ALKAWARIN JINI CHAPTER 6 BY _HAWWA MUH’D USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Haba mai babban suna.. Ta ina ne ka tab’a ji haka ya faru..?? Ka tuna fa babu yadda za’ayi ayi aure ba tare da amincewar mahaifanka ba,tunda bai baka goyon baya ba,me yasa kake son yin amfani da damuwarka wajen kaucewa matsalar ka..?? Shin baka tunanin hakan zai sake janyowa mahaifinka ya aikata wani abu daban a gaba..??”
Shiru Hammad yayi bayan sauraren baffa babu abunda yake yi,yayin da zuciyarsa ke hasaso maganganun Daddy’nsa,tabbas yafi kowa sanin mahaifinsa mutum ne mai tsatstsauran ra’ayi wanda idan har ya fad’i magana tamkar yankan wuk’a,baya tab’a soke magana idan har ya riga ya furta haka nan ba’a tab’a canja masa ra’ayi,shi d’in tsayyaye ne wanda baya tab’a d’aukan ra’ayin kowa,kamar yadda yayi masa wannan sanin tuni ya san da kamar wuya ace tunda ya yanke masa hukuncin tafiya ya janye,to amma duk da bai fito ya nuna k’in amincewarsa k’arara akan lamarin ba,ai ya kamata ace yayi na’am da buk’atarsa,tunda
shima bai musa hukuncinsa a kansa ba,lallai ne yana buk’atar ya fahimci wani abu,,,shin ra’ayin Daddy akan karatunsa yake ko kuwa yarinyar da yake so ne bata yima Daddy’n ba..?? Ko kuwa dai da gaske ne bai isa aure ba..?? Wannan shi ne tunanin da yayi ta fama da shi,sai dai ya kasa fahimtar komai
“Ina tunanin yin haka ba shi ne zai haifar mana da d’a mai ido ba,,hakur’in dai shi yafi cancanta muyi mu duka,in sha Allah da sannu komai zai zo mana k’arshe..Amma batun d’aura muku aure duk ba shi ne mafita ba,neman amincewar mahaifa da sanyawar albarkarsu abune da yake da matuk’ar muhimmanci a rayuwa,,idan ka samu iko kayi k’ok’arin fahimtar da mahaifinka muhimmancin yin hakan,saboda wasu lokuta al’amura sukan canja kansu,,sai dai ina horonka daka kasance mai yiwa mahaifanka biyayya akan duk abunda za su umarce ka matuk’ar bai sab’awa fad’in Allah (S.W.T) ba ko koyarwar Annabi (S.A.W),yin hakan zai sa ka had’u da alkhairin da baka tab’a tunani ba a rayuwa..Amma ina so ka k’ara hak’uri..”
Fuskarsa sam babu wani alamu da yake nuna zai iya yin hak’uri kamar yadda baffa yake so,a hankali ya kifa kansa a k’asa yana tunanin maganganun baffa tun daga farko har k’arshe,cikin tsantsar damuwa ya kai hannu ya d’auke hular dake kansa ya ajiye a k’asa zuciyarsa banda ingiza shi babu abunda take tunaninma duka ya rasa wanda ya kamata yayi,ya d’auki lokaci cikin wannan yanayin da baya iya bambance a inda yake kafin ya d’ago jajayen idanunsa da damuwa ta sauyawa launi ya sauke su akan baffa,shi kansa baffa ko daya kalli yanayin da yake ciki sai da yaso bashi tsoro bcos tunda yake bai tab’a ganin wani ya shiga makamancin yanayin da Hammad d’in yake a ciki ba
“Subhanallah..! Muhammadu me yake faruwa da kai haka..?? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..!”
Wani murmushi ya saki mai ciwo,cikin muryansa daya jima da sanyaya ya furta
“Babu komai baffa..Am fine..!”
Girgiza kai baffa ya shiga yi yana fad’in
“A’a Muhammadu ka fad’a min abunda ke damunka..Shin kaga yadda ka koma kuwa..? Me yasa baza ka sanar da ni gaskiya ba..?? Nima fa kamar mahaifi nake a gareka..Kayi k’ok’ari ka fad’a min idan damuwar ka..!”
Kansa ya shiga moving asides nd yana gripping lips cike da tsantsar damuwa
“Nothing baffa..Am fine..!”
Shi dai baffa ba jin turanci yake ba saboda haka ko da Hammad yayi magana bai fahimci me yake fad’a ba,ci gaba da tambayarsa
“A’a Muhammadu baka sani ba,ka daina cewa ka sani..Ka daure dai ka fad’a idan ina da damar taimakamaka sai nayi..Amma zama a cikin damuwa ba shi da amfani..”
Saurin kallon baffa yayi yana sakin murmushi,cike da yarda da kai ya furta
“Baffa da gaske zaka taimaka min..?? Idan kaji abunda nake muradi zaka yi min..?? Baza ka k’i ba,ko da ba haka kake so ba..??”
“In sha Allah zanyi k’ok’arin yi maka idan har ina da ikon yin hakan..”
Wani irin murmushi ya saki mai kama da mutum ya samu matsalar kwakwalwa kafin ya ce
“Baffa ka auramin ita..Na san Daddyna zai karb’i aurenmu nan gaba,baffa batun ace har sai lokacin daya amince ne zaka auramin ita da nisa sosai,ya kamata ace baffa ka fahimci halin da zuciyoyin mu zasu shiga..Please baffa i implores u..”
Kallonsa kawai baffa yake yi dan yadda yake abu kamar zararre lamarin fa ya fara d’aure masa kai,tunaninsa me yake faruwa da Hammad d’in haka lokaci guda ya sukurkuce masa,tabbas idan har ace dan soyayyar da yake yiwa y’arsu ne ya kamata yayi wani abu da gaggawa idan kuwa ba haka ba tofa yasa rai da ganin abunda yafi wannan muni da tashin hankali,cike da yin na’am da shawarar da zuciyarsa ta kiyasta yayi saurin d’agowa ba tare da tunanin komai ba ya furta
“Shi kenan Muhammadu na amince..Amma akwai sharud’a..”
“I will agree baffa..Duk abunda zaka fad’a bazan musa ba,matuk’ar zaka auramin ita..”
Kallonsa kawai baffa yaci gaba da yi har yayi shiru dan kansa
“Tabbas..Mai babban suna na amince zan aura maka ita,,amma ba a irin wannan lokacin ba..”
Murnar sace ta fara k’ok’arin komawa ciki,nan da nan y’ar fara’ar dake saman fuskarsa ta fara disashewa
“Baffa sai yaushe ne zaka aminta da batuna..I swear zan rik’e ta amana ka yarda dani baffa..”
Zafafan hawayen da suka biyo bayan maganarsa su suka tilasta masa yin shiru,izuwa yanzu kam ko da baffa yaga yanayin da yake ciki ga hawaye a fuskarsa tuni tausayin Hammad ya gama ratsa masa zuciya,sai dai kawai yana jin ba lallai ne ya iya yi masa abunda yake so ba
“Kayi hak’uri Muhammadu nima ba’a son raina hakan zai faru ba,idan da ace ina da ikon aura maka ita a yanzun zanyi,sai dai nasan babu yadda za’ayi ko da na aura maka ita ku tafi tare sannan ba lallai ne mahaifanka su amince ba..”
Saurin katse shi Hammad yayi ta hanyar fad’in
“Amma baffa idan ka d’aura mana aure na tabbatar kaima zaka fi samun nutsuwa daga irin maganganun dake yawo cikin garin nan,sannan ko babu komai su kansu jama’ar dake surutun zasu saurara daga lokacin da suka tabbatar da kasancewar mu ma’aurata.. Ka aminta dani baffa,,ni kaina ko da na tafi zan kasance ne a kullum ina tunawa da cewar akwai *ALK’AWARI* akaina,sannan ba zan manta da cewa akwai mutanen dake jira na ba,hakan zai bani damar yin abunda ya kaini na kuma dawo gare ku..Idan dan batun ko baka sanni ba ko asalina mahaifina ba b’oyayye bane,na san ko da ace kuna zaune a nan baza ku kasa sanin chief judge Aliyu Sani ba..”
“Haka ne Muhammadu kayi gaskiya,sai dai babufa ta yadda za’ayi ni da kaina na aikata abunda kake so,saboda idan har na yarda na d’aura muku aure za kayi tafiya ne mai nisa,yayin da mu da ita za ka barmu muna zaman jira,sai dai zan iya yi maka abu guda shi ne,zan iya karb’ar sadaki na ajiye har zuwa lokacin da zaka dawo..”
Sam Hammad bai so haka ba,dan haka suka ci gaba da tirzawa da baffa,shiru baffa yayi zuwa wani lokaci sannan yaci gaba da cewa
“Bazan iya amincewa da wannan buk’ata taka ba Muhammadu,bayan na sani da yawa daga cikin ma’abota ilimi sunyi maganganu dangane da irin wannan matsalar,dan haka ina so ka saurari abunda zan fad’a maka game da abunda kake son na aikata,,,kamar yadda yazo wasu daga cikin magabata sun iyakance adadin watanni shida (6) a matsayin wanda mutum zai yi a halin tafiya sannan yadawo wajen iyalinsa,ba don komai ba sai dan saboda sun dogara ne da abunda aka ruwaito daga sayyadina Umar ibn khattab (R.A),malamai su kace asali kuma a shari’ance ba’a samu wani nassi daga Manzon Allah (S.A.W) ba wanda ya kayyade adadin kwanakin da miji zaiyi baya gari a yayin da yayi tafiya,to amma an samu wani *(ASAR)* daga sayyadina Umar ibn khattab (RA) cewa ya k’ayyade watanni shida (6) ga sojojin da suke a wajen yak’i,wannan kuma yana daga cikin *IJTIHADI* ne wanda Sayyadina Umar (R.A) yayi lokacin da ya tambayi y’arsa nanna Hafsat (R.A) akan hakan,sai dai babban abunda ya kamata a lura da shi a nan,shine yanayin canjawar zamani da kuma wurin da ake zaune,ko shakka babu zamanin sahabbai (Radhiyallahu anhum ajma’iyn) yafi wannan zamanin da muke ciki inganci da kuma adalci,sannan b’arna bata yi yawa ba kamar ta wannan zamanin da muke ciki.Dan haka kaga kenan abu mafi kyau shine ya kamata ace miji da mata suyi tsarin da zaifi dacewa da zaman takewarsu domin su sukafi kowa sanin yanayin halinsu,sai suyi tsari gwargwadon k’arfin sha’awarsu,su iyakancewa kansu adadin kwanakin da suke ganin zasu iya jurewa ba tare da sunyi jima’i da juna ba,saboda akan samu bambamci tsakanin wata matar da wata haka shima mijin,sannan kaga wata matar yarinyace matashiya tana da buk’atar ace miji baiyi nisa da ita ba,wata matar kuma girma ya kamata dan haka koda zai kai shekara baya nan baza ta damu ba,duk da cewa abu mafi kyau shine indai da hali anfiso matafiyi yar ik’a tak’aita kwanakin da yake yi yana dawowa wajen iyalinsa idan yayi wata tafiya,amma idan ya kasance akwai wani uzuri to babu laifi akansa idan ya dad’e koda kuwa ya haura watanni shida (6) ne acan din idan bukatar hakan takama,kamar wanda ya tafi neman magani ko kasuwanci a wani gari ko wata k’asar mai nisa,ko kuma misali kai da zaka tafi neman ilimi,amma idan har yanajin tsoron faruwar wata fitina ga iyalinsa saboda kasancewarta mai yawan sha’awace ita ko kuma dad’ewar sa a can d’in zata haifar masa da sab’ani tsakaninsa da surukansa,to ya kamata ya rik’a dawowa da wuri saboda kaucewa wannan matsala,kada yayi dad’ewar da zata zama sanadin rabuwarsa da matarsa (domin neman k’arin bayani sai ku nemi Almughniiy na ibn k’udaamah cikin majmuu’ul fataawa 32/271),saboda haka abunda nake so ka fahimta a nan shi ne,ba wai yin auren ne matsala a gare niba,A’a abunda zai faru gaba shi nake ji,dan haka hukuncin da zan yanke a nan shi ne..!”
Saurin taron numfashin sa Hammad yayi da fad’in
“Na amince baffa da duk hukuncin ka,amma dan Allah kayi min rai ka yarda na bada sadakin kafin tafiyata,iya wannan alfarmar kad’ai ta isarmin baffa,daga shi bazan sake cewa komai ba,duk hukuncin daka yanke am ready na karb’a ko da zuciyata bata so,,amma baffa ka duba hakan..Pleasee..!”
Jimm baffa yayi yana nazarin maganarsa,ganin hakan da yayi dai² yake da baffa yak’i amincewa buk’atarsa yasa shi had’e hannayensa guri guda ya shiga rok’on sa kamar idan yak’i amincewa zai kece da kuka,ajiyar zuciya baffa ya saki cikin kaiwa mak’ura kafin a hankali baffa ya furta
“Shi kenan Muhammadu,,,idan har dan wannan ne na aminc..!”
Tun kafin ya k’arasa cikin k’arajin murna tuni Hammad yayi sujudush-shukhur,lokacin daya d’ago bakinsa sam yak’i rufuwa banda kalmomin godiya babu abunda yake jerawa ga ubangiji (S.W.T),,Baffa kansa yadda yaga yana murna sai da lamarin ya sake d’aure masa kai,nd yau rana ta farko ya sake tsinkewa da lamarin ubangiji,cikin zuciyarsa fad’i yake “idan ba Allah ba babu wanda ya isa ya sanya soyayya mai k’arfi tsakanin bayinsa kwatankwacin wannan da idanuna suke ganemin”,,sun jima sosai a zaune banda godiya babu abunda Hammad ke yiwa baffa,kafin daga bisani baffan yayi masa bayanin ya kamata a rubuta yarjejeniya akan maganar,gudun ko da gaba idan yajewa mahaifansa da batun suka k’i amincewa zai zamanto akwai gagarumar hujja da dole tasa su yarda,cike da k’warin guiwa Hammad ya amsa nan baffa ya aika domin a nemo masa k’annensa wato baban Sabina da baban LADO,sai wasu amintattun dattawa daga abokansu da ake zaman lafiya a garin da yasa aka fad’awa,ko da suka zo a gabansa baffa ya zayyana musu bayanin duk yadda suka yi da shi da irin hukuncin daya zartar akan lamarin,babu wanda yaga laifinsa cikin abunda ya aikata kasancewar dama tuni duk wani hukunci shi yake yankewa akan ahalin nasu,kamar yadda ya ambata tun da farko nan Baffa ya wakilta dattawan nan biyu domin su zamo waliyyai ga Hammad yayin da baban LADO da baban Sabina suka kasance waliyyan Sabina,bayan nan baffa yasa aka kawo masa takardu da alk’alami daga cikin gida yayi musu jawabin abunda za’ayi sannan ya fara rubutu da larabci akan takarda ta farko,yayin da yake karanta duk abunda yake rubutawa a fili har ya gama rubuta takardun *ALK’AWARIN* da suka k’ulla d’in akan Sabina da Hammad,sannan batun sadaki daya bayar wanda za’a ajiye kamar yadda ya buk’ata daga nan zuwa lokacin da Allah zai dawo da shi,bayan ya gama ya sake karanta musu sannan ya tambaye su ra’ayinsu dan gane da hakan,ba’a samu wanda ya musanta batun ba a cikinsu,ko da baffa ya tabbatar babu wanda yake da abun cewa nan ya ja layi guda shida a k’asan kowace takarda ma’ana inda kowa zai sa hannu wanda kuma shi yake sake tabbatar da kowa yayi na’am,daga nan baffa ya rattaba sa hannu,sannan Hammad da waliyyansa daga nan aka mik’awa baban SABINA da baban LADO duka suma suka sa hannu,takarda d’aya baffa ya d’auka ya mik’awa waliyyan Hammad yana fad’in
“Wannan takarda dana baku,na baku ita ne ba don komai ba,sai dan ta zama shaida agareku da kuna tunatarwa bisa *ALK’AWARIN* da kuka d’aukarwa kanku,wanda na tabbata kallonta a koda yaushe zai kasance yana tunatar da ku muhimmancin rik’on amana da cika *ALK’AWARI* da Allah (S.W.T) ya ambata a cikin suratun-Nisa’a (aya ta 58):”Lallai ne Allah yana umarnin ku da ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.Kuma idan zaku yi hukunci a tsakanin mutane,ku yi hukunci da adalci.Lallai ne,Allah madalla da abunda yake yi muku wa’azi da shi.Lallai ne Allah ya kasance mai ji ne,kuma mai gani ne”. Sannan Allah mad’aukakin sarki ya sake fad’a a cikin suratul ma’idha (aya ta farko) inda yake cewa:”Ya ayyuhallazhiiyna aamanuu aufu bilk’u’uud… Ma’ana:-Yaku wad’anda suka yi imani! Ku cika alk’awurra..(ilaa akhirul aya) kamar yadda mu duka muka shaida kuma muka amince zamu cika wannan *ALK’AWARIN*,saboda haka nasan tunawar zai zame mana alkhairi baki d’aya sannan kuma ya bamu iko tare da damar aiwatar da wannan umarni na mahaliccinmu..”
“Wannan gaskiya ne,,Malam Ibrahim kayi gaskiya,hakan ya kamata sosai..”
Wata takardar ya sake d’auka ya mik’awa su baban Sabina yana mai fad’in
“Kuma ina son ku ajiye wannan a gurinku dan ya zama shaida ko da zuwa gaba..”
Bayan nan ya bawa HAMMAD guda shima ya rik’e guda,daga nan baffa ya yiwa waliyyan Hammad umarni da su bada sadaki ga waliyyan Sabina,sunyi komai yadda ya dace kuma bisa tsari,sannan suka tabbatar da batun aure bayan dawowarsa,daga haka sai baffa yayi umarnin da a rufe taron da addu’ah bayan nan ya sallami kowa..+
Fitarsu a d’akin ya rage daga shi sai Hammad kawai dan haka a nan sai baffa ya samu damar yin magana da shi cikin nutsuwa,yayi masa nasiha mai shiga rai,bayan sun gama kasancewar duk maganar tasu a gaggauce ne ya tura aka kira masa Sabina don itama yayi mata bayani,ko da tazo bayan ya had’a su duka sai da yayi musu nasiha sosai,kafin yayi mata bayanin abunda ya faru a tak’aice,sunyi sallama da Hammad sannan baffa ya fita ya basu guri domin suyi sallama,lokacin ko da baffa ya fita a d’akin wani irin kallo Hammad ya shiga binta da shi kamar zai had’iyeta,,ita kuwa tun da baffa ya fita ya barsu bata iya d’agowa ba bare ta kalleshi ta gano a yanayin da yake ciki,duk da dai ta tabbatar itan tana cikin matsanancin farin ciki ta san ko shakka babu shima d’in haka yake,tayi nisa cikin duniyar tunanin makomarsu a yanzun da kuma gaba ta tsinto hannunta cikin nasa,a matuk’ar firgice ta d’ago ta kalleshi,kwantaccen murmushin da taga yanayi mata yasa ta sake kallon hannayensu ba tare data iya cewa komai ba ta kuma sauke kai k’asa
“My Lady..! Shin baza ki dago ki kalle ni ba..?? Am ur’s fa daga yanzun,kina da right na kiyi ta kallona har sai kin ji kamar ki maidani ciki dan…”
Siririyar dariya ta saki tana k’unshe baki da d’ayan hannun,shi kuwa gogan nan ya shagala da kallonta,sai da tayi mai isarta kafin yasa hannu ya d’ago chin d’inta yana tambaya
“My Lady.. Na fad’i wani abune da yake ba dai² ba..??”
Dakatawa tayi daga dariyar da take tana girgiza masa kai,murmushi ya sakar mata,zuwa wani lokaci ya saki ajiyar zuciya muryarsa cike da sanyi yana fad’in
“My lady..! Kafin na tafi..I have only one wish da nake son sanar dake…Ina fatan baza ki gagara yi min ba..!?”
D’if wuta ta d’auke mata jin lokaci guda ya ambaci tafiya wanda ita idan a son ranta baza tak’i ace ya zauna tare da ita fover a k’auyensu ba
“For da sake of Allah..! Ina rok’onki ki kasanace mai rik’e min amanar kanki,nd *ALK’AWARI* na akanki,i know tafiyan da zanyi zan jima ba tare da munga juna ba,buh ki kasance mai kiyaye kanki da amanar kanki dana bar miki,in sha Allah zan kasance mai rik’e miki amanar kaina,bazan tab’a manta *ALK’AWARIN* ki akai na ba,har naje na dawo..Kin ji..!?”
A hankali ta girgiza masa kai irin na bata so ba d’in nan hawaye suna sakko mata
“Ohhh! Ya rabb,,pleasee mana baby don’t cry,tun ban kai ga tafiya ba kina son yin kuka,kina son sawa kanki ciwo ne ko.?? U have to know tafiyan da zanyi nan kawai zan yi shi ne amma ba dan ina so ba,sai dan kasancewarta umarnin mahaifina nd idan na tafi na tabbata zan rayu ne cikin k’unci da damuwar rashinki,wannan dalilin ya sanya a kullum nake cewa,idan babu ke ba zan iya rayuwa ba,,,please my Lady kada ki nuna min haka dan Allah,domin kuwa yin hakan ka iya tarwatsa sauran farin cikin da zan tafi da shi.. Ina Son ki sosai,ba zan iya barin *ALK’AWARIN* ki akaina ba,ya kamata kisan da wannan..”
Fad’awa tayi jikinsa tamkar wacce mayen k’arfe ya fisga ta k’ank’ame shi,duk da yanayin da suke ciki hakan bai hana su jin ratsawar kyakykyawan electrification a cikin jininsu ba,murmushi ya saki mai sauti yana caressing bayanta a hankali yana sakin sanyayyun ajiyar zuciya,ita kanta ajiyar zuciyar take dan yadda take jin kamar kada ta rabu da jikinsa,yayin da kyakykyawa kuma daddad’an fragrance na scent’s d’insa da suke ratsata suna sake taimakawa jikinta wajen sanyaya duk wani gab’ar dake da aiki,luf ta sake yi a jikinsa har na tsayin mintuna kafin ya d’ago ta yana fad’in
“My Lady.. Ya kamata kiyi min izinin tafiya bcoz tafiyan da zanyi yana da nisa sosai nd lokacina ya kusa cika..”
B’ata fuska tayi cike da sakarci tana son yi masa kuka,cikin sauri ya janyo ta yana fad’in
“No..! Babe u know what..!?”
Da sauri ta furta
“Me ne..!?”
“Shi kenan ma barshi kawai..”
B’ata rai tayi tana k’ok’arin matsawa yayi saurin kamota yana murmushi
“Sorry.. Sorry babe..!”
“A’a ni dai ka sake ni,,kaga fa babu kyau yin haka..”
Murmushi ya saki mai sauti cike da zolaya yana kallonta
“Ohhh..! Dama babu kyau..!?”
Kallonsa tayi saurin yi itama da mamaki kwance a saman fuskarta tana fad’in
“Ehh! Ai nasan kaima ka sani..”
“Nooo! ni ban sani ba..”
Harar wasa ta masa sannan tace
“To d’an sake ni..”
“Na k’i.!”
Yayi maganar yana mak’ale shoulder,”uhmm” tace ba tare data sake yin magana
“Uhmm! What..!? Speak ur mind.. Kin san idan baki fad’a yanzun ba babu lokaci ko..?”
Gimtse fuska tayi cikin sauri ta fizge jikinta daga rik’on da yayi mata,da saurin shima ya sake kamota ya dawo da ita jikinsa,rik’on tsam yayi mata wanda yasa ta kasa kyakykyawan motsawa
“Pleasee..! Ka sake ni..”
“Idan nak’i fa..!?”
“Zanyi ihu kowa yaji..”
“Da gaske za kiyi ihu..??”
“Ehh! Mana..”
“Uhmm! Bismillah to yi maza ina sauraronki..”
Yana fad’a yana juyo da ita suna fuskantar juna still yana rik’e da ita tsam a jikinsa har k’irazansu na had’uwa,marairaice masa tayi kamar za tayi kuka tana fad’in
“Pleasee..! Ka sake ni..Kada wani ya shigo..”
Dai² fuskarta ya matso da tasa yana cewa
“I can’t.. Till kin yi ihu kowa yaji..”
Jin abunda ya fad’a,ba tare da zuciyarta ta kawo mata tunanin komai ba ta kalleshi bayan ta murgud’a masa baki can k’asa ta ce
“Ai dai kasan zan iya yi..!”
Gira ya d’age mata shima yana cewa
“Yeah! I know u can,,buh try kiga abunda zai faru..”
Sam bata san me yake shiryawa ba,dan haka kawai sai ta b’are masa baki cike da shagwab’a za tayi ihu,cikin azama shima ya fizgota kana ya had’e bakinsu guri guda……
Idonta ta waro waje tana kallonsa da matuk’ar mamaki ba tare data iya yin ko da tari ba,nd a hakan da suke a mak’ale da juna kowanne tunanin da ke damun kwakwalwarsa daban,,lower lip d’inta dake cikin bakinsa ya sake rik’ewa sosai,,a hankali ya shiga murzawa da lip’s d’insa cikin wani irin birkitaccen salo yana kallon tsakiyar idanunta,saurin lumshe nata idanun tayi cikin yanayin mutuwar jiki,bcos a yanayin da suke ciki bata jin zata iya jurewa kallon k’wayar idanunsa,a lokaci guda kuma tana had’awa da sauke sanyayyar ajiyar zuciya,shirun da yaga tayi ba tare data yi k’ok’arin k’wacewa ba ko son hanashi yasa shi cikin nutsuwa ya fara socking nasu gently nd calmly kamar wanda ta cewa tana buk’ata,salon da yake tafiyar da su shi kansa a lokacin bai san ya iya shi ba sai a yanzun,a hankali yaci gaba da socking nasu kamar ya samu lollipop,,ganin yadda tun a kiss notice d’insa sun fara k’ok’arin kwancewa har yana neman wuce gona da iri ne yasa tayi saurin rik’e masa hannu tana marairaicewa kamar za tayi kuka,wanda sai a lokacin ya fahimci a inda yake da abunda yake k’ok’arin aikata wanda yasa shi dakatawa sannan ya raba bakinsu,a hankali ya maida kansa saman wuyanta yaci gaba da sauke wahalallun numfashi,sai daya tabbatar ya saisaita nutsuwarsa buh har lokacin bai daina twitching breathe ba ya fara mata magana cikin muryar rad’a
“My Lady..! Allow me to go..”
Saurin bud’e ido tayi wanda ke bayyanar da tsoro k’arara a saman fuskarta haka nan muryanta duk da cikin shagwab’a ne amma ana iya rarrabe tsoron dake cikinta,tana kallonsa ta furta
“Ina..!?”+
“Lokaci yana tafiya..! Nd bana so mu samu sab’ani da Daddyna akan tafiya ta..”
Kai ta girgiza kawai ba tare data yi magana ba
“Kin amince na tafi..!?”
Nanma ta sake girgiza masa kai,a hankali ya saki numfashi sannan yasa hannu ya d’ago chin d’inta
“Thanks..Babe.! Zanyi kewarki..”
Sai ya d’ora mata peck a chicks,muryansa a k’asa yana kallon yanayin da fuskarta ta bayyanar mai cike da damuwa
“My Lady..! Do u have any problem with my trip..!?”
Girgiza kai tayi a hankali alamun babu,murmushi ya sake yi mata
“Ok..Shin kina da sak’on da zaki fad’a..!?”
Kai tsaye tace “A’a babu..”
“Toh..! Ni ina da shi..Kina son ji..?”
“Ehh!”
“Shi kenan..Ki kula min da kanki..!”
Runtse idanunta tayi saurin yi,dan yadda ta fara k’osawa da jin kalmar “Ki kulamin da kanki” a bakonsa sam tak’i k’arewa,ga shi ta rasa dalilin da yasa yake ta maimaitawar
“To ni kuma nace masa mene game da nawa amanar..??”
Bcos kalmar tasa tana tab’a mata zuciya a duk lokacin daya fad’eta,a hankali wasu irin pain tears suka gangaro mata sai tayi saurin kai hannu zata goge ya rigata,jin lallausan palms d’insa a fuskarta yasa ta sake lumshe ido hakan sai ya sake bawa sauran hawayen dake mak’ale damar zubowa saman kyakykyawar fuskarta
“Ohh..! Ya rabb! Ka ceci wannan bawa naka..!”
Yadda yayi furucin yasa ta saurin bud’e idanunta ta sauke su a kansa,one eyebrow ya d’age yana tambayarta a hankali ta girgiza masa kai,murmushin k’arfin hali yayi mata sannan ya mik’e while yana sake cewa da ita
“Please my Lady… Ina son ki kasance mai yawan tunawa *ALK’AWARI* na akanki,kamar yadda nayi miki *ALK’AWARI* ba zan tab’a barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matuk’ar muna a tare da juna,kema ki kasance kamar haka,bcos ina fatan nan da wani d’an lokaci ki tabbatar da hakan,bayan kin zamo mata a gare ni,,,ke kad’ai zuciyata ta amincewa my Lady,,saboda na tabbatar dake ne kad’ai zan iya rayuwa…Ki kula min da kanki..Ina son ki sosai abar k’auna..!”
Sabon kuka taji yana son sake taho mata,nan da nan ta tsaya cak a inda take,dakatawa yayi shima yana kallonta cikin muryan tashin hankali yana fad’in
“What’s happened..!?”
“Nothing..!”
“Kina so na yarda..!?”
Shiru tayi bata amsa ba,d’an matsowa yayi jikinta yana kallonta k’asa²
“Tell me..what’s..!”
“To ka d’an matsa,,sai na fad’a maka..”
“I can’t,,ki fad’a a haka..”
Girgiza kai tayi
“A’a bana iyawa. ”
“Me yasa..?? Kusancin mune bakya so..?”
Shiru tayi dan da kunya ta iya fad’a masa haka d’in ne,d’an murmushi yayi mata
“A haka kike so muyi sallama..?? Na tafi bana farin ciki..??”
Saurin girgiza masa kai tayi
“Ok.. Good..Tunda haka kike buk’ata..”
Ja baya yayi kad’an daga inda take while yana fad’in
“Na matsa my lady.. Hope hakan yayi miki..!?”
“A’a..!”
Da mamaki ya kalleta,a zuciyarsa yanaa fad’i
“A’a.!? Kamar yaya kenan..Me take nufi da A’a..??”
A fili kuwa kallonta kad’ai yayi ya jinjina kai
“Shi kenan tunda hakan bai miki ba..Lemme go..Ina tunanin idan muka kasance bama tare zaki fi haka sakewa ko..!?”
Sunkuyar da kai tayi k’asa can k’asan mak’oshi ta furta
“Nifa ba haka nake nufi ba..”
“Uhhuumm..! Yimin bayani to yadda zan fahimta..”
Yadda tayi k’asa da kai ta kasa d’agowa bare ta amsa masa yasa shi sake maimaitawa
“Am waiting.. Kimin bayani tunda ba abunda kike nufi ba kenan..Yaya ne kike nufi..??”
Bata d’ago ba bare ta kalle shi,cikin sigar son ta b’atar da maganarsa ta ce
“Halla tawa’adhniy.! annaka izha yunhiy..raja’ata ilayya..”
(Ina so kayi min ALK’AWARI cewa idan ka kammala abunda ya kaika..Zaka dawo gare ni)
Murmushin da bai san ya taho masa ba ya sakar mata
“Wane irin *ALK’AWARI* ne kike so nayi miki..Wanda zai tabbatar miki da cewa zan dawo gare ki.. Bayan wanda nayi a baya..?”
*”ALK’AWARIN* da yafi kowanne..!”
Yana murmushi yake tambayarta
“Wane *ALK’AWARI* ne kike zaton zai fi kowanne a gurinki..??”
Jimm tayi tana tunani,sake tambaya yayi amma tayi shiru ta kasa cewa komai
“Ok..Let us construct the most biggest pledges..”
Kallonsa tayi da alamun tambaya a fuskarta
“Me kenan..!?”
Yana murmushi yake bata amsa
“U want me to promised..Shi ne nake son cika miki burinki..Kafin na tafi..Hope zaki kasance cikin farin ciki a duk lokacin da kika tuna ni..”
“To amma..”
“Stop..lemme preceed..”
Bakinta taja ta b’ame tana ci gaba da kallonsa,rufe idanunsa yayi a hankali kamar mai jin bacci zuwa wani lokaci kuma ya furta
“Do u have a razor.!?”
“Ehh!..”
Ta bashi amsa kai tsaye Bcos bata san me zaiyi da shi ba daya tambaya
“Uhhuumm..! Can u help nd brought it for me..Please..!??”
Kallonsa ta d’anyi sannan ta mik’e tana niyyar fita,har taje bakin k’ofa yayi magana
“My lady.. And cup too..Please.!”
Ficewa tayi cikin sauri tana amsa masa,mintuna biyu da fitarta sai gata ta dawo,da sallama ta shigo d’akin tana b’oye hannunta a baya,murmushi ya sakar mata kafin ya mik’a mata hannnsa alamun ta bashi,sak’e dunk’ule hannu tayi tana kallon gefe
“To wai mene za kayi da su.??”
“Give it to me please,,koma mene zanyi yanzun zaki gani..”
Jikinta a sanyaye ta mik’a masa tana kallonsa,saboda ita dai jikinta yana bata lallai ne zai yi wani abu daban,sabuwa fil d’in razor data masa masa da k’aramin cup irin na cikin dinner set,ko daya karb’a idanunta na kansa har ya fara k’ok’arin fito da razor’n daga cikin shell,ko daya zaro a hankali taga ya bud’e palms d’insa na dama ya d’ora ta a kai yana saita hannun a kan cup d’in,,zuciyarta tsabar fargabar ganin abunda yake shirin aikatawa ji take kamar zata fito waje dan tsoro,cikin azama ta isa gabansa tun kafin ya kai ga yanka hannun tuni har ta rik’e shi idanunta suna fidda hawaye
“Mene ne wannan d’in kake shirin yi..??”
“Ohh! Babe ba wani abu bane zanyi,sake ki gani..”
“A’a.. Ni dai gaskiya ban yarda ba..”
Murmushi yayi mata yana fad’in
“Ok.. Naji *ALK’AWARIN* ne bakya so.. Ko har kin fasa..!?”
“To haka dama ake yin *ALK’AWARI..??* Ni ai ba wannan nace ina so ba,idai dan wannan ne ni kam na yafe..”
“Ni kuma kinga ina so ba,nd bana tunanin zan iya hak’uri na yafe..”
Marairaicewa tayi kamar za tayi masa kuka tana kallonsa
“Please..Ni dai na yafe,,kada kayi..Ka ji..?”
Murmushi yayi mata sannan ya janye hannunta data rik’e shi,yana kallonta fuskarsa d’auke da fara’a irin wacce kafin ta goge sai an d’auki lokaci,taga ya sake saita razor yana shirin yanka jikinsa,saurin rufe idonta tayi tana cije baki,tsakiyar tafin hannunsa yayi cutting kafin kace me tuni har jini ya fara fita,hannunsa ya zubawa ido yana murmushi kafin ya kamo hannunta yasa mata razor yana fad’in
“Ur turn my Lady..!”
A hankali ta bud’e ido tana kallonsa,irin kallon da yaga tana binsa da shi sam baiyi kama dana wanda zai iya yanka jikinsa ba,murmushi yayi mata can k’asa yana fad’in
“My Lady.! Ina son ki,ya kamata ki san cewa shi so da kike gani tamkar tab’o ne,adadin yadda ka yi tsalle ka fad’a a cikinsa adadin haka ne zai baka wahala a lokacin da ka tashi fitowa,,ina fatan mu rik’e juna da amana har abada.Tare da fatan d’orewar farin cikin mu..”
Rufe idonta ta sake yi a hankali tana matse rezar a hannunta d’aya,sam Hammad baiyi zaton zata iya yin hakan ba sai ganin jini kawai yayi yana d’igowa daga hannunta,cike da tsantsar mamakinta ya kamo hannunta,tafin hannun ya bud’e ya zare rezar dake ciki sannan ya had’e hannayensu guri guda,jinin dake tsatstsafowa ta cikin hannayen nasu yaci gaba d’iga cikin kofin a tare,ajiyar zuciya ta saki mai k’arfi cike da k’arfin hali ta bud’e baki duk da idanunta suna a kulle amma bata damu ba,bcoz burinta a lokacin shi ne ta iya fada masa abunda take ji game da shi
“A yau na shirya tsaf saboda ina son na k’ara bayyana maka matsayin ka a gare ni,tabbas YAYANAH zuwan ka gare ni yasa ka zamo min wani jigo na d’orewar farin ciki a zuciyata.A kullum tun daga lokacin da muka fara had’uwa da juna fuskar ka ce kad’ai abunda nake kallo na samu farin ciki.Kada ka damu da rashin bayyana maka gaskiyar *AL’AMARI* na da banyi ba tun a baya,,amma a yau kuma a ranar da nake jin babu dad’i sakamakon rabuwar da zamuyi yasa ni jin bazan iya sake b’oye maka wannan sirrin ba,shi yasa kai tsaye nake sanar da kai abunda ke k’unshe cikin zuciyata,,duk da bawai ina cikin yanayin jin dad’i bane,ina son furta maka cewa INA SON KA! INA SON KA!! INA SON KA.!!!”
Wani irin murmushi yake saki mai tattare da shauk’in jin irin kalaman da take masa amansu,tunda yake tare da ita kusan sai yace yau ne rana ta farko da yaji kalamai makamantan wad’annan sun fito daga bakinta,,shin shi kuwa me ya kamata yayiwa Allah baya ga yayi ta godiya a gare shi bisa tarin ni’imomin da yayi masa.!? K’ura mata idanunsa yayi yana kallo kamar bazai daina ba,yana shirin sake yin magana sai ga Hamudan ya shigo cikin d’akin kamar wanda aka cillo da fad’in
“Yaya wai baffa yace lokaci yana k’urewa.. Kuma wai an fara kiran sallah..”
Saurin dawowa hayyacinsu suka yi,a hankali Sabina ta janye hannunta dake mak’ale a nasa ta matsa gefe kad’an tana k’urawa tafin hannun ido,sai daya kalleta sannan ya amsawa Hamudan
“Ok.. Kace da baffa yanzun zan fito..In sha Allah..”
“Toh” ya amsa sannan ya fice a guje dan isar da sak’o,mik’ewa tayi tsaye ta wuce gaba,tana niyyar fita ya dakatar da ita ta hanyar kiranta,cak ta tsaya sai dai bata yarda ta juyo ba,handkey dake aljihunsa ya zare a sannan ya zagayo ta gabanta,a hankali ya kamo hannunta ya shiga d’aure mata inda ta yanka,yana gamawa ya juya zai bar wajen ta rik’o masa hannu,a hankali ya juyo yana kallonta,d’an kwalin dake kanta yaga ta zame sannan ta d’ago hannun tana d’aure masa had’e da yi masa murmushi,shi kam kallonta kawai yake dan idan da ace labari ne ake bashi tsaf zai musanta,amma sai gashi ya gani a zahiri,,saida suka sake d’aukan mintuna ak’alla uku suna ma juna wani irin kallo mai kama dana *BANKWANA* irin na har abada,kafin suka fito kowanne sai b’oye hannu yake yana gudun aga abunda yake jiki,,a lokacin kusan zan iya cewa ya wuce a kira yanayin da yamma dan yadda Maghreb sosai ya kawo jiki,ko data raka shi iya karta zauren gidan ta tsaya suka sake yin sallama a karo na sau babu adadi ya barta akan sai yazo ziyartar su,,daga nan ya juya ya fita yana waiwayenta,,itanma kasa barin gurin tayi har sai data ga sun d’auki hanya,duk da haka bata hak’ura ba,sai data sake mak’alewa a zauren gidan tana lek’ensu,ba ita ta koma cikin gida ba har sai data daina hango su,a lokacin ne kuma wani irin kuka mai tattare da k’unci ya taho mata dan yadda take jin jikinta na bata kamar shi kenan daga wannan lokacin sun rabu kenan bazata sake ganinsa ba,da gudu ta koma cikin gida duk da yadda take k’ok’arin had’iye kukan,tun kafin ta kaiga k’arasawa tuni har kukan ya kwace mata.
A b’angaren su Hammad kuwa lokacin daya fita daga zauren,zazzaune ya tarar da su baffa suna jiran fitowarsa,lokacin ko kafin suyi sallama sai da yayiwa dattawan da suke tare alkhairi,sannan ya buk’aci ganin waliyyansa a keb’e,,yayi musu godiya akan alkhairin da suka gwada masa sannan suma yayi musu hasafi fiye dana sauran sannan suka yi sallama da shi,a lokacin kuma zak’in alkhairinsa yasa d’aukacin mazauna gurin suka shiga binsa da addu’o’in fatan alkhairi da sauka lafiya.Sannan suka d’auki hanyar raka shi,sun fara tafiya sai ya waiwayo ya kallo k’ofar gidan kamar wancan lokacin daya gabata cike da k’awa,,a lokacin tana tsaye tana hangensu,,shima ko daya kallo gurin zuciyarsa cike take taf da fatan ubangiji yasa idan ya tafi nan da wani d’an lokaci ya dawo zuwa ga abar k’aunarsa sannan ya juya suka ci gaba da tafiya,yayin da yake jin zuciyarsa cike da wani irin matsananciyar fad’uwar gaba,hannunsa ya d’ora dai² saitin zuciyansa ya dafe yana karanta duk addu’ar data zo bakinsa,a haka har suka fito titi inda yake barin motarsa,har bakin mota sai da suka rakashi,backseat na motan ya bud’e ya fito musu da kayan dake ciki,sannan ya dank’a sak’on *ABAR KAUNARSA* a hannun baffa,duk dama dai da fari kamar baza su karb’a ba,amma ganin irin magiyar da yake yi sai yasa suka karb’a,suka yiwa juna godiya sannan suka yi bankwana ya kama hanyar tafita suma suka kama hanyar komawa cikin k’auyensu..
Tun da ya daidaita kan motarsa a bisan asphalt (kwalta) ya shiga shek’a gudu ba na wasa ba,kasancewar titin babu yalwar motoci bare cunkoso yasa kafin awa guda sai gashi ya iso cikin gari,lokacin daya shiga gida tun kafin yayi parking sai daya fara bin carports d’in da kallo,cike da farin cikin samun nasarar ganin babu motar Daddy yayi hamdala sannan ya gyara parking ya fito,,a gurguje ya haura sama ba tare daya tsaya bin d’akin Mammansa ba dan lokacin daya fito bai tsaya sallah a wudil ba ya taho,nd yanzun kuma tuni aka idar da sallah,bai iske kowa a parlor’n ba dan haka direct ya wuce bedroom d’insa,tun daga shigarsa d’akin ya tabbatar da lallai akwai wanda ya shigo,dan yadda ya fita ya bar shi ba haka d’akin yake ba a yanzun,saman resting chair daya jibge outfit,luggage’s da duk wasu muhimman kayan da zai tafi dasu ya sake kalla,babu komai a gurin ko ina a tsaftace kamar ba’a shigo ba,hatta da handkey bai samu a yashe a gurin ba,gefe inda luggage’s d’in suke ajiye ya sauke idanunsa a hankali ya saki ajiyar zuciya sannan ya tasamma hanyar toilet,a gaggauce yayi wanka bayan ya d’auro alwala ya fito,sai daya fara gabatar da sallah sannan ya fara shiri,within a few minutes tuni har ya kammala,landline dake cikin d’akin yayi kira dashi,bayan an d’auka ya sanar da mai maganar yazo ya fitar masa da kayansa,cikin girmamawa aka amsa masa sannan ya ajiye ya fita,bedroom d’in Mamma ya wuce,a lokacin itama bata jima da idar da sallah ba,tana zaune saman pray mat tana addu’ah ya shigo da sanyin jiki,daga gefenta ya samu guri ya zauna yana jiran ta idar suyi sallama,a gaggaucen itama ta k’arasa addu’o’in sannan ta waiwayo gefen da yake
“Son..Tafiyar ta tashi ne..!?”
A hankali ya jinjina kai sannan ya bud’e baki da kyar ya ce
“Ehh! Mah..”
“To..! Sai muce Allah ya tsare,ya bada nasara cikin abunda za’a je nema,,ubangiji ya k’ara kare min ku baki d’aya,,sai dai ina so a koda yaushe nasihata ta kasance itace abun tunawarka,a kullum ina maka nasiha akan ka kasance mutum na gari wanda ba iya mu da muka haifeka ba,al’ummah gaba d’aya za tayi alfahari da kai,,ka kasance mai kiyaye dokokin Allah a kanka,duk abunda kasan ya sab’a dokar mahaliccinmu ka zama mai guje masa,,sannan kada ka manta irin rayuwar da kayi a baya,wacce dukaninta kayi tane a cikin yarenka,k’asar ka kuma cikin jama’arka duk da akwai wad’anda addininmu ya bambanta da su amma ba kamar inda zaka je bane,yanzun a tafiyar da zaka yi zaka had’u ne da jama’ar da fiye da rabinsu addininku ya bambanta,,sab’on Allah a gurinsu basu d’auke shi a bakin komai ba,ina horonka daka kasance mutum mai tsare kansa daga dukkan abunda kasan ubangiji zai yi fushi da kai,,,a k’arshe ina sake yi maka nasiha daka kasance mai yawan jin tsoron Allah,sannan ka kiyaye lokacin ibada,in sha Allah nasara tana tare da kai..Allah ya dawo min da kai lafiya..!”
Jikinsa yayi mugun sanyi da nasihar Mamma,a hankali sai ya bud’e bakinsa
“Ameen Mah.. Na gode sosai da nasihar ki,,,in sha Allah kamar yadda kika sanni,zanci gaba da kasancewa haka har k’arshen rayuwa,ina fatan za kici gaba da sani cikin addu’o’inki,,kamar yadda nake yi miki fatan Ubangiji yayi miki tsayin rai mai amfani..”
Tafiya dai kamar Hammad bazai yi taba a wannan daren dan yadda aketa sallama,,lokacin ko da zai fito tare suka fita duka gidan,Mamma,Bassam da BADRA suka masa rakiya har airport Daddy ne dai da baya garin,,duk abuda za’ayi a kan idanunsu aka gama masa komai aka fara kiransu,jikinsu duka a mugun sanyaye ya rungume y’an k’annensa sannan ya juya ya tafi,a tak’aice dai suma kansu su Mamma’n basu suka koma gida ba sai da suka ga shigarsa cikin ad’d’a’irah (jirgi) sannan suka koma suna masu binsa da addu’o’in fatan samun nasara,haka nan jikinsu duk a sanyaye..
Lokacin daya tsinci kansa a gaban jirgin da zai nisanta shi da k’asarsa a karo na farko a rayuwarsa tun bayan fara soyayyar sai ya tsinci kansa cikin wani irin kasalan da bai tab’a tsintar kansa a cikinsa ba,duk da ba yau ne karon farko daya fara shiga jirgi ba,amma yau sai yake jinsa a damuwa,dan haka da kyar ya shiga d’aga k’afafunsa ya fara taka stairs d’in jirgin,yana tafe yana waiwayen bayansa ma’ana k’asarsa yayin da yake jin kewar tafiyar da zaiyi ya bar duk wani abu nasa mai muhimmanci,lokacin daya je k’arshen matakalar tsayawa yayi a bakin k’ofa ya kasa shiga,ak’alla sai daya d’auki tsayin minti guda yana kallon k’asa ba tare daya wuce ciki ba har sai da wanda yake bayansa yayi masa magana sannan ya d’auke idanunsa a hankali ya juya zuwa ciki,shigarsa a cikin jirgin babu jimawa ya fara duba seat number d’insa yana tafiya yana duddubawa har ya kaaiga inda idanunsa suka nuna masa 9c,hamdala yayi ga ubangiji sannan ya matsa,yana niyyan wucewa ya zauna sai yaji an tab’a shi ta baya,cikin nutsuwarsa ya waiwaya bayansa cike da son ganin waye ya tab’a shin,idanunsa suka yi arba da……
*Hak’ik’a rayuwa da mutuwa duk nufin Allah ne akanmu,shi yake da ikon yanke hukunci game da rayuwar mu duka,tsara labari ba komai bane face nishad’i,ku sani cewa dan wani ya mutu ko wani ya rayu ba abune daya kamata muyi magana akansa ba,tunawa da cewa lallai wata rana muma zamu mutu k’arin imani ne kamar yadda kissar Annabi (S.A.W) da sahabbansa ta zo ku karanta domin na tabbata zaku amfana,,,wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune tare da Sahabbansa,sai ya fara tambayar su d’aya bayan d’aya,sai ya fara da Sayyidina Abubakar Assiddik’ yace:”Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?” Sai Sayyidina Abubakar yace:Abunda na fi so a duniya 1-Zama a gaban ka,2-Kallon ka,3-Ciyar da dukiya ta gare ka,,Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar bin Khaddab,Manzon Allah (S.A.W) yace:”Yaa Umar! Me ka fi so a duniya?” Sai Sayyidna Umar yace:Abunda na fi so 1-Ayi min umurni da kyakkyawan aiki ko da a b’oye ne,2-A min hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,3-Da kuma fad’in gaskiya ko da tana da d’aci.Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman bin Affan yace masa: “Yaa Uthman! Me kafi so a duniya?” Sai Sayyidna Uthman d’an Affan yace:Abunda na fi so a duniya,1-Ciyar da abinci ga mabuk’aci,2- Yad’a sallama,3-Yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya koma ta wajen Aliyyu bin Abiy ‘Daalib,yace masa: “Yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?” Sai Sayyidna Aliyyu yace: abunda na fi so a duniya,1-Azumi a lokacin rani,2-Karrama bak’o,3-Yak’ar abokan gaba da takobi.Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari,ya ce masa: “Yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya? Sai Abaa Zarri yace:Abunda na fi so a duniya,1-Yunwa,2-Jinya,3-Mutuwa.Sai manzon Allah (S.A.W) yace:”Saboda me yasa kake son su?” Sai Aba zarri yace:1-Ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,2-Ina son jinya don zunubi na yayi sauk’i,3-Ina son mutuwa saboda saduwa da ubangiji na.A wannan lokacin sai ga Mala’ika Jibrili (A.S) ya saukko zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ),sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku,1-Isar da sako,2-Bayar da amana,3-Son nakasassu.Daga fad’in haka kuma sai ya tashi zuwa sama sannan ya saukko a karo na biyu yace Allah mad’aukakin sarki yana karanta muku sallama,hirar manzon Allah da sahabbai tayi dad’i,harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku,1-Harshe mai ambatonsa,2-Zuciya mai tsoronsa,3-Jikin da aka jarrabce shi da balaa’i kuma yayi hakuri.Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah,, dan haka y’an uwana kada ku manta da Addu’o’i guda uku a cikin sujjadarku..1-“Ya Allah ina rok’on ka kyawawan halaye,2-“Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace,3-“Ya Allah mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka..Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne.Sannan lada ku manta Ubangiji (S.W.T) ya fad’a a cikin littafinsa mai tsarki cewa:”Shi ne wanda ya halitta mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku,ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawun aiki,shi ne mabuwayi,mai gafara.”(Suratul Mulki aya ta 2)..Dan haka hak’uri akan komai na rayuwa shi ne mafi alkhairi a garemu,,Allah ya datar damu duniya da lahira..Ameen.👏*
_Tunatarwa ne gare ku masoya..💞_
••••••••••
A wannan wayewar gari kusan abunda ya afku a daren jiya ba iya garin Wudil kad’ai ya tab’a ba,dan zamu iya cewa garuruwa da dama sun samu afkuwar iftila’i iron wannan,sai dai babu inda akayi rashin da akayi kwatankwacin na garin wudil,saboda nasu lamarin shi ne akan gaba a dalilin munanarsa,daya zama akusan duk hanyar da mutum zai ratsa ta cikin wannan yanki na *KAUSANI* d’ai²kun unguwanni zuwa k’auyuka ne mutum zai shiga ya fito ba tare da yaji labarin anyi mutuwa ko an samu jikkata ba,wani gidanma tun kafin ka shiga zaka jiyo koke²n ahalin gidan a sakamakon rashin da suka yi,,yayin da wasu ke kukan mutuwa wasu kuwa nasu kukan ya ta’allak’a ne dalilin rasa muhallinsu da suka yi,haka nan wasu kuma wa rasa dukiyoyinsu da suka yi ya kawo faruwar hakan.
A cikin k’auyen su *SABINA* ma hakan ce ta kasance,,sai dai su nasu garin tun wayewar gari yake shiru,baka jin sautin komai face k’ugin manyan Van’s zuwa caterpillars,haka nan da zarar ka nufo k’auyen tun daga farkon sa zaka fara cin karo da rufin gidaje wanda iska ta d’age daga muhallinsu tayi watsi da su,wani gurinma kana kallo ba sai ka sake ba saboda yadda al’amarinsu ya munana a daliliniftila’in daya faru kusan a nan d’in nema yafi afkuwa.Can daga gefe kuwa motoci ne na y’an jaridu,jami’an tsaro wanda suke da alhakin kare faruwar had’ura,sai kuma wakilan gidan gwamnati,,duka ilahirin jama’ar garin da suke raye an tare su guri guda,majinyantan kuwa tuni har an nufi asibiti da su domin basu taimakon gaggawa,,yayin da har lokacin y’an jaridu suke kan d’aukan rahoton abunda ya faru,har ma da aikin zaro ragowar corpses (gawarwaki) da k’asa ta binne,,,ahalin gidan su Sabina zaune gefe guda sunyi jigum²,fuskokinsu d’auke da damuwa,alhini gami da tashin hankalin da zaisa mutum fahimtar suna d’aya daga cikin ahalin da sukayi rashi a wannan yankin,,idanunsu sunyi wani irin jajir saboda tsabar kuka,damuwa mai girma bayyane k’arara a fuskokinsu,da yasa a wannan lokacin ma ko magana babu mai iya yinta a cikinsu saboda al’amarin ya matuk’ar girgiza su ba kad’an ba.
Yinin ranar sur aka shafe ana aikin ciro gawarwaki amma ba’a gama ba,wanda a k’arshe saboda hak’ar k’asa da akayi ya fara zurfi ya janyo k’asa taci gaba da k’ok’arin fara amsawa,wannan dalilin yasa akan dole aka dakatar da hak’ar k’asar.Daga nan aka tattara matattu da rayayyu a manyan Van’s sai sauran y’an kayayyakin su da suka tsintsinta akayi hanyar cikin gari da su.
A ranar bayan an kawo su aka wuce da gawarwakin zuwa asibiti domin sake tantancewa,,ak’alla sai da aka d’auki kwanaki biyu tsakani kafin a bawa ko wane ahali tasu gawar,bayan anyi musu sutura aka sallame su a babban filin gidan sarauta sannan aka kaisu gidanjensu na gaskiya,,cikin wad’anda aka rasa sun had’a har da Baffa,,Baban Sabina kuwa da Baban LADO duka suna kwance a gadon asibiti,sakamakon karaya da suka samu,hakama sauran mutanen gidan da dama sun samu raunuka,,Bayan y’an kwanaki da faruwar wannan *AL’AMARI* duk da gwamnati ta killace al’ummar wannan yanki ta bawa sauran jama’ar da suke raye tallafin muhalli a cikin mabambanta daga unguwannin dake garin kano,,wanda a cikin wad’annan jama’a ya had’a har da ahalin su Sabina,inda suka samu matsuguni a cikin unguwar *Kawo* dake hotoro.Gaba d’aya faruwar *AL’AMARIN* ya zo musu ne a bazata mai tare da wani irin chanjin rayuwa mai tattare da damuwa a sanadiyyar rasa elder da suka yi a wannan zuri’ah..+
*FLORIDA STATE,U.S.A..*
Suna fitowa daga *Pura bean coffee company* direct hanyan komawa skul suka d’auka,suna tafe suna hira yayin da a b’angaren Hammad kuma yayi shiru yana sauraren su kasancewarsa dama ba gwanin da za’a jishi yana magana ba,,tun kafin suyi nisa da inda suke ya fara jin jikinsa yana yi masa babu dad’i,babu wanda ya fad’awa irin yanayin da yake ciki,a haka suka ci gaba da tafiya cikin dauriya har suka shigo cikin skul ba tare da yayi magana ba,a lokacin ne kuma jikinsa ya sake d’aukan wani irin sanyi,kafin a hankali kasala ta fara saukar masa,jikinsa ya sake k’ank’amewa cikin blazer dake jikinsa dan dama yanayin garin akwai sanyi,,yayin da Sadeeq da Sultan suke ta fira abunsu cikin nishad’i ba tare da sun kula da yanayin da yake ciki ba har suka shigo room d’insu,wanda rashin kulawa irin nasu yasa ko da suka ji yayi irin wannan shirun hakan bai sa sun fahimci abunda ke faruwa ba,inda bed d’insa yake ya nufa,da baya ya zame ya kwanta while k’afafunsa na k’asa,ba taare daya iya cire ko da blazer d’in jikinsa ba bare takalmansa ya runtse idanunsa,,ajiyar zuciya ya shiga jerawa irin wacce sai mutum na cikin tsananin damuwa ko yayi kuka,haka nan yake jin jikinsa na sanar masa lallai akwai abunda ke kan faruwa da wani na jikinsa,to amma abunda bai sani ba shi ne,da Daddy’nsa ne,Mamma,Bassam ko kuwa BADRA..?? Ne ke cikin mawuyacin yanayi aka kasa sanar masa,duk ya kasa fahimta,,,cikin k’ank’anin lokaci damuwa ta sake rufe shi,kallonsa Sultan ya juyo yayi yana shirin yi masa magana ya ganshi cikin wannan yanayin da sauri ya nufo inda yake yana fad’in
“Broah.! What’s wrong..!?”
Bai iya d’agowa ba bare ya samu damar bashi amsa,shima Sadeeq cikin sauri sai ya matso kusa da su yana kallonsu while yana fad’in
“Dude what’s happen..??”
Sultan ne ya waiwayo yana kallonsa da fuskar damuwa
“Nima dai abunda ya bani mamaki kenan,yanzun fa muka shigo dukanmu,yanzun kuma na ganshi kwance,shi ne nima nake tambaya amma yak’i magana..”
Kallon mamaki duka suka tsaya yi masa kafin Sadeeq ya tambayae shi
“Man.! Wai mene ne hakan,mufa kana neman samu a damuwa.! Ya kamata ka fad’a mana abunda ke faruwa.”
Da kyar ya mik’e ya zauna har lokacin idanunsa a d’an rufe saboda yanayin da yake jin jikinsa kamar anyi masa mahaukacin duka,,ba tare daya amsa musu ba ya mik’e cike da rashin kuzari ya d’auki waya,Number Daddy ya fara kira,yadda wayan ke sounding a haka shima zuciyarsa ke bugu tsoro fal ransa da taraddadin abunda zai jiyo idan an d’auka,muryar Daddy ya jiyo cike da k’oshin lafiya yana magana ta cikin wayar,sai daya sake sakin ajiyar zuciya kafin yayi masa sallama,bayan ya amsa sannan ya gaida shi cikin sanyin murya,duk da yanayin da yaji Daddy ya amsa masa gaisuwa ya bashi k’warin guiwan fahimtar lafiya k’alau suke,amma bai fasa tambayar lafiyarsu ba,take Daddy ya sake tabbatar masa da lafiyarsu,ajiyar zuciya ya sauke,suka d’an tab’a hira dan dama sun kwana biyu basu yi magana da shi ba,cikin tsautsayi har za suyi sallama a lokacin sai ya sakowa Daddy batun yana son zuwa ya duba su saboda yana jin kewar gida sosai,ko bari Daddy baiyi ya kai k’arshe ba ya tari numfashinsa yana fad’a masa ya bari kawai ba sai ya zo ba,gara yayi zamansa ya maida hankali sosai kan karatunsa,idan dan ta sune a duk lokacin da suka so zasu zo su ziyarce shi,amma shi d’in yayi zamansa sam bai ji dad’in hukuncin da Daddy yayi masa ba,a ganinsa yana tunanin kamar bai dace ace yayi masa haka ba saboda yadda duk abunda Daddy’n yace yayi yana kamanta yi masa biyayya,haka nan yayi ta tunanin dalilin da yasa Daddy’n ya hana shi zuwa. Damuwa fal ransa suka yi sallama da Daddy,bayan ya katse kiran ya kira Mammansa,sun gaisa da ita cike da girmamawa itama ya sanar da ita damuwarsa da duk yadda suka yi da Daddy babu jimawa,,har ga Allah duk da a gabanta suka yi wayar bata so akace Daddyn ga hana shi zuwa ba,saboda ko itama tana jin kewar ganinsa,buh duk da hakan sai tayi ta kwantar masa da hankali akan yayi hak’uri tunda Allah yasa suna yin video call lokaci zuwa lokaci,kada ya sawa kansa damuwa in sha Allah zata yiwa Daddy maganar idan yaso sai suzo su duba shi a skul d’in,godiya yayi mata sannan suka yi sallama ya ajiye wayar,,sake lumshe idanunsa yayi dai² lokacin Sultan ya gama cika da abunda yayi musu,a fusace ya juya ya bar wajen dan ganin rainin hankalin daya shuka musu,shima dai Sadeeq juyawar yayi ba tare daya sake cewa komai ba ya bar wajen.
Bayan barinsu a kusa dashi,ajiyar zuciya yaci gaba da saukewa,lokaci guda kuma tunaninta ya fad’o masa a rai,tabbas yana jin kewarta tun ba yau ba,kuma saboda dalilinta nema ya damu da son zuwa 9ja,badon komai ba sai dan yaga a halin da take ciki yanzun,,sai gashi tun ba’a je ko ina ba daga fad’awa Daddy har ya datse masa hark’alla ta hanyar hana shi zuwa,,duk da ba wannan ne karo na farko daya shirya yin tafiyar ba,amma rashin barinsa sosai yasa shi jin babu dad’i,saboda kusan sau uku kenan yana niyyar zuwa uzurori suna gifta masa wanda ala dole yake hak’ura tunda uzurin ya zame masa wajibi ne idanma baiyi ba babu wanda zai masa,sai gashi a lokacin daya gama sa rai a karo na k’arshe da yake nufin zuwan saboda ganin ya samu dama Daddy ya nuna k’in amincewarsa,,a wannan daren kam dan dai ana cewa bacci b’arawo ne da Hammad kam sai yace bai san da wane lokaci ne ya runtsa ba,bcos gaba d’aya ya rasa nutsuwar sa a dalilin tunani da yayi ta fama da shi.Tun daga wannan rana kuma sai ya zama ko da wasa bai sake shirin zuwa ba dan Daddy yace masa matuk’ar ya taho da saninsa ko babu zai b’ata masa rai,shi yasa ala dole ya yakice batun zuwan bai sake tayar da shiba,haka nan ko da yaga suma d’in basu jeba sai yak’i bin ba’asin dalilin k’in zuwan nasu,,a haka ragowar lokacin da yayi masa saura yaci gaba da tafiya…
*ONE YEAR LEAVE…*
*NIGERIA.*
Kimanin shekara guda kenan da faruwar al’amarin,wanda tun a bayan afkuwarsa a lokacin da gwamnati ta shiga lamarin su,sai ya zamanto bata yi watsi da su ba,bayan tallafin muhalli data bawa ko wane ahali,sannan ta samawa da dama daga cikinsu guraren aiki duk da kasancewarsu basu yi karatu ba,ta hanyar yi musu adalci a matsayinsu na y’an k’asa ta tallafawa rayuwarsu,,sannan batun k’ananun yara kuma ta d’auki nauyin karatunsu ta hanyar rarraba su makarantu musamman wad’anda ke cikin karatu kafin afkuwar al’amarin.
Tun bayan dawowarta daga extra lesson saboda gabatowa jarabawar S.S.C.E da take shirin zanawa take zaune cikin d’aki ta tusa litattafanta kamar tana bitar abunda ke ciki,uban tagumin data rafka shi ne kad’ai abunda mutum zai kalla yayi saurin gane hankalinta sam baya tare da abunda idanunta ke kali,,zuwa wannan lokacin tunaninsa ya jima da cika nata zuciya,y’an guntayen hawayen da suka ziraro mata a sakamakon tunawa da tayi babu ta hanyar da zata san ya dawo yasa takai hannu saman fuskarta ta goge hawayen,dai² lokacin Inna ta sawo kai tana shigowa cikin d’akin,akan idanunta duka taga komai daya faru,har tayi kamar zata fita kuma zuciyarta cike da tausayin y’ar tata ta k’araso ta zauna kusa da ita,har ta zauna Sabina bata sani ba sai data dafa kafad’arta sannan ta d’ago idanunta a hankali,girgiza kai Innar tayi cikin nuna alhini da damuwa tana cewa
“Haba Sabina..! Haba..!! Yanzun ace ke kenan ba zaki ji fad’an da nake miki ba,me yasa ne jam kike son komawa haka,sai kace ba musulma ba,ace ko wane lokaci idan kika zauna sai kin zubar da hawaye,,shin me yasa ne kam bakya ji..!? Na sha fad’a mikifa addu’ah itace abunda yafi kamata mu duka muci gaba da yi,in sha Allahu sai kiga ya dawo ya same ki kamar yadda ya tafi,ubangiji shi ya k’addara faruwar komai dan haka idan kin fad’a masa zai ji rok’on ki har ya biya miki buk’atun ki,,muyi ta addu’ah kinji,kada kice kin gaji,da yardar Allah sai kiga komai ya wuce tamkar ba’a yiba..”
Kanta ta sunkuyar k’asa tana sake share hawaye,kan nata Inna ta shafa sannan ta kamo hannunta ta rik’e
“Yanzun dai abunda nake so dake shi ne,kiyi k’ok’arin ragewa kanki damuwa,kina addu’ah nima ina taya ki,da yardar Allah komai zai zama tarihi..”
“In sha Allah Inna zanci gaba da yi..”
“Yawwa to..! Ko kefa ai gara ki saki jikin ki,ubangijin daya raba ku wata rana shi ne zai sake had’a ku da yardar sa..”
K’asa² ta amsa da “Allah yasa.”
Sai da Inna tayi mata nasiha sosai kafin ta fita ta barta tana shirin tafiya makarantar islamiyya tunda Allah yasa sun sake samun ci gaba..
A gefen Hammad kuwa,tun kwanaki uku da suka gabata suka dawo k’asar tafe da d’umbin nasarori,sai dai rashin samun lokaci da yasa bai tafi tun a washe gari ba kasancewar saukar dare suka yi,,yau kam daya k’udurcewa ransa komai zai faru sai dai ya faru,yasa cikin shauk’i gami da begen abar k’aunarsa,dan tun daya tashi yake ji a ransa bazai iya jiran rana ta fad’i ba tare da yaje ya gano su ba,tun bama baffa ba daya d’auke shi matsayin d’a,,kyakyatawan murmushi ya saki yana shafo mustache d’insa da hutu ya sa ya sake cika da duhu,a fili ya furta
“Baffa in sha Allah ina hanyar zuwa na ganka.!”
A hanzarce yayi shirin tafiya cikin wani d’anyen baby bazin african getzner mai kalar coffee da aka yiwa aiki da milk d’in thread,ya kawo hula da ake cema tangaran ya murza,banda k’amshin dad’ad’an turarukan sa a lokacin daya fito babu abunda ke ratsa hanya,haka nan fuskarsa cike da annurin zaije ga abunda yake matuk’ar k’auna ya fito,ko da yasa aka shigar masa da kayayyakin da yayi musu tsaraba a sabuwar motar da Daddy ya siya masa k’irar Highlander tokunbo full option,sai yayi ma Mamma sallama kana ya fice a gidan,sai daya biya ya d’auki Sultan a gida kafin su d’auki hanyar garin Wudil,,tafiya suke a motan ba tare da wani hira ba sai cool music dake tashi,tunda suka d’auki hanya haka nan sai yake ganin tafiyar kamar an k’ara mata nisa,ko kuma dai dan ya jima bai zo bane yasa yake ganin hakan,ko kuwa dai dan ya damu ya iso ne shi yasa tafiyar tayi masa nisa oho,agogon hannunsa ya d’ago ya duba lokacin da suka iso mararrabar daya saba tsayawa,parking yayi daga gefe sannan suka fito,sai da suka d’an jira ko zasu samu wanda zasu bawa ajiyar motan,ganin basu samu ba sai yada su d’aukan hanya dan yanayin gurin yayi shiru babu hayaniya bare suga alamun mutane,wannan dalilin yasa kawai sai suka yanke shawaran su tafi,sai daya tabbatar ya rufe ko ina kafin suka tsallaka d’ayan hanunun suka ci gaba da bin hanyar da zata kaisu cikin k’auyen,,tafiya suke yayin da a b’angaren Hammad yake jin fad’uwar da gabansa keyi tun fitowarsu daga gida tana sake tsananta,,tsaf suka gama sharo hanya,sai dai ko da suka iso dai² inda yake tunanin abunda ya rage musu su k’arasa gidan take idanunsa suka fara nuna masa makeken fili babu gini ko kad’an a cikinsa,dan yadda gurin yake ma kamar wanda aka sa tsintsiya aka share ko kuma wanda ba’a tab’a zama a cikinsa ba,duk wani gini da yake ganin ya sani babu shi kwata² a gurin tamkar wanda aka shafe,hajijiya ya fara gani a idanunsa data sashi tsayawa cak yana sake bin filin gurin da kallo cike da tsantsar tashin hankali ya shiga sambatu…..Hak’ik’a rayuwa da mutuwa duk nufin Allah ne akanmu,shi yake da ikon yanke hukunci game da rayuwar mu duka,tsara labari ba komai bane face nishad’i,ku sani cewa dan wani ya mutu ko wani ya rayu ba abune daya kamata muyi magana akansa ba,tunawa da cewa lallai wata rana muma zamu mutu k’arin imani ne kamar yadda kissar Annabi (S.A.W) da sahabbansa ta zo ku karanta domin na tabbata zaku amfana,,,wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune tare da Sahabbansa,sai ya fara tambayar su d’aya bayan d’aya,sai ya fara da Sayyidina Abubakar Assiddik’ yace:”Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?” Sai Sayyidina Abubakar yace:Abunda na fi so a duniya 1-Zama a gaban ka,2-Kallon ka,3-Ciyar da dukiya ta gare ka,,Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar bin Khaddab,Manzon Allah (S.A.W) yace:”Yaa Umar! Me ka fi so a duniya?” Sai Sayyidna Umar yace:Abunda na fi so 1-Ayi min umurni da kyakkyawan aiki ko da a b’oye ne,2-A min hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,3-Da kuma fad’in gaskiya ko da tana da d’aci.Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman bin Affan yace masa: “Yaa Uthman! Me kafi so a duniya?” Sai Sayyidna Uthman d’an Affan yace:Abunda na fi so a duniya,1-Ciyar da abinci ga mabuk’aci,2- Yad’a sallama,3-Yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya koma ta wajen Aliyyu bin Abiy ‘Daalib,yace masa: “Yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?” Sai Sayyidna Aliyyu yace: abunda na fi so a duniya,1-Azumi a lokacin rani,2-Karrama bak’o,3-Yak’ar abokan gaba da takobi.Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari,ya ce masa: “Yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya? Sai Abaa Zarri yace:Abunda na fi so a duniya,1-Yunwa,2-Jinya,3-Mutuwa.Sai manzon Allah (S.A.W) yace:”Saboda me yasa kake son su?” Sai Aba zarri yace:1-Ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,2-Ina son jinya don zunubi na yayi sauk’i,3-Ina son mutuwa saboda saduwa da ubangiji na.A wannan lokacin sai ga Mala’ika Jibrili (A.S) ya saukko zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ),sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku,1-Isar da sako,2-Bayar da amana,3-Son nakasassu.Daga fad’in haka kuma sai ya tashi zuwa sama sannan ya saukko a karo na biyu yace Allah mad’aukakin sarki yana karanta muku sallama,hirar manzon Allah da sahabbai tayi dad’i,harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku,1-Harshe mai ambatonsa,2-Zuciya mai tsoronsa,3-Jikin da aka jarrabce shi da balaa’i kuma yayi hakuri.Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah,, dan haka y’an uwana kada ku manta da Addu’o’i guda uku a cikin sujjadarku..1-“Ya Allah ina rok’on ka kyawawan halaye,2-“Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace,3-“Ya Allah mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka..Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne.Sannan lada ku manta Ubangiji (S.W.T) ya fad’a a cikin littafinsa mai tsarki cewa:”Shi ne wanda ya halitta mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku,ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawun aiki,shi ne mabuwayi,mai gafara.”(Suratul Mulki aya ta 2)..Dan haka hak’uri akan komai na rayuwa shi ne mafi alkhairi a garemu,,Allah ya datar damu duniya da lahira..Ameen.👏*
_Tunatarwa ne gare ku masoya..💞_
••••••••••
A wannan wayewar gari kusan abunda ya afku a daren jiya ba iya garin Wudil kad’ai ya tab’a ba,dan zamu iya cewa garuruwa da dama sun samu afkuwar iftila’i iron wannan,sai dai babu inda akayi rashin da akayi kwatankwacin na garin wudil,saboda nasu lamarin shi ne akan gaba a dalilin munanarsa,daya zama akusan duk hanyar da mutum zai ratsa ta cikin wannan yanki na *KAUSANI* d’ai²kun unguwanni zuwa k’auyuka ne mutum zai shiga ya fito ba tare da yaji labarin anyi mutuwa ko an samu jikkata ba,wani gidanma tun kafin ka shiga zaka jiyo koke²n ahalin gidan a sakamakon rashin da suka yi,,yayin da wasu ke kukan mutuwa wasu kuwa nasu kukan ya ta’allak’a ne dalilin rasa muhallinsu da suka yi,haka nan wasu kuma wa rasa dukiyoyinsu da suka yi ya kawo faruwar hakan.
A cikin k’auyen su *SABINA* ma hakan ce ta kasance,,sai dai su nasu garin tun wayewar gari yake shiru,baka jin sautin komai face k’ugin manyan Van’s zuwa caterpillars,haka nan da zarar ka nufo k’auyen tun daga farkon sa zaka fara cin karo da rufin gidaje wanda iska ta d’age daga muhallinsu tayi watsi da su,wani gurinma kana kallo ba sai ka sake ba saboda yadda al’amarinsu ya munana a daliliniftila’in daya faru kusan a nan d’in nema yafi afkuwa.Can daga gefe kuwa motoci ne na y’an jaridu,jami’an tsaro wanda suke da alhakin kare faruwar had’ura,sai kuma wakilan gidan gwamnati,,duka ilahirin jama’ar garin da suke raye an tare su guri guda,majinyantan kuwa tuni har an nufi asibiti da su domin basu taimakon gaggawa,,yayin da har lokacin y’an jaridu suke kan d’aukan rahoton abunda ya faru,har ma da aikin zaro ragowar corpses (gawarwaki) da k’asa ta binne,,,ahalin gidan su Sabina zaune gefe guda sunyi jigum²,fuskokinsu d’auke da damuwa,alhini gami da tashin hankalin da zaisa mutum fahimtar suna d’aya daga cikin ahalin da sukayi rashi a wannan yankin,,idanunsu sunyi wani irin jajir saboda tsabar kuka,damuwa mai girma bayyane k’arara a fuskokinsu,da yasa a wannan lokacin ma ko magana babu mai iya yinta a cikinsu saboda al’amarin ya matuk’ar girgiza su ba kad’an ba.
Yinin ranar sur aka shafe ana aikin ciro gawarwaki amma ba’a gama ba,wanda a k’arshe saboda hak’ar k’asa da akayi ya fara zurfi ya janyo k’asa taci gaba da k’ok’arin fara amsawa,wannan dalilin yasa akan dole aka dakatar da hak’ar k’asar.Daga nan aka tattara matattu da rayayyu a manyan Van’s sai sauran y’an kayayyakin su da suka tsintsinta akayi hanyar cikin gari da su.
A ranar bayan an kawo su aka wuce da gawarwakin zuwa asibiti domin sake tantancewa,,ak’alla sai da aka d’auki kwanaki biyu tsakani kafin a bawa ko wane ahali tasu gawar,bayan anyi musu sutura aka sallame su a babban filin gidan sarauta sannan aka kaisu gidanjensu na gaskiya,,cikin wad’anda aka rasa sun had’a har da Baffa,,Baban Sabina kuwa da Baban LADO duka suna kwance a gadon asibiti,sakamakon karaya da suka samu,hakama sauran mutanen gidan da dama sun samu raunuka,,Bayan y’an kwanaki da faruwar wannan *AL’AMARI* duk da gwamnati ta killace al’ummar wannan yanki ta bawa sauran jama’ar da suke raye tallafin muhalli a cikin mabambanta daga unguwannin dake garin kano,,wanda a cikin wad’annan jama’a ya had’a har da ahalin su Sabina,inda suka samu matsuguni a cikin unguwar *Kawo* dake hotoro.Gaba d’aya faruwar *AL’AMARIN* ya zo musu ne a bazata mai tare da wani irin chanjin rayuwa mai tattare da damuwa a sanadiyyar rasa elder da suka yi a wannan zuri’ah..+
*FLORIDA STATE,U.S.A..*
Suna fitowa daga *Pura bean coffee company* direct hanyan komawa skul suka d’auka,suna tafe suna hira yayin da a b’angaren Hammad kuma yayi shiru yana sauraren su kasancewarsa dama ba gwanin da za’a jishi yana magana ba,,tun kafin suyi nisa da inda suke ya fara jin jikinsa yana yi masa babu dad’i,babu wanda ya fad’awa irin yanayin da yake ciki,a haka suka ci gaba da tafiya cikin dauriya har suka shigo cikin skul ba tare da yayi magana ba,a lokacin ne kuma jikinsa ya sake d’aukan wani irin sanyi,kafin a hankali kasala ta fara saukar masa,jikinsa ya sake k’ank’amewa cikin blazer dake jikinsa dan dama yanayin garin akwai sanyi,,yayin da Sadeeq da Sultan suke ta fira abunsu cikin nishad’i ba tare da sun kula da yanayin da yake ciki ba har suka shigo room d’insu,wanda rashin kulawa irin nasu yasa ko da suka ji yayi irin wannan shirun hakan bai sa sun fahimci abunda ke faruwa ba,inda bed d’insa yake ya nufa,da baya ya zame ya kwanta while k’afafunsa na k’asa,ba taare daya iya cire ko da blazer d’in jikinsa ba bare takalmansa ya runtse idanunsa,,ajiyar zuciya ya shiga jerawa irin wacce sai mutum na cikin tsananin damuwa ko yayi kuka,haka nan yake jin jikinsa na sanar masa lallai akwai abunda ke kan faruwa da wani na jikinsa,to amma abunda bai sani ba shi ne,da Daddy’nsa ne,Mamma,Bassam ko kuwa BADRA..?? Ne ke cikin mawuyacin yanayi aka kasa sanar masa,duk ya kasa fahimta,,,cikin k’ank’anin lokaci damuwa ta sake rufe shi,kallonsa Sultan ya juyo yayi yana shirin yi masa magana ya ganshi cikin wannan yanayin da sauri ya nufo inda yake yana fad’in
“Broah.! What’s wrong..!?”
Bai iya d’agowa ba bare ya samu damar bashi amsa,shima Sadeeq cikin sauri sai ya matso kusa da su yana kallonsu while yana fad’in
“Dude what’s happen..??”
Sultan ne ya waiwayo yana kallonsa da fuskar damuwa
“Nima dai abunda ya bani mamaki kenan,yanzun fa muka shigo dukanmu,yanzun kuma na ganshi kwance,shi ne nima nake tambaya amma yak’i magana..”
Kallon mamaki duka suka tsaya yi masa kafin Sadeeq ya tambayae shi
“Man.! Wai mene ne hakan,mufa kana neman samu a damuwa.! Ya kamata ka fad’a mana abunda ke faruwa.”
Da kyar ya mik’e ya zauna har lokacin idanunsa a d’an rufe saboda yanayin da yake jin jikinsa kamar anyi masa mahaukacin duka,,ba tare daya amsa musu ba ya mik’e cike da rashin kuzari ya d’auki waya,Number Daddy ya fara kira,yadda wayan ke sounding a haka shima zuciyarsa ke bugu tsoro fal ransa da taraddadin abunda zai jiyo idan an d’auka,muryar Daddy ya jiyo cike da k’oshin lafiya yana magana ta cikin wayar,sai daya sake sakin ajiyar zuciya kafin yayi masa sallama,bayan ya amsa sannan ya gaida shi cikin sanyin murya,duk da yanayin da yaji Daddy ya amsa masa gaisuwa ya bashi k’warin guiwan fahimtar lafiya k’alau suke,amma bai fasa tambayar lafiyarsu ba,take Daddy ya sake tabbatar masa da lafiyarsu,ajiyar zuciya ya sauke,suka d’an tab’a hira dan dama sun kwana biyu basu yi magana da shi ba,cikin tsautsayi har za suyi sallama a lokacin sai ya sakowa Daddy batun yana son zuwa ya duba su saboda yana jin kewar gida sosai,ko bari Daddy baiyi ya kai k’arshe ba ya tari numfashinsa yana fad’a masa ya bari kawai ba sai ya zo ba,gara yayi zamansa ya maida hankali sosai kan karatunsa,idan dan ta sune a duk lokacin da suka so zasu zo su ziyarce shi,amma shi d’in yayi zamansa sam bai ji dad’in hukuncin da Daddy yayi masa ba,a ganinsa yana tunanin kamar bai dace ace yayi masa haka ba saboda yadda duk abunda Daddy’n yace yayi yana kamanta yi masa biyayya,haka nan yayi ta tunanin dalilin da yasa Daddy’n ya hana shi zuwa. Damuwa fal ransa suka yi sallama da Daddy,bayan ya katse kiran ya kira Mammansa,sun gaisa da ita cike da girmamawa itama ya sanar da ita damuwarsa da duk yadda suka yi da Daddy babu jimawa,,har ga Allah duk da a gabanta suka yi wayar bata so akace Daddyn ga hana shi zuwa ba,saboda ko itama tana jin kewar ganinsa,buh duk da hakan sai tayi ta kwantar masa da hankali akan yayi hak’uri tunda Allah yasa suna yin video call lokaci zuwa lokaci,kada ya sawa kansa damuwa in sha Allah zata yiwa Daddy maganar idan yaso sai suzo su duba shi a skul d’in,godiya yayi mata sannan suka yi sallama ya ajiye wayar,,sake lumshe idanunsa yayi dai² lokacin Sultan ya gama cika da abunda yayi musu,a fusace ya juya ya bar wajen dan ganin rainin hankalin daya shuka musu,shima dai Sadeeq juyawar yayi ba tare daya sake cewa komai ba ya bar wajen.
Bayan barinsu a kusa dashi,ajiyar zuciya yaci gaba da saukewa,lokaci guda kuma tunaninta ya fad’o masa a rai,tabbas yana jin kewarta tun ba yau ba,kuma saboda dalilinta nema ya damu da son zuwa 9ja,badon komai ba sai dan yaga a halin da take ciki yanzun,,sai gashi tun ba’a je ko ina ba daga fad’awa Daddy har ya datse masa hark’alla ta hanyar hana shi zuwa,,duk da ba wannan ne karo na farko daya shirya yin tafiyar ba,amma rashin barinsa sosai yasa shi jin babu dad’i,saboda kusan sau uku kenan yana niyyar zuwa uzurori suna gifta masa wanda ala dole yake hak’ura tunda uzurin ya zame masa wajibi ne idanma baiyi ba babu wanda zai masa,sai gashi a lokacin daya gama sa rai a karo na k’arshe da yake nufin zuwan saboda ganin ya samu dama Daddy ya nuna k’in amincewarsa,,a wannan daren kam dan dai ana cewa bacci b’arawo ne da Hammad kam sai yace bai san da wane lokaci ne ya runtsa ba,bcos gaba d’aya ya rasa nutsuwar sa a dalilin tunani da yayi ta fama da shi.Tun daga wannan rana kuma sai ya zama ko da wasa bai sake shirin zuwa ba dan Daddy yace masa matuk’ar ya taho da saninsa ko babu zai b’ata masa rai,shi yasa ala dole ya yakice batun zuwan bai sake tayar da shiba,haka nan ko da yaga suma d’in basu jeba sai yak’i bin ba’asin dalilin k’in zuwan nasu,,a haka ragowar lokacin da yayi masa saura yaci gaba da tafiya…
*ONE YEAR LEAVE…*
*NIGERIA.*
Kimanin shekara guda kenan da faruwar al’amarin,wanda tun a bayan afkuwarsa a lokacin da gwamnati ta shiga lamarin su,sai ya zamanto bata yi watsi da su ba,bayan tallafin muhalli data bawa ko wane ahali,sannan ta samawa da dama daga cikinsu guraren aiki duk da kasancewarsu basu yi karatu ba,ta hanyar yi musu adalci a matsayinsu na y’an k’asa ta tallafawa rayuwarsu,,sannan batun k’ananun yara kuma ta d’auki nauyin karatunsu ta hanyar rarraba su makarantu musamman wad’anda ke cikin karatu kafin afkuwar al’amarin.
Tun bayan dawowarta daga extra lesson saboda gabatowa jarabawar S.S.C.E da take shirin zanawa take zaune cikin d’aki ta tusa litattafanta kamar tana bitar abunda ke ciki,uban tagumin data rafka shi ne kad’ai abunda mutum zai kalla yayi saurin gane hankalinta sam baya tare da abunda idanunta ke kali,,zuwa wannan lokacin tunaninsa ya jima da cika nata zuciya,y’an guntayen hawayen da suka ziraro mata a sakamakon tunawa da tayi babu ta hanyar da zata san ya dawo yasa takai hannu saman fuskarta ta goge hawayen,dai² lokacin Inna ta sawo kai tana shigowa cikin d’akin,akan idanunta duka taga komai daya faru,har tayi kamar zata fita kuma zuciyarta cike da tausayin y’ar tata ta k’araso ta zauna kusa da ita,har ta zauna Sabina bata sani ba sai data dafa kafad’arta sannan ta d’ago idanunta a hankali,girgiza kai Innar tayi cikin nuna alhini da damuwa tana cewa
“Haba Sabina..! Haba..!! Yanzun ace ke kenan ba zaki ji fad’an da nake miki ba,me yasa ne jam kike son komawa haka,sai kace ba musulma ba,ace ko wane lokaci idan kika zauna sai kin zubar da hawaye,,shin me yasa ne kam bakya ji..!? Na sha fad’a mikifa addu’ah itace abunda yafi kamata mu duka muci gaba da yi,in sha Allahu sai kiga ya dawo ya same ki kamar yadda ya tafi,ubangiji shi ya k’addara faruwar komai dan haka idan kin fad’a masa zai ji rok’on ki har ya biya miki buk’atun ki,,muyi ta addu’ah kinji,kada kice kin gaji,da yardar Allah sai kiga komai ya wuce tamkar ba’a yiba..”
Kanta ta sunkuyar k’asa tana sake share hawaye,kan nata Inna ta shafa sannan ta kamo hannunta ta rik’e
“Yanzun dai abunda nake so dake shi ne,kiyi k’ok’arin ragewa kanki damuwa,kina addu’ah nima ina taya ki,da yardar Allah komai zai zama tarihi..”
“In sha Allah Inna zanci gaba da yi..”
“Yawwa to..! Ko kefa ai gara ki saki jikin ki,ubangijin daya raba ku wata rana shi ne zai sake had’a ku da yardar sa..”
K’asa² ta amsa da “Allah yasa.”
Sai da Inna tayi mata nasiha sosai kafin ta fita ta barta tana shirin tafiya makarantar islamiyya tunda Allah yasa sun sake samun ci gaba..
A gefen Hammad kuwa,tun kwanaki uku da suka gabata suka dawo k’asar tafe da d’umbin nasarori,sai dai rashin samun lokaci da yasa bai tafi tun a washe gari ba kasancewar saukar dare suka yi,,yau kam daya k’udurcewa ransa komai zai faru sai dai ya faru,yasa cikin shauk’i gami da begen abar k’aunarsa,dan tun daya tashi yake ji a ransa bazai iya jiran rana ta fad’i ba tare da yaje ya gano su ba,tun bama baffa ba daya d’auke shi matsayin d’a,,kyakyatawan murmushi ya saki yana shafo mustache d’insa da hutu ya sa ya sake cika da duhu,a fili ya furta
“Baffa in sha Allah ina hanyar zuwa na ganka.!”
A hanzarce yayi shirin tafiya cikin wani d’anyen baby bazin african getzner mai kalar coffee da aka yiwa aiki da milk d’in thread,ya kawo hula da ake cema tangaran ya murza,banda k’amshin dad’ad’an turarukan sa a lokacin daya fito babu abunda ke ratsa hanya,haka nan fuskarsa cike da annurin zaije ga abunda yake matuk’ar k’auna ya fito,ko da yasa aka shigar masa da kayayyakin da yayi musu tsaraba a sabuwar motar da Daddy ya siya masa k’irar Highlander tokunbo full option,sai yayi ma Mamma sallama kana ya fice a gidan,sai daya biya ya d’auki Sultan a gida kafin su d’auki hanyar garin Wudil,,tafiya suke a motan ba tare da wani hira ba sai cool music dake tashi,tunda suka d’auki hanya haka nan sai yake ganin tafiyar kamar an k’ara mata nisa,ko kuma dai dan ya jima bai zo bane yasa yake ganin hakan,ko kuwa dai dan ya damu ya iso ne shi yasa tafiyar tayi masa nisa oho,agogon hannunsa ya d’ago ya duba lokacin da suka iso mararrabar daya saba tsayawa,parking yayi daga gefe sannan suka fito,sai da suka d’an jira ko zasu samu wanda zasu bawa ajiyar motan,ganin basu samu ba sai yada su d’aukan hanya dan yanayin gurin yayi shiru babu hayaniya bare suga alamun mutane,wannan dalilin yasa kawai sai suka yanke shawaran su tafi,sai daya tabbatar ya rufe ko ina kafin suka tsallaka d’ayan hanunun suka ci gaba da bin hanyar da zata kaisu cikin k’auyen,,tafiya suke yayin da a b’angaren Hammad yake jin fad’uwar da gabansa keyi tun fitowarsu daga gida tana sake tsananta,,tsaf suka gama sharo hanya,sai dai ko da suka iso dai² inda yake tunanin abunda ya rage musu su k’arasa gidan take idanunsa suka fara nuna masa makeken fili babu gini ko kad’an a cikinsa,dan yadda gurin yake ma kamar wanda aka sa tsintsiya aka share ko kuma wanda ba’a tab’a zama a cikinsa ba,duk wani gini da yake ganin ya sani babu shi kwata² a gurin tamkar wanda aka shafe,hajijiya ya fara gani a idanunsa data sashi tsayawa cak yana sake bin filin gurin da kallo cike da tsantsar tashin hankali ya shiga sambatu…..
*Afuwaan fan’s.. Kun san na sanar daku idanuna ke ciwo kwana biyu,shi yasa bana iya yi muku posting,,amma kuci gaba da hak’uri in sha Allah komai ya kusa zuwa k’arshe da yardar Allah..*K’ok’arin fad’uwa ya shiga yi a gurin banda sambatu babu abunda yake yi cikin tsananin damuwar da ko iya tantance abunda yake fad’a baya yi,da sauri Sultan yayi k’ok’arin taro shi dan yaga yadda ya taho yana fad’in
“Easy Man..!”
A dak’ile ya d’ago idanunsa da tashin hankali yasa su rinewa lokaci guda ya watsa masa su,duk da yana jikinsa amma bakinsa bai mutu ba
“Me kace..!?”
Ya tambaya cikin b’acin rai kamar Sultan d’in ne ya janyo faruwar lamarin,,yanayin da Sultan ya ganshi ciki shi ya tabbatar masa da lallai akwai damuwa mai girma a tare da shi,dan haka sai ya danne nasa b’acin ran ya sake rik’o shi
“Muje kawai..!”+
“Muje ina..!? Gidan wace uwar kake son muje bayan banga abunda nake muradin gani ba tsawon shekara..!?”
Fuskarsa d’auke da wani irin fushi irin wanda tunda Sultan yake tare da shi tsayin tasowarsu bai tab’a ganinsa a cikin kwatankwacin saba,,d’an girgiza kai yayi dan yadda a lokacin yake ganin damuwar da Hammad d’in yake ciki ita tasa shi yi masa irin wannan maganar,rarrashinsa ya fara bayan yayi wearing fuskar damuwa yace
“Ina kace min da zamu je.!?”
Ajiyar zuciya ya shiga saki mai k’arfi yana girgiza kai shima,lokaci guda kuma wasu irin hawayen k’unci suka fara taruwa ta gefen idanunsa
“Me yasa za kiyi min haka..!? Me yasa³..!! Me yasa sai lokacin da kika bari na shak’u dake,na sabarwa da kaina soyayyar ki,,me yasa zaki guje ni a dai² lokacin da kika san nafi buk’atar kasancewa tare dake,,shin baki san a yanzun ne nake marmarin zuwa na ganki ba..? Kin sani nayi miki *ALK’AWARI* akan zan dawo gare ki duk runtsi duk wuya..Me yasa da kika san zaki tafi ki barni baki sanar dani inda zaki je ba..!? Why zaki min haka..!? Why..??”
Kallonsa kawai Sultan ya tsaya yi da matuk’ar mamakin ganin yadda ya dage yana magana shi kad’ai,tab’a shi ya d’an yi cike da rashin fahimta
“Broah! Wai lafiyar ka kuwa..!? Ya za’ayi ka dunga magana kai kad’ai ne..?? Wace ce kake magana akanta..?? Ya kamata ka sanar dani abunda yake faruwa..”
“Ban san ta ina ne zan yi maka bayani ka fahimce ni ba,,buh ina cikin rud’ani d’an uwa,,kwakwalwata ta kasa fahimtar abunda ke shirin faruwa..! Ka fad’a min inda zan ganta..”
Ajiyar zuciya Sultan ya sake yi kafin ya d’an bubbuga kafad’arsa
“No Broah..! Ya kamata dai ka nutsu kamin bayanin da zan fahimci damuwarka,,kasan bani da sani akan abunda kake magana,duk na shiga duhu wollahi..Ka fitar dani daga wannan k’angin..”
“Ban sani ba..! Ban san ina ta tafi ba..?? Ka fad’a mata ta dawo gare ni,nayiwa Baffa *ALK’AWARI* zan kula da ita..! Me yasa to bata jira ni ba.. Me yasa tayi tafiyarta ta barni bayan na fad’a mata da ita kad’ai zan iya rayuwa..!!”
Runtse idanu Sultan yayi,ko da ace Hammad bai sanar da shi dukkan abunda ke faruwa ba,lallai ne zuwa yanzun a matsayinsa na Psychologist ya iya fahimtar *AKAN SO* ne Hammad ya shiga damuwa
“To amma meya janyo faruwar *AL’AMARIN..??”*
Ya k’arashe zancen da tambayar kansa
“Ban san dalilin da yasa ta iya tafiya ta barni ba..D’an uwa ka fad’a mata ta dawo,nayi mata *ALK’AWARI* da *JININ* jikina zan kula da ita fiye da yadda zan bawa kaina kulawa,ka fad’a mata ta zo gare ni..!”
Yadda yake surutai yasa Sultan gyara tsaiwarsa yana binsa da kallon tausayi cikin k’ank’anin lokaci duk ya fita hayyacinsa kamar wanda yayi jinyar shekara,to wai shi shin ta ina ne zai fara bashi hak’urihar su samu damar binciko abunda yake faruwa..?? Allah ya san zuciyarsa bashi da masaniya kan abunda abokin nasa yake magana,kafad’ar Hammad ya sake rik’owa duka biyu yana fad’in
“Relax broah..! Let us leave..”
“Babu inda zani,,har sai na gano inda ta tafi..!”
“A’a broah baza ayi haka ba,,ya kamata fa ka nutsu sosai,,idan ka duba yanayin gurin nan,kaima kanka zaka gane hakan,, gurin nan baiyi kama da gurin da mutane suke rayuwa ba,koma mene ne yake faruwa ya kamata muyi bincike kafin mu tabbatar da abunda ya faru,in sha Allah zamu gano gaskiyar abunda ya faru..”
Tunda ya fara magana yake kallonsa da jajayen idanunsa masu cike da tsoro,,girgiza kai yayi yana sakin ajiyar zuciya
“Babu fa inda zani..Kawai kayi tafiyarka ka kyale ni,,ko dama ace na bika damuwar rashin ta shi zai zame min *AJALIN SO..!”*
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. Allahumma ajirna fiy musibatin wa’aklufna khairan minha..!”
Addu’ar da Sultan ya fara yi kenan a fili,yi yake yana sake maimaitawa,har ya samu Allah ya taimake shi Hammad d’in ya cafka suka ci gaba da maimaitawa tare,,dama dalilinsa nayi kenan a fili,bcos yana ganin idan cewa yayi masa kace kaza,yasan yadda yayi spark lokaci guda d’in nan zai yi wahala bai zazzage shi ba,shi yasa ya gwammace yayi a filin,idan ya dace sai ya karb’a,hamdala yayi a ransa na jin dad’i kafin ya dafa shi da muryan rarrashi
“Let us move Broah,,in sha Allah zamu binciko komai,kada ka damu,kai dai ka bar komai a hannu na,da yardar Allah babu abunda zai same ta,,nayi maka *ALK’AWARI..!”*
Tsare shi yayi da kallo kamar mai neman wani abu akan fuskarsa,cikin d’agawar sauti ya furta
“K’arya ne..! Ba zaka ganta ba,,,ta yaya ne zaka ganta..? A ina..?? Nima fa bata sanar dani dalilin da yasa ta tafi ba..? Kai d’in ta yaya zaka gano inda take..?? Eyyy!?? Ka fad’a min..!”
Lumshe idanu Sultan yayi sannan ya sake rik’e shi
“I promised.. Zan nemo,,saboda kai..Buh kayi hak’uri yanzun mu koma gida..”
Da kyar badon Hammad yana so ba,sai dan ganin yadda Sultan d’in yake ta bashi baki ga fuskarsa cike da damuwa sannan ya sakko akan su koma d’in,,lokacin da suka fito daga surk’uk’in hanya dai² suna fitowa bakin titi inda suka bar mota,suna niyyan shiga su wuce cikin gari,sai ga wani dattijo bisa tsohon keke yazo wucewa,da ganinsa zaka kasan ya gaji sosai dan kallo d’aya zaisa mutum fahimtar ba iya talauci ne kad’ai yasa shi tsufa ba,har da rashin kyakykyawan muhalli da cima mai kyau,wannan ne dalilin da yasa tsufansa yayi saurin bayyana,,ganin yana niyyar wuce su a gurin cikin sauri Sultan ya matsa daga jikin motar yayi masa sallama,,har ya d’anyi gaba da inda suke duk sa keken ba wani sauri yake da shi ba,sai kuma ya dawo yana amsawa,gaisawa suka fara yi da Sultan dan shi kam Oga Hammad tuni ya shige cikin mota bcos bazai iya ci gaba da jurewa tsaiwa ba,,kallon Sultan dattijon yayi bayan ya sauko daga saman antique bike d’insa,dan daga dukkan alamu akwai magana a tare da shi,sai da Sultan ya juya ya kallo hanyar da suka baro sannan ya furta
“Baba dan Allah idan babu damuwa tambaya nake da,,ban sani ba ko Allah yasa ka sani..”
“In sha Allahu samari,, idan har na sani me zai hana na sanar da kai..?”
Jinjina kai yayi cikin farin ciki sannan a hankali yaci gaba da magana
“Baba.! Dama Baba tambaya nake sonyi game da k’auyen dake a ta wancan hanyar..!”
Shiru dattijon yayi yana bin inda Sultan d’in yake nunawa da hannunsa
“Eehh! Toh! Samari,gaskiya ban san wane k’auye ne kake magana akansa ba,da yake yanzun gaskiya abubuwa sun sauyawa sosai,ta iya yuwuwa abunda kake son tambayar ko na sanshi ko akasin haka,,amma shin kuna neman sani ne akan wani abu..??”
“Ehh! Baba…Dama dai akwai wad’anda muka zo nema ne,saboda kasancewar mu bak’i,to kuma dai mun d’auki lokaci bamu zo ba,,shi ne yanzun da muka zo mun tarar babu kowa sai filin gurin kawai..Shin ko kana da sani akan abunda ya faru da jama’ar garin,ko kuma dai canja gari suka yi,shi ne abunda muka gaza fuskanta..”
“Allah sarki..! Kai kuwa yaro,,shin baka samu labarin irin abunda ya faru da mutanen wannan gari ba da jimawa..??”
Girgiza kai sultan yayi alamun bai sani ba,dattijo cikin jimamin yaci gaba da magana
“Ai kuwa samari idan har akan mutanen dake zaune *RUGAR MALAM SHEHU..!?* Kake magana da jimawa suka bar wannan gari sakamakon iftila’i daya fad’a musu..”
Shiru Sultan yayi yana sauraron labarin da yake bashi kan bala’in daya faru watannin da suka gabata,,jikinsa yayi wani irin sanyi da jin irin k’addarar data same su,har dattijon ya gama bashi labarin bai daina jimanta *AL’AMARIN* a zuciyarsa ba,godiya yayi masa gami da alkhairi,sannan yayi masa sallama ya juya ya bar gurin da sanyayyun guiwoyi.
A mota ya tarar da Hammad kwance a kan seat na mai zaman banza,,yana shigowa ya tada motar suka kamo hanyar dawowa gida,tun da suka d’auko hanya babu wanda ya iya cewa komai,tun bama Hammad ba da damuwa tasa shi yin shirun dole,shima kuma Sultan dalilin da yasa yak’i yi masa magana kenan saboda yasan idan yace zaiyi masa magana ma a yanzun ba lallai ne ya iya tsayawa ya fahimci abunda yake son sana shi ba,,,har suka shigo cikin gari kalma d’aya bata had’a su ba,sai karatun da Sultan d’in ya musanya musu a maimakon cool music da suka sa a tafiya su da yake tashi.
Tun kafin su k’araso gida tsananin damuwar da yake ciki tuni ta haifar masa da zazzafan zazzab’i baya ga ciwon kai da yayi masa mugun kamu,lokacin da suka shigo gidan ma a daddafe ya fita daga mota,da tainmakon Sultan suka shigo cikin parlor,da Mamma suka fara arba,,tunda suka shigo tana kallonsu jikinta ya bata akwai matsala,hankalinta ta tattara akan Hammad dake wani irin tafiya rik’e a jikin Sultan tana tambaya
“Son..! Lafiya..!? Sultan me yake faruwa ne..!?”
“Mah relax..! Am fine..”
Cikin dauriya yana rik’e forehead yayi maganar
“Sultan,,me yake faruwa da shi wai..!?”
Ta sake tambaya,sai daya tabbatar ya zaunar da shi sannan ya d’ago yana kallon Mamma da fuskar damuwa
“Mamma..! Wollahi i dunno how..!”
“A’a sultan,,kaima kasan babu yadda za’ayi na yarda da abunda zaka fad’a min,,tunda na san tare kuka fita..”
“Wollahi Mamma ban san komai akan abunda yake faruwa da shi ba,buh a yadda dai na fahimta koma mene ya janyo shigarsa wannan yanayin baya rasa nasaba da *SO..!”*
“So kace..! Soyayya kake nufi ko kuwa..!?”
“Ehh! Mamma..Tabbas soyayya ce silar faruwar komai..”
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..”
Abunda ya fara fitowa daga bakin Mamma kenan tana kallon Hammad daya kwanta rik’e da kansa
“To yanzun kun je hospital ne.. Ko kuwa gida kawai kuka nufo kai tsaye..!?”
“A’a Mamma dawowarmu kenan yanzun..”
Inda tabar wayarta ta nufa,ko data d’auka line Daddy ta soma kira cikin damuwa,,sai da wayar tayi ring kamar zata katse kafin ya d’auka,bata iya jiran su gaisa ba ko amsa sallamar da yake mata ba ta hau fad’in
“Daddy…Please ka turo mana doctor gida yanzun.!”
Jin abunda ta fad’a ne ya sashi saurin mik’ewa a kid’ime daga saman kujeran da yake kai har yana neman yin tuntub’e
“Asiya..! Me kike fad’a..!? Me kuma ya faru.!?”
“Please daddy,, ni dai kawai nace ne kasa doctor yazo yanzun,koma mene ne sai bayan yazo nefa duka zamu sani..Amma dai akwai matsala..”
“Ok..Ok.! Ina zuwa..”
Yayi saurin katse kiran,hannunsa har karkarwa yake gurin neman number doctor’nsu, ba tare da shima ya tsaya b’ata lokaci gurin amsa gaisuwar saba cikin tak’aita magana yayi masa bayanin iya abunda ya fahimta,,cikin gaggawa kamar yadda Daddy ya sanar da shi ya shirya kayayyakin aikinsa da yasan zai buk’ata sannan ya fice daga hospital d’in.A ta gefen Daddy kuwa tun kafin k’arasowar doctor ya sake kiran Mamma dan jin abunda ke faruwa suke neman likita da gaggawa haka,da kyar Mamma ta d’an samu nutsuwar da har ta iya fad’awa Daddy iya abunda ta sani cikin damuwa, shima dai jimamin ya shiga yi kamar yadda take,a lokacin suna tsaka da magana likitan ya k’araso,da hanzari ta yiwa Daddy sallama saboda tana son bada nutsuwarta akan bayanin da zaiyi,,da taimakon ma’aikatan gidan suka samu suka maida Hammad bedroom d’insa bayan nan likita ya shiga aikisa,,duk wani binciken da gwaje² kusan babu wanda baiyi masa ba,,bayan dogon lokaci daya d’auka yana bincike yayi masa alluran da yasan zasu taimakawa jikinsa kafin ya buk’aci yin magana da Mamma,shi kansa likitan lokacin da yake nufin sanar da ita ciwon nasa jikinsa a sanyaye yake da *AL’AMARIN* na Hammad,,amma saboda k’arfin hali a hakan bayan ya sharce gumi ya kalli kafin ya sake yin shiru yana nazari,Mamma kam ko da taa yayi shiru ita da kanta ta bud’e baki tana tambayar sa
“Doctor..! Har yanzun baka ce min komai ba,,matsalar tasa ba babba bace ne..!?”
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya d’ago kansa daga kallon takardun sakamakon gwajin da yayi masa,yana niyyar yin magana kuma kiran Daddy ya shigo wayarsa,da hanzari ya d’auko wayar yana fad’in
“Afuwaan Hajiya,,alhaji ke kira.”
Da kai ta amsa masa,sannan ya d’auka muryan Daddy cike da tashin hankali akan rashin sanin abunda ke faruwa da gudan jininsa yake tambayar likitan
“Doctor..! Wai shin mene ne actual na abunda ke damun Hammad ne..? Na jira² tun d’azun amma shiru har yanzun banji ko wane irin magana ba dangane da larurar tasa..Me yake damunsa ne..!?”
Ajiyar zuciyar dai ya kuma yi,murya a sanyaye cike da rashin hope ya fara magana
“A gaskiya ranka ya dad’e,,Hammad na cikin mawuyacin hali,,dan a maganar nan da nake yima,kamar yadda bincike ya tabbar,a ko wane irin lokaci zuciyarsa zata iya bugawa..”
“Whattt..!? How dare u.!? Ta yaya ne wannan problem d’in zai faru da shi..!?”
Ga Mamma kuwa kalmar “Innalillahi wa’inna ilahi raji’un”,taci gaba da maimaitawa a zuciyarta,yayin da take kallon Hammad dake kwance saman bed a kwance kamar gawa
“Sir..wannan matsalar fa ba laifina bane,sannan kaima ba naka bane..Kawai dai abunda zan iya cewa ko nace na fahimta game da shi shine,akwai abunda yake so,ko kuma dai ta iya yiwuwa yayi loosing wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa da yake expecting samu..”
Shiru Daddy yayi daga gefensa banda zagaye tamfatsetsen office d’insa babu abunda yake tamkar mai safa da marwa
“To yanzun doctor mene ne matsalar kenan..!?
“Ehh to matsala dai a yanzun shi ne mu samu zazzab’in dake tare da shi ya sauka,matuk’ar ba haka ba kuwa,,zan iya cewa sai dai kawai muyi hak’uri..”
Murya a d’age Daddy ya tambaya
“Kamar yaya muyi hak’uri doctor.!? Kana son fad’a min ne Hammad zai mutu ko me kalamanka suke nufi..!?”
“A’a ranka ya dad’e,, sam Ba haka nake nufi ba,,amma dai abunda yafi a yanzun shi ne zamu yi k’ok’arin ganin zazzab’in ya sauka,kafin mu yanke hukuncin abunda zai iya faruwa da shi nan gaba..”
Hankalin Daddy idan ya kai million a wannan lokacin tofa ya kai mak’ura wajen tashi,ko da yaji likitanma yana fad’ar wannan maganar guiwoyinsa tuni suka sake yin sanyi
“Shi kenan doctor,, duk abunda ya dace ayi kana tare da shi kayi masa,sannan abunda nake so shi ne ina son ka bawa Hammad kulawar data dace,matuk’ar zata warware matsalar Yarona,fatana shi ne ace ya kasance cikin k’oshin lafiya..”
“In sha Allah, ranka ya dad’e za muyi iya k’ok’arin da zamu iya wajen ganin munyi duk yadda kace..”
Godiya sukama juna sannan cikin damuwa Daddy ya kife wayar bisa table,saman armchair da aka tanada domin ganawarsa da guest ya zauna yana aza chin d’insa bisa hannayensa daya dunk’ule,yayin da damuwa mai girma ta bijiro masa a dalilin ciwon Hammad.
(Ni kuwa dai da nake gefe nace Daddy kenan,,ai ina tunanin bai kamata ka shiga damuwa akan ciwon Hammad ba,tunda tun asali kai ne mutum na farko daya bada gudunmawar assasa dukma abunda ya faru,,shin fan’s kunga laifina a nan dan na fad’i gaskiya..?)
A can gida kuwa,bayan da likitan ya ajiye wayar Daddy, da kyar Mamma ta iya kallon shi saboda tashin hankalin da bayaninsa ya jefata,ta jima tana tunani kafin ta samu k’warin guiwar tambayarsa
“To yanzu likita,meya kamata muyi masa wanda zaisa shi fita daga halin daya shiga..!?”
“A gaskiya ina ganin dai tabbas a yanzun,abunda yafi kamata ace anyi masa shi ne,kamar yadda na fad’a tun farko,wato ayi k’ok’arin ganin zazzab’in dake tare da shi ya sauka,bayan shi kuma sai dole mu kasance masu yin taka tsantsan da duk abunda zai iya maida shi halin daya tsinci kansa a ciki,ta hanyae kwantar masa da hankali,saboda ta haka ne kad’ai nake ganin zamu iya yin nasarar yak’ar duk wata damuwa dake tare da shi..”
Sun jima sosai itama suna tattaunawa da likitan akan matsalar tasa kafin likita yayi prescribing magungunan da zasu taimaka masa jikin yayi kyay,daga nan yayi sallama da Mamma bayan ya sake duba jikin nasa ya ta batar lafiya saman ya tafi.
Tun daga wannan ranar ak’alla zan iya cewa sai da Hammad ya shafe sama da sati biyu kwance yana fama da jikinsa,kafin cikin hukuncin ubangiji sauk’i ya fara samuwa,sai dai d’an abunda ba’a rasa ba ta fannin tunani da damuwa da yakan shiga a wasu lokutan,duk da likita ya sanar masa ya daina sa damuwa a ransa,buh mun san dama abune mai matuk’ar wahala a gare shi ace lokaci guda ya iya cire tunanin da yake damun zuciyarsa,sai dai ko a hankali yau da gobe,dum da kasancewar kullum yana tare da Mamma,Sultan,Bassam nd BADRA da a kullum d’in suke k’ok’arin ganin sun sashi farin ciki,,sai dai kuma a duk lokacin da zasu yi abun dariya ko da su d’in ya basu dariyar ba lallai ne idan ka kalli fuskarsa ka fahimci wane irin yanayi ne yake ciki ba…..