SOORAJ
CHAPTER 3
Hanunta tasa da sauri ta goge hawayen daya sauƙo mata akan ƙuncinta, kitchine ta koma ta tare da cigaba da wanke wankenta…… +
RAJ
Tsaye yake agaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bango, idanuwansa wanda suka sha ruwa sukayi jajur ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa. Maganganun Abba gaba ɗaya sun gama dagula masa lissafi, ko tantama bayayi koda sun nemo zaɓinsu sun aura masa awannan karonma bazai iya jure zama da mace ba, dole zai saketa, sannan kuma dole ne zasuyi fushi dashi, ayanzu kam baya tunanin zai sake yarda alaƙa ba masa nauyin wata ƴa mace akansa, koda sau ɗayane yanason iyayenshi su fahimcesa amma kuma hakan ya gagara, kashe shower’n yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan weast ɗinsa, baidamu da yanda jikinsa ke ɗigan ruwa ba ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito, idan yace zai iya baje damuwowin dake ranshi to tabbas ƙwaƙwalwa da zuciyarsa bazasu iya ɗauka ba, kaya ya sanya ajikinsa tare da ɗaukan car key ɗinsa yafice daga cikin ɗakin, direct compound ɗin gidan ya nufa, wata baƙar 4matic ya buɗe yashiga tare dayi mata key, tun mai gadi baigama wangale gate ɗin da kyauba ya cilla hancin motarsa waje.
Tafiya yake amma gaba ɗaya hankali da tunaninsa suna wani waje daban, ababban ƙofar asibitin yayi parking, yau bakamar ko yaushe ba, don bai shigar da motar tasa ciki ba kamar yanda ya saba.
Direct office ɗin Dr.Yunus ya nufa, yana knocking aka bashi izinin shigowa, kujera yaja ya zauna tare da miƙawa Dr.Yunus hannu sukayi musabaha, cike da fari’a Dr.Yunus yace. “Yajikinnaka ina fata dai ankama waƴanda suka aikata laifin?”
“Dasauƙi!” Sooraj yafaɗa aɗan gajarce kasancewar bayason zancen yayi tsawo.
Murmushi Dr.Yunus yayi domin sarai yasan halin Sooraj sai mutum ya shekara yana masa magana baitanka ba.
Gyara zama Dr. Yunus ya sakeyi tare da cewa “Result ɗinka yana ajiye tun after 1 week” Wata ƴar drawer dake jikin table Dr.Yunus ya jawo tare da zaro wata farar envelope.
Miƙawa Sooraj yayi tare da cewa “Komai yananan daidai, nayi duk wani bincikena dazanyi Sooraj amma gaskia bangano wata sabuwar matsala ba, magungunan dana baka acan baya sune kawai zakana sha har abubuwa su daidaita!” Dr.Yunus yafaɗi haka cike dason kwantar da hankalin Sooraj.
Wani murmushin gefen baki wanda yafi kuka ciwo Sooraj yayi, shikaɗai yasan wani irin zafi zuciyarsa keyi masa awannan lokacin, karɓan takardan kawai yayi tare da sake bawa Dr. Yunus hanu sukayi musabaha, daganan yafice daga cikin office ɗin, wani irin kallon tausayi Dr.Yunus keyiwa Sooraj, sosai matsalan Sooraj ɗin ke ɗaure masa kai, iya binciken duniya sunyi shida abokan aikinsa amma sam su basu iya gano matsalan Sooraj ba, hasalima komai nasa lafiya lau yake bashi da wata tawaya a halittar jikinsa. .
Tunda yafito daga cikin office ɗin Dr.Yunus yake ganin duhu a idanuwansa, cikin cijewa ya ƙarasa wajen da motarsa take, yana shiga ya kifa kansa ajikin steering motar tare da fesar da wani breath me ɗumi, aƙalla yaɗauki kusan mintuna 9 ahaka batare dako motsi yayi ba, gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya cak.
Da ƙyar ya iya ɗago kansa, idanuwansa tamkar jan garwashin wuta haka suka koma, Envelope ɗin da Dr.Yunus ya basa ya buɗe, tare da zaro wata ƴar farar takarda dake ciki, ahankali ya warwareta tare da sauƙe idanunsa akan rubutun dake cikin takardan . Yana gama karanta abun dake cikinta ya duƙunƙuneta tare da rumtse idanunsa da ƙarfi. Laɓɓan bakinsa yaɗan ciza tare da ɗauko wata lighter ya kunna, takardan yakawo jikin lighter’n take ta kama da wuta, sauƙe glass ɗin motar yayi ƙasa tare da cilla takardan waje, take takardan ta ƙone ƙurmus, key yayiwa motarshi tare da cillata kan titi yabar wajen….
STORY CONTINUES BELOW
Ziyada kuwa tana kammala wanke wankenta, ta shige ɗaki bata kuma sake fitowa ba, duk da cewa zaman ɗakin bawani daɗi yakeyi mata ba amma kasancewar bata da abunyi yasanya ta gwammacewa kanta zama waje ɗaya.
***
After 3 days.
Tunda Abba yayiwa Sooraj maganan aure sai ya zamana Sooraj baya zaman gida kwata kwata, idan yafita tun safe bazai dawoba sai after Sallan Isha, kafunnan Abba yajima da dawowa suna tare da Ummu, sam bayason Abba yasake ɗago masa da wannan maganan domin magana ta gaskiya aure agareshi bamaiyiwuwa bane.
Itakuwa Ziyada adaddafe haka take rayuwar cikin gidan duk dama Ummu na sake mata amma bawai wani sabawa sukayiba shiasa takejin kanta atakure, kallone kaɗai abun dake ɗebe mata kewa ayanzu, daga gefe guda kuwa tana lissafin hutunsu wanda yanzu saura musu 1 week sukoma makaranta, har Allah Allah take lokacin yazo, duk da batasan menene makomarta a wajensu ba, batasaniba ko zasu koreta ko zasu barta…
5:15 pm.
Kwance yake akan makeken bed ɗinsa wanda yaji bedsheet na alfarma, dagashi sai long pencil jeans yayinda earpiece ke saƙale a kunnuwansa, gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗinsa, Samsung Galaxy S20 ɗinsa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira. Saida wayar takusa katsewa sannan ya zare earpiece ɗin dake kunnensa, ganin sunan Abba nayawo akan screen ɗin wayar yasanyashi ɗaga wayar da gaggawa, yana kara wayar akan kunnensa. Abba dake tsaye cikin falonsa jin Sooraj ɗin ya ɗaga wayan yasanyashi cewa.
“Kazo kasameni yanzu afalona!” ƙit yakashe wayan batare dayaji me Sooraj ɗin zaice ba.
Ahankali Sooraj yasauƙe wayan daga kunnensa tare da sauƙe ajiyar zuciya, rufe laptop ɗin yayi tare da zuro ƙafafunsa ƙasa, wata bruberry button shirt fara ya ɗauka ya sanya ajikinsa, bedroom slippers yasanya aƙafansa kana yafice daga cikin ɗakin. Tun da ya doshi falon Abban yaji zuciyarsa na bugawa, sam baison sakejin wani abu dazai ɗaga hankalinsa.
Zaune yasamu Abba akan kujera yana duba jaridan daily trust dake riƙe ahanunsa, zama yayi akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunsa. “Sannu da hutawa” yace da Abba cikin nutsuwa.
Gyara zama Abba yayi tare da aje jaridan dake hanunsa. Kallon Sooraj ɗin yayi sosai tare da ɗanyin gyaran murya. “Ina ka ajiye maganan da mukayi dakai? Shin kasamo wacce kakeso ɗin kokuwa?” Abba yatambaya babu alaman wasa akan fuskarsa.
Ɗan shiru Sooraj yayi tare da haɗiye wani yawu me ɗaci da lokaci guda ya tsaya masa amaƙoshi. “Kayi haƙuri Abba, amma Bansamuba!” yafaɗi haka cikin raunanniyar murya.
“Shikenan babu ma buƙatar kasamo da kanka, Na auramaka ƴaƴan abokaina basau ɗaya ba basau biyu ba kana sakosu babu wani babban dalili, to ayanzuma zan sake ɗaurama aure da ƴar abokina Alhaji Naseer, ina tabbatarmaka da cewa wannan shine naƙarshe, sannan kuma koda wasa idan ka sake kayi gigin sakinta wallahi! wallahi!! babuni babu kai, zan janye hanuna daga duk wani lamarinka, ai kai ba ƙaramin yaro bane kasan daidai kakumasan ba daidai ba, wannan umarni nake baka saika shirya inaso acikin satinnan kaje ka ganta, sannan kuma tana shekaran ƙarshe na kammala degree ɗinta, saboda haka da zaran tagama za a ɗaura muku aure, tashi kabani waje!!!” Abba yaƙare maganar murya akausashe.
Sooraj dake zaune wani irin jiri ne ke ɗibansa, tamkar sauƙan garwashi ajiki haka yaji sauƙan maganganun abba acikin kunnuwansa, take idanunsa suka sauya kala daga farare zuwa jajaye, wani irin ɗaci yakeji amaƙoshinsa, da ƙyar ya iya tashi yanufi hanyar fita daga falon, da kallo Abba yabisa har ya ɓacewa ganinsa, shikam har acikin ransa yasoma zargin ko aljana ce ta shafi Sooraj ko kuma asiri aka mishi, saidai koma menene shidai yana kan ra’ayinsa na dole Sooraj sai yayi aure, domin aganinsa idan da akwai mace akusa dashi to ko bakomai zata rage masa kaɗaici.
Sooraj kuwa koda yabar part ɗin Abba kai tsaye garden yanufa, wani irin ƙunci yakeji azuciyarsa, jiyake kamar yaita tsala ihu kozai samu relief, zama yayi akan wata beautiful chair tare da lumshe idanunsa, wani irin zafi zuciyarsa keyi masa ahankali yake ambaton sunan Allah acikin ransa lokaci guda yaɗanji zuciyarsa tayi sanyi, sake lafewa acikin kujeran yayi tare da maida idanunsa ya kulle tamkar wanda yake bacci.
Ziyada ce ta fito daga part ɗinsu, hanunta ɗauke yake da wani bowl me kyau, sanye take cikin riga da wando na Indian mai kama da pakistan, dayake kalan kayan blue ne shiyasa suka mata kyau sun karɓi white skin ɗinta sosai, ɗan kwalin kayan ta yafa daga kanta zuwa ƙirjinta. Kai tsaye take tafiya zuwa Inda Ummu tace taje ta ciro mata mango, zatayi mango juice. Tana jefa ƙafanta acikin garden ɗin wani Irin sassanyan ƙamshi yadaki hancinta, wani irin ni’ima ne ke tashi acikin garden ɗin, sanyine me daɗi yake ratsa ko ina najikinta, baki buɗe haka take kallon komai dake cikin garden ɗin sosai wajen ya ƙawatu, ƙamshin kayan itatuwane kawai ke tashi. Cikin nutsuwa take tsinkan jajayen mango ɗin. Ahankali ya ware idanunsa ya sauƙesu akanta, lumshe idanunsa yayi tare da sake buɗewa, duk da cewa bayanta kawai yake iya gani amma yanayin yanda take motsa jikinta yasanyashi kasa ɗauke idanunsa akanta, tana kammala tsinkan mango’n tajuya daniyan barin wajen, batare data kulaba tayi tuntuɓe da wani ɗan itace take bowl ɗin dake hanunta ya faɗi mangon ya watse. Bisa tsautsayi itama ta faɗi akan guiwowinta, rumtse idanunta tayi cike dajin zafi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da miƙewa tsaye bowl ɗin ta ɗauka tashiga bin Mangon da ya watse tana ɗauka da ɗaɗɗaya, tana maidawa cikin bowl, kanta aƙasa yake hakan yasa sam bata lura da akwai mutum awajen ba. Batare data luraba taji tataka wani abu tamkar ƙafan mutum, tana ɗagowa sukayi ido huɗu dashi, wani irin faɗuwa gabanta yayi take ƙirjinta yashiga dukan uku uku, ɗago idanunta dake ƙasa tayi take suka faɗa acikin nasa idanun, wani irin abu taji, wanda yataso tundaga ɗan yatsan ƙafarta har zuwa kanta da jijiyoyin jikinta. Pink lips ɗintane suka soma rawa da’alama magana takesonyi amma ya maƙale, ahankali yayi ƙasa da rikitattun idanunsa, sauƙesu yayi akan small lips ɗinta wanda suketa ɓari sukaɗai.Kauda idanunsa gefe yayi tare da ɗauke duk wata annurin dake kan fuskarsa. Ziyada dake tsaye tsaye still akansa cikin wata sarƙaƙƙiyar murya tace.
“Kayi haƙuri….ban…kula bane!” +
Bai juyo ya kalleta bama bare tasa ran zai tanka mata, saboda haka ta ɗanja da baya tare da nufar hanyar fita da ga garden ɗin, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi wasu ruwan hawayene suka cika idanunta, itakam batasan me yasa tazama wawiya har haka ba, sam batasan meyasa dazaran abu yashiga tsakaninta dashi take saurin kuka ba, da wannan tunanin ta isa ga babban ƙofan da zai sadata da falon Ummu, hannayenta tasanya ta share hawayen dake kan fuskarta, sannan ta buɗe ƙofar tashiga.
Shikuwa Sooraj tunda yakawar da kansa gefe baisake koda ƙwaƙƙwaran motsi ba, lumshe beautiful eyes ɗinsa yayi tare da maida kansa jikin kujeran, daddaɗan iskan dake hurawa acikin garden dinne ke ratsa ko ina na jikinsa, hakan yasa yaji zuciyarsa ta ƙarayin sanyi.
Zieyada kuwa atare da Ummu suka haɗa Mango juice, babban jug ɗin da mango juice ɗin ke ciki Ummu ta bata tace tasanya a fridge, koda tasanya mango juice ɗin acikin fridge kaitsaye ɗakinta ta wuce, faɗawa kan gado tayi tare da lumshe manya manyan idanunta, da sauri ta ware idanunta tare da tashi zaune, hannayenta tasanya duka biyu ta murza eyes ɗinta, wani irin ƙaton ajiyar zuciya ta sauƙe alokacin da ta fuskanci cewa gizo ne idanunta ke mata, bawai shiɗin bane, wani irin yaar taji ajikinta sakamakon tunowa da cikin kyawawan idanuwansa da tayi, tabbas idanunsa kaɗai sun isa rikita duk wata ƴa mace, matuƙar zata kallesu, wani irin sirrin kyau ne ke ƙunshe acikin idanunnasa, aduk randa tsautsayi yasanyata kallon cikin idanunsa ji take kamar zata suma, wasu abubuwane ke yawo ajikinta yayinda takejin kanta kamar wata wawiya, eye balls ɗinsa tamkar magnet ne acikin nata idanun dake matuƙar zautar da ita, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta wanda bata san ma tayi ba, sakamakon tunawa da kyakkyawar fuskarsa da tayi.
“Yana da kyau sosai!!”
Tafaɗa abayyane cikin wata irin murya me sanyi. “Ko abacci ma kyau yakeyi, shi komai nasa me kyau ne!!!” Tasake faɗa tana me murza ƴan yatsun hanunta, itakanta batasan maganganun da take faɗa suna fitowa fili ba, gaba ɗaya ashagalce take, fararen ƙafafunta ta zuro ƙasa tare da tashi tsaye, direct wajen window ta nufa, ɗan yaye labulen window’n tayi tare da soma bin ko ina dake cikin compound ɗin gidan da kallo, idanunta ta tsayar asetin ƙofar shiga garden ɗin, dai dai lokacin yafito daga cikin garden ɗin hanunsa riƙe da wani green apple, tafiya yake kansa tsaye yayinda skin ɗinsa keta walwali kallo ɗaya zaka masa kasan hutu da kudi sun zauna masa, tundaga wajen da take tana iya hango yanda tarin suman dake kansa ke sheƙi, gashi ya kwanta luf luf tamkar sajen dake kwance akan fuskarsa, bata taɓa ganin wani irinsa ba, shi na dabanne ko acikin maza, hannunta takai ta dafa glass din dake jikin window’n, fuskarsa kawai take kallo, akullum tana mamakin yanda yake rayuwarsa babu annuri akan fuskarsa, koda yaushe haka yake baka taɓa ganin dariyarsa, kafun kaji maganarsa ma wahala ne, shi komai nasa is difference, Maganan aurensa ne ya faɗo mata lokaci guda ta marerece fuska tare da ɗan taɓe soft lips ɗinta. “Wace zata aureshi?” tambayar da tayiwa kanta kenan azuci, amma sam batasani ba har sautin maganan yafito fili. Soft lip ɗinta na ƙasa taɗan tsotsa tare da soma karyar da yatsun hanunta, idanunta ne sukayi raurau kamar wacce zatayi kuka, ɗago kanta tasakeyi da niyan kallonsa, amma kuma saitaga kome kama dashi babu awajen, sake labulen tayi tare dakomawa kan gado ta zauna. “Mene nawa? Meyasa nake tambayar kaina abubuwan da basu shafeni ba? No wannan ba halina bane kawai sharrin zuciya ne!” Tafaɗi haka cike da tuhuman kanta, domin sam tasan tunanin rayuwarsa ba huruminta bane. Remote taɗauka tare da kunna ɗan madaidaicin tv plasman dake ɗakin, tashar MBC Bollywood takamo inda tasamu suna nuna film ɗin Sushant Singh da Kriti Sanon wato Raabta, yanayin film din sosai yaɗauki hankalinta musamman yanda taga suna wata kalan rayuwa a daji, sam saita manta da tunanin komai ta bada hankalinta ga kallo.
STORY CONTINUES BELOW
_RAJ_
Koda yabar garden direct babban falon gidan ya nufa, babu kowa afalon kamar koda yaushe hakan yasa kaitsaye yawuce ɓangarensa, yana shiga ya murzawa ƙofarsa key, gaba ɗaya zaman gidan ya ishesa, ayanzu bayason damuwar kowa ta dameshi, saboda haka yaciro wani tablet dake jikin bedside drawer ɗinshi, ɓare maganin yayi ya jefa abakinsa sannan yabi da ruwa, toilet ya wuce ya ɗauro alwala domin alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba, direct masallaci ya wuce, tunda yayi Sallah Magriba bai tashi ba har saida ya sallame isha yayi azkar, yana fitowa daga cikin masallacin yasoma jin jiri na ƙoƙarin kadashi, lokaci guda kansa yayi masa nauyi, idanunsa sukayi luhu luhu, cikin dauriya yake tafiya ahaka har ya isa gida, yana shiga cikin bedroom ɗinsa ya soma rage kayan jikinsa, dagashi sai long jeans haka ya faɗa kan royal bed ɗinsa tare da jawo pillow ya ɗaura kansa akai, wani irin duhu yake gani a idanunsa, har takai ma da ƙyar yake iya buɗesu mintuna kaɗan wani irin nannauyan bacci ya ɗaukesa, daga yanayin yanda yake baccin idan ka gani kasan bana lafiya ba….
Washegari.
Tun da safe Ummu da Ziyadah keta ƙoƙarin haɗa breakfast a kitchine kasancewar yau Abba zai koma KD, jirgin ƙarfe 9 zaibi shiasa Ummu keta ɗawainiya tanason yayi break kafun yatafi, don ita tace dawowarta ba yanzuba saboda Sooraj. Ba abun da Abba yakeso kamar Tuwo hakan yasa yauma Ummu tuwo takeyi masa da moringa soup wanda yaji cow meat da biscuit bone, ƙarfe takwas daidai suka kammala gaba ɗaya aikinsu, Ziyadah ce ta jere komai akan dinning table, Koda Ummu tagama serving ɗin Abba kujera taja ta zauna, har Abba yafara cin abincin ya ɗago ya kalli Ziyada wacce tayi shiru kamar me tunani. “Jeki ƙiramin yayanki” Abba yafaɗa yana me duban tsadadden agogon dake ɗaure a hanunsa, cike da ladabi tamiƙe tare da nufar inda zai sadata da ɗakinsa, duk da cewa ƙirjinta dukan uku uku yake, amma haka ta daure, tana tura kanta acikin corridor ɗin da direct zai kaika ɗakinsa ta shaƙi daddaɗan ƙamshinsa wanda yake matuƙar hautsina tunaninta, wani irin sanyi taji yana busata cikin sanyin jiki taƙarasa jikin ƙofar ɗakinnasa, hanunta na rawa tayi knocking amma shiru ba’a amsa taba, cike da tsoro tasakeyin wani knocking ɗin nanma shiru babu amsa, ɗan jim tayi tare da juyawa zata koma, tunani tayi idan takoma me zata faɗawa Abba tace tayi knocking ba a buɗeba ko me? hakan yasa tayi karambani’n murɗa handle ɗin ƙofar, kamar da wasa kuwa taji ƙofan ta buɗe, wani daddaɗan ƙamshi tare da sanyin AC ne suka daki fuskarta har saida ta lumshe idanunta. Ahankali taɗan kutsa kanta cikin ɗakin, kwance yake akan bed yayi irin kwanciyarnan ta ruf da ciki, dagashi sai dogon wando gaba ɗaya gadon a hargitse yake tamkar wanda akayi kokuwa akansa, kallonsa tayi tundaga ƙasa har sama, gaba ɗaya kwanciyanma baiyita a dai dai ba, domin kusan rabin ƙafafunsa suna lilo suba a sama ba suba a ƙasa ba, gangarjikinsa ne kawai ke kan gadon, idanunta ne suka sauƙa akan bayansa inda fresh white skin ɗinsa ke shining yana fidda ƙyallin zufa, mamakine yakamata ganin jikinsa na fidda gumi, domin kuwa sanyin ac ne keta tashi acikin ɗakin, hatta tiles ɗin dake malale aƙasan ɗakin yaɗauki sanyi sosai, sam takasa sanin bacci yake ko kuwa idanunsa biu, cikin yanayi naɗan tsoro ta ɗan tako zuwa tsakiyan ɗakin, muryarta akarye tace “Yaa…” kasa ƙarasawa tayi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da rumtse idanunta, gaba ɗaya jarumtarta ta tattaro tace “Ya–yah!” Jin shiru bai amsa ba yasanya tace “Dama Abbane yace naƙiraka!” shima dai shiru babu amsa hakan yasa taɗan matsa kusa dashi, jin zuciarta take kamar zata fashe saboda fargaba, da ace zai juyo ya kalleta alokacin to tabbas abu me sauƙine ta sume masa awajen. “Ya–Yah katashi!” Ta sake faɗa tana ɗan leƙa fuskarsa, domin yanzukam taga alamun cewa bacci yakeyi. Ko motsi baiyiba balle tasaran zai bude idanunsa har yatashi kamar yanda take ɓuƙata, cike da karanbani taɗan sanya hanu ta bugi katifan da yake kai, tun tana ɗan bugawa ahankali harta gaji taɗan buga da ƙarfi, still ko motsawa baiyi ba, hakan yasa tasa hanu tashiga jan bedsheet ɗin dayake kai cikin shagwaɓan da batasan ta iyaba tace.
“Please Ya–yah wake up!” cikin bazata taga ya mirgino tare da juyowa hartana iya kallon fuskarsa saidai kuma bai buɗe idanunsa ba, da sauri taɗauke idanunta daga kan faffaɗan chest ɗinshi, cike da ƙosawa taɗan bubbuga ƙafafunta aƙasa murya agajiye tace “Nidai dan Allah katashi aikoni fa akayi!” Bawai baitashi bane duk abubuwan da takeyi masa yana jinsune tamkar amafarki, sam ƙarfin maganin baccin da yasha baigama sakeshi ba, ko sallan asuba daƙyar ya iya tashi yayi nanma agida yayi baije masjid ba, ƙasa ƙasa yaɗan buɗe sexy eyes ɗinshi wanda sukayi masa matuƙar nauyi, dishi dishi haka yake ganinta hakan yasa ya maida idanunsa ya kulle, sam batama lura da cewar ya ɗan buɗe idanunsa ba, blanket ɗin dayake kai taja da ƙarfi waiko zai tashi amma sam ko sake motsawa baiyi ba, hawayene suka cika idanunta sai kawai ta juya tabar masa ɗakin. Tana shigowa cikin falon tasamu Abba da Ummu tsaye harsun kammala cin abincinsu. “Ya haka naganki ke ɗaya ina Sooraj ɗin?” Ummu ta tambaya tana me ƙarewa Ziyada’n kallo, domin kuwa baƙaramin jimawa tayi aɗakin Sooraj ɗin ba.
STORY CONTINUES BELOW
Sunkuyar dakai ƙasa tayi cikin muryarta me sanyi tace. “Bacci yakeyi, tun ɗazu nake tashinsa kuma baitashi ba!”
“Bacci?” Ummu ta tambaya cike da mamaki.
Kai Ziyada ta ɗaga mata alamar “Eh”
“Badamuwa ku barshi idan yatashi zamuyi waya, yanzuma haka nakusa makara!” Abba yafaɗi haka yana me nufar hanyar barin falon, Ummu ce ta rufa masa baya, ita kuwa Ziyada ɗakinta ta wuce domin kuwa lokacin da MBC Bollywood zasu fara haska series ɗin Ishqmeinmarjawan *(حب خادع)* ya kusa kuma bataso tayi missing saboda sosai series ɗin keyi mata daɗi.
11:00 am daidai ya soma ware idanunsa ahankali har ya buɗesu duka, gani yayi kamar ɗakin na juya masa hakan yasa ya maida idanunsa ya rufe, mintuna uku tsakani yasake buɗewa, yanzu kam daidai yake ganin komai, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi wani iri tamkar anyi masa duka, hannunsa yakai ya shafa tulin sumar dake kansa wanda yasha askin afro, ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da miƙewa tsaye, hannu yasanya ya zuge zip ɗin wandon dake jikinsa, yana tafiya haka yacire wandon sannan ya buɗe wata ƴar glass drawer sabon white colour bathrobe na maza ya ciro ya sanya ajikinsa, direct bathroom ya wuce, wanka yayi sannan ya haɗa da brush, yana fitowa ya jona handryer, dashi yayi amfani wajen busar da lallausan gashin kansa, sama sama yashafa mai ajikinsa, wani oil and body perfume me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa. Kasancewar yau Jumma’a yasanya shigar da zaiyi yauɗin ta da bance, duk da cewa shi baiwani damu da manyan kayaba amma time to time yana ɗan sanyawa, wata haɗaɗɗiyar getziner blue colour wacce kuɗinta ya haurawa 40k ya zaro daga cikin tarin kayansa wanda yawansu basu faɗuwa, wani haɗaɗɗen half cover shoe me kalan blue wanda akawa samansa ado da ɗan ratsi ratsin golding ash ya zaro daga ma adanan takalmansa, takalmine me kyaun gaske wanda aka sanya kuɗaɗe wajen sayansa, Hulan daya zaro ma ta musammance itama ajikinta akwai ratsi ratsin golding ash da blue, Saida yagama kimtsa kansa cikin getziner’n wacce tasha ɗinkin half jumper, sosai yayi wani irin kyau me ɗaukar hankali, takalma ya zura aƙafafunsa sannan ya soma ƙoƙarin ɗaura agogon sa na companyn Gucci me tsadan gaske, yana kammalawa ya sanya hula akansa, baƙaramin kyau Sooraj yayiba acikin wannan shigan, wani irin ɗaukar hankali kwalliyartasa keyi, ga sajensa daya kwanta akan fuskarsa, juyawa yayi yaɗan kalli mirror, shikansa baƙaramin kyau yaga yayiwa kansa ba, musamman yanda kwarjininsa yasake bayyana afili, sosai ya fito a cikakken Namiji wanda ya amsa sunansa, turarukansa ya ɗauka ya feshe jikinsa da su take ɗakin ya gauraye da sassayan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa, wayarsa yaɗauka yasanya acikin aljihunsa tare da ɗaukan key ɗin Black Range rover car ɗinsa, cikin takunsa me ɗauke hankali yake tafiya Iya kyau yayishi har ya gaji (Team RajZiyada please kuyi imagine yanda Sooraj ɗinku ya haɗe.lol) 1
Ahankali take saƙƙowa daga kan step ɗin dake cikin falon, Plate ɗin da taci abincine riƙe ahanunta tafito daniyar zata kaisa kitchine, ƙamshin dayake kashe mata jiki yake kuma sanyata acikin wani irin yanayi shine yafara dukan hancinta lokaci guda ya gauraya da numfashinta, saboda tsabar daɗin ƙamshin batasan sanda ta lumshe kyawawan idanunta ba, tana buɗesu kuwa idanunta suka sauƙa akan zallan kyawu da kwarjinin dake dosowa cikin falon, wani irin dokawa taji ƙirjinta yayi, take jikinta yasoma karkarwa kamar maijin sanyi batare data kulaba tayi missing step ɗaya take tatafi zata faɗi da sauri tariƙe ƙarfen dake gefen matattakalan plate ɗin hanunta kuwa faɗuwa yayi dayake plate ɗin irin na cikin gift set ɗinnan ne tassss haka ƙaran fashewarsa ya cika falon, jin ƙaran fashewan abu abayansa yasanya shi juyowa, ido huɗu sukayi shida ida, kallon yanda plate ɗin ya tarwatse awajen yayi, baiko sake kallon gefen da take ba yasakai yafice daga cikin falon yana gyara zaman agogonshi, ita kuwa Ziyada tamkar wacce aka dasa haka ta kasa motsa koda ɗan yatsan ƙafanta ne, wani irin ƙarya idanunta ke mata don har yanzu gani take tamkar yana wajen. 1
“Zieyadah!”
Ƙiran sunanta da Ummu tayi shiyayi sanadiyar sauƙar da idanunta ƙasa murya asanyaye tace “Na’am”
Kallon plate ɗin daya tarwatse aƙasa Ummu tayi cikin ɗan mamaki tace.
“Ya akayi haka ta faru?”
“Umm dama bankula bane shine yafaɗi!” Ziyada tafaɗa tana me ƙoƙarin maida ƙwallan dake cikin idanunta.
“Inadai baijimiki ciwo ba?” Ummu ta tambayeta cike da kulawa.
“Eh!” tasake faɗa murya araunane.
“Shikenan to kidai kula kada yamiki illa, ni zan fita bazan jimaba zan dawo ki kula sosai” Ummu tafaɗa tana me gyara zaman gyalen dake jikinta.
“Adawo lafiya” cewar Ziyadah tana me ɗan satan kallon Ummu wacce tasha ado da gwala gwalai masu tsadan gaske, itakam da badon ɗan zaman da tayi acikinsu ba to tabbas da zatace ba Ummu bace ta haifi Sooraj domin sam jikin Ummu bainuna hakan ba zallan kudi da jindaɗi haɗi da wayewa kawai jikin Ummu ya nuna.
Haka Zieyada ta gyara wajen amma gaba ɗaya tunaninta yana wani waje daban, daga wani ɓangare na zuciyarta kuwa daɗi takeji ranan monday zasu koma makaranta.
Sooraj kuwa yana fita haɗaɗɗiyar car ɗinsa ya shiga tare da bata wuta, kai tsaye Central Mosque ya nufa domin samun sallan jumma’a, koda aka idar da sallan daga masallacin direct JABI LAKE yanufa don sunyi da Mas’oud zasu haɗu acan.Inda yake zaune wani secret wajene me kyau da burgewa, wajen tamkar garden haka yake domin anƙawatasa da korayen furanni masu sanyin ƙamshi.
Zaune yake akan wata haɗaɗɗiyar chair wanda aka ƙawata tsakiyanta da wani haɗaɗɗen table me kyau, drinks ne kala kala ke jere asaman table ɗin, gefe dashi Mas’oud ne ke sipping coconut juice, yayinda Sooraj ke aikin latsa wayarsa, azahirin gaskia idan kaga yanda gaba ɗaya attention dinsa ke kan wayan zakayi tunanin wani abu me amfani yake aiwatarwa, saɓanin haka kuwa kwata kwata hankalinsa ba ga wayar yake ba, idanunsa ne kawai ke kan wayan amma gaba ɗaya tunaninsa yayi nisa izuwa wani ɓangare na daban, duk abun dayake Mas’oud na kula dashi, ɗan aje cup ɗin coconut juice ɗin yayi tare da duban Sooraj… 2
“Bazaka taɓa daina sakanka adamuwa ba matuƙar bazaka fito ka faɗa mana damuwarka ba, haka kuma bazaka warke daga ciwon dake damun zuciyarka ba matuƙar ba zaka amayar da abun dake cikinta ba, har yaushene zakana ɓoye matsalanka RAJ? taya kake tunanin zaka samu sassauci da kuma nutsuwar zuciya bayan bakanemi hakan ba? shin ni bankai na zama abokin da zaisan matsalarka bane RAJ? tun muna ƙanana muke abota me yasa har yanzu bankai jigon dayakai sanin sirrinka ba?” Duka waƴannan tambayoyin Mas’oud yayiwa Sooraj alokaci ɗaya fuskarsa ɗauke da damuwa.
Ɗan numfasawa Sooraj yayi tare da ɗago kansa, ɗan kallon Mas’oud yayi sannan ya kau da kansa gefe, lips ɗinsa ya ciza tare dayin wani shu’umin murmushi, wanda shikaɗai yasan ma’anarsa, cikin husky voice dinsa yace. “Babu wani wanda zai fahimci matsalata Mas’oud, idan nafaɗa maka matsalata ba lallai ka yarda ba, idan nace maka bansan waneneni ba nasan bazaka taɓa yarda ba, wannan dalilin shiasa banason nayi sharing damuwata da kowa, saboda damuwata damuwata ce ni kaɗai!” cikin wani irin yanayi ya ƙare maganar tare da haɗiyan wani saliva me ɗaci da ya tsaya a maƙoshinsa.
Cike da mamaki haɗi da rashin fahimta Mas’oud yace “Banfahimci inda kalamanka suka dosa ba Sooraj, me hakan yake nufi?”
“Aure ne banaso Mas’oud, sam banason zama da kowace mace, nafison nayi rayuwata ahaka” ɗan tsagaitawa da maganan yayi tare da kallon kansa, daɗan ƙarfi ya cije laɓɓan bakinsa kana yaci gaba da cewa “Bazan taɓayiwa wata mace amfani amatsayin namiji ba, niba kamarka bane bakuma kamar sauran maza bane, inada rauni Mas’oud inada rauni wanda yake barazanar durƙushewar rayuwata, ita ƙaddara tana iya zuwa wa bawa aduk yanda baizata ba, ta ɓangarena haka tawa ƙaddaran take, amma banajin akwai wata wacce zata rayu dani ahaka, banajin zanyi wani farinciki…. ” Kasa ƙarasa maganan yayi sakamakon wani irin nauyi dayaji ƙirjinsa yayi, bada kowani lokaci yacika yin magana me tsawoba, hakan yasa yanzu yakejin kansa tamkar zai faɗo ƙasa, yayinda yakejin tamkar ana hura masa wuta acikin ƙirjinsa. Bottle water Mas’oud ya miƙo masa, babu musu ya amsa bai aje bottle water’n ba har saida ya tabbatar da babu wani sauran ruwa acikin goran, wani irin ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe, ɗago idanunsa da suka soma rikiɗewa daga farare zuwa jajaye yayi ya kalli Mas’oud daya kafesa da idanu, wani ɗan murmushi yayi tare da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan fuskarsa.
”Zan tafi, kada ka manta ranan monday muna da meeting” yanakaiwa nan azancensa ya miƙe tsaye kota bakin Mas’oud bai tsaya jiba yayi gaba, binsa Mas’oud yayi da kallo har ya ɓacewa ganinsa, wani irin iska me zafi Mas’oud ya fesar tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa, sai ayanzu brain ɗinsa ke ƙoƙarin harhaɗo masa matsalolin Sooraj, batun yauba ya kamata ace yagano menene matsalan, tunanine barkatai suka shigo cikin brain ɗinsa, wasu abubuwa daya tuno da kuma maganganun da sooraj yafaɗa masa yanzu sune suka taimaka wajen kawo masa haske daga duhun daya shiga, wani irin faɗuwa yaji gabansa yayi yayinda bugun numfashinsa ya soma fita da sauri sauri, abayyane ya furta.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un!!” kansa ya kifa ajikin table ɗin, take yaji ruwan hawaye naƙoƙarin cika idanunsa, da sauri ya yi ƙoƙarin maidasu, car key dinsa ya ɗauka, haka ya bar wajen jiki babu ƙwari.
STORY CONTINUES BELOW
Sooraj kuwa tafiya kaɗan yayi ya gangara gefen titi tare da yin parking din motar, kansa yakifa akan steering motar tamkar me bacci, aƙalla yaɗauki sama da 30 minute awajen har saida yajisa ya fara zama normal sannan yasake ta da motar ya cillata kan titi.
***
Monday.
Kamar yanda duk wani ma’aikaci da student’s sukasani Monday ranace me mahimmanci agaresu, sannan kuma ranace da ko wani ɗalibi yakewa kansa shirin makaranta na musamman kasancewar ansha hutu harna tsawon kwana biu.
Ɓangaren Ziyada ma hakance takasance domin kuwa yau zasu koma makaranta inda zasu tafi S.S.2
Tun ƙarfe 5 da ta tashi tayi sallan asuba bata yarda takoma bacci ba, ƙarfe shida da rabi daidai ta shiga toilet donyin wanka.
Wanka da brush tayi sannan ta fito ɗaure da towel ajikinta, zama tayi agaban mirror tare da ɗaukan body lotion ɗinta ta shiga shafawa ajikinta, normal green tea powder ta shafa akan fuskarta tare da goga wani man leɓe me kalan pitch, eye black pencil taɗauka tagoga acikin idanunta, take idanunnata suka ƙara bayyana kyawu da girmansu, tashi tayi daga gaban mirror’n tare da buɗe drawer tazaro gogaggun uniform ɗinta, tsab tashirya kanta cikin riga da wando na uniform ɗinnata wanda yake matuƙar amsar jikinta, zama tayi akan bed tare da ɗaukan white socks ɗinta ta zura a ƙafafunta, dogon gashin kanta ta kanannade tare da kamasa da ribbom, ɗan madaidaicin hijab ɗinta ta sanya, ƙarasawa gaban mirror tayi tare da duban kyakkyawar fuskarta, ita kanta tasan tayi mugun sauyawa wani irin haske tare da kyau ne suke sake bayyana atattare da ita akullum kwanan duniya, sau da dama idan ta dubi kanta amadubi takan ga kamar ba itace Ziyadan ƙauye ba, kamar sauyata akayi, musamman ma yanzu da hips ɗinta suka ƙara cikowa shape ɗinsu yazama abun ɗaukar hankali, shiyasa bata taɓa yarda ta zauna haka batare data rufe jikinta ba, ita kanta yanzu tasan cewa cikar ƴan matancinta da bai bayyana ba ada, shine yake bayyana yanzu, domin kuwa ayanzu babu wani abu daya rage na ƴanmatanci ajikinta da baifito ba, saidai kuma ita kaɗaice tasan haka kasancewar bata yarda kayan da take sawa su nuna hakan.
Tana kammala kimtsa kanta tajawo ƙatuwar school bag ɗinta ta aza akafaɗanta, har wani sanyi takeji aranta yau zataje taga ƙawayenta Nasmah da Shukrah sosai take kewarsu.
7:15 am Ahankali take sauƙowa daga kan step ɗin yayinda ta kanannaɗe hannayenta acikin hijabinta.
Ummu ce zaune acikin katafaren falon, laptop na companyn apple ne aje agabanta da alama wani aiki takeyi, kasancewar har da wani ɗan madaidaicin farin glass dake sanye a idanunta.
Karasowa cikin falon Ziyada tayi cike da ladabi tarusuna tare da cewa. “Barka da da safiya Ummu Ina kwana!”
Juyowa Ummu tayi fuskarta ɗauke da murmushi da “Lafiya” ta amsa mata sannan taƙara da cewa
“Har kinshirya da wuri haka?”
Murmushi tayi tare da ɗan kaɗa kanta alamar “Eh”
Agogo Ummu takalla taga babu wani sauran time hakan yasa tace da Ziyada ta ɗauki food flask ta sanya abinci aciki tatafi dashi, hakan kuwa Ziyada tayi, koda tazo fita daga cikin falon tsaida ita Ummu tayi ta bata 500 tace tasaya chocolate, cike da jin nauyi Ziyada ta girgiza kanta alamar bazata amsa ba.
Murmushi Ummu tayi ta tura mata kuɗin acikin jakanta sannan tahaura sama. Fitowa tayi daga cikin falon tana ƙara gyara zaman school bag ɗinta wanda yake rataye kan kafaɗanta. Kamalu driver ta tarar tsaye ajikin mota yana jiranta, tafiya ta cigaba dayi tana me gyara igiyan jakar makarantarta. Kansa tsaye yake tafiya yana me ƙoƙarin maida wayarsa daya amsa ƙira yanzu cikin aljihun wandonsa, babu wanda yakula da wani acikinsu, sam bata ankaraba saiji tayi ta buge mutum, kafun ta gama daidaita nutsuwarta ma tuni fitinannen ƙamshinsa ya gauraya da numfashinta, aɗan daburce taja baya, chest ɗinsa daidai saitin inda kanta ya buga ya ɗan riƙe, bakinta na rawa tace “Dan Allah kayi haƙuri bansan kana zuwa bane!”
STORY CONTINUES BELOW
Kallonta yayi daga ƙasanta har sama, yana kawowa daidai fuskarta yatarar da ƙwalla sun cika idanunta, ƙiris suke jira su gangaro. Wani irin haushi da takaicinta ne suka cikasa, cikin wata murya me ɗauke da amo yace “Are you insane?”
Ƙasa tayi da kanta aikuwa saiga hawaye kam sun ziraro kan kuncinta. Wani baƙincikintane yasake kamasa, hannunsa yakai ya kamo haɓanta tare da ɗago fuskarta, manya manyan idanunta ta zaro waje tana kallonsa, bazato ba tsammani ya hankaɗata gefe yayi shigewarsa abunsa, ƙiris yarage tafaɗi, wani irin wawan ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ɗaukar school bag ɗinta data faɗi ƙasa ta nufi wajen Kamalu driver.
Tunda suka ɗauki hanyar makarantar take tunani, akan fuskarta kuwa hawayene caɓa caɓa, wasu na koran wasu.
“Me turetan da yayi yake nufi? wulaƙanci kenan kome?” abun da take ta tambayar kanta kenan. Wata zuciyarta ce tace da ita “Baki da hankali Ziyada, dama irin waƴannan mutanen idan ba alfarma ba mene zai haɗaki dasu? sam baki da daraja da kimar da zaki raɓesu” Hannu takai kan fuskarta ta share hawayenta, aranta taƙudiri aniyar zatayi karatu sosai itama ta zama wata, daganan saita fita daga cikin rayuwarsu baki ɗaya. Da wannan tunanin azuciyarta har Kamalu driver ya ajiyeta acikin makarantar, tun bata gama fitowa daga cikin motar ba Nasmah ta taho da sauri ta rungumeta, wani irin daɗi Ziyada taji tuni ta manta da wata damuwa itama ta rungume Nasmah…
“I miss u so much my ƙawa!” Nasmah tafaɗa cike dajin daɗin ganin Ziyada.
“Miss you too!!” Ziyada itama tafaɗa tana murmushi, ƙarasowar Shukra yasa Ziyada sakin Nasma, ta rungume Shukra dukansu dariya suka sanya cike dajin daɗin ganin juna, suna maƙale da juna haka suka nufi wajen taron assembly, koda aka kammala assembly’n direct sabon ajinsu suka nufa S.S 2A. Kamar yanda suke a wancan ajin hakama suke a wannan ajin sit ɗinsu ɗaya, Ziyada ce ke tsakiya sai Nasma da Shukra dake gefenta.
Ƙarfe 10 am daidai aka fito dasu break, kai tsaye wajen da aka tanada na musamman doncin abincin ɗalibai suka nufa, soyayyen doya da chicken sauce din da Ziyada ta zo dashi shi suka fara ci kafun daga bisani suka ɗaura da snacks.
11:00 am
Mota ƙirar Jeeb ce baƙa tayi parking awajen da ake faka motoci dake cikin school ɗin, Farouk wani irin ajiyar zuciya me sanyi ya sauƙe tare da lumshe sexy eyes ɗinsa, sai yanzu yaji sanyi acikin ransa da ya gansa acikin makarantar, zare key ɗin motar yayi tare da buɗe murfin motar ya fito, sanye yake da jumper na shadda sky blue wanda taji aiki me kyau, sanye yake da tsadaddiyar hulan zanna akansa wanda ta ƙarawa fuskarsa kyau, sosai yayi kyau sai fidda ƙamshi yake, bayi da tantama akan inda zai sameta saboda haka direct office ɗin principal yanufa, koda yaje permission ya nema akan yanason ganin wata ɗaliba mesuna Ziyada Mansoor Mainasara, domin da wannan sunan akayi mata register. Da yake principal ɗin ya sanshi, babu ɓata lokaci ya tura S.S 2A don aƙirata kasancewar a time ɗin sungama break harsun koma class.
Ba ƙaramin faɗuwa gaban ziyada yayiba jin wai ana ƙiranta daga office ɗin principal, gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, a iya saninta bata da wani wanda zaizo nemanta, haka ta nufi office ɗin principal ɗin zuciyarta cike da fargaba, a corridor ɗin dazai sadata da office ɗin idanunta sukayi mata tozali dashi, wani irin duka taji ƙirjinta yayi sai kawai ta tsaya cak tare da sunkuyar da kanta ƙasa, murmushin daya bayyana cute dimples ɗinsa yayi tare da takowa zuwa gareta, wani irin kallo yakeyi mata, komai nata ya sauya tasakeyin kyau sannan taƙara girma duk dacewa ba jiki tayi ba amma tabbas kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa ta ƙara girma. Gaf da ita ya matso har yazama baifi saura taku ɗaya tsakaninsu ba. “I miss you!!” yafaɗa cikin wata irin murya yana me kallon small lips ɗinta.
Murmushine ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta, ahankali taɗago da fuskarta idanunsune suka faɗa cikin na juna ƙasa tayi dakanta tana mai wasa da yatsun hanunta, sam bataji wani abuba da takalli cikin idanunsa, saɓanin Oga Sooraj da idan takalli cikin beauty eyes ɗinsa take rasa nutsuwarta.
Kallon yanda take lallanƙwasa yatsun hanunta yayi, yaɗan saki murmushi, jiyake kamar yajawo ta jikinsa ya bata tight hug, komai nata na musammanne babu abun dake burgesa atattare da ita kamar sanyinta.
“Muje mu zauna ko!” yafaɗa yana meyi mata nuni da wata bishiya wacce ƙasanta ke ɗauke da wani bench wanda akayi da cement. Bata iya musa masa ba saidai har yanzu kanta aƙasa yake, zama tayi akan bench ɗin tare da jawo hijab ɗinta ta ɗan rufe gefen fuskarta, shima akan bench ɗin ya zauna har ƙamshinsu na iya gauraya waje guda. “Nayi kewarki da yawa, bazan sake bari kiyimin nisa har haka ba, bansan da yaushene kika kama zuciata ba, please My cute babyy na ki juyo na kalli fuskarki!” yaƙare maganar cikin sanyin murya.
Har acikin ranta taji kalamannasa saidai tanaji kamar sunyi mata nauyi. Hannayenta tasanya taɗanja hijab ɗinta baya, tare da ɗago kanta ta kalleshi, shi ɗinma kallonta yake, murmushi ya sakarmata tare da ɗanyin ƙasa ƙasa da idanunsa, wani iri taji ajikinta hakan yasa itama taɗanyi masa murmushi. Cikin muryar shagwaɓa tace “Shine kaɗauko ni daga aji bayan kasan karatu zamuyi ko!”
“am sorry babyyyna inason ganinki sosai shiyasa.”
Murmushi tayi tare daɗan satan kallonsa, Idanunsa ɗaya ya kashe mata hakan yasa ta cusa kanta acikin cinyoyinta tana sakin wani smile, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa ya duba, time ɗin dazai koma office yakusa hakan yasa shi kamo hanunta, da sauri taɗago kanta ta dubeshi murmushi yayi mata tare da sake matsowa daf da ita, cikin wata irin murya me sanyi yace. “I love you!!!””I love you!!!” ya faɗa slowly yana me murza yatsun hanunta dake cikin nasa. +
Da sauri ta ɗago golding eyes ɗinta ta kallesa, wani irin abune taji yana yawo acikin jikinta, sam batasan me yasa wani yanki na zuciyarta ke ƙoƙarin accepting ɗinshi ba, hannayenta dake cikin nashi ta soma ƙoƙarin zarewa, babu musu yasake hannun nata, sai dai kuma be janye mayun sexy eyes ɗinsa daga kanta ba. Murmushin daya bayyana kyawunta tayi tare da miƙewa tsaye, batare da ta kalleshi ba tace “Zan koma class”
Shima miƙewa tsaye yayi tare da ɗan sakin murmushin daya sanya dimples dinsa loɓawa, wani farin envelope yazaro daga cikin aljihunsa, wanda aka ƙawata bayan envelope ɗin da zanen flowers masu sheƙi, gwanin burgewa, miƙa mata envelope ɗin yayi, ɗago ɗara ɗaran idanunta tayi ta ɗan kalleshi, mumushi yayi mata kamar zai shige jikinta haka ya sake matsowa gaf da ita, yanayin idanunsa ne suka sauya, take taji wani sabon abu na sauƙa ajikinta. “Pleaseee!!” yaja maganan tare da ɗan ƙanƙantar da idanunsa. Adaburce tashiga kakkare jikinta, sam bata sabayin irin wannan kusancin da wani namiji ba, gaba ɗaya duk abun da Farouk keyi mata ganinsu take wasu daban, kowacce kalma da zata fito daga bakinsa jinta take tayi mata nauyi, takan rasa nutsuwarta idan taganshi akusa da ita sosai, domin wani irin faɗuwar gaba takeji, ganin irin mood ɗin data shiga yasanyashi sake kamo soft hand ɗinta, envelope ɗin ya ɗaura mata akan hanunta, tare da bin kyakkyawar fuskarta da ido, sam batasan da yaushene kuma ya akayi taganta tana tafiya ba, sauri tashiga yi burinta ɗaya taganta acikin class, gaba ɗaya ma ta manta da cewa basuyi sallama ba. Shikuwa Farouk wani killer smile ya sake bayan yaga shiganta cikin class, baisan me yasa ba hakanan yake losing control ɗinsa idan yana kusa da ita, ayanda ya fahimce ta yarinyace wacce take real innocent, batasan komai agame da soyayya ba, da wannan daman zaiyi amfani wajen koya mata sonsa, zai koya mata yanda zata sosa fiye da kowa, daga ƙarshe kuma zaiyi ƙoƙari wajen ganin ya sameta amatsayin Mallakinsa, sosai yake sonta, sosai yake kuma son kasancewa tare da ita. Da wannan tunanin ya ƙarasa wajen da yayi parking motarsa. 4
Kamar wacce aka jefo haka ta faɗo cikin class ɗin, ko izinin shiga ajin bata nema ba. da yake a bencin gaba suke kuma malamin dake cikin class ɗin, gaba ɗaya hankalinsa naga board yana rubutu, shiyasa bai kula da shigowanta ba harta zauna, kallonta Shukra da Nasmah sukayi, cikin ƙasa ƙasa da murya Nasma tace. “I hope ba wani abun kikayi ba, naga jikinki duk yayi weak”
Sai alokacin taɗan soma dawowa sense ɗinta, murmushi ta ƙaƙalo tare da girgiza kanta alaman babu komae. Nasmah bata sake cewa komai ba ta maida hankalinta ga karatun da ake musu.
Duk abunda Malamin Chemistry ɗin ya koya musu ta bayan kunnen Zieyaderh yabi ya wuce, sam ko kaɗan hankali da tunaninta ba akansa suke ba, tunaninta yayi nisa ne izuwa wani waje daban, Farouk shine wanda yayi tsaye aranta. 1
“I love you!!!”
kalmar daya furta mata shiketa dawowa cikin tunaninta, lumshe beauty eyes ɗinta tayi tare da sakin wani murmushi wanda batasan da bayyanarsa ba, hakanan taji wani sanyi aranta, sosai daɗin kalman ke ratsata, kulawa shine abun da ta rasa tun tana ƙarama, kalmar Soyayya kalmace da babu wani wanda ya taɓa furta mata shi, hakan yasa takejin ayanzu tamkar wani kyautan farinciki Farouk ya bata, duk da cewa kai tsaye bazata iya tantance me takeji agame dashi ba, amma tabbas zuciya koya take tanason me kyautata mata, tana a wannan tunaninne har malamin chemistry ɗin yafita batare da ta saniba, kasancewar period ɗinsa ya ƙare, dafa ta da Shukra tayi shi yayi sanadiyar ɓacewan tunanin da take. 1
STORY CONTINUES BELOW
“Lafiyanki ƙalau kuwa Zieyaderh?”
Shukra ta tambaya tana me ƙarewa fuskar Zieyaderh’n kallo.
Board ta kalla tare da ɗan waiwayawa bayanta, cikin mamaki tace.
“Wae ina chemistry teacher’n ya fita ne?” 2
“Da ke zai tsaya jira?” Shukra ta bata amsa tana me harhaɗa text books ɗin dake watse saman desk ɗinta.
Murmushi kawai Zieyaderh tayi tare da duban Nasmah, cikin sakewa tace.
“Gaskiya ban fahimci abun daya koyarba please Nasmah taimaka min”
Dukansu tsaida abunda sukeyi sukayi tare da kallonta.
“Bazaki taɓa fahimta ba ae tunda anzuba miki kalaman love acikin brain ɗinki” Shukra tafaɗa tana me guntse dariyar dake ranta.
Hararanta Zieyaderh tayi tare da cewa “Love kuma?”
Dariya Nasmah da Shukra sukayi tare da tafawa, kallonsu tayi kawai itama saitayi murmushi,
jujjuya envelope ɗin dake hanunta ta shiga yi.
“Lover gurl!” Shukra tafaɗa tana dariya.
Kallonta Zieyaderh tayi, cikin yanayi na shagwaɓa tace “Allah Shukra banaso fa” Dariya dukansu suka sanya, envelope din dake hanunta ta soma ƙoƙarin buɗewa, duk suka zuba mata ido.
Wani golding colour neck chain ne me kyau da tsadar gaske ne ya bayyana acikin envelope ɗin.
“Wow!!” Nasma da Shukra suka haɗa baki wajen faɗa, da sauri Nasma ta karɓi envelope ɗin ta ciro chain ɗin, saboda tsabar kyawun chain din har ɗauke musu ido yake.
Kallon Zieyaderh Nasmah tayi tare da cewa “Gaskiya guy ɗinnan ya haɗu, wannan chain ɗinfa na gold ne, zaikai 50k fa!”
“Wasa ma kike, zai iya kai 60k wannan neck chain din, gaskia guy ɗinnan ya iya bada gift” Shukra tafaɗa tana me jujjuya chain ɗin ahanunta.
Zaro idanu Zieyaderh tayi sakamakon jin kuɗin chain ɗin, cikin yanayi na tsoro tace.
“Zan maida masa gaskiya ni bazan karɓa ba”
Baki Nasma da Shukra suka sake suna kallonta, cikin nuna mata batasan me takeyi ba Shukra tace “Zaki mayar masa fa kikace?”
“Eh, bazan iya sawa ba gaskiya” Zieyaderh tafaɗi haka har acikin azuciyarta.
Dariya suka sanya su duka biyun, cikin dariya Nasmah tace
“Allah har yanzun baki waye ba babe, ae idan masoyinka ya maka kyauta baka maida masa.”
Murmushi kawai Zieyaderh tayi kana ta kifa kanta akan desk, wani abune taji ya tsaya mata arai, har abada bazata taɓa manta matsayinta da kuma wacece itaba, sam bazata yaudari kanta ba, tanajin su Nasmah nata yaba neck chain ɗin tayi musu shiru,, Shigowan Islamic teacher yasanya su yin shiru, tare da bada hankalinsu gareshi. Gaba ɗaya wunin ranan Zieyaderh asukurkuce tayishi, abu biyune ke tsaye aranta, ƙarfe 5 pm daidai aka kaɗa musu ƙararrawan tashi. Amatuƙar gajiye takejin kanta, sama sama sukayi sallama dasu Nasmah, kana tanufi inda Kamalu driver ke tsaye yana jiranta, gidan baya ta buɗe ta shiga, duk da cewa tafi yawan zama agidan gaba, don bata damu da zaman gidan baya ba.
Tunda suka ɗauki hanya ta maida hankalinta kan titi, sanyin AC’n dake tashi acikin motar ne ya sanya tasomajin sanyi, hakan yasa ta duƙunƙune jikinta. 1
Saida sukazo gaban tamfatsetsen gate ɗin gidan Kamalu driver ya danna horn, take aka wangale masa gate ɗin gidan ya tura hancin motar ciki.
Wata Black colour jeep ce tayi parking a gefen gidan, wanda tun barowarsu makaranta take biye dasu batare da sunsan da hakan ba. Murmushi Farouk yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, key ya sake yiwa motar tare dayin reverse, sai yanzu yakejin sanyi aransa, sam bada wasa yakeson Zieyaderh ba, so yake ya mallaketa, so yake ta soshi fiye da yanda zata so kowa, aransa ya gama yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa, saboda haka da confidence ɗinsa ya juya yakoma inda ya fito.
STORY CONTINUES BELOW
Kamalu driver na gama daidaita parking, agajiye ta buɗe murfin motar ta fice, school bag na riƙe ahanunta ta nufi hanyar da zai sadata da babban falon gidan, bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin falon, babu kowa afalon sai TV plasma wanda yaketa aiki shi kaɗai, direct sama ta wuce, kamar zata wuce ɗakinta sai kuma ta ƙarasa gaban ɗakin Ummu tayi knocking, daga cikin ɗakin Ummu dake zaune tana karanta jarida tace “Yes come in”
Tura ƙofar ɗakin tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, ganinta yasa Ummu taɗanyi murmushi.
“Barka da gida Ummu” Zieyaderh tafaɗa cikin ƙasa da kai.
“Yauwa Zieyaderh kindawo ko, ya school ɗin?”
“Alhamdulillah!” Zieyaderh tafaɗa still aɗan kunyace, domin har acikin zuciyarta tanajin girman Ummu.
“Masha Allah, to je kicire uniform ɗin akwai abinci a dinning” Cike da kulawa Ummu tafaɗi haka.
Miƙewa Zieyaderh tayi tare da cewa “to”
Har ta fice daga cikin ɗakin Ummu bata daina kallonta ba, hakanan alkunyan Zieyaderh’n ke burgeta, sam baruwanta da rawan kai, komai nata acikin sanyi takeyinshi, tabbas zata sowa ɗanta Almustapha samun kyakkyawar yarinya kamar Zieyaderh, ta yanke hukunci aranta zata samu Mas’oud suyi magana, lallai tanason ganin iyayen Zieyaderh, don tanason nemawa ɗanta Almustapha auren Zieyaderh a wajensu, tasan Almustapha bazai taɓa ƙin zaɓinta ba, musamman ma idan yaga Zieyaderh tasan dole zai sota, dama kuma shi bai da wata matsala bakaman SOORAJ ba wanda komai nasa aƙa’idance yake.
Zieyaderh kuwa tana shiga cikin ɗaki ta soma rage kayan jikinta, towel ta ɗaura aƙirjinta tare da shigewa bathroom, da ruwa me ɗan ɗumi tayi wanka, take taji gajiyan dake nannaɗe a muscles ɗinta sun soma warwarewa, Ko body lotion bata shafa ajikinta ba ta zura wata slim net gown red colour ajikinta, wanda take da guntun hannu, sosai rigan tayi mata kyau, hasken fatanta yasake bayyana sosai, wani mayafi me shara shara ta ɗauka tayane kanta zuwa ƙirjinta dashi, ko bedroom slippers bata sanya ba haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice, wani irin yunwane ke ƙwaƙulan cikinta, kaitsaye dinning area ta nufa, food flask ne masu kyaun gaske jere a kan babban royal table ɗin, kulan farko data buɗe white rice ne aciki wanda yaji carrot da piece, ɗayan kulan kuwa chicken soup ne wanda za aci shinkafan dashi, su kaɗai ma sun wadaceta hakan yasa bata bubbuɗe sauran food flask ɗin ba, ɗiban abincin tayi ta sanya a plate, direct kitchine ta wuce don ɗaukan ruwa, sam bata taɓa tunanin zata tarar da wani acikin kitchine ɗinba kasancewar yanda taji gidan ya ɗauki shiru alamun banda Ummu da ita babu kowa acikin gidan, bata damu da gyalenta daya zame daga kanta har yayi sanadiyar fito da tsefeffen gashin kanta ba, kasancewar gyalen yana da santsi shiyasa yaketa zamewa ajikinta.
Tanashiga kitchine ɗin taga baki ɗaya wutan kitchine ɗin akashe suke, abun da bata taɓa gani ba kenan, gashi garin yasoma yin duhu hakan yasa bakomai dake cikin kitchine ɗin take iya gani ba, dayake tasan wajen da makunnan wutan suke sai kawai ta ƙarisa ta kunna wutan, take haske ya mamaye gaba ɗaya kitchine ɗin, bata damu data waiga bayanta ba ta nufi wajen fridge, buɗe murfin tayi ta ciro bottle water me ɗan sanyi. Tana juyawa idanunta suka faɗa cikin nashi, take ta sake goran dake hanunta ya faɗi ƙasa, buɗe manya manyan idanunta tayi cike da mamaki taɗan kalleshi, zaune yake akan saman wata ƴar madaidaiciyar drawer, dagashi sai long jeans ba shida ko riga ajikinsa, fresh naked skin ɗinsa sai shining take, wani cup ne riƙe ahanunsa wanda cikinsa ke ɗauke da black coffee, tun shigowarta cikin kitchine ɗin yake kallonta, harzuwa yanzu kuwa bai ɗauke idanunsa akanta ba, wani irin bugawa taji heart ɗinta nayi amma saita ɗan daure, tsugunawa tayi ta ɗauki goran ruwan tare da miƙewa tsaye, gaba ɗaya a tsarge takejin kanta, Ahankali ta juya ta nufi hanyar fita daga kitchine ɗin.
Cikin husky voice ɗinsa yace da ita. “Zoki bani ruwa”
Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa taɗan saci kallonsa, har yanzu bai ɗauke idanunsa akanta ba, zuwa tayi ta buɗe firjin tare da ɗauko masa bottle water me sanyi, cikin yanayi naɗan rusunawa ta miƙa masa, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta, da sauri yakawar da kansa gefe tare da taɓe baki, cikin rashin kulawa yace “Ajiye” agefe dashi ta ajiye, cikin sanyin jiki ta juya zata fice daga cikin kitchine ɗin.
“Waye kika ajiye da zai kashe miki wutan da kika kunna?” ƴajefo mata tambayar yana me jujjuya spoon ɗin dake hanunsa.
Tsayawa tayi daga tafiyan da takeyi tare da juyowa, jiki asanyaye ta ƙarasa ta kashe makunnin wutan, tana fita daga cikin kitchine ɗin ta saki wani wawan ajiyan zuciya, tare da ɗaukan plate ɗin abincinta da sauri ta haura sama. Shikuwa coffee ɗinsa ya cigaba da sha, sam duhun dake cikin kitchine ɗin bai damesa ba, sometimes yafison zama acikin duhu fiye da zama acikin haske. 2
Aƙasa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, har yanzu ƙirjinta be daina bugawa da ƙarfi ba, hannu tasanya acikin plate ɗin, saidai takasa kai koda loma ɗaya ne na abincin cikin bakinta, gaba ɗaya tayi losing nutsuwarta, ganinsa da tayi yanzu ya matuƙar hautsina tunaninta, ba komai ke ruɗar da ita ba kamar zallan kyau da kwarjininsa, sosai takejin wani iri aduk sanda tayi gamo dashi, lumshe kyawawan idanunta tayi tare da jingina bayanta da jikin gado, shock ɗin da ta shiga lokacin da idanunsa ke yawo ajikinta tane, ya shiga yadawo cikin brain ɗinta. Haka ta daure ta cuccusa abincin wa cikinta zuciyarta cike da tarin tunani, tana kammalawa tayi sallan magriba, bayan tayi sallan isha ne tabi lafiyan gado, da yake agajiye takejin kanta take bacci ɓarawo ya ɗauketa.
_SOORAJ_
Yana gama sipping black coffee tea ɗinsa, ya aje cup ɗin tare da miƙewa tsaye ya fice daga cikin kitchine ɗin, direct ɗakinsa ya wuce, toilet yafara shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala, wata blue t-shirt ya sanya kana ya wuce masallaci.
Bashi yadawo gidan ba sai ten pm dai dai, wanka ya sakeyi sannan yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi, ɗan ƙaramin towel ya ɗauka agaban dressing mirror ya shiga goge kansa, duk da cewa bai shafa turare ba amma gaba ɗaya ƙamshin sabulun da yayi wanka dashi ya cika ɗakin, wani body lotion wanda baya kama jiki sosai ya shafa ajikinsa, turarensa me sanyin ƙamshi ya ɗauka tare da fesawa, cumb ya ɗauka ya taje kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa, ɗan kallon kansa yayi amadubi lokaci guda kuma ya kawar da kansa gefe, pink lips ɗinsa ya ɗan ciza, wani tunanine yazo ransa hakan yasanyashi sakin murmushin daya bayyana zallan Kyawunsa, shi kansa baisan da yayi murmushin ba, direct gaban drawer ɗinsa ya nufa tare da zaro kayan dazai sa, riga da wando na black jeans ya sanya ajikinsa wanda sukayi matuƙar yi masa kyau, White kambas masu kyau yasanya aƙafafunsa, tare da ɗaura hulan white facing cap akansa, sosae da sosae yayi kyau harma baka iya tantance kammaninsa saboda yanda hulan ta ɓoye fuskarsa, wayoyinsa ya ɗauka tare da ɗaukan car key ɗinsa, yana fita daga cikin ɗakin ya murzawa ƙofar key tare da tura key din cikin aljihun wandonsa, koda ya fito ko ina dake cikin gidan ya ɗauki shiru, direct parking space ya nufa, mota ƙiran kia yashiga tare dayi mata key, koda ya iso bakin gate taradda Maigadi yayi yana ta zuba gyangyaɗi, wani silent horn ya danna, take maigadi yatashi a zabure, cikin daburcewa ya wangale masa gate ɗin, ba ɓata lokaci Sooraj ya cilla hancin motar sa waje, kasancewar dare ne hakan yasa babu wani hayaniya sosai akan tituna, tuƙi yake cike da nutsuwa yayinda ya saƙala earpiece akunnensa.
Duk da sanyin AC’n dake tashi acikin motar hakan bai hanasa sauƙe glass ɗin window ba, wani irin ni’imtaccen sanyine ke ratsa jikinsa wanda har ma yafi na AC daɗi.
TRANSCOP HILTON. +
Wangale masa makeken gate ɗin akayi, asukwane ya tura hancin motarsa cikin ƙawataccen compound ɗin hotel ɗin, ababban parking space ɗin hotel ɗin yayi parking motarsa.
Ahankali ya zuro da ƙafafunsa waje, cikin takunsa me ɗauke da nutsuwa haka ya nufi cikin hotel ɗin, direct babban ɗakin da zasu gudanar dawani important meeting ya nufa, gaba ɗaya kowa da kowa sun hallara shi kaɗai kawai ake jira, kasancewar shine jagoran meeting ɗin shiyasa basu fara ba dole saida suka jira yazo, aƙalla sun ɗauki sama da 1 hour suna tattauna maganganu wanda gaba ɗaya su yasu suke abunsu, Sooraj kam maganarsa bata wuce “Eh” ko “A’a” Ko kaɗan basu wani damuba domin dama acikinsu babu wanda baisan halinsa ba, 11:30 pm daidai suka kammala meeting ɗin, kowa ya kama gabansa, koda ya baro Transcop Hilton baikoma gidansu ba, direct gidansa ya wuce kasancewar gobe zai koma bakin aikinsa na Bank.
Washegari.
Kamar koda yaushe 7:15 daidai take kammala shirinta na zuwa makaranta, yauma hakance ta kasance domin tuni ta shirya kanta cikin uniform ɗinta, school bag ɗinta ta ɗauka agurguje tafice daga cikin ɗakin, bata tarar da kowa acikin falonba gashi har 7:30 takusa sam kuma bataso tamakara, buɗe ƙofar falon tayi ta fice, Kamalu driver ta iske tsaye yana jiranta, tana shiga cikin motar yaja suka tafi.
***
Tun 7 daidai yagama shirya kansa cikin wani tsadadden maroon colour suit and white long sleeve shirt, sosai yayi kyau acikin suit ɗin, wani dark maroon toms ƙiran company’n Italy yasanya aƙafafunsa, sosai kwalliyan nasa ya sake ƙawata. Agogon rolex ne ɗaure a tsintsiyar hanunsa, gaba ɗaya gashin kansa sai shining yake yana ɗauke ido, saboda sosai yasha gyara, kamar wanda akawa ɓarin turare ajiki haka yake tashin ƙamshi, sabuwar black car ɗinsa mercedes benz yashiga, direct bank ɗinsu ya nufa, tun fitowarsa daga cikin mota mutane keta kawo masa gaisuwa, sama sama yake amsasu yana wucewa, koda yakai office ɗinsa ya samu komai nead, dama kowa yasan bayason ƙazanta shiyasa always ake tsabtace masa office ɗinsa, sosai yatarar da aiki na jiransa saboda haka tunda yaje bai wani huta ba aiki kawai yaketayi a computer.
STORY CONTINUES BELOW
_Zieyaderh_
Tun fitowansu break take jin kanta wani iri, ga wani amai da tashin zuciya dake damunta, haka dae tayi break adaddafe suka koma class, duk su Nasmah na lure da ita, saboda ko magana sosai yau din batayi, ƙarfe 1 daidai aka fito dasu sallah, zuwa lokacin abun yasoma fin ƙarfin tunanin Zieyaderh, saboda ciwon sosai ya tsananta, gawani irin zazzaɓi daya rufeta, koda ta idar da sallah cusa kanta tayi tsakankanun cinyoyinta ta saki kuka me sauti, don bazata iya jurewa ba, sosai mararta ke murɗawa, gawani sabon ciwon ciki me tsananin azaba da takeji, ganin irin yanda take kuka yasa Nasma da Shukra kamata suka fice daga cikin masallacin, aƙasan wata bishiya suka zauna su dukansu, cike da kulawa haɗi da damuwa Nasmah ta dubi Shukhra wacce idanunta sukayi raurau alaman itama kuka takesonyi. “Ki kula da ita Shukhra banaje na faɗawa discipline master, nasan zai faɗawa principal!” kae kawai Shukhra ta iya kaɗa mata alamar taji, saboda itama zuciyarta cike take da rauni haɗi da tausayin halin da Zieyaderh ke ciki, don zuwa yanzu numfashinta har seizing yake kamar zai ɗauke,
Sauri Nasmah keyi don taga ta isa office ɗin discipline master, kamar daga sama taji anƙira sunanta.
Tana juyawa tayi tozali da Pharouk, da sauri taƙaraso gareshi, kallonta yayi daga sama har ƙasa, ganinta aɗan hargitse yasanyashi cewa.
“Lafiya kuwa naganki ahaka? Sannan kuma ina kuka shige tun ɗazun naketa nemanku?”
“Zieyaderh ce batada lafiya sosai, yanzuma office ɗin discipline master zanje!”
Sexy eyes ɗinsa yaɗan waro tare da cewa. “Tana ina? Meke damunta? Muje kinunamin inda take!”
Babu musu Nasmah ta juya shikuwa yabi bayanta.. Lokacin dayaga Zieyaderh na kuka baƙaramin tashi hankalinsa yayi ba. Shida kansa ya je office ɗin principal yasanar dashi cewa zai wuce da Zieyaderh asibiti, su Nasmah ne suka sata acikin motarsa sannan suma suka shiga, zuwa lokacin gaba ɗaya hankalinta yasoma gushewa. Da wani irin speed Pharouk kejan motar. A babban haraban asibitin yayi parking, zuwa lokacin bata da ƙarfin da zata iya ko da taka ƙafarta ne, batare da tunanin komai ba Pharouk ya sanya hannayensa duka biyu ya ɗagota zuwa jikinsa, tamkar ƴar baby haka ya ɗauketa yayi cikin asibitin da ita, duk dacewa baya cikin ishashshiyar nutsuwa amma duk da haka daya ɗagata saida yaji wani shock ajikinsa. Emergency aka wuce da ita, take aka shiga bata kulawa.
Nasma da Shukhra gaba ɗaya basa cikin nutsuwarsu, ganin haka yasanyashi lallaɓasu tare dace musu su koma makaranta shi zai kula da ita, babu yanda suka iya dole haka suka hau taxi suka koma makaranta, saidai kuma gaba ɗaya hankalinsu naga Zieyaderh har acikin ransu basason wani abu na cutarwa ya sameta.
Zama yayi akan wasu kujeru tare da sanya tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa, numfashi yake fitarwa ahankali, wani irin feeling yakeji ajikinsa, daga wata ɓangare na zuciyarsa kuwa tunanin halin da take ciki yake, yana awannan yanayinne aka fito da ita daga emergency room ɗin, kwance take flat akan wani gado me ƙafafun taya, kaitsaye ɗakin hutu aka wuce da ita. Likitan da case ɗin ke hanunsa ne yace da Pharouk ya biyosa office.
Zama Pharouk yayi akan kujeran dake fuskantar na Doctor, cikin damuwa yace. “Yajikinnata?”
“Kada ka damu jikinta da sauƙi dama bawani babban ciwo bane, nace dama tana irin wannan ciwonne aduk sanda zatayi period ko kuma yanzune abun ya soma?” Doctor ya tambaya yana me ɗan rubuce rubuce ajikin wata fafar takarda.
Shiru Pharouk yayi cike da ɗaurewan kai, kwata kwata shi bai fahimci me Doctor’n yake nufi ba.
Ganin haka yasa Doctor ɗin gyara zama tare da duban Pharouk.
“Munyi mata alluran bacci, tana buƙatar hutu sosai, menstrual pain ne insha Allah idan tafarka zataji sauƙi, saidai irin wannan ciwon baicika warkewa ba harsai mace tayi aure, wasu kuma yakan daina idan sun haihu, wasu kuma ko basuyi aure ba idan suka dace da magani yana iya dainawa, so amma nata yanada tsanani sosai gaskiya, yakamata akula, sannan tarage yawan shan zaƙi, saboda shima yana ƙara ciwon sosai, ga wannan magunguna ne da zaka nemo saboda idan tafarka tasha” Dr Ya faɗi haka yana me miƙawa Pharouk wata ƴar farar takarda.
Karɓan takardan Pharouk yayi tare da yiwa Doctor’n godiya.
Koda yafito daga office ɗin Dr direct ɗakin da aka kwantar da ita ya nufa, ahankali yaƙarasa gaban gadon da take kwance, gaba ɗaya gashin kanta ya watse akan pillow, yayinda kyakkyawar fuskarta tayi fayau, bakinta kuwa har ɗan bushewa yayi saboda wahalan da tasha, numfashi take fitarwa ahankali, kallon kyakkyawar fuskarta yayi tare da sanya hanu yashafi lallausan gashin kanta, wani irin tausayi da soyayyarta ne suka sake dirarwa zuciyarsa, kallonta ya shigayi sosai, yaune karo na farko daya fara ganinta babu hijab, ashe duk iya tunaninsa da yanda yake fasalta kyawunta azuciarsa tama wuce haka, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta, wanda har ana iya hango saman breast dinta, domin wuyan rigan yaɗanyi mata yawa kaɗan. Lumshe idanunsa yayi tare da jan numfashi mai tsawo, hanunsa ya zare daga cikin hair ɗinta tare da ɗan matsawa baya, wani irin abu yakeji ajikinsa na musamman agame da ita, kawar da kallonsa yayi daga gareta, domin kuwa idan ya yarjewa zuciyarsa yaci gaba da kallonta, to tabbas zai iya losing control ɗinsa. Jiki asanyaye yajuya yafita daga cikin ɗakin, azuciyarsa kuwa tattauna maganganun da Dr ya faɗa masa yakeyi. Aƙaton pharmacy’n dake gefen asibitin ya saya magungunan, motarsa ya shiga tare dayi mata key, inda ake saida fruits yanufa, duk wani kayan fruit saida ya saya sannan kai tsaye yadawo asibitin.
Har zuwa wannan lokacin bata farka ba, zama yayi akusa da ita tare da zaro wayarsa daga cikin aljihunsa ya soma dannawa.
Jin kamar tana ƙoƙarin motsawa yasashi tashi da sauri yaƙaraso inda take, hanunsa yakai ya taɓa goshinta. Daidai lokacin aka turo ƙofar ɗakin, waiwayawa yayi don atunaninsa likitane sai kuma yaga saɓanin tunaninsa, wani kyakkyawan farin gaye idanunsa suka gane masa, wanda yake sanye da maroon suit me tsananin kyau da tsada, kallo ɗaya kayi masa zakasan ko wanene shi, matashin saurayi, maiji da kuɗi, ilimi, wayewa,ƙasaita, jinkai, da kuma miskilanci, domin ko alaman annuri babu akan kyakkyawar fuskarsa, hannaye Pharouk yasanya acikin aljihun wandonsa tare da kafe wanda ke shigowa cikin ɗakin da ido. Yanayin takunsa kaɗai ya isa sanar dakai cewa shiɗin wanine, baigama shigowa cikin ɗakin ba, Doctor ya biyo bayansa.
“Tafarka ne?”
Dr Ya tambayi Pharouk yana me ƙoƙarin ƙarasawa gaban gadon.
“A’a” Pharouk yabasa amsa ataƙaice yana me kallon mutumin da shigowarsa ya tsaya masa amaƙoshi.
Babu wanda ya saurara acikinsu ya ƙarasa gaban gadon, kallon fuskarta yayi tare da dawo da kallonsa ga ƙirjinta, rumtse idanunsa yayi tare da cije lips ɗinsa, lokaci guda yaji wani irin ɗaci amaƙoshinsa, hijab ɗinta dake gefe da ita ya ɗauka, hannayensa ya sanya ya tallafota tare da sanya mata hijabin, ransa na ƙuna haka yajawo hijab ɗin ya rufe mata ƙirjinta dake buɗe, lokaci guda idanunsa suka sauya kala daga farare zuwa jajaye. Juyowa yayi ya kalli Dr cikin lion voice ɗinsa yace “Inason kayi discharge ɗinta yanzu”
“Babu damuwa ae dama ba wani babban ciwo bane” Cewar Dr
Cikin rashin fahimta Pharouk yace.
“Saboda me za a sallameta bayan bataji sauƙi ba?” yanayin yanda yayi maganan daɗan zafi yasanya, Dr sakin murmushi nuna masa SOORAJ dake tsaye ya haɗe fuska, yayi tare da cewa “Yayanta ne inaga yafiso subata kulawa agida ne”
Dummmm haka Pharouk yaji ƙirjinsa ya buga, atare suka kalli juna shida Sooraj, wani irin kallo sukawa junansu mai ɗauke da tarin ma’anoni. Wani killer smile Pharouk yayi tare da miƙawa Sooraj hanunsa cikin wata murya me amo yace “Am Pharouk” Wani kallo Sooraj yayiwa Pharouk, daga ƙasa har samansa sannan yaɗan taɓe baki shima ya miƙa masa hannu suka gaisa, saidai da sauri Sooraj ya zare hanunsa daga cikin na Pharouk tare da kawar da kansa gefe, Murmushi Pharouk yayi tare da ƙarasawa gaban gadon, hannunsa yakai daniyar taɓa fuskarta, kafun hannunsa ya gama sauƙa akan fuskarta tuni Sooraj yayi masa wani irin riƙo wanda ya sanya Pharouk ɗagowa da sauri ya kallesa, ido cikin ido haka suke kallon juna, kai Sooraj ya girgiza masa, sannan ya ɗauke idanunsa daga kansa, kallo Dr da yazama kamar wani statue agarin kallonsu yayi yace.
“Thank you Doctor”
Hannayensa duka biyu ya sanya ya ɗago Zieyaderh dake bacci, akafaɗansa ya ɗaurata tamkar ƙaraman yarinya ƴar shekara 3, ko kallon inda Pharouk yake baiyiba yafice daga cikin ɗakin.
Bin bayansa Pharouk yayi da kallo tare da sakin murmushi. Azuciyarsa yace.
“SOORAJ!!! Yanzu aka soma wasan.”Yana fita daga cikin ɗakin direct hanyar dazai sadashi da compound ɗin asibitin ya nufa, baidamu da kallon da jama’a keyi masa ba. Yana isowa jikin motarsa ya buɗe gidan baya tare da kwantar da ita akan kujera, yana shiga yaja motar da wani irin speed yabar cikin asibitin, ransa amatuƙar ɓace yake wanda baisan dalili ba, hakanan yakejin wani ɗaci amaƙoshinsa. Yanayin yanda yake sharara gudu akan titi yasanyasa isowa gida cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, ko jira agama buɗe masa gate ɗin gidan baiyiba ya tura hancin motar ciki. 4
Yana gama daidaita parking ya fito tare da buɗe gidan baya ya ɗauko ta, still akan shoulder ɗinsa yasake ɗaurata, wata hanya daban naga ya nufa ba wacce zata satadashi da babban falon dake cikin gidan ba, ajikin wata ƙofa naga ya tsaya tare da sanya key ya buɗe, ahankali yatura kofar ya shiga, wani ɗan corridor ne wanda gefe dashi wani haɗaɗɗen swimming pool ne wanda aka ƙawatasa, ruwan ciki gwanin ban sha’awa, sai kuma wasu ƴan tsirarun shukokin flowers da suka ƙara ƙawata kyawun wajen, wata ƙofar yasake buɗewa, wanda ya sadashi da ɗakin baccinsa, kasancewar bayan ƙofar shiga ɗakinsa wanda ke cikin babban falon gidan, akwai wata ƙofa ma wacce take ta bayan compound ɗin gidan. Ƙofar ya mayar ya rufe tare da murza mata key, ƙarasawa gaban makeken gadonsa yayi tare da birkito da ita ta dawo kan hannuwansa, cike da tsananin muguntan dake ransa yasaketa tafaɗa kan gadon da ƙarfi, atake ta saki wani ƙara tare da sakin wani marayan kuka, hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa, tare da tsayawa ƙyam yana kallonta, sam fuskarsa ko alaman wasa babu.
Agalabaice ta sanya hannayenta ta riƙe weast ɗinta dake ciwo kaman zai ɓalle, sam batama gama sanin awacce duniya take ba, kasancewar alluran baccin da akayi mata baigama saketa ba, azaban sakinta da ƙarfi da yayi akan gado ne yasanyata farkawa, ahankali idanunta suka ɗan soma washewa saidai duk da haka bata gani sosai, idanuntane suka sauƙa akan fuskarsa, adaburce taja jikinta baya, duk da cewa bata gama dawowa hayyacinta ba, amma hakan bai hanata tsorata data gansa ba, kukan da takeyi ta tsayar, tare da sanya white teeth ɗinta ta datse lips ɗinta, alaman wani waje nata nayi mata zafi. 3
Sooraj dake tsaye ya harɗe hannuwa ganin yanda take ciccije baki, yasanya cikin husky voice ɗinsa yace da ita “Tashi!”
Da sauri tasoma yunƙurin sauƙa daga kan gadon, tana aje ƙafafunta aƙasa, wani irin jiri ya ɗebeta tare da ƙoƙarin kada ita, da sauri tasanya hannayenta duka biyu ta dafe bango, siririn kuka tasaki marar sauti, don masifar tsoronsa takeji, kallon jikinta yayi sannan ya kalli white bedsheet ɗin dake shimfuɗe kan bed ɗinsa, idanunsa yaɗan zaro tare dasanya hannu ya dafe goshinsa, aɗan harzuƙe yace.
“Bakida hankali ko? Ɗauka maza kije toilet kiwanke minshi yanzunnan, sannan kuma ki tabbatar da cewa yafita!!” yafaɗi maganar agadarance yana meyi mata nuni da bedsheet ɗin. Dubanta takai kan gadon, nan taga jini yaɗan ɓata tsakiyan bedsheet ɗin, wani irin faɗuwa gabanta yayi take taji wani masifaffen kunya ya rufeta. Kanta aƙasa ta sanya hannu tashiga jan bedsheet ɗin, duk da cewa dishi dishi idanunta suke gani sannan kuma babu wani ƙarfi ajikinta, hakan yasa komai takeyinshi cikin sanyi, ɗaukan bedsheet ɗin tayi tare da nufar wata ƙofa ta daban atunaninta nanne toilet, daga yanayin tafiyarta kaɗai ya isa sanar dakai cewa bata cikin hayyacinta, don har yanzu pain ɗin bai saketa ba. 2
Hannunsa yasanya ya damƙo ta, yanayin irin riƙon daya mata ba na wasaba ne, don har saida wani ƙashi dake cikin hannunta yayi ƙara, ƙafarsa yasanya ya daki ƙofar toilet ɗin, take ƙofar ta wangale, hankaɗata cikin toilet ɗin yayi tare da jawo ƙofar ya rufe. Zama yayi akan wata kujera tare da ɗaukan laptop ɗinsa yashiga dannawa, gaba ɗaya wani irin takaicinta yakeji.
STORY CONTINUES BELOW
Itakuwa Zieyaderh rasa inda zata sanya bedsheet ɗin tayi, wani irin bacci tare da jiri ne ke fusganta har bata iya ganin gabanta sosai, wani bucket ta ɗauka tare da sanya bedsheet ɗin aciki, ruwa ta zuba acikin bucket ɗin sannan tajefa sabulu, tsugunnawa tayi ta zubawa bucket ɗin ido, tama rasa ta ina zata fara, ganin tsayuwan ya isheta yasanya ta zauna daɓas aƙasan tiles tare da jingina bayanta da jikin bango, 5 minute kacal bacci ya ɗauketa awajen.
30 minute ya ɗauka azaune yana daddana laptop ɗinsa, kwata kwata shi yama manta da ita, ƙiran sallan magriba da akasomayi ne yasanyashi rufe laptop ɗin tare da miƙewa tsaye. Ahankali ya tura ƙofar toilet ɗin yashiga bakinsa ɗauke da addu’a. Hannayen rigarsa yasoma naɗewa tare da ƙarasawa gaban sink. Alwala yayi yana cikin wanke ƙafarsa na hagu idanunsa suka sauƙa akanta, saida yaji wani irin faɗuwar gaba domin shi sam yama manta da ita, cike da mamakin yanda tabaje tana sharar baccinta yashiga ƙare mata kallo, ga bucket agabanta sannan kuma ga bedsheet da sabulun wankansa nan acikin bucket ɗin, sabulun ya narke saboda yasha ruwa, itakuwa baccinta take tana sauƙe ajiyar zuciya. hankalinta akwance.
Ƙafansa yaɗan sanya ya zungureta, ko motsi batayi ba, wani murmushin da iyakansa leɓen baki yayi, gaban babban bathtube ɗin wankansa ya ƙarasa, ruwan sanyi ya tara har saida yacika bathtube ɗin, ƙarasowa gabanta yayi tare da ɗan durƙusawa ya ɗauketa, kamar wata ƴar tsana haka ya jefata acikin bathtube ɗin, aruɗe ta buɗe idanunta da sukayi luhu luhu sannan sukayi ja, wani irin sanyine ke ratsata. Juyawa yayi cikin halin ko inkula yafice daga cikin toilet ɗin, cikin daurayi ta fito daga cikin bathtube ɗin, gaba ɗaya kayan jikinta sun jiƙe jaƙab, ahankali take taka ƙafafunta da takejinsu kamar bazasu iya ɗaukanta ba. Bazata iya jurewa azabobin dayake gana mata ba, ganin bakowa acikin ɗakin yasanya tanufi hanyar fita, saɗaf saɗaf take tafiya kamar munafuka, ƙofar corridor ɗin ta buɗe ahankali, kanta tasako taɗan leƙa babban falon, kamar dai koda yaushe babu kowa acikin falon, da sauri ta fito ko tsaya rufe masa ƙofar batayi ba, daɗan sassarfa ta soma haura step ɗin dazai sadata da ɗakinta, tana tafiya tana waigen ƙofar ɗakin Ummu, kamar ɓarauniya haka ta buɗe ƙofar ɗakinnata ahankali tana shiga ta kulleshi gam, jiƙaƙƙun kayannata tasoma cirewa, sannan ta wuce bathroom. Adaddafe ta haɗawa kanta ruwan ɗumi, tayi wanka, har yanzu pain ɗin bai gama saketa ba, saima wani sabon fever daya sauƙa ajikinta, pad ta ɗauka ta kimtsa kanta sannan ta sanya wata doguwar riga me ɗan nauyi, domin kuwa sosai takejin sanyi, duk da cewa akwai yunwa sosai acikinta amma bata damu da neman abinciba, kan gado ta hau tare da jan blanket ta rufe gaba ɗaya jikinta, jikinta sai rawan sanyi yake, haka ta lumshe gajiyayyun idanunta da suketa ambaliya wajen fitar da hawaye. 2
Ganin har ƙarfe 7 Ummu bataji motsinta ba gashi yau bataga dawowanta ba yasanya hankalinta yaɗan tashi, saboda haka tafito don dubata.
Ahankali Ummu tatura kofar ɗakin tashigo bakinta ɗauke da sallama, ganin Zieyaderh nannaɗe acikin bargo yasanya Ummu ƙarasawa wajenta da sauri cike da kulawa tace.
“Zieyaderh lafiya kike kuwa?”
Zieyaderh da duk jikinta ke rawan sanyi, ta girgiza kanta cikin ciwo tace.
“Ummu zazzaɓine ke damuna!”
“Subahanallah shine kuma bakizo kin faɗamin ba? ba’a zama da ciwo ae, sam hakan ba kyau, kin maci abinci kuwa?” Ummu ta tambaya.
Kai Zieyaderh ta girgiza alaman.
“A’a”
Juyawa Ummu tayi tafice daga cikin ɗakin.
Mintuna kaɗan saiga Ummu ta dawo hannunta ɗauke da plate da kuma cup ɗin tea, kan bedside drawer ta aje plate da cup ɗin, bargon da zieyaderh ke lulluɓe dashi Ummu taɗan yaye tare da miƙar da ita zaune, cup ɗin tea ɗin Ummu ta bata, babu musu ta amsa, ahankali takeshan tea ɗin, sai da tasha kusan rabin cup ɗin, kafun Ummu ta amshi cup ɗin, plate ɗin soyayyen dankali da ƙwai wanda yaji sauce Ummu ta miƙo mata, nanma bata musaba ta amsa, ahankali takecin abincin duk batajin wani daɗin bakinta. Pain reliever Ummu ta bata tasha, sannan tace da ita ta kwanta tayi bacci, luf tayi akan gado tana maida numfashi ahankali, cikin wasu mintuna ƙalilan bacci ɓarawo yayi gaba da’ita.
STORY CONTINUES BELOW
Tunda Yafita sallan Magriba bashi yadawo gidanba sai 9 pm, direct toilet ɗinsa ya wuce, wanka yayi yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi, sama sama yashafa body lotion, white trouser yasanya, tare da feshe jikinsa da turare me daɗin ƙamshi, Luf yayi akan gadonsa tare da cusa kansa cikin pillow, sanyin AC ne ke ratsa naked skin ɗinsa, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, ƙoƙarin faɗa da tunaninsa yake, sam bayason wani abu yasake damunsa, a ƴan kwanakinnan yana yawan jin zuciyarsa nayi masa zafi, sam bayason ciwonsa yayi ƙarfin da harsai kowa ya gane yana ɗauke da ciwon zuciya, akullum yanaji ajikinsa bashi da wani sauran farinciki daya ragemai, numfashi ya fitar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa, duk yanda zuciyarsa taso da yayi tunani yaƙi bata daman hakan, yajima sosai kafun yasamu bacci ya ɗaukesa.
Washegari.
7:00 am daidai yagama shirya kansa cikin navy blue suit, Sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake, waya da key ɗin motarsa ne riƙe ahanunsa, cikin nutsuwa yake takunsa har yakai bakin ƙofar da zai fitar dashi daga cikin falon. Muryar Ummu da yaji abayansa yasanyashi tsayawa, juyowa yayi cikin ɗan rusunawa yace.
“Good morning Maaa”
Murmushin daya bayyana tsananin kamanninsu dashi Ummu tayi tare da cewa
“Morning how are you?”
“Am fine!” ya amsa ataƙaice yana me gyara wrist watch ɗinsa.
“Kasanar da Mas’oud Zieyaderh batajin daɗi, sannan yau bazata samu zuwa school ba ya kamata asanar” Ummu tayi maganar tana me ƙoƙarin zama akan kujera.
Kansa kawai ya jinjina alamar yaji kana yafice daga cikin falon.
Sosai tasha bacci sai 10 tafarka, Alhamdulillah ta ɗanji sauƙin jikinta, saidai kuma duk da haka bakinta babu daɗi, fitowarta daga wanka kenan, wani riga da sket ƴan kanti tasanya, sket ɗin irin rubber pencil ɗinnan ne yayinda rigan takasance me buɗaɗɗen kafaɗa, sosai kayan sukayi mata kyau ajiki, rubber hijab tasanya ajikinta, sannan tanufi ƙasa, ahankali take saƙƙowa daga kan steps ɗin, Ummu ce zaune afalon tasha ado cikin wani tsadadden lace maroon colour wanda yayi matuƙar amsar jikinta, gefe da ita wata matace wacce bazata wuce shekarun Ummun ba itama zaune ta caɓa ado, dagani basai anfaɗa ba kasan naira yazauna musu su dukansu. Cikin ladabi taƙaraso tare da durƙusawa ta gaidasu, fuska ɗauke da murmushi Ummu ta shafa kan Zieyaderh’n tare da cewa
“Kintashi? har baccin ya isa kenan, to ga can break fast akan dinning”
Murmushi Zieyaderh tayi tare da miƙewa tsaye tanufi dinning area. Hajiya Munah dake zaune tabi Zieyaderh da kallo, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Ummu cikin yanayi naɗan mamaki tace.
“Hajiya Sulaimiyya ina kikasamo wannan kyakkyawar yarinyar kodai daga ƙasarku take ne?”
Murmushi Ummu tayi tare da cewa. “Ƙanwar Mas’oud ne abokin Sooraj, ai kindai san Mas’oud?”
Murmushi Hajiya Munah tayi tare da cewa “Ayya gaskiya balaifi yarinyar akwai hankali, uwa uba gata da kyau masha Allah!”
“Wannan halayyan nata shiyasa nakeson haɗata aure da Almustapha, nasan bazaiyi takaicin samunta amatsayin mata ba” Cewar Ummu wacce ke sipping pineapple juice ahankali.
Murmushi Hajiya Munah tayi tare dacewa “Gaskiya kinyi tunani me kyau, amma ae zai fi kyau ki haɗata da Sooraj, don aganina yafi Almustapha buƙatar mace akusa dashi”
Aje glass cup ɗin hanunta Ummu tayi tare da duban Hajiya Munah, wani murmushi me ciwo Ummu tayi cikin wani irin yanayi tace “Saikace bakisan waye Sooraj ba Hajiya Munah? hmmm Sooraj ɗin da baibzauna da matan da suka amsa sunansu mata ba ma, mene zaiyi da ƴar wannan ta tsitsiyar yarinyar da duka duka shekarunta basu wuce 18 to 19 ba”
Ajiyar zuciya Hajiya Munah ta sauƙe tare da cewa “Allah ya kyauta”
Da “Ameen” Ummu ta amsa daganan suka ci gaba da hiransu.
Zieyaderh kuwa zama tayi akan dinning tare da zubawa kanta pepper chicken soup, and chips, ahankali take tsakalan abincin don gaba ɗaya bawani daɗinsa takeji ba. Koda ta kammala ɗakinta takoma magungunanta tasha kana ta kwanta, tashar Mbc Action take kalla da haka har bacci ya ɗauketa.
Dayake magungunan da tasha suna da ƙarfi sosai hakan yasa ba ita ta tashiba sai wajen 5 na yamma, wanka tayi tare da sanya wata blue gown marar nauyi, yunwa takeji sosai hakan yasa tashiga ƙoƙarin zura hijab ɗinta don sauƙa ƙasa, jin anturo ƙofar ɗakinne yasanyata waigawa da sauri, ido biyu sukayi da Ummu wacce fuskarta ke ɗauke da murmushi.
“Barka da yammaci Ummu” tafaɗa murya asanyaye.
“Yauwa, dama wai me gadine yanzun yashigo yace wai wani yana sallama dake awaje, shine nace ko kunyi da wani zaizo wajenki ne?”
Idanu Zieyaderh ta zaro, lokaci guda ƙirjinta yashiga wani irin bugu, bakinta narawa tace “Ni….ni…kuma?”
“Eh haka dai yace, yanaga kin tsorata? Maza kije kiga ko wayene bakyau kabar mutum yana jira!” Ummu nagama faɗan haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.
Tsorone ya kama Zieyaderh adaburce ta sanya hijab dinta,kana ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice. Bataga Ummu afaloba kai tsaye saita nufi hanyar waje.
Koda tafito compound ɗin gidan idanunta tashiga warewa ko zata hango wanda akace na nemanta.
Tun fitowarta daga cikin falon yake kallonta, sosai tayi masa kyau acikin hijab ɗin dake jikinta, ashe sosai uniform ke ɓoye kyawunta. Kamar wanda akace tawaiga bayanta, hangosa tayi tsaye ajikin black car ɗinsa mercedes benz, sanye yake da riga da wando na bugaggiyar shadda Blue colour wanda tayi matuƙar yi masa kyau, mamakin ganinsane kwance acikin ranta amma saita sunkuyar da kanta ƙasa tare da nufar inda yake, murmushine kwance akan fuskarsa yana me kallonta harta ƙaraso. Cikin siririyar muryarta tayi masa sallama. Bai amsa sallamannata ba saima tsayawa kallonta da yayi, jin shiru bai amsa mata ba yasanya ta ɗago kanta ta dubeshi, idanunsune suka sarƙe cikin na juna, yanayin kallon daya mata yasanya ta sauƙar da idanunta ƙasa da sauri tana murmushi. Kansa yaɗan sunkuyo yana leƙa fuskarta, ganin haka yasa tasanya tafukan hannunta ta rufe fuskarta da sauri.
“Jiya nakasa bacci saboda bansan wani hali kike ciki ba, amma ganinki danayi yanzu yasa naji sanyi araina, basai ma kin faɗa ba nagane kinji sauƙi” Yafaɗi haka cike da tsantsar nuna kulawarsa gareta.
Har acikin ranta taji daɗin maganganunsa, domin tanada buƙatar kulawa sosae.
Ɗan matsowa kusa da ita yayi hartana iya jiyo sassanyan ƙamshin dake fita ajikinsa. Hannayensa yakai ya zame hannunta dake kan fuskarta.
Cikin wata irin sweetness voice yace “Kullum ƙara kyau kike, komai naki me kyaune, zanso kasancewa dake akoda yaushe sannan akowacce rana, please faɗamin kina sona?” yaƙare maganar yana me juya idanunsa akan kyakkyawar fuskarta.
Lumshe kyawawan idanunta tayi sosae zuciyarta ke bugawa, batasan me zatace masa ba, sannan kalamansa sunyi mata nauyi sosai, shikaɗai ya lura da mota ƙiran black range rover dake shigowa cikin gidan, kasancewar ita tabawa ƙofar gate baya, sannan gaba ɗaya tunaninta yatafi izuwa wani wajen daban. Ahankali taɗan buɗe idanunta tasaci kallonsa, abun da bata saniba shima kallonta yake sai kawai idanunsu ya sauƙa acikin na juna. Da sauri ta kawar da kanka gefe tare da sanya hijab ɗinta ta kare gefen fuskarta, idanunta ne suka sauƙa akan motar da ta shigo cikin gidan, wani irin masifaffen tsorone ya kamata take jikinta ya soma ɓari, lokaci guda jikinta yashiga fidda gumi, yana gama daidaita parking ɗin motar yafito, sanye yake da white t-shirt and combat army jeans, baƙaramin kyau yayi ba sosai kayan suka fitar da kwarjininsa. Cikin isa yake takunsa yana me dosowa cikin gida, saidai abun mamaki bai ɗago kai ya kallesu ba, bawai kuma don baigansuba tun shigowansa idanunsa sukayi masa tozali dasu, baya baya Zieyaderh keyi tana me ƙoƙarin ɓoyewa abayan Pharouk, tuni hawayen tsoronsa sun cika idanunta. Yayinda shikuma yake daɗa kusanto inda suke, fuskarsa sam babu alaman wasa ko murmushi akanta.Cikin nutsuwa yake takunsa, tuni Zieyaderh ta koma bayan Pharouk ta ɓoye, rumtse idanunta tayi ƙam cike da fargaba. Ƙamshin turarensa da yacika hancinta ne yasanya jikinta ya soma rawa, saboda tasan zuwa yanzu yana gab dasu. Sam bai kallesuba balle yasa aransa cewa da gaske mutanene awajen, kansa tsaye ya wuce. +
Aƙalla taɗauki kusan 5 minute ahaka, idanunta a rufe suke, jin shiru bataji motsin kowa ba yasanya tasoma buɗe idanunta ahankali, da beuty face ɗinsa tasomayin arba yayinda ya kafeta da sexy eyes ɗinsa, waro idanunta waje tayi tare da ɗanja da baya tashiga waige waige.
Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi, tare da ɗan kashe mata idanunsa ɗaya.
“Tsoron me kikeyi haka? ba Brother ɗinki bane?”
Kanta ta sunkuyar ƙasa tare da sauƙe ajiyar zuciya, duk da bata ganshi awajenba amma amatuƙar tsorace take domin batasan wani hukunci bane zai biyo baya.
“Meyasa kikejin tsoronsa? Ya hanaki kula kowa ne? Waye shi awajenki? Please tell me karkimin ƙarya!” yafaɗi haka yana me gyara tsayuwarsa tare da kafeta da idanunsa….
Sallama ɗauke aƙasan maƙoshinsa yashiga cikin falon, kai tsaye ɗakinsa ya nufa.
“SOORAJ!” Ummu dake zaune acikin falon taƙira sunanshi.
Cak ya tsaya da tafiyan, ahankali ya ɗan juyo ya kalleta.
Fuskarta babu alaman wasa batare da ta kalleshi ba tace “Badai ka ɗauki maganganun da Abbanka yayi maka amatsayin wasa ba?”
Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, baijin zai iya furta wata kalma awannan lokacin.
Sanin halinsa yasanya Ummu cigaba da cewa. “Kashiga hankalinka Sooraj, yakamata ace kasan mekakeyi, sai yaushene zaka fuskanci cewa ka girma? sai yaushe ne zaka nemawa kanka mutumci da daraja tahanyar yin aure? Ashe kafiso koda yaushe muta faɗa muna nanatawa duk akanka kai kaɗai? Idan kasake mahaifinka yayi mummunan fushi dakai to wallahi ba zakaga da kyau ba, sannan kuma gobe Almustapha zai dawo ka tura mota a ɗaukosa!” Ummu tafaɗi maganganun fuskarta babu alaman wasa.
Kansa kawai ya jinjina alaman yaji, ko 1 second baiƙara ba ya juya ya shige ɗakinsa.
Da kallo Ummu tabisa, tarasa hali irin na sooraj wani kalan alfano gareshi, ita tahaifesa amma batasan a ina yasamo wannan miskilancin nasa ba, sam itakam ba haka take ba.
Yana shiga cikin ɗakin ya murzawa ƙofarsa key, kayan jikinsa ya shiga ragewa, towel ya ɗaura ya shige bathroom, ruwa ya sakarwa kansa tare da sanya hannunsa na dama ya dafe bango, lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗaga sama ruwa ya shiga dukan fuskarsa, saida numfashinsa yasoma barazanan ɗaukewa sannan ya sauƙar da kansa ƙasa, numfashi yashiga fitarwa akai akai, yana mejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.
Ƙanƙance idanunsa yayi tare da lumshesu alokaci guda. “Zieyaderh!!” yaƙira sunanta in a cool voice ɗinsa. 1
Kanta ta ɗago tare da ɗan satan kallonsa, cikin muryarta me sanyi tace. “Na’am!”
“Inasonki!” Yafaɗa asanyaye yana me karyar da kansa gefe.
Kanta tajinjina tare da ɗan sakin murmushi, ƴan siraran laɓɓanta dake motsawa ahankali ya kalla.
Da alama maganace abakinta amma tanajin nauyin furtawa.
STORY CONTINUES BELOW
“Bakiji daɗin zuwana ba ko?”
Kanta ta girgiza alaman “A’a”
“To meyasa ba kya farinciki? Natafi ko kin gaji da ganina?” Ya tambaya yana me zura hannayensa acikin aljihun wandonsa.
Kanta ta girgiza cikin wani irin yanayi na shagwaɓa tace
“A’a nifa bance haka ba!”
Idanunsa ya lumshe har cikin ransa yaji salon shagwaɓan nata ya taɓasa, cikin ƙasa da murya yace “to faɗamin”
Tafukan hannayenta tasanya ta rufe fuskarta tana dariya.
“Pleaseeee mana baby faɗamin kina sona?”
Kasa jurewa tayi da sauri tajuya cikin yanayi na ɗan gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin gida, murmushi Pharouk yayi tare da binta da kallo, wani irin sanyi yakeji acikin ransa, duk da cewa bata furta masa da bakinta ba, amma tabbas yasan bataƙinsa, don baiga ƙiyayyarsa acikin ƙwayan idanunta ba, motarsa ya buɗe ya shiga tare dayi mata key, mai gadi ne ya wangale masa gate, haka yabar cikin gidan zuciyarsa da tunani kala kala, gaba ɗaya ayar tambayarsa ya ɗigata ne akan SOORAJ.
Da ɗan gudunta tashigo cikin falon, tana rufe ƙofar ta saki wata ajiyar zuciya tare da sanya hannu ta dafe ƙirjinta, ƙoƙarin daidaita nutsuwarta tayi sannan takalli ɓangaren Sooraj, jin gabanta ya faɗi yasanya ta haura sama tana shiga cikin ɗakinta tafaɗa kan gado tare da lumshe idanunta, wani iri takeji azuciyarta, batasan dalilin da yasa takejin Pharouk awani ɓangare na zuciyarta ba, saidai kuma ako da yaushe kalamansa daɗi suke mata.
Luf yayi akan gadon tare da sake cusa kansa cikin pillow, gaba ɗaya ya rasa inda zai tsoma kansa yaji daɗi, ba yason yakai gayin abun dazai dameshi daga baya hakan yasa ya jure duk wata damuwarsa, sosai yakejin rauni azuciyarsa, musamman dangane da matsalarsa,,, yajima yana saƙawa da kuncewa acikin zuciyarsa kafun daga bisani bacci ɓarawo ya sace sa.
Washegari.
Alhamdulillah yau taji daɗin jikinta sosai hakan yasa ta shirya kanta tsab cikin shigar uniform ɗinta, hakanan takejin sanyi azuciyarta, ahankali take saƙƙowa daga kan step ɗin. Ƙaran takun takalmanta yasanya shi ɗago da kansa, dai dai lokacin itama ta ɗago kanta, idanunsune ya sauƙa cikin na juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, shima kansa ya kawar tare da ci gaba da sipping coffee ɗinsa.
Sumu sumu haka taƙarasa sauƙowa daga kan steps ɗin, ahankali take tafiya harta ƙaraso inda yake, cikin wata irin murya me sanyi tace “Ina kwana!”
Bai amsata ba hakan yasa taɗan ɗago kanta ta kalleshi, ganin kamar baisan tana wajenba yasanya ta soma wasa da yatsun hannunta tana me murzasu, cikin yanayi naɗan shagwaɓa tace “Ina kwana Ya…yah?”
A yanzu kam ɗago kansa yayi ya kalleta saidai haryanzu bai amsa mata ba, jiki asanyaye ta gyara zaman school bag ɗinta sannan tanufi hanyar fita daga cikin falon.
Kamalu driver tasamu tsaye ajikin mota, da sauri ta ƙarasa tare da buɗe gidan baya ta zauna, tana ƙoƙarin aje school bag ɗinta, ya buɗe ƙofar motar ya shigo, ƙamshinsa take yacika ko ina dake cikin motar, mamakin shigowarsa cikin motar ne ɗauke akan fuskarta. School bag ɗinta ta rungume aƙirjinta tare da duƙunƙune jikinta waje ɗaya, tunda suka ɗauki titi yake ta faan latsa wayarsa, gaba ɗaya kwarjininsa ya cika mata ido, musamman yau da yasha ado cikin white and black suit, sai ya zamana yaƙara kyau. Aƙofar makarantar tasu Kamalu driver yayi parking motar, kamar marar gaskiya haka ta buɗe ƙofar motar tafice, ko taku uku batayiba taji ƙaran tashin motar, tana waiwayawa taga sunbar wajen, tana shiga cikin school ta haɗu dasu Nasmah, gaba ɗayansu hankalinsu atashe suke tambayarta yaya jikinta, sosai taji daɗin kulawarsu agareta da haka suka wuce class.
STORY CONTINUES BELOW
Ƙarfe Biyu daidai jirginsu ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin Abuja, wani kyakkyawan saurayi wanda aƙalla bazai haura 29 years ba, shike sauƙowa daga kan matattakalan jirgin Sanye yake da riga da wando na jeans masu kyaun gaske, kai tsaye baza’a ƙirasa da fari sol ba, sannan kuma shi ba baƙi bane, yana daɗan tsayi daidai misali sannan yana da faffaɗan jiki, daga yanayin shigarsa kaɗai zai sanar maka da ɗan gaye ne, fuskarsa ɗauke take da murmushi, Kamalu driver yana hangosa ya ƙarasa garesa da sauri cikin yanayi naɗan girmamawa yace “Ranka ya daɗe barka da zuwa”
Murmushi Alhmustapha yayi tare da bawa Kamalu driver hannu suka gaisa, cikin muryarsa yace “Yauwa Kamalu barka da aiki!”
Tunda suka baro airport ɗin Kamalu driver ke ta masa zuba, yayinda shikuma yawan maganartasa ba sosaiba saidai murmushi kawai da yakeyi.
Gyara zama Shukra tayi cikin kulawa tace “Me yasa zaki tauyewa kanki haƙƙi Zieyaderh? indai kina sonsa kawai ki amsa masa, mene aibun Pharouk? Sam bashida wani aibu komai nasa mai kyau ne, inta ƙaicemiki babu wata ƴa mace da zataga Pharouk kuma ta ƙishi coz ba Namijin wasa bane”
Sunkuyar dakai Zieyaderh tayi tare daɗan ciza lips ɗinta, “Bansan ya zanyiba Shukhra amma karki manta nafaɗa miki matsayina bai kai ace naso Pharouk ba, duk da bansan wanene shiba amma nasan ko sama zata haɗe da ƙasa yafini tsatso me kyau, da kuma gata, banason na tozarta rayuwata Shukhra!” taƙare maganar idanunta cike tab da ƙwalla.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da sakin murmushi “Wannan ba hujja bane Zieyaderh, ana iya auren shegiyama wacce bata da uba, balle keda kike da uba, balallaine don bakisamu kulawan mahaifanki yazamana kin tauyewa kanki haƙƙi ba, ke macece idan baki zaɓi mijin da zaizame miki garkuwa ba me kenan kikayi? Ki farka daga baccin da kike Zieyaderh akowacce ƙwanan duniya ƙara girma muke, ayanzune yakama musan dacewa muma matane sannan ayanzune yakamata mukau da wani shashanci da yarinya wanda ke cikin sense ɗinmu, yes nasani bamu da wasu shekaru masu yawa amma kuma babu wani abu na ƴan matanci ayanzu daya ɓoye kansa ajikinmu, zamu mori damarmu ne kaɗai idan mukayi amfani dashi tun muna ƙanana, alokacin da muka girma kuwa bazamu taɓa morarta da kyauba, saboda alokacin bakowa ne zaizo ya kallemu yace yana sonmu ba, ayanzu kuwa kowa so da sha’awarmu yake” Ɗan tsagaitawa da maganar tayi tare da sanya hannunta ta dafa kafaɗan Zieyaderh.
“Ki amincewa Pharouk Zieyaderh, inada tabbacin Pharouk bazai taɓa nuna miki tsana tsangwama da kuma kyara ba!”
Wani irin ajiyar zuciya me ƙarfi Zieyaderh ta sauƙe, tabbas tasan abunda Shukhra ta faɗa gaskiya ne, saidai kuma tayaya zata furtawa Pharouk cewa tana sonshi? Idan har taso Pharouk menene matsayin tunanin Mr.helper dake kwance acikin zuciyarta? Da sauri takawar da wannan tunanin acikin zuciyarta. Murmushi tayi cike da son samawa kanta ƙarfin guiwa tace “Zan faɗa masa komai game dani Shukra, idan har zai soni ahaka to nima zan amasa masa, saɓanin haka kuwa shikenan zanjira wata ƙaddaran”
“Bazai taɓa gudunki ba Insha Allah!” cewar Shukra. Dariya suka sanya su dukansu.
5:10 pm zaune take acikin motar gaba ɗaya tunaninta yayi nisa izuwa maganganun da sukayi da Shukhra, sanyin AC’n dake tashi acikin motarne ya cakuɗa da daddaɗan ƙamshin turaren sa, duk da cewa baya cikin motar amma zaman dayayi acikin motar da safe yasanya har yanzu ƙamshinsa bai bar cikin motarba, hakan yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi wani iri, jingina bayanta tayi da jikin kujeran motar tare da lumshe idanunta, sosai ƙamshin yake jefata cikin wani irin yanayi. Sam batasan da cewa sun iso gidan ba saida taji Kamalu driver ya tsaida motar. Jiki asanyaye take tafiya harta kawo ƙofar falon, tura ƙofar falon tayi ta shiga, da ƴar siririyar muryarta tayi sallama, Amustapha dake tsaye acikin falon ya juyo ahankali yana me amsa mata sallaman, idanunsune ya sarƙe acikin na juna, da mamaki akan fuskarsa ya shiga kallonta, Itama kallonsa take, “Almustapha” Muryar Ummu da suka ji yasa suka ɗauke idanunsu akan juna.
Ummu ce taƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da murmushi.
Kallon Zieyaderh tayi tare da cewa “Zieyaderh ga ɗana Almustapha”
Mamakine ya bayyana akan fuskar Zieyaderh amma saita share,cikin sakin fuska tare da murmushi taɗan rusuna tagaidashi, shima murmushinne akan fuskarsa ya amsa mata, har yanzu yana me dubanta don baigaji da kallonta ba. Harta haura steps bai ɗauke idanunsa akanta ba, Murmushi Ummu tayi sannan ta juya tafice daga cikin falon don dama fita zatayi.
Da ƙarfi ya buga table ɗin dake gabansa ransa amatuƙar ɓace yace “Get out Aneesa!!”
Murmushi Aneesa tayi tare da juya idanunta dake cike da ruwan hawaye, laɓɓanta ta ciza, “Bazan tafi ba RAJ Why kake kyarata? menene bani dashi? Kyau,Ilimi, dukiya, ko kuma me?” Ta tambayeshi hawaye suna mai sauƙa daga cikin idanunta.
Ransa amatuƙar ɓace yace “Kifitarmin a office!!!”
Murmushi mai ciwo Aneesa tayi cike da son ƙuntata masa tace “Baka sona saboda kai bakayarda da kanka bako? Hmmmm najima da sanin abunda kake ɓoyewa RAJ, najima da gane cewa kai Rago ne, Kafito fili kafaɗamin cewa kai ba Namiji bane mana, Ohhhhhh nagane kanajin kunyar sanar da duniya cewa kai wani marar amfanine ko, bansan meyasa ba duk da nasan cewa kai ba Namiji bane amma na liƙe maka, wallahi RAJ saika aure ni koda……” Wani irin bahagon mari SOORAJ ya sauƙe mata akan fuskarta wanda saida yagigita ta. Bata gama dawowa cikin hayyacinta ba ya ɗamƙi wuyanta da ƙarfi, mannata yayi da jikin bango tare da sanya hannunsa da ƙarfi ya yaga rigan dake jikinta, dayake doguwar rigane ajikinta hakan yasa ya yagata har ƙasa, take surar jikinta ya bayyana, idanunsane suka rikiɗe sukayi wani irin jaaa tamkar anwatsa masa barkono, lokaci guda jikinsa ya ɗauki ɓari tamkar wanda aka jonawa shocking.
“Ni ba Namiji bane ko? Yess niba Namiji bane, amma yanzu zanyi miki abun da wanda ba Namiji ba bazai taɓa iya yimiki shi ba” yana gama faɗan hakan ya wurgata saman table, tare da sanya hannu ya zare belt ɗin dake jikinsa.Wani irin jiri ne ke ɗibansa, duhu shine abun dake neman mamaye ganinsa, jin duniyar yake gaba ɗaya tana juya mai, da ƙyar ya iya buɗe ƙofar ya fito hannunsa dafe da kansa. Jefa ƙafafunsa kawai yakeyi batare da yana kula da inda yasa gaba ba, da ƙyar ya iya kawo kansa wajen motarsa, yana shiga yayi mata key. Sam baya wani iya ganin gabansa da kyau, yanayin yanda gateman yaga yayo kansa da motar ne yasanya babu shiri da sauri ya buɗe masa gate, mamaki kwance akan fuskarsa na irin tuƙin gangancin da yaga yanayi. +
Da wani irin speed yake tuƙa motar shikansa baisan wani irin gudu yakeyi ba, babu babban abun tashin hankali da tsoratarwa kamar yanda ƙwayoyin idanunsa suka rikiɗe suka zama jajur dasu, gaba ɗaya jijiyoyin dake jikinsa duk sun tashi sunyi raɗo raɗo, mussamman forehead ɗinsa wanda jijiyoyi suka fito sukaɗi raɗa raɗa. Irin gudun da yakeyi akan hanya ne, yasanya mutane da yawa ke kauce masa, da ƙarfi ya daki gate ɗin gidan wanda don kansa saida ya buɗe, aguje mai gadi ya fito don kowa yaji irin dukan da akaiwa gate ɗin yasan ba lafiya ba. Da gudu yashigo cikin gidan kodamuwa da gaban motarsa da ya lotse baiyi ba. Wani irin bahagon parking yayi. 2
Ummu da Almustapha ne suka miƙe atare sakamakon jin yanda aka buga ƙofar falon da ƙarfi, waigawansu yayi daidai da shigowansa cikin falon, ƙirjin Ummu ne yashiga bugawa da sauri ganin yanda yake tafiya yana gauraya hanya tamkar wanda ke cikin maye, sannan kuma ga hannunsa dafe da forehead ɗinsa.
“SOORAJ!” Ummu taƙira sunansa aɗan razane.
Bai waiwayo ba baikuma tsaya da tafiyan dayake ba kana kuma bai amsata ba, ya nufi hanyar da zata sadashi da ɗakinsa.
“RAJ!” Almustapha yaƙira sunansa, kamar yanda bai amsa Ummu ba haka bai amsawa Almustapha ba, haka ya buɗe ƙofar corridor ɗinsa ya shige. Da sauri Ummu tarufa masa baya, baifi saura taku uku tsakaninsu ba ya shige cikin ɗakinsa tare da murzawa kofar key, mamakine ya kashe Ummu hakan yasa ta tsaya cak, don tunda ta haifeshi bata taɓa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba.
Ajikin ƙofar ya zame tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa. “Me yasa bazaka fito ka faɗawa duniya cewa kai ba Namiji bane? RAGO!” waƴannan kalaman suke ta yawo acikin brain ɗinsa suna me hautsina duk wani lissafin nutsuwarsa. Idanunsa da suka kaɗa suka zama jajur ya buɗe tare da sauƙesu akan mirror, zumbur kamar wanda akawa allura haka ya tashi ahankali yashiga takawa har ya ƙarasa gaban mirror’n, tsayawa yayi yana me kallon kansa, da sauri sauri yashiga cire rigan dake jikinsa, take murɗaɗɗen surar jikinsa da buɗaɗɗun muscles ɗinsa suka bayyana acikin madubin, 6 packs ɗin dake kwance raɗa raɗa akan cikinsa yakai hannu ya shafa, ɗauke hannunsa daga cikinsa yayi ya taɓa fuskarsa da tayi jajur tsaɓan tsananin ɓacin rai da yake ciki.
“DA GASKE KAI BA NAMIJI BANE!!”
Zuciyarsa tafaɗa masa haka batare daya shiryawa jin hakanba, wani irin ihu yayi tare da sanya hannunsa ya naushi madubin, take ya tarwatse awajen, hannunsa ne ya shiga ɗigar da jini amma ko ajikinsa, wani ƙaton glass wanda yake kamar madubi ansanya rose aciki ya ɗaga tare da wurgi dashi, ƙaran fashewan Glass ɗin take ya cika ɗakin, tamkar wani zararre haka SOORAJ yaci gaba da wurgi da duk wani abun daya gani, gaba ɗaya ya watsar da kayan shafan dake kan mirror’n sa, kalmar da akace shiba Namiji bane, ita ce kawai keta yawo acikin brain ɗinsa, haka yakeji kamar zai haukace.
STORY CONTINUES BELOW
Hankalin Ummu ne yakai ƙololuwan tashi jin irin ƙaran fashewan abubuwa dake fitowa daga ɗakin Sooraj, Almustapha ne yaƙaraso da hanzari cike da mamaki yake kallon Ummu, hankalinsa atashe yace “Meke damunsa ne haka?”
Hawayene kwance acikin idanun Ummu amma saitayi ƙoƙarin maidasu cike da damuwa tace “Almustapha bansani ba, kafun nazo ma ya rufe ƙofarsa, bantaɓa ganin Sooraj acikin irin wannan yanayin ba, bana fata acemin shaye shaye Sooraj yayi, domin sam ni ajinina ban haifi Mashayi ba, don Allah Almustapha kamasa magana ya buɗe ƙofarnan!” Duk yanda Ummu taso hana ƙwalla fitowa daga cikin idanunta saida suka fito.
Hankalin Almustapha amatuƙar tashe yashiga bubbuga ƙofan yana ƙiran sunan SOORAJ.
Ya soma fita daga hayyacinsa, gaba ɗaya ya birkita ɗakin, yayi watsi da komai. Jinine ke ɗiga ahanunsa sosai, gaba ɗaya ya ɓata ƙasan ɗakin da ɗigo ɗigon jini. Wani irin jiri ne ke ɗibansa, hakan yasanya shi faɗawa kan gado ya lumshe idanunsa, jiyake kamar duniyar zata kife tsabar tsananin ciwon da kansa ke masa.
Tun yanajin yanda Almustapha ke buga ƙofar har ya daina jin komai, sakamakon wani wahalallen bacci daya ɗaukesa.
Ummu kuwa ganin yaƙi buɗe ƙofan yasanya taje ta ɗauko spire key na ɗakinsa, Almustapha ne ya buɗe suka shigo atare, mamaki da tsorone ya bayyana akan fuskokinsu sakamakon yanda suka ga ɗakin ya sauya kammani, ga kuma ɗigo ɗigon jini akan tiles, kan gado Ummu ta kalla nan ta hangoshi yayi kwanciyar ruf da ciki, hannunsa kuwa duk jini ne wanda ya bushe.
Da sauri taƙarasa tare da sanya hannu ta taɓashi “Sooraj!!” Ta ƙira sunansa murya araunane, kana taɗan leƙa fuskarsa. Wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe alokacin dataga bacci yake. Kallon Almustapha dake tsaye yayi shiru tayi, sannan tashiga ƙarewa ɗakin kallo, gaba ɗaya Sooraj ya hautsina komai, fasssun glasses da mirrors ne zube aƙasan ɗakin wanda idan baka kulaba tsab zasu raunata ka.
“Mutafi” tace da Almustapha tana me wucewa gaba, babu musu ya rufa mata baya.
Kallonta Almustapha yayi tsananin damuwa ne bayyane akan fuskarsa yace “Dama bashida lafiya ne Ummu? ko akwai wata damuwa ne?”
“Lafiyanshi ƙalau Almustapha ko da safe ma anan yayi breakfast, bansan mene yasameshi ba, ban taɓa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba. Ko na ƙira Abbanku ne?”
Da sauri Almustapha yace “Karki ƙirashi Ummu, Isha Allah babu wata matsala maybe anɓata masa rai ne, kinsan Sooraj tun muna ƙanana bai iya ɓacin rai ba”
Ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe sakamakon jin abun da Almustapha yace, tabbas SOORAJ bai iya ɓacin rai ba sam, idan ransa ya ɓaci to sai gyaran Allah. Daga nan bata sake cewa komai ba ta haura sama.
Zieyaderh ce zaune akan gado sanye take da dogon wando marar nauyi wanda yakasance rubber pencil, sai wata ƴar farar vest marar hannu, tayi shigarne saboda ana yanayi na zafi, jin motsi kamar za’a shigo ɗakin, yasanya ta ɗaukar hijab ɗinta dake kusa da ita ta sanya da sauri, tana gama sanya Hijab ɗin taji ana knocking ƙofa, bedroom slippers ɗinta ta sanya kana ta nufi jikin ƙofan, tana buɗewa tayi arba da Ummu, ɗan matsawa baya tayi zatayi magana Ummu tarigata da cewa. “Kije ki kimtsawa Yayanki ɗakinsa, sannan kuma kiyi hankali wajen shiga ɗakin akwai fasassun kwalba zasu iya raunataki!” bata wani tsaya jin ta bakin Zieyaderh’n ba ta juya ta nufi ɗakinta, Mamakine yaɗan kama Zieyaderh musamman yanda taga damuwa kwance akan fuskar Ummu, sannan kuma Ummu bata taɓa cewa ta gyara masa ɗaki ba sai yau, da wannan tunanin acikin ranta ta sauƙo ƙasa kai tsaye ta nufi ɗakinsa, ko lura da Almustapha dake zaune acikin falon ba tayi ba.
Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama, da fasassun glasses ɗin dake ƙasa tasomayin arba, baki buɗe take ƙarewa kowani kusurwa dake cikin ɗakin kallo, mamakin yanda aka hargitsa ɗakinne ya kamata, don kuwa ancire komai daga ma’ajinsa anyardashi ƙasa. Kallon Beedshet ɗin dake yashe aƙasa tayi sannan ta dawo da kallonta kan gado inda yake kwance, ƙirjinta ne taji yaɗan buga don ayanda taga ɗakin ahaukace batayi tsammanin ganin wani acikinsa ba. Idanunta ne suka sauƙa akan hannunsa wanda ke ɗauke da jini, wani irin tashi tsikar jikinta yayi, har saida ta ɗan ciza laɓɓanta. “Kenan shine yayi duk wannan abun?” tambayar da tayiwa kanta kenan tana me duban jinin dake jikin tiles ɗin. cikin takatsantsan ta ƙarasa gaban gadon tare da kafeshi da ido. “Meke damunshi? Bashi da lafiya ne?” zuciyarta ta tambayeta tambayar da bata da amsa. Ganin saƙawa da kuncewa ba nata bane yasanya ta ɗauki abun shara da packer tashiga tattara glasses ɗin, tana kammalawa ta ɗauko moper tayi mopping ɗin wajen, room freshner ta fesa acikin ɗakin take ko ina yaɗauki ƙamshi, kayan shafansa ta jere masa akan mirror sannan ta ninke bedsheet ɗin dake ƙasa ta ɗaurasa akan gado, saida ta maida komai dake cikin ɗakin nead kafun ta buɗe fridge ta ɗauko ruwa wanda bashi da sanyi sosai, audugan da ta gani acikin drawer ɗinsa ta ɗauko, ahankali taƙaraso jikin gadon tare da zama daɓas akan carpet ɗin daya kewaye gadon, dayake hannun nasa me ciwon ba’akan gadon yake ba hakan ya bata daman sanya hannunta ta kamo nasa hannun, ruwa ta ɗiga ajikin auduga sannan tashiga goge masa busashshen jinin dake hannunsa, ahankali takeyi kuma cikin nutsuwa gudun kada ta tashesa.
Ahankali yaɗan buɗe idanunsa da suka ƙanƙance, cute face ɗinta ya kalla da kuma small lips ɗinta, maida idanunsa yayi ya rufe yana mejin yanda take lallaɓa hannun nasa tamkar wanda aka bawa ajiyan ƙwai, sam batasan da cewa ya farka ba,domin gaba ɗaya tabada hankalinta ga aikin da takeyi, tas ta goge masa jini har ya zamana tana iya ganin yankewan da yayi, wani irin tausayinsa ne taji ya kamata, tasan dole idan ya farka sai ciwon yayi masa zafi, wata ƙila yanzu ma yanayi masa zafi, tunowa da haka yasanya taɗan sunkuyo da kanta, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta adaidai kan ciwon, tayi hakanne saboda ta sama masa sauƙi, kasancewar idan taji ciwo in tana hurashi baya yi mata zafi, hakan yasa tashiga yi masa.
Wani irin sanyi yakeji na ratsa jikinsa, duk da cewa ciwon bayayi masa wani zafi sosai, amma hakan da tayi masa ya sanya ya samu relief, don har wani sabon bacci yaji yana fusgarsa, luf yasakeyi akan gadon tare da sake lumshe idanunsa. Sai yanzu yakejin ya dawo cikin sense ɗinsa, sai yanzu abubuwan da yayi ɗazu ke dawowa cikin brain ɗinsa, shiru yayi yana mejin yanda zuciyarsa ke bugawa, tabbas SHI BA NAMIJI BANE yau ya sake tabbatarwa kansa da hakan, duk da cewa tuntuni yasan yana da rauni ta ɓangaren mu’amala da mace amma baiyi tunanin matsalartasa takai har haka ba, bazai taɓa iya biyawa wata mace buƙatarta ba, sannan bazai taɓa iya alfahari da kanshi amatsayin cikakken Namiji ba, baisan menene Sha’awa ba, bai taɓa jiba bai kuma san ya akeji ba, baisan ya Sex yake ba bai kuma san ya daɗi da rashinsa yake ba. Tabbas shi gwanine akowani ɓangare amma awannan ɓangaren shi rago ne. Zuwa yanzu ƙwaƙwalwarsa takusa daina aiki domin kuwa tunani na neman illata ta, Meyasa bayajin Sha’awar mace? Me yasa bazai taɓa iya yin sex da mace ba? Me yasa bayajin wani abu na musamman ajikinsa dan gane da kowacce mace? Waƴannan tambayoyin sunjima suna barazanan tarwatsa zuciyarsa wajen neman amsarsu amma har yau baisamu amsan ba, hakan yasa ya rufe sirrinsa yabar abun amatsayin ƘADDARA me girma agareshi. Ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauƙe, tare da rumtse idanunsa da ƙarfi, shi LOOSER ne, amma duk da haka baya fatan ci gaba da zama looser akoda yaushe, saboda haka ayanzu baijin zai baiwa hawayen dake cikin idanunsa daman fitowa……
(Kowani bawa da irin ƙaddaransa, haka kuma kowani labari da irin yanda aka tsarashi, tabbas nasan nan gaba kaɗan zanzo wajen da bazai taɓa yi muku daɗi ba, bakuma zanzo wajen ason raina bane ba, labarinne yazo ahaka, sai ansha gwagwarmaya, sai anfuskanci ƙalubale, sai kuma anjure ake kaiwa ga daɗi, tabbas wasunku nasan bazasu iya juran wannnan wajenba, nasan ƙorafe ƙorafen ku zaita iskeni, nasan zakuyi challenge’s ɗina, wasunku zasu faɗamin magana mai daɗi, wasunku kuwa zanji saɓanin haka daga bakunansu, tun ayanzu ina fuskantar challenge’s daga wajen wasu, tabbas nice me labari kuma nice me rubutu, idan asonane ako da yaushe nayi abun dazai faranta ranku, wannan shine kullum fata na, watarana inada important abun da zanyi amma haka nake squeesing nayi typing duk dan nafaranta muku, shin me zanji araina idan kuka jefeni da magana marar daɗi? kunaga zanji ƙarfin guiwa da farincikin sake yi muku wani fejin da zaku karanta? Tabbas nasan kuna ƙoƙari sosai sosai,musamman yanda kuke mini votes da comment, har acikin raina ku na dabanne My Wattpadians people, acikinku wasu ke faranta raina akuma cikinku wasu ke disturbing ɗina, amma nidai ina muku son so, nasan wasu mutane dagangan suke faɗan wata maganan duk dan su ɓata raina, amma babu damuwa dukanku ni inasonku…. Ni mutumce me ƙaunar duk wani maisona…. Please! Please!! Pleaseeeee!!! Idan kinsan nan gaba kaɗan zaki fito kiyi challenging ɗina akan labarinnan don Allah ki haƙura da karantawa wannan roƙo ne nayi muku masu challenge’s ɗina. Love You all and Son So My A hankali idanunta ke lumshewa da alama bacci takeji, amma kuma har izuwa wannan lokacin bata daina hura masa iskan dake bakinta ba. Ahankali yake fitar da numfashi, yana mejin sanyi na sauƙa acikin zuciyarsa, juyo da kansa ɓangaren da take yayi tare da sauƙe gajiyayyun idanunsa akanta, itama ɗago manya manyan idanunta tayi ta kalleshi, hakan yabawa idanunsu daman sarƙewa acikin na juna, wani irin mimmiƙewa gashin dake jikinta sukayi, take tsikar jikinta ya shiga zubawa, tamkar wacce aka watsawa ruwan sanyi, ba komai ya haifar mata da hakan ba kuwa, face arba da sexy eye balls ɗinsa da tayi, wanda suke lumshewa ahankali tamkar na mejin bacci. ƙasa tayi da idanunta, batare da ta sake hannunsa dake cikin nata ba, ƙofar ɗakin aka buɗe hakan yasa ta ɗago kanta da sauri ta kalli ƙofan, Almustapha ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, da sauri tatashi daga zaunen da take tare da sakin hannunsa ta koma gefe. Ƙarasowa cikin ɗakin Almustapha yayi yana me ƙare mata kallo, cikin muryarsa me sanyi yace. “Ya tashi ne?”
Kai kawai ta iya gyaɗa masa alamar “Eh” Raɓawa tayi tagefenshi ta fice daga cikin ɗakin. Binta yayi da kallo harta fice, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da juyowa ya kalli Sooraj wanda ko motsawa baiyi ba.
“RAJ” Almustapha yaƙira sunanshi.
“Ummm!” Sooraj ya amsa masa akasalance yana meƙoƙarin tashi zaune. 1
Kallonsa Almustapha yayi sosai sai kawai yayi murmushi tare da cewa. “Ya jikin naka?”
“Wani yace maka banida lafiya ne?” Sooraj ya faɗa yana me ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon.
“No ni ne kawai nake tunanin baka da lafiya, ko dai mutanen naka ne suka motsa?” Almustapha ya tambaya yana me ƙoƙarin gimtse dariyan dake bakinsa.
Hararansa Sooraj yayi baice dashi komai ba ya nufi hanyar da zai sadashi da bathroom, sarai yasan iskancin Almustapha yawane dashi, yanzu idan ya tsaya yadinga ɓata ransa kenan.
Dariya Almustapha yayi tare da jawo laptop ɗin Sooraj ɗin yashiga amfani dashi.
Luf tayi akan gado tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai, ƙwayan idanunsa ne keta yiwa nata idanun gizo, lumshe idanunta tayi tare da sakeyin hugging pillow’n dake hannunta, hancinta takai kan hannunta wanda tariƙeshi dashi, sosai hannunnata ke ƙamshinsa, wani irin kasalane taji yana sauƙa mata, tabbas ayanzu tayarda da cewa shiɗin na musammanne, kamar yanda komai da ya shafesa yake na musamman.
Tari yake sosai acikin toilet ɗin, wanda har hakan yaɗauki hankalin Almustapha dake zaune akan gado, ɗan tsayawa yayi ajikin ƙofar toilet ɗin, tare da cewa “RAJ are you Okay?” shiru baiji ya amsa masa ba, hakan yasa ya tura ƙofar bathroom ɗin, da sauri ya ƙarasa wajen Sooraj dake tsaye agaban sink yana goge bakinsa da tissue.
Idanu Almustapha ya zaro tare da duban tissue ɗin dake hannun Sooraj hankalinsa amatuƙar tashe yace
“RAJ jinin mene wannan?”
Hararansa Sooraj yayi cike da ƙosawa yace
“Amma dai ban gayyatoka ba ko?”
Fuskar Almustapha babu alaman wasa ko tsokana yasake cewa. “RAJ jinin menene wannan? please tell me dama baka da lafiya sosai har haka ne?” Gaba ɗaya Almustapha ya ɗaga hankalinsa.
“Bakina ne ya fashe!” Sooraj yafaɗa ataƙaice yana me sanya ruwa ya shiga wanke bakinsa.
Kamar statue haka Almustapha ya tsaya yana kallon Sooraj, sam bai yarda da cewa wai bakinsa ne ya fashe ba, cikin yanayi me ɗauke da tsananin damuwa yace
STORY CONTINUES BELOW
“Shi kuma tarin da kake fa?”
“Uhhhhhh! am tired, please Mustapha leave me alone!!” Sooraj yafaɗi haka yana me dafe forehead ɗinsa, sam bayason irin wannnan tambayoyin da Almustapha keyi masa.
Jiki asanyaye Almustapha ya juya ya fice daga cikin toilet ɗin, saidai har cikin ransa yasan wannan jinin daya gani abakin Sooraj bana lafiya ba ne.
Almustapha na fita Sooraj ya sanya duka hannayensa ya riƙe weast ɗinshi, iska ya fesar ta bakinsa tare da lumshe idanunsa, shikansa yasan bai taɓayin tari yaga jini ba sai yau, sai alokacin ya tuna da cewa sam bayashan maganinsa. Wanka yayi kana ya ɗauro alwala, towel ɗaure a weast ɗinshi ya fito, black jeans and black t-shirt ya sanya, duk Almustapha na kallonshi, ganin zai fita baice dashi komai ba yasanya Almustapha tashi da sauri ya bishi, atare suka tafi masallaci…..
Saturday.
Kasancewar yau ba makaranta hakan yasanya tun tashinta tashige kitchine, zuwa yanzu ta iya abubuwa da dama na dangane da girki, saboda haka kafun Ummu ta sauƙo ma ta kammala kusan rabin aikin, ɗauke da murmushi Ummu ta shigo cikin kitchine ɗin.
“Zieyaderh!” Ummu taƙira sunanta.
Barin aikin da takeyi tayi tare da juyowa, cikin ladabi tace ” Ummu ina kwana”
“Lafiya lau” Ummu ta amsa mata tana me ƙarasowa cikin kitchine ɗin.
Atare suka kammala aikin, kamar koda yaushe Zieyaderh ne ta jere duka abincin akan dinning, Ƙamshin turarensa ne yafara sanar da ita zuwanshi, hakan yasa ta kasa ɗaga idanunta. Shine agaba Almustapha na biye dashi abaya haka suka nufo wajen dinning ɗin, Ummu naganinsu tasaki murmushin jin daɗi.
“Morning Maaa!” Sooraj ya faɗa agajarce yana me ƙoƙarin zama akan kujera.
“Morning” Ummu ta amsa tana me ɗan shafa kansa.
Rungumeta Almustapha yayi tare da yimata kiss a forehead ɗinta cike da kulawa yace.
“Good Morning Ummuna!” Murmushi Ummu tayi tare da shima da shafa kansa tace.
“Morning My Son”
Tana ɗago idanunta suka faɗa cikin na Almustapha hakan yasa ta saki murmushi tare da cewa “Ina kwana”
Murmushin shima yayi mata haɗe da cewa “Kintashi lafiya?”
“Lafiya” ta amsa tana me ƙoƙarin serving ɗinsu.
Ɗan satan kallon Sooraj tayi, taga gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa, cikin sanyi tace.
“Yayah Ina kwana!”
Shiru yayi kamar bazai amsa ta ba sai kuma ya amsa mata da “Lafiya” acan ƙasan maƙoshinsa.
Kamar yanda tasani kuma taga bashida wani abun sha daya wuce fruit salad, hakan yasa ta ajiye wani glass bowl wanda ke ɗauke da fruit salad agabansa.
Serving ɗin kanta tayi sannan ta zauna, Ummu da Almustapha ne kawae keta hira, itakam dama mezatace acikin hirarsu, shikuwa SOORAJ dama kowa yasan ba magana yake ba…. Jin hirar su Ummu na damunsane yasanyashi miƙewa tsaye yabar wajen, da kallo Ummu tabisa har ya shige ɗakinsa.
Ahankali Zieyaderh itama tamiƙe tsaye don dama tuntuni ta ƙoshi da abincin, damar tashi kawai takejira. Sunanta da Ummu taƙira yasanyata dakatawa daga yunƙurin barin wajen da takeyi.
“Zauna inason magana dake” Ummu tafaɗa tana me ƙokarin aje kofin tea din dake hannunta.
Ƙirjinta ne yashiga bugawa lokaci ɗaya taji gabanta ya faɗi, aɗaɗare ta koma ta zauna akan kujera, miƙewa tsaye Almustapha yayi tare da ɗaukan kofin tea dinsa yabar wajen.
“Zieyaderh!” Ummu taƙira sunanta.
Bata iya amsawa ba saidai ɗago kai da tayi ta kalli Ummun jiki asanyaye.
STORY CONTINUES BELOW
Ummu bata wani damu da rashin amsawannata ba tace “Nayi magana da Mas’oud saidai abun da yafaɗamin akanki ya matuƙar girgizani, inaso kifaɗamin gaskiyar wacece ke? sannan kuma inason sanin ina mahaifanki suke da har zaki nesanta kanki dasu, karkimin ƙarya don banason ƙarya, Inajinki!” Ummu tafaɗi maganar tana me maida gaba ɗaya attention ɗinta ga Zieyaderh.
Ƙirjinta ne ya buga take idanunta suka cicciko da ƙwalla, bakinta na rawa tace. “Banda mahaifiya tun ina ƙarama ta rasu, natashi agaban Mahaifina da kuma matarsa sam bansan wani abu waishi soyayya ba, kullum cikin ƙunci da kaɗaici nake rayuwa, babu wani wanda yadamu da farinciki ko jin daɗi na, bansan kowa daga cikin dangin mahaifiyata ba saboda naji Babana yace ita ba ƴar garinmu bace, ban kuma san inane garinsu ba, tun ina ƙarama nayi sabo da wahalwahalun rayuwa, duk wani rashin gata ya ƙare akaina, sam babana bai ɗaukeni ƴa wacce ya haifa acikinsa ba, bansan daɗin mahaifi ba” Kuka ta fashe dashi tare da kifa kanta ajikin table, saida tayi kuka sosai sannan ta ɗago kanta hawayenta ta share kana ta cigaba da bawa Ummu labarinta, kama daga kan zancen aurenta da tsoho ɗan dashe har izuwa yanzu da take tare dasu, durƙusawa tayi akan guiwowinta cikin kuka tace “Ummu ki gafarceni saboda ni Ya Mas’oud yayi miki ƙarya.”
Hawaye ne suka cika idanun Ummu, tabbas yarinya ƙarama kamar Zieyaderh bai kamata ace an banzatar da ita har haka ba, ya kamata ne ace anbata kyakkyawan kulawa.
Kafaɗunta Ummu takama ta ɗagota cike da kulawa tashiga share mata hawayen dake kwaranya akan fuskarta.
“Ya isa daina kukan haka nan, naga kanki yayi datti ɗauko mayafinki muje shagon saloon!” Ummu tafaɗi haka cike da kulawa.
Jiki asanyaye haka Zieyaderh ta haura sama don ɗauko mayafinta. Da kallon tausayi Ummu tabi bayanta, bawani jimawa sosai sai gata ta dawo sanye da hijab ajikinta.
Ko amota shirune ya biyo baya tsakaninsu, dan kowa da abun dayake saƙawa acikin ransa. Ummu kam tuni tagama yanke shawaran abun dake ranta, wayarta ta ɗauka ta turawa Almustapha da Sooraj text akan tanason ganinsu, daga haka ta aje wayarta.
Sosai aka gyarawa Zieyaderh dogon gashinta, lokaci guda ya ɗauki ƙamshi da walwali, daga shagon saloon Super market suka wuce, sosai Ummu ta sai mata kayan kwalliya dana sawa masu kyaun gaske, daganan suka ɗauko hanyar dawowa gida.
Tana sanya ƙafarta acikin falon idanunta suka sauƙa acikin na Almustapha wanda yasha kyau cikin baƙaƙen kaya. Da sauri tayi ƙasa da kanta, don har acikin ranta batajin daɗin irin kallon da yakeyi mata, kai tsaye ta haura sama nan tabar Ummu afalon.
Ummu na zama akan kujera Ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya fito, sanye yake da army 3 guater jeans da kuma black t-shirt, fuskarsannan babu alaman farinciki ko sakewa akanta, haka yaƙaraso cikin falon, akan kujeran dake facing na Ummu ya zauna tare da ciro phone ɗinsa daga aljihun wandonsa yasoma dannawa.
Gyara zama Ummu tayi cikin yanayi na kulawa tace “Banƙiraku nan don na faɗa muku wasa ba”Kallon Almustapha tayi cikin kulawa taƙira sunanshi, da “Na’am ya amsa mata tare da ɗagowa ya kalleta.
“Nasan banice na haifeka ba, amma kuma kana mini biyayya tamkar yanda zakayiwa mahaifiyarka, haƙiƙa amatsayina na yar mahaifiyarka inada ƴancin dazan iya zartar da duk hukuncin da naso akanka, kasani tamkar yanda nakeson ɗan cikina Sooraj kaima haka nake sonka, saboda haka na zaɓa maka matar da zaka aura ina fatan bazaka watsamin ƙasa a ido ba?”
Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannuwansa ya kama na Ummu. “Bazan taɓa iya bijirewa umarninkiba Ummu, ke uwace agareni saboda haka ina maraba da duk wani zaɓinki”
Murmushin jin daɗi Ummu tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa cike da ƙaunarsa tace “Nagode sosai Almustapha Allah ya maka albarka!”
“Ameen Ummu, amma wace me sa’ace haka tayi gamdakatar ɗin samuna?” cike da zolaya yayi tambayar.
Dariya Ummu tayi tare da cewa “Kanason sani?”
“Sosaima” Almustapha yabata amsa cike da zaƙuwa.
Duk abunda suke yanajinsu yana kuma kallonsu, amma ko uhummm baice ba, azahirin gaskiya wayarsa yake dannawa abaɗini kuma gaba ɗaya hankalinsa na garesu.
“ZIEYADERH itace wacce na zaɓama kuma itace wacce zatayi daidai da rayuwarka!”
Maganar Ummu data faɗane yasanyashi ɗago da kansa ahankali ya kalleta..
“Zieyaderh!”Almustapha ya maimaita sunan abakinsa, kansa ya sunkuyar ƙasa fuska ɗauke da murmushi yace
“Na’amince!”
Tsaida duk wani abu da yakeyi yayi yana kallonsu, hakanan yaji tamkar ruwan jikinsa na ƙonewa.Sunkuyar da kansa ƙasa yayi tare da ɗan ciza laɓɓansa, idanunsa ya mayar kan wayansa, samun kansa yayi da kasa cigaba da amfani da wayan, ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi weak. +
“SOORAJ!” Oummu taƙira sunansa.
Ɗago kansa yayi ya kalleta batare daya amsa mata ba, itama bata nemi amsawar nashi ba taci gaba da cewa “Kaji abun da muka tattauna akai, amma bakace komaiba, sannan kuma inaso na yaba maka game da namijin ƙoƙarin taimakon da kayiwa Zieyaderh, insha Allah, Allah Zai baka lada!” Oummu tafaɗi maganar tana murmushi.
Ko Uhumm baice ba, sai ma kallon Oummu’n daya keyi, ganin damuwarta dana Almustapha zasu kasheshi yasanyashi tashi gaba ɗaya yabar musu gidan.
Kwance take luf akan bed ɗinta, biscuit ne ahannunta tanaci da kaɗan kaɗan, turo ƙofar ɗakin da akayi ya sanyata tashi zaune da sauri, ganin Oummu yasanya tasakin murmushi tare da cewa “Barka da shigowa Oummu”
Murmushi Oummu tayi tare da zama akan wata kujera, cike da kulawa tace. “Magana nazo muyi dake Zieyaderh!”
Gaban Zieyaderh ne ya faɗi, amma saita dake tare da cewa “To”
Murmushi Oummu tayi tare da dafa kafaɗun Zieyaderh’n tace “Inaso kishirya ƙarshen wannan week ɗin zamuje ƙauyenku dan inason naga mahaifinki!”
Dummm haka ƙirjin Zieyaderh ya bada wani irin sauti, hawaye ne suka cika idanunta alokaci guda, bakinta na rawa tace “To!”
Murmushi Oummu tayi don tafahimci cewa tsoron zuwa ƙauyen Zieyaderh keyi, cikin son kwantar mata da hankali tace “Kar kisanya tsoro aranki idan munje bazan barki ahannunsu ba zandawo dake nan, kawai dai naga ya kamata ace mahaifanki susan inda kike ne!”
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyaɗa kanta kawai, alaman ta gamsu. Oummu na fita daga ɗakin. Zieyaderh ta fashe da kuka, sosai tayi kewar babanta, ko awani hali yake ciki Allah masani? duk da cewa bai nuna mata ƙauna ba, amma ita har gobe, akwai ƙaunarsa acikin jininta, saboda koba komai Uba Uba ne koda baikasance na gari ba.
MONDAY
Cikin yanayi naɗan sauri sauri yake tafiya, don 8 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa garin Lagos. Sanye yake da black and white suit wanda suka matuƙar yi masa kyau, black cover shoe ne ƙiran kamfanin Gucci sanye aƙafansa me tsadan gaske. ƙamshi kawai yaketa zubawa, yayinda gashin kansa keta shinning na mayukan da aka shafa masa, yau kam masha Allah Yayi kyau har ya gaji da haɗuwa.
Manta biology text book ɗinta da tayi, yasanya ta taho cikin sauri don komawa ta ɗauka, sam bata kulaba saiji tayi sunyi karo da juna, wanda hakan yajawo zubewan documents ɗin dake hannunsa. Da sauri taja da baya ƙirjinta na bugu da ƙarfi, idanunsu ne suka faɗa cikin na juna, hakan yasanya taji tamkar an jona mata shocking, kallonta yayi sannan ya kalli ƙasa inda documents ɗinsa suka zube, da sauri ta durƙusa ƙasa hannunta har rawa yake wajen harhaɗa documents ɗin waje ɗaya. Agogon hannunsa ya kalla yaga 7:30 kuma sai ya biya ta office kafun ya wuce airport, gashi duk gani yake kamar bata sauri wajen tattara documents ɗin. Itakuwa bakomai ke cinta ba face tsoro hakan yasa gaba ɗaya bata sauri, ƙamshin mayen turarensa dake zautar da ita ne, ya daki hancinta sosai, hakan yasa ta ɗan ɗago da kanta, daidai lokacin shi kuma ya ɗan ranƙwafo don tattare documents ɗin, kanta ne ya bugi haɓanshi wanda hakan yasashi rumtse ido, ahankali yace “Auchhhh!!” dan ya ɗanji zafi sosai.
Sakin documents ɗin tayi tare da sanya hannuwanta ta rufe bakinta, wani sabon tsoro ne yasake kamata, baki na rawa tace “Kayi haƙuri Wallahi bansaniba ne!!”
STORY CONTINUES BELOW
Baikulata ba haka yasanya hannu ya shiga tattara papers ɗinsa da suka watse. ganin haka yasa itama tashiga tayasa tattarewa, gaba ɗaya ƙamshinsa ya jefata acikin wani irin yanayi, jin kanta take cikin wani baƙon yanayi, har wani iska ne ke shiga jikinta. Idanunta ne yakai kan wani papers da iska ke shirin kaɗasa wani wajen, da sauri takai hannunta zata kamo paper’n, shima hannunsa yakai batare da yayi zato ba yaji hannunsa ya sauƙa akan nata, atare sukaji wani shock da sauri yajanye hannunsa daga kan nata tare da ɗaukan paper’n ya miƙe tsaye, baijira komai ba ya nufi wajen motarsa wanda tuni dama driver na jiransa, yana shiga gidan baya driver yayiwa motar key suka fice daga cikin gidan. Saida taji alamun fitansu sannan ta iya miƙewa tsaye daga tsugunnen da take, batare da ta saniba wani murmushi ya bayyana akan fuskarta take kuma saiga hawaye sun ziraro daga cikin idanunta, Wallahi ko za akasheta bazata iya fassara abun da takeji dangane dashi ba, tausayi ne? rauni ne? Ita duk takasa ganewa, tasan koma menene tabbas abun da takeji akanshi na musammanne, idanunsa kaɗai da ta kalla ya sanya taji wani iri ajikinta, tabbas da zata samu mai bata amsar abun da takeji dangane dashi da taso hakan fiye da komai, watarana idan tagansa sai taji kamar tasanya masa kuka, watarana kuwa jitake kamar taje da gudu ta shige jikinsa tayi kuka sosai, wataƙila hakan zai ɗan sama mata salaman abun dake ranta. Sam tama manta da cewa text book zata ɗauko sai kawai ta koma tashiga mota.
Luf tayi ajikin kujeran motar, ƙamshinsa da har yanzu takejinsa acikin hancinta shiyayi fatali da duk wata nutsuwarta, sam tarasa me yasa takejin ƙamshin nasa har yanzu duk da cewa baya tare da ita, hannunta takai tashafi fuskarta, sai alokacin ta gano daga inda ƙamshin ke fitowa, sake kai hannunta kan hancinta tayi tare da shunshunawa, tabbas hannunta da ya taɓa ne ke ƙamshin, wani irin sanyi taji acikin zuciyarta, ɗaura hannun tayi akan fuskarta tare da lumshe idanu, ahaka har suka iso cikin school ɗin. Yau kam tayi late duk da cewa bahaka tasoba, don sunada biology, kuma shine first period, bakuma taso tayi missing lecture ɗin biology ko kaɗan, ai kuwa tana zuwa bakin class ta iske malami aciki, da ƙyar ya barta tashiga cikin ajin, tana zama akan chair ta sauƙe ajiyar zuciya, hannu Nasmah tasanya ta ƙasa ta muntsineta akan cinyarta, ƙasa ƙasa tayi dariya tare da rumtse ido alaman taji zafin muntsinin, hakan da tayi kuma sai ya tuna mata da MR.HELPER ɗinta, yanayin yanda ya rumtse idanunsa da kuma yanda yace “Auchhh!!” Baƙaramin kyau yanayin yayi masa ba, musamman yanda pink lips ɗinsa suka motsa abun saiya ɗauki hankalinta, sai ayanzu moment ɗin kedawowa cikin brain ɗinta da kyau, wani murmushi tasake tare da lumshe idanunta.
“Kenan shima yanajin zafi idan abu yasameshi?” A zuciyarta ta tambayi kanta, wani murmushin ta sakeyi alokacin da ta tuna da kyawun idanunsa, a iya tsawon rayuwarta itakam bataga irinsa ba, bata kuma tunanin zata taɓa ganin wani irinsa. Ataƙaice dai har biology teacher’n yafita, bata tsinci komai daga cikin darasin daya koyar ba, gaba ɗaya hankali da tunaninta yau akan Mr.Helper yake.
Su Shukra da kansu yau sun fuskanci cewa tana cikin farinciki, don koda aka fita break zagewa tayi tayita zuba musu surutu.
7:59 AM
Gyara zama yayi tare da ɗaura sit belt ajikinsa, bayansa ya jingina ajikin luntsumemiyar kujeran dake cikin jirgin, 8:00 daidai jirginnasu ya ɗaga zuwa sararin samaniya, tafin hannunsa yakai ya rufe fuskarsa, ko hakan zaisa yaɗan rage stress ɗin dayake ciki, ahankali yaji wani baƙon ƙamshi na ratsa cikin hancinsa yana me cakuɗa da numfashinsa, mamakine yakamasa don sam baisan daga ina ƙamshin ke fitowa ba, ɗan waigawa bayansa yayi, dayake ɓangaren business class ne kowa sha’aninsa kawai yake, babu kowa kuma akusa dashi dasai yace na kusa dashine ke ƙamshin. Sake shunshuna hannunsa yayi, sai alokacin ya tabbatar da cewa tabbas hannunsa ne ke ƙamshin, bawani turarene me ƙarfi ba, irin dai turaren nanne da idan mutum yasa saima ka matso kusa dashi kafun kajiyo ƙamshin. “Itace!” yafaɗa in a silent voice ɗinsa, sake kai hannun kan hancinsa yayi tare da ɗan taɓe lips ɗinsa. Azuciyarsa yace.
“Su ƙamshi manya” Jarida ya ɗauka yashiga karantawa tare da watsar da duk wani tunani dake ransa. 2
STORY CONTINUES BELOW
Hadari ne sosai ya haɗu agarin kasancewar anacikin yanayi na damuna, 3:30 pm, fitowarsu sallan La’asar kenan.
Tana idar da sallan ta fito daga cikin masallacin, sosai take matuƙar son yanayi irin wannan, ahankali sanyin iska ke busa ko ina, hijab ɗinta iska keneman yayewa, da sauri tasanya hannuwanta ta kameshi ƙam ajikinta. Yanayin na fusgarta hakan yasa kai tsaye ta nufi wajen da garden ɗin makarantar yake.
Ƴan tsirarun ɗalibai ne awajen, kowa harkan gabansa kawai yake. Gefe da garden ɗin wasu kujeru ne masu kyaun gaske da aka tanada don zama, tana zama aka soma yayyafi hakan yasa tatashi da sauri don komawa cikin makaranta. Idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsaye yake ya sanya duka hannuwansa acikin aljihun wandonsa, idanunsa ƙyam akanta fuskarsa ɗauke da beautiful smile, cike da mamakin ganinsa tasaki murmushi tare da sanya hannu ta kare kanta, kasancewar zuwa lokacin ruwa ya fara sauƙa kaɗan kaɗan. ganin haka yasanyashi takowa yazo gab da ita, cikin sexy voice ɗinsa yace.
“Kina tsoron ruwa ne?”
Murmushi tayi wanda har saida ya bayyana white teeth ɗinta, kanta ta kaɗa masa alamar “Eh” ruwane ya ɓarke me ƙarfin gaske hakan yasa lokaci guda ta ruɗe, shikansa ƙarfin ruwan yabasa mamaki, hannunta ya kama zuwa wani ɗan rumfa dake wajen, duk da shigarsu rumfar iya kawunansu kawai ruwan zai tare amma banda gangar jikinsu. Cikin yanayi na tsoro ta naɗe hannayenta akan ƙirjinta, kallonsa tayi da fuskarta dake jiƙe da ruwa. Murmushi yayi mata tare da ɗage mata giransa ɗaya, itama murmushin tayi masa tare da sake takure kanta waje ɗaya, don bawai sun tsirane daga ruwanba, har yanzu yana dukan jikinsu, tuni uniform ɗinta yajiƙe sunbi jikinta sun lafe, shikansa Pharouk gaba ɗaya ya jiƙe duk da cewa akwai denim Jacket ajikinsa hakan bai hanashi jiƙewa ba. bakinta har rawa yake saboda sanyi.
“Zieyaderh!” yaƙira sunanta akasalance.
Ɗago fuskarta tayi ta kalleshi, idanunsa ya sauƙe akan beautyful lips ɗinta wanda suka jiƙe suke kuma ɗigar da ruwa, wani irin tashi yaji tsikar jikinsa yayi, take lissafin kansa suka shiga kuncewa, wani irin saliva dake maƙale a maƙoshinsa ya haɗiya, sam bata ɗauke idanunta akansa ba, yanayin sanyin da take ji yasanyata lumshe idanunta tare da ɗan buɗewa alokaci guda, hakan da tayi baƙaramin kyau yaƙarawa face ɗinta ba, take yaji wani irin different feelings na sauƙa ajikinsa, ji yake kamar yajawota jikinsa ya bata professional kissing, amma mene sunansa idan yayi hakan? jingina bayansa yayi da jikin bango tare da lumshe idanunsa, bugun zuciyarsa ƙaruwa take, wani irin maganaɗisun sha’awarta ne ke fusgarsa, lokaci guda mood ɗinsa ya sauya. Cikin zaƙuwa da tsayuwan Zieyaderh ta juyo ta kalleshi acikin yanayinta na shagwaɓa tace “Am tired!!” Ahankali ya buɗe idanunsa wanda sukai ja ya sauƙesu akanta, wani irin yarrr taji ajikinta sakamakon kallon cikin idanunsa da tayi, batasan irin wannan yanayin ba hakan yasa ahankali tace “Are you okay?”
Akasalance yayi murmushin daya bayyana dimples ɗinsa.
“Yes am okay!” yafaɗa yana me ƙare mata kallo, murmushi tayi masa sannan ta juya tacigaba da kallon ruwa sam ta manta bata maida hannuwanta ƙirjinta ta kare baiyanar dasukayi ba, don saboda yanayin sanyin da ake ciki yasanya tsikar jikinta mimmiƙewa, hakan yasa nipples ɗinta ma suka miƙe tsaye, har idan kayi mata kallon tsab zaka iya ganinsu. Sauƙan idanunsa akan ƙirjinta baƙaramin gigita masa tunani yayi ba, take yaji tunaninsa ya tsaya cak, da sauri ya ɗauke idanunsa daga kanta tare da sanya baki ya cije laɓɓansa. (Nasan team RAJ, zasuce inama da ita da Sooraj ne😝) Wani irin tsawa da aka buga ne ya matuƙar firgitata har batasan sanda ta dawo baya da sauri ba, sambata kula ba ta faɗa jikinsa, ƙamƙame jikinta tayi ƙaƙam tare da rumtse idanunta. “Innalillahi” kawai take ambata acikin zuciyarta don ta tsorata, ashe ba ita kaɗaice ke ambatan hakan ba harda Pharouk don alokacin da bayanta ya mannu da ƙirjinsa baƙaramin ruɗewa yayi ba, har numfashinsa saida yashiga seizing na ƴan wasu minutes. Hanneyansa dake rawa yaɗaura akan shoulder ɗinta, hakanne ya bata damar dawowa cikin hankalinta, da sauri ta matsa gefe, cikin wani irin kunya ta jawo hijab ɗinta ta rufe fuskarta. “Me na aikata haka?” ta tambayi kanta cike da nadama. 2
Matsowa yayi gab da ita tare da sanya hannu ya ɗago haɓanta, hijabin ya ja baya fuskarta ya bayya, da sauri ta kulle idanunta don batajin zata iya haɗa idanu dashi.
Murmushi yayi mata ahankali ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta, kiss yayi mata a forehead ɗinta, tare da kai bakinsa daidai saitin kunneta ahankali yace “Ki kulamin da kanki!” Yana gama faɗan haka ya juya acikin ruwan ya tafi, yayi hakane saboda matuƙar ya ƙara some minutes awajen, zai iya hugging ɗinta. (Chab lallai Pharouk yau zakasha zagi awajen ƴan team ɗin SOORAJ) 9
Buɗe idanunta tayi ahankali cike da fargaba da kuma tsoron abun daya mata, babu wani namiji daya taɓa yi mata kiss saishi, mekenan hakan yake nufi? ta tambayi kanta cike da mamaki, kallon bayansa tayi don zuwa yanzu yayi mata nisa, tafiya yake kamar baidamu da ruwan dake dukansa ba.
*SOORAJ*
Tsaye yake acikin wata baranda, dagashi sai wani white crazy jeans dake sanye ajikinsa, bashida ko riga sosai murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana, glass cup ne ahannunsa wanda ke ɗauke da ruwan inibi, ruwa da iska ake sosai, amma ko kaɗan baijin wannan sanyin ajikinshi. Hakanan yakejin kansa cikin wani bad mood, baikuma san dalilin hakan ba, tunanin dake maƙale azuciyarsa ayanzu yafi komai damunsa, meyasa yake ganinta acikin idanunsa? meyasa yakeji tamkar anrubuta wani abu daya shafeta acikin zuciyarsa? yana da buƙatar sanin meyakeji, da kuma dalilin dayasa yakejin hakan acikin rai da zuciyarsa.
Ahankali ƙarfin ruwan ke tsagaitawa, ganin haka yasa cikin sauri ta nufi farfajiyan makarantar, harda ɗan sassarfa take haɗawa wajen shigewa cikin ajinsu, Nasmah da Shukra dake tsaye bakin window sukayo wajenta da sauri cikin damuwa suka haɗa baki wajen tambayanta ina taje “Garden” ta basu amsa ataƙaice. Sunyi mamakin hakan amma sai kawai suka share suka cigaba da hiransu.
Ruwan na tsagaitawa aka tashesu ko 5 ma batayi ba, saboda sosai garin ya ɗau sanyi. Atare suka fito ita dasu Nasmah, daidai lokacin wata baƙar Car ƙiran Jeep ta kunno kai cikin makarantar, tsayawa sukayi a compound ɗin makarantar Zieyaderh na ta baza idanu ko zata hango Kamalu driver. Ƙasa yayi da glass ɗin motar tare da kafeta da idanunsa, ahankali ya danna horn, hakanne ya ɗauki hankalin ɗalibai da yawa har kowa yajuyo yana kallonsa, idanunta ne suka sauƙa akanshi, tsananin mamakine ya kamata, tabbas tasan ita yazo ɗauka, to ina Kamalu driver? ya ma akayi yasan antashesu? Duk bata dame amsa mata waƴannan tambayoyin, hakan yasa tayiwa su Nasmah sallama tanufi inda yake. Tana buɗe murfin motar wani sassanyan ƙamshin turare ya daki hancinta, saidai wannan turaren sam ba irin wanda yake gigita tunaninta bane. Ɗan satan kallonsa tayi tare da cewa “Ina wuni”
Bai amsa mata ba sai dai murmushi da ya bayyana akan fuskarsa. Har suka soma tafiya babu wanda yasake ce da ɗan uwansa wani abu, saidai kuma yana yawan satan kallonta lokaci zuwa lokaci, aranta mamakin yanda halinsu ya kusan zuwa ɗaya take. “Kenan su duka familyn su haka suke?” ta tambayi kanta azuci. “Uhmmm gwara wannan ma ae yana murmushi amma wancan Mr.Helper ɗin kam, ko murmushinsa bantaɓa gani ba” Ita kaɗai take magana da zuciyarta har suka iso gaban wani tafkeken mall.Agaban ƙaton mall ɗin yayi parking motar tare da dubanta, murmushi ɗauke akan fuskarsa yace “Muje ki rakani sayayya” +
Mamakine ya bayyana akan fuskarta, amma sai ta share bata nuna ba, buɗe murfin motar tayi tare da fitowa waje. Yana gaba tana biye dashi abaya, haka suka nufi cikin ƙaton mall ɗin. Direct ɓangaren kayayyakin mata suka nufa, ita dai binsa kawai take, aranta tana me mamakin ganin sun shigo wajen sayayyar mata, ɗan juyowa yayi ya kalleta, matsawa gefe yayi tare da yi mata nuni akan ta shige gaba. Kallonsa tayi alaman me hakan ke nufi. “Muje mana ko bazaki tayani zaɓa bane, matata zan sayawa kuma agemate ɗinki ce, shiyasa nafiso ki zaɓa mata masu kyau!” Ya faɗi maganar yana me jujjuya wata brown ɗin abaya dake hannunsa. Murmushine ya bayyana akan fuskarta.
“Kenan dama yana da mata?” tayiwa kanta tambayar cike da ɗan mamaki. Jin cewar matarsa zai sayawa, yasanya duk wani abu da tagani idan ya mata kyau saita ɗauka, dogin riguna kala uku ta zaɓa masa masu kyaun gaske, wanda suke asalin ƴan dubai new designer. Da ace tasan kuɗinsu da bata ɗauka ba, don kowanne kuɗinsa yakai 35k, kaya masu kyau ta zaɓa masa, duk wanda ta ɗauka sai yayi murmushi yace yayi, daga ɓangaren kayayyaki ɓangaren chocolates and sweets suka nufa, wannan kam shida kansa ya ɗauka, sai ya duba wanda baida zaƙi sosai sannan yake sanyawa acikin basket ɗin dake hannunsa.
Koda suka kammala, cewa yayi tajirasa awajen da ake biyan kuɗi, komawa cikin mall ɗin yayi ya shiga dube duben ƴan abun da yake da buƙata.
Yana dawowa ya biya kuɗin, wani daga cikin yaran dake aiki awajenne ya kai musu kayan mota.
Ahankali yake murza steering motar, yana me gutsuran diary milk chocolate ɗin dake hannunsa, kallonta yayi tare da ɗan sakin murmushi “Hummm” yafaɗa yana me miƙo mata chocolate ɗin alaman ta amsa. Murmushi itama tayi masa tare da kaɗa kanta alamar “A’a”
“Bafa kyauta bane, gutsura zakiyi ki bani!” ya faɗi haka yana me mayar da chocolate ɗin bakinsa.
Idanunta ta waro cike da mamaki, sai kuma abun yabata dariya wanda har hakan yasa ta dara, kallonta yayi tare da cewa “Kina mamaki ne? bazan iya baki duka bane shiyasa!” Yayi maganan murmushi ɗauke akan fuskarsa.
“Nagode ma” Tafaɗa tana me gimtse dariyan dake bakinta, gaba ɗaya yasata nishaɗi don yanayin yanda yayi abun sai yazama tamkar wani small babyyy.
Daga haka babu wanda yasake ce da ɗan uwansa wani abu har suka iso gida. ƙoƙarin buɗe murfin motar take muryarsa ya dakatar da ita, inda yake cewa tashiga da kayan da suka sayo ciki, gidan baya inda aka sanya kayan ta buɗe tare da ciro ledodin ta wuce cikin gidan da su. Bata samu kowa afalon ba hakan yasa kai tsaye ta wuce sama, tsayawa tayi ajikin ƙofar ɗakin Oummu tare dayin knocking. “Yes,Come in!” Oummu dake ciki ta bada amsa ataƙaice. Tura ƙofar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama. “Oummu naganinta ta saki murmushi tare da cewa.
“Ƴan makaranta andawo kenan?”
Murmushi itama tayi cike da girmamawa tace “Eh nadawo, Oummu sannu da gida!”
“Waƴannan ledodinfa na menene?” Oummu ta tambaya fuska ɗauke da mamaki.
“Ummmm dama Ya Almustapha ne yace nashigo dashi ciki!” tafaɗa cikin sanyin murya tana me aje ledodin.
Murmushi kawai Oummu tayi tare da cewa “Aini nace yaje ya ɗaukoki, kasancewar naga anyi ruwa garin duk yaɗau ki sanyi, gashi Kamalu ma bayanan, ki cire uniform ɗin sai kici abinci ko!”
STORY CONTINUES BELOW
Kai ta kaɗa alamar “To” sannan ta juya ta fice daga cikin ɗakin.
Tana shiga ɗaki ta soma cire uniform ɗin, gaba ɗaya wani irin sanyi takeji, ruwan daya daketa baƙaramin shiga jikinta sanyinsa yayi ba, gashi harwani ciwo ciwo takejin kanta nayi. Da ruwan ɗumi tayi wanka kana ta sanya wata doguwar riga me kauri, rigan irin jallabiyannan ne na mata, amma tana da kauri sosai, sannan kuma haɗe take da hula, hulan ta sanya ta rufe kanta. Saida tayi sallan Magriba sannan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito don samawa cikinta abinci. Ahankali take sauƙowa daga kan matattakalan falon, tunkafun ta gama sauƙowa, ƙamshin turaren daya zame mata abunso ya daki hancinta, lumshe idanunta tayi tare da waresu alokaci guda, mamakine yakamata na rashin ganinsa afalon, don tasan tabbas indai taji ƙamshinsa to yana wajenne. Harta gama sauƙowa daga kan steps ɗin bata iske kowa acikin falon ba, kai tsaye kitchine ta wuce, kasancewar yau ba a haɗa abinci akan dinning ba. Fried cous cous and egg sauce aka dafa, kaɗan ta ɗiba don bata wani cika cin abinci da yawa ba, buɗe ɗayan food flask ɗin tayi, nan taga pepper soup ne na chicken’s aciki, rufewa tayi don wannan ɗinma kaɗai ya isheta. fridge ta bude ta ɗauko ruwa, daidai lokacin Oummu tashigo cikin kitchine ɗin, ganin Zieyaderh a kitchine ɗin yasanya ta cewa.
“Yauwa Zieyaderh zoki kaiwa Sooraj coffee yana ɗakinsa” 2
Wani irin ƙululuuuuu haka ƴaƴan cikinta suka hautsina, ambatonsa ba ƙaramin faɗar mata da gaba yake yi ba, batasan mene dalili ba koda zancensa ake sai taji gabanta ya faɗi, ko kuma taji zuciyarta ta tsinke, ganinsa kuwa baƙaramin je fata acikin wani irin Yanayi yake ba. Bata gama idar da tunanin nata ba, Oummu ta miƙo mata wani tray me ɗan faɗi, wanda samansa ke ɗauke da kayan haɗin coffee da kuma ɗan madaidaicin cup me kyaun gaske, sai kuma small flask. “Idan kinje ki haɗa masa, ai dai kinga yanda na haɗa masa ranan ko?” Oummu ta tambaya tana me miƙa mata tray ɗin. Kamar wadda aka zarewa laka ajiki haka ta amshi tray ɗin tare da cewa “Eh nagani” Ficewa tayi daga cikin kitchine ɗin, yayinda zuciya da ƙirjinta keta bada wani irin sauti.
Dawowarsa daga Lagos kenan, dama baije don ya kwana ba, socks ɗin dake ƙafansa ya cire sannan ya zare suit ɗin dake jikinsa, maɓallan long sleve ɗinsa yashiga cirewa, yana kammalawa ya cire rigar tare da zare white singlet ɗin dake jikinsa, belt ɗin wandon shi ya zare yana me ƙoƙarin zame wandon ƙasa yaji ana knocking ƙofarsa, bai kula ba ya cigaba da cire kayansa, jin still ana knocking ɗinne yasanya shi ɗaukan wani 3 guater jeans ya sanya, ko gama zuge zip ɗin wandon baiyi ba, ya nufi wajen ƙofar ransa aɓace, ko damuwa da yanda saman maranshi ta bayyana baiyi ba. Itakuwa Zieyaderh dake tsaye gaba ɗaya atsorace take, harta gama yanke shawaran cewa zata koma kawai tace da Oummu ƙofar a kulle take. Da wani irin fushi ya buɗe ƙofar, idanunsu suka faɗa cikin na juna, kallonta yayi from head to toe sai kawai yasaki wata tsuka me sauti tare da komawa cikin ɗakin, ganin haka yasa jikinta ya shiga ƙyarma ba shiri ta bi bayansa, hannunta har rawa yake wajen aje tray ɗin, ƙoƙarin haɗa masa coffee ɗin take ya juyo tare da soma tahowa inda take, cak ta tsaya daga haɗa coffee ɗin da take, tare da sunkuyar da kanta ƙasa, tabbas kunnuwanta sautin takunsa suke jiye mata, wanda ke ɗauke da alaman cewa gareta yake zuwa, hakan yasa wani uban tsoro ya lalluɓeta, wanda har ya kaita ga kasa ɗaga kai ta kalleshi. Taku biyu kacal ya rage atsakaninsu yace. “Ke!!”
Da sauri ta ɗago kanta aɗan daburce tace “Umm!” sake matsowa kusa da ita yayi wanda hakan yasa gaba ɗaya takusa ficewa hayyacinta, gab da ita yazo har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sosai ta ruɗe sakamakon ganinsa agabanta, baƙaramin cika mata idanu yayi ba, gaba ɗaya ba ta iya ganin komai don yacika mata gaba da faffaɗan chest ɗinshi, haka ta zama wata ƴar cukula agabansa, gaba ɗaya jikinta ɓari yake.. Cikin wani irin husky voice ɗinsa yace. “Ke baki da hankali ko? Haka aka koyar dake bugun ƙofa?”
Yanzu kam ba iya gangar jikinta bane ke rawa, harma da laɓɓan bakinta, cikin daburcewa tayi ƙasa da idanunta don bazata iya kallonsa ba, idanunta ne suka sauƙa akan waist ɗinshi wanda har saman mararsa ta bayyana, kasancewar har yanzu bai ƙarasa jan zip ɗin wandon nasa ba, wasu jijiyoyine kwance akan maran nasa wanda suka mimmiƙe, ga wani irin murɗewa da cikinsa yayi, da sauri ta rumtse idanunta, tana me ƙara ƙanƙame jikinta. “Badake nake magana ba!!” Yafaɗa atsawace. Baƙaramin tsorata ta wannan tsawan yayi ba, har batasan lokacin da ta ƙanƙame jikinta sosai ba, bakinta na rawa tace “Dan Allah kayi haƙuri, Allah Bazan sake ba!”
STORY CONTINUES BELOW
Kallon fuskarta yayi tare da ɗan cizan laɓɓansa, hannayensa ɗaure akan waist ɗinsa yace. “Buɗe idanunki!”
Kasa buɗe idanunnata tayi saima rawan jiki data ƙara, tare da kullesu ƙam.
“I say open your eyes!!!” Yafaɗa murya akausashe. Tun kafun ya gama idar da zancen, ta buɗe idanunta tare da sauƙesu akansa. Sarƙewar idanunsu waje guda yasanya idanunta sukayi wani irin juyawa, take suka wani irin lumshewa luuuuu kamar zata sume. Cikin tsawa yace “Wallahi idan kika sumemin saina wanka miki mari stupid girl!!” ae kuwa tamkar wanda ya watsawa ruwan sanyi saigata ta tsaya cak akan ƙafafunta, tare da sake maida idanunta ta rufe, saidai ya kasheta amma tabbas bazata iya kallon cikin ƙwayan idanunsa ba, musamman ma ayau, idan kuwa tace zata sake kallonsa to tabbas sumewa zatayi koda kuwa kasheta zaiyi bayan ta farfaɗo.
Tsaki yayi tare da nuna mata hanyar ƙofa murya akausashe yace. “Out!”
Ae kamar jira take haka ta tattari ƙasan riganta aguje ta fice, baki ya buɗe yana mamakin yanda tasa gudu kamar wacce aka turowa dodo. “Wannan yarinyar anya tana da lafiya kuwa?” Tambayar daya yiwa kansa kenan cike da mamaki, ƙofarsa ya rufe tare da murza mata key, bathroom ya shige tare da sakarwa kansa shower.
Aguje ta haura steps ɗin dake cikin falon, tana kaiwa ɗakinta ta shige tare da rufo ƙafar, kan gado ta faɗa tare da lumshe idanunta, har yanzu jikinta baiwani gama daina ɓari ba, saida ta ɗauki kusan 8 minute tana maida numfashi, kafun tasamu daman dawowa cikin nutsuwarta. Shiru tayi tare da cusa kanta acikin pillow, yau kam gaba ɗaya brain ɗinta ta cushe, yayinda tunaninta kuwa gaba ɗaya ya gudu.
Ruwan shower ne ke dukan lafiyayyar fatan jikinsa, yayinda hannunsa ɗaya ke dafe da bango, akasalance ya buɗe idanunsa, kasancewar yajima tsaye ruwa na dukansa, hakan yasa idanunnasa suka ɗanyi ja. So yake ya goge wannan tunanin daga cikin ransa, so yake wannan idanun su fice daga cikin nasa idanun, so yake duk wani abu dake cikin zuciyarsa ya goge, baishirya ɗaukan wannan ƙalubalen ba, bakuma yajin zai shirya har abada, hannu yasa ahankali ya kashe shower’n, tare da ɗaukan wani nead towel ya ɗaura akan waist ɗinshi. Haka ya fito daga cikin bathroom ɗin jikinsa na ɗigan ruwa, wani ɗan ƙaramin towel ya ɗauka ya shiga goge jikinsa, sama sama ya shafa mai ajikinsa, sannan ya sanya long jeans, shida kansa ya haɗa coffee ɗin yasha, jin ana ƙiraye ƙirayen sallan Isha ne yasanyashi miƙewa, wata farar rigar Dolce and Gabbana mai kamar na sanyi ya sanya, kasancewar ana yanayin sanyi hakan yasa ya jawo hulan dake jikin rigan ya rufe kansa dashi. Yana fitowa ya haɗu da Almustapha shima masallacin zaije saboda haka atare suka wuce.
Washegari.
Tun seven yagama shiryawa, wayarsa ya ɗauka tare da turawa shugaban makarantar text message, ko 4 minute ba ayiba saiga ƙiran shugaban makarantar ya shigo wayansa. Fuska yaɗan taɓe sannan ya ɗaga wayar, bayan sun gaisa ne, Principal ɗin yace.
“Naga saƙonka amma banƙi ta taka ba, saidai bakowa muke bawa irin wannan uniform ɗin daka buƙata ba, mukan bawa ire irenta ne yara da sukayi aure basu kammala school ɗinba, to idan zasu ci gaba da zuwa shine muke basu, amma tunda haka ka keso babu damuwa”
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa “Nagode, sannan kuma karka manta idan ansamu wani problem ka ƙirani, kamar yanda kaƙirani a wancan time ɗin da aka kaita hospital, so ba matsala always zaka iya nemana!”
“Okay dont mention” Principal din ya faɗa tare da aje wayan.
Shima wayartasa ya aje tare da ɗaukan cover disigner shoe ɗinsa ya shiga sanyawa, iya kyau kam yayi sa, saidai kuma amma fuskar nan ahaɗe take babu alamar fari’a akanta.
Zaune suke su duka uku akan dinning ɗin, sanye take da kayan uniform ɗinta na riga da wando, ahakali take tsakalan chips ɗin dake gabanta, gaba ɗaya batajin daɗin zama acikinsu don haryau ganinta take amatsayinta na bare. Gaba ɗayansu ƙamshin turarensa ne ya cika hancinsu. Cikin ƙasaitarsa yake tahowa hannunsa ɗauke da wata ƴar briefcase me kyau, kujera yaja ya zauna cikin ƙasan maƙoshi yace “Barka da safiya Oummu” murmushi tayi masa tare da cewa “Barka, hope kunyi waya da commisioner?”
Kansa ya kaɗa mata alamar “Eh”
STORY CONTINUES BELOW
Mood ɗinta ne yaɗan sauya tare da cigaba da cewa “Ya faɗa maka cewa yarannan da suka harbeka sun faɗi wanda ya turosu ko? gaskiya nikam nashiga fargaba da tsoro, indai har akan aikinka za a iya turowa akasheka, me kenan kake tunanin zai faru anan gaba? zasu iyayin komai!” ta ƙare maganar fuskarta cike da damuwa.
Kafun Yayi magana Almustapha yace “Nima nayi mamaki ƙwarai da akace wai MR.J.J ne yaturo ayimaka hakan, wani irin tsananin gabane ke tsakaninka dashi ne wae? Meyake nema dakai ne, tunfa sanda aka baka BM yakejin haushinka, gaskia yanzu kam baikamata mubarshi ba!” ya ƙare maganar cikin yanayi naɗan ɓacin rae.
Aje mug ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa “Its Okay, anyi arresting ɗinshi jiya” yana gama faɗan haka ya miƙe tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa, briefcase ɗinsa ya ɗauka ya fice, duka suka bishi da kallo, hakanan yake shi koda yaushe baiso ayi magana me tsawo dashi, sai kace marar gaskiya.
Ture plate ɗin abincin dake gabanta tayi tare da ɗaukan school bag ɗinta dake gefe ta rataya.
Zieyaderh Oummu taƙira sunanta, “Na’am” ta amsa asanyaye. “karki manta inkin dawo ki sameni aɗakina kinsan gobene tafiyarmu” “To” kawai tace sannan ta juya tafice daga cikin falon, tana fitowa compound ɗin gidan shikuma motarsa na fita daga cikin gidan, mota tashiga ranta duk ba daɗi.
Ko amakaranta yau bata wani sake ba, bayan sundawo break ne aka turo wae principal na ƙiranta, saida gabanta yafaɗi amma haka ta daure taje, wata leda ya bata wanda ke ɗauke da wasu sabbin uniform har kala uku yace mata daga yau su zatana sanyawa. Sosai tayi mamaki amma sai bata nunaba ta amsa kawai ta fice, koda taje aji suka duba kayan, sket ne irin high waist ɗinnan wanda ƙasansa yake da faɗi, sai kuma wata ƴar rigar makaranta fitted da hijab ɗinta wanda idan tasa zai ɗan sauƙo mata kaɗan. Mamakine ya kashesu su dukansu. Shukra ce tace “Wannan fa kayan bakowa kesawa a school ɗinnan ba, kodai kinzama house wife ne bamusani ba?” hararanta Zieyaderh tayi tare da turo baki gaba cikin takaici tace “Ni bawata house wife ɗin dana zama!” dariya suka sanya su dukansu, daga haka sukaci gaba da hiransu, kaɗan kaɗan take sa musu baki. Har aka tashi sukuku haka takejin kanta, koda ta koma gida ko falo bata sauƙo ba, haka ta ƙare kwanciyarta aɗaki… Washegari Saturday. Ƙarfe 8 daidai ta kammala shiryawa cikin kayan da Oummu ta bata tace tasanya, riga da sket ne na tsadaddiyar atamfar Vlisco, wacce taji ɗinki, sket ɗin irin pieces ɗinnan ne yayinda rigan takasance fitted, sosai kayan suka amshi jikinta, kasancewar atamfar kalan Maroon gareta hakan yasanya ta sanya maroon hijab ajikinta, sosai tayi kyau duk da cewa batayi wani kwalliya akan fuskarta ba, flat shoe ɗinta ta sanya tare da kallon kanta amadubi, ita kanta tasan tayiwa kanta kyau. Saida suka biya ta wani super market Oummu tayi sayayya sannan suka ɗauki hanyar zuwa KD inda acan ƙauyen su Zieyaderh yake. Ƙarfe 1 na rana daidai suka iso cikin ƙauyen nasu na Saminaka, tun daga lokacin ƙirjin Zieyaderh ke dukan uku uku, da ƙyar take iyayiwa Kamalu driver kwatance har suka iso ƙofar wahalallen gidansu, tun shigowarsu ƙauyen yara kebinsu yayinda manya kuwa ke bin haɗaɗɗiyar motarsu da kallo. Shawo kwanan Malam Garba kenan hannunsa ɗauke da wani buhu, turus haka yaja ya tsaya yana me bin motar daya gani fake aƙofar gidansa da kallo. Da sauri ya ƙarasa daidai lokacin kuma su dukansu suka fito daga cikin motar, koda zata shekara ɗari ne batanan bazai taɓa kasa gane jininsa ba, bakinsa abuɗe fuska ɗauke ɗa mamaki yake kallon Zieyaderh, itama kallonsa take lokaci guda hawaye suka wanke mata fuska, ji take kamar taje ta rungume Baban nata, amma kuma tanajin tsoro. “Ziyada!” yaƙira sunanta muryarsa na rawa. Kasa amsa masa tayi sai kawai ta fashe da kuka. Shima hawayene kwance acikin idanunsa. Kamar wadda aka wurgo daga sama haka Inna Ma’u tafito daga cikin gidanta, don tuni labari yakai mata cewa wata haɗaɗɗiyar mota fa faka aƙofar gidanta. Bakinta awangale taƙarasa gaban yarinyar da take kallonta kamar Zieyaderh, hannu tasa taɗan taɓa fuskar yarinyar dake kuka, “Laaaaa ha’ila wallahi itace, shegiyar gari kin gama gararanbanki kindawo ko?” Inna Ma’u tafaɗa tana me ƙarewa Zieyaderh kallo, mamaki kuwa aranta kamar zai kasheta. Ƙasa Zieyaderh tayi da kanta, Malam Garba shine wanda ya kama hannunta tare da duban Oummu dake tsaye yace.
“Hajiya kushigo daga ciki!” Babu musu Oummu ta bi bayansa yayinda yake riƙe da hannun Zieyaderh, aikuwa Inna Ma’u ma rufa musu baya tayi bayan ta tsaya ta gama ƙarewa motar da sukazo da ita kallo, harwani yawu ta haɗiya natsananin kwaɗayi dason abun duniya, musamman ma da ta hango ɗan ragowan lemun fanta dake gaban motar.
Gudu gudu sauri sauri haka taje ta ɗauko tabarma ta shumfuɗawa Oummu baki har kunne tace “Hajiyan Birni zauna mana!” Murmushi Oummu tayi tana me kallonta sannan ta zauna aranta tace “Kamar bayanzu tagama zagi ba” Malam Garba da kansa ya kawo musu ruwa, ita dai Zieyaderh laɓewa tayi abayan Oummu, don har cikin ranta tana jin tsoron abun dazai biyo baya.
Gyara zama Oummu tayi tare da ɗagawa baban Zieyaderh gaisuwa, amutumce ya amsa, kafun tasake wata magana Inna Ma’u tayi saurin cewa. “Mutanen Binni Sannu marabanki da zuwa Hajiya!” Still murmushi Oummu tayi tare da jinjina kanta alaman yauwa. Batare da ta bari kowa acikinsu yace wani abuba tace “Lallaima Zieyaderh wato dakika gudu kaina kikeso na aurawa tsoho ɗan dashen? ko kuwa kina tsammanin nida ubanki muna da kuɗin da zamu biyasa abun daya kashe ne, wallahi mudai kin cucemu akan guduwarki saida duk wani ɗan abun dana mallaka ya ƙare saboda ɗan dashe cewa yayi sai mun biyasa kudin daya kashe, kin cuceni kin cuci mahaifinki wallahi!!” Imma Ma’u tafaɗi haka tana me matse wasu munafukan hawayen ƙarya data ƙaƙalosu da ƙyar. Sake cewa tayi “Amma Allah ne zai mana sakayya, koda yake ma ai yanzu nasan kintara kuɗi sosai ko bakomai zan fanshe asarata” tana murmushi ta ƙare maganar. Oummu kam mamaki al’ajabi haɗi da tsoro al’amarin matar ya bata, wato dai ita ko agaban wayene bazata iya ɓoye maitanta ba. Cikin sauri taɓuɗi baki zata sake cewa wani Abu, da sauri Malam Garba yace “Ya isa haka Ma’u, dafari ya kamatane mufara sanin ina taje bawai irin waƴannan kalaman yakamata ayi mata ba” afusace Inna Ma’u tajuya zata faɗa masa baƙar magana sai kuma tatuna da wani abu tafasa. Saita fara yaƙen ƙarya tana me ƙarewa komai dake jikin Zieyaderh kallo. 2
Murmushin takaici Oummu tayi tare da kai dubanta ga Baban Zieyaderh, sannu ahankali tayi masa bayani akan cewa ɗantane ya
ya tsinci Zieyaderh bawai yawon iskanci ta tafi ba. Ajiyar zuciya me ƙarfi Malam Garba ya sauƙe tare dayiwa Allah godiya daya sanya ƴarsa ta faɗa hannu na gari. Itakuwa Inna Ma’u afakaice take hararan Oummu aranta kuwa cewa tayi “Kuji ƙaryan banza, yo koma gaskiya ne wayasan abunda sukeyi dashi ɗannaki, kai banma yarda ba yanda yarinyarnan tayi ɓul ɓul da ita akwai abun da take aikatawa wata ƙilama cikine da ita” tana gama ƙimtsa zancen zucinta tayiwa Zieyaderh ƙuri, ba inda take kallo kamar cikinta, wai adole saita gano ko cikine da ita, burinta bai wuce taga tumbinnata yaɗan taso ba ta tabbatar da zarginta. 3
Godiya sosai Malam Garba ya shiga yiwa Oummu na irin riƙon amanar da tayiwa ƴarsa, don har acikin ransa yana me nadamar irin rashin kulawan daya nuna mata abaya, sannan kuma yana ƙaunar ƴarsa sosai, dan itace kaɗai jininsa aduniya, amma yazaiyi da sharri da kuma tsoron Inna Ma’u da yake, duk itace ummul aba’isin faruwar komai. Miƙewa yayi yace zaije ya samo musu fura. Aikuwa yana fita Inna Ma’u tace “Hajiyan birni ince dai ɗannaki daya tsinceta gidanki ya kawota ba gidansa ba?”
Mamakine ya kama Oummu cike da mamakin tambayar tace “Mekike nufi?” da sauri Inna Ma’u ta washe baki tare da cewa “A’a babu abun danake nufi kawai dai tambaya ne, ke Zieyaderh cire lufayan mana kisha iska” Tafaɗa cike da zaƙuwan son ganin yanda cikar halittan Zieyaderh’n ya koma, tayi rantsuwa matuƙar taga cikin Ziryaderh yaɗan tasa to wallahi saita cucesu maƙudan kuɗaɗe. (Chaii guys Inna Ma’u fa ta tsananta😆)
Kallon Oummu Zieyaderh tayi, idanu Oummu ta mata alaman karta cire mayafinta, aikuwa saita yi burus da maganan Inna Ma’u. Wani irin malolon baƙin cikine ya cika zuciyar Inna Ma’u, don sarai ta ga lokacin da Oummu tayiwa Zieyaderh’n idanu. Aranta tace “Wallahi ko zaku mutune saina laƙaba muku wani sharrin dasai kunbani kuɗi ƴan iska”
Babu jimawa Malam Garba ya dawo hannunsa ɗauke da ƙwaryan nono, babu wani ƙyama haka Oummu ta zage tasha nonon daganan tace da Malam Garba idan ba damuwa tanaso tayi magana dashi. “Magana kuma dashi kaɗai?” Inna Ma’u ta tambaya tana zare ido. Babu wanda ya kulata saima iso da Malam Garba yayiwa Oummu zuwa soro tayanda babu wanda zaiji abun da suka tattauna, cike da fahimtan juna Oummu tayi masa bayanin duk wani abu dake tafe da ita, har acikin ransa yayarda da matar da kuma kamalanta saboda haka atake ya amincewa buƙatarta baƙaramin daɗi Oummu taji ba, nan suka tsaida magana cewar zata turo manya don atsaida magana, inda shikuma yace ko babu wasu manya ya yarda da ita ya bawa Ɗanta Almustapha Auren Ƴarsa Zieyaderh, duk lokacin da suka shirya kawai suzo ayi biki.Da tsananin farinciki ɗauke akan fuskar ko wannensu Oummu da Malam Garba suka shigo cikin gidan, Inna Ma’u na ganin hakan wani ƙaton baƙinciki ya ɗarsu azuciyarta, hakanan taji ajikinta cewa hanyar ƙaruwa suka tattauna, ae kuwa nan ta ƙudura aranta cewa Oummu na tafiya sai tayi maganin Malam Garba, yadae santa ae yakuma san wacece ita. +
Kallon Zieyaderh Oummu tayi fuska ɗauke da murmushi tace “Inaga ya kamata ae ace mutafi tun yanzu, kada tafiyan dare ya kamamu”
Jin abun da Oummu tace yasanya ƙirjinta bugawa, ahankali ta ɗago idanunta tare da ɗan satan kallon mahaifinnata, cikin rashin sa’a tasamu shiɗinma kallonta yake, da sauri tayi ƙasa da kanta, murmushi yayi tare da cewa “Bakomai kuje Zieyaderh Allah Yakiyaye hanya ya tsare, nima inanan zuwa tunda yanzu nasamu adreshin inda kuke.”
Wani irin sanyi ne Zieyaderh taji na ratsa zuciarta, sam batayi tunanin mahaifinta zai barta ta koma ba.
“Chab amma kuwa Garba kayi banzan hali, yanzun barinta zakayi ta koma, oh wato kaidai ba ka gaji da jin zagin da mutane ke mana agarinnan ba, karka manta fa duk akan ɓatanta sunanmu ya ɓaci, to babu inda zataje tananan tadawo kenan!” Inna Ma’u ta faɗa amasifance, don sam bata tsammaci haka ba.
“Haba Ma’u meyasa ne bazaki sanja ba, dan Allah Kibar yarinyarnan tayi tafiyarta, tafara karatu acan birni, tsayar mata da karatunta bashida wani amfani” Malam Garba yafaɗi haka cikin ɗan lallashi saboda yasan halin kayansa sarai ba mutumci.
Cike da kumfar baki Inna Ma’u tace “Dole kace haka mana saboda ƴar kace, ai dama ninasan banice na haifeta ba, kuma zaman birni kam wannan algungumar ƴar taka ta gama yinshi…..” Bata gama rufe bakinta ba taji sauƙar wani abu me ɗan nauyi akan cinyarta, idanu ta zaro lokaci guda tare da haɗiye maganan dake bakinta, take yanayin fuskarta ya sauya daga ɓacin rai zuwa murmushi. “To Alhamdulillah, irin wanga farare bugun can babban birni, Hajiyan Birni Allah ya ƙara arziki!” Inna Ma’u tafaɗa bakinta har kunne, kuɗine masu yawa Oummu ta aje mata don rufe bakinta, ai kuwa lokaci guda sai ga bakinnata ya rufu . cike da nishaɗi tace.
“To yanzu sai yaushe zaku kuma dawowa?” yanayin yanda tayi maganan tana me ƙoƙarin cusa kuɗin cikin lalitantane yabasu daria amma sai suka gimtse, ɗauke da ɗan murmushi Oummu tace.
“Nan bada jimawa ba Insha Allah, Nangaba kaɗan kema nasan zaki kaimana ziyara!”
“Sosaima kuwa, kice ziyarori ma ba iyaka ziyara kaɗai ba, don fa basau ɗaya zanzo ba!!” Inna Ma’u tafaɗa cikin jin daɗi, dama ita abun duniya shine kanta.
Har wajen mota suka rakasu, bayan motar Oummu ta buɗe wanda ke shaƙe da kaya, Kamalu driver tasanya ya shiga ciro kayan yana kaiwa cikin gidansu Zieyaderh, kayan abincine kala kala da kuma wata leda dake ɗauke da kayan sawa, atamfofi da shadda irin na maza, godiya kam ba irin wanda baban Zieyaderh baiyi mata ba, duk da yanuna mata cewa kayan sunyi yawa, amma saitace masa ba komai, koda ta bashi kuɗi ƙin amsa yayi babu yanda batayi dashi ba amma haka yaƙi amsa, Inna Ma’u kuwa daɗine ya isheta, musamman ma ganin ana shigar da kayan abinci cikin gidanta. Haka su Zieyaderh suka baro cikin ƙauyen zuciarta cike da kewan babanta. Har bacci tayi a hanya kafun su iso, gaba ɗaya zaman mota ba daɗi ji take duk jikinta yayi mata wani iri.
Suna isa gida kowa ɗakinsa ya wuce, don gaba ɗayansu agajiye suke, da ruwan zafi tayi wanka kana tabi lafiyar gado.
Sunday.
Yawanci duk ranan weekend atare suke cin abinci akan dinning, tun 8 tatashi tayi wanka, riga da sket na 1million stones tasanya wanda suka amshi jikinta sosai, tayi kyau. Wani ɗan madaidaicin mayafi ta sanya ta rufe jikinta, a kitchine ta samu Oummu cike da ladabi ta gaida ta, fuska ɗauke da fari’a Oummu ta amsa mata, yauma kamar koda yaushe itace ta shirya gaba ɗaya abincin akan dinning. Ƙamshin turaren Almustapha daya shiga hancinta shi yasanyata ɗago da kai ta ɗan kalleshi, ƙasa tayi da kanta tare da gaidashi, amsa mata yayi yana me jan kujera ya zauna, sosai yau ɗin tayi masa kyau acikin shigarta, duk da cewa bai taɓa ganin kwalliya akan fuskarta ba amma gaskiya tana da kyau sosai.
STORY CONTINUES BELOW
Oummu da Almustapha ne suke taɓa hira kaɗan kaɗan yayinda ita kuma take serving ɗinsu, tunaninsa ne kwance aƙasan zuciyartaz hakanan taji wani iri da bataga ya fito ba, tunaninta ne ya katse sakamakon wani daddaɗan sanyin da taji yana ratsa jikinta, gefe guda kuma ni’imtaccen ƙamshinsa dake zautar da’ita ne yashiga cakuɗa da numfashinta.
Sanye yake da blue crazy jeans and Blue t-shirt mai kyau da tsada ƙiran company’n D&G, sosai yayi kyau kwarjininsa yasake bayyana, yayinda gashin kansa kuwa sai shinning yake, kujera yaja ya zauna, dakansa yayi serving kansa, wajen haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda kansa ke ƙasa, yau babu waya ahannunsa amma duk da haka yi yake kamar hankalinsa baya garesu, gaba ɗaya wajen ya ɗauki shiru, kowa abincinsa yakeci yayinda akabar mutane biyu daga cikinsu da saƙar zancen zuci, gaba ɗaya hankalinta yana garesa, so take ta ɗago idanunta ta kallesa amma fargaba ya hanata.
Tissue Oummu ta ɗauka ta goge bakinta tare da dubansu su dukansu, cikin nutsuwa tace “Ina da buƙatar hankulanku agareni dukanku!” Almustapha ne ya fara aje cokalin dake hannunsa tare da duban Oummu, itama Zieyaderh ɗago kanta tayi ahankali tana me kallon Oummu’n, shikam ko motsawa baiyiba, kana bai kuma daina shan tea ɗinsa ba.
Gyara zama Oummu tayi tare da cewa.
“Sooraj da Almustapha inaso nayi maganannan ne agabanku saboda ko ba komai kamar yayye kuke awajenta, sannan awajenta zataji maganar amatsayin sabuwace, saɓanin ku da kuka taɓa jinta” ɗan numfasawa tayi kana tace..
“Zieyaderh!”
Tun kafun ta kammala maganganun nata ƙirjin zieyaderh ke bugawa, asanyaye tace. “Na’am!”
Tashi Oummu tayi daga inda take zaune, tare da jawo wata kujera ta zauna gab da Zieyaderh’n, hannayen Zieyaderh Oummu ta kamo cike da son gamsar da ita tace.
“Haƙiƙa kowacce uwa tanaso ɗanta ko ƴarta su samu abokan zama na gari, burin kowacce uwa adunia shine ƴarta mace ta dace da mijin aure, haka ma kuma ɗanta namiji ya dace da macen aure, tamkar ƴa haka na ɗaukeki Zieyaderh, bazan taɓa son wani abu dazai cutar dake ba, bazan miki dole ba, saboda kema kina da ra’ayi kamar kowa, halayyanki da kuma irin nutsuwarki yasanya naji ina kwaɗayin da ki ƙara zama acikin zuri’ata, duk da cewa munatare dake ayanzu, amma anan gaba ba lallaine mukasance tare ba, dole watarana aure zai ɗaukeki ya nesantaki damu, bazanyi baƙinciki ba idan kika samu adalin miji daga wani waje na daban, amma zanfi so ace daga cikin zuri’ata kika samu wannan adalin mijin, ba daga wani waje daban ba, kamar yanda nace bazan miki dole ba, ba kuma umarni nake baki ba, saidai ganin ya cancanta yasanya ni yin tunanin haɗaki aure da ɗana Almustapha!”
Dummmmmm tamkar ankwaɗa mata katuwar guduma akan ƙirjinta haka taji, yayinda agefe guda kuwa taji sauƙan kalaman Oummu acikin kunnuwanta tamkar almara, wani irin abune taji ya sarƙemata maƙoshi, take tasoma tari har saida manya manyan idanunta suka rikiɗe daga farare zuwa jajaye, da sauri Oummu ta ɗauko ruwa ta bata, cikin ikon Allah tanasha tarin ya ɗan lafa, jingina bayanta tayi da jikin kujera tare dayin ƙasa da kanta, me Oummu ke faɗane? Kodai kunnuwanta ne basuji mata da kyau ba? Aure kuma da Almustapha? Waƴannan tambayoyin sune cike aranta, ganin komai take kamar ba da gaske ba. Dafa shoulder ɗinta Oummu tayi cike da kulawa tace “Karki taɓa cutar da kanki Zieyaderh, idan har kinaga hakan zai sa ki cutu to karki ɓoye ki sanardani, bazan taɓa miki dole ba, nayi hakanne kuma badon na cutar dake ba saidon ina kwaɗayin ganinki cikin zuri’ata, duk da nasan cewa banice na haifi Almustapha ba, amma inayi masa son da nake yiwa ɗana SOORAJ, kuma ina masa kwaɗayin zamowarki mata a garesa!!”
Hawayene suka cika idanun Zieyaderh, har takai ga sun soma sauƙa akan hannunta, wani irin bugawa zuciyarta keyi, ita kanta batasan awani irin hali take ciki ayanzun ba, gaba ɗaya kalaman Oummu sunzama tamkar wani sinadari na bayyanar da raunin zuciyarta.
Ganin hawaye na ɗiga daga idanun Zieyaderh yasa Oummu cewa.
“Ya isa daina kukan, idan kingama cin abincin kije ki kwanta, komai ya wuce nafahimci halin dakike ciki!” tana gama faɗan haka ta miƙe tare da soma ƙoƙarin barin wajen. Da sauri Zieyaderh ta riƙo hannun Oummu, cak Oummu ta tsaya tare da juyowa, ɗago manya manyan idanunta tayi bakinta na rawa tace.
“Kiyi haƙuri Oummu ba ina kukane saboda banason abunda kikazomin dashi ba, nayarda ke uwace agareni, saboda haka NA AMINCE!” taƙare maganar ƙirjinta na mata wani irin suka, yayinda gaba ɗaya gaɓɓan jikinta sukayi weak, so take tafashe da kuka me sauti, so take ta kalli koda ɓangaren da yake ne kozataji sanyi, so take yace wani abu, to amma metakeso yace ɗin, itama kanta batasani ba.
Cike da farinciki Oummu tashafa kanta cikin ƙaunar biyayya irin nata tace.
“Nagode sosai Zieyaderh nakuma ji daɗi da baki watsamin ƙasa a idona ba, haƙiƙa ke yarinyar kirkice, Insha Allahu Kuma zakiyi alfahari da wannan haɗin, kije ɗaki ki huta kinji!” Oummu ta ƙare maganar cike da lallashi. Babu musu kamar wacce ƙwai ya fashewa ajiki haka ta tashi daga zaunen da take, har yanzun bazata iya ɗaga idanunta ta kalli ko wanne daga cikinsu ba, cikin ƙwallan da suka sake cika idanunta ta haura sama daɗan sauri burinta taje tayi kuka kozataji sauƙi aranta. 1
Tunda suka fara maganar har kawo iyanzu bai koda ɗago kansa ya kallesu ba, sannan baidaina abun daya keyi ba, da kaɗan kaɗan yake sipping tea ɗin da tsabar zafi har tiriri yake, hayaƙin dake fita acikin kofin tea ɗin shine ya sanya gaba ɗaya fuskarsa ta ɗanyi zufa, sam baijin wannan zafin shayin akan harshensa hasalima tamkar wanda yakeshan ruwan randa haka yaji test ɗin shayin ya sauya a bakinsa.
Kallon Oummu dake tsaye tana murmushi Almustapha yayi jikinsa asanyaye yace
“Oummu kinaga kamar ba matsala kuwa?” Still murmushi Oummu tayi tare da dafa shoulder ɗinsa cikin kulawa tace.
“Babu wata matsala Almustapha ka kwantar da hankalinka, kaidai ka shirya bikinka yakusa zuwa Insha Allah” Tana gama faɗan haka ta wuce zuwa ɗakinta.
Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannu ya dafa saitin zuciyarsa, har acikin ransa yaji wani irin farinciki, da sauri yatashi ya nufi ɗakinsa sam yama manta da Sooraj dake zaune agefensa.
Shikaɗai ya rage zaune akan dinning ɗin, ahankali ya aje cup ɗin dake hannunsa, tare da ɗaukan tissue ya goge bakinsa, miƙewa tsaye yayi kai tsaye ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, baijin zai samu relief idan ba shower ya sakarwa kansa ba, bathroom ya shiga tare da kunna shower, tsayawa yayi saitin shower ɗin ruwa na dukan kai da jikinsa, ahankali yake fidda wani numfashi me zafi. 4
Tana rufe ƙofar ɗakinnata da gudu ta faɗa kan gado, kanta ta cusa acikin pillow tare da sakin kuka me sauti. Sosai tayi kuka wanda ita kanta batasan na menene ba, batasan metakeji acikin zuciyarta ba, saidai tabbas tasan tanajin wani irin yanayi na babu daɗi, ya zatayi idan bata amincewa Oummu ba, ko ba komai su ɗin sunkasance mutane masu tsananin karamci agareta, idan har bata amince da maganan Oummu ba menene sunanta? BUTULU? tabbas Oummu tabata kulawa, sannan duk da batasan wacece itaba ta zauna da ita bata ƙyamaceta ba, shin saɓamata daidai ne? koma badon Oummu ba kodanshi ya cancanci tayiwa mahaifiyarsa biyayya, koba komai shiɗin wani ne na musamman awajenta, idan taƙi aminta da maganan mahaifiyarsa tabbas tasan bazaiji daɗi ba, amma kuma meyasa takejin wani abu dangane dashi? meyasa baice wani abuba alokacin? “Mekikeso yace?” wata zuciar ta tambayeta, shiru tayi da kukan da take tare da soma sauƙe ajiyan zucia akai akai.
Kusan 30 minutes ya ɗauka ruwa na dukan jikinsa, da ƙyar ya iya kashe shower’n tare da ficewa daga cikin bathroom ɗin, sauya shigarsa yayi zuwa wani white yard wanda yaji ɗinkin half jumper da wando, sosai kayan sukayi masa kyau, saidai rashin walwalan dake kan fuskarsa na yau ya zarce na kullum, ɗan makullin motarsa ya ɗauka tare da wayarsa kana yafice daga cikin ɗakin.
Tuƙa motar yake amma batare dayasan ina ya nufa ba, ganin ya soma gajiyawa ne yasanyashi gangarawa gefen titi yayi parking ɗin motar, ahankali ya kifa kansa akan steering motar, shikansa baisan mene dalilinsa na tsayuwa awajen ba, baisan dalilin daya sanya yakejin kansa acikin wani irin bad mood ba, mekenan? me hakan yake nufi? hakanan yaji kansa acikin damuwa, to amma abun tambayar shine damuwar tasa na menene? shikansa baisan akan mene yake damuwan ba, dalilinsa na sanya kansa cikin damuwa yayi ƙaranci, tabbas yanaji ajikinsa cewa idan har ya bari tunanin dake ƙwaƙwalwarsa yasamu mafaka acikin ƙirjinsa to tabbas zuciyarsa zata buga.Ɗago kansa yayi daga jikin steering motar tare da sakin wani murmushi mai ɗauke da tarin ma’anoni, agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba, ƙarfe 11 dae dae, ɗan ƙaramin tsuka yayi tare da tada motar ya cillata kan titi.
Zieyaderh kuwa tana gama koke kokenta baccine ɓarawo ya saceta wanda sai yanzun ta tashi, ji tayi yanayinta ya sauya tamkar wata marar lafiya, bathroom tashiga tayo wanka, tare da dawowa ta zauna akan gado, tv ta ƙurawa ido amma azahirin gaskiya hankali da tunaninta ba ga tv’n yake ba, tunaninsa ya matsanta mata, lallai tana da buƙatar me fayayyace mata halin da take ciki, Shukra, itace wacce ta fara faɗo mata arai, tabbas tasan idan tasamu Shukra to zata fayyace mata komai, to amma idan Shukra ta bata amsar da zai hautsuna tunaninta fa? ajiyar zuciya ta sauke tare da soma ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta, sam yau haka taji zaman gidan ya isheta, komai jinsa take ba daɗi.
Wuse zone 4
SOORAJ, zaune yake akan wata kujera dake kusa da haɗaɗɗen dinning table ɗin dake cikin falon, cup ɗin coffee ne agefensa yayinda yake signing ɗin wasu papers dake gabansa, Mas’oud ne ke zaune akan kujeran dake facing nasa, wayar dake hannunsa ya ajiye tare da kai dubansa ga Sooraj, cikin yanayi na ɗan damuwa yaƙira sunansa.
Batare daya tsaida aikin da yakeyi ba, batare kuma daya ɗago ba yace “Ummm”
Gyara zama Mas’oud yayi tare da cewa “Oummu tayimin magana akan auren Almustapha da Zieyaderh, sannan tace dani gobe Abba zaizo nakuma ce mata zan sameshi muyi magana, gaskiya RAJ nayanke shawaran zan sanar da Abba komai adangane da rashin lafiyanka!”
Aje pen ɗin hannunsa yayi tare da ɗago kansa ya dubi Mas’oud.
“Faɗa masa matsalata bashida wani amfani Mas’oud, kabari kawai badai aure suke so nayi ba, nashirya zanyi” Yafaɗi haka cikin halin ko inkula.
“Yin aurenka bashine mafita ba Sooraj samun lafiyanka shine abunso, ya zakayi da matar idan har baka samu lafiya ba?” Mas’oud ya tambaya cike da tsananin tausayinsa.
Murmushin gefen baki Sooraj yayi tare da ɗan cizan lips ɗinsa, adai dai wannan lokacin shikaɗai yasan me yakeji.
Ɗan numfasawa Mas’oud yayi tare da cewa “Amma RAJ auren Zieyaderh da Amustapha abun na damuna sosae!”
“Why?” Sooraj ya tambaya ataƙaice.
“Sooraj” Mas’oud yaƙira sunansa. Ɗago kai yayi ya kalli Mas’oud ɗin batare daya amsa ba, shima Mas’oud din kallonsa yake, tabbas shikam akwai abun daya jima yana hangowa acikin idanun SOORAJ, amma baitabbatar da abunba sai ayanzu, wani tarin tausayin Sooraj ɗinne yasake kamasa, haƙiƙa Sooraj baisan komaiba agame da so, shi mutum ne wanda yake rayuwarsa shi kaɗai, baya sharing damuwarsa da kowa, saboda haka ba lallai ya fuskanci cewa wani abu na damunshi ba, koda ma yafahimci hakan ba lallaine yasan menene abun ba. Kawar dakae gefe Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye key ɗin motarsa ya ɗauka tare da cewa “Nagama signing papers ɗinnan, ka kula sai munyi waya!”
Kasa ce dashi wani abu Mas’oud yayi harya fice, shikam Allah Yasani tausayin SOORAJ yake, tabbas yau ya hango damuwa me tarin yawa a cikin idanun SOORAJ.
Monday
Tun kafun 7 yau tagama shiryawanta, bata da wani buri wanda ya wuce taje ta sanar da Shukra damuwanta kozata ji sauƙi acikin zuciyarta, duk yanda Oummu taso ta tsaya tayi break ƙi tayi haka ta tafi makarantar da yunwa acikinta.
STORY CONTINUES BELOW
Shiru Shukra tayi tare da ɗan nazantar maganganun da suka fito daga bakin Zieyaderh.. “Bansan ya zanyi ba Shukra, bansan me yasa nakejin haka dangane dashi ba” Zieyaderh tafaɗa cikin yanayi na damuwa.
Murmushi Shukra tayi tare da dafa shoulder ɗinta, gyara zama tayi tare da cewa “Zaki iya yarda da cewa kin kamu da son sa?”
Idanu Zieyaderh ta zaro waje tare da dafe ƙirjinta dake bugawa, cikin yanayi na tsoro tace “SO fa kikace Shukra?”
“Eh SO, karki yarda ki ƙaryata zuciyarki akan alamomin so da take gwada miki, tabbas Son shi kike Zieyaderh, don so ne kaɗai ke kawo waƴannan alamomin, idan ba so ba, me zae sanya dan kinganshi gabanki yana faɗuwa? me zaisa tunaninsa ya samu mafaka azuciyarki ba dare ba rana? Idan baso ba me zai sanya tsananin tausayinsa wanzuwa acikin ranki? Wannan duk alamomin SO ne Zieyaderh, hmmm bana faɗa miki SO ya wuce duk wani tunaninki yana zuwa da alamomi masu yawa, haƙiƙa sonda kike masa irin sane wanda yake sanya ciwo azuciya, kiyarda kawai sonshi yana daga cikin ƘADDARA’nki!”
Shiru Zieyaderh tayi tare da rumtse idanunta, tabbas bazata iya ƙaryata Shukra ba, domin itama zuciyarta ta gamsu da hakan… “Menene amfanin wannan son? menene amfanin son wanda baisan kanayi ba, meyasa zuciyata tayi mini haka, tabbas idan nasoshi na so kaina dayawa saboda ba ajina bane!” Zieyaderh ta faɗa murya araunane.
“So baruwanshi da aji ko rashinsa Zieyaderh, kiyi fata wata ƙila shima ya soki!” Shukra tafaɗa cikin son ƙarfafa mata guiwa.
“Soyayyata bata da amfani Shukra, saboda ɗan uwansa zan aura, wani riba zan samu idan naci gaba da sonsa Shukra?” hawaye har sun cika idanunta.
Ajiyar zuciya Shukra tayi tare da cewa “Kicire sonsa azuciyarki Zieyaderh, haka shine samun sauƙin kai da zuciyarki”
Hawayen dake cikin idanunta ne suka gangaro ahankali tasa hannu tashare, “Nayarda inasonka, amma zan barwa zuciyata ita kaɗai, zan jure duk wani zafi da ƙunci, idan har soyayyarka zata zauna azuciata bazata fice ba, ko ba komai watarana ita zata tausheni” maganan da takeyi acikin zuciyarta kenan… Haka taƙare gaba ɗaya wunin ranan cikin damuwa, sam walwalanta ya ragu babu wani jin daɗi atattare da ita. Koda aka tashi amakaranta data koma gida aɗaki ta zauna, ko abinci bata fito taci ba, damuwar SOYAYYARSA ne kwance aƙasan ranta.
Tun ɗazu yaketa juyi akan makeken gadonsa, shikansa baisan tunanin me yake ba, yasan ƙaddara tana iya sauyawa ako da yaushe amma baya fatan tasa ƙaddaran ta sake sauyawa, saboda zai iya jure komai amma banda sabon baƙon yanayin dayake samun kansa aciki kwana biyun nan, yasani shi mai rauni ne ako da yaushe… Kansa ya cusa acikin pillow tare da sakin wani numfashi me zafi, baitaɓajin ciwon ƙaddaransa ba sai ayanzu, yanaji ajikinsa cewa zuciyarsa nason wani abu, to amma metakeso? shine abun daya kasa sani, sau da dama yakanjinta awani ɓangare ne na zuciyarsa, amma asannu sannu sai yakejin gaba ɗaya ta mamaye zuciyarsa, kowani bugun numfashin da zaiyi da fargaba yake tafiya, ada baisan wani damuwa da zafin zuciya ba, amma asannu yanzu duk ta dalilinta yasansu, yana da buƙatar sanin me hakan yake nufi, baisan mezai kira abun ba, amma wani lokaci yakanji dama ace bai santa ba kwata kwata, yakanji inama da ace baizama silan taimakonta ba wataƙila da bata shigo rayuwarsa ba, akullum ji yake kamar an rubuta wani abu daya shafeta acikin ƙirjinsa, saidai babu wanda zai sanar dashi me hakan ke nufi. Idanunsa da suka kaɗa sukai ja ya ware tare da ɗaukan wayansa ya turawa peter saƙo, akan yayi masa booking flight, kallon agogo yayi yaga ƙarfe 7 na dare, ahankali ya sauƙo daga kan gadon tare da ƙarasawa gaban drawer ɗinsa, wata black trolly ya jawo tare da buɗe sip yashiga ɗebo kayansa yana zubawa acikin trolly’n, yagama sawa aransa cewa acikin waƴannan satuttukan bazaiyi zaman Nigeria ba….
***
Dariya sosai Yasmeen keyi wanda hakan ya matuƙar harzuƙa Aneesa, cikin yanayin fushi tace “Wallahi indai ina da rai bazan taɓa barin SOORAJ ba dole sai na koyardashi yanda zaiyi ya zama namijin gaske!”
Gimtse dariyan da takeyi Yasmeen tayi tare da cewa “Bakida hankali Aneesa, ko kin manta nice wadda nafara son SOORAJ acikin zuciyata? Ke Sha’awar SOORAJ kawai kikeyi Aneesa nikuma ba iya sha’awaba sonsa nakeyi, bandamu ba don kince shiba Namiji bane, ni indai zanna ganinsa akusa dani akullum zan iya jurewa, please Aneesa kibarmin SOORAJ dan Allah Ina burin kasancewa dashi”
Tsuka Aneesa tayi tare da cewa “Duk da cewa shiɗin bashida amfani amma duk da haka inajin sha’awarsa, aranannan naso ace dagaske fyaɗe zaimin, tabbas nasan danaji daɗin da wata mace bata taɓajiba, don hakan ni awajena bazai zamanto fyaɗe ba, hmmm amma haka guy ɗinnan yatafi yabarni da yagaggen riga ko breast ɗina bai iya taɓawa ba!!” Aneesa taƙare maganar cikin yanayi na ƙufula.
Dariya Yasmeen tasakeyi tare da cewa “Bazan hanaki ba Aneesa, amma inaso ki sani bazan janye daga son SOORAJ danake ba saidai mu duka biyun Allah Yabawa me rabo sa’a”
***
Kasancewar Yau Abba zaidawo hakan yasa Oummu tun safe take ta shirye shiryen dawowarsa, tsaye take a kitchine tana ƙoƙarin harhaɗa abincin da tayi akan tray… Almustapha ne yashigo cikin kitchine din fuskarsa ɗauke da ɗan damuwa. Kallonsa Oummu tayi cike da mamakin ganin yanayinsa tace “Almustapha lapia kake kuwa?”
Murmushi yayi tare da cewa.
“Tsoro nakeji Oummu”
Shaye da mamaki Oummu tace “tsoron me?”
Ƙasa yayi da murya tare da cewa “Tsoron abun da muka shirya, nayi wani tunani, yakamata mugayawa RAJ gaskiya Oummu kinsan zuciyarsa, kar azo ayi abunnan kuma yace bayaso, sannan karkuma bayan anyi yazo yace zaiga laifina”
Murmushi Oummu tayi tare da cewa “Karka damu Almustapha, naɓoye hakanne bawai don wani abuba saidon inason wannan auren yafi waƴancan auren nasa ƙarko, jikina yajima da bani cewa awannan karon SOORAJ bazai saki matar da zan aura masa ba, kayi haƙuri Almustapha mucigaba da gudanar da shirinmu ayanda muka tsara!”
Murmushi Almustapha yayi tare da ɗaukan yankakken apple yakai bakinsa cikin yanayi na jin daɗi yace “Amma gaskiya Oummu kada asa lokacin bikinnan da yawa, don kinsan bazan iya jurewa ba watarana kada nayi abun dazai sanyashi gane plan ɗinmu!”
“Karka damu banajin bikinnan zai wuce 3 weeks saboda nima akwai abun danake hangowa, saidai kuma ita yarinyar ce bansan yazataji ba idan taji haƙiƙanin wanda ta aura.”Amatuƙar gajiye ta dawo daga makaranta, gaba ɗaya ƙafafunta ciwo suke, kasancewar yau ɗin kusan awa guda suka ɗauka tsaye acikin Lab, tana shiga cikin ɗaki tasoma rage kayan jikinta, wani white towel ta ɗaura aƙirjinta wanda ya kawo har kan santala santalan cinyoyinta, bathroom ta wuce kai tsaye, wanka tayi tare da ɗauro alwala. Wata pencil tightly skin gown tasanya wanda bayanta taƙasa yake aɗan tsage, sosai rigan tabi haɗaɗɗiyar surar jikinta ta lafe, wani ɗan madaidaicin hijab ta sanya ajikinta, kai tsaye tanufi ɗakin Oummu, tana knocking door ɗin, Oummu ta bata izinin shigowa, Zaune tasameta akan wata luntsumemiyar kujera dake cikin ɗakin, gabanta wasu takardune yayinda hannunta ke ɗauke da pen. Da murmushi akan fuskarta ta amsawa Zieyaderh gaisuwan da tayi mata, tare da ɗan zare farin glass ɗin dake sanye a idonta tana me cewa “Ya school ɗin?” “Alhamdulillah!” Zieyaderh ta amsa aɗan sanyaye, ƙatuwar leda wanda ke ɗauke da tambarin sunan wani super market Oummu ta miƙo mata tare da cewa. “Ungo amshi Kayan da kuka saya da Almustapha ne, ashe wai ke ya sayawa sai kimasa godiya” +
Asanyaye takarɓi ledan dake shaƙe da kaya, cikin sanyin daya sake zama sabo agareta tace “Oummu kitayani godiya, nagode sosai!”
Murmushi Oummu tayi irin tasu ta manya tare da cewa “Ae kinfi kusa dashi ayanzu zai kyautu kiyi masa godiyan da kanki!”
Murmushi kawai tayi cike da kunya ta sadda kanta ƙasa tare da miƙewa tsaye, da ƙyar ta iya jan ledan don tana da nauyi, haka tafita daga cikin ɗakin tanajin wani iri acikin zuciyarta. Tana shiga ɗakinta ta Zazzage ledan akan gado, tabbas sayayyan da sukayi ita dashi ne, sam bata wani ji farinciki ba, juyawa tayi ta fice aɗakin don samawa kanta abun da zata ci, batajin cin wani abu hakan yasa ta tsiyayo fresh milk me sanyi, kanta aƙasa take haura step ɗin da zai sadata da samannasu, sam bata kula da cewa shima yana zuwa ba, haɗuwarsu waje ɗaya ne yasanya gaba ɗaya fresh milk ɗin ya zube masa ajiki, cikin tsautsayi cup ɗin ya faɗi ya tarwatse a wajen. Aɗan razane ta ɗago kanta ta kalleshi, daidai lokacin shima ya ɗago kyawawan idanunsa, idanunsune suka sauƙa acikin na juna, da sauri tayi baya kasancewar sunyi matuƙar kusa da juna, bisa tsautsayi ta aje ƙafanta akan fasassun glass, wani irin ƙara ta sake tare da rumtse idanunta ƙam, beautyful eyes ɗinsa yaɗan zaro waje tare da kallon ƙasa inda ƙafanta tuni har ya soma fidda jini. Ƙaran da tayi shiya janyo hankalin Oummu, da sauri ta fito tare da ƙarasowa inda suke, cikin yanayi na damuwa tace
“Subahanallahi me ya faru?” cikin tsananin zafin dake ratsa har ƙwaƙwalwarta, ta buɗe idanunta da suka tara ruwan hawaye kana sukai ja, yunƙurin ɗaga ƙafanta ta somayi, amma zafin da takeji ya hanata, hakan yasa ta saki wani ɗan siririn ƙaran wahala, small pink lips ɗinsa ya ɗan ciza tare da raɓawa ta gefenta zai wuce. “SOORAJ me kayi mata ne?” cewar Oummu tana me ƙoƙarin kama ƙafan Zieyaderh don ta duba, fuska ɗauke da ɗan mamaki yasake ɗan waro Idanunsa alaman ni kuma mezan mata, kana ya taɓe lips ɗinsa.
“Subahanallah tayaya haka ta faru? Glass fa ta taka” Oummu tafaɗa tana me riƙe da ƙafan Zieyaderh, wanda har yanzu yake fidda jini, ƙarasowan Almustapha cikin falon kenan ya taraddasu atsaitsaye, da sauri ya ƙaraso garesu yana me cewa “Lafiya kuwa Oummu me ya faru?”
“Fasashshen glass ta taka, please zoka riƙemin ita naɗauko first aid box sai kayi mata treatment!” Oummu ta faɗa cike da tausayin halin da Zieyaderh ke ciki.
Babu musu Almustapha ya haura kan step ɗin tare da sanya hannayensa duka biyu ya kama kafaɗun Zieyaderh, wanda hakan yasa harta ɗan kwanto cikin jikinsa. Sauƙe hannayensa akan kafaɗunta, yayi daidai da bugawar zuciyarsa, da sauri ya rumtse idanunsa tare da dunƙule hannuwansa, lokaci ɗaya yaji wani irin jiri na neman kadashi, aɗan hanzarce ya juya cikin azama yabar falon.
Da taimakon Almustapha ta iya ɗingisawa zuwa kan kujera, sosai takejin zafi domin kuwa glasses ɗin sun ɗan caketa sosai, Oummu ne ta dawo hannunta ɗauke da first aid box, zama Almustapha yayi akan sofa tare da ɗaukan ƙafannata ya ɗaura akan wani ɗan madaidaicin stull, da cotton yayi using wajen goge mata jinin da ya ɓata ƙafannta, hannunsa yasa ya kama ƙafan, cike da kulawa ya shiga dubawa ko akwai wata ɓoyayyar kwalba dake a
cikin ƙafar, ganin babu yasanyashi ɗaukan hydrogen ya haɗa da auduga ahankali yake ɗan goga mata akan ciwon, kuka tasanya me sauti tare da rumtse idanunta, sosai takejin zafin hydrogen ɗin, murmushi Almustapha yayi ganin yanda take kuka tana me cije baki, cike da salon tsokana yace.
“Haba Bae da zafi ne?”
STORY CONTINUES BELOW
Tsaida kukannata tayi tare da buɗe jajayen idanunta, samun kanta tayi da murguɗa masa baki tare da yunƙurin zame ƙafarta daga hannunsa, murmushin daya bayyana white teeth ɗinsa yayi tare da cewa “Am sorry ai nama gama!” Kallon Oummu tayi tare da ɗan marairaice fuska, Murmushi Oummu dake tsaye tana kallonsu tun ɗazu tayi, aranta kuwa cewa tayi “Anya abun danayi kyautawa ne?” “Idan baizama kyautawa ba to tabbas za a ƙirasa da son kai!” Wata zuciyarta ta bata amsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa. “Allah shine shaidana nayi hakane don samun nutsuwa da salama azuciyar su dukan biyun, idan hakan bai yiwu ba kuwa to tabbas ko mai ya faru NI CE SANADI, sannan hakan zai zama kamar rashin adalci ne ga rayuwar ZIEYADERH!” maganan da Almustapha ke matane ya sanyata dawowa daga tunanin da take, inda yake cewa
“Yakamata taje ta huta, daga nan zuwa da safe karta taka ƙafan muga idan babu wani matsala shikenan, idan kuma mukaga ƙafar ta kumbura sai muje hospital!” Ya ƙare maganar yana me ƙoƙarin rufe first aid box ɗin dake gabansa. 1
Da taimakon Oummu Zieyaderh ta iya ɗingisawa zuwa ɗaki, adaddafe ta iya yin alwalan sallan magriba saboda zafi da ƙafan ke mata, haka ta samu tayi sallah nanma saida dabara don dazaran ta shumfuɗe tafin ƙafanta aƙasa tofa zafi zai ratsa gangar jikinta. 1
Yana barin falon haka yaji zuciyarsa nayi masa wani iri, yanajin yanayinsa duk ba daɗi, peter dake ta zaman jiransa tun ɗazu a waje yana ganinsa yataso da hanzari tare da buɗe masa murfin motar, shiga cikin motar yayi ransa duk ajagule, kallon agogonsa yayi yaga 5:50 am. Tsuka yaja tare da lumshe idanunsa da suka ɗan nuna alamun ɓacin rai acikinsu, 6 daidai jirginsu zai tashi amma gashi har yananeman yin late akan wannan stupid girl ɗin, wani siririn tsuka yaja akaro na biyu, shikam ya lura kamar yanda take mashiririciya haka komanta ma yake, yayi imani haukane kaɗai yake wanzar da irin tsoron da yake ganinta aciki da zaran ta ganshi. Hakanan yakejinsa cikin ƙuncin rai, suna isowa airport ya buɗe murfin motar agurguje, da sauri peter ya miƙo masa wata ƴar black trolly wanda abubuwan amfaninsa ne ke ɗauke aciki. Amsa yayi kana yashiga can cikin airport ɗin, saida ya kammala komai kafun yataho agurguje ya shiga cikin jirgi don 5 minute kacal ya rage flight ɗin ya tashi. Yana zama akan kujera ya sauƙe wani irin ajiyar zuciya tare da jingina bayansa da jikin kujeran, sit belt ya ɗaura kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, kamar yanda jirginsu ya tashi zuwa sararin samaniya haka arai da zuciyarsa yake fatan ace damuwarsa tayi ƙaura daga gareshi, awannan tafiyan yanason samawa zuciyarsa nutsuwa sosai, musamman akan sabon cutar da ta ɗauko mai wanda yakasa sanin gabansa balle bayansa. 1
Kwance take luf akan gado yayinda ta baza gaba ɗaya gashin kanta akan pillow, duk da cewa anɗau wasu mintuna dajin ciwon nata amma har yanzu tanajin zafi, wannan zafin da takeji ajikinta shine zafin daya tafi har zuwa cikin zuciyarta, ko wani bugu ɗaya na zuciyarta yakan zo matane da wani sabon sauyin yanayi, akowanni daƙiƙa ji take soyayyarsa na hauhawa acikin zuciyarta, sake gyara kwanciyarta tayi tare da lumshe idanunta.
SINGAPORE
Adaidai wannan lokacin shima ya gyara kwanciyarsa tare da lumshe kyawawan idanunsa, ako wani bugun zuciyarsa ɗaya yana tafiyane da sauye sauyen tunani da yake samu daga ƙwaƙwalwarsa, hannunsa ya ɗaura adaidai saman mararsa tare da ware idanunsa, sauƙesu yayi akan haɗaɗɗen adon zanen dake kewaye saman ɗakin, daga gefe guda kuwa ƙoyayen wutane keta aikinsu wajen bada kaloli masu ma’ana da ɗaukar hankali, domin duk bayan ko wani second kowanne daga cikinsu yake fidda wani irin diffrent colour na haske me kyau, daddaɗan sanyin garin da kuma iskan da ake shiya sanya yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak, sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na sau ba adadi, burinsa bai wuce bacci ya ɗaukesa ba, don zuwa yanzu zuciarsa takai ƙololuwa wajen matsawa ƙwaƙwalwarsa da tunani, bayan haka kuma gashi akwai gajiya sosai atattare dashi, sauda dama yakan zurfafa tunaninsa akan rashin lafiyansa, saidai kuma yasan komai na Allah Ne sai idan yasone zai baka lafiya, saɓanin haka kuwa kowani irin magani zakasha kodako yana maganin cutar taka sai kaga baiyi maka komai ba, yana matuƙar buƙatar lafiyarsa ayanzu saboda yanaji ajikinsa cewa nan gaba kaɗan zai cire rai da rayuwa, da kuma samun ingantaccen farinciki, tabbas ƙaddaransa babbace amma zaici gaba da ɗaukanta ahaka har izuwa lokacin mutuwarsa.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan tayi sallan asuba bacci tayi sosai hakan yasa ba itace ta farka ba sai after 8. aɗan zabure tatashi daga kwancen da take tare da sanya hannu ta murza idanunta, ganin hasken rana ya bayyana raɗau ta window’n ɗakinne yasanyata zuro ƙafafunta ƙasa da sauri, agurguje tayi wanka tare dayin brush, koda ta fito sama sama tashafa body lotion ɗinta, sauri sauri tasanya kayan uniform don tasan zuwa yanzu tayi latti sosai, zama tayi akan bed tare da jawo cover shoe ɗinta wanda yake na makaranta, ƙoƙarin sanyawa ta somayi, ciwon dake cikin tafin ƙafanta ne yasoma yi mata ɗan zafi sakamakon safa data sanya, shikuma ciwon baison zafi, ɗan rumtse idanunta tayi tare da soma ƙoƙarin tura kafanta cikin takalmin. Turo ƙofar ɗakin Oummu tayi bakinta ɗauke da sallama, ganin Oummu yasanyata sakin murmushi tare dayin ƙasa da kanta cikin girmamawa tace da Oummu
“Ina kwana!”
“Lafiya lau, kinsamu tashi kenan yanzu shigowana na biyu kenan, ya ƙafan naki?” Oummu ta tambaya cike da kulawa.
“Da sauƙi Oummu, saidai yana ɗanmin zafi amma basosai ba”
Kallonta Oummu tayi tare da cewa
“Yanaganki cikin uniform? halan dai baki san ƙarfe nawa bane yanzun ko, kuma ma ai bazaki iya jigilan zuwa school da wannan ciwon aƙafanki ba!” Oummu tafaɗa cike da kulawa
Cikin yanayi naɗan sanyi ta gyaɗa kanta, don bata da abun cewa.
Murmushi Oummu tayi tare da dafata cike da kulawa tace “To kizauna yau ba zuwa school don mahaifiyar Almustapha da kuma wasu daga cikin ƴan uwana sun taso musamman don zuwa ganin amaryarsu!” Oummu taƙare maganar tana murmushin jin daɗi.
Faɗuwar gaba da tsinkewar zuciyane suka ziyarceta alokaci guda, amma saita ɗan daure ɗago kanta tayi ta kalli Oummu, murmushi Oummu ta mata cike da son ƙarfafa mata guiwa tace “Karki damu kanki akan komai Zieyaderh, ninan matsayin uwa nake awajenki idan kina da abun da kikeso ko abun da bakyaso duk ki sanar dani nikuma Insha Allah Zan sha re hawayenki, nasan ƴan uwana dukansu masu fahimta ne, so bakida wata matsala dasu nakuma san insha Allah Zaki samu ƙauna ta musamman daga garesu, karki damu kinji!” Oummu taƙare maganar cike da lallashi.
Kai Zieyaderh ta kaɗa mata alaman “To”
Cike da jin daɗi Oummu tace “Yauwa ki saki jikinki, ki cire uniform ɗin zan turo akawomiki abinci, sannan kizauna cikin shiri don anjima zan turo meyin kwalliya tazo ta gyaramin ke”
Kasa cewa komai tayi har Oummu tafice daga cikin ɗakin, ɗan guntun murmushin dake kan fuskarta ne ya koma, take kuma saiga hawaye suna gangarowa daga cikin idanunta, da sauri ta sanya hannu ta share cike da tausayin kanta, haƙiƙa tasan duk wannan abubuwan suna faruwa ne kawai saboda tarasa abu ɗaya aduniyarta wannan abun kuwa bakomai bane face UWA MAHAIFIYA haƙiƙa duk wata Uwa haskece ga rayuwar ƴarta mace matuƙar itaɗin takasance UWA ta gari, UWA itace ginshiƙi sannan kuma farinciki arayuwar ƳAƳANTA, hannu takuma kaiwa ta share hawayenta, sakamakon knocking door ɗinta da taji anayi, tana buɗewa tayi kiciɓus da Nabila hannunta ɗauke da tray ɗin abinci, Nabila ɗaya daga cikin tarin ƴan aikin gidanne amma ita tana ɓangaren kitchine ne, itace me share sharen kitchine da goge duk wani inda aka ɓata, fuskarta ɗauke da ɗan murmushi ta amshi tray ɗin, yayinda Nabila ta juya ta koma, aje tray ɗin abincin tayi tare da soma bubbuɗe plates ɗin dake saman tray ɗin, plate ɗin farko soyayyan doya ne da egg sauce agefe, plate na biyu kuwa pepper soup ne na kayan ciki, ɗayan plate ɗin kuwa shawarma ne me zafi har turiri take, duk acikin abu ukun babu cimarta, hakan yasa da ƙyar ma ta iya cin doyan, sannan ta haɗa da tea, kaɗan taci abincin ta ture gefe, bathroom tashiga ta wanke hannunta, tray ɗin ta ɗauka da niyan sauƙa ƙasa, aikuwa 3 steps kawai ta kawo sukayi kiciɓus da Oummu tare da wata ƴar budurwa dake bayanta, wacce aƙalla bazata haura 27 years ba, murmushi Oummu tayi tare da duban budurwar cikin sakin fuska tace
“To Bilkh gama ƴar tawa please kiyi mata irin wanda kika jima bakiyi ba!”
Murmushi wacce aka ƙira da sunan Bilkh tayi cikin hausarta me bada wani irin sauti tace “Bakomai Hajiya Insha Allah zaki yaba da wannan aikin sosai!”
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi Oummu takumayi tare da ƙwaɗawa Nabila ƙira, dama dayake tana kusa hakan yasa tataho da sauri, tray ɗin dake hannun Zieyaderh Oummu ta amsa tare da miƙawa Nabila tace takai kitchine, duban Zieyaderh tayi cike da kulawa tace “Zieyaderh wannan itace Bilkh shahararriyar me kwalliya ce, please ki bata haɗin kai, maza ki mata jagora zuwa ɗakin ki”
Murmushi Zieyaderh tayi tare da cewa “To” itadai har yanzu kanta akulle yake don batasan menene za a mata ba. Suna shiga cikin ɗakin Bilkh ta baje ƙaton ƙaton akwatin meckup ɗinta wanda tazo da shi. Kallon Zieyaderh tayi tare da ce mata taje tayi wanka, musu banata bane hakan yasa ta wuce toilet, wanka tasakeyi kana ta ɗauro babban towel ajikinta wanda bazai bayyana tsiraicinta ba, tana fitowa Bilkh ta zaunar da ita tare da fiddo da wani tsadadden mai daga cikin akwatin meckup ɗinta ta shiga shafa mata, ita Zieyaderh abunma mamaki ya bata don bataga amfanin shafa mata mai ba bayan itama tanada nata hannun, tana kammala shafa mata mai ɗinne ta zaro wata galleliyar atamfa wacce taji ɗinkin fitted gown me kyau, wanda yana daga cikin kayan da Oummu ta miƙo mata lokacin da Zieyaderh ke wanka, miƙawa Zieyaderh rigan tayi tare da cewa tasanya, amsa tayi tare da komawa bayan drawer ta laɓe anan tasanya rigan gudun kada Bilkh taga tsiraicinta, ita kuwa Bilkh abubuwan da zata buƙata taketa haɗawa, sosai rigan ya zauna ɗas ajikin Zieyaderh baƙaramin kyau kuwa tayi ba, akan wata kujera Bilkh ta zaunar da ita, saida tayi mata duk wani abu daya kamata kafun cikin nutsuwa ta shiga tsantsarawa Zieyaderh meckup akan beauty and innocent face ɗinta. Bawani lokaci sosai suka ɓata ba kasancewar ba wani meckup aka mata akan fuskar nata sosai ba, simple ne amma yayi kyau sosoi, take tsananin kyawun Zieyaderh ya sake bayyana, tsantsara mata ɗaurin ɗankwali Bilkh tayi bayan ta nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyan kanta, wani haɗaɗɗen sari me kyau da tsada kalan ja Bilkh ta ɗauka, miƙar da Zieyaderh tsaye tayi tare da soma nannaɗa mata sarin ajikinta, kasancewar atamfar dake jikinta baƙine me ratsin ja, hakan yasa baƙaramin matching yayi da material sarri ɗin ba.
“Wow!” Bilkh ta faɗa bayan ta gama nannaɗawa Zieyaderh sarri ɗin, ita kanta sosai kyawun Zieyaderh ya ɗauki hankalinta, haƙiƙa ita kanta tasan ta iya kwalliya wanda zai gyara mace ya me da mummuna kyakkyawa, amma awannan karon tana da tabbacin cewa ba kwalliyarce tayiwa Zieyaderh kyau ba, ita Zieyaderh’n ce tayiwa kwalliyan kyau. Turaruka masu ƙamshi da tsada ta fesawa Zieyaderh wacce tazama so silent. Shigowar Oummu cikin ɗakinne yasa duk suka kalleta. Fuska faɗaɗe da murmushi tace “Masha Allah, lallai Bilkh aikinki yayi kyau!”
Murmushi Bilkh tayi tare da cewa
“Hajiya ita yarinyar takice me kyau!”
Murmushi me sauti Oummu tayi sannan taja hannun Zieyaderh suka fice daga cikin ɗakin, yayinda Bilkh kuma ta ɗauki wayarta ta soma latsawa. Tun shigowansu cikin katafaren falon Oummun dayake na musamman gaba ɗaya waƴanda suke cikin falon suka maida kallonsu gareta, matane su Uku zaune acikin falon kowacce idan ka ganta kamar ka latsa jini yafito tsabar fari da jin daɗi, kallo ɗaya zaka musu kafuskanci cewa manyan masu akwai ne. Cike da fari’a ɗaya daga cikin matan wanda itace bata da yawan shekaru kamar na su Oummu ta tarbo su, hannun Zieyaderh wacce kanta ke ƙasa ta riƙe tana me cewa “Masha Allah!” agaban sauran matan ta zaunar da Zieyaderh kan wani lallausan carpet.
Atare duka matan suka haɗa baki wajen cewa “Masha Allah!” don kowaccensu ta yaba da kyau da kuma ƙuruciyar Zieyaderh, duk da bata ɗago kanta sun kalleta da kyau ba amma kunyanta kaɗai ya isa gamsar dasu. Cike da ladabi Zieyaderh ta gaidasu, dukansu suka amsa fuska asake cike dajin daɗi. Oummu ce tace taje ta kawo musu drinks da kayan fruits, aikuwa babu musu Zieyaderh ta miƙe, cikin mintuna kaɗan ta cika musu gaba da kayan fruits da drinks wanda duk tanayin aikinne cikin nutsuwarta, ba laifi sukam sun gamsu da yanayin tarbiyan yarinyar sosai, fatansu ɗaya shine Allah yasa tazamo itace matar zama agareshi. Koda ta kammala gabatar musu da komai ɗakinta ta koma tare da ƙarasawa gaban madubin ɗakin ta shiga duba irin kyawun da tayi, don zuwa lokacin Bilkh tama jima da tafiya. Wani irin murmushi me sanyi tayi tare da sanya hannu ta shafi fuskarta daketa fidda ƙyallin kyau hancinta kuwa sai shinning yake.
Gyara zama Hajiya Sauba tayi tare da duban ƴar uwarta cike da jin daɗi tace “Gaskiya Sulaimiyya na yaba da hankalin wannan yarinyar sosai Allah yabasu zaman lafiya!”
Da Ameen Oummu ta amsa tana murmushi.
“Nima kuwa na yaba ƙwarai Allah yasanya alkhairi, amma fa wani hanzari ba gudu ba Sulaimiyya yakamata ace anyi bikinnan acikin watannan, saboda banga amfanin jinkirtawa ba” Cewar Aunty Laylerh.
“Wannan tunanin shine araina Aunty Laylerh, kuma Insha Allah zamusa auren nan bada jimawa ba, domin kuwa daren jiya maganan auren mukayi da Abbansa yakuma ce zasuje shida abokinsa har can garin su yarinyar!”
Murmushin jin daɗi su duka sukayi tare dayin addu’an Allah yatabbatar da alkhairi acikin auren.Hira Oummu da ƴan uwanta sukayi sosai inda suka cigaba da tsara yanda bikin zai kasance. Aunty Muhibbat wanda takasance itace ƙaramar cikinsu ta kalli Oummu tare da cewa “Ni aganina idan babu damuwa, zamanta ya dawo wajena saboda kinga ina tare da shuwa arab saboda haka ba ƙaramin gyara zata samu ba” murmushi Oummu tayi tare da cewa “Hakane amma aikinsan tana zuwa makaranta, duk da ma dai muntsara kan cewar awannan year din zata zana waec nd neco ɗinta” +
Cike da jin daɗi Aunty Muhibbat tace “To Allah yasa ayi komai dai a sa’a” da “Ameen” suka amsa su dukansu, basu wani jima sosai ba suka kama hanyar tafiya bayan sun jibgewa Oummu tsarabobi masu yawa da suka kawowa surukarsu Zieyaderh.
Ɓangaren Zieyaderh kuwa jin kamar ta takura yasanya cikin nutsuwa ta shiga warware sari ɗin dake jikinta tare da aje sa gefe. Ajiyar zuciya ta sauƙe akaro na barkatai, tare da ɗan jingina kanta da saman gadon da take zaune akai, tunanine cike fal azuciyarta, turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasanyata ɗago kanta ta kalli bakin ƙofan, Nabila ce tashigo cikin ɗakin cikin ɗan rusunawa tace “Hajiya tace ayi mata ƙiranki”
Murmushi Zieyaderh ta ɗanyi tare da ƙoƙarin miƙewa tsaye “Ganinan zuwa” tafaɗa tana me zura bedroom slippers aƙafanta. Kai tsaye ɗakin Oummu’n ta nufa, ɗan tsayawa tayi ajikin ƙofan tare dayin knocking. Sanin cewa itace yasa Oummu dake zaune akan gado ta bada izinin shigowa, da sallama ɗauke abakinta ta shigo tare da neman waje taɗan rusuna daga gefe.
Oummu da yawancin lokuta fuskarta baya rabo da murmushi yanzun ma murmushine ɗauke akan fuskarta, miƙowa Zieyaderh wata haɗaɗɗiyar ƴar jaka me kyau tayi, amsan jakan Zieyaderh tayi tana me kallon Oummu cike dason ƙarin bayani, “Kyautane daga surakanki, inafata zakiyi murna zakuma ki yaba da kyautar!” Oummu tafaɗa tana me ƙoƙarin manna farin glass akan idanunta.
Jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi sunkuyar dakanta ƙasa tayi asanyaye tace “Nagode sosai Oummu amma sai nake ga kamar kyautan sunyi yawa, duk dama banga menene aciki ba!”
Murmushi Oummu tayi tare da cewa “Bana tunanin kyautar tayi yawa kedai ki amsa kawai, gaba kuma idan kunsake haɗuwa sai ki musu godiya”
Cike da jin nauyin Oummu’n tasake yi mata godiya sannan tatashi ta wuce ɗakinta. Koda taje zama tayi akan gado tare da buɗe jakar, wani ɗan box me kyau da burgewa taciro daga cikin jakan, tare da buɗewa, wani danƙareren agogon hannu na gwal ne ya bayyana acikin kyakkyawan box ɗin. agogone na mata me matuƙar ɗaukar hankali, kyawawan duwatsunsa sai ɗauke ido suke, sake fito da wani box ɗin tayi wanda har yamafi wancan ɗin girma, shi kuwa wani irin danƙareren sarƙa da ɗankunnen gwal ne acikinsa me kyaun gaske, sosai design ɗin sarƙan ya mata kyau, har batasan sanda ta saki lallausan murmushi akan fuskarta ba, ganin kyaututtukan nada yawane yasanyata zazzage jakan gaba ɗaya akan gado, nan tayi arba da wasu arebian gown masu kyaun gaske, tare da wasu kwalaben humra masu ƙamshi irin masu kama jiki ɗinnan, cike da jin daɗi ta tattara kayan ta maida cikin jaka, sosai kayan suka mata kyau saidai kuma tasan matsayinta baikai nanba, bai kamata ace amatsayinta na ƴar wanda ba kowa ba ayi mata irin wannan hidiman, shigowar Nabila cikin ɗakinne yasanya ta tsaida duk wani abu da take tana kallonta. 1
“Hajiya tace ashaida miki kina da baƙo awaje”
Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi yayinda taji gabanta ya ɗan faɗi cikin yanayi naɗan mamaki tace “Baƙo?”
Kai kawai Nabila ta iya kaɗa mata alamar “Eh” kasa cewa komae tayi har Nabila ta juya ta fice daga cikin ɗakin, Vail ɗinta me kyau da walwali ta sanya tarufe jikinta, cikin fargaban sanin ko waye haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita, bata samu kowa afalon ba hakan yasa kaitsaye tanufi ƙofar da zai sadata da compound ɗin gidan.
STORY CONTINUES BELOW
Tsaye yake ajikin motarsa ƙirar jeep yasha kyau cikin shigarsa ta half jumper White and blue colour, yayinda ya kafa hular Zanna bukar mai adon blue akansa, haɗaɗɗen sajen dake kwance akan fuskarsa ne ya kwanta luf akan ƙuncinsa, yana ganinta yasaki murmushinsa mai kyau wanda har saida gefe da gefen kumatunsa suka loɓa, ganinsa baƙaramin faɗar mata da gaba yayi ba,take mood ɗinta ya sauya daga ƙwarin guiwa zuwa raunin zuciya, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kasa ƙarasowa inda yake, murmushi yayi ganin ta tsaya batare da ta ƙaraso garesa ba, ahankali yashiga takawa har zuwa inda take, daddaɗan ƙamshin turarensa ne yasanar mata da zuwansa, ahankali ta ɗan lumshe idanunta tare da buɗesu, kanta taɗan ɗago ta kallesa, idanunsune suka sarƙe acikin na juna kasancewar shiɗinma kallonta yake, kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saima wani irin marairaicewa da idanun nata suka yi, shiɗinma kallonta yakeyi da sexy eyes ɗinsa wanda suke wani irin lumshewa kaɗan kaɗan, cikin wata irin murya me sanyi yace “Anan zaki barni bazaki bani wajen zama ba?”
Kanta ta sunkuwar ƙasa tare da ɗanyin murmushi, kallonta tamayar ga wajen ɗan shaƙatawan dake cikin gidan wanda aka ƙawatashi da wasu kujeru guda huɗu masu kyau gaba ɗaya flowers sun zagaye wajen yayinda sukayiwa rumfar dake wajen ƙawanya, kallonsa tayi sannan tanufi wajen shima ya rufa mata baya. Akan ɗaya daga cikin kujerun ta zauna yayinda shima ya zauna akan kujeran dake facing nata. Ƙasa tayi da kanta tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta murya asanyaye tace. “Ina wuni!” murmushin daya bayyana dimples dinsa yayi batare daya amsa taba sai idanu daya zuba mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, don kokaɗan meckup ɗin dake kan beauty face ɗinta bai goge ba, jin shiru bai amsata bane yasanyata turo bakinta gaba aɗan shagwaɓe tace “To ba gaisheka nake ba kuma kaƙi amsawa!” Murmushi yayi harsai da haƙwaransa suka bayyana. “To ae banji bane, please kiɗan ƙara ɗaya sainaji!” Yafaɗa cikin salon kwaikwayon maganarta. Idanunta ta ɗago kana taɗan watsa masa hararan wasa tare da ɗan murguɗa masa ƙaramin bakinta dayasha baby pink colour lipstick, lumshe idanunsa yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran, wani irin shauƙi ne ke shigansa, sosai yanda tayi da bakinta yayi masa kyau, cikin wani irin yanayi yace. “Kullum ƙara kyau kike, idan kina fushi kyau kike ƙarawa, idan kina murmushi kyau kike ƙarawa, haka ma idan kina gabana kyau kike ƙarawa, inajin kamar sonki acikin jinina yake Zieyaderh, ko sau ɗaya ne please ki amsa min cewa kina sona!” yaƙare maganar yana me kafeta da mayun idanunsa wanda suka ɗan sauya kala, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da ɗan ciza laɓɓanta, ƙirjinta ne yake bugu da sauri, maganan aurenta da Almustapha ne yazo yayi tsaye aranta, tabbas tanajin wani abu na daban dangane da Pharouk, to amma bata da tabbacin cewa wannan abun soyayyace, koda ma acd sonsa take mecece amfanin soyayyar? yanzu burinta shine ta koyawa zuciyarta soyayyar Almustspha, dan sai da soyayya ne kaɗai zata iya kyautata masa azaman aurensu. Ɗago idanunta da sukayi raurau da hawaye tayi daniyar yiwa Pharouk magana, saidai tuni maganan nata ta maƙale sakamakon Ido biyu da sukayi da Almustapha dake tunkaro inda suke, ganin ta tsaida idanunta abayansa yasanyashi ɗan waigawa don ganin abunda take kallo, idanunsa ne suka sauƙa akan kyakkyawan saurayin dake zuwa garesu, kwata kwata bai wuce saura taku shida ya ƙaraso inda suke ba, tashi tsaye yayi yana me fuskantar saurayin, daidai lokacin Almustapha ya ƙaraso, dayake shi jan ajin nasa baya hanasa fari’a, hakan yasa bawani ɓata lokaci ya miƙawa Pharouk hannu don su gaisa, ganin haka yasa Pharouk ma bashi hannu suka gaisa, cike da kulawa Almustapha ya kalli Zieyaderh wanda kanta ke ƙasa, hakanan gabanta keta faɗuwa, cikin muryarsa me ɗauke da nutsuwa yace “Inason aron baƙon naki naɗan wasu mintuna, inafatan bazan takuraki ba?”
Wani iri taji yayinda wani irin nauyi da kunyarsa suka lulluɓeta alokaci guda, jikinta asanyaye ta miƙe tsaye tare da kaɗa kanta alaman “Babu komai” cikin nutsuwa haka tajuya tanufi cikin gida, ita kanta bazata iya tantance awani hali take ciki ba awannan lokacin. Kamar wanda ƙwai ya fashewa haka ta haura sama ko lura da Oummu dake tsaye a bakin kitchine batayi ba, Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da duban hanyar da Zieyaderh’n tabi, wani irin fargabane taji ya kamata, sai yanzu takejin tsoron haɗin da tayi, musamman ma da taga yanayin da Zieyaderh’n tashiga ayanzu, shiru tayi tare da faɗawa wani sabon duniyar tunani.
Ita kuwa Zieyaderh tana shiga ɗaki ta rufo ƙofarta, samun kanta tayi da sulalewa ta zauna daɓas aƙasa, batare da ta ankara ba taji wasu hawaye masu ɗumi suna sauƙa akan ƙuncinta, tabbas wannan sabuwar ƙaddaran da ta tsinci kanta aciki tayi mata girma, ƘADDARA tana neman haɗa aurenta da Almustapha, sannan kuma agefe guda ga Pharouk da yake neman ta amsa masa soyayyarsa, ƘADDARA mafi girma awajenta kuwa itace soyayyar Mr.Helper, hannayenta tasanya ta share hawayenta, wata zuciya ce me bata ƙwarin guiwa akan ta yarda da duk wata ƙaddara da tazo mata me kyau ko akasin haka, samun kanta tayi da kwanciya luf akan gado, mintuna ƙalilan bacci ɓarawo ya saceta.
STORY CONTINUES BELOW
Pharouk. Gudu sosai yake sharawa akan babban titin gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya jikinsa, maganganun da Almustapha ya faɗa masa suketa yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa, da ƙarfi ya daki steering motar ransa amatuƙar ɓace yace
“Bazan taɓa zama looser akaro na biyu ba SOORAJ, awannan karon tabbas bazan bari kasake nasara akaina kamar lokutan baya ba, bazan taɓa bari ka auri Zieyaderh ba SOORAJ!!” wani irin murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, ahankali yashiga rage gudun da yakeyi tare da ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwa tahanyar aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa.
***
Oummu ce ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin wanda yake mallakin Mijinta ne, Abba dake tsaye yana sanya garen kayansa ya ɗan juyo tare da kallonta murmushi yayi mata tare da cewa “Saboda kawai ɗanki zaiyi aure shiyasa kika kasa zaune kika kasa tsaye ko Sulaimiyya!” yaƙare maganar cikin yanayi na ɗan tsokana. 11
Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarta tare da cewa “Yanzuma ai nashigo ne nasanar dakai abokan tafiyanka sun iso”
Murmushi ya kumayi tare da cewa “Bake kaɗai kikejin farinciki aranki ba Sulaimiyya nima inaji, saidai kuma ata wani ɓangare na zuciyata ina ɗauke da fargaban abun da zaije ya zo”
“Insha Allah Alhajina babu wani abu da zaizo sai alkhairin Allah!” Tafaɗa cikin son ƙarfafa masa guiwa.
Yaji daɗin maganan nata sosai hakan yasa yayi murmushi, har wajen motarsa Oummu ta rakasa inda ya haɗu da manyan aminansa su Uku suka kama hanyar airport, kai tsaye suka wuce Kaduna, daga nan kuma zasu shige cikin motocinsu su wuce ƙauyen saminaka. 1
Itakuwa Zieyaderh gaba ɗaya wunin yau batajin daɗin jikinta, hakanan takejin kanta cikin ƙunci, wani irin kewa me taɓa zuciya takeji yana ratsa duk ilahirin jikinta, gaba ɗaya su Shukra sun lura da rashin walwalan da takeyi kwana biyu, yanzuma zaune suke su duka ukun akan wani ɗan dakali suna me shan iskan dake kaɗawa asararin samaniya. Cikin yanayi naɗan zolaya Nasmah tace “Amarya badai wai cin amarcin aka fara tun yanzu ba? naga gaba ɗaya duk kin rame, sometimes kuma kina cikin damuwa”
Hararanta Zieyaderh tayi tare daɗan murguɗa mata baki cikin yanayin ɓata fuska tace
“Ni ba amarya bace”
Dariya Nasma da Shukra suka sanya, wanda hakan yaƙara ƙular da ita. “Uhumm kigama zille zillenki yarinya wallahi sai mun fidda ankon bikin ki ehe, sannan kuma sai mun sha rawa koya kikace Besty” Shukra tafaɗa tana kallon Nasmah. “Ƙwarai kuwa” Nasmah tafaɗa tana me gimtse dariyanta. Cikin turo baki gaba Zieyaderh ta miƙe daga zaunen da take tare da nufar hanyar da zai sadata da class ɗinsu. Kallo su Nasmah suka bita dashi harta ɓacewa ganinsu, sannan suka sa dariya, har acikin ransu su mamakinta suke na yanda gaba ɗaya tabi ta takura kanta.
Acan Ƙauyen Saminaka kuwa Tuni Abba sun gana da Malam Garba baban Zieyaderh, inda yayi musu karɓa ta mutumci, babu laifi kuma sun yaba da halin karamcin daya nuna musu, nan suka zauna suna me sake fahimtan juna, sam su Abba bada wasa suka ɗauko maganan auren ba hakan yasa lokaci guda suka gama magana inda Malam Garba ya shaida musu cewa ya basu auren ƴarsa Zieyaderh, Alhaji Maham ɗaya daga cikin aminan Abba shi ya ciro wasu kuɗi dake cikin aljihunsa inda ya miƙa amatsayin sadakin auren Zieyaderh, naira dubu ɗari ne cas, cewar da sukayi basason bikin ya ɗauki lokaci ne yasanya Malam Garba cewa suyi haƙuri suɗan bashi lokaci zuwa nan da kwana huɗu zai sanar dasu kowani lokaci ya yanke, shikuwa yayi hakanne don yanason tattaunawa da Zieyaderh akan batun auren, domin tun da aka fara batun auren baiji ta bakinta ba kuma itama tana da haƙƙi, cikin mutumta juna su Abba sukaiwa Malam Garba sallama inda suka kama hanyar dawowa cikin garin Kaduna.
……….
15 minute da tashinsu a school kenan amma har zuwa yanzu Kamalu driver baizo ɗaukarta ba kamar yanda ya saba, waige waige taɗan somayi wai kozata hangosa amma babu ko me kama dashi, gashi gaba ɗaya ƴan makarantar sun soma watsewa don tuni su Shukra ma sun tafi, ahankali take takawa harta isa bakin gate ɗin fita daga makarantar, tsayawa tayi daga ɗan gefe kaɗan tana me ƙarewa motocin da keta hada hada awajen kallo, wata haɗaɗɗiyar blue car wanda taji black tinteck ne ta tsaya adaidai gabanta, kallon motar Zieyaderh tayi amma ganin bata iya ganin wanda ke cikin motar ya sanya ta ɗauke kanta gefe,tare da cigaba da kallon hanya, ahankali ya shiga zuge glass ɗin motar, fuskarsa ɗauke da murmushi yace “My ƴar kyakkyawan budurwata!” jin muryarsa acikin kunnuwanta yasanya tayi saurin ɗagowa ta kalleshi, hakanan taji gabanta ya faɗi amma sai tasaki murmushi, da hannu yayi mata alaman da ta taho, samun kanta tayi da kasa musa masa sai kawai taɗan ƙarasa jikin motar, daga ciki yasanya hannu ya buɗe mata murfin motar, duk da cewa ƙirjinta na dukan uku uku haka ta daure tashiga cikin motar saidai bata rufe murfin motar ba, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da kama ƴan yatsunta tana wasa dasu, shikuwa Pharouk ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ƙiran sunanta murya asanyaye. Jin yanda yaƙira sunannata yasanyata ɗago da kanta ta kalleshi, gani tayi gaba ɗaya murmushin dake kan fuskarsa ya kau, zuwa yanzu damuwane shumfuɗe akan fuskarta sa, kasa ɗauke idanunta daga kansa tayi saidai kuma ba cikin idanunsa take kallo ba, tunowa da tayi cewa jiya tabarsu da Almustpha batare da tasan me Almustaphan ya faɗa masa ba yasanya taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, jitayi idanunta naneman kawo ruwa, ahankali yasanya hannunsa ya ɗago haɓarta, hakan yasa suka jefa idanunsu cikin na juna, cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa yace “Kinason aure’n?” gabantane ya faɗi dajin tambayar tasa amma kuma saita samu kanta da kasa amsa masa, fuskarsa yasake mareraicewa tare da cewa “Da gaske kenan aure za’a miki? me yasa kika amince da hakan? kinyarda arabani dake kenan ko?” yaƙare maganar yana me matuƙar nuna rauninsa akan fuskarsa.
Hawayen dake kwance acikin idanunta ne suka samu daman gangarowa batare da ta shiryawa hakan ba. Ganin hawaye akan fuskarta ya sanyashi lumshe idanunsa tare da matso da fuskarsa gaf da tata har suna iya jiyo hucin numfashin juna, jin sauƙan numfashinsa akan fuskarta yasanya azabure tayi saurin buɗe idanunta , shima buɗe nasa idanun yayi wanda suka kaɗa sukai ja, wani irin kallo daya mata ne yasanya tayi saurin jan jikinta baya tare da ture hannunsa dake kan haɓan ta, kuka ne yake neman cin ƙarfinta hakan yasa ta juya da sauri ta fita daga cikin motar, dai dai lokacin kuma motar da aka saba zuwa ɗaukanta dashi wanda kamalu driver ke ciki ya tsaya adai dai ƙofar shiga gate ɗin makarantar, da ɗan sassarfa taje ta buɗe murfin motar tare da faɗawa ciki kana ta jawo murfin ta rufe, kanta ta cusa acikin cinyoyinta tare da sakin kuka me sauti, Ko bi takan Kamalu driver dake bata haƙurin rashin zuwansa da wuri da yayi bata biba, kuka take sosai tana me kakkame jikinta, wani irin zafi zuciyarta ke mata, Me yasa har izuwa yau baice komai ba? me yasa ya hanata ganinsa har na tsawon kwana uku? tanajin zafi acikin rai da zuciyarta, safe, rana, dare, duk shine acikin rayuwarta me yasa takejin hakan? Kukanta taci gaba dayi wanda babu me rarrashi, zuwa yanzu harta soma jin haushin kanta, musamman yanda tamaida kanta wata wawiya akansa. 3
Ganin tashin motarsu yasanya Pharouk sakin wani murmushi wanda shikaɗai yasan ma’anarsa, key ɗin dake jikin motar yaɗan murza, tare da cilla motar tasa kan titi, yayiwa kansa alƙawarin matuƙar shine Pharouk to SOORAJ bazai taɓa samun Zieyaderh amatsayin mata ba. 3
SOORAJ
Ahankali yake matsowa jikinta yayinda takeja baya shi kuma yana me ƙara matsota, wani irin numfashi yake fitarwa me zafi, kasancewar takawo jikin bango hakan yasa ta tsaya cak, hakan kuma yayi daidai da ƙarasowarsa gareta, ganinsa adaf da ita yasanyata lumshe kyawawan idanunta tare da sakin wani sassanyar ajiyar zuciya, kyakkyawan fuskarta yake kallo yayinda idanunsa ke lumshewa ahankali hankali, numfashinsu ne ya cakuɗa dana juna, yayinda ƙamshin turarensu ya haɗe waje guda, hakan yasa wani irin ƙamshi mai daɗi ke fita ajikin kowannen su, fuskarsa ya manna da tata fuskar yayinda ya sauƙe hannayensa akan faffaɗan waist ɗinta, cikin wani irin yanayi ya ɗaura lips ɗinsa akan nata tare ɗan kama lip ɗinta na ƙasa ya ɗan tsotsa, wani irin abune yaji ya zirga masa har cikin tafin ƙafansa, sake kama lips ɗinnata yayi yashiga tsotsa ahankali yayinda yake fitar da wani irin numfashi, ahankali cikin rufewar ido yake ƙara tsotsan laɓɓanta, wanda hakan yasanya taɗan buɗe bakinta, ahankali ya tura bakinsa cikin nata yayinda harshenta ya faɗa cikin bakinsa, wani irin abu yaji yatsarga ajikinsa yayinda yaja wani irin numfashi tamkar wanda zai shiɗe, azabure ya farka daga baccin da yakeyi, tare da buɗe idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, wani irin zufane ke ketowa ta jikinsa yayinda gaba ɗaya gashin jikinsa suka mimmiƙe, jijiyoyin jikinsa ne suka fito raɗa raɗa, tashi zaune yayi yana ne ƙoƙarin jawo numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwacewa, yayinda yakejin tamkar ana buga masa guduma acikin kansa, wani irin ƙara yayi tare da dafe kansa wanda yakejin wani irin azababben ciwo acikinsa, hannayensa yasanya ya dafe kunnuwansa tare da rumtse idanunsa, duniyarce gaba ɗaya take juya masa.