AUREN KWANGILA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Washegari iyalin Sanata Abdulkarim su ma suka iso, suka dauko su a airport ita da Abdul’ azeez da Salah direba, don ba jituwa ce sosai tsakaninta da dangin mijin nata ba cikinsu babu wanda ya damu da harkarta, haka ake rayuwar. Don ‘ya’yanta ma ta koya musu irin halinta na raina mutane in ba wanda suke (under the same social class) ba. Da Hajiya Zainab da nata iyalin kawai ta ke mu’amala, tunda su masu farcen susa da mukami ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ita Mammah ba damuwa ta yi da harkarta ba, ita ta ke shige mata duk da haka babu wanda ya nuna mata wani hali mara dadi, an yi mata barka da zuwa kamar kowa, yaranta sun shige cikin su Usman suna ta harkokinsu, Abdu’azeez tun zuwansa washegari ya wuce Tahfiz dinsa bayan sun dauko Anty Zuwaira.
A daren ranar bayan an gama cin abincin dare, Mammah ta kwance musu zare da abawa na rayuwar Hafsat, Daddy ba ya nan lokacin kuma su ma ba ta
gaya musu halin da ta ke ciki da shi ba a kan rikon yarinyar. Ta sani idan ta fada Baffa Atiku ba zai yi masa ta dadi ba, don sau tari shi yake ‘correcting’ dinsa kan halayensa na masu jajayen kunnuwa da suka yi masa katutu. Kowa shiru ya yi cikin Www.bankinhausanovels.com.ng tausayawa, Baffa Atiku ya ce, a miko masa ita ya yi mata addu’o’i na neman tsari daga sharrin mutum da aljan, irin wadda yake yi wa duk dan da aka haifa a zuri’ arsu, mace ko namiji. Baffa Atiku malami ne sosai masanin addinin muslunci.
ZAMU TASHI
Alherin Daddy a kan yarinyar ta fada ba other dark side din ba, ta ce ya yi mata khutbah da sunan Inna Hafsatu, ya yi mata haqiqa, ya dau nauyin madararta da iliminta in Allah ya raya ta. Daddy ya gama mata komai da wannan alfarmar ba za ta tozarta shi ba a kan dan kankanin gazawarsa. Sosai haka abin yake har zuciyarta.
Anty Zuwaira ce kawai ta dan nuna hali. Yamutsa fuska ta yi, ta ce, “Adda Maryam anya ba ki yi wauta ba? Zamani fa ya canza, ba ka rikon dan da ba kai ka haifa ba saboda gudun abin da gobe za ta haifar da butulci na al’umma a yanzu”. Hajiya Maryam ta Www.bankinhausanovels.com.ng harare ta, kafin ta ba ta amsa, “Me nake so ta rama min da shi in Allah ya raya ta?”
Ta tsattare ta da ido. Zuwaira ta yi shiru, don ta rasa amsar ba ta gaskiya. Ba abin da ba ta da shi a rayuwa, me ta ke bukata jaririya ta biya ta da shi na rikonta in ta girma? Jin ta yi shiru Hajiya Maryam ta kara jefo mata tambaya. “Idan don Allah ka yi rikon a wajen wa ka ke neman sakamako?”
Gabadaya suka hada baki wajen fadin, “A wajen Allah. Allah ya ba ki lada”. Zuwairan Abdulkarim ba ta kara magana ba. Kwanansu uku cif, Zuwaira biyu suka dunguma har ‘ya’yansu suka wuce cikin Makkah don gabatar da aikin hajji. Hotel din Hilton Ambassador ya kama musu dukkanninsu. Azumi da Suhaana su kadai aka bari a Jeddah, sai maza ma’aikata. Mammah ce ta ce su zauna a gida har su dawo, duk don ta zauna lafiya da Daddy ya sake cikin iyayensa da ‘yan uwansa, babu wadda ba ya son gani din. Allah shi ne mai rayawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Aka ce ko jinjiri ya san mai kaunarsa, ba karamin sabo Suhaana ta yi da Mamma ba. Mai ba ta abinci, mai yi mata wanka, mai yi mata komai, mai lullube idanunta da murmushin kauna irin na UWA. Mai bata dumin jikin da uwa ke ba wa danta. Mai lallashinta in tana kuka, mai bata abinci akai-akai, mai kula da lafiyarta da kai ta check up asibiti akai-akai don treating lalurar ta. Mai saya mata duk wani abu na jin dadin rayuwa da yaro dan gata ke bukata. Daina ganin Mammah da ta yi cikin gidan sai ya sabbaba mata rashin kuzari da rashin walwala.
Azumi ba ta san Hafsat Suhaana na da nimoniya ba, saboda da ta zo babu A.C a dakin da ta ke, amma don samun wuri irin wanda masu aiki suka gada, da jama’ar gidan suka yi kaura, sai ta ke yi musu shimfida a falo ta kure musu A.C abinta. A lokacin ana zabga bala’in zafin nan da rana mai shiga kwakwalwa na_ kasar Saudiyyah, ta ce a ranta, “ bari mu dana A.C kamin masu gidan su dawo” . In tana shan ruwan sanyi Suhaana ta nuna tana jin ki shi, shi ta ke ba ta. Ta barta da ‘yar shimi tsakiyar AC wai ta sha iska, rannan da ruwan sanyi ma tayi mata wanka tana fadin “ zafi yayi yawa kada kiyi kuraje A kwana uku da tafiyar su Mammah, ranar cikin dare tana bacci ta ji numfarfashi irin mai fita ta baka ba ta hanci ba. Ta bude ido a hankali, ta ga yarinya na girgiza da sankarewa. Tuni ta bude ido gabadaya, ta mike zaune ta kamata tana girgizawa, tana fadin, “Na shiga uku ni Azumi. Wayyo Allah na!”.
Ta rarumo wayarta a caji bayan ta kankame ‘yar a jikinta, ta danna wa Mammah kira.
An yi sa’a Mamma ba sa barci da wuri, tana tare da su Luba, Furairah da Mariya da Murja wadanda suka iske su a can jiya. Hira suke yi a kayataccen falonsu na hotel . Addah da Inna Ramatu da Anty Zuwaira sun shige daka sun yi barci, shi kuwa Daddy da ma ba sa tare, dakinsa daban shi da Baffa Atiku da Www.bankinhausanovels.com.ng Abdul’azeez da su Farhan yaran dan uwansa, Halim ne kawai tare da Mammah, ya dade da yin bacci. Wayar Mamma ta yi kara, ta daga ta duba kamin ta amsa, Azumi ce. Haka kawai ta ji gabanta ya fadi, kiran me Azumi ke mata cikin dare haka, karfe goma sha biyu da rabi? Da sauri ta amsa, “Azumi ya ya? Ince ko lafiya?” Cikin makyarkyatar murya ta ce, “Ina fa lafiya Mammah? Suhaana ta sassankare min, numfashi ma ta baki ta ke yinsa, idonta ba ya buduwa”’Mikewa tsaye Hajiya Maryam ta yi tana dafe kirjinta cikin matsananciyar faduwar gaban da ya fi na baya. Ta daure a hankali ta ce da ita. “Wanka ki ka yi mata da ruwan sanyi?” Da sauri Azumi ta ce, “A’ah”’Ruwan firij ki ke ba ta bana filas dinta ba?” Gaskiya na ba ta sau daya da ta sa kuka sanda nake sha tana so ta sha, amma dan kadan”’.
A.C ki ka kunna mata?” Hajiya Maryam ta fada cikin son kecewa da kuka, da a kusa suke sai ta manta da yawan shekarunta ta kantsa mata mari.
Eh, toh mukan zauna a falo, kin san zafi ya yi zafi a nan Jeddah”. Mamma haushi da takaici suka rufe ta, amma kokari ta yi ta danne fushinta, tana fada wa zuciyarta laifinta ne ba na Azumi ba, domin ba ta gaya mata ba, bai kamata ta tuhume ta a kan laifin da ba ta da masaniya a kan faruwarsa ba. Cikin gaggawa tace, “Ba ki san ba ta da lafiya ba? Da nimoniya aka haife ta, ku fito get yanzu zan turo asibiti su dauke ku”Ta katse kiran, ta sake kiran Dr. Unaisa. A gurguje ta gaya mata, ta ce ba matsala za ta turo ambulance a dauko su yanzu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hankalin Hajiya Maryam bai kwanta ba sai da Dr. Unaisa ta tabbatar mata an ba ta duk taimakon gaggawar da ta ke bukata. Bacci ya dauke ta, ta kara da cewa, “ She’s now breathing normally , kwantar da hankalinki’. Ta yi ajiyar zuciya suka yi sallama. Ajiye wayar tata ke da wuya ta hango idanun ‘yan uwanta a kanta, duk suna mata kallon me ke faruwa ? Ta gaya musu, Luba ta ce, “Me ya sa ki ka ce su zauna a gida tunda kin san tana da lalura?”’ Ta yi ajiyar zuciya cikin damuwa, “Bana so ta sha wahala ne, kin dai ga yadda aikin hajji yake”’.
Duk suka yarda da hujjarta. Su Murja da basu da labari duk aka gaya musu. Tun daga ranar bayan an sallamo su daga asibiti, Azumi ba ta kara kunna A.C ba, ba ta kara ba ta ruwan sanyi ba. Tana kiyayewa wajen yi mata wanka, wato da an gama wankan a nade ta cikin shawul a sa mata suttura kafin iska ta shige ta, koyaushe tana manne a jikinta. Kullum sai Mammah ta kira don jin lafiyarta da yadda suka kwana. Tana gaya mata inda matsala komi kankantarta ta kira ta gaya mata. Cikin sati hudu cif suka kammala sauke faralinsu suka dawo Jeddah. Mammah ta ga ‘yarta ta kara girma, ta kara zama buleliya, jazur da ita wanke hannu ka taba. Ta dauke ta ta rungume tana sunsunarta, ita ma Suhaana sai kyalkyala dariya ta ke. Sunan mahaifiyarta da ta sanya mata ya kara mata kaunar yarinyar, don bayan SUHAANA da ta sanya mata, wani zubin sai ta ce ADDAH TA. Kwana uku su Adda suka kara a Jeddah Www.bankinhausanovels.com.ng jirgi ya kwashe su dukkansu, ya mayar gida Najeriya ana cike da shaukin juna, kamar kada a rabu. Abdul’ azeez binsu ya yi, ya ce zai karasa hutun nasa a gidan Kawunsa Abdulkarim tunda Tahfiz din ma da yake daukar haddar sun yi hutun aikin hajji.
**********(
Haka rayuwar gidan ta koma yadda ta ke, yau da dadi, gobe babu tsakanin Ambasada Hamza da matarsa Maryam a kan Suhaana. Yarinya tana girma shakuwa na kara karfi tsakaninta da ‘yan uwanta uku; Usman, Isma’eel da Halim. Kaunarta ga matar da ta dauka matsayin mahaifiya, wato Maryam Dakata na kara karfi. Haka nan ta saba da uwar goyonta Azumi, Daddy kuwa ko hanya ba ta hada su sai guri ya kure. A haka Hafsat ke girma, tana tashi da kwazon son karatu wanda ta tashi ta ga ‘yan uwanta ukku a kan turbarsa. Tun ba ta isa shiga Www.bankinhausanovels.com.ng makaranta ba ta haddace alifun, Ba’un har zuwa karshe. Ta haddace ABCD har zuwa karshe, ta kuma iya rubuta su. Duk kuma ta koya ne a wurin Isma’eel, Usman da Halim. Lokacin da bakinta ya fara budewa da sunan Mammah ya fara budewa ‘MOMMAH”’. Ta dauki tsawon lokaci kafin bakinta ya iya furta Ishma’el, Usman da Haleem tare da Baba Azumi. Bayan wadannan mutanen guda biyar ba ta san kowa ba, ba ta saba da kowa ba. Ba ta da wani abu mai muhimmanci da ya wuce su, sai karatunta. Ba ta taba sanya DADDY a jerin mutane ba. Ya fi mata kama da wata halitta daban, wadda in ta ganta ta ke neman maboya, ta ke zurawa da gudu wajen uwar goyonta saboda gizagon da muzuran da yake mata. Shi kuwa Abdul’azeez ko ya zo ba ta cikin shirginsa. Bai dauke ta a bakin komai ba bayan wata mutum “YAR KARO mai zaman cin arziki a gidansu. Sam ba ta cikin shirginsa, ko kyakkyawan kallo ba ta samu daga gare shi, halayensa sak! Na ubansa. Shekaru na mirginawa, rayuwa na juyawa dauke da ci gaba da nasarorin rayuwa iri-iri a gidan Hamza Dakata da sauran ‘yan uwansa da ke Najeriya, Sanata Abdulkarim ya samu_nasarar hayewa kujerar ministan huldar Najeriya da kasashen ketare, Ibrahim autan Adda ya gama karatunsa a jami’ar Ahmadu Bello ya samu aiki a Federal Inland Revenue Service (FIRS) da taimakon Dr. Hamza, yarinyar da yake nema ma Sa’adiyya an ba shi an yi bikinsa, suna zaune unguwar Jambulo a Kano. Minister Abdulkarim ne ya gina masa gida. Uncle Idris autan su Www.bankinhausanovels.com.ng Ambassador ya kammala karatun likitancin da yake yi a jami’ar Maiduguri ya dawo Kano, ya kama aiki da asibitin Malam Aminu Kano. Yayi aure da wata likita Tauheeda suna zaune a gidajen likitoci na asibitin. Kowa a gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata ya tsaya da kafafunsa, ya kafa iyali ba mazan ba, ba matan da ke gidajen aurensu ba, babu mai jiran dan uwansa ya zo ya ba shi, Ambassador Hamza da kawunsa Minster Abdulkarim sun tsaya musu, sun kafa su yadda ya kamata, zuri’arsu bakidaya sai sam-barka. Shekarar Hafsat hudu ta gama Raudha (nursery), kuma a shekarar ta wuce firamare aji biyu aka sanya ta maimakon daya (double promotion) a ‘Halah International School’ da ke birnin Jeddah, Isma’eel ya gama firamare ya_ shiga sakandire yana aji biyu, Usman na ajin karshe a firamare a shekarar nan zai fita, Halim na aji hudu, ‘yar Momma ko kuwa ‘yar karo in ji Abdul’ azeez tana aji biyu.
Sau tari in ya kalle ta daga nesa yakan tuno mahaifiyarta, musamman in ya ganta ta gifta ta gabansa, hatta tafiyarsu iri daya ce, idanunta da bakinta duk na Habiba ne. Amma fa hali ya bambanta, tun a kananun shekarunta ya lura ba ta da sakin jiki da mutane kamar Habiba, ita dai Mammah da Baba Azumi, koyaushe tana jikinsu kamar ‘yar mussa (mage), sannan su kadai ne masu jin muryarta, bako irinsa sai dai ta bi su da ido daga nesa, ko gaisuwa albarka, sai in Mammah ta ce ta gaishe shi. Sam ba ta cikin ‘yan kayansa, ba ta dame shi ba amma har gobe uwarta tana ransa. Bai damu da ita ba kamar su Ishma, haka abin yake a wajenta ita ma, ganinsa ta ke wani bako mai zuwa gidan lokaci zuwa lokaci, mai irin idanun Daddy masu gizago da muzurai kamar dodanni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Su Usman su ce ‘Mammah’, Hafsat ta ce, ‘MOMMAH’. Hausarta ba ta fita sosai. A shekarar da Abdul’azeez ya kammala karatunsa na sakandire a (Regent-Abuja) ya zana jamb , ya nemi gurbi a jami’ar Ibadan (University of Ibadan) a shekarar ne wani abin alhini ya samu wannan family.
Abin alhinin kuwa shi ne, an yi wa Ambassador Dakata sauyin wajen aiki da karin girma, daga Saudi-Arabia zuwa kasar Belgium.
*******
BELGIUM
Kasar Belgium na daga cikin
manyan kasashen Europe, ita ce headuquater ta dukkan (European Union and Nato). Babbar kasa ce mai tarin albarkatun kasa. An kirkire ta a shekara ta (1830), tana makwabtaka da kasashen Neitherland da Luxemburg. Belgium sautari a kan kira ta da “Battle field of Europe’, ko kuma ‘cockpit of Europe’ saboda karfin rundunar sojojinta. Sunan Belgium ya samo asali ne daga ‘Gallia Belgica (Roman _ province) a (100BC). Ana kiran mutanen kasar Belgium da ‘Belgians’. Belgium ta samu ‘yancin kanta a shekara ta (1830) 4th October . Manyan yaren kasar guda biyu ne; Dutch; wadanda ake kira Www.bankinhausanovels.com.ng ( Flemish) da kuma Frenchspeakers; (walloons) . Kadan daga cikinsu. kuma_ suna amfani da harshen Jamus musamman jama’ar Brussels babban birnin kasar Belgium. Brussels City, a matsayinsa na Capital Territory ya fi kowanne state na kasar girma da fadi, da hada al’ummatai daga ethnicities dabandaban. Don haka birnin Brussels shi ne inda hukumomin jakadancinsu yake, kuma a nan ne Ambasadodin kowacce kasa ke zaune.
********
Maimakon su yi murna da wannan sauyi da karin girman da Daddy ya samu sai suka shiga alhini mai dumbin yawa, suka soma tunanin yadda za su iya barin birnin Jeddah da kasar Saudiyyah bakidayanta, sun yi mugun saboda rayuwar Jeddah, shiga Harami , makarantunsu, makotansu, abokanansu da komai na garin Jeddah, ba yadda suka iya, aikin jakadanci ya gaji hakan. An sanya musu ranar tashi sati biyu masu zuwa, gida Nigeria za su fara sauka su huta na wata guda, kafin su tattara zuwa Brussels. Suhaanah, ba ta san me ake yi ba, ta ga dai Mamma nata parking kayayyaki, tana zirga-zirgar shiga kasuwanni. Siyayya ta ke kamar me a Baaba Sheriff . su Ishma kullum cikin damuwa suke. Ba ta da sha’awar wai ta tambaya ta ji me ake yi, jikinta ya ba ta ko mene ne ba mai dadi ba ne a gare su. Sai ita ma ta dauki damuwar ta sanya wa ranta. Ana gobe za su tashi Www.bankinhausanovels.com.ng zuwa gida Najeriya Mammah ta zaunar da ita tana yi mata bayani. Adda ta kina ta ganin abubuwa ba za ki tambaye ni ba? Ni wannan shirun naki yana damuna wallahi, a ce mutum ya yini zungur babu umh bare umh-umh sai karatu? Ko Mungo Park in yayi karatu ya gaji yana ajiyewa ya shiga cikin “yan uwansa a yi mu’amala mai dadi da shi, in ya ga abin da bai sani ba ya tambaya. Addah ki dinga sakin jiki da al’umma don Allah, watarana babu ni, na mutu, in kin ki yin sabo da kowa sai ni ranar da babu ni yaya zaki yi? In kin ga abin da ya kamata ki nemi sani akai, ki dinga tambaya”. Turbune fuska tayi kamar zata yi kuka “don Allah Mommah ki daina zancen mutuwa. Insha Allahu tare zamu mutu. Ban ga abin da zan tambaya
ba ne, na fahimci kamar za mu yi tafiya ne, na ji kina gaya wa Anty Safiyyah ranar litinin (gobe) za mu tafi. Na ji kina zancen tsaraba da su Addah, inda za mu je ne ban sani ba”. Murmushi Mammah ta yi, ta janyo ta gefenta na dama, “Na bari Addah, ni na so na mutu yanzu ban goya ‘ya’ yanki ba? Ban shirya miki kasaitaccen dakin aure ba? Gida za mu je, kasar haihuwarmu, inda tunda aka haife ki ba ki taba zuwa ba sai dai su su zo”Suhaana ta ce, “Nigeria?” Mammah ta ce, “Ashe kin san sunan kasarmu?” “Na sani mana, ba inda Yayan su Ishma yake karatu ba? Garinsu Adda Hafsatu da Baffa Atiku”. Dariya Mammah ta yi tana bubbuga bayanta, “Ke ba garinku ba ne? Wato na su Addah ne da Yayan Isma’el?” “Jeddah ne garinmu Mommah, da Makkah da Madinah don Allah mu ci gaba da zamanmu……” Sai ta sa kuka. Kuka sosai Hafsat ke yi Mammah da Baba Azumi suna lallashinta, Mammah na fadin, “Mutum ya taba gudun asalinsa Addata? Ba fa kasarmu ba ce Saudiyyah, aiki ne ya kawo Daddy, Najeriya ma na da dadi…” Mommah za mu dawo? Ina son makarantarmu bana son barinta”“A ko’ina akwai makarantu,Www.bankinhausanovels.com.ng makaranta sai wacce ki ka zaba zan kai ki a duniya Suhaana, daga Najeriya gaba za mu kara zuwa nahiyar kasashen Turai”’.Da _ sauri Suhaana ta katse Mammanta, “Wadanda ba sa sallah?”
Mammah ta ce, “Ba duka ne ba sa sallah ba, kowacce kasar duniya akwai musulmi akwai wadanda ba musulmi ba”.
Suhaana ta share hawaye da tafukanta, haka suka yi ta bata baki da lallashi daidai lokacin da Daddy ya leko dakin zai ma Mammah magana, ya tsinkayi kadan daga zantuttukansu. Tsaki ya yi ya dubi Mammah da ta kwantar da kan Hafsat a cinyoyinta, ya soma sakin sababi irin wanda ya saba muddin zai ga Hafsat a wuri na babu gaira babu dalili.
“Yanzu wannan gansamemiyar yarinyar ki ke dorawa a kan cinya? Gata mugun abu, to kar ki je garin da ba’a sallar ki tafi inda ki ka fito mana? Mtsw! Ni ina ki ka ajiye min takardun da na ba ki dazu da safe? Shi ne abin da ya kawo ni”. Tuni Hafsat ta hau Www.bankinhausanovels.com.ng mayarkyata irin wanda ta ke yi in Daddy na mata sababinsa wanda ta fahimci ita kadai yake yi wa a cikin gidan nan, hatta Baba Azumi gaisuwar mutunci ke shiga tsakaninsa da ita.
Mammah ta bata rai sosai, ba ta ce masa ko kanzil ba, ta mike ta dauko takardun a (bedside drawer) dinta ta ba shi ya juya ya fita yana ci gaba da fadansa. Ba ya son sangartar da ake yi wa yarinyar nan a gidan nan, shi ya sa ta raina shi, ko gaishe shi ba ta yi in ta ganshi kamar ta ga mala’ikan daukar ranta. A karshe suna jin sa yana fadin. “Maryam kin kusa kawo ni bango. Ai gida
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG