ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 28 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
RANAR LAHADI NA TASHI dukufa aiki
da duhu-duhun dare saboda shirye-shiryen komawa makaranta kuma da hidimar abincin Aliyu. Da azuhur na fiddo musu abinci, na barsu
suna ci na nufi gidan su hadiza muka taho tare,
muka zauna muka taba yar hira, sannan
ya umarcemu da mu fiddo kayanmu.
Aliyu ya bani naira dari uku, ya bai wa
Hadiza naira dari daya, muka yi godiya. Na ce na
mika wa mahaifiyata na ce mata,Ki rike kudin da
Aliyu ya bani ne na zaman makaranta, sai dai saboda a wannan zamani naira talatin ta ishi mutum ya kashe tsawon zaman sa na wata uku a makaranta” Muka yi sallama da iyayenmu muka fiddo kayanmu, Umar ya zuba mana cikin boot, muka kame a gidan baya ni da Hadiza, shi kuma Aliyu da Umar suna gidan gaba. A haka ya
sanya mana sauti mai sanyin taushi, muka rika taFiya a hankali kamar ba a cikin mota muke ba, muna tafe Aliyu yana bin wakar dake yi cikin kaset, yanà yi yana daga kai yana lekena ta cikin madubi jefi-jefi. Na rinka tunani a cikin zuciyata ina cewa, inama. a ce wannan tafiya daga ni sai Aliyu za mu yi ta,wadda za ta zarce da mu har Jihar Bauchi inda zamu yi masauki a Yankari a kuma matsayin ango da amarya, wadanda suna cikin watansu na farko da aure, da na sami damar mai da wa Aliyu martani na irin surutan soyayya da yake yi mini, da sauran abubuwan da duk masoya ke son cimma burinsu na sha’awa.
Sai karaf na ji Hadiza na zungura ta, ta ce,
“Ba ki ji maigadi na yi miki sannu da zuwa ba?”
Na yi sauri na ce,Yauwa Baba maigadi ina
wuni?”Ya bude mana get muka isa har kusa da
dakunanmu, Hadiza ta samo yan aji uku suka
daukar mana kaya. Ni kuma na tsaya muna kara
sallama da Aliyu,Ya fara yi mini gargadi yana fadin,To Asiya a ci gaba da mai da hankali kamar yadda aka saba a da, kada ki rika matsawa kanki da tunani,wannan wata dama ce ta Karshe a gare ki, idan kika kuskure ta sai kin kara maimaita shekara. To kinga gara a tsaya a yi yadda ya kamata kada a Kara mai da mana da hannun agogo baya ko? Kuma ki Kara rike
amanar zuciyata Kwarai, saboda na mallaka ta gaba daya a hannunki, kada a yi wasa da ita Asiya, kamar yadda zan taba wasa da taki ba a hannuna ta sami karbuwa har abadan abada kin ji ko Asiya? Na daga kai na dube shi muka yi murmushi mai sanyaya zuciya tareda Kara amincewa juna, sannan ya ce, Wai tunanin me kike yi ne dazu a mota har kika shagalta ba ki san mun iso ba?”Nace Kai Aliyu Yace
“Ke Asiya^ Muka kyalkyale dadariya. Yace
“Ai na san tunanin da kike yi na karanto a fuskarki, sahoda haka ran dà kika zama amaryata zan fassara miki Muka sake dubar juna muka yi
murmushi sannan muka yi sallama, ya ce sai yazo ranar ziyara.Na ce.To, mun gode Allah ya kiyaye hanya. SukaCe Amin
Na isa dakinmu na cimma hadiza har ta fara
gyara mana kaya, muka hada muka share kwanarmu.sannan muka gyara shimfidar gadajenmu.Daga nan muka fidda kayan abincinmu, muka shirya SU cikin loka,
a inda muka bar kayan
sanyawarmu cikin jakarmu. Sannan na cewa Hadiza,Gara mu kai wa hajiya metoran miyar kajinmu ta sanya mana a na,urar sanyaya abinci don gudun kada ta lalace Akan hanyarmu ne ta
dawowa daga dakin hajiya metoran muka ci karo da Kawayenmu Yan Katsina a nan fa muka fara
murna Daga nan dai muka doshi dakinmu inda muka fara hirar bayan rabuwa. Sai Fatima ta ce,
“Asiya kin canza mini, kin kara girma, kin yi kyau jikinki ya yi lub, yayin’ da fatarki ta sake sheki, ga gashin jikinki ya fara tofowa ya kwanta lambas, gwanin ban sha’awa
Nace Kai Fatima wannan irin washi sai kace wata budurwa da saurayi”Muka Kyalkyale da
dariya. Na ce,Fatima wai ina maigida Ibrahim yau
ba a bamu labarinsa ba?” Ta ce,Ashe ya Asiya kina son hira tunda kika takalo mini
abin da ke mini Kaikayi”. Sai Fatima ta
fara bamu labari har aka kira sallar magariba, muka tashi muka nufi masallaci don bayar
da farali. Washe garin litinin ba mu fara aikin aji ba saidai gyare-gyaren wurin zama,
kamar share ajujuwanmu da nome ciyawa
da ta cika mana makaranta. Sai da muka sami Kimanin kwanaki uku muna aikin tsabtace makarantarmu. a rana ta hudu ne muka shiga aji malamai suka dukufa a kan aikinsu
na koyarwa.Mu yan aji biyar masu niyyar fita a wannan shekarar, munci gaba da shirye-shiryen daukar jarrabawar mock
Malamanmu sun dukufa da Kara maimaita
mana darussan da muka riga muka yi dasu mu kuma bamu da wani takamaiman lokaci na Kanmu sai dai karatu Munyi sa,ar malamai Wannan Zamanin saboda ko lokacin karatun dare
da ake Kira high prep da na yamamci wato evening prep da aka ware mana na muyi
nazari da kanmu, basu barmu
haka nan,Ba suna nan tare damu
sun dukufa nuna mana karatu. A wannan lokaci
ina daya daga cikin shugabannin yara
na ajujuwa kanana daga dayà zuwa hudu
don na kula dasu kamar a lokacin
karatun dare ko na maraici. To ni ke da aji (1B), a
cikin kowane aji na makarantar akwai dan karamin sito, saboda haka a zamaninmu muka kara mai da wanna sito dakin karatunmu.
– Abin nufi a nan, idan mun tsare yara lokacin
karatun yamma muna koya musu irin abin da ya
shige musu duhu, to bayan an tashi
mu kan rika amfani da wannan sito don mabuyar karatu ba tare da an dame
mu ba. mu kan kai har misalin karfe
biyu na dare muna karatu, mu hudu muka mallaki
Wannan sito na ajin (1b), wato da ni da Hadiza, Rabi Lawal Kumurya, da Fatima Bala Katsina.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe