ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 9 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 9 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

 

Aliyu ya daga kai ya ce,Yaya zan yi ai ni

yanzu sai yadda ta yi dani Bayan ya sawo mana abinci su Maryam da

Hajaru suka bi Baba Suraj, sannan Aliyu ya zo ya fara matsa mini sai in koma gaba don shi ba direbana bane, na ki fitowa,

Ya ce,Idan baki fito ba zan dauko ki da

kaina Na lura ba karamin aikinsa bane, sai na bude mota na fito na koma gaba

, na makale jikin kofar

mota. Ya dube ni ya ce,

“‘Asiya babu dama” Ya girgiza kai ya yi dariya.

Muna tafe har muka isa wurin hutawa na musamman, ya dauki kayan abincin ni kuma na dauki kwalbar swan water da lemun gwangwani da sauran yan kayan cinye-ciye.

Muka isa wata babbar bishiyar mangwaro

wadda sai an duka ake shigarta saboda yawan ganye. A gindinta an kafa kujeru, a cikin farfajiyarta wani sanyi ni”imtacce ke fitowa. Sannan ya dauko kafet ya shimfida ya bude abinci ya ce,To bismillah”

Na dauki farantin abincina na dan juya gefe

guda ina ci. Ya ce,Wai ni mene ne dalilin da kike dauka ta kamar wani dodo Asiya?”

_Na ce, “Wallahi ba haka ba ne, ka yi hakuri Bayan mun gama na zuba masa ruwa a kofi, sai ya ce,Idan har kina son in sha sai kin miko mini”Na ce,Kai Aliyu da can wake ba ka?”

Ya ce, “Yanzu Asiya idan da so da kauna ai ko

a baki kina iya bani, kuma maganar da can ai yanzu ta kaura, idan dai har muna tare kamata ya yi komi saikin yi mini”

Na yi murmushi na mika masa, ya amsa cikin

jin dadi irin na ma’abota bege. Sannan ya zuba lemo ya miko mani, na amsa na sha.

Ya fiddo kwalin tabar Benson da lighter ya

kunna, na dan waiwaya na dube shi. Ya ce,

“KO amaryar tawa ba ta son warin taba ne, ni kuwa daga yau ba nar ta idan dai ba ki so”

Na daga kaina a hankali na yi masa murmushi,

na ce,Eh, lalle bana son warin taba, kuma ka san bata Kara komai sai zubar da dukiya”

Daga nan Aliyu ya yi mini alwashin ba zai sake

shan taba sigari ba. Ya bar ta haihaita-haihata. Da ya kare wannan zance nasa sai naji dadi, na dube shi sai ya fara bani sha’awa, balle da na dubi gefen fuskarsa na ga yadda dan gajeren sajensa ya kwanta gwanin ban sha’awa, ga kayan da ya sa sun yi masa kyau.

Ya shiga ka fi shadda ne, farare sol kaftan da

dogon wando da jar dara da takalma jajaye. Idan ka ga Aliyu ba za ka taba zaton yana cin abinci irin nã Hausawa ba, sai dai ko na Nasara saboda taushin fatarsa wadda ta yi lub-lub. Duk da dai shi wankan

tarwada ne ya dan fi ni hasken fata kadan.

Mun yi shiru daga ni har Aliyu, sai dai mu yiwa

juna murmushi lokaci-lokaci. Zuwa can ya dan kau da fuska sai na Kara samun damar kallonsa sosai, a inda na hango jar miya ta dan bata masa riga daga wajen

alijihu. Sai na kyalkyale da dariya, har abin ya ba shi mamaki yadda ya ji na yi dariya. Sai ya ce,Wai lafiya Asiya dariyar me kike yi?”

Na gyara zama na ce,Yallabai yau duk wanda

ya ganka sai ya shaida ka sha miyar kaji in dai an dubi aljihunka”

Ya yi sauri ya duba, ya ce,

“Ai ke kika jawo mini, kin kawo ni nan kin takura ni, da bisa tebur ne ai kin ga da baki sami damar yi mini shammata ba” Bayan mun gama yiwa juna dariya, sai Aliyu yace,

“Asiya!” Ya dan ja sunan cikin makogwaronsa. Naji wani irin abu ya sauka cikin cikina, nama rasa yadda zan yi in amsa masa.

Zuwa wani dan lokaci ya Kara kirana, na daure

na ce,Na’am Ya ce,

‘”Na san kin ji aikena jiya, kuma a bisa

tambayar da Mama Inki ta yi miki na ji dadin amsar, sai dai kuma ya ya in shigo ko mu fita?” Na Kara jan gyalena na rufe ido na yi abin da na tuna ba ya so, ni, kuma gaskiya na kasa sakewa da shi

saboda tsananin so, nake kara jin kunyarsa.

Ya yi tambâyar duniya na ki cewa uffan, har ya

gaji ya dauko biro da takarda daga cikin mota, ya ce,Ni dai yau ba za mu bar wurin nan ba sai na ji

ra’ayinki. Yarinyar nan tum ranar da na fara ganinki, kin shige mini cikin jiki

na rasa yadda zan yi, ko

barcin kirki Asiya ba na iyawa saboda tsananin so a gare ki.

Idan har kin ga tafiyarmu ba za ta zo daya ba,

kada ki kwari kanki, ki gaya mini gaskiya, ga biro da takarda ki rubuta mini gaskiyar abin da ke zuciyarki,

don Allah don Annabi kada ki gaya mini karya

Ya miko mini ma anan shiru nayi ina tunanin

Wai me zan dan gutsura masa wanda na san babu takardun da zasu ishe ni bayyana masa yadda ya sami masauki a cikin birnin raina.

Sai na daure na rubuta masa na mika masa.

Yayi yar dariya ya ce,

“Bari in fara addu’a ta neman

nasara kafin in bude?

-Ya karanta a fili kamar haka;

“‘Asiya na sonka da zuciya daya Aliyu”.

Na gyara rufa sai kawai ya taso ya fara kici-

kicin fisge mini gyalena, ye ce,

“Idan ba na raba ki da gyalen nan ba, ba za ki tsaya ki saurari abin da zan

gaya miki ba” “Kai Aliyu

Shima sai ya kwaikwayi abin da na ce, muka

kyalkyale da dariya. Sannan ya ja rawani da gyalena na yi masa wani irin kallo mai sanya tsigar jiki tashi.

A lokacin ya komo ya zauna daf dani, sai ga

wasu saurayi da budurwa sun wuce ta gabanmu yama rike da ita, yayin da ta dora kanta bisa kafadarsa. Sai najì Aliyu ya ce,

“Asiya kin ga yadda ake yi ba ki

dinga guduna ba, kina rufe mini ido kamar kin ga abin tsoro

Yana wani kashe ido wanda ke sanya duk jiki

yayi sanyi Na ce,

“Idan ka sa ranka a inuwa randa zan

zama taka komi muna iyayi.

Ya ce,Na san da haka, amma ai Allah bai ce

ka rika hana masoyinka ganin fuskarka ba ko?”Sai na sauke hannaye na ina wasa da abin hannuna. Ya Ce,

“Kin ga har na ji dadì Asiya”.

Sannan ya fara bani tarihinsa, inda ya fara da

cewa”Ni Aliyu dan Malumfashi ne kamar ke..

Nayi  sauri na dube shi, ya daga fararen

Idanunsa yace

“Kwarai kuwa, mahaifina mutumin

‘Dutsen Mane mai suna Alhaji Usman Dutsinma, wani babban soja labtanan kanal, amma bayan yayi ritaya ya komo Malumfashi da zama.

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *