ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 27 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Ya neme ni da in zuba musu kifin, sai nã
tsuguna na zuba musu, nace, Bari in zuba
wa karamin miji da yawa kada ya ce na cika rowa” Umar yace Kin san kuwa ci gare ni kamar gara Nayi murmushi, bayan sun gama shan
farfesun kifi sun yi yan tande-tande, sannan ya
bayyana mini cewa, Umar Kaninsa ne ubansu daya. ya gama karatunsa a Jami ar Bayero ta Kano, ya yi bautar kasa a Jihar Ondo, yanzu zai fara aiki Bankin U.B.A na nan garin Malumfashi.
Na zo da shine dan ya ganki ki gan shi,saboda shi zai rinka kula mini da ke, ta fannin sada wasika da kuma zuwa wajenki a duk lokacin da ya
sami dama, idan kina da wata bukata ki rinka sanar da shi. Ko da yake ni ma ba ki gaya mini bukatarki,sai dai ban san shi ba kila ya yi sa’a”
Muka hada ido da Aliyu karo na uku, muka
yiwa juna kallon kwanciyar zuciya tare da kashe ido.Shi ma Umar yana murmushi ya sunkuyar da kai kasa, sannan ya tambaye ni ko Hadiza na gida ne? Na ce,Eh, bari in je in kira ta
Sai Umar ya ce,Ina ne gidan in sami yaro in
tura ya kira ta?” Na Ce,
Daka fita gidan dake kusa da namu kana iya shiga ka yi sallama ba sai ka Tsaya
neman wani yaro ba Ya fita ya nufi gidan su hadiza, sai Aliyu yace Abubakar bai z0 bama wanna satin?”Na Ce, wasika, ya ya Baba Suraj?”
bai z0 ba, sai dai ya rubutoYa Ce, Ya tafì aiki Lagos shekaran jiya, naje naje gidan su Mama Inki jiya na ce ko suna da sako,sai Hajaru suka ba da wasika in kawo miki, suna cikin mota idan na tashi tafiya zan baki Na ce,
“Allah sarki su Hajaru, na san sun yi
maraicina Aliyu ya ce,Lalle kuwa saboda lokacin da suka ganni kamar sun ganki”
Hadiza da Umar suka shigo tare, bayan sun
gaisa tare da ‘yan barkwanci sai Hadiza ta mika wa Aliyu wani dan karamin kati tace
“Gashi in ji Mukhtar ya ce in ka sami dama ka buga masa waya a ofis ranar Litinin
Ya amsa ya duba, yace Insha Allahu zan
buga masa”Ya ci gaba da cewa,Gobe kamar
yanzu kuna cikin daji kunshe Hadiza
Tayi murmushi tace,Haba Aliyu har da
tsokana?” Sai Umar yace
“Yau dai ai baura wata biyar ku sami
‘yancin kanku’ Hadiza tace
“Haka ne fa Umar Sai ta fara hamma.
Aliyu ya dubi agogo ya ce,lalle kin ji
barci Hadiza, yanzu Karfe goma da rabi”
Daga nan muka tashi gaba daya za mu raka
su gindin mota, amma me zai faru? Hadiza da Umar na fita ni kuma har na kai bakin Kofa sai kawai na ji Aliyu ya jawo mini hannu, na juya a hankali na dube shi na sunkuyar da kai kasa.
Na ce Aliyu mene ne?” Yace
“Asiya ce” Na.ce,Ta yi maka mene ne?”
Ya ce,Ta ban sha’awa, kuma ga shi za ta gudu makaranta”Nace
“Don Allah sakar mini hannu ka ga Umar na jiranka”Sai ya yi mini wani irin kallo mai fassarawa
masoya abubuwa da dama, wanda duk yadda na so in kwatanta ba na iyawa, sai wanda so ya taba
bakuntar zuciyarsa.Mun dade tsaye. a haka, idona na Kasa ina duban kafar Aliyu wadda ke bani sha’awa matuka,yayin da idon Aliyu na bisa kaina. Sai can na ji ya jawo ni ya rufa bisa Kirjinsa, ban san lokacin da na kwantar da kaina bisa kirjinsa ba, shi kuma ya rika ja mini gashi.
Zuwa can a cikin murya mai kyarma yace
“Asiya gashin kanki na Kamshi”
*. Sai na daga kaina na dube shi muka yi murmushi, ya fiddo wata yar karamar batta mai kunshe da wani Karamin zobe na zinare, ya jawo hannuna na hagu ya sanya mini a dogon dan yatsana, sannan ya sumbaci tsakiyar tafin
hannuna, nayi godiya. Ya ce,Komai wuya, don Allah Asiya kada ki rabu da wannan zoben”
Na dago ido na ce, “Aliyu ya ya za a yi in
rabu da wannan zobe matsayin ina cikin kaunarka,alkawari ne na dauka, matsayin ina raye, to lalle wannan zobe yana yatsana. Yanzu kuma duk lokacin da ba mu tare da kai, to zan kasance mai tunawa da
kai a kowace dakika idan na dubi wanna zobe.
Abin nufi a nan, wannan zobe ya zama tamkar
fuskarka ce a gare ni” Muka yi dariya ya shafi gefen fuskata. Muka isa gindin mota inda Umar da Hadiza ke tsaye suna jiranmu. Aliyu ya bude but din mota ya fiddo wata
Katuwar jaka irin ta zuwa makaranta, ya miko mini
na amsa na ce na gode Allah ya kara dankon kauna. Su Hadiza da Umar suka ce,
“Amin Ya bani wasikar Hajaru muka yi sallama. Ya ce sai yazo kaimu makaranta gobe.
Da na isa gida muka bude jakar sai na ga
komfiles ne kananan kwali da zumar kwalba, da
gwaldinne da cakulet da sauran kayan ciye-ciye.
Na nunawa Inna ta ce,Kai wannan yaro da hidima
yake, yanzu kada ki tambayi kudin wannan kayan.
Allah ya tabbatar da alheri, yawancin mu iyaye
bamu son irin wannan hidimar, idan ba mun ga an
daura aure ba, mun fita kunyar mai neman yaro,
hankalinmu bai cika kwanciya ba.Su kuma maza idan suna neman yanmata
babu abin da suke so illa su ga suna dauke wa iyaye dawainiya, mu kuma munfi son sai ka mallaka wa yaro ya komi ya yi mata daidai ne, domin ya yiwa matarsa ne. ita ya mace sai an daura mata aure kike fita zulluminta, Allah dai ya fidda mu kunya” Na ce,Amin”
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe