HUTU CHAPTER 5

HUTU





CHAPTER 5








Kausar tinda Hydar ya fita ta zauna tana tunani, kaman yadda yace tayi tunani da zuciyarta hakan kuwa tayi kuma sosai taga illan guje mishi da takeyi, ko ba komai shima mutum ne kuma jini ke yawo a jikinshi ba ruwa ba, dole shima yayi sha’awa kuma muddi taci gaba da gujemai wata rana ze kara aure ko kuma yashiga matan banza wanda tasan har wurin Allah tanada kaso cikin zunubin daze kwasa, waya ta dauka zata kira kawayenta se kuma ta ajiye taja tsaki tace “toh yanzu me abinyi” zuciyarta tace “ki canza ways dinki” shiru tayi ta zabga uban tagumi kafin daga baya ta tashi taje gaban mirror taga makeup dinda tayi tana nan fine abinshi saboda haka ta shiga closet dinta ta dauko short skirt da wani karamin top me spaghetti hands tasa ta feshe jikinta da turare tazo ta tsaya gaban mirror tace “yes, to stop my husband from getting married again i most do whatever it is he wants” murmushi tama kanta sannan ta fita parlourn kasa ta zauna tana jiran dawowanshi.

Karan dube gate taji ta tashi ta leka ta window taga yana parking komawa tayi ta zauna gabanta na dukan uku uku dan ita kanta tasan yau dai jihadi zatayi saboda tasan waye Hydar, jin karan kofa yasa ta tashi ta tarboshi da runguma tana cewa “welcome home hubby” murmushi yayi kafin yayi pecking din goshinta yace “wannan kwaliiyan duk saboda nine, kinyi kyau” tayi murmushi tace “in ban maka ba wa zanyi wa” ya kada kai yace “babu” yana janta suka zauna kan kujera tace “are u hungry” ya girgiza kai dukda yunwar da yakeji amma yasan ba Kausar ce ta dafa ba saboda haka ya gwammace yace mata a koshe yake, hannunshi ta riko cikin nata murya chan kasa kasa kaman batason magana tace “Hubby I’m sorry, nasan bana kyauta maka amma yanzu a shirye nake dana gyara indai bazaka kara aure ba” kallonta yakeyi dan ya tabbatar ko maganan da takeyi daga zuciyarta take fito kuma ya gani dan ya tabbatar gaskiyarta take fada amma kuma tsoro ya gani kwance cikin idonta saboda haka ya sauke numfashi yace “zaki iya dani, kinfa san koni waye” tayi saurin sa kanta cikin kirjinshi tana shakar kamshi turarenshi tace “ai kaima kasan irin matar da Allah ya baka saboda haka u have to take it easy on me” yayi dariya yace “My lazy wife Allah ya bani ikon binki a sannu”.

Dariya tayi tace ” Ameen” kafin tayi wani yunkuri seji tayi Hydar ya kinkimeta yace “tinda matata tace zata gyara bari mu fara yanzu muga ko zata iya daurewa” zaro ido tayi gabanta na dukan tara tara dan harga Allah tsoron Hydar takeyi dan kuwa Hydar akwai jarumta😂. Kuka, duka, yakushi, cizo, babu wanda Kausar bata kaiwa Hydar ba amma ina bemasan tanayi ba, seda ya gama sannan yaga aika aikan da ya mata, hannu yasa cikin suman kanshi yana yamutsawa dan kuwa yasan yanzu idan Kausar ta tashi guduwa se tayi wata bata kulashi ba, rungumota yayi yana lallashinta aikuwa ta shiga tureshi tana dukan kirjinshi, be saketa ba har seda yaga tayi shiru sannan ya dauke ta suka shiga bathroom, tare sukayi wanka suka fito Kausar se shagwaba take zubawa Hydar shikuma se biye mata yakeyi hardai ya samu tayi bacci sannan ya sauke ajiyar zuciya yace “Wifey matsala” zama yayi ya sata gaba yana kallonta kaman tv har yaji kiran sallahn la’asar sannan ya tasheta shikuma ta wuce masallaci.

Washegari Monday kaman kullum Hydar ya riga Kausar fita duk da har yanzu bada izinshi take zuwa office ba amma bema damuba kuma dan yaga alaman she’s possessed by her work, yana zaune a office aka aiko mishi da letter ya bude yana karanta, gabanshi ne ya shiga dukan uku uku ganin transfer letter, yasan da maganan transfer dinnan amma kuma yasan da cewar baya ciki wa’anda za’awa transfer “toh yanzu me kuma ya faru” ya tambayi kanshi, yasan babu wanda ze mishi wannan shisshigin se colonel Idris saboda haka ya tashi rai bace ya wuce office din colonel, zaune ya ganshi yana busa shigarin a zuciyarshi yace “Alhmdllh Allah nagode maka da baka dora min wannan halin sojojin na shaye shaye da bin mata ba” colonel ne ya dago da murmushi mugunta a fuskarshi ganin letter din hannun Hydar yace ” general Hydar Ali hope all is well” Hydar da idonshi ya kankance saboda bacin rai yace “can u explain dis” ya fada yana ajiye letter din kan table colonel yayi dariya yace “kace kaima ka samu transfer, well congrats, bari mu gani wani gari aka turaka” ya fada yana bude letter din, Lagos ya gani baro baro yace “General Hydar kace ka kusa zama Lagosian” Hydar da ranshi ya baci yace “nasan u ar behind all this amma ka sani ko naje zan dawo, kujeran nan da bakaso na zauna kai sena tureka daga kanshi na zauna” da fadan haka Hydar ya fita bayan ya fizge letter dinshi colonel kuwa ya bishi da dariyan shakiyanci yace “ina nan ina jiran ranan da zakazo ya tureni daga kujeran mulki na wawa kawai, kana aikin gwamnati amma bakacin kudin gwamnati kai gaka incorruptable general” tsaki yaja sannan yaci baga ya busa shigarinsa yana karkada kafa.

Story continues below


Da daddare a gida Hydar yasa tunani gaba dan ya rasa yadda zeyi dan bayaso yayi nisa da iyalinshi gashi sati daya aka bashi yayi abinda ya dace, Kausar dake lura dashi ta kashe laptop dinta ta dawo kusa dashi ta zauna tace “Hubby what’s wrong, u seem disturbed” ya kalleta yace “Wifey ya zanyi anmin transfer zuwa Lagos kuma next week zamu wuce” ta waro ido tace “what! Transfer fa kace” ya kada kai ta furzar da iskan baki tace “ya kenan” ya kalleta yace “kinsan dai banzan barki a nan bako, dole dake zan tafi” ai da sauri tace “babu inda zan bika,  kaje duk weekend ka dinga dawowa kana dubani, nima ai inada aikina a nan” rai bace yace “aikin naki yafi mijinki kenan kome” ta girgiza kai tace “bance aiki na yafika ba amma inada aiki a kasa har zuwa nan da 2mnth dan na karba ayyuka daya saboda nasan I’m free,  kaga kuma bazan bar aikin mutane pending ba bayan na karba kudinsu” a takaice yace “ki mayar musu da kudinsu dan bazan tafi na barki ba” da fadan haka ya mike ya shiga dakinshi yana bugo kofa dan lamarin Kausar ya fara isanshi ita kuwa tabe baki tayi ta janyo laptop dinta ta kunna ta cigaba da abinda takeyi ko a jikinta (nikuwa nace ki bari ya tafi shi kadai matan lasgidi su mike kwace da kuwa akwaisu da kyau da iya jan hankali). 

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴ 

Da safe Anwar ya riga Binta tashi,  seda yayi wanka yayi sallah ya shirya cikin bakin jeans da white top ya dora red blazer akai sosai yayi kyau kaman a saceshi a gudu sannan ya fito ya shiga dakin da Binta ke kwance, sosai yayi mamakin ganinta kwance dan kuwa ya shaideta da saurin tashi tayi sallah kuma idan tayi bata komawa bacci saboda ta riga ta saba tin a gidan Zinaru inta tashi toh ta tashi kenan, tunawa yayi da zazzabi ta kwana saboda haka yayi saurin karasawa  aikuwa yaga ta hada gumi se rawar dari takeyi idonta na kafe, cike da tashin hankali ya shiga kiran sunanta amma batamasan wake kanta ba, kinkinmarta yayi suka fita zuwa inda yayi parking yasata mota sannan ya shiga yaja motan a 360 yana tsoron kar ‘yar mutane ta mutu a hannunshi ya shiga uku.

Hi-Fi hosptal ya kaita inda Khalil yake aiki har yayi parking ya hango motan yayanshi nan take ya shiga tunanin idan ya gansu yace mishi me idan ya tambaye ina ya samo wannan karamar yarinyar, saboda haka ya juya ya bar hospital din zuwa Kelina hospital, seda aka bashi sabon file dan basu da file a hospital din sannan akayi emergency da ita, Anwar ya kwashi awa daya yana safa da marwa a gaban ER din duk ya gama hada gumi,  doctor din yaga ya fito da sauri ya karasa wurinshi doctor din ya kalleshi yace “ina iyayenta” Anwar yace “basa kasar sunyi tafiya,  I’m her brother u can talk to me” doctor ya kada kai yace “follow me” a office din doctor suka zauna doctor ya dago ya kalli Anwar yace “Mal nutrition na damunta sannan kuma tana bukanta jini a kalla leda daya sannan we’ve run some tests kuma mun gano cewar she’s suffering from sickle cell disease” da sauri Amwar yace “kana nufin ka cemin SS ce meaning sickler” doctor ya kada kai yace “kwarai kuwa” zufa ne ya shiga karyo ma Anwar murya na rawa kaman zeyi kuka yace “doctor pple under dat category never make it,  they die young” doctor kallo Anwar yayi yaga ya damu sosai,  sanda Anwar yace mishi shi yayan Binta ne be yarda ba saboda bega kamanni ba amma ganin yadda ya damu yanzu se ya fara kwankwanto ko gaskiya Anwar ya fada. 

Sauke numfashi doctor yayi yace “calm down, ba dukkansu ke mutuwa ba,  it depends kan yanayin ciwon,  wasu nasu na tsanani wasu kuma baya tsanani sannan wasu basa kula da diet da maganinsu kuma basa zuwa hospital akai akai shiyasa suke mutuwa,  amma ur sister kan make it saboda naga she’s not dat weak kuma indai u will heed to my advice Insha Allah zata samu lfy” Anwar ya sauke ajiyar zuciya tareda share gumin da ya karyo  mai yace “doctor me zamuyi yanzu” doctor yace “good,  a yanzu dai muna neman blood wanda za’a sa mata sannan zan rubuta magunguna wanda zata dinga sha everyday,  and zan dinga baku appointment kuna zuwa ina dubata,  if u want ur sister to live toh kuyi abinda nace, kubi procedure and komai zezo da sauki” kada kai Anwar yayi sannan yace “Insha Allah zamuyi hakan yanzu maganan jini i think u can use mine” doctor yace “ur blood grp” Anwar yace “O+” doctor ya kada kai yace “come with me”.

A takaice dai Anwar shiya bada jini aka sawa Binta yana zaune a dakin da take kwance da drip a hannunta da hagu na dama kuma karin jini, sosai ya tausaya mata jin abinda doctor yace,  wayanshi ya dauka ya kira Asabsy dan ya karbi numbernta ya shaida musu Binta ba lfy tana asibiti cikin awa daya suka karaso itada Hajiya Anwar ya sanar musu abinda doctor yace sosai suka tausaya mata barima Asabsy da har kuka seda tayi  ganin halin da Binta ke ciki. Se yamma su Hajiya suka wuce saboda Anwar yace shi ze kwana a wurinta basu musa mishi ba sukayi tafiyarsu, tafiyan keda wuya mahaifinshi ya kirashi,  gabanshi ne fa fadi ganin kiran Dad dinshi daga wayan yayi da sallama kaman mutumin arziki Dad dinshi ba tareda ya amsa ba yace ” kazo gida ina nemanka” sannan ya kashe wayan,   nurse ya samo yace ta kula da Binta zeje ya dawo ta amsa da toh sannan ya wuce gida hankalinshi a tashe. Parking yayi a parking lot din gidansu ya karasa cikin parlor inda yaga Maminshi da Dad da Khalil zaune suna jiran zuwashi, da sallama ya karasa ciki Mami da Khalil kawai suka amsa mai Dad kuwa ya hade rai ya karasa ya zauna a one sitter yace “Dad gani” Dad cikin bacin rai yace “ina ka kwana” bakinshi na rawa yace “gidansu Mubarak” Mami tace “bamun rabaka da yaron nan ba,  babana bakaji koh” ya sunkuyar da kanshi kasa Dad yace “kaje club jiya ko bakaje ba” bam bam gabanshi ya hau faduwa Dad yace “dakai nake kamin shiru” duk ranshin gaskiyarsu basa iyawa Dad dinsu karya dan akwaishi da kwarjini,  cikin sanyin murya yace “naje” Dad ya gyara zama yace “yarinyar da aka ganku tare fa” zufa ne ya fara keto mishi dan yasan yanzu kam se Dad yayi suspending dinshi daga fita gida,  Khalil da ranshi ya baci yace “bada kai ake magana ba” cikin rawar murya yace “nima bansan taba lift na rage mata” Dad yace “karya kuma ka koyo” yayi saurin girgiza kai Dad yace “Khalil hukunta minshi” Khalil bayaso Dad yana cewa ya hukunta Anwar dan bakin jini yake jawo mishi a wurin Anwar din amma ya ya iya dole ne yayi abinda mahaifinshi yasashi saboda haka yace “ban hannunka” dama Anwar yasan hukuncinshi kenan saboda haka ba tareda da gardama ya mikawa Khalil hannunshi duka biyun Khalil hasa yatsunshi cikin na Anwar yashiga lankwasa su,  sosai Anwar ke ihu saoda azaba Mami kan runtse ido tayi, batason abinda ze taba mata Anwar saboda tafison shi a cikin yaranta dan me sunan babanta ne amma kuma shima daya bayajin magama,  Meenah dake lekensu da kan step tun shigowarshi ta fara hawaye, ganin abin ba sauki yasa ta sauko da saurinta ya fara jan Khalil tana kuka tana cewa “Ya Khalil yi hakuri baze kara ba” Dad ga kalleta yace “Mama zo” amma ko kulashi batayi ba harseda Khalil ya sake Anwar sannan ta karasa kusa da Anwar da fuskar yayi ja idonshi ya cika da hawaye amma be yarda sun zubo ba ta kama hannunshi tana murzawa tana ce mishi sannu, kallonta yayi gabadaya se fuskan Binta yafado mishi, da gani zatayi tsara da Meenah,  ya fada a ranshi yana kallonta,  muryan Dad sukaji yana cewa “tashi ka wuce daki,  kai da fita se nextweek bani mukalli motanka” dama yasan za’ayi haka a hankali ya mike yasa hannu a aljihu ya ciro makullin yatsunshi se zugi suke mai amma haka yake daure wa. Dakinshi ya shiga Meenah na biyeshi danshi he’s her favourite bro komai takeso ze mata zama tayi kusa dashi tana mishi sannu yayi murmushi yace “lil sis I’m fyn jeki inaso na huta” kai ta kada mai sannan ta tashi ta wuce shi kuma ya dauki waya ya kira Mubarak ya sanar mai cewar yaje hospital Binta na can ya kular masa da ita zuwa gobe dan Dad ya kulleshi Mubarak ciki da jin dadi yace “ok” dan dama tin jiya yakeso ya kara sa Binta a idonsa.
Babu yadda Hydar beyi ba akan Kausar ta bishi su tafi tare amma tace sam ita ba inda zata, da taga da gaske yake kuwa ta itan ze tafi se taje ya gaya mahaifinta akan ya kira Hydar ya mishi magana saboda kar ya tafi da ita, zaune yake a office yana wasu ayyuka yaga kiran sirikinshi, seda ya gyara murya sannan ya dauki wayan kanshi kasa kaman yana gabanshi yace “Daddy ina wuni” ya amsa da “Lfy lau Hydar, ygd ya iyali” Hydar ya amsa da “lfy” nan Daddy yace “kana da free time yau inason ganinka ne” kada kai yayi yace “insha Allah zanzo bayan Asr” Daddy yace “OK will be expecting u” sannan ya ajiye waya, gyara zama Hydar yayi yace “ko meyasa yake nemana?” Sannan yaci gabada aikinshi.



Kaman yadda yace zeje bayan Asr hakan kuwa akeyi, da ya tashi daga aiki seda ya koma gida yayi wanka ya canza kaya sannan ya dau makullin motan ya fita, a gaban gidan ya tsaya ya danna horn yana tuna rabonshi da gidan tun ran dinner dinsu, seda yayi parking sannan ya fito kai tsaye cikin gidan ya nufa da sallama, ba kowa a parlour saboda haka yama kanshi mazauni a kan kujera tareda dauki waya yana harkan gabanshi. Ya Ahmad ne ya shigo parlour da sallama Hydar ya amsa mishi, murmushi yayi ganin Hydar zaune ya karasa ya mika masa hannu sukayi musabaha sannan yace “dama kana nan? Ya gida ya Kausar” Hydar yace “tana lfy” Ya Ahmad ya mike yace “muje wurin Daddy dama yacemin zakazo” mikewa Hydar yayi yabi bayanshi tareda sa wayanshi a aljihu bame magana tsakaninsu har suka iso parlourn Daddy, da sallama suka shiga Daddy ya amsa musu yana sauke newspaper din hannunshi, ganin Hydar yasa murmushin shi ya fadada ya nuna musu kujera suka zauna sannan Hydar ya tsugunna ya kwashi gaisuwa sannan ya koma kan kujera bayan sun gama gaisawa, gyaran murya Daddy yayi sannan yace “Hydar Kausar tazomin da wani magana akan na kiraka nayi maka magana nace Insha Allah zan kiraka” gaban Hydar ne ya fadi a ranshi yace “me zato tace”.



Gyara zama Daddy yayi yace “ba komai bane illa maganan transfer dinda aka maka da kace lallai tare zaku tafi ita kuma tace tana da ayyukan da bata karasa ba saboda haka nakeso ka daure kaje kai kadai, daga baya idan ta gama abbubuwan dake gabanta seta biyo bayanka kaji” Kausar ta riga ta gama daureshi da jijiyoyin jikinshi dan tasan ko giyan wake yasha bazema Daddy musu ba saboda yana ganin girmanshi sosai bugu da kari kuma abokin mahaifinshi ne, cikin sanyi murya yace “shikenan ba matsala zata iya zuwa daga baya wannan ba matsala bane” Daddy yace “Alhmdllh, Allah ya maka albarka” ya amsa da “Ameen” seda suka danyi hiran aiki da sauran abubuwa sannan Hydar ya musu sallama yaso ya gaida Mom amma Ya Ahmad yace mishi bata gida, har bakin mota Ahmad ya rakashi sannan sukayi sallama ya wuce.




Gidan Ummi ya biya dan ya fada musu cewar an mishi transfer luckily kuwa Abba na gida, parlourn Abba ya wuce inda yaga duka en gidan zaune harda Zeena suna lbr suna dariya hankalinsu kwance, murmushi yayi ya karasa ya zauna a kasa kusa da kafan Abba sannan ya gaishesu suka amsa banda Ummi dake kallon yanayin dan nata, damuwa ne kwance a idonshi gashi duk rame kaman bashi ba, ajiyar zuciya ta sauke tace “ya gida da iyali” yace “lfy lau” sannan sukaci gaba da hira, chan Abba yace “son me kakeson fada naga kaman da magana bakinka” ya sosa keyarshi yace “eh dama Abba an min transfer zuwa Lagos ne” da sauri Ummi da Zeena suka “transfer” Abba ya kalli Hydar yace “son ka gani koh, yanzu idan nace mata basa tunani  suke magana sesu hade min kai”, Hydar yayi dariya yana kallon Ummi dake hararan Abba ta gefen ido, juyowa tayi tace ” son yanzu da gaske kake Lagos zaka koma” yace “Insha Allahu nan da zuwa next week” shiru tayi Abba yace “amma da iyalinka zaka tafi ko” ya sosa keya yace “a’a Abba senaje naga yanayin wurin sannan na dawo na dauke ta” Abba ya gyara zama yace “uhmm hakan ma yayi Allah ya tabbatar da alkhairi” duk suka amsa da ameen Zeena se complain takeyi zatayi miss din yayanta. Hydar bashi ya bar gidan ba se gab da magrib bayan ya cika cikinshi da abinci, yanaso ya cewa Ummi tasa mishi wani a cooler ya tafi dashi amma yana shakkan Ummi saboda haka ya musu sallama ya wuce gida, a masallacin unguwarsu ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga gida.




STORY CONTINUES BELOW

A parlour yaga Kausar tana sanye da evening gown har kasa tayi parking gashin ta sosai ta mishi kyau amma ya dauke kai ya karasa cikin parlourn, tasowa tayi zata rungumeshi yayi shunning dinta ta juyo tana kallon tace “lfy, me kuma nayi yanzu” ta karashe kaman zatayi kuka” juyowa yayi yana kallonta yace “tambaya ma kikeyi, yaushe na baki izinin zuwa gidanku da har zakije ki cewa Daddy yamin maganan tafiyar nan” narai narai tayi da ido dan tasan batada gaskiya ta karaso ta dora manta kan kirjinshi tareda zagaye hannunta kan kunkuminshi tace “I’m sorry dear, gani nayi ka kasa fahimta ta akan aikin mutane dake kaina shiyasa na hadaka dashi dan nasan zakaji maganan shi, kayi hakuri in hakan ya bata maka rai” shiru yayi na en dakiku kafin daga baya shima ya zagaye hannunshi a bayanta yana shakan kamshin shampoo dinda ta wanke kanta dashi, breaking hug din tayi tana kallonshi tace “to make up to u I’m all ur’s daga yau har ran da zaka tafi” waro ido yayi yana mamakin ita dinda keda shegen raki da laziness ce ta fada haka, lallai za’ayi ruwa har kankanra, hannunta tasa yana waving saboda yadda yake kallonta ba kyaftawa murya a sarke yace “da gaske” tace “da gaske nake, at least I can do dat much for u” murmushi yayi tareda pecking din lips dinta yace “we shall see to it, kuma karki kuskura ki gudu tinda ke kika fada” tayi dariya tace “don’t worry bazan gudu ba” da haka ya jata zuwa daki yana cewa “promise u  will give in all ur effort and won’t be lazy” tace “I promise”.



✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Mubarak be bata lokaci ba ya isa asibitin bayan ya siya necessary things dinda yake ganin zata bukata, dama already Anwar ya riga ta fada mishi ward din da take saboda haka kai tsaye ya zarce har zuwa dakinta inda ya leka ya hangota kwance ita kadai, karasawa yayi ya ajiye ledojin hannunshi sannan yaja kujera ya zauna yana kallon ta yana murmushi, a hankali ya furta ” she’s beautiful” ba tareda yasan ya furta ba, juyar da kai yayi yana tunanin da Allah kadai yasan me yake tunani kafin ya juyo ya kalleta yace “but she’s too young for that, nasan Anwar da tausayi hanya kuwa ya dandani zuman yarinyar nan?” Ya tambayi kanshi yana kallon fuskarta sannan ya sake cewa “I will have to find out, idan kuwa be tabata ba zanfi kowa morewa dan kuwa sena lashi zumanta” ya karasa maganar yana smirking, hanky dinshi ya dauko yana goge mata zufan dake tsiyayo mata a goshi sannan ya maida hanky din a aljihu ya gyara zama yana kallonta.




Wayanshi ne ya fara ringing ya duba yaga Anwar ke kira, dauka yayi yace “dude ina hospital din” Anwar da duk yabi ya damu yace “ta tashi” Mubarak yace “no bata tashi ba” Anwar yace “dan Allah ka kwana wurinta karka barta ita kadai kafin na duba ko zan samu hanyar fita gobe” dariya Mubarak yayi yace “kai fa Dad din nan naka na bada kai wlh, ka nuna mishi u ar nw a grown up man ba baby boy dinda suka saba ordering around ba” ajiyar zuciya Anwar ya sauke yace “manta da wannan mutumin, ni wlh na rasa ya zanyi dashi, yana shiga rayuwata dayawa” dariya Mubarak yayi yace “I’m hanging up, ka kokarta ka fito gobe” Anwar yace “I will, and don’t even think of laying a finger on Binta if not I will skin u alive” dariya Mubarak yayi a zuciyarshi yace “da yake idan ma na taba ta sani zakayi” a fili kuwa cewa yayi “I won’t dude bye” sannan ya kashe wayan yana gyara zaman shi kan kujera da he finds uncomfortable amma ya iya dole ya zauna hakan nan.





Binta kuwa ba ita ta tashi ba se gab da Asuba, da kyar ta iya bude ido saboda yadda ya mata wani nauyi ga wani azababben ciwon kai da takeji, kallon dakin da take takeyi har ta gano cewar a asibiti take sannan ta juya gefe inda Mubarak ke zaune kan kujera yana bacci, murmushi tayi dan a tunaninta Anwar ne, kanta ta rike saboda yadda takejin yana sara mata kafin ta mike zaune, tashi takeso tayi dan mararta ya cika tanaso tayi fitsari amma ba dama saboda drip dinda ke hannunta, a hankali ta fara kiran Anwar duk da muryanta be fita sosai amma Mubarak yaji kiran dan baccinshi beyi nisa ba, matsowa yayi kusa da ita yace “babe ya akayi me kikeso” da sauri ta matsa bayan ganin Mubarak dan kuwa gayen be kwanta mata ba kaman yadda Anwar ya kwanta mata, murmushi yayi yace “don’t worry ba abinda zan miki bari na kira nurse” kafin tace wani abu ya fita daga dakin ba dadewa suka dawo shida nurse.



Nurse din ce ta karasa wurinta tace “kinason wani abu ne?” Binta ta kada kai tace “fitsari zanyi” cire mata drip din nurse tayi ta rakata har toilet tayi abinda zatayi ta fito sannan ta mayar mata da drip din ta fita, dawowa Mubarak yayi ya zauna yace “ya jikin” tace “da sauki, ina Ya Anwar” yace “zezo gobe an kirashi a gida ne shiyasa baki ganshi ba” ta kada kai sannan ta kwanta ta juya mishi baya, ba dadewa sabon bacci ya dauke ta. Washegari da safe da taimakon Mubarak tayi brush sannan ya bata kayan fruit ta kuwa ci sosai dan yunwa takeji sannan doctor yazo ya dubata yace  zuwa yamma zeyi discharge dinta. Throughout ranan Mubarak ne yayi keeping dinta company dan kuwa su Hajiya se yamma suka zo kuma basu dade ba suka wuce, doctor yaso yayi discharge dinta amma ganin jikinta yayi zafi yasa ya barta tareda mata allurai ya tambayi Mubarak Inda Anwar yake yace mishi yana zuwa. Anwar kuwa babu yadda beyi ba akan baba ya bude mai gate amma yace “a’a” saboda bude mai gate yana daidai na barinshi aikin cewar Alhaji (Dad kenan).




Anwar duk yabi ya damu kanshi, ya rasa inda zesa kanshi yaji dadi, tunanin Binta ya mishi katutu a zuciya, gashi be yarda da Mubarak ba kawai dai saboda he’s his closest friend ne yasa ya kirashi, daukan waya yayi ya kira Mubarak dake shirin fita dan yaje ya dawo, Mubarak ganin Anwar yasa shi dauka yace “Dude yane?” Anwar yace “ta tashi?” “Eh bari na bata wayan” mikawa Binta wayan yayi tareda cewa Anwar ” ta karba tasa a kunne tareda cewa “Ya Anwar” numfashi ya sauke wanda besan cewa yana rike dashi ba kafin yace “Binta ya kike? Ya jikin? Kinci abinci?” Duk ya tambaye ta lokaci daya tace “ina lfy, jiki da sauki kuma naci abinci” kada kai yayi yace “karki damu anjima zanzo kinji, sannan idan Mubarak ya miki wani abu in nazo ki fadamin kinji” tace “toh” sannan ya kashe wayan yanasa hannunshi cikin suman kanshi.


Ana sallan isha bayan duk sunci abinci ya fito daga gida da sunan ze gaya kadan, ta backyard bayi ya haura fence ya fito abinshi, tinda yake idan Dad dinshi ya kulleshi baya fita amma yau ya karya record dan kuwa ya fito saboda baze iya zama ba bayan yasan Binta na cikin wani hali, seda yayi nisa da gida sannan ya kira Mubarak yace “dude zoka daukeni” ba dadewa sega Mubarak da mota ya shiga suka dau hanyar asibiti a mota se tsiya Mubarak ke mishi wai ya zama Daddy’s pet tinda kulleshi akeyi a gida. Da zuwansu asibitin direct dakinta ya wuce inda ya ganta zaune ita kadai tayi shiru tana tunanin makomarta, da sauri ya karasa ya rungumeta dan besan yayi miss dinta ba seda ya ganta, Mubarak dake bayanshi kuwa ji yake kaman yaje ya banbare shi daga jikinta, ganin baze iya kallo bane yasashi fita yabasu wuri, breaking hug din Anwar yayi sannan ya riko face dinta a hannunshi yana kallon ta yace “did u miss me?” Binshi da ido tayi dan kuwa batasan me yace ba yayi murmushi yace “I miss u” tareda kai mata peck a goshi sannan yace “ya jikinki” a hankali tace “muje gida naji sauki” yace “a’a Mubarak yace min doctor yace jikinki da zafi, ki bari zuwa gobe mu gani” ta kada kai yace “me zakici” tace “naci abinci, kawai jikina ne ke ciwo” ya sake rungumo ta yace “ze daina kinji” dagowa yayi yana kallon ta ita kuwa se rufe ido takeyi dan alluran ya fara aiki yace “bacci” ta kada mishi kai ya kwantar da ita tareda ja mata blanket yace “sleep well princess” yana nan zaune bacci ya dauketa shikuma ya koma kan kujera ya zauna yana kallon ta dan yama manta cewar tare suke da Mubarak.
Wasa wasa Hydar se shirye shirye yakeyi na tafiyan shi, Kausar ko kadan tafiyan da zeyi be dameta ba saboda tasan zata samu hutu da jarabar shi sannan zata fita ba tare da fargaban komai ba, duk yadda Hydar yakeso ta bishi kafewa tayi akan bazata ba, haka ya hakura ya kyaleta, yau Sunday kuma yau ne tafiyansu, jirgin yamma zasubi saboda haka tinda safe yaje yawa sirikanshi da iyayenshi sallama duk suka bishi da addu’an samun alkhairi sannan ya dawo gida wurin Kausar suka sha soyayyarsu, duk da yasan Kausar ‘yar rigima ce amma zeyi miss dinta fiye da yadda take tunani dan kuwa ta riga ta zama wani bari na jikinshi, he can’t do without her amma ita sam bazata gane wannan ba.


+

Kausar da kanta ta kaishi airport inda ga mamakinsu su Ummi da Zeena harda Abba, haka ma su Dad da Khalil duk sunzo rakiya, sosai yaji dadin ganinsu bayan sun gama gaisawa Khalil yajashi gefe tareda cewa “ka tafi da maganinka tinda Kausar ba binka zatayi ba karkaje kayi abin u will regret later” murmushi yayi yace “da maganin zan tafi, Kausar dai zata wahalar dani, ita gabadaya bata gane abinda yasa nace seta bini ba, na rasa ya zanyi ta gane” tausayi yaba Khalil dan su kadai sukasan irin halin da yake shiga in ciwon maran nan ya tashi, ganin kallon da Khalil ke mishi yasashi yin murmushi tareda dafa kafadan shi yace “don’t worry, I will be fine, kuma ai zan dinga zuwa ina weekend a nan” hararar shi Khalil yayi yace “like it’s easy” sannan ya juya ya wuce Hydar yabi bayanshi yana dariya.

Kausar seda taga da gaske gasu a airport sannan hankalinta ya fara tashi, yanzu fa da gaske tafiya zeyi ya barni ta fada a ranta tana kallon Hydar dake hira da Khalil yana dariya, wani irin tunani ne ya dinga fado mata a rai “yanzu idan yayi budurwa a can fa, idan ya fara bin mata saboda bana wurin fa” se kuma ta girgiza kai tana kawar da tunanin dan tasan Hydar bazeyi ba, seda taga tafiyan yazo gashi ana kiransu su shiga ciki idanunta ya fara ciccikowa da kwala, zuwa yayi yama iyayenshi sallama kafin ya dawo wurinta yaga idanunta na kawo ruwa, murmushi yayi ya rungumeta be damu da iyayensu na wurin ba a kunne yace mata “kukan me kikeyi bayan kece kikace bazaki bini ba” dukan kirjinshi tayi tace “idan bazan bika ba se aka maka bazanyi missing dinka ba” murmushi yayi har hakoranshi suka fito yace “u know I will miss u more” bata ce mishi komai dan a ganin ta besan yadda takeji bane, kara kankanmeshi tayi kanta nakan kirjinshi a hankali yace “Wifey I’m running late, free me” hararar shi tayi tana sakeyi yayi pecking din goshin yayi gaba, har ya yayi nisa ya kuma juyo tana daga musu hannu duk suka daga mai hannu banda Kausar dake kuka tsakaninta da Allah.

Ummi ce ta lallashe ta sannan duk sukayi sallama suka wuce itama ta shiga motanta tareda hade kai da steering tasa sabon kukan, tana nan zaune har seda taga wucewar jirginsu sannan taja motarta zuwa gidansu Miemie dan dama ta mata alkawarin zatazo. Da zuwan ta gidan tayi parking sannan ta shiga parlour inda Maman Miemie din da Kamil kaninta suna zaune suna kallo Mama tace “Amarya kece a gidan” Kausar tayi murmushi tace “wlh nice” ta zauna suka gaisa sannan ta tambaye ta ko Miemie na ciki tace tana kitchen, kitchen din ta shiga ga mamakin ta taga Miemie ta zage tana girki, baki bude tace “me zan gani haka, bakya tsoron ki kone?” Miemie ta harare ta tace “tsoron konewa se kace ba mace ba” tabe baki Kausar tayi ta zauna kan kitchen cabinet Miemie dake soya nama ya juyo tace “ya naga idonki kaman wacce tayi kuka” ajiyar zuciya ta sauke tace “ba dole inyi kuka ba, Hydar ya wuce yau dinnan” girgiza kai Miemie tayi tace “wato duk yadda na nuna miki dalilin da ya kamata ki bishi kinki binshi koh, to zauna nan a kwace miki miji” ta gama fada tana takaicin halin Kausar, hararanta Kausar tayi in I don’t care manner tace “nasan waye mijina kuma nasan mata basa gabanshi, so just forget it, nidai yanzu yunwa nakeji me kuka dafa” Miemie tace “jollof rice ne gashi chan a cooler” Kausar dake gyara zama tace “ni zanyi serve din kaina?” takaici ya ishe Miemie tace “da wa kikeso yayi serve dinki, ni ko wa? Gwandama ki tashi ki zuba dan I’m not ur maid” tsaki Kausar taja sannan ta tashi ta dauka plate.

STORY CONTINUES BELOW

Su Hydar cikin lokaci kankani suka isa Lagos dan dama tafiyan 45min ne ta jirgi, koda sukaje already mota biyu na jiransu dan dama su shida ne amma biyu ne kawai masu matsayin generals sauran duk yara ne, seda aka fara sauke Hydar da El Ameen wanda shima general ne, a Ikeja wani haddaden gida mai gini uku a compound daya, already guda daya is occupied sauran biyun kuma aka bawa Hydar da El Ameen keys ko wanne da gidanshi, sauran kuma barrack aka zarce dasu, Apartment din Hydar ne a tsakiya inda ya bude ya shiga yaga ko ina neat, an share an goge everything is shinning and sparkling, murmushi yayi danshi Allah yayishi da son tsabta, duba gidan yayi yaga gidan kasa ne me two bedroom ko wani daki da toilet se kitchen da dinning da balcony, sosai tsarin gidan ya mishi kyau gashi komai na zamani akasa, akwai komai na electricity babu abinda ze bukata. Shima side din El Ameen duk hakan dinne babu abinda aka canza, shima sosai wurin ya mishi kyau, Hydar wanka yayi ya canza kaya sannan ya dauko wayanshi ya kira Kausar wacce har lokacin ta na gidansu Miemie, sosai sukasha hiransu kaman bazasu rabu ba har seda sukaji kiran sallahn magrib sannan suka kashe wayan, Hydar beyi tunani akwai masallaci a area din ba amma ga mamakinshi se yaji kiran sallahn har cikin dakin shi kaman bayan window dinshi ake kiran sallah.

Kausar seda tayi sallahn isha sannan ta fito ta musu sallama Maman Miemie se fada take mata tace “idan kika fita ki daina bari dare na miki a waje koda ace mijinki baya gida kinji” Kausar da kanta ke kasa tace “toh mama ngd” sannan sukayi sallama bayan Mama ta hada mata kayan su na mata da baza’a rasa ba. Har bakin mota Miemie ta raka Kausar tana cewa “matar Hydar a duba titi da kyau banda gudu dan nasan halinki, kinga dai dare ne” murmushi Kausar tayi tace “toh uwata bazan yi gudu ba” sannan ta shiga motan tana dariya, seda Miemie taga fitanta daga gidan sannan itama ta shiga gida tana mamakin halin Kausar na rashin wayo da komai ya faru tsakaninta da mijinta seta fada. Kausar gudu kawai takeyi a mota tanajin wakan Magnom_ Ma baby tana bin wakan hankalinta kwance taga titi shimfide ba targada wanda wannan ya bata sha’awa yasa take gudu, takai daidai Maitama layin unguwarsu zata karya kwana ta buge wata yarinya wacce ta fito from nowhere, ihu Kausar tayi ganin yadda yarinyar ke roll a kasa tana gangara titi kafin ta buge da wani pole ta tsaya cak.



✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Binta Alhmdllh lfy ya fara samuwa, doctor yaso yayi discharge dinta amma ya kyaleta saboda wasu dalilai, sosai take shan allurai abin tausayi, Anwar tinda ya bar gida be sake komawa ba sedai yaje gidanshi da babu wanda yasan yanada wannan gidan se abokanshi, Mubarak kusan kullum se yazo duba Binta har ta fara sabawa dashi, Anwar da Mubarak ne zaune cikin motan Mubarak gaban hospital din Mubarak yace “wai kai yaushe zama koma gida” Anwar ya sauke ajiyar zuciya yace “gobe za’ayi discharge dinta, inna kaita gida zan koma gida duk da nasan hukuncin da Dad ze dauka a kaina ba karami bane” shiru Mubarak yayi kafin yace “wani gidan zaka kaita, gidan Hajiya” girgiza kai Anwar yayi yace “bazata koma gidan Hajiya ba dan nasan bazasu kula da ita yadda ya kamata ba dan su kudi ne a gabansu, ka duba fa zuwansu nawa tinda ta kwanta kuma in sunzo ko one hour basayi” shiru Mubarak yayi chan yace “kana ganin Hajiya bazatayi magana ba” murmushi gefen baki Anwar yayi ya kalli Mubarak yace “dude kaifa kayi introduce dina wurin matar amma nafika sanin halinta, dana damka mata kudi shikenan an gama magana” kada kai Mubarak yayi yace haka ne, mu shiga ciki” fitowa sukayi daga motar suka shiga  cikin hospital din.


Zaune sukaga Binta tana game da wayarta kanta ba dankwali duk gashinta ya zubo a bayanta, tin daga kofa Anwar ke murmushi har ya karaso inda take ya zauna kusa da ita, tareda sa hannunshi yana gyara mata gashin kanta, dagowa tayi tace “ina ta jiranka tin dazu” cike da mamaki yace “wani abu kikeso ne” ta girgiza kai tace “dan Allah mu tafi gida, na gaji da zaman wurin nan” yadda tayi maganan a shagwabe kaman zatayi kuka seta birgeshi, ajiyar zuciya ya sauke yace “yi hakuri gobe za’a sallame mu” girgiza kai tayi tace “nidai mu tafi bazan iya sake bacci a wurin nan ba, wari ma yakeyi” batayi karya ba dan kuwa wurin warin chemical kawai yakeyi gashi tasha alluran da yanzu ko fitsari tayi se taga kaman fitsarin ruwan allura tayi, kada mata kai yayi yace “ina zuwa” sannan ya tashi ya fita.

STORY CONTINUES BELOW

Yana fita Mubarak ya dawo inda take yace “ni baza’a min magana ba” tayi murmushi tace “ina wuni” “ni bazan amsa ba tinda seda na roka” dariya tayi tace “yi hakuri” kallonta yakeyi yana mamakin meyasa idan zatawa Anwar magana take mishi magana a shagwabe amma shi se tana mishi magana normal, ganin kallon yayi yawa ne yasata cewa “lfy” yace “lfyr kenan”Anwar ne ya shigo da doctor bayan en gwaje gwaje yace ” zaku iya tafiya amma ka dawo da ita gobe da yamma dan bata gama karban allura ba sannan ku kula da abincinta, Allah ya kara lfy” suka amsa da ameen sannan duk suka hada kayansu tasa mayafi da takalminta suka fito.


A waje se Anwar yaga ta canza mishi dan ta kara haske tayi kyau, jikinta kaman ka taba jini ya fito, murmushi yayi ya juya yaga idon Mubarak shima kyam a kanta yana kallonta, Anwar a zuciyarshi yace “yarinyar nan in tafi haka zata ruda maza” Jan hannunta yayi yasata bayan mota shikuma ya shiga gaba Mubarak ya jasu, duk a tunaninta gidan Hajiya zasu kaita setaga ba nan sukaje ba gidan Anwar sukazo, a bakin gate Mubarak ya sauke su ya wuce sukuma suka shiga ciki, a parlour ta zauna shima yama kanshi masauki a three sitter yace “me zakici” kallonshi tayi tace “meyasa bamuje gidan Hajiya ba?” Yace “zan kaiki, inaso ki gama karban treatment ne” kada kai tayi tace “banajin yunwa, ruwa zansha” tashi yayi ya bata ruwa tasha sannan ya zauna yana janta da hira, a nan gidan ya kwana tareda da ita saboda ko kadan beson yayi nisa da ita dan hankalinshi ba’a kwance yake ba, yana tsoron kar ciwon ta ya sake tashi ba kowa kusa da ita.


Washe gari bayan sunci abinci tayi wanka ya shigo dakin yace “zanje na dawo, ba lallai na dawo da wuri ba amma zan dawo na kaiki hospital” kada kai tayi tace “seka dawo” murmushi yayi tareda shafa kanta yayi pecking dinta a goshi sannan ya fita jiki a sanyaye dan kuwa hankalinshi be kwanta da barinta ita kadai ba, yana fita ya samu taxi ya kaishi gida, a kofar gidansu ya tsaya gabanshi na dukan uku uku dan yau Sunday ya tabbata Dad na gida hakama Khalil, shahada yayi ya kwankwasa baba mai gadi ya bude mishi, gaishe da baban yayi ya amsa mishi yana mai binshi da kallo, a hankali yayi sallaman da babu wanda yaji seshi da yayi kayanshi, Dad dinshi dake zaune kan dinning idon kan kofan yace “ba’a koya ma sallama bane” se a lokacin su Khalil da Meenah da Mom suka juyo suna kallon shi, Khalil juyar da kanshi yayi, Mom kuwa hawaye ne ya ciko mata dan kuwa tasan gayen danta ya kade yau, Meenah kuwa taso wa tayi tazo ta rungumeshi tana cewa “Ya Anwar I miss, ina kaje yau one week ban ganka ba”.



Hydar dake goge baki da tissue yace ” Dad, Mom na wuce inada patient da zan duba” Dad ba tareda ya kalleshi ba yace zauna, kaikuma karaso” jiki a sanyaye duk sukayi abinda aka sasu Meenah kuwa se bin Anwar takeyi, duk inda yasa kafa toh kafanta na wurin, kallonta Dad yayi yace “wuce daki” cikin siririn muryanta tace “Dad don’t be strict with him, nasan babu abinda yayi” hararan da Mom ta watsa mata yasata yin shuru ta haura sama amma maimakon ta shiga daki seta labe tana kallonsu, tsugunnawa Anwar yayi a kasa Dad yace “ina ka shiga?” shiru yayi dan bema san me zaice ba” Dad ya kara cewa “naga alaman bakada bakin magana saboda haka yau nida kaina zan maka hukunci sannan daga yau ko nan da gate bason na kara ganinka, zaka bani wayanka, wallet dinka, da everything da kasan kana dashi, sannan na soke zuwanka sch dan dama ba zuwa kakeyi ba, sannan daga yau kai zaka dinga share min compound, kayi watering din flowers din waje idan ka gama kuma by 8 ina son ganinka a company, zaka dinga wanke wanke a company kitchen har na tsawon one month” Mom na son tayi magana amma ba dama saboda tasan halin Dad amma harga Allah a ganin ta hukuncin yayi tsauri dayawa, ko Meenah dake lekansu silent tears ne suka fara zarya a kumatunta, Khalil kuwa shiru yayi danshi bemasan abinda yasa Dad ya tsayar dashi ba, ga mamakinsu seji sukayi Dad yace “Khalil shiga dakina ka duba kan window akwai dorina dauko min” ba Mom da Anwar da Meenah ba hatta Khalil seda ya kalli Dad kafin yace “ba dai dukanshi zakayi ba” “zaka dauko ko na dauko da kaina” cewar Dad fuskanshi ba alaman wasa, a saninsu babu dorina a gidan toh a ina ya samo, jiki a sanyaye Khalil ya mike ya wuce dakin Dad da sauri Meenah ta boye  saboda karya ganta amma ya riga ya ganta sedai yayi tafiyarshi kaman be ganta ba dan tsakanin ita da Anwar shakuwa ce wanda bazasu iya fasaltashi ba, Khalil ne ya dawo dauke da dorina me baki uku da sauri Mom ta mike tana cewa “wlh Alhaji bazaka dakarmin d’a da wannan abin ba, se kace wani jaki” kallon Khalil Dad yayi a hankali Khalil ya janyeta daga kare Anwar da takeyi a riketa sosai yadda bazata iya kwacewa ba se cewa take “Khalil sakeni, karka bari ya dakeshi, ciwo zeji mai”.

Khalil kam karfin hali kawai yakeyi amma koshi be goyi bayan wannan dukan ba, “mike ka dafa table dinnan” dake nade hannun babban rigarshi yayi magana, a hankali Khalil ya mike yayi abinda aka sashi tareda runtse ido yana kirga 1-10 ai kuwa be karasa ba yaji saukar dorina a bayanshi wanda bashi kadai ba su dukansu seda sukaji saukar dorinar nan, Meenah dake labe batasan lokacin da ta saki ihu ba a fusace Dad ya kalleta yace “me nace miki” ai da gudu ta bar wurin jikinta na rawa, Mom kuwa hawaye takeyi tama daina mutsu mutsun Khalil ya sake ta, a gabansu Dad ya ringa dukan Anwar har seda Mom taga jini a riganshi, ihu tayi wanda seda ya fito da Meenah daga daki, batasan sanda wani karfi yazo mata ba ta ture Khalil gefe da sauri ta karasa wurin Anwar tana kareshi cikin kuka tace “wlh sedai ka dakemu tare, amma bazaka kashe min d’a a gabana ba” Dad jikinshi ne yayi sanyi ganin yadda Mom ke kuka, Meenah da saukowa tayi tana cewa “Ya Anwar” amma shiru, tabashi tayi taga ya tafi ze fadi da sauri Khalil ya taroshi Mom da ranta ya gama baci tace “sakeshi” tsayawa yayi yana kallonta tace “bakaji bane, nace ka sakeshi koh” a hankali ya sakeshi yaja baya ta kalli Meenah tace dauko mun makullin mota da mayafi” da sauri Meenah taje ta dauko suka kama Anwar suka fita Khalil ya kalli Dad dayabi bayansu da kallo sannan shima ya fita, Dad kuwa hannu yasa ya dafe kai ya rasa gane abinda yasa Anwar keson ya bata mishin suna a gari ba.
A rikice Kausar ta fito daga motan ta karasa wurin yarinyar da ta bige, dago yarinyar tayi tana jijjigata amma shiru sema jini daya biyo hannunta, kuka tasa tana gani kaman ta kashe rai gashi area din shiru babu mutane balle ta nema taimako, komawa mota tayi ta dauko wayan jikinta na rawa ta dannawa Hydar kira toh in ya dauka me zaki ce mishi?   Wani zuciyar ya tambayeta, katse kiran tayi kafin ya fara ringing  ta dannawa Khalil kira wanda shima shiganshi gida kenan daga masallaci yanaso yaje ya duba Anwar dan tunda su Mom suka  dawo bata ce mishi komai ba. Wayanshi dake cikin jallabiyanshi ne ya fara ringing, cirowa yayi ya duba yaga Kausar ce ke kira, cike da mamakin kiran me take mishi ya daga wayan tareda sallama, Kausar ganin ya daga wayan tasa mishi kuka sosai hankalinshi ya tashi yace “Kausar lfy kike kuka, meya faru? ” cikin shesheka tace “Khalil I need ur help, nazo shiga unguwa na samu accident, na bige yarinyar mutane gashi kaman ma bata numfashi” salati yayi yace “calm down I’m on my way, gani nan zuwa” be jira amsarta ba ya kashe wayan yayi cikin gida da gudu ya dauko key din motarshi ya fito. 




Kausar kuwa zama tayi a kasa kusa da yarinyar babu tabbacin da rai a jikinta ta hada kai da gwiwa tasa kuka, batasan adadin lokacin da ta dauka ba se ganin hasken headlight  din mota tayi ana mata horn, sosai gabanta ya fadi dan a tunaninta wani ne kuma gashi ta bar motanta akan hanya saboda haka ta taso dan ta gyara parking  kafin Khalil yazo amma se ganin shi tayi ya fito daga motan ya karaso wurinta amma idonshi nakan baiwar Allahn dake kwance kasa cikin jini, juyowa yayi yace “gyara parking  dinki kin tare hanya bari na dubata” kada kai kawai ta iya mishi sannan ta shige  motanta shikuma ya karasa kusa da yarinyar, hannunta ya kama yaji pulse dinta na aiki saboda haka ya kinkime ta yakai ta mota Kausar tabi bayanshi suka kama hanyar hospital Kausar se kuka takeyi shikuma ya kira hospital  ya shaida musu gashi nan zuwa da patient kuma emergency ne. 






Shiru sukayi a mota se sheshekan kukan Kausar har suka karasa hospital  din, koda sukaje nurses na jiransu da gadon daukan marasa lfy, da taimakon Khalil suka shiga da ita ciki Kausar na biye dasu a baya emergency room  suka shiga da ita Kausar ta zauna a bakin kofa tana duk adduar da ya fito daga bakinta dan a tsorace take sosai. Sai da suka kwashe 3hours a ER kafin su samu numfashinta ya dawo sannan suka danyi gwaje gwaje akayi treating ciwukanta, fitowa Khalil yayi yaga Kausar zaune ta hada kai da gwiwa sai ta bashi tausayi, kiran sunanta yayi a hankali ta dago ganin shine yasa tayi saurin goge hawayenta da mayafinta tace “Khalil ya take, ta farfado” kada mata kai yayi yace “bata farfado ba amma numfashinta ya dawo,  muje office muyi magana kafin ki fito an gyarata seki shiga ki ganta” kada mai kai tayi sannan tabi bayanshi zuwa office din. 




Zama tayi shikuma ya dauko mata ruwa a fridge ya bata, kadan tasha sannan tabishi da kallo tana jira yayi magana ya zauna yace “fadamun ya akayi kika bugeta” goge hawayenta tayi tace “wlh yarinyar ta shigo gaban ne out of no where, nikuma koda na ganta it was already  late” girgiza kai yayi yace “yarinyar is trying to run from someone, dan naga alaman fingers da cizo da sauransu a jikinta, she was molested to the core, amma Allah ya taimake ta tayi escape, yanzu jira zamuyi ta farfado kafin musan abinyi dan seta farfado zamu samu mu gane ko tanada internal injuries” kada kai Kausar tayi tana goge hawayenta, tare suka fito zuwa dakin da aka kwantar da baiwar Allah inda Khalil ya shiga yaga komai daidai sannan yace “Kausar shigo, bari naje na dawo se in kaiki gida” kai ta kada  mishi sannan  ya fita ta jawo kujera ta zauna kusa da gadon tana kallon yarinyar dake kwance numfashinta na fita a hankali, kallo daya gabadaya setaji yarinyar ta shiga ranta, hannunta ta kai ta riko na yarinyar tana murzawa a hankali hawaye na ciko mata a ido, murya kasa kasa tace “I’m sorry” goge hawayen da suka zubo mata tayi sannan ta gyara zamanta tana addu’an Allah yaba baiwar Allahn nan lfy. 




STORY CONTINUES BELOW

Bata dade ba Khalil ya shigo da sallama ta amsa mishi yace “muje in kaiki gida” kallon gadon patient din tayi tace “waze kula da ita? “, “karki damu nawa nurses magana, kuma nima night duty ne dani” ya bata amsa,  batace komai ba ta mike yayi gaba tabi bayanshi zuwa parking lot. A mota babu me magana dan kuwa da tunanin dake damunshi, ita matsalanta yarinyar da ta buge, shikuma tunanin halin da Anwar ke ciki yakeyi har suka kai gida, kallon Khalil Kausar tayi with pleading eyes tace “Khalil dan Allah banso Hydar yasan abinda ya faru yau saboda kar ya shiga tunani,  i will tell him when I think it’s the right time” kada mata kai yayi saboda ya gane abinda tace sannan yace “karki damu, nima I don’t have plans of telling him” murmushi tamai sannan ta fita tana godiya, seda gateman ya bude mata gate ta shiga gida sannan yaja motarshi ya koma gida dan yaga ko Mom zata kulashi yanzu. 





Hydar kiran duniyar nan yama Kausar amma bata pick, sosai hankalinshi ya tashi dan yasan Kausar batakin daga wayanshi, “toh meya faru?” Ya tambayi kanshi yana sake danna mata kira  still bata dauka ba, kallon time yayi yaga past ten yace “toh kodai tayi bacci ne?” Shi kadai yake zancen zuci daga baya dai ya ajiye wayan ba tareda ya kawo komai a ranshi ba, ya tashi ya shiga bathroom ya dauro alwallah yazo ya tada sallah. Kausar na shiga gida direct dakinta ta wuce ta rage kayan jikanta tayi wanka tasa kayan baccinta sannan ta tuna da wayarta, ciroshi tayi daga jaka taga more than 15missed calls duk na Hydar ne, da sauri ta kirashi back ringing biyu ya dauka tareda mata sallama amsawa tayi tareda cewa “yanzu naga missed calls dinka na manta da wayan a mota ne se yanzu na tuna” batare daya kawo komai akai ba yace “ba damuwa, dama I thought as much, hope you’ve start missing me cus I’m missing you” gyara kwanciyarta tayi tace “off course I’m missing, I’m missing my better half my abokin fada” dariya yayi yace “nima I’m missing my rigimammiyar wife” dariya tayi gabadaya seat tuno lokacin da suke saurayi da buduwar, haka suka raba dare suna waya kafin suyi sallama ta kashe wayan ta kwanta cike da tunanin baiwar Allahn dake hospital. 

✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Mom da Meenah hospital dinda Khalil ke aiki suka kai Anwar dan anan sukeda file, suna zuwa nurses din suka kulasu saboda sunsansu, Dr Paul ne ya dubashi inda ya mishi allurai ya basu maganin pain killer yace dayasamu bacci zeji normal sedai scars dinda ke bayanshi ne ze dau lokaci kafin ya bace, godiya Mom ta mishi sannan taje ta biya bills dinsu suka wuce gida, daki suka kai Anwar ta kwantar dashi tareda ja mishi blanket, “Mom” taji muryan Anwar na kiranta, kallonshi tayi tace “son kanason wani abu ne” rike hannunta yayi yace “kice wa Dad ya yafemin kar yayi fushi dani” kwallan dake idonta ta goge sannan tace “kwanta ka huta, zan fada mishi” kada kai yayi sannan taja hannun Meenah suka fita sukaja mishi kofa. 


Gyara kwanciyarshi yayi yana tunanin Binta dan yasan tana chan tana jiranshi, gashi be ajiye mata abinci ba, koma ba waya hannunshi, rufe ido yayi yana addu’an Allah yasa tana lfy har bacci ya daukeshi.  Hajiya mai gidan dadi kuwa da safe ta tashi ita da Asabsy suka shirya dan sunsan yau za’a sallami Binta, da isarsu hospital din aka sanar dasu ai an sallameta tin jiya, Hajiya ba tareda ta damu ba suka koma gida dan tasan Anwar ze dawo da Binta gida inda Asabsy kuma ta tafi harkar  gabanta ba tareda sun wani damu ba. 



Binta kuwa bayan fitan Anwar ta samu wuri a parlor ta zauna tana danna wayan hannunta, haka tayi ta zama ita kadai har magrib amma shiru ba Anwar ba alamunshi, tayi kiran wayanshi amma baya shiga haka ta hakura ta zauna tana kallon agogo, knock  taji da sauri ta kalli kofan dan tasan Anwar baya knock, jin bugun yayi yawa ne yasa ta mike taje ta bude inda taga Mubarak tsaye yana mata murmushi, ” ina wuni” ta gaishe shi “lfy lau en mata, ykk, ya jiki?” “da sauki” ta bashi amsa tana tunanin meya kawoshi, kallonta yayi yace “Anwar fah, yana ciki?” Ta girgiza kai kaman zatayi kuka tace “tinda ya tafi be dawo ba” murmushi Mubarak yayi dan yasan yanzu ze samu abinda yakeso saboda haka ya raba ta gefenta ya shiga parlorn yama cewa “zoki bani ruwa nasha” rufe kofan tayi ta nufi hanyar kitchen ta dauko mishi rowan gora ta mika mishi sannan ta zauna akan kujera kanta kasa. 



Shan ruwan yakeyi yana kallonta yana raya yadda ze huta a jikin wannan beautiful angel din, ajiye goran yayi sannan ya tashi ya dawo hannun kujeran da take zaune yakai hannunshi fuskarta yace “abu nazo nema wurin ki, da fatan zaki bani hadin kai?” Kallonshi tayi jikinta na rawa yayi murmushi yace “karki damu bazan miki da zafi ba” sannan ya mike ya kinkinme se daki inda Binta tuni ta gano abinda yake shirin yi, duka ta fara kai mishi tana zaginshi tace “ka kyale ni banaso wlh ka kyale ni ko in gayawa ya Anwar” shi dariya ma ta bashi wai ta rasa wanda zata hadashi dashi se Anwar, ai ko a ido yafi Anwar girma da cika, direta kan gado yayi kafin ta mike ya kwanto kanta batare da ya sake mata nauyi ba, hannunshi ya kai ya yaye dankwalin kanta yana shinshina gashin kanta ita kuwa se shure shure takeyi, hannunshi daya kawo fuskarta ta gantsarawa cizo ai kuwa ba shiri ya mike yana yarfe hannun tayi saurin tashi. 



Da gudu ta nufi kofa amma kafin ta bude ya kamo gashin kanta yace “ni zaki ciza, ko dan kinga ina binki a hankali?” Shiru tayi a yayin da hawaye suka fara ambaliya a fuskarta tasa hannun ta rike hannunshi dake kan gashinta saboda azaba, be kalli yanayin da take ciki ba ya wurgata kan gado tareda komawa kanta yana kokarin cire kayan jikanta, mutsu mutsun da takeyi ne ya hanashi samun dama saboda haka ya haskata da mari a fuska yana cewa “dan ubanki bazaki tsaya ba?” Kuka tasa mai tana cewa “dan Allah ya kyale ni, ka rabu dani, ka kyakeni” amma yayi kunnen uwar shegu yaci gaba da abinda yakeyi, Anwar ne ya fado mata rai ta ringa addu’an Allah ya kawoshi yanzu dan he is her only savior, ganin Mubarak yayi nasarar yage  rigarta ta gaba har farcenshi yaji mata ciwo yasa hankalinta kara tashi, addu’an takeyi tana kiran sunan Anwar Mubarak ya kara marinta tareda cewa “kika kara kiran sunanshi sena ji miki ciwo” sannan ya sausauta murya yace “sunana nakeso ki dinga kira kinji baby” banza ta mishi ya kara jan gashinta yace “kinji ko baki ba” tace “naji” cikin kuka, murmushi yayi yana kallon kirjinta da ba wani dukiyar fulani ne a wurin ba amma shi a haka yakeso, hannu yakai yana wasa dasu ta juyar da kanta gefe  idonta ya sauka kan plate dinda taci abinci dashi jiya, tureshi ta shiga yi ya dago da jajayen idonshi yana kallonta yace “kika kara tureni sena lahira yafiki jin dadi” mikewa yayi ya fara cire kayan jikinshi ita kuwa ganin haka yasa ta tashi tayi kofa da gudu ya jara kamota ya wurga ta kan gado yana cewa “bazaki bari na biki a sannu bako?” Shiru tayi tana kallon nude image dinshi kafin ta juyar dakai yayi kwafa sannan ya dawo kan gado ya kama skirt dinta yana kokarin janshi kasa ta kai kan plate din ta dauko a hankali sannan ta seta kanshi dake kallon pant dinta ta buga mishi da duka karfinta wanda yasa plate din tarwatse wa akanshi har wasu pieces sun yanketa a cinya, shikuwa ihu yayi ya mike da sauri yana rike kanshi da jini ke fita sosai ga wani uban jirin dake dibanshi. 



Binta ganin haka yasa tayi saurin mikewa taja skirt dinta sama ta fita a 360 ba tareda ta waiga ta kalli bayanta ba, gateman din na kokarin hanata fita amma ina hartayi gaba, Mubarak kuwa cike da jin zafin abinda ta mishi ya juyo amma yaga wayam babu ita ba alamun ta, tashi yayi yasa kayanshi ya fito yana rangaji yana hada hanya shidai gateman kallon ikon Allah yakeyi dan bega shigan Mubarak ba, Mubarak left ya kalla sannan ya kalli right yaga babu alamun Binta kawai seya shiga motanshi ya dau hanyar hospital saboda jinin da ke tsiyaya daga kanshi.  Gudu takeyi bata kallon baya, dukda ta gaji amma bata tsaya ba se gudu takeyi bata kallon gaba bata kallon baya, tana kuka tana kiran sunan Anwar batayi aune ba se ji tayi mota yayi sama da ita ta gangara kafin komai ya dauke mata duniyar ta mata duhu da sunan Anwar a bakinta.
Kiran sallahn asuba ne ya tashi Kausar daga baccin da takeyi, seda tayi wanka sannan tayi alwallah tazo tayi sallah tayi azkar dinta da addu’oi sannan ta mike daga kan sallayan, agogo ta duba taga shida da rabi kuma tanada meeting da client dinta karfe takwas saboda haka se bata koma bacci ba, shiryawa ta shigayi kafin ta kammala bakwai tayi ta dau jakanta da wayarta ta fito, kulle gidan tayi sannan ta fita gateman ya bude mata gate ta taka har inda ta bar motanta jiya, seda tayi warming din motan sannan ta kama hanyar hospital dan zuwa duba yarinyar da ta buge. 



+

A harabar hospital din tayi parking inda tana parking Khalil ma na parking, fitowa tayi suka gaisa sannan tace “ba kacemin night duty kake dashi ba?” “Eh night ne amma brother na ba lfy shiyasa dana koma gida dubashi ban dawo ba dan a gajiye nake, kuma banda wani abunyi a nan shiyasa nayi kwanciya na” kada kai tayi tafara tafiya yana gefenta tace “doctors kuna kokari, ba kuda lokacin hutu, ya jikin kaninka?” “da sauki” ya bata dukda sanda ya shiga duba Anwar yayi bacci, karasawa dakin Binta tayi taga nurse tsaye tana goge mata jikinta da wet towel, gaisawa sukayi sannan nurse din ta wuce ita kuma taja kujera ta zauna tana kallon Binta. 




Da yake gari ya waye seta samu daman kallonta da kyau dan jiya da daddare kallon tsoro ta mata, murmushi tayi tace “she’s beautiful” sannan ta kai hannu tana shafa kanta wanda ke daure da bandage.  Khalil ne ya shigo tareda nurse da file a hannunshi ya shiga duba  Binta yana gamawa nurse din ta canza mata drip ta mata allura sannan ta fita, Khalil kallon Kausar yayi yana zama gefen gadon yace “jiya akwai test dinda muka mata wanda daga ciki akwai na genotype, blood group da sauransu and result ya fito, daga mishi kai tayi alaman yaci gaba, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace “as for her blood group she’s A+ while genotype nata kuma is SC meaning she’s sickler” “My goodness! ” Kausar tayi exclaim tana kallon Binta, murmushi yayi yace “Kausar calm down bari na gama” shiru tayi tana kallonshi yace “we have two types of sickler akwai SS akwai SC and she falls under SC which means akwai possibility she will have a long life saboda SC basa yawan ciwo kaman SS,  so if she’s taking her medication properly everything will be fine”. 



Kada kai Kausar tayi tana kallon Binta dake bacci, gabadaya se tausayinta ya kama ta, maganan Khalil ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada yace “again her blood is short by 35% wanda wannan zena causing dinta dizziness da lack of stress, meaning she will always be weak, amma kuma their is an advantage to her shortage of blood dan yanzu idan tayi accident and she loses lots of blood she can still survive it akan wanda blood level dinshi is 100% cus shi idan yayi accident kuma yayi loosing blood sosai he dies instantly amma in her case it won’t be like that dan se blood dinta ya kare to zero level ne zata mutu amma wannan bazesa taki karban drug ba dukda blood tonic is dangerous for her zan rubuta mata wasu magagun nan da zasu kara mata karfin jiki da kuzari”. 




Shiru Kausar tayi tana tunanin what  the girl might have gone through, to be a sickler is not easy, u have only a little hope of having a long life, they die at young age, they die early, batayi aune ba taji hawaye a fuskan ta, hannu tana ta share sannan ta kalli Khalil tace “a rubuta maganin I will pay the bills, akwai client da zanje na gani, anjima zan dawo” kai ya daga mata sannan ta sauki jakanta ta fita, Khalil yabi bayanta yaja kofan, bata tsaya ko ina ba se office nata inda tana shiga wayanta ya fara ringing, daukowa tayi daga cikin jaka, ganin Hydar ne yasata saurin dauka tareda mishi sallama, amsawa yayi cikin husky voice dinshi sannan yace “yau zan shiga office, wish me luck” murmushi tayi tace “Allah ya baka sa’a yayi albarka, may my prays always be with you” “ameen my wifey, ok I have to go will talk to you later, love you” “love you more” ta amsa mishi tareda kashe wayan sannan ta kira secretary dinta tace ta shigo da client din. 



✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴



Hydar tun asuba ya tashi, a masallaci ya hadu da El Ameen suka gaisa sannan sukayi sallah, seda suka idar sunzo shiga gida sannan suka hadu da makocinsu na uku, babban mutum ne shima me suna Alhj Bello, yana tare da matarshi da yaranshi biyu duka maza wanda dukkansu ke karatu a Ilori, sosai suka gaisa yake ce musu da dare suzo suyi dinner a gidanshi dan su san juna da  kyau wanda da kyar suka yarda, bayan duk sun shiga gida Hydar yayi wanka ya hada coffee ya zauna a parlor yana kallon news @7, tsarin gidan ba karamin kyau ya mishi ba, Inama Kausar na nan ya fada a zuciyarshi yana sauke numfashi. 



STORY CONTINUES BELOW

Tashi yayi bayan ya gama sannan ya shirya cikin sabon kakinshi wanda ya bala’in amsar shi ya look young kaman dan 25 nan kuwa yaba 30 baya, taje gashin kanshi yayi ya feshe jikinshi da turare sannan ya dau wayanshi da laptop ya dawo parlor ya zauna ya kira Kausar suka gaisa sannan ya kira Ummi itama suka gaisa ta bawa Zeena dake  shirin school itama ta gaisa sannan ya kashe ya kira Abba. 



Horn yaji alaman anzo daukan su saboda haka ya fita ya kulle kofan shima El Ameen ya fito sanye da nashi kakin daya mishi kyau, murmushi sukawa juna sannan suka kara gaisawa suka shiga mota driver yaja su se Ikeja Military  Cantonment, anan aka hadasu da wani driver inda ya kaisu offices nasu dake cikin ikoyi,  seda sukayi tafiya me tsayi kafin sukai destination nasu, manyan mutane ne a barrack din,  ga lafiyayyun office, ga training ground, sosai sukaga haduwan wurin sedai yayi nisa da gidan da aka basu saboda haka suka yanke shawaran zasuyi magana a dawo dasu kusa. 





✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴



Hajiya dai shiru shiru za’a kawo Binta baza’a kawota ba gashi yamma na neman doso kai, kiran Anwar tayi amma wayan a kashe, ganin yadda ta damu yasa Asabsy cewa “ki kwantar da hankalin Hajiya Anwar ze dawo da ita, ai ba yau ya saba dadewa be dawo da ita ba” girgiza kai Hajiya tayi tace “Asabsy ni tsoro nakeji kar ya gudu da er mutane in shiga uku dan Antyn birni ba mutunci ne da ita ba, kuma  kwana biyu ban tura mata kudi ba, nasan tana nan tana jira” ajiyar zuciya Asabsy tayi tace toh in hakane mu bari zuwa gobe in bata dawo ba se musan abinyi” kai Hajiya ta kada tana tunanin ina yarinyar mutane ta shiga. 



✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴


Zinaru kuwa kudin da ta samu dashi ta siya karamin waya ta siya kayan gumama tazo kauye tana siyarwa,  kuma ba laifi ana siya, kwana biyu bataga Antyn birni ba saboda haka yau ta dau alwashin kiranta, wayanta ta dauko ta dannawa Antyn birni kira amma bata dauka ba se a kira na biyu, “Hello Zinaru ina sane dake ki bari ina hanya ma na kusa karasowa gidanki” murmushi Zinaru tayi tace “shikenan yaya se kinzo” da haka ta kashe waya ta tashi ta daura girki kafin yayar nata ta karaso. 




Da sallama ta shiga gidan Zinaru ta amsa mata tana cewa “Yaya sanda zuwa kinsha hanya” ta fada tana shimfida tabarma, zama Antyn birni tayi tace “ke zauna da magana nazo dan ba sauki” “me kike nufi?” Zinaru ta tambaya tana kallon yayarta, “kedai ki zauna nace koh” zama Zinaru tayi ta bude kunnuwa danjin me Antyn birni tazo dashi, kallon Antyn birni tayi tace “Zinaru da matsala” cike da mamaki Zinaru tace wani irin matsala?” gyara zama Antyn birni tayi tace “kwana biyu naga Hajiya mai gidan dadi bata turon kudi ba se naje gidanta amma bata nan, kinsan me yaranta sukace cemin” kada kai Zinaru tayi tace “se kin fada Yaya” “hmmm cewa sukai wai sati daya  kenan wannan er Bintoto bata gidan kuma Hajiyan batasan inda take ba” “Me!” Zinaru ta kwakwalo ido waje tareda cewa “Inaaa ai bazata sabu ba dan bansan zancen ba, dole ta nemo min yarinya, in bazata iya riketa ba ta dawomin da ita inci gaba da gasa mata gyada a hannu amma wlh bazan yarda ba seta fito da Bintoto”. 





Ajiyar  zuciya Antyn birni ta sauke tareda cewa “me kikeci na baka na zuba, ai hanyar arzikin mu ne yazo mana a saukake, nasan kinfini bala’i shiyasa nazo na dauke ki muje birni gidan Hajiyan tare, in munje musa mata wuta ta fito mana da er mu kota biyamu miliyan biyar a kashe maganan koya kikace” “ayyrrrrr, wannan haka yake tawan,  haka zamuyi” cewar Zinaru tareda da kai hannu suka tafa sannan Zinaru ta gyara zama tace “yaushe zamu” “gobe” Antyn birni ta bata amsa tana mikewa tace “zubomun abinci inda akwai na kwaso yunwa, bari na zaga” buta ta dauka tayi bayan gida ita ita kuma Zinaru ta shiga kitchen tana shewa dan harta hango kanta da miliyan biyar, (nikuwa nace in banda shirme wata nawa kudin ze kare). 




✴✴✴✴✴✴✴✴✴✴



Anwar kafin safe yaji kwarin jikinshi wanka  yayi yayi alwallah yazo ya tada sallah, addu’oi sosai yayi yana fatan Allah yasa Binta na lfy dan dole yaje ya duba ta, saboda haka ya fito zuwa dakin Mom dinshi, da sallama ya shiga ta amsa mishi tareda ajiye littafin dake hannunta tace “Son shigo, ya jikin?” “Jiki yayi sauki Mom” ya bata amsa yana zama kan gado kusa da ita , “me zakaci in dafa ma?” Ta tambayeshi tana shafa kanshi, murmushi yayi kafin yace “duk abinda kika dafa zanci” kada mishi kai tayi sannan ta mike yayi saurin cewa “erhm Mom” juyowa tayi ya kalleta yace “kinwa Dad magana” murmushi tayi sannan taje gaban dressing mirror dinta ta dauko mishi wayanshi da wallet tace “na mishi magana, yace ya hakura amma be baka iznin fita ba, ga wayanka da wallet yace na baka” yake yayi kafin ya yasa hannu ya karba Mom shafa kanshi tayi sannan ta fita dukda taga yanayinshi amma ta basar dan dama tanaso tayi magana dashi amma seyaci abinci. 



Pancake ta mishi da tea yazo ya zauna a dinning yanata kiran layin Binta yana ringing amma bata dauka, sosai hankalinshi ya tashi, abincin Mom ta kawo mishi ta ajiye sama sama yaci ya shanye  tea din sannan yace “Mom dan Allah akwai inda nakeso naje, 30mins yayi nawa na dawo” kallonshi tayi tace “son zauna magana zamuyi” badan yaso ba sedan baya iyawa Mom musu ya koma ya zauna tace “kwanan nan na lura ka canza sosai har baka kwana gida, Son ni mahaifiyarka ce kuma bakada kamata, saboda haka inaso ka fadamin me kakeyi, wani hali kasa kanka ciki, ina kake zuwa?” shiru yayi ya sunkuyar da kanshi kasa dan besan me ze fadawa Mom ba,  baya iya yi mata karya, muddin ya bude bakinshi toh yasan gaskiya ce zata fito, “Son kai nake sauraro” kallon ta yayi sannan ya sunkuyar da kai yace “Mom mubar wannan maganan zuwa wani lokaci, inada inda zani yanzu plss Mom” “kasan Allah indan baka fadamin ba babu inda zaka dan dama mahaifinka yace konan da gate kar na bari kaje” shiru yayi tareda sa hannunwanshi cikin gashin kanshi yana tunanin taya ze fara fadawa Mom yarinya ya dauko ya ajiye a gidashi, “Ya salam” ya furta ba tareda yasan ya furta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *