AMAL
CHAPTER 2
lokacin da Amal ta shiga shekara Goma sha d’aya a duniya, “a lokacin zata shiga JSS1 inda ta kafe ita baza tayi secondary skul a k’asar nan ba, domin y’ay’an masu kud’i waje ake kaisu karatu,”inda tace yawanci y’ay’an talakawa ne suke karatu a wannan k’asar, taya ina y’ar mai kudi ace zanyi karatu cikin wannan k’asar?
Daddy ganin yanda tilon y’ar tashi ta dage yasa ya amince Amal taje waje tayi karatu.
Amma mamanta hjy Rabi wacce take kira da mum inda ta kafe Amal bazata waje karatu ba, “inda tace a nan ya aka kaya balle taje wata k’asar karatu?
Amal tayi fushi Sosai tata ta yanke, inda ta daina kulata na wani lokaci, “domin a cewarta uwarta bata Sonta, tunda bata son abunda take so, “Dad d’inta ne kad’ai ke Sonta, tunda shine yake mata abunda take so..
Bayan Amal ta Gama fushinta da Mum dinta, taje ta sami Mum dinta a d’aki akan ta barta taje waje karatu, bata son yin karatu da yaran Talakawa, musamman makarantur masu kud’i ana bama yaran talakawa scholarship
Mum tayi murmushi tare da kallon y’ar tata, tace Amal, kiyi hakuri ki duba ko wata makaranta Mai tsada sai kishiga
Tashi Amal tayi rai bace ta fita, domin tasan tunda mum ta kafe Toh ko zata mutu bazata Bari taje waje karatu ba, “wannan dalilin yasa Amal hakura amma fah badan taso ba, dan dai Anfi karfinta ne babu yanda ta iya.
Amal an shiga skul, tunda ta shiga bata hulda da kowa sai wata yarinya mai suna afra, wacce itama babanta mahaukacin Mai kud’i ne, ya ri’ke ma’kamai da dama, “wannan dalilin shine yasa Amal ke shiri da ita, “duk da makarantar yaran masu kud’i ne y’ay’an wance da wane “amma Amal ganinsu take kaman talakawa tunda tasan Daddy d’inta yafi nasu kud’i, tunda yana cikin masu kud’in Africa na y’an kasuwa na hudu yana son zama na biyu a halin yanzu domin kasuwancin shi yana ja Sosai
Tunda Amal ta shiga secondary school ta k’aro wani wulakanci, “Ga wani shegen son girma, “ko kad’an bata son raini, tasha Koran masu aikin gidansu akan laifi kalilan Wanda bai taka kara ya taka ba “yayin da wasu suke gudawa da kansu domin cin zarafin su, da takeyi, da kuma magana mara dad’i, ta dinga fad’in shi dama Talaka haka yake, “burin Talaka yaga mai kud’i ya wulakanta, toh ta Allah ba taku ba,tunda kuka zo a talakawa dole kuyi mana biyayya.
Lokacin da Amal ta cika shekara Goma sha uku a duniya, daddy d’inta ya shirya Mata wani haddan birthday party, inda tayi inviting Friends d’inta, An kashe dukiya Sosai, “a lokacin mahaifinta ya Mata kyautar da yaba kowa mamaki, inda ya mallaka Mata kud’i Naira million d’ari biyu da hamsin cikin account d’inta, “sannan yace ya bata kyautan gida a duk state din da take so a cikin Nigeria, sannan ya kara da fad’in Akwai tanadin da yayi ma y’arsa amma sai wani lokaci zai bayyana.
Rungume daddy dinta tayi tana murna, tare da fad’in “this is d best gift ever”you are d best daddy in d world
Hjy Rabi kam bata so yaba Amal wannan kyautar yanzu ba, “taso sai tayi aure ya bata, domin tana da rawan kai, gashi yanzu an bata wannan kud’in ta tabbata sai abunda ta gani yanzu
Tun daka wannan lokacin Amal ta k’aro wulakanci, tare da raina kowa, da kuma kallon kowa a d’age
Akwai sanda tama teacher d’insu raini harta zageta, “da yake skul din y’ay’an masu kud’i ne ba’a duka, shine akace tayi kneel down, a matsayin punishment d’inta.
Story continues below

Aiko Amal tayi kememe ta’ki yi, daka karshe dai fita tayi daka skul din inda ita da kanta tama kanta register a wani skul din daban ba tare da sanin iyayenta ba, tunda tana da kud’i.
Lokacin da labari ya iske iyayenta, ran hjy Rabi ya baci Sosai inda ta d’aura ma mijinta laifi, “akan abunda Amal takeyi shike d’aure Mata gindi baya son laifinta, gashi ya bata kud’i masu uban yawa, “AI dole ta dinga raina kowa, tare da ganin kowa ba kowa bane
Hjy Rabi tace Wlh makarantar data bari nan zata koma.
Daddy yace tayi hakuri ta barta tunda ta shiga wani, “ganin yanda ya kafe yasa hjy Rabi hakura
Amal tasha Koran masu aikin gidan, “inda hjy Rabi ta taka mata burki, “tun daka lokacin Amal Itama ta samo masu mata aiki daban tana biyansu,”in suka Mata abu kad’an ta koresu
Tun hjy Rabi na fad’an harta gaji ta zuba mata ido, tare da binta da addu’a, “domin abun y’ar tata na matukar bata tsoro Sosai
A yanzu haka Amal ta kammala secondary school inda ta dage ita waje zata karatu.
Amma Mum d’inta tace sam bata yarda ba
ita kam tace Wlh Indai a k’asar nan zatai karatu Wlh baza tayi ba,”domin university y’ay’an talakawa ne dana masu kud’i, “ba kaman secondary school bane,.
Hjy Rabi kam ta dage akan bazata fita waje karatu ba.
Wannan dalilin yasa har yanzu Amal ke gida ta’ki yarda tayi jamb, “sai dai tayi kudirin a waje zatai karatu koda kuwa mai Mum zata ce.
Amal bata da saurayi, domin ita Tana ganin tana da kud’i,”Inba ta samu wanda ya ninka taba toh bazatai soyayya dashi ba
Amal saboda irin nuna isa, da kuma dukiyar da ta mallaka yasa ake kiranta da millionaire Amal….. Wannan shine labarin Amal
*MUN DAWO KAN LABARI*
Washe gari da safe Usman ya shirya cikin Shiri domin zuwa wajan aiki, “Mama ta mi’ko mishi kunu da kosai tare da fad’in gashi kasha Kafin ka tafi.
Amsa yayi yana sha tare da fad’in ban cika son wannan kosan ba, “nafi son fanke wlh
Mama tace toh Usman abunda aka samu ai shi za’aci, “wani yaro na tura wai babu fanke sai kosai, “shine nace ya amso, da’a zauna haka AI gwara aci
Usman ajiye kofin kunun yayi tare da fad’in na koshi Bari in tafi.
Mama tace toh Usman, “Dan Allah ayita hakuri, wata rana sai labari, “Mai hakuri yana tare da Allah
Yace toh mama insha Allah
Fita yayi inda ya nufi titi yahau taxi, “domin cikin Abuja bako wace anguwa Mai keke napep ke shiga ba, ko machine
A dangareren gidan su Amal Mai taxi ya faka, “Usman biyanshi yayi sannan ya fita, yayi nocking aka bud’e gate din
Kai tsaye ya shiga inda ya fara gaisawa da security din gidan
Amal ce ta fito cikin shiri, “daka gani fita zatayi, “hannu ta d’aga tayi nuni da Usman Alaman yazo.
Usman yaso ya shareta amma saiya dake kawai yaje inda take
Kallonshi tayi sama da k’asa, “sannan tayi murmushi tare da fad’in “irin tarbiyar gidanku kenan? Ba’a koya maka gaida mutane ba?
Naga kanka yana hayaki, “karka manta kokai Waye, “kaifa Talaka ne, sannan Mai aiki na daka yau, “domin ka tashi daka Mai aikin Daddy ko Mum ka dawo Mai aikin Amal.
Dan haka daka yau karfe 5 nake son ka dinga zuwa aiki, 5am nake nufi, “sannan Ina son daka gobe ka Fara.
Sannan daka yau ban son in kana gabana Ina tsaye kaima kana tsaye, daka yau inna kiraka Ina son ka dunga tsugunnawa kaman yanda Kare yake yima uban gidansa
Usman ranshi ya baci Sosai, “wato shine Kare, amma saiya dake kawai, domin mahaifinta, “lallai inda badan ya fad’ama mahaifinta zai dawo aiki ba, da wlh bai dawo ba, “domin bazai d’auki raini ba, “gwara ko d’an garuwa ya zama akan wannan wulakancin….
Katse mishi tunani Amal tayi tare da fad’in hey Mr driver, “bude min kofa.
Murmushi yayi tare da bud’e Mata kofar ta shiga ya rufe kofar motar
Sannan yayi gaba abunshi
Amal dake mota tace Mai yake nufi Toh?
Cikin zafin rai ta bud’e motar ta nufi inda yake tace kai wai Mai kake ji dashi ne?
Waye Kai? Wai Mai yasa Talaka yake da zafin rai ne? Daka tafi uban wa, kake so ya tu’ka ni?
Ido ya kura ma fuskanta yana kallon k’aramin bakinta yanda take zuba bala’i da rashin kunya
Ganin ita yake kallo yasa ranta ya kuma baci, “tace am talking to you
Bai kulata ba, sai motar daya shiga ya zauna a wajan driver, “tsaki taja sannan itama taje ta shiga tare da fad’in fita ka rufe kofar
Bai kulata ba, Illa fitan da yayi, yaje ya rufe kofar motar, “sannan ya dawo ya tada motar, tare da fad’in madam Ina zamu?
Amal jin ya kirata da sunan da take so, “yasa tace cafe zaka kaini mafi kusa.
Tada fita yayi da motar suka hau kan titi, “a wani cafe suka tsaya inda ya fito ya bud’e Mata kofar motar.
Jakarta ta mi’ka mishi alaman ya amsa ya ri’ke mata.
Kallonta yayi cikin mamaki.
Lokaci d’aya kuma komai ya tuna yayi murmushi oho, “sai kuma ya amshi jakar.
Ciki ta shiga, “shima ya bita a baya.
Wata kujera ta zauna inda ta Fara danna computer din dake wajan, “shikam yana tsaye yana kallonta
Tunda yake bai taba k’are Mata kallo ba sai yau, “lallai Amal Tana dakyau gaba da baya, “sai dai ace bata da kyan hali wanda duk shine silan da yasa bai taba Lura da kyanta ba, tunda yake .
Idon Usman na kanta, “yanda take danna computer din kaman bata son dannawa, “lokaci d’aya ta tashi tare da mi’ka mishi hannu alama ya bata jakarta.
Mi’ka mata yayi inda ta ciro kud’i, ta biya tare da wurga ma Usman jakarta tayi waje
Binta yayi yana mamakin irin halinta, “ya rasa mai yasa take da hali daban dana iyayenta, “da yawa mutane na mamakin irin halinta, domin iyayenta sam ba haka suke ba, suna girmama kowa, tare da sanin darajan d’an Adam.
Amma ita Amal indai Kaga tana maka dariya ko kulaka, “Toh lallai kaima dan wani ne, ko y’ar wani.
Koda ya k’arasa bud’e Mata kofar motar yayi Wanda ya ganta a tsaye, da alama dama shi take jira yazo ya bud’e Mata kofar
Bayan ya bud’e ta shiga tare dajan wani gajeran tsaki
Bayan ta shiga Ya rufe kofar motar.
Usman tuk’i yake yana kallonta ta mirror, lallai Amal Tana dakyau, lokaci d’aya ya cire idonshi daka kan mirror din yaci gaba da tuk’i yana tunani…..
Mai yake damu nane?
Usman kai tsaye cikin gidansu Amal ya faka motar, “koda ya faka idonshi ya sauka akan Nata ta mirror itama lokacin akai Sa’a ta d’ago idonta
Wani uban harara ta sakar Mai, tare da fad’in “lafiya kake kallona? Kaman tsohon Maye.
Kufa naga alama talakawan nan Kun fiye kallon mutane, “ka wani sakar min ido kaman zaka cinye ni, Toh nafi karfinka wlh, wahallan mutum kawai, tare dajan tsaki tace fita ka bud’emin kofa jorr
Usman baice komai ba, sai fita da yayi ya bud’e Mata kofar, “domin daka yanzu yayi alkawarin zai maidata mahaukaciya ne In Tana Abu yabar biye mata, sai dai yaita manna mata hauka, “uhm Allah yasa ka iya hakurin dai
Bayan ya bud’e Mata kofar ta fito, “sannan ya rufe kofar,”kallonshi tayi k’asa da Sama riga ne da wando na wani yadi a jikinsa
Tace anjima by 6pm ka shirya cikin shiga Mai Kyau zaka fitar dani, “Ina nufin ban son kasa irin wannan kayan dake jikinka domin ban San driver d’ina yana dressing like a beggar, duk da dama u r a beggar din “sai kuma ta saki murmushi tare da fad’in Talaka bawan Mai kud’i, “Tana fad’in haka tayi gaba abunta
Usman yaji haushin magananta amma saiya basar, tunda ba dukanta zaiyi ba, dole Dai sai dai yayi hakuri.
Usman wajan masu gadin gidan ya nufa ya zauna inda suka fara fira, “d’aya daka cikin masu gadin yace kai Usman Wlh kana k’okari Sosai
Usman yace k’okarin me kuma?
Security din yace wajan tu’ka Amal mana, wlh bata da kirki ko kad’an batai halin iyayenta ba wlh yarinya bata ganin girman kowa hab…..
Usman ya dakatar dashi tare da fad’in ya isa haka, karka manta a karkashin su muke, bai kamata mu dinga gulmanta ba, kodan iyayenta ya kamata mu dinga hakuri
Security din yace hakane, gaskiya ka fad’a, “Allah ya bamu hakurin zama da ita tare da jurewa, “amma halinta sai ita Allah ya shiryata, ta gane Talaka shima mutum ne kaman kowa
usman ya amsa da Ameen tare da fad’in bari dai inje inyi Guga
Security din yace AI an kawo sabon Mai Guga, yanzu kana karkashin Amal ne, kaine driver d’inta, aikinka shine tu’kata
Usman shuru yayi yana nazari, “gaskiya baya tunanin zai jure, domin yasan duk yanda yakai da hakuri da kuma Kai zuciya nesa yasan Amal zata iya kureshi, “amma zai jaraba ya gani
Tun daka wannan ranan Usman ya zama shine driver Amal, babu wulakancin da baya gani, “babban abunda yake damunshi shine yanda yake yawan tunanin Amal, sannan ba kaman daba Wanda yanzu Idan tayi mishi Abu baya wani jin haushi Sosai, sai dai kawai ya bita da ido
Ita kuma ta gefen Amal babu abunda ta tsana kaman taga tana mishi abu yayi shuru yana kallonta
Shi usman baya jin komai game da ita, balle yace yana Sonta, sai dai abu d’aya da ya tabbata shine yanzu yana matukar jin tausayinta, domin irin rayuwar data d’aukar ma kanta abun a tausaya mata ne, gaba d’aya lamarinta babu Allah, “domin inda tasani da bata kyamaci Talaka ba, domin Allah ne yayi su, kuma shi talauci jarabawa ne, haka arziki shima jarabawa ne duka.
Story continues below

Amal ce cikin shiri yau zata Fara zuwa lecture domin tayi applying makaranta a Dubai bata samu ba, daka baya hjy Rabi ta sani, tama Amal ta tas, Wanda hakan yasa ta hakura tayi jamb inda ta sami admission a university of Abuja, ta samu political science.
Daka ita sai wata doguwar riga y’ar kanti sai karamin Gyale data yane kanta dashi
Kai tsaye waje ta fita inda ta iske Usman baya wajan motar “wani irin tsaki taja Mai sauti tare da fad’in wai Mai yasa Talaka yake da raini ne? Tafiya ta Fara har zuwa wajan gate inda ta bud’e gate din ta gansu zaune a waje suna fira shida masu gadin gidan
Security din suna ganin Amal suka tashi suna rusuna mata kaman kullum
Amal cikin fushi tace aikin da aka d’aukeku kenan koh? Wai Mai yasa ku talakawa kuke da iskanci ne? Daka yau kuje ku duka na sallameku matsiyata kawai.
Usman gaba yayi danshi ko a jikinshi
Amal tace heee mister driver come back
Zoka bud’emin kofa, ka kaini skul
Usman yace au ai naji kince kin koremu
Amal tace na koresu but banda Kai, ai kai ban so kayi gaba daka nan, nafi son ka dauwama a matsayin driver d’ina Mai min bauta
Usman baice komai ba, sai shiga da yayi, domin yasan koya tafi Mahaifinta zai kirashi,”kuma bazai iyayi mishi musu ba
Bud’e Mata kofar motar yayi ta shiga sannan ya rufe
Tada motar yayi ya fara horn “babu wanda ya bud’e domin tace ta Kori masu gadin, wanda suna waje suna jin ana horn suna tsoran su shigo ta musu wulakanci dan Haka suka k’i shiga
Amal tace ka fita ka bud’e gate din mana
Usman yace sorry madam, aikina shine driving ba gadi ba
Amal tace kai har kana da zabi ne? Karka manta kai Talaka ne, baka da wani zabi face kayi abunda millionaire Amal tace, kana Talaka badan kowa ba ina fad’a kana fad’a
Usman yace na yarda ni Talaka ne, kaman yanda kike fad’a, “amma ina son kisan wani abu, shi Talaka da kike rainawa yana da rana, domin kuwa gashi yanzu kina gani, abubuwa da yawa bakya yima kanki saishi Talakan yayi miki shi ku….
Tace enough how dare you, ina fad’a kana fad’a? “murmushi tayi na bacin rai tare da fad’in tsiyar ku kenan, girman kai da raina wanda kuke ma aiki, kalleka ka kalleni, kai ka isa in fad’a ka fad’a, har ince ga abunda nakeso kayi ka tsaya min musu, Mai kake tak’ama dashi ne?
Yace Allah, dashi nake tak’ama, kuma shine mai taimakona
Amal tace nonsense, go and open the gate right now,”oh na manta he is an illiterate
Usman murmushi kawai yayi, tare da fita ya bud’e gate din, “security din data Kora suna wajan, “Usman cikin tausayi ya kallesu, sannan ya wuce ya fito da motar ya fita danya rufe gate din
Masu gadin suka je wajan motar suna bama Amal hakuri, akan ta yafe musu su dawo bakin aikinsu
Amal ta sauke glass din motar tare da fad’in idan na dawo na ganku a nan sai nasa an rufeku, marasa hankali kawai, tana fad’in haka ta d’age glass din motar
Shiko Usman Bayan ya rufe gate din, yazo yana ce musu, suyi hakuri su tafi, domin bata san Allah ba, “yana fad’in haka ya shiga cikin motar
Yana shiga yaja motar suka nufi university of Abuja, “Bayan ya faka a parking space, bai fito ba itama bata fita ba
Ganin zai bata mata lokaci yasa tace Wai Mai yake damunka ne? Mai yasa baka da tunani ne kai.
Bai kulata ba, balle ya bata amsa
Hakan da yayi mata yasa ranta ya k’ara baci tare da fad’in “what did he mean?
Tace ka fita ka bud’emin kofa
Baice mata komai ba, sai fita da yayi ya bud’e Mata kofar, ta fito”tare da fad’in beggar tayi gaba
Usman da ido ya bita, “shi harga Allah ya gaji da wannan cin zarafin,… Lokaci d’aya kuma yayi murmushi tare da tunawa da abunda mamanshi ta fad’a mishi na cewa Mai nema sai yayi hakuri, “Kai ya d’aga tare da fad’in tabbas hakane duk mai nema sai yayi hakuri Allah ka bani ikon hakuri, Hmmm ace mutum ya Gama karatu amma aiki ya gagara, “Allah dai ya kyauta.
Koda Amal ta nufi inda za suyi lecture, zama tayi tana kallon sauran y’an class din nasu, gaba d’aya kallon raini take musu, lokaci d’aya taja tsaki, tare da fad’in Mum ta cuceni, ta rasa inda zata ce inyi karatu sai cikin wa in nan y’ay’an matsiyata din.
Suna nan zaune wani guy ya tashi daka ganinshi shima masu kud’i ne, ya fara magana kaman haka “hey guys am new hare plz ya kamata muyi exchanging numbers so dat koda muna da lecture a dinga fad’ama juna.
Duka sukace eh hakane, wani ya tashi yace nine class Rep, idan akwai lecture nike fad’ama kowa, so zaka iya bada number din’ka, ko kuma ga tawa wanda basu dashi,dan baga akwai sabbin zuwa, nan ya fad’i number d’inshi
Amal tashi tayi ta bashi card d’inta, “tare da fad’in Akwai lecture ne yanzu?
Yace a’a sai 4, “bata ko bashi amsa ba ta fita, dan bata ga amfanin zaman ba, tunda yanzu wajan 12 ne akwai sauran lokaci
Fita tayi tana tafiya, kawai saiga wani mutum kanshi d’auke da tire din gwaiba, ya bita da ido har yayi tuntube ya zubar da gwaiba din, yana nuna Amal tare da fad’in Fatima, Fatima dama baki mutu ba, Fatima dama kina Raye sai kuma ya nufeta yana k’okarin taba ta…..
Amal da sauri tayi baya tare da fad’in karka kuskura ka tabani da wannan kazamin jikin naka..
Yace Fatima nine fah mahaifinki, Mai yasa kika gujemu kikai mutuwar k’arya, gaki kuma a nan, cikin shiga Mai Kyau sai kuma kuka yaci karfinshi.
Amal kallon mamaki take mishi tare da takaicin ya kirata da y’arshi, kallon shi yayi tun daka sama har k’asa, riga da wando ne na shadda, duk sun kod’e ,takalminshi ya sid’e “tace kana da hankali kuwa? Inaga rudun tsufa ya kamaka
Yace Fatima n….
Ta daka mishi tsawa tare da fad’in uban Fatima ne, karka k’ara canza min suna, matsiyacin tsoho kawai, duk hankalin mutane ya dawo kansu
Amal tace Idan maula zakayi ka fad’amin basai kazo kayi wannan drama d’inba.
Tana k’okarin tayi gaba”ya k’ara binta yana fad’in Fatima wlh nine mahaifinki, wai kin manta nine…..
Amal tsayawa tayi tana k’okarin ta d’aga hannunta ta mareshi, “Usman dake kallonsu yazo da sauri ya ri’ke hannunta, tare da janta yayi Mota da ita, tana fusge fusge
Shiko tsohon ganin irin motar da aka saka Amal wacce yake kira da Fatima yasashi mamaki, tare da tsayawa kallon ikon Allah, yau wata biyar da rasuwar y’arshi, sai kuma gashi ya ganta a nan…… Toh fah mai ke faruwa? Muje zuwa
Amal fad’i take mahaukacin tsoho, wanda bai San abunda yakeyi ba, tsiyar Talaka kenan, zafin talauci ya sashi hauka, zai zo Ya dinga kirana da y’arsa, waima nice Fatima, “ta Ina na zama y’arsa matsiyaci Talaka dashi.
Usman dai baice komai ba, sai tukin da yakeyi, amma shima Abun ya bashi mamaki, taya zai kira Amal da Fatima harya dinga kiranta da y’arsa? “duk yanda akayi kawai tsufa ne ko kuma kama ce sukeyi da y’ar tasa, wacce yake cewa ta rasu, “Toh In banda abunshi daka ganin mutum saiya Fara kira da Fatima, kuma Bayan yace ita Fatima din ta rasu….
Amal ce ta katse mishi tunani tare da fad’in waya baka daman taba min jiki, da wannan kazamin jikin naka?
Wai Mai yasa kake k’okarin son tabani ako da yaushe? Mai yasa kake son goga min tsiya da talauci? Wannan ya zama na karshe da zaka K’ara tabamin jiki k’azami kawai, Dallah kayi sauri ka kaini gida inje in wanke wannan daudar takaicin daka Shafamin, in banda warin tsiya babu abunda jikina yakeyi
Lokaci d’aya kuma taja tsaki tare da fad’in shi dama Talaka a kullum burinshi yaga ya goga ma Mai arziki tsiya, gaba d’aya warin jikinsa nake Kazami tsaki ta kuma ja
Shidai Usman bai tanka mata ba, domin yanzu ya daina biyema haukarta Dan hauka takeyi domin Mai hankali bazai aikata abunda takeyi ba a cewar shi
Amal sai tsaki take saki tana fad’in aikin banza dana hofi, ko a gidan ubansa na zama Fatima oho, dole Dad yasa a kama wannan matsiyacin tsohon, inma Dad bai d’auki mataki ba dole ni in d’auka “akai bazan fad’ama Dad ba saiya dawo daka tafiyar da yayi amma nida kaina zan fara d’aukan mataki
Bayan sun isa Gida Kai tsaye gefenta ta nufa inda ta fad’a toilet danta wanke tsiyar da take fad’i Usman ya goga mata
Wanka ta shiga ta dad’e a toilet “Tana wanke jikinta cikin kyama da tsanar Usman yanda harya taba mata jiki yana Talaka, Talakan ma Mai mata bauta Dan aikinta, “lokaci d’aya taja tsaki tare da fad’in zan d’auki mataki akanshi cikin gaggawa shima idan ya k’ara yunkurin tabani, matsiyaci
Bayan ta fito ta d’auko mai d’inta ta Fara shafawa tare da shafa turare oil a jikinta, sannan ta d’auko body spray shima ta feshe jikinta dashi, “Fara shinshina jikinta ta farayi “lokaci d’aya taja tsaki tare da fad’in kai har yanzu ina warin jikinshi Kazami
Turaren ta k’ara fesawa amma daka ta shinshina jikinta sai tace Tana warin tsiyar Usman, dole toilet ta kara komawa dan tayi wanka, ” ta k’ara daukan lokaci a toilet din Kafin ta fito ta k’ara shafe jikinta da turare bayan tasa Mai
Wata riga tasa wanda ya tsaya mata dai dai Giwa, ko d’ankwali babu akanta ta nufi part d’in Mum dinta
Bayan ta shiga hjy Rabi tace Amal ina hanaki irin wannan shigar karki manta akwai maza masu mana aiki a cikin gidan nan
Tace kai mum miye dan nasa wannan kayan?
Hjy Rabi tace wato ke baki son gaskiya koh? Wlh Amal zanyi matukar saba miki in kina irin wannan banzar shigar
Amal kuka ta Fara tana fad’in waini Mai yasa bakya sona mum? “Dad ne kad’ai yake son abunda nake so yanzu mai shigata tayi
Hjy Rabi ganin tana kuka Kun San y’a da uwa, saita Fara Mata magana cikin sigar rarrashi, “a’a Amal taya uwa zata haifi y’a da cikinta ace bata Sonta? A ina kika taba ganin anyi haka? “kawai Amal irin abubuwan da kikeyi shine bana so, karki manta kefa mace ce, bai kamata kina irin abunda kikeyi ba”sannan irin shigar da kikeyi karki manta masu gadi naza ne, driver d’inki namiji ne, haka masu ba flower ruwa maza ne, Gamai Guga shima na miji ne, kuma duka babu muharramanki a ciki, Kinga bai dace kina irin wannan shigan ba ko kad’an
Story continues below

Amal cikin kuka tace Mum nifa yarinya ce.
Mum ta girgiza kai tare da fad’in “abunda yake had’ani dake kenan taurin kai,”ke gaba d’aya ba’a gaya miki magana ki d’auka sai kiyi tayi, “ni Kinga tashi kibar min d’aki
Amal tace Mum.
Hjy Rabi tace miye cikin fad’a
Tace Mum ni y’arki ce???
Hjy Rabi kallon mamaki tama Amal, taga yanda Amal din ke kallonta tana bukatar ta bata amsa, “Hjy Rabi tace wannan wace irin tambaya ce Amal?
Amal tace Mum kina da wasu y’an uwa talakawa ko kuma Dad yana da dangi talakawa?
Hjy Rabi tace Wai Amal Mai yasa kike irin wannan maganan ne?
Tace mum kiban amsa dan Allah
Hjy Rabi tace ai duk kud’in mutum baya rasa y’an uwa masu kud’i da Talaka
Amal shuru tayi tana tunani “Toh kodai wannan tsohon y’an uwan Dad ne kona mum…
Hjy Rabi ce ta katse Amal da fad’in gaba d’aya kin San yan uwana, kin kuma San na Dad d’inki “so Mai yasa kike irin wannan tambayar Amal
Amal tace Mum yau a skul…. Sai kuma tayi shuru ba tare data fad’i abunda tayi Niya ba
Hjy Rabi tace inaji Amal maiya faru a skul din? Fad’amin maiya faru? Cikin damuwa hjy Rabi ke tambayan Amal akan ta fad’a mata maiya faru
Amal tace Mum a duniya za’a iya samun Mai kama da wani?
Hjy Rabi dai gabA d’aya Amal nason caza mata kwakwalwa, Dan haka da sauri tace eh Amal ana samun Mai kama da mutum kuma Koba Dan uwanka ba
Amal tace Mum yau a skul wani matsiyacin tsoho Mai saida Gwaiba yazo yana cewa ni y’arsa ce sunana Fatima, wai na rasu gashi ya ganni a nan, “gaba d’aya abunda ya faru Amal ta fad’ama hjy Rabi
Salati hjy Rabi ta saki tare da fad’in wannan wani mutum ne haka? Na shiga uku amma hankalinsa d’aya kuwa? Nice na haifeki da cikina ta Ina kika zama y’arsa!?
Wannan ba k’aramin Abu bane, Aikam dole in fad’ama Dad d’inki a dau mataki
Amal tace a’a Mum kin San hankalin Dad zai tashi ki bari ya dawo Gida, sai a fad’a mishi, “amma Kafin nan nida kaina zan d’auki mataki.
Hjy Rabi tace kodai barawon mutane ne dai? Amma akan wani dalili zai kiraki da y’arsa
Amal tace Mum nifa inaga kaman talauci da tsiya yasa ya fara rudewa har baya iya gane mutane
Hjy Rabi tace iko Allah, tare da tashi tace bari inje in dawo yanzu
Kai tsaye hjy Rabi waje ta fita”koda Ta fita Usman ta kira tace ya kaita makarantar su amal tare da tambayar shi akan maiya faru?
Nan ya bata labarin abunda ya faru, gaba d’aya Hjy Rabi mamaki take, lokaci d’aya ta d’auki wayarta dake hannunta ta kira commissioner of police ta fad’a mishi abunda ke faruwa tare da fad’in bata son mijinta ya Sani saiya dawo, “amma ina bukatar ka turomin mutananka domin a Kama mutumin a tuhumeshi
Koda Hjy Rabi suka k’arasa har police din sun rigasu xuwa amma wani abun mamaki an nemi tsohon nan an rasa “sai kace Aljani har mutane suka tambaya amma babu wanda ya ganshi, “Wanda hakan yasa dole suka koma
Gaba d’aya ranan hjy Rabi ta kasa sukuni haka kawai taji abun ya tsaya mata a rai, ita tasan koda ta haifi Amal Tana cikin hayyacinta harta ri’ke amal din a hannu, balle tace ba y’arta bace, toh mai wannan mutumin yake nufi?
Washe gari Amal Nada lecture karfe 4 Dan haka ta fito cikin wata ba’kar jallabiya yayi mata kyau sai tayi kaman balarabiya
Kai tsaye wajan motarta ta nufa inda Usman ya bud’e Mata kofa ta shiga, “sannan shima ya shiga ya tada motar
Idonshi nakan Amal ta cikin glass, cikin ranshi yake fad’in idan tayi shigar mutunci tafi kyau, “gashi tafi son saka kaya k’anana
Koda suka k’arasa bud’e Mata kofar yayi inda ta Shiga lecture haka harta gama ta fito bata ga wannan tsohon ba. Kaman yanda tayi niyar Allah yasa ta ganshi tamai tujara ta nuna mishi ita sunanta millionaire Amal ba Fatima y’arsa matsiyaci Talaka ba, “Aman sai yaci Sa’a bata ganshi ba
Dan haka Mota ta nufa inda ta shiga Usman yaja suka koma Gida,
Yanzu wajan wata d’aya kenan Amal da had’uwa da wannan tsohon har yau bata k’ara ganinsa ba, “kullum hjy Rabi na tambaya kota ganshi amma amal tace bata ganshi ba
Wannan ne yasa hjy Rabi fadin hala ma mahaukaci ne, “tare da banzatar da maganan
Yau Dad din Amal ya dawo gaba d’aya gidan A kacame yake domin dawowan Mai gidan
Amal tayi murnan dawowan Dad d’in Nata, wanda take ganin duk duniya shine yafi Sonta da gaskiya
Gaba d’aya Hjy Rabi ita ta shafa’a da batun wannan tsohon ko magana bata ma mijinta ba.
Yau karfe hud’u dai dai saiga Amal cikin shiri tasa riga da wando tare da yafa wani k’aramin gyale akanta, “tsayawa tayi wajan motarta, “USMAN dake zaune yana ganinta ya gane fita zatayi shi take jira yazo ya bud’e Mata kofar, “Kai ya girgiza tare da fad’in mai hali baya taba canza halinshi.
Bud’e Mata kofar yayi ta shiga sannan ya rufe
Kai tsaye shima shiga yayi ya tada motar saida Ya fita suka hau kan titi yace ina zamu madam??
Tace kaini super market mafi kusa danan
Bai kuma cewa komai ba, sai super market d’in da suka nufa inda yakai Amal din
Bayan ya bud’e Mata kofar ta fito ya rufe tare da binta a baya suka shiga
Wata yarinya ce ta hango Usman da sauri ta nufeshi tana fad’in “Usman kaine?
Usman murmushi yayi tare da fad’in nine Sadiya Ashe rai kanga rai? Tunda muka gama skul
Amal dake tsaye tana kallonsu domin ganin yanda Sadiya ta nufosu da sauri hakan yasa ta tsaya cak
Sadiya tace badai wannan matarka bace?
Amal ta saki tsaki tare da banka ma Sadiya tsaki tana fad’in Allah ya kyauta in auri matsiyaci sai dai ke da kike fama da tsiya aikin banza, “fita tayi daka super market d’in tana fad’in mahaukaciya, dan taga wannan Wawan Talakan take wani murna kaman taga president
Sadiya tace ikon Allah, wacece wannan kuma USMAN?
Usman yace madam d’ina ce, nine driver d’inta.
Sadiya tace driver kuma? Kai d’in? “USMAN duk k’okarin ka ka rasa aikin da zakayi sai driver kaine fa muke nace mawa ka koya mana Abu.
Usman yace ya zamuyi tunda haka Allah yaso, kin San yanzu k’asan ya lalace,samun aiki sai Dan wane da wane
Sadiya tace Allah ya kyauta bani number din’ka Zan kiraka muyi magana
Usman fad’a mata yayi tare da fad’in Bari inje Kar madam tayi fushi
Sadiya da ido tabi Usman cikin tausayi inka ganshi Zaka d’auka yana cin gashin kanshi domin yanda jikinshi yake ga Tsafta, ilimi kyau da kwarjini, “amma ya k’are a driver din wancan mara kunya din, kai Allah ya kyauta k’asar nan ta lalace, “irinsu Usman masu kwazo sune suka dace a basu aiki, amma yanzu sai dan wane da wane, wani baya zuwa office dinma sai karshen wata yaji alert, wani ma tun Kafin ya gama skul din ake bashi aiki, tunda dan wani ne
Koda usman ya fita a tsaye yaga madam din tashi tana cika Tana batsewa,bude mata kofar yayi ta shiga ciki
Sannan shima ya shiga ya tada yana k’okarin Jan motar Sadiya ta fito tana d’aga mishi hannu horn yayi mata sannan ya wuce
Amal tace Asara, an daiji kunya
Lokaci d’aya taja tsaki tare da fad’in daka yau Idan kana bakin aiki kasan a bakin aiki kake, “bana son raini karka kara aikata abunda ka aikata sannan ka fad’ama wancan mad yarinyar am not your wife “in banda ta raina ni Ina ni Ina Talaka irinka Aiko a mafarki, da yake she is mad har take tambaya koni matarka ce
Tir tir Amal ni? “tunda nake babu maganar da aka taba fad’amin naji na tsana kaina kaman wannan, har abada nafi karfin Talaka irinka aikin banza da hofi……..