ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 30 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Ta ce, “Hadiza Ibrahim’ Yace, “Ashe “yata ce, kawar taki fa?”Na yi sauri na juye ganina, na kau da kai.Hadiza ta ce, “Asiya Yusuf”.Ya ce, “Hadiza za ki bai wa baban naki Asiya ko?”Muka kalli juna
da ni da Hadiza muka kyalkyale da dariya, sannan Hadiza tace, “Idan kana so sai in ba ka mana, ni na hana tsohona kawata?”Ya ce, “To ai kuwa na gode, to Asiya me kikace kina so na?”
Sai na daga kai na dubeshi, na mai da kaina
Kasa nace Tò ni na Ki baban Hadiza, sai dai kuma ga wani hanzari ba gudu ba. Nace
ba zan yaudare ka ba, ina da wanda nake so zan aura da zarar na gama makaranta”Ya yi shiru, sai zuwa can ya nisa ya ce, “To Asia na ji dadin wanna kalami naki, amma saboda Allah zan tambaye ki, yanzu iyayenki sun shaida wa
Iyayensa sun ba da ke a gare su, ko kuwa an daura muku aure?”*Na yi shiru, sannan na ce, “Duk abin da ka fadi babu daya da aka gindaya mini, sai dai ina jin wannan másoyi nawa cikin jinina Kwarai ainun, ba na jin idan ba daga gare shi ba zan iya rabuwa da shi” Sai ya yi dariya ya ce Asiya kin ji masu iya magana sun, ce rigimar duniya da mai rai ake yi, na ji dadin wadannan
maganganun naki, saboda duk namijin kirki yana alfahari da samun mace mai kamun kai da fadar gaskiya, ina ne gidanku?”Na yi masa kwatance. Ya ce, “Kada dai in ce yar gidan Baba Masinja ce’?”Na ce, “Kwarai kuwa shine mahaifina”
• Ya ce, “Shi ke nan faduwa tazo daidai da zama, daman ubangidana ne, ma’aikatarmu
daya da shi, saboda haka bari in barku ku yi karatu, sai na zo anjima bayan sallar isha'”i”. Muka yi sallama ya tafi. Bayan mun gama karatu muka kama hanyar gida, muna tafe muna zanta abin da ya faru tsakaninmu da Ibrahim. A nan nake tambayar Hadiza na ce, Yanzu Hadiza idan ke ce ya ce yana so ya ya za ki ce masa?”
Hadiza tace Yadda kika ce masa haka nima
zan ce, sai dai kuma yadda kika rika washe masa baki kina sakin fuska shine ya daure mini kai, bayan na san matsayin Aliyu a wajen ki”Na yi murmushi na ce,Nima kaina na yi mamakin ganin matsayin Aliyu a zuciyala, amma kuma sai na ji bana iya daurewa Ibrahim fuska, amma
ban san dalilin yin haka din ba Hadiza”Sai ta ce, “Kila shine mijin”Tana kallo na tasa dariya. Nace “Allah ya kyauta, amma hadiza kin Kware ni, da ganin wannan mutumin ai kin san yana da iyali, Kila ma matansa uku wa ya sani”Sai Hadiza ta ce,
“Ai ko matansa uku babu damuwa kina da daki a gidansa, sai ki zama ta hudu”.Na ce, “Hadiza ki daina yi mini baki saboda ba zan so a ce haka ta far tsakaninki da yayana Mukhtar ba Na ci gaba da cewa, “Idan yazo ma anjima ba zan
Fito ba, gara ki san abin da zaki ce masa
Ta ce, “Wannan amma da kin sha karya, ki bai wa dan tahaliki fuska, ki kuma ba shi adireshin inda zai z0 ya same ki, sannan ki ce za ki barni da zance da ‘yar murya, a’a, ki sake magana. Ni ko guna ya zo ba ni zaton zan fito yau, saboda ina son taya Inna aikin abincin baki masu zuwa gobe daga gidan su Mukhtar,masu kawo kayan zance’
Da haka muka iso gida, Hadiza ta nufi gida
nima na shiga gida ina cike da tunanin abin da zai je ya komo a kaina. Ina nan zaune tareda mahaifiyata da Zainab muna kallon talabijin har misalin karfe tara Ibrahim bai z0 ba, ina ta addu’a a raina Allah ya sa maganar dana gaya masa ta ratsa shi ya fasa zuwa, amin.Na yi tunani ko in sanar da mahaifiyata abin da ake ciki, sai na fasa saboda na tuna da maganar da ta yi
mini tun farkon zuwan Aliyu gidanmu, inda tace mini ban da janye-janye. Ina cikin wannan tunani wanda ya sanya na kasa sakewa yadda na saba, ina lura da Inna tana kallona jefi-jefi amma ba ta tambaye ni dalilin da ya sa nayi zugum ba, sai dai na san ta san akwai dalili ruwa baya tsami banza.
A lokacin sai wani almajiri ya yi sallama yace
“Wai wani mai farar mota yana sallama da Asiya
Gabana ya yanke ya fadi, na rasa abin da ke mini dadi saboda zuciyata na bani lalle na dauko wa kaina rigima ba kadan ba. Na yi shiru zuwa wani lokaci, sai Inna ta dan harare ni tace
“Ba da ke ake magana ba?”Sai na kalli almajirin da ke tsaye bakin kofar falo nace
“Jeka ka ce an ce wane ne?”Sai almajirin ya ce,
“Daman ya ce idan an tambaya in shaida miki Alhaji Ibrahim ne wanda kuka hadu dazu bisa hanya” Na yi shiru kamar ruwa ya ci ni, sannan na ce,Jeka ina zuWa Ita kuma Inna ba tare da ta ce mini uffan ba, sai ta dauki buta ta zagaya bayan daki. A nan na nemi Zainab da ta zo muje tare amma sai ta Ki amincewa saboda wai tana so ta kalli wasan Kasimu Yaro wanda an kusa farawa.
Ina nan dai har Inna ta fito ta cimma wannan
Rigimar, ta ce,Tunda ta ce ba za ta ba, to ki tafi mana kin bar mutum yana tsaye tun dazu” Na tashi da fushi na fito kofar gida, na same shi
Tsaye gindin motarsa ya goya hannunsa bisa kirjinsa.Ina takawa a hankali yayin da shi kuma ya langabe kansa yana kallo na tare da murmushi a cikin fuskarsa,
na cimmasa na yi masa sallama, sannan na gai da shi. Shi kuma ya ce, “Har na fara fidda rai ina cewa Kila ba za ki fito ba Asiya”Nace, “Me zai hana ni fitowa tunda na san nice na baka adireshin gidanmu, ko ba zan dade ba ai dole
na Fito, kai ne ma na yi zaton ba za ka zo ba da naga dare ya fara mikawa. Na ce Allah ya sa ka yi amfani da abin da na gaya maka ka hakura”
Ya yi dariya yana kada ‘yan makullai dake
hannunsa, ya ce, Wallahi Asiya idan kin ga na daina zuwa gare ki, to an daura miki aure wanda ba yadda zanyi a lokacin. Abin da ya sa kika ga na dan jima ban fito ba, saboda na yi azumi yau na gaji, lokacin da na shiga wanka kuma sai na fito na sami baki suna jira na, kin ji dalilin tsaikona”Ya dube ni ya yi murmushi. Sai na ce,
«Wane irin azumi ka yi yau?”Ya ce, “Kina nufin ke ba ki yi ko daya ba? Kinsan wannan watan azumin masu wayo ne wanda mutane suka fi kira da azumin tsofaffi’.Sai na ce, “Okey na tuna”
Yace”Yau ga shi har wata ya yi kwana sha uku
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe