ALKAWARIN JINI CHAPTER 10 BY _HAWWA MUH’D USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayyanannen murmushi yayi lokacin daya tuna da maganganun Daddy lokacin daya kirashi bedroom d’insa,ko da yake bai bada hankalinsa a gurin ba,amma tabbas yaji da kunnensa lokacin da Daddy yake shaida masa lallai² yaje yaga yarinyar a yau kafin nan da ranar d’aurin aure,sai dai kuma bayan fitowarsa daga gurin san sai ya iske abunda ya tada masa hankali,wanda shi ne batun tafiyarta gida,a lokacin ya fito yana mitar dalilinsa zaisa Dad ya tashe shi daga zaman jiranta sannan kuma yanzun yace zai tilasta masa yin abunda bai yi niyyaba,wannan dalilin yasa ko daya fita sai bai zame ko ina ba ya nufi gurin tsuntsuwarsa,itama d’in kuma duk da marmarin ganinta da yake da yaje d’in ta nemi chaja masa hankali,dan ma dai Allah yaso bai biye mata ba ya maida ita kamar wani abun wasan
yara,,murmushi ya sake yi a hankali ya kai hannunsa saman short sides with side swept haircut da aka masa tun a U.S yana shafawa,bayan wucewar kamar mintuna biyu kuma sai ya sake d’age kai zuwa sama cikin yanayi na mai tunani kafin yayi magana a fili yana mai fad’in
“Yah rabb.! Kai kake bayarwa,kuma kai kake hanawa,mu bayinka ne gajiyayyu kuma mak’ask’anta,rok’o na a gare ka a kowane lokaci na tsinci kaina a gareka shi ne ka amince min,ka datar dani ta hanyar wadata rayuwata da abunda ya kasance mafi alkhairi a gare ni,,yah ubangijina yadda ka tsara shi ne dai² mu banyinka ne,a koda yaushe k’addarawarka da hukuncin ka a garemu shi ne dai² kuma shi ne abun binmu,,na tabbata kai kad’ai ka barwa kanka sanin dalilin da yasa ka dasa soyayya a tsakanin wad’annan bayin naka,dan haka kai kake da ikon juya dukkan lamuran su kasance a yadda ka tsarasu,,ya rabbi a wannan karon ina rok’on ka kamar yadda na sabarwa zuciyata da yi maka biyayya,daka amince min ta kasance mallakina.!”
Sai da yayi addu’o’insa kafin daga bisani ya kama hanyar bathroom jikinsa babu wadataccen kuzari,,bayan yayi wanka ya shirya kansa tsaf cikin pajamas d’insa masu matuk’ar kyau sannan ya d’auki d’aya a cikin wayoyinsa ya fara dialing number Badra,wacce a lokacin tuni tayi nisa a duniyar bacci,kiransa ya farkar da ita,lalubawa tayi kusa da ita daga inda take ajiye wayar ta d’auko ta,ba tare data iya bud’e idanunta ba tayi answering call d’in cikin muryar bacci tace
“Hello.! Wane ne a kan layi..!?”
Shiru ya d’anyi yana nazartarta kafin yace
“Bacci kike yi ne Yallab’iya..!?”
Muryarsa ce tasa ta mutsike idanunta da sauri ta tashi ta zauna tana waige²
“Yah Hammad..!”
Ta fad’a da muryar tsoro
“Ya akayi..!?”
Ya tambaya cikin wannan husky voice d’in nasa na asali,bata iya bashi amsa sai dai tayi saurin cewa
“Babu komai.”
Siririn tsaki yayi sannan yace
“Ok.. Ki turomin number k’awar ki yanzun..!”+
“Toh” tace masa dan ta fahimci wacce yake nufin,tun kafin tayi wani abu tuni har ya katse kiran daga b’angarensa,zugum Badra tayi tana bin wayarta da kallo,yayin da ta zabga tahumi da duka hannayenta tana kallon kiran wayar daya katse,cikin ranta take ayyanawa ita kam ayinin yau gaba d’aya ta kasa fahimtar abunda yake shirin faruwa a tsakanin yayan nata da kuma k’awar tata,sannan gashi bata san wane ne ya dace ace ta tunkara da batun ba a cikin su biyun,shin haka kenan zata yi ta zama cikin duhu,ko kuwa zata yi k’ok’arin tambayar d’aya a cikinsu ne.? Saurin girgiza kai tayi a fili tace
“Gaskiya duka babu wanda zai yiwu,,nasan halin yah Hammad,babu ta yadda za’ayi ma na iya masa maganar.”
Saurin d’aga kai tayi da fad’in
“To.! ko princess d’in zan tambaya ne tayi min bayanin abunda yake tsakaninsu.?”
Shiru ta sake yi tana tunani,a cikin wannan yanayin na damuwa wani kiran ya sake shigo mata,k’arar da wayar tayi shi ya taimaka mata wajen dawo da ita daga tunanin data tafi,,Yah Hammad shi ne sunan da mai kiran ya bayyanar,cikin sauri ta sake answering call d’in nasa
“Da Allah kin san ke nake jira,shi ne zaki tsaya b’ata min lokaci..? Mene ne yasa baki turo min bane har yanzun,,ko kuma dai so kike nazo da kaina na amsa.?”
Cikin b’arin jiki da murya tace
“A’a A’a,, yah! Ba sai ka zo ba..”
“In banda iskanci ma nace kiyi min abu da sauri shi ne sai kin sani jiranki..?? Da me kike yi da baki turo ba har tsayin mintuna uku..?”
A sanyaye tace
“Kayi hak’uri..”
“Ki rik’e hakur’in ki ni kiyi min abunda na saki.. Saura ki bari na sake kira,kin san dai abunda zai biyo baya..”
Tana niyyar bashi hak’uri,ya sake kashe wayar ba tare daya jira cewarta ba,,contact lists d’inta ta shiga tana duba number,bayan ta duba d’in tayi masa sharing via text message,sak’on yana nuna mata ya tafi ta sauke ajiyar zuciya da fad’in
“Alhamdulillah alaa kulli halin..!”
Idanunta ta d’an runtse a hankali ta d’aga kanta zuwa kan agogo
“Ohh.! Ashe har yanzun dare ma baiyi ba..!”
Ta fad’a tana yamutse fuska kafin ta koma ta sake kwanciya.
Yana tsaye har lokacin da wayar a hannunsa sak’on ya fad’o,da azama ya bankad’e shi dan dama shi yake jira,sunan da ya gani ne yasa shi yin murmushi a fili yayi magana da fad’in
“Wow..! Kid sis,,lallai kin cancanta da ayi miki kyauta.”
Bai k’arasa maganar ba sai da wayar a jikin kunnensa,,yadda kiran yake sounding haka zuciyarsa taje bugawa,amma har kiran ya katse ba’a d’auka ba sai daya sake maimaita kira kafin ta d’auka muryarta a nutse tayi sallama without tasan waye mai kiran sai dai tana jin fad’uwar gaba,kamilalliyar ajiyar zuciya yayi a lokaci guda yana had’awa da lumshe idanunsa ya amsa mata,a bazata taji muryarsa,cikin tsantsan mamaki tace
“Kai ne..!?”
“Ehh! Nine mana,,yaya akayi ne..? Kin yi mamakin jina ne kike tambaya.?”
“A’a.! To akan mene ne ma zanyi mamakin.?”
Lafiyayyen murmushi yayi wanda sai da taji sautin fitarsa har cikin kwakwalwarta yace
“Abunda zance kenan ai,mene ne daga jina zaisa kiyi mamaki..?”
“Uhhuumm.!” Tace ba tare da tayi magana ba,jin yanayin yadda tayi masa response yasa cikin d’aga muryansa kad’an amma ba cikin yanayin hayaniya ba yace
“Hey Lady.! Speak ur mind..”
“Nace me kenan..!?”
“Duk abunda yake ranki..”
“Ni kam babu abunda yake raina bare asani na fad’a..”
“Akwai..” Yace mata cikin sauri
Tace “babu” sake cewa yayi “akwai” itama tace “babu”,ya sake fad’a ta maimaita masa “babu”,murmushi ya saki mai sauti wanda yasa numfashinta tafiya yajin aiki ya dawo a lokaci guda,kafin ta farga kuma ya watso mata tambayar
“Ni d’in kuma ina kika ajiye ni ma’am.??”
“Da a ina nace na ajiye ka ne..!?”
Kamar mai son tunawa ya d’anyi jim sai kuma yayi saurin cewa
“Cikin zuciyarki..”
“Ban fad’a maka haka ba,ni kada kayi min sharri kace na fad’a..”
“Da gaske baki fad’a ba..?”
“Ehh!” Tayi saurin bashi amsa
“Mene ne kike wani bani amsa a gaggauce ne..!?”
A zahiri tayi murmushi sai dai ba mai ba saboda yadda taji yayi maganar kamar wani soko sai taji kamar yana ganinta ta daure tace
“Mene ne kuwa daya wuce son kwanciya da nake yi.”
Siririyar ajiyar zuciya yayi har cikin ransa sai da yaji batun son ajiye wayar da tayi bai masa ba,amma a hakan duk dan baya so ya takurata sai yace
“Bacci..!?”
Tace masa “Ehh!”,d’an lumshe idonsa ya sake yi yana rik’o lower lip d’insa zuwa cikin na saman ya danne da hak’oransa,slowly bayan yayi masa wani irin tsotsar daya bada sauti mai ma’ana kafin yace
“Ok.. A huta gajiya ko.. Sai na zo..?”
Cike da zolaya bcos ita kanta bata gaji da sauraren muryarsa ba kuma bata shiryawa rabuwa da shi da gaggawa ba tayi caraf tace
“Mene ne zai kawo kane..??”
“Kina tambayata me zanzo na yine..!?”
“Ehh! Ai dole nabi ba’asi ne..”
“Uhhuumm.!” Yayi ajiyar numfashin da yasa ta lumshe ido saboda tsigar jikinta da taji ta fara tashi
“Ki jira idan nazo sai ki sake kallona ki maimaita tambayar ki,,na tabbata zaki samu amsar daya dace.. Kin ji ko..?”
“Toh” ta amsa,daga nan suka yi shiru duka har na tsayin lokaci,suna sauraren fitar numfashin juna,,shirun ne ya d’an dame shi,muryarsa kamar yana mata rad’a ko son yin bacci yace
“Lady..! Anya kina sona har yanzun kamar yadda nake yi..!?”
“A’a.. Bana yi ni dai.!”
Amsar yaji kamar fitar kibiya daga bakinta,duk da yasan fad’a kawai tayi amma take yaji jikinsa yayi masa wani iri kamar ana watsa masa narkakken ruwan dalma
“Me yasa kika daina..??”
“Saboda baka yiwa zuciyata adalci ba,a lokacin daya dace ace ta samu y’ancin kanta..”
Idanunsa yayi saurin bud’ewa yana kallon sama
“Me yasa zaki ce haka.?”
“Me yasa bazan ce ba,bayan abu ne daya riga ya faru..”
“Mene ne ya farun..??”
“Kaima ai kasan ko mene ne d’in ya faru.. Mene ne na tambaya ta.? Ko zaka cene baka sani ba..?”
“Ban sani ba,,d’an taimaka ki fad’a min,kin jiiii ladyyy..!”
Yadda yaja sunan sai daya sata sakin wahalalliyar ajiyar zuciyar da sai da taji inama ace yana kusa da ina,a hankali ta rufe itanunta had’e da fad’awa da baya a saman k’atuwar katigarta ta k’arasa kwanciya flat
“Mene ne ya faru lady..??”
Idanunta har lokacin a lumshe tace
“Me ka gani..??”
“Tambayarki nayi,,nd baki bani amsa ba kina min wata tambayar.. Fara bani amsar tambayata first,,sai ki tambaye ni..”
Murmushi tayi saboda yadda take jin dad’in firar,a hankali tace
“Babu abunda ya faru..”
“Ban yarda ba.”
“Ka yarda babu..!”
“Ok.. Tunda baki yi niyyar na sani ba.. Amm baki bani amsar tambayar da nayi ba.”
“Yaushe..??”
“D’azun.” Ya fad’a yana sauraronta
“Mene ne ka tambaya ban fad’a maka ba..?”
“Kince banyiwa zuciyarki adalci ba,,shin wane irin adalci ne na kasa yi mata.?”
“Uhhuumm.! Mu bar wannan maganar.”
“Me yasa za’a barta..?”
“Haka nan naji bana son ayi..”
Murmushi yayi k’asa² bayan yayi wani tunani sannan cikin zolaya yace
“Ok.. An barta tunda bakya buk’ata,,,buh nace za dai kizo aurena ko.?”
Wani haushinsa ne ya sake kunno mata wuyar kishinsa a zuciyarta,musamman kuma daya tuna mata da batun da take k’ok’arin mantawa a dai² lokacin da giyar soyayyarsa ta fara watangariri da ita cikin iska,a hasale ta taso masa tace
“Nazo nayi mene ne..??”
“Ki tayani farin ciki mana.. Ai zaki zo ko..?”
“Bazan zo ba..”
Ta sake bashi amsa a hasale
“Me yasa to..? Baza ki taya ni farin ciki ba kenan..?”
“Kada Allah sa kuyi farin cikin,,to ni inama ruwanna da aurenka..?? Kaje kayi tayi mana sai me.? Sauk’in nima dai ina da mai sona..!”
Tana fad’a tsabar takaicin maganar dake sussukar ta a zuciya duk da kasancewar ta bashi amsa ji tayi hakan bai mata ba sai data had’a d’a kashe wayar,a fusace tayi cilli da ita gefe had’e da fashewa da kuka.
A b’angaren Hammad yadda ya kunnota lokaci guda tana masifa ba k’aramin burgeshi ta sake yi ba,shi dai yana son yaga tana magana da shi babu kunya babu komai musamman kuma akan idonsa a cikin yanayin fushi abun sosai yake k’ayatar da shi,,lumshe idanunsa ya sake yi yayin da ya tafi tunanin moment d’insu daya gabata a d’azun da yaje gurinta,,murmushi ya sake yi mai sauti a hankali ya mik’e yana sosa k’eyarsa da aka babu gashi a gurin saboda yanayin haircut d’in da aka masa,sanda ya gama duk abunda yake kafin ya ajiye komai da yake ya fita zuwa bedroom d’in Mamma’nsa,,lokacin daya shiga a sanan gado ya sameta cikin shirinta na bacci har tama kwanta sai dai da alamun kamar akwai muhimmin aikin da take yi akan waya,sannan duka kamar bata da niyyar ziyartar d’akin Daddy’nsu,da sallama ya k’arasa inda take,bayan ya gaisheta ta amsa masa da kulawa sosai kana ta ajiye wayar a gefe ta fuskance shi
“Ba dai sai yanzun ka dawo ba ko..!?”
“A’a Mah.! Na d’an jima da shigowa,akwai dai aikin dana tsaya yi ne shi yasa ban samu damar shigowa da wuri ba..”
K’ayataccen murmushi tayi masa had’e da tambayarsa yaya ya baro su,ya bata amsa dai² abunda idanunsa suka gane masa,,daga nan suka fad’a hira kafin ya tambayeta yadda suka yi da Daddy,,ranta ne ya d’an b’aci tunawa da yadda suka k’are ta da shi,duk da dai ta nemo mafita kafin lokacin amma tana jin babu dad’i game da halayyar da yake gwadawa akansu,,a nan ta kwashe duk yadda sukayi ta sanar masa,sai dai ta b’oye masa batun Dad da yace mata dole ne Hammad d’in ya rabu da ita ko da kuwa da zinare aka k’erata ya haramtawa maaa aurenta tunda har akanta yake neman yayi jayayya da shi,haka nan batun kiran Malam da tayi shima ta kyale akan gobe idan yazo duka sa ganshi gudunma kada a samu matsala,bawai don tana zargin za’a samu wani ya kaiwa Daddy gulmar ta kai k’ararsa gurin Malam d’inba,sai dan gudun abunda zai faru kafin wayewar garin.
Godiya sosai Hammad yayiwa Mamma cikin tsananin farin ciki ya kwanta a jikinta yana sanar mata murmushi,kansa ta shafa tana masa murmushi itama,ba ita ta kyale shi ya tafi ba sai data tabbatar ta sake kwantar masa da hankali ta hanyar nuna masa amincewarta akna kada yaji tsoro wajen yin abunda zuciyarsa take so,itan zata tsaya masa,sannan suka yi sallama ya tafi bedroom d’insa cikin tsananin farin ciki da goyon bayanta akan neman auren nasa daya taso da shi gadangadan.
Lokacin daya dawo tsabar farin ciki ne yasa gaba d’aya ya manta da abunda ya faru tsakaninsu d’azun kafin ya tafi gurin Mamma,kai tsaye ko daya shigo sai ya sake d’aukar waya ya kirata,sai dai har yayi mata misscall uku bata d’auka ba,,haka yayi ta kira tana kallo saboda tsabar fushi da kishin daya rufe mata ido tak’i amsa masa,dan kansa ko daya kira bata d’auka ba sai ya hak’ura bai sake kira ba ya ajiye wayar bisan bedside drawer,,saman bed d’insa ya haye yana sakin murmushi da fatan ganin wayewar gari lafiya bcos yasan goben nan akwai kafcen da za’ayi a gidan.
(Ni kuwa dai nace danma wasu ya sani bai san wasu ba).
Lokacin daya gama zama yana k’ok’arin d’age bedspread ya rufe k’afafunsa kira ya shigo masa,,bai d’ago ya kalli wayar ba sai da yayi murmushi sannan ya ajiye bedspread d’in yana d’aukar wayar a zatonsa itace take kiran nasa,sai yayi gamo da *NEW NUMBER* yana yawo saman screen d’in wayar,haka nan ya sawa number ido kamar mai nazari shi bai d’auka ba kuma bau katse ba,har sai da kiran ya katse,siririyar ajiyar zuciya yayi yana niyyar ajiye wayar ya kwanta wani kiran ya sake shigo masa,kamar kada ya d’auki wayar haka yaji,nan take nasihar Mamma ta dawo masa cikin kwakwalwarsa akan babu kyau wulak’anci,d’aukar kiran yayi yasa wayar a hands free had’e da yin sallama,cikin siririyar muryarta kamar ta k’ananun yara sosai tace
“Hello..!”
Shiru yayi yana nazartar muryar,kafin yayi magana ta sake maimaita fad’in “hello” muryarta kamar ta mutumin dake shirin yin kuka,siririn tsaki ya saki a ciki ya katse kiran wayar,yana niyyar ajiyewa aka sake kira,d’agawa yayi da sallama cikin yanayin son rashin magana,amsawa tayi tana sakin sanyayyar ajiyar zuciya da fad’in
“My hero.. Ya kake..?”
Jimm yayi yana tunanin wace ce ita kafin ya ce
“Wace ce ke d’in..??”
“Kaii.! Yah Hammad,ko number na ma baka da shi..??”
“Ehhh!” Yace kai tsaye yana sake tambaya
“Wai wace ce ke d’in da kike magana.??”
Duk da taji haushin tambayar amma haka nan ta daure tace masa
*”FALISHA* ce..”
“Daga ina kenan..??”
Ji tayi jikinta ya hau rawa,alamun daya tabbatar mata ko sunanta ma bai sani ba,bare kuma itan kanta,to wai ita kenan wane irin aure ne za tayi,al’halin mijin ma ko saninta bai yi ba.?? Hawaye taji suna gangaro mata a hankali cikin dauriya tace
“Ur wife to be..!”
“Uhhuumm..! Yayi,to ya kike..?”
“Lafiya k’alau.. Kai fa.? Fatan kana lafiya..?”
“Lafiya.” Yace cikin alamun gajiya da magana kafin yace
“Sai da safe..??”
Cikin sauri ta tare shi da fad’in
“Haba Yaya,,me yasa zaka kashe wayan tun yanzun..?? Bayan kai ne ma ya kamata ace ka fara kira na amma kak’i,shi ne kuma na kira zaka min wulak’anci.!?”
“Koh..!”
Ya tambaya babu damuwar komai a kan fuskarsa daga maganar da tayi
“Ehh.! Kuma ma dama kasa nayi ta jiranka amma kaki zuwa..”
“Waye yace miki da zanzo..??”
“Daddyna ya fad’a min zaka zo,amma baka zo ka ganni ba.. Me yasa haka to..? Nayi ta jiranka shiru,kuma nayi jiran ka kira shima baka yi ba,sai nice da na gaji da jira na kira.?”
Kai tsaye yace
“Naje zance ne..”
“Zance fa kace Yaya..”
“Ehh! Haka nace mana..”
Yawun azabar damuwa da bak’in kishi ta had’iye tana sake tambayarsa
“Ina ne kaje..”
“Gurin uwar gidan ki na fara zuwa na gano ta..”
A zabure tace
“Whatttt.!?”
Kyakykyawan murmushi ya saki da fad’in
“Mene ne..?? Kika tsorata..??”
Muryarta cikin alamun dake bayyanar da a kowane irin lokaci kuka yana daf da zuwa mata tace
“Yaya.! Wai har mu nawa ne,naji kana maganar uwar gida..??”
“Biyu.” Ya bata amsa kai tsaye ba tare daya jira ba
“Amma ni Yaya ai ba haka aka cemin ba..”
“Ni kuma haka na tsara,,ko zaki hana ni yin tsarin da zuciyata take so ne..??”
“A’a..! To amma Yaya mene ne yasa zaka auremu mu biyu..??”
“Saboda ita nake muradin yin rayuwa da ita,,,ke kuma…!” Shiru yayi saurin yi dan yasan idan har ya fad’a mata abunda yake zuciyarsa,aka yi rashin sa’a bakinta babu linzami maganar ta komawa Daddy za’a samu gagarumar matsala a tsakaninsu
“Ni kuma mene ne nawa matsayin Yayana..??”
Ta sake tambayarsa,banza yayi mata ba tare daya amsa mata tambayar da tayi ba,jin yadda yayi shiru yasa ta sake maimaitawa,a zatonta ko bai ji bane shi yasa yayi shirun,ajiyar numfashi yayi a hankali kafin yace
“Manta kawai..!”+
“Yah.! Me yasa zan manta..?? Ni dai gaskiya ka fad’a min..”
“A’aahh..”
Takura masa ta nemi yi akan lallai ita tana so sai ya fad’a mata abunda yayi niyyar fad’an shi kuma yak’i,da yake dama tana kan hanya wannan dalilin yasa ta fashe masa da kuka da tunanin zai tausaya mata ya fad’a tunda taji k’awayenta na fad’a mata maza da yawa basa son kuka,wannan dalilin yasa tayi zaton shima Hammad yana cikin wannan ajin,amma sai taga ya nuna he don’t care da kukanta ko shirunta,k’arshe ma yaji haushi ya kashe wayarsa ya rabu da ita tana aikin rusa kuka,,yana kashe wayar ya kai hannunsa saman forehead d’insa yana matsawa da sakin wahalallen numfashi kamar wanda yayi aikin k’arfi a fili saboda takaicin data bashi ya furta
“Huh.! Headache..!”
Ko gama rufe bakinsa bai yi ba wani kiran ya sake shigowa,a hankali ya saki dogon tsaki,cikin jin haushi ya d’auka yana cewa
“Yaa aka yi ne..?”
Sheshshek’ar kuka tayi cikin muryar ban tausayi tace
“Yah Hammad,,me yasa zaka min haka..?? I think duk mutumin dake k’aunarka bai kamata ace ka saka masa ta wannan hanyar ba.. Mene ne laifina dan ina sonka.? Don kawai ina sonka sai ka wulak’anta ni.. Ahhh..??”
“Wulak’ancin na mene ne..!?”
“Kana kashemin waya al’halin baka bari mun gama magana ba..”
Idanunsa ya tsayar guri guda yana sauraren yadda take magana da muryar kuka,cikin zuciyarsa banda haushin ta babu abunda ke mak’ale a cikinta,k’arin haushin ma yadda ta sashi gaba tana tuhumarsa,shi fa gaba d’aya a rayuwarsa yak’i jinin yaga ana kuka a kusa da shi,saboda tayar masa da hankali yake,buh idan kayi masa abun da ba dai² ba kuma ya hukunta dan kayi wannan ba zai sa yaji tausayin ka ba,bcos kaika janyowa kanka faruwar hakan,shirun da yayi mata bai bata hak’uri akan ta daina ba yasa ta sake cewa
“Pleasee Yah Hammad,,idan so na ne baka yi me zai hana kawai ka fad’awa Daddy.. Kaga sai muyi hak’uri da juna,ba sai mun shiga rayuwar junaba matsaloli su fara tasowa..”
“Kinga da Allah da fari dai ki fara dakatar da kukan da kike yimin a kunne,,na biyu kuma ki kyale ni na huta,bcos a gajiye nake,so ina buk’atar hutu yanzun.. Matsalar ki ce wannan idan kina ganin fad’awa Daddy masalaha ne,ke me zai hana kice da baban ki bakya ra’ayina ne kawai..”
“Amma Yah Hammad ban san mene ne dalilin da yasa kake min haka ba,,ko kuwa dan saboda ni baka sona ne,shi yasa na kasa yin daraja a idanunka..??”
“A’ahh..! Saboda dai ke d’in kin kasance *ZAB’IN MAHAIFINA* ce..”
Ji tayi kamar an kwad’a mata guduma a tsakiyar kanta saboda yadda maganarsa tazo mata a bazata,dama tayi tsammanin jin haka daga gare shi,tun lokacin da suka fara maganar ta fahimci abunda yake son fad’a,kuma wannan shi ne dalilin da yasa ta takura masa akan lallai sai ya fad’a mata matsayinta a gare shi,sai dai ko data tambaye shi dalilin da yasa zai auresu su biyu da cewa yayi
“Saboda ita waccen ita yake muradin yin rayuwa da ita,,,amma ita kuma.!” Sai yayi shiru bai k’arasa ba,yanzun kuma ya kira ni da *ZAB’IN MAHAIFINSA* kenan ya tabbata zai aure ni a matsayin *MATAR CUSHE* wacce bata daraja..??”
Maganarsa ce ta dawo da ita cikin hayyacinta inda yake cewa
“Da Allah Malama idan baki da abun fad’a ki kashe waya,ni ina da nawa aikin da nake son yi..”
Kuka ta sake fashewa da shi saboda tsabar takaicin abunda yayi mata ko tsayawa sake saurarensa bata yiba bare ta tsaya bashi amsa,ita kanta wayar saboda bak’in ciki jifa tayi da ita,bayan tayi tsalle daga nan inda ta aiketa sai data daki jikin d’aya wall d’in dake opposite d’inta kafin ta dira a k’asa ko ina na daga sassan ta ya tarwatse ya kama nasa hanyar,yana jin sautin ya fahimci abunda ya faru,amma sai ya tab’e baki had’e da d’age shoulders sama alamun bai damu ba,,waya kuwa tuni tayi d’uu³ ta kashe kanta,kwanciya yayi abunsa bayan ya sata silent ya ajiyeta a gefe saman bedside drawer had’e da juya mata baya,,addu’o’in kwanciya bacci ya fara reciting yana gamawa yayi bismillah ya kwanta a gefen dama had’e da rufe idanunsa.
Tun da farar safiya yau a gidan da gagarumin bak’o suka wayi garin na jumu’ah,wanda ganinsa kad’ai sai da yasa kowa dake cikin gidan jikinsa ya sanyaya,,Daddy kansa ganin Malam sai da yaji wani abu ya tsirga masa a ransa,game da zuwan na Malam,saboda kaf girman gidan tun daga ma’aikata har masu mallakin gidan babu wanda bai san Malam baya tab’a zuwa haka nan ba sai idan da wani babban dalili ko wani abu ya faru sannan ne zaka ga zuwansa,shima kuma yana gama abunda ya kawo shi baya zama yake tafiya. Malam kuwa a nasa gefen babban dalilin da yasa shi doko sammako a wannan lokacin duka baya rasa samun nasaba da son ya tari Daddy a gida,shi yasa ma tun farar safiyar yasa aka kawo shi,saboda su samu suyi maganar daya dace akan lokaci kafin lokacin sallah yayi.
Isowar Malam tasa wasu cikin hadiman dake gidan suka shaidawa Mamma a kan lokaci,ita kuma tun kafin ta fito tuni har ta sa an yiwa Malam d’in masauki a parlor,kasancewar kowa dake gidan yasan matsayinsa shi yasa kafatanin duk wani wanda yake cikin gidan babba da yaro,bayan anyiwa Malam iso suka fara shigo d’aya bayan d’aya suka kwashi gaisuwa cike da girmamawa da kuma karramawa,sannan yasa ayi masa magana da Mamma saboda yana sauri,kasancewar kafin 11am yake son isa masallaci,kun san iyayen mu da kakanni a irin wad’annan b’angarorin na bautar Allah basa tab’a wasa,haka wannan kuma shi ne d’abi’ar Malam a irin wannan ranar,tun kafin yanzun sun kasance tare suke tafiya masallaci da mahaifin Daddy tun kafin Allah ya karb’i rayuwarsa.
Labarin zuwansa ko daya riski Mamma sai da tayi addu’o’i domin neman yardar Allah akan ya d’orata tayi nasara akan mijin nata,daga nan ta taso duka yaranta a gaba suka kamo hanyar sakkowa k’asan dan ayi wacce za’ayi,,lokacin da suka k’araso gaba d’aya a gabansa suka durk’usa saboda girman da yake da shi a gurinsu,ko da suka gaisa aka tab’a wasa da dariya tsakaninsu sannan Mamma ta nemi su basu guri,tashi suka yi gaba d’aya har Hammad amm sai Mamma tayi saurin dakatar da shi ta hanyar cewa ya dawo,,hankalin Malam gaba d’aya yana ga Mamma domin so yake yaji babban dalilin da yasa Daddy yace bai amince ba,kafin ya waiwayo inda yake da yake dama duk ya riga su zuwa,dogon jawabi Mamma ta janyowa Malam cikin abunda ta sani dangane da alak’ar dake tsakanin Hammad da Sabina tun daga tushiya bata yarda ta dire shi ba sai data kai har kan ganyensa sannan ta d’ora da fad’in
“Malam duk wani k’ok’arin da nake tunanin zan iya akan Daddy ya fahimci matsalar da zata iya faruwa nayi,ba don komai ba sai don ya fahimci abunda zai je ya dawo,amma ya nuna min baya ra’ayin na dunga fad’a masa,dana matsa kuma k’arshe cewa yayi tunda har akan batun auren yarinyar ne daga ni har Hammad muke neman yin jayayya da shi to ya haramtawa Hammad aurenta ko da da zinare aka k’irk’ireta..”
Murmushi Malam yayi mai sauti da fad’in
“To too! Kai yanzu Aliyu idan banda abunka kaf fad’in duniyar nan akwai wani d’an adam d’in daya isa haramta wani abu ga wani bawan,idan ba lillahi rabbal alamiiyn ba..? Shi kad’ai yake da ikon hanawa kuma yake da ikon sawa ayi dole ko ana so ko ba’a so kuma haka tilas za’ayi,ba don komai ba sai don me..? Saboda a kaucewa fad’awa cikin fushi da azabarsa.. Duk al’amarin da kaga kayi jayayya akansa amma bai fasu ba,ya kamata ka sake shi,don idan kaci gaba da ja tabbas ubangiji zai nuna maka ishara,,shi lamarin aure ba’a yi masa katsalandan domin idan ka gwada masa taurin kai k’arshe sai azo ayi kai kuma Ubangiji ya amshe rayuwarka,ka godewa Allah da har aka zo wannan lokacin babu wani abu daya same ka,sannan nima ban san da maganar ba sai yanzun,da duk hakan bai faru ba,kuma ni abunda nake so ka sani shi ne batun aure babu fashi tunda har yaro yace yana so,sai mu bishi da addu’ar fatan alkhairi..”
Shiru Daddy yayi tunda malam ya fara magana,sai dai tab’o batun hurumin Allah da yake k’ok’arin saka kansa yasa jikinsa ya sanyaya,to amma shi duk fa ba wannan bane matsalar sa,idan har aka ce an yarjewa Hammad yayi mata biyu lokaci guda ta yaya zai iya sauke nauyin kowacce a kansa,al’halin daga shi har su matan dukansu yara ne.? Ya tabbatar gidan zai zama ana samun sab’ani
“Ka godewa Allah Aliyu,a iya tsayin lokaci da nake ganin matsalolin gidajen aure zan iya cewa ban ga gida irin naka ba,biyayya dai duk irin wacce mutum yake nema da girmamawa daga iyalinsa ka samu,shin me zaisa baza ka saakawa iyalinka da tukuicin da za suyi alfahari da kai ba ko da bayan baka raye.? Wannan hanyar daka biyo ba mai kyau bace domin kuwa kana nuna musu butulci ne akan k’ok’arin kare hak’k’in ka akansu,kuma kasan me gobe zata haifar sakamakon yin watsi da nasu matsalolin..!? Saboda haka ni dai ina baka shawara idan boko tasa kake k’ok’arin danne hak’k’in iyalinka akanka kayi k’ok’arin canjawa tun kafin a samu matsala wata rana suyi maka bore.”
Nasiha sosai dai Malam yayiwa Daddy mai shiga cikin jini da b’argonsa kafin ya tambaye shi dalilinsa na k’in amincewa da maganar da Hammad d’in yazo masa da ita,nan fa Daddy yayi shiru saboda shi da kansa ya fahimci duk wani dalilin da zai kawowa Malam ba mai k’arfi bane,bare ace za’a yarda da shi,wannan dalilin yasa sai yayi shiru bai ce komai ba bare ya kaishi ga jin kunya,,ga Malam kuwa tunda yaga yayi shirun nan,kawai sai ya rabu da shi,ba tare daya tilasta masa ba,bcos shima d’in ya fahimci amsar shirun na Daddy,wanda da ace zai tursasa shi tofa k’arshe kunya zai bashi a gaban iyalinsa,,juyowa yayi inda Hammad yake zaune a gabansa ya dafa kansa da fad’in
“Muhammadu.! Allah ya albarkaci rayuwarka,,yadda kake kamanta yin biyayya akan umarnin mahaifanka,ubangiji ya dube ka,ya baka y’ay’a na gari,shiryayyu wad’anda zasu ji k’anka,masu yi maka biyayya..”
“Ameen Malam” shi ne abunda gaba d’aya suke fad’a hatta Daddy dake zaune gefensu,,lokacin bayan sun gama duk tattaunawar da za suyi akan batun daya kawo shi,suka tab’a hira wacce ta sake d’aukan su tsayin wani lokaci kafin Malam yayi sallama dasu da shirin komawa,sai dai kuma ko kafin ace ya tafi,sai daya barwa Daddy sallahun lallai² kafin nan da bayan sakkowa a masallaci yasan yadda zaiyi ya nemo masa wad’anda zasu yi masa rakiya wajen nemawa Hammad auren,tunda shi yayi furucin babu hannunsa a ciki to shi ya saka nasa.
Da girmamawa Daddy ya amsa masa,daga nan suka masa rakiya har bakin mota,sai da suka ga tafiyarsa sannan duka suka juyo jikin kowa cikinsu a sanyaye,yayin da fuskokin Mamma da Hammad kana kallo zaka hango tsantsar farin cikin da suka tsinci kawunansu aciki.Daddy shi ya fara barin gurin ba tare da yayi musu magana ba,Hammad kuwa ganin babu Daddy a gurin yasa shi rungume Mamma idanunsa d’auke da hawayen farin ciki yana fad’in
“Thank u Mah.! Ana ahabbuk..!”
“Wa’ana ahabbak-thtiir habibiiy..”
Sake k’ank’ame ta yayi yana sakin sanyayyen murmushi mai bayyanar da samun nutsuwa da kwanciyar hankali kafin ya sake ta yana fad’in
“Mah.! Ki samin albarka,,zanje gurin surukarki yanzun na dawo..!”
Ido waje take kallonsa
“Baby..! Yanzun bai yi safiya ba..??”
Kai ya kad’a mata yana fad’in
“A’a Mah,, bai yi ba,nifa d’an gida ne ko kafin wannan lokacin naje babu wanda zai tambayeni dalili,tun kafin wannan lokacin sunyi sabo da ni,kawai dai ki samin albarka..!”
Dariya tayi masa while tana bashi amsa
“Kullum a cikin saka maka albarka nake Yarona,, kai dai kaci gaba da godiya ga Allah sannan ka nemi yardarsa,in sha Allah idan har ya yardar maka babu kai babu tab’ewa.”
“In sha Allah Mah..! I will.”
“Yawwa.! To maza jeka abunka Allah ya bada sa’a.. A gaida min y’ata..”
Murmushi yayi mata yana lumshe idanu had’e da rausayar da kai alamun zata ji,sannan ya juya da sauri ya nufi carport,yana tafe yana sakin murmushi mai burgewa,sai daya shiga cikin mota ya zauna dai² sannan ya ciro handkey daga aljihunsa ya goge hawayen da suka gangaro masa,,lallai ubangiji ya isa a bauta masa shi kad’ai ba tare da an had’a shi da kowa ba,,idan ba har ubangiji yana sonsa da rahama ba,da kuma k’addarawarsa cikin al’amuran ko wane bawa,ta yaya ne yake tunanin zai samu irin wannan damar a lokacin da babu zato haka..? Murmushi ya sake yi mai ban sha’awa yana kad’a kai sannan ya fice daga gidan,,cikin sak’e²n zuci har ya k’araso k’ofar gidan yayi parking bai daina jinjina al’amarin ubangiji ba,sai daya kalli k’ofar gidan sannan yayi k’ok’arin sauke seat d’insa yayi baya da shi kad’an bayan ya zare seatbelt daga jikinsa ya d’auki wayarsa ya kira line ta,sai daya kira ta har wajen three times kafin ta d’auka cikin kumburi tana fad’in
“Mene ne kuma..??”
Dariya yayi mata mai sauti had’e da fad’in
“Fito waje..!”
Yana fad’a ya datse kiran ba tare daya bata damar yin magana ba.
A cikin gida tsabar takaici ne ya sake kunnota dama haushinsa take ji tun dare shi ne zaiyi mata titsiye yanzun,tsabar ma ya raina mata aji shi ne bazai bari tayi magana ba ya kama ya kashe waya,ai kuwa zai gane KUSKUREN da yayi,dan ita bata shiryawa hakan ba,kuma ita a niyyarta ma tace masa bata garin kawai sai bai saurare ta ba,wayar tabi da kallo bayan ta cije gefen lip d’inta na k’asa a fili tace
“Barin je naji da wacce wannan halittar yazo min..”
Tana fad’a ta zaro hijab tayi tsakar gida,sai data lek’a d’akin Innarta ta fad’a mata sannan tayi waje,lokacin data fito a dai² side d’insa ta tsaya tayi knocking glass d’in gefensa,tunda ta taho yana kallonta har ta k’araso baiyi yunk’urin tashi ba,ganinta tsaye kusa da shi yasa shi sakin murmushi kafin ya gimtse ya sauke glasses d’in da fad’in
“Mene ne.!?”
Fuskarta a tamke ta kalle shi da fad’in
“Kamar yaa..??”
Kallonta yayi ya tab’e baki bayan ya d’auke kai gefe ya ce
“Shigo ni mu tafi,kafin ki b’ata min wasa..!”
Har lokacin tana tsaye wajen da take tace
“Ban gane ba..! Ina za muje..??”
“Ke dai ki shigo mana,ko an ce miki zan saida ke ne..!?”
“Waye ya sani..”
Murmushi yayi ba tare daya sake magana ba,ita ma saita zagayo ta d’ayan side d’in,da kansa ya bud’e mata motar bayan ta shigo ta zauna ya fara k’ok’arin tada mota kamar gaske,kallonsa tayi da sauri tana fad’in
“Wai ni ban gane ba,ina ne zaka kai ni..??”
Har lokacin bai kalli inda take ba yace
“Zance zaki raka ni..!”
Hankali a tashe ta ce
“Meh..!? Wollahi ba dani ba..”
Tayi maza zata bud’e motar ta fita ya danna lock,sank’amewa tayi a zaune kafin ta waiwayo ta kalle shi
“Dan Allah ka bari,,kaga dai bana so ko.!?”
Lumshe idanunsa yayi yace
“Uhmmm! Na sani,,amma me yasa baza ki raka ni ba..!?”
“Akan mene ne zan bika..??”
“Rakiya fa zaki yimin daga nan sai na gabatar dake a matsayin mata ta da zan aura a nan gaba..”
Girar sama data k’asa ta sake had’ewa,a fusace ta d’ago za tayi magana amma kuka ya riga maganar tahowa,dole tasa tayi shiru ba tare data ce komai ba ta juyar kanta d’ayan side d’in tana kallon waje,sai data matse son ranta sannan ta saki sanyayyar ajiyar zuciya da fad’in
“Bud’e min na fita..!”
“Zuwa ina..??”
Shiru tayi masa bata bashi amsa ba,shima yayi mata shiru while har lokacin idanunsa akanta yana jin zuciyarsa kamar ya kamota ya rarrasheta,sai da suka d’auki tsayin lokaci a haka kafin ya d’ago daga kishingid’ar da yayi yana kallonta
“My Lady.. Zaki iya aurena kuwa..??”
“A’aahh..!” Shi ne amsar data bashi kai tsaye ba tare da tunani ba
“Me yasa zaki ce haka..??”
Idanunta ta sake lumshewa hawaye suka sake gangaro mata,,still tana kallon waje tace
“Saboda bana sonka..!”
Murmushi yayi mai santi sannan yace
“Ban yarda ba..!”
“Ya kamata ka yarda.” Tayi saurin sake bashi amsa
“Bazan tab’a yarda dake ba.”
“Me yasa ba zaka yarda ba..”
“Saboda ba ni kika kalla kika fad’awa bakya so na ba.”
Murmushi tayi mai ciwo kafin tace
“Idan na kalleka na fad’a shi ne zaisa ka yarda..!?”
“Ehh! Zan yarda mana..”
Juyowa tayi a fusace sai dai idanunta a k’asa tace
“Na fad’a bana son ka..!”
Murmushi ya sake yi da fad’in
“Ke yarinya ce har yanzun,idan na fad’a miki magana ki dunga yarda,,buh idan kina ganin kin isa ai d’aga idonki za kiyi ki kalleni ido da ido ki ce Hammad bana son ka,,sannan ne zan yarda kin daina sona..”
Lumshe idanunta tayi had’e da matse su gam,a hankali ta waresu tas akansa with much confidence na zata fad’a masa,,yadda kyallin hawayen suke kwance ciki suka k’awata su tamkar an tsoma cikin mai,a hankali ta shiga jujjuya su tana kallonsa,tunda ta d’ora su akansa da murmushi ke kwance a saman fuskarsa take yasa ta kasa furta ko kalma d’aya sai kallon-kallo da suke ma juna mai d’auke da manyan sak’onnin k’auna,sun d’auki tsayin mintuna a haka kafin yayi gyaran murya da fad’in
“Uhhuumm.! Ke nake saurare..!”
Kasa magana tayi sai kallon kawai da take binsa da shi,yayi magana wajen sau biyu amma bata amsa ba,wannan dalilin yasa shi kallonta a nutse,babban yatsansa ya had’a dana tsakiya ya murza har sai da suka bada sound a dai² fuskarta,saurin kyafta idanuwanta tayi,shi kuma hakan yasa shi tabbatar da batama san abunda ake yi ba,fuskarsa ya matso dai gefen kunnenta ya rad’a mata
“Haba yarinya ni dai nasan baza ki iya ba, taurin kai ne kawai irin naki yasa kike tunanin ke d’in wata jan wuya ce,,kallona kad’ai yasa ki manta inda kike ina kuma ga…”
Shiru yayi bai k’arasa ba yayi saurin komawa ya jingina yana sakin murmushi,tsuke baki tayi tana kallonsa
“Mene ne tunanin kane a kaina..??”
“Na aure ki..!?”
Ya bata amsa ba tare daya kalle taba
“Bazai yiwu ba..!”
“Ya yiwu an gama..”
Bata kalle shi ba itama tace
“Sai ayi na gani,,ba dai saina amince ne za’ayi ba..!?”
“Amincewar wa..!? Naki wai.?”
“Ehh! To da nawa.!?”
Murmushi ya saki mai sauti kafin yace
“Shi kenan,zamu gani,,buh yanzun dai kije gida,anjima idan na dawo daga masjeed zan zo sai muyi maganar..”
Yana fad’a ya bud’e mata lock d’in,ba tare data juyo ta kalleshi ba tace
“Kazo kayi min me..!?”
Tana fad’a tayi maza ta d’ora hannu kan murfin motar zata bud’e,had’e da masa gunguni,saurin fizgota yayi ta dawo,tana tahowa tayi masauki a jikinsa kamar wacce mayen k’arfe ya fizgo,rik’eta yayi sosai a jikinsa while yana kallon fuskarta,yadda duk ta firgice ta kasa d’aga ido yasa shi sakin siririn tsaki sannan ya sake ta
“Allah ya baki sa’a,ina magana kina bani amsa,wata rana idan kika yi sai dai kiji..!”
Saurin katse maganar yayi ba tare data k’arasa ba ya dai girgiza kansa kawai alamun zata ji jiki idan hakan ta sake faruwa,a tsorace ta fice daga motar ko waiwayowa bata yarda ta sake yi ba ta shige gida,yadda yaga ta fita ko waiwayensa bata yi ba yasa shi sakin ajiyar zuciya sannan shima ya tada motar ya bar unguwar.
*After salatul jumu’ah…*
Cikin sauri² Daddy ke sakkowa daga stairs yana tafe yana gyara zaman wristwatch dake d’aure a tsintsiyar hannunsa,Mamma ce ta biyo shi a baya cikin sauri tana fad’in
“Yallab’ai please..! Wait a minute..!”
Juyowa yayi saurin yi fuska a d’aure dan tun tafiyar Malam har lokacin bai yarda yayi dariya ba kuma wani magana bai had’a su ba,har ya fita masallaci ya dawo,kallonta yake har ta iso daf da shi,itama sai data kalleshi kamar yadda yayi kafin tace
“Malam fa kasan yana hanya.. Kuma..!”
“Na sani,,ba sai kin fad’a min abunda zanyi ba..”
Yana fad’ar haka ya juya abunsa ya fice,nan inda ya barta tsaye fuskarta cike da mamakinsa yasa ta sauke dogon numfashi kafin ta koma ciki da damuwa a afuskarta,,a harabar gidan bayan fitowar Daddy ya had’u da *ALHAJI MUKHTAR BABANGIDA* shima yana niyyar fitowa daga motarsa,da sauri Daddy ya k’arasa ya iske shi a gurin suka yi hannu cikin farin ciki da barkwanci irin na dad’ad’d’iyar abota data rikid’e zuwa y’an uwantaka,bayan sun gaisa suka koma can gefen garden saman wasu fararen kujeru domin su tattauna batun yadda zasu fuskanci *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* da maganar auren Hammad,duka basu jima da zama a gurin ba motar Malam ta shigo cikin harabar gidan.Mamma dake tsaye ta balcony tana sauraren taga Daddy ya fita sai taga sun nemi guri sun zauna,still tana tsayen kuma dai ta hango shigowar motar Malam,godiya ta d’aga hannunta sama tayi ga rabbul alamiiyn kafin ta samu kwarin guiwar barin wajen.
A gefen su Daddy lokacin da motar Malam ta shigo kallon *ALHAJI MUKHTAR* yayi da fad’in
“Shi kenan,ina ganin wannan maganar kuma sai dai musan yadda zamu yi da ita,dan ga Malam nan ya samu damar k’arasowa..”
“Toh.! Alhamdulillah ai tunda ya k’araso sai mu tafi ko..!?”
“A’a tafiya kam babu ita har sai Hammad ya zo.. Ni banma san ina ne ya nufa ba tunda aka sakko daga masjeed..”
Murmushi Daddy’n Sultan yayi yana fad’in
“Sha’anin yara kenan,sai hak’uri..”
Mik’ewa suka yi duka suka nufi inda motar Malam take while Daddy yana ta k’ok’arin yaga ya kira line Hammad,,a nasa gefe kuwa Hamad cikin fad’uwar gaba ya d’auki kiran Daddy da sallama a bakinsa,bayan da Daddy ya amsa yake tambayarsa
“Hammad.! Kana ina yanzun..!?”
Amsa ya bawa Daddy akan yana tare da Sultan a gidansu,Daddy cikin sauri yace
“Maza² duk abunda kake yi ka bari kazo gida ka same ni..!”
Yana fad’a ya katse kiran,duka tsakani ko mintuna biyar ba’a d’auka ba suka k’araso tare da Sultan,cikin girmamawa bayan zuwansu zuwansu suka gaida iyayen da kakan nasu wato Malam,daga nan Daddy yayi musu umarnin su shiga mota dan su samu suje gaba d’aya,,jin abunda Daddy ya fad’a yasa waiwayowa ya kalli Daddy daya shiga mota yana murmushi kafin yace
“Aliyu..! Kai da babu sa hannunka ina ne kuma kake k’ok’arin zuwa yanzun..!?”
Fuskarsa da damuwa ya d’ago ya kalli Malam da fad’in
“Ayi min hak’uri Malam,,tuntub’en harshe ne yasa ni aikata hakan.”
Jinjina kai Malam yayi ba tare da ya sake magana ba ya shiga mota suka kama hanya gaba d’ayansu.
Mamma dake tsaye har lokacin tana kallon duk abunda yake wakana bata san lokacin data saki wani kwantaccen murmushi ba,a hankali kuma tasa hannunta ta goge fuskarta da hawayen farin ciki ya gangaro.
In less than 20 minutes motocinsu suka iso line gidansu Sabina dake cikin unguwar *KAWON MAI GARI* bayan duka sun samu guri sun yi parker a gefe,sannan Malama yasa Hammad ya kira Baban Sabina,,cikin k’ank’anin lokaci Baban Sabina shima ya hallara a k’ofar gidansa da yake yasan da batun zuwan nasu,kuma har yasa an tanade su,ko daya fito gaisuwa aka fara tsakaninsu mai cike da barkwanci,daga nan suka k’arasa zauren gidan suka zazzauna a kan k’atuwar tabarmar da yasa a shimfid’a musu,fita ya sake yi ya barsu da niyyar yiwa wasu cikin mak’otan su,da kuma wasu cikin irin mutanensu tun na can wudil magana,kasancewar shima duk ya sanar dasu,kuma shi d’in suke sauraron jin yayi magana,sai kuma k’anin sa wato baban LADO da shima sanar masa.
Lokacin da suka riske su,sai da aka sake y’an gaishe² sannan Malam ya shiga koro bayanan abunda yake tafe dasu,cikin mutuntawa da girmamawa Babah ya wakilta k’anin sa Baban LADO sai wani dattijo d’aya a cikin wad’anda suka tab’a karb’awa Hammad auren a wancan lokacin suka amshi batun,,cikin mutunci da girmamawa aka yi komai aka gama,Daddy da kansa yana batun bada sadaki,Baban LADO yayi hanzarin tarar su,ta hanyar sanar da su komai daya wakana a baya,wanda ya had’a har da batun bayar da sadaki da Hammad yayi,bayan nan kuma ya d’ora musu da fad’in
“Dama mu tuni abunda muke jira shi ne lokacin da za’a tsaida batun aure..”
Mamaki sosai ya bayyana saman fuskokinsu,wad’anda basu fahimci dalilin aikata hakan da suka yi ba suka nemi farawa daga gurin Malam, shi ya fayyace musu kaf abunda ya sani,daga nan suka bukaci sanin bayanin yadda aka yi hakan ta faru,,Baban LADO dai still shi ne ya sake shaida musu kaf yadda al’amarin ya kasance,bayan gama sauraren bayaninsa jikin Daddy ya sake yin sanyi,,yayin da a b’angaren Malam kuma yake binsa da kallo cikin wani irin fuskar da sai daya haddasa masa shan jinin jikinsa,,lokacin da ake batun yanke ranar aure Daddy da kansa ya sake rok’onsu Baba akan suyi hak’uri a had’a bikin ayi shi lokaci guda tunda duka ko an yinma dai bayan auren tattarawa za suyi duka su tafi U.S kasancewar gurin aikinsa nacan,ba don su Baba sun so ba haka suka amince aka tsayar da nan da kwana biyun da suka rage a matsayin ranakun biki,duk da dai ba haka su Babanta suka so ba,sai don dattijon da suke gani a tare da su Daddy da yasa baki..
Kai tsaye su Daddy bayan sun baro gidan su Sabina sallama suka yi da Malam ya wuce gida,yayin da su biyun shi da Abba’n Sultan suka d’auki hanyar gidan su Amarya Falisha domin ganawar sirri da iyayenta akan gagarumin uzurin daya taso musu lokaci guda,tunda suma d’in da kansu basu yi tsammanin hakan zai faru ba,shi yasa ko yanzun da al’amarin ya taso musu a haka,suka ga dacewar sanar da su akan lokaci kafin azo ana k’ananun maganganu na ba’a san hakan zai faru ba,koma wasu suce an munafiurce su,,su kuma su Hammad Daddy sai ya basu izinin tsayawa suga ita Sabinar su samu damar shirya abunda suke ganin zai yi kafin sake k’urewar lokaci,a zaton Daddy yana ganin kamar Hammad d’in bai zo gidan ba kafin wannan lokacin.
Ko da su Daddy suka tafi a waya ya fara kiranta,sai dai har ya k’araci kiran bata amsa ba,dalilin da yasa yayi tunanin ko fushin da take yine yasa tak’i d’aukan kiran bayan yasan warhaka ma tana kallo,,duk dauriyarsa sai da lamarinta ya matuk’ar d’aure masa kai,buh all he knows kuma yayi believing wa zuciyarsa shi ne duk wannan abun da take da zaran an daura musu aure komai zai zame musu mai sauk’i,imma gobe ko jibi or whatever ma duka idan har Allah ya nufa sun kai lokacin komai zai zama tarihi a gurinsu,sanyayyar ajiyar zuciya yayi ba tare daya kalli side d’in Sultan ba ko taking any excuses apart from him yayi ficewarsa daga cikin motan yana dumfarar k’ofar gidansu,cikin sauri Sultan ya sauke glasses d’in motar da tambayarsa
“Dude.! Ina zaka je ne.!?”
Bai juyo ya kalleshi ba continuously yana tafiya har lokacin yace
“Kasa ido kayi kallo.!”
Yana fad’a ya wuce abunsa kai tsaye zuwa cikin gidan ya bar sultan da binsa da kallon tsantsar mamaki,a zauren gidan yayi sallama,Inna dake tsakar gida tana y’an hidimominta ta amsa masa da fad’in
“A’ah.! Muhammadu,shigo mana,kai da gidanku mene ne na tsaya a zaure.!?”
Da sallama ya shiga ciki his head where looking to the ground,Inna tayi masa masauki zuwa d’akin da Sabinar take kwana,wani sallamar ya sake yi yana shiga ciki,babu kowa a ciki sau shi kad’ai,a lokacin daya gana sauke tsammanin samunta a cikin sai ya zama bai tarar da itan ba,tun daya shigo a hankali ya fara kallon yanayin d’akin ta ko wane edge,,babu laifi gidansu dai² zaman mutum d’aya a talauce,nd cikin d’akintan ma gaba d’aya babu wani tarkace,gaba d’aya abunda ke cikinsa idan aka d’auke katifarta ta bacci sai d’an madaidaicin closet d’inta mai k’ofa biyu,lesser dake shimfid’e a cikin d’akin ta ko ina,sai ko wani d’an k’aramin table da aka yishi da katako,ajiyar zuciya ya saki a bayyane kafin a hankali ya nemawa kansa gurin zauna half a gefen katifar,yayi shiru yana tunanin ganin ta inda zata b’illo.
Sai yanzun daya zauna ne yake jin zuciyarsa tana tuhumarsa dalilin da yasa tun baya ya kasa kaima su Badra ziyara a skul d’insu,yanzun gashi har ana neman rufe shekara guda da batun zuwansu k’asar amma sam bai tab’a tunanin zuwa ba dai² da rana guda yace yau bari ya duba su,sai ko yanzun da yaji hakan yazo masa a zuciyarsa,,tunani ya sake sauyawa inda yake kallon kasa a matsayin mara sa’a,cos duk da ace ya je babu ta inda za’a ce ma baza su had’u ba,sai dai ko daya tuna hukuncin ubangiji wanda sai ya nufa ne al’amari yake kasancewa,sai yayi ajiyar zuciya a bayyane nd ya kai hannunsa kan wayarta dake ajiye gefensa yana jujjuya ta hannunsa,sai daya d’auki tsayin wani lokaci kafin ya ajiyeta yanda ya gani.
A tsakar gida bayan da Inna tayi masa iso d’akin ta duk babu wanda ya sani tsakanin ita ko Baba,buh abunda zasu iya d’orarwa kawai da batun sallamarsa shi ne Innar ta amsa daga nan kuma su da yake suna tare ne a d’akin Baban nata,yana mata bayanin komai da yadda ya kasance shi yasa basu ji lokacin daya shigo ba,bayan kamar minti uku Innar ta lek’o tana shaidawa Baba Muhammadu ne yake jiranta,izinin tafiya kawai ya bata da yake dama sun gama maganar a time d’in kawai yana tambayarta ne ko akwai abunda zata fad’a,tace masa A’a bata da shi,sallamar ta yayi daga nan itama ta kama hanyar fita.+
*FALISHA’s DOMICILE..*
K’ara ta fasa mai firgitarwa bayan da tayi jifa da wayar a fusace,had’e da sakin kuka mai tsanani tana cakumo gashinta,yadda take yi sai ya zama kamar irin wacce ta fara wucewa d’in nan ne (haukace),cikin muryar kuka take dukan tsakiyar bed d’in tana watsi da duk abunda idonta ya kai kai da fad’in
“Dama na sani.. Bazan tab’a daraja a gurinsa ba..! Me yasa..?? Me yasa³.!”
Ci gaba tayi da kuka,a cikin wannan yanayin Mamah ta shigo ta same ta,da sauri ta nufo inda take,sai data rik’o ta gam a jikinta sannan tayiwa fuskarta kyakykyawan rik’o tana mata kallon tsanaki mai tafe da tambaya
“Leesha.! Mene ne..? Me yake damunki..??”
Still sake kecewa tayi da kuka without ta furta even a single word da Mamah zata gano dalilin damuwar,jijjigata ta fara yi cikin sigar rarrashi,bayan ta kwantar da kanta a jikinta cikin muryar mai d’auke da tsantsar tausayi ta fara magana
“Yi shiru My Lee,kiyi hak’uri haka nan kinji.. Kefa amarya ce,kuma u know amare basa kuka.! Me zai sa tun yanzun zaki b’ata taron bikinki da hawaye.?”
“A’ah.. A’aahh! Mama,dole ne nayi kuka.. Ki tafi ki kyale ni kawai..”
“Me yasa ne Lee.!? Kiyi hak’uri ki bar kuka kinji,ko mene ne yake damunki ki sanar da ni kinji..!?”
Kai ta girgiza alamun toh,kafin ta fara whipping tears d’in da suka mata kaca² da fuska tana yi tana gyad’a kai kamar lizard,sake rik’o shoulders d’inta Mamah tayi tana tambaya
“Yanzu fad’amin mene ne yasa ki kuka..?? Aahh..!?”
Ido ta matse a hankali wasu sabbin hawayen suka sake gangarowa,sai da ta sake matsewa kafin tace
“Mamah..! Da gaske ne mu biyu zai aura..?”
A bazata tambayar tazo wa Mamah wanda yasa har sai data nemi rud’ewa amma ta dake bata nunawa Falisha komai ba a zahirance,da sauri ta matso kusa daita sosai tana k’ureta da kallo
“Me kika ce Leesha..!? Ku biyu kamar yaya..!? Ban gane ba.”
Gyad’a kai ta sake yi cikin kuka² tace
“Is that true Mamah..!? Just answer me with yes or no.”
Kafad’a Mamah ta d’age tana girgiza kai
“Bana tunanin haka..! Amma idan har hakan nema ai ya kamata ace mun sani tun da wuri,,to ma ke waye ya fad’a miki wannan maganar ne..!?”
“Shi ne ya sanar da ni yanzun da kansa.!”
Girgiza kai Mamah ta kuma yi a hankali ta sauke wahalallen numfashi tana cewa
“Bana tunanin wannan maganar gaskiya ne,tunda mu ba’a sanar damu da wuri ba,idan ma ace gaskiya ne,ina tunanin sai dai idan tun farko babu ita yanzun ne aka k’irk’iro ta..Amma.!”
Sai tayi shiru tana sake zurfafa tunaninta akan maganar,tabbas tunda har Falisha take kuka akan maganar da basu tabbatar ba zai yi wuya ace babu alamun k’amshin gaskiya a cikinta,toma wai idan ba gaskiyar bane me zaisa ne Hammad ya fad’i irin wannan maganar da wasa.?
“Mamah.!”
Cikin kuka tayi kiranta amma sai ta kasa furta komai,dole yasa tayi shiru tana sakin sheshshek’ar kuka mai cin rai,tarairayota Mamah ta sake yi cikin alamun da suke bayyanar da tana saurarenta tace
“Uhhuumm.! Fad’a min mene ne..!?”
“Bana son mu zauna mu biyu,,please ki fad’awa Abba,bana son zama da kishiya..”
Ran Mamah a jagule ta kalli y’ar tata tana shafa kanta cikin rarrashi
“Kada ki damu Leesha,hakan ba mai yiwuwa bane,,ki kwantar da hankalinki kinji..!?”
Kai ta gyad’a mata da sauri
“Mamah do u know something..!? Har cikin zuciyata jin ba zan iya sharing miji da wata ba,u know ina da tsananin kishi a kan abunda zuciya ta ke so,ta yaya ne zan yarda mu had’a miji da wata kucaka..!?”
“Bazai tab’a yiwu ba Leesha,, ki kwantar da hankalinki then ki nutsu sosai har mu tabbatar da ingancin maganar,ni nan da kaina zanyi magana da Abba’n ku,ya kamata ya tambaya mana iyayensa gaskiyar magana,idan har magana ta tabbata gaskiya sai dai su san yadda za suyi da waccen,saboda ba zai yiwu a had’a min y’a da kishiya ba,kina k’aramarki ace za ki zauna da kishiya,ta yaya ne za’a ce ni ban zauna da ita ba,ke ina ji ina gani,da raina da lafiyata zan yarda a kaiki gidan kishiya..!? Wannan ai abune da bazai tab’a yiwuwa ba a gurina..”
Wahalalliyar ajiyar zuciya ta saki tana sake rik’e mahaifiyar ta a jikinta sosai
“Thank u Mom,, am so proud of u..”
Rungume ta Mamah tayi back tana shafa kanta had’e da yi mata murmushi mai sanyawa zuciya nutsuwa,a hankali ta lumshe idanunta da fad’in
“Maza to ki kwanta ki huta kinji My Lee,, da safe idan Allah ya kaimu zan yiwa Abba’n ki maganar kinji ko..!? Bana son ki kuma tashin hankalinki akan irin wad’annan minor things d’in,kin fahimce ni ai.?”
Jinjina kai tayi slowly ta zame ta kwanta tana sakin wahalallun ajiyar zuciya,Mamah dake kusa da ita taja mata bedspread ta rufeta half da fad’in
“Sai da safe..!?”
“Ehhh Mamah..!”
“Ok.. Bye,,sleep tight.”
Ta d’ora mata peck a chicks sannan ta fita bayan ta tabbatar Falisha’n ta kwanta.
Tun kafin su Daddy su k’araso gidan tuni har sunyi magana da Abba’n Falisha sun sanar masa suna kan hanyar gidansa,ba tare da sun d’auki lokaci mai tsayi ba sai gasu sun k’araso,,tsarin gidan kam babu laifi,flat ne amma ya tsaru tun daga wajensa har ciki,dai² gwargwado dai yayi kyau nd dai² arzik’in mamallakinsa,a mutunce cikin rufin ashirin Ubangiji,,lokacin da suka k’araso sun samu tarba mai kyau daga hadiman gidan cikin umarnin Abba’n Falisha,bayam yasa an musu masauki a guestroom d’insa,da yake shima d’in baya gidan sun dai yi waya lokacin yana daf da k’arasowa,a gurguje lokacin bayan ya k’araso garesu ko daya shiga inda suke suka gaisa Abba’n Sultan yayi masa bayanin dalilin zuwansu,a zahiri ya nuna yayi na’am da batun nasu harma ya nuna musu ai babu komai hakan da suka yi shi ne dai² kuma sun samar da masalaha kasancewar sunyi masa bayanin komai daya shafi alak’ar Hammad da Sabina tun kafin wannan lokacin kamar yadda suma aka sanar musu,bayan sun gama magana kuma suka yi sallama da shi ya musu rakiya har bakin mota drivern su dake jira a waje yaja suka bar gidan.
Kanta a sunkuye tana kallon k’asa tunda ta fito daga gurin Babah har ta shigo d’akin,tunani take amma wani irin kwantaccen murmushi ne a saman fuskarta,har ta shigo bata san me yake faruwa ba sai dai tayi magana k’as² cikin shauk’i har tana had’awa da lumshe idanunta
“Lokacin nasara ya soma.. Gaskiya na tabbata cikin mutane masu sa’a..!”
Tun kafin ma ta k’arasa ta hango shi zaune,da mugun mamaki ta sake kallonsa not believing shi take gani ta juya zata koma waje,sai a nan shima d’in ya d’ago kansa ya bita da kallo,har ta kai bakin k’ofa zata fita ya dakatar da ita ta hanyar tambaya
“Ina kike shirin zuwa kuma.!?”
Saurin juyo tayi tana kallonsa cos da bata yardarwa kanta shi ne da gaske ba,sai data tab’e baki sannan ta dawo da baya cikin wani sabon salon had’e fuska,inda wayarta take ta nufa ba tare da tayi masa magana ba,gently tasa hannu ta d’auki wayarta ta bud’e still kuma bata yi yunk’urin masa magana ba taci gaba da clicking,number Badra take k’ok’arin kira ganin bata da niyyar masa magana yasa shi fizge wayar a hannunta shima fuskarsa a had’e
“Me kike nufi ne.!? Baki yi kama da masu irin wad’annan behaviours d’in ba,sam banyi tunanin haka daga gare ki ba.. Wai ma mene ne matsalar ne..!? Mene ne matsalarki da ni..? Ina binki kina nuna min u don’t care about me.? Me kike so nayi..??”
“Ni babu abunda nake so..”
“Ban yarda ba,,defiantly there must be something hidden.. Ki fito ki sanar min,bana son wannan halin da kike nunawa,,am frank idan zanyi abu kai tsaye nake yinsa,so bana son ki b’oye ki sanar min..”
Idanunta ta rausayar slowly sannan ta juya masa baya
“Ni na fad’a maka babu.. Tunda na fad’a ka yarda..”
“Ba zan tab’a yarda ba kuma kema kin sani.”
“Okay..!”
Ko gama bari ta kai aya baiyi ba ya mik’e a fusace ya birkitota suka fuskanci juna,yadda ya taso mata da zafinsa ya haddasa mata tsoronsa,yadda yaga ta firgice sai ya sassauta murya k’asa² yana mata magana
“Fad’amin ina sauraron ki yanzun..”
Tsabar kishinsa dake sakatar mata zuciya da tsoron daya bata har bata san lokacin data fad’a jikinsa ba ta fashe da wani irin kuka,idanunsa ya runtse yana jin haushin kansa,all he knows kuma yayi believing ma zuciyarsa at that time shi ne ya janyo zubar hawayenta,nan kuwa bai san tsabar damuwa ne da kishinsa ne suka sa ta shiga yanayin ba,hannayensa ya mayar bayanta yayi holding d’inta tight a jikinsa,calmly yake caressing spine d’inta
“Please Lady idan baki yi shiru ba zaki sa na rasa control.. Kiyi shiru haka nan ki fad’amin damuwar..”
Sai ya d’ago chin d’inta yana goge mata hawaye,shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya,a hankali ya zubawa kyakykyawar fuskarta idanu
“Uhhuumm.! Zaki fad’a min yanzun..??”
Da kai ta amsa masa sai ya kama hannunta suka zauna duka a bakin katifarta,sai da d’akin ya d’auki shiru na wani lokaci,sannan ya sake yin magana
“Lady tell me mana,ina son na koma gida da sauri cos akwai shirye²n daya kamata ace nayi wanda da ban samu nayi ba..”
“To kaje kawai ni ba saina fad’a maka ba ma..”
Wani irin kallo ya bita da shi mai shiga jiki,dan yadda tayi magana a sakarce sai daya haddasa masa jin shauk’i har k’asan ransa
“Babu inda zani sai kin fad’a min..”
Bakinta ta turo gaba cikin gungunin shagwab’a kan takurata da yayi tace
“To ni me zan fad’a maka ne..!? Nimafa ban sani ba..”
Juya idanunsa yayi akanta ya had’iye wani irin yawu
“Kina ganin wannan hanyar shi ne zai b’ille miki..?? Tun yanzun kina bani amsa a haka..!? Me kike tunani zai faru gaba.!? Ban tab’a zaton haka daga gare kiba,tun kafin tafiya tayi nisa ya kamata ki gyara,idan ma akwai wanda yake baki shawara ne,to ya kamata kice masa bakya so ya rik’e abunsa,,sam bana jin dad’in hakan,nd banyi zaton samun wannan tarbar daga gare ki ba.”
Sabbin hawaye ta sake saki cikin sheshshek’ar kuka tace
“To ni wai mene ne nayi maka da yasa kake ganin laifi na..!? Kai ba’a ce kayi laifi ba sai nice za’a ga laifina..”
Yana cikin mamakinta ya ce
“To wai mene ne nayi miki haka..? Na tambayeki tun kafin yanzun kin kasa bani cikakkiyar amsa,ta yaya ne zan san laifin da nayi.. Aahh..??”
“Dama ai baza ka sani ba,tunda ba damuwa kayi da ni ba..!”
Murmushin takaici ya saki lokaci guda ya sake kusantota har numfashinsu yana gwamuwa
“My Lady.. Ni kike fad’awa ban damu dake ba.? Ni ne wai ban damun ba.? Let me tell u to,idan baki sani ba zan sanar dake idan kuma kin sani zan tunatar da ke..”
Hannunsa yasa cikin aljihunsa yana fitowa da shi ya d’ora mata abunda ya ciro d’in a hannunta
“Kin tuna wannan..??” Kafin tayi magana ya riga ta
“Tun daga lokacin dana tafi da shi babu dare babu rana kullum ina tare da shi,gida ko office babu abunda yake rabani da shi,idan ban damu dake ba,me yasa zanyi haka..!? Soyayyar da nake miki idan har dan ban damu dake bane,me zai sa na dawo..? Tsayin lokaci na d’auka ina bulayin neman ki bau dare babu rana ko wane lokaci tunani na da lissafina inda zan ganki amma ban same kiba,nayi yawo tsakanin U.S da Nigeria duka saboda na ganki,me yasa ban manta dake ba sai yanzun.!? Haba Lady,bai kamata ki sawa ranki wai kamar ni da nake jin duk duniyata babu wata mace a zuciya ta data kai ki daraja da k’ima ki bud’e baki kice ban damu dake ba,idan har ban damu dake ba,me yasa ban shafe babinki a rayuwata ba..!? Me yasa³.!?”
Runtse idonsa yayi saboda takaicin maganar yana dafe forehead,daga haka gaba d’aya ya rasa abunda zai sake fad’a mata next ta yarda da shi
“To ai dai duk da hakan daka fad’a bai hana maka neman auren wata macen ba,har ma ka shirya ma kanka rayuwa da ita,,idan ka damu da ni me yasa zaka sawa ranka sonta..!?”
Saurin bud’e idanunsa yayi ya sauke su a kanta,murmushi ya saki mai sauti saboda ya gama gano inda ta nufa,slowly yasa hannu ya d’ago fuskarta had’e da zuba mata idanunsa
“My Lady.! Are u jealous.!?”
Saboda tana cikin damuwa har bata ma san lokacin data kad’a masa kai ba cikin sakin wasu hawayen ta k’ara da fad’in
“Ba dole naji kishi ba,mutumin da na gama killace rayuwata dominsa,rana a sama sai na tsinci labarin zai auri wata macen daban..!”
Kyakykyawan murmushi ya sake saki a hankali yana kallon motsawar bakinta,shi kam in dai yau ne to yana tunanin babu wani abu da za’a fad’a masa wanda zai sashi jin cewar shi na daban ne daya wuce samun wannan kyakykyawan labarin daga bakinta,gaba d’aya saurarenta kad’ai ya sashi zama wani speechless,sai daya d’auki tsayin lokaci yana kallonta without ya furta a single word,ita kanta a lokacin bata yi zaton daga haka zai sake cewa komai ba amma sai ta jiyo shi yana fad’in
“Thank u My Lady.. Ban san mene ne ya kamata nayi wanda zai faranta miki ba,nd ki daina ganin laifina akan waccan maganar,,buh all i knew shi ne kwata² ni ban san da maganar taba,cos nima tsintar ta nayi a sama kamar yadda kika ji,lokaci guda Daddyna yazo min da batun auren y’ar amininsa,nasan kin kin sani bai kamata ace iyayen da suka raineka ka nuna musu basu isa da kai ba.. Toh! Wannan dalilin yasa nima nayi hak’uri duk zuciyata bata so na amsa buk’atar Daddy,,gashi a lokacin ke kuma kin yi min nisa,ban san ina ne zanje na nemo kiba,ko kafin na amsa ma sai da nayi yawon nema amma still ban same ki ba,,sai lokaci guda nayi gam da katar..”
Yadda ya fad’a mata dalilinsa sai taji jikinta duk yayi sanyi,saboda jin bama shi ya ganta yace yana so ba had’a su aka yi,,shi da yake cewa yana sauri amma kasancewar hiran ya masa dad’i da yake yanzun ta saki jiki yada suka jima sosai suna ta hira kan yadda al’amura suka tafiyar musu a cikin shekarun da suka gabata da basa tare,kowa ya fayyacewa d’an uwansa yanayin daya shiga,kafin suka yi sallama ganin Maghreb ta kawo jiki,har k’ofar gida ta masa rakiya,suna tafe suna hira cikin farin ciki,,Sultan kuwa ko da Hammad ya shige ya barshi nan zaune ko daya gaji da zaman kad’aici ya fito yana d’an kewaye a cikin line,yana yi yana duba time,ganin su sun fito a lokacin yasa sai ya nufo inda suke tsaye suna murmusawa cike da shauk’i,tun kafinma ace ya k’araso Hammad daya ankare da shi babu shiri ya kalleta da fad’in
“My Lady.! Shiga gida,sai munyi waya.!”
Kallonsa tayi cikin rashin fahimtarsa za tayi magana,tunda dai ita tasan shi da kansa ya ce lallai² sai ta masa rakiya har mota shi ne kuma yanzun yake cewa ta koma,kallonta yayi saurin yi ganin ta kasa fahimtar abunda yake nufi
“Na ce kije za muyi waya..”
“Toh! Ka bari yazo mu gaisa.!”
“A’a.! Na ce kije..”
Juyawa tayi slowly zata shiga gida,tana yi tana kallonsa ganin da tayi yak’i kallonta sai ta shige ciki,a dai² lokacin da Sultan shi kuma ya k’araso,yana ganin yadda yake had’e rai yasa akwai abunda yake faruwa
“Wai kai mene ne yake damunka ne..!?”
Ya tambaye shi
Hammad kamar bai san abunda Sultan d’in yake tambayarsa ba yace “Meka gani..!?”
“Ban sani ba..!”
Shima d’in ya amsa,d’age shoulders Hammad yayi kafin yayi gaba abunsa yana cewa
“Kada Allah sa ka sani d’in..”
Ya shige mota da sauri yayi mata key,a slow ya sauke glass d’in side d’insa da fad’in
“Malam zaka taho mu tafi ne ko kuma na tafi zaka taho..!?”
Da yake sanin hali yafi sanin kama a gurin Sultan shi yasa sai bai sake tanka masa ba ya shige motar,k’wafa Hammad ya saki bayan ya d’age glasses d’in sannan ya juya kan motar cike da k’warewa suka bar unguwar.
Tun da aka sakko daga masjeed bayan fitar su Daddy a gidan y’an uwa suka fara hallara daga sassa daban² na Nigeria da k’etarenta,kafin ace Maghreb tayi tuni har gida ya d’auki harami,duk inda ka sanya idanunka jama’a ne har ba’a magana,,,suma dai can gidan su Sabina Baba duk ya bugawa dangin Inna waya ya farfad’a musu,a nan wasu daga ciki suka hau fad’a kan me yasa baza’a sanar da su da wuri ba,sai a k’urarren lokaci.? Hak’uri yayi ta basu yana fad’a musu lamarin ne ya taso a gaggauce suma duk basu san da zuwansa ba,,wasu dai sunyi uzuri amma wasu fir suka nuna basu yarda ba.Baffan Inna kuwa ko da Baba ya fad’a masa da yake shi d’in mutum ne mai sauk’in kai sai baiga lafinsu ba,yayi addu’ar fatan alkhairi sannan ya shaida masa zuwa gobe in Allah ya yarda duk suna kan hanya suma,bayan nan kuma sai suka yi sallama,shima kuma baffa a lokacin suna gama waya da Baba sai ya sake kiran wasu daga cikin dangi ya fad’a musu,wad’anda kuma suka sani yayi magana da su akan tafiyar su zuwa gobe da safe idan Allah ya nufa.
*A gurguje…*
Haka aka yi ta shirye² daga duka b’angarorin uku,wad’anda suke ganin sun shirya suka sake shiri wad’anda kuma dama basu shirya ba suka d’auki niyyar shiryawa.
Agidan su Hammad kam duk da biki ne na namiji amma shirin da suke yi masa kamar duka shirye²n gidajen uku aka had’o aka dawo yinsu a nan,yadda mahaifansa duka suke nunawa kamar ba bikin namiji za suyi ba,,a gefen Mammah lokacin da labarin neman auren da su Daddy suka je nemawa Hammad ya dawo kunnenta tana cike da tsananin farin cikin da idan har aka cire Hammad ita ce mutum ta farko da take biye masa,,cikin lokaci kad’an kafin kace me tuni itama ta fantsama shiri,da bada umarnin abunda za ayi,Daddy kam yadda yaga tana yi da jikinta a nan sake tabbatarwa kansa lallai yanzun ne ta d’auki lamarin da muhimmanci,tunda an musu yadda suke so daga ita har Hammad d’in,duk sun ware suna tsare²n yadda al’amura zasu tafi,kafin wani lokaci mai nisa tuni har an canja komai daga shirin auren mutum biyu zuwa uku..
.. Da yake suma d’in ba wasu shagali suka shirya masu zafi ba,amma yawan taron al’umma kad’ai ya isa abun mamaki,saboda duka bikin ma gaba d’aya so ake a tak’aita yinsa a iya ragowar kwanaki biyun da suka rage,cos a yadda aka tsara da zaran anyi d’aurin aure a washe gari zasu tattara su bar k’asar,wannan dalilin yasa ko da aka tashi tsara event’s sai ba’a k’irk’ire su da yawa ba,bare har su sa al’ummah gajiyawa,aka barshi daga yini da Mamma za tayi da su kansu gidajen amaren,sai kamu da d’aurin aure,wanda dama shi ne a k’arshe,kuma daga shi d’in washe gari sai subi jirgi zuwa U.S.+
Kasancewar a b’angaren Mamma tun bayan da Daddy suka dawo ta samu labarin canza tsarin bikin shi yasa sai ta nemi Badra suka yi magana,a bakin tane taji komai dangane da yanayin gidan su Sabinar,nan ta tashi nata hidimar bayan ta sata ta kira mata Sabinar,ko da suka gaisa duk dama a kunyace ne,sai Mamma tasa ta turo mata number Inna,saboda wasu secret maganar da take so suyi,a taken ba tare da b’ata lokaci ba,suna gama waya ta mata sharing number,a lokacin ita kanta Mamma bata iya jira zuwa wayewar gari ba saboda gudun k’urewar lokaci tayi ma Inna bayanin tana son zata turo masu shirya amarya ne dama shi yasa ta kira don taji nata ra’ayin,,ko da Inna taji batun tayi farin ciki sosai,daga zuciya har ranta taji ta amince da Mamma fiye da tunani,nd tayi matuk’ar dad’i da Allah yasa tilon yar tasu ta samu gidan mutunci kuma masu sonta,dan daga alamun yadda suka yi magana da Mamma kad’ai ta fahimci matar tana da halin dattako,cike da k’arfin guiwa da yarda duk da bata san Mamma’n ba bare ace ko sun tab’a had’uwa wani gurin haka Inna ta amsa mata akan babu damuwa sai ta turo sun,daga nan sai suka yima juna godiya sannan kowacce ta fad’a nata sabgogin.
*Saturday morning…*
Yau gaba d’aya da yake tun da gari ya waye,bak’i ke shigowa cikin gidan yasa hidimar ta sake yin k’arfi,,y’an Had’ejia ma duk sun samu halartar bikin,amma da yake tafiyar ba nan ba shi yasa sai tsakiyar rana suka iso,a nan gida ya sake d’aukan harami,inda mak’ota zuwa wad’anda basu san meke wakana a gidan ba,ganin taron jama’a ya fallasa musu hidimar da ake yi,,kafin ace yamma ta gabato tuni gida ya gama d’inkewa da y’an uwa da abokan arzik’i har babu masaka tsinke.
Sabina kuwa da yake tun safen kafin ma ace bak’i sun fara zuwa su Badra suka zo suka d’auketa,shi yasa duk abunda ake a gidansu bata sani ba,kuma ko da suka fito d’in ma basu tsaya b’ata lokaci ba kai tsaye suka wuce gurin saloon,,daga can suna gamawa sai suka wuce gidan su Jannat kasancewar a can zasu shirya kafin lokacin kamun yayi,kuma dama can ne Mamma ta aika da masu gyaran jikin da take so su sille mata itan,a yadda Mamma ta d’auki Sabina tun data bayyana a matsayin wacce Hammad yake tsananin so,itama take k’aunarta har zuciyar ta kuma sam bata mata kallon suruka,ita a y’a ta d’auke ta,shi yasa ma ko data tashi basu umarnin yadda zasu mata,tace tana so tsakanin kwana biyun suyi mata gyaran da duk wanda ya santa ba lallai ya iya gane taba,nd mutane da sun kalleta su san cewa yes itan ta kai amarya y’ar gaske,,saboda yadda Badra ta fad’a mata ta san gidan su ba lallai ne a samu gurin da zai ishesu ba shi yasa tace su tattaro su dawo gidan su Sultan,,,komai tare suke yinsa kamar yadda Mamma tayi musu,cos duka ta had’a su hud’u,sai dai nata daban da nasu cos haka Mamma tace shi yasa ake yin yadda ta tsara,dole tasa a komai sai an bambanta ta da su,,tun da suka dawo daga gurin saloon,a gidan suka iske masu gyaran jiki suna jira,kafin wani lokaci da dawowarsu tuni har sun duk’ufa a kanta,tun kafin 12pm har wajen Maghreb basu kyaleta ba,sune lik’a mata wancan,goga wancan,murza wancan,,before ace awanni hud’u masu kyau sun wuce tuni ta fara d’aukan kyalli,jikinta daya sake karb’ar gyara nan fatarta taci gaba da haskawa tana walwali fiye da da.
Sai da aka idar da sallar Maghreb sannan suka sa tayi wanka da wasu irin ruwaye na zallar sinadaran k’amshi,tana fitowa kuma kafin ruwan jikinta ya gama bushewa suka hau turareta tun daga kan gashi har kayan da zata sa,baiwar Allah komai akace sai dai kallo kawai ta rasa bakin magana,,da aka zo batun kwalliya ma da kayan da zata saka duka da suka fito cikin hidimar Mamma,wani had’ad’d’en plain material suka bata tasa da aka masa d’inkin doguwar riga,yadda rigar ta d’inku duk nacin mutum da son ya gane wane irin d’inki ne aka mata abun sai ya so bashi wahala,cos ba simple d’inki ne da kallo d’aya zai saurin sawa ka gane ba,daga samanta can wajen shoulders d’inta rigan yayi slide ta duka side biyun yana showing shoulders d’inta,yayin da ta wajen hannun zuwa k’asa tayi wani irin bud’ewa kamar bubu,sai dai sam ba itan bace,tana sawa suka zaunar da ita,special make-up artist da Mamma tayo hiring ta fara baje basirarta a kan fuskarta,ta b’ata sama da 1 hour tana painting all over her face sannan ta kammala,kwalliya y’ar ubansu ta shirya mata ta yadda da wuya a iya ganota farat d’aya,sannan ta mata rolling vail d’in rigar,tamkar wata baby doll da aka zana haka ta fito saboda kyau d’an ubansu da tayi,ba iya masu shiryata ba hatta su Badra abunda kawai suke fad’a a lokacin da aka gama shiryata shi ne “Masha Allah”,,wani irin open toe high heel shoe,mai feather accent da rufaffen dunduniya suka kawo suka saka mata red colour,saboda jikin material d’inta asalinsa white ne sai adon fulawoyi jajaye masu ratsin bak’i² a jiki,y’ar k’aramar Po’s mahad’in takalmin suka sake kawowa suka bata ta rik’e mai azabar kyau a hannunta,tun kafin ta mik’e tsaye tuni ta fara amsar hasken flashes,dan ta ko ina haskata kawai suke suna ihun murna,nd kowa burinsa ace shiya fara ma Hammad sharing picture ta,ita kam lokacin binsu kawai take ci gaba da yi da idanu sai d’an murmushin dake kwance saman fuskarta wanda ya sake k’awata kyakykyawar fuskar tata,deeply tana jin hawaye kamar zasu zubow mata,magana kam sam ta kasa yi musu,after sun gama shiryata,an kuma gama yiwa su Badra kiran Mamma suka yi niyya sai ga nata ya fad’o,suna d’auka itama abunda kawai ta tambaye su shi ne “Sun gama!?” Suka ce mata “Ehh! Sun kammala”,amsawa tayi da “Okay” Sannan ta katse kiran ta kira gidan su Leesha taji ko suma sun gama d’in dan gab’a d’aya so ake ayi kamun a guri guda,bayan ta kira su,daga nan ta aika da motoci gidan su Sabina dan su d’auko y’an uwan su zuwa gurin da za’ayi taron,,da yake itama Mamma’n ko da suka gama sallamar bak’i ita da Maman su Sultan sai suka wuce zuwa meena events centre d’in,saboda yafi kusa da su shi yasa suka ajiye event d’in a nan ba sai sunsa mutane wahala ba,nd gurin yana da yalwar da zai d’auki duka jama’ar su,cos ak’alla gurin yana d’aukan one thousand guests,,nd sun san dai duk taron da zasu had’a zai ishe au,,suma su Sabina ko da suka gama Mamma ta sake kiransu ta sanar musu su taho cos already har ta tura musu drivern da zai taho da su,,kafin lokaci mai nisa kuma da yake basu da nisa sai ga su sun k’araso kusan a tare suka shigo harabar event centre d’in da tawagar Falisha,kada kuso ganin yadda ake kallon-kallo tsakanin dangin amare,saboda izuwa lokacin babu wanda bai san da zaman kowa ba,labari ya gama zagayawa,haka amare yadda suka wanku ko wacce nata ahalin suna so suga ita ce akan gaba dan ta zama y’ar gaban goshi,,a tare suka jero Badra tare da su Jannat suna takewa Princess d’insu baya,suma duk sun sha ado kamar ba y’an matan hausawa ba,dama duk kuma sunfi Sabina haske shi yasa ko da suka sata tsakiya sai abun ya bada wani colour mai kyau da ma’ana,nan fa gidansu Falisha ko da ganin dangin ango a tare da ita lamarin ya fara juya musu tunani,cos duk yadda suka d’auki lamarin yaso ya zarta da tunaninsu.
Sanyayyan kid’an da ke tashi da shirun jama’a,shi ya sake k’awata gurin,amare kuma ko wacce da wad’anda suka mata rakiya suka ja gefe suka kame,”Masha Allah ” daga ko wane edge shi ne abunda ke fitowa a bakunan mutane,tun da suka shigo haka hasken camera’s yake haska su daga fitowarsu a mota,ba’a daina ba har suka zauna,,sai da aka fara yin addu’o’i na neman zaman lafiya da kariya daga fitinannun mutane da aljanu kafin a gudanar da kamu,bayan nan sai aka ci gaba da shagali,,duka a gaba d’aya cikin gurin babu wani babba namiji kaf cikar gurin mata ne zallah iya ganin mai kallo,,ko da na hanga nima a cikin taron,nan na hango dandazon masoya *ALK’AWARIN JINI* daga shafukan sada zumunta,musamman na whatsapp,facebook dama wattpad wad’anda suka zo taya wad’annan masoya murna bisa cikar burinsu,kada ku so ganin adadin jama’a abun har yaso bani mamakin ta yadda aka yi suka samu labarin auren,abun dai gwanin burgewa kowa ya kame mutuncinsa,,Sabina aka fara kamawa,sannan Falisha saboda haka mai gidan ya tsara abunsa kuma hakan aka yi,bayan da aka gama kamu taro yaci gaba,daga nan har kusan 10pm,ana abu guda kafin taron ya fara bajewa a hankali.
Su Sabina still gidan su Jannat suka so sake wucewa sai dai tun kafinma su bar wajen da yake mutane sunyi sauk’i a lokacin sai ga kiran Hammad a wayar Badra,cike da zumud’i ta d’auka ta masa sallama,yana amsawa ko gaisawa bai bari sunyi ba yace mata su jira su a nan kada su taho zasu zo yanzun su gaisa da amaren cos shi har lokacin baiji zai iya zuwa gidansu Falisha ba,amsawa tayi sannan ta sanar musu,gaba d’aya sai suka fasa tafiyar kamar yadda suka yi niyya,,cikin lokaci kamar suna kusa da event centre d’in sai gasu sun k’araso a cikin mota d’aya,su hud’u ne hakimin yana front seat a kujerar kusa da driver daga shi Sultan sai kuma Sadeeq da Bassam daya rikid’e daga k’anin ango zuwa aboki,,dukansu cikin shiga ta alfarma irin ta *Y’AY’AN GATA.*
A inda su Badra suke Bassam ya Parker mota cos shi yayo drivern d’insu daga gida zuwa nan,tun kafin ace Hammad ya fito daga mota tuni har Falisha da taga zuwansu ta nufo su tare da tawagar k’awayenta without ta rik’e ajinta,,gimbiyar kuwa tun da suka shigo cikin harabar event centre d’in data tabbatar su ne wani sabon mulki ya motso mata,sai ta sake kamewa a back seat abunta tak’i yarda ta fita,su kansu duka y’an matan nata da suke zagaye da ita babu wacce tayi k’ok’arin barin gurin saboda aji,,ga oga Hammad kuwa,lokacin da suka fito kansa tsaye yana hango tawagar tsuntsuwarsa ya nufo inda suke cos yasan a matuk’ar ya gansu tabbas tana nan itama a kusa,,Falisha da ta riga ta taho bata kai ga k’arasowa inda yake ba ta hango faruwar hakan,dole tasa ta tsayawa,yayin da tsananin kishi mai had’e da b’acin rai ya turnuk’o ta,bata iya tsayawa ba,bare ta saurari maganganun y’an tawagarta ta juya ta bar wajen.
Yallab’ai Hammad kuwa duka da yake bai wani santa ba a fuska shi yasa da yaga taron mutane sun taho sai bai wani bawa saninsu muhimmanci ba,cos yayi zaton ko duk y’an biki ne,shi yasa sai bai ji komai ba,,yana k’arasowa kallonsu Badra kad’ai yayi suka bashi guri,cikin motar ya shige inda take hakimce,,tunda taga ya shigo ta sake d’auke kai tana basarwa,murmushi yayi mai sanyi had’e da yi mata sallama,kanta yana kallon waje duk da ba komai take iya gani ba sosai saboda glasees d’in motar da suka kasance masu duhu ta amsa without ta bari sun had’a idanu da shi cos ita kad’ai tasan abunda zai iya faruwa idan ta bashi fuska at that time,ta gaishe shi a yadda take,maimakon ya amsa shima sai ta jiyo shi ya kamo hannunta cikin nasa da fad’in
“A haka ne zaki gaishe nin kina kallon wani wajen..!?”
Sai da tayi murmushi mai sanyi buh ba mai sauti ba,kafin ta d’an juyo ta dawo dai² still bata yarda ta kalleshi ba ta dai fuskanci kujerar driver da idanunta da suke lumshe kamar mai jin bacci,,hannusa ya kai ya rik’o chin d’inta sannan ya juyo da fuskarta suna kallon juna,yadda taci uban gayu duk da ya santa fiye da tunani,nd ya jimawar da zai yi wuya ace ya kasa ganeta amma wannan lokacin daya so rikicewa,saboda azababben kyaun da tayi masa,cos komai a lokacin na daban ne a tare da ita,shi yasa kawai sai ya sa mata idanu without ya iya fad’in komai or even blinking his eyes yana yi yana shafo lips d’inta da suka ci uban red wine lipstick,murmushi tayi k’asa² kafin ta sake gaida shi,da yake gogan yayi nisa wajen kallonta da enjoying moment d’in da suke ko maganar ma bai san lokacin da tayi ba zuciya da tunaninsa duk sunyi gaba,knocking glass d’in motar akayi hakan sai ya sashi dawowa cikin nutsuwarsa,slowly ya sauke ajiyar zuciya sannan ya bud’e motar da nufin duba waye,a kan Mamma idanunsa suka sauka tana masa kallon me kake yi ne a nan d’in.? Kafin tayi wa Sabina tambayar
“Dama baku tafi bane tun d’azun.!?”
A rikice saboda rashin amsar da zata bata ta sunkuyar da kai k’asa cos ita bama tasan me zata ce mata ba,kallonsa Mamma tayi tana had’e rai da fad’in
“To rasai..! Maza fito ka basu guri su wuce,,ko baka san dare yayi ba yanzun..!?”
Saurin kallonta yayi yana marairaicewa
“Mah! Please gaisawa fa za muyi muma wucewar za muyi.!”
“Gaisuwar ne har sai an shiga mota.? Me yasa ba’a yi a gaban mutane ba.!? Nifa shiririta ce bana so kuma ka sani ko.!? Maza ka fito ka bani wuri kamar na sab’a maka.!”
Sake marairaice fuska yayi yana kallonta a sanyaye sai yace
“Mah.! Please to bari muyi sallama..”
Juyawa kawai tayi tana ba tare da ta sake masa magana ba,ta kallo su Badra dake gefe tare da su Sultan suna hira,sai dai suma d’in bata musu magana ba ta wuce,ma’anar kallon da tayi musu kad’ai yasa su yin sallama da samarin suka bar wajen.
Yallab’ai Hammad dai tunda Mamma tayi magana ta kashe masa k’arfin guiwa,babu shiri suka yi sallama ya fito jiki a sanyaye,,tunda ya fito su Sultan suka sa masa idanu,haka nan suka hau masa dariya,bai tanka musu ba shi dai ya wuce ya shiga mota yana k’wafa,buh duk da haka yasan sune a ciki,coz shi dai ya kusa ganin abunda gobensa zata haifar,haka suka bar gurin duk bai yi magana da kowa ba,,suna tafiya suma su Badra suka d’auki hanyar barin gurin,direct daga nan gidan su Jannat suka nufa,a wannan daren gaba d’aya tunda suka koma suka dasa hiran yadda program d’in ranar ya wakana,ba su suka samu suka kwanta ba sai da dare yayi nisa sosai.
*Falisha’s Domicile..*
Tunda ta izgi k’afafu ta bar gurin gaba d’aya tawagar k’awayenta da k’ananun maganganu suma sai suka rufa mata baya,kafin su kai inda take har ta fad’a cikin mota,shi kansa drivern tunda yaga a yanayin da ta shigo bai jira ta bashi umarnin tafiya ba ya ja suka bar wajen da mugun gudu,tana ganin sun d’auki hanya take ta kalle² da neman ruwan hawaye saboda yadda take jin zuciyarta babu dad’i amma sun gagara sakko mata,,yadda komai ya faru take sake haskowa a idanunta,har suka shigo harabar gidansu hawaye bai samu damar sakko mata ba,amma suna shiga cikin parlor’n su ta kece da wani irin kuka hawaye tamkar an b’alle tap,,jikin Mamah ta fad’a cikin gunjin kuka tana fad’in
“Wayyo! Allah na Mamah,shi kenan rayuwata ta shiga garari,wollahi Mamah na tsaneta..”
D’agota Mamah tayi tana tambaya
“Leesha.! Mene ne yake faruwa ne..!? Yi shiru ki sanar da ni abunda yake damunki..”
“Bazan iya zama da ita ba Mamah,,wollahi zata sa zuciyata tayi bindiga..”
Gaba d’aya parlor’n yayi tsit kowa su kad’ai yake saurare,can wata dattijuwa daga gefe da tayi tsuru tana kallon ikon Allah tayi tsaki da fad’in
“Mttssww.! Yo zancen banza zancen wofi ma kenan,,ke yanzu FULAISA akan kishiya kika zo kina mana wannan gunjin kukan.? Amma wollahi kinyi asara,yo ni ai na d’auka wani abu ya faru,har ta katse min d’an baccin dana fara,,to Allah ya wadaran naka ya lalace dai..”
Sai ta sake juyawa ta gyara kwanciya tana ci gaba da mita,babu wanda ya kula da fad’an da matar tayi a tsakanin Mamah da Falisha,sai ma haushin ta da Falisha’n taji kamar ta shake ta saboda kiranta da wani irin sunan da ta tsani taji suna fad’a mata,ta kalli Mamah still idanunta na tsiyayar da hawaye
“Mamah please kiyi wani abu,Allah ni bazan zauna da ita ba.. Sai dai tayi hak’uri ta barni da shi ni kad’ai,ni gaskiya gidana bana son mu zauna mu biyu,kuma bana son muyi sharing miji,,ki taimake ni Mamah..”
Shewa wasu abokan wa’anta suka yi daga b’angaren babanta suna fad’in
“Allah sarkin dad’i inji b’arawon zuma,,yo ke Falisha har kina da bakin cewa ba zaki zauna da ita ba..!? Kece fa zaki shiga tsakaninsu cos soyayyarsa ba ta yanzun bace,mufa munji yo tarihin komai yau a gurin kamo, saboda haka ita ya kamata tace bata zama dake bawai ke ki fad’i haka ba..”
Kururuwa ta dasa cikin hayaniya ta taso kansu da masifa
“Allah sawak’e na auri ragowar wata,ai kowa yasan ni yake so ba ita ba..”
Kafin ta k’arasa rufe baki aka samu wata cikin cousins d’inta itama tayi caraf
“A’a fa Leesha, wollahi da ace je yake so ba zai miki wulak’ancin da yayi ba,,haba ni idan nice ai wollahi bai isa ba,kuma saina nuna masa KUSKUREN sa.. Har namiji ya isa yayi min haka ina matsayin mace..!?”
Zabure tayi zata sake yin magana Mamah tayi saurin rufe mata baki tana mata alama da ido akan tayi shiru saboda duka idanu na kansu,sai data lallab’a ta sosai sannan taja hannunta suka bar wajen.
A wannan daren suma dai a gidan su Falisha sun ga tashin hankali,saboda fitinar data kwana yi musu,,bak’in dake gidan kansu da kyar suka samu runtsawa cos ta hana kowa nutsuwa,suma d’in kuma sai suka kwana tattaunawa akan maganar.
*Sunday Morning..*
Da yake dama yau d’in shi ne ranar d’aurin aure kuma da wuri aka saka za’ayi d’aurin auren,shi yasa tun kafin ace 11am yayi ango da tawagarsa duk suka gama shiryawa,cikin wani irin farin cashmere wool fabric mai shara² ya fito sanye a jikinsa,har kana iya gane fari kar d’in sleeveless da yake ciki,tun daga sama har k’asa,ciki da waje da colour d’aya yayi amfani a jikinsa shi ne fari,komai daya sa babu wani mix colour fuskar san nan banda walwali babu abunda take,,su kansu su Sultan lokacin daya fito zuzuta shi sukayi ta yi,sai dai yayi musu murmushin san nan mai burgewa,,suma d’in dai kamar shi plain wool fabric ne a jikinsu sai dai su nasu clour d’in onions pink ne,sai suka yi amfani da farin colour a huluna da takalmansu,yadda suka zuba anko su uku Sadeeq,Sultan da Bassam kai ba zaka tab’a iya gane wanne ne yafi wani kyau ba,kawai dai kowa yayi kyau cikin sun babu na yarwa,,sanda suka fito suna tafe cikin wani farin Toyota tundra 2017 model,ko kafin su wuce sai da suka biya gida da yake suma ba a gidan suke ba,suka gaisa da jama’a sannan ya yima Mamma sallama,suka nufi gurin d’aurin aure cos a time d’in ma har Daddy ya fara kiran wayarsa,a gaggauce bayan sun baro gida kai tsaye sai suka nufi masallacin jumu’a na triumph dake fagge.
11:00am sharp shu ne lokacin da za’a d’aura aure amma saboda ganin family’n Falisha basu samu k’arasowa da wuri ba sai yasa aka jinkirta,wasa² abu tun wajen 11am har 12 saura babu su babu labarinsu,,kiran waya kuwa tun ana yi cikin nutsuwa har abun ya fara neman zama matsala,Daddy da kansa yadda ya dunga kiran wayar *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* abun ba’a cewa komai,hankalinsa duk ya tashi saboda rashin sanin dalilin k’in halartarsu a gurin d’aurin auren,nd kuma bai san matsalar dake afkuwa ba.
*****
A can gida kuwa b’angaren Mammah a dai² lokacin da hidima yayi hidima,taro yayi taro jama’a ta ko ina shigowa suke yi mata Allah sanya alkhairi kama daga y’an uwa,dangi na kusa da nesa,sai ga sak’o ya riskota har cikin gidan gardener d’insu ya shigo da sauri ya sanar mata ana sallama da ita a wajen,da mamaki bayyane a fuskar Mamma ta amsa sannan ta rufo masa baya,guards d’in gidan suma suka biyo bayanta har zuwa bakin get cikin shirin ko zata b’aci.
A tsaye ta iske su mutim biyu cikin manyan kaya,a bakin get d’in jikin k’atuwar Jeep k’irar Prado,tun kafinma ta k’araso su da kansu suka nufo inda take,ita dai Mamma ganinsu kad’ai sai da lamarin yaso bata tsoro amma da yake jajirtacciya ce sai ta dake bata nuna musu tsoronta a fili ba,har suka gaisa cikin mutunci,sannan d’aya daga cikinsu ya antayo mata tambayar
“Da farko dai Hajiya mu mun kasance y’an aike ne,kuma dai Allah yasa ba muyi b’atan kai ba,nan ne gidan mai *SHARI’A..!?”*
Jikin Mamma har b’ari yake wajen basu amsa da
“Ehh! Toh wanne a ciki kuke magana..!?”
D’ayan da baiyi magana ba har lokacin tun bayan gaisuwar da suka yi ya sako baki wajen fad’in
“Cheap judge *ALHAJI ALIYU MUHAMMAD* muke nufi..!”
Kad’a kai Mamma tayi tana had’iye wani irin yawun tsoro dan tunanin Mamma zuwa lokacin ambaton sunan mai gidanta ya haddasa mata firgici fiye ma da ganinsu da tayi,da wani irin frightening looks taci gaba da kallonsu tana kad’a kai
“Ehh! Nan ne..! Wani abu ya same shi..!?”
Kallonta suka yi a tare cos sun san ba lallai bane ace ta gane abunda suke nufi kai tsaye ba har sai sun mata bayani
“A’a Hajiya.. A gaskiya mu wannan batun bamu da masaniya akansa,abunda kawai muka sani shi ne,an turo mu mu kawo sak’o daga..!”
Katse su Mamma tayi saurin yi cikin hayaniya tana tambayarsu
“Dan Allah kuyi min bayanin wane irin sak’o ne..!? Ku sanar da ni sak’on na mene ne,maganar ku ta tayar min da hankali.. Kuyi min bayanin daga inda sak’on yake..!”
“Alal hak’ik’a Hajiya muma da kika ganmu nan y’an aike ne,kuma kin san d’an aike a kullum hausawa sukan ce baya laifi ko..!?”
“Ehh! Haka ne,,to amma ni abunda ban sani ba shi ne,kun ce an aiko ku,buh kun k’i sanar da ni wane irin aike ne aka yi muku,kuma daga ina ne aka aiko kun,nd gurin waye aka ce muku.!?”
Ajiyar numfashi mai maganar yayi sannan yace
“Gaskiya ne wannan Hajiya,a bisa hak’ik’anin gaskiya mu dai y’an sak’o ne da muka fito daga gidan *ALHAJI ISHAQ BUNAWA..”*
Wani irin fad’uwa gaban Mamma yayi duk da bata san dalilin aiken da akayi musun ba,sai ta jinjina kai without tayi magana ta ci gaba da sauraronsa
“Sako ne aka aiko mu da shi aka ce mu kawo nan,sannan mu tabbatar mun dank’a su a hannun wani daga cikin masu gidan..”
Cikin hayaniya Mamma ta sake tasowa kansu duk da bata so ace an san halin da ake ciki d’in,sai dai ganin yadda suke mata maganar kamar basa son fad’a matan yasa dole sai data had’a musu da hakan,hak’uri suka shiga bata cikin sigar kwantarwa da mutum hankali sannan suka fad’a mata ko wane sak’o ne,bayan sun shaida matan kuma suka fito da kayan dake cikin booth d’in motar,akwatunan lefen da Daddy ya had’a aka kai gidan su Falisha na aure da komai da aka kai take gani a gabanta,lamarin daya matuk’ar d’aure mata kai,cos bata san dalilin faruwar hakan ba,,su kam ko da suka gama fito mata da kaya suka yi sallama da ita sannan suka ja motarsu suka yi gaba,,guards da suke gefe wad’anda suka biyo ta,da sauran workers na gidan suka d’ebi kaya zuwa ciki,,cike da damuwa nd rashin sanin dalilin faruwar hakan,yasa tun kafin Mamma ta isa cikin gidan ta fara k’ok’arin kiran Daddy a waya cos ita dai bata ganewa lamarin ba.
A can gurin d’auri auren ma dai zuwa lokacin ko da ganin time yana ta dad’a k’urewa nd still babu wani magana akan an samu *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* ko wani a cikin makusantansa a waya yasa dole aka fara tunanin hanyar da za’a bi ayi solving lamarin,,wannan dalilin yasa shi kansa limamin da zai jagoranci d’aurin auren ko da yaga lokaci yana sake tafiya sai ya nemi da yayi magana da maganbatan ango saboda b’ata lokacin yayi yawa,,at dsame time da yake k’ok’arin ganin waliyyan ango,shima Malam a nasa b’angaren bisa yadda yaga babu alamun zasu zo d’in sannan duk wani k’ok’arin kiran aminin na Daddy da ake har da shi a ciki,buh shiru sai dai waya ta shiga ta katse an k’i amsawa,sannan gashi sai amfani ake da different numbers duka ko za’a same shin amma abu ya gagara,wannan dalilin yasa sai ya yanke hukuncin za’a d’aura auren Hammad da Sabinar idan yaso daga baya idan an tashi a gurin d’aurin auren sai suje su duba ko lafiya hakan ta faru.
Hakan ce ta kasance a lokacin da misalin 12pm aka d’aura auren *MUHAMMAD ALIYU MUHAMMAD (HAMMAD)* da amaryarsa *HAFSAT AL’AMIN USMAN (SABINA)* abisa mafi ingancin sadaki,,taron d’aurin auren daya samu halartar masu manyan muk’amai a cikin k’asar nan,,kada kuso ganin fuskar Hammad lokacin daya tabbatar an d’aura auren,duk wani farin ciki,nutsuwa gami da sukuni sai a lokacin ya tabbatar ya same su,farin cikin da yake jinsa a ciki,bakinsa kam ko rufuwa ya kasa yi,hamdala kawai uake yiwa Allah daya cika masa muradinsa.
Daga nan gaba d’aya taron suka d’unguma zuwa Tahir Guest Palace Hall,dake nan a Nassarawa G.R.A,,su Daddy kuwa da yake sun san da waccan matsalar ko bayan da suka baro wajen d’aurin aure,kai tsaye gidan su Falisha suka so wucewa saboda bin ba’asin dalilin rashin halartar ko mutum d’aya gurin d’aurin auren,daga cikin ahalin shi *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* d’in bare kuma shi kansa.
A lokacin suna tare da Malam sun gama tsara yadda za suyi tafiyar dan dama da shi suka yanke zasu je d’in sai ga kiran Mammah ya shigo wayar Daddy,duk da bai so d’aukan kiran nata ba cos yasan dai maganar ta bazai wuce taji an d’aura auren ko A’a ba,,sai dai ko da ganin kiran nata ba mai k’arewa bane yasa shi tilas ya amsa…..Masoyana kuma masoyan littafin alk’awarin jini,duk naga comments d’inku,sai dai kuyi hak’uri ban samu na amsa muku ba,,a gaskiya ina alfahari da ku kuma bazan iya fad’a muku tsantsar farin cikin da nayi ba bisa ganin hakan,,buh ina sake baku hak’uri saboda lokaci yayi min k’arancin samu ne yanzun,online d’inma ba sosai nake samun yinsa ba cikin kwanakin nan,nd NEPA suna mana wulak’ancin kawo wuta yanzun,sai tsakiyar dare suke bamu,wannan dalilin yasa bakwa ganin posting d’ina kamar baya,,amma ku k’ara hak’uri dani in sha Allah komai ya kusa zuwa end.*+
*****
Sallama shi ne farkon abunda Daddy yayi cikin muryar damuwa cos bai san mene ne yake going through ata b’angaren Mamma’n ba da har take masa irin wannan kiran babu sassautawa,,itama Mamma’n a nata b’angaren lokacin da yake tana cikin damuwar kayan da aka dawo da su,bayan ta amsa masa bata jira ya sake yin magana ta tari numfashinsa da tambayarsa
“Daddy.! Yanzun kuma ina kenan.!?”
Ajiyar zuciya yayi cike da damuwa cos baima yi tunanin abunda zai fito daga bakinta kenan ba sai ya bata amsa yana cewa
“Gamu a hanya zamu je gidan *ALHAJI ISHAQ BUNAWA.! Da akwai wani abu ne.!?”*
“Gidan sa kuma,,mene ne dalilin da zaisa kuje.!?”
Ta dawo masa da tambaya,numfasawa Daddy yayi yana lumshe idanunsa irin yadda Hammad yake yi sannan a hankali ya waresu yana amsawa da fad’in
“Ya kamata ne muje mu duba,saboda cikin ahalinsa ko mutum d’aya bamu gani a gurin d’aurin aure ba,,mun kira waya babu amsa,yanzun haka ma maganar da nake miki tafiya za muyi..”
Muryar Mamma duk da tana tare da damuwa sai tace da Daddy
“Ai ina ganin Yallab’ai bama sai ta kai ku da yin haka ba.!”
“Me yasa za kice haka Asiya.!? Bayan kuma kinji na fad’a miki ko mutum d’aya bai halarci d’aurin aure daga ahalinsu ba.!?”
Ajiyar zuciya tayi sannan in a calmness way tace
“Ina tunanin ya kamata ne ku fara zuwa gida ku duba sak’on da ya aiko da shi kafin kuyi tunanin zuwa inda yake.!”
“Sak’o..!? Wane irin sak’o ne wannan da zai aiko da shi a irin wannan lokaciny.!?”
Daddy ya tambaya cikin muryar jimantawa da mamaki
“Ehh! To nima dai da yake ban tsaya duba sak’on ba,amma gashi nan dai ya aiko da shi yace a tabbatar an dank’a hannun masu gidan..”
Slowly Daddy ya d’ago kansa yana kallon Daddy’n Sultan dake opposite d’insa sannan yace
“Shi kenan bari yanzun gamu nan dai zuwa har Malam,,zamu ga wane irin sak’o ne tunda sai kiransa muke yak’i amsawa,kada zamuyi wahala muje mu tarar da wani abu daban.!”
Ajiyar zuciya ta sake yi sannan tace
“Allah kawo ku lafiya..! Sai kun iso d’in.”
Daga haka suka ajiye wayar,a gefen su Daddy ko daya gama magana da Mamma da yake su Malam duk sunji wasu daga cikin maganganun Daddy a lokacin da yake wayar,na Mamma’n ne dai da yake ba a hands free wayar yake ba sai basu san abunda ta sanar masa ba,shi kuma Daddy’n ko da suka gama wayar bayanin abunda duk tace yayi musu tunma kafin ya k’arasa Malam yace suje su fara duba sak’on kafin su nufi gidan nasa,daga hakan kuwa gaba d’aya sai suka d’auki hanya zuwa mayangu road.
Tun da suka d’auki hanyar Tahir guest palace daga masallacin triumph,saboda tsananinfarin cikin da yake ji yake tunanin yanzun wane irin yanayi ne take ciki.!? Tayi farin ciki ko A’a.? Yaya yanayin fuskarta take murmushi ko kuma yanayin kuka take.? Duk yadda ya so ya gwada yanayinta a lokacin tunaninsa ya kwace,ya kasa tsayar da yanayi guda a ciki,,a hankali kuma sai zuciyarsa ta fara kawo masa tunanin anya ma zai iya zuwa wani waje yanzun ba tare daya duba ya san halin da take ciki ba.? Saboda shi dai tunaninsa a lokacin shi ne ya samu ganinta ko da bata farin ciki,shi tunda yana yi zai yi k’ok’arin ganin sunyi sharing farin cikin da yake ciki,duk da shi nashi ya zama mix-feelings ne ya tsinci kansa a ciki,,haka nan yaji dole yana so ya ganta a yanzun,,k’ayataccen murmushi ya sake saki kafin yace da Bassam
“Bassam.! Muje gidan Mamah yanzun kafin mu wuce.!”
D’if suka yi a cikin motar kowa yana mamakin wannan abu irin na Hammad,shi bazai iya hak’uri bane gar suje banquet d’in su dawo dole sai yasa sun biya wani gurin
“Amma Yaya ai naji Daddy yace mu wuce,me zai kaimu gida kuma bayan itama Maman bata nan.?”
Bai tsaya saurarensa ba yace
“Idan baza kaje ba yafi min sauk’i kace,,Yah bazan jeba,ko ka fita ka bani motar na ja kaina.!”
Girgiza kai yayi saurin yi yana fad’in
“Wane mutum,,ai duk yadda kace haka za’ayi,ranka ya dad’e na Aunty Hansai..!”
A zabure ya kalloshi da fad’in
“Me kace.!?”
Bai ita maimaita masa ba yayi shiru sai dariya da suka d’auka duka su uku
“Kan ubah.! Uban waye yace maka haka sunanta yake.!?”
Murmushi Bassam yayi bayan ya tak’aita dariyarsa da fad’in
“To shi suna Yah har sai ance ga wanda ya fad’a.!?”
Had’e rai Hammad yayi cif yana jifansa da wani warn look
“Wollahi kada ka sake KUSKUREN fad’ar wannan sunan a gaban ido na,,idan ba haka ba zan sab’a maka,kaji dai na fad’a maka,sunanta ne baka sani ba ko mene ne,da zaisa ka kirata da wabnan d’in.? Idan baza ka ce mata Aunty ba,ka kirata da sunanta HAFSAT Ko ka kirata da SABINA ya wadatar,amma kada na sake jin wannan daka fad’a..!”
Yadda yake ziraro bayani yasa take Bassam ya gane kuskurensa tun kafinma aje ko ina sai ya bawa Hammad d’in hak’uri,shi dai bai tanka masa ba yayi musu shiru har suka shigo ALU avenue,a dai² get d’in gidan yayi horn mai gadinsu daya taso da sauri yana ganin su sai ya shaida musu ai basu jima da barin gidan ba suma d’in,tambayarsa Bassam yayi ko yasan inda suka nufa ne,sai yace musu bai sani ba amma yana tunani ba zai wuce gidan Hajiya ba,ma’ana dai gidansu kenan,godiya yayi masa sannan daga nan ya juya kan motar zuwa hanyar gidan nasu.
A lokacin kusan a tare motocinsu suka shigo cikin harabar gidan dasu Daddy,sai dai motarsu tana kan gaba yayin da tasu Daddy take biye musu,fitowa suka yi dukansu da mamakin dalilin da yasa su Daddy suka yo nan d’in al’halin sun barsu a masjeed gurin d’aurin aure suna batun zasu je gidan *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* shin mene ne kuma ya faru yanzun suka dawo gida.? Duka suka yiwa kawunansu tambayoyin without sunyi expecting samun amsa a gurin wani,,wucewa suka yi zuwa cikin gidan,duk da y’an uwa da suke ta jan Hammad da tsokana,shi dai bai wani sake musu ba,saboda yanayin da yaga su Daddy sun shigo wanda yasa ya fahimci akwai damuwa,hanyar guesting room yaga sun nufa while shi kuna Daddy yana tafe yana waya,ko k’arasa wucewar basu yi ba su kuma suka shiga main parlor,lokacin dai² suna shigowa su kuma Mamma da Maman su Sultan suna niyyar fita,danhaka suka gaisa,duk dama dai gaisuwar nasu a tsaitsaye ne su Maman suka amsa duk da sun shigo gidan before su tafi gurin d’aurin aure,sai dai yanayin da suka gaisa d’azun ba shi suka gani ba yanzun,kowa dai cikinsu da abunda yake sak’awa a zuciyarsa,a hakan su Mamma’n suka wuce suka barsu a nan cikin taron y’an uwa,a tsaitsaye suka sake gaisawa da sauran mutane,sai dai ganin babu alamunsu a gidan dole yasa su fitowa suma suka bar gidan,,suna tafe a hanya bayan fitowarsu Sultan yake cema da Bassam
“LB.! Wai anya lafiya kuwa.? Nifa naga fuskokinsu Daddy cikin yanayin damuwa,,bakwa tunanin wani abu ya faru ne.!?”
Ta cikin mirror Bassam ya d’ago ya kallo su da yake suna bayan da fad’in
“Gaskiya dai nayi wannan hasashen tunma a gywin d’aurin aure,buh baza muyi saurin yanke hukunci ba,dole dai mu jira muji daga bakinsu.!”
“Yeah! It’s true,koma mene ne zai fito mu sani,idan ya shafe mu amma.!”
Shi dai Hammad baiyi magana ba cos tunanuka yake akan inda suka tafi a lokacin, side d’in da yake Bassam ya kallo saboda jin yayi shiru bai ce komai ba da fad’in
“Yaya.! Wai lafiya kuwa kayi irin wannan shirun.!? Ko dai Sahibar ce.!?”
Sai a lokacin ya waiwayo ya kalleshi yana squeezing face cike da damuwa
“Wace ce.!?”
Duka a tunaninsa ko daya fad’i haka bai kawo da Sabina yake ba shi yasa ma ya tambaya d’in
“Ur helpmate.!”
Wasu ajiyayyun murmushi ya saki yana kallonsa sai dai bai ce komai ba,murmushin shima Bassam yayi sannan ya d’auko waya a nan tsakaninsu yana clicking yana kuma ci gaba da drivern,gently yasa wayar a kunnensa yana fad’in
“Hello.! charming! Ina kuke ne.!?”
Saurarawa yayi kad’an sannan yace
“Okay good.!”
Daga haka bai sake magana ba yayi disconnecting kiran ya sake maida hankalinsa kan titi suka ci gaba da cin taya,in less than 20 minutes suka k’araso Tahir Guest palace.
Shigarsu Mamma cikin guesting room a zaune suka iske su Malam amma Daddy yana tsaye ya kasa zama sai zagaya parlor’n yakw,har k’asa su Mama suka gaida Malam sannan suka gaisa da mazajen nasu,tunma kafin wani ciki yayi magana,urgently tuni har Daddy ya kallo Mamma da fad’in
“Asiya ina sak’on da kika ce *ALHAJI ISHAQ* ya aiko.!?”
Ajiyar zuciya tayi sannan ta nuna masa gefe inda tasa aka parker kayan da suka dawo dasu,fuskar su duk su ukun a lokaci guda ya bayyanar da mamaki sai Abba’n Sultan ya kallota yana cewa
“Ehh! To munga kaya,amma.! Bamu fahimci abunda yake faruwa ba.”
Gyara zama Mamma tayi sannan ta koro musu bayani kamar yadda suka yi da y’an aiken alhajin,ran Daddy a mugun b’ace ya sake kallon kayan
“Tabbb’ d’i jan..!”
Shi ne abunda ya fara fitowa daga bakinsa followed by sanya hannayensa duka biyu cikin aljihu yana girgiza kai
“Ni..!? Kamar ni *ALHAJI ISHAQ* zai yiwa haka.!? Ni.!?”
Sai yayi shiru yana sake jinjina al’amarin,Abba’n Sultan ne yayi saurin matsawa inda yake ya dafa shi
“Dan Allah ALHAJI kada kace komai,,idan hae yana ganin yayi mana haka ne dan ya tozarta mu,ai mu godiya ya kamata mu yiwa Allah,,saboda had’a zuri’ah da *ALHAJI ISHAQ* ko bala’i.!?”
“Ai shi kenan,,Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi..”
Daddy ya sake fad’a yana neman gurin zama,amma maganar kana kallonsa zaka san yaji ciwonta
“Uhhuumm.! Lallai *ALHAJI ISHAQ* wato wulak’anta ni yaso yi kenan,,yanzun da Allah yasa nak’i amincewa da batun waccan d’aya yarinyar shi kenan yasa na cuci Hammad.!? Ai shi kenan.!”
“Dan Allah ALHAJI kayi shiru da batun,tunda har Allah yasa ba ita kad’ai ce mace ba ai duk da sauk’i,fatan mu Allah ya tsare gaba,ita wannan d’in da akayi auren da ita,Ubangiji ya albarkaci auren nasu..”
“Toh ameen.! Nayi shirun bazan kuma cewa komai ba,amma dole sai ya gane KUSKUREN sa..”
Daddy ya sake fad’a yana jinjina batun
“Dan Allah ka rabu da shi,mu yanzun ma ba sai munje ko ina ba tunda anyi haka,,yanzun kam mun gano dalilinsa na k’in amsa kiransu ai..”
Malam dai kallonsu kawai yake sai dai har lokacin bai samu damar cewa da su komai ba,har sai da Daddy suka yi shiru sannan yayi gyaran murya ya musu sallama,amsa mishi suka yi suna maida hankulansu a kansa,after shi kuma Malam d’in ya fara musu nasiha cikin hikima dangane da abunda ya faru tun daga neman auren Hammad d’in daya gabata da irin rigingimu da suka faru tsakanin Daddy da su Mamma har kawo yanzun da wannan al’amarin ya faru,,sanda ya gama tsaf jikinsu yayi wani irin sanyi,sai suka sake yi masa godiya sosai sannan ya sallami su Mamma saboda yasan dai a cikin gidan za’a buk’ace su,, suna fita yace da su Daddy suma su wuce gurin banquet d’in saboda jama’ar su dake can suna jiran k’arasowar su.
Can d’inma dai gidan su Sabina yinin bikin ne dai suke yi,y’an uwa da abokanan arzik’i cika gida,amarya kuwa da k’awayenta sai suka zama ababen kallo ga al’ummah,ba wai iya kad’ai ga y’an uwa da dangi ba,saboda azababben kyau na d’aukar magana da suka yi.Har kusan Maghreb aka kai ana yini kafin masu shirya amarya suka zo cos a yau d’in za’a wuce da ita zuwa gidan su Hammad,washe gari da wuri su kuma zasu bar k’asar,,a mak’otan gidansu suka samu gidan wata amarya da bata jima da zuwa unguwar ba,masu shiryata suka duk’ufa suka fara nasu aikin,cikin abunda duka baifi a wanni uku ba suka kammaleta a cikin wani elegance wedding attire mai kalar red wine,paisley long sleeve ne mai masifar kyau amma ta k’asa sai ya zama wani irin style mai kama da fishtail,turban suka mata a kanta da wani irin tie mai kyalkyali da beads da aka masa ado da shi shima d’in sak kayan jikinta,sannan suka kawo vail na net suka rufa mata ta baya yana binta a k’asa,around 8:pm aka kammala kimtsata,masu kwaliya suna gama musu duka suka yi sallama da su sannan suka wuce,yayin da su kuma suka fice zuwa ainihin cikin gidan tare da ita,while su duka ukun kuma suna cikin wani aspen black gown mai off shoulder da turban duka a kawunansu mai kalar gold,,lokacin da suka shiga da ita d’akin Baba suka nufa,bayan sun shiga da ita sannan suka basu guri,Baffan Inna,Baban LADO da duk wani makusanci babba a zuri’arta b’angaren Babanta da Inna suna cikin d’akin,tunda ta shiga tana ganin yadda suka had’u kowa yana binta da kallo ta sauke kai k’asa,a hankali hawaye suka fara taho mata,guri ta samu ta rab’a wani irin nutsuwa ya sake shigarta hankalinta a tashe,,baffa ne ya fara yin magana a kaf cikin mutanen gurin saboda ya fi kowa yawan shekaru,bayan yayi mata nasiha sosai mai tsumama zuciya sannan d’aya bayan d’aya kowa dake gurin ya tofa albarkacin bakinsa kafin azo kan Inna da jikinta yayi wani mugun sanyi,d’agowar da Inna tayi ta kalleta bayan tayi murmushi sannan a hankali tace
“Ni kam ba sai nace komai ba,saboda duk abunda ya dace na fad’a mata y’an uwa sun gama fad’ar sa,,abunda kawai zan iya cewa shi ne kiyi hak’uri da duk halin da zaki shiga,rayuwar aure ba kamar irin rayuwar da kika saba yi da mu bane,Allah ya baku zaman lafiya.. Ubangiji ya kad’e fitina,ya tsare hanya..!”
Slowly sautin kukanta ya fara fita yayin da jama’ar gaba d’aya wajen suke bata baki wasu kuma suna fad’in
“Zaki daina ne yarinya,,kowa da haka ya saba..”
Ita dai bata saurari kowa ba taci gaba da hawaye,fita duka sauran mutanen suka yi bayan sun gama mata tsiyar kukan da take aka barsu daga ita sai iyayenta,duk da a lokacin motocin d’aukan amarya sun k’araso amma sai da Babanta ya sake mata nasiha sosai sannan ya kawo sadakinta ya dank’a mata su a hannunta,a nan kukanta ya sake tsananta,sai dai bata karb’a sadakin ba tace ya ajiye a gurinsa,,sannan Inna tayi mata batun tayi hak’uri kada taga basu kaita da komai ba yanzun,sun samu labari ne daga Mamma tace sai an kammala ginin gidansu na nan k’asar da zasu na zama idan sunzo hutu,in sha Allah da zaran an gama d’in za su kai mata kayanta,amma lefenta da komai ankawo d’azun bayan gama d’aurin aure,kuma har anfita dasu,ita dai bata iya cewa komai sai kuka da take,a haka har aka fito da ita da kyar a cikin gidan bata daina kuka ba suka d’auki hanyar state road (gidan surukanta).
Lokacin da suka iso gidan su Hammad sosai aka yi welcoming nasu cikin mutunci da girmamawa,lamarin daya bawa ahalinta matuk’ar mamaki,sai da suka tabbatar sun dank’a amanarta a hannun surukan nata kafin suka yi sallama da su,da kuma itan suka tafi d’auke da sha tara ta arzik’i,ita dai har suka tafi suka barta bata san abunda yake faruwa ba dan har lokacin bata daina kuka ba.
Cikin yinin ranar gaba d’aya duk iya son Hammad da yaga Sahibar sa abu gaba d’aya yak’i yiwuwa,saboda tayi masa b’atan daya gagara gano inda ta shige har dare kuma bai samu yaji koda muryarta bama,,ita kuwa a nata gefen suna tare da su Badra yauma kuma tare suka kwana sai dai yau a d’akin Mamma suka zauna saboda na Badra akwai mutane cikinsa.
Hankalin Hammad fa tun safiya har dare gaba d’aya ya kasa kwanciya saboda rashin samun ganinta da bai yi ba yasa hankalinsa ya fara neman tashi,ko a wayar ma daya kira saboda takaici sai company suka masa bak’in cikin jin muryarta ta hanyar sanar masa wai not reachable,tsabar haushin daya ji shima d’in a ranar sai tunaninsa gaba d’aya ya gaza kawo masa kiran Badra ko Jannat yace su had’a shi da ita,,a wannan daren duk da yana cikin damuwar rashin ganinta da bai samu yayi ba daya sashi yayi wani irin lak’was ya koma wani quieten,magana da duk tsokanar su Sultan duk yak’i kulawa,yana jin farin cikinsa over his worried,,yayin da aka ce dare ya fara nisa kuma sai ya zama yayi isolating kansa in front of rabba,strengthening himself wajen nuna tsantsar godiyarsa ga Ubangiji (S.W.T) bisa ni’imar da yayi masa.
*In the morning…*
Tun asubah kafin ma ace gari ya gama yin haske duk wasu kayansu da komai da aka san zasu tafi da shi tuni aka gama settled nasu a motoci,lefenta ne dai da suka zo dasu daga gidan su Mamma tasa a barsu nan idan an d’inka sai a kai mata tunda dai zamansu a can d’in zaifi yawa akan nan,,bayan duk an kammala yi musu shirye² around 6:30am na wayewar litinin d’in suka fito kowa cikin shirin tafiya,(Hammad,Sultan,Sadeeq,Bassam,Jannat,Zeeharis da Badra) duka sun hallara a parlor sai itan kad’ai da ake jiran fitowarta,,sai da suka d’auki ak’alla mintuna kusan ashirin zaune a parlor suna ta hira kafin Mamma ta fito rik’e da hannunta,fuskarta nan tata d’auke da simple make-up da aka mata applying,,yauma dai kamar kwanakin da suka gabata,tana sanye da wani irin long sleeve na arabian gown bak’i sai vail d’in rigar da aka mata rolling d’insa over her head aka mak’ale da pin mai matuk’ar kyau,,tunda suka fito idanunsa ya sauka kanta,kallo d’aya yayi mata amma sai yasa shi yin ajiyar zuciya had’e da lumshe idanunsa,a hankali sanyayyar iskar ni’ima mai tattare da nutsuwa ya fara sauka masa cikin jikinsa,har suka k’araso bai bud’e idanunsa ba,amma yana jin sanyayyen k’amshin turarukanta masu k’arawa zuciya shauk’i a kusa da shi,a hankali yayi k’ok’arin bud’e idanunsa ya sake sauke su akanta,a kusa da shi Mamma ta zaunar da ita sannan ta kamo hannunsa ta had’a da nata tana masa murmushi lokacin daya d’ago ya kalli Mamma da hannunsa wanda take rik’e da shi cikin nata sai yayi murmushin shima amma bai yi magana ba
“Ga amanata nan,na dank’ata a hannunka,,buh ina so ka rik’e a zuciyarka dai² da yini d’aya idan ka bari yarinyata ta zubar da hawaye saboda kai,ka shirya karb’ar hukunci daga gare ni,,zan iya d’aukan komai amma banda ganin b’acin ranta.. Ina fatan ka fahimci kalamai na,kuma zaka na tinawa da su a ko da yaushe..??”
Kai yayi saurin gyad’a mata yana lumshe idanuna
“Shi kenan zaku iya tafiya,,ina yi muku fatan alkhairi,ubangiji yasa albarka a zaman ku,Allah kuma ya sauke ku lafiya.”
Mik’ewa yayi cikin hanzari ya rungume Mamma idanunsa suna kawo ruwan hawaye still hannunsa da nata yana a had’e kamar yadda Mamma’n ta had’a su bayan ta zare nata tabarsu rik’e da juna,k’asa² yadda ba kowa zai ji ba sai Mamma’n kawai yace
“Thank u Mah.. Ana ahabbuk-thtiir..”
“Wa’ana kamaan habibiiy..”
Murmushi yayi mai sanyi sannan ya zaro handkey daga aljihunsa ya goge hawayensa ba tare da kowa ya fahimci abunda ya faru da shi ba sannan ya saki Mamma ya d’an ja baya kad’an,,sai da Mamma tayi musu nasiha sosai dukansu har su Sultan,sannan suka sake yin sallama,suna cikin sake yin sallamar da ita ne,sai Badra ta waiga ta kuma waigawa kamar dai tana neman wani abu,Mamma data kula da ita ta kalle ta tana tambaya
“Kiddo.! Mene ne kike nema ne.!?”
D’an murmushin yak’e tayi sannan tace
“Mah.! Ina d’ayar ne wai,naga kowa amma ita ban ganta ba.!”
Gaba d’aya idanunsu komawa kanta suka yi kowa yana son jin wa take neman,Mamma dai da bata fahimci abunda take fad’a ba tace
“Wace ce d’ayar kuma baby.!?”
Satar kallon inda Hammad yake tayi cikin rad’a tace da Mamma
“Mah.! kiyi a hankali kada Yah Hammad yaji.”
Murmushi Mamma’n tayi sannan tace
“To uwata.!”
Duka parlor’n sai suka yi dariya amma banda Hammad da ya tafi wata duniyar
“Mah.! Idan ba gulma ba dama waye zaice baya so aji me yake fad’a ne.!?”
Bassam yayi maganar yana mik’ewa tsaye da hararar inda Badra take,Sultan ne yayi caraf ya amshe zancen da fad’in
“Ni kam dai Bassam bansan mene ne Daddy’s kiddo tayi maka ba,duk ka takura ta a gidan nan,ko dai².?”
“A’aahh! Ni me zai had’o ni da ita kuwa.!?”
“Fad’i gaskiya dai,ko kana tsoron za mu kwance ma zani ne.!?”
“Idan kun kwance ma baza’a rasa mai d’aure min ba..!”
Dariya suka sa masa,Badra dake kusa da Mamma ta kalleshi tana juya idanu
“Toh dai yanzun so kake kace min munafuka ko me.!?”
“Ohoo! Miki dama idan ba munafircin ba mene ne kike shirin yi.? Kince kada kowa ya ji,ai idan aikin gaskiya ne babu wanda zai k’i aji shi yana aikatawa,,ko ba haka ba..?”
Had’e rai Sultan yayi yana kallon Bassam da wani irin kallo mai kama da harara
“Malam ya isheka haka nan.!”
Dariya Bassam yasa da fad’in
“Haba.! Yah Sultan mene ne to dan na fad’i halinta.!? Ko dai kana goya mata baya ne.!?”
“Amsa kake so na baka.!?”
Gira Bassam ya d’aga masa alamun ehhh,yafito shi Sultan yayi da hannu yana fad’in
“Zo to na fad’a maka ko mene ne kake son sani.!”
Ya k’arashe maganar yana janye hannun long sleeve d’in dake jikinsa
“A’a ni ba sai na zo ba,ka fad’a a haka ma ya wadatar..”
“Tsoro kake ji wai..??”
Kai ya girgiza alamun A’a
“To zo mana,ai nima amsa ne kawai zan baka..”
“A’a ni bazan zo ba fa..”
“Tsoro ko.!?”
“A’aahh.! Tsaro dai.!”
“To kawai kaje mana,ai amsa kake son samu,ko ba haka ba.!?”
Sadeeq da yayi maganar yana kamo kafad’arsa ya tura shi gaban Sultan,saurin gocewa yayi daga inda Sultan yake yana kiran Mamma ta taimake shi,nan ma gaba d’aya suka sake sa dariya,Jannat data k’unshe baki tana dariya bata yi aune ba ta jiyo Bassam yana fad’in
“Ya dai.!? Ke masoyiya kina kallo suke yiwa abun k’aunar ki haka..!?”
A daburce ta saki baki tana kallonsa dan ko kad’an bata tab’a zaton zai fallasa ta a cikin mutane ba har haka
“Aahh.!” Sai kuma tayi shiru tana ci gaba da raba idanu,kamo shi Sultan yayi yana dariya
“Kaji yaro da rinto,wato ma soyayya kake.!? Ai kuwa sai ka jira layi ya zo kanka,,ko mu d’in an fad’a maka ba jiran muka yi ba ne.!?”
“Allah sawak’e,wane jiran zan yi..? Ku dai da kuka ga zaku iya bawa rayuwar tuzanci gudummuwa ai kunga kuna ta fama,,amma mu babu wani jiran da zamu yi.. Ko ba haka bane masoyiya..!?”
Sunkuyar da kai tayi k’asa ta kasa amsawa,a hankali shima Hammad ya matso inda suke yana fad’in
“To wai ku duk mene ne ya janyo wannan batun..!? Mu da muke da tafiya a gabanmu.!?”
“Wollahi Yaya Jerry’n Mamma ce ta taso da shi,wai sai an fad’a mata inda d’ayar take.”
Yamutse fuska yayi yana tab’e baki
“Mene ne kuma d’ayar.!?”
“Ohoo! Mata ga dai ta nan tak’i fad’a,shi kuma Yah Sultan yana wani neman bata kariya..”
Murmushi Hammad yayi yana kallon Sultan
“Yane Malam.? Wai son k’anwar nan tawa kake yi ne.!?”
Harararsa Sultan yayi cikin sigar wasa yace
“Meye ruwanka ne a nan kuma..?”
“Ruwa na kake tambaya.!? Saboda ni zan bada ita,shi yasa nake maka magana kana bani amsa a tsaitsaye.! Idan ba zaka fara girmama niba fa sai a fasaah.!”
Ya k’arashe maganar cikin salon jan harufa
“Haba babban Yaya waye ma ya isa yace ba zai girmamaka ba.!? Ai yana fad’ar haka an soke kwangilar kenan..!”
Bassam yayi magana yana wani jinjina kai da yiwa Sultan dariyar mugunta
“Yo ku soke mana,,sauk’in dai nima akwai takardun kwangilar ku da zasu biyo ta ofishina..!”
“Kaii! Dakata mana.! Kana son yi mana alfahari ne!? To idan baka sani ba,wannan kwangilar tuni ta bar k’ark’ashin ikonka,, itanma iko na ce.. Ko kana so na gwada maka ka ganu..!?”
“Ehh! Gwada d’in mu gani idan zai yiwu..!”
Murmushin gefen baki Hammad yayi kafin ya yafito Jannat yana fad’in
“Zo nan k’anwa..!”
Matsowa tayi gabansa tana sunkuyar da kai,shi kuma gogan cikin izza ya kalleta yana fad’in
“Ina so ki bani amsa kowa yaji a nan..!”
Tana girgiza masa kai tace “Toh”
“Kina son Bassam da gaske..!?”
Sai data d’ago ta kalli inda Mamma take sai kuma ta sunkuyar da kai,juyawa yayi inda Mamma take yayi murmushi sannan yace
“Mah.! Ki d’an rufe idanunki ko ki juya baya,,muna wata y’ar magana ce,to kuma ganinki a nan zaisa na rasa amsar da nake son samu..”
Saurin juya baya Mamma tayi tana fad’in
“Idan kuka ce na bar muku wajenma duk zan iya ai..”
Murmushi kawai Hammad yayi yana kallon Jannat
“D’ago ki fad’a min,da gaske kina sonsa.!?”
Kai ta kad’a masa followed by
“Ehhh!”
“Shi kenan an gama magana kuje abunku,ni da kaina zan fad’awa Daddy.!”
Ya fad’a cike da isa,kallonsa Sultan yayi yana tafi
“Da kyau jarumi..!”
D’age shoulders Hammad yayi yana kallonsa
“To ya kaji tsarin..!?”
“Sosai ka burge kam,,amma dai wannan salon kwafarsa kayi ba.!?”
Dariya Hammad yayi data bayyana jerarrun hak’oransa
“Baka yarda zan iya yin hakan bane.!?”
“A’a’a! Ko kad’an zaka iya kam,,amma dai ban yarda zaka kai maganar gabansu Daddy ba..”
Gyad’a kai Hammad yayi da fad’in
“Shi kenan kasa ido,,za kayi kallo.”
A hankali Mamma data basu baya tana dariya ta juyo da fadin
“Kaii! Ni kam kuzo ku wuce,wannan hiran naku naga alama bazai k’are ba,idan kun shiga jirgi ko kun isa can kwayi shi a can..”
“Laa! Mamma korarmu kike yi.!?”
“A’a na daifi so ku tafi ne,kada ku b’ata lokaci,idan kuka ci gaba da zama har jirgi ya tashi sai kun biya su bata lokacin da kuka sasu yi..”
Ba dan sun so ba haka Mamma ta sako su gaba har bakin mota,y’an uwa da suka zo biki suma wasu ciki suka yo musu rakiya suna masu binsu da addu’o’in fatan sauka lafiya,,sai da taga tafiyarsu sannan ta koma cikin gida tana murmushi had’e da jin kewarsu.
Motoci ak’alla uku ne suka tafi yi musu rakiya bayan nasu guda uku,Hammad da Sabina suna cikin mota d’aya,yayin da Badra,Jannat da Zeeharis suma suke cikin d’aya,sai d’ayar da su Sultan suke ciki shi da Bassam da Sadeeq,duk da Sabina ta so ace tana tare da su Badra amma ina oga ya juye yace bai san wannan batun ba,dole tasa ta hak’ura ta tafi tare da shi d’in,sai dai tun da suka shiga motar tak’i kallonsa bare tayi masa magana har suka k’araso filin jirgi bata yi ko kwakwkwaran motsi ba,,duka da isowarsu da kammala musu komai har shigarsu cikin jirgi ba’a d’auki ko rabin awa ba,,ko a cikin jirgin kansa sai suka kasance suna zaune a b’angarori daban²,sab’anin Hammad da Sabina da suke bigire guda a mafi kusancin gurin zama,kuma har lokacin da jirgi keta k’ok’arin tashi bata yarda magana ta had’a su ba,saboda ita burinta kawai ta zauna tare da k’awayenta,shi kuma fuskantar hakan da take so sai yasa shima ya gimtse yak’i bata fuska bare tace zata kawo masa wasa,a haka har jirginsu ya samu damar tashi babu wanda yayi magana da kowa.
Tafiya tayi tafiya,yayin da suka d’auki tsayin awanni masu yawa a sararin samaniya suna shek’a tafiya cikin giragizai,nan fa jikkunan mazauna cikin jirgin suka fara yin laushi,a lokacin bacci ya fara kawo sumame,,ko ita kanta sarauniyar kuramen dake gefen window bata san lokacin da bacci ya sace taba,,shi kuwa Yallab’ai mai tsuntsuwa da yake idan da sabo hakan ya zama jinin jikinsa ko gyangyad’i ya kasa d’aukar sa bare bacci. Yanayin yadda cikin jirgin ya d’auki shiru shi ne yasa shi waigawa yana d’an kallon yadda mutane suke ta faman bacci kamar a gidajensu,ai kuwa nan yaga fiye da 5/6 na mutanen cikin jirgin duk sun wula zuwa duniyar bacci,wad’anda basu yi bacci ba baifi a lissafa su ba,murmushi yayi sannan ya juya ga abar k’aunarsa yana kallon yadda take wani irin wahalallen bacci saboda wuyanta daya lankwashe,belt d’in jikinsa ya cire sannan a hankali ya matsa kusa da ita sosai yana kallon kyakykyawar fuskarta,murmushi ya sake yi gently sai ya d’ora mata light kiss a saman lips d’inta da suke ta kyalli,lamarin daya haddasa masa jin wasu irin mugun feelings suna taso masa har yayi dana sanin aikata hakan,,a duk lokacin da zai kusanci inda take shi da kansa yasan me yake ji game da ita,sai dai kawai yana daurewa ne,buh a bayan duka Daddy ya kasa fahimtar damuwar,yanzun ma da yake daf ji yake kamar kada ya kyale tunda dai yanzun mallakinsa ce,amma kasancewar yana ganinsu cikin jama’ar da babu tabbas ace wani bazai farka ba shi yasa dole ya sawa zuciyarsa hak’uri har su sauka,kura mata idanu yayi deeply yana ayyanawa a ransa a yau komai zai zama tarihi,sai ya lumshe ido yana sakin bayyanannen murmushi kafin ya bud’e idanunsa akanta,sai daya kalli bayansa da gefe saboda gudun kada wani ya gansu sannan ya juyo ya kalleta,still dai baccin take amma wannan karon a jikinsa ne saboda ya gyara mata kwanciyar shi yasa itama sai taci gaba da juyi a cikin jikinsa ba tare data sani ba,k’asan chin d’inta ya rik’o slowly sai ya d’an d’ago fuskarta dai² yadda zai iya aiwatar da abunda yake so,yana kallonta da murmushi kwance a fuskarsa kamar ance masa idanunta biyu sannan ya kai bakinsa saman nata,passionately sai ya tsotsi lower lip d’inta sannan ya d’ora mata peck a forehead da fad’in
“Sleep tight Helpmate..!”
Gyaran murya Sultan yayi dake a bayansu suke su kuma su BADRA suna d’ayan hannun a centre d’insu,ba tare daya juya ba yace
“Ya dai Malam..!?”
“A dunga yi dai ana gimtsewa dai..”
“Saboda mene ne..!?”
“Kada a ji kunya a gaban al’ummah..”
“Kunya akan halalin nawa..!?”
Sai yayi murmushi kawai daga haka bai sake cewa wani abu ba ya lumshe idanunsa yana ci gaba da shak’ar k’amshin turarukanta masu dad’i da kwantar da hankali,sake yin gyaran murya Sultan yayi ba tare da Hammad ya juya ba yace
“Fad’i abunda yake bakinka..”
A hankali Sultan ya matso daf da shi ta bayan cikin muryar rad’a yace
“Amma nace ba,,shin zaka bani k’anwar taka..!?”
“A’aahh.! Bazan bayar ba..”
“Haba yallab’ai,kayi hak’uri mana ka tausayawa wannan bawan Allah’n.!”
“Ko kuma tuzuru ba..!?”
“Ehh! Naji ni dai ko me zaka fad’a bazan damu ba,ka amince ka bani k’anwarka shi ne burina..”
“Shi kenan ka bari nayi tunani..”
Harararsa Sultan yayi ba tare da ya sake yin magana ba sai shima yaci gaba da duba magazine d’in dake hannunsa yana murmusawa,while shima Hammad sai yaci gaba da lallab’a abar k’aunarsa,yana fatan su sauka cikin salama….