TAWA TA SAMENI CHAPTER 7 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
duk yanda kika so ki san halinshi ba zaki iya ba mutum ne mai ban alajabi na wuce ina dariya,na sanar da mama aikin da yayanmu ya sani tace to na bar wankan naje na gyara mishi dakin zatayi ma su jamila in na dawo sai nayi nima nace to na shiga dakin yayanmu sai yau na yima dakin kallon tsaf,leather sit ne kujerun shi bakake ne masu girma setinau sai kayan wuta kafet da labulaye jajaye dakin sai kamshi yak nan na soma da bedroom din katuwar katifa irin wadda ba asa ta a gado din nan ce sai hanga na kayan sakawa a saman hangar akwatuna ne saiti biyu na dubi hangar rataye da kaya jibge a kan katifar ma duk kaya ne dai dai ko ina Www.bankinhausanovels.com.ng kwashe masu datti nayi a cikin wani dogon kwando irin na zuba kayan na gyara uwar daki tsaf sannan na koma falo shima nayi mishi aiki sosai na goge electronics din
komai yayi tsaf sannan na dauko turaren daki na feshe ko ina na kulle dakin,na kaima kabir,wanan shine silar fara sani aikinshi na zama mai gyara mishi
ZAMU TASHI
daki har ya zama dayan key din dakin ma a hannuna yake kullum
da safe sai na gyara nake tafya makaranta wata ranar laraba na isa dakin da sauri dan in gyara na tura naga dakin ya bude a raina nace yau yayanmu bai je training bane?na shiga ban ganshi ba na cire hijabina na ninke na ajiye a saman kujera kaina tsaye na shige uwar dakin kayan barci ne a jikina doguwar riga da wando,sam ban san yana bedroom ba na shige toilet na gyara tsaf na fito bedroom din sai a
WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG lokacin na kula da mutum kudundune cikin bargo nayi sauri na duba kan gado dan na tabbatar yayanmu ne a kwance,ya kudundune da sauri na juya zan fita sai naji yace Zo nan muryarshi irin ta marassa Ify nazo na dan duko yace ki dafa mani ruwan lipton nace to na fita zuwa dakinmu mama na samu tace har kin gama?nace banma gyara ba don yana nan ne yace akawo mashi ruwan lipton inaga bashi da Ify ne,mama tace ga wannan dibar mashi a ciki na baban sagir ne da yasa na dafa mashi dan yana fama da mura sai dai nasa kayan kamshi,nace zaisha ai yana shan na gida kuma yana sawa na diba na kaimashi na rusuna na bashi da kyar ya mike ya zauna akan gadon ya amsa duk naji banji dadi ba nace yayanmu baka da Ify ne?yace eh nace sannu,haka na koma naci gaba da gyaran falon har na gama na kara lekowa nace sannu na gama ko za’a kawo maka wani abu ne?yace ki shiga ki sanar da hajiyata sannan in ba zakiyi latti ba to ki dafa min indomie nace to cikin mintuna da basu fi biyar ba na dafa mishi hadaddiyar indomie na kai mishi…. Afalo na sameshi zaune kan doguwar kujera yana sanye da singilet da gajeran wando naja dan karamin table din glass din dake tsakar dakin na dora cooler din a kai na zuba mishi a cikin plate nasa cokali nace a baka ruwa?ya girgiza kai a raina nace yau dai ba danne dannen waya ba tare da ya dubeni yace kin fada ma hajiyata din ne?nace bata bude kofa ba,yace bani waya a cikin bedroom na shiga na wayar na kan katifarshi na dauko na duba fuskar wayar gabana yayi wani mummunan faduwa Www.bankinhausanovels.com.ng sakamakon ganin hoton anty mimi a fuskar wayar na kai mishi nace bari na gyara cikin,na shiga na gyara na fito yana cin abinci yace bani abinsha a fridge na bude coke na gwangwani na dauko mishi dan ina yawan ganin gwangwanayen coke din a cikin bolarshi na hado mishi da ruwan Cway na aje na wuce ban wani karya ba shiryawa nayi kawai nasha ruwan tea kadan don kar mama tayi min magana na fito su mami sun jima da shiryawa shi yasa ma ban tsaya saka safa ba,haj yaya mukayi karo da ita ta dawo daga dakin yayanmu ta dubi bilkisu_tace yayanku bashi da lafiya ku shiga ku gaishe shi keda saa da mami sukace to sun shiga ni kuma na tsaya daga waje ko yaya akayi ya ganni sai ji nayi yace ba zaki shigo bane ke? Na shiga da sallama na ce sannu bai amsa mani ba ya cigaba da cewa in kin dawo makaranta ki dafa mani wani abu ,karfe nawa kuke dawowa?nace biyu yace to
zan je naga likitane sai ki samar mani wani abu nace
nace me zaa dafa yace komai ma,muka fito su bilkisu
Sai wai hararata suke yi ni ko tausayin halin da yake
ciki shi ya dameni ko a mota sam na kasa sakewa duk
tunanina yana can gunshi sai kuma abin da yafi tsaya
mani a rai hoton anty mimi dake cikin wayar yayanmu
tana sanye da jar riga kanta ba dankwali tana ta WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG faman murmushi duk sanda na tino sai gabana ya fadi a ranar sukuku na yini ko yan ajinmu sai da suka tambayeni nace banjin dadi haka a mota da muna dawowa na kifa fuskata kan jakata ban da tunanin yanda yayanmu ya yini da jiki bana tunanin komai har naga karfin halina irin wannan daga hankali haka,mami ta dafa bayana tace iman wai yau me yake damunki ne?nace banjin dadi ne tace sannu na amsa muna isowa gida kowa na kokarin leka dakin don naga an karo kofar saa ta harareni tace neman suna shishigi babu kwarjini ban kula ta ba na shige dakin da sallama yana kwance sambal a kan 3sitter barci yake amma fuskarshi a sake tamkar yana murmushi don ko idonshi biyu bai cika faraa ba,wayarshi a ajiye kan kirjinshi ina mamakin irin son da yake ma waya na dubi fuskarshi gsky yana da kyau sosai cikinshi a dame tamkar baya cin abinci na kuma duba sa amma shi dogo ne don kanshi a hannun kujerar yake taga ba ma kafar shi ya dora amma duk da
haka kafar sai dai karfinashi ne ya haukan hannun
kujerar farin gajeren wando da yar tshirt itama fara sune jikinshi,na juya da niyar in fita sai naji ance me kike so?gabana ya yi mumunan faduwa nasa hannu na dafe kirjina jakata ta fadi kasa na kuma kasa juyowa jikina sai rawa yake yi nayi waje da gudu a firgice na shiga daki Allah yasa mama bata falo don haka sai na shige dakinmu,sai da na nutsu sannan na fito na shiga dakin mama ta dubeni tace ya sauran yan uwanki suka rigaki shigowa?nace yayanmu ne ya kirani yace na dafa mashi abinci kuma yaki fada min wane zan dafa yace wai kowanne na dafa,mama tace tunda bashi da lfy ne to ki dafa mashi wake da alayyahu ki sa kayan ciki akwai a fridge ki mishi hadi sosai yanda zai mishi dadin ci nace to.Da yake tun a makaranta mukayi sallah sai
na shiga aiki kawai uku da kwata na kammala aikin sai
da na watsa ruwa sannan na aiki sagir ya gani ko kofar dakin yayanmu bude take bayan ya duba ina sanye da riga da siket na farin lesi na shiga da sallama shine ya amsa gaba na na faduwa na shiga abinda na gani shine ya tsorata ni,anty mimi zaune a gabanshi a kan kujera shi kuma yana kwance tana rike da hannunshi bansan dalili ba sai naji duk banji WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG dadin ganin haka ba sannan ga wani abu da ya tokare mani kirji wata tsawa da anty mimi ta dakan ita ce kuma silar rudewa ba zaki ajiye abin da ke hannunki bar nan ba?useless kawai kin wani tsaya akan mutane,na ajiye kan table zan juya sai sannan yayi magana yace baki zuba mani ba zaki tafi,,Najuyo da sauri ban dubesu ba na dauki plate daya
da na kawo don haka na zuba mashi cokali ma daya na
kawo na sa mashi na tura table din gabanshi dan ya
tashi zaune,dakin ya dauki kamshin abinci yace ki kawo wani cokali da plate din tace no ba zan ci ba barshi,na bude fridge na fito mashi da coke da ruwa na ajiye tunda na fito nake mamakin yayanmu iya kwanakin da na dauka ina mishi aiki ban taba jin yace mani sannu ba haka ban taba jin yace abincin nan ko dakin nan baiyi daidai ba sam.Wasa wasa na zama baiwa,gyaran daki nice girki nice aike yanzu duk inda naje sai ya jirani na dawo sannan zai aiken abinda ke ban mamaki bai taba nuna min yana jin dadin abinda nake mashi ba sannan uwarshi da kannanshi sun kara sani a gaba wai mun shanye mata da kabir ma ya kan sani nayi mashi aiki amma ba kullum ba kwana biyu uku hakan ya kan ce a share mashi daki kuma idan na dafa ma yayanmu abinci shima ina zuba mashi to a cikin satin nan ya soma aiki shima aikinshi ya ragu,
Kwanaki sun shura ana saura sati ukku bikin su Anty
Mariya mami take bani Ibr komawar yayanmu in anyi
biki da kwana biyu nan duk naji ba dadi nace mata sai
ya dade zai dawo?tace a’a yace duk bayan wata shidda zai dinga zuwa saboda zancen bikinshi da mami da zaran ta gama HND dinta nace Allah ya bada sa,a
Baba shine yayi mana ankon bikin gaba daya ko da
yake kala biyar suka fitar shi kuma biyu yayi mana, ana sauran kwana goma biki da misalin karfe uku na
yamma ina tsaye bakin kofar yayanmu ina sanye da
atamfa sai karamin hijabina mai less fari takalmina fari yayanmu yace nazo zai aikeni kafin ya fito daga daki sai ga wasu abokanshi suka min sallama na amsa
sannan na gaishesu suka amsa min gami da cewa mai
dakin yana nan?nace yana ciki suka ja fararen kujerun roba da yayanmu ya zuba a gurin suka WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG zauna,sai gashi ya fito guna ya nufo da leda an rubuta SI super market a jiki,yace ga wannan ki hau mashin ai kinsan gidan su mimi ko?nace e yace to ki kaimata kuma ki yi sauri yanzun nan,ga wannan ya miko mani dari biyar na fita ba wai don nasan gidansu anty mimi ba bana dai iyayi mashi musu ne,bansan dalili ba na dai san malali suke,gidansu Amira na shiga sannan nace don Allah ta kira mani mami da wayarta mami tace gata nan ma zuwa gidansu Amiran dana soma mata bayanin cewa ta min kwatancen gidan su Anty Mimi sai tace min me zan je inyi?nace yayanmu ne ya aikeni,suka rakani suda Amira don na hau mashin tayi ma mai mashin din kwatancen inda zai saukeni muka tafi yanda Mami tayi mani kwatance haka nabi bayan na sauka a mashin nan da nana sai gani a gidansu anty mimi na shiga kannanta na samu suna wasa a harabar gidan sune
suka yi min jagora har ciki nan na sami Haj Laura da
wata kawarta suna hira na gaishesu da farko bata
ganeni ba sai da na gaya mata daga inda nake sannan
ta murtuke fuska tace zauna nan na zauna.Ta daga
murya ta kwala ma Mimi kira kan Mimi ta fito sai
wannan kawar tata take tambayarta wannan yar gidan wacece?maman tace yar gidan kishiyar hajiya ce yar’uwata itama ta yatsuna baki tace ai har ta haifi yar da takai girman haka?ko ba amaryasu ba?tace itama mana amma ai wannan agola ce sai shegen kankanba kan ta kuma cewa wani abu sai ga Anty Mimi ta fito tace gani Mumy, Hajiya ta dube ta sannan ta nuna mata ni tace ga mai nemanki nan muna hada ido gabana ya fadi tace meye kike nemana?nace yayanmu ne ya aikoni tace yace me?na isa gunta nace gashi
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG