ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 10 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Bayan na gama firamare na shiga Barewa
Kwaleji ta Zaria,ina gamawa na yi sa’a na fada
Aviation School wato makarantar koyon tukin jirgin sama ta nan Zaria.
Da farewa ba tare da bata lokaci ba, sai aka
tura ni wata makarantar a America, bayan na dawo gida Nijeriya, na dan fara aiki a Legos kamar shekara guda sai aka tura ni kwas a England, a nan ma na sami
shekara daya da rabi. Sannan na koma gida, na yi wata shida a Kano, daga nan aka maidoni nan Kaduna. Rabon Allah ya kaddara a nan za mu hadu da ke”. Sai na ji ya jawo hannuna yana ja mini yatsu, nace,Kai Aliyu”
Ya Kara kwaikwayona, a nan sai ya ci gaba da
ceWa,Asiya ina son yatsunki”
Na wani dan fizge hannuna. Ya ce,Yi hakun
kada in sanya miki cuta ko, ga kuturu?”
Na dube shi na ce,Ni dai ban ce maka haka
ba Ya ce,Ai gara ki ce mini haka da yadda kika
nuna mini”Na yi shiru na yi tagumi. Sannan yace, Bude mini lemun gwangwanin daya”
Na ce,To. Na tashicikin nutsuwa na je na dauko, na buntile bakin na zuba
a cikin kofin takarda wanda ya sayo a Hamdala, sannan na mika masa, sai hannunmu suka shafi juna. Daga nan ya kara rike mini yana murza yatsuna tare da nasa, muka yi shiru zuwa wani dan gajeran
lokaci. Sannan na daga kaina na dube shi, duba cikin sha’awa ga wanda kake so, ai sai naga idanunsa sun
kada sun yi jawur, ya ja dogon numfashi ya ce,
“Asiya ki yarda da abu daya tun da nake, wallahi ban taba samun mace da nake so irinki ba, a gaskiya bana son in matsa miki da maganar soyayya, saboda ina ganinki
kamar yarinya ainun, yanzu shekararki nawa?”
Na ce, Shekarata goma sha biyar da wata
shida”Ya ce,Kin ga ni ko, ni shekara ta ashirin da takwas, kin ga tsoho za ki aure ni in Allah ya yarda Na yi tunanin shekarun da ke tsakaninmu, sai naga shi tsaran Yaya Aminu ne kenan. Na ji dadi kwarai saboda haka nake son ta kasance tsakanina da
mijina, don in ji dadin yi masa shagwaba
A wannan lokaci ne ya ce,
“Asiya ina son ki gaya mini dan gajeran tarihinki”Sai na gaya masa mahaifina da sana’arsa da labarin unguwarmu da kannena, da Yaya Abubakar, har na ce masa yanzu ne ya samu shiga A.B.U Zaria. Sannan na gangaro a kan rayuwata a makaranta, a nan
nake tambayarsa ko Mami Usman kanwarsa ce? Ya ce,Eh” Mami Usman makarantarmu ta gama tana gaba
damu da aji daya. A wannan lokaci ne na yi tunanin nasan mahaifin Aliyu mutum ne mai arzikin gaske. Na fada cikin raina,
“Anya kuwa tafiyarmu zata yi tsawo da Aliyu? Ganin ni dai ba “yar kowa ba ce,
karewa ma mahaifina masinja ne kada in auri Aliyu yan'”uwansa su rika wulakanta ni, amma kuma ai bada su zan zauna ba da Aliyu zan zauna” Sai ya katse mini hanzari ya ce,
“Asiya gaskiya
kina da kokari kamar yadda Suraj ya gaya mini,saboda haka kina gamawa sai ki wuce makarantar gaba ba tare da bata lokaci ba
Ya ci gaba da tambaya ta wane irin aiki kike da sha awar yi nan gaba? Na ce,
“Gaskiya har yanzu ban
tsai da aiki daya ba, saboda ina sha’awar in zama lauya ko “likita ko kuma in karanta fannin sanin aiki da komfuta mai kwakwalwa. Saboda haka ina Kara tunani
kafin in gama sakandire” Ya yi murmushi yace,
“To fa! Matukin jirgin
sama mijin lauya ke nan za a yi, Allah ya tabbatar mana Ya Kara rike mini hannu, na ce, “Don Allah Aliyu tashi muje ka ga su Suraj yanzu na san sun fara gajiya da jiranmu’
Ya yi sauri ya duba agogo, ya ce,
“Wai! Wai!! Yau zan ci kwakwa da surutun Suraj, tashi mu tafi” Bayan mun zuba kayan cikin mota sai na rike murfin kofar na ki shiga na tsaya ina kallon sa. Ya ce,
“Ya ya lafiya kikaqi shiga?”Na ce,Yallabai
gyalena””. Ya ce,Ai ya zo kenan”.
Na yi shiru, sannan na ce, “Gaskiya baza ni ba
idan har ba ka bani gyalena ba
Ya ga lalle da gaske nake yi, sai ya ce,To shigo in baki”Na shiga na zauna na dan sha bula, sai ya warwaro shi daga bisa kansa, ya ce,
“To tsaya In lulluba miki in ko ba haka ba, ba zan ba ki ba”. Na dan harare shi. Ya ce,
“Oho dai harararki ba ta yi mini komi sai
dai in ji dadi”Ya lullu6a mini a kaina ya fiddo mini da fuska,ya ce, “To kin ga yadda ake yi ran da duk kika kara
rufe mini fuskata kika hana ni ganin dan fetalin nan mai kyan tsari, idan na amshe gyalen ke da ganinsa sai ran da kika zo gidana
Muka yi dariya gaba daya. Sannan ya fiddo
“yar takardar da na rubuta mishi ya kara karantawa ya girgiza kai.
Na ce, “Don Allah ka bani in yaga”
Ya ce,
«What? In Allah ya yarda wannan
takardar har
*ya yanmu sai sun ganta. Amma gaskiya
kina da rubutu mai kyau”. Ya yi murmushi na maida masa, sannan muka ja mota muka tafi. Suraj na kwance cikin lema yana karatun New
Nigeria, yayin da su Maryam da su Hajaru suke zaune gefen ruwa suna shan lyiskirim. Suraj na hango, mu ya
fara dura wa Aliyu zagi.
Ya ce,Wallahi mantawa na yi da ma baka
shawarar ku tafi ku barmu a nan, na manta sabon shigane kai wajen soyayya, yanzu haka ko sallah baku yiba?”Aliyu ya yi dariya ya ce,
“Laifin Asiya ne”.Na yi sauri na ce,
‘Babu ruwana Baba Suraj ya ce,
“Abin da za ayi yanzu mu Karasa gidanka Aliyu mu yi sallah tun da la’asar har ta
Dama gidan Aliyu a bayan Hamdala yake kusa
da asibitin nan Nursing Home. A gaskiya gidan yana da kyau, dakuna uku ne da falon shakatawa, falon kam
ya tsaru da gani ka san mai shi ya saba zama kasashen waje, inda duk ka hanga hotonsa me, sai kuwa na
mahaifiyarsa amma babu na mahaifinsa wanda ban san dalili ba.
Amma a zuciyata na ce,
“Lalle akwai Kauna
mai tsanani tsakanim Aliyu da mahaifiyarsa”.
“. Duk da take mace, amma ana iya gane kamar su guda a sarari.
Gadon da ke dakin Aliyu ban taba ganinsa ba,
• ko da yake a ina zan ganshi. Wani irin makeken-gadone, ina ganin katti shida na iya kwanciya ba tare da
wani ya matsi wani ba. An Kawata shi da kayan ado yA
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe