AMAL CHAPTER 1

AMAL





CHAPTER 1




Wata mota ce ta tsaya a gaban wani super market, “kiran Prado, gaba d’aya motar tinted ne baka ganin wanda ke cikin motar, sai dai Shina motar ya ganka.

Gaban motar aka bud’e wani matashi, chocolate colour ya fito daka cikin motar, cikin k’ananan kaya, ” bud’e Bayan motar yayi Wanda hakan ya tabbatar dashi driver din wanda ya bud’e ma kofar motar ne, “wata yarinya ce Fara sol Doguwa, ta fito daka cikin motar, sanye take cikin k’ananan kaya English wear, ” kana ganin yarinyar kasan y’ar wani babba ce, domin batai Kama da matar aure ba ko ince wacce zata mallaki dukiya tata ta kanta, yarinyar tana dakyau duk yanda mutum yakai da kushe, inya kalla Amal zai ga kyawun da Allah yayi mata.

Bata ko kalli saurayin dake tsaye ba, wanda ya bud’e Mata kofar kenan, ta wuce cikin super market d’in, cikin tafiyar ta wacce takeyi kaman bazata taka k’asa ba.

Shiko saurayin daya tu’kota Kai ya girgiza alaman mamakin irin halin wannan yarinyar, “kwata kwata bata d’aukan duniya da sauk’i, “lokaci d’aya kuma yayi d’an murmushi tare da fad’in “dukiya yasata take ganin kowa ba komai bane, amma bata biyo halin ubanta ba, domin ba haka yake ba, “mutum Mai daraja dan Adam da girmamashi.

Amal kam koda ta shiga super market d’in, “tsayawa tayi tana jiran Usman driver d’inta kenan, tana jira ya shigo ya ri’ke mata basket, “kallo d’aya zaka mata Kaga bacin rai a fuskanta, wanda wannan bacin rai din bana komai bane saina Usman daya k’i shigowa ya ri’ke mata basket, “cikin bacin rai ta fita tare da nufa motar inda ta ganshi a cikin motar zaune abunshi yana waya “ranta taji ya kuma baci Sosai, “Wanda yasa ta Fara buga glass din motar.

Usman bud’e Mai yakon ya bud’e kofar motar, saiya sauke glass din motar, “ranta taji ya kuma baci Sosai tare da tambayan kanta Mai yake nufi ne?

Usman yace “Amal lafiya kin gama ne?

Wani irin kallo ta watsa Mai tare da fad’in “karka k’ara kiran sunana a wannan k’azamin bakin naka, daka yau kar in k’ara ji, “karka manta kaine sabon driver d’ina daka yau, “kuma dole kayi abunda nake so, “kar in k’araji ka kira sunana dole ka kirani da madam ko hjy, “sannan maza ka fito ka ri’ke min basket, koni kake so in d’auka da kaina?

Usman kallonta yake, “abunda tayi bai bashi mamaki ba, danya dad’e yana aiki a gidansu, yana ganin yanda take ma mutane, “yana kallonta ne saboda tace ya kirata da hjy ko madam, yarinyar da bata wuce shekara Goma sha bakwai ba, ta kalleshi Wanda yayi 30yr tace ya dinga ce mata madam, “dan murmushi yayi tare da bud’e kofar dan yasan Mai nema dole yayi hakuri, sai dai bazai d’auki raini ba, duk da yana aiki a karkashinta.

Ganin ya fito yasa tayi gaba, “Tana fad’in tsiyar Talaka kenan sai girman kai, “da nuna isa, “in banda raini kana Talaka Ina Kai ina girman kai.

Usman binta yayi cikin super market d’in “inda ya daukan mata basket din kaman yanda ta bukata, “gefen perfumes ta tsaya, inda ta Fara jida kaman ba gobe, “ta d’iba da yawa sannan ta nufi gefen Mai “ta d’auki Wanda take amfani dashi tasa cikin basket din da Usman ke ri’ke dashi, “Tana gama d’iban Mai din tayi gaba wajan biyan kud’i, “shima binta yayi inda ya ajiye basket din aka fara k’irga kayan data d’auka, “fad’a mata kud’in kayan akayi ta mi’ka atm d’inta inda aka cira a POS,  aka bata, “Tana amsan ATM din tabar wajan. 

Kai Usman ya girgiza Alaman wannan tayi nisa, “bayan ansa kayan a Leda ” Usman ya d’auka tare da fitar dasu, “koda ya fita a tsaye ya ganta alaman bazata bud’e motar ba saiya bud’e Mata sannan zata shiga, “booth yaje yasa kayan sannan ya bud’e Mata motar ta shiga ya rufe, “shima shiga yayi tare da tada motar sukai gaba 

Kunna radio yayi inda ake Labarai “kaita d’aga tace kashe radio dinnan, “bana son hayaniya. 

Baice komai ba ya kashe tare daci gaba da tafiya “Koba komai zai barta kodan mahaifinta, domin shi yasan darajan mutane 

Koda suka k’arasa gida, yayi horn Mai gadi ya wangale tankamemen gate din gidan, “Kai tsaye ya shiga da motar,”bayan ya faka ya bud’e ya fito inda ya nufi booth ya kwashi kayan data siyo ta ya wuce dasu 

Amal dake zaune cikin mota “ganin ya wuce yasa ranta ya baci Sosai tare da fad’in mai yake nufi? Gashi ya kashe motar babu AC, dole yasa ta bud’e kofar motar da kanta ta fito cikin k’unan rai 

Kai tsaye itama cikin falon gidan ta shiga, “inda ta ganshi yana k’okarin fita daka falon, “hannunta ta d’aga zata wanke shi da Mari da sauri ya ri’ke mata hannun…. 

Tare da kallonta yace karki Fara, “dan Ina aiki a karkashin mahaifinki bashi bane zai baki dama ki wulakantani ba, “ni Talaka ne amma bazan bari aci mutunci naba, “sai yau na k’ara yarda da baki da hankali, baki San darajan d’an Adam ba…. 

Cikin zafin rai tace nika ri’ke ma hannu da wannan k’azamin hannun naka? 

Lallai kayi kuskure wajan tabama millionaire Amal hannu, kana Talaka, shine zaka saka hannunka ka ri’ke min nawa? Ko Mai arziki bai isaba, balle kai ‘kazami , jahili matsiya… D’aga hannunshi yayi zai mareta Wanda hakan shi yasa tayi shuru….. 

Usman ri’ke hannun nashi yayi cikin bacin rai ba tare daya mareta d’inba, “yace kinci darajan masu daraja, “sannan Ina son ki sani daka yau bazanci gaba da aiki a nan ba, saboda ke, domin bazanci gaba da tu’ka jahila irinki ba, mara tunani, ni Talaka ne, amma na fiki tunda Nasan darajan d’an Adam, Indai duniya ce zata koya miki hankali, “Wanda bai zo cikin taba Tana jiranshi balle keda ke cikinta, mahaukaciya, “yana fad’in haka ya fita fuuuu 

Amal kam mamaki take, yauce rana ta farko tunda take a duniya wani yaci mata mutunci, “kuma Talaka, “lallai yayi kuskure saina nuna mishi banbanci tsakanin Mai kud’i da Talaka, saina nuna mishi dole Talaka yama Mai kud’i biyayya, lokaci d’aya ta kalli hannunta daya ri’ke cikin kyama tare da fad’in wannan k’azamin hannun nashi yasa ya ri’keni, murmushi tayi tare da fad’in I will teach him a lesson that he will never forget in his life, this is a promise from me young millionaire Amal……Hmmm ikon Allah muje zuwa muji wacece wannan Amal din 

*masu tambaya cewa wannan novel din kona kud’i ne? A’a na kyauta ne bana kud’i bane, so kowa zai iya karantawa, is just a short story for my love once* 

Amal da sauri ta haura Sama, direct d’akinta ta nufa, inda tayi toilet tasa soap ta Fara wanke hannun da Usman ya ri’ke mata cikin kyama, “tare da fad’in sai yayi daya sanin tabamin jiki da yayi, “matsiyacin Talaka. 

Koda Usman ya fita, taxi yahau inda yace akai shi, dutsen Alhaji, koda suka k’arasa a kofar wani Gida suka tsaya, gaban gidan kwata ne, k’ato sai wani katako da akasa ake hawa a wuce, cikin gidan ya shiga da sallama. 

Amsawa akayi, wata mata dake d’aki tace Usman ne? ” yace eh nine Mama, sannu da gida. ” Tace yauwa , Har an dawo? Naga kazo da wuri yau. 

Yace eh wlh mama na ajiye aikin ne bazan iya ba. 

Salati ta saki tare da fad’in dan Allah Usman ka rufa mana asiri, kasan fah kaine komai namu, da wannan aikin muka dogara, yanzu inkace ka ajiye ya zamuyi? 

Yace mama Allah zai rufa asiri, tunda Dai anyi karatun, sai a gode ma Allah insha Allah za’a samu aiki, Koba yanzu ba. 

Mama tace wani aiki, yau shekaranka hud’u da Gama karatu amma babu aiki, “yanda wannan k’asar ta Gama lalacewa sai kana da hanya zaka samu aiki, in baka dashi kuma sai dai kaita zama, “yanzu yanda aiki ke wahala Aiko masu hanyar ma sai sunji jiki suke samu, balle kai dan Talaka, “Toh wai maima akama a wajan aikin ne daka ajiye? 

Yace bazan d’auki wulakanci ba, ko kad’an. 

Mama tace shi Alhajin ne ya wulakanta ka? 

Yace a’a, tare da fara bata Labarin abunda Amal tayi mishi, “da kuma abunda ya fad’a mata. 

Mama tace oh ikon Allah, amma Aida baka biye mata ba, “yace Mama sai in bari ta mareni? 

Tace ba haka nake nufi ba, ina nufin da baka biye mata har ka ajiye aikin ba, mai nema ai baya zuciya, sannan Mai nema sai yayi hakuri, kasan shi Mai kud’i ganin Talaka yake ba komai ba, “Ina son koda gaba ka samu wani aikin kayi hakuri, gaba d’aya duniyar kwaya nawa ce ma? “in ba’a hakuri da juna ai mutum bazai taba samu yakai inda yake soba…. K’aran wayar usman yasa mama yin shuru 

D’auka Usman yayi yaga Alhaji Sulaiman Kura, dannawa yayi tare da gaidashi cikin girmama. 

Bayan Alhaji ya amsa yace kai Usman Mai yayi zafi kaida ibtisam harka ajiye aiki? 

Nan ya fara bama Alhaji labari, tare da fad’in Alhaji kayi hakuri Nasan kana mutunta na k’asan ka, rainane ya baci har takai da hakan. 

Alhaji yace Usman, tun sanda na d’aukeka kana mana Guga, nake ta Lura dakai, na kuma yaba da hankalinka, wannan shine silan dana tambaya kace ka iya tuki sai yasa nace ka dinga tu’ka Amal, badan komai ba sai dan na yaba dakai da kuma hankalinka, ina son ka dawo bakin aikin ka gobe sannan kayi hakuri da Amal kasan yarinya ce k’arama. 

Usman yana ganin darajan Alhaji da kuma mutuncin shi, wannan shine dalilin da yasa yace zai dawo aikin. 

Bayan ya kashe wayan, ya fad’ama mama yanda sukayi. 

Story continues below


Mama tace toh kaita hakuri kaji, wata rana sai labari, Allah yayi maka albarka, ga abinci can a d’aki na ajiye ma. 

Yace toh tare da shiga d’akinshi inda babu komai sai katifa da filo, da kuma ledan d’aki, sai akwatin kayanshi, da d’an k’aramin tv irin akwati tin nan. Bude abincin yayi yaga tuwo ne miyan kubewa d’anya, “Fara ci yayi bayan ya wanke hannu. 

Amal ita ta kira Dad d’inta ta fad’a mishi komai, duk abunda ya faru bata boye Mai ba dan a duniya komai tayi saita fad’a mishi, Mum d’inta ce take boye ma Abu dan tana da fad’a, “koda ta fad’a ma Dad d’inta yayi mata nasiha akan bata kyauta ba, inda ya nuna mata dan Adam daraja gareshi, “tace daddy Talaka nefa shi. 

Murmushi yayi tare da fad’in Amal ai duk d’aya muke muda su, kika sani koya fiki a wajan Allah ma,aida Talaka damai kud’i duk d’aya ne wajan Allah. 

Amal cikin ranta tace Tabdi aiko da ban banci, tsakanin Talaka damai kud’i, domin Mai kud’i zaici abunda yake so, shiko Talaka sai dai yayi hakuri yaci abunda yazo Mai, sannan Mai kud’i yakan kwanta waje Mai Kyau, amma Talaka fah? Hmmm 

Jin tayi shuru yasa Daddy din Nata fad’in zan kira Usman din in bashi hakuri, karki k’ara yin haka Kinji?.. 

Tace daddy Talaka zaka bama hakuri? Gaskiya daddy ka barshi, harda ri’ke min hannu yayi da nazo zan mareshi, yaune rana na farko da Talaka ya taba y’ar autar daddy kuma millionaire Amal din daddy, Mai millions d’ari biyu cikin account d’inta, yarinya y’ar shekara Goma sha shida. 

Daddy yace mata hakane my daughter, nidai banso ki k’ara yimai haka, bama shiba kowa, saboda dan Adam yana da daraja. 

Tace toh daddy kaman taji yanda ta amsa Mai, “amma tana kashe wayan tace haba taya za’a had’a AI har abada Talaka Mai bauta ne Gamai arziki, kuma koni zan so ka dawo aiki danna muna maka ka taba Amal. Wacece Amal 

Wacece Amal? 

Amal y’a d’aya tilo wajan Alhaji sulaiman kura 

Alh Sulaiman kura dan asalin garin Kano ne, shahararren dan kasuwa, wanda yana mutum na hudu a cikin y’an kasuwa na Africa masu kud’i, sunanshi ne na hud’u, Alh Sulaiman matarshi d’aya hjy rabi, hjy rabi macece Mai son addini da tsoran Allah, sai dai abu d’aya da yake damunta a rayuwar duniya shine rashin haiyuwa. 

Duk sanda ta samu ciki, saiya zube, inko ta haifi cikin dan sai yazo a mace, Hjy Rabi tayi mugun damuwa wanda hakan ya haifar mata da hawan jini, gashi ta kasa cire tunanin abun, duk yanda Alh Sulaiman yai Mata bayani akan ta cira abun haiyuwa ba na Allah ne amma abun ya gagara, “Tana matukar son taga ta haiyu “domin a kullum kukanta d’aya kar tazo ta daina samun cikin tunda tana ta Asaran kwanta na haiyuwa, tunda kullum tana girma ba rage shekaru take ba,. 

Har taba mijinta shawara akan ya k’ara aure, amma ya’ki inda ya fad’a mata haiyuwa na Allah ne, kuma komai lokaci ne,. 

Ganin yaki k’ara hauran nan ma ta shiga damuwa Sosai, daka karshe dai ya yarda zai K’ara auren, a lokacin taita fama da ciwo saboda tunani inda akace Mata in bata rage tunani ba, ciwon zuciya zai iya kamata, “sanda Alh Sulaiman yaji haka ya tsorata Sosai, domin ina bala’in son matarshi, ganin haka yasa ya Mata alkawarin zai K’ara aure da take so tayi mishi hakuri ta bashi lokaci kad’an, wata rana Alh Sulaiman yaje meeting suna dawowa shida tawagarshi motar da suke ciki yayi hatsari inda wani mai trailer ya bugesu, Duk Wanda yaga motar zaice wa inda suke cikin motar sun mutu, domin irin kundun balan da motar keyi , sannan ta fad’a wani rami. 

Nan aka fara k’okarin cire motar inda Alh Sulaiman ko motsi bayayi, haka shima driver d’inshi, direct asibiti aka nufa dasu, jiki duk jini duk Wanda ya gansu zaice Sun mutu, “koda labari ya iske hajiya rabi ba k’aramin tsorata tayi ba inda ta nufo asibitin cikin tashin hankali da fargaba, ganin halinda mijinta ke ciki yasa ta yanke jiki ta fad’i inda aka d’auketa aka fara Mata taimakon gaggawa 

Bata dad’e ba ta Farfado inda aka gano Tana d’auke da ciki harna wata biyu da sati d’aya, ita kam bata cikin take ba, burinta mijinta ya tashi, 

Driver din da yake tu’ka alh Sulaiman shikam ya rasu, Alh Sulaiman kam ya bugu waje da dama, harda wani k’arfe daya bula Mai wajan gabanshi, nan dai akaita gwaje gwaje inda likitoci suka gano inya rayu ya tashi bazai K’ara haiyuwa ba, domin ya samu mummunan rauni a wajan, wanda bazai iya ma mace ciki ba. 

Duk wannan abunda ake bai Farfad’o ba, 

Hjy Rabi kam iya Tashin hankali ta shiga, tana nan dai zaune kusa dashi, cikin dare ya farka tare da salati, da sauri hjy Rabi taje ta kira Dr, inda ya fara dubashi, Nan yace jiki yayi tunda ya farka. Hjy Rabi take kwana dashi, dan tace bazatai nesa dashi, cikin ikon Allah kwana biyar da yayi a asibiti yaji jikinshi da sau’ki Sosai, har yana iya zama, da kam sai dai kwanciya. 

Inda yake tambaya Ina driver d’inshi? “Nan hjy Rabi take shaida Mai Allah ya mishi rasuwa shi. 

Alh Sulaiman harda kuka yayi domin yaji mutuwarshi, wanda yake ganin kaman shine sila, Nan yace hjy Rabi ta kira Mai PA d’inshi. 

Bayan PA yazo, Alh Sulaiman yace abama iyalan driver d’inshi daya rasu million biyar, sannan akai musu kayan abinci, in yana da yara a d’auki nauyin karatun su, ” “Nan PA yace an gama ranka ya dad’e, tare da fad’in Allah ya k’ara maka lafiya. 

Ganin yanda ya damu da mutuwar driver d’inshi yasa hjy Rabi fad’a mishi tana d’auke da ciki, yayi murna Sosai….. Toh daka hjy Rabi har Alh Sulaiman babu wanda Dr ya fad’ama bazai K’ara haiyuwa ba….. 

Plz ba kullum zan dinga posting ba ayi hakuri. But inna samu lokaci Zanyi kullum din. 



Alh Sulaiman yaji dad’in samun cikin matarshi Sosai, tare da ro’kan Allah yasa Kar wannan ya zube, ko inta haiyu dan ko y’ar su koma. 

Alh Sulaiman yayi wajan sati uku a asibiti yana jinya, inda jikinshi yaji sauk’i Sosai, ranan da Dr yazo da niyan bashi sallama “Alh Sulaiman yace Dr ko ina naji sauki sai dai kasana Ina jin wani iri kaman bani ba. 

Dr shuru yayi can ya kalli hjy Rabi yace madam dan bamu waje muyi magana. 

Alh Sulaiman yace a’ah babu komai, iyalina ce ka fad’a kawai a gabanta 

Dr yace OK tare da kallon Alh Sulaiman yace sakamakon had’arin daka samu ka samu ciwo a kasanka Wanda mukai gwaje gwaje muka tabbatar bazaka k’ara samun haiyuwa ba har abada ba. 

Wani irin ihu hjy Rabi ta saki tare da kuka, Tana fad’in yanzu Idan wannan cikin ya tafi shikenan baza muga Kwan muba? 

Shiko Alh Sulaiman kasa magana yayi, sai Innalillahi’wa inna ilaihirajiun da yake ta faman nanatawa, kanshi na k’asa ya kasa koda motsashi, lallai wannan itace tashi kaddaran, “sai kuma hawaye lokaci d’aya ya fara zuban mishi, “lallai Dan Adam ba komai bane, ba’a gama maka hallita sai ranan daka koma ga Allah, yau gashi irin jarabtan da Allah yayi mishi”dukiya Allah ya bashi kaman hauka, bai masan Mai zaiyi da itaba, amma kuma gashi yanzu bazai iya bama mace ciki ba Innalillahi’wa inna ilaihirajiun. 

Lokaci d’aya tausayin matarshi ya kamashi, wanda ta kwallafa rai akan son taga ta haiyu, Koba komai kaima yau ace ga naka dan. 

Dauriya yayi tare da fara bama hjy Rabi hakuri akan tabar wannan kukan, tayi hakuri. 

Kallon Dr yayi tare da fad’in Dr do whatever but make sure wannan cikin dake jikin iyalina yazo duniya ba tare da wani matsala ba, “plz Dr sai kuma ya fara kuka gwanin tausayi, lallai Allah yakan jarabci bayinsa shi gashi Allah Ya bashi dukiya masu yawa, amma gashi baida y’ay’a, wani kam Allah ya bashi haiyuwan amma babu dukiyar na abinci ma dakyar ake samu. 

Wasu kam gudun haiyuwar ma suke, domin basa so 

Dr yace kayi hakuri Alh insha Allah zata haiyu lafiya da yardan Allah, ku d’age da addu’a, “kallon hjy Rabi Dr yayi tare da fad’in hjy kiyi hakuri insha Allah zaki haiyu lafiya, wannan cikin naki zaizo duniya insha Allah cikin koshin lafiya 

Sai dai ina son ki cire wani damuwa, fargaba ko tsoro, domin hakan zai iya kawo barazana ga cikin, domin Mai juna biyu ba’a so a ganta cikin damuwa 

Cikin kuka hjy Rabi ta Fara fad’in Dr damuwa ya zama dole, tunani ma ya zama dole, domin inba ganin wannan cikin nayi yazo duniya ba, wlh banda kwanciyan hankali, na tabbata idan na rasa wannan cikin Zan shiga cikin wani mugun mawuyacin hali, “Ina son ganin ganin jinina, Indai na rasa wannan cikin shikenan kuma. 

Dr yace hjy ki kwantar da hankalinki insha Allah zaki haiyu cikin koshin lafiya, sannan wannan baby din zai zo duniya ba tare da wani damuwa ba, “but Ina son ki dinga kula Sosai, banda yawan aiki, banda d’aukan Abu Mai nauyi infact ma duk wasu aiki wanda zaisa jiki ya jigata kar kiyi, “saboda gudun barazana da cikin naki 

Story continues below


Nan Dr yasa aka basu magani,sannan suka nufi Gida, tunda suka koma Alh Sulaiman gaba d’aya ya shiga damuwa Sosai, shiba takanshi yake ba Illa matarshi hjy Rabi, wacce ta shiga mugun damuwa, domin ya tabbata inta haifi cikin nan baizo da raiba akwai tashin hankali yanda take da yawan saka abu a cikin ranta. 

Shi yayi imani da Allah da kuma kaddara, yasan wannan itace kaddaran rayuwarshi, toh amma Inda hjy Rabi ce wannnan laluran ya sama yasan dole yace zai K’ara aure, dan haka yanzu tunda shine dole yayi mata adalci shima 

Hjy Rabi na zaune a d’akinta Wanda an kashe mishi dukiya kaman baza’a mutu ba, tun a wannan lokacin, hannunta ri’ke da apple tana ci. 

Saiga Alh Sulaiman ya shigo hannunshi d’auke da takarda yana fad’in sannu da hutawa?.. 

Tace yauwa, yanzu ai nake son in Gama cin apple  dinnan inzo in sameka, ashe kana tafe. 

Yace eh, ina son kayi ma abunda zai faru yanzu kyakyawan fahimta, lallai hjy Rabi abunda zanyi yanzu ya zama dole ne, bawai dan bana sonki ba, “Wlh hjy Rabi sonda nake miki shine silan da yasa na kasa aure sanda kika ce inyi dan inga kwai na, amma na’ki domin Nayi imani da Allah haiyuwa daka gareshi ne 

Nasan inda ke wannan laluran ya sama komin daran dad’ewa saina k’ara aure, domin inga kwai na, “Toh gashi niya sama dan haka Ina son kiyi hakuri kije na sakeki saki d’aya tare da mi’ka mata takarda 

Tashi tayi da sauri tana fad’in Alh Mai kake fad’i haka? Saki fah kace? 

Sai kuma ta saki kuka, amma Alh bakai min adalci ba wlh, “Ina baka shawara kayi gaggawan maidani Inba so kake damuwa ta kasheni da abunda ke ciki naba. 

Ko kasan abunda yasa nake damuwa? Wlh Alh kai nake jin tausayi, tun Farko nike da matsala, tunda sau nawa Ina bari? Kaga nice Mai matsalan, wlh zan zauna dakai koda zan rasa wannan cikin duk da Nasan ba abu bane mai sauk’i inna rasa wannan cikin, Amma dole in zauna dakai domin ina Sonka, “Mai yasa kayi wannan tunanin akai na? Alh duniya saita tsinemin inna Barka, kaika sani ko daka wannan shikenan nima Kwan nawa? Dan Allah Alh kayi hakuri ka dawo dani. 

Wlh zan zauna dakai har karshen rayuwa na, koda na rasa wannan cikin kuka take Sosai tana bashi hakuri akan ya dawo da ita tun Kafin wani yaji wannan zancen 

Gaba d’aya zuciyar Alh Sulaiman ta Gama karaya, musamman kukan da takeyi, “Alh Sulaiman yace Rabi ban son saboda ni ki shiga wani hali, wlh rabi Nima Nasan rabuwa dake da Nayi Zan shiga wani hali Sosai 

Cikin kuka tace Alh so kake ka sani cikin damuwa? Alh Ina kiyaye duk wani abu saboda gudun Kar in rasa wannan cikin yau gashi zaka sakamin damuwa wanda zai iya zama barazana gareni 

Alh Sulaiman da sauri yace na dawo dake Rabi kina matsayin matata, “lallai kinyi min halacci mai kike so inyi miki a rayuwa? 

Tace ina son ka zauna dani a matsayin matarka har karshen rayuwata, karka kara tunanin sakina a rayuwa dan Allah 

Alh Sulaiman yace Nayi miki alkawari, sai kuma me?.. 

Tace karka karayin aure ban son kamin kishiya. 

Murmushi yayi tare da fad’in nayi miki alkawarin bazan k’ara aureba, “sai kuma me 

Dariya tayi tare da fad’in  wannan ya isheni kawai, bana bukatar komai daka wannan 

Alh Sulaiman yace an gama nima zan bada tawa kyautar, zan raba dukiya ta kashi hud’u, na baki dayar kyauta halak malak, sannan abunda zaki haifa shima na bashi kashi d’aya, sauran kashi biyun zan bada kashi d’aya ga marayu d’aya kuma Inci gaba da kasuwanci na dashi, zan fad’ama barrister d’ina komai 

Hjy Rabi tace a’ah Alh baza’ayi haka ba gaskiya, taya zakai haka kuma? A’a ban amince ba 

Alh Sulaiman yace kawai kiyi min addu’a kawai, na riga Na yanke hukunci 

Hjy Rabi kuka tasa tana Mai kaunar mijin Nata tare da tausayinshi. 

Tun daka wannan lokacin hjy Rabi da Alh Sulaiman suke ta rainon cikin dake jikinta. 

Cikin hjy Rabi yakai wata takwas, gaba d’aya bata aikin komai domin Alh Sulaiman ya hanata aiki, sai dai komai Ayi mata, gashi hjy Rabi bata son zama tafi son taita aiki, Amma mijinta ya hana haka ta hakura 

Lokacin da cikin hjy Rabi ya cika wata tara wata ranan Monday cikin dare ta tashi da na’kuda, aiko nan akai asibiti da ita, inda ta kasa haiyuwa da kanta saida aka mata cs, cikin ikon Allah ta haifi y’arta mace, koda ta farka taga abunda ta haifa ba k’aramin murna tayi ba ,sai dai yarinyar y’ar karama da ita gata Fara sol da ita gwanin sha’awa. 

Alh Sulaiman ya kashe dukiya ranan suna,inda yarinya taci sunan mahaifiyar hjy Rabi, Maryam shine suke kiranta da Amal, Bayan suna da sati biyu suka bar Kano inda suka koma Abuja da zama gaba d’aya 

Amal ta taso cikin gata, komai takeso shi Alh Sulaiman yake mata, gaba d’aya baya son yaga ana mata fada ko wani abu, gashi tunda Amal ta Fara tasowa take da rigima da kyamar masu aikin gidansu, hjy Rabi bata mata wasa ko kad’an domin tana ganin inta barta tana haka nan gaba zata sha jiki, domin ita macece, gidan wani zata,”inko Alh Sulaiman yaga ana ma Amal fad’a ya dinga fad’a kenan yana fad’in ai yarinya ce karama duk da shima wani lokacin yakan mata nasiha Idan tayi wani abun 

Amal Tana da kyama, ba kowa bane idan ya taba abuba Amal keci ba, ga fad’a da tsiwa, tun tana karama 

Lokacin data shiga shekara biyar aka sata makarantar boko, dama an dad’e da sata islamiya, Amal tun tana y’ar karama take son girma, domin abunda ta gani masu aikin gidansu Na mata suna girmamata, ko a skul kullum sai tayi fad’a da wasu y’an ajinsu, saboda rigima irin Nata….. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *