ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 21 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
kunshe da matan aure kamar hudu da yawan
Yaya manya da kanana. Na sami matan gidan na gudanar da ayyukan tsakar gida, masu girki na yi, masu wanki na gefen
famfo suna yi: Sai na sami wata mata na zaune a inuwa tana murza taliya, bayan na gai da ita na tambaye ta, ko Jamila na nan? Ta ce mini,Eh, Ke Zilai raka ta dakin Jamila”
Na sami Jamila zaune bisa gado tana yiwa
wata yar karamar yarinya kitso wadda a bisa
dukkan alamu kanwarta ce, ta amshe ni a mutunce duk da dai ba ta san ni ba.
Bayan mun gaisa ta kawo mini ruwan sha,
sannan na shaida mata tare muke da Suraj. A nan fa ta dafe kirji tana Kyalkyala dariya, tace
“Ki bari don Allah, shine baki bani sani ba?”
Nan take ta sanya kanwarta ta kawo mini
abinci, ita kuma ta nufi zaure inda ta bude dakin baki ta share shi, ta yi ta kai da komowa tana shiryawa su Suraj abinci. Bayan da ta gama kintsa musu wurin zama, taTa bemi su suraj suka shigo don su gaisa kuma susha ruwa suci abinci ni kuma dana gama cin abinci saina fita nayi alwala na ba da farali, na dauki hodar Jamila na gyara fuskata, sannan na sake sabon wani daurin Na tsaya ina kallon hoton Jamila da Suraj wanda yake rataye a dakin, da ganinsa na san lalle sun dace da juna, saboda ita ma Jamila ba a barta
baya a fagen kyau ba Sambaleliya ce jawur da ita kamar tada, sai dan fadin baki da labba sirara, yayin da idanuwanta masu girma, amma sun dan shiga inda suka karawa
hancin ta . Ina ta kallon hotonta ne tayi sallama ta shigo, ta ce,
“Ki yi hakuri na barki ke kadai, ga shi ko
hotuna ban ba ki kin yi kallo ba. Su Suraj kuma sunce ki fito ku tafi?* Na ce,
“A’a, babu komi ba ni in kalla ai ba
sauri nake yi ba, iyakar mu Malumfashi” Bayan na gama kallon hotuna ta ce in zabi
•wadanda nake da sha’awa, na zabi kala hudu, uku ita kadai, yayin da dayan ita da Suraj. Ta ba ni jan baki da jan farce, da gazar da man shafawa, na yi godiya, na ce,
“Ina fata ita ma zata ziyarce ni wata rana”
Ta ce, Insha Allah daga yau zumunci ya Kullu
Ta yi mini rakiya har gindin mota inda su
Aliyu ke jirana, sai Aliyu ya ce,Jamila Asiya tayi
miki bayanin kanta?” Ta yi murmushi ta ce,
“Ai ba sai ka tona taba
da ganin irin shigar da kuka yi ai an san ka sami abokiyar rayuwa bana, tunda na Fito naga yadda kake ta washe hakora ai na san kwanan zancen Yace
“Amma yadda kika yankan zan rama,
kin dauki bashi wannan karon’ Yana dariya ita kuma ta ce mini,Don Allah Asiya idan kin ji ina yi wa Aliyu tsiya ki yi shiru
kawai, ba ki san irin tsiyar da yake yi mini bane amma ,,,,,,,,,,, nace To Mama Jamila”
Sai Suraj ya fashe da dariya, ya ce.
“Asiya har kin yi saurin kiran ta Mama haka, maimakon kice muka yi dan barkwanci na abota,sannan Aliyu ya fiddo da kudi naira hamsin ya bata, ya ce kada ta sanya idon ganinsa gobe sai dai Suraj, saboda yanzu yana da gurin zuwa. Ta ce,
“Nima ba gayyarka, ka bar ni da angona mu sake”” Yace
‘”Oho dai ba ni rako shi gobe”
Da la°asar likis muka iso unguwar muta
Kofar Fada a Malumfashi, muna taka birki Kanina Yusuf yana shara, ya sharo zaure har ya fito bisa baranda yana sharewa, sai ya ji tsayuwar mota.Juyowa ya yi da sauri ya dago kai, ya hango mu nan take ya jefar da Isintsiya ya nuto mu yana fadin Yaya Asiya barka da sauka• Sannan ya gaida su Suraj
Sai Aliyu ya bude but din mota ya fara fiddo
kaya, aka dorawa Yusuf talabijin, ni kuma na nemi in dauki akwatina, sai Aliyu ya ce,
“Gafara nan raguwa ke za ki iya dauka”
Na sakala jakata na nufi cikin gida, na tsai da
Yusuf kan hanya na tambaye shi Yaya Abubakar nanan?
Ya ce,A’a, ya tafi Zaria”Na ce,
“Ina fata ka share dakinsa?»
Ya Ce,Eh, na share, bakin za su dan huta
ne?Na ce masa,eh Sai ya ce mata,
“Baki son dakina?”Na ce,
“A’a, naka dakin ba kujeru sai gado
kawai, shi kuma Yaya Abubakar yana da kujerun zama Muka isa cikin gida, Zainab ta fara tsalle tana murna ga Yaya! Ga Yaya!
A lokacin Inna na kewaye, na rungume Zainab muna murnar ganin juna.
Shi kuwa Yusuf yana aje talabijin ya ci gaba
da jido sauran kaya, sa’ilin nan ne Inna ta fito, na ce,Inna. Ta ce, Uwani sannu kin iso, ya ya su Inki?” Na ce,Lafiya lau, tare muke da su Baba Suraj, bari in kai su dakin Yaya Abubakar k0 ruwa sun sha ko Inna?’
Ta ce, “Eh, kwarai kuwa Ita kuwa Zainab hakora sunai rufuwa, sai Yusuf ya fara shigowa da manyan kwalaye yana
ajewa, ya ce,Inna wallahi wanna kayan da Asiya ta sanya anko suka yi da wani mutum cikin wadanda suka kawo ta, ko saurayinki ne Asiya?”Sai na harare shi na ce,
“Ina ruwanka?” Na yi sauri na dubi Inna, sai na ga ta daure fuska, sannan tace
“Ke ni je ki daki ki dauko mini kwanon sha da
murfi ki debi ruwa a tulu ki kai musu, bari in yi
sauri in dama musu fura Zainabu ta kawo musu” Na ce,To”. Na Fita na ce,Su shigo daga
ciki Na aje ruwa, sai Suraj ya ce, “Bari in riga ka shan ruwan tun da yanzu nine surukinka
Sai Aliyu ya ce,Komi ka yi mini yanzu
daidai ne, amma kada ka manta zan dau fansa wata rana Suraj ya ce,Ba dai ka rama ba sai dai ka rame, ko ya kika ce Asiya”?”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe