SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 1 BY FATYMA SARDAUNA

SHU’UMIN NAMIJI CHAPTER 1 BY FATYMA SARDAUNA

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani irin gudu black colour car ƙirar RANGE ROVER ke falfalawa akan babban titin dake cikin garin *ABUJA* …+

Gaban wani irin makeken gate motar ta tsaya, minti kaɗan kuma ta soma wani irin ƙara kamar zata cire kunnen maisaurare, cikin mintuna ƙalilan maigadi da jikinsa ke rawa ya wangale makeken gate ɗin, da gudun bala’i ya cinna hancin motar tasa ciki, daga yanayin yanda yayi parking kaɗai ya’isa nusar dakai cewa wanda ke cikin motar, cike yake da iskanci haɗi da zallan taɓara… Duk yanda naƙosa wanda ke cikin motar yabayyana nasamu damar ɗauko muku hoton fuska da surarsa amma abun yaci tura, domin dai shegen ƙin fitowa yayi bare nasamu ganinsa…….1

15 minutes ya kwashe cas batare daya sanyo kansa waje ba, a hankali yasako ƙafarsa waje wacce ke ɗauke da tsadadden black canvas mai ɗauke da fararen igiyoyi a samanta, a hankali yagama fito da duka jikinsa daga cikin motar, Masha Allah !! shine abun dana furta lokacin dana gama sauke idanuna akan shi, kyakkyawa ne ajin farko, haɗaɗɗen matashi maiji da kyau haɗi da zallan kuɗi uwa uba hutu, fari ne tas banda sajensa dakuma tulin gashin kansa babu abun dayake baƙi ajikinsa,, saurayi ne mai cikar zati da kuma haiba, yana da cikar sura dakuma ƙaƙƙarfan jiki, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa mutum ne ma’abocin yin gym, kyakkyawar fuskarsa tana ɗauke da yalwatattun idanu masu ɗauke da brown eye balls acikin su, sannan kuma yana da dogon hanci gwanin burgewa, bakinsa kuwa ɗan ƙarami ne, mai ɗauke da ƴan saffa saffan laɓɓa light pink colour, gashin girarsa dana idanunsa a yalwace suke tamkar dai wanda yayi ƙari, wani irin haɗaɗɗen sajene yayi mawa fuskarsa ƙawanya, wanda kuma haddashi yaƙara wa fuskar tasa kyau, jikinsa kuwa gaba ɗaya a murɗe yake, sanye yake da White t-shirt fara ƙal ƙal da’ita, yayinda wandon jikinsa yakasance black pencil jeans wanda ya kamasa sosai, sai ƙafarsa dake sanye da black canvas, kunnensa kuwa saƙale yake da earpiece, da’alam dai ƙiɗan sa yake sha,, yayi matuƙar kyau sosai, fuskarsa tana ɗauke da wani asirtaccen murmushi mai ƙayatarwa da burgeqewa,, hanunsa riƙe da car key ɗinsa yadoshi wani haɗaɗɗen gini, dake cikin harabar babban gidan nasu, da’alama dai nanne babban falon gidan…..

Wata haɗaɗɗiyar Farar Mata wacce bazata wuce 47 years ba ke zaune akan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon, tasha ado cikin wani irin danƙareren lace mai kyau da tsadar gaske, a zahiri idan kaganta zakai zaton batawuce 35 years ba, bakomai yasanya hakan ba fa ce tsananin hutu dakuma tsantsar jindaɗi da yabayyana ajikinta wanda hakan ya ɓoye asalin shekarunta,, iya gwala gwalan dake sanye a wuyanta haɗi da kunnenta, kaɗai ya’isa ya tabbatar maka dacewa itaɗin baƙaramar mai tarin dukiya bace…. Da wani irin fito yashigo cikin falon yanayi yana kaɗa makullin motarsa dake saƙale cikin yatsarsa manuniya,,

“Hello Mom “

saurayin yafaɗa cikin unigue voice ɗinsa…

Murmushi wacce aka ƙira da suna Mom tayi haɗe da cewa ” Your Well Come My Son”

Bai amsa mata ba saima zama yayi akan kujeran dake kusa da’ita yana mai yunƙurin cire takalman dake ƙafansa……

*((Wannan salon na dabanne My Fans kubiyoni domin jin wanene *SHU’UMIN NAMIJI !!* *wayeshi ? menene halinsa ? wace gwagwarmaya za’a tafka ? Saikun biyoni zakusan komai, takunce dai Mrs Sardauna, kada kumanta wannan labarin yasha banban da sauran…. ))*Inakaje ne wai *ΖAID* tunsafe rabon dana saka acikin idanuna ?” Mom tatambayeshi,

ɗan taɓe bakinsa yayi haɗe da cewa “aiki ne yaimin yawa a office, Labisat takawomin abinci.. ” yanakaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga cikin falon…. Murmushi kawai Mom tayi domin tafahimci cewa Shu’umanci’n Zaid ɗinne yatashi….1

Wani irin haɗaɗɗen gini naga Zaid yanufa, wanda yake can gefe da makeken lambun gidan, key yasanya haɗi da buɗe wata ƙofa, wani irin haɗaɗɗen falo mai masifar kyau Zaid yashiga wanda nake tunanin nanne mallakinsa, Masha Allah, falo ne daya amsa sunan sa falo, cike yake da abubuwan more rayuwa, kujerune irin leather sit ɗinnan farare ƙal ƙal zube a tsakiyar falon, yanda kujerun suke da haske kaikace ba’ataɓa hawansu ba,, tsakiyarsu kuwa wani haɗaɗɗen brown chanies carpet ne shumfuɗe mai taushin gaske, wasu irin ƙawatattun curtains brouwn colour ne suka taimaka wajen sake bayyana kyawun falon, duk da cewa bawani tarkacen kayan ƙyale ƙyale bane a falon, amma hakan bai hana falon yin kyauba, kallo ɗaya zakamawa cikin falon katabbatar cewa mamallakin wannan katafaren falo, baƙaramin ɗan gayu bane,, tundaga falo Zaid yasoma cire rigarsa yawurga kan kujera, yana tafiya yana cire wandon jikinsa ahaka ya isa cikin haɗaɗɗen bedroom ɗinsa, saida yacire duk wani kayan jikinsa, kafun ya shige cikin bathroom ɗinsa, koda na leƙa cikin bathroom ɗinnasa saida nayi tsananin mamaki, wai ace banɗaki aka kashemawa kuɗi haka tamkar wani fadan shugaban ƙasa ? hmmm ALLAH yakyauta….

Fitowa yayi ɗaure da towel a ƙugunsa, yayinda jikinsa ke jiƙe da ruwa, gaban makeken dressing mirror ɗinsa dake cike da mayukan shafa haɗi da turaruka kala kala yanufa, saida yatsane ruwan jikinsa, kafun yasoma murza tsadadden lotion ɗinsa akan haɗaɗɗiyar fatan jikinsa,, komai dai cikin tsanaki yakeyi harya kammala,, riga da wando yakuma sawa, saidai wannan karon Blue colour garesu, sun kuwa matuƙar amsar jikinsa,, Wayarsa ƙirar iphone 11 pro max ne tasoma ruri alamar shigowar ƙira,, harta katse Zaid bai ɗauka ba, wani ƙiranne kuma yasake shigowa,, ɗan ƙaramin tsuka yaja haɗi da nufar inda wayar take,, Zee shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi haɗi da kara wayar akan kunnensa batare da yace komaiba, “Hello Baby !! zee tafaɗa cikin wata irin shaiɗaniyar muryarta, ɗan ƙaramin murmushi yayi haɗe dacewa “Ya’akayi ne Zee ?” jin abun dayace yasanya Zee sake gyara zama haɗe da ƙara kashe murya tace ” Ina guest house ɗinka pls Baby kazo… ” Okay ” yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar yacusa cikin aljihun wandonsa,, knocking ƙofar ɗakinnasa akashiga yi, cikin muryan faɗa faɗa yace “Uban waye ke bugamin ƙofa kamar yasamu falon Ubansa ?” Labisat dake tsaye riƙe da tire ɗin abinci ahanunta, taturo baki gaba haɗe da cewa “Bro nice fa, abincinka nakawo ma ka” tsaki yakuma ja haɗe da cewa “Oya maidashi fita zanyi, innadawo nazo naci ” sumi sumi haka Labisat tajuya da abincin…..

Wata haɗaɗɗiyar Blue car yashiga haɗe da bata wuta yafice daga cikin gidan…..

Kaitsaye G.R.A yanufa inda acan guest house ɗinshi yake, yana zuwa maigadi ya wangale masa gate yacusa motar tasa ciki……

Jin tsayuwar motar shi yasanya Zee tashi da sauri tanufi hanyar fita daga falon, da sassarfa taje tafaɗa jikinsa haɗe da goga masa breast ɗinta, cikin kirsa tace ” sannu da zuwa babyna,, wannan munafukin murmushin nasa yayi mata haɗe da cewa “Ƴan Mata yakike ?” “lafiya ƙalau ” tabashi amsa daidai lokacin dasuka ƙaraso cikin katafaren falon,, janyeta yayi daga jikinsa haɗe da zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon ” Kawomin ruwa ” yafaɗa daidai lokacin daya cire rigar jikinsa,, cike da kwarkwasa Zee tamiƙe haɗe da ɗauko masa goran ruwan faro acikin friedge,, karɓa yayi yakafa bakin gorar abakinsa, tas yashanye ruwan haɗi da cilli da goran ruwan hanu yamiƙa ma Zee akan tataho gareshi, aikuwa dama jira take dan haka taɓalle duka aninayen gaban rigarta, take manya manyan breast ɗinta suka bayyana,, kansa yanutsa acikin breast ɗinta, bayan yayi mata masauƙi akan cinyarsa, cikin salo yacire mata gaba ɗaya rigar dake jikinta, hatta breziya bai barmata ba, bakinsa yaɗaura akan nipples ɗinta, yashiga yi musu wani irin kalan tsotso yayinda hanunsa, ke kan bayanta yana shafawa ahankali, tuni Zee taƙara rikitasa da salonta, ɗaukarta yayi caɗak suka nufi bedroom, kwantar da ita yayi flat akan gado, bayan yacire komai najikinta, yanda yake wasa da’ita kaɗai yasanya Zee ficewa acikin hayyacinta, domin Zaid ƙwararrene awajen iya sarrafa mace,, cikin mintuna ƙalilan Zaid da Zee suka faɗa duniyar ashsha duniyar Mazinata, (Ya Allah kakaremu daga aikata Zina Ameen)…….

*****

*ZARAH ! ZARAH !!* wata mata dake zaune kan tabarma keta kwaɗa gira,, “Na’am” wacce aka ƙira da suna Zarah ta amsa tana mai fitowa daga cikin wani ɗaki,, wata kyakkyawa matashiyar budurwa wacce bazata wuce 20 year ba tabayyana gaban wannan matar da ke aikin ƙwaɗa ƙira, cike da girmamawa tace Inna gani,, “Au dama tunɗazu kinajina iskancine yahanaki amsa ƙirannawa kome ?” matar tafaɗa tana mai gallamawa yarinyar dake duƙe a gabanta harara,, cikin tausasa murya Zarah tace “Kiyi haƙuri Inna wallahi, banjiki bane inacan ciki ina shirin makaranta, yau muna da lecture’n safe banso na makara ” “Uwar Lecture kuke dashi da ubansa, inkinga kinfita agidannan to wallahi kinga mamin aiki nane ” Inna tafaɗi haka tanamai tsakace haƙoranta da tsinken dake riƙe a hanunta,,,, cikin sigar lallami Zahra tace “Dan Allah Inna kiyi haƙuri idan nadawo sainayimiki duk abun dakike so ” “Zaki tashi kisoma aikin dana saki ko kuwa saina mangareki banza mai kama da aljanu ” Inna tafaɗa cikin faɗa , cikin sanyin jiki Zahra tatashi daga gaban Inna…. Wanke Wanke tafarayi sannan tayi sharan tsakar gida dana ɗaki,, saikuma hurawa Innar wuta, koda takammala aikin nata har 9 tayi, sam bataso ace yau tayi latti ba domin kuwa suna da lecture 8:00am, shikenan yauma lecture’n Sir Adam yasake wuceta kamar dai yanda yawuce ta wancan satin….. hijab ɗinta mai launin ruwan ƙasa tasanya, haɗe da saɓa jakarta a ƙafaɗanta, fitowa tayi tasamu Inna nazaune, bakin murhu tana ɗumamen tuwo, “Inna nizan wuce makaranta ” Zahra tafaɗa,, “To uwar ƴan boko saikin dawo, aikin kenan bacas ba as saidai zuwa makaranta, da Mijin aure kika fito dashi, kikayi aure aida nahuta da wannan wahalar taki ” Inna tafaɗa cike da bala’i.. Itadai Zahra batasake ce da’ita ƙalaba, tasakai tafice daga cikin gidan, tana fitowa ƙofar gida, zazzafan hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, dasauri tasanya hanu tashare hawayenta, kana tacigaba da tafiyarta………

nayi mistake nasa guest house ɗin Zaid na G.R.A, to ba G.R.A zansaba mistake ne, guest house ɗin Zaid na Maitama ne ba G.R.A )
+
Har takawo bakin titi bata samu abun hawa ba, gashi yau antashi da wani irin zafin rana, duk da cewa taran safe ne amma hakan baihana ranan bayyana zafin taba, tsaye tayi abakin titi tanamai ƙaremawa motoci da mashunan dake wucewa akan titin kallo, har izuwa yanzu mai adaidaita sahu ko ɗaya baizo yagil ma akan titin ba, takusan minti 12 tsaye a wajen kafun tasamu wani mai adaidai ta yaɗauke ta, kaitsaye babban jami’an da take karatu suka nufa…. Kamar koda yaushe abakin titi tace mai adaidaita ya sauƙeta domin dokace ba a shiga jami’an da motar haya, saidai idan motar kanka kokuma machine, nanma saidai in mallakin mutum ne… Ɗalibai ne iri da kala ke gudanar da harkokinsu acikin makaranta, wasu na hira da samari wasu kuwa na karatu, kamar dai yanda kukasan ƴan jami’a keyi,, kaitsaye tanufi gindin wata ƙatuwar bishiya wanda anan ƴan course ɗinsu ke tare, da’alama dai fitowarsu kenan daga lecture…. Da sallama ɗauke a bakinta taƙarasa garesu, bako wanne daga cikinsu bane suka amsa sallaman nata ba sai ƴan tsiraru, wasu ko da kallon banza suka rakata,, musamman ma ƴan matan dake wajen, koka ɗan hakan bai dameta ba domin dai hakan ba sabon abu bane a wajenta, musamman ma idan tayi la’akari cewa ita da su ɗin akwai banbanci, domin dukansu ƴaƴan manya ne itakuwa ƴar talaka ce futuk, shiyasa ma koda wasa bata yunƙurin haɗa kanta dasu,, zama tayi a gefen Aminiyarta Husna… ” Yauma saida kikasakeyin missing lecture, anya kuwa Zahrah wanan exam ɗin da zamuyi baza’a samu matsala ba ?” Husnah tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,,
ajiyar zuciya Zarah ta sauƙe, haɗe da cewa ” Bansan yazan yi ba Husnah wallahi dole ce take sawa nayi latti gashi unguwarmu a kwai ƙarancin abun hawa ” Zahrah ta ƙare maganar daidai lokacin da take ciro wani hand out a jakanta, “shikenan mukoma gefe saina koyar dake abun dana gane, domin ni wallahi lecture ɗin Mr Adam sam bana ganesa ” Husnah tafaɗa tana mai yunƙurin miƙewa tsaye…. Duk da cewa tazo latti amma tafahimci darasin da Husnah takoyar da’ita, tamkar ma tananan akayi…….
Basu suka kammala lectures ɗin dasuke da shiba harsai 5 pm, a gajiye take liƙis uwa uba ga yunwa dake ƙwaƙulan cikinta, rabonta da abinci tun 10 am nan ma Husnah ce tasaya musu snacks da drinks a Cafeteria, ɓatare da ta tsaya wani abu ba tashiga Adai dai ta sahu tayi yo gida…
*MAITAMA*
Zaid da Zee kuwa ayar su suka sheƙe sosai, domin Zee har kuka saida tayi mawa Zaid, wanda hakan kuma ba baƙon al’amari bane wajensa, domin sau da dama idan yayi sex da Zee tofa saitayi masa kuka, na azaba ko na daɗi wannan ne kuma baisani ba,, tsaye yake agaban dressing mirror dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan busar da gashinsa da yakeyi da hand dryer, Zee dake kwance akan makeken gadon ɗakin shame shame, kuwa ƙura masa idanu tayi, itakam Allah yasani, Zaid yana matuƙar burgeta, tanajin son gayen har cikin zuciyarta, saidai tasan cewa ko sama da ƙasa zasu haɗe, Zaid bazaitaɓa auren ta ba, saidai tana godemawa Allah ahakan ma daya bata daman raɓansa, domin raɓan Zaid ma sai mai sa’a, kuma sai macen da ta amsa sunanta mace ƴar gayu da aji….
Tsab yagama shiryawa haɗe dayi mawa kansa feshin turare mai daɗin ƙamshi,, Car key ɗinsa ya ɗauka haɗe da wayarsa, hanu yasa acikin aljihun wandonsa, kuɗi ya ciro bandir ɗin ƴan dubu dubu, ya cillamawa Zee akan cinyarta, batare da ya kalleta ba yace ” Kada ki tafi sai kin kimtsamin gado na ” yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin bakinsa ɗauke da fito,,, a maimakon Zee taji haushin yanda yamata, saima murmushin da tayi haɗe da lumshe munafukan idanunta, afili ta furta cewa “Allah kamallakamin Zaid amatsayin mijina”…..
Tundaga Zauren gidan nasu ta ke jiyo tashin muryan Inna dana Baffa da’alama dai sana’artasu ta kullum sukeyi wato faɗa,, shahada kawai tayi tadoshi cikin gidan, domin dai tasan tana shiga tofa kanta faɗan zai dawo… Aikuwa a rubuce yake tana sawo kai cikin gidan, Inna ta ce “Kekuma uwar gantali saiyanzu aka tashi daga makarantar ?” cike da ladabi Zahrah ta rusuna haɗe da cewa ” Baffa ina wuni “….”Daban wuni ba zaki ganni ? nace daban wuni ba zaki ganni ?? Baffa yakuma faɗa cikin tsawa, kai kawai zarah ta girgiza haɗe da nufar ɗakinta,, kwanciya tayi luf akan ƴar katifanta, zuciyarta cike da tunanin halin rayuwa dakuma yau da kullum….
Koda Zaid yabaro guest house ɗinsa bai zarce ko’ina ba sai wani babban Club ɗin dake cikin garin abuja, makeken Club ne mai kyau da tsaruwar gaske, irin Club ɗin nan ne daba kowa ke zuwanshi ba sai wane da kuma ɗan wane, Club ne na manyan guys, da kuma manyan ƴan mata, kamar ƴaƴan shugaban ƙasa da sauransu, amma idan dai har kai ba wani bane kuma ubanka ba kowa bane to fa baka isa shiga wannan haɗɗɗen Club ɗin ba, Zaid kuw yamaida wannan Club ɗin kamar ɗakin baccinsa, domin kuwa zaiyi wuya ace ya kwana ɗaya baijeba…
Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata tsakiyar Club ɗin dasu, yana zama wata ma aikaciyar Club ɗin tanufu inda yake hanunta ɗauke da tire na glass wanda samansa ke ɗauke da glass cup guda biyu, da kuma zungureren tsadaddiyar kwalban giya, kasancewa duk wani ma’aikaci dake cikin hotel ɗin yasan, abun da Zaid ɗin ke sha idan yazo wajen… Duk yanda ma aikaciyar Club ɗin nan ke kwarkwasa Zaid baiko ɗaga idanunsa ya kalleta ba, domin shi baimaga macen dazai kula ba kaf cikin Club ɗin, balle kuma ita banza mai aiki…. Cike da nutsawa Zaid yakafa kansa ya kwankwaɗi giya son ransa, saida yayi tatul tukun yabar cikin club ɗin, bayan yayi waya da Asmee ƴar wani minister dake cikin Naija, cewa tazo ta samesa a guest house ɗinsa……
*WAYE ZAID ?*
Zaid tantirin Mazinaci ne kuma ɗan giya, uwa uba baida mutumci ko ƙaɗan, sannan kuma komai kayi masa baka burgesa, Zaid yana da Munanan halayya, Zina shine babban ciwon daya riga yayi mawa jiki da zuciyarsa ƙawanya, Zaid Mazinaci ne na ƙarshe, iskancin sa yake zubawa babu mai hanasa, domin dai iyayensa sunriga da sungama shagwaɓasa, bayajin maganan uban kowa, duk wata haɗɗɗiyar mace wayayya dake cikin garin Abuja babu wacce batasan Zaid ba, domin iskancinsa ya shahara yayi ƙarfi, kasan cewarsa kyakkyawan saurayi mai wanka da naira, yasanya wasu ƴan mata ke matuƙar ƙaunarsa, sannan kuma suke burin mallakansa, amma saidai sama yayiwa yaro nisa babban ma saidai kallo….Alhaji Ma’aruf Chanji* shine sunan maihafin Zaid, Babban mutum ne da ake da mawa dashi acikin Nigeria, yana da kuɗi sosai, sannan mutum ne mai kyautatawa na ƙasa dashi, bashi da rowa ko kaɗan, matarsa ɗaya *Hajiya Safara’u* kuma itace ma haifiyar Zaid, daga Alhaji Ma’aruf har Hajiya Safara’u shuwa arab ne, Allah yayi musu baiwar kyau ga dukiya, shekaransu biyu da Aure Allah ya azurtasu, da haihuwan ɗa Namiji, wato Zaid, Zaid dai kyakkyawan gaske ne, domin tsananin kyawunsa ke sawa yake shiga ran jama’a, Zaid tun yana ƙarami yataso da wani irin Shu’umanci, ga mugunta, haka zalika baruwansa da shiga harkan kowa, hatta iyayensa kuwa, gaisuwa kawai keshiga tsakaninsu, duk yanda suka so yasake dasu amatsayinsu na mahaifansa, amma abun yaci tura, Sosai Iyayen Zaid ke nuna masa tsananin ƙauna, da tattali, asalin sana’ar Alhaji Ma’aruf shine Chanjin kuɗaɗe, yayi ƙaurin suna a sana’ar, sannan kuma yatara maƙudan kuɗaɗe, ganin harkan nasa natayin gaba dukiyarsa na ƙara yawa, yasanyashi tattarawa yakoma America da zama, can ya cigaba da business ɗinsa, duk ko yanda yaso Hajiya Safara’u tabiyo sa America suzauna ƙiyawa tayi, saidai Zaid yayarda yabi mahaifinsa, inda a can yasoma karatun sa,, Zaid yanada shekaru goma a duniya mahaifiyarsa ta haifa masa ƙanwa maisuna Labisat, Labisat dai kyakkyawar yarinyace suna kama da Zaid, saidai a gaskia Zaid yafita kyau sosai, domin idan kaga Zaid zakai tunanin ba ɗan Nigeria bane,,,, acan America mahaifin Zaid kasuwancinsa kawai yasa a gaba, amma sa’i da lokaci yana zuwa Nigeria duba iyalansa,, Yanayin yanda yake gudanar da kasuwancinsa a America yasanya bashida wani kyakkyawan lokacin da zai kula da ɗansa wato Zaid, kullum Alhaji Ma’aruf idan yafita office baya dawowa sai dare, shikuwa Zaid rayurwasa yakeyi da turawan abokansa, wanda yayisu acikin school ɗin dayake, kunsan dai su turawa, babu wani abun daya damesu iskanci sun maidashi kamar ruwan sha, domin dai dayawansu ba addinin Allah suka sani ba balle su kiyaye, tun Zaid na da shekara 17 yafuskanci abokansa na school suna neman mata, shikuwa sam alokacin mata basa gabansa, duk da kuwa cewa suna kawo masa tallen kansu, amma baya sauraransu, duka abokan Zaid turawa ne, sai mutum ɗaya wato *ABID* Abid cikekken ɗan Nigeria ne cikin garin Abuja shima gidansu yake, sannan babansa shine Minister’n Man Fetur na Nigeria gaba ɗaya, Abid hatsabibin ɗan iska ne kuma tantiri domin kuwa tun yana ƙaraminsa yasan yanda zai jagwalgwala mace, Zaid da Abid a bota suke sosai, domin jininsu yazo ɗaya,, duk da cewa Zaid yana da ƙarfin sha’awa amma bayabin mata, saidai wani zubin yakan ɗan mawa mace kiss da dai sauransu,, lokacin da Zaid yake matakin lavel 2 na degree ɗinsa lokacin yana da shekara 21, Allah ya jefomasa ƙaddaransa kuma Hargitsi mafarin halakarsa,,, wata rana sunje yawon shaƙatawa shida saiɗanun abokansa, ya haɗu da wata ƴar iskan baturiya mai suna Nicky, abun daya fa ra ɗaukar hankalin Zaid game da Nicky shine kyawu da surarta, Nicky irin fitinannun matan nanne, shu’umai wanda idan suka ɗiga tsamansu akan abu tofa sai sun sameshi, tunda Nicky tayi ido huɗu da Zaid gaba ɗaya hankalinta yatashi, domin kuwa Zaid yayi mata hundred percent, bawani ɓata lokaci tabayyana masa soyayyarta a gareshi, Zaid kuwa dake ɗan izza ne saiya soma ja mata aji,, daga ƙarshe dai daya tabbatar da cewa itaɗin bata bibiyar maza sai ya amsa soyayyarta suka cigaba da shan love ɗinsu,,+
Watarana Zaid yana kwance a ɗakinsa, sai ganin Nicky kawai yayi sanye da wani irin ɗan iskan kaya wanda yabayyana komai na surarta a fili, ganin da yayi mawa Nicky a haka baƙaramin ɗaga masa hankali yayiba, wata irin sha’awa yakeji mai ɗaga hankali, koda Nicky tafahimci haka saita yi amfani da damanta tasake ruɗa Zaid da irin salonta, jawo Nicky yayi jikinsa yashiga sun batarta tako ina, a rannan sheɗan yaribaci Zaid har yakusanci Nicky, tun da yake a duniya baitaɓa sanin ya daɗin Sex yake ba sai awannan ranan, baisan ya ƴa mace take ba shidai kallon su kawai yake, amma sai gashi yau yasani,, wani irin gamsuwa Nicky tasamu da Zaid a ranan wanda bata taɓa samun irin shi da ga wani ɗa Namiji ba,, tundaga Wannan rana Zaid yazama mashahurin ɗan iska kullum yana tare da Nicky suna aikata Zina, arana sai Zaid yayi Sex da Nicky sau Biyar,
Zaid mutum ne mai ƙyan ƙyami, shiyasa kwata kwata baya neman sauran matan turawa domin yasansu kowa buɗe ma ƙafa suke yashige,, Nicky ce kaɗai abokiyar watsewarsa, itama dan yafuskanci cewa bata mu’amala da kowani na Miji ne, sannu ahankali Zaid yasoma shan giya, koda Abid yafuskanci cewa abokinnasa ya soma baza iskancinsa, sai yasake haɗasa da wasu ƴam mata gangariya, aikuwa Zaid baiƙiba, nanfa iskancinsa yaci gaba da tumbatsa, haryazo ya fi ƙarfin Nicky, Ƙaurin isknacin Zaid har yaɗara na abokansa,domin ko Abid yanzu Zaid yafisa sanin kan mace da kuma iya iskanci,,,, duk wannan halin da Zaid ke ciki Dadynsa Alhaji Ma’aruf baisaniba, yanacan yasa harkan kuɗinsa a gaba, yakuwa mallaki dukiya masu mahaukatan yawa,, akwana atashi Zaid ya kammala degree ɗinsa, cikin ikon Allah kuwa yasamu kyakkyawan result, domin dai yanada ƙoƙari sosai, iskancinsa baisa yadaina karatu ba,, bawani ɓata lokaci Zaid yawuce London domin yin masters ɗinsa acan, hmmmm zuwansa London yaƙara masa iskanci sosai, shima Abid biyosa london ɗin yayi suka ci gaba da zuba iskancinsu acan,, Zaid yazama tantirin shu’umi idan yaga mace matuƙar tayi masa tofa saiyayi sex da’ita,, duk wannan tsawon shekarun da Zaid yaɗauka aƙasashen duniya, sauɗaya tak yazo Nigeria nanma satinsa biyu kacal ya tattara ya koma,,
Kwanci tashi Zaid yakammala Masters ɗinsa, take kuma wani Babban banki dake london suka nemi da yayi aiki dasu, sam bai amince da buƙatarsu ba, domin shi yafiso yayi kasuwanci, maƙudan kuɗaɗe Dadynsa yasanya masa wajen gina masa wani katafaren kamfani a London, shahararren kamfani aka gina masa na ƙera takalma da jakakkuna new styles, masha Allah cikin ƙanƙanin lokaci kamfanin Zaid ya shahara a faɗin duniya domin, kaya masu kyau da inganci suke bugawa,, Zaid yana karatu kuma yana kasuwancinsa harya kammala P.H.D ɗinsa, isakanci kuwa yaci uban na da,, wasa gaske saiga Zaid ya mallaki Company’s a ƙasa she da dama, lokaci ɗaya Zaid yayi wani irin mahaukacin kuɗi, baiyi ƙasa a guiwa ba ya dawo Nigeria yakuma gina wani kamfani’n da ake ƙera gyalelluka wato vails, tunda ya dawo Nigeria baisake komawa ko wacce ƙasa ba, domin yaji ƙasar tasa wato Nigeria tayi masa daɗi, company’s ɗinsa na ƙasashen waje kuwa, yasanya amintattun mutanensa suna kula masa da su……
Cigan Labari…Haka Zaid da Asmee suka ɓata dare suna iskancinsu, basa ko tsoron Allah mahalicci,, haƙiƙa zuciyar Zaid ta bushe ƙarau, baya ko tuna azabar da Ubangiji zaiyi masa, aduk sanda yaje garesa batare da ya tuba ba…….
+
Kasancewar yau basu da lecture sai 12 pm yasanya gaba ɗaya aikin gidan itatayi shi, yayin da Inna ke kishingiɗe akan tabarma,, da bala’i Baffa yashigo cikin gidan ” Wallahi ni nagaji bazan iyaba ehe, ace akan yarinya kwara ɗaya tol duk inda nagilma mutane zagina sukeyi, to bata saɓuwa, ke Zahrah inakike ne dan Ubanki ?” Baffa yaƙare maganar cikin hargowa, Zahrah dake cikin kitchine tafito jikinta a sanyaye domin tasan kwanan zancen,, “Lafiya kuwa Malam kashigo gida kana ɓaɓatu ?” Inna dake kwance tatambayeshi, ” Kema kinsani ai akan wannan yarinyar ce mana Zahrah taƙi fito da Miji tayi aure, tananan koda yaushe cikin bulayin zuwa makaranta, makarantan da ba tsinana mata komai zaiyi ba, to wallahi nagaji, ko ina gulma ake wai nakasa riƙe amanar da ɗan uwana yabani, naƙi aurar da yarinya nasata karatu, bayan nafi kowa tsanar wannan ɗan iskan karatun da takeyi ” “Ke Zahrah !!” yaƙira sunan Zahrah da kakkausar murya, batare da yabari ta amsa masa ba yaci gaba da cewa ” bazan iyawa zagin mutane ba, nabaki nanda wasu kwanaki ki fito da miji koda kuwa musaki ne na tattaraki nayi miki aure batare da wani kayan ɗakiba, kije can ki ƙarata ” Baffa nakaiwa nan a zancensa ya sakai yashige cikin ɗaki, Inna tarufa masa baya,,, ɗaki Zahrah ta koma haɗe da zama akan ƴar yalolon katifarta, ” ya Allah gani gareka kafi kowa sanin halin da nake ciki ya Allah kakawomin ɗoki ” wasu zafafan hawayene suka shiga sauƙa daga kan fuskar Zahrah, maganar kenan koda yaushe Miji Miji, wai shin ina zata samo mijin da zai aureta ? tun da take a duniya Namiji ɗaya ne yataɓa cewa yanasonta, kuma shima tundaga wannan ranan bata sake sashi acikin idanun taba, tayi imani cewa tana da tsantsar kyau da kuma sura, wanda zai iya janyo hankalin ko wani ɗa namiji zuwa gareta, amma maiyasa babu wani Namiji dake kallonta ballan tana harya furta mata kalman so ? tayi mawa kanta tambayar da bata da amsa,, jin motsin Inna a tsakar gida yasa tayi saurin share hawayenta, haɗe da ficewa daga cikin ɗakin, kuɗi Inna taciro daga kunkuminta, haɗe da miƙamawa Zahrah tace “Ungo maza kaima wa Ladidi mai adashe kice mata ga zubina na jiya ” “to” kawai Zahrah tace haɗe da nufar hanyar fita daga gidan, domin dai dama sanye take da hijab ajikinta, al’adar ta ce bata zama babu hijabi, saidai idan a ɗakinta take….
Tafiya take tana kallon ƙasa, yayinda hannayenta ke naɗe akan ƙirjinta, da gudun gaske ya shawo kwanar saura ƙiris ya doketa, Allah ne kawai yasa tayi saurin matsawa gefe,, parking motar yayi haɗe da leƙo kansa waje ta window’n motar ” Uh sorry Zahrah ina fata dai bantaka ki ba ?” ɗan guntun murmushi tayi haɗe da cewa “A’a baka takani ba” wani irin shu’umin kallo yabita dashi haɗe da cewa “Ina zaki ne haka da tsakar rana ?” ” Aika zani ” Tabasa amsa a taƙaice,, “Okay shigo na rage miki hanya mana ” yayi maganar yana mai yunƙurin buɗe mata murfin motar, “A’a kabarshi kawai nagode” bata jirayi mai zai ceba tasakai tayi tafiyarta,, murmushi kawai Bash yayi haɗe da figar motarsa yayi gaba…..
*Wacece Zahrah ?*
Malam Adamu Muhammad haifaffen ɗan jihar Yola ne, su biyu ne a wajen iyayensu shida ƙaninsa Hayatu, Malam Adamu yakasance mutum mai mutumci da kuma karamci, Matarsa ɗaya Zainab, Zainab, asalinta buzuwar Niger ce fatauci yashigo da mahaifanta Nigeria, Mahaifan Zainab dana Malam Adamu suna da kyakkyawan alaƙa kasancewarsu maƙotan juna, tun Zainab na ƙarama Allah yasanya mata soyayyar Malam Adamu acikin zuciyarta, kasancewarsa kyakkyawan bafulatani, duk da dai tafisa kyau nesa bakusa ba, cikin ikon Allah Zainab nakai lokacin daya kamata ace anyi mata aure, iyayenta suka Aura mata Malam Adamu, zama sukeyi na lafiya da ƙaunar juna,, watarana iyayen Zainab suka shirya don zuwa Niger, ahanyarsu ta zuwa sukai gamo da ƴan fashi, suka harɓesu, sosai Zainab tayi kukan rashin iyeyenta, da ƙyar dai Malam Adamu yasamu ya rarrasheta, akwana a tashi kwatsam ciki yabayyana ajikin Zainab, sosai sukayi murna da samun ƙaruwa da Allah yayi musu, cikin Zainab nada Wata Tara tahaifo kyakkyawar ɗiyarta mai matuƙar kama da ita, saidai ita ƴar harta ɗara Zainab a kyau duk da kuwa kyau irin na Zainab, anyi shagalin suna lafiya inda yarinya taci sunan mahaifiyar Zainab wato *FATIMA* ana ƙiranta da *ZAHRA* Zahrah tataso cikin gata da kulawar iyayenta, saidai muce masha Allah,, watarana ne Malam Adamu yatattara matarsa da ƴarsa suka koma garin Abuja da zama, cikin wata unguwa da’ake ƙira Suleja, yakama musu hayan wani ɗan ƙaramin gida,, sana’ar saida takalma Malam Adamu keyi, yana da ɗan teburinsa a nan yake kasa takalman roba da su silifas (slippers), cikin ikon Allah kuwa,Allah baya hanasa na abinci da kuma na ƴan biyan buƙatun da ba’a rasaba, Watarana Malam Adamu ya tsinci wasu maƙudan kuɗaɗe a ƙasa, daya bincika kuɗin shine yataradda adireshi (Adress) na mai kuɗin acikin jakar daya tsinci kuɗin, a shema wanda ya wurgar da kuɗin, a nan gaba da unguwarsu kaɗan yake kuma yasanshi sunansa Alhaji Umar, Malam Adamu baiyi ƙasa a guiwa ba wajen kaimawa Alhaji Umar kuɗinsa, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗi sosai, nan yaɗauki maƙudan kuɗaɗe yabamawa Malam Adamu, amma Malam Adamu haka yaƙi karɓa acewarsa, shi don Allah yayi bawai don abiya saba, aikuwa Alhaji Umar yaji daɗin hakan, haka dai Alhaji Umar da Malam Adamu suka soma zumunci, watarana Malam Adamu na zaune, Alhaji Umar yaƙirasa yace mai yasayamasa gida anan suleja, bakaɗan ba Malam Adamu yayi farinciki, har ƙwallan murna saida yayi, gidane daidai da zaman talaka Alhaji Umar yasai mawa Malam Adamu, ɗakuna huɗu ne acikin gidan sai ɗan madaidaicin filin tsakar gida, da kitchine da kuma makewayi, Koda Zainab tazo taga gidan itama taji daɗi sosai, bawani ɓata lokaci suka tattaro suka dawo gidan,, a kwana a tashi Asaran mai rai, wata rana aka wayi gari Baban Malam Adamu ya rasu, sosai mutuwar tajigata ƴaƴansa, amma babu yanda suka iya duk wani mai rai mamacine sunriga da sunyi imani da hakan,, bawani ɓatalokaci Malam Adamu ya ɗauko mamansa suka dawo garin Abuja da zama,, baifi wata uku da dawowar Goggo (Maman Malam Adamu) Abuja ba, tace ga garinku nan, Allah sarki su Malam Adamu sunkuma jin zafin rashin mahaifiyarsu,, bayan wani lokaci Hayatu yayi aure, Malam Adamu ne yace masa yadawo nan Abuja su zauna, tunda akwai ɗaki a gidansa, Hayatu bai ƙi ba, yaɗauko matarsa suka dawo,, tundaga kan Zahrah Malam Adamu da Zainab basu sake haihuwa ba, Zahrah tanada shekara huɗu Malam Adamu yasanyata amakarantar furamari (Primary) Zahrah yarinya ce mai hazaƙa sannan kanta yana ja sosai, kwanci tashi Zahrah ta kammala makarantar furamari (primary) ɗinta, bawani ɓata lokaci Malam Adamu yasama mata gurbin cigaba da karatu (Admission) a wata junior school dai dai da ƙarfinsa,, Zahrah na aji ɗaya a junior school, Mama (Zainab) takwanta rashin lafiya, abu kamar wasa hardai takaisu ga asibiti, kwanan mama ɗaya a asibiti Allah yayi mata rasuwa, kuka kam Zahrah da Malam Adamu sunsha shi, domin kuwa sunyi rashin jigon rayuwarsu, haƙiƙa Zahrah tayi rashin uwa ta gari, shiko Malam Adamu yayi rashin mace ta gari,, sati ɗaya da rasuwar Mama Malam Adamu yakwanta jinya, abu kamar wasa saigashi ko tashi baya iyawa, Wata rana ne aka wayi gari Malam Adamu baya numfashi, Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un !! Zahrah tayi kuka bana wasaba lokaci guda tayi rashin farincikin rayuwarta,,,,, koda Alhaji Umar yazo ta aziya, baiyi ƙasa a guiwaba, cewa yayi ya ɗauki nauyin karatun Zahrah harta ƙare jami’a, yayinda riƙon Zahrah yadawo wajen Hayatu da matarsa (Baffa, Inna) sam Zahrah batajin daɗin riƙon da Baffa da Inna keyi mata domin tsananin tsangwama suke nuna mata, gahi Baffa yahau kan ɗan gadon da Babanta ya bar mata yacinye,,, Ayanzu Zahrah tana da shekara 20 aduniya, kuma harzuwa yanzu Alhaji Umar ne ke ɗaukan nauyin karatunta…..
Cigaban Labari
Adai dai bakin titin yayi parking motarsa, domin sam shikam baijin cewa zai iya shiga, wannan unguwar talakawan da tsadaddiyar motarsa, shi sam baisan ma uban me yasa Bash yayi guest house ɗinsa a wannan unguwar ba,, zama yayi a cikin motarsa haɗe da ɗaukar wayarsa yadanna mawa lambar (Number) Bash ƙira, ringing biyu kawai wayar tayi Bash da ke kwance jikin wata ƴar iskan sa ya ɗaga,, “Ina bakin titi ” yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar tasa,, baiwani ɗau lokaci ba saiga Bash ya ƙaraso,
“kaga *SHU’UMIN NAMIJI* maifirgita ƴan mata, Shu’umi mai sace zuciyar duk wacce yaso, ko shaiɗan yana tsoron shu’umancin ka !!” Bash yafaɗa dai dai lokacin dayakema kansa masauƙi acikin motar, ɓata fuska Zaid yayi haɗe da cewa ” Kai ni duk ba wannan ba waishin meyasa ka tsalleki ko wani unguwa kazo nan kayi guest house ɗinka ?, ka duba fa gidajen area’nnan gaba ɗaya na talaka wane ” Zaid yaƙare maganar yana maibin gidajen da kallon ƙyama,, murmushi Bash yayi haɗe da cewa
” Bazaka gane bane my man, amma wallahi ƴan mata nake samu a arean nan bana wasaba, kai bana ta ƙaice maka, yarinya sai ta kawomaka budurci (virginity) ɗinta a ɓagas, badon komai ba sai don tsananin talauci daya adda beta, yanzu haka akwai ƴan mata a ƙasa idan kana buƙata..” Bash yaƙare maganar yana murmushi mai ɗauke da nuna shi tantirin ɗan iska ne,,
taɓe baki Zaid yayi haɗe da cewa “Bazan iya iskanci da low class ba gaskia, kudai kuyita fama harku ɗaukomawa kanku wata cutar, yaƙare maganar yana ƴar dariyan mugunta,,
gyara zama Zaid yayi haɗe da cewa ” Nazo maka da wani babban harka ne idan zakayi ” shima Bash gyara zama yayi da kyau haɗe da cewa “Inajinka abokina “
Zaid ya buɗe baki zaiyi magana kenan idanunsa suka sauƙa akan wata kyakkyawar budurwa, wacce ke sanye da hijab iyaka guiwarta, hijab ɗin irin mai roba ɗinnan ne, hakan yasa ya bayyana duk wata sura na jikinta, wani irin abu Zaid yaji daga ƙasan ƙafarsa harzuwa cikin kansa, yayinda tsikar jikinsa yashuga zubawa, a hankali ya lumshe kyawawan idanunsa, da alokaci guda suka kaɗa sukai ja, koda yabuɗe su don sake kallon wannan halittar da’idanunsa sukai masa to zali da’ita, sai yaga saɓanin haka, domin ko a alamar gilma wanta baigani ba, saurin fita daga motar yayi haɗe da soma waige waige ko Allah zaisa yaganta, amma ko alamar ta bai gani ba……..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *