AFUWA BOOK 1 CHAPTER 2 BY JAMILA HALLIRU G/DUTSE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Hajiya Ummi a yanzu na yarda da shawarar da kika ba ni a’baya, don haka Anas zai gamu da ni, wallahi sai yabi ra’ayina dan nice na haife shi”. Zaune take q dakin mahaifiyarta ta hade kai da gwiwa tana ta sharbar kuka ita yanzu bakin ciki goma da ashirin ne ya hadar mata da farko dai abinda anas yayi mata na biyu kuma tunanin kwana a cikin wannan gida na ubanta wanda ko fanka babu ciku balle kuma ayi maganar inji
Ta dago kai ta kalli innarta tana kokarin tuka tuwo ta sake jin wani kunci a cikin ranta shin wai mai yasa ta yanke hukuncin tahowa gida ne? Mai yasa ba zata zauna ta gasa shi ba, gaskia ba zata iya kwana cikin sauro ba don inma ta haqura ta kwana babu yaddah za,ayi ta runtsa kunji fa masu karatu kamar ba gidan ubanta ba ko kuma ba a cikin gidan tayi rayuwa ba tayi saurin mikewa don bin umarnin zuciyarta inna ta dago daga tukin tuwon tace ya naga kin miqe ba cewa yayi zaizo ya daukeki ba
Eh haka yace amman naga dare ya soma yi wata kila wani uxurin yake don haka gara na tafi
ZAMU TASHI
Bilki ta fada ba tare da tana kallon Innar ba. – . Ita ma ta maida kai da yin abin da yake gabanta tare da cewa. gaida gida”. Ba tare da ta amsa ba, ta yi waje zuciyarta cike da jin haushin Anas, wai mai yasa zata koma, mai yasa zata yi masa fushi kuma ta koma bayan bai nuna mata ya gane kurensa ba? Anya
ba zata koma ba? Ki je, wallahi in kika yarda ‘ kika koma ba yadda za a yi ya zo dan shi ma yayi fushi. °Wata zuciyar kenan ta ke yi mata wannan gargadin. Haka ta haKura ta shiga a daidaita sahu, ta – -koma tana Kulla irin gashin kuman da zata yiwa _. Anas din. Www.bankinhausanovels.com.ng
******
“Anas!” Dadi ya yi kiransa da murya mai karfi da yasa Anas din tsorata, dan haka ya amsa . cikin kidima. “Mai ya hana ka zuwa wajen Nafisa bayan mahaifiyarka ta baka umarnin lallai ka je?” “Kayi bahuri daddyy wallahi jiya na yi niyyar zuwa,
hadari ne ya hana shi yasa, amma yau zan jen. “Yi min shiru maKaryaci, a ina akayi ; hadarin ana tafka sanyi, kai ne ka hada hadarin ko?” Yayi saurin dagowa domin ya manta yanzu lokacin sanyi ne, dan -haka ya sunkuyar da . ’ kansa yana tunanin yadda za a yi ya sanya wani a cikin zuciyarsa bayan Bilkisu. Anas tashi ka bani waje, kuma wallehi kada ka yarda na sake jin labarin ba kaje wajen Nafisa ba, domin yau saura Www.bankinhausanovels.com.ng sati biyu bikin, kuma dole kaja wa matarka kunne a kanta, dan kada a kai ta tayi mata ko kuma ta koya mata diban albarka, duk da nasan da wahaia Nafisa tayi koyi da irin dabiunta shi dai Anas bai ce komai ba, shin yaya zai yi ya iya hada wata diya mace.da bilkisu kuma har yayi musu adalci? A gaskiya da — wahala. Haka ya mike ya fita duk jikinsa babu laka, dan tunanin yadda za ma a yi ya tunkari Bilkisu da wannan maganar. Kuma ya san ya ma zama dole ya gaya mata, sai dai duk abin da zata yi tayi, wata Kila ma ta rage yi masa wulaKanci a gaban abokansa
‘da ma sauran jama’a shi yasa zai gaya mata, inyaso ta fashe dan haushi.
Babu wata damuwa a tare da ita sai ma alamun jin dadi da ya bayyana. Ta dan kalle shi tace.
“Anas wallahi ni ba zan taba shiga damuwa dan kawai zaka yi aure ba asali ma dadi na ji.
Anas kai da kanka ka san ni ba Karamar mace bace, duk inda zan juya dole maza da mata su bini da ido, mata su yi tsaki saboda takaici, Maza suyi cizon yatsa da burin. samun mace kamar ni. Anas ni na san ba zaka taba auro mace kamar ni ba, dan haka ta zo wata Kila rabon a sha wahala ne”.Ta sake dubansa da kyawawan idanunta, ta yi masa wani lallausan murmushi, tace. “Ka daina damun kanka, domin na kere kowace irin diya mace da zaka auro, dan haka ina ~ yi maka fatan alkhairi”tana gama wannan magana ta mike tsay Da sauri Anas ya dago ya dube ta, bakinsa abude yace —A’a Bilkisu ina kuma za ki?” . Tace, “Zana je in kwanta, domin ka san lokacin barcina yayi”“Haba Bilkisu mai yasa kike so ki Kaurace min yan..Www.bankinhausanovels.com.ng
Anas ka rufa min baki”Bilki ta katse masa magana da yin tsawa. “Kana bani mamaki, domin makantar da kake ta Karya. Anas niba ballagaza bace balle ace duk sanda kazo gare ni ina lale da kai, sai ka ‘ bari in ka auro kucakar matar da aka jona maka sai ka juyata duk yadda kaso, dan na San ba zata – kai ga ajina ba”.Anas ya karyar da kai, yace.“Shi kenan uwargida sarautar mata, ai duk _ + yadda kika ce haka zaayi”. Ta yi wani luuu da ido, tace. “Ka bari sai nayi tunani, kuma kai da kanka ka san bana bi sai dai a bini”Ta juya tayi waje tana wani karairaya.
Anas ya runtse ido dan yadda son Bilki kullum ba ya raguwa sai Karuwa, shi yasa a ‘yanzu ya soma neman tsari da ‘wannan wahalar SOn
Ita kuwa Bilkisu har ga Allah ba ta ji komai a cikin ranta ba, dan ba ta dauki wannan aure da muhimmanci ba, dan tana ganin Nafisa a cikin munana ma zata iya zama lamba biyu, in dai ba ta zama lamba daya ba, dan ta santa sosai diyar yar Momy ce mahaifiyar Anas, kuma ya sha gaya mata cewa, kaf a cikin danginsu babu wanda. jininsu bai hadu ba kamar Nafisa; amma saboda tsautsayi ake son hada su aure. Wannan tunani na Bilkisu shi yake Karawa zuciyarta Karfi da jin kai, kuma ta Ki saka abin koda akan harshenta ne, balle kuma yaje zuciya.
BAYAN SATI BIYU
An sha biki ba laifi duk da angon ba ya so, amma tsoron iyayensa ya sa ya yi wani abu.
_ Akwati goma ya yi wa Nafisa, ita kuwa uwar girman kai ta ce sam sai dai abata kudin. ~ domin ba ta buKatar wata sutura, wai ko dan kada~ Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisar ta sa ita ma tasa ace sun sanya iri daya, gara ta nunawa duniya da akwai bambanci. Haka aka sha biki aka kai amarya gidanta, . kuma kowa ya watse. Abin da yafi bawa. Nafaisa mamaki, yadda ta kasa sanya angonta a cikin ido ‘tsayin kwana goma sha biyu koyaushe sai taji Kugin motarsa ya fita Yau ma ji ta yi ya fita dama ta gaji da zaman-shiru dan haka ta fita ta hau sama, wajen Bilkisu wai ta kai gaisuwa a matsayinta na Yaya . Babba Tayi mamakin jin abin da Anas yake fada _cikin daga murya da fushi.. “Wallahi Bilkisu kin yi Karya, dan na gaji da yadda kike juya ni kamar raKumi da akala, daga yau na kafa miki doka ta dole kibi wani umarni da. na baki in kuma kinqi wallahi zaki gane kuranki”“Anas kana magana ne mai kama. da tatsuniya, wai dole sai na haihu tunda nace bazan haihu yanzu ba ai sai ka zura min ido kuma kana so na haihu ne duk in zama tsohuwa komai nawa ya saki ka zo kuma kana tsanata? Wallahi ba zai yiwuba, kuma wallahi ni ban taba jin irin wannan ba in ‘ya’ya kake so ai ba nice kawai matarka ba, ka ga wata Kila ita zata yi biyayya a gare ka, kasancewarta wadda ba ta da matakan tsaro a jikinta.
Ni kuwa ka kalle ni tun .daga sama har Kasa zaka ga babu abin da ban hada ba, dan haka ka tafi da Allah in ka cika kai mai zuciya ne kada ka kuma zuwa inda nake har sai ta haihu kun yaye, ka gani Bilkisu ta damu da kai, ko kuwa?”“Bilki haka kika ce? Da bakinki ko?” Haka na ce Anas, dan na san ko baki mahaifiyarka ta yi maka ba zaka iya yini ba ka ganni ba balle iyayin shekara daya ko biyu”.. ° “Anas ya kada kai cikin bakin ciki ya fita Jin ya taho ne ya sa Nafisa juyawa a _ hankali ta sauka ta shige dakinta.
Shi ma ,Anas dakinsa ya shige, ya fada bandaki ya fesa wanka, sannan ya shirya a cikin kaya marasa nauyi ya feshe jikinsa da turare, ya nufo dakin Nafisa. Tana kwance saman doguwar kujera tana karanta wani littafi ADALCI KO ZALUNCI? Ya yi sallama ya shigo. Da sauri Nafisa ta tare shi tana nuna masa kulawa, kuma tana jero masa sannu da zuwa.Ya saki murmushi ‘ya dube ta, sai ya ji . wani irin tausayinta ya kama shi, domin Allah ba zai bar shi ba dan yana zaluntar baiwar Allah ba gaira babu dalili. ; Nafisa ta durKusa a gabansa idonta cike da Www.bankinhausanovels.com.ng hawaye, tace. “Yayana dan Allah ka yi min AFUWA domin tun farko haka Allah ya Kaddara, kwma ka. san wani ba ya auran matar wani, dan Allah kayi hakuri ka karbe ni a metsayin matarka Wallahi _ zan yi maka biyayya kamar yadda baiwa keyi’ wa Sarki, ko kuma ubangidanta biyayya”’. . Ta sake runtse idonta, sai hawaye suka Kara tsawaita Ta sake kallonsa ta ci gaba da Anas na san kana Kina saboda bani da. kyau, ko kuma kana ganin munina. Anas na godewa Allah, domin in an fika, to kai kuma kefi kare, dan haka har Allah Ya karbi numfashina ba zan taba raina halittata ba, dan nima ganina nake babu ya ni, dan Allah dan uwana kayi min AFUWA kai ma ka dinga kallona kan fuskata da kyau kamar yadda ni ma nake ganinta haka”. Anas da duk jikinsa ya mutu dan tausaya mata, shi ma ya durkusa yana goge mata hawaye, cikin murya mai taushi yace.
, “Ki ‘yi hakuri Nafisa, wallabi ni bana gudunki domin muni, dan ban ganki da shi ba. Nafisa ki yi min AFUWA”. Anas fada cikin marairaicewa. Nafisa ta yi masa murmushi, duk kuma da dumbin hawayen da suke zubowa daga. idonta. Tace.
“Na yi maka AFUWA dan uwana, duk da ba kai min laifi baYa runtse idanu yace. -Na gode. ‘yar uwata, Allah ya sa sai mutuwa ce zatarabaumu dake”.Nafisa ta ji kunya ta rufeta, dan haka ta mike ta shige dakida gudu.
Anas ya yi mumnushi ya mike shi ma yabits Www.bankinhausanovels.com.ng
***********
Yadda ta ke taunar, kai da kanka ka san har da rainin wayo a cikinsa, dan tana yi tana yi masa kallon sama da Kasa. Sai da ta hadiye ta
dauki lemo mai sanyi ta kora ta juyo ta kalli Anas cikin isa da iko ta ce.
“Anas mai ka zo gaya min bayan ka san laifin da ka yi min?” Anas jikinsa duk rawa yake, ya dago ya yi mata murmushi ya ce.
“Haba madam, ai ni na san bana faifi a wajenki, dan duk abin da na yi za a iya yi min AFUWARSA ko da…”
“Yi min shiru Anas”Bilkisu ta fadi haka cikin tsawa.
Hakan ya sa ya-yi saurin hadiye ragowar maganar da ke bakinsa ta,dawo ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa ta dauki Kafa daya ta dora akan ~ daya, sannan cikin isa da mallaka ta soma kiran sunan Safiya.
– Ai kuwa Safiyar kamar tana labe, sai ga ta da sauri cikin girmamawa ta durKusa a gabanta ta ce. “Anti ga ni”
Ganin Bilkin ta yi mata wani kallo ta watsar ta ce.
“Dama so nake ki soya min ragowar hantar nan ki kawo min yanzu ina buKatarta”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Safiya tayi dan jim kamar tana tuna wabu, sai da Bilkin ta doka mata tsawa da cewa “Ba ke nake yi wa magana ba?” Ta yi firgigit tace. “yi hakuri Anti, wallahi dazu Anti Nafi ta ce in yi mata farfesunta, ni kuwa na yi ban yi zaton zaki buKata ba shi ya sa na yi, amma akwai kaji sai in kawo miki tunda ya ishe ki…” “Dabba! ‘yar matsiyata, wato ni in bar abu – _amma a bawa wata mummuna ta cinye saboda ba _ a saba ci a gidan iyaye ba ko? To wallahi taciwa kanta bacin rai, ko kuma in yi mata dukan da zai sa dole ta yo aman abin dataci”. Anas da ke gefe ya yi Kuri yana kallonta, ya hurar da numfashi ya dubi Safiya yace. — “Safiya je ki kinji in kin je ki turo min – Nafisa”.. – Dama Safiya haka ta ke so, dan yadda ta tsani irin wannan balbalin bala’in da Bilki take yi mata. Ta fita da rawar jiki tana karkarwa. . Bilkisu ta yi saurin juyawa ta kalli Anas a murtuke tace. Www.bankinhausanovels.com.ng “Mene ne nufinka Anas?” Kafin ya yi magana Nafisa ta shigo cikir ladabi da biyayya, ta yi musua sallama. . Duk su biyun babu wanda ya tanka mata, ita ma hakan bai sanya ta ji haushinsu ba, dan. inda sabo ta saba.Ji ta yi shirun ya‘yi yawa, dan haka ta. katse shirun da cewa. “Gani Yeya kace inzo Bilki ji ta yi bakin ciki ya cika mata zuciya, ta dubi Anas tace. “Anas ka gaya wa wannan jakar daga yau kada ta kuma kiranka da Yaya, dan ba kowane ~baki ne ya iSa ya sauya maka suna ban dani ba, dan haka kada ka kumA yarda da wannan. Kuma ka yi azamar gaya mata abin da ya sa kayi kiranta dan ka san bana buKatar duhu a gabana”. Anas ya dubi Nafisa, yace. “Nafi da izinin wa kika shiga kicin’ din matar gida ki ci abin da ya dace da ita kadai taci . shi? Da sauri Nafisa ta kalle shi kamar zata yi “‘magana, kuma sai ta fasa. ; Ganin haka ya sa Anas yace. To daga yau ina so in ja miki kunne, duk . abin da kike so a cikin gidan nan ki tambayi matar gidan in ta ba ki umarni ki yi, in kuma ta ,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG