AHUMAGGAH CHAPTER 3
Da safe na dade akan gado na kafin na sauko,wanka na shiga zuciya ta cike da mamakin abunda yayi jiya. Ina gama shiryawa na fito na wuce kitchen Na girka masa abinci,bai amsa gaisuwa ta ba bare yace min ya jiki,kuma tun Ina jera mashi abincin ya kore ni ko bari nayi serving dinshi ba baiyi. Haka rayuwata ta kasance like a living hell,ban isa bayi ignoring duties dina ba amma innaje inayi kuma baya kyalewa na karasa sai ya korani Duk sai naji nagaji da ibadan,haka Nayi ta sa kunne ko zanji ance zamu tafi gida amma shiru har muka cinye kwana takwas Kullum inna zauna sai na tuno kano I seriously missed ammuh adama ita kadai ce nake tunanin zata warware min duk wani matsala ta,. haka nayi ta zaman hakuri ban tashi jin meke faruwa ba kuwa sai da najiyo shi yana waya. Ashe cewa sukayi ya sake saka musu lokaci wanda hakan ne ya jawo delay din tafiyar mu. Aranar Cikin dare su kayi meeting dinsu,it was very successful komai ya tafi mashi dai dai. Da safiyar Allah kuwa ko wanke ido banyi ba yasa aka tarkato ni da kaya na na shiga mota akan zamu koma kano Tsaban iya shege shi sai yabi private jet dinsa nikuma yasa aka bi mota dani Kusan tafiyar kwana biyu ana jan mu,banda yawan bacci ba abunda nake yi a motar har muka iso kano Muna isowa naje na gaida jahan Aarah cikin sauki bata ce min komai ba har na fito. Wajen Ammu adama naje,muka gaisa tana kallo na tace baaahi?..Meye faru ne naga kamar kin fada… Nace banji dadi bane amma na warke. Taje ayyah,Allah ya baki lpya khaldun ya sanda haka kuwa? Ko da shike ma naga kamar tun shekaran jiya shi ya dawo me kuka tsaya yi to? Nan na shiga bata labarin abunda ya wakana ina maganan bansan ma hawaye na sauko min ba Kunya yasa Ban dai gaya mata abunda ya faru akan period ba Nace sabida ni yayi kusan buga kansa ko meeting din ma adalili na aka daga har muka ja lokaci.. Ammu Adama Ta ji tausayi na sosai ita da shike ta fahimce mmbi sosai ko fadan ma bata min ba Tace muje ki huta kici abinci,kafin anjima kije ki gyara mashi site dinsa kinga tunda baki gidan nan ba wanda yaje ta wajen Ban yo musu ba,hakan kuwa ya faru ammu ta gama petting dina nayi wanka na huta Chan anjima naf shirya naje site dinsa na shiga kimtsawa fiye smda kwana biyar bamu nan nayi aiki sosai sai dana gaji. A Kitchen dinsa na tsaya na jira domin na mashi abincin dare mai gaba daya,koda nagama nayi serving dinshi baiko kalle ni ba yace min get lost Dama nikam nagaji dan haka da murna na bashi waje,sai dai ko karasa isa site dina banyi ba ba sai ga aikan sa akan cewa naje na karbi kayan da aka shigo dashi yanzun na jera masa a closet kafin yayi bacci Haka na koma na karbe tarin kayan nasa,wasu irin super huge designer shopping bags ne mai dauke da designers shoes perfs,watches and other clothings. Zama nayi anitse ina jera su,ina kuma binsu da kallon sha’awa ,Allah kadai yasan yaushe za’a saka su dan anan dinma akwai kaya da uban yawa wanda ko taba shi baiyi ba. Bayan kwana biyu ranar na tashi da safe sai naga ko ina agidan ya cike da motoci anata sharing plesantries da formalites. I was surprised na fito inata raba idanu, koda naje dakin gogan nawa ma yau a kulle take kuma shima baya ciki. Ammu adama ce ke sanar da ni ashe yan uwan mahaifin khaldun ne suka iso tun daga kasar iran din bada sakon jajen su akan abunda ya same shi kuma tace zasuyi mana Kwana biyu So the house become 5 times busier than normal Da shike gangamin jinin sarauta ne sai suka taho da dokokin su masu tsauri da ban mamaki Wai tare za’a dinga cin abinci kuma duka masu girkin gidan zasu hada kai suyi girki dan haka aka hana abinci ako wani sashi akan bazamu koma normal duty ba har sai sun bar gidan. Tun daga ranar ayyuka suka ragu ma kowa cos komai a dunkule ake yinshi Kullum akan shirya food gathering a babban royal hall din gifan kamar wani feast kuma haka zasuyi ta hira da jahan ana shakatawa. Sai dai anata wannan shagali nr amma ban taba ganin gogan nawa ya fito ba . Iya kaci yazo ya gaishe su ba a sake ganin sa. Gashi jahan tace nabar aikin kar na dafa mashi komai ko dan yazo ya zauna acikin su Amma taurin kai yasa yaki ya kula su har yanzu. Daga haka Kusan kwana biyar ya dauka baya cin girkin gida,shiyasa ma kullum zaka ganshi a daki ranshi a bace On the 6th day daya gaji,sai ya fara aikawa ana kira na yana kuma tursasa ni ina dafa mashi kananan abinci kamar su couslow,noodles,salad da pancakes curstad etc Gaba daya abun nashi sai ya bi ya ishe shi,nikenan bazan dan huta ba duk dama kowa ya sami ragowar hutu? I was literaly upset with him inna ganshi ma haushi nake ji Wani bin sai yaga Anata abubuwa awaje masu sa nishadi zaisa a kirani na dafa masa abu,ko dan baya so kowa ya san yana sani aiki, kullum nakanyi kukuni sai yayi kamar baya jina3 Toh Yau Ina kallon fire works da yamma ne sai ga kiran sa daga site Ina tahowa naga kwanukan abincin jahan Aarah ta sa an kawo mashi dan dole wai yaci Tsawa ma yamin tsaban ranshi abace yace min” kwashe wayannan abun agabana.. Bance ufffan ba na kwashe zan tafi,yace get me some Noodles..kiyi min sauri. Da gafen idanuna na kalle shi,ina saita kaina zan dau hanya Bansan kukunin nawa ya fito sosai ba sai gashi na furta “Mutum Yana xaune waje daya kullum sai ciye ciye Yake kamar mace mai karamin ciki,Har da dan guntun tsaki na. Stop right there….Ji nayi yace me kika ce? Dan haka a firgice na juyo. Yadda ya zaro idanun shi ya kalle ni nagane komai.. The answer Was clear …ashe da karfi Na fadI Hakan kuma yaji ni Shikenan yau na na mutu na lalace.!!! One time jiki na ya fara rawa. Da wani irin muryan fusata ya dube ni again yace just turn around. Nayi saurin juyi baki n dakan sa yace babu ko..muryana na rawa Ko da ban dago ido na ba nasan kallon fushi yake bina dashi. Sai na fara bashi hakuri. He remain quiet for some moment fuskan sa a matukar daure kuma nasan ba zai maimaita tambayar daya min bane bayanin abunda na fadan kawai yake jira wanda ahalin yanzu bani da ita. A hankali na dago kaina na dube shi,ban bari mun hade ido ba nayi saurin sauke kaina,karkarwa jiki na yake kamar wacca aka soka ta a kankara. Nasake furta Im..m soryy,dan Allah kayi hakuri..ni bada kai nake yi ba. Wuf ya mike tsaye kamar wanda zai gwada min mari,a tsorace na matsa gefe tun Kafin na gyara tsayuwa na fashe da kuka sai naji yana cewa Kin sanni kuwa?. Hawaye ne na suka fara saukowa kafin na girgiza kai. A hatsale yace words!!! Yana mai dada firgita ni da sautin Buga table din dinning din da tafin hannunsa daya yi gashi tsaban karfin daya sa saida dishes duka suka canza Ma zauna. I mentally killed myself dan haka a firgice na amsa shi da ‘e”,kuka na farayi mai ban tausayi shikuma baice uffan ba ya matso ta gaba na yana bina da wasu mugayen kallo. Sai da yyi bitting lips dinsa kafin nan Yace na far wasa dake ko? yarinya baki sanni ba I bet inkin sanni bazaki yi wasa dani ba. Nama kasa amsa shi”..don a lokacin hawaye sun gama wanke min fuska Tsoron yanayin sa tuni yasa sai na zuba gwiwa ta a gabansa kamar zan lashe kafar sa. Im sorryyyy…bana karawa Ke wace ce da zanyi tambaya bazaki amsa ni ba? Who the hell did you think u are. Ya daka min wata shafaffiyar tsawa mai tafe da aji A sukurkuce nace Im no one sir ….wallhy ni ba kowa bace kayi hakuri dan Allah. Ban taba jin yayi tsaki ba sai yau Ya dan dago kai kansa kasa ya dube ni yace Banga alaman kinsa me kike yi nai ba inda kuwa kin sani bakin ki bazai barki ki furta min wayancan kalaman akan fuskata ba. Ni dai kuka kawai nakeyi sabida fushin nasa gaba daya ya rudamin ciki da tsoro. Yace ure very dumb and stupid as well,and for that zan iya korar ki agidan nan kuma babu wani mahalukin da zai sanda ke har abada. Cikin kukan na dago ma kalle shi eye to eye,i know i cant loose this job so i guickly manage to say kayi hakuri… “What did you say…?anan Na daga murya dan a karo na farko da naji ya maimaita min tambaya kenan…ki maimaita abun da kika fada min.. Sai naga ya jawo dining chair ya zauna yana facing dina da wata irin bakar fuskan bacin rai. Tuni na dada zubewa kan kafarsa nace dan Allah kayi hakuri…kar ka kore ni. Yace hakuri ko?.. Im giving you 2scndz say it or u will leave forever. Yadda naga ya sha kunu nasan komai ma zai iya faruwa,.. Chak wajen ya dauki shiru bakajin sautin komai sai na shessheka ta. Tunowa da yace 2seconds,sai na lumshe ido na…dai dai zai mike tsaye kenan nayi saurin furta kalaman cewa’ “Sai mutum yana zaune waje guda kullum sai ciye ciye kamar mata mai karamar ciki”1 Cikin matsanin cin kukan tsoro maganan ya fita abaki na,shikuwa baice ba ina ganin sa ya mike tsaye slightly yana duban agogon sa.. Tunanin abunda zai biyo baya ya hana zuciya ta sakat,i cursed the devil daya sa ni na furta wannan kalami… Toh yau inya koreni ina zanje? Gashi Na samu an dan rufa min asiri,ci sha sutura ga karatu.. sam bana son na rabu da wannan dama..kuka na cika gaba da mashi jikina duk ya yi sanyi ga tsananin tsoron daya mamaye ni. Its not over…ya furta yana kallo na.. Ki bace min naga waje…u disgust me. a birkice na mike da gudu na zanyi waje dai dai bakin enterance din shigowa sai charaf naji na ture mutum kamar zamu fadi amma sai naji an damke hannu na an dago ni….. Kuka mai dauke da firgita nakeyi amma still Wani Dammm kirji na ya buga tsaban tsorn dana ji. Daga ido nayi domin naga wanda ya rike ni,kwasam sai mukayi ido hudu da wata kyakywar mace fuskn ta8 dauke da alaman tambaya akan yanayin data ganni yanzu.1 “I cundt cry my voice out anymore jajayen idanu na na saka a nata muna kallon kallo don a Take zuciyata ta gano ta, ta kuma tuna min sunan nata wato SUBAYAH…!!kanwar khaldun saood1 Sosai take kama da jackquline fernandaz she is the Only sister dake bin khaldun sa’ood,daga gani babu tambaya kamanin jini da kuma dadin karawa da chan ma na ganta a hoto a ibadan sai yasa bani da wata shakku akan ta.. Magana tayi min amma banji da kyau ba. ‘Sabida Saukar muryan ta a kunne was mesmerising me sai naji gaba daya jiki na ya mutu daga bisani ji nayi tace”Why r crying?…sai Ta riko ni gently ta matso kusa dani cike da nuna damuwar ta akaina,nan na shiga sidda kaina kasa ina neman kufce hannu na daga nata ko dan na gaishe ta… Sai Ta sake maimaita tambayar ta tare da cewa meye sunan ki? A hankali Na dago,a dan tsorace da niyyar furta sunana “bahiyyah”sai dai ko motsa bakin nawa banyi ba..sai gashi na hango shi yana doso mu… I clearly remembr his furious voice asking me to go out,dan haka bana kaunar ya sake gani na bare na kara laifi ma kaina. “duk dama nasan kuskure na ne dana mance matsayi na har nake furta masa kalaman kininibi da rashin da’a…” Yana isowa daf da mu sai naji na kara firgita …Tsaban tsoron danaji sai nayi fizga daga hannun ta zan waske da sauri ta riko ni amma ganin ina kicin kicin zan kwace kaina ga sabbin hawaye sun fetso min a ido na yasa itama ta maida hankalin ta wajen da nake kallo.. “ohhhh ta furta as she looks more alluring ..Murmushi kawai tayi data ga shine Sai ta dube shi ta dube ni,ta Dada fadada murmushin,basai angaya mata ba yanzun ta fahimci damuwa ta. Bata sake min hannu ba har ya iso gare ta,..kaina na kasa don haka banga ya yanayin fuskan sa yake ba. “Nasan dai ya jawo ta jikin sa lightly ya kuma dora mata kiss a goshi banji me sukace ba sabida da harshen larabci sukayi zancen nasu Khaldun yana matikar kaunar subayah,you can tell daga yadda yake mata kallo cikin kulawa da kewa “After his mum zaka iya fahimtar subaya itace weakness dinsa a duniya. Inaji tace masa da mijin ta suka zo tuntuni suna shashen jahan kawai bazata iya jira bane tace zata zo ta dubashi Har kamar zaiyi dariya sai ya hango yadda ta rike hannu na cikin nata,a hakan ma wai baisan da ni awajen ba kenan din sosai nake faman boyewa abayan ta ina sunkuyar da kaina Nidai kwata kwata ba a sake nake ba. Ke!!!….ya dan daka min tsawa cikin kasaita. Dan saida naji tsikar jiki na ya tashi. “Whats she doing here…ya maida tanbayar kan subaya indirecly yana mata alaman ta sake min hannu na bar wajen. Subayah kowa murmushi tayi cikin sassanyar taushin murya tace c’mon Aaban(angel).. Sai ta dafa kadafar shi tace…my only khaldun in the world, kayi hakuri mana..! nasan laifin ta ne Domin dan uwana baya hukunci haka kawai… Ta juya ta kalle ni tace Hey girl comn say”asfii”..go on…rusuna ki fada mashi yayi hakuri…sai ta jawo ni dan dole ta aje ni tsakiya. Nikuma Nayi saurin rusinawa gaban sa da duka gwiwa na.. Tun kafin na furta komai tace repeat after me. “Ana assfi khaldun….” Cikin dauriya na maimaita “ana asfii khaldun” banjira komai ba Amma ko kallo na baiyi ba ma Ya dada hade rai ya kau da kansa gefe. “Dan dariya tayi ta lafe jikin sa Da Larabcin tayi masa magana cike da shagwaba shima ya mayar mata in few words fuskan sa a dakile. zai bar mu a wajen sai yy mata alaman kar ta dame sa da magana na ya dan tura ta gefe ya wuce. I dont knw how she did it,batare da tayi magana ko nayi ba ta min alamar abunda zanyi,sai na tsinci kaina kuwa da biye mata… Ana assfi!!! ….khal..dun please Please im sorryy..!..sai murya na yayi dadi gashi yana dan rawa ayayin da na sake Ina bin bakin subayah hannu na duka biyu a rike da kunnuwa ta kamar yadda tayi itama. Dan Shiru ne ya ratsa wajen sabida dana yi hakan har ya dan dakatar da tafiyan sa sai dai bai juyo ya kalle mu ba. Ta kifta min ido akan na sake maimaitawa ,tun kafin na sake maimaitawar kuwa ya dago ya kalle ni a takaice …amma duk hankalin sa yana dai kan sister sa data maraice fuska on my behalf. Finally…ya furta its ok. Subaya ce ta fara ce masa thank you kafin na furta nima..’ Dukan mu bamu damu da yanayin yadda ya fitar da maganan ba muka hau lissafin Godiya Already wanda kallon mu ba bai ishe shi ba. Bayan tafiyar sa. Murmushi tayi ni kuma na sauke wani shegen ajiyan zuciya ina godiya ma Allah Da ya turo wannan kyakwar mata. Kokarin goge sauran hawaye na nakeyi zan tashi nagode mata naga ta juya abunta zata tafi. da sauri nace Ant..ant..Anty…. ma..aaam.. muryana har na rawa na biyo ta. Cikin nitsuwa ta juyo tana kallo na har na iso gaban ta… I wanted to bow down kadan dan nace mata nagode ina kokarin rusunawa naji ta dafa kafadu na tana mai tallafo ni tsaye With more serious tune tace.”rusunawar me zakiyi min? Kefa mace ce kamar nim… yar adam mai daraja. Are you sick!Ko ba Yanzu kika gama ce min anty ba? Mamakin saukin kanta yasa na dada kallon ta cikin ido. ‘Sai ta tabe baki kawai iirin ‘mmmh. .comon Its enough,ni bana bukatar too much respect ok,i see Ure a very cool girl menene sunanki ma? Cikin sanyin jiki Nace sunana bahiyyah Bayabo a fallasa tace Nice one!!ni sunana subayah hamood.. Nice golden sister yaya sa’ood. “…ni dai Shawarar da zan baki shine kar ki na bata ma yaya na rai kinji?inkika yi hakan bazamu shirya ba. Na gyada kaina Da sauri Nace nagode maaam… Tayi murmushi tace u can called me subayah ban damu ba… na girgiza kaina alaman ah’a bazan fa iya ba. Hannu na ta rike Dan dole Muka fara tafiya a tare cikin hira Tana min tambayoyi anan tasan aiki na da matsayi na agidan.. Because she was so nice har bansan sanda na gaya mata exact abunda ya faru ba ayanzun. Dariya tayi sosai domin kuwa na lura muna maganan ne tana dada jin kauna ta aranta. But how?har ace ganin farko mutun yaji ka burge sa?…. “..naki binta site din jahan..! Duk dama taso mu shiga tare amma naki sam.. Gani nayi ga bakin masarautar persia ga kuma shikan shi ogah na khaldun a zaune,aradun Allah nasan i cant just manage to stay busy acikin su. Rabuwar mu da subaya nayi daki na,itama tana shiga site din jahan taci karo da mijin ta watoh barister SADAAT adeel.2 Shi din Kyakywar namiji ne in his late 20s jamar khaldun,barister sadat ya gaji ilimin lawyanci da iya bida cases na sharia both mentally and tactfuly.. Tsananin kwarewa yasa Sadat ya zama wani abun tsoro wajen iya munafurci da juya yanayin zance4 …wanda ya kasance dan riko ne wajen wani balarabe a kasar saudi arabiya inda suka tare da subaya. A chan kasar rajiskhan suka hadu da subaya a lokacin taje yawon bude ido da step bro dinsu wato naval captain KAAMIL HAMOOD dake iran a dawlat khatoon a nan subaya da sadat suka kulla soyayya Yau auren su shekara biyu amma Bai taba barin ta ta haihu ba…3 Subaya is a chronic hypetensive patient shiyasa koda wasa bata son ta bata ranta akan komi sannan bata daukan duniyan da zafi kowa takan bi dashi cikin respect bata tsawwala wa.1 Don Abu kadan na daga mata hankali sai ciwon hawan jinin ta sai ya kwantar da ita har kamar zata mutu Yau da gobe sai Allah,Mutum daka ganshi ba mai iya masa sai ubangijin sa Sau dayawa hausawa su kance sanin halin mutum sai Allah kana tare da mutum ne amma ba kasan dawani irin zuciya yake tare da kai ba Naga hakan a duniya sau abu adadi amma sai yau naga ga subaya mace mai hankali mai daraja mijin ta tana matukar kaunar sa,. sai dai shikan sa saadat din Dalili ne na son zuciya ya kawo sa rayuwar ta.3 sadaat yazo ne ya yaudare subaya inta mutu yaci arzikin ta amma har yau bata gane hakan ba… 16 A yanzu ana neman karfe 10 na dare hira ake yi tsakanin yan uwa da iyaye, kowa yana zaune anayi da shi amma banda khaldun sa’ood dan daya zo din ma ko minti 10 baiyi ba ya koma site dinsa. Yau dai su subaya da sadat ne bakin marmari agidan jahan aarah sai tarairayar su takeyi Zaman su duka a babban farfajiyan falon gidan tare da jahan Aarah da sauran yan uwan su da suka zo jaje daga persia, ya isa ya sanar maka da yanayin zamantakewar su tsaf. Dan Daga an kawo korafi akan sadaat zai bada uzurin sa. Subayah kuwa Tuntuni kare shi take musamman da Jahan aarah tayi musu talala akan rashin zuwan su nigeria na tsawon lokaci. Duk da haka ana kewar juna sosai dan anan site din jahan subayah tayi baccin ta ayau.., Washe gari da safe gidan ya tashi a daqule domin yau bakin persia zasu koma Chan masauratar su na badiatl jamal a iran. Ko ina ya cirke da shirye shirye like a big Happy family once again aka hada bababan family feast na breakfast kafin kowa ya watse. Toh Khaldun sa’ood baiya cin abincin taro. hasali abinci inba shi daya bane zaici to shida mahaifiyar sa kadai akan teburin Dan haka sai da na hada mashi komai yadda na saba yi mashi yaci abunci yayi wanka ya kimtsa tsaf kafin ya fita da niyyar zuwa ya iske su awajen da suke cin nasu abincin Yau kam Ban ko damu ba sabida ko kallon arxiki nasan bazan samu wajen sa ba beside ni kaina nasan darajar subaya naci badin ita ba ba hala tsakani na dashi da ba haka ba. Yana isa inda suke ya rusuna like a true gentleman yayi gaisuwa Kowa yasan halin sa na man of attitude and few Words,don haka ba wana ma ya daga hankalin sa. Don Anan ba wanda su kejin dadin sa face jahan Aarah da subaya dayake lailawa.. Tsakanin sa da saadat is a direct enmity. .. kwata kwata jinin su bai hadu ba dan ko gaisawar fatar baki basuyi ba sai cake cake magana da suke yi ma juna cikin zamba da aminci.2 Abun bai yi tsamari ba ma sai da alhj hamood mahaifin su ya kira video call akan zaiyi magana dasu baki daya Khaldun yaso ace sadaat ya fita daga cikin su amma haka subaya taki fir har da dan bata rai,sai da jahan ta sa baki aka barshi.. Bayan gaisuwa da godiya,alhj ya fara da bada hakuri ma yayan shi na cewa ya boye musu abunda ya faru dashi acikin kwanakin baya har zuwa inda ya hadu da bahiyyah. Abun ya girgiza su sosai Musamman ma khaldun sa’ood da yake jin kansa babban jami’in soja kuma jajirtacce. Toh Ashe fitar sa agidan ranar us aka kaishi ana cigaba da binciken wanda sukayi attcking dinsa ana kuma jinyar sa,shine sai ya turo bahiyya da begham yar uwansa ta gefen mahaifiyar sa . Da shike gen hamood garau yake maganan so thy have no worries akan wani tashin hankali daga wajen Subaya.. Yan uwansa dake wajen km duk suna sane da komai,Alhj Yayi musu nasiha Yayi godiya kafin ya katse kirar. Shikam Khaldun bai wani ji dadi aransa ba wai har ace mahafin sa ya shiga irin wannan yanayi ana kuma boye masa.. Take ranshi ya fara baci dadin karawa da Sadaat ya dage ya zakee yana cewa shi ma zaiyi wani abu akai Har da cewa ai Yasan aikin makiyan su ne kuma a duk randa aka kama su shi zai dauki ragamar case din da hannun sa. Kowa dai na fadar albarkacin bakin sa jahan tana dada fayyace musu kan labarin da ya afko da basu sani ba. So Bayan tafiyar bakin persia. Zaune agefen mahaifiyar sa a chan cikin wata katafaren sleek style luxurious bed room din wanda aka tsime sa da royal purple canopy queen size bed ya zauna ko inan dakin dark wall ne mai dauke da white edges sai wasu shegun gold lanterns masu sheki da haske Jahan tana ta magana amma Khaldun Shiru yayi dan sosai yake fushi da kowa ma . Su biyu ne a dakin subaya tayi rakiyar sadaat zaiyi tafiya wani wajen. Dawowar ta kenan jahan ta sauko suka fara maganan cikin fahimtar juna. Inda khaldun ya nuna tsananin rashin jin dadin sa akan lamarin Tace Allah ya huci zuciyar ka,angel yaushe ka dawo daga naka hidiman da za’a dame ka da irin wayannan case din..besides its all matter of security reason. Yace what nonsense security reason ne zaisa Dad ya zauna tsawon sati biyu yana boye a wani wajen ni ban sani ba? And who are the incompetents gurds dake tare da shi ina suke lokacin da akayi attacking dinsa? I will deal with them kar suyi tunanin zan kyale su. Sa’ood calm down pls..Cikin damuwa subaya tafada tana dafa shi ya ture hannun ta a masife Dont tell me to calm down,U mean my dad have to sustain bullet?what if that girl was not there Wato sai ya mutu kenan ko? Jahan shiru tayi tana jin sa tasan in ranshi ya baci is not soo easy a shawo kansa …subayan ce dai take famar susuce masa fuska tana lalllaba shi har sai da ya masife su tass kafin yayi shiru. Cikin lallami da taushin murya jahan tace “kayi hakuri its ok komai ya riga ya wuce! Daga nan sai bai kuma sake magana ba. Nan magana ya ta da magana inda subaya ta nace sai dai a abada bahiyya matsayin ta da suka yi niyya tun farko.. Jahan dama bata da matsala da hakan dama kawai neman izinin su da kuma karin yarda tsakanin ta da bahiyyah ya rage mata yanzu dan iya zaman bahiyya a gidan bataji ankawo karar ta cewa tayi mummunan abu ba. And tunda taga khaldun bai kore ta ba to lallai yarinyar akwai hakuri Subaya kam is super excited already she cant even wait to call bahiyyah her sister. Bangaren Khaldun kuwa ko sake kallon su ba bare yayi responding haka Kuma ya tashi ya bar su a dakin suna ta fayyace fayyace. By noon suka tattauna su uku da jahan da subaya da Alhj gen hamood ta video call Inda ya basu goyon baya dari bisa dari akan tunda sun gamsu da halayen ta kawai suyi adopting din bahiyyar ta dawo one of the hamoods. Murna wajen subaya kamar zatayi tsalle,dan sosai take jin bahiyya aranta duk dama bata zauna da ita ba. Washe gari koda suka sanar ma khaldun cewa za’ayi adopting bahiyya shiru yayi daga bisani yace shi babu ruwansa da wata bahiyyah… He object the fact that yarinyar dake masa dafe dafe ce za’a laka masa dawowa yayan ta. Yama ki shiga zancen Kuma Dan dolen su suka kyale shi. ***** Nikuwa Ummah adama ita ta dinga bani shawarwari tun kafin su jahan Aarah du tumtube ni akan maganan. Tace min Allah ne ya kashe ya baki bahi…dan haka idan suka kawo miki maganan adoption maza ki amince Anan har tarihin kywawan halayen su sai da ummah adama ta bani. Kamar wasa aka kira ni a sashen jahan su biyun suka tambaye ni ko zan amince da qudirin su! Babu abunda ya bani sha’awa kamar yadda Jahan ta bani tabbacin cewa kar na amsa su dan na faranta musu ko dan tsoro domin kuwa maida ni cikin jinin su ya wuce yanke hukuncin cikin wasa. Sai kawai na amince nayi godiya sosai harda kuka mai ban tausayi Nan suka jawo ni for the first time duwawu na ya zauna kan lallausan chairs dinsu.. Da yamma aka kira ni again babban lawyen alhaji gen hammod ne ya ziyarce gidan Domin aiwatar da proper official adoption procedures Anan aka maida suna na asali wato bahiyyah Ahmad alba kafin aka sa HAmood a karshe. My file name was reading bahiyyah A. hamood Sai Aka bani official papers din adoption nayi signing Haka ma na family property and rights da suka bani kyauta duk na sa hannu. Wallhy ji nake kamar mafarki nakeyi dan ko murmushi bana iyayi sai yake. “TAbbas Tsarki ya tabbata ga ubangijin mai yin yadda ya so, shikenan fa rana daya na dawo cikakkiyar doughter of gen hamood and jahan Aarah, Sister to a brigadier genaral khaldun sa’ood and his sister subayah. A take rayuwa ta sauya min,ranar kwana nayi ina godiya ina salloli Na tuno ammu abbu da junnut sosai har na rasa wani kalman zan faranta ma ubangiji na rai da shi. Kawai sai na daura niyyar yin azumi guda daya batare da na fada ma kowa ba. Haka ammuh adama ta sake maida ni wani site daban wanda yake asalin cikin sashen da jahann Aarah da su subaya ke zama. Nima yanzu inada whole flat site mai dauke da wata kafurar neutral background. Ko ina An tsime shi da monochromic additives,dark beige drapery curtains,a tsakiyar space din dakin akwai stylish ottoman bench mai square pattern Tv sets da katoton silk bedding with plenty maching cushions da cubic headboad agefe. Wayyyo duniya sabuwa.. Closet dina kawai wani dakin ne mai zaman kansa… Duk da yadda abubuwa sukayin kyakwan juyin masa,sai dai Ban taba komai ba tukun don jikina ko kadan bai sake ba. Umma adama ce ma tasa ni dan dole na dauki daya daga cikin doguwar rigunan abaya dake closet din na saka sabida nasan na shiga wani matsayi arayuwa, da shike da azumi abaki na sai ban fito ba nayi kwanciya ta. Ina farkawa As expected subaya ce na gani,cike da fara’a ta rungume ni tana cewa happy sisters day” Sai da na tsinci kaina da mayar mata da dariya Ta riko hannu na tace min,ki sake jikin ki kinji ,mum is already calling Zakuyi magana da dad Wani dam naji kirji na ya buga,sai nayi yake kawai nace toh muje.. Tana gaba nabiyo bayan ta,na samu khaldun na zaune awajen alaman magana sukeyi har zan zauna kasa jahan tayo saurin riko ni tace kar na rusuna .. Nikuwa Duk hankali na nakan sa shi ko kallo na baiyi ba Har ya gama amsa wayar sa ya tashi ya fice abunsa I was lost in tot of him,gani nake dan banje aiki site dinsa ba nakeji wani iri ko yaya yau ya yi?waye ya dafa masa abinci oho? Come here BAhiyyah Jahan ce ta tsare min tunani da mika min waya Anan Dukan su suna ji Mukayi magana mai cike da girmamawa da Alhj hamood Shima karfin gwiwa ya dada min harda tuno min cewa na taba kiran sa mahaifi na a da chan dana taimake shi dan haka shima yanzu na dawo yarsa na har abada. Hawaye na su suke dada nuna musu sincerytin godiya ta. Dan dole na na sake da su, yanzu na fara ce ma Subaya big sis.. Jahan Aarah kuma ta sakamin suna mai dadi wato BAHIYYATUL NOOR. Sai aka dawo cemin baahi, ko ace min Noor bahiyyahn ma ba kasafai suke kira na da shi ba1 Duk wannan hidiman mu ukun mu muke yinshi sai idan alhj hamood ya kira gashi sadaat mijin subaya baya nan Yayi tafiya. Tun ranar ba wanda ya sake cemin nayi wani aiki agidan amma zuciyata cike take da damuwa da yadda khaldun saood ke yi anashi shashin He dindt say a word about me Ni dai nasan bai amince da ni a matsayin yar uwansan bane. Gashi haka kawai nake jin i really missed him,i wanna be with him ko da kallon sa nayi3 Bayan kwana biyu Jahan ta kira mu da rana da shike khaldun da ita yake yin lunch kowa ni lokacim Wani daure fuskn sa yayi da yagan mu akan dinning table da alaman fada jaahan tayi masa akan kin accepting dina dayayi.. Nikuwa ko iya hada ido dashi banyi ba Amma sosai naji dadi dana gansa ko na komai naji sauki Gashi dan kwana biyun kacal danayi cikin gata har kalar fatar jiki na ya fara amsa sabon ya nayin daula da ake zuba mashi. Bayan mun zauna Anan Har jahan ta kare Maganan ta ba wanda ya amsa fiye da subaya. Last last cewa tayi zata yi tafiya akan zata je kasar turkey.. Wayar sa nayin kara ya mike tsaye “Ya dora mata kiss a goshi yace safe jouney mother”.ya hade rai bai jira amsa ba ma ya tafi abunsa. Bayan sun bishi da ido sai duka suka dawo suka kalle ni,kaina akasa yake dan nasan muddin ina waje nasan he will remain pissed off. Fuskata ya nuna damuwar hakan Amma bansani ba nadaiyi shiru na sunkuyar da kaina kasa.! Har Subaya zatayi magana Jaahan tace wait sai ta kira sunana cikin lallami tace Baahi? sai Na dago a sanyaye Nace yes ma.. Tace kar ki daga hankalin ki,zai saba da ke amma ba yanzu ba ko!.. Sai Nayi murmushi nace bakomai na fahimta. . Sai dai alfarma daya nake nema Tace mebene? Jahan pls ki bari na cigaba da yi masa aiki kamar yadda na saba masa da chan. With full objection jahan tace a’ah ban amince ba Bazaki yi wani aiki agidan nan ba Ban taba sanin inada liver ba sai yau Tsintar kaina nayi ina ce mata,zanyi hakuri da khaldun ni dai Tayi hakuri ta barni nayi masa aiki dan nafijin dadin kula dashi fiye da dawowa equal dinsa Besides am his sister now duk abunda zanyi mashi is out of family bonding so no quest. Da wannan kalmomin nawa sai na burge su matukar burgewa Duk dama da kyar jahan ta amince subaya har da cemin zata rinka ta yani wasu Abubuwan domin mu jawo shi har ya aminta dani. “Cike da raha da fahimtar juna muka watse kan tebur Karfe 2 Jahan Aarah ta bar kasar nigeria zuwa turkey. So washe gari da safe khaldun saood ya sha mamaki ganin nayi resuming duty sai dai ko kallon arziki ban samu ba bare cikan ki! Daga yadda naga yaci abincin sosai I can tell that he misses me too.1 Naji dadin hakan araina,dana gama mashi komai sai na je dakin big sis subayah,she was all excited murna take sosai kawai dan mijin ta sadaat zai dawo. Anan nayi wanka har ta koya min salon hade haden bathing gels ta inda zai goge min fata na nayi kyau nayi tass Anan na fahinci Wanka ma iyawa ne fa,dan akallah abubuwan tttala jiki dake bathrum din mu yaci ya dauke ka awa biyu yana wanka bai gama ba Haka ma ta cancada min kwalliya ta koya min yadda zan nayi,gashi nayi dan karan kyau Da shike ina kama da Ariana grande sai kawai take bin salon parking gashin ta kamar yadda takeyi alwys on pony tail Idan ta tattala min shi sai ta sake sauran jelar cukun ya zube abaya na Yau ma Doguwar abaya bakake muka sa iri daya sannan mu kaje shoping mall. We had fun,har sai da naji ina kaunar big sis subaya sosai Dan kuwa tsakanin ta da Allah ta bude min zuciyar ta tana jan ajikin ta Munyi shoping kamar wanda zasu bar duniya. Ina da komai agida amma Komai ta sake siya min,shoes bags,make up lingeriea da jewries gani take kamar zabi na zaifi min1 Haka ma iphone11pro din kamar bai ishe ni ba ta kara min da samsung galazy x10. Cikin wata kafurar jeep kirar jaguar ake tuka mu4 Dan dole na na koyi surutu dan kuwa subaya is quiet intresting and jovial… Tun da muka dawo Gidan shiru,tana dakin ta tana shirye shiryen tarban mijin ta nima ina daki na ina damar tausasa kaina domin har yanzu zuciyata tana dauke da fargaban abubuwan dake faruwa dani wani bin sai naga kamarr duk karya ne But I have no choice than to accept my new life this way. Wanka nayi irin yadda big sis ta koya min My choice of body wash was makari,honey,goat milk set nivea,da wasu set of papaya scrub banda ma hand wash feet wash knuckle da under arm and pits Wasu abun ma bansan su ba. And My hair was going milk and egg sets both shampoos and conditioners ,wani handle din zakaga an shake su da zallan ogarnics wasu kuma irin su himalaya sets ne And little of revlon da oriflame. Kirji na daure da baby pink towel na fito na yi yan shafe shafe na Ban fara lura da jyaun na ba sabida tunanin khaldun sa’ood ya cike min kirji na. Simple mermaid Gown nasa sabo daga shoping stuff din da mukayi dazu2 Kalar ja da baki ne dan haka dana tufke pony tail dina sai na lullube shi da bakin turban cap At Around 5.45 pm na fito zan nufi site din khaldun Taku nake dayan biyu ina jin dadin jiki na kwasam sai nayi tuntube kamar zan fada naci da baki naji an riko ni a hanzarce Wani lumshe ido nayi Kirji na saida ya buga dana dago thinking and wishing ina bude ido zanga khaldun amma sai naga wani halittar daban Da uban sauri na kwace hannu na Shikuwa mutumin ya sakankance ya zuba min hadadden idanun shi akan surar jiki na baya ko kiftawa 3 A kadaddafe na bude baki Nace sorrry, na juya zan haura bansake kallon sa ba… Da alaman ya sume dan kuwa sautin takalmi na ne ya fargan da shi Da Har zai yi magana sai Charaf big sis subaya ta shigo ta iske shi. Da saurin ta cikin fara’a ta rungume shi tana cewa baby is back,sai na juya kadan ,naga dai yana wani jajjan aji Suna gaisawa,basai an fada min ba na gane mijin ta ne Inaji yana ce mata who is this? Yana nuna ni. Subaya batayi kasa a gwiwa ba ta Kwalla min kira Dan dole na sake dawowa gaban su Wani shu’umin kallon kurel da gayen kemin yasa kaina ya daure Bai daga idanun sa ba har sanda subaya ta riko hannuna na zuwa gaban sa da kyau3 Tace this is bahiyyatul noor.. My new sister ka tuna?wanda na gaya maka a phone Uhhhhhh…yess yace adan dakile daga ji kasan bai ma saurare ta da kyau lokacin datake gaya masan bane Ita kuwa sai da ta sake ware masa bayanai akaina har sanda ya gamsu2 Sai yamin murmushi Yace ure welcome to the family..nace thanks ..ya fada min sunanan sa barister sadaat adeel Ba yabo ba fallasa nayi murmushi. I was not comfotable dai na yi excusing dinsu na nufi part din khaldun Dinner na shiga hada mashi,still thinking of yadda mijin big sis yayi ta kallo na dazu Toh shikuma haka yake!l? Kaina na bi da kallo “Ko dai laifi nane dana sa shaped gown, kowa dai yasan mermaid gown na nuna shape din mace sosai So I started regreting Da nasan dressing din baiyi dace da na wanda za’ayi ma kallon mutunci ba da bazan sa ba. A wanni fannin kuma i was kind of happy hala tunda yau nasa kayan da wannan kyakwar mijin big sis din ya rude maybe i will get to catch khaldun’s attention7 Bansan meyasa ba har cikin raina nake jin tsananin bukatar sanin matsayi na a zuciyar khaldun sa’ood. Ni kadai a kitchen din inata sake sake don tunanin khaldun na cigaba dayi har na kammala hade haden abinci na. Da shike dinner ne ban dafa abubuwa masu nauyi ba,i left the kitchen unkept sai naje site dina,ina shiga daki ban wani bata lokaci ba bayi na shiga na dauro alwala nayi sallahn magrib da isha kafin na nazo na gyara ma simple make up dina zaman sa. Misalin karfe 7.55pm na sauko da serving trays na aje kan dinning dinsa ko gama jerawa banyi ba na tsinkayo sallamar sa da tamkar ma kanshi yakeyi. Na gaishe shi kasan wuyar sa ya amsa with his face bayabo ba fallasa Direct ya taho zai zauna kan dining chair kamar yadda ya saba,so i quicky compose my self na tara dan karfin hali na ja masa seat kamar sarki ya zauna gently still bai kalle ni ba..! Plates na shiga jerawa gaban sa na bude wata mayyar girki mai dadin qamshi, rich spaghetti shingella jolloff mai dauke da fresh brown meat meals.. I notice how he look at the food da gefen idon sa sai nayi boyayyen murmushi Spagehtin na zuba dan dai dai sai na zuba meat balls guda hudu manya aciki. Redberries na zuba a wine glass,nasan yana matukar kaunar fresh mango juice shima na aje masa shi agefe. Daga nan tsayuwa nayi a gefe yana ci,sai dai yau din na lura kamar he is not comportable da hakan daddaya ma yake ci kamar wanda abincin bai masa dadi ba. Qamshin jiki na ne ya ruda shi,nikuwa Ko kadan ban kawo araina cewa na birkita ogan da qamshin turare na ba,nasan zai iya yiyuwa yana son qamshhin lavender sabida jahan Aarah shi take yawan amfani da shi. Bandai kawo tunanin komai araina ba,don nasan turarrukan sa aduka arabian designers ne daga qatar, saudi arabia, dubai ko kuwait, Idan bai saka su ba toh clive christain ne ajikin shi hardly yake shafa made in srilanka duk dama yana dasu kuma sun hadu. Kusan rabin awa yau nayi agaban sa ababu ababu sai da yayi rabin cinye duka abincin dake warmer ahaka ma Baima sha beries din ba naga da kanshi yau ya mika hannu ya zuba mango juice ya sha,da cup din ya nufi dakin shi bai sake duban inda nake ba. Nikuwa a Kullum burge zuciya na yake i so much love his hard nature.. khaldun Namiji ne mai ji da control, karyan ka kagano abunda ke sa shi farinciki cikin sauki bare kuma weak point dinsa.5 He is one of a kind,bazan boye muku ba har mafarkin fuskan sa nakeyi most times ko da ba a bacci ba.8 Haka kawai Kwana biyu Sai na lura da na dage da aiki na na kula dashi,toh da shike ma yasan yanzu nima yar gida ce kona yi mistake baya ce min komai. Sai ya dawo tsakani na dashi We are back in the era of few words and blatard queitness. Yau Kwana biyar kenan ina zuwa site dinsa amma baifi sau daya yayi mun magana sentence daya ba. Ko ajiki na musamman da na tursasa zuciya ta tunanin sa a kullum Gashi inata shirin rubuta waec next month,tunanin khaldun sa’ood gaba daya ya hana ni lura da duk wani abun dake gaba na. Har da Sadaat mijin anty subayah da kullum sai naga ya zuba min shanyayyun idanun sa yana bina da kallo. I begin toh dislike him,ban cika ganin yana tarairayar big sis ba amma sai naga sis subaya kamar wacce bata da aikin yi sai nashi . He is a demigod to her,as she practically worship him. tsaban so da nuna biyayyar ta a gareshi har bacci abinci bata iyawa sawa abaki inbata gansa ba. Shikuma babu ruwan sa,in gaka yana wasa da dariya mai tsayi da da ita to yace taje ta kira ni ne kuma nazo din.. Na lura da shi Yana so muyi ta hira anma nikam jinina bai hadu da shi ba sam Akwai indian serie da nake yawan kallo na mance sunan sa but akwai khushi da arnav toh babu maraban wannan sadaat din da mijin anjali wato shyam.1 I just dislike his looking attitudes Shiyasa idan big sis subaya bata kusa nakan yi sauri naje daki na na rufe kaina na ina karatun dole,bana sake saukowa sai ta dawo Haka ma da safe ko da daddare a site din khaldun zan bata lokaci na. Nidai Sam naki na sake fuska ta wa mijin big sis,har ya kaiga ya fara sata tana biyo ni kitchen din khaldun tana ganin mena keyi I love her soo much yawanci sai naja ta muyi ta hira har tana tayani girki,ita kuma burin ta bai wuce inna gama muje tare wajen mijin ta muyi hiran ba. Hakan da sukeyi na takurani amma sabida saukin hali irin nata sai na kanje haka zaiyi ta kawo min hirarra ki shidai yana so yaji labarin yadda nake so na gina rayuwata nan gaba Like makarantar da nake so nayi,my future career and stuff. Subaya is the lit ana hirar ma sai kaga tana ta dariya abun ta,kullum zuciyar ta daya ne,sam bata lura da cewa mijin ta ya kamu da yaudarraren so na bane a zuciyar sa Nikuwa ayadda nakejin bana son halayen sa,ko a kafata aka daura min shi yarwa zanyi,badon bai cika namiji ba,sadaat ma mugun kyakkwar namiji ne ajin farko kawai halin sa ne sam baimun ba. Cikin wannan zaman namu Kwasam sai ga Convoys na motoci suna shigowa . Dama mun fito mu biyu da big sis raka sadaat din ne wai zaije aiki Riga da skirt na saka na trim orange satin shirt na yafa karamin mayafi da flair royal blue daga sama na har kasa D&G ne. I look queit and spoilt,kyau na ya saje da matsayi na. Muna tsaye daga farfajiyan gidan Agaban mu Aka jera convoys din motoci A jerin farko Motocin jeep kirar ford ne dukan su hudu da sojoji Na biyar din Aka bude kofar Jahan Aarah ce ta fito Duka murmushi mukayi muna karasowa big sis Subaya ta riko hannu na muka rungume ta tare muka mata welcome Jahan AarahTaji dadi sosai Like she was longing to hear my voice cike da wani irin sanyin murya irin na manya kuma kasaitatum mata ta dan dago haba na. tana murmushi tace bahiyatul Noor,i hope you miss me? naji dadin ganin ki haka..may ur happiness sway on the wings of eternity2 Murmushi na sosai ya fafadada na amsa ta da ameen ina mata godiya, Tanbayar ta nayi yaya hanya? ,..wani murmushin tayi ta dan shafa cheek dina kafin ta amsa ni da kar na damu. Wani lokaci sai nayi ta kallon ta haka kawai…this woman is killing me,gaba daya sanyin dake tafe da Ajin ta na burge ni.2 She talks like a real queen yo ko Alhj hamood daya kasance jinin sarauta bazai gwada mata kasaita ba. The second version of the convoy was motoci masu kofa biyu kirar cadillac xi farare Kar su uku. Wani saurayi aka bude ma kofa ya fito,baima jira an gama rufewa ba ya taho gaban jahan da murna sa ya rusuna ya fara zuba mata kirari da girmamawa itama cike da jin dadi take yabon sa tana tambayr sa lpyar iyayen sa. But Who is he? Na kare masa kallo daga sama har kasa ina tambayar kaina Naga big sis subaya ma murmushi take Har gayen suka gama gaisawa da jahan ya juyo gare mu. Wani jahilin murmushi suka exchngin shida big sis He hugged her lightly,tace welcome Huh?Ashe a duniya zan sake ganinka…? Sai yayi dariya yace of course bagani ba. Dogo ne fari kar kamar bature but he is very handsome yana da pink lips blond hair da manyan idanu.1 “agarin gulma na unknowlgly His eye caught mine ban kuwa dauke ba ina kallon shi sama da kasa har sanda ya dage min gira,sai yace ma subaya wace ce wannan? Ya juyo again”Heloo pretty bird..ya mika min hannun shi kamar yaga babyn rubber nikuwa naki mayar masa sai nayi durus da fuska ina kallon shi Kamar naga tababben zombie. Wani unxpected hadiyan tawu yayi ya maida knsa yana sosa keya Ko jahan saida tayi dariyar mu subaya ta dafa kafadu na tana murmushi tace masa hey shahrul easy.. She is my sister fa.. Jahan tace yeah…enough now. Ya kamata mu shigo ciki ko m,duka muka ansa da yes Gaba jahan din tayi sai nabi bayan ta da sauri Na bar big sis subaya da mutumin yana tambayar ta irin taya akayi na dawo sister su shi bai sani ba Inaji take wasa da hankalin sa suna dariya bata gaya masa komai ba dai tace ai dan ya dade baizo bane shiyasa baisanni ba. Nikam Asalin Site din jaahan naje nayi zamana dan ko kadan bana son hayaniyar kowa. Sunan mutumin shahrul,he is a medical doctor dan gidan uwar gidan shugaban kasar Oman Best and childhood friend din khaldun sa’ood Tsaban amintakar su ne yasa shahrul yake yawan yin hutun sa a wajen Khaldun a camp har ya iya hausa sosai. Amma tunda aiki da career ya raba su sai kowa yayi wuyan gani. As usaul Site din khaldun din subaya tayi da shi. Khaldun was happy to see him amma bazaka gane hakan ba sabida yanayin sa. Hira kawai sukeyi tsakanin su ayi larabci ayi turanci ayi hausa Big sis dataga abun nasu nayi ne,kawai sai ta fita ta barsu ta dawo muka cigaba da hidimar mu wajen jahan. Jahan is atill worried da maganan girkin da aikin da nake yi ma khaldun,nikuma naki ji sam Sai da big sis subaya ta bata labarin cewa khaldun yafi cin abinci na fiye da yadda taga yake ci a ko ina kafin ta saduda Chan bayan isha’i sadaat ya dawo suna tare da big sis yau ma shi ya bata min raina I was not happy da big sis take cewa ai daya dawo gidan ni ya fara tambaya. Yanzu haka nasan anata tunanin tana murnan cewa mijin ta sadaat yana haka ne sabida ya gwada ya na son duk abun da take so. Wai shin wani irin zuciya take da shi ne da bata ganin wannan tsarin nasa matsayin cin fuska? A gaskiya bazan ji dadi ace miji na baida wani aikin yi sai maganan wata ba ko da kuwa sister nane.. Atleast there is limit,..not always…na sadaat yayi yawa har abun haushi. Da wannan tunanin nake girki my face isnt looking so cool Duk dama yau shigar hausawa nayi so na fito daban,atampa koriya shar riga da skirt tamin kyau sosai. Godiyan Allah ma yau abinci dayawa zan dafa ma khaldun tunda bashi kadai bane Sai nasa araina yau kam bazan biye ma big sis ba bare ma na bada sadaat daman kallon fuska. So i quickly made dinner,offal pper soup,crispy jollof rice na hada da soyayyen kaza sai na shirya simple brown yamballs mai shake da flake fish. Kunun gyada mai madara da mango juice as usual. Toh nakai abincin dinning amma banga ya fito ba Sai da big sis ta zo dubawa ko nagama sai take cemin a dakin sa zanyi serving dinsu tunda bashi daya bane. Tana tafiyar ta na kwashe abincin na je bakin kofar dakin nasa I knocked for 20seconds sannan aka bani izini na shigo,Sake hade ido mukayi da shahrul saiya kau da kansa da sauri kamar bai gane ni ba nikuwa tsaf na kalle su duka. Shi Ya sauya kaya zuwa wata tsadadiyar velvet engilan cow bow style baki da ja. Shikuma khaldun sanye yake da wata hot pure white shirt wanda ake kira naked cashmiir ya dan matse kadan yana zaune gefen gadon shi ya wani bude button din rigar gaban faffdan kirjin sa half closed. He looks sexy ni kaina da na dan yi gulman sa araina i was seriously tripping for him ban ma sani ba. Dana gama gulma na Cikin ladabi na aje abincin agaban su nayi gaisuwa Shahrul ne kawai ya amsa ni,cos tun da ya tambaye khaldun labari na yaki ya kula sa sai bai sake ba. Ina kann zuzzuba abincin a faranti shahrul ya tambaye ni sunana,he is so cool na kanyi boyayyen murmushin da har bana amsa magana sai na aje plate na dan nitsu a hakan sai na dada burge sa shima Ban lura ba ashw Khaldun kallon mu yake har wayar sa yayi kara,na dade banji masifar sa ba sai yanzu gaba daya duk hankali na sai ya koma kansa har ban cika jiyo maganganun shahrul din bama. Abun da zan iya tunawa shine naji yace zaiyi mana sati agidan Yadda na zuba ma khaldun din aka na zuba ma Shahrul kuma Ina wajen suka fara cin abincin Khaldun baice mana uffan ba Shahrul was awwed,shi mamaki ma yake dayaga na tsaya agafe suna cin abinci,bai san wai aiki na bane hakan Aransa Sai ya shiga tausaya min har da kokarin sa wajen sani a cikin hirar su,a wasa yace ma khaldun im such a great cook shikam daga yau wannan abincin zan nayi masa. Watoh shi fresh brown yamball mai flaked fish din ya burge sa sosai. Khaldun kam tsaki yayi,dan ma ya bani haushi sai yaki cin yam balls din ya tsame offals da jollof din yaci Shahrul kuwa yana ta yaba ni,nima yake kawai nake iyayi bana cewa uffan. So i packed the plates bayan sun gama..kitchen na nufa ina kan wanke wanke sai ga big sis Na dan kalle ta sai naga kamar bata wani jin dadi? Nace big sis…. Tace baahi har yanzu baki gama bane? Kinsan darling bazai barni ba inbaki zo ba Wani boyayyn ajiyan zuciya na sauke Nadan yi kafin na tsame hannu na a kumfa na fuskance ta Big sis kiyi hakuri..kinsan su biyu ne,the other one.. he eats slow dole na jira shi..cikin kissa sai na dan yamutsa fuska na dafa kai, Tace whats wrong kin gaji ko! Nace ah’a kawai kaina kemin ciwo Tace uhh ok am so sorry..to bar wannan abun kije za akawo miki magani yanzu. Da haka muka rabu ta tura ni daki naje nati kwanciyata nikaina bansan ya suka kare da mijin ta ba. Haka dai na samu wannan saran nakanbi duk wani hanyar da zan ki sam na hadu da sadaat don na lura Acikin masu min shisshigi har gwara ma abokin khaldun wato shahrul shikam he is just a nice person babu wani attachement sai nake bashi girman sa sosai. Most time idan naje serving dinsu ya dinga yabo na kenan duk dama abokin shi ya sha nuna masa baiya son hakan dayake min. A dayan bangaren kuwa kwana biyu sadaat hankalin shi yayi mugun tashi da baya samun gani na. Ga big sis ma ta dan shiga busy da aikin ta kwana biyu baya ko samun wanda zai ji labari na awajen sa. Ita ceo ne na business companies din cosmetics guda uku wanda suka kasance natane na gashin kanta. Haka kawai sadat Sai ya yi fushi irin fushin munafurcin nan wanda daga shi sai zuciyar sa suka sani… Nikuwa tun ranar da khaldun suka fito wajen jahan tare da abokin sa shahrul Naji irin bakaken maganan da sadat ke jefa masa akan yaki accepting dina a matsayin sister sai na fahimci kishi da tsana ne a zuciyar sadat game da khaldun. Arayuwar sa Komai da biyu yake yi its obvios yana fama da haushin nafi bada lokaci na ma khaldun agidan ne fiye da kowa Sadaat shiyayi sanadiyar har shahrul ya gane cewa ni adopted child ne. Hakan yasa naji na dada tsanan halayen sa. Da sassafen ranan asabar ana gobe shahrul zai tafi,har nayi serving dinsu break fast na fito Kenan daga kitchen sai naji tahowar mutum akan stairs baima lura da ni ba Ina daga kasa ne shi kuma yana saukowa so Tun daga kan arniyar black sport canvas dake kafar sa na soma kure kallo na har na iso fuskan sa da saura kadan facing cap dinsa ya rufe. Shi kadai ne awajen kuma Yayi matikar kyau All in black theme adidas sport wears ko wayar sa bai dauko ba. Badge din rigar da jan logo haka ma jikin canvas din akwai jan logo Gefe na rabe dan nasan ko ya ganni bazai ce min uffan ba. But i was wrong,ji nayi ya bani oder 2 glasses of mango juice da pancake sai ya fita. kitchen din na nufa na fara kwaba pancake ina soyawa,sai ga big sis itama sanye da pink sport wear.. Bansan sanda na zo jikin ta ina murmushi ba don kuwa ko kai ka kawo kushel duniya kaganta kasan ta hadu Ina zakije Haka?… You look so beauttfl sis i was exited sai nayi mata maganan kamar yadda take min in tana yaba ni Kwabe fuska tayi jocklingly amused bata kula ni ba ta bi kan table din da kallo tace wai shi Aaban(angel) bazai barki kisha iska bane? Jiki fa kullum a kitchen,bahiyyah meyasa bazaki ce ma mum aikin ya isa haka ba? Kallon salon da tayi maganan nayi nabita da murmushi I knew this is not her word zai iya yuwa shawaran da mijin ta yake bata kenan so that na bar zuwa wajen khaldun sood. Nace karki damu big sis… Ina de basket ball court zakije? I wll join you in 10 minutes Tace ok ta dan shafa kaina tayi murmushi tayi waje. A wajen kuma Khaldun da shahrul sune a katon luxurios basket ball court dake kusa da wata katoton Aqua maria pool suna game dinsu cike da nuna jarumta Suna ta hirarraki Shahrul sport wears na kamfanin nike yasa all white shikam ya cire cap dinsa ba kamar khaldun ba.. Shi saood Kallo daya zaka masa ka fahimci Training din sojoji na jinin sa he is so full of energy ga kwarjini kamar dan sarkin aljanu.. To da sassafen ma sadaat sun gamu da shahrul khadum bai sani ba kuma anan sadat ya san cewa zasuyi sport din Shigar sa gida sai yace ma subayah itama ta shirya suje suyi wasa. Murna take ta yi duk ta dauka ko duk romantic treat ne bata san don zunzurutun neman maganan khaldun yayi hakan ba. Haka suka fito sunyi kyau acikin shirin su,kallo daya khaldun ya masu ya kau dakai ya cigaba da dribbling da ball kamar bai san da zuwan su ba shahrul kam tsayawa yayi ya dinga ma subaya dariya yana tsokanan ta. Tunanin meye Khaldun din yake oho sai ball din ya kufce a hanun sa charaf sadaat ya chafke ya kuma bishi da dariyar mugun ta Tsaki mai sauti yaja suka dago ido Wani banzan kallo suka watsa ma juna Tare da sauke miskilin murmushi sadaat din ya buga masa ball din a kirji yace masa “Lets play … Tsaki khaldun yayi,he got pissed …am out ..ya furta cikin wuya zai juya ya bar wajen Wait…Subaya ce ta taro sa cikin wasa waiit wait Khaldun.. .. Sai ta maraice fuska tace afraid? Toh shikenan Am going to be in ur team Aaban pleasssse let play..ta dada marairaice mashi Haushi take bashi musamman daya lura indai akan mijin ta ne toh ko taga ya daure fuska sai ta daga kanta tayi kaman bata san ma yanayi ba.. Haka dai ya amince. Team khaldun and subaya da team shahrul and saadat. Nikam ina ciki ina hada masa oder sa bansan me ake ciki ba. Wasa ne mai zafi ya fara wakana Musamman tsakanin khaldun da sadaat domin kuwa karfi suke gwada ma juna Har An ture subaya a kasa yafi sau a kirga sai kawai ta ja gefe tayi shiru tana lura da su. She dont really like their hidden hatred. Amma ya ta iya khaldun kusan kowa ma ba so yake ba. Tayi nisa cikin tunanin kawai sai na katse ta,tray ne a hannu na na cinnamon flavoured pancake da 2 glass of mango juice . Subaya tayi min murmushi na mata alaman bari na aje tray din nazo… Dan wulgawar da nayi gaban su sai sadaat ya ganni a yunkurin farko da gangan ya sa elbow ya buge shahrul a hanci fa wani irin mummunan bugu har sai da ya fadi a kasa yayi kara.1 “Shah”…khaldun ya furta da sauri yayi kansa yana duba shi ransa ya dada hadewa kamar wanda zai tashi ya rama masa Big sis itama ta taho tana tambayar sa are you ok? Sadaat din sai ya sa fuska kamar bai sani ba ne yayi hakan sai ya shiga ce ma shahrul Im sorry dude.. Nidai Tsaye nayi da farantin,ina kallon ikon Allah Nasan dai shahrul ya basar da zafin dayake ji ne don kar khaldun yace zaiyi reacting.. Shikuwa khal Sai yace masa su shiga gida kawai amma haka shahrul yaki fir yace kawai suyi wasan ai he is ok.. Nikuma Khaldun bai ce min komai ba sai na aje Juice da pancake din akan ottoman Bench kusa da ruwan pool na dawo na tsaya nida big sis. Kana ganin fuskn ta kasan She is worried for shahrul dan naga fuskan nata dauke yake da damuwa .ita kanta ta gane cewa shahrul baice komai ba ne sabida baya son khaldun ya dau abun da zafi But It neva worked don kuwa ana fara sabon game din khaldun sai da ya nemi dai dai setin bakin saadat ya zuba mashi gwiwan hannu dagangan sai da yayi tumble din bazata yasa ihu.10 Kowa yasan khal baya bada hakuri ahaka ma riirike shi shahruul yayi cikin harshen larabaci ya na dan masa masifa cewa meye haka? Subaya tuni ta dago mijin ta a birkice tana dubasa,tsaban haushin da zafin da bakin sa yake sai yana tutture hannun ta ajikin shi Bata ji dadi ba sam ta dago ta kalle khaldun daya tsime,shahrul ne kawai yake ce ma sadat yayi hakuri is a mistake. Sabida ni sadaat ya waske yace musu bakomai besides ai shima yayi mistake din dazu. Haka aka bar magana Kamar da gaske sun fahimce juna Aka sake komawa sai dai dukan su da abunda ke ransu. Subaya tace ma saddat su koma daki ita kam game over kawai muje gida bai amsa ta ba Nan khaldun ya min ido akan na kawo drink ma shahrul, banyi kasa a gwiwa ba na dauko farantin ina tafe Ina daf dasu na daga kafa ta kenan naji kwal abu mai karfi ya ture ni tsundum na fada acikin ruwan pool Sadaat ne ya sake ball ya gangaro bazata naci karo dashi kowa yaha hakan Amma dukan su basu motsa ba Big sis subaya zata zo ta cire ni sadat ya finciko ta,yace bazakije ba yanayi yana kallon khaldun alaman tunda sunfi kusa dani to su cire ni mana Nikuwa inata wutsil wutsil cikin ruwa Hankalin subaya ya tashi tana ta kira na tana ce musu su taimake. Sadaat Haka yaki ya sake ta,khaldun ma ya dauke kansa ya hade rai. Shahrul hankalin sa ya mugun tashi da irin wasan banzan da ke wakana tsakanin sadaat da khaldun sai kallon su yake yi cike da mamaki. Haka aka barni A cikin ruwa ina kokarin fitowa the pool its too big dan haka da kyar nake diving. Daga karshe Shahrul din ne yayi tsaki ya tashi zai zo ya taimaka min A fusace khaldun ya riko sa yace please let go in,wai kai ka jefa ta ne? “Khaldun..subaya ta tsawatar.. amma ko ya kula ta sai Ya ma ja hannun shahrul dagske Zasu bar wajen Abun ya dada ba sadat haushi A fusace ya juya yace ma big sis And you too.. Ai bake kadai bace ya agidan nan,that girl is both your sister right?,idan wani banza is weak and wicked enough yana azabtar da ita so be it Get in doors.. Ya mata nuni da hanya Subaya zata yi magana..ya tsare ta rai a bace ya ce NOw.. Da sauri ta shiga gida ta barsu su ukun. Zai motsa kenan Khaldun ya tsare sa yace” i hope i dnt hear you calling me weak and wicked? Shahrul dhe tsaye na kallon su yace sa’ood pls stop it. Please let me help the girl dan Allah ku bari Shikuwa Sadaat abunda yake so kenan yaga dai ya bata ma khaldun rai kamar yadda yagani yanzu,baisan tsawar daya yi ma yar uwansan bane ya shake sa Lets go..shahrul y dada jansa amma yaki motsawa sadat kaima ka shiga gida mana the game is over Comn dudes Wani fizga khaldun yayi cikin bacin rai yace ma shahrul baza a cire ta ba,shi da baiya azabtar da itan sai ya cire ta. Sadaat yace yess i will… zan cire ta mana,am just waiting for you to go..am human i dont enslave girls Im not like you.. Ran khaldun ya dada baci sosai Da kyar shahrul ya rike sa . Sai ya fara tunanin meye ruwan sadat da aikin da nakeyi mashi, da chan shi yace ina masa aikin ne harda wani zai masa wannan zagin? Bacin ransa sam babu kyan gani Wani fixge jikin shi yayi ya taho bakin pool din ya kalle ni”get out”… ya daka min tsawar da sai da na firgice na fito a ruwan batare da na sani Go inside now.. A tsorace na wuce shi da gudu I went inside cryng my balls out. ….gaba daya tausayi na ya kama shahrul sosaii Haka suka watse kowa yayi hanyar sa Ziciyar sadaat kuwa kamar zai fashe dan baiso hakan ba A daki na big sis Subaya ce tayi ta bani hakuri har nayi bacci. Dana je serving dinsu dinner yau kam shahrul bai sake fuskan sa ba. Duka sunyi shiru sun basar da juna Alaman wani abun ya shiga tsakanin su kowa sai shan qamshi yake. Little did i know that,saboda ni shahrul yayi masifa sosai ma khaldun dazu Ba wai don ina masa aiki ba shi kin accepting dina dayayi a matsayin yar uwan sa ne ya dame sa. Ai kuwa Ko uffan baice masa ba,Taurin kan khaldun ya wuce misali dan shika dai yasan meyasa yake yin haka a duk korafin da shahrul yayi har washe garin ranan bai masa dai dai da ya amsa shi ba. Da safe dana zo serving dinsu shahrul sai ya ce min zai tafi,yace na dinga hakuri and he enjoyed my cooking sosai, cewar sa wata rana zai sa akawo ni oman na na zauna dashi ko dan na dafa mashi daddan abincii shida mum dinsa. Duk dama nasan hakan bazai yuwa ba amma naji dadi sosai,nace masa nagode’..ban ma kar a dora wani kalma ba Na ci karo da wani banzan kallon da khaldun yake mana,don kuwa hararar da khaldun din ya watsa min kadai ya hana ni amsa shi musamman maganan zuwa oman da shahrul yayi. Today i notice a little bit of jelousy a yanayin sa sai kawai nayi shiru.36 Duk dama fushi nake da shi da naga ya nuna alaman kishi na aransa a Take naji zuciyata ta yafe mashi komai.