ALKAWARIN JINI CHAPTER 4 BY _HAWWA MUH’D USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya fad’a da wannan husky voice d’insan while yana kallon cikin idanunta,ita kam saurin janye idonta tayi daga kallonsa,sannan ta maida hankalinta zuwa kan hannunta,a lokaci guda shima Hammad ko da ganin tana neman juye masa ruwan ajiki sai yayi saurin rik’o gefen tray d’in nd still yana sake kallonta,sai a lokacin ta fahimci dalilinsa nayin magana dan yadda ta kusa kifar masa da tray d’in a jiki a dalilin kallonsa data tafi yi har bata san lokacin data kusa yin b’arin ba
“Sorry..!”
Ta fad’a tana gyara rik’on tray d’in a hannunta sai dai ya kasa zama stable saboda yadda duk jikinta yake rawa sannan ga shi sun kusanci juna wanda hakan yasa yanayin da suke ciki d’in yake neman yin tasiri akanta,kan tray d’in ya maida hankali ba tare daya sake kallonta ba ganin ta kasa tab’uka komai ya ce
“Uhhuumm! Saki..!”
Hannayenta tayi saurin janyewa daga rik’on da tayima tray d’in sai dai ta kasa motsawa a gurin,yadda ta girke ita bata yi gaba ba kuma bata yi baya ba,nd still tana nan a tsugunen tamkar wacce akayi sculpturing nata (sassak’a) sai yasa shi d’an kallonta kad’an,ko daya ajiye tray d’in a hankali ya sake d’agowa ya bita da wani shu’umin kallo,har ya bud’e baki kamar zai yi magana kome ya tuna kuma sai yaja baki yayi shiru,,har lokacin tana gabansa kamar mai d’aukan darasi ba tare data iya motsawa ba,haka shima bai ce mata ko ci kanki ba bare tayi tsammanin zai ce ta matsa,dan kanta ko data gaji da tsugunon sai ta d’an koma baya kad’an kafin ta mik’e duka ta juya da niyyar ficewa,,a hanakli yasa hannu ya d’auki ruwan yana k’ok’arin sha,har yasa kofin a bakinsa yaga ta mik’e tana shirin fita,kofin yana jikin bakinsa bayan ya kalleta sai ya d’an zame shi kad’an cikin wani murya yana fad’in
“Where do u think to go..!?”
K’yam ta tsaya a gurin ba tare data sake iya motsawa ba,shi kansa Hammad bai zato ba yaji maganar yayi escaped a bakinsa,a hankali ya d’an datse harshensa had’e da runtse idanunsa sabofa yadda maganar yayi masa fitar bazata,ta d’auki lokaci a tsaye a gurin ba tare data juyo ba,ko da ganin bata juyo d’in ba nd ya san bawai ji ne bata yiba sai yasa shi basarwa cikin shan k’amshi kuma yana sake cewa
“Kin manta sharad’in dana fad’a miki..? Ko kuwa kina sane ne,ganin daman bani amsa ne baki yi ba..??”
Still tana tsaye a gurin ta kasa juyowa bare ta kalleshi sai dai jikinta duka ya gama mutuwa,yadda yake magana da kowane motsawar second a duk lokacin da zasu had’u ita kam duk da tak’i jinin a dunga nuna mata isa nasa yanayin yana bala’in tasiri a cikin jini da b’argonta,musamman na yau data ganshi a lokacin da bata zata ba,ji take kamar ta koma gabansa ta tsaya nd ta bud’e baki ta tambaye shi shin ya dawo kenan ko kuwa zai koma..? Saboda yadda a y’an kwanakin da suka gabata taji wani irin kewarsa a tare da ita duk da bata san yaushe ne har tayi irin wannan sabon da shi ba da har zaisa taji rashin irin hakan a tare da ita,,buh a yanzun kam tana jin guiwoyinta a sanyaye duka da al’amarin sa,nd haka nan yanayinsa data sake gani yanzun a cikin idanunta sam bai mata kama dana mutumin da zata tsaya a gabansa tayi masa irin wannan shirmen bane,mutumin da ganinsa a daf da ita kad’ai yasa ta shiga razani,shin yaya zata kasance idan har aka ce tsaya gaba da gaba tayi masa irin wannan tambayar..?? Wannan tambayar shi ne ya fara zuwa mata arai,wannan dalilin yasa nan take sai ta sake tsintar kanta ciki wani irin zarani kenan wanda ta rasa gano dalilin da yasa take shiga irin wannan yanayin a wasu lokutan,tayi nisa a cikin tunanin abunda ya kamata tayi,nan ta sake jiyo shi yana fad’in
“U can go..Tunda haka kika zab’a..”
Daga haka bai sake magana ba ya shiga wasa da car keys d’insa,yanayin yadda yayi magana ya tabbatar mata bai ji dad’in abunda tayi masa ba,a hankali nd cikin rashin kuzari ta d’an waiwaya kad’an ta kalleshi kafin ta juyo dukanta,shi kam bai ko kalleta ba har ta fara takowa dan yadda ta sa shi jin wani iri har cikin zuciyarsa,cikin sigar jin haushi taga ya sake tab’e baki sai dai bai yi mata magana ba har ta koma ta zauna,shiru ne ya ziyarci d’akin na wani lokaci daga shi har ita babu wanda yace da kowa komai,a hakan har baffa ya dawo ya tarar dasu,lokacin ko daya shigo ya tarar da su duka sunyi zugum wa juna babu mai cewa komai,a hankali sai ya girgiza kai yana fad’in
“Uwata..! Ke kuma haka akeyi sai ki bar mutum shiru babu wani magana,ke kinyi shiru shima kin barshi shirun..Dad’in samarina kenan da su ne nasan yanzun da tun shigowa ta najiyo karad’in su..”
A hankali ta sake nutsewa cikin jikinta dan kunyar da kalamanta baffan suka sata ji tana d’an murmushi sama²,shi kuwa gogan d’agowa yayi ya kalleta sai daya sake tab’e baki kafin ya kalli baffa dake neman gurin zama yana cewa
“Baffa wai dama tana magana ne..!? Ni tun da nake zuwa ban tab’a jinta tana hira da kowa ba..I thought ma she’s a deaf..!”
Sarai taji me yace sai dai baffa da bai gane me ya fad’a a last ba,buh duk da hakan sai yayi murmushi
“A’aahh! Sosai ma,,ai kuwa uwata tana magana sosai,sai dai ko da yake baku yi sabo ba shi yasa take zama shirun..”
“Uhmm! Ai kuwa dai baffa sai dai idan ku take iya yima magana,,,amma ni ina tunanin tunda na santa bana jin zan iya tuna abunda na tab’a jin daga gareta.”
Dariya baffa ya sake yi shi kuma hakan sai yasa yayi amfani da sautin dariyar baffa wajen furta
“Shi yasa nayi zaton ko kurma ce ai..!”
Saurin d’agowa tayi ta zuba masa ido jin abunda yake fad’a,sam bata yi tsammanin idanunsa suna kanta ba a lokacin dan haka sai ta shagala wajen kallonsa,muryarsa ta tsinto k’asa² kamar na mutumin dake son yin rad’a
“Kallon fa..Na mene ne.!?”
Saurin sunkuyar da kai tayi k’asa dan ko kad’an bata yi tsammanin ita yake kallo ba,cikin k’unk’unin masifar abunbuwan da yake mata tun zuwansa duk da ta kasa gane ma’anar hakan ta furta
“Kaii..! shi wannan ya cika baud’ad’d’en hali,,yanzun yayi magana kamar ba shi yayi ba..huh.!”
Wani mugun smirk ya saki ba tare daya kalleta ba ya furta
“Baffa..! Ni kam wai mene ne asalin sunanta ne..!?”
Murmushi baffa yayi kafin ya kalle su duka
“A’aahh! Wannan kuma ka tambayeta gata nan gama nan,kasan ance wak’a a bakin mai ita yafi dad’in sauraro ko..?”
Jinjina kai yayi yana murmusawa,ba tare daya kalleta ba ya furta
“Y’an mata..! Mene ne ainihin sunan ki ne..!?”
Sai data harare shi kafin ta furta
*”HAFSAH..!”*
Jinjina kai yayi kafin yace
“Suna mai dad’i.. Buh mene ne ma’anar sunan naki ne..I hope dai kin sani ba wai sunan kawai su baffa suka sa miki,ba tare da kin san ma’anar saba..!”
Wannan karon sai data d’ago ta kalleshi kafin ta harare shi tana girgiza kai a hankali,aaboda yadda yayi tambayar gani tayi kamar da rainin wayo a cikin maganarsa,baffa kuwa yana jinsu yana kishingid’e sai murmushi kawai da yake yi
“Malama kada ki k’ara yimin wannan abun daga yanzun,,,dan haka wannan ya zama na k’arshe da zance kinmin wani abu..A kiyaye ko dan gaba..!”
Kallonsa tayi saurin sake yi a tunanin ta zata ga yana kallonta,amma sai taga hankalinsa kamar yana kan keys d’insa,d’auke kainta tayi itanma sannan ta bud’e baki da kyar tace
“Origin of name Hafsa,was the name of prophet Muhammad (P.B.U.H) wife,nd a daughter of sayyadina Umar bin khattab (R.A),,in English HAFSAH has different meaning first of it,beautiful,moon,young lioness nd…!”
Jinjina kai yake tayi tunda ta fara magana,haka nan jin yadda take furta ko wane harafi a muhallinsa kai kace ita ne asalin grammar
“Masha Allah.. That’s great..Bravo alaik..!”
Yadda yayi maganar yana lumshe ido tare da jinjina kai ba tare daya bari ta k’arasa fad’an abunda ke bakinta ba yasa ta sakin d’an murmushin jin dad’i itanma,a hankali kuma jin tayi shiru sai ya sashi d’agowa,shi kansa lokacin ko daya d’ago ya ganta tana murmushi har cikin ransa sai da yaji dad’in hakan,a nan ne har ya shagala da kallonta na tsayin lokaci,while deeply kuma yana tambayar kansa
“Ohh.! Ashe dai da gaske tana da baki har haka..? Why to ni a lokuta da dama take min shiru..!? Kenan hakan yana nufin laifina ne ko me..??”
D’an murmushi yayi kafin ya sake yin magana a zuci
“Lallai kuwa zanyi ta saki magana a duk lokacin da muka had’u,,imma kin shirya ko baki ahirya ba..!”
Cikin dabara ya d’ago ya kalli baffa dake kishingid’e idanunsa a kulle,sannan a hankali ya maida kallonsa kanta cikin hikima irin nasu na Psychologist ya shiga watso mata tambayoyi kan abubuwan da suka shafeta,duk da ba kowanne yake samun amsa ba dan yadda take magana,amma dai yana samu ta amsa wasu kai tsaye wasu kuma sai ta d’an yi jim,nd wasu ma shiru kawai take bata amsaau sai dai ya tsallake su,,wannan lokacin kam duka k’in barinta yayi ta motsa a gurin,nd wani abu daya d’aure mata kai shi ne,lokacin da yake yiwa baffa wani magana,wanda yasa ta binsa da kallon mamaki sai dai bata fahimce shi ba,abunda ya faru kuwa shi ne a lokacin suna magana da baffa sai taji shi yana cewa
“Baffa..Ni kuwa ina son fad’a maka wani magana,,ko tambaya zance nema i dunno know how ya kamata ace nayi maka maganar,buh tun tuni nake son ace nayi ta,amma dai..!”
Sai kuma yayi shiru yana kallonta k’asa²,murmushi baffa yayi yana gyara zamansa daga kishingid’a zuwa zama sosai da fad’in
“Toh..! mai babban suna..Ina sauraronka,,zaka iya fad’a min ko wane magana ne kada kaji shakka,ni ai matsayin d’a kake a gurinmu,mene ne abunda zaisa ka kasa sanar min kuma..?”
Murmushi yayi cikin hikima kafin ya furta
“Wollahi baffa,wata na gani ne a cikin garin nan,,to amma kuma ni abunda ban sani ba shi ne,shin ko zata iya zama dani..??”+
Murmushi baffa yayi irin nasu na manya kafin ya amsa masa
“A’aahh! Mai babban suna,,dama wannan ahi ne maganar da kake jin nautin fad’a,amma kuwa anya yanzun akwai yarinyar da zata kalli saurayi kamarka ace ta nuna bata ra’ayi..? Ai wannan abun a duba ne..Na tabbatar duk macen da zaka ce kana so bawai iya nan garin ba,a ko ina take a fad’in duniyar nan,ko da ace y’ar wani mai muk’ami ce,na tabbata ba zata tab’a k’inka ba..Sai dai kuma dan wani dalili nata can..Amma bana jin za’a samu..”
Murmushi ya sake yi mai k’ayatarwa kafin ya ci gaba da kallon reactions d’inta ta k’asan ido
“To amma baffa,,idan kuma aka samu akasi fa iyayenta suka nuna basa ra’ayin na,a matsayina na wanda ya fito yak’in neman aurenta..!?”
Dariya baffa ya sake yi sannan ya ce
“Shi yasa tun farko ai na fad’a maka,yadda na fahimci halayenka gaskiya bana zaton za’a samu wani uba da bazai so mutum irinka ya kasance suruki a gurinsa ba,yadda na d’auke ka a zuciyata bana tunanin akwai wata yarinya da sata fito tayi da’awar ta fi k’arfin kana,yo ko k’asar masu jajayen kunnuwa idan da zaka je a gujema zasu dunga kawo kansu bare mu a nan..Saboda haka ina son ka fad’a min ko y’ar gidan waye in dai har a cikin garin nan take,na yi maka alk’awarin ni da kaina zan shige maka gaba har sai na tabbatar da ka sameta..”
Murmushin jin dad’i yayi saboda yadda kalaman baffa suka gama faranta masa,,ga *SABINA* kuwa duk wannan surutun da yake yiwa baffa tuni nutsuwarta ta jima barin gangar jikinta,dan a wannan lokacin bana jin ta fahimci akan mene ne suke tattawar bare har ta iya gano wani abu ko kuma inda maganar tasu ta dosa,,though ma dai duk da bawai ace ya ambaci suna ba ne,amma haka nan sai ta fara jin zuciyarta tana tsinkewa,runtse idanunta ta d’anyi a hankali yayin da take jin wasu irin bak’in yanayi suna ziyartar ta,cikin sauri ta mik’e ta nufi hanya ba tare data yi musu magana ba,har ta isa bakin k’ofar fita baffa ya kallota yana fad’in
“Uwata ina kuma zaki je,,naga kin tashi..Ko kuwa har kin gaji da hiran..!?”
Ba tare data juyo ba sai dai yanayinta zuwa lokacin gaba d’aya ya sauya
“A’aahh! Baffa zan jene na sha magani,,naji kaina yana min ciwo..!”
Ta gefe ya kallota yana sakin murmushi dan gaba d’aya ya gama fahimtar inda ta nufa da dalilin da yasa ta tashi
“Subhanallah! Amma uwata yanzun nan fa lafiyar ki k’alau kuna ta hira..!”
“Ehh! Baffa nima yanzun ne naji kan nawa yana sarawa..Shi yasa zanje na duba magani,kafin ya dame ni..”
Ta karashe maganar had’e da dafe goshinta da take jinsa kamar zai fad’o k’asa
“Sannu uwata Allah ya baki lafiya,,maza to ki hanzarta ki samu magani ki sha kinji ko..sai ki d’an kwanta ki huta..!”
“To baffa..”
Tana fad’a tasa kai ta fice ba tare data jira taji me zasu sake tattaunawa akai ba,idanunta cike da damuwa take tafiya wanda yasa ko ganin inda take jefa k’afafunta ma bata iya tantancewa,a haka har ta k’arasa shigewa d’aki,da shigarta ciki ko data tsinci kanta a tsakiyar d’akin kan gado ta kife had’e da sakin wani karayan kuka mai tattare da ban tausayi…..Da kallo ya bita har ta fice daga d’akin,haka nan sai yaji zuciyarsa tayi masa wani iri sakamakon yanayin da yaga ta fita a ciki,wanda kallo d’aya kawai da yayi mata tuni ya tabbatar masa ba k’alau take ba,jikinsa ne ya sake yin sanyi da lamarin,nan take yaji zuciyarsa ta fara tambayarsa
“Shin mene ne hakan ka aikata Hammad..?? Me kake nufi ne da yarinyar mutane..? Shin Wannan shi ne abunda dama kake buk’atar yi..?”
Shiru ya d’anyi na wani lokaci ba tare daya iya ko da tari ba sai maganar da zuciyarsa ke yi masa da yake sauraro,maganar baffa ce ta katse shi daga duniyar daya tafi
“Mai babban suna,, na tambaye ka amma naji kayi shiru..Nace shin wace yarinya ce,,kuma a ina take..!?”
Dogon numfashi ya sauke a hankali cikin rashin kuzari ya furta
“Baffa..Dama.!”
Sai ya sake yin shirin nd deeply yana jin kamar idan ya tona sirrin zuciyarsa ga baffan bazai tab’a amince masa akan maganar ba
“Uhhuumm! Ina sauraren ka..Ka fad’a min duk abunda kake da buk’ata,, in sha Allah ni kuma zanyi iya yina akai da yardar Allah,har saina tabbatar da cewa ka samu wannan abun..”
Jimm ya sake yi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin mugun bugu,a hankali ya maida idanunsa ya kulle kafin cikin sanyin jiki ya furta
“Baffa ba kowa nake magana akanta ba data wuce *SABINA,* ita nake so,ba kowa ba,kuma ita ce nake nufi..Duk maganar da nake yi akanta ne baffa,,tun daga ranar dana fara ganinta har yanzun na tsinci kaina a cikin wani irin hali,wanda ban tashi fahimtar abunda ke shirin faruwa da ni ba sai cikin kwanakin nan da nayi ban zo ba,,dan Allah baffa ina rok’on ka,ko da ace bayan kasan wannan sirrin bazaka k’i bani ita ba,,nayi maka *ALK’AWARI* baffa kuma na tabbatar maka da cewa zan kasance mai rik’e ta amana,,ba zan tab’a cutar da ita ba,hakama bazan bari a cutar da ita ba..Idan har kuma kana ganin baka amince dani ba baffa,kana da ikon hana ni ita,,amma wannan wani sirri ne daya kasance daga zuciyata..Sai kuma idan har ace ka riga kayi mata miji,na tabbata babu yadda zanyi dole ne nayi hak’uri sannan na janye maganata..!”
Shiru baffa yayi yana saurarensa nd idanunsa duka akan Hammad d’in har ya dasa aya ba tare daya iya cewa da shi komai,jin yadda yayi shiru yasa Hammad d’ago kansa dake sunkuye ya d’an kalli baffa da idanunsa da suka fara sauyawa,irin kallon da yaga baffan yana yi masa shi ne yasa shi sake sauke kai k’asa,sun d’auki ak’alla mintuna biyar shiru babu wanda yayi magana,kafin baffa ya nisa tare da fara magana
“Tabbas.! Mai babban suna wannan *WANI AL’AMARI* ne mai girma kazo min da shi,,sai dai ni ban isa na yanke hukunci ba,har sai mun jira munga abunda Allah zai yi,,amma wani hanzari ba gudu ba,kaga mu nan a da,bisa al’adar gidan nan da muka gina rayuwarmu akanta shi ne,mun kasance muna aure ne na zumunci,ta yadda mukan had’a y’ar wannan da d’an wannan,duka a cikin gida muke aurar da yaranmu ba don komai ba sai dan gudun fad’awa cikin matsala,sannan kuma mun sani cewa yin hakan zai sake taimaka mana wajen rik’e junanmu da mutunci kuma bisa amana,babu yadda za’ayi ace mu cutar da junanmu,sai dai kuma a kwanakin da suka gabata,idan har baka manta ba ni da kaina na soke irin wannan maganar auren na zumunci da muka kasance muna k’ullawa tun shekarun da suka gabata,saboda wani dalili da kuma matsalolin da suka fara shigo mana cikin danginmu,,duk da cewa ni da kake gani nine babba sannan duk hukuncin dana zartar da shi ake amfani a gidan nan,hakan ba wai yana nufin zan yanke hukunci akan maganarka da Sabina kai tsaye bane…A tsarin addini da kuma al’ada da muke tafe akansa tun iyaye da kakanni shi ne,matuk’ar yaro yaga y’ar mu,ko d’anmu yaga wata yarinyar ya nuna yana ra’ayinta da gaske bawai da wasa ba,to zai sanar da magabatansa ko kuma mu a sanar damu,daga nan sai mu da su mu zauna mu tsayar da magana ta gaskiya..”
Shiru baffa ya d’an yi yana jan numfashi,ko kafin yaci gaba Hammad yayi magana
“Shi kenan baffa,in sha Allah kamar yadda ka fad’a,nima zanyi k’ok’arin na zauna mahaifana akan maganar,kuma in sha Allah zaka same ni mai bin duk wani sharad’i da dokar da zaka sakamin akanta,matuk’ar dai ace bai sab’awa addini ba..”
Murmushi baffa yayi masa duk da kan Hammad d’in yana k’asa
“Hakan yana da kyau sosai MUHAMMADU,,halayenka da tarbiyyar ka suna k’ara bani sha’awa,,,to amma kai d’in kana ganin idan har akace dan ka nuna kana son yarinyar data fito daga zuri’ah irin tamu,ina nufin kasantuwarmu talakawa kaga mu daku ba d’aya bane,shin yaya matsayin wannan maganar zai kasance a gurin mahaifanka,,shin kana ganin zasu d’auki batun har su amince maka..!? Ya kamata fa kayi wannan tunanin..”+
“In sha Allah baffa bazasu k’i ba,talaka da mai kud’i dukafa bayin Allah ne,haka kuma a lokaci guda idan yaso sai ya canja AL’AMARIN,,Talakawa ya koma mai wadata,shi kuma wanda yake ganin shi mawadaci ne a wayi gari ya koma talakawa,,ni ina ganin wannan ba abun damuwa bane baffa,Allah shi ne farkon abunda ya kamata ace bawa yasa a gabansa,dan haka ina ganin babu wata matsala da za’a samu ta wannan fuskar..”
Jinjina kai baffa yayi cike da gamsuwa kafin ya ce
“Toh..! Shi kenan ai,tunda har kana ganin baza’a samu matsala ba,zan baka dama daga nan har zuwa wasu kwanaki,ka samu kuyi magana da maganbatan naka,in yaso duk yadda kuka yi da su sai ka sanar dani ko..!?”
“In sha Allah,, baffa dana koma zanyi k’ok’arin sanar da su..”
“Masha Allahu..! Allah ya bamu sa’a,sannan yasa muji alkhairi..”
Da “ameen” ya amsa yana sake sunkuyar da kai,baffa kam murmushi yake ta saki dan yadda maganar ta faranta masa rai ji yake kamar duka duniya babu wanda ya kai shi shiga tsantsar farin ciki da batun,,shi kansa Hammad idan da ace za’a tona zuciyarsa a lokacin ta wani gefen fari k’al take dan yadda baffa ya nuna aminceaarsa akan maganar,sai dai kuma ta wani gefen yana jin zuciyar sa cike da tsoro,shin ta yaya ne zai tunkari Daddy’nsa da wannan batun,tun ba yanzun ba ya riga yasan halinsa nd waye shi d’in,idan har dan ace ta Mamma ne baya tunanin zai samu matsala da ita,to amma Daddy fa..? Ta wace hanya ne zai bi yayi masa bayani.? Da wace fuska ne ya kamata yabi ya sanar da shi..?
“Shin ko dai zan bi ta wajen Mamma ne kawai..?? Na san bazan samun matsala da ita ba.. Anya ba itan zan fad’awa ba kawai na huta,idan yaso sai mu bar maganar a tsakanin mu ba sai Daddy ya sani ba,daga nan har zuwa lokacin da komai zai daidaita sai muyi k’ok’arin sanar masa,i know zuwa lokacin babu abunda zai faru,nd duk wani matsalan danake tunanin za’a samu ma zuwa time d’in nayi solving nasa.!”
Shi kad’ai yake magana a zuciyarsa buh sai dai duk ya rasa yadda zaiyi,,maganar baffa ce ta sashi d’agowa cikin hankalin sa
“Amma! Mai babban suna ina tunanin wani abu kuma..”
Maganar baffa tazo masa a wani irin yanayi da tasa shi jin fargabar abunda baffan zai sake fad’a a gaba,cikin rikicewa ya bud’e baki yana fad’in
“Baffa..! Shin da akwai matsala ne..!?”
“Ko kad’an babu wata matsala,,kawai dai ina son sanar da kai wata magana ne.”
Sake gyara zama yayi yana tankwashe k’afafu yayin da k’irjinsa ke tsananta harbawa
“To baffa..Allah yasa alkhairi ne..!”
D’an murmushi yayi masa sannan ya ce
“K’warai kuwa alkhairi ne da yardar Allah,,kamar yadda ka sani yanzun zamani ya sauya,,kamar yadda aka samu ci gaba da kuma sauye²,wad’anda sune suka sa mu ta dole muka watsar da al’adunmu na hausa/Fulani,,,a da za kaga anyi aure ba tare da ma’aurata sun san juna ba,wasu ma duka ko da sun tab’a had’uwa gabanin ayi auren zaka tarar had’uwarsu d’in bata kai ta azo agani ba,,to shi ne nake ganin kamar ya dace ace ka samu K’ANWAR nan taka ku fara fahimtar juna da ita,tunda naga yanzun haka ake yi ko..!? Idan yaso in Allah ya ara mana rai da lafiya kuma kun daidaita falillahil hamd,muma zamu so hakan,bawai ace kai tsaye mun yanke hukunci ba ko..!?”
Gawurtattun ajiyar zuciya ya jera saukewa,cikin tsananin jin dad’in maganganun na baffa ya saki murmushi mai k’ayatarwa
“Haka ne baffa,,in sha Allah za’ayi duk yadda kace,,na gode sosai Allah ya k’ara girma,yaja da nisan kwana..Ubangiji ya jik’an magabata..”
“Ameen ya rabb,,Allah yasa mu kuma mu dace..Idan namu lokacin ya zo mu cika da imani..”
Shima da “ameen” d’in ya amsa masa,,daga nan kuma hiran nasu sai ya koma jefi² nd duka ya ta’allak’a akan harkokin noma da kiwon da suka kasance suna yi,,har yamma Hammad yana cikin k’auyen,inda duka yinin ranar yayi shi a cikin gidan su Sabinar,ba shi ya tashi tafiya ba sai can bayan la’asar sosai.
Lokacin daya tashi tafiya baffa da kansa yasa a kira masa Sabinar suyi sallama,ko data k’araso baffa fita yayi ya basu guri,,tun data shigo kanta yake a k’asa sam tak’i yarda ta had’a ido dashi,yadda ta sunkuyar da kai sam babu wanda zaiyi tunanin tana magana,shima kansa Hammad d’in yadda yaga ta zauna tayi shiru sai ta sashi yin murmushi
“Me yake damunki ne my lady.!?”
Ya watso mata tambayar,a hankali ta d’an d’ago kanta dake sunkuye ta kalle shi,shima d’in itan yake kallo nd still fuskarsa da fara’a ba kamar wasu lokutan ba da har take jin shayin ta d’aga kai ta kalleshi,one eyebrow ya d’age mata alamun tambaya,cikin sanyi ta d’an kad’a masa kai kafin tace
“Babu komai..!”
“Sure..!?”
Ya sake tambayar ta,kai ta sake girgizawa sannan tace
“Ehh.!”
D’an murmushi yayi cikin salon sa na zolaya kafin yace
“Kan ya daina miki ciwon..!?”
Saurin sake d’agowa tayi ta kalleshi buh sai bata ce komai ba,illa wani irin salivary data had’iye,sake sakin murmushi yayi amma wannan karon mai sauti
“My lady..Kada fa ki nuna zaki min wayo..Dan ni nan da kike gani babu abunda zaki b’oye min a kaf halayenki..Zuwa wannan lokacin idan har akwai wani abu da ban fahimta ba a game da d’abi’unki,,Ina tunanin to sai dai..!”
Shiru ya sake yi yana murmusawa,sake sunkuyar da kai tayi,shi kuwa yana kallonta nd yana sake murmusawa
“Ohh.! Wato yanzun ma ni kad’ai zaki bari nayi ta magana..!? Am not a radio fa,,kin sani sai surutu nake,al’halin ban wani saba da yawan magana ba..”
“Uhhuumm..!”
Tace ba tare data sake cewa komai ba
“Speak ur mind my lady..!”
Ba tare data d’ago ba can k’asa tace
“Ni babu abunda zance dama..”
“Uhumm! Shi kenan,tunda baza kice ba,,saboda ni..Zan tafi,idan kina da wani sak’o ina sauraro ki sanar dani..!”
Shiru ta d’an yi ba tare data ce komai ba,haka nan yanayinta a hankali sai ya fara sauyawa,duka yana monitoring nata da duk wani motsinta,ba tare da tayi aune ba sai ganinsa tayi a daf da ita,cikin wani irin muryan da bata tab’a jin yayi magana da shi ba yace
“My lady..! A haka ne za muyi sallamar..?”
Tun daga idanunta har zuwa kan toes d’inta babu inda baya motsawa a jikinta,yanayinsa a yau da al’amuran sa ita kam gaba d’aya sun fara bata tsoro,gani take kamar ba shi ne wannan miskilin mutumin data sani ba wanda ko magana ma sai ya zama dole yake yinta,,d’an ja baya tayi kad’an ta bar kusa da shi kafin ta shiga sakin ajiyar zuciya akai²
“K..ka.gaida gida..Allah ya tsare hanya..!”
Iya abunda ta iya furtawa kenan shima cikin sark’ewar harshe,a hankali ya sake yin murmushi kafin ya matsa baya shima yana hard’e hannayensa a k’irjinsa ya zuba mata idanunsa
“Na gode my lady..Buh ban karb’i wannan sallamar taki ba..”
Idanunta ta d’an runtse a hankali cike da dauriya sannan tace
“Sai wanne ne zaka amsa..!?”
D’an jimm yayi yana kallonta yana murmusawa kafin ya ce
“Umm! Har sai kin..!”
Jin bai k’arasa fad’a ba yasa ta d’an d’agowa ta kalle shi kamar za tace wani abu kuma sai yaga ta sake sauke kanta k’asa ba tare da tayi maganar ba
“My lady..! Ba zaki tambayi me zan fad’a ba..!?”
Shiru tayi masa na wani lokaci har sai da yayi zatonma ba zata yi magana ba sannan yaji tace
“Mene ne zan tambaya..!?”
“Abunda zan fad’a na fasa..”
Murmushi ta d’anyi kana tana d’an tab’e baki
“Uhmm! Ai ka fasa fad’a ne shi yasa kayi shiru..”
Sake murmusawa yayi cikin sigar zolaya kuma ya furta
“Ummm! A’a! Kawai dai dan bakya ra’ayin jin abunda zan fad’a ne yasa kema baki damu ba ko da nayi shirun..”
Idonta ta d’an lumshe sannan ta sake bud’ewa,deeply kuwa fad’i take
“Dan dai baka san yadda nake son jin bane shi yasa kaima d’in kayi shirun,,da ace ina da k’arfin guiwan da zan iya tambaya,babu abunda zai sa na gaza tambayarka..! Ya Allah..!”
“Shi kenan my Lady,,ba dan yamma yamin ba,nd ina tunanin yadda hanya zai kasance min ni kad’ai,,da nayi ta zama a nan har sai kin min magana..Buh ban so ace zan tafi na barki ba..”
“Ya tafi ya barni..!? Me yasa ne yake min wad’annan maganganun masu kama da surkulle..!? Na kasa fahimtar inda kalamasa suke tafiya ni kam..!”
Can k’asan zuciyarta take ta maganar ita d’aya.Hammad kam ranar ba shi ya tafi ba sai daya gama zolayarta sannan suka yi sallama ya fito,wad’anda ya tarar a tsakar gidan yayiwa sallama sannan suka yi sallama da su baffa daya iske a k’ofar gida,kana suka d’auki hanyan rakashi kamar yadda suka saba a lokacin biyar har ta gota.
Sai around 6:30pm ya shigo gidan,yanayin da yake ciki na farin ciki a lokacin duk da wani b’angaren nasa yana jin fargaba duk wanda ya sanshi babu yadda za’ayi ya kasa gane farin cikin dake tare da shi. Yana tafe yana murza carkeys dake hannunsa,lokaci zuwa lokaci kuma ya saki murmushi idan ya tuno yadda suka yi da ita,shigowarsa cikin parlor’n tayi dai² da tsaiwar Mamma a bakin staircase d’in daga sama,kallonsa ta ci gaba dayi har ya gama shigowa yana niyyar zama a parlor’n ya tsinkayo muryanta a sama tana fad’in
“HAMMAD..! Daga ina kake da wannan lokacin.!?”
Ko kafin ya d’aga kansa sai da yayi murmushi sannan ya d’an d’ago yabi inda ya jiyo muryanta da kallo,yanayin fuskarta da yayi arba da shi nan ya sashi saurin mik’ewa daga zaman da yayi ya nufi hanyan staircase d’in,still tana a tsayen tana kallonsa har ya gama haurawa saman ya isketa,daf da ita ya tsaya kafin ya rik’o hannayenta duka a cikin nasa
“Mamma..! Na fita ne tun safe..Nd..!”
Hannun ta zare daga nasa kafin tayi saurin d’aga masa wanda shi ne sanadiyyar yin shirun nasa daga fad’ar abunda yayi niyya
“Amsan tambayar da nayi maka kawai nake buk’ata.. Daga ina kake..!?”
Kallon ta ya d’anyi kafin ya rausayar da kai yana fad’in
“Mamma naje skul ne..Nd uzurin gaggawa ya taso min ne,shi yasa na fita ban sanar miki ba..”
“Ban yarda ba Hammad..”
Saurin sake kallonta yayi,yadda ta had’e rai da gani kasan da gaske take bata yardan ba har zuciyarta,marairaicewa yayi cikin sigar son tabbatar da magannar sa sannan yace
“Mamma i swear, ban je ko ina bafa..”
“No! Hammad..Kasan bazan yarda ba..Saboda haka ka fad’a min gaskiyar inda kaje..Kada ka manta fa tun nice nan na haifeka,nd tun safe baka gidan nan,na san kasan da haka ko..!?”
Kai ya shiga gyad’awa
“Ehh! Mamma buh..!”
“Shhhh.! Ya isa haka,,muje na shirya maka abinci kaci..Na san tun safe zai yi wahala ace ka sama cikinka wani abu ko..!?”
Sake gyad’a mata kai yayi cije da sanyin jiki,nd a b’oye kuma yana sakin ajiyar zuciya,ita da kanta taja hannunsa suka bar wajen sai data tabbatar ta raka shi har bakin bedroom d’insa sannan ta tsaya tana kallonsa tana shafa fuskarsa
“Maza kaje kayi wanka ka shirya kaji..zan had’a maka abincin kafin ka fito..”
A hankali ya rausayar da kai yana had’iye yahu,sakin hannunsa tayi sannan ta juya tana murmushi,saurin rik’o hannunta yayi nan ta tsaya kafin ta juyo ta kalle shi,kamar bazai yi magana ba,kuma sai cewa yayi
“Mamma..! Idan na fito akwai maganar da nake so muyi..Please.!”
Ajiyar zuciya tayi sannan ta gyad’a masa kai itanma
“Ok..! Je ka fito d’in,, ina nan ina jiranka kaji Yarona..”
A hankali ya kad’a kai sannan ya juya ya shige ciki,sai data tabbatar ya wuce ta bar wajen,shi kansa Hammad sai lokacin daya shiga ciki sannan ya fara tunanin anya bai yima kansa gaggawa ba kuwa da har yake k’ok’arin sanar da Mamma tun yanzun…? Ko kuwa dai zai bari ne har zuwa gaba sannan ya shaida mata,to amma idan har bai fad’a mata ba lamarin ya kwab’e masa yaya zaiyi a nan gaba…?
Wad’annan tambayoyin sune suka fara zuwa kwakwalwarsa a lokaci guda…..
Rasa yadda zaiyi da tunanin daya addabar shi yasa shi runtse idanunsa a hankali sannan ya d’ora hannunsa d’aya a saman goshinsa yana matsawa kad’an² while d’ayan ya hannun ya d’ora shi saman waist d’insa yayin da zuciyarsa take masa wani irin suka,k’asa² yake furta duk addu’ar daya zo masa a baki,ya d’auki tsayin lokaci kafin ya jinkirta,zuwa wani lokaci kuma a fili ya furta
“Ya rabb.! Help me..Mene ne zanyi na fita a matsala ne..?? Should i inform Mamma or..!?”
Sai kuma ya d’anyi shiru yana tunanin hanyar daya kamata ya bi wajen sanar da itan idan har hakan ya kama yayi,ya d’auki lokaci mai tsayi banda zarya da zagaye bedroom d’in babu abunda yake wanda shi kansa bai san iya adadin lokacin daya shafe a cikin wannan yanayin ba.+
A b’angaren Mammansa kuwa tun bayan data bar wajensa kai tsaye kitchen ta nufa,ita da kanta ba tare data sa wani cikin housemaid d’insu aiki ba,ta shirya masa abinci mai sauk’i nd wanda tasan ba zai d’auki lokaci ba,ko data gama sannan ne ta sa housemaid d’in su shirya mata dining itan kuma ta koma danta kira shi tunda taga har lokacin shiru babu labarin fitowarsa,,har ta hau saman bata ga alamun ya fito ba,dan haka kai tsaye ta nufi bedroom d’in nasa,a hankali ta kai hannunta saman handle d’in k’ofan ta murd’a,yadfa taji k’ofar a kulle nd alamu sun nuna daga ciki ne aka kulle,sai ta d’anyi jimm a gurin,AL’AMARIN kuma daya sata fara tunanin anya lafiya yake..? Hankalinta a d’an tashe ta shiga knocking k’ofar had’e da fara kiran sunansa,,yana tsaye har lokacin a tsakiyar d’akin ba tare da yayi abunda ya kai shi ba,haka nan duka hankalinsa ma shi kam a lokacin duka baya tare da shi,knocking d’in da Mamma keyi tana kiransa shi ne yayi sanadiyyar dawowarsa cikin nutsuwarsa,da sauri sai ya juya ya nufi bathroom dan yasan ganinsa da ita idan har taga baiyi abunda tace masa ba,har ya kai bakin k’ofa yana niyyan shigewa kuma sai ya fasa had’e da dawowa baya,dai² bakin k’ofan ya tsaya jin yadda take kiransa daga ji kasan ba’a nutse ita kanta take ba
“Hammad..! Na ce ka bud’e min k’ofar nan..Hamma..!”
K’afin ta k’arasa fad’a ya bud’e k’ofan da sauri,kusan karo suka yi yayi saurin rik’o ta,d’agowa tayi cikin sauri ko da ganinsa a yadda ta barshi sai ta shiga k’ok’arin gyara tsaiwarta tana sake k’are masa kallo,kula yayi da irin kallon da take masa nan take yasha jinin jikinsa nd sai ya shiga sauke kai k’asa da yake yasan ba shi da gaskiya
“Hammad..! Me zan gani..!? Dama kana tsaye kana jina amma ka gagara amsamin..!? Ka kyauta kaji ko..Ya maka kyau..”
“Mah..Please..!”
“Ni ba saika bani hak’uri ba,amma abunda kayi ka sani ba ni kayiwa ba..Kanka kayiwa,,ace kana ji amma ka kasa amsamin,shi kenan ai,,,sai dai ni kam na rasa gane kanka duka a kwanakin nan..Me kake b’oyewa ne Hammad.!?”
A hankali ya d’ago da niyyar yin magana tayi saurin d’aga masa hannu nd tana jinjina kai cike da mamakinsa
“Yayi maka kyau Hammad,,ka kuma kyauta,,sai dai ka sani ko mene ne kake b’oyewa wata rana dole zan sani..Ko da ace baka so ba..Ka ci gaba da b’oyewa tunda babu wanda kake so ya sani..Allah ya taimaka..”
Tana gama fad’a dan yadda ranta yake a d’an b’ace nan ta juya zata fice,saurin rik’ota yayi yana girgiza mata kai alamun kada ta tafin,wani irin kallo ta bishi da shi kafin tayi magana
“Mene ne kuma..? Ina baka son kowa ya sani ne shi yasa ka gwammace zama cikin damuwa..!?”
“A’aahh! Mamma duka fa ba yadda kike tunani bane..”
“Idan ba haka bane,yaya ne Hammad..? Idan da ace kana so na sani,babu ta yadda za’ayi kana ji na bud’e murya nayi ta rafka maka kira,na san kana jina kuma kasan nice nake kiranka,amma me kayi..!?”
Sunkuyar da kai yayi k’asa yana runtse idanunsa
“Shiru..!? Kamar ni nayi kiranka Hammad,,amma kayi shiru ka kasa amsawa..Shi kenan Hammad,kaje ga abincin can idan ka gama yana jiranka..”
Sake juyawa tayi da niyyar tafiya ya sake rik’e hannunta gam a nasa,wannan karon a fusace ta juyo dan iya b’aci ranta ya b’aci da abunda yayi d’in
“Sake min hannu Hammad..Ka san ban fiya son wasa ba a wasu lokutan ko..!?”
Kasa sakin ta yayi kamar yadda ta buk’ata,zuwa lokacin ba idanunsa kad’ai suka birkice ba hatta da jijiyon kansa tuni duka sun gama bayyana afili,tsawar data yi masa ne ya sashi saurin sakin hannun nata yana binta da kallon mamaki,da b’ari a cikin muryansa yake fad’in
“Mah please..Ki saurare ni,wollahi i will explain..!”
“Kamin shiru Hammad,da kasan zaka min bayanin kana ji ina kiranka ka kasa amsawa..!?”
“Mah please,,kiyi hak’uri Zan miki bayanin komai..I promised u zan fad’a miki..!”
Yadda yake a birkice zuwa lokacin yasa ta yin jimm tana k’are masa kallo kafin ta ce
“Uhhuumm.! Ina sauraren ka,buh don’t try to lie on me..Ka san zan gane.”
“Mah..! I know u will understand,,buh ki d’an zauna tukun sai na miki bayanin..”
Da farko kamar baza ta zauna ba,kome kuma ta tuna sai ta nemi guri a saman resting chair tana basarwa,a kusa da ita ya zauna sannan ya sake rik’o hannunta,cikin nutsuwar dole ya fara mata bayanin abunda yake faruwa,kaf babu abunda bai sanar da ita ba,,yanayin kallon da take masa tun daya fara bata labarin ne yasa jikinsa yin sanyi,a hanaki kuma sai ya sunkuyar da kansa k’asa lokacin daya gama bata labarin,ci gaba tayi da kallonsa har na tsayin lokaci kafin tasa hannu ta d’ago chin d’insa ta zubawa fuskarsan nan mai cike damuwa idanunta
“Hammad..! Kalle ni nan..!”
Ta fad’a cikin wani irin muryan da bai tab’a jin tayi masa magana da shi na,kasa d’agowa yayi kamar yadda tace d’in,ajiyar zuciya ta sauke kafin taci magana,muryanta cikin rauni zuwa lokacin
“Hammad.! Na ce ka d’ago ka kalle ni..!”
A hankali ya d’aga idanunsa ya sauke su a fuskarta sai dai cike yake da tsoron abunda zai fito daga bakinta dan yadda yaga yanayin da take ciki,marairaicewa yayi kamar zai mata kuka yana girgiza kai ba tare data kula da abunda yake yi d’in ba ta furta
“Da gaske kake..Kana son ta..!?”
A bazata maganar ta tazo masa,buh duk da yana cikin tsaka mai wuya sai daya saki siririn murmushi,sake rik’o fuskarsa tayi a hannayenta biyu tana fad’in
“Kayi magana kai nake sauraro..Na ce da gaske kake..!?”
Kai ya girgiza kafin ya ce
“Ehh! Mamma buh..!”
Saurin sakin fuskarsa tayi kafin taja baya kad’an
“Shin ka san abunda kake shirin aikatawa Hammad..?? Kasan mene ne zai faru kuwa idan har ka bari Daddy’nku yaji wannan maganar..!?”
Girgiza mata kai yayi alamun ya sani
“Ka san irin halin da zan shiga a sakamakon wannan maganar da kazo da ita idan har ya sani.!?”
A hankali ya sake girgiza kai
“Me yasa Hammad..? Bayan ka sani amma kake k’ok’arin saka mu cikin damuwa..!?”
Da kyar ya iya raba lab’b’ansa kafin ya furta
“Mah..duka ba komai ya sani yin haka ba face soyayyar ta.. Ki taimaka kiyi ma Daddy bayani,,i know he’ll understand..”
Jinjina kai tayi tana had’iye yahu sannan ta mik’e tsaye
“Shi kenan Hammad,tunda haka ka zab’a mana daga ni har kai,,zanyi iya k’ok’arin da zan iya na fahimtar da shi..Amma ka zauna cikin shiri,kasan hukuncinsa akan magana irin wannan bana wasa bane,daga yanzun zuwa ko wane irin lokaci dole ne dukanmu na san zamu fuskanci hukunci..!”
Tana gama fad’in haka gudun kada ya sake cewa zai fad’a mata wani maganar tayi saurin ficewa a d’akin,ajiyar zuciya shi kansa ya shiga jerawa lokacin daya tabbatar ta bar d’akin kafin ya zame ya kwanta saboda sarawan da kansa yayi a dai² lokacin,ya jima a kwance cikin wannan halin kafin ya tashi a daddafe ya nufi bathroom da niyyar sawa jikinsa ruwa ko zai ji dama².
Mamma kuwa lokacin ko data fita a d’akin nasa cikin tsantsar tashin hankali ta isa nata bedroom d’in,tana shiga ta maida k’ofar ta kulle kanta,duka tunanin ta a lokacin da damuwarta shi ne ta yaya ne zata fuskanci Daddy da wannan maganar bayan ta san burinsa da sharad’insa akan duka yaransa..?? Shin yanzun ta ina ne zata nemo mafita,sannan da wane irin k’warin guiwa ne zata tunkari shi ta sanar da shi buk’atar Hammad d’in a gare shi na zuwa nema masa auren yarinyar da yace d’in..?? Tambayoyi ba iyaka suka dunga zuwa mata a zuciya da kwakwalwarta buh ta kasa tantance wanda ya kamatama tayi adopting.
Wannan ranar ko nace dare dukansa yazo mata ne a wani irin hargitse,nd ta dage kan lallai sai tayi finding hanyan daya kamata tabi wajen shaidawa Daddy irin matsalar da za’a iya samu idan har yak’i amincewa,,a wannan lokacin kuwa taimakon da Allah yayi mata a wannan ranar duka daddyn baya garin,da bata san inda zata sa kanta ba dan tsananin tashin hankali,,har gabannin ketowar alfijr bata iya runtsawa ba,sai dai kuma a lokacin ne wani irin bacci ya fara kawo mata farmaki,buh still tana sake enduring kanta akan ba zata kwanta ba har sai ta samo abunda take nema d’in,sai da taga alamun zata iya fad’uwa sannan ta hak’ura shima d’in a dalilin bacci ne da yake neman cin k’arfinta yasa sai ta yankewa kanta shawaran d’auro alwala,bayan data d’auro alwala ta shimfid’a pray mat sannan ta daidaita a tsayen ta kabbara sallah duk da yadda take jin jiri na d’iban ta kad’an²,nafila tayi sassauk’a mai gajerun surori kafin ta shiga jera addu’o’i akan ubangiji ya bata nasara,nd ya saka mata juriya akan duk abunda zai biyo baya,,ta d’auki tsayin lokaci tana addu’o’i kafin ta d’an jingina bayanta da jikin bed still tana ci gaba da lazimi a hakan.
A b’angaren Hammad shi kansa a wannan daren bai iya runtsawa ba saboda fargabar abunda zai biyo baya idan har Daddy ya san da zaman wannan maganar,haka nan sai bayan lokacin daya sanarma da Mamma abunda ke faruwan ya fara dana sanin rashin dakatar da ita daga fad’awa Daddy,haka nan sai a lokacin ya fahimci irin matsalar da yake k’ok’arin jefa ta,tabbas ya san kafin daddy ya same shi dole ne sai yayi mata fad’an ita ne ta bashi goyon bayan da har zai zo masa da irin wannan batun,dan haka shi kansa a daren kasa runtsawa yayi,,duk da yadda kansa ya addabe shi da ciwo amma ko kad’an bai samu daman runtsawa ba,wannan yasa ciwon sai ya sake had’e masa,yana kwancen banda juyi babu abunda yayi ta fama da shi a daren,,har aka fara kiraye²n sallah bai samu daman runtsawa ba.A hakan da yake lokavin da yaji kiran sallah ya lallab’a ya shiga bathroom ya d’auro alwala,sai dai ko daya fito d’in nan yaji bazai iya fita ba,nan a d’aki yayi sallah sannan ya koma ya sake kwanciya,zuwa lokacin kuwa ko idanunsa da kyar yake bud’e su,kafin safiya tuni har zazzafan zazzab’i ya saukar masa.
Lokacin da gari ya gama wayewa,har around 12:15pm yana kwance cikin mantle ba tare daya iya ta shi ba bare ya iya sanar ma da wani a gidan,,Fitowar Mamma a karo na sau babu adadi yasa ta kula da har lokacin bai fito ba,dan haka sai ta yanke shawaran duba shi ta gani ko lafiya yake,while deeply tana jin zuciyarta tana tsinkewa,a bakin k’ofar bedroom d’insa ta tsaya tayi shiru zuwa wani lokaci kafin ta fara knocking,shirun da taji ba’a amsa ba ba kuma ayi mata alamar da zata gane cewa da mutum a ciki ba yasa ta jin hankalinta yana k’ok’arin sake tashi,cikin sauri sai ta tura k’ofar nd tana sake kiran sunansa,d’akin gaba d’ayansa banda duhu babu komai a cikinsa,duk da gari ya gama wayewa a lokacin har azhr tana neman kawo jiki,amma idan har kana ciki babu yadda za’ayi ka gane hakan,fluorescence d’in d’akin ta shiga k’ok’arin activating nd tana sake ambaton sunansa,idanunta ne suka sauka kansa a kwance cikin mantle duk ya duk’unk’une daga gani ba sai ta tambaya ba tasan akwai damuwa,cikin sauri ta isa kusa da gadon tana maimaita fad’in kalmar
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..!”
Sai data zauna daga bakin gadon sannan takai hannunta ta d’an janye mantle d’in tana tab’a jikinsa
“Hammad..! What’s wrong with u..!?”
Ko idanunsa baya iya bud’ewa zuwa lokacin amma a hakan so yake ya bud’e su dan yayi mata magana,yayin da wasu irin hawayen azaba suke biyowa ta gefe,da sauri ya maida su ya runtse yana sakin numfashi da kyar
“Mah..!”
Abunda kad’ai ya iya fad’a kenan,yana sake runtse idanunsa,saurin d’ora hannunta tayi a saman kansa cike da tausayin halin da yake ciki take fad’in
“Lemme call ur Dad..!”
Tana k’ok’arin tashi shima d’in duk da halin da yake ciki sai k’ok’arin mik’ewar yake,da sauri ta dakatar da shi cikin rud’ewa tana fad’in
“A’a Hammad.. Koma ka kwanta ina zuwa yanzun.”
Cikin sauri bayan ta maida shi ta kwantar sannan ta fice,bedroom d’inta ta koma da niyyar d’auko wayarta sannan ta sake dawowa d’akin nasa,ba tare data iya zama ba ta shiga neman line Daddy’nsu,sai data masa kira ya kai uku kafin ta samu ya d’auka,bai ko tsaya jin me zata ce masa ba ya hau fad’in
“Haba Asiya,,mene ne yasa baza ki iya hakur’in jira kiga na kira ki back ba,,u know ina meeting,nd still kina sake kira na..Duk da nake shugaba kin san saina girmama doka kafin na k’asa dani su bi ko..!?”
Ajiyar zuciya ta saki ba tare data kula da fad’an da yayi mata ba,da kamar ta b’oye masa halin da ake ciki d’in sai taji yin hakan ma wani laifin ne zata k’arawa kanta a burinsa idan har ta bari sai daga baya zai sani
“Am really sorry Yallab’ai..! Buh idan ban yi haka ba,yaya kake so nayi..!? Ka tafi ka barmu yau kwana nawa kenan ko kiranmu kaji halin da muke cikima baka yi ba,,,forget ma,shin dan na kira na shaida maka cewa yaronmu ba shi da lafiya sai ya zama laifi..??”
Saurin katse ta yayi cikin d’aga murya da fad’in
“Yaronmu kika ce..?? Wanne a ciki..? Hammad ne ko Bassam..?”
Yadda yake a d’an rud’e yasa ta saisaita muryanta sannan ta furta
“A’a Hammad ne..!”
“Ya Allah..! Amma shi ne ba zaki sanar dani tun da wuri ba..?? Wannan wane irin sakaci ne haka kike yi Asiya..??”
Shiru tayi masa tana jin yadda yake naganar a d’an hasale,sai data bari ya gama fad’an sannan ta shiga bashi hak’uri nd ta shaida masa duka ciwon nasa ba’a d’auki lokaci ba,itanma shigowarta kenan ta iske shi bashi da lafiyan,ajiyar zuciya Daddy yayi sannan yace mata a yau d’in zai baro duk abunda yake yi ya taho duk dare,nd yanzun zai kira doctor’nsu ya sanar da shi halin da ake ciki,daga haka ko sallama bai jira sunyi ba ya katse wayen sannan ya kira likitan ya sanar da shi,,ko daya gama wayan hankalinsa kasa kwanciya yayi nan take yasa ayi canceling zaman nasu,,,kafin wani lokaci tuni har yasa masu tsaronsa sun d’auki hanyar airport da shi.
Within 45 minutes da zuwan likitan da duba jikin na Hammad zuwa yi masa allurai ya tafi,har motocin Daddy shida escorts d’insa sun fara jeruwa a harabar gidan,securities d’insa ne suka fara fitowa ko kafin su bud’e masa k’ofar motan tuni har ya bud’e ya fito,babban mutum ne da ak’alla shekarunsa baza su wuce (65) ba,sai dai yanayin daular da yake ciki da zaisa ayi masa kallon kamar bazai kai hakan ba,,cikin shiga ta alfarma ya ratso ta tsakiyar securities d’insa yayi gaba,a baya suka shiga binsa,ba tare da yabi ta kansu ba ya nufi hanyar da zata sada shi da ainihin cikin gidan nasa…..
*Na riga da na sanar da ku tun farko,yanzun ba sosai muka cika samun wuta ba,kamar yadda nasan da yawa kun san da matsalar da ake fama da ita kenan a gari,nd chajin engine kunsan bai cika value ba,dan haka daga ni har ku sai mun k’ara hak’uri..*😢
Shigowarsa cikin parlor’n ya iske shiru alamun babu kowa a ciki,dan haka kai tsaye ya ratse hanya ya nufi hanyan staircases d’in,cikin sauri yake tsallake su kamar zai tashi sama,daga nan bai tsaya ko ina ba sai a cikin bedroom d’in Hammad dan yadda yake jin hankalinsa har yanzun bai kwanta ba duk da Mamma ta fad’a masa ciwon na lokaci guda ne,da ita ya fara arba lokacin daya shiga cikin d’akin,sallama yayi wacce ita kanta a ciki² yayi ta sannan ya nufi gurin da Hammad ke kwance a saman gado,dai² kansa ya d’an tsaya kafin ya kaalli sashin da Mamma ke zaune jigum,a hankali ya sunkuya ya shafa suman kan Hammad dake wani irin wahalallen bacci sannan yayi pecking nasa a chicks,k’asa² ya furta
“Maybe u are down now,but with the love nd care that we are for u,u shall soon recover..Get well soon baby..”
(Ni dai sakin baki nayi a gurin dan yadda naji daddy ya kira saurayi kamar Hammad da baby,shin dan Allah ku fad’a min ni kuma me za’a kira ni da shi..?? face smile).
Dai² k’afafunsa ya koma ya zauna yana kallon yaron nasu zuciyansa da wani irin pain na ganin halin daya iske shi a cikin,har lokacin bai iya furta ko da kalma d’aya ba wa Mamma,ita kanta Mamma’n k’arfin hali ne kawai take izuwa lokacin dan tasan matuk’ar ace yasan dalilin ciwon na Hammad dole ne a kwashi drama a gidan,cikin dauriya tana kallon mijin nata ta furta
“Welcome home dear..!”
Kai ya jinjina mata ba tare daya amsa ba,zuwa can kuma yana kallon Hammad ya furta
“Me likita ya sanar dake game da ciwonsa..!?”
Sai da tayi jimm while itama tana kallon Hammad d’in ta furta
“He say’s yayi stressing kansa ne da yawa,shi yasa ciwon ya masa mugun kamu lokaci guda..”
D’an yamutse fuska yayi sannan ya maida hankalinsa duka kanta
“Kina nufin kice min akwai wani abu dake damunsa da bai iya sanar miki ba..!?”
D’auke kai Mamma tayi zuwa gefe ba tare data bashi amsan tambayar da yayi mata ba
“Asiya..! Dake nake magana,ina son ki sanar dani dalilin da yasa kika yi wannan sakacin..”+
“Ya sanar da ni komai,,buh..!”
“Buh what..!? Mene ne dalilin da yasa baza ki sanar da ni tun da wuri ba tunda kin san matsalar.!?”
D’an kallonsa tayi tana cije gefen lip kafin tace
“Haba Yallab’ai,, ta yaya ne har ka bani wannan damar,,kada fa ka manta tsayin kwanaki uku kenan baka kira mu kaji a halin da muke ciki ba,wannan fad’an naka ai na rashin gaskiya kake yi..!”
Kallonta yayi wani iri kafin yace
“Asiya..! Ban tambayeki wannan ba,ko nayi fad’a kan gaskiya ko nayi akan rashin ta,wannan duk ba damuwar ki bane,all i know shi ne na barki da yara nd kin san amanar su duka tana hannun ki,ni ban tambayeki komai ba yanzun daya wuce dalilin da yasa baki sanar dani ba..”
Yadda taga neck veins d’insa sun fara d’agawa alamun a ko wane irin lokaci zai iya d’aga murya yayi mata fad’a,tsam sai ta mik’e tayi waje ba tare data tanka ba,kallon ta yayi ya jinjina kai sannan ya mik’e a fusace yabi bayanta,tana shiga bedroom d’inta shima yana shigowa
“Asiya..!”
Ya kira sunanta da wani irin murya,a hankali ta waiwayo ta kalleshi kafin ta d’an juya a ranta tana fad’in
“Na san dama za’ayi haka.!”
Baya ta sake juya masa kafin ta amsa
“Me yake damunki ne.. Ina magana kina juya min baya..!?”
“Baka damu ka san damuwata ba,,to ni wace cema da za’a damu da damuwarta,aikina kawai na kula da kai,gidanka da yaranka..Ko ba shine aikin daka d’auko ni nayi ba.!?”
Tana maganar tana bud’e closet tamkar mai neman abu,rufe idanunsa yayi sannan ya k’araso inda take,ta bayanta ya tsaya a hankali ya rungume ta yana sakin ajiyar zuciya,,sanyin daya ratsata sakamakon yamayin rik’on da yayi mata yasa ta lumshe idanunta,cikin nutsuwa haka nan muryansa a sanyaye ya furta
“Haba masoyiya,, me yasa ne wasu lokutan kike son ki fad’a min irin wannan maganar,al’halin kin san nafi kowa jin b’acin rai da jinsu..!?”
Juyowa tayi k’ok’arin yi,tana kallon cikin idanunsa take fad’in
“Idan banyi haka ba,yaya kake so nayi,tunda ka nuna min fifiko akan yaranka..? I thought ko dai ace ba nice mahaifiyar data haifa maka suba,ya dace ace ko rik’on su nake kayi min irin hakan..?? Zuciyafa bata da k’ashi,yaya kake tsammani idan akace yaran nan ba nawa bane..? Kana ganin zasu samu irin wannan kulawar ne,ko kuwa ita matar taka zata juri ka dunga nuna mata fifiko akan yaranka..? Ba ni kad’ai ba koma wace mace ce idan har zaka nuna mata haka zata yi k’ok’arin zare hannunta ne akan yaranka matsawar ace yaran ba nata bane,,haka nan abunda kake min akansu gaskiya ya fara damuna,nima fa ina da nawa hak’k’in akan su,akan wane dalili ne zaka na gwadamin fin k’arfi akansu..? Ni fa na haife su..”
Yadda take fidda maganar dalla² fuskarta da alamun damuwa yasa dole Daddy ya sake sassauta murya,a hannakli ya kamata sannan suka nufi bakin bed d’inta,sai daya zaunar da ita sannan shima ya zauna,cikin sanyayyar murya ya fara mata magana
“Look Asiya..! Ya kamata ki fahimce ni,nd ki fahimci inda magana ta ya nufa,ko kad’an ba wai ina nuna miki na fiki iko da yaranmu bane,kiyiwa lamarin nan kyakykyawan fahimta,duk abunda kika ga ina yi ina yinsa ne ba don komai ba sai don ina son na gina rayuwarsu,,ta inda ko da ace bama raye ni dake zasu yi alfahari da cewar mun basu tarbiyyar daya dace mu basu a matsayin mu na wad’anda Allah ya dank’a amanar su a hannunmu,,idan naji kina irin wad’annan maganganun akan irin haka na kanji babu dad’i,sannan kina sawa na fara tuhumar kaina da ko na tauye hak’k’in ki da Allah ya d’ora shi bisa wuyana..”
Shiru tayi tana saurarensa har zuwa lokacin da yayi shiru,kafin ya ci gaba
“Shi kenan Asiya, amma ya kamata ki sanar dani matsalar da ake ciki,tunda Allah yasa na dawo yanzun..”
Numfasawa tayi kafin tayi magana
“Ehh toh.! Ni dai a iya sanina da kuma maganar da muka yi da shi a jiya,shi ne ya zomin da batun wata yarinya ne daya ganta kuma..!”
“What..!? Yarinya kika ce,,wannan wane irin maganar banza ne kike yi..!?”
Shiru tayi cikin ranta tana jin yadda maganarsa ya dake ta nd dama dole ne tasan za’a yi hakan
“Ya kamata ki sani har yanzun Hammad bai kai munzalin da zan masa aure ba,ni a gurina har yanzun yana matsayin k’aramin yaro ne,nd idan lokacinsa yayi da kaina ba sai wani ya sani ba ko shi ya fad’a min zan masa aure final..!”
“Haba Yallab’ai.. Wannan maganar taka ai ba mai yiwuwa bane,tunda har yanzun da kansa ya fito ya nuna auren yake so mai zai hana ayi masa,shin kasan matsalar da k’in amincewarka zai haifar..?? Kayi tunani kafin ka yanke hukunci..”
“Na ruga na yanke hukunci,,kin san magana d’aya nake bana maimautawa,to yanzun zai maimaita miki shi ne matuk’ar Hammad aure yake so a wannan lokacin bazan tab’a yi masa ba,sannan ina so ki jawa yaron ki kunne matuk’ar yace zai ja da magana ta akan wannan zancen,zan zare hannuna akansa,dan haka sai ya zab’a cikin biyu,,ni ko kuma maganar auren..”
Sosai rnta ya b’aci akan furucin da yayi buh ya zatayi idan har ta nuna zata bijere..?? Ita kanta ta san ba abune mai wahala ba ya zazzaga mata ruwan bala’i,to amma shin idan ta bar shi aka samu matsala fa..? A matsayinta na mahaifiya ita abun zai fiwa ciwo dan haka dole ta mik’e tsaye tayi yak’i da wannan ra’ayin nasa idan kuwa ba haka ba tofa lallai daga ita har Hammad suna cikin matsala,saurin dak’ile tunanin ta tayi sannan ta kalleshi
“Amma fa Yallab’ai kada ka manta wannan ra’ayi ne kawai irin naka,ba wai addini ne yace dole sai yaro ya had’a master’s ko sama da haka ya isa aure ba,akwai bambanci mai nisa tsakanin rayuwar mu ta da,da kuma yanzun,ya kamata kaima ka fahimta..”
“Asiya..!! Ki yimin shiru da wannan maganar,hunkuci ni ya dace na yanke shi ko..? To na gama magana,ba rashin lafiya ba idan mutuwa zaiyi matsawar akan wannan maganar ne,wollahi na gwammace na rasa shi,dad’in abun ai ba shi kad’ai na haifa ba,idan ya mutu ina da wasu yaran,Bassam da *BADRA* sun isheni rayuwa..”
Jinjina kai tayi cike da takaici,ba tare data sake tofa wani abu cikin zancen ba ta mik’e tana shirin fita
“Ina zaki je da kika tashi..!?”
Chak ta tsaya a bakin k’ofar kafin ta bashi amsa cikin jin haushi
“Mene ne amfanin da zamana zai yi maka ni kuma..? Ina cewa maganar ta k’are..!?”
Girgiza kai yayi dan yasan a fusace take da shi akan maganar, buh ya zaiyi dole ne ya nuna mata k’in amincewarsa tunda shi dai har ga Allah, bai shirya yiwa yaransa aure a k’ananun shekaru kamar na Hammad ba (amma fa a ganin daddy),,shi kad’ai yasan iya adadin wahalar daya sha a rayuwa,dan haka dole ne ya tsaya ya gina rayuwar yaransa,nd itanma yasan yadda zai ji da lamarinta,dan haka zai zuba mata ido yasan da sannu zata yi fushin ta sakko,,bayan fitar Mamma shima ficewa yayi daga d’akin.
A b’angaren Hammad kuwa tun kafin shigowar Daddy bedroom d’in ya farka,kasancewar bai bud’e idanunsa ba yasa koda yaji muryan Daddy’n sai bai nuna alamar ya farka d’inba,haka nan tsoron abunda zai biyo baya idan har suka yi four eyes da Daddy yasa shi k’in bud’e idanun nasa,dan haka lokacin da Daddy yake masa addu’ar samun sauk’i duk ya jishi kawai yayi kamo ne a kwancen,haka ma maganar da suka fara da Mamma,sai dai tun daga lokacin da suka fita a d’akin nan ya bud’e idanunsa a hankali yana dafe kansa da yayi masa nauyi kafin ya d’an mik’e a hankali ya jingina bayansa jikin pillow,maganaganun Daddy ne suka fara masa yawo akai,tabbas yasan dole ne a samu matsala,kamar yadda yasan ko wane ne mahaifin nasa,haka ma ra’ayinsa akan su,,ya jima zaune yana tunani daban² akan matsalar kafin ya tashi a daddafe ya nufi bathroom.
A can b’angaren Mamma kuwa ko data fito daga bedroom d’in k’asa ta sauka tayi zamanta a parlor,tunanin abun duniya duk ya sata gaba,a lokacin ji take inama ace tana da hali,tabbas da sai dai ayi duk wacce za’ayi akan maganar,,ta jima zaune a parlor’n shiru kafin ta mik’e ta nufi kitchen da niyyar shirya ma mai gidan nata abinci.
A b’angaren Daddy shima tun daya fita a d’akin bai ko sake bi takan Mamma ba,haka halin da Hammad d’in yake ciki bai sake dubawa ba,a haka har aka d’ebi tsawon kwanaki biyu ba tare da wata maganar kirki ta gifta tsakaninsu da shi ba,duk da yana garin kuma a cikin gidan amma sam idan har yana zaune baza kaji yayi musu magana ba,idan har ka ganshi yana walwala ko hira to k’addara tsakanin Bassam ne ko *BADRA* a tare da shi,bayan su kuwa indai ya kama Mamma ko Hammad nan zaka ga yana shan k’amshi.
A cikin wannan yanayin ne jikin Hammad d’in yayi sauk’i,yayin da kwanakin suka yi dai² da lokacin da suke shirin komawa skul.Tun daren ranar Saturday bayan sun gama tsayar da maganar komawarsu skul shi da sultan,a lokacin bayan ya dawo gida misalin k’arfe 8:pm ya yanke shawaran sanarma Daddy.Kamar ko wane lokaci yana shigowa ya iske su duka a parlor suna sauraren labarai a BBC NEWS,gefen Mamma ya nufa sannan ya nemawa kansa guri ya zauna,cikin ladabi ya gaida Daddy sannan Mamma,duk da a ciki² Daddy’n ya amsa bai wani damu ba dan yasan dama za’a rina,,duk da dai har yanzun Daddy’n bai tada masa maganar ba,buh yasani tun a kwanakin da aka yita dole ne duk ranar da suka had’u ya zazzaga masa fad’an da yayi masa tanadi,Mamma kam cike da so da kulawa ta amsa masa,sannan Badra dake jikin Daddy ta kallo shi tana fad’in
“Yah Hammad sannu da dawowa..”
D’an murmushi yayi mata yana jinjina mata kai alamun amsawa,murmushin ta mayar masa sannan ta sake maida hankalin ta akan labaran da suke sauraro,nan Bassam ma ya masa barka da shigowa,bayan ya amsa masa duka parlor’n ya sake d’aukar shiru har zuwa lokacin da aka k’are labaran.
Daddy ya kalla yana son yi masa magana buh duka yaga ya maida hankalinsa akan Badra dake masa zancen skul itama,,Duk abunda yake yi idanun Mamma na kansa,dan haka cikin kulawa ta dafa hannunsa dake daf da ita tayi masa alama ta hanyar lumshe idanunta akan ya kwantar da hankalinsa,d’an murmushin k’arfin hali yayi mata sannan k’asa² kamar mai tsoron faruwar wani abu ya furta
“Daddy..! Dama gurinka na zo..!”
Da fari Daddy shiru yayi kamar bai ji shi ba,har sai da Mamma ta d’ago ta kalle shi kafin ta maimaita masa
“Yallab’ai..! Hammad yana magana,nd naji kayi shiru baka ce komai ba..”
D’agowa yayi da kansa cikin had’e rai kafin ya furta
“Sarai naji shi,,na kuma ji abunda ya fad’a.!”
Yanayin amsan daya bayar yasa dukansu da suke zaune kowa hankalinsa ya koma jikinsa,ita kanta Mamma’n yanayin da yayi maganar nan take yasa taja bakinta bata sake ko da tari ba,,Jikin Hammad a sanyaye ya sunkuyar da kai kafin ya furta
“Daddy..! Dama ina son sanar da kai ne cikin satin nan zamu yi resuming skul..”
Tun kafin ya rufe baki tuni har Daddy ya furta
“Allah ya tsare hanya..!”
Sannan ya sake jan baki yayi shiru,,sake sunkuyar da kai yayi cikin sanyin jiki duk da ya fahimci yanayin da Daddy’n yake ciki buh bai fasa magana ba
“Buh..Daddy..!”
“Buh daddy me..!? Me zanyi maka Hammad..??”
Kansa a k’asa ya runtse ido,cikin zuciyarsa banda addu’o’i babu abunda yake ja akan Allah ya sanyaya zuciyar mahaifin nasa
“Tambayarka nake, me zan maka..??”
Sai daya sauke dogon ajiyar zuciya kafin ya furta
“Daddy batun fare ne (kud’in tafiya) nake son yi maka..”
Sai da Daddy yayi murmushi kafin ya kalle shi yana fad’in
“Wane kud’in zan baka..!? Ni ne zan d’auki kud’ina na baka,al’halin ban isa na saka doka abiba..? To bari kaji,kasan Allah k’wandala idan har daga aljihuna zai fito daga yau matuk’ar baza ayimin biyayya ba,babu wanda zan sake amfanawa komai in dai da dukiya tane..Dan haka kana da zab’i biyu,ko dai kayi abunda nake so,nima nayi maka abunda ya dace a matsayin mahaifi,ko kuma kayi wanda ranka ya zab’a maka amma ka sani zan zare hannuna da duk wani tallafin da nake baka..Saboda haka zab’i ya rage naka..”
Shiru duka parlor’n suka yi gaba d’aya maganar Daddy babu wanda bata sa yaji damuwa ba
“Amma Daddy nifa banyi maganar aure ba,yanzun kawai dai..!”
“Hammad..! Kenan rainamin wayo za kayi ne..?? shi kenan mu bar wannan magana,,ina fatan kaji duk abunda na fad’a maka,dan haka daga nan zuwa lokacin da zaka zo ka same ni akan ka janye maganarka,ka shirya ganin abunda baka yi tsammani ba..”
Tun daga haka Daddy bai sake masa magana ba,,ga Hammad kuwa magana yake son sake yi amma sao Mamma tayi saurin dafa hannunsa tana girgiza masa kai alamun yayi shiru,sai daya kalleta kafin yaja bakinsa yayi shirun kamar yadda ta umarce shi,,bayan kammar mintuna goma,yayin da parlor’n ya koma shiru tamkar gidan makoki,dan haka nan Hammad yayi musu sallama sannan ya nufi sama,yayin da yake jin zuciyansa tana masa babu dad’i,akan yadda Daddy’n ya nuna maganar ma baya da buk’atar jinta,,yana barin gurin Mamma ma tabi bayansa,kai tsaye ta nufi bedroom d’insa nan kuwa ta tarar da shi zaune yayi shiru fuskarsa bayyane da damuwa mai girma,a kusa da shi ta zauna tana shafa kansa,sam bai san ta shigo ba sai data tab’a shi sannan ya farga da zuwanta,ajiyar zuciya ya sauke kafin ya zame ya kwanta a jikinta yana ci gaba da sakin ajiyar zuciyan,a hankali ta fara shafa kansa cikin sigar rarrashi da kulawa har na tsayin wani lokaci ba tare da wani a cikinsu yace komai ba…..