KE NAKESO CHAPTER 3

KE NAKESO





CHAPTER 3





Shigowar Mama ne ya ceci Mai-jidda. “Hamamatu ku je falo. Yahanasu ta kai maku abinci”. +

“To Mama mun gode.”

Suna cin abinci ne. Wayar Mai-jidda ta yi kara. Mamaki ne ya kamata, da ta ga sunan da ke kan (Screen) dinta. Dan Kano? Mikewa ta yi ta-cewa Hamamatu tana zuwa, gefe can ta matsa ta amsa cikin murya kasa-kasa. “Assalamu-Alaikum.”

“Wa’alaikumus-Salam.” Ya fada cikinnatsuwa.

Ajiyar zuciya ta yi boyayyiya, sannan ta-ce. “Ba dai wani laifin na yi ba aka kira a tuhumeni da ranar Allah?”

“A’a, koda kin yi, ai ke kam dole a dauke idanu.”

“Hmm! Yayana ke nan, Yaya iyali. Yaya kwana biyu?”

“Lafiya lau! Alhamdulillahi.”

“Yau kuma me ya faru aka tuno da ni? Kwanaki wayarka ba ta shiga”.

“Eh na dan yi tafiya ne, lafiya lau. Na ji shiru ne nace bari na bugo na ji ko har an shafa Fatiha ne ba mu da labari? Ko dai abin da ki ke nemana, ki fada min kenan?” 2

“A’a haba, ayi haka? Wannan karon dai ba za ka tsallake ba, sai ka halarci daurin aure.”

“To, tunda za a ba ni wannan damar, ni ma kuma ba abin da zai hana ni zuwa da yardar Allah. Yaya Dutse?” 2

“Lafiya lau, yau kam gani a garinku. Tunda kai ka ki zuwa”.

“Wai lallai muna da manyan baki ashe, sai dai mun yi sabani, na je wani daurin aure a Kaduna”.

“Ka dai gama doje-dojen ka. Wataran dole ka nuna kanka.” 1

Dariya ya yi cikin kasaita, sannan ya-ce. “Kar ki damu, ba ni da niyyar boye miki kaina har abada, bari na bar ki yanzu, daga baya zan kira, sai na ji dalilin nemana da ki ke yi”. 2

“To shi kenan, na gode a gaida Madam”.

Ta kashe wayar, yayin da abubuwa da dama suka motsa a cikin kirjinta. Ta zauna kenan za ta ci-gaba da cin abinci, sai ga wata wayar, ta duba ta ga Alhaji Yusuf ne.

A hankali ta amsa cikin murya mai taushi take magana. “Mun iso lafiya… Eh… anjima dai zan koma gidan Yaya Maryam”. Murmushi ta yi, sannan ta-ce. “To shi kenan Allah ya kai mu.” Sannan ta kashe wayar.

“Kai Anty Hauwa, wanann irin murmushi haka, kin zama Hot-Line fa, wannan na ajiyewa, wannan ke bugowa. Da gani dai, wani ya taki sa’a kenan.” 3

“Kai Maman Mimie ke dai ayi sha’ani, wai an cuci na daji. Amma dai ana ta addu’a”.

“To Allah ya tabbatar da alkhairi, yanzu za ki yi mana nisa kenan.”

“A’a wane nisa kuma, ai ana tare. Bare ma fa da saura tukuna, ana dai kan fahimtar juna”.

STORY CONTINUES BELOW


“Dama da haka ne ai, sannu a hankali har Allah ya sa a dace, ko kuma dai da wani ne daban?”

Nan take gaban Mai-jidda ya yanke ya fadi, ta daga idanu ta dube shi a bakin kofa, ba ta amsa ba, ta ji ya-ce. “Idan kun gama, sai ku kirani a waya, ni zan fita”.

Matarsa ce ta amsa masa tare da mikewa ta isa wurin sa. Mai-jidda dai kanta na kasa ba ta ji me Hamamatu ta-ce ba, bare ta ga me ta yi. Sha’anin Hamama da Abdul-Aali sai su, don ko a gaban waye Sweety take ce masa. 22

Haka shi ma baya boye son da yake mata a gaban kowa. Sai dai yau hankalinsa na kan Mai-jidda da yadda ya ga kanta a kasa, saboda haka bai wani bawa Hamama Attention sosai ba.

Ya wuce. Ko da ya dawo, da yaran duka suka fita. Yaya Maryam ta yi murnar ganin su, ba su dade ba su Hamama suka koma nan suka bar Mai-jidda.

Yaya Maryam ta dubi Mai-jidda tana dariya Mai-jidda ta-ce “Meye?”

“A’a ni kin ji nace wani abu ne?”

“Su yi mana, haka kawai za ki fara dariya ne?”

“Na ga har kin shirya da mutumin ki, tunda ga shi har kun fara zagaye ‘yan-uwa”.

“Tab! Yaya Maryam dole ne ya sa ki ka ga haka, ni meye gami na da shi?” Mai-jidda ta fada hade da dauke Tray din kofuna zuwa kicin, da ta dawo ne. Yaya Maryam ta-ce “Umma dai ta fada min duk abin da yake faruwa”.

“Na san kuma ta fada miki, yadda ban amince ba, da yadda kuma na gama magana da Alhaji Yusuf, har ma zai turo ayi masa tambaya.”

“Duk na fahimci komai, sai dai ba na tsammanin Abdul-Aali yana da shirin barin ki nan kusa, bare ma har ya ga wani ya aure ki”.

“Ni ban san me yai maku ba, duk ku ke biye masa, akwai rashin dacewa kwarai a wannan al’amari, amma sam ba ku gani, ki na ganin dai yadda na ke da matarsa.

Amma ko kunya baya ji a gaban matarsa, sai kin ga wani mayataccen kallon da yake min. Kai wasu mazan ma dai sai a hankali Wallahi”. 4

Yaya Maryam ta yi dariya iya isarta, sannan ta-ce. “Allah ya gyara al’amarinki Mai-jidda, na ga dai haka aka yi kafin Dokta ya zo, kuma daga karshe kin bada kai, bori ya hau, yanzun ma ina ga hakan za a kuma maimaitawa. Tarihi zai maimaita kansa kenan”.

“Don maza sun kare, sai na tabbata a auren ‘yan gidan?” Yaya Maryam ba ta ba ta amsa ba. Can barci ya dauke ta, ba ta farka ba, sai la’asar ta tashi, jikinta ba dadi.

Don haka ta watsa ruwa, sannan ta nemi magani ta sha. Tana karatun Al-Qur’ani ne A’isha ta shigo ta-ce. “Anty Mai-jidda wai ki zo falon Baba. Uncle Abdul zai yi magana dake”. 3

Mai-jidda kanta ta girgiza, yau kam za ta fadawa Sarkin nacin nan magana ta karshe, idan kuwa ya nemi ya matsa mata, ta san matakin da za ta dauka, don makaho bai san ana kallonsa ba, sai an taka shi.

Abdul-Aali na zaune a falon yana jiran fitowar Jidda, ya yanke shawarar bi da ita a hankali, har sai ta fahimci inda ya dosa, sannan ya kara dago mata maganar aure, tunda yin hakan da ya yi tun daga farko ne ya tsorata ta. 5

Tana zama a falon, ba tare da ta sake gaishe shi ba ta-ce. “Ban san wane irin zuciya ka ke da ita ba da ba ta fahimtar kalmar a’a. Ina tsammanin lokaci ya yi da za ka daina yaudarar kanka, domin ba abin da zai yiwu tsakanin mu.”

Murmushi ya yi ya-ce. “Jidda kenan, ni ba maganar da ta kawoni ba kenan, ki maida wukar. Ni na kasa fahimtar wa ya tsani wani a tsakanin ni dake ne, ganin tun dawowata ke ce ki ke fada min kalamai marasa dadi.”

Mai-jidda ta sassauta fushinta, don sai ta samu kanta da rashin jin dadin yadda ya dauki batunta, ta-ce.

“To idan ba abin da ya kawo ka ba kenan, me za ka fada min wanda ba za ka iya fada ba a gaban matarka dazu?”

STORY CONTINUES BELOW


“Na zauna na yi nazari, akan abin da na zo miki da shi, kuma na sa kaina a matsayin da ki ke ciki, na san na yi kuskuren zuwa miki da wannan maganar.

Wanda na san da wuya ki dauke ta da sauki, kasancewar ga yadda abubuwa suke. Wannan ya sa na ke so na ba ki hakuri kan duk wani abin da ki ka fuskanta a dalilina a baya.”

Wani dadi ne ya ratsa zuciyar Mai-jidda, ta dago idanunta ta dube shi. “Na ji dadi da ka fahimci me na ke nufi, kuma ba komai. Komai ya wuce. Kuma ba a kara tuna komai.”

“Da fatan kuma ba za ki fadawa kowa a kan na tsaneki ba, ko kuma batun da na zo miki da shi. Ni kuma zan taya ki addu’a. Allah ya zabar miki da abinda ya fi alkhairi”. 4

“Ameen, na gode.”

Ya mike tare da cewa shi zai wuce.

“Ba ka sha ruwa ba, ka jira don Allah na kawo ma”.

Haka ta sa ya zauna ta kawo masa zobo mai sanyi da ruwa. Ta tsiyaya masa a (Glass Cup), sai da ya sha ne, sannan ta taka masa zuwa motarsa. “Ku, ku na nan har nan da kwana biyu ko?” 5

“Eh, ku yaushe za ku wuce?”

“Kin san abinka da Dan kwadago, lokacin komawata aiki ya yi, so zuwa ran litinin Insha-Allahu za mu koma. Idan ba so na ke su koreni ba.”

Mai-jidda ta yi dariya har sai da ya yi dan sauti kadan. Kyawawan hakoranta suka bayyana, ya tsaya yana kallonta da gaske ita ta dauka ya hakura ne. 2

Shi ya sa ta saki jikinta da shi, bude masa kofar motar ta yi, sannan ta-ce. “To mun gode Abdul-Aali, ayi kwadago da kyau. Allah ya kiyaye hanya”.

Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Alhaji Yusuf “Hauwa!” Da sauri ta matsa da baya, saboda yanayin fushin da ta gani a tare da shi, ta kuma rasa me za ta ce masa, don a hakikanin gaskiya, duk wanda ya ganta da Abdul-Aali a wannan lokacin, zai dauka da wani abin. 7

“Ka yi hakuri Yallabai ba abinda ka ke tunani ba…”

A take anan Abdul-Aali ya yi tunani, to hell with, sannu a hankali ya rufe marfin motar ya-ce da Alhaji Yusuf.

“Kwarai abin da ka ke tunani ne.” Ya raba ganinsa tsakanin Alhaji Yusuf da Mai-jidda, wanda bakin su ya kusa taba kasa, don tsabar mamaki. 2

“Babu tantama kan tunaninka, ka yi hakuri, na san kai mutumin kirki ne kuma na yaba kwarai da yadda ka ke nuna kulawarka ga Jidda.

Sai dai ina son ka sani (I’m Wild) akan Jidda, kuma idan akwai yadda zan yi, to daga yau ba za ka sake ganinta ba, ko a gida ko a ofis”. 3

Wannan bayanin nasa ya sa Alhaji Yusuf da Mai-jidda suka kasa furta komai, tsantsar mamaki, da ya tabbatar ya samu hankalin Mai-jidda, ya yi mata wani murmushi hade da kashe mata ido daya. 11

Sai da ta ji wani abu ya yi tsalle a cikin ta, yayin da da kyar ta hana kanta daga hannunta a wannan lokacin, tsabar bakin cikin da take ji tare da wani abu da ba ta san meye fassarar sa ba. 2

“Ina dawowa saboda ke Jidda.” Ya zauna cikin motarsa, sannan ya rage glass ya-ce “Gobe Insha-Allahu”.

Kafin ta-ce wani abu. Alhaji Yusuf ya koma motarsa, ya ja a fusace, jikinta a mace ta koma cikin gida.

Tana yanka ganye, tana ta fada. “Idan an ce maku baya son farin ciki na, ku bi ku rinka kare shi, idan ban da mugu, waye zai zo bayan ba aurenka zai yi ba, ya rinka korar maka masoyanka na asali.

Ni ban san inda zan je da ba zai bi-ni ba, ba na son na kara ganin ko fuskarsa, kin san wani nishadin da yake samu kansa a ciki, ganin bacin raina? Mugu kawai. Allah sai ya saka min.”

Yaya Maryam ta rike hannunta ta-ce. “Hankali Mai-jidda za ki ji ciwo, kin gama yanka ganyen.” Mai-jidda ta kalli (Chopping board) din taga yadda ta yi fici-fici da alayyahon. 3

STORY CONTINUES BELOW


Ta shafa goshinta cikin damuwa, game da sauke ajiyar zuciya. Yaya Maryam ta-ce. “Anya Mai-jidda ba ki dau maganar nan da zafi ba kuwa?”

Hawaye na bin fuskar Mai-jidda ta-ce. “Ina zaman zamana, ina lallaba rayuwata. Mugu ya shigo ya wargaza min komai, sai na yi sa’a na samu Alhaji Yusuf ya saurareni kuma, batun aiki na kam na san ina komawa Dutse, zan samu takardar sallama.”

“Ba ki yarda da son da Alhaji Yusuf yake miki ba kenan?”

“Ba zancen haka bane, ba ki san yadda Abdul-Aali ya kure shi bane, sai kin ga yadda ya bar gidan nan.”

“Abu mai sauki, idan ba kya so ki rasa shi, sai ki kira shi daga baya ki ba shi hakuri, kafin nan ya huce. Ai fushin masoyi, hutu ne.”

Gaba daya sai Mai-jidda ta ji ba anan hankalin ta yake ba, damuwarta ta fi yawa akan fushin da take yi da Abdul-Aali.

Randa za ta koma ne ta daure ta je gidan Abba, saboda tayi masu sallama, koda kuwa tana shakkun haduwarta da Abdul-Aali, a halin da take ciki.

Ai kuwa suna gaisawa da Mama, sai ga shi ya shigo kamar wanda yake jiran zuwanta gidan, dauke kanta ta yi, ba ta damu da ta gaishe shi ba, koda kuwa a gaban Mama ne, don ya kai ta makura.

Sai ga Muhammad ya shigo fuskarsa duk kunu. Yana nuna wa Mama wai yau ya sha dadi. Mama ta kama shi ta-ce. “Mu je na wanke ma, haka Yahanasun ta bari, ka yi da jikinka?”

“Mama ki kara min masa tukun”. 3

“Ka koshi haka nan, sai anjima kuma mu je na dauraye ka.”

Mama tana fita a dakin. Abdul-Aali ya zauna a bakin gado kusa da kujerar da Mai-jidda take zaune ya-ce. “Jidda…”

Kallon shi ta yi a fusace, sannan ta mike za ta fita daga dakin da sauri ya bi bayanta, ya tura kofar. A razane Mai-jidda ta zaro idanunta ta-ce. “Ka bude min kofa, ba na bukatar jin komai daga gareka”.

“Zan bude, amma ki zauna mu yi magana tukun”.

“Dole ne magana da kai? Ka bude min kofa, tun kafin Mama ta san me ake ciki, me ka ke tsammanin za ta yi tunani, idan ta ga ka kulle kofa, bayan ina cikin dakin? Ko dama manufarka kenan?”

Ya yi ajiyar zuciya, sannan ya bude kofar. “Jidda, ki yi hakuri ki ba ni minti biyar, mu yi magana ta fahimta.”

“Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra’ayina a minti biyar”. 2

“Ko za ki gwada ki gani?” Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. 1

Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa.

Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya.

“Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?”

“Wace irin tambaya ce wannan?”

Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta “Ki amsa min, me ya sani game dake?” Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba.

“Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? 3

Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?”

Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. “Ya san cewa ba kya son shi?”

This is the limit. Abdul-Aali ya kai ta makura. “Yaya aka yi ka san duk wanann a tare da ni?”

STORY CONTINUES BELOW


“Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani”. Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. 7

“Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!

“Ki fada ko za ki ji dadi a ranki, amma dake da ni mun sani.” Kan Mai-jidda ya kulle, mutumin da ya fi kowa tsanarta. Yaya za ayi ya maida hankali kan abin da ya shafe ta.

Har ya san su tamkar tafin hannunsa. “Yaya aka yi ka san duk wannan, bayan ka-fi kowa tsanata?”

Hannu ya sa ya shafo sumarsa, ya gaji da jin wannan kalmar a bakinta. “Jidda ki na son ki san hakikanin yadda na ke ji game da ke? Jidda duk duniya ba abinda na ke so kamarki, idan ki ka dauke Mama da Abba.” Dubansa ta yi, yayin da amsarsa ta haddasa mata wani saran kai . 6

Mai-jidda ta bude baki, tana kallon ikon Allah, yau kuma ga wata sabuwa inji ‘yan caca. Cikin kifkifta idanu ta-ce. “Engr. Abdul-Aali Sani, ba ka san me ka ke fada ba. Ina ga minti biyar dinka ya yi, za ka iya fita.

Koda yake dakin mahaifiyarka ne, ba ni da damar korar ka, ni ya kamata na tashi na tafi.” Ta fada hade da mikewa za ta fita, hannu ya sa ya riko bakin mayafinta, don ya tsaida ta, amma kallon da ta masa, ya sa ya sake ta ba shiri.

“Kar ka sake kuskuren yin haka, don ka san wasu abubuwa game da rayuwata, ba shi bane zai ba ka dama ka kafa hakkin mallakarka a kaina, sannan ko da wa na ke tare, kar ka sake yi masa magana. 2

Bare har ka nemi korarsa ta hanyar karfi ko dabara, saboda ba ni, ba kai. Idan ko ka yi kuskuren sake tunkarata.

To Hamamatu za ta san sirrinka, don haka ka san yadda aka yi ka cire ‘so na’ a zuciyarka, tun kan yayi maka lahani marar gyaruwa. Ka san kuwa da muguwar rawa, gwamma kin tashi”.

Abdul-Aali ya ji dacin da ya fito a kalamanta, hakan ya kara ingiza shi game da abubuwan da zuciyarsa ke karanto masa, na tsantsar son Mai-jidda.

“I don’t care, duk abinda za ki fada, ki fada, amma ina so ki san wannan karon ba zan ja da baya ba, na yi kuskuren a baya, amma ba zan sake maimaitawa ba da yardar Allah. Domin kuwa Jidda KE NA KE SO! 8

Kuma hakan ba zai taba canzawa ba, idan ki na tsoron ki bari abin da ke ranki ya bayyana, saboda gudun bacin ran Dakta ko kuma tunanin me zai faru idan ya sani.

Then guess what Jidda? Dakta ya rasu, ke kadai ki ke ganinsa da rai, idan ki na ga aurena da za ki yi, zai muzanta dangantakata da tasa, to kuwa ki san haka za ki muzanta dangartakarki da shi.

Idan kika auri koma waye ne, ba ni ba, tunda kamar yadda suke ba muharramanki ba, haka ni ma ba muharraminki bane. Don haka na bar miki kiyi duk abinda ki ke ganin ya dace. Amma kar ki umarci zuciyata da ta daina sonki, domin, don ta so ki aka halicceta.” 2

Hawaye ne daya na korar daya a idanunta, ba ta iya ce masa komai ba, ya fice daga dakin a fusace. Mama tana falo ta gama jin duk abinda ya faru tsakanin su. 8

Ita ta dade da sanin cewa da wata a kasa tsakanin Abdul-Aali da Hauwa tun kafin yau musamman yadda yake yawan sintirin zuwa Dutse ganin su tun dawowarsa.

Amma sanin Hauwa ta san zai yi wuya Abdul-Aali ya samu yadda yake so. Tana shiga dakin ta samu Mai-jidda tana share hawayenta da sauri.

“Hauwa lafiya dai na ji kamar hayaniya”

Yau ta ga ta kanta kar dai Mama ta jisu? Da wani ido za ta ganta yanzu? Duk Abdul-Aali ne ya jawo masu wannan bala’in. Yaya za ta fara kallon idon Mama ta-ce wai Danta ya mata tayin ya maye gurbin daya Danta da ta rasa, bayan ta san tare suka yi kukan rashinsa?

“Babu komai Mama, Ni zan wuce kar dare ya min” Mama ta kare mata kallo ta-ce “To shi kenan Allah ya kiyaye hanya, ki gaida wurin su Umman, akwai sakon da na hada a leda yana falo sai ki kai mata.”

“To ta gode Allah ya bar zumunci, ya karo girma.”

Nan Mama ta ji wani dadi a ranta, tabbas lokaci ya yi da Hauwa’unta za ta dawo gida. 5

Tana fita ta same shi a mota ba ta ko kalli inda yake ba ta fara takawa za ta isa bakin titi domin ta nemi abin hawa zuwa gidan Yaya Maryam. Amma ganin yana bin ta, ya sa ta tsaya, bude glass din ya yi ya-ce.

“Ki shiga na kai ki.” Ba tare da ya kalli inda take ba yake magana, hakan ya sa ta bude gidan gaba ta zauna sannan suka tafi, ba wanda ya-ce wa Dan-uwansa komai. 2

Shiru ne ya ratsa motar sai sanyin A.c dake tashi nan Mai-jidda ta ji tsikar jikin ta na tashi, a hankali ta sauke glass din motar saboda hayaniya ya Dan shigo, ko za ta samu sassauci.

“Sorry, A.cn ya miki yawa ne?” ya tambaya hade da kai hannu ya kashe na’urar ya sauke glass din bangaren shi, sai da suka isa kofar gidan Yaya Maryam ne ya-ce “Allah ya kiyaye hanya, gobe muma za mu wuce. Sai Allah ya dawo da ni.”

Ta juyo ta dube shi idanunta cike da hawaye, ba tare da ta iya cewa komai ba gudun kar ta saki kuka ta fice daga motar. “Jidda kenan…” ya fada tare da sa motar a reverse.Ta dai ci-gaba da zuwa aiki sai dai ko da Alhaji Yusuf ya zo Dutse bai neme ta a ofis ba, hakan ya sa ta san har yanzu dai fushin yake yi.

Don haka bayan ta tashi a wajen aiki ranar laraba ta nemi wayarsa. Yana dauka ta-ce “Yallabai, kaina bisa wuya ina neman afuwa, wani laifi na yi haka har za ka shigo ka wuce ba tare da neman ganina ba?”

Alhaji Yusuf ya saki ajiyar zuciya sannan ya-ce “Hauwa ke kadai kin iya dagawa mutum hankali ki kuma kwantar masa, yanzu wace rigima ki ke nema za ki ce baki san laifinki ba?”

“Yallabai, kai dai ka sa lokaci kawai ka zo gida sai mu tattauna”

“To shi kenan, ina fata dai ba zan tarar da wannan Dan zafin kan naki ba?” 3

Dariya Mai-jidda ta yi ta-ce. “Wannan kuma tsohon zance kenan, ai madar ka ce, sai yadda ka yi.”

Alhaji Yusuf ya yi murmushi ya-ce. “To ranki shi dade, sai kin ganni da daren, don gobe zan koma Kano Insha-Allahu”.

“Ba laifi, sai na ganka.”

Tana kashe wayar, ta kalli agogon bangon da ke manne a dakinta, karfe shida ne, yanzu ba da dadewa ba za a kira sallar magariba.

Don haka ta mike, ta dan shiryawa Alhaji Yusuf abin tarba. Sannan ta yi sallah. Zuwa issha ta shirya tsab! Don haka Alhaji Yusuf take jira, domin su gyaro ta.

******

“Na san na yi kuskuren rashin fada maka ko ma menene manufar Abdul-Aali tun farko, amma ba na so ka bari ya zame mana matsala a tsakani.”

“Hauwa, ai ba sai kin fada ba, tun farkon haduwata da shi, na so na gane hakan, amma kuma idan har zai rinka yin haka, wataran zai kureni, in dai a kanki ne.”

“Ba ma fatan ma ya kai ga haka, yanzu dai mu bar wannan maganar, tunda ya wuce. Yaya hidima da fama da mu?”

“In dai da irinki zan yi ta fama Hauwa, to lallai da na ji dadina.” 1

Mai-jidda ta yi murmushi cikin sunne kai. “Yanzu dai mu bar wancan maganar, hankali na ya kara kwanciya.”

“Na ji dadin hakan”.

“Yanzu na kara jin karfin gwiwar turo magabata.”

“Wai, ai Yallabai ba abin da zai girgiza ka.” Murmushi ya yi, ya ci-gaba da kara gwada mata matsayinta a rayuwarsa. Hankali kwance ranar suka kwashi hirar su, ba wani wanda ya daga masu hankula. Da ya tashi tafiya ne, ya dauki wata ‘yar jaka ya ba ta.

Ta yi masa godiya, kasancewar Baba yana kwance a kofar gida akan taburma, ba tayi masa rakiya har waje ba. Nan ta juyo muryarsu sama-sama suna gaisawa da Baban.

Turare ne mai dan karen kyau, ya kawo mata, sai kudi a rafarsu ‘yan dari bibbiyu. Ta ji dadin turaren, kasancewarsa marar karfi sosai, sannan yana da dadi tamkar kamshin fure.

Bayan Alhaji Yusuf ya tafi ne. Ta yi shiru tana kwance a dakinta, haka nan ta tsinci kanta cikin kadaici da rashin sanin madafa, wani sayau! Take jin ta tamkar fanko.

Ba dai wannan bane karo na farko da Muhammad ya tafi Kano hutu don haka ta san ba kewarsa ke damunta ba, sannan ta dade da daina kuka cikin dare idan ta tuna Dakta.

Ga shi kuma ta shirya da Alhaji Yusuf har ya jaddada mata batun tambayarsa, karshen wata, ta rasa me yake sanyata jin abubuwan da take ji a lokacin. 3

Nan tunaninta ya fado kan Abdul-Aali, komai a tare da shi da abinda ya shafe shi, damuwa ce da rikicewa a tare da ita, wannan ya sa ko sa shi a tunaninta ba ta cika son yi ba.

STORY CONTINUES BELOW


Amma kuma don radin kansa, tunanin ke kai mata ziyara, musamman kan maganar da ya fada mata a dakin Mama. “Shin dama Abdul-Aali na so-na ne?

Amma wane irin so ne ake nuna shi ta hanyar kiyayya? Oh Yaya za ayi ma na rinka tunaninsa?” 1

Nan ta ji wani mutuwar jiki ya sauka mata. Ta dai hana kanta tunanin Abdul-Aali a zahiri. Amma sai da ya addabeta cikin barci, don kuwa ranar mafarkin sa ta rinka yi. 4

********

Wani irin kuna ta ji da tashin hankalin da ba ta taba samun kanta a ciki ba iyaka rayuwarta, idan mafarki ne, ba abinda take so, ta gani illa farkawarta.

Kallon sa take yi kamar ya rikide ya zama wata halitta daban, ko kuwa yana rike da makamin katse mata rayuwa. Ya fara damuwa da shirunta, don haka ya-ce. “Ba ki ce komai ba Hamamatu.”

Wai ance shiru ma amsa ne, haka dai take zaune tana kallonsa, tsawon minti biyar, ba ta furta komai ba, ganin haka. Abdul-Aali ya sa hannu ya riko tafin hannunta, wanda bai yi nasarar zama a ma’ajiyinsa ba.

Hamama ta-ce “Why, me ya sa za kai min haka Abdul-Aali? Ka san muhimmancin da ka ke da shi a gareni kuwa? Ka san yadda na dauke ka, za kai min haka. Anya ka min adalci kenan?

Na sallame komai na, saboda kai, ba ni da kamarka, shi ne za ka saka min da haka? Me ya sa ba ka bar mu a Kano ba, ka yi tahowarka kai kadai? Or better yet ka taho da amaryarka?

Na kasa yarda da abin da ka ke fada min, aure fa ka ce za ka yi. Wai me na rage ka da shi Sweety? Iyaka kokarina ina yi maka a gidan nan, idan akwai abinda ka ke so na gyara, sai ka fada min, amma aure?” 4

Nan ta fashe masa da kuka, ina ma da zai iya mata bayanin dalilin da ya sa zai yi wannan auren? Amma ba za ta so ji ba. Ta dago ta-ce.

“Wato shi ne abin da ka ke so, kasa na ke maka addu’a akai ko? Har da wani dauko gyara, ni ina murna za ka sabunta mana wuri da yara a sake, ashe kudurinka kenan, lalle na miji sai dai a bar shi. Allah ya baka sa’a.” 11

Ta mike ta wuce dakinta hade da bugo kofa. Abdul-Aali yana zaune a falon kansa a cikin tafukan hannunsa.

Kansa ya kulle gaba daya, amma ko ba komai ya sauke abin da yake damunsa, don tun ba yau ba yake son ya fadawa Hamamatu ya na so ya kara aure, amma ya rasa ta inda zai fuskanceta, dadin karawa, bai samu hadin kan Jidda ba. 1

Haka ya kwana biyu bai gane kan Hamamatu ba, daidai da abincinsa a gidan idan ya tambaya, sai ta-ce. “Ka jira amaryar ka idan ta zo, sai ta dafa ta ba ka. That is, idan ba ta cika maka ciki da soyayya ba.” 7

Murmushi ya yi, ya fita ya nemi abinda zai ci, idan ya samu wata walwala a gidan, to daga wurin yaransa ne, yana dawowa za su makale shi suna ba shi labarai.

Shi kuwa yana biye masu. Amma hanklinsa na kan Hamama, yadda ranta ke kuna, har wasu lokutan ta sauke fushinta kan yaran, ba gaira ba dalili ta fadasu da fada ko ta bugesu. Ranar Mimie ta kaiwa mari a gaban sa, ya fusata. 2

“Lafiyarki Hamamatu? Yaya za ki mata irin wannan bugun? Akan me za ki sauke fushinki a kanta? Idan ki na fushi da ni, to ki sauke a kaina, amma kar ki kara sa yaran nan a gaba”.

“Yau kam ka gwada min ba ni da matsayi a rayuwarka da yaranka da matar da za ka aura sun shige maka gaban komai, wai ma na tambaye ka, a dan dawowarmun nan ne har ka ganta ku ka daidaita, ko kuwa dama tun can ni ka rufa da maganar?”

“Hamama ki bar maganar nan haka, na ga dacewar na sanar dake ne, saboda na fita hakkin ki, amma ba na so ki daga hankalinki akan wannan maganar har ya bata zamantakewar mu. 2

Idan kin bada kofa, hakan na iya sawa ki ga bambanci a tare da ni, amma idan ki ka kwantar da hankalinki, ba abinda zai canza, wannan auren da zan yi, ba yana nufin na daina sonki bane, ko kina da wani aibu a tare da ke, ki dauke shi a matsayin kaddarata da ta ki ne.” 5

STORY CONTINUES BELOW


“Wace ce za ka aura?” Ta tambaya a dakile.

Nan ne ya sa hannun sa ya riko kafadunta a hankali ya-ce. “Zan fada miki wannan, amma ba yanzu ba. Saboda haka ki natsu ki kwantar da hankalinki.

Ni Abdul-Aalin ki ne har yanzu, kar ki yi tunanin ko auren da zan yi wata za ta kwace miki wani abu daga gareni. Ba abinda za a gwadawa Hamamatuna”.

Ya fada yana mata wani murmushi, mai kashe jiki, ita kuwa duk da hakan yayi mata tasiri, tsumewa ta yi ta-ce. “Ina ce dai mace za ka auro, ko ma me za ka fada, sai ka fada, amma ba za ka fahimci me yake gudana a cikin zuciyata ba.”

Ya dai samu ta kwantar da hankalinta, duk randa abubuwan suka motsa kuwa sai ta hau binciken wayarsa, da gangan yake bari wataran, saboda ya san ba abinda za ta gani, burinta shi ne ta ga wa zai aura, waye ta dauke mata hankalin Sweety dinta.

*******

Tana kallo har ya ja zip din jakarsa, ba ta ce masa komai ba, kasancewar ba wai tana goyon bayan wannan tafiyar bane. Asali ma shi ya shirya kayansa ma, don duk wani abin da ya shafe shi, ta sauke daga kanta, saboda haushinsa da take ji. 7

Mamaki kawai yake ba ta, yadda ta ga ya rikide, tamkar ita ba komai bace, ita dai za ta so ta ga koma wace ce ta daukewa mijinta hankali haka, yake wannan bare-baren, don abin ya wuce gaban komai.

Wataran tana masa magana ma kamar hanakalinsa baya wajen, sai tana nata, sai ya ba ta amsa. Ta yi wa kanta fada ma ta daina like masa, tunda yayi mata maganar aurensa, don ta san ita za ta sha wuya.

“Yaushe za ka dawo?” A sanyaye ta tambaya.

“Sai kun ganni.”

Wata irin dariya Hamamatu ta saki. “Ya Allah, Oh ni yau Abdul ina ka samu wannan yarinyar ne? Anya ko ba gamo ka yi ba?” 8

Kallon da yayi mata ne, ya sa ta shiga taitayinta ta bar dariyar. “Seriously, na kasa fahimtar yadda son mutum zai shigeka farat daya, ya kidima ka yadda ka ke a yanzun nan”.

Murmushi ya yi ya-ce. “Wannan na daban ne shi ya sa, idan kuma ki na da lokaci sai ki zauna nayi miki shi filla-filla.

Wanda na san yayi miki nauyi da yawa ba za ki iya dauka ba, so ki kula da gida da yara, kafin na dawo, Sweety”. Da wannan murmushin a fuskarsa, ya sumbace ta. Sannan ya fita a dakin. 4

Sulalewa ta yi kasan kafet din dakin, ta fashe da kuka, ta san ita da Abdul-Aali kam shi kenan, ba ta yafewa duk wacce ta shiga tsakaninsu ba. 7

*************

Ta dawo daga ofis ne ranar Juma’a ta samu motar Mukhtaar a kofar gidansu, ba ta yi mamaki ba, kasancewar ya kan zo ya gaishesu, za ta shiga cikin gida ne ta kofar zaure, ta ga ya fito daga kofar falon Baba, don haka ta tsaya suka gaisa. “Yaya su Mama?”

“Lafiyarsu kalau, suna gaisheku. Har kin taso daga ofis kenan?”

“Wallahi, ka san yau (Short day). Na ga kamar ba kai kadai bane?”

Mukhtaar ya sosa kai, ya-ce. “Eh, da Kawu Garba muka zo.”

Mai-jidda ta dube shi a ranta tana nanata Kawu Garba? Kanin Abba da yake Zariya kenan fa, shi yake shige masu gaba idan al’amuran auren gidan ya tashi.

Me ya kawo shi wajen Baba? Nan da nan ta fahimci ko me yake faruwa, ta zare idanu. “Mukhtaar, Abdul-Aali ya zo Kano ne?”

“Anty Hauwa…”

Ba ta jira ta ji me Mukhtaar zai ce ba, ta wuce cikin gida a fusace. Khimar dinta ta cire kawai ta dau wayarta, ta nemi sunan Abdul-Aali ta danna masa kira.

Yana ganin wayarta, ya yi mamaki kwarai, don wannan ne karo na biyu da ta kira shi a wayarsa. “Me ka ke tunanin ka ke yi? Ka na tsammanin za ka sani na aure ka dole ne, ba na son alaqar dake tsakanin Baba da Abba ya baci, don haka tun wuri ka san yadda aka yi ka janye maganar nan, tun kafin su Kawu Garba su tafi”.

STORY CONTINUES BELOW


“Shi kenan damuwarki?” 5

“Eh, idan kuma ba ka janye ba, zan fadawa Hamama duk abin da ake ciki.”

Ta ba shi dariya. “Sai dai kamar kin makara, don ta riga ta sani, saboda haka ki sake lalubo abinda za ki min barazana da shi, don na fada miki wannan karon ba ja da baya.”

“Hmmm! Ban san me zance maka ba, amma mu zuba ni da kai.”

Ta kashe wayar cikin fushi ta zauna a daki ranar ba ta ko ci abinci ba. Muhammad ma wajen Umma ya gama sintirin sa.

Ba ta dai ji kiran Baba ba a wannan ranar, amma hakan bai sa hankalinta ya kwanta ba.

********

Hakan ya sa tana shiga falon inda aka ce yana jiranta, ta yi zamanta ba ta ce masa komai ba.

Da yayi mata magana ne ta-ce. “Hankalinka ya kwanta, ka samu abinda ka ke so ai, sai ka sakar min mara, za ka iya komawa Portharcourt hankalin ka kwance, tunda ka yi yadda ka ke so, ba mai sace maka ni”. 1

Baya gajiya da kallonta har ta gama, hannunsa daya yana tallafe da bakinsa, “Ameen da addu’arki. Allah ya ba ni abin da na ke so. Allah ya ba ni ke.

Amma zan fi farin-ciki idan ki ka kwantar da hankalinki, ki ka tayani son ki, saboda kar ki hadu da wata cutar.

Ji yadda ki ke tada hankalinki. Abdul-Aali ne ya-ce yana son ki ba wani abin tsoro ba. A iya sanina kuwa, ba wanda ya taba ce min ni abin tsoro ne.” 4

Ta rasa yadda za ta yi da wannan mutumin, idan banda munafurci, wai shi ne mai sonta, cikin tausayin kanta fuska a narke, ta durkusa har kasa. Yana ganin haka ya mike ya-ce. “Jidda meye haka?”

Ba ta kula shi ba, ta-ce. “Don Allah Abdul-Aali, ka rabu da ni, ka koma rayuwarka da ka saba, ba tare da ni a ciki ba, ko Turai ne ka koma, amma don Allah ka bar ni, kar ka sake tunani na, ka yi hakuri ka cireni a ranka.

Don ba zan iya auren ka ba, za ka cutar da ni, idan har ka aureni, saboda ba zan iya zama da kai ba alhalin ka na matsayin kanin Dakta, ba zan iya sonka ba, ban san me ya sa ka ke cewa ka na so-na ba, Alhali da ni da kai mun san ba haka bane.”

Kallonta yake yi, a ransa kuwa tamkar ana kara rura masa wutan sonta ne, duk lokacin da ya kalleta, musamman a irin wannan yanayi da take kuka, ga kuma tausayinta da yake lullube shi, wanda idan zai iya tunawa ya fi ganinta a wannan yanayin.

Ji yake yi kamar ya daga ta daga durkusonta, ya zaunar da ita yayi mata alqawura masu dama wadanda za su sa ta fita daga kunci. “Ki na nufin idan na zo da wata siffa, ba ta kanin Yaya Rayyan ba, za ki iya so na Jidda?”

Mai-jidda ta tsayar da kukanta, ta dube shi, yayin da zuciyarta ke bugawa fiye da tunaninta har take tsoron kar ya fashe a kirjinta.

“Abdul-Aali ba zan taba iya son wani ba kamar yadda na so Dakta, wannan ita ce gaskiyar magana, kuma the earlier you know the better.” Ta mike ta zauna a kujerarta a takure.

“Shi kenan, tunda haka ne, amma za ki iya auren wani koda ba ki son shi kenan?”

“Me ya sa za ka ce haka, bayan ka san amsar?”

“Saboda za ki auri Alhaji Yusuf, kuma bayan kin san ba kya son sa, shin kin masa adalci? Kin san abin da ya fuskanta, kafin ya zo miki da maganar aure ko kuwa bayan ya zo miki da ita? Kin san tashin hankalin da ki ka jefa matarsa da shi kansa, duk don yana so ya kawo ki gidansa.

A tunaninsa za ki mayar masa da wannan soyayyar, ki haifa masa kyawawan yara kamar ki? Kin san me zai fuskanta idan ya kasance ya auri matar da har yanzu take soyayya da wanin sa?”

Idanunta a rufe ta-ce. “Ka daina shiga rayuwata Abdul-Aali, ka daina dagula min lissafi, ka daina damuna, a farke ko a mafarki, ba na son ganinka, ba na son jin muryarka.” 8

STORY CONTINUES BELOW


Kallonta yake yi a nishadance, tamkar ya samu wani majigi na fim. (Oh! how he loved her), yana son Jidda da yawa. 2

“Na barki Lafiya Jidda, kin bawa kanki amsa, ina kuma fatan ki gane shi, tun kan lokaci ya kure miki.”

Idanunta sun yi jawur! Haka ta bi-shi da kallo har ya bar falon. Anan ta zauna tana kuka, har Baba ya shigo, ta goge hawayenta tana shirin fita ne ya-ce. “Hauwa dawo nan.”

Ta riga ta san me zai ce mata, don haka kawai zama ta yi tana sauraren sa. “Lafiya ki ke wannan irin kuka? Kullum ina fada miki, duk abin da ya shige miki duhu, to addu’a ce maganinsa.

Saboda bakin-ciki da abinda Allah ya turo mana, tamkar rashin yarda da qaddara ce, wanda ko mai kyau ko marar kyau, imanin mu ya rataya ne a amincewa da wannan qaddarar.”

Ta daga kai alamar amsawa, ta goge hawayen nata, sannan Baba ya-ce. “Akwai wasu takardu da Kawun marigayi suka kawo jiya, wasu filayensa ne suka fito, to an raba su, shi ne aka kawo miki takardar na wurin Muhammad, saboda haka sai ki adana shi.”

Ta yi shiru tana jiran Baba ya dago mata maganar Abdul-Aali, amma shiru bai ce komai ba. Yana miko mata ta-ce masa. “Na gode, shi kenan Baba?”

Ya dubi kumburarren fuskarta ya-ce. “Eh shi kenan, idan kin shiga, ki yiwa Laraba magana.”

Ta fita jiki ba kwari, dama takardun fili ne suka kawo su Kawu Garba, shi ne ta tada hankalinta har da kiran Abdul-Aali, wato shi kuma sai ya biye mata, nan take haushin kanta ya kamata, ta rasa me yake mata dadi. 5

Da dare ta daga wayarta ya yi sau biyar tana son ta kira ta bawa Abdul-Aali hakuri. Amma ta rasa da me za ta fara? Da kyar ta danna lambar, ya yi ta Ringing. Kafin nan ya daga, kamar ta ajiye.

Nan kuma ta rasa me za ta ce da ta ji muryarsa. “Uhmm… Dama na kira ne… Ka yi hakuri, na yi maka wata irin fahimta.

Baba ya ban sakon da ya kawo su Kawu Garba, to amma me ya hana kayi min bayani, ka bari na yi ta fada maka son raina?” Ta fada cikin jin kunyar kanta.

Ya gyara hannunsa, ya rike wayar sosai, sannan ya-ce. “Well! Ko ba komai na san ina damunki ko a mafarki, don haka za mu iya cewa mun yi daidai kenan ko? We are even.” 4

Wata kunyar ta sake kamata “Ni yaushe nace maka…”

“Kar ki musa, dazu da kike ta kuka, ki na magana, kin dauka ba na jin me ki ke fada ne? Ai idan Abdul-Aali zai auri Jiddansa, sai duniya duka sun sani. 4

Saboda haka ba zancen boye miki komai, ki dai zauna cikin shiri, don jiki na ya ban nan ba da jimawa bane”. 1

Matsalarta da shi kenan, shi ya sa ta sake tamke fuska. “Hmm! A mafarki kenan.”

“Jidda a zahiri, kuma ke da kanki za ki shaida hakan.” 1

“Dama abin da ya sa na kira kenan, don na ba ka hakuri. Amma kar hakan ya sa ka yi tunanin, idan ka yi da gaske, za ka share”.

“Na ji ranki shi dade, mu kwana lafiya. Idan na dameki a mafarki kuma. You can always call, mu yi magana.” 1

“Allah ya sawwaka.” Ta fada hade da kashe wayar. Sannan ta samu kanta da murmushi, tana juya wayar a hannunta. Muhammad ta gani a kwance a gefenta, ta fita daga dan guntun duniyar da ta fada. 8

Ta shafa kan yaron, sannan tayi masu addu’a ta kwanta.

Ba kalmar da ya zo mata a rai, tana farkawa washegari, sai. “Maye”. Ta ja tsaki, domin yau ma dai sai da aka kuma, mafarki dai kamar wani hadin baki. 7

********

Walida ta kasa daina dariya, tunda Mai-jidda ta ba ta labarin abinda ya faru. “Don Allah ki daina, kar su F and A su ji ki, ni dai dole wannan satin na yi magana da Alhaji Yusuf.

Idan ya shirya kawai, su iso gida, don ina tabbatar miki yadda take-taken Abdul-Aali take, zai iya saceni ya kai ni gidansa.” 2

“Ya isa? Da sauran sa, ai Jiddan mu me tsada ce”.

“Kar ki sake kirana Jidda, wani wai ‘Jidda’ yadda ki ka san sunan yanka na kenan. Abin da ya fi ba ni mamaki wai har ya fadawa matarsa tsabar azarbabi.

Bayan ko karbuwa bai samu ba, ni ce ita na shirga masa wulaqanci kala-kala, shi ba anan ba, shi ba a can ba, mu ga ta tsiyar”. 1

“Yanzu kam maganar Abdul-Aali ta fara zama gaskiya, na fara yarda ke ce ki ka tsane shi, shi bai tsaneki ba.”

Wata sabuwa, tana samun Alhaji Yusuf da maganar zuwa tambaya sai ya-ce. “Kar ki damu, ina bukatar lokaci tukun, saboda wasu dalilan da suka taso”. 2

Mai-jidda ta yi masa wani irin duba. “Kamar dai musamman ka taho min da albishir, idan zan iya tunawa a dokance ka ke lokacin, me ya faru yanzu kuma?”

“Hauwa, Yayar ki ce Wallahi ta samu Mum dina da maganar. Allah kadai ya san me ta fada mata, yanzu haka ta-ce ita ba ta san wannan zancen ba, amma dai ina kan lallaba ta. Insha-Allahu komai zai daidaita, kin san sha’anin iyaye.”

Kan Mai-jidda a kasa ta-ce. “Haka ne kam, to Allah ya shige mana gaba.” Jikinta a sanyaye suka rabu ranar. A ce mutum kamar Alhaji Yusuf, sai abinda matar sa take so, zai yi, ai an samu matsala. 7

Daga nan ta fara tunanin anya ba kuskure za ta yi ba kuwa, idan ta karfafa batun sa? Sai dai za ta ba shi lokacin kamar yadda ya bukata.

********

Dariya yake yi, jin bayanin Mai-jidda. “Hauwa, easy slow down, ban gane ba.”

“Hmm! Ni ma kaina ban gane ba Yayana, a bangare guda Alhaji Yusuf, wanda matarsa ta san hanyar da za ta bi ta sa shi yin son ranta. 6

Ka ga baida iko akan gidan sa, a bangare guda kuwa Abdul-Aali, na fada maka irin nuna isarsa.

Da ganin kamar ya fi kowa sanin komai, kuma sai abinda yake so za a yi. It’s like dole ne na aure shi, tunda ya-ce min yana bukatar hakan.”

Ta nisa sannan ta-ce. “Kaina ya daure, ban san abin yi ba, wasu lokatan ji na ke yi kamar da na yi zamana haka, ban sake dago maganar aure ba.”

“Hmm! Na ji damuwarki, kwarai ki na cikin matsala sosai. Abu mai sauki, shi ne na zo mu ga juna, idan muni na bai miki yawa ba, sai mu yi auren mu hankali a kwance, tunda ni dai ba ki da matsala da ni”.

Dariya ta yi ta-ce. “Ka bar wannan maganar don Allah. Ina bukatar addu’a, don ita-ce kawai mafitar”.

“Kar ki damu, kullum ina miki addu’a. Batun zuwa na kuma da gaske na ke miki, kwanan nan za ki ganni Insha-Allahu, don yanzu na kusa na samu zama.

Ki duba ki gani fa shekara nawa, muna magana, duk da on and off ne, ai lokaci ya yi da za mu hadu. Ko ba haka ba?”

“To shi kenan, sai na ganka, amma dai Allah ya sa kar ka zo min da wani abin kwaba lissafin, don hannu na cike yake da matsaloli.” 1

“Kar ki damu, sai dai na tayaki rage miki su.”

“Na gode kwarai, da kasancewarka a rayuwata.”

A lokacin ji ya yi da za ta manta da kowa, ta amince da shi ya shiga rayuwarta da kyau da ya huta radadin da yake kwana da shi a rai.

“Ran yaushe zan zo?”

“Duk randa yayi maka, ba laifi.”

“Sai kin ganni. Insha-Allahu.” Ta kashe wayar cikin jin dadi.

*************
Watanni biyu kenan rabon da ta sa Abdul-Aali a ido, sai dai jefi-jefi su kan yi waya, nan ma idan ya kira baya mata magana irin ta da. +

Iyaka ya tambayi lafiyarsu ita da Danta, sai kuma aike da yake bayarwa ta hannun Mukhtar a ba su. Har kasan ranta hakan yana damunta. 5

Shin ko wani boyayyen shiri ne yake da shi, wanda ya sa shi yin hakan? don ita al’amarin Abdul-Aali na ba ta tsoro.
1

Wannan zuwan Mukhtar da ya yi, ta zaci kamar na kullum ne, sai yake ce mata “Anty Hauwa fa kati na taho miki da shi, aiki ya sameki, sai ki rabawa jama’armu na nan”.

“Haba, Mukhtaar har abin ya tabbata kenan? Masha-Allah! Allah ya nuna mana lafiya, ya sanya alkhairi.”

“Ameen-Ameen, na ga alamar dai zan riga ki, tunda har yau Alhaji Yusuf bai ce komai ba”.

“Kai ni rabu da sha’aninsa, ni auren ma ba shi bane a gaba na yanzu, nan wani wai shi Jamil ya zo ya karaci shirmensa, ina jinsa. It will never be the same”.

“Yaya za ayi to Anty Hauwa, haka rayuwar take sai hakuri. Amma fa akwai solution, sai dai idan ke ce ba ki so”.

“Solution? Ni din wata matsala ce da za a solva ni?” 2

Ya yi dariya ya-ce. “Kusan haka, don ni dai ko da Dakta yake kwance, ce min ya yi baya son bacin ranki kuma ba zan bari, ina ji, ina gani ba, ki na cikin bacin rai, alhali akwai yadda za ayi na kawar da shi.”

“Wanda shi ne mene fa?”

“Yaya Abdul-Aali!” 1

Mai-jidda ta hada rai, No wonder, ita dai ta san dole sai yana da wani Plan, idan ba haka ba ai shirun ya yi yawa, yanzu kuma kanin sa ya turo ya yi mata ta karkashin kasa kenan. 2

“Ban san muna haka da kai ba Mukhtaar. Na dauka kai kam ko kowa ba zai bi bayana ba, kai me taya Dakta kishina ne, amma kuma har da kai?”

“Ko kadan ba haka bane, kasancewata tare da ke din ne, ya sa na ga dacewar hakan, domin Yaya Abdul-Aali ne mutum na farko da ya zo min a rai, idan na duba na ga wanda zai sa ki farin-ciki.”

“Wa ya fada maka hakan?”

“Ni dai kawai na sani, ko kuma ki na so na tona ne?”

Murmushi ta yi, “Ba sai ka na da abin tonawan ba.”

Mukhtaar ya yi dariya, sannan ya-ce. “Tsakanin ki da Allah, duk randa na zo garin nan, ba ki jin kamar ki tambayeni me ya sa ba ki ganin Yaya Abdul kwana da yawa?” 3

Shiru ta yi, domin tamkar ya bude zuciyarta ya gani. Amma kuma ba za ta taba amincewa ba.

“Kai dai sannu da kokarin dikake.”

“Tunda sun yi haka, ni dai na yi shiru, sai kin shigo dai, idan kuma ki na son ki san dalili, to kar ki damu zan fada miki, duk lokacin da ki ka shirya”.

Haka suka yi sallama da Mukhtaar, ya tafi ya bar ta da tunani tirim! A zuciya, na rashin samun mafita.

Satin da ya kama ne, suka yi waya da Mabruka, sun zo Kano, don haka idan ta dan huta, za ta iso mata Dutse. Murna dai ba a cewa komai a wurin Mai-jidda, kusan shekara guda kenan rabonta da aminiyarta.

STORY CONTINUES BELOW


A kwance take, ta ji wayarta na kara. A tunaninta Mabruka ce, don haka tana dagawa ta-ce. “Har kun iso?”

Muryar da ta ji ne ya sa ta yi saurin tsuke bakinta. “Ke ma Assalamu-Alaikum!

Kunya ne ya kamata. “Haka ake amsa, waya ne?”

“Ban san kai bane, na dauka kawata ce Mabruka”.

“Wato kowa cikin doki ake, daga wayarsa tawa ce, sai anyi min yanga ko? Ba ki ga Message dina bane jiya?”

Nan take ta tsume. “Oh Message dinka? Ban gama fahimtarsa bane, shi ya sa ba ka ga amsa ba”.

Ya san sarai tana da niyyar wasa da hankalinsa ne, don haka ya-ce. “Shi kenan, idan ki ka dauki lokaci mai tsawo wurin fahimta kuwa, sai dai ki gani, a aikace”.

Mai-jidda ta gyara zamanta ta-ce. “Ba za ka iya ba.”

“Try me!” Kafin ta-ce wani abu, ya kashe wayar, tana cikin tsuma, ta ji wayar na sake kara, tana dagawa ta-ce. “Idan kayi min haka, za ka yi da na sani…”

“Woah, me ya yi zafi haka, da wa ki ke magana Mabruka ce fa, mun iso, ina ga fa sai kin turo Abdul-Majid mun bata hanya”.

“Oh sorry, to bari ya zo yanzu, kuna daidai ina ne?”

Nan da nan ta sa aka je aka iso da su, a falon Baba ta saukesu, kasancewar tare da Hafiz suka zo, sai da ta tarbesu suka gaisa tukun. Hafiz ya-ce. “Mai-jidda, mun ta jira mu ji an kira mu biki, amma shiru, hakan ya sa muka taho da kanmu”.

“Kai Baban Farida, kai ma har da kai, ka daina bari Mabruka tana fada maka tatsuniya.”

Hafiz ya yi dariya sannan ya-ce. “Tatsuniya ko? Mun dai san Koki ta Gizo ne, saboda haka idan ta yi tsami, za mu ji ai.”

“Zama da madaukin kanwa….”. Mai-jidda ta fada tana dariya.

“To ni dai na bar ku, zan duba wani aboki na a cikin gari, kafin nan kun gama gulmarku”. 3

“To mun ko gode. Ke tashi mu shiga ciki.” Ta daga Farida a hannunta tana mata wasa, suka dawo ciki, nan suka sake gaisawa da Umma, kafin su koma daki. “Yau kuma Alhaji Yusuf din ne ake ta yiwa diri haka?”

“Hmm! Ai da Alhaji Yusuf ne da sauki, na san ranar karewarsa ni da Abdul-Aali ne”.

Mabruka ta zaro idanu tana kallonta. “Abdul-Aali, kanin marigayi?”

“Shi fa”.

“Me ya faru da muguntarsa da tsanarsa har ya hadaku ku ke waya?”

Mai-jidda ta dauki tumbler ta zubawa Mabruka lemo, sannan tace “Wai wani dogon labari kenan”. Mai-jidda ta-ce. “Ai abin ba a cewa komai sai du’a’i, tun ina tunanin wasa yake yi, na fara tunanin zai ji kunya, ya janye, yanzu kam abin ya zamo na karfi da yaji ne”.

Mabruka dai ta kasa rufe baki. “Yau kin shiga uku, kin ga abinda ki ke yiwa maza ko ga shi kin je kin janyo wa kanki Engr Abdul-Aali Sani”.

“Allah ya shiryeki Wallahi, ba ki san yadda na ke Allah-Allah ki iso ba, mu yi shawara”. Nan Mabruka ta gyara zama kan gadon Mai-jidda da kyau hade da tankwashe kafafunta.

“Ina aka tsaya da batun Alhaji Yusuf kuma?”

“Yana shawara.” Mai-jidda ta fada hade da juya idanunta. “Na tsani komai ma ni yanzu, ba abinda yake min dadi”.

“Ba abinda zai miki dadi, saboda ba ki samu abin da ki ke so ba”. Ta fada hade da kurban lemon da Mai-jidda ta zuba mata.

“Ni ba abinda na ke so, baya ga kowa ya barni na huta.”

Mabruka ta yi dariya ta-ce. “Allah ya bude miki idanu, yanzu me ku ke ciki da Engr Abdul-Aalin?”

Mai-jidda ba ta da amsa, illa mika mata wayarta da ta yi ta bude mata Message din da ya turo mata jiya. 3

STORY CONTINUES BELOW


Zare idanu ta yi, bayan ta gama karantawa. “Kin san idan ya yi haka, ba ki da mafita? Yaya za ki kalli Abba da Mama, bayan kin ki amincewa?”

“Taimake ni dai, nace maku Abdul-Aali mugu ne, duk duniya ba na biyunsa.”

Mabruka ta yi dariya sosai, sannan ta-ce. “Dole dai mu san mafita, tsaya ma tukuna, ya fadawa matarsa zai yi aure?”

“Eh, haka dai ya fada min kwanaki da nace zan mata waya”.

“Amma ki na tunanin anya ta san ke yake so?” Mai-jidda ta yi shiru, tana tantamar hakan, don yadda ta san Hamamatu kamar yunwan cikinta, da tana da labari da ta dira a Dutse.

“Ba ta sani ba. Me ki ke nufi?”

“Lokaci ya yi da za ta san cewa Abdul-Aali ke yake so…” 5

“Ke fa ba ki da kyau, za ki je ki sa ta daga hankalinta a banza, bayan ni ba auren sa zan yi ba.”

“Oh, ke yana nan ya kidima miki rayuwa, ke kuma sai ki zauna banda kuka da tausayin kanki, ba abinda ki ke yi ko? Shi ma ai yana da duniyarsa, saboda haka sai ki dan wargaza masa, zai sarara miki.” 3

“Ni gaskiya ki sake shawara, wannan bai min ba, duk abin da zai sa na bata da Mamin Mimie, ba na son sa, hakan ya sa tuntuni ban sanar da ita ba, saboda kowa ya san yadda take son mijinta.” 2

“Allah Sarki, mijinta kuwa ga shi ya bige da haukar son matar Dan-uwansa. Kai wannan gida naku akwai kallo, don Allah ki amince ya aure ki mana.”

“Da ma ba ki zo ba. Farida ta fi-ki amfani.” Ta fada tana bankawa Mabruka harara.

“Maganar gaskiya, ke me ya sa ba ki son maganar auren Engr. Abdul-Aali?”

Murmushi ta yi ta-ce. “Ke ma kin fi-ni sani, har sai nayi miki bayani?” Idanunta suka kawo kwalla, ta yi saurin hadiye su.

“Yau ina ganin ikon Allah, na san ba ni na fara fada miki wannan maganar ba, amma kin yi wa kanki adalci kenan?”

“Ban san me na yiwa kaina ba, abin da na sani shi ne zuciyata ba tawa bace da zan bada ita ga wani.”

“Yaushe ne auren Mukhtaar din?”

“Sati na sama. Insha-Allahu, za ki je ne?”

“Idan kin gayyace ni ba. Ko ba komai zan duba Mama, ya kwana biyu ban ganta ba, dattijuwar kirki, ai ko albarkacinta ma ya ci ki saurari Engr.”

“Na ji, shi kenan.” Har sai yamma Hafiz ya dawo ya dauke su. Mai-jidda ta cika Farida da kyaututtuka iri-iri. Kwana ta yi tana tunanin abin yi.

***********

Ta tashi a aiki ne suka fito da Walida, suna sallama, inda kowacce za ta wuce gida, sai ga motar Alhaji Yusuf. Walida ta-ce.

“Mai-jidda ga mutumin ki fa”. Mai-jidda ta-ce “Mutumina ko mutumin matarsa.”

“Ni kin ga tafiyata, Mai-gida zai dawo daga tafiya, bari na je na kammala aiki na, sai da safe.”

Kafin ya yi Parking. Walida ta zille ta bar Mai-jidda, hakan ya sa Mai-jidda tsayawa daga bakin ofis din, don su gaisa. Amma sai ta ga yana kiranta a waya, ba tare da ya fito daga motar ba.

Alhaji Yusuf baida dama. Cikin taku daidai ta karasa har motarsa. Yana bude motar, ta gane nufinsa, ta shiga su tafi. “Yallabai da fatan ba sace ni ka zo yi ba, da yammacin nan?”

Dariya ya yi ya-ce. “A tsakanina da ke, waye ya iya sata, bayan ke har cikin jiki na ki ka shiga, ki kayi min sata?”

Mai-jidda ta yi murmushi, ta bude kofar motar ta shiga. “An wuni lafiya?”

STORY CONTINUES BELOW


“Alhamdulillahi! Sai dai na kasa sukuni har sai na taho ganinki, hakan ya sa ki ka ganni da yammacin nan.”

“Yallabai, wai har ni ce zan hanaka sukuni? Ayi min afuwa, to me zan yi? Ka samu sukuninka?”

Murmushi ya yi, ya tada motar, ita dai tafiya kawai ta ga suke yi, ba tare da ya fada mata komai ba. “Abu daya na ke so, kuma kin san shi. Hauwa, mu yi aure.”

Ta dube shi cikin yanayi na sakin fuska, ai ko dama can maganar da suke yi kenan. “Ba wata shekara ba, ko wani wata, mu yi aure cikin wannan watan.”

Wannan ya sa ta ke masa duban mamaki. “Ina sonki da yawa, kuma ba na son na rasa duk wani dama da zan samu na mallakarki a matsayin matata.” Kallonshi takeyi idan don kyaune da fasali da ma abun hannu Yusuf karshe ne, domin kana ganinshi kaga wadannan a zaune tare dashi, haka nan ilimi. Gashi yana da shekaru don a babu a babu ta san zaiyi arba’in da biyar, so kwarai tana ganin kimanshi. 2

Musamman yanda ya iya kalaman kwantar mata da hankali duk lokacin da ya ganta cikin damuwa. Ko bai fada ba ta san yana sonta sosai. Matsalar dai daya ce ta gidansa.

“Yusuf.” Ta kira sunan sa a tsanake. “Kai ma ka san na amince da kai, kuma babu wata wasa a tsakanin mu, ni a shirye na ke da na aureka, muddin kai ba ka da sauran matsala da iyalinka.”

Ta dubi yatsunta ta-ce. “Ni dai fatana ya zama ko na amince gaba kar a kuma samun wata matsala, idan ka gama warware matsalar Yayata, to shi kenan ko gobe za ka iya isowa gida, wannan ba laifi.”

“Kar ki damu da wannan, mun zauna mun yi magana sosai. Kuma ita ma (Hajiya). Mum dina ta fahimci komai, don haka babu sauran abin da za ki yi shakku akai.”

A gaban (Sahad Stores) ta ga sun yi Parking, nan suka shiga ya mata saye-saye, sannan suka koma gida, wajen biyar da rabi suka isa kofar gidansu Mai-jidda.

“To Hauwa, na gaishe ki, ni zan koma kenan Insha-Allah.” 7

“Amma yanzu za ka koma, ba za ka bari zuwa da safe ba, idan Allah ya kai mu?”

“Kar ki damu, mun saba tafiyar dare, zuwa issha Insha-Allahu ina Kano. Gobe dai ku na da baki”.

Mai-jidda ta yi murmushi mai hade da ‘yar jin nauyi sannan ta-ce. “To Allah ya kai mu, ya kuma kiyaye hanya. Sai da safe kenan.”

“Allah ya kai mu lafiya, take care.”

Wani yaro ya kira, ya sa ya shigarwa Mai-jidda da sayayyar da ya narka kudi wurin yi mata su, bayan ya fito, ya dauki kyauta yayi masa, sannan ya shige. 5

Umma tana ta kallon yaro, sai shigowa yake yi da kaya niki-niki a hannu.

“Mai-jidda, kasuwa ki ka wuce ne daga wurin aikin?”

“Hmm! Umma, Sahad muka fito da Alhaji Yusuf, yanzu ya ajiyeni, ya wuce Kano. Yana mika gaisuwarsa ma.”

Umma ta rike haba sannan ta-ce. “Da dai ba ki da wannan rigimar, na rasa amfanin sa a yanzu, me ya kai ki sa shi kashe kudi da yawa haka?” 2

“Umma, musamman ya daukeni a wurin aiki muka tafi, haka duk abin da ki ka gani, sa ni a gaba ya yi, sai da na dauke su. Ni ko yanzu zan iya mayar masa da su.”

“To Allah ya amfana, amma kin san Babanku ba zai so hakan ba, musamman yadda ki ke karbar kayan hannun sa.” Mai-jidda dai shiru ta yi, ba ta ce komai ba.

Bayan an idar da Sallah ne, ta watsa ruwa, suna cin abinci da Ummanta, sai ga Abdul-Majid ya shigo. “Yaya Mai-jidda, ke kam ba ki san wani abu ba?”

“Don Allah, idan za ka yi magana, ka yi kai tsaye, meye na kame-kame?”

“Ke dadina dake ba kya more zance Wallahi. To dama zance miki ne, ki shirya ki fito Injiniya na son ganinki ku yi magana, tare da shi muka yi sallar magarib a masallaci.”

STORY CONTINUES BELOW


Yau ta ga ta kanta da shegen nacin wannan mutumin, yanzu kuma ko me ya kawo shi? Don ya ga sakon da ya turo mata, bai yi tasiri ba, shi ne zai kinkimo kafafu ya taho da kansa. 4

******

A falon ta same shi, ko ruwa yau ba ta fito masa da shi ba, don ya riga ya kai ta makura.

A tsume ta gaishe shi, maimakon ya amsa mata gaisuwar, sai cewa ya yi “Dole ki bata rai, ki na kau da kai, kin san ba ki da gaskiya, shi ne har da wani ficewa yawo da wannan mutumin ko?” 2

Ta dago kai fushi har diga yake yi a fuskarta ta-ce. “Na sha fada maka ba ruwanka da wanda ya zo wurina, don haka ban ga meye damuwarka ba.”

Ya sauke ajiyar zuciya, domin kansa ne yayi masa zafi sosai. “Na ji ba ruwana, amma idan har za a rinka daukar min ke ana zuwa yawo, ai atleast na cancanci na sani ko?” 7

“Wannan ma bai shafe ka ba. Yaya su Mama?”

“Lafiyarsu kalau, suna gaisheki.”

Bayan ya amsa mata ne ya-ce. “Jidda, har yau ba ki ce komai ba, wannan yana nufin shi kenan, na yi duk abin da na ga ya dace?”

“Wannan kam ai tuntuni radin kanka ka ke yi, don haka damuwarka. Ni dai na fada maka matsaya ta, domin kuwa tsakani na da kai, ba maganar so, bare kuma aure, idan za ka hakura ka daina bata lokacin ka, da ya fi mana duka.”

“Me ya sa ki ke wahalar da ni ne, eyye Jidda?” Ya fada a marairaice.

“Ba zancen wahala, ni na fada maka ra’ayina game da kai, ba zai yiwu bane, asali ma gobe Alhaji Yusuf zai yi tambaya. Insha-Allahu saboda haka ka ga magana ta kare.”

Wani tashin hankali Abdul-Aali ya tsinci kansa a ciki marar misaltuwa. “Na ji Jidda, tunda haka ne.

Amma kuma ina son ki san I won’t go down, ba tare da fighting a kanki ba. KE NA KE SO! Kuma KE ZAN AURA Insha-Allah, don haka ki zauna cikin shiri.” 8

“Kana nufin ko ina so, ko ba na so sai ka aureni?”

Murmushi ya yi mai kashe jiki ya-ce. “Oh Jidda, kina so za ki aureni, sai dai ki ki furtawa ko ki ki nunawa, saboda kar nace miki na fada miki. Amma ba za ki yi nadama ba. Insha-Allah.”

Jin shi kawai take yi, ta san babatu yake yi kawai, tunda ita-ce mai amincewa, zabinta za ta aura, ba abinda zai sa ta auri Abdul-Aali kuwa.

Ta rasa ma yadda aka yi, kamar ba ciki daya ya fito da Dakta ba, koman su daban, a bangare guda Rayyan mutum ne mai hakuri da gentleness, sannan ga tausayi akan abin da yake so.

Daya bangaren kuma Abdul-Aali mutum ne mai naci, nuna isa da zafi akan abin da yake so. Haka suka rabu baram-baram! Ranar.

*****

Farin ciki ne fal! Ya cika ta da yamma da Abdul Majid ya zo ya sanar da Umma bakin Baba sun iso. Ko ba komai, yau idan aka yi magana mutanen Alhaji Yusuf shi kenan, domin ta riga ta san abu guda, muddin Baba ya amsa abu, to ba me sa shi ya canza.

A daren Alhaji Yusuf ya shaida mata. “To, gimbiya an samu Baba da magana kuma ya yi farin-ciki da zuwan su, ya kuma bada lokaci ya-ce zai same su da amsar tambayar.”

“To Allah ya sa a dace, na ji dadi kuwa”.

“Na gode sosai Hauwa, ba abinda zan ce miki, domin ba ki san irin farin-cikin da na ke ciki ba.”

Haka nan ita ma ta tsinci kanta da farin-ciki, domin ko ba komai ta kusa ta yar da kwallon mangoro, ta huta da nacin kuda. Take ko tayi waya ta fadawa Yaya Maryam abun da yake faruwa.

“Maa sha Allah nayi murna kwarai, Allah sanya alkhairi ya kade fitina.”

“Ameen Ya Maryam, ina su Aisha suke?”

STORY CONTINUES BELOW


“Tana ciki tana home work ne inaga.”

“To ki gaishe su, sai da safe.”

“Allah ya tashe mu lafiya.”

********

Da safe ta shiga gaida Baba ne, yake cewa “Ni Hauwa, ban gane abu guda da yake faruwa ba?”

Nan ne gaban ta ya fadi, me kuma yake faruwa? “Jiya da safe Alhaji Sani ya kirani a waya yake min maganar ki da Dan wajensa Abdul-Aali, sannan kuma da yamma, sai ga mutanen Yusuf Takai sun zo min da makamanciyar maganar.”

Nan ne gaban Mai-jidda ya shiga dukan uku-uku! Yaya Abdul-Aali zai turo? Bayan ba ita bace ta sa ya yi hakan, ai kuwa za ta cewa Baba ba ta son sa.

“To duka dai nace zan waiwaiye su. Yaya za ki sa duka su sameni lokaci guda, bayan kin san yadda tsakani na yake da Alhaji Sani?”

“Baba, dama fa Abdul-Aali ba wai mun daidaita bane da shi.”

“Ban gane ba ku daidaita ba, bayan ina ganin ko wane sati biyu ko sati yana sintirin kan hanya dominki?”

Tayi shiru, ai ta san yawan zuwan Abdul-Aali sai yasa Baba ya yi magana, don dama shi bai cika son tara samari ba.

“Ni dai idan zan ba ki shawara, tunda kin ga Abdul-Aali dai Dan-uwan mijinki ne mai rasuwa, kuma ko ba komai, kin hada jini da su. Ko don kulawar Dan nan da kuma mutuncin da yake tsakani, ina ga zai fi dacewa, ki koma wancan gidan.” 2

Mai-jidda kuwa tashin hankali ne ya hana sashin iya furucinta dake kwakwalwarta ya motsa, bare ya aikata aikinsa na magana…

Jin ta yi shiru Baba ya-ce. “Kar ki damu da maganar shi Yusuf, ni zan san yadda zan masu magana, amma idan kuma ki na ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi, fani’iman. Zabi naki ne”.

Mai-jidda dai tana zaune, ba uhm! Ba uhm-uhm! Can ya-ce ta tashi ta je, ba tare da ta ce komai ba, ta bar falon.

Kwananta biyu tana tunanin wannan batu na Baba, bugu da kari ga sakon da Abdul-Aali ya turo mata kwanaki. 2

Hakan ya sa a safiyar kwana na biyun, ta-ce “Umma dai na yi shawara ne, na ke son na fada miki”.

Umma ta-ce. “To shawara kuma?” Abin ya bawa Umma mamaki ganin kwanakin nan duka. Mai-jidda ba ta da lokacin komai daga aiki sai tunani, randa ba ta tunani kuwa, to sai a sameta tana kuka.

“Na amince zan auri Abdul-Aali”. Ba Umma kadai ba, har ita mai bayanin furucinta ya ba ta mamaki kwarai. Abdul-Majid kuwa da yake bakin kofa, kwashewa ya yi da dariya ya-ce. “Umma Wallahi wani abu ya shiga kan Yaya Mai-jidda”. 7

Harararsa ta yi. “Wa ya ce ka sa baki a maganar mu?”

“Wai gani na yi duk duniya, ba wanda ki ka tsana irin Injiniya, haka kawai ki tashi a barci ki ce shi ki ke son ki aura, ai dole nace an samu matsala.” 6

Umma ma dai ta zargi hakan har cikin ranta, amma dai sai ta-ce. “Wani abu ne ya faru Mai-jidda? Ko dai dole aka saka ki?”

“Umma, na canza ra’ayina ne, ko kuwa don nace ba na son sa, sai ya zama ba zan iya auren sa ba?”

“A zamanin nan wa yake auren rashin so? Amma tunda haka ne, shi kenan, zan fadawa Baban ku. Allah ya sanya alheri.” Mai-jidda ta ji wani abu ya wuce mata a wuya da kyar. 1

*******

Satin da ya kama ne, ake ta hada-hadar bikin Mukhtaar, gidan a cike yake da jama’a kasancewar an kwana biyu ba ayi biki ba a gidan.

Jama’a da dama sun samu halarta, wannan ya sa su Mai-jidda ba su ga ta zama ba. Suwaiba ma ta taho da yaranta daga Kaduna.

Sai dai duk inda Hamamatu take, to Mai-jidda ba ta cika sakewa ta yi hira ba, saboda nauyin ta da take ji, tana mamaki da har yanzu ba ta san ita Abdul-Aali yake nema ba.

STORY CONTINUES BELOW


Ta kuma rasa hanyar da za ta bullowa abin, don haka ruwansa idan ya ga dama ya fada. Gidan Mukhtaar dake Jan-bulo za a kai amarya, don haka kasancewarsu gidan maza, ba wata hidima sosai za ayi ba, sai walima da aka shirya na zuwan amarya.

Ranar Asabar da yamma ta koma gidan Yaya Maryam da Mabruka, nan suka dan taba hira, kafin Hafiz ya zo daukanta, dukkan su mamakin Mai-jidda suke yi.

“Meye ku ke min wani irin kallo? Ku ka matsa da cewa na tausaya masa, na duba albarkacin su Mama ko kuwa Muhammad, abin da na duba kenan kuma na amince, za ayi finalizing komai, sannan ku na min kallon zombies.”

“Kawata shin kina farin-ciki da zabin ki?”

Mai-jidda ta-ce “Eh mana, me zai sa na amince, bai cin hakan?” Ta rangada masu karya. 1

“To Allah ya tabbatar da alkhairi ya nuna mana lafiya.” Ta tashi zuwa kicin ne. Yaya Maryam ta-cewa Mabruka. “Kin yarda da gaske ta amince?”

“Hmm idan dai Mai-jidda ce za ta aikata, ki daina mamaki, abin tausayin dai Engr. Abdul-Aali ne.” 2

Mabruka na tafiya ta shirya ta-ce. “Yaya Maryam zan koma na san war haka an kusa kai amarya.”

“Ba za ki jirani mu tafi tare ba?”

“Ke da nawan (Saibi)kin nan, sai dai na tafi da A’isha, kya shirya Nabil ku taho tare.” Suka wuce kai tsaye gidan bikin, suna zaune ne Mai-jidda ta-ce.

“Wai yau Mukhtar ba dama buri ya cika, tun dazu ya kasa zaune, shi ayi a kai masa amaryarsa, yana ji da Kamilar san nan.”

Kwafa Hamamatu ta yi ta-ce. “Hmm! Duk na lokaci kadan ne, lokacin da zai tashi maka mata wulakanci, kina ina?”

Mai-jidda ta dubeta a razane, saboda ta manta da halin da ake ciki “Yaya kike kallona haka? Ko kina nufin ba ki san Abdul-Aali aure yake shirin yi ba?” 5

Mai-jidda ta nemi yawu, ta hadiya don ta jika makoshinta da ya bushe. Nan da nan ta rasa, a take ta bude ruwan da ke gefenta ta kwankwada, sannan ta-ce. “Mamin Mimie, haba dai, ke kuma mu bar maganar nan”. 4

“Da gaske na ke fada miki, ai namiji, sai a bar shi, yana can sai bare-bare yake yi, a garin nan suka hadu. Allah kadai ya san ma ko yana can wurinta, shi ya sa ma ki ka ga ban yi wani dokin tahowar ba.” 4

Mai-jidda dai banda ware idanu, ba abin da take yi, ta rasa yadda za ta kashe maganar ba tare da tona kanta ba. Sannan tana tunanin yadda za ta yi, duk randa Hamama ta gane ita mijinta yake so. 2

“Ai mazan ne sai hakuri, ke dai ki kwantar da hankalinki, ki zuba masu idanu. Allah ya shige miki gaba”. 8

“Ameen, na gode Anty Hauwa, ni na dade da share maganar a raina, shi kansa Abdul-Aalin na dade da sa shi a gefe, zaman yarana kawai na ke yi.”

“Akan me ya sa? Mijinki ne, sai ki bari don zai yi aure, ki nisancen shi? Ban ga dalilin hakan ba, ba sai ki jira ki ga anyi auren ba ma tukuna?”

Hamamatu ta yi murmushi ta-ce. “Allah ko? Na yarda dake Anty Hauwa, ke dai sai mun zauna, za mu yi shawarar abin yi.” 1

“A’a ki samu dai Anty Suwaiba sune manya.” 4

Tana fadan hakan a ranta ta-ce. “Abdul-Aali ka cuceni, da wane ido zan kalli Mamin Mimie, bayan ka hada mu fada?”
4

****

Ran lahadi da safe ta gama gyara dakin Mama, kasancewar kafa ta dan dauke, tana zaune tana karyawa. Ya shigo cikin uwar dakin. Ba tare da ta ce masa komai ba, ta ci gaba da cin abincinta. “Ba tayi ne abin ma?”

“Bari na sa Yahanasu ta sako maka wani, wannan ya kare.”

“Miko min shi zan ci haka nan.” Ya fada yana kallon yadda take shan kamshi.

STORY CONTINUES BELOW


“Wai kai matarka bata baka abin karyawa bane, ka fito za ka cinyewa mutane nasu?”

Kasa-kasa yake kallonta. “Jidda ki yi abinda ki ke so, miko min Plate din”.

“Ni ban gama ba.” Ta fada fuska a gintse.

Gani kawai ta yi ya sauko ya zauna, ya sa hannu a cikin Plate din abincinta.

A razane ta dube shi, sannan ta-ce. “Allah ya shiryeka Wallahi. Kai ba ka ma jin nauyin Mama, ko ba komai gidan nan a cike yake da jama’a”.

“Ban gansu ba anan, ke kadai na ke gani, kuma ko ni ne na yi batan kai? Kamar dai wancan satin, an min tambayar auren ki, kuma har da kudin aure na bayar, saboda haka, idan za ki ci abinci, ki san da cewa tare da mijinki za ki ci, ko kuma ki jira sai ya koshi, ki ci.” 5

Idanunta ta kada, sannan ta zare hannunta, ba ta ida cirewa ba, ya rike ya-ce. “Zauna ki karasa.”

Yau tana ganin ikon Allah, wata tsiyar sai a wajen Abdul-Aali. “Ka san me ka ke shirin yi kuwa? Jiya Mamin Mimie take fada min halin da take ciki, a rashin sanin cewa ni ce matar da za ka aura, ka san ba kyau yanke tsakanin zumunci ko?” 8

Kofin shayinta ya dauka, daidai setin gun jam bakinta ya sa bakin sa, ya kurba a hankali, sannan ya ajiye. Mai-jidda tana kallonsa, kamar ta fincike shayinta. 10

“Me na ke shirin yi, ko me muke shirin yi? Na danne bakinki, nace miki ki amince da aurena? Ke da kanki ki ka ce kin amince, don haka kar ki yarda ki dora min laifi.” 5

“Ai duka Dan-uwan dayan ne, idan ba ka matse baki na ba, ai na amince ne, bayan ka yi min barazana da abinda ka san ba zan ki ba ko? So cheap of you. 2

Ba za ka iya sa macen da ka ke so, ta so-ka ba, sai ka bi ta karkashin kasa. Har da sa Abba a cikin maganar”. Idanunta ta sake juyawa. Ta ja tsaki a ranta.

Kallonta ya yi ta kasan idanu, ya dade bai ji abin da yake ji yanzu ba game da ita. Hakan ya sa ya yi saurin mikewa, don ya wanke hannunsa. 2

Amma kuma ganin Hamama da ya yi a tsaye ne, ya sa shi tsayawa cak! Mai-jidda ta mike, don ta ga me ya hana shi tafiya, kasancewar tsawon Abdul-Aali ya tare mata kofar. 6

Tana mikewa, ta ga Hamamatu a bakin kofar dakin, ji ta yi tamkar za ta fadi, don tsabar tashin hankali, ta daga idanu ta dubi Abdul-Aali ta hadiyi sauran abin da ke bakinta. 1

Kafin ta san abin fadi, jin saukar mari ta yi a fuskarta. Daidai lokacin da Abdul-Aali ya daga hannu zai rama mata. Mai-jidda ta yi saurin rike hannun shi, ta matsa da baya. 8

Hamamatu ta-ce. “Dake ni Abdul-Aali, ka mareni. Munafukai. To Allah ya tona asirin ku, wato abin da za ki min kenan Anty Hauwa? Amma, kin ba ni mamaki kwarai, yadda na ke ganin girmanki da mutumcin ki. 2

Ashe za ki iya cutar da mutum kamar ni? Kai kuma shi ya sa ka ke ta kaffa-kaffa, kar na san matar da za ka aura, wato ka san sharrin da ka kulla kenan ko?” 1

Ta sauke hucin numfashi ta-ce. “Ke kuma idan shi namiji ne zai iya aikata hakan, ashe ba ki san ciwon ‘ya mace, na ‘ya mace bane?

Har ki na da bakin ba ni shawara, kin cuceni, kin shige jiki na, kin san duk wani sirrina, sannan kin zagaya za ki auri mijina. To Allah ya fi-ku munafukai.”

Hayaniyar da ke tashi a dakin ne ya sa su Mama shigowa, tana ganinsu su uku, ta san an yanka ta tashi kenan….! 1

Mama ta-ce “Lafiya? Me yake faruwa?” Cikin kuka Hamama ta-ce. “Mama ki na gani, ashe Abdul-Aali wai Anty Hauwa zai aura, shi ne ya yi ta boye min. Yau Allah ya tona asirinsa, na dawo na ba shi wayarsa, ya manta. 1

Ashe shi kam ya taho wajen rabin ransa ne har ma tare suke cin abinci, yanzu ashe ko kunyar Dan-uwanka ba za ka ji ba. Yana mutuwa za ka aure masa mata?” Magana take yi, ba ta ma damu da Mama na wurin ba, don bacin rai. 5

Mama ta dubi Hamama ta-ce. “Zauna Hamamatu, ki kwantar da hankalinki ki yi hakuri…” 2

“Mama yaya zan yi hakuri, bayan sun cuceni? Idan dai har ya aureta, to ni kuwa ba zan zauna ba gidanmu zan koma.” 2

Abdul-Aali ya shafo sumar shi cikin damuwa. Mai-jidda kuwa tuni ta koma gefen gado ta zauna, sai kuka take yi. “Ya isa haka nan, ki saurareni. Na san da ciwo abin da ki ke ji yanzu. 2

Amma kuma kin san komai da lokacinsa da kuma qaddarar sa, don haka ba na so ki tada hankalinki, da ki ka san zai kara aure, ai kin kwantar da hankalinki, saboda Hauwa zai aura, ai ina ga da sauki ko?

Tunda kin san halinta kuma ita ma ta san naki, amma don Allah kar ki sake cewa za ki tafi, ki yi hakuri ki yi zaman ki, ke da gidan ki kuma ina za ki je?”

Hmmm! Inji mai ciwon hakori, ita jin Mama kawai take yi, dama ta dade da sanin cewa ta fi son Anty Hauwa a kanta, don haka mikewa kawai ta yi ta bar dakin. Da sauri Abdul-Aali ya bi bayanta zuwa mota… Mai-jidda da take dunkule wuri guda kuwa. Mama ta dubeta ta-ce. “Ki bar kuka Hauwa, kar wannan abu ya tayar miki da hankalinki.”

“Mama dama abin da na ke gudu kenan, saboda na san tashin hankalin da hakan zai haddasa, amma ya kasa fahimtar hakan. Yanzu Yaya zan yi da Hamama? Ya shiga tsakanin mu.”

Mama ta-ce. “Abu mai sauki, meye abin rikitarwa, bayan wannan ma shi zai sa ku kara hade kanku ku zauna lafiya, amma ku na tayar da hankulanku. Insha-Allahu ba komai, shi ya san yadda zai shawo kanta ta hakura, kar ki samu wani kokwanto a zuciyarki.” 2

Mikewa ta yi ta wanko fuskarta, sannan ta kimtsa ta-ce za su koma Dutse, nan Mama ta sake ba ta baki, amma Mai-jidda ta san abin da kamar wuya, gurguwa da auren nesa.

Ta tafi da zuciya mai nauyi kafin ta shiga gida a Dutse, ta gama yanke shawarar rabuwa da Abdul-Aali, don ba abinda yin hakan zai kawo sai kunci da bakin ciki da rarrabewar zumunci, gwamma ta hakura ta amince da sharadinsa. 2

Lokacin ne damuwa ta-ce wa Mai-jidda salamu-alaikum! Domin kuwa ta rasa me daya za ta yi. Shin za ta auri mutumin da ya tsaneta ne, don ta zauna da Danta, ko kuwa za ta rabu da Danta, don ta auri mutumin da take ganin yake da kyautatawa? 6

Ba ta fadawa kowa a wurin aiki ba, game da baikonta da Abdul-Aali, don haka ba ta tare da wani shakkun labarin ya isa ga Alhaji Yusuf, ta fi son ta fada masa da kanta. Cikin satin kuwa ya zo daga Kano, kai tsaye ofis din su Mai-jidda ya shiga, kowa sai kallonsa yake yi, amma ko a jikinsa.

“Yallabai lafiya? Lokacin aiki ne fa.” Ta fada a hankali tana ‘yan waige-waige. Kujera ya ja ya zauna sannan ya-ce.

“Ina ruwana da lokacin aiki, na zo ganinki ne kuma ke zan gani, ko kina da wata matsala da hakan?”

Kai kawai ta girgiza, ita dai nata ido, don ta rasa me daya za ta yi.

“Za mu je gida ne, ko anan za ka ganni?”

Ta fada tana kallonsa. “Nan ma ya yi, gobe ne ranar da Baba ya-ce zai sanar da Kawuna ko me ake ciki, hakan ya sa na taho.”

Mai-jidda ta ji kamar an zunduma mata guduma a ka. Yau ta shige su, idan Alhaji Yusuf ya samu labarin abin da yake faruwa. Yaya za ta yi? Me ya sa komai baya tafiya mata daidai ne?

“Allah ya nuna mana.” Da kyar kalaman suka fito daga bakinta tana yake, haka Alhaji Yusuf Takai ya zauna suka sha hirarsu, ko a jikinsa, yayin da Mai-jidda take jin zuciyarta tana mata gudun fanfalaki, wurin neman hanya ma-fi sauki da za ta sanar da shi komai. Yana fita ‘yan ofis din, suka hau mata tsiya. “No wonder Hajiya, muka ga ke din ta daban ce. Allah ya sanya alkhairi.”

Tana makale da murmushi a fuskarta har suka gama, ta dubi Walida ta damke cikinta dake ta faman juyawa. “Na ga ta kaina Walida, zan tada yaki a garin nan. Yaya zan yi da Alhaji Yusuf? Ina matukar tausaya masa, kuma ina muradin kasancewa da shi, sai dai matsalata a yanzu, ita-ce Injiniya ya kai goro gida.”

Walida ta dubeta galala cikin sauri-sauri ta-ce. “Ga-rin yaya? Ki na kallon ina ya kai goro gida? Kin manta kin tsane shi, baya sonki, ba kya son shi? Me zai sa ku yi aure? Me ya kai goron shi gidanku? Mai-jidda ki na kwaya ne?”

“I know, na yi hauka ko Walida? Ban san yadda zan yi ba. Ba na son Alhaji Yusuf ya tafi, kuma ba na son a yi rigima, don ita na baro a Kano da matar Abdul-Aali ta gano ni yake nema da aure.”

“Big issues. Mai-jidda, big issues. Ina da shawara”.

“Menene fada min da sauri.”

“Ki fadawa Alhaji Yusuf gaskiya”.

“What! Kin ma ce na rasa mijin aure kenan, don ni kam ba zan auri Abdul-Aali ba.” Walida ta tsaya kallonta sannan ta-ce. “To kuwa dole ki zaba ko Abdul-Aali ko rigima da su Baba”. Har gwamma rigima da Baba zai zo ya wuce, amma Engr. Abdul-Aali, Danger zone. 1

STORY CONTINUES BELOW


Ranar ba ta jira lokacin tashi ba, ta koma gida, don ta rasa me yake mata dadi, kamar da wasa ta kira Muhammad ta-ce masa. “Muhammad, a san Uncle Yusuf da Uncle Abdul-Aali ko?”

Muhamamd ya-ce. “Eh na sansu, ba duk suna kawo min kayan wasa da abin dadi ba. Kuma Uncle Abdul yana kai ni yawo.”

Eh ta amince tunanin yaron zai dan karkata, saboda kayan wasa, amma dai da shi za ta yi shawara, watakila ya dan fita tunani. “Ka san Mamin su Mimie?” Ya daga mata kai. Sannan ta ci-gaba. “Ka na son mu je gidan su Uncle Abdul-Aali mu zauna da su Mimie, amma Mamin su Mimie tana fada da mu, ko kuwa ka na son mu je gidan Uncle Yusuf bamu fada da kowa? Well, ana dan fada amma ba da wanda muka sani ba.”

Muhammad ya yi shiru, yana kallon Mamansa wani iri. “To Mama me ya sa za mu bar gidan Umma?” Eh fa, yana da Point anan. Tunda ta rasa abin da za ta zaba, me ya sa ma za ta sake wani auren?

“Ba ka san taimakon da kayi min ba, na gode Muhammad dina. Allah yayi maka albarka, je ka yi karatunka.” Yana fita, ta saki ajiyar zuciya. Idan ta-ce ta fasa auren su duka shi kenan ai, kowa ma ya hakura. Gaba idan Allah ya fito mata da wani daban, sai ta aura. 2

*******

Jikinta ya yi sanyi, ganin irin kallon da Baba yake mata, daga bisani ya-ce. “Hauwaa, ina fata ba kwaya ki ka fara sha ba ko?” Ta san maganar ta girmama, wannan ya sa ta kasa amsawa. 2

“Don dai mai hankali kam ba zai dau maganar da ki ke fada ba, akan me za ki yi ta yawo da hankalin mutane, kin dauka haka zan sa miki ido. Yau ki budewa wannan kofar gidana, gobe ki shigo da wannan, sannan ki kasa tsinana abin arziki da mutum guda?

Wanda na ke ganin kin zaba, har an kammala magana, bayan kin san irin mutumcin dake tsakani na da su, za ki zo ki ce kin fasa a warware, an fada miki kitso ne baikon da za a tsefe shi, duk randa aka ga ya tsufa? Ba na son rashin mutumci. Umman naki tana ina? Ta bar ki ki ka yi wannan shawarar? To shashancin ya isa haka. 1

Daga yau kar na sake ji kin yi irin wannan maganar. Kuma tunda kin kasa tsaida ranki wuri guda, zan yi magana da Alhaji Sani a daura auren kawai, sai mu ga ta warware baiko. Shirmen banza, shirmen wofi. 2

Ashe idan ba ki yi tunani don kanki ba, ba za ki yi don Danki ba? Kin tsaya ki na ruwan ido, wani ruwan ido, ya rage miki kuma? Ki tashi ki wuce min anan.”

Tana hawaye, ta fito daga falon. Umma ta bi-ta da kallo, ai dama ta san a rina, kuma Baba ya mata daidai da ya warware Mai-jidd,a amma ace mutum baida alqibla.

Ganin abin ya fi karfinta ne, ta nemi ganin Alhaji Yusuf, sai dai koda ya zo, ta rasa ta inda za ta fara masa bayani. Kwatsam! Sai ga Abdul-Aali. Allah take roko kar ya lalata mata ranta, don yanzu kam ya gama batawa, abin da yayi saura kadan ne. Kiris! Take jira su yi kaca-kaca! Don ita komai ta fanjama-fanjam!

Sun gaisa da Alhaji Yusuf, sai dai duk cikin su, ba wanda ransa yake kal! Wuri ya samu ya zauna ba tare da ya-ce da Mai-jidda komai ba, ganin haka ta rasa me za ta yi daya. Abdul-Aali ya sauke jaridar da yake karantawa, sannan ya-ce “Kar na takura ku fa, ku gama tattaunawarku, zan jira.” 6

Alhaji Yusuf ya kalle shi, ransa a bace. “Ina ga zai fi dacewa ka ba mu (Privacy), don magana mai muhimmanci muke tattaunawa”.

“Oh, ni ne kar ka damu. Sallamar ku ba ta dameni ba.” Ganin kallon da Alhaji Yusuf yake masa ne, ya sa ya dubi Mai-jidda ya-ce. “Oh, ba ta fada maka ba kar dai?”

“Me kenan?”

Mai-jidda ta hau rarraba idanu, zuciyarta na bugawa tamkar zai sa ta gudun fanfalake. 1

“Ba ta fada maka cewa ta karbi kudin aurena ba?” Mai-jidda ta zaro ido, ai wannan wulakanci ne, yana magana tamkar laifinta ne, ko kuwa ita mahandamiya ce. 7

STORY CONTINUES BELOW


Haka ya ci gaba. “That’s strange, ganin cewa Next week za a daura auren, idan Allah ya ba mu aron rai.” Da Alhaji Yusuf da Mai-jidda duk suka kalle shi cikin mamaki a karo na biyu. Alhaji Yusuf ya tsani nuna isar Abdul-Aali sosai.

Mikewa ya yi ya-ce. “Look, Engr. Don ka na gani ina (Tolerating) abubuwan da ka ke yi, wannan ba shi zai sa ka yi ta kai ni makura ba, don kawai ka na neman aurenta wannan ba shi zai ba ka dama wajen wulakanta ta ba. Yanzu wane irin sabon wasa ne wannan?” 3

Abdul-Aali ya yi murmushi. “Sorry, ka ji haushi, amma gaskiya na ke fada maka, idan har da ta damu da abin da ka ke ji game da ita, ina ga da ba ta bata maka lokaci ba, kamar yadda na fada mata tun farko, bata lokacin ku take yi, domin tana da mijin aure.” 4

Abdul-Aali ya sa hannu ya mikawa Alhaji Yusuf daya daga cikin katunan dake cikin envelope din da ya shigo da shi. “Yanzu ka gaskata?

Ni ban kullaceka da komai ba, nema ce ta hada, kuma Jidda ta fidda zabinta.” Ya fada yana kallon Mai-jidda da take zaune kamar an dasa ta a wurin. “Zan ba ku wuri ko da wani bayanin da za tayi maka, wanda ya fi nawa.”

Ya mike yana kallon Mai-jidda, ya fita zuwa kofar gida. Alhaji Yusuf ya maida ganin sa ga Mai-jidda cikin mutuwar jiki da rashin kwarin gwiwa. “Hauwa! Me ya sa za ki min haka?” 8

A take hawayen da suke mintsinin idanunta suka sake kamar an bude famfo. “Bayan kin san da wannan maganar, ki ka sake jaddada min kan cewa komai ya wuce, babu wannan maganar, idan babu ita me yake faruwa yanzu?”

Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya. “Khair, tunda kin yi zabinki. Allah ya tabbatar miki da alkhairi.” Yana shirin fita ne. Mai-jidda ta yi sauri ta sha gaban sa.

“Yallabai, ka yi hakuri, kwarai ba haka na so ka samu wannan labarin ba, na rasa yadda zan sameka da wannan maganar ne, saboda abubuwa sun fi karfina. Amma ni kaina da da akwai yadda zan yi.

Da na yi domin na kawar da wannan al’amari da kuma halin da ka shiga dalilina, da na kawar. Hatta Baba na samu da maganar nan, amma abin bai kare da dadi ba. I had to choose tsakanin ka da dana Muhammad.” 1

Alhaji Yusuf ya fiddo da idanunsa da suka yi jazur! Da bacin rai ya-ce. “Yanzu wannan mutumin don rashin imani, rabaki da Danki zai yi, don za ki auri wanin sa?”

Mai-jidda ta matse kwallar da yake idanunta, ita ta dade da sanin Abdul-Aali mugu ne na karshe, karya yake yi, ba sonta yake yi ba.

“Ba komai Hauwa, ni ne na yi duhun fahimta da na dade da amincewa da abin da idanuna suke nuna min, duk da haka bai faru ba. Tabbas na so ki kasance matata, ki kara haskaka min rayuwa. Amma I guess, kowa rabon sa yake samu a duniya, yau Yayarki za ta zuba ruwa a kasa ta sha”. 6

Ya fada cikin murmushi, ita ma Mai-jidda duk da halin da take ciki, sai da ya ba ta dariya, “Ba ka yi fushi ba?”

“Hauwa, zuciya ba ta da kashi, tabbas na ji zafi kwarai, amma ba zan tursasa miki abin da zai jawo miki matsala ba, ko kuwa abin da ba kya so ba, haka na so da tun farko kin fada min abin da ake ciki, da jinyar da zan yi wa zuciyata, ba ta yawaita ba.” 2

Ba tare da ya saurari komai daga gareta ba, ya fita daga falon, tun kafin ya kasa jurewa.

Mai-jidda ta rasa me yake mata dadi a duniya, duk sai ta ji wani iri. A hankali ta dauki katin tana dubawa, yanzu da gaske Baba ya matso da auren nan? Nan ta kara jin haushin Abdul-Aali ya kamata, kamar daga sama ko ta ji muryar sa.

“Ke dama haka ake yi? Yaya za ayi ki kula wani, bayan kin san da baikon wani a kanki. Ke ma kin san ba auren sa za ki yi ba. He is too safe for you, ke kuma Jidda, ah ki na son challenge wanda ki ka san na yi miki dai-dai da hakan ko?” 2

“Ka tashi ka tafi.” Ta fada cikin dacin rai.

“Ba ke na zo gani ba, kin riga kin janyo min enough damuwa a gidana, so wannan sakon Baba ne, idan ya zo ki ba shi”. 21

Mai-jidda ta bude bakinta, cikin mamakin kalamansa, ba ta yi aune ba, ta ji wasu hawaye suna bin fuskarta, wulaqancin Abdul-Aali sai shi.

“Ba laifinka bane, ni na jawo wa kaina. Kuma na yi na farko, na yi na karshe, yanzu har kana da bakin ka ce min ni na jawo maka matsalolin gidan ka? Wa ya zo inda wani yake ya-ce yana son aure? 2

Wa yake ikirarin yana son wani? Wa ya zauna a wannan ranar ya ci abinci da matar da ba tasa ba? Waye aka makala wa kalmar da ba halayyarta ba? Wa aka cuta a wannan tafiyar. Abdul-Aali idan ba ni ba?”

“Jidda…”

“Uhm-uhm! Ya isa, ba yau ba, yau kam ka gama iya damejin da za ka yi a wuni guda, kai kanka ka san abinda kayi, ka samu amincewata, idan ni ce kai ba abin alfahari bane don na aureka.

So stop gloating (Ka bar jin dadin nasararka). Sai anjima”. Ta tashi ta shiga gida, ta bar shi da katunan a hannun kujera. 3

Kai ya mayar jikin kujera game da shafo kansa cikin damuwa.

Randa ya bi Hamamatu gida, tana zuwa ta fara sa kayanta a akwati.

“Hamama, ki saurareni. Me ki ke yi haka. Don Allah ki zauna mu yi magana”.

“Hmm! Abdul-Aali ai na gama magana da kai, ka yanke shawarar kara aure, ka kuma boye min matar da za ka aura, sai yau da na ganewa kaina ko wace ce, shine ka ke da lokacin magana? Well guess what. Kunne na ya toshe, saboda jin kalaman soyayyar da mijina yake fadawa matar wansa”.

“Please, kar ki dau abin nan da zafi…” Ya riko hannunta, amma ta fizge cikin zafin rai, tana gama kwasan iya abinda hannunta yakai kai, ta ja zip.

“Kar kuma ka yi tunanin biyo ni, saboda ba zan dawo ba.”

Ba yadda bai yi da ita ba, ta ki ta saurare shi, ta tattara ta tafi gidan su. Haka ta bar yaran a gida, wai dama ba da su ta zo ba. Ramla kam da ta tsorata da hayaniyar da ake yi, sai kuka ta sa, haka ya yi ta rarrashinta yana gani. Hamama ta tafi, sai da dare ya je ya samu mahaifinta, domin ya bada hakuri.

“A’a Abdul-Aali, me ya faru ne na ga Hamama ta dawo gida hankali a tashe?”

Nan Abdul-Aali ya fada masa abin da yake faruwa. “Ha’a to haka abin yake?” Ya aika aka kirawo Hamama da Hajiyarta, suka shigo falon, tana ganin Abdul-Aali, ta hada rai domin koma me ya zo nema, ita ba mai yin hakan bane.

Hajiyarta ta kafe kasa ta-ce ai an cuci yarinyar a duba a gani, ganin haka Alhaji ya-ce su shiga ciki. “Abdul-Aali, kar ka damu Insha-Allahu za ta koma.

Yanzu dai ka bari ta dan huce, ranta ya sosu da yawa. Amma za ta dawo, an taba haka, daga za ayi aure sai ki bar gidan ki, kuma wannan ba wai auren da aka haramta shi bane.” 2

Abdul-Aali ya yi godiya, ya tafi ransa a bace.

Daga karshe dai sai da Abba ya sa baki a maganar sannan. Alhaji ya tsaya aka ba ta hakuri har ta koma, bayan ta shafe sati a gidan su. Sannan duk artabun da ake yi. Wai Jidda ce za ta tada hankalinta, shi ya rasa gane kanta ma.

Washegari ya maida su Hamama Portharcourt, saboda makarantar yara shi kuma ya koma bakin aiki, bayan bikin Mukhtaar. Dole sai da ya ba su excuse din satin da ya yi, baya nan.

***********

Mai-jidda tana shiga ciki, ta dauki wayarta ta nemi Dan Kano, watakila idan ta yi magana da shi, hankalinta ya kwanta. Saboda ko wace damuwa ta kai masa, shi ya san yadda yake yi ya sa ta nishadi. 5

“Assalamu-alaikum, my Hauwa. Yaya ki ke?” 1

Ajiyar zuciya kawai ta yi. Hade da runtse idanu yaya za ayi muryar mutum kawai ta saukar maka da kwanciyar hankali a take? 3

“Na’am lafiya kalau. Yaya aiki da iyali?”

“Alhamdulillahi! Sai dai Hauwa anya ki na lafiya, na tsinkayi damuwa a cikin muryarki.”

Runtse idanunta ta sake yi cikin damuwa hawaye suka gangaro mata daga idanu, “Babu komai, kawai dai na bugo ne mu gaisa.”

“Kar ki boye min komai, ki fada min damuwarki Hauwa.”

“Ka san komai.”

“Kiyi hakuri, kwarai naso zuwa mu tattauna, ban san yanda zanyi ba abubuwa sun min yawa lokaci guda. Bana so na yawaita fada miki kiga kaman ina jan ranki ne amma…”

“Kar ka damu, ka gaida iyali, sai da safe.” Da sauri ta katse wayar, tun kafin ta yi kuskuren fada masa cewa shi take so. ko ya zo ko bai zo ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *