AL-AMARIN ZUCI
CHAPTER 1
“Uwani! Uwani!” wata mata ta sa baki sai kira takeyi, matar bazata gaza shekaru arba’in da uku ba a haife, tana zaune cikin madafin da ke cike tirim da hayakin da ya fito a sanadiyyar hada wutar da take ta kokuwar yi da fitinanniyar itacen da aka samo mata wanda ya riga ya jike. Tari takeyi ba kakkautawa, idanunta cike taf da hawaye ta sake daga muryar ta “wai shin Uwani bata gidan nan ne?”
“Na’am Inna” yarinyar ta amsa da sauri hade da ajiye kayan da suke hannun ta tana nadewa, akan gadon bonon ta, da gudu ta fita daga dakin nata, ta nufi Innar ta tana haki.
“kiyi hakuri Inna, yanzu zan wuce” ta fada idanuwanta a cike taf da hawaye. Dan karamin dakinta ta koma, ta dau mayafi sannan ta wuce gidan kakannin ta. Gidan da ya zamewa Uwani tamkar gidan su.
A hanyarta ta tafiya ce ta karewa yanayin kauyen nasu kallo. Duk da kauyen su wani karamin kauyene a inda ba a san da shi ba, shine kawai inda ta sani kuma take so har cikin ranta. Ba abin da ta fi so irin yanayin sanyin garin, koren ganyayyaki, ihun yara suna wasa. Ba abin da baya burge ta a dan karamin kauyen nasu, amma sai gashi yanzu a cikin kankanin lokaci zata bar shi ta bar komai a baya.
“Assalamu alaikum” ta fada a sanyaye.
Mama ta fito kenan daga bayi da buta rike a hannun ta lokacin da ta ga jikarta tan.
Story continues below
“wa alaikumussalam, sannu da zuwa, lale” Mama ta fada hannun ta rike da habar ta cikin mamaki “ina kika fito da sassafen nan? na san innar ki ce ta turo ki ko?”
Uwani ta rike habar mayafin ta tana wasa dashi fuskar nan a turbune, “ba inna bace ta turo ni wai na muku bankwana, kafin motar daukata ta iso?”
Mama tayi murmushi “to kuma shine ranki duk yabi ya baci haka?” Tsohuwar ta mika mata hannun ta alamar tazo kusa da ita.
“Mama, ko karyawa fa bata bari nayi ba, ban san me yasa take daukin taga ta rabu dani ba zuwa rayuwar da ban san yanda take ba.”
Mama ta kare mata kallo ba tare da tace komai ba sai can tace “me ya sa zaki ce tafiyar da bata da amfani a gareki, Allah ne kawai ya san abun da yafi alkhairi a gareki, saboda haka shi zamu ci gaba da roko alherin Sa a garemu. “
“Shiga ciki zaki samu danwake a roba, yafendon ki Mairo shi ta dafa”
Uwani kam barin su tayi suka zubo, bata tare nata hawayen ba. Yaya ma za ayi ace ta manta abun da Innar ta ta fuskanta a dalilin ta? yanda ta tsaya tsayin daka ta kare mata mutumcin ta. Dalilai da dama da fushi da yarinta suka hanata gani a da, yanzu ya zama lallai ta yi yanda Innarta ta umurce ta.
Wajajen karfe sha daya na safe ta shiga bangaren kawunta wanda yake gida daya ne da su Mama can ma ta musu sallama, da zuciya mai radadi da nauyi ta bar gidan, a kullum zata kasance mai kewar lokacin da ta debe a wannan gida mai dimbin tarihi, oh yanda ta rinka yiwa Mama fitsarin kwance da take karama, da yanda ita da su Falmata suke satan gyadar Mairo idan bata nan . Bata jira kawun nata da Baba suka dawo ba saboda sun riga sun wuce kasuwar dabbobi bazasu dawo ba sai bayan Almuru.
Tana barin gidan Mama rafin kukanta ta tafi ta masa kallon karshe, nan ne wurin kebewarta da Falmata suyi ta labarai iri iri na rayuwa, suyi kuka idan abun bakin ciki ya same su su kuma dara su sha iskar damina idan suna cikin nishadi.
Story continues below
“ni na zaci an wuce nan, haba ina ‘yata mai kwazo da himma da juriya? ki goge hawayen nan haka”
“Baba, me yasa Inna zata tura ni? me yasa ta bar sona kaman da?”
Malam Habu ya gyara zaman shi ya fuskanci Uwani. “Uwani, na san ke yarinya ce mai tarbiyya da natsuwa, sannan ina da tabbacin cewa kin san yanda mahaifiyar ku take ji game dake. Gidan nan da zaki je, da ‘yan uwanki zaki zauna, Allah ya kaddara rayuwa daban-daban zaku samu ke kin girma a kauye su kuma a birni.” malam Habu da ya tabbatar ya samu hankalin ta sai ya ci gaba, “yanzu, akwai dalilin da ya sa Innar ki yanke wannan hukuncin, ina son kisan cewa addu’o’in mu na tare da ke kuma addu’a bata faduwa kasa, na san idan kinje zaki fahimci wannan dalilin da yasa inna take son ki tafi. Allah ya miki albarka.”
“Na gane Baba, na gode. Allah ya bar mana kai domin kaine ginshikin rayuwar mu.”
“Yauwa Uwata ko ke fa? yanzu ki gama shiryawa ki zo ki wuce kar kuyi dare, kin san ban cika son tafiyar dare ba.”
Uwani ta sabi akwatin gwangwaronta, tana kokawar daurawa a kanta, malam Habu ya karba mata “Je ki samu Innar ki tana daki”. Uwani tayi murmushi sannan ta bar dakin zuwa na innarta. Ta same ta sai faman ninke kaya takeyi. Ko da taji shigowar ta bai sa ta bari ba saboda tana tsoron kar ta kasa jure rabuwa da ‘yar ta. Uwani dai tana kula da Innar ta, don kuwa dakin tsab yake, saboda wataran ita har tsabtar innar tata na damunta, don haka ta san kawai ta damu da batun tafiyar tata ne. to idan bata so na tafi me ya sa zata tura ni? kai tambayoyin nan sun isa haka, wannan zai iya kasancewa karo na karshe da zata hadu da innar ta a cikin lokaci mai tsawo, bazata kuma yi amfani da lokacin wurin tambayoyin da basu da amfani ba. Da gudu ta karasa ta rungume innarta “na san zakiyi kewata, nima haka zan yi kewar ki da Muhammad, Suhail da kuma Amina. Don Allah inna kina shan maganin ki kan lokaci, sannan kar abar Amina da Suhail su rinka bin su Madu, suyi karatu sosai saboda su samu ci gaba a rayuwa. Bana so su bar karatun su a rabin hanya kaman yanda na…” nan da nan tayi shiru domin toshe wannan madacin da ya taso mata a duk lokacin da ta tuna wannan bangare na rayuwar ta. Wannan wani bangare ne wanda da akwai yanda za ayi ta manta dashi kwata-kwata da ta manta.
Direban yana jiran ta a mota, inna ta tanada masa abinci da sha irin na mutanen karkara sai da yayi kat.
Suna tafe ta tuno maganar da Baban ta ya fada mata “kar ki damu da Inna, ina nan zan kula miki da ita da kannen ki, kiyi karatu sosai sannan ki dage da addu’a, idan mun samu dama zamu zo mu ganki kin ji?” Uwani kuka kawai ta sa mai tsuma rai don ita dai kawai ta san ya fada ne me zai sa wani yazo gidan mutumin da ko fadin sunan sa an haramta a zur’ar su?
Ta riga tayi zurfi a tunani kaman daga sama taji direban yace “yarinya, ki bar kukan haka kar kiyi rashin lafiya, zaki saba a hankali, kinga nima daga kauyen na zo gashi har na saba.” A hankali ta daga idanuwan ta da sukayi luhuluhu don kuka.
“Sunana Mallam Sule” mutumin nan ya fada
“Ni suna na Aneesa amma kowa Uwani yake kirana”
“Malam sule yayi murmushi yace “Ah ashe babban suna ke gareki, to ai da karfin hali aka san manyan mutane. Ina tabbatar miki zaki ji dadin zaman ki a can a hankali.”
Uwani dai murmushi tayi kawai tana dariyar rashin sanin Malam sule domin da ya san irin shaquwarta da innarta da bai fadi haka ba.
Bata san iya tafiyar da suka yi ba akan titi, saboda tayi zurfi a tunani wani lokacin har gyangyadi ya dan sace ta, idan ta bude idanu sai ta gansu a wani gari.
A karo na karshe da ta bude idanunta ya faru ne saboda wani irin kara da ta ji na karfe a kan karfe, a birkice ta zauna tana kifkifta idanu saboda razana.
Uwani ta wulwulo daga motar har ta kusa faduwa amma tayi saurin damkar kofar saboda kar ta karasa kasa. Wata mata akalla tafi innarta sosai a shekare mai mulmulallen jiki ta tunkare ta, tana zaton dai ita ce Baba saratu, saboda haka tayi maza ta durkusa don kwasar gaisuwa a wajen dattijuwar. “ina wuni?” Baba saratu da sauri ta tare ta sannan ta dago ta “lafiya kalau, ‘yar nan kun sha hanya. Yaya hanya dai?” uwani cikin in-ina tace “l…lafiya”
“Don Allah tashi, kar kina durkusawa idan zaki gaisheni kinji ko?” Uwani tayi saurin girgiza kai alamar ‘eh’.
“Yawwa, ko ke fa? Yanzu mu shiga ciki ki huta ko?” daga wannan lokacin Uwani taji tasu zata zo daya da Baba Saratu.
Baba saratu tayi ta tafiya dasu a kan wani dan dandamali, wanda ya bude zuwa wani katon fili a gefen gidan, a nan ne Uwani taga wasu tsuntsaye masu kyau da ban sha’awa suna fidda sautin waka mai dadi, nan da nan taji tana son su. Komai na wannan gida ya dauke hankalin Uwani matuka, haba shiyasa Falmata tace birni abun tsorone. dazu-dazun nan ji tayi an tsane ta ne da aka turo ta yanzu kuwa har abun cikin sa sun fara burge ta. Hannun ta ya hau bari bakin ta na kakkarwa , yaya za ayi ta saba da duk wadannan abubuwan, anya Malam sule ba zolayanta kuwa yake yi ba da yace zata saba, kai ta fara tantaman hakan.
“Likita, yaya jikin nasa?” doctor Ahmad ya kama hannun Sagir da ya miko masa don su gaisa
“Alhamdulillah, yanzu ya fita daga hatsari sai dai yana bukatar hutu”
Sagir ya saki numfashin da bai san yana rike dashi ba. “Zamu iya ganin shi yanzu?”
“Eh zaku iya shiga, sai dai ku shiga da daddaya, saboda yanzu baya bukatar wata hayaniya.”
Story continues below
Sagir ya dubi bayan shi inda ‘yan gidan su suke tare “Hajiya, ki shiga ki duba shi, likitan yace da daddaya za a shiga” Itama ta girgiza, Sagir ya lura da hakan, Hajiya tana daya daga cikin tsayayyun matan da ya sani masu karfin hali, shi shaida ne ga hakan. Ta rasa yaran ta biyu a take sannan bata karaya ba, ta bar aikin ta don ta kula da iyalanta sannan ta kasance a gefen mahaifinsu lokacin da yake fama da siyasa. Kowa na mata kallon mace mai kamar maza, sai dai karkashin wannan karfin hali da tsayuwar dakan tata akwai mace mai rauni da take bukatar tattali da kulawa da kuma soyayya.
Rashin lafiyar mahaifin su yasa nan da nan ta fahimci cewa zata iya rasa soyayya da kulawar na kusa da ita a ko wani lokaci. Sagir bai taba ganin birkicewar ta ba irin ta yau. Ya gagara rarrashin kansa, yana tsaye a dakin jira, yana tunanin wani labari likita zai zo musu dashi, bayan an natsa.
“Yaya Sagir ka shiga Hajiya ta fito” muryar kanwar sa yaji ya fito dashi daga wannan dogon tunani, murmushi ya musu. Hamdiyya yanzu ta gama jami’a tana aure a Kaduna labarin Abba ya samesu cikin dare hakan yasa suka doka sammako suka taho, Kamal kuwa yana digirin sa na biyu a fannin sanin hikimar doka (law), Aisha autar su kuwa tana aji daya a jami’a.
“Aisha shiga ki gaida Abba, amma ki goge wadannan hawayen tukunna.” ya fada a tsaurare.
“To, Yaya Sagir” sai da ta goge ta shiga.
“Yanzu na samu labari, yaya jikin nasa?” Aadil ya fada yana duban Sagir. Yayinda Sagir ya shafo sumar shi da hannun sa daya, “yanzu kam da sauki, Alhamdulilah. Watakila su koma gida gobe. Ban son shiga da fitan mutanen nan yayi yawa, sannan kuma shima yafi son ya ci gaba da karban magani a gida.”
“To Allah ya kara sauki.”
Da karfi ihu da kururuwan ya cika gidan, ba shiri duk mahalukin dake gidan ya hallara domin ganin me ya haddasa wannan kururuwa. wasu na tuntube suka isa, sai da waje ya lafa Baba Saratu tace “Menene? ina macijin yake?”
Story continues below
Hajiya Juwairiya ta juyo ta dube ta cikin mamaki “Maciji!”
“eh, hajiya mun ji ihun ki mun zaci kumurci kika gani.”
Hajiya ta kare musu kallo gaba daya sannan tace “Na rasa me nakeyi har yanzu da dolaye irin ku, babu wani maciji”
“To hajiya me ya saki ihu?” Baba saratu ta tambaya ba tare da ta tankawa ce musu dolaye da akayi ba.
Ai da ganin shi duk suka zare jiki suka watse daga wurin, ta juyo ta musu mummunar kallo ne itama ta ganshi. Alhaji Mahmoud ya shigo bangaren ne bayan jiyo hayaniyar da yayi daga isowar shi gida. Bin sa tayi zuwa falon shi na cikin gida, ba tare da yace qala ba.
Hajiya Juwairiya mace ce mai shekaru arba’in a duniya, uwar ‘yanmata uku sannan itace mace ta biyu da Alhaji Mahmoud ya aura, duk da kasancewarta ‘yar gaban goshi a wajen mijinta, yana tare mata komai na rayuwa amma bai hanata, tilasta masa ware mata nata kason ba domin itama taci karenta ba babbaka, hakan yasa ya bude mata shago a kasuwar Garki ya kuma shake mata shi da kaya. A kullum tana daukar kanta wanda ake damawa dasu a babban birnin tarayya, don ita kawayenta ma daga matan ministoci sai matan ‘yan majalisan dattawa.
Uwani ko da take zaune rungume da bango ba abun da takeyi in banda aikin sharban kuka, fatan ta daya bangon ya tsage ta shiga ko zata huta, tunda ta gane akanta da akwatin ta ake wannan mujadalar sai ta kara tantamar maganar malam Sule, yanzu gashi yan kayanta ma an zubar mata dasu. Tana kukan ne taji hannu a kafadarta “tashi ki shigo na kaiki daki.” Baba Saratu ta fada tana dagota daga durkuson datayi.
“Wannan shine dakin ki yanzu, zan samo miki abun da zaki ci, ki saki jikin ki kinji?” Baba saratu zata fita ne Uwani tace “Ina son na zaga ko zaki nuna min inda zanje?”
“Ba damuwa, kinga wannan kofar nan ne bandakin ki, da dakin wanka a hade.” nan Baba saratu ta shiga gwada mata yanda zata yi amfani da bandakin da yanda zatayi idan ta gama amfani dashi. Tirkashi! yanzu kam ta fasa wancan rantsuwar da tace bata taba ganin abun da ya kai dakin ta kyau ba, wannan bayin ya taka dakin ya shanye a kyau, tunda abu kaman ta kwanta a ciki ga dan karen kamshi. Yanzu wai duk wannan da gaske ne? Birni abun tsoro ne, abu daya da yake sa ta girgiza shine idan ta tuno da muguwar matar dazu da ta zubar mata da kaya, yaya zata zauna lafiya a gidan da matar gidan bata son ta zauna? ina ma ace Baba Saratu ce matar gidan.
A hankali bacci barawo ya sace ta, ba tare da ta samu amsoshin tambayoyin da suke cike fal a zuciyarta ba. Tayi mafarkin sabon gari, kofofi masu kara, da mata mai ihu, daren wani dogon dare ne a gareta, kafin kiran fari ta farka. Da Baba Saratu ta shigo ta samu har tayi wanka ta gayara gado.
“oh ni saratu! wace irin yarinya ce ke? yaran gidan nan basu aikin komai, bare su gyara gadon su”
Uwani ta kalle ta wani iri “Ni fa ba ‘yar gidan nan bace, ni bakuwa ce. Sannan nayi ta neman tsintsiya ban samu ba”
Story continues below
Baba Saratu batayi mamaki ba saboda daga ganin wannan ta san ita daban ce. “me zai hana ki zo muje kicin ki tayani hada kalaci?”
Uwani ta zare manya-manyan idanun ta “da gaske? to amma ina matar jiyan nan kar ta min fada fa?”
“kar ki damu zata sauko, kawai ki dauke ta a maytsayin uwa”
Baba saratu ta bude kofa Uwani na biye da ita a baya.
***** ********** ********
“krrr! Krrr!” agogon kan tebur da ke gefen gadon ta ya buga sau uku kafin ta tashi a birkice fuskar ta duk nauyin bacci. bata samu kyakkyawan bacci ba duk tsawon daren jiya, banda juyi ba abun da ta kwanayi sai tuno abun da ya faru jiyan take tayi, bayan Alhaji Mahmoud ya zauna a kujerar falon sa ya dubeta da tsananin bacin rai wanda bata taba ganin irin sa ba na tsawon shekaru.
“Juwairiyya, ban taba tsammanin hakan daga gareki ba, bazan lamunci abun da kikayi yanzu ba, ki kula da takunki, tun kan ki wuce iyakarki” Yana fadan haka ya mike ya bar mata falon duk sun san me yake nufi da furucin sa, yaya hakan zai faru da ita?
Tsaki tayi ta ture mayafin ta sanna ta sauko a kan gadon domin ta shirya.
“me kuma yau suka samu suke ta keta dariya kaman an basu kujerar makka?” Hajiya Juwairiyya ta fada a ranta, tana shiga kicin din kowa yayi tsit, duk suka hau kwasar gaisuwa.
“me kuka samu da sassafen nan da zai sa ku zauna ku taru haka kaman ‘yan kwuikwiyo?” a nan ne suka hada ido. idanun Hajiya Juwairiyya cike da kyama da tsana, yayin da na Uwani suke cike da tsoro da fargaba.
“to hajiya”
Uwani ta bi baba Saratu yayin da kowa ya kama gaban sshi yaci gaba da aikin sa. ita kuwa uwani saura kiris ta saki fitsari tsabar tsoro. Ba abin da tafi so illa ta koma kyauyen su wurin Innarta, ko ba komai ba wanda ya taba ce mata tana wari bare yayi yunkurin amai don tana wurin.
“kin kwace dakin ‘yar uwata” yarinyar ta fada
“um… kiyi hakuri don Allah, wallahi nima nan aka ce na shigo da na zo ban san dakin ta bane, bari na fita na koma gun Baba Saratu, ni daman dakin yana ban tsoro” uwani ta fada a daburce.
“A’a, kar ki damu. Da ma na kawo miki wasu kaya ne ki sa kafin ki sayi wasu. Jiya mummy ta sa an fitar da akwatin ki” ta danyi shiru kafin tace “kiyi hakuri, amma kin san meye? gwamma da ta wurgar kin ga Daddy na sai ya saya miki sabbi, idan akwai abun da kike so ki fada min”
Uwani ta tsaya sototo tana kallon ta har ta kasa cewa komai, da kyar tace “na gode…”
Story continues below
“Sunana na asali Aneesa ne amma kowa Uwani yake ce min”
“To ai sunan kin yafi dadi, ni dai da sunanki zan na kiranki daga yau kin yarda?”
Uwani daga mata kai kawai tayi. “zauna na gyara miki kanki yana ta diga”
“Yaya kika bar kanki yayi karfi haka, gashi kina da gashi mai yawan gaske, kula yake bukata akai akai”
Khazeena ta sake sa dariya tace “to na tambaye ki yanda kike kula da kan naki?”
“yuck! man shanu? ai zai yi wari sosai.”
Khazeena ta shiga shafa mata wasu mayuka masu kamshi a kanta
“wani irin shampoo kike amfani da shi?”
Uwani tace a ranta a yi mata wani gyara kuma bayan yanda take jin ta fes a yau din nan.
Daga wannan lokacin dai kawance ya fara kulluwa a tsakanin Uwani da khazeena, au ashe Khazeena tace Uwani ta koma Aneesa daga yau.
Da misalin karfe goma na safiyar ranar ne mutumin da Aneesa ta baro iyaye da kakanni domin shi ya nemi ganin ta a wurin cin abincin su dake babban falon shi. Tana saka kafafu a cikin dakin takara ganin wata duniya mai ban al-ajabi, wai! idan ta koma Inna zata sha labari a ran ta take wannan tunanin. Idanun su na haduwa Uwani ta dawo taitayin ta, sai da taji wani abu yayi tsalle a cikin cikin ta lalle matar nan abun tsoroce, ba shiri ta zame ta zauna a kasa nan da nan kuwa taji dariyar ‘yan matan da ta riga ta samu a dakin cin abincin. Aneesa ta rufe idanun ta tana tunanin ina ma zata bace bat ta ganta a dakin Innar ta.
“Sameeha!” wani murya dakekke ya fada, nan da nan dakin yayi tsit.
Aneesa ta bude idanuwanta a hankali taga ‘yan mata biyu, daya kusan sa’arta daya kuma Aneesa ta fita, duk suna kallon ta cikin fushi banda sabuwar kawarta Khazeena kuma karamar su.
“Aneesa, tashi ki samu kujera kema ki zauna ko? Ki saki jikin ki, nan ma gida ne, ‘yan uwanki ne. Daga yau kuma tare nake son mu rinka zama muna cin abinci” ta kalli mutumin da wai shine mahaifinta na ainihi wanda har yau ta gagara yadda da hakan. Nan take taji wani abu a cikin ranta shin tsoro ne ko kuwa fushi?
Daga baya Aneesa ta kebe a dakinta tana tunanin yanda zamanta a wannan gidan zai kasance, ga kuma gaggarumin banbancin da ke tsakanin rayuwar birni da na kauye. “yaya zanyi wannan rayuwa? Sameeha tana fushi dani don na kwace mata daki, Zaheeda ko magana bata min, mummyn su kuwa bata ki ta sare min kai na ta raba shi da gangan jikina ba. Yaya zan samu rayuwa a cikin wannan duniya mai ban tsoro?”. Sunci abincin su yayin da ita kam Allah ya gani wasa tayi-tayi da nata farantin don bata saba cin irin wannan ba.
Story continues below
Daddy yace “ku wannan abun naku baya karewa ne? Yaushe na baku kudin kuka zuba a wayar ku?”
“daddy, ya dade fa.” ta fada a shagwabe. A take ya zaro dubu goma ya bata yace tasa a wayar ta. Sauran ma dubu biyar-biyar ya basu. Aneesa dai ta kula ba abun da ya fi burge su irin raba kudin da daddyn yayi, don kowacce na damkar tata ta tashi tayi gaba. Wai shin basu kula da dimbin son da mahaifinsu yake nuna musu ba? Ta kula yana musu haka ne don yaga ya sanya su farin ciki, ita kuwa ba abun da take nema a rayuwarta irin soyyayyar mahaifi da tayi rashinsa har ya zamto yana mata ciwo idan ta gwada koda mafarkin samun hakan ne. Har sai da malam Habu ya shigo rayuwarsu.
“Tashi kije da yamma idan Allah ya kaimu sai kuje kasuwar da mummyn ku.”
“to, na gode. Allah ya amfana ya dada rufa asiri”
Hajiya Juwairiya ta tabe baki a ranta tace kaji min ‘ya da kinibibi naga uwarki ma tayi bata share ba.
******** ******** **********
Tunda Abba ya nemi ganin shi jikinsa ya bashi da wata a kasa, don dai duk wayewar gari idan ba dai ba ya kasar ba to sai ya je ya gaida iyayensa ko ya kira su a waya. Tunda har Abba bai jira zuwan shi da safe ba, dole haka ya jingine abubuwan da suke gaban shi ya nufi Main house dake Asokoro. Mai gadi ne ya bude katon kofar karfen da ya dangana shi da harabar gidan, ya shiga yana waya, sai da ya karasa ya sa wayoyin a silent, sannan ya sauko, duk ma’aikatan gidan suka zo suka kwashi gaisuwa. Ya amsa musu fuska a sake. Sannan ya shiga, sashin Hajiya Khadija ya fara shiga tukun.
“yanzu ko Aisha take ce min taji kaman muryar ka nace ai ka shigo da safe zai yi wuya idan kaine”.
Sagir ya danyi murmushi ya samu gefen kafan Hajiya ya zauna, don shi kam duk inda Hajiyar sa take zaune nan yake zama tukun sannan su gaisa ko suyi duk shawarar da zasuyi wasu lokutan kam har kwanciya yanayi a kan kafafun ta, ta shafa masa kan shi tana masa addu’o’i, ko kuwa suyi wata hirar daban. Da farko tana janye shi a jiki wai don shi dan fari, ya nuna mata idan zata masa haka to ba ruwanshi da ita shima tun yana karami suke haka, har dai ta saba ko a ina Sagir yana kusa da ita.
“Hajiya kun wuni lafiya?”
“lafiya kalau, Alhamdulillah. Sai dai kai din kana lafiya kam?”
“kalau, Hajiyata. Abba ne ya nemi ganina shi yasa na dawo”
Aisha ta shigo da plate din kayan marmari a hannunta da kuma ruwa marar sanyi sosai ta ajiye a gefen shi sannan suka gaisa.
“Ke wannan kina zuwa makarantar ma kuwa?”
Aisha tana murmushi tace “ina zuwa Yaya.”
“ki dai sa himma kin san gidannan kaf ba dolo, kar ki zama zakka”
“Hajiya kin ji shi ko?” Hajiya Khadija tayi murmushi taci gaba da wuridin ta. Sai da ta kare tace “kun fi kusa. ka karasa gun Abban naku nima yanzu zan zo na bashi abinci.”
“Yaya kana ganin Hajiya da Abba wai har Abba ne sai taje ta bashi abinci.”
Sagir ya dake kaman ba shi bane ya gama zolayar ta. “Hajiyar sa’ar ki ce? duk kun bar al’adun da matan da sukeyi, da kuna ririta mazajen ku ai da kunji dadi duniya da lahira”
“Kayii hakuri, to amma Yaya ni banyi aure ba”
“Hajiya kina jin shi ko? bayan shima na san Abba kiran da ya masa bai wuci na auren ba”
Hajiya tayi murmushi bata cika sa baki ba a magana indai ta shafi Sagir ne, saboda yana da wani matsayi a ranta da ita kadai ta san shi.
Story continues below
“idan yaji ki ko kin san bazaku shirya ba.”
A falo ya samu Abban, bayan sun gaisa ne yace “Sagir, ina so ka sauraren da kyau” Sagir ya lankwasa kafar sa ya tattara dukka tunanin shi ga Abban nasa, ya san koma meye ne yana da matuqar muhimmanci, domin yanda abokai suke da juna haka tsankanin sa da mahaifinsa, ba boye-boye tsakanin su. Hakan yasa tunda ya kira shi falon shi yasan maganar ta girmama.
“Kaman yanda na fada maka, lokaci baya tare da ni ko kai, duk abun da zamuyi a rayuwar nan muna sawa a ranmu cewa wataran zamu bar duniyar nan, akwai wasu abubuwan da idan da hali kuma ina son ganin su kafin lokacin barina yayi.” Sagir ya kifta idanu yana tunanin ba wannan maganar ba kuma!
Sagir yace “naji Abba”
Sagir yaji mamaki kwarai amma kasancewar sa asalin dan kasuwa da ya iya boye abun da ke cikin sa bai bari ya nuna a fuskar sa ba. “na san zaka ji mamaki amma nayi abun da na ga ya dace ne, amma ace mutum kamar ka, kamfanonin ka nawa a kasar nan banda wajen kasar ma? Amma baka da lokacin nemawa ‘ya’yanka uwa ta gari? ga kannen ka har sun taso. Kana ganin dai Azhaan dan wurin marigayi Usman har ya shekara Uku, amma kai baka ma ajiye iyalin ba bare tara zuri’a. Ko shikenan daga kanku sunan mu sai ya kare baza a ci gaba da yada al’umman manzo S.A.W ba? kaje kayi tunani”
“Naji Abba Allah ya shige mana gaba.”
“Sai dai yace a bata wata shida saboda ‘yan wasu dalilai, idan lokaci ya cika sai ka shirya kaje ku daidaita”
“Allah ya nuna mana lafiya”
“Ameen.”
Sallamar Hajiya Khadija ce ta katse musu hirar tattalin arzikin kasa da suka koma yi.
“Ai yanzu kam, hirar ta isa haka sai kunci abinci kuma ko?”
“kaji Hajiyarka wai tsakanin mu take so ta shiga, ke dai idan zaki zubo ki zauna ayi hirar da ke to.”
Sagir yayi murmushi yace “Abba Bismillah, ina da tattaunawa da wasu ‘yan chaina munyi dasu 8.30 zasu sameni”
“to Allah ya bada sa’a kinji wai ki rike tuwon ki shima ya kusa samo mai dafa masa”
Hajiya Khadija tayi dan murmushi mai gidan ta dai baya tsufa da barkwance. Nan ya musu sai da safe sannan ya wuce. Shi yanzu bai san wani jagwal din kuma za a hada masa ba, yana zaman-zaman shi don dai Abba ne ya kawo shawarar ba yanda ya iya. Wai ma me yasa zai bata lokacin sa, kafin wata shida an canza wata shawarar ai. Allah dai ya kai rai lafiya.
Washegari da safe ya nemi Aadil akan ya same shi a gida. Aadil yayi mamakin hakan don dai yau laraba ya kamata yana office. Sai dai bayan jin abun da yake damun abokin nasa yasan me ya hana shi fita. Don a duniya Sagir zai iya yaki da kowa da komai ya cimma nasara a harkar kasuwa da juya kudade amma idan an zo bangaren mace nan tsiyar take.
“To yanzu naji matsalar ka, me yasa baka fadawa Abba akan abun bazai yiwu ba?”
“Kai ma da na fada maka kaga irin kallon da kake min ne da zaka ce na fadawa Abba?”
“Meye abin yi?”
Story continues below
“Ina so, idan lokacin yayi ka tuna min kawai.”
Aadil ya bishi da idanu “meye kake kallona kaman na canza launi? yaya maganar mu ta jiya ne, ka tura wa Al-Qasim bayanan rahoton?”
“eh na tura masa.” shi dai mamaki yakeyi irin yanda lokaci daya Sagir zai iya canza yanayin shi, ka kasa sanin halin da yake ciki.
“jiya mun tsaida maganar nan da su Chi Wung, saboda haka ana dab da fara kwangilar in sha Allah.”
“Alhamdulillah, Allah ya bamu sa’a, kafin nan kai ma kayi ta yin istikhara Allah ya maka zabi akan maganar Abban”
shiru Sagir yayi kawai ya sako hannayen shi duka biyu ya shafo sumar shi.
“na gode Aadil sai na fito”
“oh, daman zaka fito office?”
“Babu abun da zai hana Sagir Daggash yin abun da ya saba, in dai da rai da Lafiya”
Aadil ya dauki makullin motarsa ya wuce Office.
Abun mamaki yana fadawa Aadil matsalar shi sai yaji sauki a ran sa don haka, sallar waduha yayi sannan ya karasa shirin sa cikin business suit din HUGO BOSS.
******* ****** ******
“ki sa kadan, kadan fa ya isa rike min da kyau.” Aneesa tace
“Yau naga ikon ALlah, haka akeyi?” Khazeena ta takarkare duka karfinta ta damka
“Na gidannan da yawa shi yasa”
“Kina ga bazamu kara fulawa ba? ko dai mu kira Baba Saratu?” Khazeena ta fada tana rarraba idanuwa.
muryar Baba Saratu sukaji a bayan su “yanzu don Allah me kukeyi? sai Hajiya ta zo ta same ku a nan ko?”
“Baba Saratu, dan wake muke kwabawa, ina koyawa Khazeena ne, kin san tace dukkan su basu iya girki ba? nace to da anyi auren su yaya zasuyi? mu a kauyen mu abun kunya ne kikai aure baki iya aikin gida ba shi yasa nake koya mata”
“Baba Saratu kinga yau har danwake mun kwaba. mummy sai tace zamu kone idan mun shiga kicin mu bari a yi daga baya ma koya”
“To ya isa haka nan, kun kwaba kun janyo min aikin jifa danwake ai, ke Uwani wa yace miki kowa ke cin danwake a gidannan”
Aneesa tace “mu sai muci kayan mu, Malam sule yace min yana ci kema kuma ranar naga kinyi ke da Hannatu”
“Aneesa, daddy da zaheeda ma suna ci, mummy da Sameeha ne kawai basu ci”
Haka dai akayi ta kititr kitir kafin kace meye, Aneesa da Baba saratu sun jefa danwake, sai sukayiwa mummy da Sameeha nasu abincin. Khazeena ko ba wanda ya kaita murna yau tayi abun kai.
Bayan sun gama ne suka je suka watsa ruwa kafin lokacin cin abinci yayi. Ana tsakiyar cin abinci Khazeena ta dubi Daddy tace “yau fa daddy dani da Aneesa mukayi maka abincin rana”
“Kai haba? ashe dai ke din babbar maigirki (chef) ce ban sani ba. Amma dai na san Aneesa ce ta kwaba ba ke ba ko?”
nan da nan ta hada rai tace “na taya ta fa rike roban kuma ni na dafa kwan salad din ma” Mummy kuwa tunda taji da Aneesa akayi girkin sai ta zare hannu a nata abincin wai ta koshi. Alhaji Mahmoud bai kula ta ba, ya ci gaba da hira da yaran sa. A hankali ya kula da Aneesa, yarinya ce mai alkunya da girmama na gaba da ita, komanta tamkar mahaifiyarta hatta yanayin su ma iri daya ne, wani lokacin idan tayi magana sai ya zaci ko Halima zai juya ya gani, haka dai yake isti’aza shi yasa bai cika son dadewa yana hira da su ba sai yace su shiga ciki, saboda yawan tunani da hakan ke haddasa masa wanda banda tsantsan alhini ba abunda hakan ke sa shi.
Story continues below
“Daddy, mun karasa sayayyar Aneesa ma, ka san yanda take son karatu? mummy tace daga kauye tazo amma ta iya turanci fa, sai dai bata iya fadan wasu abubuwan ba amma ina gwada mata idan mun dawo school.”
Daddy yaji dadi a ransa, ya san Halima ko za ayi yaya bazata bar jinin sa ya wulakanta ba, duk da kuwa shi ya wulakanta ta.
“Haka yana da kyau ai Khazeena, ki taimakawa wanda yake bukatar taimako sai kiga Allah ne kawai zai biya ki, wataran tun a duniya zaki fara ganin sakamako.”
“ko daddy? to bari naje su Sameeha zasu je silverbird kallon fim, nima zan bisu”
“To adawo lafiya”.
Sun gama shirinsu tsab, hatta kayan da Aneesa zata sa Khazeena ce ta zaba mata, sun fito suka samu Sameeha da Zaheedan basu iso ba don haka suka tsaya a jikin mota suna jiran su. Aneesa dai hankali da wayon Khazeena ke bata sha’awa yarinyar shekaranta goma sha uku amma tana da sanin ya kamata.
“Sameeha, shine don ke zaki kaimu sai ki ki fitowa da wuri?”
“Ke na tsaya (recieving call) amsa waya ne, shiga mu tafi motar a bude take ai.”
Aneesa ta sa hannu zata bude kofar baya su shiga ita da khazeenan sai Sameeha tace “ke kuma fa ina zaki shiga?” jikin Aneesa yayi sanyi matuka, ita dama ba wai son sabgar Sameeha takeyi ba don kwata-kwata halayyar ta ba burge ta sukeyi ba.
“Haba Sameeha? itama ai zata je kallon fim din ne.” Khazeena ta fada cikin kare Aneesa.
“Wannan dattin ne zamu dauka mu shiga da ita cikin kawayen mu?” abun yayi wa Aneesa zafi don haka sai tace “Khazeena ku je kawai naji kaina yana min ciwo ma”
“Wallahi Sameeha (you are so mean) baki da kirki”
“Yaya za’ayi kima fara cewa na sa wannan abun a mota ta, idan zaki sauka ki bita ne kema to, naga taku tazo daya tun da kin zama ‘yar kanzaginta, mai mata sayayya.”
Khazeena ta fita a motar ta buga marfin kaman siririn hannun ta zai balle.
“Aneesa kiyi hakuri kizo muje Daddy ya bamu kudin Malam Sule ya kai mu”
“ki bari kawai, me zai hana muje na kara miki karatun fiqhun ki, tunda jiya kin kara min english?”
“Meye kike ta kallona kaman baki taba ganin ‘yar kauye ba?”
Sai da tasa khazeena ta dan dara “me yasa su Sameeha suke miki haka?”
“Ba komai, zasu daina, bamu saba bane tukun”
“Amma ai kinyi sati uku fa a gidan nan gashi ni na saba dake, me yasa su basu son ki?” Aneesa tayi shiru tana tunanin ba wannan karon bane ta fuskanci kyamatar da jama’a suke nunawa gareta, amma ba sabo a cikin sa sam.
“Kowa da wanda jinin sa ya shaku, yanzu bakiga ke da Baba Saratu kuna sona ba?”
Dadi ne ya cika ta fal da taji wannan bayanin saboda kullum da kuka take bacci na rashin innarta amma ranar tayi bacci ba kuka.
Kafin Aneesa ta cika wata biyu a gidan ta sace zuciyar kowa, ba abun da yake burge mutane game da ita, irin girmama na gaba da ita da kuma farfar dinta da jama’a. har yau dai Mummy bata bari ta shiga sashin ta, don haka iyakan su idan sun hadu a kitchen ko falon daddy. Da yake ita kicin ne wurin hirar ta, tana koyan girkin zamani gun Paul me girkin Daddy, na gargajiya kuma gun Baba Saratu, da yamma kuma idan su Khazeena sun dawo daga makaranta ta koyi karatu a wajen ta.
“eh ba na magana bane, kin san text na waya ai tunda kince babanki na Kunuwal yana da waya”
“eh yana da ita.”
“to kamar text ne zata turawa, amma a take zai na tafiya amsa yana shigowa sai dai shi ba a cire kudi sosai.”
“oho, haba ashe tana da kawaye da yawa.”
Khazeena kuwa zama daa aneesa yana sata nishadi don bata rabuwa da abun ban daria haka suke xama cikinsu baba saratu suna shan labaran ban daria kala kala na gari bam bam daga wajen masu aiki
“Ni gaskiya bana son wulakanci, yaya za ayi sai zan tafi makaranta sai bazaku ajiye min komai na ba, mummy gaskiya ki kori wannan Hannatun, wai ita meye aikin ta? idan ta gyarawa mutum wuri kullum sai bazata ajiye masa abun sa yanda ya bari ba.” Zaheeda ta fada tana huci tamkar tukunyar da ta tafasa +
“Yi hakuri Zaheeda, ina Hannatun bari na kirata tazo ta duba miki.” Mummy ta fada cikin lallashi.
“Gaskiya mummy ni idan tasake min haka kawai zata koma kauyen su ne,” nan fa aka taso keyar Hannatu wai tazo ta nemi rigar saman uniform din Zaheeda (blazer).
Gaba daya gidan sai da ta tada kowa saboda sababin da takeyi wai ‘yan aikin gidan sun raina ta’. Suna zaune zasu karya ne, Daddy yace “wai meye ne tun da sassafe nake ta jin hayaniya a gidan nan?” nan da nan kowa tayi tsuru da idanu, “ina magana kuna jina?” ganin daddy ya bata rai sai Khazeena tace “Zaheeda ce bata ga uniform dinta ba shine tace sai mummy ta kori hannatu tunda bata ajiye mata kayanta inda ya dace” Harara Zaheeda ta sakar mata ta doki kafarta ta kasan table.
Daddy yace “Haka akayi zaheeda?” bai jira amsarta ba yace “ashe daman maganar da nake fada muku baya zama a kunnen ku ko? na sha fada muku, mutum komin kashin sa yana da daraja, kuma don kina sama da wani ba wai yana nufin ki musguna masa bane, don yau kunga tarin ‘yan aiki a gidan nan saboda ina da ikon daukan su? Watarana idan bani dashi fa wa zai muku komai? Idan kukayi wasa duk sai na sallame su, ku kama ayyukan gidan sai muga ko da dadi. kar na kara jin wani ya sake raina wani dan aiki ko da ma ba na gidan nan bane.”
Jikin ta yayi sanyi amma ranta yayi mummunar baci, don me yasa Khazeena zata fada har Daddy yayi mata fada, duk laifin wannan Aneesan ne tun da ta zo gidan ya daina dadi.
Haka ta figi jiki suka tafi makarantar. Sameeha ko ranar bata da lecture tana gida, don haka ita da Aneesa aka bari, mummy kuma ta tafi shagon ta da yake Garki modern market.
Suna fita Aneesa ta tattare kwanukan kan tebur din, don tun ba yau ba mummy ita take sawa ta kwashe daddy na barin wurin, don haka kafin ma tace ta tattara sai ta kwashe. Ta gama kai kwanukan tana goge kan tebur din ne ta ga wayar Sameeha.
Ta daga zata kai mata kenan, sai sako ya shigo mata. Aneesa tace “yawwa ga chatin nan bari yau kam nagani.” Ta sa hannu yanda taga Sameehan nayi a kan glass din wayar taga sakon ya budu.
6
Babe i’m really missing you, can’t wait to see you. I miss those soft lips…
Aneesa ta karanta sakon ta nanata, ta fahimci komai na sakon to amma me yasa kawarta zatace mata tana kewan bakin ta? Sai ta kara dubawa Hamza ta ga sunan mai sakon. Nan Aneesa ta kara kidimewa. Yau me ya hada Sameeha da namiji da zata rinka wannan maganar dashi? Carab sai kuwa sukaci karo da ita. Sameeha ta tuna ta bar wayarta a falo ta dawo da wuri don ta dauka ta manta bata kulle wayar ba. Kawai sai ga shi taci karo da Aneesa “wai ku a kauyen ku ba ku tafiya a hankali ne? ko da yake naji ance da tumakan ku da mutanen ku duk daya ne.” 9
Ran Aneesa ya baci sosai amma bata nuna mata ba. Wucewanta kawai tayi daki, ba tare da ta bata wayar ba.
Wuni Sameeha tayi tana neman wayar nan. Aneesa bata ce mata komai ba, wayar na dakin Aneesa sai da aka tashi cin abincin dare Aneesa ta fito da wayar ta cire ta a silent, ta ajiye a gefen ta.
STORY CONTINUES BELOW
“Zaheeda sake flashing wayata tun safe fa, ban san missed calls nawa zan samu ba da messages.”
Aneesa tace “menene kike nema?” Kowa ya juyo yana kallon ta cike da mamaki, saboda kullum in za a zauna a watse baza ki taba jin muryarta ba.
“Wayata mana ke baki san komai ba”
“Oh ko shine wannan?” Aneesa ta daga wayar tana jujjuyawa. Sameeha tayi maza ta wafce wayar “A ina kika samu? tun safe nake ta nema.”
“Kin san ‘yan kauye ba komai suka sani ba kina ta cewa BB, ni kuma waya dai na san ko da turanci Handset ake ce mata. shi yasa ban san me kike nema ba” 4
“kin amsa min wayata?” Sameeha ta tambaya cikin fushi.
Daddy yace “Sameeha ba kin samu wayarki ba, sai ki duba ai zaki ga su wa suka kiraki. Aneesa sunan wani kalar Handset ne BB din ai, kema fa ashe baki da waya ko na bawa Mummyn ku ta saya miki taki?”
“A’a Daddy ni kam babu wanda zan kira ko nayi chatting dasu, idan na samu lambar Babana zan baka sai ka kirasu muyi magana da Innata.”
Ita kuwa Sameeha tana karbar wayarta da wuri ta juya ta nufi dakin ta. Ai kuwa nan ta samu kusan rabin sakwannin da Hamza ya turo mata duk an karanta. ta rasa abunyi, “ko da yake ma meye zan damu kai na, wannan bakauyar ma ko karatu ta iya ne, hala danne-danne kawai tayi ta yi. Nan da nan ai ta makala wa wayar tata makulli (password).
Aneesa ko kusan kwana tayi tana tunanin irin lalacewar wannan al’amari, ace yarinya tana gidan su gaban iyayenta amma tana aikata irin wannan abu da saurayi, har suna hira a waya akan abun amma iyayenta basu sani ba? sannan kuma su suke dunkula makudan kudade suke bata ta saka a wayar, ita sai taji kwata-kwata wayar ma bata ran ta.
****** ****** *******
“Mama, ni hankali na sam ba a kwance yake ba, shiru ba labarin yarinyar nan ko a wani hali take ba wanda ya sani, nace Malam Habu ya kira Malam Sule yaji ko lafiya amma sai yace ai da akwai damuwa zasu kira”
“to ke Halima meye naki na daga hankalinki? sai kace ba ‘yar fari ba, kin bi sai wani maganar ta kikeyi”
“Mama ai dole na damu, na zauna a birni na san kuma irin sharrin da ke cikin ta.”
“Ke dai kiyi fatan komai lafiya, yarinya tana gidan babanta, muna zaune a nan sai kiga ta zo dubamu”
“To Allah yasa, na hada Suwaitun nan ma nayi magana da Zainabu, idan ta shigo zata kwasa ta kai mun Gombe.”
“to yayi kyau, Allah ya amfana yasa a mora, ai da ke da dan uwanki ba abun da zamu ce muku sai son barka, ALlah ne kawai zai saka muku da alherin sa.”
“Addu’arku kawai muke bukata.”
sun dan taba hira kafin tace “yara sun kusa tasowa daga makaranta, Malam ma anjima kadan zai dawo, gwamma na kammala aikin nawa”
“To ki gaishe su, jiya ai nan sukayi yammaci, anayi ana taba fadan”
Inna ta mike tana saka takalman ta “hmm, neman dai duk su dameki, bari nayiwa Mairo sallama na wuce.”
“Innar Uwani har tafiya ne?” ai kuwa sai ga Mairo da tsohon cikinta,
“Lah yanzu fa nake cewa bari na miki sallama, ashe kin taso. wannan cikin naki fa sai kina motsa jiki, Allah ya raba lafiya. naga kumburin kafafuwan sun fara sauka”
“Ah, da sauki gobe ma zan kara komawa Mataniti in Allah ya kaimu”
“To, Allah ya kaimu.” Mairo ta raka Innar Uwani bakin zaure sannan ta koma ciki.
Ai kuwa a ranar da yamma Malam Habu ya shigo gida da sauri yabawa Inna waya, wai Uwani ce ta kira daga Abuja.
aukin Dadi Inna zabura tayi ta amshi wayar a hannunshi.
STORY CONTINUES BELOW
“Assalamu Alaikum, Uwani. Kina lafiya?”
Haba Aneesa daga jin muryar Inna sai ta hau tsallen dadi, ta manta ma a gaban su Daddy da mummy take, da wuri ta koma gefen dining tace “Inna ta, lafiyata kalau, kefa? yaya su baba da su muhammadu da Amina? kowa dai lafiya? nayi kewar ku, yaya saka?”
“Lafiyar mu duk kalau, alhamdulillah, yaya wajen mutanen gidan naku?” Inna ta samu bakin gado ta zauna.
“Inna gaskiyar ki birni abun tsorone, kin ga manyan tituna, da manyan tv har kan titi fa? ina karatu da yarinyar gidanmu, yanzu tasa kowa Aneesa yake kirana ba me cemin Uwani, ina koyar girkin zamani a wurin paul… kinsan maza ke musu girki a nan? ga Baba Saratu tana kula da ni…” haka dai hira yaki karewa, aka mikawa kannenta duka suka gaisa, sannan suka ajiye wayar. “kar ki cinye musu katin su” Inna ta fada mata. A take taji tayi da nasanin cewa da tayi bata son waya, da ko karamace irin ta Baba Saratu Daddy ya saya mata, zata rinka jin muryar Innarta kullum kan tayi bacci.
****** ******* ******
“Tabdi, Hajiya duk wannan kayan wai na meye ne, gasu masu kyau kullum idan nace zan dau daya sai ki hana, na rasa me kikeyi da su tirim a wardrobe din ki.”
“ke, sauko daga wurin nan, ajiyar ki ko tawa? wai ni baki da daki ne a gidan nan da zaki zo kina min bincike a nawa dakin?”
Aisha ta turbune fuska “Mutum da dakin maman shi ace bazaiyi yanda yake so ba, don Allah kayan waye ne?”
“ajiyar yayan ku ne”.
Da sauri Aisha ta dirko daga kan kujerar da ta hau “Yaya Sagir din ne yake tara kayan aure, bayan ko maganar auren baya so?”
“Bai ma san ina ajiyewa ba, yaushe za a jira shi? hadawa kawai nakeyi, randa yace ga matar sai a sayi sauran abubuwan.”
“kai Hajiya kina ji da yaya Sagir din nan, ni da na kusa turo miji gida baki ko sayi tsinke na ba sai shi da bayi da niyyar auren.”
Hajiya ta zungure kan Aisha “ke baki da kunya ko? bace min daga daki.”
Tana dariya ta fita ai ko fitar ta ke da wuya sai ga Sagir ya shigo.
“Hajiya wai me yake damun yarinyar nan ne, sai guje-guje takeyi a cikin gida, nace kusa ta fito da miji har yau taki, zan hada ta da duk wanda naga ya dace”
“Ai duk daya ne, idan ka zaba matan ma kayi dai-dai, amma shin kanaga kayi adalci, kana yi mata fada akan abun da kai ka gagara yi? shiru na ba wai yana nufin zaman ka hakan baya damuna bane”
Sagir shiru yayi kamar ruwa yaci shi, tunda har Hajiya ta sa baki a maganar nan to tashi ta same shi, shi basu san meye damuwarsa bane shi yasa. “To hajiya, ai ba a ki ba Allah ya kawo lokaci mafi alheri. Ya kuma zabar da ta gari.”
“Ameen, ameen”
Shiru yayi yana waigawa can yace “ni hajiya yaya yau naji gidan shiru ne, ko Azhaan bai zo weekend bane?”
“Au Azhaan ne, ai wai ana biki can gidan su maman, kuma kowa sai tambayar shi yakeyi don haka sai yayi zaman shi can.”
“Mata dai da biki duk zasu takura yaro, ta ina ma zai samu wurin bacci oho” nan dai Sagir ya shiga fada.
Hajiya tace “yo, uwarsa zata kwanta danta bai kwanta bane, ita tasan yanda zatayi kayan ta ai, kai bada da ba sai sa damuwa a rai kafi kowa iyawa.”
Ya san inda maganar zata je ta zagayo don haka yayi shiru, daga bisani yace “zan duba Abba, daga masallaci ni na wuce in sha Allah, gobe idan Allah ya kaimu tafiyar tawa zuwa Germany tana nan, ni ina ga munyi sallama daga yau kenan. Da safe Hassan zai ajiyeni a airport In sha Allah.”
STORY CONTINUES BELOW
“To, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah yayi albarka kan abunda zakuje yi”
“Ameen, na gode Hajiya. ga wannan ku rike a hannunku, wannan kuma na makarantar Aisha, zan sameta don ta faye kashe kudi.”
Hajiya tayi godiya da addu’a sannan tace “ai nace maka ka sama mata abunyi ka rabu da ita kaki”
“wani sana’a zatayi wannan mai sanyin jikin. Idan ta samu abu mai kyau, sai ta koya, kinga ko da tayi aure zata samu abun yi bazata yawaita samun matsala da mijin ta ba”
“Kai har ka gama tsara mata ma kenan, idan kuma ta gama karatun kuma taga aiki zatayi fa?”
“A to wannan kuma tsakanin ta ne da mijinta, bari naje an kusa kiran sallah”
“To Allah ya kiyaye.”
Ya fito can kofar gida ya samu Abban da Kamaal sukayi alwala sannan suka wuce masallaci.
******** ******* ******
Tana zaune a gefen kejin Huda tsuntsun yana ta rera wakar sa, ita kuwa tana nazarin darasin da sukayi da malamarta ne, don yanzu wata guda kenan da malama take zuwa koya mata karatun darussa biyar a gida. Musamman Daddy ya dauko ta, bayan ya fahimci firamare kawai Aneesa tayi sannan kuma gata da sha’awar karatun. Yakan zauna suyi hira da ita don ya san matsalolin ta. Hakan na kara kwantarwa Aneesa da hankali, tayi nisa a nazarinta kaman daga sama taga Sameeha ta nufi inda take zaune. bata zaci wajen ta zata tsaya ba, sai ta ganta a gabanta. “ina wayata?”
Aneesa ta kalleta sorroo “Wace waya kuma?”
“Don Allah bana son munafurci, ba yau kika fara dauke min waya ba ai, kuma yau ma ta sake bata wa zan tuhuma idan ba ke ba?”
“Ni irin wayar ki bata dameni ba, abun da banda fitina ba abun da take haddasawa? ki dai duba da kyau, ban san me kike fada ba. Don na taba tsintar wayar ki kuma bai baki daman ki ci zarafina ba.”
” Kin dai taho da halin ku na beraye kin kawo mana gida.”
Ta juya ta bar Aneesa a wurin, a take Aneesa taji ta bar jin nishadin karatun. Da dare sai ga Baba Saratu wai mummy na kiranta. jikinta ya fada mata kan meye ne wannan kiran.
Tun zuwanta gidan yanzu watanni biyar kenan amma sai yau ta taba shiga dakin Mummy. “Zauna ke, meyey haka kinzo kin tsayawa mutane a kai kamar wata pol waya. Ko kuwa a kan mutane aka koya miki tsayuwa?”
Aneesa ta samu wuri a bakin kafet din dakin ta zauna kan ta a kasa.
“Gani mummy, ance kina nema na?”
“Eh na kiraki ne kan maganar wayar Sameeha, tun kafin magana taje kunnen Daddy ki fito da ita.”
A take Aneesa taji hawaye sun ciko mata idanu, tun da innarta ta haifeta an kirata abubuwa da dama, amma ba a taba mata shaidar sata ba Allah ma shaida ne.
“Ni fa ban dauka mata wayar ta ba…”
“Ki min shiru, idan ba kina so nasa su Hannatu su bincika dakinki ba, ke ba ‘yar gida ba amma daga zuwanki an zo an addabi jama’a a kanki, daga ke har Halima ba wanda ya isa ya kawo min bacin rai a cikin gida, idan ma abun da aka turo ki kiyi kenan. na gaba yayi gaba. kin saba halinki can a kauye nan kam bazakiyi ki share ba. kudin wayar nan sai ya sayi gidan ku na Kunuwal.”
“Mummy, tsakani da Allah ni ban dauki wayar ta ba, ta duba da kyau, idan ta san zata rinka damuwa akan wayarta idan ya bace ai sai ta ajiye da kyau.”
“Iye, lallaai wuyarki tayi kauri ina magana kina magana? don me bazata damu ba? Tunda ita tasan darajarta ai, yanzu haka ana nemanta baza’a sameta ba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Mummy wallahi hirar banza takeyi da wayar…”
“lalala ji karya wallahi ki min shiru don kin fallasu shine zaki min sharri? Sameeha tayi sauri ta taso ganin asirinta zai tonu.
“ku tashi kuje, da safe zamu karasa maganar.”
Aneesa tana fita daga dakin hawayen da tayi kokarin mayar dasu a dakin mummy suka gagara tsayawa, ita ta dade da sanin sharri bashi da dadi, kuma in sha Allah bazata bari a daura mata abun da ba ita tayi ba, sai dai ta koma kauyen su ita kam yafi mata. “haka kawai an raba mutum da danginsa sannan ni ba dadin nan nake ji ba, tunda na zo banda zagi da hantara ba abun da nake samu a gidan nan. kawai don na dau aniyyar ko me zai faru a nan zan zauna saboda yiwa inna biyayya amma ai da na dade da barmuku gidan ku.” haka ta kwana juyi ko ta fara bacci sai ta tuna.
Da sassafe ta tashi kaman yanda ta saba, bayan tayi sallah, ta je ta tada Khazeena tunda dakin su daya da Zaheeda, tare take tashin su, tun Zaheeda na zaginta har ta daina. Dakinta ta koma ta gyara shi tsab sannan ta shirya, duk tabi ta kagara a gama wannan shari’a ta huta da nauyin zuciya, ita ba abin da take gudu irin zuciyar mutum. Da ikon Allah kuwa, sai Malam sule ya shigo da waya wai yana goge mota da safe ya sameta a kasan kujerar motar. Hankalin Aneesa ya kwanta sosai, duk da kuwa ba wanda ya bata hakuri akan satan da aka daura mata.
****** ********* ************
Ana ta shirye-shiryen kama azumi, kowa na farin ciki da shigowar wata mai albarka, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Alhaji Mahmoud ya zauna da iyalin sa Hajiya Juwairiyya domin tattaunawa kan wata muhimmiyar magana.
“Daddy, yara sunce kana nema na?”
Murmushi yayi sannan yace “hajiya da kanta, yanzu har sai na nemeki zaki leko ki taya ni hira? kwanan nan naga kina kara shanawa, ke tamkar bakya tsoron shigowar azumin ma.”
“Daddy kenan, yanzu a hakan? ina ta fama da sintirin shago ga hidiman gida ina naga jin dadi?”
“Ke dai ki godewa Allah.”
“Kullum gode masa mukeyi ai. Menene wannan abun farin cikin da naga yau bakin ka ya gagara rufuwa?”
“Wato wani abun alkhairi ne ya same mu. Akwai wani maigidana da mukayi zaman mutumci dashi, to kwanaki ba da jumawa ba yazo min da maganar dansa, yana son na bashi ‘yata a kara dankon zumunci.” Nan fa hajiya Juwairiyya ta gyara zamanta, wani maigidane da ba a fadin sunan sa?
“A wancan lokacin na ce ya saurara min zuwa wata shida kafin nan. To yanzu dai lokaci ya cika, kuma mun sake magana dashi jiya-jiyan nan, na takaice miki dai zai turo dan nashi su daidaita gobe idan Allah ya kaimu. Shawarar da nake nema a nan shine, shin kina ga ‘yarki zata amince da wannan hadin, wato bata da kowa ko?” 1
A take kan mummy ya kulle, yaya ma za’ayi daddy ya mata wannan tambayar tunda ya riga da yace ya yarda yaro yazo ya ganta ai magana ta kare.
“Wace ‘yata daya kenan ka san na zama uwar yara” ta fada tana dariya.
Daddy yace “Aneesa nake fada, tunda itace babba”
A take Hajiya taji wani abu ya tokare mata kahon zuci, yanzu ga yaranta uku rak sai a tsallake su, a bada wacce ko kaya bata gama iya sawa ba?
amma dai ta dake “Daddy, ai tunda kace kun kammala magana da shi mahaifin yaro, ai sai yazo idan sun daidaita ai shikenan, tunda dai ba auren dole za ayi wa yarinya ba.”
Alhaji Mahmoud yayi jim, “haka ne kam, ba zancen auren dole, sai dai ni da kaina na san yaran gidan akwai su da kamala shiyasa da ya kawo maganar naji nayi sha’awar hada zuri’a dasu.”
“to, Allah ya bada sa’a. Amma dai ba yanzu bane auren ko?”
To ke banda abunki, Juwairiyya yaushe ma suka daidaita da har zaki dauko maganar aure yanzu, idan ma an bukaci yin hakan ai sai munga inda hankalin yaran ya fuskanta tukun. Aikin gaggawa ai daga shaidan aka san shi”
STORY CONTINUES BELOW
Ta karya wuya sannan tace “ai naga abun ne da zafi-zafi aka dauko maganar.”
Alhaji Mahmoud dai ya fahimci inda mummy ta dosa don haka, bai bata damar ci gaba da maganar ba, yace a kawo masa ruwan zafi zai sha tea.
Hajiya Juwairiyya tunda ta bar falon maigidan banda sintiri ba abun da takeyi a daki ta gagara zaune bare tsaye, yanzu yarinyar nan ta fito daga kauye futuk a zo wai dan maigidan Alhaji za abawa ya aura? maigidan Alhaji ma fa ba abokinsa ba, ina da sakel dole dai ta dau mataki. Da wannan tunani a ranta ta aika a ka kira mata Sameeha.
“Mummy to baki tambaye shi ko dan gidan waye bane?”
Sameeha ta fada hankalinta dubu ya tashi, yanzu yaya ma za ayi ace za a mata aure? sannan tayi yaya da saurayinta bayan sun kulla alkawura da dama? yanzu ashe har a wannan zamanin ana zabawa mutum miji?
“kin san halin Daddy, idan baya son magana yasan yanda yakeyi ya katseta”
“To amma mummy rayuwata ce fa, ni har ga Allah na mayar sai a kauye ake auren hadi”
“To ke idan kina da wanda kike so, ba sai ki fada masa ba magana ta kare. shi dai ya fi so ne yaga ya aurar da ke hankalin sa ya kwanta, tunda kinga kanwar ki ma ta taso kwanan nan zakiji ana maganar auren ta.” mummy ta fada cikin yanayi na lallabi.
Sameeha tayi shiru, tana tunani. Yanzu ta yaya zata fara kawo Hamza tace daddy ya musu aure, na farko ajinsu daya a jami’a, bayi da ko aikin yi, kuma a nashi ganin ma tukun aure ai ba na irinsu bane tukun. Ita kuma shi kadai take so, tabashi soyayyarta da komai nata. Sai dai ta san tana kawo masa maganar to zasuyi kacakaca ne dashi.
“A’a mummy ni bani da tsayayye. Amma gaskiya bana son auren da za a zo ana min gori.”
“Hakuri zakiyi mu lallaba daddy din naku, a hankali sai a san abunyi.”
Sameeha ta kwantar da kanta jikin kafadar mummy tace “to naji mummy”
******* ********* *******
Hankalin Sagir gaba daya ya tashi tunda Abba ya sake masa maganar zuwa ganin yarinyar nan. shi abubuwan da suke gaban shi ma sunyi yawa, bai ma kula da lokacin ya karato ba. Abu daya zaiyi kawai, wayarsa ya daga ya nemi lambar Aadil.
cikin minti biyu sai ga Aadil ya shigo office din Sagir. “Sagir lafiya dai yaya na ganka wani iri?”
“Ka bari kawai, Abba ne ya sa min tension kan wancan maganar”
Aadil yaja kujera mai juyawa daya na zaman baki ya zauna akai
“na zaci ai an wuce nan akan maganar, har yanzu dai waccar matsalar ce?”
Aadil ya tambaya yayin da ya dauki kofin ruwan sanyi.
“Har yanzu dai, in takaice maka wannan satin kam da na kai wa Hajiya ihsani ma cewa tayi bazata amsa ba sai taji inda maganata da Abba ta kwana”
“Babbar magana, yanzu meye abunyi? kaga ya zama dole ka ajiye ayyuka dai mu kokarta mu dubo yarinyar nan.”
“yanzu abun yi shine… kana wani abu ne anjima da yamma?”
“a’a, ba komai.”
Sagir ya kawo ajiyar zuciya ya sauke “ina so kaje ka ganta kuyi magana”
Ba shiri Aadil ya kware da ruwan da yake sha, “ni kuma?”
“Eh, koma wacece bana son ta san ni ke neman ta, zan kirata daga baya idan ka bani go ahead din cewa komai yayi daidai, kai ka san irin macen da nake nema, ba wai soyayya bace a gabana.”
Aadil bai yi wata-wata ba yace “eh, wacce ta iya magana zata iya turanci cikin jama’ar ka, kyakkyawa wacce za ka shiga ko ina da ita, mace mai ilimi da sanin ya kamata, wacce zata kula da al’amuranka duk sanda baka nan kana wajen (meeting ko merger… and the list goes on). Sagir kasan da cewa macen aure kake nema ba sakatariya ba ko? sannan uwar ‘ya’yanka kake nema ba wani kamfani da zaka saya ka sayar wataran idan ka gaji dashi ba.” 2
STORY CONTINUES BELOW
Sagir yasa hannu ya shafo sumar kanshi “Aadil, ka sanni ka san bazan iya yin duk wannan ba kuma a karo na biyu, kawai kayi abun da kaga ya dace.” 1
“shi kenan tun da kace haka, ina ne address din?” 3
***** **** ****
Mummy ta gama sawa an shirya abinci kala-kala na tarban bakon ‘yarta, hatta kayan da zata saka ta fitar ta ajiye a kan gado, Sameeha ko ranta duk a cunkushe yake, tana son fita amma ta rasa yanda zatayi, wajen karfe hudu kuwa sai akayi waya ana neman mummy a shago, don haka itama sauri tayi ta shirya ta leko dakin su Khazeena, ta samu Aneesa da Khazeena suna ta aikin karatu kaman mayun boko. Bata ce musu komai ba taja kofar tayi gaba.
Aadil dai yana tafe yana ta sake-sake a ran shi “Wannan wani irin murdadden ra’ayine Sagir yake dashi sai Allah, ace macen da zaka aura ma baka da lokacin zuwa ka ganta? To ko ta yaya zata amince ayi auren ma oho.”
Yana isowa adreshin yayi bayanin ko shi wayene, aka bude masa get ya shigo. Mai gadi yayi wa Baba Saratu magana akan ga bakon ya iso, don haka ta bude kofar falo.
“Aneesa, ga bakon Sameeha nan ya iso, kuje ku kai masa ruwa, na duba dakinta ban ganta ba.”
Aneesa ta ajiye littafin dake hannunta
“To, Baba Saratu.”
Khazeena tace “to, haka zaki je ko fuskarki baki gyara ba?”
“Ina ruwanki, bakona ne? kuma ai dazu nayi wanka, don nice na kawo son kwalliya duniya sai na sake yin wata? ki taso muje mu gaishe shi.”
Khazeena ta mike, suka dau mayafan su sannan suka isa falon Daddy inda Aadil yake jira.
Kamshin turaren falon da na jikin sa ne ya gauraye ko ina mutum na shiga zai tadda wani daddadan kamshi
“Assalamu alaikum,” Aneesa ce ta fara shiga da tire din kofuna da ruwa a hannun ta. Ya amsa mata sallamar ta, a kan centre table ta ajiye masa tiren ta koma gefen kafet ta zauna sannan tace
“Sannu da zuwa”
“Yawwa, yaya kika zauna a gefe ki zauna a sama mana.”
Lokacin ne Khazeena ta shigo itama ta gaishe shi, ta ajiye kwalayen lemu da farantin kayan tabawa. Tzo daidai kunnen Aneesa tace “bari na sake dubata a dakin mummy”
“Kece kanwar tamu ko, sunan ki ma rowar shi kike min ne?”
Khazeena tana dariya ta rufe fuska. “Ni bani da rowa, sunana Khazeena wannan kuma Aneesa ita ce babbar yayar mu.”
Aneesa ta mata nuni da ido akan ta tafi da sauri. Aadil yace “To kinji tace ita bata rowa, har sunan ki ma ta fada.”
Yana dariya Khazeena ta bar falon, nan ne Aneesa tace “Ina wuni?”
“Lafiya kalau, kin ganni ni kadai ko?
Cikin hanzari ta shiga bayani “kayi hakuri fa, ta dan fita ne ba ni bace kazo gani, bata san yanzu zaka zo ba, amma tana dawowa”
Aadil yayi murmushi, yace “ba komai, nima kiyi hakuri yana da wani uzuri ne yace nazo mu gaisa zai samu lokaci sai ya zo ku gaisa sosai.”
“Ni fa da gaske nakeyi, ‘yar uwata ce zaka gani”
“To shi kenan naji, tunda bata nan kin ga ai ke mun gaisa, idan ya samu lokaci yazo sai su gaisa ko me kikace?” 1
Aneesa dai kanta na kasa da kyar take magana, don bata saba magana da mutumin da bata sani ba.
ta mike ta zuba mishi ruwa, “bismillah,”
“Na gode, kema a Baze din kike karatu?”
“A’a ba a can make karatu ba, Sameeha ce take can ajinta daya yanzu.”
“Yayi kyau.”
“Shi abokin naka me yakeyi, har ya gagara zuwa ganin kanwata sai ya turo ka”
Aadil ya kada harshe “wa yace miki ya gagara zuwa ne?”
“To, me zai hana shi zuwa ganin macen da zai aura?”
“kina fushi kaman kece akayiwa laifin, baki dauki uzurinmu ba kenan.”
“Ni ba fushi nakeyi ba, kuma uzurin ku kam sai ku jira wacce kukayiwa laifi.”
Aneesa ta mike, ka dan taba abincin bari na nemeta a waya, nasan batayi nisa ba yanzu zata zo, kaga sai ka bashi amsa cikakkiy idan ka ganta”
Tana barin falon Aadil yayi shiru yana tunani, yanda yaga hankalin Aneesa da Khazeena ya san sunzo gidan kwarai, don haka bayi da fargaba.
Can Aneesa ta sake shigowa “don Allah kayi hakuri mun barka kana ta jira, maganar gaskiya wayarta ce a kashe amma zamu isar da sako kar muyi ta ajiyeka kana da abubuwan yi”
“Ba komai, na gode. Kya gaishe ta, ko ba komai mun gaisa ai, an kulla zumunci kuma mun yaba da irin karban mu da akayi.”
Aneesa taji kunya ya lullubeta, yana fita ta koma wajen su Baba Saratu, “Amma ita Sameeha ina ta shiga wayar ta a kashe sannan ba wanda ya san ta fita.”
“To amma ba tare da mummy suka fita ba?” Zaheeda ta tambaya.
“Naga fitar hajiya ita kadai ta fita. Yanzu dai kuyi shiru kar ku fada tukun idan hajiyar ta dawo sai a san abunyi.”
ai ko bai wuce minti ashirin da tafiyar Aadil ba sai ga Sameeha ta dawo, kowa idanu ya zuba mata.
“lafiya kuke kallo na haka?”
“idan mummy ta dawo zakiyi bayani ai” Zaheeda ta fada
“me ya faru?’
Baba saratu tace “ke ina kika shiga ana ta neman ki tun dazu? bakin ki har suka zo suka tafi bake ba dalilinki.”
“Nifa makaranta na shiga, ana nemanmu”
“shine wayar ki a kashe, sai da Aneesa fa taje tayi ta bashi hakuri.”
“test muka shiga shi yasa na kashe wayar tawa.” ba wanda ya sake ce mata komai. mummy na dawowa ta nemi sanin ko bakin sun zo.
“eh, mummy ya zo, amma Sameeha bata nan Allah ya so abokin sa Aadil ne yazo shi baya nan.”
“Ban gane Sameeha bata nan ba?”
Tana nade gyalenta, Khazeena ta mata bayanin komai da yanda Aneesa ta taimaka ba aji kunya ba.
Nan take ta sa aka kira Sameeha “wai ina kika shiga tun dazu, bayan kin san kina da bako. duk kin kwaba min lissafi, me kike son na fadawa daddy?”
“Mummy, waya aka min muna da test hakan yasa na fita da sauri ban samu nayi waya na fada muku ba.”
“Ai wannan shiririta ne, tun farko da ba ki amince ba ai na san me zan fadawa daddy sai ya sa a tsaida shi amma yanzu kin sa mutane jin kunya. Yau din nan zan fadawa daddy duk abin da ya miki ke kika jawo ba ruwa na.”
“Mummy kiyi hakuri.” a ranta kuwa dadi ne fal, Allah yasa ma ya fasa, fatan ta kenan.
Mummy dai, tunaninta daya ne kar Daddy yayi wa yara maganar su bashi labarin abun da ta shirya don haka ta kwabe su kaf akan kar magana ta kuskura to koma kunnen Daddy.Tunda Aadil yazo yace masa bai sameta a gida ba, hankalin sa sai ya kwanta, ko ba komai zai bawa Hajiya uzurin cewa basu gama tattaunawa da yarinyar ba. Don haka da karfin gwiwarsa ya nufi main house, don a can yau yake da shirin shan ruwa. Yawancin lokuta idan dai yana gari yafi shan ruwa a Main house, wannan Ramadan din kuwa har an kai uku amma bai je shan ruwan ba, sai yau. +
Hannatu ce ta shigo dakin su Sameeha ta sanar da ita akan tayi bako a waje, don haka ta dauki wayarta cikin mamakin ko waye ne, don ita kam bata barin kowa ya iso gida nemanta. Yau dinma ta fita ne don taga waye me shirin tono mata asiri yasa Daddy yayi mata maganar aure. A kan kujerar harabar gidan ta same shi. Ita dai tunda ta iso taga ba wai ta san me shi bane.
Shi kuwa Aadil tun fitowar ta ya tsaya yana mamakin kodai yayi batan gida ne, to amma yaushe ya zo, ba ana gobe za akama azumi bane? Gashi yau azumi an kai uku kenan, yaya za ayi ya manta gidan. Lalle nan ne sai dai hala ba Sameeha… kafin ya karasa tunanin yaga yarinyar da ta keta mutumcin atamfar nan da wani dinki dakyar take numfashi ta ja kujera ta zauna, duk rabin krijinta a waje.
“Lafiya dai Malam, ban gane ka ba”
Aadil yayi murmushi “Ai kya maida wukar mu gaisa ko?”
Ta dan saki jiki kadan. “Sunana Aadil, kwanaki uku da suka wuce na zo ban same ki ba. To sako ne nayi mantuwa ban bada ba shiyasa na kara dawowa yau, da fatan banyi laifi ba.”
Sameeha tayi shiru tana tunanin abunyi, kafin ta nisa tace “kaga Aadil na farko, ni bani da ra’ayin jin sakon ka, kai asalima wanda ya turo sakon baya gabana ina da wanda nake so don haka ka bashi hakuri.”
Aadil yayi shiru cikin jimamin yanda akayi wannan yarinyar tayi batan kai ta fito a gidan da yake tunanin gidan mutumci ne. Don haka sukayi sallama, ya isa gurin mai gadi ya mika masa sakon, ya fitar da takarda da biro yayi wani rubutu sannan ya bayar yace a hada da sakon a isar cikin gida.
Dalleliyar motarsa ya fada ya kama hanyar gida, a zuciyar sa kuwa ya gama shirya abun da ya dace yayi.
Bayan sati guda da yin wannan al’amari ne Alhaji Mahmoud ya nemi ganin Aneesa a falonsa, da jin hakan Hajiya Juwairiya hankalinta ya tashi tasan asirinta kam yau zai tonu, dama niyyarta idan anga Sameeha, sai ta cewa Daddy din anzo anga Aneesa amma shi yaron yace Sameeha ce ta masa, amma sai hakan bai faru ba. Yanzu kam dai bata da sauran dabara tanaji tana gani ‘yar da tafi tsana a duniya ta wuce falon mahaifin nata ba tare da tayi komai a kai ba. 2
STORY CONTINUES BELOW
“Aneesan Innarta, yaya karatun dai ana ganewa ko?”
Kanta a kasa tace “Eh, Daddy wanda ban gane ba munayi da Khazeena amma tace itama basuyi wasu ba a makaranta sai dai na tambayi Zaheeda.”
“To yayi kyau, kinaga zaki iya jarabawar tare da su Zaheeda ko dai a bari sai wani shekarar ayi miki register?”
Ba abun da ya fadowa Aneesa a lokacin irin yanda har zata iya kara wata shekara ba tare da taga Innarta ba.
“Zan gwada yi yanzun ma, ai da dan sauran watanni”
“Allah ya baku sa’a.” bayan Daddy ya dan yi shiru ne sai kuma yace “Ni mamana, baki fada min yanda kukayi da bakon ki ba.” ya fadi hakan da alamar jiran bayani daga gareta.
Ita kuma kanta sai ya kulle bakonta kuma? Hala dai bakon da ya zo wurin Sameeha Daddy yake nufi.
“Baki ce komai ba, kun daidaita ko har yanzu baku gama tunanin ba”
“Daddy ai da yazo bai samu Sameehan ba”
“Shi kuma me ya hada shi da Sameeha, Sameeha zai aura ko ke?”
Nan take taji gabanta ya yanke ya fadi, duniyar da take kuma yana neman ya hadiyeta. Wai me take shirin ji? Ina ita ina auren dan birni? Dan birnin ma mai ilimi wanda kuma Mummy taso Sameeha ya aura. Don su kam dai ce musu akayi Sameehace ke da bako.
“Mummy tace Sameeha ke da bako, ko da bakon yazo ya bada uzuri akan abokin sa bai samu isowa ba saboda ayyuka amma zai sake juyowa, sai muka bashi hakuri saboda Sameeha ta tafi makaranta zana gwaji”
Daddy yayi shiru cikin alamar nazari “Ba komai to tashi kije, idan kin shiga kiyi wa mummy din naku magana”
“Na gode Daddy.”
Jikinta a sanyaye, ta koma daki tana isa ta bude marfin wardrobe dinta mai dauke da ledar da ta adana shi wuri guda. Hannunta na rawa ta bude takardar ta sake karantawa.
“Sannu da dawainiya, mun gode da tarbar da kikayi mana, kuma mun yaba da halayenki na kwarai, ki sa mana rana sai abokina yazo domin ku kara tattaunawa, ki huta lafiya” 6
Ta nade takardar a bayan takardar dai sunantane rada-rada a rubuce, tunda Baba Saratu ta mika mata wannan sakon ta boye da kyau don gudun rikici sai dai yanzu kaman itace ta rikice.
“Shin dama ni aka turo a zo a gani ko Sameeha? To tunda basu sami Sameeha ba me yasa suka amince da ni ko kuma wani rudani ne daga wajen su?” tambayoyi fal a cike a ran Aneesa, ta shiga bude abubuwan cikin ledar nan, kayan shafe-shafe ne irin na mata masu tsadar gaske da turarurruka taga an rubuta YSL a jiki sai kayan makulashe. A kasan kayan ne taga kwalin wayar Nokia a ciki.
Gumi ne ya keto mata, wai shin sun san wa Uwanin Malam Habu suka tarkatowa wannan shirgi kuwa? sun san me rayuwarta ta Kunuwal ta kunsa? sun san cewa duk inda ta shiga babu farin ciki a wurin kuwa? Nan da nan ta shiga tara kayan a leda tana maidasu, harda ‘yar guntun wasikar ma ta jefa a ciki.
Hajiya Juwairiya da taji kiran Daddy hankalinta idan yayi dubu to sun tashi. Ta shiga jikinta na rawa, amma ga mamakin ta bai dago mata zancen ‘yar Halima ba bare tasha tashin hankalin da ta yi zato.
****** ******** ***********
“Abba, munje mun tattauna da yarinyar, yanzu dai jira mukeyi ta bamu lokacin da za muje muji ko me ta yanke game da al’amarin, amma munyi na’am da hankalinta, da kuma tarbiyyarta” Aadil ne ke ta kwararo zance, Sagir kuwa kansa na kasa don ba yanda za ayi yacewa Abba bada shi aka je ba, don haka ya bar Aadil da aikin kwararo bayani.
“Ah to yayi kyau, duk abun da ake ciki dai sai na sani saboda a sa manya a maganar. Allah ya tabbatar da alheri”
“ameen, mun gode Abba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Kaima sai kayi kokari ai ka samowa kanka, ko sai ka jira abokin naka ya soma tukun?”
Aadil yana dariya ya dan sosa keyarsa sannan yace “Yallabai, muna ta kokari dai.”
Bayan sun fita ne suka nufi ofis don akwai sauran ayyukan da suka saura musu na hada rahotannin kamfani da sukeyi da sauran ma’aikata, akwai wadanda suka ware zasu kara musu kudin aiki sai su dawo bayan isha zuwa karfe sha daya su rage aikin kafin kowa ya watse.
“Sagir, kai yaushe kake da shirin mu koma ne? Naga Abba fa ya sa wuta har maganar sako manya yakeyi.”
“Naga alama kai dadin abun nan kakeji,”
“Ni naga yarinya nace maka tayi sosai, ka shirya kawai muje muji me zata ce ya gagare ka?”
“To ba shikenan ba sai kai ka aureta.”
Aadil ya juya ya kalli Sagir “kai sai ana maganar gaskiya sai ka koma wata maganar daban,”
“Na ji, idan mun kammala wannan aikin gaban mu zamu je India inaga bai wuce muyi kwana uku ba idan Allah yaso, muna dawowa sai muje nima ko zan huta da wannan damuwar”
“Zaka gode min, muna nan da kai”. Sagir ya adana motar a ma’adanar motar shugaban kamfani sannan suka shiga.
Daggash-Adebayo and sons katafaren wurine sosai wanda ya kunshi kamfani da ofis-ofis na ma’aikatan, harda gidajen ma’aikata yawanci masu kula da ayyuka, akawu, mataimaka, masu bada shawara masana ilimin fannoni da dama nan ne ofishin su yake. Sagir shi ke kula da ofishin su na Abuja, kasancewar sa mutum mai hannun jarin da ya fi kauri shine shugaban kamfanin (CEO), sai Ahmad Adebayo wanda yake kula da kamfanin magungunan su dake legas, sai dai zuwan Sagir kamfanin ne suka kirkiri bangaren kerekere da gine-gine a tsarin kamfanin. Sauran ofisoshinsu kuwa suna garuruwan daban-daban kaman Ibadan, Kogi, Kaduna, Bauchi da Kano. 2
Ranar wata Asabar ne gidan Alhaji Mahmoud sukayi manyan baki, wadanda suka shigo da kayan arziki iri-iri. Bayan duka matan nan sun gama shigowa falon mummy ne, aka fara gaisawa kasancewar Azumi ne, ba zancen kawo kayan ciye-ciye. Hajiya Juwairiyya dai da ganin su ta san daga babban gida suka fito, tana bin kowaccen su da kallo, har sai da suka shararo bayanin abun da ke tafe dasu.
“Da farko zan fara bude mana wannan zama da addu’a cike da fatan alkhairi, ayi salati ga annabi, a karanta Fatiha da qul a’uzai.” bayan an kammala ne wannan matar tayi bayanin kanta “Ni sunana Hajiya Munnira, wadannan duk ‘yan uwa ne da abokan arziki, daga gidan Alhaji Mustapha Daggash muka taho, wannan kayan dai na toshin ‘yar ku kuma ‘yar mu ne tunda yanzu an zama daya.”
Hajiya Juwairiyya ta nemi numfashinta tana neman ta rasa shi saboda yanda yake fita a gaggauce. Hankalinta ya tashi aure kuma? 2
“ina ‘yar tamu ne tun shigowar mu bamuga amaryar ba.”
“Ai kin san yaran, suna can wurin karatu.” Ta samu ta fada da kyar tana yake.
“To ba komai, tunda kina nan, sai mu miki bayanin komai”
Nan fa su Hannatu suka shiga jero kaya ana ta bayani wai duk kayan toshi ne.
Ita dai inda kanta ya kulle Alhaji Mahmoud bai ce mata za a zo kawo kaya ba, sannan bai sanar da ita cewa ga ‘yar sa da ya bayar ba, daya zuciyar tace mata maganar Aneesa fa da ya miki? Nan da nan ta kau da wannan zancen, yaya ma za ayi su dauki ‘yar kauye su zuba mata wannan arzikin ai yafi karfin ta. Kudin dinki ma fa da suka sa a kasan akwatin dubu dari biyu. Tab ina yarinya ai baki iso nan ba tukun. 2
Tana ta yaken dole dai, har ta samu bakin suka tafi, ta umurci ‘yan aikin gidan su jido kayan a jibge a falon Daddy.
Ai kuwa yana shigowa gidan da kayan yayi arba, murmushi yayi ya wuce dakinsa. Bayan sun gama buda baki ne yaran duka sun shiga ta same shi da maganar.
STORY CONTINUES BELOW
“Da rana kawai sai ga baki.” Tana fadan haka ta dake. Yayi murmushi wato sarautar ta motsa amma bata san shima da ‘yan mulkin ya shigo ba. 1
“Na sha’afa ban sanar dake ba, sun koma lafiya dai ko?”
Baki a bude cike da mamaki tace “Da ka sanar da zuwan baki ai inaga da an shirya musu tarba ta girma, amma ace anzo gidan Alhaji Mahmoud guda ba tare da an koma da abu mai kauri ba ai bai dace ba”
“Na san Hajiya tana nan, ba abun da zai kasa”
Taga alama ya na neman ya manna mata ne don haka tace “Sai dai ban san wace ‘yar tawa aka bada ba batare da sanina ba”
“Kina da wata ‘yar da ta kai ayi mata aure ne yanzu bayan Aneesa?”
Ai yana tabbatar mata da zargin ta taji komai ya kwance mata, yanzu duk kokarinta na ganin Halima da zuri’ar ta sun tozarta ya tashi a banza kenan? eh mana, tunda ba yanda za ayi wannan yarinyar ta shiga wannan daular ta bar uwarta a kauye, nan da nan taji cikinta ya juya.
“ko kuwa kina da tacewa ne wannan karon, ba sai daga baya ki zo ki bi ta bayan fage ba.” da ya kula bakin ta ya mutu ne sai yace
“A tunanina, an riga an zama daya zaki dauki yarinyar nan a matsayin ‘yar ki, ko da a rashina ke mai riketa ne, amma har zan kawo maganar aurenta ki juya ki maidashi kan ‘yar ki. Allah da ikon sa na fahimci hakan. Don haka an kammala magana aure kuma ba fashi da yardar Allah, idan kin isa kuma ki hana shi mugani.” ya mike ya shiga daki. A nan ta buga tagumi na rashin sanin mafita. 2
Aneesa kuwa zama cikin mutan gidan ya gagare ta tunda aka kawo kayan toshinta, sai ta fara kula da canji wajen mummy, ko ta gaisheta ba lallai bane ta amsa, don haka aikin gaban ta kawai takeyi. Ranar Daddy ya ce ta shirya ana jibi Sallah zata tafi Kunuwal gaishe da su Inna har sai an gama bikin Sallah.
Wannan labari ne ya kunsa mata farin ciki a tare da ita marar misaltuwa. Tana komawa daki ta hau kimtsa kayan da zata tafi dasu. Su Baba Saratu kuwa an cika su da hirar abun da za a farayi da an isa.
Da dare ta gama goge kayanta tana jera su ne a cikin jakar tafiyarta. Sai ga Khazeena ta shigo tana haki
“kefa lafiya nagan ki haka?”
“ke kam ki tashi ki shirya kinyi baki”
“Baki ni kuma?” Aneesa ta dafa kirji, to ita wa ta sani kuma?
“Ke dai ki shirya, kin tuna Uncle Aadil da yazo ranan?” 1
“Eh, na tuna shi. me ya faru?”
Khazeena taja hannaun ta zuwa kofar wardrobe dinta ta ciro kaya tana zaba mata “Yazo dashi da abokinsa Uncle Sagir, wanda naji daddy yace shi zaki aura”
Nan take jikin Aneesa ya hau tsuma. “To ni kuma naje nace musu meye?” 1
Khazeena tace “Nima ban sani ba, amma dai ki shirya suna falon Daddy, bari naje na hado musu abun sha”
Tunda Khazeena ta fita a nan ta bar Aneesa ba tare da ta iya yin komai ba, yau ta ga ta kanta me zata ce masa? Ita ba iya zancen mutanen birni tayi ba.
Wata zuciyar tace ki gaishe su kawai ki tsuke bakin ki.
Hakan ko akayi, bayan minti goma ta sa kayanta, fes da ita, ta gyara fuskarta daidai gwargwado ta daura dankwalin atamfarta blue mai ratsin fari da bakin layi sannan ta yafa mayafinta ta karasa falon inda ta same su zaune. Kanta a kasa ta nemi wurinta na kullum a bakin kafet kamar an zana sunanta a wannan wajen. 2
“sannunku da zuwa”
Sagir ya juyo kallo daya ya mata ya kau da kai. 2
Aadil yace “Yauwa sannu da fitowa, kin fito lafiya? Mun samu an karbi uzurin kenan”
Kanta na kasa tayi murmushi. “yau kam Allah ya kawo shi, ina fatan mun wanke laifin namu?”
Aneesa tace “Daman bance kun min laifi ba, wa ‘yaruwata ce”
“Ni dai ina tsamman kece Aneesa” Aadil ya fada cikin zolaya. “kuma dai da sunanki akayi tambayar nan.”
Ita dai Aneesa ba abun da yake damunta illa jagorar tafiyar baya uhm baya uhm-uhm bayaga wayoyi dayake ta amsawa.
Ashe Aadil ma abun ya dame shi, don haka yace “To ni bari na dan barku ku tattauna ko?” Ya mike yana kallon Sagir.
Aadil na fita Sagir ya maida hankalinsa gareta. Ya rasa me yake damun Aadil da zai kalli wannan yarinyar yace ta dace dashi? shi Sagir Daggash da ya shiga duniya ya kewaya yaga kyawawan mata ace ya nunawa duniya wannan ‘yar yarinyar a matsayin matar shi? don haka daurewa yayi yace “ina tsamman Aadil ya sanar dake ko ni waye ne?”
A sanyaye Aneesa tace “eh”
“To yayi kyau, a ina kike karatu?” Shiru tayi kafin tace tasan a rina ina ita daman ina auren gogaggen dan boko a matsayinta wacce ta tashi a kauye mai matsayin karatu iya aji daya a sekandire.
“Ba nayi” ta bashi amsa a takaice
“Baki kammala ba kike nufi?” ya tamabaya hannayensa a sarkafe cikin juna.
“A’a, ban shiga jami’a ba amma ina shirin rubuta jarabawar dai bana” 2
Rausayar da kansa yayi gefe guda a ransa yace oh Aadil ka cuceni, aure zanyi ko reno? 6
“To, Allah ya bada sa’a. mun gaishe ki zamu wuce.” 1
Aneesa ba abun da take tunani irin Allah ya hada ta da miskilin mutum. Tunda ya fara magana ko kanta na kasa.
“ina fatan ba wata matsala ko?”
“Eh, ba matsala, sai dai idan Allah ya kaimu karshen Ramadaan zanje ganin mahaifiyata a garinmu” 3
Ya dago kai yana dubanta. “To Allah ya kaiku lafiya, idan kinje ki gaishesu kafin mu zo. Na dauka Hajiya ce mahaifiyarki”
“A’a ban dade da zuwa nan ba, Innata tana aure ne a Kunuwal”
Wani gari ne kuma wannan oho ‘uhmm’ kawai ya iya cewa, yana jira ya fita ya samu Aadil. 1
Ya nuna mata wata jaka yace “Ga wannan tsarabar India ce ba yawa, ki bawa su Khazeena ce ko?”
“Eh,”
“Sauran kuma sai kiyi amfani dasu.”
“Ka shiga dawainiya da yawa. Mun gode Allah ya amfana ya kara rufa asiri.” 3
Murmushi yayi iya labban bakin sa kasancewar duk da yarinyar bata masa ba, yaji dadin addu’o’in da ta masa. 2
“To meye laifina? bakace na tamabayeta matakin karatunta ba, mace kace na duba halayyarta kuma na dubo na yaba da halayyar kwarai.”
“Yanzu tsakanin ka da Allah kayi adalci ka dubeni ka ga wannan yarinyar kamar zata karye ta dukunkune kai a kasa kaman da surukanta take magana, shin kaga dacewarta da gidana? Ka san ko sunan garinsu ban taba ji ba a rayuwata, hala ma wani kauye ne futuk”
“Me yasa kake tunanin ko matsayin mutum ne a rayuwa kawai zai taka rawar gani a rayuwar aure? kasan meye boyayyan al’amarin da yake tare da ita? ko kuwa wacce ka shaida da itan hakan ya hana abubuwa lalacewa?”
Tunda Aadil ya tabo inda Sagir baya son zuwa a rayuwarsa sai ya kau da zancen.Gaba daya gidan ya hautsine sai kace yau take sallah, banda murna da farin ciki ba abun da ke tashi a gidan Malam Habu na Kunuwal. Yau ga Uwani ta zo daga birni kowa sai cicirondon zuwa ganinta yakeyi, wasu an ce musu Uwani ta dawo tamkar balarabiya don kyau, wasu ko ce musu akayi sai sunje su ga yanda fatarta take sheki kamar an canza mata fata. Ko ma dai menene Uwani dai uwanin da suka sani ne ‘yar Inna da malam Habu, wayewace kawai ta kawo wannan canjin. 8
Yana zaune a kan tabarmar gindin bishiya, inda suke taruwa su rakashe suna hirar banza da wofi, wani sa’in a kawo maganar gidan makwabtansu wani sa’in na gidajensu, a nan ne aka fasa kanun labaran.
“Ai Nata’ala, na gaya maka sai ka ga yanda ta dawo wanke hannu ka taba, ni wani kalan yadin da na hango a jikinta alqur’an ban taba ko mafarkinsa ba. Kai kaga wata dalleliyar motar da ta dawo da ita? tafi wacce ta dauke ta a kyau da girma da komai 2
Iro yace “Ai ba zancen sanyi, kawai abun da za ayi gobe ka shirya da farin safiya, ka cafko kajin ka guda uku kaje kayi barka da sallah ko za ayi dace” 1
Nata’ala ya hakimce duk yana jin jawabin abokan nasa, yayinda shi ya gama nisa a tasa duniyar…
Bayan ribibi ya lafa ne suna zaune ita da Inna a tsakar gida Aneesa ta dubi Inna tace “Inna Daddy, ya miki bayanin komai ko?”
Inna ta tabe baki tare da gyara bakin zanin ta sannan tace “Uwani kenan, ai ni magana ta fatar baki ta dade bata hadani da mahaifinki ba, bare kuma abun da ya shafe ki. Ko tafiyar kin nan ma da Malam aka gama komai kafin na amsa.”
Aneesa ta gyara zamanta tace “Inna don Allah ina son na san takamammen laifin da Daddy yayi miki, ko kuma abun da ya raba ki dashi. Don ni kam zuwana naje da tsanarsa sosai a raina amma na tarar da shi ba a yanda na dauke shi ba. Na san mun muzanta an zarge ki kuma ta dalilinsa amma don Allah ina son ki fada min.”
“Zan fada miki a lokacin da ya dace, yanzu ki fada min, shin kin amince da zabin da ya miki?”
Kan Aneesa a kasa, wannan wani abu ne da take dadewa wajen kashe lokaci don ta samo amsar shi amma a kullum sai ta gano cewa bata sani ba, amma kuma meye amfanin sanin ma?
“Inna don Allah ki fada min?” Aneesa ta shagwabe fuska amma sam Innar ta taki, don haka suka shiga hirar shirye-shiryen sallah. Aneesa ta ja bakinta tayi shiru da niyyar washegari idan taje ganin jinjirar Mairo zata tambayi Mama kuma tasan a can kam za a bata labari.
Da wannan zumudin a ranta tayi bacci.
****** *********
“Yanzu haka zaki fita da sassafe?”
“Inna yanzu zanje na dawo, hala kuma daga gidan Mama ta can zan wuce gidan Falmata.” 2
“Idan kin gama sai ki zo ki sa min hannu a miyar sallar ko?”
“To Inna.” cikin dauki ta fice daga gidan. sauri take a hanyarta, duk da kowa ta gani yana son gaisawa da ita a hanya, sabanin da, da kowa yake gudun a ganshi tare da ita.
“Ai ke kam yarinyar nan a gaishe ki da iya doka sammako.”
“Mama kar kice min bacci kikeyi, sai kika tuna min da Abuja, sai ki ga mata har taran safe bata tashi a bacci ba.” 3
“wai wai wai, ina ni ina kai tara a kwance, ai sai jiki yayi ciwo. Mun ga tsaraba jiya kaca-kaca, Malam Sule ya shigo har nan muka gaisa ya ajiye mana. Allah ya amfana.” 1
Muryar Baba sukaji ya shigo cikin gidan “a’a baba yau bakaje kasuwar bane?” Aneesa ta fada.
Ya zauna kan kujerar sa mai kwanceccen baya “Bayan an sake ni anyi sabon miji kuma ina naga ta walwala bare zuwa kasuwa?” 1
STORY CONTINUES BELOW
Aneesa tayi dariya sosai sannan tace “Ai ba a daura ba, idan kana so ba sai nace na fasa ba.” haka dai sukayi ta barkwance daga bisani suka gaisa, sannan ta wuce sashin Mairo don ganin jinjira, wacce aka sanyawa suna Hauwa’u amma Inna wuro suke ce mata kasancewarta mai sunan uwar Mairo.
Komawarta ta samu Baba ya fita kofar gida don haka ta bajewa mama bukatarta na son sanin ko meye maqasudin rabuwar iyayenta da kuma ma’anar kalmar da aka dade ana caba mata wato “Uwani ‘yar Halima ai gado tayi.” Nan ma Maman cewa tayi Innarta ta fada mata. “ni kam sai gwarani kukeyi ku taimaka ku fada min”
“hmmm idan kin sani akwai abun da zaki iya gyarawa ne? komai ya wuce, ya ci gaba da rayuwar sa itama ta ci gaba da tata”
“Ina son na sani ko akwai abun da zan koya a cikin labarin da zai sa na kiyaye yin kuskuren da dayan su yayi a rayuwar aure. Tunda nima ana shirin nawa”
Jin haka Mama tayi ajiyar zuciya “Ki je dai Innarki ta fada miki ai waka a bakin mai ita tafi dadi.”
Haka dai Aneesa ta tafi gidan Falmata jiki babu kwari. Falmata na son jin hirar birni irin Abuja yayinda Aneesa take son jin tarihin iyayenta.
Ranar dai batayi bacci ba sai da ta sake samun innarta akan lallai tana son sanin ciwon da Mahaifiyarta mama, take alhinin fada mata da bakinta don gudun tuno bakin cikin wancan lokacin. A nan ne Inna ta daddara.
“Hakika ni Halima na ga rayuwa, wanda nake farin ciki da shi da wanda ko a mafarki bana fatan sake ganin shi. Tun ina cikin kuruciyata kanin Babanmu baban su Zainabu da yake Gombe ya zo ya tafi dani saboda ya sani nayi makarantar zamani tare da yaransa, kasancewar hakika yafi Babanmu rufin asiri, a wancan lokacin. Munyi kukan rabuwa da su Mama yayinda mutanen gari kowa yayi ta aibanta abin da sukayi da rashin godiyar Allah, tunda ai ‘ya mace anyi ta ne don ta yi aure ta kula da miji da yaranta don me yasa su zasuce tasu ‘yar tayi boko?”
Aneesa ta gyara zamanta.
“Basu canza shawara ba, su ka barni har na kammala karatuna na firamare. Nakan zo lokaci-lokaci na gaida su mama da Baba a gida, a haka ne baban su Zainabu yace ya sama mani makarantar kwana ta Doma inda zan ci gaba da karatu, to nan ne akayi takun sak’a da babanmu, domin kuwa ya k’yakishe kasa yace ‘yar sa ta gama boko. Da kyar dai aka shawo kanshi, sai da yayan mu yasa baki ya barni yace amma yana sama min miji zan dawo ayi mani aure.
Na koma da wannan yarjejeniyar, ai kuwa ko shekara biyu ba a rufa ba, sai ga baban su zainabu ya taso keyata a gaba, A lokacin da na hadu da Mahmoud a gidan wata yar su Zainabu wai shi kanin mijinta ne yazo daga Zaria, kafin kace meye zance yayi nisa har kunnen baban Zainabu. Wannan yasa ya sakoni a gaba don na bayyana komai gaban baba a san abun yi. An yi bincike mai tsawo, kasancewar sa mutumin Zaria, sai da aka hada da jama’armu na can tukunna sannan aka gano gidan su da kuma ko shi waye.” Inna tayi shiru tana murmushi kaman wanda take tariyo lokacin a kwakwalwarta “a wancan lokacin na dade banga mutum mai son kyautatawa nasa ba da na kusa da shi irin Mahmoud, wato mahaifin ki. Ba aje ko ina ba, aka daura aurena da Mahmoud muka tattara muka koma Kaduna inda yake aiki a lokacin.
Tunda muka tafi lafiya kalau, ba abun da yafi farin ciki a gurin su mama irin hakan. Don hankalin kowa ya kwanta sun aurar da yarinya lafiya, ba kaman yanda ake zaton zan dawo ba daga birni a lalace. An ce wai idan an ji shiru ma lafiya ne, a tunanin su kenan. Amma a nawa bangaren labari ya sha bambam anyi auren mu da Mahmoud da wata goma sha daya sai gani niki-niki da tsohon ciki da akwati guda, kana ganina kuma ka san nasha wahalar tafiya.
Sai da na natsa komai ya lafa tukunna babana ya sa ni a gaba da tambayoyin ko lafiya? banda kuka ba abunda nakeyi haka dai suka hakura suka barni har washegari tukun. A hankali na shiga warware wa mama abun da ya faru.
Wato randa muka bar garinnan mun tafi cikin farin ciki da daukin juna, mun sami watanni biyu masu kyau cikin zaman lafiya kafin komai ya juye akasin hakan.
STORY CONTINUES BELOW
Wato kwatsam ganin Mahmoud nayi sun dawo da wata mata gida ko kadan ban kawo wani abu a raina ba, ban kuma tambayesa ko wacece bakuwar tamu ba, na tarbe ta da kyau, sai da yamma ne ya kira ni, gaba daya yanda naga ya daburce na san akwai matsala don ban taba ganin sa cikin wannan yanayin ba. Cikin dai kame-kame ya hau min bayanin wai wannan bakuwar tamu amaryata ce. Iyayensa dama sun bashi mata, to amma ya riga ya ganni kuma ni yake so don haka ne ya aureni ya kuma basu hakuri akan zai auri zabin su daga baya. 4
Bazan iya fayyace miki halin da na tsinci kaina a ciki ba a wannan dare, nayi kwanan bakin ciki a wannan rana amma kuma mijina ne dole na zauna nayi masa biyayya. Sai dai ni nake kidana nake kuma rawana, domin kuwa tun zuwan amarya ba zaman lafiya tsakani na da Mahmoud, yau an daura mini sata gobe an mani sharrin hana mutanen gidan abinci wato amaryar dai, duk na zauna na hadiye gaba daya. A haka har na samu juna, ganin haka ya kara tunzura amarya wurin sake sabon shiri, ba gaira ba dalili sai Mahmoud ya dawo gida da wani zafaffen fushi ya hau jibgata kaman an aiko shi, wani lokaci haka zai fita bai bani kudin cefene ba, sai dai nayi ‘yar dabara na samu wanda zan ci, wai ni a gidan Mahmoud akwai randa na jera kwana biyu ina jika garrin kwaki ina sha, ran na ukun ne naji jiri na dibata na san lokacin neman mafita fa yayi. Amma menene mafitar?
Har ya kasance ni da na sa Mahmoud a ido sai ayi sati yana wurin amarya, kasancewar ya kamawa amaryar sa gidan gefen mu. Haka na zauna nayi ta renon cikin jikina, cikin kunci da bakin ciki gashi ba halin tafiya gida saboda a lokacin ko kudin mota bana maganinsu. A haka ne dabara ta fado mani na soma shiga makwabta ina musu kitso saboda na samu na abinci. A wancan lokacin gilmawar motar sa kawai ke tsakani na da Mahmoud, daga zuwan amarya zuwa watanni biyar sai da ya zamana bani da girki a gidan. Ni nake ciyar da kaina na kuma biyawa kaina bukatun yau da kullum, gashi dai mutane suna yi mun kallon ina hutawa ne, mijina mai motar yayi, gidan mu mai kyau na zamani amma basu san ba nan gizo yake sakar ba, raina a cunkuse yake.
Wataran idan nayi wa mutane kitso ma bai wuci a bani sabulu ba ko mai, duk da suna taimakawa amma nafi bukatar kudin ko ba komai zasu tare wani abun. A hankali na kula Mahmoud kaman ma bai san ya ajiye wata abu a gefe ba bare ya tuno da abun da yake cikin ta.
Ranar da naga abu ya isheni ne na sabi gyale na shiga gidan amaryata, bata ko bari mun gaisa ba, ta taso. “lafiya zaki shigo kan mutane babu izini?”
“kiyi hakuri nayi sallama, amma da bata kama na shigo bangaren ki ba ni ba me yin hakan bane, ni na shigo na roke ki ne kiji tsoron Allah a al’amuranki, ki bari mijin mu ya kwatanta adalci a tsakanin mu, meye ribarmu yau ace muna kai shi ga halaka bayan koda ba ya tara mu don yana son mu bane ai a karkashin sa muke, kuma bazamu so cutuwar sa ba. Kiyi wa Allah ki rinka fada masa gaskiya, don yau ya fifita ki akaina ba karamin abu bane a wurinsa gobe ya fifita wata kuma a kanki.” Sai da ta gama karemin kallon banza tukun ta daura
“ki je dai kiji da tsiyarki, ko an fada miki ba musan asalin ki bane, kin fito daga kauye futuk kinga maiko kin manne, ko zuciya babu miji ya daina shiga wurinki amma baki gane jirwaye yake miki ba, nice ke da tuni na wuce inda nafi kauri.”
Ni Halima wai akeyiwa gorin Mahmoud yau, haka dai na bar gidan jiki a sanyaye, duk wannan bai isa ba ranar na dawo daga gidan wata wacce nake zuwa yiwa kitso na samo sabulu, da omo, ledar na rike a hannuna na sa dan mabudi zan bude gidan sai naji kofa a bude. A tsorace na sa kai na shiga, ina lekawa kuwa ashe Mahmoud ne ya shigo wai yaji dalilin da zai sa na je na tayarwa matarsa da hankali. Mamakin sa ne ya sa ban bashi amsa ba, sai tambayar kaina da nayi, shin kuwa Mahmoud din da na aura ne wannan, a lokacin ne shi kuma idanunsa suka kai kan ledar hannuna ya wabta ya bude.
“Meye wannan kuma?” cikin in ina da kidimar da tsawar sa ta haddasa min nace “sabulu ne da omo” a fusace ya jefar da ledar yace “A gidan uban wa kika samo su?”
STORY CONTINUES BELOW
Maganar tayi mani ciwo amma na daure nace “sana’a nakeyi na samu, shin ko ka damu da sanin ci da sha na a cikin wannan watannin ma kuwa Mahmoud? ka mance da abun da kabari a tare da ni? ka mance da alkawarin da ka min na kula da kaunata har karshen rayuwa? ashe haka kaunar take na wata biyu Mahmoud?” mari ya kai mani sai da na ja da baya. “Tukun ma da izinin wa kike fita a gidan nan? da har zaki ce min sana’a” yayi mini dariyar da tafi kuka ciwo wato na takaici sannan yace “wani sana’a ma kika iya da har zaki je ki samo kudi?”
“Wato manufarka, kai baka kawo ba sai na zauna na kashe kaina da yunwa alhalin hakan ba gagarar ka yayi ba? kasan hakkina da kake tauye mini kuwa?”
“Baki san ina tauye miki hakki ba sai kin nemi matsuguni da tufar sawa kin rasa tukun” ya bugi teburin tsakiyar falon. 2
Tsoron kalamansa da kuma halin da zan shiga idan ya ida aikata abun da ya furta ne yasa na gagara fadin komai, har ya fice. Da yamma na koma shagon unguwar mu, na kai wa me shagon omo na da sabulu nace ya taimaka ya canza min da suga kulli daya da taliya. Ina kallon irin kallon da mai shagon nan ya soma mini tunda ya kula da halin da nake ciki, na tausayi amma ba yanda ya iya, kuma yana tsoron tambayar ko me yasa yana kallon mijina a gari amma kullum ina sintirin kayan masarufi? Ranar dai da ya gaji da wnanan shirun sai Umaru mai shago yace min “Ba komai lokaci ne komai zai wuce.” ya kara min karfin gwiwa a wannan ranar.
Haka na kara wata guda cikin lallama rayuwa, cikin uquba da kewar gida, cikin ma sai ya dade yake motsawa saboda rashin koshin lafiyata da kuzari, ban san zancen awu ba kam haka nake jabe a gida cikin tunanin maganar malam Umaru mai shago.
Sai dai ban san haka komai zai kare ba, randa Mahmoud ya dawo gida yana ta ihun fada, na shigo falon na same shi. “yau kam Allah ya tona asirin ki, wato daman kin san me kikeyi a gari kina zubar min da mutumci zaki wani zo ki ce min sana’a kikeyi don ki ciyar da kanki. Ashe sana’ar taki daman haka take?”
Nace “Ban gane ba Mahmoud, me kuma ya kawo wannan tashin hankalin, ni ban taba cewa ka bani wani abu naka dole ba, alhamdulillah, Allah gatan kowane, kuma Shi yana sane da komai Shi da Yasani a wannan yanayi da nake ciki shi zai cireni.” 2
Ban tashi jin komai ba sai saukan belt a gadon bayana “Ni zaki cewa Allah, kinje kina yawon iskanci, har zaki kawo min ciki kice min nawa ne?” 2
Bakin cikin da wadannan munanan kalamun suka haddasa min ne suka rufe min idanu da kunnuwa naji kamar bana duniya, wato abun ya kai ga yau rashin mutumcin Mahmoud ya tashi a kaina ya koma shegantar da cikin jiki na.
Ban san lokacin da na wanka masa mari ba. Sai da nayi, na koma lungu na dunkule rike da baki na, nan ya rufe ni da duka ina dunkule don kar ya samu cikin jikina. Yana gama jibgata son ransa, ya ce na nemi inda dare ya min ya sakeni. Kuma bashi bani bare kuma wannan abun ya fada tare da nuna cikin jikina. Cikin kuka na kwana, da safe na tattara komatsaina, na dauki sarkar da ya saya mini farkon auren mu na wuce kasuwa na sayar da ita sannan na nemi motar Gombe, bana ko jin ciwon da ya haddasa min a jikina. Zuciyata garin mu kawai take so kuma naga iyayena. Haka na iso da burin samun kubuta daga waccar rayuwar. Amma sai kuma ga magana ta bazu a gari, ai nayi cikin shege ne mijina ya gane ya kuma hadoni da abu na, ban san yanda akayi aka murda labarina ya koma hakan ba.”
Aneesa cikin kuka irin mai zafi a makogoron nan take tuno wasu abubuwan da ta fuskanta a rayuwarta, nan take taji ta kara son mahaifiyarta a ranta.
“Innata to me yasa ki ka yarda na koma hannun wannan azzalumin mutumi…”
Nan take Inna Halima ta katse ta “kul, kar ki kuskura ki fadi mummunar kalma a kan mahaifinki, wanann yana daya daga cikin dalilan da yasa ban taba baki labarin nan ba, saboda bana so ki tashi da kiyayyar mahaifinki a ranki, hakika na yi yaki nayi fama da jama’a har Allah ya kawo Malam Habu garin nan a matsayin malamin makaranta, ya samu labarina kuma ya amince ya aureni alhalin ko auren fari bai taba yi ba, tun ina tsoron sake jiki dashi gudun abun da ya faru a baya har dai ya nuna min shi dan halak ne.
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ya fahimtar dani idan aka cutar da mutum kuma yana da daman ya rama cutar da akayi masa amma yayi hakuri to lallai shi ya rabauta. Da wannan dalili ya ci galaba a kaina lokacin da mahaifinki, ya nemi magana dani akace masa nayi aure, ya nemi malam Habu ta gurin mai gari akan yayi nadama kuma yana so ya gyara kuskuren da yayi a baya, tun ba yau ba yake bin mu da maganar amma naki amincewa sai lokaci daya, da naje gidan suna aka yada magana wai wasu yaran haka aka shigo mana dasu gari ba a san ubannin su ba. Ganin cewa na san sarai waye mahaifin ki kuma na san yana neman ki idanu a rufe ya sa na amince rikon ki ya koma hannun shi kaman yanda hakan ya dace a shari’ance.”
Ranar dai Aneesa kuka Inna kuka, haka suka raba dare kafin Malam Habu ya leko yace “koke-koken nan ya isa mana, ko sai ruwan idanun naku sun kare ne a dare daya har ku rasa nayin kukan rabuwar auren Uwanin?”
Washegari aka tashi safiyar Sallah, duk gidan da ka leka zaka tarar da annashuwa da farin ciki, kowa ya kure a daka, ana ta hidimar sada zumunci, da mika kyaututtukan abinci. Da yamma bakon nasu ya iso, sai dai kowa yaji mamakin ganin wannan bako a wannan lokacin. Malam Habu ne ya fita suka gaisa tukun sannan yace “Bari a musu magana sai ka shigo ku gaisa, sannu fa kun sha hanya”
Alhaji Mahmoud yabi shi da kallon tausayi, yanzu haka suke rayuwarsu amma hankulan su a kwance, ya dubi gidan da kyau. Yanzu a nan Halima take rayuwarta? nan take yaji wasu hawaye suna neman kwararo masa, amma ya hadiye su. Sai kuwa ga Malam Habu ya shimfida masa tabarma a dan falon karban bakin sa, a hakan ma gidan malam Habu yana cikin daidaikun gidajen da aka mulmule da siminti a garin. 2
Inna da jin anyi bako tayi maza ta hada fura, ta sa a kwano mai kyau ta baiwa Amina ta kai, ta dan daura jalof din taliya da yaji hadi sannan ta bar Aneesa wurin duba girkin ta yayibi luffayanta ta nufi falon, sai dai bakon da ta gani ya haddasa mata mummunar faduwar gaba, wanda kuma labarin da ta bawa Aneesa jiya yana daya daga cikin abubuwan da suka dawo mata da ciwonta sabo fil.
Bata bari damuwar ta bayyana a fuskarta ba, ta zauna daga bakin kofa ta gaishe shi, ta kuma masa sannu da zuwa, shi kuwa kallonta yakeyi bata canza ba sosai, sai dai da tana cikin hutu fiye da wannan ya san zata dade tsufarta bai fito ba. Sai da ta sake ce masa yaya hanya sannan ya amsa.
“Bari yara su iso maka da abinci”
“A’a alhamdulillah, sai da naci abinci a Gombe sannan na karaso.”
“Cimar mu ta Kunuwal dai ta canza ba irin wanda ka sani bane a da”
Dukan su sukayi shiru, shi ya san da gayya ta fadi hakan. 2
Malam Habu ya yi sallama ya shigo falon, aka sake gaisawa, Inna Halima ta mike zata tafi yace
“Zauna muyi magana mana”
Wai shi wannan ya zaci har yanzu a karkashin ikon sa nake ne? ta masa wani irin duba, tana jin fushi na taso mata, sai da ta zauna sannan ya ci gaba “Kaman yanda na sanar muku a waya, anyi tambayar auren Aneesa kuma an bada ita. Malam Habu kayi hakuri na maka katsalandan cikin al’amari don kowa ya san kaine kafi cancanta ka auradda Aneesa wato, amma ganin gidan mutumci ne suka miko wannan maganar yasa na yi tunani har na amince ba tare da na tunkare ka ba. amma yanzu da suka zo da batun aure, al’amarin sa rana da komai, naga ya dace nayi tattaki nazo domin a tattauna a tsanake.”
Malam Habu ya gyara zama yace “Yallabai, ai komi kayi yayi daidai domin kaine mahaifin Uwani, mu dai fatan mu Allah ya sa ayi a sa’a Allah ya bata zaman lafiya da mijinta ya bata ingatacciyar rayuwa”
Kaman daga sama suka ji Inna tace “Amma dai an bincika bayi da mata ko? ko kuwa baya shirin yin wani auren? Don kar a zo a sashi dole ya sa rayuwarta a hatsari.” 7
Jin hakan yasa mazan duk sukayi shiru, daga bisani ta mike taje ta dauko musu abinci ta koma cikin gida abinta.
Ai wannan ma wani salon tsiya ne sai da ka gama shirin aure zaka taho kace wai kai ‘yarka ‘yarka, bayan baka san wuyanta ba. 2
Bayan sun kammala ne, Alhaji Mahmoud ya nemi ganin Aneesa don suyi sallama zai wuce Gombe washegari jirgi zai maidashi Abuja. Gaishe shi tayi kawai ba tare da ta tsawaita hirar tasu ba, ya nemi sanin ko yaushe take son komawa, Tace “Daddy ko nan da sati daya?”
Tana ta addu’ar Allah ya sa ya amince ne a ranta, sai kawai taji yace “to shi kenan sai ki zauna da shirin ki nan da rana ita yau.”
Da suka zo sallama ne, Inna ta bukaci ta sanar da shi wata muhimmiyar magana. “Sai dai magana ta karshe da ya kyautu a fadawa yaron nan da zai auri Uwani shine; Uwani fa ta taba yin aure!”