AL-AMARIN ZUCI CHAPTER 2

AL-AMARIN ZUCI






CHAPTER 2






Duk inda ran Hajiya Juwairiya ya kai kololuwa to ya baci akan al’amarin Alhaji Mahmoud, yaya za ayi sallah ta Allah, mutum ya dauki kafafuwa ya bar iyalinsa wai yayi tafiya. “Wace irin tafiya ce da muhimmancin yinta ya kai bazaka kasance da iyalinka ba lokacin da aka fi so kowa ya kasance cikin farin ciki? zai dai je koma ina ne ya dawo ya sameni a cikin gidan nan. sai naji dalili, haka kawai”

Ai kuwa washegari sai ga waya wai a je dauko shi a filin jirgi karfe daya na rana, kaman ta share shi taki tura driver amma sai taji lallai ta zaku da sanin inda yaje don haka nan da nan ta fadawa direbansa ya tafi dauko shi, kasancewar ta aiki malam Sule Kasuwa.

Kafin isowar shi kuwa ta tanadi komai da tasan zata bukata na bala’i, shi din kawai take jira ya dawo. Sai dai yanayin da ta ganshi lokacin da ya shigo gidan ne ya hanata sauke duk wani tanadi da ta masa, sai ta koma kallon ikon Allah. Wannan shine a doki mutum a hanashi kuka, shi da bata musu rai shi da shigo musu gida a tsume? 1

Haka tayi ta binsa da kallo ko zai ce mata wani abun amma bai fada ba, da yaransa suka zo masa sannu da zuwa da barka da sallah ma, sama-sama ya amsa yace su barshi ya dan kwanta baya jin dadi ne kwata-kwata. Asalin cikin ran Alhaji Mahmoud idan za a tona shi to idan banda dimbim dana sani marar amfani da ya ke ciki to sai kuma tausayin Aneesa da dalilin kuskurensa ya jefa rayuwarta cikin dimbin garari.

Bayan ya gama tunanin abunyi ne ya daga waya ya kira Alhaji Mustapha akan yana so ya bashi lokaci zai zo gida suyi magana.

****** ******* ******

Ya fito daga dakin taro ne ya samu wayar sa cike da lambar Hajiya, tayi ta kira da yake ya kashe sautin wayar bai ji ba, nan da nan ya kirata. “Hajiya, kiyi hakuri mun shiga taro ne…to ba komai yanzu ma ina kan hanyata in sha Allah”

Bayan ya isa main house ne ya tarad da dalilin neman nashi da sukeyi, shiru yayi yana kallon su da daddaya “Meye kuka zuba min ido haka?”

“Yaya Sagir kai muke jira kace wani abu”

Sagir yace “ke Hamdiya ba ke bace uwar gayya, ai komi kikayi daidaine”

“To Yaya Sagir ka duba mana ko da akwai abun da zaka kara ko kuma za a canza”

Dariya yayi sai da sauti ya fito wanda yakan dade bai yi hakan ba. “yanzu a kan wannan har kara wani zakuyi? Ku baku san zafin neman kudin bane, shi yasa kuka iya kashesu.”

Aisha ta yi tsam tace “Yaya Sagir na mayar zaka ce muyi amfani da wannan idan kaje U.K zaka sayo mata wasu a can, tunda ita ta daban ce?”

“Hajiya na rantse yaran nan sun baci da son banza, ku rufe wannan din ma yayi, idan lokaci yayi ku kai musu akwai wasu kayan a wurina zan hado sai na fito dasu da safe ku sa a ciki”

Dukkan su suka kalli juna suna mamakin wai Yaya Sagir ke tara kayan auren shi, ba daman suyi dariya domin ya hada rai wacce tayi kuskuren yi kuwa ta gane kurenta.

STORY CONTINUES BELOW


Yana fita a dakin kaman wanda aka sace balon balon sai suka dauki tafi da dariya. “Ni ban zaci ko tunanin auren ma yana samun lokacin yin sa ba bare har ya ga abu wai ya saya mata. Ke ranar Yaya Aadil fa ce min yayi da kyar ya ja shi suka je suka ga Aneesan, inaga sai da ya ganta ne ya yi wannan saye-sayen wai wa yaga yaya Sagir na soyayya”

Aisha ta miko hannu suka tafa da Hamdiyya. Hajiya tace “Kun raina yayankun nan da yawa, ko Kamal bakuyi masa haka”

“Hajiya saboda yana ji da mune shi yasa muke ji dashi.”

Ana ta shirye-shiryen auren Aneesa da Sagir gadan-gadan amma sau biyu kacal ango da amaryar suka taba ganin juna duka-duka hirar su idan an hada bai fi na minti talatin ba. Idan da wani abu ma sai dai Aadil ne yake daukan rahoto ya kuma kawo rahoto wa bangare biyun. Har ya zamana Aneesa da su Khazeena dai da Aadil suka fi sabawa kasancewarsa mutum mai raha da saurin sabo, nan da nan ya shiga ran kowa, hatta Zaheeda takan zauna su gaisa kafin su watse su bar shi da Aneesa.

A cikin irin haka ne wataran suna maganar zaban ranar da ya dace, ya dauko nakurar hannunsa (ipad) tukunna ya duba tsarin ayyukan abokin nashi sannan yace “inaga idan aka saka nan da sati shida zaku samu lokaci sosai, saboda zanyi magana da Lawal sakatare ya soke wasu abubuwan daga ayyukan Sagir domin ku samu lokacin zama da juna…”

Tana shiru tana kallon shi yana ta magana kafin tace “Wai ni kam me Uncle Sagir ya maka a rayuwa da kake bauta masa haka? Ka nema masa mata, ka masa zance, sannan ta kaiga hatta ranar auren sa ma kai zaka zaba masa? Wai shin ka fada mini gaskiya ina da wata kima kuwa a wajen uncle Sagir?” 2

Aadil yayi shiru yana kallonta, ya san duk abun da ta fada tana da hakkin fadin shi sai dai inama da zai iya mata bayanin matasayin Sagir a wurin shi? Matsayin sa ya wuce komai don haka yace mata “kwarai kuwa kina da kima da daraja a idanunsa, idan ba haka ba me zai sa har ya aure ki?”

“Ina tantaman haka, mutumin da neman kudin sa da aikin shi sun fi masa komai bana tsamman yasan girman alaqar da take tsakanin dan adam, ina gudun tafka wani kuskuren da na daukarwa kaina alqawarin ba zan sake bari hakan ya faru a gareni ba”

“Aneesa, ba dai tunanin fasa auren nan kikeyi ba?” Aadil ya tambaya cikin hanzari

“Bazan fasa ba, amma zuciyata na raya min abubuwa da dama game da Uncle Sagir wanda kaf ciki ba ko daya da ya zo daidai da tunanina bare ya kwanta min a rai.”

“Anee…” Aadil ya kirata amma kafin nan ta mike

“Allah ya bamu alheri uncle Aadil.”

Ta juya ta shige cikin gida. Dakinta ta wuce, tana tunanin ta san irin wahalar da mahaifiyarta tasha a auren rashin so, kuma bazata bar kanta ta fada wannan rayuwar ba, ba zatayi zaman jiran yaushe zata ga mijinta ba, ko kuma da wani irin yanayi zai zo mata ba. A bari a kan cewa uncle Sagir bayi da lokaci saboda harkokinsa amma idan da ya dauketa wata aba, da ko waya wannan zai rinka kiranta su gaisa. Komai Aadil ne zai mishi kaman wani abun yake tsoro, nan ta tsaida tunaninta “shin ko akwai abun da Sagir Mustapha Daggash yake tsoro?”

Aadil yana barin gidan Jahi ya wuce gidan Sagir. Yana shiga falon shi a nan ya sameshi yana ta duba wasu takardu, hannu yasa ya rufe files din.

“Lafiya?”

Aadil ya dubeshi cikin bacin rai “Don Allah idan baka tsoron fushin su Abba idan har auren nan bai yiwu ba, ka tausayawa yarinyar nan, wallahi tana cikin matsanancin damuwa, tun tana iya boyewa har ta gagara, na fahimci damuwarta kuma tana da gaskiya. Yaya za ayi ace matar da kake shirin aure amma baka damu da ka san ko wacece ita ba? Bare har ka bari ta fahimci ko kai waye ne? ko ka fi so ita ma tana zuwa sai a ce bata da lafiya ta tafi garin su?”

A nan ne Sagir ya mike tsaye, yana dakatar da Aadil “Naji duk abun da kace, amma kar ka kara jawo wancan maganar, Aneesa bata da wani abunyi da wancar maganar kuma bana son ma ta san da ita. Sannan idan kawai ganina ne matsalarta, da kai da ita kun samu babban aiki, saboda a haduwa biyu da nayi da ita na fahimci ko wacece Aneesa, bana bukatar wani karin lokaci da ita domin naci gasar gwajin maza da take so tayi a sikeli don ganin ko ya kamo kafan mahaifinta ko ya dara a wurin daraja mace. Saboda haka idan har ganin Sagir ne matsalarta, daga yau bata da matsala ta saurareni karshen sati.” Ya bude file din sa sannan yace “aiki nakeyi kafin ka shigo if you don’t mind”. 1

STORY CONTINUES BELOW


Aadil yayi murmushi “Ba laifinka bane Sagir. Abu na karshe kuma, ka nemi wani dan aikan don na gama nawa, kudinka bazasu iya biyana aikin da nake maka ba. Allah ya tashe mu lafiya.” Ya sa kai ya fice daga falon a fusace 4

Sagir ya sa hannu ya shafo kan hancinsa da tsakanin idanunsa cikin damuwa. Haka ya kwana cikin rashin kuzari, saboda duk abun da zai je ya dawo bai taba kure Aadil ba, yau kuma a kan maganar auren nan ya bata wa abokin sa rai. 3

Haka akayi kwana biyu ana takun saka tsakanin abokai biyun. Daga karshe dai Sagir ya yanke abunyi daya, ya shirya cikin rigar sweatshirt ja da farar shirt ta kasanta ya hada da wandon chinos kasancewar ana dan taba sanyi, takalmin sau ciki mai laushi ya saka cristallo na Boss, turarensa na kullum ya saka sannan ya fito ya dauki motarsa bai tsaya ko ina ba sai gidan su Aneesa.

Aneesa dai da ta samu sakon isowar Sagir, hada rai tayi a ranta tace “mutum sai iko, shi wato koman sa a tsare yake amma bai damu da tsarin al’amuran mutune ba ko?” wata zuciyar tace “ya san baki da abun yi ne ai ko yaushe kina zaune cikin gida.”

Sai da Khazeena ta sake shigowa tace “Wai bazaki fita bane inji mummy kin ajiye mutum kin tsaya kina ta mulki”

Aneesa ta buge keyar Khazeena tace “kuma duk abin da mummy din ta fada sai kin maimaita ne? Ai ina fitowa yanzu”

“Ba duka fa na fada ba, tace wai an ishe su da sintiri cikin gida sai kace a kanku aka fara aure”

Aneesa shiru tayi kawai tana tunanin wai yaushe ma uncle Sagir kam yazo gidannan da har za a sa masa kahon zuka?” Ta karasa shirinta cikin dan hanzari doguwar riga peach color ta saka ta saka karamin mayafi mai kalar kasa da ya turu (chocolate color), ta fito falon Daddy na ciki ta same shi an riga an kawo masa kayan ciye-ciye.

Kamar kullum gurin zamanta na gado taje ta zauna, kaman zai yi magana ya fasa , bayan sun gaisa ne dakin yayi shiru sai karar na’urar sanyaya dakin da yake tashi a hankali.

“ke nake saurare, na fahimci kin bukaci gani na” 7

Ta rasa me zata ce masa, duk sai ta nemi karfin halinta da uwar surutunta ta rasa, kwarjinin wannan mutumin yayi masa yawa shi kadai. 2

“Na san zuwa yanzu kin fahimci tsadar lokacin SD, idan kin gama ganin nawa zaki iya sanar dani saboda ina da sauran abubuwan yi, kin san ba duniyar Aneesa ce kawai da akwai ba” 9

Wannan kalaman nasa yasa ta dago kanta tace “Wai me kake jin tsoro ne game da sakewa mace, zuciyarka da ruhinka, da har zai sa ka gagara fahimtar macen da zaka aura? Idan kallon ka nake bukata ina tsamman wannan aikin hoto ma kawai zai gamsar. Ina son sanin abun da yake a tare dani da kake kin hada lokacin ka da nawa?”

Ya ma rasa abun cewa jin abubuwan da suka fito daga bakin ‘yar ficilar yarinyar nan. Ya tabbata da Aisha ce ko wata ta fada masa maganar nan da ta samu rabon ta, amma ga mamakin sa ya gagara cewa komai. 2

“ko don kana ganin auren hadi za a mana, ban cancanci ka bani darajar da macen so ta cancanta ba? Ni dai kawai ina son nasan aibu nane tun kafin wanann tafiyar tayi nisa.”

Ajiyar zuciya yayi yace “Na fahimci damuwarki, amma ni ba dalilin da yasa baki gani na ba kenan. Na karbi laifina, amma ki dan kara min lokaci saboda wasu al’amurana su daidaita.” 2

Sauke ajiyar zuciya tayi ko ba komai yau ta fadi cikinta “To Allah ya nuna mana, Ya kuma ci gaba da shige maka gaba a duka al’amuranka”

Sagir sai ya rantse yace ba mutum daya bace tayi addu’ar nan da wacce ta warware shi yanzun nan.

“To an yi min izinin tafiya?”

Abun ya bawa Aneesa dariya tace “Haka ake sallamar zance a birni?”

STORY CONTINUES BELOW


“To kika san ko ni din dan koyo ne?” 2

oh ashe ya iya zolaya shima. A juri zuwa rafi dai…

Ranar dai ga mamakin kowannen su, sun samu ni’imtaccen bacci yayinda Sagir ya kwana yana mamakin kanshi. Washegari ya nemi Aadil suka yi sulhu saboda a cewar sa an kashe wutar rigimar. 2

********** ********** ********

Kaman a cikin mafarki take jin gunjin kuka, can kuma sai ihu da alamar bugu. Hayaniyar mutane ne yasa ta farka don ganin me yake faruwa, hijabi ta zura ta fito falon. Sameeha ta samu ana jibga, da kyar Daddy ya rike mummy yana cewa “Juwairiya, ya isa haka, nace ki barta haka” 2

Nan take jikin Aneesa ya dau bari, “Ni zatayi wa karya? Nan Aneesa tace ta ga me yake wayarta, ta tashi ta karyata sannan yau wannan yarinyar har kin kai ki jawo mana abin magana?”

“Ya isa haka, ki kwantar da hankalin ki sai ayi mata magana, bugu bazai canza komai ba”

“Daddy, ka duba fa, hotonta a wayar Zaheeda kowa yana yadawa ta BB sune ‘yan shaye shayen sheesha a jami’ar su, wannan irin abu da me yayi kama?” 5

Baba Saratu ta daga Sameeha data kukkumbura don bugu tayi ciki da ita. Nan fa Aneesa jikinta a sanyaye ita da kannen ta suka koma daki sidik-sidik, sai dai damuwa ya hana kowa baccin kirki ranar a gidan.

Alhaji Mahmoud ya zauna yana fuskantar Mummy “Ni na sa muku ido ne naga iya gudun ruwan ku, saboda wancan satin anmin waya daga makarantar su Sameeha bata halartar aji, suna son suji ko lafiya don sun shaida min akan sun dade da fadawa matata abun da yake faruwa amma basu ga canji ba” 2

Mummy taji kaman ruwa ya cinye ta “Ashe mugunta ma idan zakiyi sai kiyi wa ‘yar cikin ki, a gabanki tana aikata abun da kinsan ba daidai bane amma kika sakar mata tayi yanda take so. kina sane da bata zuwa lakca amma baki dau mataki ba bare ki fada min ni na dauka, yanzu abun da kika gani ya miki dadi? Ai baza ka kwakume danka ka soshi na fitar hankali ba kayi tunanin duniya zata soshi. Kinga bugun da kika mata zata sameshi sabo ta dauka an juya mata baya an tsaneta ne, tunda tun da ba a kwabe ta ba.” 2

“Wallahi Daddy ni ko da Aneesa tace ga abin da ta gani na zaci ko don ta ji haushin abun da ya faru ne zata mata sharri.”

“Meya faru?” Daddy ya nemi ji. Mummy ta hau kame-kame “ke nake saurare.”

Nan ta kawo labari tiryan tiryan ta zuba mishi “Sannan da naji bata je makaranta ba na zaci na lokaci daya ko biyu ne, a tunanina idan aka takura mata zata fandare” 2

“To gashi yau sake ya mata yawa har ta iya shan maye a idon duniya ba tare da jin kunyar kowa ba.” Daddy ya nisa sannan yace “Daga yau bana son waya hannun kowaccen su, sannan kuma na soke makarantar Sameeha, zan sanar a masallatai idan da wanda yake neman mata ya zo ya sameta” 3

Hajiya Juwairiya nan ta fadi gwiwa kasa tana rokonsa “Daddy kar ka mata haka, ‘yarka ce, na san tayi kuskure amma wannan hukuncin ya mata tsauri, ta dai zauna a hana ta fita a hankali idan an ga nitsuwarta sai ta fito da miji ayi mata aure kar ka mata auren sadaka”

“Waye zai san halayyarta jin ki yazo da sunan sonta yakeyi ya aura? kowani mutum mace ta gari yake nema, yau ko yaranda suke lalata dasu idan ance ya fito ya aura zaice shi baya so. Don haka ni dai na fada miki, ko ta shiga hankalinta cikin nan da watanni uku ko kuma na bada ita sadaka. Ai bata fi karfin sadakar ba, kuma daga yau ita zata rinka duk hidindumunta, zan bawa masu aikin gidan nan hutu idan ta horu na watanni uku zata fuskanci rayuwa ba wasan yara bane, a hakan wai har kike mata kwatan mijin aure mtsssw” Ya shura takalmansa ya yi bakin kofa. 4

Mummy taci kuka har ta godewa Allah, ta dade bata tsinci kanta cikin irin bakin ciki kaman na wannan rana ba. 4

Ranar asabar ne Alhaji Mahmoud ya kwashi iyalansa, suka tafi Zaria domin gaida iyaye, duk da iyayensa duk basu duniya ya riki baffansa a matsayin uba da yake shawara dashi. Ita Hajiya Juwairiyya dai tun wancan ranar sama-sama take da mai gidan, da isarsu Zarian ma yace ita da yara zai bar su a gidan iyayenta shi zai shiga gari yin wasu abubuwan.

Gidan Malam Ibrahim mai iri ya isa, bayan sun gaisa ne yake tamabayan shi iyalin. “Ai tare ma muke na ajiye su can gida su dan huta tukun”

“Ayya yayi kyau, kwanaki mun samu sako, Allah ya biya ya kuma dada rufa asiri”

“Amin-amin, Baba dama na zo ne kan maganar da mukayi kwanaki. An dai tsaida maganar auren ita ‘yar wajen nawa. Kaman yanda suka zo nan akayi tambaya to yanzun sun same mu da maganar rana ne shine nace bari na fada maka, kafin na shaida musu, to amma sai ina tunanin ko na bari a hada ta da ‘yar uwar ta Sameeha?”

Alhaji Ibrahim ya dan jinjina kai sannan yace “To to, ita ma ta fidda mijin kenan”

“A’a tukun na dai”

“To kana ganin za ayi haka kuwa? tunda wannan ita har an tsaida magana mutanen kuma sun nuna da gaske sukeyi, ai kaga baza a jinkirta ba kar suga kaman ana musu wasa da hankali ne. Don haka inaga a fara yin wannan din idan itama ta fidda gwani sai ayi mata nata wani lokacin”

“to Baba, na gode Allah ya ja girma in sha Allah zan shaida musu sai ayi maganar ranar.”

“Allah ya nuna mana, Allah ya sa alheri a ciki” nan dai Malam Ibrahim yayi ta sa albarka.

Can ya je ya dauke su, suka shiga cikin gida sukayi gaisuwa kowa yaga Aneesa kasancewar sau daya ta taba zuwa sai wannan karon tafi gane mutane da dama. kwanan su daya a gidan Alhaji Mahmoud na Zaria sannan suka koma Abuja.Da yammacin ranar juma’a ne ta sanar da su Mama shirin da baban Uwani yayi na maganar aure. +

“Ya tsaida shawarar zai taho da bakin shi nan a daura auren, amma ganin irin bakin nasa bazasu sake ba, yasa nace su daura kawai a can Zaria”

“Ke Halima me ya kaiki shiga maganar, tunda yayi kara saboda a daura a gidan da yarinya ta tashi ai ya gama komai”

“hmm Mama sai kace baki sanshi ba, mutumin da ya kyamaceni da inda na fito me zai sa ya kawo mijin Uwani da dangin sa suzo suma su kyamaceta?”

“Ke dai dadina dake kina da riko, abun da ya wuce ba ya wuce ba?”

Inna Halima jikinta yayi sanyi don Mama ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, saboda haka tayi shiru da manganar, amma ita dai tace tunda ya san ‘yarsa yaje can ya daura mata aure, ita addu’arta ma kawai ta wadatar ba sai taje ba.

Malam Habu dai haka suka sata a gaba suna bata baki, daga bisani aka tsaida magana za a zo Kunuwal daurin aure.

“Hajiya, don Allah ki bari haka nan, duk zamu aika musu, su Inna Munira ma sun shirya komai yanda duk wanda aka gayyata bazai samu mishkila ba.”

“to ai dole ne mutum ya duba, tunda kinga baza ka tara jama’a kazo kaji kunya ba ko?”

Humaira tace “ho, Hajiya duk farin ciki ne, ni kaman Yaya Sagir ba dan fari ba”

Hajiya bata bata amsa ba, ta nufi falonta inda ta bar wasu baki suna jiranta.

Sagir ne ya shigo dakin yana nemanta Hamdiyya tace “Tana tare da baki a falonta.”

“Kai ni fa shi yasa bana son biki-bikin nan, duk a bi a takura mutane mutum da gidansu a hana shi sake” 4

“Yaya Sagir don kai fa a ka taru a taya ka farin ciki,”

“Naji, ina Azhaan tun shigowata ban gan shi ba na kuma hadu da maman shi a falon Kasa”

“Yaya Kamaal ne ya fita dashi.”

Ya nemi bakin gado zai zauna sai yaga kaya “Donn Allah ki kira yaran nan su kwashe kayan nan sai ku bar guri wani iri kaman tashin duniya?”

Hamdiyya ta kula dai kaman akwai abun da yake damun yayan nata don haka ta nemo masa Hajiyar ta samu ya fita ko zasu huta da mita.

Anty Sameera ce ta shigo dakin “lafiya kuwa yau naga Yaya Sagir a birkice, yana tamabayata Azhaan, Kamaal ya dawo dashi amma bai tsaya ta kanshi ba kuma ya fice a gidan”

“oh kema dai kya fada kaman wanda ya zare, haka auren ke razana maza harda irin su Yaya Sagir?” Anty Sameera ta samu kujerar dake gaban gado ta zauna, “kika san ko Antyn naki ce ta razana shi? tunda ai kin san shi ba daga nan ba”

“Anty Sameera kenan, sai kin ganta very innocent, haduwar mu ta farko ta burgeni, bata da wani irin iyayi da eye service, kuma yarinyace wallahi yayi dacen mata tsakaninta da Allah take zama da mutum kuma ta fada maka cikin ta”

STORY CONTINUES BELOW


“Ai kice yayi sa’a ma, to me zai tayar masa da hankali, sai dai naji ance iyakarta sakandire tayi ko?”

Hamdiyya ta san halin Anty Sameera da damuwa da matakin rayuwa don haka sai tace “Ai ba daga nan take ba, sai ki ga wanda batayi makaranta bama idan ta samu tarbiya, tafi akan wata mahaukaciyar mai digiri din, mu dai fatan alheri kawai zamuyi musu.”

“To Allah ya basu zaman lafiya”

“Ameen.” Azhaan ne ya shigo da gudu ya dare jikin Hamdiyya, nan suka ajiye wannan maganar.

Aadil ne yayi ta sintirin shirye-shiryen saukan baki a Gombe aka kama masaukai. Idan ka ganshi zaka zaci shine angon don hidima. 4

Tun ranar laraba Aneesa da su Khazeena suka kama hanyar Kunuwal, Hajiya Juwairiya kuwa tace zata zauna saboda kula da sha’anin nan Abuja da kuma baki, randa za a taho da amarya.

Gidan su Sagir kuwa Hamdiyya, Anty Sameera, Hajiya Munira, da Hajja Baana wata kakar Sagir ne suka tafi don taho da amarya amma su ana gobe daurin auren suka tafi.

A Kunuwal Inna Halima da Malam Habu sai inda karfin su ya kare wajen tanadar abun tarbar baki, musamman tun ran litinin Malam Habu ya je Gombe domin sayayyar kayan abinci, Alhaji Mahmoud ya bada isassun kudade ko da wani abun zai taso. Haka Inna ta dunkula da kudaden da ta jima tana ajiyansu ta damkawa ‘yar uwarta Zainabu da dogon list ita da kanwarta Salma suka shiga suka hada kayan Dokke. koda Daddy yaji shirye shiryensu yace duk abunda za akaiwa Hajiyar sagir su bari sai a saye su a Abuja, don haka duk kayan dakin da ake sakawa a ciki ya saye su tamkar wa wata amaryar za a kaiwa.

Dakin Aneesa aka gyarawa bakin da suka taho daga bangaren ango, an cire gadon bononta da ‘yan tarukucenta aka sa katifu biyu akayi shimfidi na alfarma. Cikin tarun Inna Halima ta bude sabon kafet ta shimfida musu. Inna Munira da Hajja Baana kuma aka ajiye su a dakin Inna yayinda ita Innar ta koma dakin Malam. Abinci kuwa a madafinta ta samu mata daga gidan Baban Zainabu masu yi musu aiki sun saba da yin aiki irin na maraya, don haka su suke ta daurawa suna saukewa ita kuma tana fama da baki. Ba a dadewa an ajiye musu wancan an dauke wannan. 3

Amarya Aneesa kuwa da su Khazeena can gidan Mama suka tare aka bude musu daki guda aka gyare shi tsab shima. Ita dai Khazeena abun sha’awa yake bata, komai fes-fes ga randunan Mama na kofar daki ko bata jin kishi sai ta fito shan ruwa wai a dole, kan kace meye har tayi kawaye a Kunuwal.

Falmata ma tana nan da yaran ta biyu ana ta hidima da ita.

Da dare sun zo kwanciya ne aka shigo musu da lanta saboda babu wuta an dauke, Anty Sameera tace “Don Allah, Hamdiyya ina Yaya Sagir ya samo mata a irin wannan kauye haka? Yanzu haka zamuyi kwanan zafi?”

“Kin san ance matar mutum kabarin sa, don haka ko cikin rami take sai kiga Allah ya kawo sanadi sun hadu. ki ga dai ‘yan mata har da zaurawa yanda suke ribibi kan Yaya Sagir amma sam shi ba wacce take gaban shi, da ikon Allah Aneesa na zuwa sai yayi na’am”

“Haka ne kam, naji Hajiya sai da tayi da gaske tukun ya tsaida maganar auren ma.”

Hamdiyya dai ta kula har da guntun kishi yake damun Anty Sameeran kasancewar tun bayan hatsarin Yaya Usman da Yaya Jamal a jirgi da yayi sanadin rashin mijinta wanda dan kanin hajiya ne da ya girma a hannunta, ya barta da tsohon ciki. Ta zauna a gidan Hajiya har ta haihu, to a wannan lokacin Yaya Sagir na fama da tashi matsalar don haka akayi tunanin ko zai aureta ya ci gaba da rikon ta da na yaron ta amma Sagir din yace “A barta tukun ta gama fita daga alhinin rashin mijinta, idan tagamu da wanda take so sai ta aura ni zan mata komai da ita da danta.” daga nan magana ta salwance ba yanda Goggonsu Yaa fanna wato mahaifiyar Anty Sameera bata dage ba kan maganar amma magana dai ta bi ruwa. Tun wancan lokacin ita kuma batayi wani auren ba sai gashi yanzu da iliminta, da wayewarta da komai Sagir ya tsallaka zai yi aure, wa zai aura? wata ‘yar kauye wacce bata san komai ba. 16

STORY CONTINUES BELOW


Ranar daurin aure ne da safe aka shiga shigowa da Kususuram wato lefen Aneesa kaman yanda yake a al’adar kanuri, abun ba acewa komai don kaf masu kallon kayan basu taba ganin abu kwatankwacinsa ko kuwa mai tsadarsa ba. Don haka Uwanin Inna dai tayi goshi.

Wannan satin dai Kunuwal yaga al’ummar da bai taba gani ba, yara da manya kowa bikin Uwani ‘yar gidan Malam Habu ne a bakin sa. Wasu suce ai asalin babanta mahaifi ma yazo wani hamshakin mai kudi. Inna kuwa sai gata tana bada ruwa ga matan da suka ce ai cikin shege tayi ta haifi Uwani.

A wani bangaren sai taji farin ciki da cin galabar da akayi akanta, ko ba komai dai garin kunuwal sunga gatan uwanin Inna.

Nata’ala kuma yana zaune duk abun duniya yabi ya isheshi, yanzu kam lalle yasan ya sallamar da uwani tunda yaga jiga jigan da suka taho wannan sha’anin yasan abun ba na yin shi bane. Tun da Uwani ta sa kafa ta tafi yake ta faman da na sanin hakan har jiya bai cire tsammani ba, amma daya ga komai yau a idanun shi sai ya tuno maganar da Innar Uwani ta fada masa lokacin da ya nace da bibiyar Uwani duk inda ta shiga a gari.

Kwanan shi uku kenan kofar gidan Malam Habu yake wuni ko Uwani ta fito su tattauna, yana zaune a soro sai ga Inna Halima ta fito da mayafi har saman kai.

Inna ta dubi Nata’ala tace “wai ni kam saki nawa kayiwa Uwani?”

Nata’ala yana shiru sai wurli-wurli yakeyi da idanu.

“tambayarka nakeyi” ta fada cikin daga murya

“In… Inna saki uku ne.”

“To, ina tsamman dai-dai gwargwado ka san addini, nima kuma na sani, idan ma baka san addini ba ka dai san duk duniya ba inda ake saki uku a kuma ci gaba da zama da mata ko? To don haka nake son kayi hakuri da Uwani, Ka yafe ta saboda babu kome a tsakanin ku.” Kan Na Ta’ala na kasa ya ci gaba da sauraro.

“Ni sakin da ka mata bazan ce maka bai mini zafi ba, saboda ba uwar da zata so ‘yarta ta bar darajar dakin aure. Amma abun da yafi mini ciwo shine, yanda yarinyar nan ka san tana dauke da juna, wannan abun ya faru, sannan bako kunya ko tsoron Allah kuka mata sharri, kuka bata mata suna wai ‘yata Uwani ce ta yaudari wani zuwa daki, bayan kai ka san ko wacece matarka. Hakan duk bai muku ba, ka dauki tsumagiya kayi ta jibga kaman an aiko maka wahayi, ka sa kafa ka tsallaketa a halin ha’ula’i, har hakan yayi sanadin rashin dan tayin ta. Idan zan yafe maka sakin da kayi wa Uwani na wulakanci, bazan yafe maka bar min ‘yata da kayi a halin kaka ni kayi da kayi ba. Sannan ina so ka san da cewa kaje ka adana yanda kake adanan kayan sakawarka a akwati rayuwace, kaima zan maka addu’a Allah ya baka haihuwa kuma za ayiwa naka.” 8

Tana fadin haka ta share kwallan da ya gangaro gefen idanunta, ta bar Nata’ala a zaure yana ta faman ruzgar kuka yana kaico! ya kwashi mintuna da dama yana tunanin asarar mace da yayi a wurin Uwani, shi kanshi shaida ne tunda ya auri wannan ‘yar talikar, bata taba barin bacin rai ya same shi ba, itace bashi abinci a baki, itace share masa gumi da yi masa fifita, sai yayi bacci take sa hakarkarinta a kasa. Lokaci daya ya lalata komai, tun wancan lokacin kuwa Aneesa bata sake sha’awar aure ba, sannan kuma ko da tayi sha’awar ma wa zai taya?

Uwani ‘yar Halima ai gado tayi, wannan kalma ba karamin bakanta ran Uwani yakeyi ba, duk abun da ake fada akanta baya damunta, irin abun da ake fada kan innarta, ba yanda Uwani batayi da Innarta ba akan ta mata bayanin ma’anar wannan kalma amma sai Innarta ta shiga share kwalla ko kuma tace “ba komai rayuwace komai zai wuce.”

kai ba aje ko ina ba abun da akayi shekara da shekaru ana boyewa ya fito gari wato “Inna Halima taje birni da sunan aure amma tayi cikin shege mijin ya koro ta da tsohon cikin da ya gane ba nashi bane.”

Lallai ne mai hakuri yakan dafa dutse har ma yasha romonsa, garin da suka kyamace su, suna kyarar su yau sune suke bidiri kowa yana son ace yasan Malam Habu da Zuri’arsa.

STORY CONTINUES BELOW


An daura auren Sagir Daggash da Aneesa Mahmoud , Malam Habu ne ya bada ta. Tsabar farin ciki hatta Baban Halima sai da yayi kwalla. Aneesa kam ana can gidan mama sai fama akeyi da ita, akan ta tashi ta shirya saboda yau zasu wuce, amma sam hawaye kaman an balle famfo. kowa yayi rarrashi har ya gaji, don haka aka sanarwa Innarta, gashi ita kuma tana fama da baki. Hamdiyya tana zaune sun gama shiri suna jira a taho da amarya a kama hanya ne sai ga wayar Sagir.

“Hamdiyya, mikawa Aneesa wayarki nayi ta nemanta bana samu”

Hamdiyya tayi murmushin jin dadin jin yanda yayanta yake marmaarin ji daga amaryarsa. Fatansu daman ya kasance mai farin ciki da wannan hadin da aka masa domin kuwa ya cancanci farin ciki a rayuwarsa ko don yanda farin cikin jama’a ya dame shi na kusa dashi da kuma na nesa.

“Bata nan tana gidan kakarta amma bari yara su kaini sai na bata”

Amina aka sa ta raka Hamdiyya, sai da suka isa gidan Mama ta tarar da artabun da akeyi, haka dai da kyar ta saurareta, har ta amsa wayar.

“Aneesa, lafiya me yake faruwa naji muryarki haka?” Shiru tayi, ta yaya ma zai mata wannan tambayar bayan yasan yau ranar kukan ta ne?

Sagir ya runtse idanun shi ya bude, kar wannan yarinyar ta janyo masa matsala mana, yanzu meye damuwarta ko dai daman bata amince da auren bane? to ma wai wa yace mata sai mutum ya amince ne? Dadine ma ya mata yawa bata san meye damuwa ba tukun. Da yaga tunani ba inda zai kai shi ne yace “Na kira na fada miki mu zamu kama hanya, zamuyi reception a Gombe sannan mu wuce. Sai kun iso.”

“To, Allah ya kiyaye hanya” abun da kawai ta iya fada kenan, zai kashe wayar ne yace mata “Amma ina son ki bar kukan nan haka ya isa kina jina ko?” 6

Gyada kai tayi kamar yana ganin ta sai kuma ta tuna bazai san ta amsa masa ba don haka tace “eh.” Ta kashe wayar, ya cire wayar a kunnensa ya duba ya ga ta tsinke, ya girgiza kai a ransa yace “wa yake tsinke wayar SD ba tare da yace ya gama ba? Aadil ka hadani da gamo na” 12

Sai wurin karfe shabiyu da rabi aka samu amaryar ta nutsu sannan kakannin ta suka mata nasiha, aka tafi da ita gidan malam Habu can din ma dai hakan ne. Da kyar aka banbareta daga jikin Innarta, aka sata a mota, su Amina da Suhail kaman su shige su bita suke ji. Mota guda ta daukar kaya aka shake ya bi bayan ayarin suka dau hanya.

Sai dare suka isa Abuja, can gidan Hajiya Khadija aka wuce saboda yanzu Uwanin Inna ta zama Aneesan Sagir. Farkon zuwan Aneesa birni tayi tunanin gidan Daddy gidan sarki ne, yanzu kuwa da ta ga gidan su Sagir sai ta rasa da me zata hada shi, don tun da take bata taba ganin gida mai girman gaske da kyau ba irin na Alhaji Mustapha Dagash, ginin zamani ne sosai wanda yafi kama da gine-ginen ingila. A wani bangaren na gidan ne aka shirya mata masaukinta, amma da yake bata da yawan kawaye, daga itane sai Falmata, Baba Saratu, Sameeha dasu Khazeena a dakin. Falmata ta samu mijinta ya barta ta taho, amma ta baro yaran wurin Innarsa. Saboda masu ganin dakin Aneesa daga Kunuwal zasu koma bayan kwana biyu sai ta bisu su koma Kunuwal tare. Dakin sai kamshin turaren wuta da sanyin A.c yake yi. Ga dai abinci nan an ajiye kula-kula sai dai ka dibi wanda kake so ka bar na bari, abun sha ma dai kala-kala, dakin ya sha shimfidu na alfarma masu laushi daga zanin gadon har zuwa kilishin kasar dakin. Akwai bandaki a cikin dakin wanda shima dai sai kamshin yakeyi. 6

Baba Saratu ce tace “to, ni zanje gida, Hajiya ta turo malam Sule, Sameeha zaku wuce ne ko kuna nan sai da safe?”

Sameeha ta yamutsa fuska alamar gajiya sannan tace “kai Baba Saratu zamu koma kawai gobe idan Allah ya kaimu sai mu zo mu raka ta gidan nata kafin nan ribibi yayi sauki”

Aneesa ta dube su idanu fiki-fiki “yanzu tafiya zakuyi Baba Saratu?”

“eh, can ma gidan akwai ayyuka kuma su Hannatu ne kadai abubuwan zasu musu yawa, da safe idan mun dan rage zamu dawo in sha allah, ko da akwai abun da kike bukata sai a taho miki dashi”

STORY CONTINUES BELOW


“eh, cikin wardrobe dina akwai ‘yar karamar jaka zaki ganta a shirye ita nake so.”

Falmata ta mike tana musu sai da safe har bakin mota ta rakasu garin dawowa ne sai da ta bata. Da tambaya ta samu ta dawo dakin da aka ajiye Aneesa ta sha kallo a wannan gida na alfarma.

“Uwani, kinga duniyar da Allah ya saka ki cikin ikon Sa? ai na sha fada miki Allah ba azzalumin bawanSa bane sai wanda ya zalunci kansa, kinga yau ranar hakurin ki yazo. Da ikonSa Ya daga ki cikin kyara da rashin wadata da kuma kyama na jama’a yasa ki cikin rayuwar wadata da soyayya da kuma daukaka, me ya saura banda ki gode maSa?”

Aneesa murmushi tayi kawai, Falmata abun ya bata mamaki “wai ke sai naga kaman ba kya murna, haka can gida kan mu taso ki kayi ta wani kuka me gigita mutum. Shin ba kya son wannan auren ne? ko kuwa Na Ta’ala yafi miki?”

Aneesa tayi saurin dago kanta tace “Don Allah rabani da wancan sunan, ko tuna fuskar shi bana son yi”

“to ai yanayin kin ne sai naga kaman kewar sa ya hanaki sakewa ki ji dadin abun da kika samu kanki a ciki”

“sam ba haka bane, kawai ina tunanin rayuwata ne”

“Ai yanzu kam tunani ya kare a wurinki sai dai ribatar abun da kika samu, mu kuma muce me?”

“Falmata ki godewa Allah ko ba komai kina tare da Garban ki, yana son ki yana ji da ke komai yana miki kuma kina ganin shi duk lokacin da kika so, ya san hakkin ki. Duba da irin halin mutanen mu na karkara amma baya barin wani ya shiga masa al’amuran gidan sa ai ko wannan ma abun so ne.”

Falmata ta nisa tana shakar daddadan kamshin tuararen wutan tace “shi yasa ake so mutum kullum ya dubi na kasa da shi a rayuwa zai dada godewa Allah”

Aneesa tace “kar kiga wannan katon gidan, ko kayan da yake cikinsa ko kuwa babban birni ko kyale-kyalen da ke cikin sa, ki duba AL’AMARIN ZUCIN ma’abota wannan abubuwa shine muhimmi. Ni yanzu tunda aka daura auren nan har zuwa isowar mu zuwa yanzu kinga alamar walwala a tare dani? kinga alamar angon yana da lokaci na? Ki duba fa ko isowar mu bai tambaya ba.”

Falmata tace “lalle Inna ta miki nisa. Har zaki iya bude baki ki aibanta mijin ki ko abun da yayi miki?”

“Ba haka bane, ni ina tsoron kar ya kasance baya so na ne aka masa dole ko kuma akwai wani abu a tare dani da baya so, a idanun ki nayi auren so, kinga yanda ya kare min bare wannan da kyautana akayi masa. Sannan hakan yana sa nayi tunanin yanzu ma kenan ina kuma idan ya samu labarin duhun da yake cikin rayuwata?” 3

“Mahaifinki yafi ki hangen nesa tunda kuwa ya hadaki dashi , addu’a zakiyi Allah ya sanya alheri ya kuma baki ikon kyautatawa mijinki, har ki rinjaye shi ya fada tsundum cikin soyayyarki ya zama sai kin bashi daman matsawa daga gefenki”

Falmata ta bawa Aneesa dariya da wannan maganar “ameen”.

Sunyi ta hira suna daukan shawarwari daga bisani sukayi shirin kwanciya, wajen karfe sha biyu Aneesa ta ji bugun kofa a hankali. Ganin mai shi bai shigo ba yasa ta mike cikin yanayi na bacci ta yafa mayafinta sannan ta bude kofar. Ganin shi da tayi a tsaye ne ya haddasa mata wani irin rawar jiki da bakin ta ma ya gagara magana. Da ya kula ta sa masa ido kamar wata (zombie) yasa ya dawo falon da ke manne da dakin ya zauna a kujera, ba tare da yace komai ba ta fahimci yana son ganinta ne don haka ta jawo kofar a hankali don kar ta tada Falmata.

A kasa nesa da kafafuwansa ta zauna cikin sanyin murya tace masa “ina wuni?”

A hankali ya dubeta, ya katse mata baccin ta, da ma ya barta sai da safe ya bar mata sakon to amma yaga rashin dacewar hakan ne shi yasa ya zo.

“Lafiya, kun iso kalau ko?” ya fada cikin muryarsa mai taushi da natsar da mai saurare ya so jin abun da yake fada. A lokacin Aneesa taji haushin daura masa laifin rashin yin hakan da yayi, watakila yana ta fama da jama’a ne.

“Eh, Alhamdulillah”

wai ita wannan bata magana ne, sai amsa kawai ta iya bayarwa, Sagir ya tambayi kanshi. “ina fatan babu wata matsala ko?”

“Eh. su Hajiya duk sun wadata mu da komai, Allah ya saka da alheri”

“To, yayi kyau daman na taso ki ne saboda wani aiki ya taso min wanda zai sa dole kasancewata a wurin yana da muhimmanci, don haka gobe da safe in sha Allah zan tafi amma ina sa rai bazai dauke ni lokaci mai tsawo ba, kiyi min afuwa.”

Aneesa kam Allah Yana gani bata san daga ina ba sai jin hawaye tayi sun gangaro mata, kanta na kasa tace “Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, Allah ya bada sa’a.”

“Ameen,” ya fada hade da mikewa, tana zaune a inda take ba zato ba tsammani taji ya sa hannu ya shafi saman kanta, sannan ya wuce cikin takunsa na kwalisa. Bata san iya lokacin da ta dauka a wurin ba tana jiran tsikar jikinta ya kwanta, a hankali ta mike ta koma daki.

Falmata ta juya tace “lafiya, ke da wa naji kuna magana?”

Aneesa ta danyi murmushi kasancewar duhun dakin ya tarewa Falmata ganinta tace “ba kowa, ruwa naje sha a falo”.

Zuciyarta ta rasa matsayar da zata kasa uncle Sagir ta ajiye, a zahiri dai shi mutum ne da al’amura da dama basu gabanshi wanda kuwa harda ita a ciki, a bangare guda kuwa sai taga kaman akwai abun da yasa ya ke kasancewa hakan musamman idan lamarin ya shafeta ne, koma dai menene Sagir Daggash wani babban aiki ne a gabanta da sai ta zage damtse zata warware. Yanzu me mutane zasuyi tunani? An kawota gidan miji da kwana daya ango ya tafi ya barta, haka ta kwana cikin tunani.CIKIN DAKIN TARO A LEGAS +

“Amma ta yaya kudade masu tarin yawa haka zasu bata a cikin tsawon watanni biyar kacal, dole a bi duk inda suka shiga a samo su, Auwal ina son ka min magana da John na security office, kowa ya hada duk abun da ya dace bazan bar garin nan ba sai an kaddamar da binciken da za ayi don ganin yanda mukayi wannan sakacin.” Sagir ya dubi akawun kamfanin su na kera magani da bada shawarwari kan harkan magunguna, “Kuma ko da wasa bana son hakan ya sake faruwa. Don duk wanda sakacin yake daga gareshi zai iya rasa aikinshi”

Bayan shugaban yayi shiru ne ya bada dama ga sauran daraktocin kamfanin su bada albarkacin bakin su da shawarwari waken shawo kan wannan matsalar.

Sai da suka sallami kowa ne, taro ya watse suka zauna shi da Mr. Ahmed Adebayor suna kara tattauna matsalolin da suka shafi kamfanin nasu.

“Arch. Sagir, wadannan kudadaden ba kanana bane, a tsawon watanni biyar, kana ganin yanda muka bullowa wannan al’amari yayi? Wani amsa zamu bawa investors din mu da kuma wadanda suka amince da aikin mu?”

“Na sani Mr. Ahmad shi yasa nake son nayi maganin wannan abun ta hanyata. duk wanda ya ke wannan aikin (diverting) kudin kamfanin nan, dole yana da wasu hanyoyi na musamman da ya samu hanyar yin hakan, wannan ya nuna min cewa wani mai babban matsayi ne a wannan kamfanin. Don haka wannan mitin da na tara na kira kowa ne saboda duk wanda yake kwashe kudaden nan zai nemi ya rufe takunshi(he will try to cover his moves) wannan zai taimaka mana sosai, da kanshi zai fallasa kanshi zai yi wani dan karamin kuskure, akwai abubuwa uku da nake son na bincika kafin nan”.

Suna gama tattaunawa (apartment) dinsa da yake Ikoyi ya koma, sai a lokacin gajiyar ya karasa sauko masa, wanka yayi ya nemi abinci yaci. Sannan ya dauki wayarsa, ya samu missed calls da yawa wasu na kostomomin su ne, wasu kuma abokan sa ne yasan da dama sun kira ne su masa murnar aure. Sai da wannan tunanin ya zo masa ne ya tuna, nan da nan ya nemi lambar wayarta. Amma kaman kullum tana ta ringing ba a dauka ba yaja tsaki “wai me yasa aka kirashi mobile idan ba a tafi da gidanka dashi oho, bakauya kawai.” Aisha ya nema ganin suna tare zai fi saukin samunta.

Sun gama shiryawa za a kai Aneesa gidan Sagir ne wayar ta shigo, Aisha ta shigo ta mika mata wayar, tana karba sai da ta tuno sallamar su na jiya, amma kuma sai ta tuno yanda ya tafi ya barta “Yaya hidima? Sun barki kin huta kuwa ko dai suna ta faman miki abubuwan al’adu?” 6

Duk da tana cikin fushi amma murmushi tayi mai karamin sauti sannan ta toshe bakin wayar ta matsa can kuryar dakin sannan ta ci gaba da magana.

“Ai jama’a rahama ne, yaya aiki?”

A gajiye ya amsa mata “lafiya, don Allah ki tafi ko dakin Hajiya ne ki kulle kiyi bacci idan kika biye musu, haka zaki yi ta fama da ciwon kai” 7

Taso ta fada masa ran Hajiya ya dan sosu da tafiyar sa amma tayi shiru. shi kuwa a bangarensa tunanin irin artabun da sukayi da Hajiya da taji baya gari yakeyi, akan hakan har tace masa an fasa kai Aneesa sai ya dawo ya dauki matarsa. Da kyar yace tayi hakuri baya son mutane ma su san baya nan wata kila ya juyo washegari da yamma.

“Muna shirin tafiya ne ma yanzu…”

Oh, za a kaita gidan shi ne fa ko? nan take sai yaji wani iri “kuyi hakuri, na kusa kammala abubuwan da suka kawoni, idan akwai wani abu ki nemi Aadil. Me yasa bakwa son rike wayar ku ne a hannu ayi ta neman ku ba a samu?” 6

STORY CONTINUES BELOW


“Tana cikin akwati ne kayi hakuri”

“Akwa… akwati dai? don akwati akayi waya? kun faye shirita da kauyanci” ya dan ja tsaki. Ta san ranshi ya baci don haka tace “Kayi hakuri bazan sake ba.” 8

“To, ki kiyaye, sai da safe” ya girgiza kai yaja tsaki wannan wace irin yarinyace? 7

“Allah ya kaimu”. Wannan kusan itace maganar da tayi da uncle Sagir mafi dadin saurare a wajenta saboda yanda ya nuna kulawar sa a gareta, duk da dai ya kirata bakauya. 3

An kai Aneesa gidan Sagir dake Jahi, babban gidane da ya tsaru sosai; gidan sama ne na zamani, dakuna uku a sama ko wane da bayan gidan sa sai falo daya mai ban sha’awa, a kasa kuma faluna biyu ne da dakuna biyu sai dakin karatu da kicin. komai an tsarashi na zamani, komai na bukatar rayuwa akwai shi agidan hatta cokali sun same shi a cikin gidan. Don haka kayan sawanta da na amfaninta kawai aka jera mata wanda su Inna suka mata da wanda Daddy ya mata, kayan aurenta kam duk suna ajiye ko daya ma bata dinka ba. Sai kayan dakinta da bata san inda aka kai mata su ba, nan ma ranta ya baci wato an raina mata abun da iyayenta suka mata kenan.

Hankalin Hajiya Juwairiya ba karamin tashi yayi ba, ganin irin arzikin da Sagir da ‘yan uwansa suka mallaka, wanda har zai sa duk dimbin dukiyar da Daddy ya narka ya sayi kaya ace a adana su idan ya tashi za a zuba mata a wani gidan nasu, gashi ba abun da yafi damunta irin yanda taga da gaske matakin da Daddy ya dauka kan Sameeha ba sassauci, hidiman bikin nan kaf da akayi anyi wa kowa dinkuna na alfarma na fitan biki, amma bai bar musu kudi a hannun su ba saboda yace abun da yake kara bude musu idanu kenan, yarinyar har tausayi take bata.

Duk iya kokarinta don ganin bikin nan ya kasa amma sai da akasin hakan ya faru, Allah kadai yasan me Halima taje tayi a kauyen su da hankalin kowa ya koma kan ‘yarta. Haka dai tayi kwanakin bakin ciki a wannan lokaci na bikin Aneesa, don haushi ma ta gagara zuwa ganin gidan nata, yara sun dawo sai koda gidan sukeyi da yanda akwai wasu abubuwan jin dadi na zamani da basu ma san shi ba cikin gidan. kwafa tayi tace “hmmm, aikin banza, don ya lodo mata wannan kayan an gaya masa ta san me akeyi dasu ne? ko bai san ta wuro ya dauko bane?”

Khazeena tace “mummy me yasa ba kya son Aneesa ne? ni banga me take miki ba” 4

“da Allah rufe min baki, baki da wayo baki san inda yake miki ciwo ba, da kyar na samu uwarta ta bar gidan nan saboda kar ma ta haifeta har mahaifinku ya fi son ‘yarta akan ku amma aje-aje sai da uwarta tayi ta surkulle aka dawo da ita, kuna ji kuna gani tafi ku daraja a gidannan ku da gidan ku, an bata miji mai kudi (multi billionaire) yayinda kuna gani aka maida Sameeha tamkar ‘yar aiki a gidannan. amma ba wani abu nan da kwana biyu ne, auren ma ai zamuga inda zaije tuni zai fahimci an shuna masa matar da bata da ilimin komai banda kauyanci da jahilci ba abunda ya cika kwakwalwar” 4

Khazeena tace “Amma mummy tana da kirki fa, kuma ban taba ji ta zage mu ba, duk da ta san kin rage mata sayayyar da Daddy ya bada kudi ayi mata, amma bata taba cewa komai ba. Haka lokacin da aka hana Sameeha zuwa makaranta sai da tayi kuka saboda ta san muhimmanci ilimi kuma tana so muyi shi sosai, mu amfana.”

“hmm, yaro man kaza, duk wannan munafurci ne ke kam ai tayi nisa a jikin ki bazaki gane hakan ba”

Zaheeda tace “Dama mummy ai bata lokacin ki kike yi wurin yiwa Khazeena wannan bayani, ana fada mata gaskiya tana nata, idan don itace kaura ma zatayi gidan Aneesa”

Khazeena ranta ya baci, me yasa ita karamar cikinsu ita kadai take ganin gaskiyar abubuwa? Don haka ta mike ta bar dakin Mummy din.

Falmata dai da masu zuwa kallon dakin Aneesa duk sun tattara sun koma Kunuwal, labari kuwa ya gama baza Kunuwal Uwanin Inna kam tana aljannar duniya.

Hajiya Khadija sai fada takeyi “idan banda a wurin yayanku ina aka taba kana daura aure ka dauki kafa ka tafi ka bar mata, ina laifin idan tafiyar ta kama dole to ka dan saurara a watse sai ku tafi tare. Aisha sai ki shirya ki je ki tayata zama kafin ya ga daman dawowa”

STORY CONTINUES BELOW


Abba ko dake Sagir ya masa bayanin muhimmancin tafiyar sai bai damu ba yace musu “Tunda dai zai dawo ba guduwa yayi ba ai sai kuyi masa uzuri tunda kamawa tafiyar tayi”

Tafiyar su Falmata ba karamin kewa ya haddasawa Aneesa ba duk da Hajiya ta turo Aisha su zauna kafin ya dawo, Sagir dai yace mata zasu dawo tun daren jiya amma gashi yau har rana tayi shiru ba labari, wayar sa kuwa ita bata adana lambar ba don haka tayi tunanin kiran Aadil don taji ko lafiya. Amma kuma ta fasa, yaya za ayi ta bari wani yasan ko lambar mijinta bata da shi a wayarta. Haka dai ta wuni a darare, Aisha ta taya ta sun kimtsa wuri, hankalinsu ya zo daya nan da nan don Aneesa ta kula Aisha mai sanin ya kamata ne sannan tana da faram faram, tana kallonta ne tana gwada yanda banbancin ta yake da yayanta, da sam shi bayi da wannan sakewar.

“Anti Aneesa kinyi shiru, yaya dai ko dai duk tunanin Yaya Sagir din ne?”

Aneesa tayi saurin sadda kai kasa duk da dai ba da wata manufa take tunanin Sagir din ba dai tunaninsa takeyi.

“Me zai sa ni kuma nayi tunaninsa?”

“Ke kuwa kike da dalili, tun jiya idanun ki suke kan kofa, to ki buga masa waya mana kiji ko ya taso?”

“A’a na san ma suna hanya tunda yace zasu dawo ai zasu dawo da yardar Allah, sai dai jiya yace min”

Aisha tayi dariya “ho, Antina kenan kin dai damu kawo wayarki sai mu kira shi, tawa ba caji.”

Aisha ta fada yayin da ta daga wayar a hannun kujera. Aneesa tayi shiru tana tunanin abunyi kafin tace “lambobin waya ta sun goge ko zaki sake sa min lambar tashi?”

Aisha ta lallatsa lambar Sagir ta kuma adana mata kafin ta danna, sai da ya fara kara tukun ta mikawa Aneesa. Yana dagawa ta matsa gefe “Hello..” har Sagir ya fara magana sai kuma yaji muryarta cikin amo mai sanyi tace “Hello”

Runtse idanunsa yayi sannan ya bude su cikin rashin sanin mafita yace “kun jini shiru ko?” ya fada cikin murya mai taushi.

“Daman na kira ne naji ko lafiya? kace kuna tahowa jiya amma bamu ganka ba”

“Ban kammala abun da naje yi bane sai yau da safe amma yanzu haka ma ina filin jirgi zamu taso. Aishan tana nan ko?”

“Eh tana nan, Allah ya kawo ku lafiya”

“Ameen” ta ajiye wayar sannan ta dawo ta zauna a falon “Aisha tace lalle abun sirri ne wato shine harda boyewa”

“yace wai suna filin jirgi”

“Eo, bari na fadawa Hajiya sai a saka abincin dare dashi tunda mun san yau zai dawo”

Aneesa tayi maza tace “A’a da kin barshi kawai, tunda na ga akwai komai a gidan ba sai mu daura ba?”

Aisha ta dubeta “Har zaki fara aiki tun yanzu? Ni kam idan nayi aure sai nayi wata hudu ana min aiki. Sai na gama zagaya duk inda nake son naje na honeymoon kafin na dawo na fara aiki”

Aneesa ta zare idanu cikin mamaki tace “To yaya zaki san meye mijin ki yake so da wanda baya so?”

Aisha tayi shiru sannan tace “Ba sai ya fada min ba?”

“ya miki aikin komai kenan, gwamma a hankali ki karanceshi ki fahimta zai fi jin dadin sanin kin damu da al’amarin shi”

“Kai Alhamdulillah, ko ba komai na san Yaya Sagir ya samu mace mai son shi”. A take Aneesa tayi tunanin anya kuwa? Ita dai ta san bata son Sagir kawai dai ta amince da auren ne saboda Allah, saboda tayi wa mahaifinta biyayya, amma ita daman tana da wata damace ta yin soyayya? Wacce tayi a baya ma a wautar ta da yarinta ta mayar shine so, amma yanzu dai ta san ba so bane tayiwa Nata’ala, haka yanzu ma ta san ba so bane takeyiwa uncle Sagir, sai dai muradin son ta kyautatawa zamantakewar aure.

STORY CONTINUES BELOW


Suna aikin abincin ne a kicin Aisha take mata bayanin Sagir “kinga Yaya Sagir yana son shan kayan marmari sosai, abinci mai nauyi kuma yafi son shi da rana da safe da dare bai cika cin abinci ba ya fi son abu mai ruwa-ruwa ko mai dan sanyi ko kuwa madara fresh milk. Idan kuma a sanyi ne kullum zaki samu flask din shayi me dauke da kayan kamshi a ciki a tare dashi.”

Aneesa kuwa sai dadin hirar tasu take ji ko ba komai ta fara sanin akwai abun da uncle Sagir yake so a duniya banda kasuwancinsa da wayoyinsa da tafiye-tafiye.

Haka Aisha ta shiga tamabayar Aneesa rayuwarta a Kunuwal. Nan Aneesa ta fara bata labarin kawancenta da Falmata, da kuma su mama da Mairo. Har suka gama aikin in banda dariya ba abun da Aisha takeyi.

A kan teburin cin abinci suka jera komai, sannan Aisha tace “ki shiga ki kimtsa na san yanzu Yaya ya kusa isowa gida tunda sun sauka tun dazu.”

Aneesa tayi yake, ita Aisha a tunaninta ina daukin dawowar yayan ta ne? bata san idan banda fargaba ba abunda hakan ke haddasa mani ba.

Ta idar da sallar la’asar kenan taji karar horn din mota a bakin get, nan da nan gabanta ya shiga dukan uku-uku. Yau yaya zatayi? Nan da nan ta kimtsa abun sallar tata, ta dauki mayafi madaidaici ta sa a jikin ta sannan ta fito falon, da yake tun zuwan ta gidan da daya daga cikin dakunan kasa take amfani, kasancewar maigidan bai yi mata bayanin inda zata yi amfani dashi ba. Ita dai banda mai gadi da ta gani, sai ko yaron da hajiya ta turo ya zo ya taya su dan share-sharen da baza a rasa ba bata ga wasu mutane a gidan ba, don haka ko da suka gama abinci duk ta saka musu ta kira Musa yaron da ya taya su kimtsa wuri ya dauka musu kowa da nashi.

Yanzun ma dai Musan ne ya karbi kayan hannun Sagir ‘yar jakar komfuta ce kawai sai wasu ledoji masu kyau, yana shigowa da su Aneesa ta karba a hannunta. Can babban falo ta wuce dashi ta adana, sannan ta dawo shigowarta karamin falon da ya sada mutum da kofar gidan yayi daidai da shigowar Sagir, yana sake da T-shirt da wando da kuma budaddiyar ‘yar sama wanda tafi kama da (blazer) a kan T-shirt din, ta kula dai kusan haka yafi saka kayayyakin sa, ita kuma riga da zani ce ta atamfa mai ruwan goro a jikinta, ta rufu da mayafi mai ruwan kasa. sun shafe kusan second uku suna kallon kallo kafin tace “Sannun ku da isowa” 1

Juyawa yayi yana duba ko tare suka shigo da wani, hakan da yayi ya sa Aneesa dariya, kasa kasa sautin dariyarta ta fito.

“Bismillah, ko a nan zamu ci gaba da tsayuwa? Don ni dai na gaji zan iya bacci a tsaye ma”

Tayi saurin matsa masa daga hanya “Yi hakuri,”

Bin bayan shi tayi da ta ga ya haura sama sai tayi zamanta a falon kasa don bata san me zata fara yi ba, gaba daya wani tsoro-tsoro yake bata. Aisha na fitowa daga daki kawai taga Aneesa ita kadai.

“Naji kaman shigowar Yaya Sagir”

Aneesa ta amsa mata da “eh shine, ya haura sama”

Aisha ta dube Aneesa ta dubi hanyar kayatacciyar matakalar zamanin da ya kwanto cikin makeken falon tace “oh, don ina nan shine bazaki tarbi mijin ki ba, ni kam kinga tafiyata dama Hajiya tace nazo kafin ya dawo ne kuma tunda ya iso kalau, na barku lafiya”

Aneesa tayi tsalle ta cafko hannunta cikin kidima, “Don Allah kiyi hakuri kar ki tafi, yaushe kikazo? muna ‘yar hirar mu, ki bari sai bayan kwana biyu, kafin nan na gama sabawa sai ki koma.”

“so kikeyi ayi jajjage dani kenan, wanda ya ajiye ki ya gwada miki sabawa, ni kam kinga tafiyata tunda zama na ma ya hanaki kula dashi gashi ya dawo tafiya.”

Aneesa cikin rashin fahimta tace “To ni kuma me zan bashi? na ajiye masa abincin sa kuma ba sanin dakin da yake ma nayi ba, ba sai na jira ya sauko ba?” 2

Aisha ta rufe ido tana dariya tace “wannan kam zan baki lambar Ya’a Hamdiyya ta fada miki abinyi. ki gaishe shi idan ya sauko”

Aneesa tayi narai-narai da idanu zatayi kuka “yanzu da gaske tafiya zakiyi?”

“Ba abin da zai sameki, ba ga Yaya Sagir nan ba?”

Aneesa tace cikin in-ina “Tsoro yake bani, baya dariya” 6

Aisha ta bude baki zatayi dariya ne ta daga idanu tayi ido hudu da yayan nata don haka tayi saurin dakewa Aneesa kuwa ta cigaba “sannan idan yana magana kaman zai bugi mutum, gashi ni ban saba dashi ba kuma…” 4

Muryarsa taji yace “Aisha! kawo min ruwa marar sanyi sosai”

Aisha ta san ya fada ne don ya katse musu magana don dakin cin abincin sa akwai abun zuba ruwan sha.

Aneesa na juyowa taga ya canza kaya zuwa polo shirt da wani wando mai laushi, da takalma kirar silifas masu laushi a kafafun shi, a ranta tace “a falon ma sai an sa takalmi?” suna hada ido taga ya sha mur, don haka ta kara shiga taitayin ta.

Yana zama a kujerar cin abincin ya dubi Aisha yace, idan kin kammala na fadawa malam Hassan zai mai dake main house”

Aisha tace “yaya Sagir da motata ma na taho”

“okay to ba damuwa, bari na gama sai nazo”

Haka Aneesa ta tsaya wuri-wuri da idanu ta rasa bakin magana, gashi daga dawowarsa tayi laifin da bata san na meye ba ko kuwa yaushe tayi shi.

Yana gama cin abincin ya dauki daya daga cikin ledojin da ya taho dasu ya bata yace “Ga wannan ki kaiwa Hajiya, dayan kuma naki ne.”

Ta bude tana duba abun da ya kawo mata nan ta hau murna tana godiya, Aneesa dai nata ido. Kaman zatayi kuka karfi da yaji ya kore Aisha da wayo harda mata kyauta, yanzu me Aisha zata yi tunani?

Aisha ko murna da tazo tafiya ta rike hannun Aneesa tace “ki kula da kanki, da kuma yayana, ki daina zaman falon kasa” harda kanne mata ido daya. 2

Aneesa sai taji duk kunya ya kamata, kaman tabi Aisha takeji. Ko kuma da uncle Sagir din bai dawo ya bata musu jin dadin su ba.

Tana shigowa daga rakiyar Aisha ta samu yana zaune kan doguwar kujera yana amsa waya, ganin haka yasa tayi sauri zata wuce daki, amma yasa hannu ya kirata. sumui-sumui ta zauna a kan kafet. Tana jira har ya gama wayar sannan yace “ina zakije?”

“Daki.. zan koma”

“Yaya ina nan zaki wuce daki ki barni, bayan don ke na kammala da wuri na dawo?” 2

Maganarsa ta bata mamaki kwarai don haka tayi saurin dago manyan fararen idanuwanta ta dubeshi, nan kuwa ta samu shima kallonta yake yi.

“Sai dai ban sani ba ashe tsoro nake baki ko?”

“a’a ba haka bane…” ta fada a sanyaye. 5

Cikin murya ta rashin wasa yace da ita “bana son kina ko wace irin magana da kowa, idan da akwai abunda ni nake miki kikaga ya dace na sani ki sameni ki fada min. Aisha ba sa’ar yin irin wannan maganar da ita bane, ko so kikeyi ta raina ni har da ke din ma?”

Ta girgiza kanta idanunta cike da hawaye.

Nan dai ya mike yace mata zai tafi masallaci. Tunda tayi sallah, itama kan sallayarta ta zauna tana wuridi har aka kira isha bata ji dawowarshi ba. Kasancewar bata bukatar yin wani girki bata daura ba, sai da ta idar ta dama kunu ta dan sa a flas don ita tana son sha, shi kuwa sai ta nemi wani flas din ta zuba masa ruwan zafi ta ajiye, kofi da kayan hadin shayi yanda takeyiwa Daddy a giddy.

Tana kwance a dakinta ba abun da take tunawa irin Innarta, tana can tana ta tunani, ita dai ta dau alkawari ba za ta taba bari, zuciyarta ta wahala ba irin yanda innarta ta sha wuya, don haka ne ma take tsoron sakewa da Uncle Sagir, sai akaci sa’a shima bayi da ra’ayinta don haka take ga kaman zamansu zai yi daidai.

Tana tunani har bacci ya kwasheta a kan kafet. Sagir kuwa da ya dawo bai sameta ba, sai ya hada shayinsa yasha yana kallon labaru da ya ji shirun yayi yawa ne, ya leka dakin da take ya samu tayi bacci da kayanta da hijabin ta duka. kanshi kawai ya girgiza, sannan ya ja kofar ya fito. Ya kashe wutan ko ina sannan ya koma kan kujera ya kwanta, saboda yayi tunanin ko zata iya tashi taji tsoron fitowa neman wani abu.Tunda ta bige kan kafet bayan isha’i bata tashi sanin inda take ba sai da lokacin tashinta yayi, ta farka taga kayan jikinta duk sun shashaketa. Da sauri ta shiga bayan gida ta watsa ruwa sannan ta fito ta fara nafilfilu kafin lokacin sallah yayi. Sai da taji shirun yayi yawa ne tsoro ya soma kamata. Ta fara Allah-Allah a kira Sallah tayi sallah, ai kuwa kaman ladan ya jiyo kukanta nan ya shiga kwado kiran sallah a masallacin kusa da su. Tana idarwa ta gyara abun da zata gyara a dakin ta kimtsa cikin wani material mai laushi marar nauyi, dinkin ya mata kyau nan ta nemi mayafin da ya shiga da su ta yafa sannan ta fito falon tana sanda, zata wuce kitchen domin sarrafa abin karyawa, ji tayi kawai yace “kin tashi lafiya?” +

Da sauri ta juyo a birkice, kasancewar falon duhu ne kaf ya karade shi, da taimakon wutan lantarkin da suka haska waje tamkar safiya ne yasa ta hango hoton surar shi a zaune kan kujera.

A hankali ta dawo suka gaisa, “yaya naga kin fito da sassafe haka?”

“Daman abinci nake so na hada”

Ya kare mata kallo sannan yace “tun da sassafe?”

“Eh, ban saba baccin safe ba, kuma bani da abun yi”

“To, ba laifi. Amma kiyi shi cikin karanci don naga kunu a flask shi nake bukata kawai”

Nan ta tuna da kununta na jiya ita bata ma sha ba, tace masa “Tun na jiya ne fa?”

“ke ba sha zakiyi ba?”

Ta amsa masa yace “To idan har ke zaki sha me zai hana ni sha?”

Jin hakan yasa ta mike, ta tafi kicin din. Tana bude flask din taga da zafinsa sosai, ita bata taba tunani mutum kaman uncle Sagir ma ya san kunu ba bare ya sha. Kofi mai fadi ta dauko ta ajiye ma’adanin suga akan tire da cokali ta koma falon zata ajiye a dining yace mata ta kawo masa falon. Ta lura wani aiki yakeyi a komfutarsa, sai dai yana kallo ta saka komai kaman bata da jini a jiki. Ita kuma duk tsoronsa kesata hakan don kar ta mishi shirme ya sake ce mata bakauyiya. 4

“Ga wannan ki yi amfani dashi.” ya mika mata takwaran ledar jiya da ya baiwa Aisha, tana budewa taga shigen ta Daddyce ipad taji suna kiranshi.

Ta sa hannu ta karbi kwalin.

“Na gode” ta fada a sanyaye.

“kin san me akeyi dashi?

Cikin jin kunya tace masa “a’a, ina dai ganin irinsa a hannun Daddy”

“To shima kamar komfuta yake, zaki iya shiga yanar gizo sannan yana da abubuwan da aka zuba a ciki don amfanin ki. na sa miki abubuwan karin ilimi a ciki, kasancewa ban cika zama ba zai debe miki kewa idan kika samu wani abunyi. Idan na samu lokaci zan gwada miki yanda zakiyi amfani dashi, an miki setin komai ansa kudi, kafin nan sai ki adana”

“To, na gode”

Zata tashi ne yace “Wai ni Aneesa ni dodon ki ne? Me yasa kike rabe-rabe idan ina wurin?”

Nan da nan idanunta suka raina fata

“Bana son kina yawaita jin tsorona haka, nima mutum ne kamar ki kinji?”

“Eh”

“Shi kenan, ni karfe bakwai zan wuce ofis akwai abubuwan da nake bincike, zan iya dadewa kafin na dawo, idan kina so nayiwa Aisha waya tazo ta tayaki zama, ko kuma ki kira su Khazeena duk wanda ya miki, sai dai bana son yawan surutu kin ji ko?”

“eh, ayiwa Aishan magana idan bata da wani abunyi”

“To ba damuwa. Abu na karshe, idan sun zo su tayaki mayar da kayanki sama daki na hagu daga hawan ki.

“zamuyi in sha Allah.” 1

Bayan fitan shi ne, ta haura sama kofofin nan tabi tana bude su, dakin farko da ta bude komai a kimtse yake kaman sabbin zubi, ga wani kamshi mai kwantar da hankali da ya ta’allaka da dakin, komai mai launin ruwan toka ne, sai dai launin wani abu ya turu fiye da wani abun har ciki ta karasa nan tayi arba da wani makeken ma’adanin kayan sakawa da takalma(walk-in closet), budadde kowanne an jera su a wurin da ya dace, ita Aneesa dai mamakin yawan su da kuma lokacin da aka diba ana jera su takeyi. Nan take ta gane nan ne dakin maigidan, don haka ta juya ta fita ta bude daya dakin shi kuma komai nasa fari ne, ba wani tarukuce a cikin sa nan ma ta fita ta bude dakin da uncle Sagir yace nan ne nata, babban dakine sosai, harda wurin zama mai dauke da kujeru biyu da dan teburi a tsakiyar su, daga bakin wundon dakin kuma wata kujerace ta alfarma wanda mutum za iya kishingida a kai. Komai a ciki ruwan kasa ne mai ratsin ruwan gwal, duk dakunan sun mata kyau sun kuma dace da tsarin mai gidan. A dakin nata ne ta bude har cikin bandaki. Komai gwanin ban sha’awa a cikin bandakin. Tana karewa gidanta kallo ne, taji karar kararrawa a kasa, nan da nan ta sauka ta bude don ta san Aisha ce ta iso.

STORY CONTINUES BELOW


“Meye amfanin tafiyar taki jiya ba gashi yau kin dawo ba?”

Aisha ta shigo ta ajiye abubuwan hannunta a kan tebur din falon. “hmm ina ni ina zama, so kikeyi nayi laifi kenan.”

“yaya wurin su Hajiya?”

“Lafiyarsu kalau. Tace a gaishe ku, wannan nono ne tace a kawo muku. Bari na sa a fridge”

“To mun gode. Su Anty Sameera sun koma ne?”

“Eh jiya suka tafi gidan mamanta a kano wato goggonmu Yaa Fanna kenan”

“Ayya, ban yi sallama da Azhaan ba”

“Ina ruwan Azhaan zasu dawo ai, don a gidan yarta Yaa Amina ta nan garin suka fi zama.”

Aneesa ta kawo mata kayan sha da tabe-tabe sai da ta dan huta sannan tace ta tayata kaura. “Yaya Sagir ya nuna miki dakin kenan?”

Aneesa ta dubi Aisha tace “ke kin faye zolaya, daman saboda rashin sanin dakin ne yasa muka zauna a wannan tunda an samesu a bude, gudun kar muyi laifi yasa na ajiye a nan. Yau yace wai na mayar dakin sama.”

Aisha ta daga mata gira sama sannan tace “Iye, yayi kyau ai.”

Haka dai suka wuni suna kwashe kaya suna kimtsawa, daga bisani suka daura abinci nan ne Aisha take tambayarta “Anti Aneesa, ni idan kin tashi wani aiki zakiyi?”

Aneesa tayi shiru cikin tunani kafin tace “aiki kuma?”

Aisha ta mata duban mamaki sannan tace “Haka zaki zauna, ba abunyi? ko dai bakuyi shawara da yaya bane?”

Aneesa cikin jin kunya da nauyi tace “Ai ni ban fara jami’a ba, na dai yi jarabawar gama sakandire duk da banyi karatu mai nisa ba, ban san ko zanci ba”

Aisha mamaki ne mai dadi ya kamata “Amma Anti Aneesa yanda na ganki, fes da wayewarki ba zan taba tsammanin bakiyi nisa da karatu ba. Me yasa to baki ci gaba ba? ko dai baki da sha’awar karatun ne?”

“Ina son karatu sosai, sai dai a garin mu yara mata basu karatun boko mai nisa, sai dai na muhammadiyya, iyakan mace dakin miji to meye amfanin karatunta? Da kyar Innata ta samu na kammala firamare ina aji daya na sakandire aka cire ni wai sai dai ayi min aure.”

Aisha ta kama baki cikin al’ajabi “lokacin kuwa kin wuce shekara sha biyu?”

Aneesa ta girgiza mata kai alamar a’a “Shekarata goma sha uku lokacin” idanunta sun ciko da hawaye cikin tuno rayuwarta ta baya.

“Gaskiya tunda kince kinyi jarabawa idan sakamakonki yayi kyau ki dage kiyi karatu ko zaki samowa kannenki da sauran yan garin ku hakkinsu na samun ilimi.”

“Ba wanda ya kaini wannan burin, amma bani da ikon yin hakan, tunda na farko nima yaushe na ilimantu?”

Cikin zakuwa Aisha tace “zan fadawa Hajiya, idan yaya Sagir ya amince ba sai ki koma makaranta ba?”

Aneesa don murna bata san yaushe ta tafa hannayenta ba. “Da gaske? kina ganin zai yarda?”

“Muyi fatan hakan, idan yaga zama haka ya dameki zai nemi kiyi wani abun ba sai kice makaranta kike so ba?”

“Ke ni bari kiga wani abunda ya ban dazu wai iPad, ni ban iya amfani dashi ba kuma yace sai ya samu lokaci ya gwada min, ko zaki nuna min amfaninsa?”

Nan Aisha ta hau tayata murna “wannan fa sabuwar yayin da take kasuwa kenan. Gaskiya yaya Sagir ya burge ki da wannan tsarabar, bari ki ga ba wuya cikin lokaci kadan zaki fahimta.”

Suna kammala ayyukansu suka makalewa abun Aneesa suna ta fama, basu san shigowar shi ba, sai da ya hau saman dakin Aneesa sannan suka ganshi tsaye a bakin kofa nan da nan Aneesa ta mike tana masa sannu da dawowa. Ganin ya juya zai fita Aisha ta mata idanu akan ta bi bayan shi da ta ga alamar bata da niyyar yin hankan.

STORY CONTINUES BELOW


“Naga har kun kammala aikin naku, amma baku ji shigowa ta ba.”

“kayi hakuri kofar a rufe take bamuji shigowar ka ba. Yaya aiki?”

A bakin kofarsa ya tsaya, don haka itama tayi cak yana duban ta, duk da ana ce mata ita mai tsawo ce amma Sagir na ganin tsakiyar kanta. “lafiya kalau. Me kuka ajiye na abinci?” 5

Nan ta fara kame-kame don jolof din taliya sukayi da ya ji kayan lambu, ganin tunda yace ba da wuri zai dawo ba sai sukayi meat pie suka ajiye masa.

“Da yake kace ba da wuri zaka dawo ba, jolof din taliya na mana, akwai meat pie da dan kayan tabawa, ko a hada maka nono Hajiyarka ta aiko mana da safe?” 5

“Ki sa min taliyar kadan ki bar min nonon sai da dare zan sha idan Allah ya kaimu”

“To, shi kenan?” ta tambaya kanta a kasa.

“eh, zan dan kwanta kadan sai an kira la’asar zan fito ki ajiye min abincin a falo kawai”

Bayan Maghriba ne ya cewa Aneesa “ki shirya zamu maida Aisha gida sai kema ki gaida su Hajiya”

“to, bari na fada mata.”

Aneesa ta fito cikin wani shige na wani leshi mai zubi na daukan hankali kalar ruwan daurawa da ja, kayan sun fito da ita sosai musamman da ta zabi wani setin da Daddy ya saya mata na azurfa da akayi feshi da gwal sannan aka masa ado da dutsen yakut, ita dai bata san darajar sarkar ba ta san dai tana da kyau kawai fayendra taga an rubuta a jikin kwalin. Ta yi kwalliya daidai gwargwado, tana rike da mayafinta ne Aisha ta ganta. “maa sha Allah Anty Aneesa kinyi kyau sosai.” nan take ta dauke ta a hoto da wayarta, kaman yanda take da hotunanta da dama. Yana saukowa ne daga sama Aneesa tayi saurin saka mayafinta a jikinta sannan suka fito waje, tunda aka kawota sai yau ta fito daga gidanta.

Aneesa na zaune a gaba, Aisha ce me zuba surutu a motar ita dai Aneesa banda kamshin turaren uncle Sagir da kuma ganinsa da takeyi ta gefen ido ba abinda take yi a motar. A haka har suka isa, Falon Abba suka fara shiga sun samu ya dawo daga masallaci kenan.

“Sannunku da zuwa, ke Aisha haka akeyi sai kina zuwa kina dawowa, idan zaki zauna can ki zauna ko kuma kema ayi miki auren kije gidanki, amma yau kije gobe ki koma?”

“A’a Abba fa yaya Sagir ne yace naje yau na tayata zama suna da aiki zai dade a ofis”

“A to na mayar gidan Aneesa ne ya burge ki sai ince kema kiyi gidanki mana” Sukayi dariya, Aisha ta wuce ciki.

“Aneesa kuna lafiya ko ba wata matsala dai?”

“eh, Abba lafiya kalau, Alhamdulillah”

“to yayi kyau haka ake so. Sagir kaita gurin Hajiyar mana su gaisa”

Sagir ya mike Aneesa ta bi bayansa zuwa sama inda falon hajiyar yake. Nan suka sameta tana zaune da carbi a hannunta. Sai da ta idar tukun Aneesa ta gaisheta cikin ladabi sannan tayi godiyar nono da aka aika musu.

“A’a ba komai, da fatan ba wata damuwa ko?”

“Aa babu.”

Nan Hajiya ta dubi Sagir tace “me zai hana tunda baka samu zama ba, Aneesa ta dawo nan idan ka natsu ko kuma ka samu hutu sai ta koma gidanta, amma ace ta wuni ita kadai ba abokin zama sai an dauko masu tayata zama ai inaga hakan yafi ko kuwa?” 1

Sagir dai ya san Hajiya magana ta masa a dabarance Hajiya bazata gane bane, a irin matsalolin da kamfaninsu yake fuskanta a yanzu, yanzu ba lokacin hutu bane ko zama har sai ya zo karshen wannan bincike.

“A’a Hajiya idan ta dawo nan kuma, nan gaba idan tafiya ta kamani sai ta kara dawowa kenan? Ai sai ta saba a hankali, ba zata rasa ‘yan tayata hira ba.”

STORY CONTINUES BELOW


“To shikenan, amma ka san da cewa su Aisha sun kusa komawa makaranta ko?”

“To Hajiya zan duba na gani.”

Bayan an kawo musu kayan marmari harda wanda Aneesa bata taba gani ba, kadan ta taba nan ma sai da hajiyar ta dan matsa sannan ta sha kadan. Sagir yace “Hajiya, mun gaishe ku, sai da safe zamuje can gidan su Aneesa mu gaishe su can ma”

“To yayi kyau. Allah ya taimaka ya kuma hada kawunan ku.”

Dukan su biyun a ciki suka amsa. Aneesa saboda kunyar Hajiya yayin da shi Sagir kuma bai ga muhimmanci amsawar ba kasancewar baya tunanin wai Aneesa zata samu wani matsayi a ran shi, tukun duka-duka ma nawa take? 9

Daga Main house gidan Alhaji Mahmoud suka wuce, Daddy yayi murnar ganin su sosai, yayinda aka bar Hajiya Juwairiya da yake hakora, su Khazeena duk falon suka dawo aka gaisa, nan ne Daddy yake cewa sakamakon jarabawar su ya fito. Ta danyi kokari ba laifi, sai dai da Aneesa ta gani sai tace Daddy dai ya kareta ne kawai amma wani kokari ne wannan da credits uku kawai ta samu sai sauran kuma darajar pass ta samu.

Wajen karfe goma suka bar gidan, ita dai tana dunkule da takardar sakamakon bata nunawa kowa ba. Suna hanyar komawa gida ne Sagir yace “kinyi jarabawa ashe bani da labari?”

“A’a wannan ba komai bane, na gwada ne naga ko zan iya dama da sai zuwa wata shekarar kafin nan na gama shiryawa sai nayi.”

“kinyi kokari ai, komai da gwaji ake farashi, yanzu baki ga kinyi nasara ba? mutane nawa suke tunanin su yi amma basuyi ba?”

Aneesa taji gaskiya a wannan maganar tasa don haka bata tanka ba. Suna shiga dakinta ta wuce a sama ta ajiye sakamakon a kan gado sannan ta shige wanka. Fitowarta sai ba takardu ba labarin su, ta tsaya nema ne ta sha’afa da kanta, bata ji karar shigowarsa ba dadi da kari kofofin lafiyayyu ne basu da kara bare mutum yaji alamar budesu. Sai juyawa tayi ta ganshi a kan kujerar bakin kofa. Da sauri ta fara neman zanin da take daurawa tayi sallah ta lulluba a jikinta, bakin gashin kanta wanda ya sha kananun kitso ya dan jike daga wankan da ta fito ya manne a wuyanta.

“wani abu kike nema?”

Cikin kidima tace “Na ajiye takarda ne a nan na fito ban gani ba.”

Sai ta hango ambulan din a hannunsa. “Ina tsamman dai zaki kara himma wani karon idan kika zana jarabawar? don wannan sakamakon ba abinda zai miki” ya daga takardar yana nuna mata a wulakance kafin ya ajiye mata a gefen kujerar. 8

Cikin zafin nama ta iso kujerar ta dauke takardar “shi yasa ban nuna maka ba ai tun a hanya, tunda kauyawa ai ba su san komai ba, yaya kake tunanin na ci jarabawar dama?” A ranta tace har da wani cewa anyi kokari dazu tunda na gwada yin jarabawar. 2

Ya mike zai fitane tayi maganar don haka ya juyo ya karewa bakin maganarta ta kallo. Aneesa da ta ga kallon yayi yawa sai ta soma tsarguwa, ta sauke idanunta kasa, hannu ta ga ya sa yana kawowa jikinta, cikin hanzari ta matsa baya, ganin hakan sai Sagir ya dake yace “ki gyara zanin rufuwar taki ya zame.” Yana fada ya ja mata kofa ya kulle. 7

Nan Aneesa taji kamar kasa ya bude ta shige ciki, shi abun da zai mata daban ita abun da ta kawo a ranta daban. Hakan yasa washegari bata bude kofarta da wuri ba don gudun haduwarsu bata san da wani ido zata kalleshi ba idan har suka hadu, bayan abun da tayi jiya.

Tana aiki ne da rana sai ga sallama, ta duba agogo ta san ba lokacin dawowar uncle Sagir bane don haka ta lulluba mayafinta da ta sakala a bakin kofa, taje ta bude kofar, tana budewa taga Aadil.

“Wai munyi fushi sai yau zaka leko mu uncle Aadil?”

“Dadina dake ba kya daukewa mutum kafa, ayi min uzuri. Ai kinga bai dace na dameku da sintiri ba shi yasa na dan saurara.”

STORY CONTINUES BELOW


Falon Sagir ta kaishi sannan ta kawo masa ruwan sha da lemo. “ai da na zaci ma baka gari tun ran lahadi ka bace bat.”

“ina nan wallahi, ayyuka ne sukayi mana yawa”

Aneesa tayi murmushi “Da kai da abokin naka ban san wanda yafi bautawa aikin nan ba. kullum ku kenan ba ku gajiya”

Aadil yayi dariya “Ai daurowa takeyi, matsala muka samu a cikin lissafin kamfani shi yasa kika ga mun birkice don nemo asalin wannan damuwar, amma yanzu kam alhamdulillah za ayi meeting din karshe nan da kwana biyu”

“Allah ya kaimu, ya kuma warware komai.”

“Ameen, ni na gaishe ku zan wuce”

“haba har zaka wuce, na kusa gama abinci fa kuma shima ya kusa dawowa, ka jira ku gaisa mana?”

“a’a kiyi aikin ki a hankali, ni a koshe nake don daga wurin cin abinci na fito”

Aneesa tace “hmm to wai sai kuyi ta yawon cin abinci bayan zaku iya rike gida”

“Maganarki tafi karfina, ke dai kiyi ta sani a addu’a. Tunda Yallabai ya daure yayi nima ina ji a jikina na kusa in sha Allah.”

“To Allah ya nuna mana”.

Bayan ya tafi ne mai gadi ya shigo da manyan daskararrun kaji guda goma, da katon katon na juice haka ta jera kajin a babban freezer, juice din kuma ta sa su a store kasancewar akwai wasu daman a fridge. Nan ta kara tsayawa a kitchen din tana kallon kayan ciki, kusan na kamfani daya ne, komai me amfani ne da muhimmanci, bai cika tarkace ba amma kana gani kasan komai na manya ne.

Har sai yamma lis tukun sannan Sagir ya dawo gidan, ta amshi jakarsa ta masa sannu da dawowa, amma yau amsawa kawai yayi ba tare da ya nemi wata magana a tare da ita ba, ita kuma tana jira ya natsu sai ta fada masa abun da Aadil ya kawo musu, amma har dai akayi sallar isha bata ga fuska ba, yana shan madarar sa yana amsa imel a komfutarsa. Don haka ta samu wuri ta zauna har lokacin labaru bai ce mata komai ba ganin haka sai ita ta dago maganar

“Umm, dazu ma fa uncle Aadil ya zo da rana ya kawo kaji, da drinks na sa su a freezer”

Bai cire kanshi a komfutar ba yace “uhmm, yayi kyau mun gode”. Ita dai kanta ya daure, duk iya sanin ta da uncle Sagir duk da bai cika shiga sha’aninta ba bai taba tsume mata ba sai yau don haka ita ma ta kama kanta ta haura sama tare da ce masa sai da safe. Tana hawa matakala, yana binta da kallo har ta karasa hawa cikin natsuwa, ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “daman na san duk tunanin su daya yake”. 5

Bai sake waiwayarta ba ya kashe komai shima ya haura dakinsa. Haka dai washegari akayi wannan zama ta HALIN KO IN KULA, sai kwana na biyun ne ta fito da safe ta same shi a falo yana karanta jarida, ta gaida shi kaman yanda ta saba sannan ta shiga hada abun karyawa.

“Ga wannan sai ki cika duk abun da ya dace, fom ne na makarantar sekandire babban aji, wato aji hudu kenan. Zaki fara wannan zangon da za a fara karatu” Aneesa ji tayi kaman mafarki takeyi, don murna bata san lokacin da ta yi saurin karbar fom din ba tana ta godiya tana dubawa.

A lokacin sai tayi masa kama da yarinya sak, kai ya girgiza ya wuce dakin karatun sa don wunin ranar bayi da niyan fita ofis daga gida zaiyi duka ayyukansa kasancewar suna da meeting da yamma sai a lokacin ne zai fita. A ranar Aneesa ta nemi lambar malam Habu ta kirasu don ta basu wannan kyakkyawar labarin. 7

Ai kuwa gaba daya gidan murna ta kama su, Innarta ma ta karbi waya nan Aneesa ta fara bata labarin yanda wancan sakamakon bai yi kyau ba amma gashi yanzu Sagir ya sake bata wata dama.

Ihun murnar da Sagir yaji ne daga dakin karatunsa ya dameshi ya fito yaga Aneesa nata surutu a waya tana tsalle “Inna in sha Allah, bazan watsa masa kasa a ido ba, zan dage nayi karatu sosai har sai na fito da sakamako mafi kyau.” Inna ta saka albarka sukayi sallama. Daidai lokacin Sagir yace “idan zakiyi magana a waya ki rinka sassauta muryarki saboda ina aiki a ciki kuma kina damuna” 6

“kayi hakuri, na zaci ka fita ne” ganin yanda ya hada rai, sai ta nemi murnar da takeyi dazu ta rasa, haka ta koma kicin ta ja kujera ta zauna sai sharban kuka takeyi. Sai da tasha iya isanta ne taji hannu a kafadarta tana ganin shi ta cure guri guda saboda taji tsoron ko shima dukanta zaiyi yanda Mahmoud ya daki Halima.

Ganin yanda tayi saurin kare kanta da hannayenta sai ta bashi tausayi, tabbas duk abun da yake akwai a yarinyar nan na kuruciya da kauyanci to haka akwai wani abu a tare da rayuwarta na abun tausayi.

“Ban yi niyyar baki tsoro ba, ki bar kukan nan haka. Ni zan je ofis anjima muna da taro da sauran ma’aikata da daraktocin kamfani”

cikin shesshekar kuka tace “to, Allah ya bada sa’a”

Hannunta ya janyo daga kicin din ya kaita falon shi, ya zaunar. A gefenta ya zauna hannunta na cikin nashi har yanzu, sai dai ita tsoro ya hanata sakewa gaba daya ta sankare.

“Aneesa, sai kin rinka hakuri dani kinji? Ba ko meye na miki zaki zauna kina kuka ba, ina fama da abubuwa da dama, ina mu’amala da jama’a da dama ina ganin matsaloli kullum ana kawo min koke-koke masu ban al’ajabi da ban tausayi, gidan nan da kike gani nan ne kawai nake dawowa na tserewa duka wadancan al’amura nayi tunani mai kyau. To hakan yasa idan aka dameni a gida nake saurin fusata amma ba wai don kece kika dameni ba. kin gane ko?”

kai ta gyada masa cikin hawayen tausayin shi da tausayin kanta. A hankali yasa hannayensa masu taushi ya goge mata hawaye tare da ce mata sai ya dawo.



Bayan tafiyarsa ta dade tana tunanin al’amura da dama. Na farko dai ta kula da cewa uncle Sagir dai mutum ne da ya san ya kamata kuma yana da kirki ba kaman yanda ta daukeshi ba. Amma sai dai matsala daya, yanda yake iya canza yanayin shi farat daya yakan bata tsoro, anya bazatayi kuskure ba idan ta bari ya shige mata zuciya?
Suna zaune a dakin taron da ya kunshi kujerun danyar leda masu jikin karfe mai sulbi wadanda suka zagaye makeken teburi na gilashi mai kwana hudu, teburin ya fiye tsawo maimakon fadi, gaban ko wannen su ruwan sanyi ne da kofuna da kuma lemuna, sannan akwai siraran na’uran magana a gaban kowani mutum da ke da mazauni a wannan teburin, duka mutanen da suke hade a wannan daki su suke murda kambun kamfanin Daggash-Adebayor and sons, wanda yake ciyar da ma’aikata dubbai da suke aiki kasan kamfanonin su da ma’aikatansu a fadin kasar Nijeriya da wajenta.

Idan ka duba fuskokin su gabaki daya zaka fuskanci farin cikin cimma burin su da kuma nasarar warware matsalar da ta sha gaban su. Yayinda zukatansu ke cike da mamakin wanda aka kama da laifin juyar da kudin kamfani da na ma’aikata zuwa wani boyayyen ma’adanar kudi a ketaren kasar.

Bayan taro ya watse kamar kullum Mr. Ahmad da Sagir ne suka saura a dakin taron. “Amma abokina, nayi mamakin gano Dr. Okoli da kayi cikin kankanin lokaci”

“Mr. Ahmad na jinginar da abubuwa da dama kafin na samu gano bakin zaren da taimakon Mr John babban security officer din mu”

“To Amma yaya ka gano shi?”

“Ka tuna lokacin da mukayi shawarar daukar hayar kamfanin binciken kudade da kuma kadarorin sabbin kamfanonin (financial forensics) da duk zamu saya mu dunkule dasu (merger) gudun rikice-rikice?”

“Okay, lallai na tuna”

“Na nemo su ne, muka hada takardunmu da accounts din mu sukayi binciken da zasuyi daga fannin su suna turo min rahoto, bana son na saka mutane da yawa a binciken saboda koma waye ne zai iya yi. Binciken da akayi dai ya nuna mana Dr. okoli yayi amfani da ilimin komfutar sa ne wajen shiga network din mu a matsayin shine akawun wannan kamfani, wato yayi satar hanya (hacking) ta wannan hanya ne a ko wace rana duk kudin cinikin da zasu shiga bankin mu to kason shi suna shiga nashi ma’adanar yayinda a wurin mu zamu ga tamkar kudaden sun shigo mana”

“To amma abun da na gagara ganewa yaya akayi sai yanzu aka fahimci wannan matsalar?”

“Na saka ayi binciken dukka abubuwan da kamfani ta mallakane maimakon nan da wata uku kaman yanda aka saba yi kowani shekara a nan ne Auwal yake shaida min wurin bincike sun gane wata matsala sun samu (glitch) a asusun kamfani.”

“To ai Alhamdulillah, tunda Allah ya sa an gane kuma an damka shi a hannun hukuma. congratulations, sai dai na san abokina mun shiga hakkin amarya da yawa, wannan aikin ya taso lokacin da tafi bukatar ka a kusa.”

Sagir yayi dariya. Ahmad ya ci gaba “Ai ina ga yanzu kam tunda komai ya zo karshe sai ka dauki hutu haka nan. Daman ka cancanci wannan hutun yanzu na kula wannan shekara ta uku kenan da baka dauki hutu ba ko sau daya”

“Ayyukan ne muna nan ma yaya suka kare…”

Ahmad ya tsayar dashi “wannan karon ba musu, kayi sabon aure, sannan madam ta cancanci ka bata time. Daga gobe ina son naga takardar hutun ka shine magana ta karshe” 5

STORY CONTINUES BELOW


Haka dai suka mike suka bar dakin taron, Sagir ya dauki abun da zai dauka a ofis din shi, masinjan sa ya karba ya shige masa da jakarsa mota kamar yanda ya saba. Ofis din Aadil ya leka yace “yaya muje ko? ko kai kam kana nan?”

“Ina nan? Ai nikam na gama laushi gida zanje na huta. Kai dai da ka saba aikin sai ka kwana a nan”

“Kun sani a gaba kai da Ahmad, amma kar ku damu idan korata kukeyi zan tafi har sai kun nemo ni”

Aadil yayi dariya, yana kulle ofis dinsa ne yace “kaman zaka iya”.

****** ******** ********

“Daddy, don Allah fushin nan haka ya isa, kayiwa Allah ka bar yarinyar nan ta koma makaranta, watanta guda fa a gida, ai war haka kam ta dauki darasi”

Hajiya Juwairiya ta sanya Alhaji Mahmoud a gaba, kwana biyu kenan sai magiya take masa akan yayi sassauci wa yarinyar

“Ai na gama magana, me ya saura kuma? wata uku nace zatayi, idan ta koma baya ai hakan zai mata zafi, ko zatayi kishi tayi karatun. Ke kin san iya kudin da muke kashewa kan karatunta, amma a hakan ne take neman ta sa mana kasa a ido, ga kanwarta yanzu har ta gama itama, saka su zanyi a gaba nayi ta tarawa? Don haka nan da wata biyun nan idan zata fito da miji na mata aure gwamma ta fito dashi idan kuma ba haka ba koma waye na samu yana so zan aura mata shi.”

Ai nan hajiya Juwairiyya hankalinta ya kara tashi ta zare idanu “kar ka mata abun da kayiwa ‘yar Halima”

Daddy ya juyo ya dubeta a fusace “Ita ‘yar Halimar ba mutum bace? ko ita bata da gata ne? Sannan da na mata hakan inace tana zaune lafiya da mijinta wancan satin suka zo kinga alamar bakin ciki a tare da ita? Don haka ki bi dani a hankali kan maganar Sameeha ran kowa zai iya baci a gidan nan.”

Da taga duk abun da tayi bai yi aiki ba sai ta mike tace “Allah ya baka hakuri. Zata zauna, zata kuma nemi miji”

“Da yafi kam, mu kwana lafiya” yana fada ya juya sai dai da ya ga tana tsaye har wannan lokacin ne, ya juyo yace “Ko da wani abu ne? ni zan shiga na kwanta ne”

Jikin Hajiya Juwairiya yayi sanyi ta kada kai ta juya zuwa nata dakin, wanda yanzu shekara guda kenan rabon da ta hada daki da Alhaji Mahmoud duk kuma ba don komai ba sai a kan wata bakauyiyar tsohuwar matar shi Halima da ‘yar ta.

Tana zuwa daki ta zube a kan gado tana kuka “Halima kin cuceni kin tarwatsa min farin cikina, ba kya gidan nan ma amma kin kewayeni da bakin aniyyarki. yaushe zaki daina bibiyata da sharri? kema yanda na dandani bakin ciki sai kin dandana” haka tayi ta sambatu ita kadai a daki.

******** **********

A dakinta ya sameta ta idar da sallar isha’i, batayi doguwar addu’a ba kasancewar taji shigowarshi ba wai ta hanyar kara ko takunsa ba a’a kamshin turaren sa ne ya sanar da ita.

“Sannu da dawowa”

“Yauwwa sannu da ibada, me aka roka mana ne?”

Tayi dariya hade da rufe fuskarta cikin tafukan hannu. “Dariya na baki? Na san addu’arki na karbuwa ai saboda ina ganin aikinsa.”

“Yaya kasan ina maka addu’a?” Ta tambaya cikin mamaki,

“Wace mata ce batayi wa mijinta addu’a? Idan da akwaita ki fada min”

“Yaya taron ku? kace zaku shiga taro da yamma”

Sagir ya dan kishingide kan doguwar kujerar da ya saba zama a dakin sannan yace “Alhamdulillah, komai ya tafi yanda muke so. Mun kuma warware matsalar da kenan.”

“Mun godewa Allah, Allah ya dada kareka da al’amuranka, ya kareka kuma daga dukkan wani sharri. Ya hadaka da karin nasarori”

“Ameen” ko ba komai yakanji dadin kyawawan addu’o’inta a gareshi. Hakan yana faranta ransa, don haka ne yace “Inaga kafin a koma makaranta zan dauki hutu a wurin aiki domin mu samu lokaci sosai mu fahimci juna ko zaki bar tsorona ko?” 7

STORY CONTINUES BELOW


“Ni fa ba haka bane, kaine sai na kasa gane wani yanayi kake ciki a ko da yaushe” Ta fada cikin shagawabar da bata san ma tayi shi ba.

“Yau zan samu abinci kuwa? na dawo da yunwa” Ya fada ba tare da ya tanka bun da tace ba.

Da sauri ta mike daga kan abun sallar, ta nufi hanyar fita, binta yayi da kallo kafin shima ya mike ya shiga dakin sa ya watsa ruwa. Yana saukowa ya samu ta shimfida ledar cin abinci a kasan falonsa ta ajiye kayan abincin, da su farantai. Sai da ta zuba mishi farfesun kaza, sannan ta zuba mishi jollof din kuskus da tayi shi da su hanta da kayan lambu. “Ke bazaki ci bane?”

Tare da jin nauyinsa tace “A’a ka gama ci tukun, zanci.”

“Naki wayon, ke dai kina son kiyi ta kallon lomana.”

Ita mutumin baya fasa bata mamaki, idan ya zolayeta kaman bashi ba, don haka bata bashi amsa ba ta nemi faranti itama ta zuba nata dan kadan, haka sukayi ta cin abincin ba tare da wata kwakkwarar magana ba.

Yana gamawa abunka da sabo komfutarsa ya bude yana duba wasu manyan zanunnukan da kamfaninsa sukeyi wanda shi da kanshi yake shugabantar kungiyar da suke zanen. Ganin haka Aneesa ta kwashe kwanukan tace “sai da safe”

“Ashe kwanan nan zakiyi kiba.”

“Na’am?”

“kina kwanciya daga cin abinci kam ai kin budewa kanki hanyar cututtuka iri-iri kenan cikin su kuwa harda kiba”

“A’a daman zan shiga ne saboda na bari kayi aikinka”

“Wa yace miki ban iya hira ina aiki ba?”

Shiru tayi saboda ita gaba daya bata san me take ji ba idan tana tare da Sagir. da yaga rashin sakewa a tare da ita yace “To shi kenan, sai da safe ni dai ba ruwana idan kikayi kiba kar kice ban fada miki ba”

Tana son zama saboda kar tayi mummunar kiba sannan kuma tana ga kamar zolayarta yakeyi don haka ne ta samu kujera ta zauna. Tunda ya sa mata idanu akan zaman kafet. “wai ke wannan abun baya damunki ne? ki wuni dashi ki kwana dashi?” 2

Ta dubi khimar din jikinta tayi dairy “Ni fa bada shi nake kwana ba”

“kin iya gardama ko?” da jin haka taja bakinta ta tsuke, hade da cire mayafin ta nade shi, ganin ta zauna shiru yasa ya kunna mata telebijin sannan ya kammala abun da yakeyi kafin ya kashe komfutar tashi.

“kina nan ko zaki shiga? zan kashe abubuwa”

“eh” kawai ta iya cewa ita kanta bata san me take nufi ba.

“eh meye?”

“zan shiga”

“To ki jirani na kashe abubuwa kema ki ga makunnin komai saboda koda tafiya zata kamani wataran.”

Tana biye dashi yana kashe ko wani wuta yana mata bayanin komai ita dai zuciyarta idan banda dukan uku uku ba abin da takeyi. Yana hawa tana binshi a baya ganin yayi hanyar dakin sa yasa itama tayi hanyar nata dakin.

“Ba kya jin tsoro ne?” ya tamabaya ba tare da ya juyo ba. 3

Ai kaman ta doka tsalle tace tsoron takeji sai dai kash abun tsoron ba a dakinta yake ba shi wanda yake neman ceton shine dodonta, da sauri ta kada kanta kamar wata mutunmutumi. Ya waiwayo ya ga abun da takeyi murmushi yayi yace 1

“Sai da safe.” tana tsaye a bakin kofarta sai da taji ya shiga dakinsa tukun ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya. Tana shiga ta danna makulli wa dakinta.

Duk Sagir yana jin shigarta da kuma sa makullinta. “Ban san me yasa ni kuma jarrabawata kenan ba. Wai shin wani abu ne matsalata? ko kuwa dai sa’ar mace ce bani da shi? Haka ya raba dare yana tunanin abunyi, domin yarinyar nan Aneesa, tana son shiga inda zai masa ciwo, kuma bazai iya daukar wata cutarba, har yau bai gama jinya ba.

STORY CONTINUES BELOW


****** ****

Randa suka cika sati biyu ne da aure, Daddy ya tattaro kan iyalansa domin su zo suga dakin Aneesa, wai ranar murna ba kamarta domin zama takeyi tamkar a kurkuku, tun daren da sukaci abinci tare da Sagir bata sake ganin wata kwakkwarar walwala daga gareshi ba domin wuni yakeyi a wannan dakin karatun nashi yana aiki, a dole wai ya dau hutu, yamma nayi kuma a gefen garejin gidan akwai dakin motsa jiki can yake zuwa. 5

Sai ya gaji sannan ya shige yayi wanka, dare nayi sai ya fice ba abun da yake damunta irin rashin sanin inda ma yake zuwa. Ko dai shima irin na Daddy zai yi mata? takan tambayi kanta “kai a’a Sagir bazai yi haka ba, Daddyn ma dole ce ta sashi, to shi Sagir dole bazata iya sashi ba?” haka dai take wuni tunani. Shiyasa ganin su Daddy ba karamin dadi ya haddasa mata ba. Ta shiga kawo musu abubuwa daban-daban, sannan ta zauna suka gaisa. “Mamana ai wannan gidan ya miki girma ke kadai, yaya kike aikin gidan?”

“Akwai Musa yakan shigo ya min shara ni kuma sai na kula da sauran ayyukan.”

“to, sannu da kokari me zai hana to ko Hannatu tazo ta tayaki da wasu abubuwan”

“Daddy ba komai, nan da nan ma nake kammala aikin da yake ba ko ina aka cika amfani dashi ba, sai dai idan na bukaci hakan zanyi magana.”

“to shi kenan tunda kince hakan,” Hajiya Juwairiyya tana shiru idan banda kallon tsarin gidan da takeyi ba abun da ya dameta, yanzu fa da komai ya daidaita da ‘yarta ce a wannan daular. Ai yara ma basu bata labari da kyau ba, gashi ta zaci yarinyar zata bar gidan tuntuni amma shiru kakeji kaman an aika bawa garinsu. 8

Haka dai suka gama zamansu kafin nan Aneesa tace ai sai dai mummy ta shigo ta ga gidan tunda Daddy ya ki. Cikin karfin hali ta tashi ta lelleka, dakin uncle Sagir ne kawai bata kai Mummy ba. “ga wuri kam yayi kyau, sai a rinka gyara kar a lalata abubuwan dai “

“To mummy” Aneesa ta amsa mata zuciyarta fes.

har dai suka zo tafiya Sagir bai dawo ba don haka su daddy suka ce ta gaishe shi.

“Daddy, yaushe Khazeena zata zo min weekend?”

Daddy yai murmushi yace “Har neman ‘yan zuwa weekend kikeyi? Zan sa malam Sule ya kawota ran Juma’a ta wuni miki dai idan Allah ya kaimu. Ai tayi katuwa da zuwa hutu” duk suka sa dariya, har mota ta raka su.

Sai wajen karfe goma ya shigo, tun tana daukin bashi labarin zuwan su Daddy har daukin ya kwanta don haka sannu kawai ta masa ta bashi abun da ta san zai bukata sannan ta wuce dakinta, tayi shirin kwanciya, tana karatun addu’ar bacci yayi sallama ya shigo dakin. Ta razana da ganin shi tunda bai saba shigowa dakin nata dai-dai wannan lokacin ba.

“yau ba a sa mukulli bane.?”

Tamabayar ta sa tasa tayi saurin sauke hannayenta na addu’a. Ita bata san laifi tayi ba, ashe sa mukulli a gidan nan laifine? shi yasa mana ya daina yi mata magana, yau ta shige su.

“kayi hakuri ban san baka son sa mukulli ba, naga kana rufe ko ina ne idan zaka shiga shi yasa nake kulle nan ma”

kai shi damuwar yarinyar ma yayi mata yawa, ga kuruciya ga kauyanci ga shi ita Aneesa ce! “Wai na tambayeki mana Aneesa?”

Ta tattaro hankalinta duka tana sauraran chi “Ban ce ki daina tsoro na ba?”

“Ka ce” ta amsa a sanyaye.

“To idan ina gidan me zai cinye ki da har sai kin kulle kofa?”

“Babu, kawai na saba ne” ta fada masa gaskiya.

“To daga yau ki rinka barmin kofarki a bude sai na miki sai da safe kinji? idan kuma tsoro kikeji, ki koma dakina idan ya so sai ki rufe kofar, kinga hatsarine ki kulle kanki ta ciki alhalin komai na iya faruwa, ba fata ba idan wani rashin lafiya ya taso miki yaya zakiyi, ke kadai a ciki?” 2

STORY CONTINUES BELOW


“Naji zan daina rufewa.” Sagir ya kula kaman kakkarwa takeyi. Nan ya sa hannu ya taba goshinta, yana yin hakan kuwa nan da nan Aneesa ta manne kaman zata shige jikin gadon.

“baki da lafiya ne?” ya tambayeta a hankali.

“A’a” ganin bai ji zafin jiki a tattare da ita ba kuma gashi ita kadai sai bari takeyi yasa ya kashe A.Cn dakin. “idan kinji sanyi ya miki yawa ki rinka kashe A.c kar ki cutu. sai da safe”

Yazo tashine ya sa hannu ya kashe wutar kan gefen teburin dake manne da gadon nata(night stand). A take numfashinsu ya gaurayu. Da sauri ya fita daga dakin domin tsoronshi daya ne kar ya sake kuskuren da ya maimaita a baya. 2

Haka dai ya cinye sati guda a hutun nasa, kullum Aneesa tana son tambayarsa inda yake zuwa da dare amma tana jin tsoron yin hakan, don haka har tabari ya zamo mata jiki.

Ranar da Sagir ya gama hutun sa wanda shi a ganinsa an dauke masa abune mafi muhimmanci a rayuwa, tamkar an hanashi numfashi yakeji idan baya aiki, don haka randa hutunsa ya kare sai yaji yadawo daidai. Aneesa tabbas taga canji a wannan lokacin saboda kusan an koma ‘yar gidan baya ne ma ba ‘yar gidan jiya ba, don a jiya dai ko ba komai tasan suna hira daga karfe goma zuwa sha daya kuma zai je ya mata sai da safe. Amma yanzu wataran sai tayi bacci yake shigowa, idan ma ya dawo da wurin ka rinka jinsa a waya kenan yana labarin kayan aiki, da kamfanoni da kudade masu yawa har na fitar hankali, masu razanarwa, wasu bata iya kidaya su ba ma.

Dadinta ma dai daya, zuwan Aisha da Khazeena yasa ta iya amfani da ipad dinta, haka zata dauka tana bincike kan abubuwan da taji sun shige mata duhu ta shafin google, wataran idan taji wani turanci mai girma a wurin uncle Sagir sai ta gwada neman ma’anarsa. Har dai lokacin fara zuwa makarantarta yayi, da uniform dinta da komai a Wuse makarantar take. An mata register an bata ajin da zata rinka zama, kullum malam Hassan direban Sagir ne yake kaita ya kuma dauko ta.

Sati biyu da fara zuwanta makaranta ne ta dawo gida, tayi ayyukanta kaman yanda ta saba, sai dai yanzu tana jin wahalarsu tunda tana dawowa daga makaranta kicin take fadawa sannan ta kimtsa dakinta. Ita dai bata taba shiga dakin Uncle Sagir ba tun da ta leka na farko, don haka take jin wani iri cikin sanin cewa tana matsayin matar shi amma bata damu da tsabtace muhallinsa ba.

Hakan yasa tana gama aikinta na rana, ta shiga domin ta gyara dakin Sagir amma abun da ya bata mamaki shine, yanda ta samu dakin komai a kimtse, zanin gadon ma an canza shi da wanda ta gani ranar. Nan take ta jinjinawa tsabtar Sagir, ta shiga bandakinsa girmanshi ne ya dauke hankalinta, ta tsaya tana duba abubuwan cikin bandakin tana shakan kamshi irin na Sagir, tabbas aiki ne ya sameta daga bisa dukkan alamu Uncle Sagir mai matukar tsabta ne, sai ta dage saboda abu kadan zai iya sa yaga kazantarta. Sai da taji ana kiran magriba ne ta farga da lokaci ya tafi, tayi saurin fitowa daga bandakin. Turus! taja ta tsaya domin dai mai daki ya dawo, ya cire coat din sa yana nade hannun rigarsa da alama shirin shiga alwala yake yi. 2

Ta rasa me zata ce masa da kyar ta samu muryarta tace “sannu da dawowa, daman… uhmm na shigo na gyara dakin ne sai… sai…”

“Ki kwantar da hankalinki Aneesa ke da dakin mijinki, wa zai ce miki wani abu koda kwana kikayi a ciki. just relax” 14

Tayi shiru ta tsaya tana kallon shi tamkar sauna. Haka yazo ya wuce ya shiga bandakin ya barta a wurin. Tsabar rashin sanin abunyi haka ya fito ya sameta. “lokacin Sallah fa zai wuce indai a nan kike da niyyar tsayuwa”

Da gudu ta bude kofar dakin ta fita zuwa dakinta tana haki, “yau na ga ta kaina me nake tunani har zan bari uncle Sagir ya kamani a dakinsa?”

Wanka kawai tayi da yake tana fashin Sallah, sai ta sauko don ta shiryawa maigidan abinci, tun kafin ya dawo ya same ta a falo ta rasa abun ce masa.

Ta gama shirya tebur din ne sai gashi ya shigo, don haka ba zancen tsira sai jan kujera daya tayi ta zauna.

“yaya makarantar dai? kina gane karatun?”

“eh, ba laifi.”

shiru sukayi duka sai karan cokali da faranti kawai zaka ji a falon. “ki shirya bayan isha’i zamuje unguwa”

Ta so taji inda zasuje amma yanzu nauyin sa take ji don haka ta amsa masa sannan ta hau sama don ta shirya.

Ko da ta sauko domin su tafi taga alama shima ya canza kayan ne domin yau kam jamfa ta gani a jikin sa, sun masa kyau kuwa farare kar dasu. Gidan Hajiya Munira suka je kanwar Hajiya, sannan suka je gidan su Uncle Sagir din. A can sukayi hira har sai goma da rabi suka kama hanyar gida, a motane yake ce mata “ranar Asabar ki shirya muna da baki, su biyar ne wasu abokan kasuwancina ne ‘yan china, sai ki duba ko da wani abun da zaki bukata na aiki idan babu sai a kawo. na ga dai ba laifi kin iya abinci amma kin iya na mutane da yawa?”

Aneesa taji dadin yabawar da Sagir ya mata “Eh zan jarraba na gani”

“Idan bazaki iya ba fa, nayi order wurin caterers”

Hankalinta ya tashi yanzu idan ta masa ba daidai ba fa? To amma bazata bari tana nan Uncle sagir yaje yana sayan abinci wa bakinsa a waje ba, bayan ya sanar da ita muhimmancinsu me amfanin koyan girkin da ta kwasa wajen paul, sannan abu mai sauki ga intanet yanzu. Don haka tace

“Ka barshi kawai zanyi, Allah ya kaimu; zan duba da safe sai na rubuta”.

Tun a daren Aneesa ta fara binciken abun da zata shirya don tarban bakin uncle Sagir. Ranar dai ta gayyaci Aisha da khazeena don su tayata aiki. Tun da rana suka fara shiri, ta shirya table din dai-dai mutum shida wato da uncle Sagir kenan. Abinci kala hudu sukayi, biyu irin na mutanen china wanda suka samu yanda akeyinsa a internet, biyu kuma irin dai abincin mu na gargajiya, don suma su taba irin abincin mutanen mu, sunyi abun sha a wadace da kayan marmari. Saman wurin tara kwanukan abinci suka jera komai, tebur din ma suka kawata shi da jeren filet (table setting) mai kyau. Sai da suka kalla suka tabbatar komai yayi tukun, suka kunna turaren wuta ya kama gidan sosai.

Aneesa ta gama shiryawa bayan tayi wankan yamma kaman yanda ta saba ne khazeena tace mata su suna falon sama.

“To nima gani nan fitowa.”

Sun zauna suna hira nan ne khazeena take fadawa Aneesa ai “Daddy yace Sameeha ta yiwa Hamza magana ya fito suyi aure tunda ita ta dage shi kadai take so, kuma ajinsa biyu a jami’a ni dai naji mummy nacewa iyayen Hamza sunce bai kai aure ba”

” lallai daddy ya dau maganar da zafi kenan”

“Tab kinajin yace tunda Hamza bazai aureta ba zai bada ita wa duk wanda yace yana so?”

Aisha tace “sai naji tausayinta, Aneesa ki sama mata miji mana?”

“woo ni me ya kaini? sai dai mu taya ta addu’a Allah ya sa Daddy ya huce ya barta ta ci gaba da karatunta ko zata samu mijin aure a hankali”

“Ai yanzu ta daina aron waya ta kira Hamza tunda yaki maganar auren”

“Da ya fi mata kam daman, me zai sa ta tsaya kula mutumin da ta san bata lokaci kawai sukeyi ba zancen aure a tare dashi, ai wannan neman ma bai dace ba”

Bayan sunyi sallah ne suka ji shigowar su Sagir. Aneesa ta sauka don ta masa sannu da isowa ganin bai hauro ba, ashe tare yake da bakin. Nan tayi turus, gashi sun riga sun ganta don haka ta karasa cikin falon ta gaishesu cikin harshen turanci, Allah ya taimake ta daman da mayafinta take yawo a cikin gidan. Nan ta musu sannu da zuwa.

Ranar ce karo na farko da yaji Aneesa tayi turanci, yaji mamaki kawarai bai zaci zata iya zance da turanci ba, ya zaci sai dai a rubuce don haka ba karamin burgeshi yaji tayi ba. 6

Bayan bakin sun tafi ne su Aisha suka tayata kimtsa kwanuka kafin suka tafi. Tana kula da wani dadi da taga uncle Sagir na ji. Ita ma tayi farin ciki da taga bata kasa ba wurin kyautata masa da bakinsa.

Aneesa ta mai da hanakalinta akan karatu bata da matsalar komai, a hankali kuma tana kara sabawa da uncle Sagir, duk da yawan ayyukansa, ya ware ranar asabar kullum yana gida ba ya aikin komai sai amsa waya da hira da matarsa Aneesa. Wani lokacin kuma ya shiga dakin karatu saboda baya son ya dameta idan tana da karatun yi, a haka har suka zana jarrabawar wannan zangon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *