ZUCIYA CHAPTER 3

ZUCIYA CHAPTER 3

Kallansa take cikin tsananin mamaki ya sake murmushi yace ” Riga tafa? Ko kin barmin wannan d’in? ” Kasa tai da kanta sannan a hankali tace “na d’auka ka tafi ai. ” Datti yace ” me kuke nufi kenan ka santa dama? Sani bana taimako ba? ” Ashraf yad’an yi murmushi dama so yake ya kular da Datti yace ” sani kuwa tunda ji jiya a d’akin ta na kwana. ” Yai maganar yana kallan Nafi, gaba d’aya kowa ya kalleshi, Datti ya rike haba yace ” Kwana? ” Ashraf yai wani murmushin rainin hankali sannan ya ya d’aga kai yace ” Uhm hum” Hannee da mamanta suka kalli Nafi cikin mamaki, Dan litti shima mamaki ne taf a ransa lalai wannan gayen ashe dan duniya ne? Nafi ce tayi baya da sauri tai cikin gida, kallan kofar data shiga sukai suna tunanin me kuma zatai. Nafi kam tana shiga da sauri tai d’aki tana tafe tana murmushi takasa gane dalilin murmushin nata, rigarsa data ninke d’azu ta dauka abin haushi ba tada turare hakan yasa ta fito, suna tsaye sai gata ta dawo. Datti yai tsaye yace “Gungumar Munafuka ina kika je? ” Rigarsa ta mikamai fuskarta a sake tace ” danaji bakai min magana ba sai na d’auka tafiyarka kayi. ” Ashraf ya amsa yace” ina kuwa zan tafi? Bayan nasan kina cikin wani hali? ” Salati Datti yasa yace ” yau na shiga uku lalai yarinyarnan ke ba karamar ‘yar iska bace, a haka kowa ya ganki sai ya d’auka ke ta Allah ce ba’asan tsantsar munafircin ki yafi na shaid’an ba, yanzu dan iskanci da so kikai ki auri Ali bayan kin gama lalata da wannan? ” Cikin mamakin kalamansa Nafi ta dago ta kalleshi, lalata? Me kenan? Maman Hanne ma tace ” Gaskiya Nafi kin ban mamaki ban taba tunanin zaki aikata haka ba. ” Itakam Hanne harara kawai take makama Nafi. Ashraf ne ya kallesu yace ” Gaskiya bakuda adalci, wato kai kana mahaifinta sanda nace ta taimakeni baka shi mata albarka ba ka yabe ta ba, sai yanzu dana fad’i na kwana a d’akin ta kaf cikinku ba wanda yai tunanin lalai kila ba abin banza akai ba. ” Ya d’an furzar da iska sannan ya matsa daga inda suke, ta baya ya zaga ya cire rigar jikin sa yasa tashi, tunda ya juyo ya fara tahowa kowa ya kuramai ido, lalai wannan gayen bana karya bane, tafiya yake cikin isa Nafi itama ba’a barta a baya ba gun kallansa, Hanne kam kishi duk ya isheta. Ashraf har ya karaso basu daina kallanshi ba, D’an litti ya dafa yace ” Babban gaye me kake tunani ne? ” D’an litti ya had’iyi miyau yace ” Kai Ashraf gaskiya she is beautiful. ” Ashraf ya sakeshi tare da mikama Datti rigarsa yace” mu zamu wuce. ” Datti kam sam ya kasa magana, kallan Nafi yai yace ” muje ko? ” Kallan mamaki tamai dan ita batasan shine mijin ba lokacin kanta ma kasa sai dai ta kasa mai musu nan ta kalli Datti tace “Baba mun wuce. ” “Ah to shikenan, sai munzo ganin gida, d’an litti ya kawo mu. “datti yai maganar yana kalle kalle. Nafi tace to. Maman Hanne ta mata sallama sai dai ganin yanda Hanne ta hade rai yasa Nafi ta juya ba tare da ta mata magana ba. ” Sunanan tsaye har suka hau mashin, nan suka nufi hanyar Gwaram inda zasu hau mota. ******** Sunyi tafiya sosai kafin su isa, nan D’an litti yakaisu inda zasu shiga mota, wata karamar golf suka samu D’an litti jiyai Ashraf yace ” Shata muke so. ” Dasauri ya jawo rigarsa yace ” Ashraf kasan me kake fad’a kuwa? Inkace shata yana nufin fa ku biyu za’a kai har kano kaga kuwa zaka biya money panty. ” Ashraf yai d’an murmushi yace ” meye kuma panty? ” D’an litti yace ” Kudi dayawa nake nufi. ” Kafadarsa Ashraf ya dafa yace ” Plenty ake nufi. ” Yana kainan ya wuce gun driver yace ” Muje ko? ” Nafi ce ta kalleshi sanda taga ya bud’e mata bayan mota ta shiga, ya dawo inda yabar D’an litti a tsaye kamar gunki ya ciro dubu uku ya bashi yace ” Nagode sosai d’an litti Allah ya karama ilimi. ” Kallan kudin yai yace ” Ashraf ina zan kai kudin nan? ” Murmushi yamai sannan ya mikamai wata dubu d’ayan yace ” ka ba abokinka. ” Ya juya ya nufi motar, tsayawa yai yana tunanin ko dai yabada number wayarsa in case ko iyayenta zasuzo Kano? Kai ya girgiza alamar a’a lalai dole ne ya koya musu sanin darajar yarinyar nan, dan ya kula zaman dasuke tare da ita ne yasa ba wanda yake ganin darajarta da mutuncinta. Shima bayan motar ya shiga, Nafi kam tana zaune duk jikinta a sanyaye, bata taba shiga mota ba sai yau, sai dai taitajin labarin agun Hanne yau gataa ciki, Driver ya tada mota. D’an litti ne ya matso da sauri ya turo kansa ta window yace ” Nagodee Ashraf sannan yanzu na rike plenty ko? ” Ashraf ya mai murmushi yace ” kana burgeni ta yanda kake kokarin yin turancin nan, Allah ya hada fuskokinmu da alkairi. ” Murmushi sukama juna D’an litti ya dagamai hannu yace “Sai munxo gidan ka. ” Kai ya daga nan mota ta ja suka fara tafiya………. Sun danyi nisa a hanya kad’an Ashraf ya kalli Nafi sannan yai gyaran murya, d’agowa tai ta kalleshi da idanunta, Yad’an mata murmushi sannan yace ” Nafisa? ” Gabanta ne ya fad’i jin ankirata da cikaken sunnanta, sai dai bata amsa ba sai dai hankalinta data tattara zuwa kansa. Ashraf ya cigaba ” ki nutsu zamuyi magana mai mahimmanci ne. ” Ta d’aga kai alamar tanaji. Ashraf yadanyi ajiyar zuciya sannan yace ” Nafisa bazan miki alkawarin so ba, ba kuma zan miki alkawarin kulawa ba sai dai zan miki alkawarin ni Ashraf bazan taba bari ki wulakanta ba. ” Kanta na kasa sai dai gaba daya gabanta har yanzu bai daina bugawa ba, ya cigaba ” Na aureki ne domin ceton rayuwarki daga gun mutanen nan da babu imani a zuciyarsu, sai dai inaso ki kama bakinki kamar yanda nima zan kama. ” Dagowa tai cikin mamaki ta kalleshi yace ” kada ki kuskura ki fadama kowa na aureki, wannan sirri ne a tsakaninmu ni dake, karki fadama kowa wannan shine abinda zai kareki.” Idanunta ne suka fara cicikowa nan ta shiga kokarin maidasu, kai ta daga mai alamar ta fahimta, Ashraf ya cigaba ” Nafisa zan ajiyeki a gidanmu har Allah ya kawo miki wanda kike so shima yake sanki, in kun aminta da juna sai in sauwake miki ki aureshi……… ” Kallan datamai ne yasa yai shiru shima, me kenan? Abinda zuciyarta ke raya mata kenan? Wani irin aurene a ranar aurenta ake mata zancen saki???? Ashraf yadan juya kai sannan yace ” Bazaki fahimci me nake nufi ba yanzu amma na sani nan gaba zaki gane, a inda zamuje zakiga zuciyoyin mutane iri iri sai dai inaso ki daure ki zauna da kowa a yanda yake. ” Nafi wanda hawaye yake yawo a fuskarta tai saurin jan mayafi ta tarufe fuskarta, kallanta yai sai dai ya za’ayi? Dole ne ya fadamata gaskiya……. Nafi tai shiru sai dai tunanin dake zuciyarta yawa garesu sai dai tasan abu d’aya dama, tabbas Dan binni ba santa yake ba taimakon ta kawai yai kamar yanda ta taimakeshi, tana ta tunani har bacci yai awun gaba da ita. Ashraf kam yayi shiru yana tunani, tabbas motarsa lafiya kalau ya ajiye ta, to amma mezai sa lokaci daya burkin motar yakiyi? Girgiza kai yai da sauri yace ” zato zunubi, ikon Allah ne. ” Bakin wani katon gida Ashraf yace mai yai parking, daga bakin gate din mutane ne sosai a tsatsaye sannan wasu dauke da speaker da cameras hakan yasa Ashraf yasan ‘yan jarida ne a gun, kallan Nafi yai wacce ke zaune yace ” Nafisa kin gaji ko? ” Kallansa tai sannan ta girgiza kai alamar a’a, ya dan murmusa sannan yace ” mun iso. “+ Ta kalli waje ganin mutane yasa ta kalleshi, ya bud’e motar ya sauka sannan ya zaga ya bud’e mata, a hankali ta fito jikinta duk a sanyaye, ya kalli driver d’in yace ” bari in kawo ma kudin ka. ” Ya amsa da to, juyawa yai ya fara tafiya, bai karasa gun mutanen ba kawun sa wato kanin babansa ya hangoshi cikin tsananin mamaki da farinciki ya taho da saurinsa, kusa da Ashraf ya tsaya yama kasa magana sai dariya kawai da yake ya kankame hannun Ashraf, mamakin da ya kamani banga Ashraf yana farinciki sosai ba sai dai yace ” Kawu na tada muku hankali ko? ” Wanda ya kira da kawun ya gari fadada murmushinsa yace ” Ashraf duk mun daga hankalinmu ganin jiya a rafin wudil muka wuni cur ana nemanka an rasaka tsoro yasa muka fara tunanin ko ka cika sai dai mahaifiyarka taki yarda sam tace lalai kana nan da rai. ” Yad’an yi murmushi kadan sannan yace ” Bari na shiga ciki, sannan dan Allah aba mai mota kud’i.” Kai ya daga mai cikin farin ciki, Ashraf ya juya ya kalli Nafi dake tsaye yace ” Mu shiga ko? ” Kallanta kawu yai saidai baice komai ba, Nafi kam a hankali ta karasa inda yake, nan suka fara tafiya, hannu kawai ya dagama ‘yan jarida suka nufo inda yake, bai jirasu ba ya nufi gate, ya shige ciki. Inalilahi abinda Nafi ta fada kenan a fili, wani tafkeken gida ta gani, ba wai haduwaa kad’ai ba gida ne kato flat flat dayawa, in ka gani zaka dauka ko gidan hayane na masu kud’i sai dai Ina gida ne na Marigayi Alhaji Saminu wato mahaifin Ashraf, ya gina wannan tafkeken gidan ne saboda yazauna shida d’an uwanshi sannan yayi flat dayawa ne saboda in ‘ya’yansu sun taso kowa ya kama flat daya ya zauna da nasa iyalen. Wannan kenan. Ashraf har yad’anyi nisa ya juyo a bakin gate yaga Nafi a makalle tana ta fadin Inalilahi, a hankali ya tako yazo inda take, ya kalleta yaga ta runtse ido tsam, yace ” Nafisa muje ko? ” Kallansa tai a tsorace tace ” Muje ina? ” Ya nuna mata hanya yace ” ciki mana. ” Yawu ta hadiya tace ” Dan binni nan din inane? ” Ya dan canza fuska kadan yace ” badai baki yadda dani ba? ” Kai ta girgiza da sauri alamar a’a, yace” good, to in har kin yadda dani muje ko? ” Duk da tsoro bai bar ranta ba sai dai bata daina binshi a baya ba, can wani flat sukaje, suna karya kwanar flat din sukaga wata yarinya wacce batafi sa’ar Nafi ba rike da faranti zata shiga ciki, Ashraf yace ” Little! ” yafad’a tare da daga mata hannu. Cikin mamaki ta juyo, ganin Yayanta batasan sanda ta saki farantin ba wanda ke dauke da lemon kwalli akai ba, da gudu ta karaso gunsa ta rungumeshi, sai kuka. Ya dagota kadan yace ” Little kukan fa? ” Hawaye take tace ” Yaya ina ka shiga? Hankalinmu ya tashi sosai. ” Kanta ya shafa sannan yace ” to naji ya isa haka, ya dan juya ya kalli Nafi yace ” Little zan shiga ciki so nake ki shiga da wannan tai wanka taci abinci ki bata kayankk tasa. ” Kallan Nafi tai sannan tace ” waccece? ” Yace “Zan fada miki, Mumy fa? ” Tace ” duk fa muna bangaren Umma muna zazzaune, mumy jiya cir ruwa kawai tasha. ” STORY CONTINUES BELOW Ya dan juya kai, little tace ” Yaya ya kamata kaje ka ganta kafin ka shiga ciki dan da alama nan kafara zuwa. ” Kai ya juya baice komai ba, Kallansa tai cikin rashin jin dadin yanda sam baya kula mahaifiyarsu sosai bayan kowa yasan yanda take tsananin sanshi, zatai magana kawai ta hango Aneesa ta taho da gudu, ganin tana kallan wani gun yasa Ashraf ya juya hakan yaba Nafi damar juyawa ta kalli gun itama. Da gudu ta taho sai data kusa zuwa inda suke sai kuma ta tsaya daga nesa ta kafe Ashraf da ido idanunta na zubar da hawaye, Nafi ta bi Ashraf da kallo, yanda taga yana kallan ta yasa tasan akwai wani abun tsakaninsu. A hankali Ashraf ya fara takawa zuwa inda take tana tsaye tana mai wani kallo mai tattare da ma’a noni sanda hawaye nabin kuncinta. Nafi tai tsaye jiki a sanyaye tana kallansu, sai da Ashraf yazo kusa da ita kawai ta gifta ta gefensa tasa gudu, ta kusa da Nafi ta wuce, ta nufi inda little ta nufa d’azu. Turus yai agun, jikinsa duk yai sanyi, little ta kama hannun Nafi tace ” wuce mu tafi xasu fara abin nasu. ” Sun je zasu shiga sai ga mutane kowa ya taho harda Mumy da Umma sun taho gun Ashraf, sudai suka karasa ciki. Kallan fallon Nafi tai, aranta tace ” lalai rayuwa tana wani gun. ” Sunje shiga d’aki Nafi ta kalli Little jin sheshekar kuka, Little tai murmushi tace” Neesan yaya kenan yau sai yayi lalashi mai karfi kafin abarmu musamu bacci. ” Nafi ta kalli kofar d’akin jikinta ya kara sanyi, Little tace” karki damu inda sabo sun saba, ita shagwab’a shikuma saurin b’ata mata rai shiyasa wannan kukan harya fara daina damuna. ” Nafi ta jinjina kai sannan tace ” Amma kuna kama da ita. ” Little tai murmushi tare da tura kofar d’akin tace ” Yaya tace ta gurin uba, shi kuma ya Ashraf yaya nane na gun uwa. ” Kallan mamaki Nafi ta mata tace ” Ban gane ba. ” Dariya Little tai tace”Maman Mu ce ta auri baban Ya Neesah bayan Baban Ashraf wato yayan babanmu ya rasu. ” Nafi ta zaro ido cikin mamaki zatai magana sai idanunta yakai kan tangamemen d’akin, kallo tabi d’akin dashi cikin tsananin mamaki lalai dukiya tana wani gun, yanzu nan d’akine? Jitai Little tace ” Yes. ” Nafi ta hadiye wani yawu cikin mamaki, take kallan d’akin. Ashraf kam yana tsaye gurin ‘yan uwansa manyan ‘ya’ya maza na kanin babansa da kuma kannensa, yake kawai yakeyi dan shikansa yasan ba kowa bane yake farin cikin dawowarsa sannan shi ya kosa subarshi yaje ya lallab’a Neesarsa. Mumy ta kalleshi tace ” Ashraf kai wanka sai kazo kaci abinci ko??” Ta sani sarai bazai amsa mata ba sai dai tasan zaiyi abinda tace, kallan yayen sa yai yace ” Zan shiga ciki.” Yana kai nan ya wuce, nan suka juya, dadi da farin ciki ya kama Mumy da sauri ta nufi hanyar kitchen dan shiryamai abinci, duk wannan kin kulatan da Ashraf yake sam bata ganin laifinsa tasan dole ya ji haushi daga mutuwar mahaifinsa ba dadewa ta sake aure kuma gidan datake da anan take sannan ta auri kanin mahaifinsa. Ashraf har ya nufi bangarensu ya zagaye ya koma bangaren su Aneesa. Nafi dake zaune akan gado sai dan tsalle take kadan taji ana kwankwasa kofa sannan taji muryar Ashraf ya na cewa “Neesah?? ” Nafi tadaina wasa da gadon, tai shiru tana jin Ashraf, ya dan dade yana knocking kafin yace ” shikenan Neesa na dauka kece ta farko da zaki fara farincikin ganina shine zaki shige d’aki kina jina ina magana? Shikenan na tafi. ” Nafi tanaji daga ciki cikin wata murya mai salo da jan hankali tace ” Amma yaya kasan halin dakasani kuwa? Jiya ko bacci kasa yi nai ina tsoron kar in fara ace min ga gawarka can. …….” Kasa karasawa tai, Ashraf ya murmusa yace ” Neesah ki bud’e inganki please….” Nafi ta sauka daga kan gadon ta zauna a kasa, murmushi ta kakaro da kyar tace ” dama ai baice yana sona ba, kuma ya sanar dani hakan, shikenan.” Tanajin motsin bude kofar. Ashraf na shiga ya karasa inda take akan gado, tana ganinsa tasa pillow ta rufe fuskarta, Ashraf ya matso sosai saitin kanta ya kwantar da kansa yace ” Ko kallo na bazakiyi ba? Na d’auka yau in kika fara kallona sai na kwace kaina? ” Ta dago a hankali ta dan harareshi sannan ta dau pillow din ta makamai ta kara makamai, ta daga zata sake na uku yai saurin rikewa, yace ” ya isa to dear ai kin huce ko? ” Ya fada yana mata wani kallo……. Little ce ta fito daga toilet ta kalli inda Nafi take tace ” zo ki shiga kiyi wankan. ” Nafi ta mike jiki a sanyaye ta karbi dan towel din da little ta mika mata, kallo tabi towel din dashi tace” dan wannan abun zan daura? “+ Little tai murmushi tace ” to dame zaki daura? Ni shi kadai garen. ” Kallan zanin jikinta tai tace ” na d’aura wannan. ” Little ta saki murmushi tace ” ya sunan ki? ” Nafi a kasan zuciyarta so take tace Nafisa sai dai ta rasa me yasa batasan akirata da haka tafisan tadinga jin wannan sunan daga bakin Ashraf, “Nafi. “ta fada tana Kallan little. Tad’anyi murmushi tare da mika mata hannu alamar gaisuwa tace “ni kuma Maryam amma little ake cemin ko kice little Maryam, mu biyu ne masu suna maryam babbar riketa akai agidan har tayi aurenta. ” Nafi ba tare data mika mata hannu ba tace” li?? Hmm nidai Maryam kawai zan dinga ce miki. ” Little tai murmushi sannan ta kara mika mata hannu tace ” mu gaisa to. ” Nafi ta noke tare da girgiza kai tace ” ba maza bane ke gaisawa?” Little ta fizgo hannun Nafi tace “Mata ma nayi ai musabaha ce. ” Kai Nafi ta jinjina, little tace “shekararki fa? ” “16.” Little tad’anyi tsalle kadan tace “nima haka. ” Sukai murmushi a tare, Nafi ta daura zani ta nufi inda little ta kira da bayan gida, Da gudu Nafi ta dawo ta kalli Little tace ” kina nufin anan zanyi wanka? Ta ina? Ta yaya kuma? ” Little ta kalleta tace “muje in nuna miki.” Nafi ta ja ta tsaya, Little tace “Nafi muje mana. ” Dum Nafi ta mata itadai tsoro take ta ina zatai wanka a wannan gun? Little tadan had’e rai tace “Shikenan bari in je in fadama Ya Ashraf. ” Da sauri Nafi ta rike rigar Little jin an anbaci Ashraf tace “Zanje Maryam. ” Little tadanyi dariya tace “muje to. ” Sunje toilet nan Little ta nunama Nafi yanda zatai wanka, ganin hankalin Nafi yaki kwanciya da shaya yasa little ta tararmata ruwa a baho tace hakan fa? Nafi tai murmushi alamar gwara hakan. Nan little ta fita ta barta. ********** Ashraf kam suna shiryawa da Neesah ya wuce bangarensa, ko ince bangaren mahaifinsa shikadai ne a bangaren saboda duk yanda akaso asashi cikin ‘yan uwansa maza kin yarda yai yace ” lalai shidai a bangaren Mahaifinsa yake san zama. ” Yana shiga ya wuce toilet yai wanka ya zura doguwar riga sannan ya fara rama salolinsa. Bayan ya idar ne yaga sakon meeting a babban falo, in kuwa za’ai wannan taron to acan ake cin abinci. An sanar da kowa akan akwai meeting a babban falo saboda dawowar Ashraf. ********** Nafi ta fito daga wanka ta shafa mai kawai littleta bata doguwar rigar atamfa tasa, saboda little ta fita kiba hakan yasa rigar bata mata kyau ba ga wuyan rigar sai fad’owa yake, ga ta kima daurin dan kwalinta ta matse kanta tamau. Itadai little taso mata magana sai dai tasan daga zuwan mutum gari bazai wuyo ace ya canza abinda ya saba ba, gashi tana tsoron karsuyi latti wajen meeting. STORY CONTINUES BELOW Nafi na gamawa little ta kama hannunta tace “muje ko? ” Nafi wanda gabanta ke faduwa tace ” Maryam gani nake ni bai kamata inje ba. ” Dariya Little tai tace”to yaya na kira na tambaya yace muje tare yanasan introducing d’inki. ” Nafi ta kalleta da mamaki tace “me? Inkiro me? ” Dariya little tai tace “ke dai muje kawai. ” Nan suka fito sunyi sa’a Neesah ta riga ta fita, nan suka taho har zuwa babban falo. Katon falo ne sosai wanda gefe aka kawatashi da wani round din dinning table manya guda biyu, d’aya maza ne a zazzaune d’ayan kuma mata ne, sai dai duk a kusa da juna suke. Tunda suka shigo kowa ya zubama Nafi ido yana mata kallan mamaki sai dai banda Ashraf wanda ke zaune fuskar nan tasa kamar yanda ya saba a murtuke, Haka little ta jata har zuwa inda zasu zauna. Zuciyar Nafi kam kamar zata fado saboda tsananin tsoro da ganin mutane dayawa maza da mata, kanta na kasa, sunje zama kawai tai tuntube ta fad’i, kwashewa akai mata da dariya sai ta samu kanta cikin tsananin tsoro ta kasa mikewa, Ashraf ne ya kallesu ran nan a had’e ya kalli Nafi wanda itama shi take kallo ya mata alama data tashi. Jiki a sanyaye ta mike little ta taimaka mata ta zauna. Kanta ta sunkuyar, kawu yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu yace “Bismillah.” Nan kowa ya fara zubama kansa a binci, Umma kuwa mahaifiyar Aneesa da ita Aneesan sun kafe Nafi da ido. Kowa ya fara zuba abinci, itadai Nafi a zaune take sai gabanta dake ta faduwa, ganin batada niyyar zuba abinci yasa Little ta zuba mata shinkafa da miyar carras sannan ta matso mata da papper chiken da salad, Nafi ta kalle ta sannan ta d’au chokali, ganin yanda kowa yakecin abinci yasa ta fara cin shinkafar a hankali, sai dai lomarta biyu taji inaa bazata iya cigaba da ci ba, gani tai kamar kowa kallanta yake, ta zaune tare da matse kafafuwanta dake rawa, little ta kalleta tace “Nafi tafiya fa kikai kici abinci mana? ” Nafi ta kakaro yake tace ” a koshe nake ai naci abinci a mota Yayanki yaban doya da kwai. A hankali sukai maganar, Ashraf yadan kalli inda take ganin bataci abinci baiyi mamaki ba, ta ina zata iya cin abinci a cikin mutane? Bayan kowa ya gama ne Kawu yai Hamdalla sannan ya fara magana “Alhamdulila Allah ya taimakemu d’an mu ya dawo da ransa da kuma lafiyarsa wannan ba karamin abin farinciki da alfahari bane, lalai Muna godiya ga Allah wanda yasa muke zaune yau da Ashraf kamar yanda muka saba. ” Kowa ya jinjina kai alamar jin dad’i, akace Ashraf yai magana. Shiru yadanyi nawasu dakika kafin yace ” Nagode da kulawarku, Sai dai inaso in nuna muku Nafeesa wacce itace sanadiyar zamana anan gurin haka, Itace wacce ta taimakeni a lokacin da nake tunanin yanke alaka da duniya, Allah ya kawomin ita ta taimakeni ta ceci rayuwata. “ Jin haka yasa kowa ya kara kallan Nafi wacce kanta ke kasa, sai gabanta daya tsananta fad’uwa. Wani daga cikin mazan gun yace “Lalai Ashraf to dan ta taimakeka shine ka taho da ita nan ko me? Iyayene batadaso ko me? ” Ashraf ya bugamai wani kallo baice komai ba, Umma mahaifiyar Aneesa tace “Ashraf ina ganin gaskiya Nuhu ya fada in ta taimakeka sai a bata kud’i ban gane dalilin tahowarka da ita ba. ” Ashraf ya dan kalleta kadan nan ma bai tanka ba, Mumy tai murmushi tace ” tunda ya taho da ita akwai dalilinsa nayin hakan nasan halin Ashraf sarai. ” Kansa ya juya sai dai fuskarnan a had’e take tamau, nan aka dan fara musu wasu suce ya kamata wasu suce bai dace ba, Anisa kam kallan kyana kawai takema Nafi. Cikin wata kakkausar murya mai zafi Ashraf ya mike yace ” Me? Dan na taho da yarinya shine ake cece kuce? A kan wani na ajiye ta ko me? Ko kuwa anaso ace ni Ashraf ban isa in kawo wanda na ga dama cikin gidan nan bane? ” Wannan kalamai dayai ya gigita kowa itakam Nafi idanunta ne suka ciciko tsoro ya kara kamata, Kawu ya kalli Ashraf yace ” Kada ka manta Ashrac akwai iyayenka anan, taya dan ranka ya baci zaka hada da kowa ka fara fad’a? ” Ashraf ya kalli Asim sannan ya kalli inda Nafi take yace “Duk wanda yake ganin hukunci na bai mai ba sai ya tareni muyi magana. ” Yana kai nan yai waje, Umma tabishi da kallo, Mumy kam da sauri ta mike ta bishi. Nan aka cigaba da ‘yan maganganu, little ta kama hannun Nafi tace “Nafi mu bar nan ko? ” Suna kokarin mikewa sai ga Ashraf ya dawo daga bakin kofa kawai ya kalli Nafi sannan ya kalli Aneesa yace ” Neesah inasan ganinki. ” To fa gani nai Nafi ta mike itama Aneesa ta mike, Umna ta kalli Nafi tace ” ke yake kira? ” Nafi wanda itakam jitai kamar yace “Nafeesa”tai tsuru tana kallan Umma. Aneesa wani haushi ya kamata, a zuciye ta bangaje Nafi tai gaba. Nafi ta tsaya cak kamar gunki sai hawaye, Kawu ya mike shima da zuwanta bai wani burgeshi ba yai waje. Little ta taso ta kama hannunta Asim yasa dariya yace “ko dai akwai wata manufa ne a tahowa da wannan kwailar? ” Yai maganar yana kallan Nafi aka kwashe da dariya, sudai sukai waje. Suna fita Nafi tasa kuka. Aneesa kam a gefe taga Ashraf ta karasa inda yake fuska a had’e tace ” menene? ” Shima fuskarnan a had’e yace ” ki fadama ummanki tadaina min abinda takemin menene nata dan na taho da Nafisa? Akan wani zata zauna? Ko kuwa yarinya ce ita daza’ace wanka ma yi mata za’ai? ” Aneesa ta kalleshi cikin bacin rai tace ” Yaya dama saboda kamin fada ka kirani? Sannan yanzu kace Neesah amma dayake yarinyarcan yar rainin hankali ce ta d’auka wai ita kake kira. ” Ashraf ya kalli su Nafi dake tahowa ganin tana kuka ya kalli Aneesa yace ” ki fadama Umma tadaina min haka sannan kema na dauka ko me na kawo gidan nan zakibi bayana in har kina sona, na gode da nunamin din dakikai abinda nake tunani ba haka bane. “yana kainan yai gaba. Nafi tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Aneesa ta maida kanta kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *