je
da ke ba” Ta wani murguda baki tace “Kar aje din” Gyada kai yyi ya juya ya nufi kofa ya fita, a hankali Heedayah
tace “Mami wucewa yayi?” Mami tayi murmushi tace “Ehh” Heedayah ta marairaice tace “Did he want to be wicked
like that man” a kunnen Shuraim da ya fito parlon Abbansa shi ma, Mami tace “Which Man?” Heedayah tace “Wnn
da ya tafi da ni a mota jiya mana, wannan da Abba yace ya min karatu ni ban san sunansa ba… Kawai nasan shi
mugu ne” A hankali Shuraim dake jin duk abinda take cewa ke tafiya xuwa dakinsa, Mami tace “Toh kansa yyi ma mugunta ai ba ke ba” Heedayah tace “Aa ni yake yi ma ba kanshi ba” Mami ta kama hannunta suka bar wajen. That
same day da yamma Mami na main parlor tana danna wayarta tare da Heedayah da su Rabi’ah da suka dawo
islamiyya aka bude kofar parlon, Mumy ce ta shigo da sallama sakale da handbag dinta, Su Khadijah suka ta fi da
gudu cike da murnan ganinta suka rungume ta, Mumy ta shigo parlon tana murmushi tace ma Mami “Sannun ku da
gida” At first Mami bata yrda da ita take ba sai da ta kalleta ta ga ita take kallo, tace “Yauwa sannu da xuwa” Mumy
tace “Don Allah akwai dari biyar wajen ki xan ba d’an sahu wai ba shi da canjin dubu daya” Mami tace “Ohk,
Rabi’ah shiga bedroom gaba mirror akwai kudi ki dauko” Rabi’ah ta tafi xuwa bangaren Mami, Mumy tace “Ban da
ma yanxu yan sahun sun xama abinda suka xama nan nan da Marafa wai dari biyar” Mami tace “Toh Allah ya rufa
asiri” Mumy ta tabe baki tace “Ameen dai” Rabi’ah ta fito ta mika ma Mumy dari biyar din Mumy tace “Aa kai masa,
ni bari in shiga ciki duk na gaji wllh” daga haka ta wuce bangarenta Khadijah ta bi ta da sauri, Mami ta d’an yi wani
boyayyen murmushi tana ci gaba da danna wayarta. Junaid na tsaye babban pharmacy bayan ya basu takardan
maganin da yake nema, pharmacy uku yana xuwa sai su ce bbu eye drop din, amma wnn na hudun ya ci sa’a an
samu, wani mutumi ne tsaye gefensa cikin shiga ta alfarma, ya siya magunguna shi ma ana masa packaging dinsu,
da yake pharmacy din yawanci duk manyan mutane ne ke xuwa, Daga gefen Mutumin kuma wata matashiyar mata
ce sanye da hijab har kasa warce baxata wuce 38 ba, Mutumin ya amshi maganin kenan matar ta yanke jiki ta fadi
nan kasa, wanda hakan ya jawo hankalin mutanen wajen, Mutumin wanda da alamar mijinta ne ya durkusa da sauri
ya rikota, Junaid ya duka shi ma yana mata sannu cike da tausayin ta, ledan hannun Mutumin junaid ya amsa,
Mutumin ya daga ta suka fita pharmacy din mutane na mata sannu, Junaid ya bi bayansu har xuwa gun wani
lafiyayyen mota, sai bayan da Mutumin ya taimaka mata ta shiga motar sannan junaid ya mika masa magungunan
dake hannunsa yace “Allah ya sauwake….” Mutumin yyi murmushi yace “Ameen mun gode, thank you very much”
Junaid ya mayar masa da murmushin yace “No thanks, amma da ku yi kokarin wucewa asibiti daga nan she looks so
sick” Mutumin yace “In sha Allah, nagode” Junaid yace “You are wlcm sir” daga haka ya juya ya koma cikin
pharmacy din don biyan kudin eye drops da ya xo siya, waya ya gani kwance kasa daga inda matar ta fadi, ya duka
ya dau wayar ya sake fita da sauri amma har motar su ya bar haraban pharmacy din, juyawa yyi ya koma ciki rike da
wayar….. Sai da Magrib Junaid ya isa gidan Abba da eye drops din Heedayah, Mumy dake xaune parlor ya gaisar da
ladabi, ta amsa da fara’a tace “Sannu da xuwa” Ya xauna nan parlon yace “Ya gida?” tace “Alhmdllh, Ya sunan naka
kuwa?” Ya kalleta yace “Junaid” tace “Maa sha Allah, ka shiga tana can ciki, da kuwa a nan take xaune tace bari taje
tayi sllh….” Junaid ya mike yace “Toh…” Da sallama ya bude kofar parlon Mami, ya ga Heedayah kadai xaune tana
cin apples da aka yanyanka mata a plate, dauke plate din yyi a hankali, bayan ta cinye na hannunta xata dau wani ta
ji wayam, ta gama lalube lalubenta amma bbu alamar plate, a hankali ta dinga bin parlon da kallo kamar xata yi kuka
tace “I know it’s youuu” ya ja hancinta ya ajiye mata plate din sannan ya xauna saman kujera, Mami ta fito tace “Ka
samo drops din?” Yace “Sure…” Wani sabon ringing ya ji a aljihunsa, lkci daya ya tuna wayar mutanen daxu, ya ciro
wayar sannan yyi picking call din ya kai kunne tare da sallama, bayan sun gaisa normal Junaid Yace “Sorry daxu
you lost ur phone at the pharmacy, na fito kuma naga ka wuce, ina ta jiran kira tun safe ba a kira ba” daga daya
bangaren Mutumin yace “Yea ban lura bane da wuri wllh, thank you very much, I almost gave up but nace nayi
trying kawai sbda contacts dina” Junaid yyi murmushi yace “Toh where shud we meet sai ka amshi wayar?”
Mutumin yace “Yanxu dai muna hospital da Madam, but Alhmdllh da sauki, and in sha Allah gobe da safe xa mu
koma Abuja, we resides there… so I don’t know ko xaka fada min inda kke…” junaid yace “Ayya, to I will try and
bring the phone to you tomorrow in sha Allah” Nan suka yi sallama Mutumin na kara masa godiya…. Heedayah tace
“Toh me yasa ka dauke min Apples dina?” Ya saci kallon Mami da ta juya ta koma ciki, sannan ya mike ya koma
inda take yace “Ban sani ba” tace “To kai ma ba ruwana da kai….Junaid ya ja hancinta yace “Ni da wa?” Tace “Kai da wnn mana, ni ban san sunansa ba, kai sai ka dinga tsokanata shi
kuma sai ya dinga buge min hannu yana min fada” fitowar Mami ya sa Junaid ya mike yace “Mami sai da safe, xan wuce” Mami tace “Ka ci abinci ai?” Yace “Na ci” Mami tace “Toh Allah ya tashe mu lfya” kofa ya nufa, Heedayah
tace “Mami ina xa shi?” Mami tace “Xai wuce gida” Heedayah tace “Mami me yasa baxai tsaya a nan da mu ba?”
Mami tayi murmushi tace “Ai xai dawo” Heedayah tace “Ni ina son ya tsaya a nan” Junaid ya kalleta daga bakin
kofar da yake tsaye ya bude kofar ya fita. Da asuba aka tashi da ruwa sosai, wajen shidda da rabi Mami na parlonta
aka kwankwasa kofa, mikewa tayi ta bude kofar Shuraim yyi kasa da kansa yace “Ina kwana?” Tace “Lafiya lau”
yace “Xa mu yi karatu ne” Juyawa Mami tayi ta wuce daki, Heedayah na ta bacci tun bayan da ta tada ta yin sllh
asuba, Mami ta tada ta, ta sa mata Hijab sbda garin yyi sanyi sosai suka fito, har snn Shuraim na tsaye bakin kofa,
Mami ta mika masa ita, ya kama hannun suka fita parlon ya kulle mata kofarta, Heedayah dai har snn idonta a
lumshe yake tana bin sa, da sauri ta bude idanuwanta jin ta ci karo da sofa a parlor, ko tsayawa Shuraim bai yi ba har
ya isa study area din Abba still holding her hand ya xaunar da ita nan kasa, kamr xata yi kuka tace “Shine ka buge ni
da kujera?” Strictly yace “Kin san Allah idan kina min magana a gidan sai na fasa maki baki wataran, I have no
business with you, if u dare talk to me again I will injure you” Yana yin yanda yake maganan yasa Heedayah tayi
shiru bata dai ce komai ba, he was so serious, fuska daure yace “Sai na ce ki fara karatun??” A hankali ta fara karato
suran da take, yana ta danna wayarsa har ta kai inda ta tsaya shekaranjiya, tace “Na gama…..” Sai bayan kusan minti
biyar ya ajiye wayar hannunsa sannan ya daura daga inda ta tsaya, his recitation was waow, kamar wani balarabe,
Bai tsaya ba sai da ya sauke suran gaba daya snn ya daga kai yana kallonta, baccinta take hankali kwance bayan ta
jinginar da kanta da arm chair dake wajen, ya dinga kallonta sannan ya kalli agogo dake nuna karfe bakwai ya mike,
parlor ya wuce ya ga Rabi’ah sanye da schl Uniform yace “Je ki tada wnn yarinyar ki kai ta ciki” Bai jira cewarta ba
ya wuce xuwa dakinsa. Abba na kallon Mami yace “Listen Rahinah, I know u are not after the income or anything of
such, but….” Ta girgixa kai tace “But what Barrister? Ba mu yi da kai xan ajiye aiki ba, ba mu yi haka da kai ba, I
can’t… Aikina ya xama jinin jikina, it’s part of me, I like my profession, ko ba komai I do help innocent soul that are
not quilty and I enjoy doing that, so why are you trying to deprive me of the joy? Tunda har na iya kula da nawa
yaran still ina aiki, har na aurar da daya, I can take care of little Heedayah also with my work, just that before 3 xan
dinga dawowa gida….” Abba ya kasa cewa komai, can ya jinjina kai yace “Toh shkkn Rahinah baxan takura ki ba, I
agree ki ci gaba da aikin ki” Tana kallonsa tace “I appreciate, Anjima matar da xata dinga kula da Heedayah when I
am away xata iso, monthly xa a dinga biyanta dubu ashirin, I will pay that….” Yace “No you don’t need to….” tace
“A’a na sa a raina ni xan biya, I took that as my responsibility since I can be with her fully….” Yace “Toh kin san
matar da xa a kawon” Mami tace “Ehh to ban santa ba garinsu daya da wata childhood frnd dita Shamsiyya, she said
shesy good kuma xata iya” Abba yace “Shhkn, Allah ya mana jagora” tace “Ameen Great Man” D’an murmushi yyi
yace “So ynxu dai tare za mu dinga fita da safe?” Dariya tayi tace “Not at all, karfe goma ni xan dinga fita, sai nayi
ma Heedayah duk abinda ya kamata, ido kawai Mai aikin xata sa mata har in dawo” Abba yace “Alright” Karfe
goma saura matar da Mami ke jira ta iso gidan bayan an mata kwatance ta waya, Mami ta fito main parlor, matar da
baxata wuce talatin ba ta sauka har kasa ta gaisheta, Mami tace “Sannu da xuwa ya hanya” Matar tace “Alhmdllh
Hajiya” Mami tace “Ya sunan ki?” Matar tace “Sunana Karime” Mami tace “Toh karime aikin ki ba wani da yawa
bane, amma yana bukatar saka ido da kula…” Karime tace “Duk an koro min Hajiya, Kuma in sha Allahu xan iya,
har ma da aikin gida idan da akwai duk xan yi babu damuwa….” Mami tace “Toh Alhmdllh, yanxu dai mu je in nuna
maki inda xa ki ajiye kayan ki” Karime ta mike da sauri ta dau Ghana must go dinta ta bi bayan Mami, Dakin masu
aiki Mami ta kai ta, Mai aikin Mumy dake xaune dakin ta gaida Mami, Mami ta amsa sannan ta sa karime ta ajiye
kayanta suka fita, Mami ta kai karime parlonta tace “Nan ne bangarena, bana son ku wuce nan ke da ita, in dai tana
bukatan wani abu na ci ki bar ta ita kadai ki tafi kitchen ki nema mata, xan nuna maki kitchen din da Inda komai ke
ajiye…. Tsakanin ki da Allah nake son ki kulan min da yarinyata bbu ha’inci” Karime tace “Kai Hajiya ai d’a na kowa
ne, xaki sameni me riketa da gaskiya in sha Allahu….” Mami tace “To maa sha Allah…. Ki tafi can dakin naku,
warce kika samu a ciki daxu ta nuna maki inda xaki ajiye kayan ki sannan ki dawo….” Karime ta mike ta nufi kofa
tace “Toh Hajiya” Mami ta xauna saman kujera don tayi deciding yau baxata fita ba xata yi monitoring yanda
Karime xata kula da Heedayah. Junaid ya mike daga xaunen da yake yace “To Mami ai ni baxan san size din sweater
da xan siyo mata ba, Kuma wani irin takalmi kenan?” Mami tace “To kai makaho ne? Look at her mana before
going…” Ya dai yi shiru bai ce komai ba, can ya nufi kofa murya can kasa yace “Sai na dawo….” har xai fita tace
“Then go with her kar kaje ka siyo wanda baxai yi mata ba har takalman ma a gwada mata, ka siyo ma Farida ma
takalma biyu with a sweater” ya juyo yace “Toh” Mami ta kalli Karime dake xaune kasa tace “Ki duba daki ki dauko
Hijab dinta da takalmi xa su fita, ai na nuna maki inda suke” Karime tace “Toh Hajiya” Da sauri ta shige dakin
Mami, Heedayah dake xaune gefen Mami ta washe fararen hakoranta jin xa a fita da ita, Mami na lura da ita ta
girgixa kai ta d’an yi murmushi, Shi kansa Junaid kallonta yake, Karime ta fito da sauri ta sa ma Heedayah hijab
dinta da takalmi, Mami ta mike xata shiga daki don dauko turare ta sa mata, Karime ta dauke cup din da Heedayah
ta sha cornflakes ta fita xata kai kitchen din da Mami ta nuna mata, a parlor ta tadda Mumy xaune tana kallon tv duk
da gaba daya bata ma san abinda ake a tvn ba, Kwarjinin Mumy kadai ya isa a gane ita ma matar gidan ce, Karime ta
d’an duka tace “Sannu da hutawa Hajiya” Mumy na kallonta a dakile tace “Yauwa…. Ke ce sabuwar mai aikin da ta xo yau?” Karime tace “Ehh ni ce” Mumy ta d’an saki fuska tace “Sannu da xuwa, daga wani garin kika xo?” Tace
“Daga kano na xo Hajiya, a can mariri iyayena suke” Mumy tace “Maa sha Allah, ai ko nasan Mariri…” Karime tace
“Allah sarki” Mumy tace “Toh kin ci abinci kuwa” Karime tace “Na ci wllh Hajiya” Mumy tace “Toh ki saki jikinki
kin ji, ko me kike bukata ki xo ki sameni….” Karime ta kara dukawa har kasa tace “In sha Allahu Hajiya, Nagode
Sosai sosai, Allah ya kara girma” Mumy na murmushi tace “Ameeen” Karime ta mike ta wuce kitchen, Mumy ta bi
ta da kallo….. Ba a dau lkci ba sai ga Junaid ya fito rike da Heedayah, Junaid ya gaida Mumy, da fara’a sosai ta amsa
tace “Sannu Junaid, xa ku fita ne” yace “Ehh xa mu je mu dawo” Mumy tace “Ke ‘yar fara ba gaisuwa?” Heedayah
dai tayi shiru, Junaid ya duka dai dai fuskarta yace “Can’t you greet?” A hankali tace “ina kwana” Mumy tayi dariya
tace “Ina wuni dai xa ki ce baby” Heedayah tace “Ina yini” Mumy tace “Lafiya lau, xo in gyara maki Hijabin” Junaid
na rike da Heedayah ya kai ta har gaban Mumy, Mumy ta gyara mata Hijab din tana kara goge mata bakinta tace
“Me kika ci haka?” A hankali Heedayah tace “Cornflakes Mami ta bani” Mumy tace “Ahh Lallai ga alama, to sai
kun dawo” Junaid yace “In sha Allah” yana rike da hannun Heedayah suka nufi kofa, Mumy ta bi su da kallo har
suka fita parlon sannan ta sauke ajiyar xuciya tana jijjiga kafa. Anguwa ce ta manyan mutane da suka yi fice aka
kuma san da su a kasa Junaid ya shiga, a hankali yake driving, Lkci lkci yake kallon Heedayah dake gefensa xaune
ta jinginar da kanta da glass din motar idonta a waje kamar dai me gani, Junaid yace “Tell me what you are
seeing….” ta juyo xuwa Inda take jiyo muryarsa a hankali tace “Darkness” shiru Junaid yyi driving slowly, can ya
kamo hannunta daya murya can kasa yace “What color?” Ta wara ido tace “Just dark” Bai kuma cewa komai ba yyi
parking dai dai wani gida da yake tunanin gidan da yake nema ne sbda number da ya gani daga gefen gate din gidan,
dialing din number dake call logs dinsa yyi ba a dau lkci ba aka daga, yace “Gani a kofar gidan if I’m not mistaken”
ajiye wayar yyi bayan an sanar masa ana xuwa, Heedayah tace “Ina muka xo?” Yace “Somewhere” tayi shiru kmr
me son gane ma’anar somewhere da yace, can tace “Ohk wani waje?” Murmushi yyi yace “Yes” Bude gate da aka yi
yasa ya kalli gate din ta cikin tinted glass dinsa, Mutumin jiya ne ya fito gate din, Junaid ya bude motarsa yana
kallon Heedayah yace “Ki jirani in dawo yanxu” Ta 6ata fuska tace “Noo plss go with mee” yace “Yanxu xan dawo
am not going anywhere” Ganin kiris ya rage ta fara kuka ya dau wayarsa yace “To rike min…” daga haka ya fita
daga motar ya kulle ya nufi gun Mutumin dake tsaye, gaisawa suka yi, Mutumin yace “Fatan dai ban mu yi
inconveniencing dinka ba, mu ma anyi delaying flight dinmu ne” Junaid na mika masa wayarsa yace “No, not at
all…” Mutumin ya amsa yace “I am very grateful, ni Sunana Ahmad” Junaid yace “I am Junaid” Alhaji Ahmad yace
“Nagode kwarai Junaid” Junaid yyi murmushi yace “Babu damuwa, ni xan koma” Alhaji Ahmad yace “Toh Allah
ya kiyaye, da numberka ka kirani ai…” Junaid yace “Ehh” Alhaji Ahmad yace “To maa sha Allah I will save it” daga
haka Junaid ya koma motarsa ya tada, Alhaji Ahmad dai na tsaye har yyi reverse ya wuce….. Karfe shidda saura
Junaid ya koma gida tare da Heedayah bayan ya siya masu rigunan sanyi da takalma ita da Farida, Mami ta dauko
eye drop da ya siyo jiya bayan ta kai kayan daki tace “Barrister yace idan ka xo sai ka gaya min yanda xa ayi da
wnn” Junaid ya amshi ledan maganin ya fiddo su guda biyu yace “Wannan idan xata yi bacci da daddare xa a sa
mata just two drop in each of her eye, shi kuma wnn idan ta tashi da safe, it’s should be everyday ba a skipping…..”
Mami tace “Toh shkkn Allah ya sa a dace, su kuma maganin mene?” Yace “Toh ana sa rai with the help of this idan
an xo yin operation din idon baxa a samu matsala ba idan Allah ya yrda….” Mami tace “Toh Allah ya sa” Mami tace
“Babu wani wanda xata dinga sha?” Yace “A’a, sai dai in bincika” tace “Toh Shkkn….” Mikewa yyi yace “Ni xan
koma Mami” tace “Baxa ka jira ka ci abinci ba?” Yace “Aa xan wuce” tace “Toh sai gobe” Khadijah ce ta shigo
parlon Mami da sallama hannunta daya rike da plate me dauke da cake da aka yanka gida biyu yan madaidaita, daya
hannunta kuma da wani cake din tana ci, ta karaso gun Heedayah dake xaune tace “Mumy tace ki dauki naki” Mami
ta kalli Karime dake rakube waje daya tace “Ki amsa ki ajiye mata” Karime ta taso da sauri ta karba, Khadijah na
kallon karime tace “Dayan aka ce ke ma ki dauka” Karime ta kalli Mami, Mami tace “Toh an gode” Khadijah tace
“Cousin dinmu ne yyi birthday” Mami tace “Allah ya raya sa” Khadijah ta juya ta bi ta gefen Junaid ta fita, Mami na
kallon Heedayah tace “Xa ki ci cake?” Heedayah ta gyada mata kai, Mami tace “Toh bata Karime ke ma ki dau naki”
Karime ta mika ma Heedayah daya ita ma ta dau daya ta fara ci, Heedayah na kallon Inda take jin muryar Mami tace
“Mami in tsan masa?” Mami ta kalli Junaid dake tsaye bakin kofa har sannan tayi murmushi tace “Cinye kayan ki ya
wuce” Juyawa Junaid yyi ya fita dakin, Heedayah ta fara cin cake dinta, dai dai bakin kofar shigowa yau yyi karo da
Salima, tana rike da gyalenta da jaka a hannu, suna hada ido ya bata hanya…. Cikin wani siririn murya tace “Noo ka
wuce mana ai kai ka bude kofar….” Ya kara kallonta sannan ya bi gefenta yace “Thank you” tace “Haba thank you
kuma, ai kai ka bude kofa” shi dai bai tsaya ba kuma bai ce komai ba yyi wucewarsa, ta bi sa da kallo ko kiftawa
bbu… Karime ce kitchen bayan Magrib tana dafawa Heedayah Indomie, tana xuba Indomie din cikin ruwan dake
tafasa kan gas aka bude kitchen din Mumy ta shigo, ganinta tace “Aiki kike yi Karime?” Karime tace “Ehh Hajiya
Indomie nake dafa mata” Mumy tace “To ke kin ma ci abinci kuwa” tace “Ehh dama na rana bai kare ba….” Mumy
tace “Na rana kuma, kin ga idan kin kai masu Indomien ki xo ga cous cous a kula ki diba ki ci kin ji, abincin rana ai
ya huce yanxu” Karime tace “Toh Hajiya Nagode Sosai” Mumy tace “Amma fa kar ki wani ce ma uwar dakin ki
nace ki xo ki amshi abinci ke dai kawai ki shigo kitchen ki diba kije can dakin ku ki ci” Karime ta risina tace “Toh
Hajiya” Mumy ta ajiye cup din hannunta ta fita kitchen din…..