ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 22 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Na sunkuyar da kaina Kasa na ce,
“Baba Suraj wannan maganar taku ce ta manya ta fi karfina”Na fadì hakan ina murmushi. Sai ga Zainab ta yi sallama da muryar ta mai zaki suka amsa mata, ta aje kwanon fura sannan a cikin nutsuwa ta gaishe su.Aliyu ya ce,Wannan Zainab din da kike ban
labari ce ko Asiya?”Na ce,Eh, ita ce”
Ya ce,Zo nan Zainab”Ta je wajensa ya rika yi mata wasa, ya ce,Gaskiya Suraj duk yadda ka so ba ka taba samun daidai ba, abin da nake nufi a nan shi me, abincin bariki ba ka hada shi da Kauyukanmu. Ba za ka taba
samun irin wannan furar a Kaduna ba”
Suraj ya yi dariya ya ce, “Kai dai santi za ka
yi mana Aliyu Sai na yi karaf na café na ce,
“A’a, Baba Suraj ba maganar santi ba ce yana da gaskiya a nan, masu furarmu na nan ba su kai wa injin da kansu zasu surfa su dake garin a turmi da tabarya, amma matan Kaduna ba za su yi máka haka ba, sai dai injin saboda haka dole ta nan ta fi gardi”Suraj ya ce,
“Eh,lallai na yarda, don haka ban
damu da shan fura ba a Kaduna Aliyu ya ce,
“Zainah ajinki nawa?” Ta ce,Ajina hudu a firamare”Yace Baba na nan gidan?”Ta ce,
“Tun da safe suka tafi Katsina shi da
Malam Bawa, gai da wani dan ‘uwansu da aka yiwa tiyata, amma ya ce yau zai dawo”
Mukace Allah ya ba shi lafiya” Sannan Suraj yace Asiya gara ki gaya wa Yaya Aisha za mu shigo mu gaisa”Na shiga na shaida mata, ta shimfida mana yan tabarmi a falo, su Suraj suka shigo ciki Aliyu na rike da hannun Zainab, yana mai cike da jin kunya ba ya ko iya daga kansa sosai.Ita kuwa Inna tayi lullubi da gyalenta na atamfa, ta zauna a kan, dandamalin ba kin Kofa na dakinta, ta sunkuyar da kanta kasa kamar ta ce kasa
bude in shigo saboda jin kunya, Ni kuma na shiga dakina ina sauraren abin da zai biyo baya,Bayan sun gama gaisawa ta tambayi lafiyar gidan su Mama, su kuma suka yi mata jajen mara lafiya da Baba ya je dubawa. Zuwa wani dan lokaci Suraj ya ce,
“Yaya Aisha ga abokina Aliyu wanda ke
son Asiya”Yana dariya ya fadì hakan.
“Kai Suraj da shirme kake, wannan
kuma Ai tsakaninku da hajia inki, ne ni kuma meya tsoma ni cikin wannan zance” Ya ce.
“Ai dama mun gama magana da ita
mun shaida miki ne kawai don karambani irin
nawa Ta ce. Gara da kace karambani”
Da suka gama gaisawa suka yi sallama suka
Fito. Daga bisani suka aiko Yusuf in z0, na same su a zaure. Aliyu yace
“Asia za ni gida in gai da su sai da dare zan zo ko kin gaji?”Na rabe jikin bango na ce,
“A’a Suraj yaCe.Wai yau gidanku zasu yi
mamakin ganin har zaka kwana biyu a
Malum fashi Aliyu yaCe
“Wallahi kuwa, zuwan kwana daya ma na rabu da yi, ai ga gimbiyar da ta jawo ni
nan. A nan fa ake yinta kaza ta jawo zakara
Suka fashe da dariya. Na raka su har gindin
mota ina mai godiya a gare su, na juyo zan shiga gida sai ladiza ta leko kofar gidansu ta kwalla mini kira, na ruga aguje muka rungume juna, sannan muka karasa cikin gidansu.
Inna hafsatu ta tare ni da murna, ta ce,
“‘Asiya me suke baki yarinya nan da nan kin canza?” Madiza taCe, Wallahi ba ki ji yanda kike zabga kamshi ba kamar wadda ta fito daga kasar waje Lokacin Zainab ta biyo ni, ita ma tace,Yaya Asiya wallahi kin yi Kiba, kin yi jawur, Kaduna da dadi ko?”Na ce,
“Sosai ma kuwa, ga ni’ima”Daga Inna Hafsatu har Hadiza zuwa Zainab
haka suka dinga yi mini tambayoyi ina basu amsa, da kyar na samu muka kebe a zaure da ni da Hadiza da tazo yi mini rakiya. A nan na sami damar bata labarin Aliyu, tayi mamaki
yanzu har na sami saurayin da ya kwance mini kai, sânin halina akan samari
Na Ce,Wallah Hadiza Aliyu ba kai kawai
ya kwance mini ba, harda zuciya babu wani noti daya rike mini ita, Aliyu ya kwance mini ita tsaf. Ni yanzu inba Aliyu ba sai rijiya
Muka kyalkyale da dariya muka. Na ce,
“Na rasa inda zan aje Aliyu a sararin zuciyata, ya riga duk ya mamaye mini gabobin jikina da dimbin so da Kaunar sa Hadiza ta sa hannu ta rike habar bakinta tana saurarona, tare da jinjina abin da nake fada mata.Sannan tace
*Gaskiya Asiya idan da a kwanakin
baya ne kika gaya mini wannan maganar zanyi tir da ke, amma cikin halin dana shiga bayan tafiyar ki da kwana uku, sai ince babba gareki Kin san lokacin da za ki tafi Kaduna kin bar
Inna Aisha za ta biki Katsina a unguwar Galadanci, to Allah da ikonsa sai ta nemi da in raka ta dani da Zainab, muka kashe sati guda a katsina. To ashe ni ma nawa rabon ke kirana, a inda Allah ya hada ni da wani sandirin saurayi mai suna Mukhtar kafin soli. Muna tafiya da ni da Zainab mun fito gidan Hauwa Bello kawarmu, sai ya sha gabanmu da mota, ya matsa mini da son ya rage mini hanya, har dai na gaji na shiga ya kai mu
Galadanci, ya kuma ce zai dawo da yamma na
amine masa. Bayan ya yi zuwa kamar sau uku wajena, na tabbata yana sona na hakika babu maganar yaudara, sai na ba da kai bori ya hau. Kafin dai mu bar Katsina sai da Mukhtar ya kawo mahaifiyarsa suka
gaisa da Inna Aisha, yanzu halin da muke da
Mukhtar ya zama dan lelen zuciyata, ina ji da shi kamar raina, yadda ba ni son in rasa raina, haka ba ni son in rasa shi.
Duk asabar a nan Malumfashi muke shan
hirarmu sannan ya koma gida Katsina, gobe ma insha Allahu zai z0, daman duk ya Kosa ya ganki, tunda na ba shi labarin yadda muke da ke”Na nuna mata jin dadina da al’amarinmu yaZo lokaci daya haka, mun sami samarin da muke
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe