AL,AMARIN ZUCI CHAPTER 4

AL,AMARIN ZUCI





CHAPTER 4






Hajiya Juwairiya tana zaune banda ikon Allah ba abun da take gani, ita ta rasa ma da wanne daya zata ji, bakin cikin da ta tsinci kanta bata taba mafarkin zai sameta ba. Wannan tashin hankalin dai ya samo asali ne a safiyar jiya.
+

Lokacin da Daddy ya tara su yana shirin fita wurin aiki “Abun da yasa na taraku a nan abubuwa uku ne, na farko dai na je nayi magana da makarantar su Sameeha zata koma karatunta amma an mai da ta ajin baya saboda differing da na mata tun a wancan lokacin na session din da ya kare” Nan da nan Sameeha ta hau murna tana godiya, Mummy ma abun yayi mata dadi ba iyaka.

“Na biyu kuma shine kwanaki, akwai wanda ya zo neman izinin ya nemi auren Sameeha, kuma na amince masa don haka Sameeha zaki iya ganin bako a ko wani lokaci” Nan take zuciyar Sameeha ta hau bugawa saboda ta tsorata ganin ita har ga Allah mutum daya da ya kwanta mata a rai ya mata nisa saboda ba yanda za ayi yama fara aurenta, a bangare daya kuma ta samu Daddy ya fara damuwa da al’amarinta, har ya amince da wannan mutumin idan ta kuskura ta nuna kin amincewarta to bazata kwashe lafiya ba, don haka ta qudurta zata samu Aneesa ta nemi shawara a wajenta game da abunyi. 4

“Abu na karshe kuma ina so na shaida muku, idan Allah ya kaimu wata mai kamawa ina da niyyar kara aure” 13

Fuskokinsu ne gaba daya ya hasko tsoro da razana hade da mamaki. Zaheeda da Khazeena suka ce “Daddy Aure?”

Hajiya Juwairiyya kam tsabar razana ta gagara magana sai kifkifta idanu takeyi kawai. “Daddy wani abu Mummy tayi maka?”

“A’a Khazeena aure ai ana yin shi ne don bautan Allah, da kuma cika da kamalar rayuwar dan Adam ba sai Mummy ta min wani abu ba, lokaci ne kawai yayi, kuma ina so ku dau maganar nan, cikin natsuwa duka na san kun girma kuma kowacce da tunaninta kowa aure zatayi nan gaba kadan kuma ba laifi bane ku samu wata ko a same ku. Ina son ku dauke ta kamar yanda kuka dauki Mummy.”

Jikin su kaf yayi sanyi, ya san tabbasa zai samu matsala wajen bullo da wannan maganar amma kuma ya duba yaga abun da kawai zai yi kenan ya kashe wutar gidan shi.

“shi kenan ku tashi kuje.”

Sameeha ce tace “Daddy a ina ka samu matar?”

Ya dubi sashin da Mummy take zaune ba uhm ba a’a yace “kuje zan fada muku daga baya.”

“To, Allah ya kaimu”

Haka yaran suka watse daga falon, a hankali ya juyo ya dubeta “Juwairiya…”

Hannu ta sa ta dakatar dashi “Mahmoud, ka cuceni, ka wulaqantani, ka musguna min, abin da za ka min kenan? Duk hukuncin da ka dauka a kaina na dauka na rungume shi amma hakan bai isheka ba shine zaka kara aure a wannan shekarun? Ka tuna fa ka fara aurar da ‘ya’ya, so kakeyi kana haihuwa yaranka na haihuwa? kai duk a bar wannan zancen, a gaban yarana zaka bani wannan mummunar labarin ashe haka tsanata da kakeyi yayi zurfi a zuciyarka?”

“Sam babu ko daya, ni ban ki ki ba, ba kuma muzanta ki nayi ba, ina da dalilina na yin wannan maganar a gaban yara. Amma idan hakan bai yi miki ba sai kiyi hakuri. Auren nan da zanyi dukan mu ya fi mana rufin asiri.”

STORY CONTINUES BELOW


“Rufin asiri Daddy? Da wannan auren rashin mutumci da kake nema kayi ka zubar min da mutunci na da kima ta da naka kai kanka, gwamma ka sallameni”

“Ashha, hala kin manta ne, ai na fada miki ni da sakin mace kam har abada, nayi akan Halima kuma ya kare.”

“Halima! Halima! ko da yaushe sunanta kenan a bakin ka, baka tuna cewa ita matar wani ce yanzu, ko kuma har yanzu soyayyar tata yake juya maka kwakwalwa? Halima kam ai ta barka na rabaka da ita kuma ta tafi har abada.” 7

Alhaji Mahmoud yayi shiru cikin takaici yace “Exactly, abu daya da kika min a rayuwa da bazan yafe miki ba kenan, kema kuma kin san shine dalilin da ya sa na juya miki baya, don kin raba ni da Halima ba shi yake nufin bazan iya sake wani auren ba, kuma hakan zanyi a kan idanun ki kina ji kina gani, idan yaso wannan ma sai ki koreta.” 2

“Daddy kar ka min haka, zan iya rayuwa da kai ko da bana shiga dakin ka amma bazan iya ganin wata mata a gidanka ba.”

“ke kika samu wata kika cireta?” 4

Daddy yayi shiru yana tuno lokacin da ya dawo gida ya sanar da ita, yayi shawarar dauko ‘yarsa dake wurin Halima ya hada da yaransa, ta nuna fushinta amma ya ganar da ita komai a tunaninsa don tana tunanin kar tarbiyyar Uwani yazo ya bata na yaranta ne, sai dai tun tafiyar Halima yake son ya bita amma ya gagara, a hankali shekaru na shudewa yana kara yawaita ibadarsa girma na kara shigarsa, yaji son tsohon iyalin shi yana dawo masa, sai dai kan ya ankara ya makara domin Halima ta yi wani auren, hakan ya sa ya dage zai karbi ‘yarsa ko zai ganta ya rage masa nadamar rabuwa da Halima. 3

A daren da ya fada mata ne, ya shigo falonta yaji hirarta da yarta a waya “kin san tashin hankalin da Daddy zai jawo mana, wai ‘yar Halima zai kawo ya hada da yaransa?” … “ki duba kiga duk kudin da muka kashe domin ya rabu da Halima da abun cikinta, amma bayan wannan shekarun yazo yana kwakwarsu”… “Ni koma meye zan iya yi don na raba Mahmoud da jinin Halima, saboda yana sonta da yawa, ni kuma bazan iya hada soyayyarsa ba da wata mace”… Tana cikin wayar ne ya bayyana a fuskarta, a hankali taso ta wayance tana fadin “Hello… hello… network ba kyau”

“ke da waye kike waya?” ya fada cikin mutuwar jiki da mamakin jin kalamanta.

“Daddy, yaushe ka shigo nida Yaya Lantanace”

“Yaya Lantanar ce ta baki shawarar ki rabani da matata? ko kuwa ita ta kaiki gurin wani mutum marar imani da sanin ciwon kanshi don na baki fili da doki ki ci karen ki ba babbaka?”

Ganin ba yanda zata kare kanta da alama yaji komai ne yasa ta durkusa ta fara kuka “Daddy, sharrin shaidan ne, ka yafe min. Tun wancan lokacin ban sake zuwa neman asiri ba…” 2

salati yasaka ya sanarwa mai sama “Juwairiyya, Asiri fa kika ce kinji kalmar ta zauna a bakinki? yanzu duk zaman da nakeyi dake zaman cutata kikeyi? Na baki rayuwata kaf, na rasa abun da nafi so a rayuwata, saboda aurenki a ganina zan farantawa iyayen mu rai, ke ‘yar uwata ce fa kika mini haka? shin akwai digon imani a zuciyarki kuwa?”

“Kayi hakuri Daddy, AL’AMARIN ZUCI ne kuma na tuba”

“Wannan kuma tsakanin ki da Allah ne, ni kam tsakanina da ke ya kare”

Tashin hankali, nan take ta zube kasa ta cire dankwali hannu a saman kai tace “Daddy, ka duba yaran nan don Allah kar ka furta saki, me zance musu? Ina zamu je?”

“Ni bazan sake ki ba, kuma yara nan gidan mahaifin su ne. Ke kuwa zuwa kikayi don haka daga yau kar na sake ganin kafarki a dakina.” 3

Tana rusgar kuka ya fita ya barta, tun wancan lokaci kuwa Mummy take ci da zuci, yayin da Daddy ya tattara ta ya ajiye a gefe. A idon duniya hajiya dai na shanawa, idan yaso mata tsiya sai ya rinka zolayarta ta zaci ko ya zo neman sulhu ne. To amma yanzu yaga wannan zaman bazai yi musu ba shi yasa ya nemi mafita. sai dai ya qudurta a ransa idan yayi aure zai dage mata dokar shiga sashinsa saboda ya kasance mai adalci.

STORY CONTINUES BELOW


Kwanaki uku Hajiya Juwairiyya tayi cikin halin damuwa ko kasuwa ta daina zuwa bare uwa uba gidan kawaye. Gashi ba yanda batayi da Daddy ya fada mata wa zai aura ba yaki sanar da ita.

********

Aneesa ta gama jin bayanin Sameeha ta jinjina zancen, sai da ta fada mata batun tambayar izinin aurenta ne Aneesa ta kwashe da dariya tace

“Me kikace? Don Allah sake fada naji”

“Haba yanzu ke dariya na baki? Maganar gaskiya nake fada miki, don Allah kar ki yi da karfi wani yaji”

“Abun farin cikin kike boyewa wani kar yaji”

“Ba ma anfanin mutum ya fada miki matsalarshi, yanzu na san Uncle Sagir na dawowa shi zaki fadawa” Sameeha ta turbune fuska.

“To wai Sameeha don na fada inaga ai sakon ki zai fi saurin isa, kunnen da ya dace”

Sameeha zatayi magana ne, sai suka ji sallamar Sagir a cikin falon, da wuri Sameeha tayi mata ido akan kar ta ce komai.

“Me aka samu kuma yau Sameeha? An canza wurin yin laccar girkin ne?”

“Uncle Sagir ai yanzu kam na gama kwas, sai dai wasu su koya”

“To yayi kyau. haka aka fi so ai, kinga zamu zo cin abincin amarya da karfin gwiwa, ko ba komai mun san akwai garanti, tunda a wurin master chef ta koya”

“Kai dai ko wani lokaci ka samu banda yaba Aneesa ba abun da kakeyi ko cikin wayo ne.”

“Ah, haka kika ce? To ai ita din abun yabawa ce shi yasa.” ya fada yana kallon sashin da Aneesa take zaune kafin nan ya wuce dakinsa na kasa.

“Sameeha ina zuwa”

“ke ni kam na fada miki damuwata zan tafi sai munyi waya.”

Aneesa tace “wai me yasa kuke min haka ne, haka ranar su Khazeena suka zo da Baba Saratu, daga shigowar shi wai zasu tafi ai sai kusa yayi wani tunani daban”

Haka dai Sameeha taki zama, ba yanda Aneesa ta iya dole ta barta ta tafi.

Bayan Aneesa tayi wanka tayi shirin kwanciya ne taji motsi, don haka ta bude kofa a hankali sai ga Sagir da sandan shi ya hauro sama.

“Lah, Uncle Sagir. Me yasa ka hau sama, zaka tabo kafar ka fa, da ka kirani nazo na baka abun da kake so…”

Sagir ya dubeta, yace “Ba damuwa, nazo daukan abun da nake so din ne, kashe wuta ki sauko, yaya bazan hau ba sai ki tafi ki barni bayan ke kike fadan na faye motsa kafar tawa da yawa”

“To naji muje ina zuwa, da sauri ta kashe wutar dakinta, ta dau gyalenta sannan ta biyo shi, yana dingisawa har suka sauka.

Sai da suka shiga dakin ne tace “Me zan kawo maka?”

“Sai kace ina korarki? Ba abun da nake so sai ke. zaki iya bani?” kai tsaye taji maganar don haka baki a bude Aneesa ta zazzaro idanunta, “Ni kuma uncle Sagir?” 5

“eh ke, ke ba kya sona?”

“yaya za ayi na… ina son ka mana” 2

Sai da ta fada ta gane me yake nufi tayi saurin rufe bakinta da hannu bibbiyu, hannu yasa ya cire mata a bakin.

“Uncle Sagir, ni ba haka nake nufi ba.”

Sagir ya kara matsowa kusa da ita yace “ba na hanaki ce min Uncle ba?”

“ka hana, na kasa dainawa ne, na saba”

A cikin kiftawar ido ya mata abun da yayi bata san me zata yi amfani dashi ba wajen bayyana yanayin da ta samu kanta, sai da taji jiri ya dan kwasheta, sannan ya sake mata fuska. Da sauri ta zauna a bakin gado don kafafunta nema sukayi su gagari daukanta. 4

STORY CONTINUES BELOW


“Idan kika sake ce min Uncle sai na sake miki irin wannan”

Nan Aneesa ta shiga zazzare idanuwa. Ta mike zata fita, yace “ina zaki je?”

“Daki…” ta fada a tsorace

“Ai daga yau baki da wani dakin da ya wuce nan, ko so kikeyi a kara mai dani asibiti saboda hawa sama da sauka?”

A hankali ta girgiza kanta, nan dakin Sagir ta kwanta. Ga mamakinta, da ta rufe ido ba abun da take tunowa sai abunda Sagir ya mata kuma a sabanin da da ko tunanin hannun na miji tayi ya taba ta sai ta samu kanta a dimuwa da damuwa, yau wani farin ciki ne taji yana ratsa ta. 3

“Ran da nayi hatsari na hadu da Nata’ala a Kunuwal”

Ba shiri Aneesa ta juyo gefen da Sagir yake kwance ta dubeshi. Yau ta ga takanta me ya fadawa Sagir?

“Ya ban labarin duk abun da ya faru.”

Aneesa ta bude baki tace “Duka?”

Ta tambaya tana jiran amsar da zai fito daga bakin sagir, shi kenan zai tsaneta; mutum daya da ta samu ya damu da ita ba tare da ya san duhun da take dashi a rayuwarta ba yau ya san sirrinta ai shikenan mafarkin da tafara na samun wuri a zuciyarsa zai rushe.

“Eh duka, me yasa ke baki taba fada min ba?”

Nan tayi kasa da idanunta da sukayi narai-narai, tana wasa da bakin rigar baccinta.

“Saboda, kai ma zaka zargeni kaman kowa”

“Me yasa zan zarge ki? Me yasa zaki sawa ranki akan kowa na zargin ki da hakan”

“Saboda anyi ta magana a lokacin, rayuwata ta zafafa ta kuntata, ko ina na wuce sai an nuna ni, bana iya shiga ko ina ko da kuwa yiwa Innata aika. Sai gidan su Mama kawai nake zuwa, Falmata ce kawai a kawayena bata zargeni ba, sai Fatu kanwar Nata’ala. wadanda na tashi dasu suka sanni suka san ni wacece sun zargeni. saboda ni ina mace, ba mai yarda da shaidata. Shi kuma zai iya bada kowace irin shaidar karya kuma akarbi tashi shaidar. kowa ya zargeni, me yasa kai bazaka zargeni ba?”

Sagir yayi shiru yana sauraronta cike da tausayin abun da ta fuskanta a rayuwa a lokacin da take cikin karancin shekarun da bai wuci tana fama da karatunta ba ko kuma tana fama da yanda zata fuskanci barazanar girma da kula da kanta. Amma ita kadai, an mata auren kuruciya ta koyi zama da haka tana kula da mijinta, ta samu juna a wannan shekarun tana fama da wahalhalun da mace take dauka domin kawo rai duniya, wannan bai ishi wani azzalumi ba zai kama matar dan uwansa ya danne ta. Ai wannan dabbanci ne da rashin sanin ciwon kai.

A take Sagir yaji fushi ya taso masa marar misaltuwa, bayan duk wannan wanda ya ajiye ta har zai tsaya ya saurari cewa wanda yayi wa matarsa haka zai ce matar sa ce take wani irin shiga a cikin gidanta na aure shi yasa ta tunzura shi ya aikata mata hakan? shin duniyar da muke akwai adalci? shin za a daki mutum sannan a hana shi kuka?

A take Sagir ya samu amsar tambayar Aneesa “Saboda ni naga abun da dukan su basu gani ba,” ya sa hannu ya dago habarta yana kallon cikin idanunta “Naga kyakkyawar zuciyarki, naga gaskiyarki naga mutumcin ki, na kuma san darajar ki” 5

“Ashe zaka iya sona a haka? zaka iya sona bayan abun da aka min? zaka iya sona bayan kasancewata ‘yar kauye, bazawara wacce kuma ta kasance an yi wa fyade?” 11

“Aneesa, ko a wani hali na tsince ki ni mai sonkine kuma kar kiyi tantamar ke ba abun a so bane, domin ke mutumce, wanda Allah ya bawa daraja Ya kuma sa kima a tare dake.”

“Me yasa zaka ce haka don naji dadi?” ta fada muryarta na rawa.

“Ban fada miki haka don kiji dadi ba, na fada miki hakan don hakan ne gaskiya, a dalilin wannan halayen naki har kika iya sa zuciyar Sagir ta iya kewa, ta iya bege ta kuma sake so.” 4

STORY CONTINUES BELOW


Wannan magana ta Sagir ta tsaya sosai a zuciyar Aneesa.

“Saboda haka nake son daga yau, ki cire duk wani tsoro a ranki, ki ci gaba da rayuwarki. kar ki bari wanda bai san mutumcin rayuwa ba, bai san darajar dan Adam ba, kai bai ma san me ya zo yi a duniya ba, ya hanaki samun taki rayuwar.”

“yaya zanyi rayuwa bayan sanin cewa irin Munkaila suna nan da yawa a fadin duniya?”

“Baza ki iya canza duniya ba, amma zaki iya canza mutum farawa daga kanki, idan kika daina tsoro zaki fadawa ‘yar uwarki kar taji tsoro ta daga muryarta idan hakan ya faru, wata kuma ta hana hakan faruwa watan kuwa zata iya kasancewa ke, Aneesa” 3

A hankali taji ta soma kuka mai tsuma rai.

Sagir ya sa kanta kan kafadarshi yana rarrashinta, har tayi bacci a haka. Sai da asuba ta farka ta ganta a dakin Sagir, nan ta tuna duk abun da ya faru jiyan. Da karfin jiki ta mike domin jiya Sagir ya kara mata karfin gwiwa, kuma ya shaida mata cewa koma a yaya take a hakan yake sonta. ita Uwanin Inna yau ta samu wanda yake mata so na asali duk da ya san duhun dake cikin rayuwarta, ya maye mata shi da haske me zata nema bayan wannan a rayuwarta?

Suna cin abinci ne Sagir ya dubeta tayi nisa cikin tunani, ya sa hannunsa saman nata dake kan teburin “Har yanzu baza ki bar maganarcan ba ko?”

“A’a ba haka bane, jiya ne Sameeha ta sameni da wata magana mai daure kai wai Daddy zai yi aure”

Sagir yayi murmushi “To don daddy zai yi aure shine kanku zai kulle meye a cikin karin auren?”

Aneesa ta zaro idanu “meye fa a ciki kace? shekarar su ashirin da mummy sai yanzu yaga matar da zai aura? Ni kam abun bai min dadi ba”

“To ai ba don ya muku dadi ko rashin dadi zai yi abunsa ba, kuma ba kuna taku rayuwar ba sai ku hanashi tashi? Ku dai mata daga an tabo ku maganar kishiya to an samu damuwa”

“Ba maganar kishi bane…”

“To maganar meye ne? ku dai ku masa fatan alheri, tunda yaga zai iya ai shikenan, kuma ba laifi bane zai yi.”

“Haka ne kam. Allah ya kade fitina, ka san wai ya bada izini wani yaje neman auren Sameeha? ita kuma jiya tace bata san waye bane za ta gani, gashi bata son neman fadan Daddy sannan kuma ita da wanda take so ta rasa yanda zatayi. ko ya taba fada maka waye ne cikin hira?”

“Me yasa zai fada min?” Sagir ya fada fuskar sa kyam ba tare da ya nuna komai ba. 8

“To Allah dai ya bata mijin da zai ci gaba da tarbiyyantar da ita, tunda ALlah ya sa ta gyara halayenta, amma ina tsoron wanda bazai fahimceta ba ya aure ta” 1

“Daddy ya fiki jin tsoron hakan don haka duk wanda zai bari yazo neman aurenta to tabbas ya san me zai iya, ita ta fada miki waye a ranta?”

Aneesa tayi dariya har hakoranta suka fito “Ta fada, amma tace ko kai kar na fadawa.”

“Shi kenan, tunda ni kin mai dani bare.” ya fada bayan ya kurbi ruwa.

“Na isa, kai kam ka wuce komai amma kuma sirrin ‘yar uwata ne”

“Idan abun ya gagareku ke da ita ai zata fito kowa ma yaji ku,” ya mike tsaye rike da sandar shi. “zan makara akwai taron da muke dashi karfe hudu na yamma, zan je ofis yanzu”

“To, Allah ya dawo da kai lafiya. “

“Ba za a raka ni mota bane, ko sai na fame kafata”

“Idan na kaika mota wa zai kaika cikin ofis din idan ka isa?”

“Idan kina so zaki iya shiga motar ai sai mu tafi tare sai kin kaini har kujerata sai ki dawo gida”

“Na gode, aikin da nake dashi a cikin gidan nan ma kawai ya isheni, ba sai ka kara min wani ba” 4

STORY CONTINUES BELOW


“Lalala aikin mijin naki ne kike gudu?”

“Uncle Sagir ni ba haka nake nufi ba.” bata ankara ba taji ya sake mata dai irin na jiya, kissing dinta yayi har sai da ta manta inda take.

“Idan baki daina ba zan kara miki hukuncin da ya fi wannan”

Ya sa kai ya bar dakin cin abincin. yau ita kam ta ga ta kanta, dole dai ta rinka kama bakinta wannan uncle din ya isheta haka kawai ayi ta ladabtar da ita da wani abu mai rikitarwa. 10

Sagir yasa ta shirya ya kaita asibiti, tun a gida ya mata bayani yana so ya kaita likita ta duba lafiyarta a mata full check up. Ta amince kai tsaye, hatta gwajin HIV sai da aka mata sannan suka koma gida.

A wannan satin ne Hamdiyya ta haihu har ma ta dawo gidan Abba don haka Sagir yace ta shirya da yamma ya kaita ta dubo su.

“Kai Anti Hamdiyya wannan yaron dai sak uncle Jamil, sai kiyi ta cewa da ke yake kama.”

Aneesa ta gyara rikon jaririn a hannunta, Hamdiyya tayi dariya tace “kowa dai da abun da yake fada”

“Allah ya raya, ya kuma dayyaba, me kuka sa masa suna?”

“Mai sunan Abba ne, Muhammad Al-Mustapha. wai ke na rasa sai yaushene zaki kawo mana baby kinyi shiru abunki” 3

“ke gashi kin kawo mana tubarkallah, ai sai a bari yayi kwari kaman Azhaan kafin wani kuma yazo ko?”

“Eh, amma ina tsamman ba da Yaa Sagir kikayi wannan shawarar ba ko?”

Aneesa tayi murmushi “ko ni kaina na isa nayi wannan shawarar? lokaci ne kawai bai yi ba.”

“ni baki ban labarin turarrukan nan ba da lallen, naga baki aiko karban wasu ba, sannan ban ga hannunki da kunshi ba.”

“Tunda kika ban ma ledar na wardrobe dina ban bude ba.”

Hamdiyya ta mata kallon mamaki “Amma lallai sai a gaishe ki, haka kike zama da yayan nawa ba gyara ba kamsashe jiki?”

Aneesa tace “Ba ina wanka ba, ai bana zama da kazanta”

“Ke baki san sirrin da turare yake dashi ba a wurin ‘ya mace ko? Gashi kin auri Kanuri ya riga ya saba da kamshi kin zo kin zauna haka, ai haka ba kyau. Yanzu ba kya tunanin duk da yana son ki yace da zaki kara da gyara jiki da gashi da kin fi haka a ranshi? Ai mace da ado aka santa ko a tarihin musulunci. Ke dai kawai fitane ba a so tayi dashi ko kuma ta bayyana shi wa ajnabi dinta.” Aneesa dai shiru tayi tana tunani yanzu banda su turaren jiki da na fesawa da take dasu sai ta hada da turaren hadi dasu lalle da wani gyara na daban Sagir zai kara sonta?

“Kinga lalle kuma yana da sirri daban-daban shi yasa ba a wasa dashi, bayan ado da kyau da yake karawa mace, yana kareta daga cututtuka, yana gyara fata, ya kare jikin mace daga sanyi ya kara dumamata sannan babban abun kuma ga lada saboda sunnace.” 5

Kafin Aneesa ta koma gidanta dai sai da Hamdiyya ta sharto mata sirrin turarruka daban-daban tun daga miski har zuwa hadin turaren lalle. 4

Tana zuwa gida ta bude ledar dake kunshe a wardrobe dinta ta bude, ko wani kwalban turare Hamdiyya ta rubuta mata sunanshi da kuma yanda zatayi dashi, don haka ta dauki kwalba daya ta kai shi bandaki, don wannan na wanka ne, ta ajiye sauran kan madubinta. Sai da ta bari sun ci abinci da Sagir ya fita bayan isha kaman yanda ya saba sannan ta koma dakinta ta cancara wanka ta mulke jikinta da wannan hadin turaren lallen, ta barshi ya bushe a jikinta sannan ta fito ta shafa mai ta dauki mulmulallun turaren ta turara jikinta da shi, kafin ta zabi wani kayan bacci mai laushi a cikin kayan auren da Sagir ya mata. Ita kanta laushin kayan baccin take ji tana nishadi. Ta kashe wutan dakin ta burma hijabinta sannan ta sauko. A falon ta sameshi yana kallon Tuesday life a NTA. “sannu da dawowa.” ta fada sannan ta zauna a kasa kusa da kafafunshi.

STORY CONTINUES BELOW


“yau kuma zaman kasan aka tuno ne? Tun dazu na shigo ban ji motsinki ba”

“Ina dan kimtsa wuri ne kayi hakuri, na kawo maka madara ne ko tea zaka sha?”

“ki barshi kawai, kwanciya zanyi ma, gobe akwai site din da zamuje dubawa kuma ina bukatar hutu kwanan nan ban cika zama ba gashi akwai tafiya a gabana sati na sama in sha Allah”

“To shi kenan, bari na kashe wutan kicin nazo.”

Tana shiga dakin ta cire hijabinta tana shirin kwanciya sai gashi ya shigo dakin don haka da wuri ta shige bargo, bai ce mata komai ba sai da ya kwanta tukun ya kashe wutar dakin ya bar na gafen gado, taji yace “yau kam kin saki liman dinne?’ 10

Maganar ta bata dariya, a hankali taji hancin sa a cikin gashinta wanda tunda Khazeena ta kaita wani wurin gyara a salon matar ta gwada mata yanda zata na kula dashi, kitso sai bai dameta ba, “ko kefa, amma kiyi ta shake kanki kamar wata marar gaskiya.” Aneesa tana ji a hankali ya shiga yi mata wani abun da ya shallake tunaninta, a hankali jikinta ya soma macewa, amma bayi da niyyar sassautawa don haka tace “wannan kuma hukuncin meye ne?”

“Wannan shine hukuncin hana zuciyata sakat, da kuma sani jira da akayi tayi”

A hankali tace “Ni kam ba abun da na maka, kayi hakuri.”

“Hakuri kam ai nayi shi yanzu kam lokacin wani abun ne daban” a hankali ya shiga mata wani abu a kunnenta wanda yasa daga nan bakinta ya mutu murus, domin dai wata duniya dungurgum Sagir ya kwasheta ya kai. 6

Ko da tayi sallah tayi shirin fita domin shiryawa zuwa makaranta, Sagir yace “yau fa ba zuwa makaranta.” Ta tsaya a takunta ta dawo dakin domin dai ita kam yanzu Sagir ya zama mata abun buya. “Ina da gwaji fa yau a makaratar.”

“ki zauna ki huta”

Zatayi magana yace “Bana son gardama, kuma ki bar abun karyawar ma sai anjima, ki kwanta sai anjima ki tashi” ya fada cikin murya ta rashin wasa. 1

Ba yanda ta iya haka ta koma ta kwanta cikin jin dari-dari. Tana ji tana gani ya hanata zuwa makaranta shi kuma ya tashi wai zai shirya ya fita.

“kai fita zakayi?”

“eh mana ba ki ga ina shiryawa ba?”

“To ni me yasa bazan je makaranta ba har na rasa gwaji na?”

Ya sunkuyo kan gadon ya sumbaci saman kanta yace “saboda ina son ki huta, idan na dawo zamu ci gaba daga inda muka tsaya” Nan ne yayi murmushi. 13

Ita kuwa da sauri ta sa kanta a cikin bargo, ya tafi daga wurin yana dariyarta.

Sai da yaga ta kusa yin latti ranta duk wani iri ne yasa yace “shirya sai na ajiye ki a makarantar”

Ta zaro idanu “kai zaka kaini da kanka?”

“Eh, ba kya son kawayen ki su ga mijin ki ne?”

“A’a kawai dai na tambaya ne, ni bani da kawaye ma a makaarantar. To ban shirya ba, ban maka breakfast ba”

“kije ki shirya kawai ki sauko da wuri”

Da sauri ta bar dakin nashi, ta shirya ta dauko takardunta ta dawo.

Tana saukowa ta samu Sagir ya hada musu tea ya kuma hada sandwich “Ka iya abinci ne dama?”

Murmushi yayi “ki zauna kici ko kuma duka muyi latti”. Maganarta yake tunani, ai idan bai iya girki ba sai an tambaye shi domin ba aikin da Hajiyarsa bata sasu tun suna yara kasancewar dukansu manyan ‘yan maza ne, dole su take sawa su tayata aiki.

Cikin nishadi yake tukin har suka isa makarantar, Aneesa tayi sauri zata fita don karfe takwas ta cika, Sagir ya riko hannunta, “ki kula da kanki sosai” Cikin jin kunya Aneesa ta bar motar ta nufi ajinsu, tun tana tunanin kowa ya san me tayi jiya har dai ta gane ita kadai ta san abunta ta saki jiki, lokaci-lokaci tana sakin murmushin da babu gaira babu dalili. 7

********

“Don Allah ka daina wasa da hankalin yarinyar nan haka Aadil, me yasa baza ka fito kace kai kake neman aurenta ba? Bayan ka san kai take so.” 4

“ina son na ga ko da gaske ta canza ne”

“Ashe har zaka iya gwada abun da kake so koda ka san yin hakan yana wahalar da abun son ka?” Sagir ya fada cikin mamaki “Ni ina gani kawai ka fada mata zai fi muku sauki”

“Wai yaushe ka zama mai bada shawara a soyayya ne, (last i checked) Sagir Daggash bayi da lokacin soyayya.”

“Kai dai ka samu kuyi auren ku zaka gane koma dai menene,”

“Haba, kace ‘yar ficiciyar yarinya ta koya maka darasi” 7

Sagir ya sha mur “shi yasa kai ba a sirri da kai ai, kayi aure ma ko zamu huta baka tuwon mu.”

“oh abun ma gori ne?”

“Gwamma ana taba maka dai gorin inaga zaka fi daukan abun da muhimmanci”

Fitar Aadil daga ofis din Sagir yaji lallai maganar Sagir gaskiya ce yau zai je ya samu Sameeha.Amaryar daddy dai ta iso, gangariya da ita. Aunty Fatima mace ce kyakkawa, ga son mutane ‘yar jihar Katsina ce ta taba yin aure Allah yayi wa mijin rasuwa amma bata taba haihuwa ba. A nan Abuja Daddy ya ganta gidan wanta wanda abokinsa ne har suka daidaita.
13

An tafi Malumfashi a can aka dauro auren. Mummy kam a wannan lokacin ta gama amincewa ta rasa wannan fadar da ta taso, don haka ta zuba idanu. Gashi dai an mayar mata da mukamin zuwa dakin maigida tun kafin auren amma kishi da fushi suka hanata lekawa. Da ta tada rikici ne ta dage sai dai Daddy ya ajiye Aunty Fatima a gidan sa na Zaria ba zata zauna gida daya da ita ba.

Daddy kuwa yace “Idan har kina son zama kan ‘ya’yanki dole ki bi tsarina, kuma bana son wani tashin hankali a gidannan , duk wacce tace fitina zata haddasa min, to kofa a bude take” hakan yasa ta ja bakinta tayi shiru, fi’ili iri-iri dai tana ganin shi. Amma bata da bakin magana, ita ta kula ma sai lokacin girkin Anty Fatima ya zagayo a karshen mako sai yace mata sun tafi Zaria, ko kuwa wani garin daban, hakan ba karamin tayar mata da hankali yakeyi ba, wai yau itace kishiya zata gwadawa juya miji? Wai rayuwa juyi-juyi don haka ba yanda ta iya. Wani lokaci tana kokawa yarta halin da take ciki “gaba daya na fada miki ya zama kaman wani zararre, wani abun idan yanayi ma kaman wani karamin yaro a dole ya auri mai karancin shekaru ‘yar zamani.” 3

“Ato ai ke kika ki shawarata da tun farko ko kafa bata taka cikin gidanki ba, bare ki ga abun takaici.”

“Hmmm wai inji mai ciwon hakori, ai ni Yaya Lantana yanzu tsoron yin wani abun nakeyi, na tsorata da Mahmoud, wannan karon muddin ya san da saka hannuna a al’amarin gidan sa to kashina ya bushe. Dadin dadawa nayi a kan Halima, amma kiga ba aje ko ina ba aikin ya warware duk da dai da farko anyi nasara. Na tsorata da wannan lamari. ke dai ku tayani addu’a Allah ya dawo da hankalinshi kaina, don naga alama wannan Fatimar ‘yar duniyace da gaske takeyi” 4

“To shi kenan tunda kince haka”

Suka yi sallama da yaya Lantana ta shiga tunanin wasu dabarun, haka kawai a zo a sameta da miji a kwakwabe shi, bayi da wata katabus sai abunda mata tace masa? oh ni Juwairiyya ashe abun haka yake? 3

******

Inna dai baki har kunne saboda ranar Uwani tana hanyar zuwa ganin gida, su Amina kuwa an kasa zaune an kasa tsaye, can anjima an leka waje an sake dawowa ciki, duk dai gadin isowar Uwani ake tayi. Wannan tahowar, Malam Hassan ne ya kaisu filin jirgi sai dai maimakon taga sun bi yanda taga sunyi a tafiyar su Turkey, yau wani karamin jirgi taga Sagir ya nufa, ita dai binshi takeyi a baya, masu iniform din kusa da jirgin suna gaisheshi, shima ya gaida su, sannan suka shiga jirgin. Yanayin tsarin cikin jirgin ma ya banbanta da wancan, an shigo musu da kayan su, nan dai taji kaftin din yana bayanin tashi, Aneesa ta dubi Sageer tace masa “yaya har za a tashi banga mutane sun zozzo ba?”

Hannunshi ya saka cikin yatsunta “Mu kadai zamu tafi, shatar jirgin na dauka mana” 9

“Uncle Sagir gaba daya? Me yasa?” ta fada cikin dafe kirji da zare idanu.

“Saboda ina son ki san matsayin da kike dashi a rayuwata. kuma saboda zan iya”

Nan dai tayi shiru, tun ba da tafara ji yana zagaye tafin hannunta da dan yatsarsa ba. Ba a dauki lokaci ba suka isa filin jirgin jihar Gombe dake Lawanti. Nan suka tarar da wani abokin huldar Sagir yazo tarbar su.

“Na gode, Haruna.”

Haruna ya rike hannun Sagir sukayi musabaha “Ah, ba komai yallabai. Ga motar nan, direba zai kai ku duk inda zaku je.”

“Zamu wuce tare ai ko? Saboda akwai maganar da nake so mu tattauna”

“To ba damuwa.” Haruna ya sallami direban, yace ya je da motarsa zasu hadu a cikin gari.

STORY CONTINUES BELOW


Ya zo zai zauna a mazaunin direba ne Sagir yace “bari kawai na jamu” ya mikawa Sagir key din sannan ya koma kujerar gefe.

Aneesa dai tana zaune a baya banda daukin ganin Innarta ba abun da takeyi. Tana jin su Sagir suna ta bayanin kasuwancin su. Wani dadi ne yake cike fal a zuciyarta musamman idan ta dubi wannan mutumin da yake magana yana juya kamfanoni da aikace-aikace, da ma’aikata da maqudan kudade wai idan ya juya farat daya, shi nata ne dungurgum mai sonta ne kuma me iya mata komai don ganin farin cikinta ya kuma share mata kwalla. Ita da ba kowan kowa ba amma Allah ya dagata ya kaita wannan matsayin, ba abun da takeyi sai dai ta godewa Allah. kullum kuma addu’a takeyi Allah ya bata ikon kyautata masa ta kuma soshi kwatankwacin yanda yake sonta koma fiye.

Lokaci-lokaci a tsakanin hirar Sagir da Haruna, Sagir yakan kalli madubin motar su hada ido da Aneesa, wani murmushi take masa wanda shi kadai yasan tasirinsa a tare dashi.

Misalin karfe uku suka shiga Kunuwal, sun samu tarba mai kyau. Bayan sun tattauna da Haruna, Sagir ya ajiye shi a Gombene sannan suka wuto. Dakinta na kuruciya ta ajiye kayanta tayi Sallah. Bayan sun gaisa da Inna ne ta koma falo wurin Sagir. “uhmm har wani dadi kikeji irin kin ga Innarki ko? to idan kun gama gaisawa sai ki fito.”

Aneesa ta dafe kirji ta marairaice fuska tace “iyaka ganin gidan kenan? ko hira fa bamuyi da ita ba, ban je wurin su Mama ba, sannan kuma banga Falmata ba…”

“to naji shikenan, baki ga danginki ba, kiyi hakuri yau dai ki huta, gobe idan na juyo sai a zagaya dangin dani ko?”

Nan tayi ajiyar zuciya ta sake fuska “wai! har ka tsoratani na zaci da gaske kakeyi komawa zamuyi”

“Idan kince mu koman ma ai zamu iya.”

Da sauri tace “Na yafe, ni kam ina nan kai dai ka sauka lafiya”

Sagir ya rike baki “oh haka ma zaki ce ko? ba komai zamu tattara mu koma ai, ni zan wuce yanzu”

“Har kaci abinci?”

“Eh yanzu mukaci da Malam Habu” sai da yazo tafiya Aneesa taji wani iri.

“Allah ya kiyaye hanya, to goben da karfe nawa zaka zo?”

Sagir ya kura mata ido tayi narai-narai da idanunta “Wata zatayi kewata kenan.” Da sauri ta rufe idanunta tace “Nifa ba haka bane, kawai ina son na sani ne saboda na shirya da wuri ba kace zamu fita gaishe-gaishe ba?”

“to naji, kaman da yamma yayi ai. Sai ki shirya min beta.”

Aneesa tunaninta daya yaya za ayi ta zauna har sai gobe da yamma taga Sagir? “Allah ya kaimu.” 9

Yasa hannu ya janyota barin jikinsa sannan yace “sai da safe.” A hankali ta shaki kamshin jikinsa ba tare da tace masa komai ba ta juya cikin gida abinta.

Ranar hira suka raba dare sunayi da Innarta, tana bata labarin karatunta da kuma rayuwar Abuja. Nan ta fito da hotunan da sukayi a Turkey ta nunawa Inna. Ta bata labarin wani zuwan da Sagir yayi da ita Lagos har kamfanin su na can sai da ya kaita ya kaita wurare daban-daban na bude idanu kafin su dawo. Inna kuwa farin ciki ne fal a zuciyarta ganin yau ga Uwaninta ta samu cikakkiyar rayuwa, ta auri mutumin da ya ke darajata ya kuma san mutumcinta.

Sai da Aneesa ta zo kwanciya ne duk tunanin Sagir ya bi ya dameta, ko yayi bacci yanzu? ko me yaci da dare? ko a ina zai kwana? duk dai tambayoyin da suka isheta kenan. 5

Har ta dan fara bacci taji wayarta na kara ta duba taga maigidan ne, cikin zakuwa ta zauna kan katifarta ta sa wayar a kunne. A tsanake cikin sassanyyar murya tace “Assalamu alaikum”

Sagir ya amsa mata “har kinyi bacci ne? na zaci har yanzu anata hira da Inna”

“Mun yi hirar har mun gama na yau kam, kowa ya shiga. yaya gajiyar ka?”

STORY CONTINUES BELOW


A hankali Sagir ya rufe idanu ya budesu “akwai gajiya, yau kam idan na kwanta bazan tashi da wuri ba, kashe wayoyina ma zanyi ko zan samu na dan huta”

“ya kamata kam, yaya kayi da abinci?”

“Bayan kin ki ki biyoni ki dafa min.” Aneesa tace “sai na bi ka Gombe don kawai na ma girki, bayan gaka da jama’a da wuraren cin abinci?”

“oh kin fi son nayi ta yawon cin abinci ko?”

“Ba haka bane, naga dai yaushe nazo gidan ne ma?” 3

“Tunda kince haka to ki shirya gobe idan nazo zamu koma.”

“Don Allah kayi hakuri, laifin me nayi? nayi kewar gida sosai ba kace zaka barni nayi sati daya ba?”

“Na fasa, ki zauna da shirinki kawai”

“Yau na ga ta kaina don Allah My dear kayi hakuri” 4

“yanzu kam na tabbatar sai za ayi lallami ake kakaba min my dear din nan, naki wayon. Haka kawai zaki sani kwana ni kadai bayan gaki minti ashirin a kusa dani”

Kunya ya rufe Aneesa tace “naji zan na ce maka My dear kullum, amma don Allah ka barni nayi sati sai na koma, idan kana so ma ka tafi Abuja ka ci gaba da sabgoginka sati nayi sai na taho”

“Na barki ki taho da wa?”

“Ba sai na shiga mota ba.”Aneesa ta fada ita kanta tana auna zancen.

“Ke ma da gangan kika fada. Sai da safe kuma ki zauna da shirinki”

Yana fadan haka ya kashe wayar, yau ita kam ta bo’esu yaya zatayi da wannan mutumin daga wasa sai magana ta koma gaske, tsakaninsa da Allah yanzu kwana daya zai barta tayi?

Haka ta hakura da tunani ta kwanta bacci. Da safe tana shiryawa gidan Falmata ta doka sammako, Falmata kuwa murna ne ya cika ta fal. Dama labari ya isota akan aminiyarta ta iso gari. Aneesa ta taya Falmata shirya yaranta sannan suka zauna sai hirar yaushe gamo sukeyi.

“Ni meye labari ne, kinga yanda kikayi bulbul kika canza?” 2

“kai aminiya ke dai da son zance kikeyi”

“A’a yanzu dai na san Sagir ya bar dawainiya dake an koma ji da juna”

“hmm, Falmata kenan ai al’amarin Uncle Sagir sai shi, wani ji da juna kuma?”

“Ban gane ba?”

Aneesa ta yi ajiyar zuciya tace “ki ga dai tunda akayi bikin mu yanzu kusan shekara kenan sai yanzu nazo ganin gida amma wai sai yace kwana daya zanyi bayan ya sa min ran zan fi haka dadewa”

Mamaki ya kama Falmata “to, kika san ko da akwai abun da ya sa shi canza shawara?”

“Ba wanin nan kawai dai nayi subul da baka na tambayeshi yaya yake kula da kanshi shi kadai. shi kenan wai na shirya yau idan yazo zamu juya, ni ban san wani irin ra’ayi bane dashi. Lokaci daya sai ya juya kaman wani mai juju”

“Ni banga meye abun tada hankali ba anan, tunda shi yaso kizo yanzun kuma har ya kawo ki da kanshi, don yayi ra’ayin ku koma ai bazai kawo sanadin fada ba, a ganina kiyi kawai yanda yace. Idan kika masa gardama gobe kuma kika bukaci zuwa gidan kina ga zai yarda ya bari ki zo?” 2

Kuma dai Falmata ta fadi gaskiya, don haka Aneesa ta sallamawa ranta shi kenan zata bishi, amma ba haka ranta yaso ba sam. 4

“To daman ke kam ai Innarki kike son gani kuma kin ganta kun gaisa, sai gidan Mama da sashen su Mairo idan banda nan ki fada min ina kike da shirin zagawa?”

“Tabbas kinyi gaskiya hakan ne kawai, naji shawararki zan bishi mu koma.”

“ke kam ban fada miki ba dai Garba ya samu aiki a Gombe.”

STORY CONTINUES BELOW


“kai haba? na muku murna kwarai, kice ana ta shirin kaura kenan. Shi kenan su Aliyu zasu shiga makaratar su a can”

“in sha Allah, hakan dai muke fata, yanzu dai rikicin da ake ciki Innarsa ta dage wai sai dai ya barmu a nan yana zuwa yana komawa, wai yanda baya shayina idan muka tafi sai yanda na yi dashi a can, kin taba jin irin wannan maganar? yau ina ni ina raba shi da mahaifiyarsa?” 3

“Haka Inna Dadayon ta fada?”

“Shi yasa ma, baki ga na daukantu kan maganar tafiyar ba, ni dai ina ta addu’a Allah ya zabar da abun da yafi alheri.”

“Ameen, wannan shine babba, ki bashi shawarar ya bita a hankali har ya samu ya rabu lafiya da ita, kin san sha’anin iyaye. Kar yaga kaman baki damu ba, daga baya yazo yayi dana sanin yin hakan ya daura miki laifi, kuma uwa uba idan tayi fushi dashi to kin ga fa masifa na iya aukuwa, shi yasa a rabu dai lafiya a hankali Allah yasa ta fahimta.”

“Hakane, Ameen.” ta kawo wa Falmata zani sai kuma yaranta ta kawo musu ‘yar kanti masu kyaun gaske. Sai godiya aminiyarta takeyi

Sai kusan azahar Aneesa ta koma gida, ta taya Innarta aikin abinci, suna cikin aikin ne tace “Inna, daman ina son na fada miki ne yace yau idan yazo muka je gaida su Baba zamu koma”

Inna tayi shiru kadan sannan tace “ba dai Abujan kuke da shirin komawa ba?”

“ban dai sani ba, sai idan ya zo zamuyi magana dashi.”

“To Allah ya kawo shi lafiya” Aneesa ta amsa a ranta, daf la’asar ne tayi wanka ta dauro alwala sannan ta zo ta shirya a cikin leshi marar nauyi mai kalan shudi da digodigon baki, ta fito fes da ita sai shanawa takeyi. Inna dai dadi ne fal a zuciyarta ganin Uwanin ta na walwala, hakan yasa ta kara godewa Allah. Wajen karfe hudu aka ce musu Sagir ya iso, Aneesa ta shiga kai masa abinci ta samu sai hira yakeyi da Muhammadu kaninta.

“Ya cika ka da surutu ko?”

Sagir yace “A’a Muhammad fa abokina ne, kuma hira mukeyi ba ruwanki, kinaga har motar katakonsa ya ban kyauta?”

Muhammad ya fita daga falon da gudu.

Aneesa ta dubi Sagir tace “Ina wuni?”

“lafiya kalau, yaya shan gida?”

A tsume ta amsa saboda har yanzu bata huce ba kan maganar tafiyarta. Ya kula da ranta a bace yake don haka yace

“wani abu ne ya faru naga kaman kina makoki?”

Murmushi tayi kadan sannan tace “ba wanda ya mutu, yanzu Uncle Sagir don Allah baza ka bari na kara ko kwana biyu ba?”

“Au daman a kan wannan maganar ce kika wani hada rai? Ai na gama magana ni dai, idan kin shirya ki zo muje gidan Baban mu gaishe su”

“To kaci abinci kafin nan”

Ta tashi cikin sanyin jiki ta dauko khimar dinta sannan tayiwa Inna sallama, akan zasu je su dawo. Suna fitowa taga ya nufi mota, ita kuwa ta fara takawa ganin haka yasa ya girgiza kai ya rufe kofar motar sannan ya bi sawunta. “Baza ki ce min da kafa kike son tafiya ba sai kawai kiyi gaba? ko dan ni ban san gidan ba?”

Tana shiru bata ce masa komai ba, suna tafiya a hankali ba tare da ta kula shi ba har suka isa gidan Baba, sun samesu duka a gida.

“to wai kin jita, wato har gida zaki jawo min shi ki nuna min ko? To naga dai ko haske na bayi dashi bansan me zaki nuna min ba” Duk suka yi dariya, bayan an gaisane Aneesa tace bari ta je sashen Mairo su gaisa, nan ta bar Sagir suna ta hira da Baba.

Mairo ta biyo Aneesa suka gaisa da Sagir sannan suka musu sallama akan su kam sun wuce “sai idan sun samu dogon hutu kuma in sha Allah sai mu taho” Sagir yayi wa su Baba bayani.

STORY CONTINUES BELOW


“To yayi kyau, Allah ya kara hada kanku ya baku zuri’a dayyiba.” Nan Ya cika su da alheri sannan suka fito suna barin gidan Baba, Aneesa ta kara sauke kai kasa tana takunta dai-dai Sagir yace “don nazo garinku shine kike nuna min hali?” 4

Da sauri Aneesa ta juyo ta dubeshi “Nifa ba hali nake nuna maka ba, kayi hakuri idan kaga kaman hakan ne.”

“To meye ne?”

“Ba komai, ya wuce. Muje kar dare ya mana”

“Kafin nan ki kaini rafin da kike zuwa da Falmata.”

Aneesa ta dube shi ta tuna lokacin da ta bashi labarin rafin kukanta. War haka kuwa wurin gwanin ban sha’awa ne. Don haka suka dau hanya suka gangara a hankali. Suna isa taga Sagir ya nade hannayensa a kirji yana kallon wurin cike da sha’awa ga korayen ganyayaki ga iska mai sanyi, zata juya ne ya sa hannu ya rike nata, tayi saurin juwaya tana waige-waige “uncle Sagir mutane zasu ganmu fa’

“Meye to don sun ganmu, ba hannun mijinki kika rike ba? idan kina so ki kara kwana shi kenan, sai na jiraki gobe mu koma hakan ya miki?”

Aneesa murna ya cikata fal, amma kuma sai tayi tunanin wata kila yaga yanda ta bata rai ne yace haka don taji dadi. Nan da nan tace “Ba damuwa, mu koma yau din kawai tunda hakan kake so. wani lokacin sai na zo na kwana biyu”

Sagir ya sake hannayenta suka juya zuwa gida.

“Amma Uwani yanzu zaku dauki hanya? yanda garinkun nan yake da nisa?”

Aneesa tace “Inna a zuwa ma fa da jirgi muka taho, amma yanzun ban san ko yau zamu wuce ba”

Inna tayi shiru sannan tace “Ke dai ki maida hankali, ki kula da mijinki, ba ruwanki da damuwa da abun hannun sa duk abun da ya baki ki gode masa ki kasance mai masa addu’a kar ki kuma takura masa ko ki fitine shi don kin ga komai kike so yana miki. komai na rayuwa a sannu ake cimmashi”

“Naji Inna na gode, zan kiyaye.”

“Kije kuna yin dare.”

Aneesa kaman tayi kuka nan taji da ma tacewa Sagir din ya tafi, amma haka dai ta daure tayi sallama dasu sannan ta shiga mota. Bayan ta cika kowa da tsarabarshi.

Sai da suka dau hanya Sagir yace “kuka kikeyi? ko mu juya ne?”

Girgiza kai tayi da sauri, parking yayi yace sai tayi shiru su ci gaba da tafiya, ta goge hawayenta.

Maimakon taga sun dauki hanyar fita gari sai taga ya shiga cikin gari, wani gida taga sunje mai kyaun gaske daga gani ma sabo ne gidan. Bata tambayeshi ko ina suka zo ba tunda taji sunyi waya da Haruna abokinsa sai ta zaci ko gidan sa suka zo. Amma bayan sun sauka sai taga Sagir ya fidda makulli ya bude gidan.

“Ba za ki shigo bane?”

Nan ne Aneesa ta fahimci ashe ta tsaya ne kaman hoto, daman ba yau bane zasu wuce Abujan ya hanata zama da Innarta? Tabbas yau ta gane kuskurenta.

Tana zaune bayan ta idar da Sallah, Sagir ya aika musu abinci mai kyau ita dai mamaki ne ya hanata cin abincin, har yau tana kwatanta yawan arzikin Sagir a ranta amma duk randa ta kayyade yawanshi sai ta ga ya wuce tunaninta, wai yanzu gidan da suke ciki mallakar Sagir ne, ita har tsoro kudin sa suke bata yanzu kam.

Sagir ne ya shigo dakin sanye da T shirt da jeans, “Na zaci kinyi bacci ne, kin barni ni kadai a falo”

“A’a idanu na biyu, yaushe zamu tafi?”

“Sai karfe goma na safe in sha Allah, kina da abunyi ne?”

“A’a kawai ina son zuwa gidane.” Ta mike tana nade khimar dinta da abun sallah. Bata ankara ba taji wasu hawaye suna bin fuskarta “Aneesa me ya faru kuma?”

“Babu, nima ban san sun zubo ba.” Ta daga kanta sama alamar neman hadiye hawayen. Sagir ya matso kusa da ita ya kurawa fuskarta idanu sannan yace “yaya kina kuka zakice babu, haka kawai hawayen ki suka zubo? Bazaki fada min dalili ba?”

Nan kukan Aneesa ya koma mai sauti ta zauna a kasan kafet ta saki kukan iya karfinta.

“kina daga min hankali fa ki fada min me ya faru? wani abu na miki? ko kuwa wani abun nace?”

Ta share ido daya da bayan hannunta sannan tace “kawai, abubuwa ne suka min yawa, na gagara sabawa dasu cikin lokaci kadan. Na tashi a rayuwar da komai kashinsa ina jin dadin sa kuma itace kawai rayuwar da na sani da dadi da ba dadi. Na zagaya cikin kauyen mu kaf da kafata, na kwana a gadon bono na tashi na taya Innata aiki sannan lokaci daya ka sabar mani da yawo zuwa kasashe, garuruwa daban daban, shiga jiragen shata, sannan yanzu ko wani gari naje Uncle Sagir ka sayi gida ka fada min ta ina zan saba da duk wannan. Sun min yawa sun wuce tunani na, a saman duk wannan ka daukeni ka mayardani tamkar daidai nake da tsarin rayuwarka bayan zai yi wuya na kamo kafarka.” 3

Sagir ya sa hannu ya kwantar da kanta a kafadarsa “Aneesa me ya kawo wannan maganar kuma?”

Ya dago kanta ya share mata hawaye “ki daina kuka, kar ko daya daga cikin abun da kika lissafa ya shiga tsakanin ki da ni, da ni da ke duk daya ne. Kuma duk abun da kika fada ina yin shi ne saboda zan iya miki kuma ina son na miki.”

“Na san zaka iya min, shine kuma dalilina; tsakani na da kai banbanci ne sosai ba kadan ba, yau gashi na gani tunda koda ni na iya zama a duniyarka kai ba mai iya jure zama a tawa duniyar bane.”

“Saboda nace mu koma gobe shine yasaki tunanin zaman Kunuwal ne bazan iya ba?”

Kanta na kasa bata ce masa komai ba, “Ya Allah, me ya kawo wannan tunanin a kanki?”

Aneesa tace “Tunda kai bazaka iya zama a duniyata ba, shine ka daukoni ka dawo dani duniyarka? Ni rayuwata gaba daya a kauye take idan zaka karbeni da ni da asalina to bani da matsala amma idan zaka soni ka kyamaci asalina …” 14

Sagir ya rasa me ma zaiyi a wannan lokacin ya gwadawa Aneesa kuskuren da tayi wurin fahimtar manufarsa a hankali ya hada fuskokinsu yace “Ta yaya zakiyi zaton zan kyamaci abun da ya bani rayuwata? Kunuwal da jama’ar da ke cikinta sune ke, Aneesa ni kuma kece rayuwata kina jin zan iya kinsu? Har cikin raina asalinki yake da muhimmanci a gareni, kaman yanda bana kyamarki haka bana kyamar garin da kika fito akan meye zan ki ki da asalinki, bayan nima mutum ne kuma ba dabara ta bace ta bani duk abun da kika ga na mallaka. Na yarda ina da arziki mai tarin yawa, amma ba shi zai sa na ki ki ba. Bana son kina wannan tunanin a ranki ko kadan kar ki bari kokwonto ya shigeki dangane da al’amarin mu domin ko zan rabu da tarin arzikina to ke bazan daina sonki ba.”

A hankali ya sumbaci lallausar labbanta wadanda hawaye suka jika.

A wannan ranar Aneesa ta karasa sake ragamar zuciyarta ga Sagir, ta rungumi rayuwarsa ta hada da tata, ta gaskata cewa tabbas ya dauketa ya bata wani matsayi da ba macen da ta taka a zuciyarsa da rayuwarsa. Wannan yasa ta sakankance cewa ita da Sagir sun dace babu banbanci a tare dasu, AL’AMARIN ZUCI ya riga ya hadasu.Ana ta shirye-shiryen auren Sameeha da Aadil, don haka Aneesa bata ga ta zama ba, tun da aka shiga satin bikin suke sintirin kasuwa, da shirya kayan da amarya zata yi amfani dasu. Daga ta dawo daga makaranta to aikin kenan, sai da suka gama ne ta samu kanta, saboda amaryar ma kanta ta daina fita. Gashi makarantar ma tayi zafi saboda yanzu saura zango daya su fara zana jarrabawar karshe. Gajiya ce taji tana sauka a jikinta don haka tayi tunanin idan tayi wanka ta dan mike watakila ta warware.

Shigowar Sagir gidan ne ta farka sai dai da wani matsanancin ciwon kai ta tashi don haka ta nemi magani tasha. Tun dawowar shi ya kula da canjin da yake tare da Aneesa 2

“Lafiya yau na ganki haka? Yau ma kunje kasuwar ne?”

“A’a ai mun gama zuwa kasuwa, kaina ne yake min ciwo tun dazu da na tashi a bacci, amma na sha magani”

“Allah ya sawwaka, kar dai ki sake shan magani haka ba tare da likita ya rubuta miki ba, bari na gama sai muje asibiti a duba ki.”

“Nifa lafiyata kalau, ciwon kai kuma ai ba wani ciwo bane face gajiya, da na samu isasshen hutu zai daina, gajiyar sintirin nan ne.” 3

“Tun kafin auren ma kun bi kun daga wa kanku hankali me yasa baza ku gaji ba? ki dai shirya kizo muje ta can zamu je main house mu gaishe su.”

Tunda taga ya dage ta san zasu bata ne idan bata shirya ba, saboda haka ta dauko khimar dinta ta sauko.

Asibitin da suke zuwa ya kaita sai da aka dauki temperature dinta aka gwada jininta BP da nauyinta sannan aka mikawa likita file dinta, tare da Sagir suka shiga. Likita ya gama mata tambayoyin da ya kamata sannan yace “Madam zamu rubuta miki gwajin fitsari da na jini gobe sai ki kawo sample a nan lab din mu.” Sagir yayi godiya wa likita sannan suka fita “Yanzu me ya sameki da likitan ya ganki, simple abu amma sai kinyi gardama akai” Tana jinsa ya gama fadan sa bata ce masa komai ba, can main house sukayi hira sannan suka koma gida.

Da safe Sagir yace bazata makaranta ba tukun sai ta je gwajin da likita ya rubuta mata don haka asibiti taje da safen. Tana can ne Sameeha ta kirata a waya take shaida mata a ranar za a kai kayan aurenta. Hakan yasa ta nemi Sagir a waya akan tana so ta bi gida idan ta gama da asibiti. “ba damuwa sai ki fadawa malam Hassan din ya kaiki, amma karki dade, kinga ba kya jin dadi”

“to na gode.”

Aneesa tana zuwa ta samu Anty Fatima ma ta dawo daga Zaria kenan suka gaisa bai dade ba masu kawo kaya suka iso, sun samu tarba mai kyau, bare Mummy bata son a ga kashinta don haka sosai aka marabce da bakin ranar har ‘yan gida nasha-nasha aka wuni, su Khazeena ne kan gaba wajen kallon kaya. Suna tafiya Aneesa ta shiga dakin Sameeha tace “ke kuma kina ina ana ta bidiri, Zaheeda tace ta ga abubuwan da take so duk zata kwashe tunda baki san me aka kawo ba.”

“ki rabu da ita, zanyi maganinta.”

“A’a me yayi zafi idan nata yazo sai kema ki kwasa. Yaya dai amaryar uncle Aadil abu kamar wasa wai wani sati daurin aure. Da fatan dai yana kula mana dake?”

“Aneesa kenan har sai na fada? ai Uncle Aadil ba daga nan ba” 2

“Manya iyayen soyayya, Allah ya tabbatar da alheri yasa a yi a gama lafiya”

“Ameen, kinaga Daddy ya soke mana wasu events wai shiri daya kawai za ayi , a tafi Zariya a karasa bikin a can?”

“kema dai dama kina tsamman daddy ne zai yarda da wasu tsirfe tsirfe? a dai yi addu’a koma me za ayi Allah yayi wa auren albarka kawai.”

“Ameen, haka Aadil yace.”

“Ni kinga zan gudu my dear yace na koma da wuri, kuma kinga gwamma na gama shiri a tsanake kar nayi mantuwa.” 3

STORY CONTINUES BELOW


********

Tana kwance da yamma a kan kujerar dakinta saboda ciwon kan ya matsa mata ta bukaci samun hutu, Sagir ya turo kofar ya shigo, a hankali ta bude idanu ta dube shi ya zauna a gefenta ya kura mata idanu.

“Lafiya? me ya faru kake kallo na haka?”

“Babu abun da ya faru, likita ya kirani game da sakamakon ki.”

Ta dan gyara kwanciyarta, me kuma likita zai samu ai tasan bata lokacin su kawai sukayi, ta riga ta san gajiya ce kuma zata warware…

Bata idda tunaninta ba taga Sagir ya rarumeta ya kwakume “Alhamdulillah, da Allah ya nuna min wannar rana” 3

Ta dube shi kasake “wace rana?”

Ya saketa a hankali yace “Aneesa likita yace ba ciwon kai kawai ke damunki ba, kin samu shigar ciki ne shi ya haddasa miki canji a jikin ki” 3

A take Aneesa ta rufe idanunta da tafukan hannu cikin jin kunya. A ranta kuwa dadi ne fal a ciki, yanzu ita take dauke da dan Sagir a jikinta?

Tun shigowarsa ranar bai sake fita ofis ba, ko unguwar darensa ranar bai je ba wai yana gadin Aneesa ko akwai abun da take bukata. 11

Washegari Asabar ne saboda haka Aneesa bata da buqatar zuwa makaranta, amma taji da ma akwai ta samu ta kubuce wa bibikon Sagir motsi kadan yace yaya take ji yaya jikinta. Ranar Lahadi ne da safe sai ga Anty Sameera ta zo da Azhaan, Aneesa ta karbe su hannu bibbiyu, taji dadin samun Sagir da tayi a gida, da ta yi niyyar barin Azhaan ne ya wuni amma sai ta rakashe ta samu wuri.

“A’a big man, yaya school?”

Azhaan yace “uncle Sagir lafiya, ka san mummy ta saya min sabon school shoes?”

“kai lallai mummy ta kyauta, sai ka bani tsohon kenan”

Azhaan ya dubi kafan Sagir yace “To ai sun maka karami. sai dai na bawa Anty Aneesa”

kowa yasa dariya.

Sagir ya dubi Sameera yace “Babu wani problem dai ko? yaya wurin su Yaa Fanna?”

“Lafiya kalau, ba wata matsala, Yaa Amina tace na gaida ku”

“To mun gode”

Sagir yana gama gaisawa dasu ya koma kan al’amarin Aneesa, wannan abu dai ya matukar bawa Sameera mamaki, Sagir dai da tasani Sagir Daggash shi ke dauko ruwa ya bawa Aneesa a baki, ya zauna gefenta yana aiki, motsi kadan ya tambaya ko lafiya. Da abun haushin ya soma mata yawa ne tace “Yaya Sagir Aneesan bata da lafiya ne?” 3

Sagir yace “Sarautar ce dai ta motsa” ganin Sameera tayi magana sai yayi tunanin wata kila ta takura da yanda yakeyiwa Aneesan ne don haka yace “Ni ina dakin karatu, Aneesa ki ajiye wayar ki kusa idan akwai damuwa ki kirani.” 4

Sameera kaman zatayi kuka, yanzu wannar ‘yar kauyen da take gani Yaa Sagir baza a je ko ina ba zai koreta ita ce take juya shi haka? daga gani kuma yayi nisa ba jin kira. Anya kuwa zuwanta gidan nan ma da takeyi na kawo Azhaan weekends yana da wani tasiri a wurin Sagir kuwa don ta kula ko kallo bata isheshi ba. 7

Aneesa taja hannun Azhaan suka je kitchen ta hada masa rice krispies, suka zauna tana bashi yana bata labarin makarantarsa. Sameera ta kare mata kallo sannan ta mike tace “Ni zan wuce”

Aneesa tace “na dauka zamu dade anty Sameera?”

“A’a kiyi hakuri, ina da abubuwan yi a gari.”

“to shi kenan, amma dai zaki bar mini Azhaan kam, anjima zamu dawo dashi in sha Allah”

“Ba damuwa.” Aneesa ta rakata har bakin kofa sannan ta koma suka ci gaba da sabgarsu da Azhaan sai da yayi kat ta kunna musu cartoon suna kallo, sai ga Sagir ya fito, “naji ku shiru, Sameeran ta tafi ne?”

STORY CONTINUES BELOW


“Eh ta tafi wai tana da abunyi a gari, shine nace mata ta bar Azhaan zamu mai dashi.”

Sagir ya shafa kan yaron yace “Azhaan zaka zauna gun Anty Aneesa ko zamu je yawo?”

Da sauri yaron ya mike yace “Uncle Sagir zan bi ka.”

“To shi kenan, tashi muje.” Aneesa ta dube su gwanin sha’awa sai taji sun burgeta, kullum al’amarin Sagir da Azhaan yana bata sha’awa yanda suka shaku, kasancewar Sagir din yaron ya tashi ya sani a madadin mahaifinsa. Sai da yamma suka shigo gidan Azhaan na haki, hannunsa rike da ledojin kayan wasa da na ciye-ciye.

Aneesa tace “Wato kuka tafi ka barni ni kadai ko? gobe bazan maka fruit salad ba idan ka zo” ta nade hannayenta a kirji ta tsume.

Azhaan yace “kawo kunnenki na fada miki.”

Aneesa ta durkusa dai-dai tsawonsa, Azhaan yayi dariya ya rage murya sannan yace “secret ne, Uncle Sagir ya hana fada”

“hmmm kai da Uncle Sagir kuka hada plan ko? to shi kenan, nima ina da plan dina kuma bazan fada maka ba.”

“Please Anty Aneesa ki fada min zan baki kyautar sabon kekena da Mummy na ta saya min.”

“to na gode, muje na maka wanka sai na fada maka plan dina.”

********** ********* *******

Ranar alhamis Aneesa taje gidan Daddy kasancewar ranar mummy ta shirya liyafar da za ayi wa Sameeha, gidan a cike yake, domin kuwa kawayen Hajiya Juwairiyya da kostomominta, ‘yan uwanta da na daddy duk an hallara, Anty Fatima ma ta gayyaci bangarenta. Komai anyi shi na girma da aji haka nan amarya tayi fes gangariya da ita, Sai da dare aka tafi filin taron. Aneesa ko waya na jaka tana ta hidima ta manta da kanta, sai da taro yayi nisa ta duba hadaddiyar agogon dake manne a hannunta taga har sha daya saura. Da sauri ta zabura ta bude jakar hannunta, tana daga wayarta taga missed calls din Sagir har biyar.

Yau ta ga takanta, me tayi? yanzu ran Sagir zai baci akan abun da tayi, sai da ya nanata mata ta rike wayarta a hannu saboda kar yazo bai sameta ba. Tana kokarin neman sa a waya ne, taji MC na bayani a bututun magana akan ana neman Aneesa a waje. ko sallama batayi da kowa ba bayaga wadanda suke zaune tare, ta mike da sauri ta fita tana rarraba idanu, a jikin motarsa E-class ta hango shi a tsaye ya goya hannayensa a kirji kafafunsa a nade cikin juna. Sauri takeyi amma sai tana ji kaman bata tafiya, musamman da taga irin kallon da Sagir din yake mata. 4

Ba tare da yace komai ba ya bude motar ya shiga, maimakon ta samu natsuwa saboda rashin maganar tasa a’a sai hankalinta ya kara tashi. Nan da nan taga gwamma ta bashi hakuri watakila kan su isa gida ya huce.

Ta dan dubi gefen da yake taga ya hada gabas da yamma, amma haka dai ta daure tace “Uncle Sagir kayi hakuri, wayar tana jaka kuma ban ji vibration din ba saboda hayaniya ban san ka iso ba” 1

A fusace Sagir ya dubeta “Meye amfanin wayar idan baza a amsata lokacin da ya dace ba, sannan kin san condition din da kike ciki, amma kika zauna a wurin hidima har sha dayan dare, ashe idan ba a gama ba hankalinki bazai baki ke ki nemi tafiya gida ba?”

Ganin ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ta san tsayawa yi masa bayani ma bata lokacinta zatayi don haka tayi shiru ta gama jinsa har suka isa. Suna komawa wanka tayi, tayi shirin kwanciya gashi tana da tashin sassafe don haka ta shiga don ta kwanta, amma sai da ta dade da kwanciya sannan ya shigo dakin. Ita bata san wani irin fushi yake dashi ba, abu kadan idan ya hau sai an dage ya sauko?

Washegari ma bai sake dauko maganar jiya ba, sannan bai sake mata fuska yanda itama zata dauko maganar ba don haka ita ma sai ta basar, taje makaranta ta dawo. Tana kara duba jakar tafiyarta Zaria ne ko tayi mantuwa sai taji karar bude gate, dubawan da zatayi daga windon dakinta taga Malam Hassan yana fita da mota. Ta san dai an sauko masallaci don haka da sauri ta kira shi a waya don tace masa ya jirata tana saukowa ya kaita gidan Daddy su hadu da sauran masu wucewa Zaria, don tacewa Aisha ma su hadu a can gidan Daddy kawai. Yana daukar wayar yace “Assalamu alaikum hajiya” 4

STORY CONTINUES BELOW


“wa’alaikumusalam, malam Hassan naji kaman fita zakayi, ina saukowa yanzu don Allah”

“to, daman yallabai ne yace na same shi a can ofis ban san ko zaki kirashi ba sai kiji”

“Ah, to ba komai kaje kawai zanyi magana dashi”

Ta kashe wayar tana mamaki, to lafiya Sagir zai nemi malam Hassan yanzu? ta san dai yana tare da Nuhu. Gashi yanzu kusan uku saura, ai zasu yi dare ga Khazeena tace mata har an tattafi. Ko da yake hala kudin mai zai bashi. 2

Aneesa dai tana zaune zaman jira da taga har tayi la’asar shiru ba malam Hassan sai ta nemi wayar Sagir, sai da yayi ringing sosai sannan ya daga.

“Hello, uncle sagir yaya aiki?”

“lafiya, yaya dai zamu shiga meeting yanzu wani abu ne?” ya fada a gaggauce

cikin jin mutuwar jiki da yanayin amsar tashi tace “Daman batun tafiya Zarian ne naji Malam Hassan shiru, su Aisha kuma suna jirana a gidan Daddy”

“Zaria? ke din wai zaki Zaria? me zaki je yi?” 8

Tambayar ta bata mamaki sannan ta mata zafi, yaya Uncle Sagir yake mata kaman bai san da kanwarta ce take aure ba?

“A can za a karasa bikin ai, na dauka mun gama maganar”

“eh mun gama magana, amma yanzu na canza shawara ki zauna gida ban ga amfanin tafiyar ba”

Ran Aneesa ya cunkushe wani mololon bakin ciki ya lullubeta a take taji wasu hawaye masu dumi suna gangaro mata.

“Uncle Sagir, kowa zai hadu, sannan gobe za a daura aure ni kadai ce zan zama bana cikin ‘yan uwana?”

“kar ki damu zan sanar dasu lalurar ki, bana son kina yawo da karamin ciki don haka ki hakura da zuwa” 4

Bakin ciki ne yasa ta kashe wayar ta wurgata kan gado, me yasa Uncle Sagir zai mata wannan hukuncin? Wato shi yasa yayi shiru ya san me ya tanadar don ya hora ta ko? Amma ya cuceta yaya za ayi ta rasa bikin Sameeha yanda ta tsaya aka shirya komai a ce za ayi bata nan? Nan ta zauna a dakin taci kuka har ta gode Allah, kwalliya kam tuni ya tafi garin su tayi fici-fici da ita. Can taji wayarta na kara ta daga tana ganin sunan Aisha tace “Aisha idan akwai sauran masu tafiya kawai ki bisu, ni kam tafiyata ta fasa”

“iye, irin ke da angonki zaku taho ko? Ba damuwa sai kun taho zan bi motar su Khazeena yanzu ma haka muna tare, sai kun iso”

Aneesa tana kashe waya sai ta sa wani sabon kuka, ita Aisha ta zaci wai da Sagir zasu tafi idan zashi daurin aure bata san ma ya mata bakin cikin tafiyar ba. Tana jin shigowar motarsa kasancewar gidan yayi tsit, amma taki sauka.

Sagir yana shigowa ya ga alamar gidan ya san Aneesa ta hau don haka bai bi ta kanta ba ya shige dakinsa. A can ya duba mails dinsa yayi wayoyin da zaiyi kafin nan ya nemi angon don su karasa tattauna hidimar washegarin.

Sai da ya kammala tukun ya yanke shawarar leka halin da take ciki kasancewar ya san halinta sai ta wuni bata ci ba bata shaba. Yanda ya sameta kuwa ya tabbatar masa da zarginsa “Aneesa, meye hakan kuma? Akan rashin zuwa biki shine zaki dawo da kanki haka? kin san da cewa dai ba ke kadai bace yanzu? Ba zan lamunci duk wani gangancinki ba akan abun da bai taka kara ya karya ba wanda har zai janyo kiyi wa baby lahani, don haka ki nemi abu kici ki tattara tunaninki kuma ki kwantar da hanakalinki, akan ki aka fara rashin zuwa biki?” 4

“haba, Uncle Sagir ‘yar uwata ce fa? kuma har ta sa rai zanje sai kuma nace mata na fasa me yasa ka hanani tafiya?”

“Idan da bake a duniya hakan zai hana auren Sameeha? Batun dalilin hana ki zuwa kuwa, hakan naga dama kuma magana ta kare bana son a sake nanatawa.” 6

Jin haka Aneesa ta mike ta shige ban daki ta wanke fuskarta da bakinta sannan ta zo ta kashe wuta ba tare da ta saurari fitar shi ba tayi kwanciyarta.

“Baki ji me nace bane? ki tashi ki nemi abu ki sa a cikinki, nima kuma yunwa nakeji ki tanadarmin abun da zanci.”

Kuka ta saka marar sauti mai zafi a ciki, ta mike yau kam ta san Sagir mugu ne, daman kirkin karya yake mata. Ta sauka tana ta gwara kwanuka a kicin din ta dawo masa da kunu a mug. 6

“ke ina naki?” ya tambaya taga dai alamar bayi da niyyar fita daga dakin.

“Na sha a kicin” ta fada a dakile.

“Kin san bana son gardama ko karya don haka zauna ki karba.”

Tana ji tana gani ya dura mata kunun nan, sannan ya shanye sauran, ai kuwa yanda tasha bata so, haka cikinta yaki rike shi da gudu tayi bandaki ta hau kwazar dashi a toilet, Sagir na tsaye a kanta yana rike da kafadunta banda sannu ba abunda yake mata. Ya zuba ruwa ya bata ta kurkure bakin ta wanke fuskarta sannan ya rikota zuwa dakin ya kwantar. A gefenta ya kwanta yana shafa kanta “To ba ga irinta ba, yanzu a wannan halin da kike ciki wani gidan biki zaki fara zuwa kina takura kanki?” 4

Ita har ta tsani yana maimaita kalmar ma don haka ta juya masa baya, amma Sagir bayi da niyyar kyaleta nan ya shiga sunsuna gashinta yana mata wani salo, tana ji tana gani ya daketa ya hanata kuka karfi da yaji.
Tana sallah, ta sauka don ta shirya abun karyawa, ta san sammako Sagir zaiyi zuwa Zaria. Abun haushin da ya dameta ma shine tayi kokarin taga ta tashi da fushin rashin tafiyarta amma ta nemi fushin ta rasa sai ma wani jin dadi da takeyi idan ta tuna duniyar da Sagir kan iya kaita a duk sanda ya so. Tana gamawa ta koma dakinta ta sha wanka ta ci kwalliyarta kaman ba ita bace jiya ta ci kuka. Tana saka dankunne ne ya shigo dakin ya tsaya daidai kanta ya rungumota ta baya. ‘yar cikin danyar shaddace mai ruwan madara a jikinsa da alama bai sa garen bane, sai kamshin sa na musamman dake tashi a jikinsa. “Yau baza a tayani karyawa bane?” 52

“Yanzu daman zan sauko, kayi hakuri.”

“Fushi ya kare kenan.” Duk da ba sosai take jin haushin sa ba sai ta sadda kai kasa tace “Wane ni yin fushi da kai Uncle Sagir, tunda har kace ai shike nan magana ta wuce. Duk yanda na so tafiyar nan bai kai son ganin na bi umarnin ka ba.” 5

Ya dubeta cikin so wannan yarinyar akwai iya kalami “Tunda kince haka, na baki umurnin kema ki shirya sai mu tafi tare” 5

Da sauri ta juyo ta fuskance shi idanunta suna bayyana farin cikin da ta tsinci kanta “Da gaske?”

“Eh, amma idan kika dade wurin shiryawa kuma na tafi na barki”

Da sauri tace “Ai ma a shirye nake, mayafi kawai zan dauka da jakata.” cikin murna ta makale masa wuya.

“Idan baki sakeni ba daga ni har ke bazamu tsira wurin Aadil da Sameeha ba don zamu rasa daurin auren.” Da sauri ta sake shi ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Ya mike tare da lakace hancinta ya bar dakin. Kafin kace meye ta shirya ta fito fes da ita cikin wani lace mai launin koren ganye da aka masa ado da ruwan hodar da ta turu (Fuchsia pink), ta fito da lafaya da ta shiga dashi sosai ta nada.

Ba abun da zata cewa Aisha domin kuwa ita ta koya mata wannan shigen. Ita kanta ta yaba da kwalliyar tata a madubi. Ta nemi takalman da basu fiye tsawo sosai ba ta saka, jakarta kuma serviette ta jefa da wani setin kayan kwalliya na kamfanin l’oreal, lip balm, turarenta na channel, sai wayarta da chewing gum mai kamshi.

Tun daga kan matakala tana saukowa a hankali Sagir ya bita da kallo yana mamakin yanda a da yake mata kallon karamar yarinya ya gagara kallon macen da ke gaban shi, yanzu ko zuciyarsa har wani alfahari takeyi da samun mace kamar Aneesa. Suna karyawa rabin hankalin Sagir na kanta, ta kula da hakan ne yasa ta kara yauki tana cin abincin kaman bazata ci ba can tace ita ta gama. 3

“Haka zaki na zama da yunwa? kin san jiya ma ba wani abun kirki kika ci ba, sannan yanzu zaki kama hanya amma ba za ki sa abu a cikin ki ba?”

“Na koshi, bana son zuciyata tayi ta tashi ne a mota shi yasa.”

“To shi kenan, amma muna isa ki nemi wani abu ki sa a cikin ki”

Ta amsa mishi a sanyaye. Bayan ya kammala ne yace wa Malam Hassan ya fito da mota, “Sun dauki abincin su ai?” Sagir ya tambayi Aneesa

“Eh tun da na gama na kira Musa ya dauka musu.”

Sagir ya jinjina mata, kullum yana tausayin yanda take aiki cikin gidan nan ya kissima maganar a ransa yana gani zai yi magana da Hajiya ko za a samu wadanda zasu rinka taimaka mata da aiki don yanzu ga wahalhalun ciki ga karatu abubuwan zasu mata yawa.

STORY CONTINUES BELOW


Suna tafe a mota taji Sagir yana waya da angon, wai su Uncle Aadil ba dama yau murna ba acewa komai. Suna gamawa tace “Na san Uncle Aadil ji yakeyi kamar sha daya bazatayi ba a daura auren. Tun shekaranjiya zumudi waya kan waya, har Sameeha ta daina dauka”

“yanzun ma cewa yakeyi yaya har yanzu bamu taso ba? kin san mutum idan ya hadu da abun da yake so to fa ba a cewa komai.” Ta dubeshi tayi murmushi.

Sun dau hanyar Kaduna radio ke ta aiki a motar, Sagir ya rage muryar shi yace “shi wannan ba a sa shi a zauna a gida ne sai idan za a fita?”

Ya sa yatsu biyu yana murza lafayyar jikinta. Aneesa tayi dariya tace “Ba a sawa, ai zai takura mutum.” 7

“Gashi kuwa ya miki kyau.” Ya fada yana kallon cikin idanunta, da sauri ta boye fuskarta a cikin garenshi. 9

A hankali ya rada mata “Malam Hassan yana ganinki ta madubi” ba shiri ya sa ta matsa gefe yana dariyarta. Cikin nishadi suka isa, zuwansu kofar gidan Daddy har an dan fara taruwa, don haka ba tare da sun sauka daga mota ba, Sagir ya jira malam Hassan ya fita sannan ya dauki bandir din dari biyar-biyar yace “Ga tukwuicin kwalliyar yau, duk da dai biki za a tafi a ka yi ta.”

Aneesa ta yi wannan murmushin da tasan Sagir yafi so tace “Duk da biki zanje, na san da Uncle Sagir dina a gefena shi yasa nayi. Na gode, Allah ya kara budi ya dada rufa asiri, ya kuma biya maka dukkan bukatunka na alkhairi.” Wannan maganar da ta fada masa sai da ya janyo mata samun rabonta, riko habarta yayi ya bata kwakkwayar tukuici a baki, sannan ya sake ta. Aneesa ta juya taga ko da me ganin su amma ganin duhun glass din motar yasa ta sauke ajiyar zuciya. Ta rike mabudin motar ne yace mata “ki kula da kanki fa, sannan don Allah kina shiga ki nemi abu ki ci.”

Ta fita daga motar zuciyarta a cike fal da farin ciki, dakin mummy ta fara zuwa ta gaisheta. Mummy ta amsa ba yabo ba fallasa bare yau tana farin ciki zata aurar da diya. Ta bi Aneesa da kallo ganin yanda ta kara wani haske da sheki, ga shiga ta alfarma nan a tare da ita ko ba komai ta san ta samu kwanciyar hankali. Haka take fata Sameeha ma ta zauna lafiya da mijinta.

Tana shiga dakin amaren su Sameeha da Aisha suka fara mata tsiya, “kinga manya masu tafiya cikin class, ba a tahowa da yaku bayi sai an jira oga ya tako baya” 5

Aneesa tace “sai kuji dashi ai, Sameeha ke kiji da fargaban barin gida kina biyewa wadannan.”

“Zuciyata fal da farin ciki wani fargaba ya saura?”

“Za ma ki gane kuren ki ai, yanda ya bi ya matsu yaga an taru an shafa an watse sai kin shiga hannu zaki gane shayi ruwa ne” 6

Aisha ta sa dariya sannan tace “Anty Aneesa yaya banga an shigo da jakarki ba. Ko ke bazaki wuce Jos din bane”

Aneesa ta gyara zama tace “hmmm ke dai bari abun dogon labari ne. Bari kiga na sa maasa a ciki na ko zanji daidai, har wani jiri nakeji”

“uhm-uhm wannan jiri jirin dai kam sai a hankali”

Aneesa tayi fari da idanu tace “fulakon abinci nayi nazo ban koshi ba gashi yanzu yunwa na tambayata ki rike fassarar ki” 5

Sameeha tace “Aisha ki rabu da ita idan tayi tsami zamu ji.”

Da misalin karfe sha daya da minti goma aka daura auren Sameeha Mahmoud da Aadil Yahaya. Farin ciki ya rufe duk wanda ya halarci taron bare wadanda akayi taron don su. Ana gama daurin aure angwaye suka wuce inda aka tanada domin yin reception nasu. yayin da a cikin gida kuwa sai shirye-shirye akeyi na tafiyar amarya da masu kaita Jos don dama kususu kam da su aka daura aure. Kasancewar iyayen Aadil a can suke za a wuce da amarya can a karasa biki kafin nan kowa ya watse, yawanci jama’a daga Zaria kowa zai koma gidansa mutane kalilan aka ware wadanda zasu raka amarya Jos din. 4

STORY CONTINUES BELOW


Bayan Azahar ne Sagir ya kira Aneesa yace ta same shi a falon Daddy. Sai da ta kara gyara fuskarta ta fesa turare mai sanyin kamshi sannan ta tafi falon. Da shi da angon ta samu a zaune “Wai yau Uncle Aadil buri dai ya cika, ina fatan dai baza a sake cewa ‘yar uwata bata da natsuwa ba?”

Aadil ya sa dariya yace “ke kuma zamuyi haka dake? Ai wancan tsohon zance ne. kin ga yanzu kin kara samun matsayi daga kanwa kin koma babbar yaya.”

“A to gwamma mu sani ne ai, Allah ya bada zaman lafiya ya kawo zuri’a dayyiba.”

Aadil ya amsa da Ameen. Sagir ya dubeta yace “kinci abincin kuwa?”

Nan da nan ta kara kasa da murya cikin wani salo tace “eh naci.”

Sagir ya kula da hakan da tayi sai dai sunyi rashin sa’a ba su kadai suka gane hakan ba, Aadil yace “Bari naje na sallami su Buhari suna waje.” 2

“To ba matsala”

Aadil na fita Sagir yace “Yaya to zamu iya tafiya ko?”

“Sun kusa tafiya ko zamu dan jira mu ga tafiyar su?”

“To shi kenan, idan sun tafi sai ki sameni a mota. Baki dai sake hararwan ba ko?”

Kai ta gyada masa,”Dazu Malam Hasan ya shigo da wata jaka yace a bawa Sameeha, tana mika godiyarta, Allah ya saka da alheri”

Sagir yace “Ameen, ba komai” Ta mike zata fita ne dai-dai lokacin Aadil ya shigo yace idan ta shiga tayi musu magana su fito.

“Kai Uncle Aadil, za dai akai maka matar” Nan suka sa dariya ta koma cikin gida.

Biki dai anyi shi lafiya baki kuma kowa ya koma gida lafiya an bar ango da amarya da halayensu.

Suna komawa kuwa ranar litinin ta ci gaba da zuwa makaranta, Hajiya ta sama musu wata mata da zata na tayata ayyuka, a hankali Aneesa ta gwada mata komai.

Sau da yawa idan ta dawo daga makaranta ma zata samu Iyatu ta gama ayyuka. A ta bayan kicin dama akwai dakuna, daya daga cikin dakunan Iyatu take amfani dasu. Yayinda masu gadi da su Malam Hassan suke can Boy’s quaters

Aneesa ta gama rajistar dukkan jarrabawan da zata zana saura watanni uku a fara jarrabawa, don haka ba wasa karatu sosai takeyi. Amma da zaran Sagir na gida to zata tattara komai ta ajiye a gefe domin lokacinsa ne. Hankalinsu ya kwanta da juna kuma tunda take bata taba dagowa Sagir maganar Ummi ba, haka shima bai tambayeta ba duk da yasan ta samu labarin. 1

********

Ranar asabar da safe ne Khazeena ta kirata a waya hankalinta a tashe tace “Aneesa ke kam ga Sameeha a gida sai kuka takeyi babu yanda ba ayi da ita ba ta fadi me ya sameta taki magana. Yanzu dai Daddy yace ya nemi wayar uncle Aadil inaga yana kan hanya ban san me ya faru ba. Ki kirata ki gwada tambayarta ko zata fada miki” 4

Aneesa nan take taji zufa ya feso mata hankalinta ya tashi, me zai faru da har Sameeha zata koma gida wata biyu da aure? Kai wannan babbar matsalace don haka da sauri ta shiga dakin karatun Sagir ta same shi.

“lafiya dai Aneesa? yaya na ganki haka?”

Cikin tashin hankali ta fada masa abun da yake faruwa “Aadil ya taba fada maka suna da wata matsala ne?”

Sagir yayi shiru yana tunani, “Babu, ki kwantar da hankalinki koma meye ne a tsanake za a warware shi.”

Aneesa dai hankalinta yafi bata suje gida suji me ake ciki amma Sagir yace tabari sai abu ya lafa tukun na.

Suna zaune a falon Sagir da yamma sai sukaji buga kofa, Aneesa ta zabura daga cinyar Sagir inda tayi wa kanta matashi, ta nemi mayafinta sannan ta je ta bude kofar. Mummy ta gani a tsaye a wurin. Jikin Aneesa dai ya bata ba kalau ba.

STORY CONTINUES BELOW


“Mummy sannu da…”

“Rufe min baki munafukar banza munafukar wofi, ai ni daman nasan za ayi haka, ki hada jini da Halima ki zama baki da sharri?”

Kan Aneesa ya daure me ya kawo wannan maganar kuma?

“Mummy ki shigo ciki muyi magana…”

Sagir yana jiyo hayaniya hakan yasa ya mike ya fito bakin kofa ganin Hajiya Juwairiyya abun ya bashi mamaki kwarai.

“Ni me zan shigo nayi a gidanki? kinji dadi kin haddasa min fitina da tashin hankali a gida hankalinki ya kwanta, kina tunanin zaki tauna taura biyu ki share ko? To ina son ki san kinyi kadan.”

“Hajiya me yake faruwa ne? kiyi hakuri ki shigo ciki ayi magana a tsanake ai hakan bai dace ba.”

“Ni zaka fadawa abun da ya dace da wanda bai dace ba? Ai wacce ya kamata ka fadawa wannan tana karkashin inuwarka kuma ta dade tana damfararka amma son da kake mata ya rufe maka idanu.”

Ran Sagir ya fara baci, wani irin abu ne mata zaki baro gidanki kizo kina tayar masa da hankalin iyali sannan ga ma’aikata suna kallo.

Da kyar ya samu ya lallaba Mummy ta shigo karamin falo ta zauna.

“Hajiya, kiyi hakuri daga bisa dukkan alamu an bata miki rai, amma ina son na san wai me yake faruwa ne?”

Aneesa na gefe banda hawaye ba abun da takeyi.

“Abun da yake faruwa shine matarka tana nema ta kashewa ‘yata aure”

Maganar ta daurewa Sagir kai ba shi kadai ba harda Aneesa, “Ban gane ba. Wani abu Aneesa ta fadawa Sameeha?”

“Baza ka gane ba, Abokin ka dai amininka da ka rike a matsayin dan uwa soyayya yakeyi da matar ka” 3

Sagir ya zabura cikin fushi jin wannan kalma abakin Mummy amma kuma ya dakatar da kanshi jikin sa na bari yace “Hajiya, kin san ina baki dukkan girman da ya dace na bawa mahaifiyar Aneesa, amma ina son ki san wannan irin zance bai kamaceki ba. Don haka duk abunda Aneeesa ta miki wanda bai miki ba, ke matar babanta ne zaki iya kiranta ki fada mata, amma ki wanke kafa ki zo gidanta ki daura mata irin wannan sharrin a gabana mijinta wannan bazan lamunta ba don haka idan bazaki damu ba don Allah ki koma gida.” 5

“Da kyau, ai ba haka banza ba. Zasu barka haka ne? yau ni kace na fita na bar maka gida, zan fita amma ina son ka bincika wannan maganar da kyau, domin kuwa ‘yata da idanunta ta ga kwakkwarar shaida kan cewa lallai mijinta yana son ‘yar uwarta kuma matar abokinsa” 4

Aneesa kam tsabar girman wannan rikici ta kasa kwatanto tashin hankalin da ta tsinci kanta. Kuka kawai takeyi jikinta na tsuma. Mummy na fita Sagir ya ja kofa ya rufe ya dawo ya samu Aneesa. “Ki daina kukannan haka,”

“Wallahi my dear ban san me yasa mummy wannan maganar ba, ban san me kuma take magana a kai ba, kai shaida ne tun da nake ban taba son kowa ba sai kai. yaya ma za ayi da aurena na so wani da namiji bayan mijina?”

Tana kuka tsakaninta da Allah yayinda take mamakin irin wannan fitina da Mummy tazo dashi. Sagir ya rungumo Aneesa jikinsa yana rarrashinta “Ya isa haka, na san an samu misunderstanding ne amma koma meye ne zan warware shi. kiyi hakuri”

Cikin kuka ta daga masa kai, to amma me zai sa Sameeha tayi wannan tunanin har tayi yakinin cewa tana da kwakkwara shaidar da zai nuna haka? Bayan hakan ma ta bar gidan mijinta da kwatakwata watan su biyu da aure? dole akwai wani abu mai daure kai a wannan al’amari.

Sagir yana tabbatar da hankalin Aneesa ya kwanta ya ce “Ni zan fita, zaki zauna a nan ko na kaiki gun Hajiya?”

“ba komai sai ka dawo.”

Bayan Daddy ya nemi ganin Aadil ne domin jin musabbabin rikicin daga wurinsa sai ya kira Sameeha, Anty Fatima da Mummy a falon shi yace “Ke sameeha nayi magana da mijinki, kuma ya shaida min duk abun da kika fada. Amma kuma ya min wani bayani mai gamsarwa, don haka ina so ki saurareshi ku fahimci juna.”

Mummy tace “meye abun fahimtar juna, yarinya taje ayi ta cutar ta. Tunda ya fito yace baya son ‘ya ta shikenan ni ina son ta”

“Juwairiyya idan rai ya baci ai ba aso hankali ya gushe, don haka nake son ki kwantar da hankalinki”

Anty Fatima tace “hakane”

Mummy ta banka mata harara ita bata ga meye wannan takeyi a falon nan ba, abu bai shafeta bama sai ta sa kanta duk kuma Daddy ne ya daure mata gindi.

“Abun da nake so dake Sameeha ki saurare shi ya miki bayanin komai. Anjima nake son ki shirya ki koma dakinki.”

Sameeha ta dago ta dubi Daddy “Allah Daddy bazan iya zaman gidan ba.”

“Wani irin maganace haka, ba za ki iya zaman gidan ba gidan wa zaki zauna? ko an gaya miki haka ake zaman aure, daga kin samu matsala da mijinki sai fuuu ki tafi gidan ku?” 7

“Daddy ai gaskiyarta ce, yaya za a dake ta a hanata kuka?”

Jin haka Daddy yace su tashi shi kam ya gama magana suyi abun da suke so.

Sagir yana fita Aadil ya nema. Suna haduwa yaga yanda abokin sa ya shiga wani irin yanayi.

“wai me yake faruwa ne? Hajiya ta zo gida dazu tana wasu maganganun da ban gane kan su ba, yaya aka yi har haka ya faru ne?”

Aadil yacewa Sagir ya zauna, “Lafiya kalau kawai dai wani dan rashin fahimta aka samu daga wurin Sameeha”

“Ban gane dan rashin fahimta ba bayan yarinya tana gidansu. Ba dai korarta kayi ba ko?”

“A’a sam da kafarta ta tafi”

“Wai me yasa baza ka fada min asalin me ya faru bane? me yasa Hajiya taje tana zagin Aneesa wai zata kashe mata auren ‘yarta?”

Aadil yayi shiru ya rasa ta inda zai fara fuskantar aminin shi da wannan bayani mai rikitarwa, wanda ya hana shi bacci na darare masu dimbin yawa. Don haka yace “kar ka damu komai zai wuce, kai dai kawai ka san cewa duk abun da yaje ya dawo ni bazan taba cutar da kai ba ko na maka abu na kaskanci. Ka wuce komai a wurina Sagir, ka daga ni daga babu ka kaini matsayin da nake a yanzu duk abun da nake takama dashi ko ‘yan uwana suke takama dashi Allah ya sa ta sanadinka duk na samu hakan don haka kar ka bari wani abu ya shiga tsakanin wannan.”

Sagir dai kanshi ya kulle me yasa Aadil zai na irin wannan maganar? Sai dai idan abun da hajiya ta fada… inna lillahi wa inna ilaihirraji’un

“kana nufin duk abun da Hajiya ta fada gaskiya ne?”

Aadil yayi shiru ya rasa amsar da zai bawa Sagir, sai ji kawai yayi hawaye suna gangaro masa ya kau da kai gefe ya goge su kafin ya juyo yace “Duk wannan a baya ya faru kuma ya wuce, sannan kuma ina son na fada maka Aneesa bata san komai ba akan maganar nan…” 4

Sagir idanun sa a runtse ya mike daga kujerar ya dakatar da Aadil “Tun yaushe kake son matata? kafin auren mu ko sai da na aureta?” Sagir ya matsa kusa da Aadil ya cakwamo wuyar rigar sa yana jijjigawa “Abun da zaka saka min dashi kenan Aadil? Matar da na aura kake so? ka shigo gidana ina nan da bana nan kuyi hira kuyi wasa da dariya ashe kana da wata manufa a tare da kai? Haba Aadil a matsayin dan uwana na dauke ka. Ka bani mamaki ka kuma bani kunya you disgust me!” ya sake shi har sai da Aadil ya tafi tagal-tagal kamar zai fadi. 5

Sagir ya bude kofa ya fita Aadil ya bi bayanshi yana kiransa amma ran Sagir ya kai makura wajen baci.Tana zaune a falo tana jiran shigowarshi taga ya shigo fuuuu ya wuce dakinsa, hakan ya daga mata hankali sosai don haka ta bi bayanshi taji ko me ya faru. A hankali ta bude kofar dakin ta sameshi a zaune kan kujerar dakin sa ya kama kai da hannu bibbiyu yana huci. +

Sai da ta karasa gaban shi sannan ta tsuguna tace “Uncle Sagir me ya faru?”

Tana shirin kai hannayenta ta riko nashi hannun ne ya dago kai da karfi sai da ya ba ta tsoro, “Me ya faru kike tambayata? “K in bude kofa wa aminina har ya nemi shiga gonata shine zaki tambayen me ya faru idan baki bashi daman ya so ki ba ta yaya har hakan zai faru? wai ni matar da nake so nake ikrarin babu kamarta, itace aminina zai kalli idona yace min yana sonta?” 8

Mamaki ya kara kama Aneesa ta rike baki tana kuka ta gagara cewa komai tsabar tashin hankali me yasa Sagir zai zargeta?

Ya kwantar da kai a saman kujera yana kallon silin “Ba laifin ku bane ni na yaudari kaina da tunanin cewa zan samu macen da zata soni tsakani da Allah, na manta da asalin halin ‘ya mace na sakankance na bari innocence din ki ya yaudareni,” ya dago kanshi yana dubanta a durkushe kan kafet din “kema kina sonshi ko Aneesa?” ya tambaya cikin wata gajiyayyar murya. 2

Tambayar ta matukar girgizata ranta yayi masifar baci, ta tsinci kanta a wata bakuwar duniya da ke dauke da tsantsan duhu, ta mike tsaye tace “Ashe har zaka iya bude baki ka min wannan tambayar? A tunani na mun riga mun sa labule a wannan fage na tantamar kaunar da mukeyiwa juna. Yau uncle Sagir idan har nayi haka ba kai kadai na yaudara ba, har da ni kaina. Idan nayi haka na butulcewa ni’imar ALlah a gareni. Na zaci son da ka ke mini ya wuce haka na zaci koda duniya zasu taru a kanmu kai mai goyon bayana ne. Amma sai dai kash ka zama mai tuhumata mai zargina a lokacin da na fi bukatarka a tare dani” 3

Murmushi yayi na takaici yace “Dole ce ta sa na tuhumeki, tunda mutum daya da na fi amincewa dashi ya yaudareni, macen da na so ta yaudareni ta canza asalinta saboda wata bukatarta, na fara samun hazo yana lullube min tunanin abun da na yarda dashi da wanda ban yarda dashi ba.”

Aneesa ta kalleshi cikin zafin rai, anya wannan Sagir ne ke mata wannar maganar? Ran ta yayi baki ba abun da take gani a gabanta sai bacin rai da kunci “Don radadin abun da tsohuwar matarka tayi maka ya haddasa maka rashin yarda da ‘ya mace, sannan aminin da ka amince masa ya yaudareka wannan bai baka daman ka zargeni akan laifin da ban aikata ba, wannan yana nuna maka ka kula da zabin da kakeyi a rayuwarka. By the way, ina ma da zuciyata bata wahaltu da son ka ba, ina ma da ba kai na aminta dashi ba da yau duk bamu ga wannan rana ba saboda na san da Aadil bai tuhumeni ba da shine a matsayin da kake a yanzu sai dai kash kaddara ta riga fata!” Ba shiri Aneesa taji shimfidar mari a fuskarta, tare da wani kururuwa da Sagir ya mata yace “Get out of my room, ki bace min da gani.” 17

Bata jira ya sake maimaita buqatarsa ba ta fice daga dakin kuka takeyi wannan hawayen yana korar wani. Daki taje ta dauki mayafinta da wayarta a hannu ta dauki jakarta mai kudi a ciki ta fice daga gidan. Ta isa gate kenan sai ga motar Kamaal ya shigo gidan. Kamaal dai yaga alama Aneesa bata kula ma da shigowarshi ba don haka yayi reverse ya tsaya a gabanta.

Kamaal ya fito ya samu Aneesa “babbar yayata lafiya kuwa na ganki haka? Ina zaki je?”

Aneesa tayi saurin share hawayenta. “Lafiya zan dan fita ne”

“Fita kuma yanzu? yaya na ganki a kafa Ya Sagir din baya nan ne?”

Wani irin bakin ciki taji da ya ambaci sunan Sagir “yana ciki.”

STORY CONTINUES BELOW


Kamaal ya san dai akwai matsala don haka yace “ki shigo to na kaiki inda zaki je din”

“A’a Kamaal da ka bari nan nan kusa ne yanzu zan je.”

“Ya Sagir din ya san kin fito?”

Shiru tayi bata tanka masa ba, ganin haka yasan da walakin “ki zo muje ciki ki fada min me ya faru?”

“A’a Kamaal kai dai ka shiga ni bazan koma ba.”

“Yanzu ke ina zaki je?”

Sai da ya tambaya ma tukun tayi tunanin shin ina ta dosa? Tana da wurin zuwa a halin yanzu a garin nan? Duk wadanda ta sani a dalilin sagir ne, sai ko gidan Daddy wanda ba ko tantama ba wurin zuwanta bane a yanzu yanda taga fushin Mummy.

“Gombe zan tafi.”

Abun yaso ya bawa Kamaal dariya yace “Gombe, a hakan yanzu? ki shiga mota muje gida wurin Hajiya idan safiya tayi sai na bada mota a kaiki”

“a’a ka barshi kawai ina da kudin mota.”

“ke dai shiga muje wurin Hajiya to sai na kaiki tashan”

Ganin ya dage kuma suna ta tsaye kan titi yasa ta amince ta shiga suka tafi gidansu Sagir.

Hajiya na zaune a falon Abba sai ga Kamaal ya shigo tare da Aneesa, ta dubi Kamaal ta mayar da ganinta ga Aneesa ta san dai ba kalau ba yanda taga fuskarta kozai-kozai. “Kamaal lafiya? yaya naga Aneesa haka?”

Kamaal ya samu kujera ya zauna yace “Ato gata nan dai ki tambayeta, don ni kam tun a hanya taki ta ce min komai”

Aneesa ta zauna a kan kafet ta gaida hajiya.

“Me yake faruwa Aneesa? Sagir din baya nan ne Kamaal?”

“Tace yana nan don ban shiga cikin gidan ba daga gate muka hadu da ita.”

“To shi kenan, tashi ki je sama ki samu abinci ki ci idan kin huta zan zo muyi magana”

Aneesa ta tashi jiki ba kwari, duk Kamaal ne ya jawo mata, yanzu yaya zata fara duban hajiya ta fada mata abun da danta ya zargeta dashi?

Tana tashi Hajiya ta dubi Kamaal tace “Nemi Sagir a waya ina son nayi magana dashi, wannan ba kalau ba hakan bai taba faruwa ba, duk yanda akayi tashin hankali sukayi.”

wayar tayi ta ringing kafin ya dauka, jin muryar hajiyarsa yasa ya samu natsuwa. Amma da jin tace tana son ganin sa ya san akwai matsala don haka da wuri ya tashi ya canza shigen jikinsa ya fice daga gidan bai san ma Aneesa bata gidan ba.

Yana zuwa ya tarar da Hajiya a falonta, bai ga Aneesa ba kasancewar tana dakin Aisha.

“Sagir, me yake faruwa haka? yaya naga Aneesa da dare-daren nan? kasan cewa Kamaal a bakin titi ya ganta me yayi zafi haka?”

Ran Sagir ya kara baci dangane da lamarin Aneesa, yarinyar nan tana nema ta wuce gona da iri. “Hajiya Aneesan a bakin titi? Ni ban san ma ta fita ba, ita me tace ya faru?”

Hajiya ta dube shi da kyau ta san yana boye mata wani abu don haka tace “ba abun da ta fada tana dakin Aisha tun zuwanta banda kuka ba abun da takeyi, wannan ya tabbatar min da cewa lallai ka san me ya faru, tunda mace dai zamanka takeyi kuma bazata kada kafafu ta bar gidanta ba sai idan ta samu matsala da wanda take zaman shi, saboda haka ka daina min wasa da hankali, idan ka san kai ne silar fitar ta to tun wuri kayi maganin haka, ka lallabata ku koma. Ai hakan ba mutumcin ka bane ana ganin matarka a bakin hanya cikin dare.” A ranshi yace “of course me take dashi da zata fada miki? tunda bata da gaskiya” 3

“Hajiya ai da ta san tana da gaskiya da baku ganta a nan ba, amma tunda hakan ta zaba sai tayi zamanta har randa ta ga dama sai ta koma.” 4

Hajiya ta dubi Sagir tabbas wannan wani babban al’amari ne, saboda Sagir bayi da halayyar sa in sa da ita. Don haka bazata matsa Aneesa ta koma ba tunda har Sagir ya furta hakan.

STORY CONTINUES BELOW


“shi ke nan, Allah ya kyauta. Kaje sai Abbanka ya dawo zamu tattauna koma meye ne a ke ciki ina son dai kasan ba a yanke hukunci cikin fushi, kuma hakuri akeyi a lamarin aure. Idan da ana saurin yin hukunci ko kuma saurin fushi kan ko wani kankantar abu jinka wani aure ne zai dade? Kana tsamman da zaka tashi ka ganni da mahaifinku?”

Sagir yana ji Hajiyarsa ta gama bayani, bai ga Aneesan ba har ya bar gidan. Idan ta ga dama ta tabbata a nan he doesn’t care.

Washegari Hajiya ta sa Aisha suje gidan da Aneesa ta dauko duk abun da take bukata ta dawo nan, don hajiya ta kula kaman Aneesan tana da juna, in banda Sagir mace kam ai abun lallabi ne musamman a yanayin da take ciki yanzu. Dakin da Aneesa ta zauna a farkon aurenta da Sagir Hajiya ta sa aka gyara mata kullum za a kaita makaranta ta dawo da ita, tayi karatunta amma tunanin abun da ya faru tsakanin ta da Sagir ya hanata duk wata walwala. Haka ta debe kwanaki dai dai har biyar ba labarin Sagir, sannan a bangarenta ma bata ko kwadayin ganin shi. 2

*******

A bangaren Aadil kuwa abubuwa sun rincabe masa ya rasa abu daya da yake masa dadi, matarsa ta tafi gidansu, abokinsa ya fita hanyarsa ko sun hadu a ofis sai dai suyi maganar aiki daga nan kuma shi kenan Sagir sai yayi kamar bai taba ganin sa a titi ba ma.

Bai san yanda akayi kuskuren barin hotunan Aneesa a wayarsa ba har tsautsayi yasa Sameeha ta gani ta tuhume shi, da guda daya ne ya san irin bayanin da zai mata amma suna nan da yawa. Ya dade da sanin cewa zuciyarsa tayi garaje wurin so wa kanta abun da take haramtacciya gareta. Tun ba yau ba ya kamu da matsananciyar son Aneesa, amma sai dai ya makara saboda ya riga ya furtawa Sagir sunan ta a matasayin matar da ta dace dashi. Tsakanin sa da Sagir kuwa, ko da me yake so a duniya zai iya bari domin Sagir saboda ba abun da Sagir bai masa ba a rayuwa. Har yau baya manta musabbabin abotarsa da Sagir. 16

Shekarar su ta farko a jami’a, Aadil ya kasance wanda aka hada su daki a cikin hostel tare da Sagir. A wancan lokacin Sagir bai cika magana ba. Sabgar gabanshi ne kawai a tare dashi, a wannan dakin kuma akwai mutune uku wanda banda tunkaho da arziki da son rayuwa da shashewa ba abun da suka sa a gaba, har ma ya kasance idan har kai baka irin rayuwarsu to sai su raina ka suyi ta maka wulakanci iri-iri. A tunanin su saboda talaucin su ne yasa basu fitowa gari a dama dasu. Sagir yana shiru bai taba ce musu komai ba har dai suka fara kureshi, a taka masa katifa da takalmi a kashe wutan daki idan ya tashi karatu abubuwa kala-kala.

Shi Aadil baya cewa komai tunda ya riga ya saba haka ya tashi ko makarantar sekandire kasancewar da kyar Babar shi take hada masa na kudin makarantar ma. Watarana anyi hutu ne Sagir yayi abunda ya razana ba ‘yan block din su kadai ba hatta duka makarantar domin kuwa ranar da dalibai zasu yi hutu yayi waya yace yana son a taho masa da motocin gidan su gaba daya saboda akwai wasu abokansu da zasu tafi tare. 1

Kowa ya razana da yaji wai Sagir din wannan block din ne aka taho dauka a manyan jifajifan da ba wanda take kasa da miliyan biyar tun a lokacin. Nan ne ‘yan dakin su suka gane ashe Sagir ba kanwar lasa bane, ganin haka yasa Aadil ya tunkare shi yace “Kar ka bari su rude ka har su sa ka canza akalar rayuwarka ka gagara fuskantar abun da ya kawo ka nan.”

Sagir yaji dadin shawarar Aadil ya san kuma gaskiya ya fada don haka ya ci gaba da rayuwarsa yanda ya saba, a hankali ya zama ba a raba su da Aadil, hakan yasa ya fahimci yanayin rayuwar Aadil ta banbanta kwarai da nashi don haka ya daukewa Aadil registration sannan ya sanar wa mahaifinsa ko wani hutu shi yake mayar da Aadil gida ya kuma ba wa iyayensa abun masarufi, har suka kare karatunsu, suna gamawa Sagir ya tafi turai karo karatu amma sai da ya tabbar Aadil ma ya samu gurbin masters din shi a Najeriya kasancewar Babarsa bata da lafiya ba dama ya tsallaketa ya tafi. Hakanan duk wata jigilar asibitn babarsa Sagir ne ya dauki nauyin komai.

Yana dawowa ya bada sunanshi aka dauke shi aiki. Mutumin da baya saka kansa a gaba da komai ai mutum ne. Wannan yasa har abada Sagir yake da kima a idanun Aadil ko da ya fuskanci son Aneesa ya masa nisa ya yi kokarin yakiceta saboda duk son da yake mata yafi son Sagir da ita, bazai bari kuma ta shiga tsakaninsu ba, sai dai zuciya bata da kashi wannan bai hana shi jin kewarta ba ko kuma son ganin kyakkyawar fuskarta ba. yawanci hotunanta da yake dasu a dp din Aisha yake samu yayi saving. Rana daya da ya san ya hakura da Aneesa har abada itace ranar da Sagir yayi hatsari, yanda yaga tashin hankalin da Aneesa ta shiga ya san lalle farin cikinta na tare da Sagir. Ya sa wa ransa dangana ya hakura da ita.
4

STORY CONTINUES BELOW


*********

Kai tsaye Aadil ya samu Sameeha, bai samu matsalar fitowarta ba wannan karon kasancewar ta san Daddy yana gida sabanin lokuta hudu da ya zo a baya. Tana shigowa ta samu kujera ta zauna tare da juya masa baya. Murmushi yayi na karfin hali sannan yace “Shin zaki tuhumi zuciyata da laifin da bata san ta aikata ba? Na san na yi kuskure da ban sanar dake me nakeji ba game da Aneesa tun kafin aurenmu. Amma ke kanki kinsan ina sonki kuma shafin Aneesa wani shafi ne da ya riga ya shude a rayuwata, koda Sagir ba abokina bane bazan ci gaba da son Aneesa ba saboda ta zama matar wani, na mance da shafinta kuma ina son ki san ke ce sabuwar shafin da ke rayuwata a yanzu Sameeha, idan kika mana haka kina ga kinyi mana adalci? ki taimaka ki dawo mu fara rayuwarmu kamar yanda take sabuwa mu ci gaba da kawata ta. Give me a second chance, please”

Sameeha tayi shiru tana jin Aadil hawaye suna zuba mata, musamman da ta tuna Aneesa ta taba ce mata ko wani mutum yana bukatar dama ta biyu, kuma Daddy ya bata dama ta biyu. Tsakani da Allah ita bata san me yasa ta bar gidan shi ba, kishi ne ko fushi ko mamaki, kuma tasan a wancan lokacin abun da tayi daidaine sai dai bata bashi daman yayi mata bayanin komai ba. Kuma ta san Aneesa bazata taba son wani alhali tana da aure ba.
3

Don haka dawowar da tayi gida ya sa ta samu lokacin yin tunani game da wannan al’amari, tana son mijinta kuma ta san shima yana sonta, hakan yasa bata ba da kai ga zugar da mummy ke yi mata ba. Ta dago kai ta share hawayenta sannan tace “Naji bayaninka ina son ka bani lokaci nayi tunani”

Aadil yayi tsam sannan yace “ina ganin kaman na baki iya wannan lokacin ba kya ganin cewa muna asarar lokacin da ya dace ace muna kara fahimtar juna? kiyi hakuri ki bi mijinki dan maraya ku koma gidanku yau?”

Sameeha taji dadin kalamansa ta san kuma iya gaskiyarsa ya fada mata don haka tace “zanyi magana da su Mummy tukun”

” Shikenan, gimbiya duk yanda kikace” 2

Aadil ya bar gidan cike da farin ciki ya warware matsala daya saura daya, wanda ta fi tsauri.

Tun satin da wannan abu ya faru Sagir ya tafi Singapore dangane da wani aiki kwanan shi hudu a can, amma ya tsinci kansa da rashin jin dadin aikin, a hakikanin gaskiya ma sau da dama sai an nanata magana sau biyu ko fi kafin ya fahimci me ake nufi a dakin taron. Wannan yasa ana gama taron bai tsaya ko ina ba sai filin jirgi.

******

Da safe ta samu Hajiya a dakinta bayan sun gaisa ne tace “Hajiya daman ina son naje na duba Innata ce jiya da dare sunce min jikin ta ba dadi har ma an mayar dasu asibitin Gombe, to amma na kira wayar shi bana samun shi.”

Hajiya tayi shiru tana tunanin al’amarin Sagir ita kanta yanzu kam ya fara kaita makura, yaya za ayi matarka bata gidanka sannan kace a barta sai randa ta huce. ku fadi me ya hada ku kuma duk ya gagare ku.

“Subhaanallah, Allah ya bata lafiya. Ki shirya anjima in sha Allah sai Direba ya kaiki, amma dai kafin nan ina son yau kiyiwa Allah ki fada min wai me ya hadaki da Sagir kuke irin wannan fushi da juna?” Aneesa tayi shiru kaman yanda ta saba idan aka mata wannan tambayar “ko dai ni baki daukeni a matsayin mahaifiya bace?”

Nan da nan Aneesa tace “ba haka bane Hajiya kiyi hakuri, ni dalilina na rashin fada shine, wanda nayiwa laifin ma na ga bai ce komai ba.”

Nan dai Aneesa ta fadawa Hajiya abun da ya faru, amma ta dauke ce masa da tayi tayi da na sanin aurensa.

“kai amma yaran nan da shiririta kuke, yanzu wannan wani irin maganace? ki bari Sagir din zai zo ya sameni, kiyi tafiyarki har sai ya janye maganar da ya fada sannan ya daukeki a gidannan, kije ki dawo kar ki damu ko?”

Da wannan karfin gwiwa Aneesa ta shirga kayanta a akwati har Aisha na mata tsiya, “wannan jibgegen akwatin dai da fatan zaki dawo, kar kisa mu taho biko”

Aneesa tayi murmushi ita kadai ta san me ta shirya a zuciyarta.

Har dai ta tafi hankalin Hajiya Khadija ba a kwance ba dole Sagir ya san me yake ciki don taga alama bai dau maganar nan da muhimmanci ba.

Suna isa Gombe asibiti suka fara zuwa ta duba Innarta, a zaune a kan gadon ma ta sameta an jinginar da ita a jikin filo, ba shiri Aneesa ta fada jikin Innarta tana kuka, kuka yaki ci yaki cinyewa Mairo tace “Lafiya Uwani, meye haka ai bazaki tada hankalinki ba, marar lafiya ai addu’a zaki mata. Abunda da sauki ma anyi gwaji an gano ciwon taifod ne ke damunta. Su duk basu san Aneesa kukan tausayin Innarta da ita kanta takeyi ba. Tayi alqawari abun da ya samu Innarta bazai sameta ba, sai dai kaman hadin baki abun da ya sameta itama sak na Innarta ne. Da kyar ta samu ta share hawayenta.

“Inna yaya jikin naki?”

“Da sauki Uwani, ki daina kuka, ke da mai gidan ki kuka zo ne?”

“A’a ni kadai na taho da direba, shi yayi tafiya” ta fada saboda bata son ta tayarwa su Inna da hankali. Zuwanta Inna ta kara kwanaki hudu a asibiti sannan aka sallame su tare da rubuta musu magunguna. Aneesa ce ta bada kudin magungunan kasancewar jinyan da ta kwanta yasa Malam Habu ma kudin hannunsa sunyi kasa. Amma bazai fada ba yana ta buga-bugan nemowa. Wannan yasa Aneesa tace musu Sagir ne yace a bawa Inna. Ko tuno sunanshi tayi bakin ciki take ji bare kuma ta furta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *