KAWUNA
CHAPTER 4
Jiri jiri taji yana ɗibar ta da sauri ta dafe bangon falon idanuwanta na zubda kwalla, Sir Salman kuwa yaja dogon tsaki sa’annan ya kalli Surayyah ya ce “Surry muje ko?” daga haka ya sanƴa kansa yayi ficewar sa daga cikin falon, Suhailat kuwa kaɗan ya rage ba tayi kukan kura ta afka mai ba tsabagen yadda take jin zuciyarta na tafarfasa wannan kuma wani irin rayuwace? Shin waye wannan matar? Kafin ta kaiga bawa kanta amsa ta tsinkayo muryar Surayyah tana cewa “hummm Amaryar mu sannunki dafatan kin iso lfy, kuma kin shirya zaman haƙuri? Ke in banda abinki mai yakai ki auren Salman? Mutumin da bai taɓa son ki a rayuwarsa ba? Wacce yake son ma nasa an fasa auren nasu ballantana ke? Ai mugun cin sa’a ki kayi malamina ya ce dole babu wanda ya isa ya raba rabon dake tsakanin ki da Salman da kema mafarkinki bazai taɓa ka san cewa gsky ba, so never mind a haka ma zaki fi jin zafin auren sa, don mijinki a tafin hannuna yake sai yadda nayi da shi, Allah ya baki ikon jurewa na barki lfy”.
Surayyah ta ida maganarta haɗida juyawa Suhailat baya tana karkaɗa mazauninta tayi gaba abin ta, ta bar Suhailat a daskare kaman wacce a ka zarewa batir a jiki, “innalillahi wainna ilaihir rajiun” shine abin da bakin Suhailat ya shiga nanatawa sau babu adadi, kuka mai ban tausayi ta ɓarke da shi ta zube a ƙasan tiles ɗin falon tana faman nanata hasbunallahu walni’eemal wakil “hummm Suhailat ina jiye miki ranar nadama, ranar da zakiyi kuka da idanuwanki ranar da zakiyi kaicho da zaɓin ki, ina mai shawartar ki ƴata ki guji ranar nadama wanda nayi imani wannan ranar zata zo miki wallahil azeem Suhailat ranar nadama zai zo ya iske ki”. Maganar da Momy tayi mata jia ya shiga ruri a cikin kwakwalwarta, sunan Momy Suhailat ta shiga kwala kira dama abin da Momy ta hango mata kenan? dama duk daɗin da take ji na cewa ita ce silan raba auren Salman da Abee dama duk ba yinta bane yin karuwarsa ce? Innalillahi wainna ilaihir rajiun tun ba’a je da nisa ba rayuwarta ya fara sauyawa? Ko dai Allah na sakawa Abee ne? Ya za tayi da rayuwarta ita yanzun? Tana da kishin da wlh ba zata iya jure ganin Salman da wata ba shin mainene mafita a gare ta?”
***************************************
Ganin cewa shekarun Yape sun ja ta fara tsufa sosai, ya sa ta bawa Alhaji shawarar ya naimoma Diddi wacce zata riƙa kula da ita (nanny) dan ita yanzun ba lafiya ta cika ba, hakan ko a kayi Alhaji ya sa a ka naimawa ɗiyarsa mai kula da komai nata duk ƙarshen wata ana biyanta albashi, Nenne deejah ita ce wacce Yape ta sa a ka kawowa Diddi a matsayin mai kula da ita, mijinta da ƴaƴanta su 4 duk sun rasu sakamakon gobara da ya tashi da su da daddare ita Nenne a wannan lokacin tayi tafiya taje can ƙauyensu sai dawowa tayi ta iske abin da ya faru.
Bayan ankawo ta tafara kula da Haleematu sosai, shaƙuwa ta musamman ya shiga tsakanin Haleematu da Nenne deejah dan sosai Nenne ke gwadama Diddi so, sun yi matuƙar shaƙuwa Nenne ta dawowa Haleematu tamkar mahaifiyar da ta haifeta bata bar Haleematu tayi kukan rashin mahaifiya ba, har takai takawo ma Yape ta baiwa Alhaji shawarar a kan ya auri Nenne duba da irin shaƙuwar dake tsakaninta da ƴarsa, sam Alhaji yaƙi a cewar sa shida aure har abada.
***************************+***********
6years later (bayan shekaru 6)
Haleematu ta girma yanzun sosai dan a yanzun shekarunta 10 a duniya, Nennen ta kullum tana ƙara gwada mata so ga mahaifinta ma wanda ya ɗauki son duniya ya ɗaura mata sosai mutanen nan biyu ke gwadama Haleematu so, babu mai ƙaunar ganin hawayenta komai ta faɗa sai anyi mata shi babu abin da ta naima ta rasa a rayuwarta ba tasan mainene maraici ba sam don ita har yanzun ɗauka take Nenne ita ce mahaifiyarta.
Komai tare Nenne da Haleematu suke yi daidai da kwanciya yanzun tare suke yi da a BQ Nenne ke kwana amma ganin Haleematu itama can take satar jiki taje ta kwana yasa Alhaji cewa Nenne ta kwaso komai nata ta dawo cikin gida su riƙa kwana tare da Haleematun.
Story continues below

Sosai kowa ya matsama Alhaji a kan ya auri Nenne ita kaɗai zata iya kula masa da ƴarsa, saboda ƙaunar da Alhaji ke yiwa Haleematu yasa shi amincewa da auren Nenne dan yaga irin tsananin soyayyar da ƴarsa ke yiwa Nenne, saboda samuwar dawwamammiyar farin ciki a fuskar ƴarsa ya amince ya auri Nenne Deejah.
Bayan Auren Nenne da Alhaji da wata biyu Yape ta rasu.
*************************************
A haka Haleematu da Nenne da mahaifinta suka ci gaba da rayuwa, yanzu Haleematu na da shekaru 15 a duniya inda take ss1 a makaranta Islamiya kuwa ta jima da kammalawa.
Bayan shekaru 2
Hajia Nenne yanzun kam ta goge ta zama babbar mace kuɗi da hutu sun zauna mata sosai, yanzun kam sai abin da ta ce a ke yi a cikin gidan Alhaji komai ta ce shine final sosai Alhaji ya sake mata komi sai yadda ta ce a yi abu kawai a ke yi, a wannan tafiyar ne kuma ta sauyawa Haleematu ta juya mata baya dan yanzun taga ta zama gida kankat komai itace ontop, Haleematu ya zamana yanzun har tsoron haɗa ido da Hajia Nenne take sosai matar ke gwada mata ƙiyayya yanzun, mahaifinta ma yazun ɗar ɗar yake yi da ita, a duk lokacin da taje gun sa ta tambayesa ya bata abu sai ya koreta ya ce ” shikenan ke baki da aiki kullum sai dai a baki a baki abu? toh ki ɓace mun da gani mi hokkatama sisi’am (bazan baki sisi na ba)”
****************************************
Kan kace mai tuni Hajia Nenne ta soma gasama Haleematu aya da tsakuwa sosai take azabtar da Haleematu, a haka har Nenne tazo ta haɗe kanta da masu aikin gidan wajen ƙuntatawa Haleematu sosai suke azabtar da marainiyar Allah, wanke wanke girki aike wankin kaya duk Haleematu a ke sawa tayi mahaifinta kuwa yana gani amma bayida ikon hanawa sai ma dukanta da yake yi in an kawo masa ƙarar taƙi yin wani abu.
Mutum ɗaya ne kawai Hajia Nenne ta kasa samun kanshi, shine direban gidan shi kuma wannan direban yana da yaro ɗan saurayi yana karatu a jami’ar Kano (diploma) bayan ya gama karatunsa sai ya dawo gidan da mahaifinsa ke aiki, ganin yaron na zaman banza kawai babu aiki babu sana’a yasa Mahaifinsa roƙo masa Alhaji a kan ya bawaiwa ɗansa aiki tashin farko Alhaji ya ce ya riƙa tuƙa Haleematu yana kaita makaranta.
A haka Usman ya dawo direban Haleematu inda a kullum shike kaita makaranta ya kuma dawo da ita, har takai takawo shaƙuwa mai ƙarfi ya shiga tsakanin Haleematu da Usman duk abin da a ke aikata mata a cikin gidan su tana faɗi masa shi kuma yata bata haƙuri “Haleematu kiyi haƙuri duk abin da yayi farko zaiyi ƙarshe kinji sa’annan kita addu’a sosai Allah zai waiwayo gare ki in sha Allahu”
^**************************************
Hajia Nenne bayan ta mallaki gida ta ga komai yanzun a ƙarƙashin ta yake ta dawo da ƙannenta cikin gidan Faruk da Asma’u, inda a ka tura Asma’u England bayan ta kammala candy ɗin ta, shi kuma Faruk yana zuwa office tareda Alhaji.
Haleematu na Ss3 Hajia Nenne ta fitini kowa a kan lalle lalle sai ancire Haleematu a makaranta an mata aure, saboda Hajia Nenne ta fuskanci Haleematu da Usman direba sun faɗa soyayyar junansu, har sawa tayi Usmsn ya dawo direban ta, ta sauyawa Haleematu wani amma duk da haka soyayyar su sai abin da yayi gaba.
Ganin Haleematu na son ruguza mata shirine ya sata dagewa lalle lalle sai anma Haleematu aure kuma ƙaninta Faruk zata aura dan ya ce mata yana son Haleematu, Shi kuwa Faruk a wannan lokacin sai ya nuna ma Alhaji sosai yake ƙaunar Haleematu.
Alhaji kuwa sai yayi wa Faruk alƙawarin zai basa Haleematu saboda yana matuƙar ƙaunar Faruk, Hajia Nenne kuwa duk abin da ta ce shine daidai a gun sa.
Haleematu kuwa a wannan lokacin haƙurinta yakai maƙura ba zata iya jurewa ba, dan ita macece mai mugun sanƴin hali sosai take ƙaunar Usman dan haka ta kyanƙeshe ƙasa ta zauna ƙeƙam ta ce a tafau ita kam ba zata auri Faruk ba Usman zata aura, ƙannensa sosai suka zo suka basa haƙuri a kan ya bar Haleematu ta auri zaɓinta amma Alhaji yaƙi ya ce ” shi kam ya rigada ya gama magana kuma wannan alƙawari ne ko bayan ransa bai yarda Haleematu ta auri kowa ba face Faruk, In har kuma zasu ci gaba da shiga har karsa toh zai raba zumuncin dake tsakanin su babu shi babu su har abada, dole ne Haleematu ta auri Faruk”
Ita kuma Haleematu ganin harta Baffanninta ma Alhaji bai ji maganarsu ba ya sata lokaci ɗaya ta fetsare, duk ladabi da biyayyar da take yiwa mahaifinta ta ajiye shi gefe, mahaifinta na magana zata mayar masa a duk lokacin da ya ce mata “ke wallahi na rantse miki baza ki taɓa auren wannan yaron ba, Faruk zaki aura”. Taɓe baki Haleematu take yi sa’anan ta ce “Baba wallahi tallahi ko kashe ni zaka yi bazan auri Faruk ba Usman zan aura wallahil azeem” daga haka take miƙewa tayi tafiyar ta Hajia Nenne tayi ta zaginta ita kuwa ko a jikinta.
Ana cikin wannan hargitsin mahaifin Usman ya rasu inda ko kafin mutuwarsa ya roƙi ɗansa a kan ya rabu da Haleematu in har yana son ya ci gaba da zama yana aiki a cikin gidan Alhaji. Bayan mahaifin Usman ya rasu sai ya zamana ba shi da kowa sai Haleematu ita kaɗai yake kallo yaji daɗi, ita kuma ganin halinda Usman ke ciki ita ce kaɗai yake gani yaji dama dama a cikin zuciyarsa ya sata kuma rantsewa wallahi Usman in sha Allah shine mijin aurenta. Wannan shine dalilin guduwan Haleematu da Usman inda suka je wajen ƙannen mahaifin Haleematu suka wakilci auren su ita da Usman a ka ɗaura musu aure.
Bayan an ɗaura auren suka dawo gidan mahaifin Haleematu shi kuwa tuni labarin auren da ƙannensa suka ɗaurawa ƴarsa ya dawo kunnen sa.
“Ƙannena su suka ɗaura miki aure, amma ki sani daga yau bani bake har abada diga rana irin tayau kada ki ƙara kirana da sunana a matsayin ubanki, ke kaɗai ce kwaina a duniya toh a yau na sallamawa duniya ke, kada ki kuskura ki sake takowa inda na ke, In har kina son farin cikina kuma kina so In ci gaba da rayuwa toh shine kiyi nesa dani saboda idan har ina ganin ki ina jin wani irin baƙin ciki a cikin zuciyata”
ALHAJI ya nisa kafin ya ci gaba da cewa “ina ma haka Allah ya barni a duniya ban taɓa haihuwa ba, da In haifi ƴa irin ki wacce bata san darajan mahaifinta ba, Allah ngde ma daka ɗauki ran Faɗi bata ga irin yarinƴar data baro a duniya ba, ki fita ki barmun gida keda talakan mijinki”
Murmushin daya fi kuka ciwo Haleematu tayi ba tareda ta ce uffan ba ta waiwayo ta kalli Hajia Nenne wacce ke binta da kallon tsana ɓangare guda kuma tana jin daɗin korar da Alhaji yayi wa Haleematun, murmushi ta sakin ma Nennen sa’anan ta juya ta kama hannun mijinta wanda sam baiji daɗin abin da mahaifin Haleematu ya aikatawa ƴarsa ba ai hannunka bazai ruɓe ka yanke ka zubar ba.
Barin gidan suka yi dan sanin inda dare yayi musu a tafiyar su ne suka ga alamun ana farautar rayuwarsu kamar aiko da mutane a kayi don a kashe su. Haleematu tayi imani da cewa Hajia Nenne ita ce ta aiko musu wa’inan mutanen don a kashe ta yadda zata mallaki komai na dukiyar mahaifinta.
Ƙannen Mahaifinta su suka taimaka musu suka basu kuɗi da tallafi suka roƙesu da suyi nesa da garin Adamawa don Hajia Nenne baza ta taɓa barin su susha iskan duniya lfy ba.
Wannan shine asalin barowar Haleematu daga ahalinta suka yada zango itada mijinta a garin Kano a cikin wannan unguwar da muke cikinta har yau *janbulo*.
**************************************
Dogon lumfashi Mancy ta sauke sa’anan ta kallo ƴaƴanta wa’inda take hango tsananin tausayinta shimfiɗe a kwayar idanuwansu, murmushi tayi ta ce ” Abee wannan shine tahirina, kuma karki yi tunanin wai cewa tunda shekaru sun ja yanzun Mahaifina yana naimana a’a har rana irin tayau ya sallamawa duniya ni ya ce wa duniya ƴarsa ta mutu ba shida ƴa yanzun Faruk da Asma’u sune ƴaƴansa Asma’u har yanzun ba tayi aure ba duk da ta girmeni Faruk ma baiyi aure ba suna can suna ɓarnar dukiya son ransu dan Alhaji ya sakin masu komai da komai, don haka Abee wannan lamarin ba abu bane mai sauƙi.
Dogon lumfashi Abee ta sauke tausayin iyayenta musamman Mancy ya gama mamaye ta, shin Hajia Nenne wacce irin macece mai nene ribarta na aikatawa marainiyar Allah haka? lumfashi ta sake saukewa kafin ta ce…….
Numfashi ta sake saukewa kafin ta ce ” Mancy zan miki wani alƙawari”
Murmushi Mancy tayi dan ko ba’a faɗi mata ba ta san mai Abee ke shirin faɗi mata a matsayin alƙawarin, numfashi Mancy ta sauke sa’anan ta ce ” toum Abeedah ina jin ki”.
Abee ta ce ” Mancy a yau ni Abeedah na yi miki alƙawarin maido da farin cikin ki, kaka sai ya amsheki da hannunsa sa’anan sai ya wulaƙanta Hajia Nenne, rayuwarta zai tagayyara in har ina numfashi sai na cika miki wannan alƙawarin.”
Daga haka Abee ta miƙe da saurinta ta bar falon ta koma ɗakin su, dan ranta na wani kalan azalzalanta, ta tsani mutane masu hali irin na Hajia Nenne ji take kaman tayi fiffike ta dira a gaban Nenne a daidai wannan lokacin da na lahira sai ya fita jin daɗi.
Numfashi Mancy ta ƙara saukewa kafin ta ce ” Farhana miƙe ki ɗau Haris ki kai sa ɗaki”, Miƙewa Farhana tayi ta ɗau Haris tayi hanƴar ɗakin su da shi.
Abbi ya kallo Mancy ya ce ” Mancyn yara mai kike tunanin Abee ke shirin aikatawa ?”
Murmushin da ya daɗa fiddo da sirrin kyawunta tayi kafin ta kallo Abbi ta ce ” Ummm Abbin yara in dai har Abee ce abin da take shirin yi shine zuwa garin Adamawa, kuma nasan ba zata taɓa hutawa ba har sai ta dawo da martabar mahaifiyarta da mahaifinta a idon Kakan ta, wannan shine alƙawarin da zata cika”
Murmushi Abbi yayi ya ce ” Allah yayi mata jagora”
“AMEEN”
***************************************
Kwance take lamo a kan gadon ɗakin su, tunani ne tunkushe a cikin ƙwaƙwalwarta ta kama wacan ta warware wancan, ganin tunanin bazai amfana mata da komai ba ya sata miƙewa ta ɗauro alwala ta tada salla, ta jima tana roƙon ubangiji ya kawo mata mafita, dan tabbas tana so ta dawo da martabar iyayenta, tana so duniya su shaida su ɗin ma suna da asali.
Shiru tayi jin wani tunani ya kutso mata ” Hayfa? Tabbas haka ne Hayfah ta taɓa bani lbrn ƙanwar kakarta na aiki a gidan Alhaji Abubakar Gidado Dala, Alhamdulilah Allah na gode ma daka kawo min wannan tunanin”.
Abeee ta raya hakan a cikin zuciyarta, kwana tayi addu’a a kan Allah ya amshi addu’arta ta samu ta shiga gidan Alhaji Abubakar, don taci alwashin gyara harkar gidan.
Washe gari tana ta shi a bacci bayan ta kammala dukkannin abin da ya kamata, tayiwa iyayenta sallama ta kama hanƴar gidan su Hayfah, tana so taji labarin Alhj Abubakar tunda dai tasan Hayfah ba zata rasa sanin wasu abubuwa da suka danganci Alhjn ba tunda har ƙanwar kakarta na aiki a gidan.
************************************
“Abeedah Usman yau ke ce a gidan namu?”
Murmushi Abee tayi ta ce ” kai Hayfah Kabir da ban zuwa ne toh?”
“A’a baki zuwa zan iya ƙirga lokutan da kika zo gidanmu ma”.
Dariya dukkanin su sukayi a lokaci guda kafin Hayfa ta tsagaita da nata dariyan ta kafe ƙawarta da idanu na wasu sakanni har sai da Abee ta tsargu ta ce ” kallon fa namai?”
Fuskar tausayi Hayfa tayi kafin ta ce “kiyi haƙuri Abee komai mai wucewa ne, kiga yadda kika koɗe kika rame kin sa damuwa a ranki, shi kaɗai ne namiji a duniya? kina da kyawu sosai Abee irinki maza dubu ke so, ki godewa Allah wlh daya raba tarayyar ki da Sir Salman don na tabbata lamarin auren ku babu alkairi ne shiyasa Allah ya raba, matar mutum kabarin sa………..”
Story continues below

Hayfa bata ida maganarta ba ƙarar ringing tone ɗin wayarta ya ƙatseta, ɗaukar wayar tayi ta kara a kunnenta haɗida sallama, kallonta Abee tayi jin abin da Hayfar ke faɗi “innalillahi wainna ilaihir raji’un yanzun kina ina? Oh Kano zaki zo asibitin malam Aminu? Toh Allah ya kawo ki lafiya, sannu gwaggo kinji Allah ya ƙara lafiya”
Daga haka ta kashe wayar, Abee cikin mutuwar jiki ta ce “waye ba lafiya Hayfah?”
Dogon numfashi Hayfa taja kafin ta saki ta ce “kin san wannan ƙanwar kakar ta mu da na taɓa labarta miki tana aiki a gidan wannan hamshaqin mai kuɗin nan Alhj Gidado Dala? toh itace wai ba lafiya, har likitoci ma sun samata sharudɗa yanzu ma wai an turata tazo taga likita anan Aminu Kano.”
Abee ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi ta ce “toh yanzun wazai ci gaba da yi mata aikin a can?”
“Ban sani ba Abee”
Cikin zaƙuwa ganin tabbas Allah ya amsa addu’ar ta ta ce “ko dai zaki mun hanƴa ne inje inyi aiki a gidan?”
Da mamaki Hayfah ta kallo Abee kafin ta ce “kije kiyi aiki? Keko mai yayi miki zafi haka Abee?”. Shiru Abee tayi ta rasa maima za ta ce wa Hayfar can ta nisa ta ɗago ta kallo Hayfa ta ce “babu komai kawai dai inaso nayi nesa da gida ne, ina so na manta abin da Sir Salman da Suhailat suka aikata a gare ni”.
Dogon a jiyan zuciya Hayfah ta sauke ta ce “ƙawata haka ne, amma bari na ƙara kiran Gwaggo muji” gyaɗa mata kai tayi alamun amincewa, Hayfa ta ɗaga wayanta ta danna lambar Gwaggo bugu ɗaya biyu Gwaggo ta ɗaga bayan gajeruwar gaisuwa da suka sake yiwa juna Hayfah ta jefo wa Gwaggo tambaya “yanzun Gwaggo in kin dawo Kano waye zai ci gaba da yi miki aikin?” Gwaggo ta ce “eh dama kafin na tafi zan naima wacce zata maye gurbina, Hajiar gidan ta ce na kawo musu wacce zata gajeni, amma har yanzun ban samu ba dan Hajiar ta ce bata son Hausa Fulani yare take so kuma tsohuwa”
Kallon Abee Hayfa tayi kafin ta ce “toh Gwaggo ni ko akwai wata ƙawata da take so tayi aiki amma ina zuwa” daga haka Hayfah ta datse kiran ta kalli Abee ta ce “Abee kinji fa abin da ƴan gidan suka ce, kin san mai zamu ce?” ABEE ta girgiza kai alamun a’a, jinjina kai Hayfah tayi alamun toh ki saura “Muce masu ke yare ce, tabbas babu abin da zai hanani na taimake ki Abee, abin da za’a yi zan kira Gwaggo nace mata ke ba hausafulani ba ce ke inƴamura ce, dan haka zan ce Gwaggo ta taimaka ta sama miki aikin, karatu zaki ci gaba but kin tabbatar iyayen ki zasu barki?”
“Iyayena zasu bar ni Hayfah, dan sai da mukayi magana da su”
Hayfa ta ce “In sha allah zaki je gidan mutumin nan zaki yi aiki, zuciyar ki zata sake ki manta da Sir Salman, zaki je ki dawo lafiya in Allah ya yarda”
Daga haka Hayfah ta kira Gwaggo ta ce mata “kin ga Gwaggo wata ƙawata ce take naiman taimako tana so ta ci gaba da karatu toh basu da kuɗi amma ba bahaushiya ba ce inƴamura ce, mai zai hana ki sama mata aikin, amma fa ba tsohuwa ba ce” shiru Gwaggo tayi kafin ta ce “Toh shikenan Hayfatu zan gayawa Hajiar duk yadda a kayi zaki ji”
“Tohm Gwaggo mun gode” ta ce “ba komai Hayfah zuwa gobe zan kira na shaida miki yadda mukai da Itan in sha Allahu”.
Daga haka suka yanke kiran, Abee murna kaman zai kasheta ji take kamar ma har ta samu aikin, godiya take yiwa Ubangijin ta sosai wato haka Ubangiji yake tsarin sa In wani abun ya taso maka in dai ka miƙa masa kukan ka sai Allah ya kawo maka hanƴa cikin sauƙi, ita daa har bata san ma yadda zata samu taje gidan ba amma gashi Allah ya kawo mata lamarin cikin sauƙi.
***************+********+***********
Bayan kwana 3 Hayfah ta kirawo Abee ta shaida mata Gwaggo ta ce mata Hajiar ta yadda tazo ta kamawa Gwaggon aikin tunda ancewa Hajiar ita ba bahaushiya bace, Abee harda kukan murnar ta kamar tasa ruwa a ƙasa ta sha tsabagen daɗi, nan taje ta sanarwa iyayenta dukkanin abin da ya faru sosai Mancy da Abbi sukayi murna kowa sai yi mata fatan alkairi yake, Mancy ta ce “Abee kada ki kuskura daga zuwan ki wannan gidan ki nuna koke wacece” murmushi tayi ta ce ” Mancy ai canza kamanni zanyi” kallonta Mancy tayi ta ce “canza kamanni kuma?” “Eh Mancy shigar inƴamure zanyi dan Hajiar ta ce bata son Hausafulani suna yi mata aiki” jinjina kai Mancy tayi don tafi kowa sanin waye Hajia Nenne za ta iya yin fin haka ma ” Allah ya tsareki Abee daga dukkanin sharri” rungume Mancy Abee tayi cikin jin daɗi ta ce “Ameen Mancyn mu bari ma naje nafara zana billen” daga haka kowa ya ƙyalƙece da dariya, daga nan Abee ta soma zana ma kanta bilalluka intayi bille iyayenta da ƙannenta su kallo ta su tuntsure da dariya su ce “Abeee Wannan billen baiyi ba” ita kuwa Abee sai taita cuno baki waje ita fa a lale a dole tana so ta canzawa fuskarta kamanni yadda da sun ganta zasu ɗauka ita inƴamura ce ta gaske, su Mancy in tayi wani billen su ƙelƙece da dariya har da riƙe ciki, rabon da Abee tayi dariya ko taga dariya a fuskar Family ɗin ta har ta manta sai yau da suka tsinci kawu nan su cikin farin ciki.
Nan dai ta samu Mancy ta zana mata billen kowani ɓangare uku uku, Abbi ya ce uku ukun sun yi ta barshi, Mancy ta ce “Abee baki ganin cewa zasu gane zana billen nan kikayi?” Waro idanuwanta waje tayi kafin ta ce “wa! ai bazan taɓa bari su san cewa zanawa nayi yanzun haka fashin goshi zan yi”
***********************+*+************
Washegari Abee ta shirya cikin dressing ɗin ta na inƴamurai in ka ganta bazaka taɓa musawa a kan ita ba yare ba ce, bayan ta gama shirinta iyayenta suka yi mata fatan alkairi. Ta kama hanya bayan sunyi waya da Gwaggo a kan su haɗu a tasha, isar ta tashan suka gaisa da Gwaggo bayan tayi mata ya jiki ta amsa ta ce ” Abeedah ga yarinƴata Faɗime da ita zaku can adamawar ita tasan gidan Alhaji kuma baza ku wahala shiga gidan ba dan duka ma’aikatan gidan sun santa, Hajia ta riga da ta san da zuwan ki , Allah ya taimaka ya bada sa’a Abeedah Faɗime zata yi maki jagora in sha Allahu” murmushi Abee tayi ta ce “Ameen Ameen Gwaggo Nagode sosai Allah ya saka miki da aljanna ya ƙara miki lafiya” “Ameen ƴata”. Sallama Gwaggo tayi masu da fatan sauka lafiya Abee da Faɗime suka shiga Mota suka kama hanƴa, Abee na zaune shiru a cikin motar tana tuno halin rayuwa yau in ba dun ƙaddara ba bata taɓa
tsammanin cewa zatayi tattaki har garin Adamawa ba.
Wasa wasa sun kai kusan ki manin mintuna hamsin, zaune a cikin tashar mota amma babu Hamid babu dalilinsa, Abee kam har ta soma gyangyaɗi, Faɗime kuwa miƙewa tayi tana dube dube ko zata hango motarsa. Can kuwa ta hango motar Hamid na dunfarar inda suke a jiyan zuciya tayi tana mai hamdala don itama ta gaji sosai. Hasko fitilar motar da yayi daidai saitin fuskarta ya sa ta saurin buɗe idanuwanta lokaci guda kuma tana kare fuskanta da bayan hannunta, muryar Faɗime taji tana cewa “miƙe muje Abeedah, ga Hameed ɗin yazo” jin wanda zai zo ɗaukan su ne ya sata fasa masifar da tayi niyyar yiwa wanda ya haskota da wutan mota.
Miƙewa tayi a sukwane, tana mai gyara zaman ƙaton gilashin dake manne a saman fuskarta, lokaci guda kuma ta na mai daukan gana must go ɗin ta, a tare suka isa wajen motar. Hamid ya dube su ya ce
Story continues below

Horn ɗin da Hameed direba yayi ne ya dawo da ita daga duniyan tunanin da ta faɗa, a firgice ta ɗago da kanta ta sauke idanuwanta a kan tafkeken gate ɗin gidan Alhaji Abubakar gidado Dala, a.k.a mahaifin Mancy (Diddi), Kankan Abeedah da Farhana da Haris, surukin Usman Dambatta. “Innalilahi wa’inna ilaihir raji’un”, shine abin da bakin Abee ke furta wa zata iya rantse wa da kyawawan sunayen Allah, tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin gida mai shegen kyau irin wannan ba, ai wannan yafi ƙarfin mansion a cewar Abee lol.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
A hankali bayan wasu na’urori sun gama tantace motar, gate ɗin gidan ya soma buɗewa a hankali, baki, kunne, hanci, ido duka Abee ta wangale tana mai kiran sunayen Allah, harga Allah bata taɓa tsammanin cewa irin gidajen da take kallo a tv suna bayyanuwa a zahiri ba, in kana da kuɗi babu abin da ba zaka iya yi ba. Gaskiya wannan gidan zata iya kiran sa da aljannar duniya, wata kau wannan gida ya tafi da imaninta, anan gidan Mancyn ta dama ta taso? Anan tayi wayau? Ta girma? Kai! Tab a kan namiji ta gudu ta bar wannan gidan? Lalle ance so hana ganin laifi. Ita ma ai dalilin gorin da wanda take so ya mata ne ya sata zuwa naimo asalin ta, bata taɓa tsammanin cewa za ta yi tattaki tazo har wata ƙololuwar jihar Adamawa ba.
Bata gama shagala ba har sai da idanuwanta suka hasko mata cikin gidan, Ma sha Allah. Shine abin da bakinta ya riƙa furta wa, wajen parking lots Hameed ya wuce yayi parking, Abee kuwa ƙare ma wajajen kallo kawai take tayi motoci na ƙece raini shi take gani a fake a kowani lungu da saƙo na wajen da motar da suke ciki ta faka. Taɓa ta taji anyi da sauri ta waigo ta kallo Faɗime wacce ita ma Abeen take kallo.
” Ki fito muje mana Abeedah”, a hankali Abeedah ta sanƴa ƙafafuwanta waje ta fito, tana ƙare ma filin wajen kallo lalle lantarkin masu kuɗi ma daban yake dana talaka, irin fitulun dake fiddo da haske yana haskaka ko ina a cikin gidan, zaka rantse safiyar asuba ce yanzun a maimakon 11 na dare. Hannun Abee Faɗime taja don ta lura Abeee bata ma duniyar mutane. A hankali ta ce ” Faɗime gidan nan ako chau (akwai kyau),” murmushi tayi kafin ta ce “Wallahi kam, kaɗan ma kika gani ai, cikin gidan ya linka nan kyau”.
Chan gefen masu aiki suka wuce inda nan ma sai da Abee ta kama yin shahada, tsaruwan ginin ya tafi da ita, wannan ko kwatan haɗa shi da gidan su ai ba’a yi ba. Muryar wata mata da a ƙalla zata kai ki manin shekaru 55 a rayuwarta, ta katse tunanin Abee in da ta ce ” Sannun ku da hanƴa, yanzun isowar ku? Hajia Kam ta haura sama tun ɗazun, gobe dai ganin na ku zai yiwu ina gani”, matar ta ƙarasa maganar tana mai ƙarewa Abee kallo, Faɗime ta ce ” wallahi kuwa Auntin Aiki, Hanmeed ne bai samu yazo ɗau kan mu da wuri, shikenan toum Allah kaimu goben”. Abee kuwa ta ce ” ina wuni Aunti”,
“Lafiya lau, ya hanya!?” “Alhamdulillah”
“Ya sunan ki?” , Murmushi Abee tayi kafin ta ce “Abeedah nike” jinjina kai Auntin aiki tayi kafin ta ce zuje masauki su kwanta su huta.
Ɗaki guda Auntin Aiki, ta ware musu suka shiga ko wacce tayiwa kanta makwanci, katifar kawai ta isa ta sa mutum bacci bare kuma ACn dake ta kaɗo iska mai daɗi, Abinci suka ci kafin suka yiwa juna sai da safe.
Abee kuwa naiman baccin tayi a lokaci guda kuma ta rasa shi, tunani ne birjik a cikin zuciyarta.
” Yanzun da’ace kowa ya san ita jikar Alhaji Dala ne, da koda wasa Salman bazai fasa aure na ba kenan? Suhailat ma duk da mahaifinta mai kudi ne ita ma ba zata sama damar hana yuwar aure na da Salman ba? Ya Allahu, Ya waduud kai kaɗai ka san sirrin ɓoye, ya Allah kasa hakan shine mafi alkairi gare ni da iyayena duka, Ya Rabbi dan tsarkin kyawawan sunayenka, ka musanƴa mun wanda yafi Salman alkairi ya Rabbi ka cire mun son sa a cikin zuciyata, ka basu zaman lafiya da zuri’a ɗayaba shida ƙawata(Suhailat)”. Daga haka bacci ɓarawo ya sace ta.
Washe gari✍️
Washe gari da misalin ƙarfe 1:30pm, Auntin aiki ta aiko a kirawo mata Abee, Faɗime ta kallo Abee kafin ta ce ” Ina ganin Hajia ta fito kenan, Allah ɗora ki a kan ta Abeedah”, murmushin da yafi kuka ciwo Abee ta saki kafin ta ce “Ameen ya Rabbi”, daga haka ta sanƴa kanta ta fita a ɗakin. Bayan sun gaisa da Antin Aiki, tayi mata ya gajiyan hanƴa sa’anan ta ɗaura da cewa “Yauwa Hajiya ta aiko kiran ki, muje ko?”, gyaɗa kai Abeedah tayi, kafin ta juya tabi bayan Antin aiki don zuwa sashen Hajia Nenne. Sosai tsarin part ɗin Hajia ya birge Abee, komai yaji zamzam a farfajiyan sashen nata.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Da sallama ɗauke a bakunansu, suka ƙarasa shigowa cikin falon. Falon cike yake da samari da ƴammata da a ƙalla zasu kai kusan su 15, zaune a cikin falon Hajia Nenne, gaban su kuwa an cike shi da kayan ciye-ciye da shaye-shaye gefe guda kuma sautin kiɗa ne ke tashi yadda kasan gidan club, mamakin Abeee kuwa bai gama linkuwa ba har sai da idanuwanta suka sauka a kan matar gidan, Hajia Nenne. A hankali take saukowa daga matakalen benen dake a cikin falon, taci adonta cikin wani dakakkiyar leshi mai launin ruwan gwal, saman wuyanta kuwa manne yake da wani danƙareriyar sarƙan gwal, babbar macece mai cin zamaninta a yanzun kallo ɗaya tak zaka yiwa Hajia Nenne kasan cewa tana cikin daula, hutu da kwanciyar hankali sun gama ratsata ta ko’ina, macece doguwa mai ƙiban gaske, fatar jikinta babu abin da suke fitarwa sai sheƙi da kyalkyali mai ɗaukar ido. Ƙamshin turarenta da yayi azamar gauraye falon shi ya sanar da isowar ta, da sauri mutanen cikin falon suka shiga ƙimtsa kawunansu waje ɗaya, ɗaya bayan ɗaya suka riƙa gaisheta tana amsa musu cike da fara’a. Kallon Antin aiki tayi kafin ta ce ” muje ɗayan falon”, daga haka ta sanƴa kanta ta bar falon, samarin nan kuwa suka ci gaba da iface ifacen su, Abee tabi bayan Anti har suka isa cikin falon Hajia Nenne, ma sha Allah, Abee ta furta a ƙasan maƙoshinta.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Wuri suka samu suka zauna a ƙasa, sun kai kusan mintuna 15 a zaune a falon kafin Hajia Nenne ta a jiye danƙareriyar wayarta da suka shigo suka iske tana amfani da shi. Gyaran murya tayi kafin da sauri Anty ta ce “Barka da hutawa Hajia”, gyada kai kurum tayi kafin ta juyo tana ƙarewa Abee kallo wacce itama a lokacin ta gama gaidata, kallon Abee take sama da ƙasa kafin ta ce ” Sunanki?” Da sauri Abee ta ce “Abeedah Usman”,
” ke wace yare ce?”, Idon Abee a ƙasa ta ce
” Ni igbo ne”, gyaɗa kai Hajia tayi cike da gamsuwa don yarinƴar tayi kama da inƴamurai kam, ta ci gaba da cewa ” tohm, idan zaki mun aiki bana son sa ido. Kiyi abin da yake gabanki, sa’anan ki gama gabanki, idan kuma har kika ce zaki samun ido toh kam za kiji babu daɗi, kiyi rayuwarki irin ta ƴar aiki muma muyi tamu,” nan dai Hajia Nenne ta kafawa Abee dukkanin sharudɗan gidan da masu aiki ya kamata su sani da kuma wanda ya kamata su kiyaye. Jinjina kai kurum Abee tayi cike da taƙaicin Hajia Nenne, a zahiri kuwa murmusawa tayi kafin ta ce ” in sha Allah, zon keyaye Hajjia(zan kiyaye Hajia)”, jinjina kai tayi ta ce ” toh, aikin ki shine kula da sashen mijina ma’ana ke zaki riƙa kula da wasu abubuwa na sa, kama daga abincin sa ke zaki riƙa dafawa, na ganki dai haka kamar kina da tsafta. So mijina kuma abincin da ake dafa masa daban ne ba irin wanda a ke yiwa kowa ba ne,saboda yana da diabities mallitus type2, abincin da yake ci is different from others, list din abincin nasa yana kitchen ɗin zaki gansu. Yana da kyau ki tsaya ki gane irin abincin da zaki dinga kai mi shi, kin iya irin su tuwon alkama da su cheese etc. dai ko?”, Gyaɗa kai Abee tayi ta ce ” Eh in sha Allah babu matsala”,
Story continues below

” Zaki dinga gyara masa bedroom dinsa (ɗaki), amma sai in har bayanan ne zaki riƙa shiga kina gyara masa ɗakin, idan yana nan baki isa kije koda kusa da ƙofar ɗakin mai gidana ba, idan ya fita office zan baki makulli kije ki gyara mi shi ɗaki, a cikin mintuna ashirin ki gama ki fito. Abinci kuma girka wane kawai naki, da kuma kai ma sa shi a jere a dining table daga nan sai ki kama gabanki”.
Tirr ƙashi, Abee ta raya hakan a cikin zuciyarta, lallai ma Hajia Nenne a ka gyaran ɗakin mijinta nata ma masu aiki ne ke yi mata, zata iya dafa Alqur’ani ta kuma buga ƙirji ta ce tunda take a rayuwarta Mancy bata taɓa barin su wai su gyara ɗakin da mahaifinsu ke kwana ba, kullum Mancy ke gyarawa da kanta a cewar ta bata son ladan ya wuce ta, sa’annan ɗakin mijinta sirrinta ne. Hajia Nenne kuwa masu aiki kankat ma take sawa suna gyara ɗakin mijin nata, Allah kyauta ya shirya matan dake barin ƴaƴansu musamman ma masu aiki suna gyara uwar ɗakan mazajensu Allah yasa su gane ameen. (Wajen kwanan mijinki sirrinku ne). Numfashi Abee ta sauke ta ce ” toh Hajia in sha Allah zan ki yaye komi da komi sa’anan zaki sameni mai riƙe amana”, ” da ko kin kyautawa kan ki” Hajia Nenne ta faɗi. Daga haka suka miƙe suka bar sashen Hajia Nenne, Abeee kuwa tsananin mamakin su waye wa’innan ƙattunan samarin dake zaune baje baje suna jin daɗin rayuwarsu, su na hole ayar su yadda suke so a cikin falon, yaƙi barin ta tayi sukuni.
Washe gari Abee ta soma aikin ta, inda a ka bata uniform ɗin masu aiki wando baƙi da riga mai ratsin baƙi da fari, sosai uniform ɗin ya amsheta tayi kyau sosai a cikin kayan. Kitchen ɗin kakanta (Alhaji Abubakar) a kai mata iso. Auntin aiki ta nuna mata dukkanin abubuwan da ya kamata tayi da irin launin abincin da ya kamata yau ta yiwa Alhajin.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Tsarin gidan da kyawunsa yanzun kam sun daina baiwa Abee mamaki, don tabbas ta sani gidan kakanta ya haɗu iya haɗuwa an zuba basira iya basira wajen tsarin ginin gidan, misalin ƙarfe 7:30am dai dai ta kammala haɗa masa breakfast ɗin sa, sosai Abee ta zage damtse wajen tsarawa kakanta abincin sa, yau dai zai ci abincin jikarsa ƴarinƴar ƴarsa oh Allah na Mancy na, da sauri Abee ta ɗauki wayarta dake a kan kitchen island, lamban Mancy ta danna bugu ɗaya biyu Mancy ta ɗaga cike da zullumi Mancy ta ce ” Abeedah, kece? Ina kika shiga tun jia baki kira mu kin sanar mana ko kun isa lafiya ba, duk kin bar mu cikin zullumin tunanin halinda kike ciki, kun isa lafiya? Kina ina yanzun? Kun haɗu da Hajia Nenne? Alhajina fa shima kin gan sa?”
” Waiyooo Mancyna, wallahi nayi kewarki wayana tun jia a kashe ban da chaji kuma ban samu na jona ba sai yau, Mancy waiyoo Allah. Mancy ina ma kina kusa kiga abin da nake gani, wallahi Mancy gidan kakana yayi ta ko ina”, Abee ta ida maganarta cike da zumuɗi lokaci guda kuwa tana rage sautin muryarta don kar wani yazo wucewa ya jiyo muryarta sa’annan yaji tana hausa raɗau kamar jakar Kano, Mancy kuwa a gefe guda godiya tayiwa Ubangijinta da ya tsare mata ƴarta ya kai ta wannan gari lafiya, murmushi Mancy tayi ta ce
” Abeedah baki amsa min tambayata ba”
“Oh, Mancy yi haƙuri wallahi ba zaki gane yadda gidan Kaka ya tsaru ba ne, naga Hajia Nenne sa’annan yanzun haka na gama yiwa Kaka karin kumallo ne ma zan kai masa na a jiye” , murmushi ne ya sake kwacewa Mancy dadi na ratsa jikinta,
Story continues below

” Dagaske Abeen Abbin ta?”
Gyaɗa kai Abee tayi tamkar Mancy na kallon ta, daga nan kuwa ta soma labartawa Mancy dukkanin abin da ya faru daga zuwan ta cikin gidan har samarin da ta gani suna holewar su, har haɗuwar su da Hajia Nenne yadda sukai abin da suka tattauna d.s.s, duk Abee ta labartawa mahaifiyarta. Jim Mancy tayi na wasu sakanni kafin ta ce ” Abee ki riƙe kan ki gam, kar ki sake ki nuna ko ke wacece, ki riƙe maganganun da Nenne ta faɗi miki gam-gam, don kuwa sosai zata saka miki ido, don haka take yiwa kowani ma’aikacin da ke cikin gidan Abbana, idan har taga kina kiyaye dukkanin abin da ta hana ko ta ce kiyi toh sosai zaki zama ta hannun damarta ke kuwa a wannan lokacin ne zaki sama damar aikata abin da ya kawo ki cikin gidan, kin ji abin da na ce miki ko Abeedah?”, Gyaɗa kai Abee tayi cike da amincewa da maganganun mahaifiyarta sa’annan ta ce ” Mancy in sha Allah zan ɗau maganarki, zanyi duk yadda kika ce bazan taɓa baki kunƴa ba sai na dawo miki da farin cikin ki da yardar tsarkin mulkin Allah” . Murmushi sosai Mancy tayi, son ƴarta na daɗa mamaye ilahirin gaɓoɓin jikinta. A hankali ta ce ” Allah ya yiwa rayuwarki albarka Abeedah, Ubangiji kema ya maido miki farin cikin da kika rasa a baya, Rabbi ya musanƴa miki shi da wan da ya fisa alkairi. Nagode sosai ƴata mahaifiyarki na alfahari da ke, Allah ya yiwa rayukanku albarka da ke da ƴan uwanki”. Allah sarki Mancy, uwa tagari kenan a kaf rayuwarta ba zaka taɓa samun Mancy da wani mummunar hali ba, macece jajartacciya mai son addini da ƙaunar ƴaƴanta da mijinta ba zaka taɓa jin Mancy ta jefi ƴaƴanta da kalmomi munana ba kullum cikin yi musu addu’a da sanƴawa rayukansu albarka take, koda ko a ce sun yi mata mummunan laifi.
(Haka a ka san mahaifa mata su riƙa sanƴawa ƴaƴansu albarka su daina jefa ma su munmunar baki, bawai wa’inda zasu zage ƴaƴayansu uwaka, ubanki, banza shegia d.s.s wallahi bakin uwa dafi ne a kan ƴaƴanta koda ƴaƴanki sun miki abin da yayi mugun ɓata miki rai karki zagesu sanƴa musu albarka ko ki roƙa musu shiriya shine kawai gatan da zaki iya yi musu. Allah ya sa mu gane Ameen).
” AMEEN AMEEN, Mancy wallahi ina ƙaunarki a kullum ina yiwa Ubangijina godiya da ya mallakamun ke a matsayin mahaifiya, Mncy don Allah ki yafe mun dukkanin laifukan da na yi miki a baya kinji, ki gaida Abbina da Farhana da Harees wallahi nayi kewarku ina ƙaunarku sosai”, ba tare da Abee ta jira amsar da Mancy zata bata ba tayi saurin katse kiran saboda wani irin kuka da ya tokari maƙoshinta. Saita kanta tayi sosai kafin ta fito ta jerawa Alhaji abincin sa, da ta ga komi yayi dai dai yadda take so ta kama gabanta, ta wuce sashen su don karyawa tayi wanka ta ɗan samu tayi bacci tunda yau Sunday Alhaji bazai fita ba yau babu gyaran ɗaki kenan sai gobe.
4days letter (bayan kwana 4)
Rana tsaka Abee taga an soma gyaran gidan, yawan kaɗe-kaɗen da a ke sakewa a cikin gidan, da yawan samarin dake shigowa duk taga sun rage, samarin sun rage zuwa sosai. tunda ta zo gidan ta lura kullum cike yake da samari da ƴammata, su saki kiɗa a ta rawa ana shashewa kamar gidan ƴan iska suna gudanar da party(fati). Asma’u (wannan ƙanwar Nennen da tayi karatu a England, wacce Mancy tace har yau ba tayi aure ba fatan kun tunota?), Ita Asma’un samarin dake shigowa cikin gidan abokanta ne, ita da kanta take haɗa musu party a cikin gidan. Hajia Nenne kuwa ta ɗaure musu baya, abokan Faruq ma haka zasu cike cikin gidan a chashe yadda kasan gidan club, ƴan uwan Hajia Nenne ma yanzun sun cike gidan sai yadda suka yi kawai suka ce a ke yi a cikin gidan.
Asma’u babbar macece mai ji da kanta sosai, in har ka ganta ba zaka yarda cewa takai shekaru 40 ba, zaka fi tunanin bata fi 30 zuwa da uku ba, saboda yadda take shan gayu abinta, Asma’u ƴar gayu ce sosai ga kuɗi ga kyau ga kwanciyar hankali duka ta haɗa. Ƴar gayu ce na tashin hankali.(lol)
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Gyara sosai Abee taga anayi a gidan, abin ya mugun ɗaure mata kai ko wani abun za’ayi? Shine tambayar da Abee kewa zuciyarta, gefe guda kuwa ta lura da yadda Asma’u keta wani rawar kai da iyayi ko mai yasa take hakan? ohon mata. Yau ya kasance ranar Litinin (Monday) bayan Abee ta gama aikinta, ta dawo part ɗin su don yin wanka, girke girke da soye-soye taga ana tayi a babban kitchen ɗin gidan. Kodai baƙi za’ayi ne dama shi yasa a ke ta gyara-gyaran gidan? Abee ta tambayi zuciyarta. Da sauri ta ƙarasa cikin ɗakin su, ta iske Faɗime zaune tana cin shinkafa, da sauri Abee ta ƙaraso wajen ta sa’annan ta ce ” wai Faty baƙi za’ayi a cikin gidan ne?”, Murmushi Faɗime tayi kafin ta ce “ke kuwa baki san waye ke tafe cikin gidan nan ba?”, Girgiza kai Abee tayi alamun bata da masaniya, “lallai kam, an barki a baya, toh ki zuba ido kawai kiga mai zuwan, amma mutum ɗaya ne fa duk a ke ta yiwa wannan hidimar, ba kiga yau Alhaji ko aiki bai je ba? Ya tsaya ya tarbi abin son sa abin son kowa ma zan ce miki”, Faɗime ta ida maganarta haɗida miƙewa ta bar cikin ɗakin, ba tare da ta sake barin Abee ta kuma tambayar ta wani abin ba. Shiru Abee tayi tana nazarin baƙon da za’ayi ɗin don ta gani tun ana saura kwana 4 yazo a ke ta shirye-shiryen tarban sa, samarin da ke zuwa duk sun daina, shigar banza da su Asma’u da sauran ƴan uwan Hajia Nenne suke yi duk sun daina yi, kowa ya natsu kirip. Duk yadda za’ayi wannan baƙon yana da muhimmanci a cikin gidan nan ko dai ma wane ne zata zuba ido ta gani.
Da misalin ƙarfe 2pm daidai, motocin da suka je ɗaukar sa a airport suka soma kutso kai cikin harabar gidan, parking ko wacce mota tayi sa’annan wani body-guard yayi saurin azamar buɗe masa ƙofar mota, ƙafafuwansa ya soma fitarwa a hankali kafin daga bisani cikin nutsuwa ya fito cikin motar gaba ɗaya.
Sanƴe yake cikin wani Red suit, suit ɗin sosai ya amshe shi kasan cewar sa Farin mutum abu jaa na amsar fatarsu, yana da matsakaicin tsayi daidai da shi fari ne tas mai yawan gashin kai da ƙasumba(saje). Idanuwansa suna manne cikin wani ɓakin tabarau (spectacles), fuskarsa babu yabo babu fallasa iya kyau kam mutumin nan a jin farko ne, Allah yayi halitta a wannan wajen, kekkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa burin ko wata ƴa mace.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
A hankali bayan fitowar sa cikin motar, guards ɗin suka soma gaida shi cikin ladabi da biyayya. Hannunsa ya riƙa miƙa musu suna musabaha, daga ƙarshe yayi azamar haurawa ƙaramin matakalen bene dake a wajen(outside) farfajiyar gidan don sa da shi da part ɗin sa.
Asma’u ce ta fito daga sashenta, taci ado cikin wani ɗin kin riga da skirt sosai ya amsheta sai yalki take, da zuba ƙamshi.
” Hameed, kun iso ne?”
“Eh Hajia, Barkan ki dawar haka”, ba tare da ta amsa gaisuwarsa ba ta ce ” yana part ɗin Alhaji ne?”
“A’a Hajia yana na sa part ɗin”. Ba tare da ta sake cewa uffan ba ta juya tabar wajen, Hameed kuwa ya ɗan jaa guntun tsaki a hankali ya ce ” iska tana wahalar da mai kayan kara, fisabilillahi ina sugar mommy ina matashin saurayi?”.
” Ta jika ta sa a ka kore ka aiki babu ruwan Faɗime”, Faɗime wacce isowarta kenan ta mayar wa Hameed amsa. Murmushi yayi kafin ya ce ” Boss man, nanan kam kema kin san ba tada wannan authority ɗin dai ko?” Dariya Faɗime tayi don kaf masu aikin gidan nan babu wanda baiyi murnar dawowar Boss man ba, sosai suke cikin farin ciki da annashuwa yanzun suma za’a fara kallon su kamar mutanen gida, zasu sama ƴancin kansu na wasu ɗan lokaci(freedom).
” Allah yasa wannan karan yayi kusan shekara ɗaya kafin ya koma” Hameed ya ce, dariya sosai Faɗime tayi kafin ta ce ” taab kaima kasan hakan bazai taɓa kasan cewa ba, muddin Hajia Nenne tana numfashi a doran ƙasa kam” Faɗime ta ƙara sa maganarta kamar mai yin raɗa, gudun kar wani yaji abin da ta faɗi.
Abee kwata-kwata bata samu damar ganin wannan baƙon ba, dalili kuwa an hana su shigowa part ɗin yau gaba ɗaya, sai dai in zaka kai kayan abinci ko zaka je kwasan kwanuka, Abee kuwa tana cikin masu zuwa kwashe kwanuka don haka ba tayi wani yunƙurin sake shiga ɓangaren masu gidan ba. Faɗime ce ta kallo Abee wacce ke tsaye tana nazarin wasu abubuwa dake a cikin kitchen ɗin, ” Abeedah, kyabar wannan tunanin kizo muje kwaso kwanuka sun danna bell alamu sun gama, jira suke muje mu kwashe”, gyada kai kurum Abee tayi sa’annan tabi bayan Faɗime suka jero a tare don zuwa cikin gidan. Bayan sun kwashe kwanukan da’aka ɓata suka tattaro suka kai wajen wanke-wanke don a wanke su.
Hareeerah da Abeedah tsaye a cikin kitchen suna ɗan taɓa hira jefi jefi kafin lokacin ɗaura sanwar dare yayi su fara. Hajia Nenne kamar an jefo ta cikin kitchen ɗin suka jiyo muryarta tana faɗin ” yauwa dama ku nake naima”, maido da hankulansu gaba ɗaya suka yi wajen ta don jin mai ke tafe da ita, don Hajia Nenne bata cika shiga babban kitchen na gidan ba iya kaci ta bada umarni (command), da mamaki ko waccen su ke jiran ji daga bakinta. “yauwa dama ku biyu kuke girki, ke dake dafa mana, da ke mai girkawa Alhaji. Anjima tare daku za’aci abinci a babbar falo, yauwa ke Abeedah nasan baki san da dawowar Hammad ba, toh yana da ƙa’ida abincin da ake ci idan ya dawo a lissafe yake, saboda shi baya son cin abubuwa barkatai don kula da lafiyar kowa da kowa balance diet a ke yi a duk lokacin da ya dawo cikin gidan nan, abincin da za’a girka da safe daban, diet ɗin rana ma da za’aci daban na dare ma haka. In kun gama tare daku za’aci abinci don haka kuyi sauri na barku lafiya.” Daga haka Hajia ta juya tabar kitchen ɗin, Abee kuwa tsananin mamakin al’amarin ma ya kasa barin ta, waye shi? Yaron Hajia Nenne ne? Mai yasa yake da ka’ida? Mai yasa yake cin abinci tare da masu aiki? Mai yasa ya damu ta lafiyar kowa?. Duk wa’innan tambayoyin suke yawo a cikin kwakwalwarta, ta kasa sanin inda zata samo amsar su, Mancy bata sanƴo wannan Hammad ɗin acikin jerin sunayen ƴan gidan ba, ko dai shima ɗan uwan Hajia ne? Lura da yadda itama take kauɗi da zuwan nasa. “Wannan wani irin mutum ne?” Dariyar da Abee tajiyo Hareerah nayi ne ya sanƴata lura da a fili tayi zancen zucinta, tsayawa kallon Hareerah kawai Abee tayi kafin can ta tsinto muryar Hareerar tana faɗin
Story continues below

” Hammad Kenan, baka fara’a baka dariya amma zuciyarka akwai alheri da tarin haske a cikin ta, kin ga shi babu ruwan shi da nuna bambanci kowa a wurin sa duk ɗaya ne, bayi da dai fara’a bai da wasa kuma, baya sakin fuska samsam in kin ga haƙoran Hammad a waje yana murmusawa ko dariya toh ki tabbata yana tare da Alhaji ne shi kaɗai ke ganin fara’ar Hammad. Sa’annan duk yadda kike ko kallo baki ishe shi ba, kallo ɗaya yake miki na sunnah, saboda shi ustaz ne idan ya kalle ki sau ɗaya shima a ce by mistake bazai ƙara kallanki ba, kuma duk abin da ma’aikaci ya dafa toh tare da shi za’aci kuma a guri ɗaya, haka ƙa’idar sa yake.” Jin-jina kai sosai Abee tayi cike da mamakin wannan bawan Allah, zuciyarta na azalzalar son ganinsa da sanin waye shi?. Nisawa tayi kafin ta ce ” toh shi yaron mai gidan ne?” Murmushi Harirah tayi ta ce ” aa ɗan gidan ƙanin mai gidan ne, amma mai gidan ne ya raine shi a hannunsa ya taso, ya mai da shi kamar ɗan sa idan kika gan shi ma kamar sa ɗaya da Alhajin, ke bama zaki ce ba ɗan sa bane, ai shi mai gidan nan ma bai taɓa haihuwa ba!”. Sassauta murya sosai Harira tayi yadda babu mai iya jiyo abin da zata faɗi sai Abee, kafin ta ci gaba da cewa ” inɗan fesa miki, ance ya taɓa haihuwa amma dai baza’a ji mutuwar sarki a bakina ba, kin ga nayi shiru.” Ta ida maganarta haɗida ɗaukar tray ɗin da ke gabanta, Abee ji tayi gabanta ya faɗi maganar Harirah na ƙarshe ya ɓata mata rai, ya za’ayi a ce mutuminnan yana da ƴa harda jikoki amma ya shaidawa duniya wai bayi da shi?, Wani kalar zuciya gare shi da bata yafiya? A sannu zai gane gaskiya zai gane irin ramin da matarsa take haɗa masa. Dogon a jiyan zuciya Abee tayi kafin ta miƙe don su ɗaura abincin dare, zuciyarta cike da son ganin Hammad indai ya tabbata yaron ƙanin kakanta ne, kenan Hammad Baffanta ne? (Kawu), godiya ta shiga yiwa Ubangijinta cikin zuciyarta don koba komai Allah ya fara nuna mata danginta.
Misalin ƙarfe 7:30pm, suka kammala jera abinci a saman dining table, a gajiye suka koma sashen su don yin wanka kafin su je cin abincin. Abeedah kuwa fargaba ne duk yake ta ɗawainiya da ita musamman idan ta tuna yau fa zata ga kakanta mahaifin uwarta, tun zuwan ta cikin gidan bata taɓa samun damar ganin sa ba, wayarta dake maƙale a caji ta janƴo a hankali ta shiga naiman layin Mancy bugu ɗaya biyu Mancy ta ɗaga cikin sallama.
“Assalamu alaikum, Abeen Abbinta yakike ya hidima?”
“Umm Mancy wallhi inanan lafiya ƙalau, albishirin ki?”, Murmushi Mancy tayi ta ce “goro fari sol”,
“Kina ji Mancy?, Yau in sha Allah zan haɗu da kaka”, gaban Mancy ne ya yanke ya faɗi sosai take tsoron haɗuwar ɗiyarta da mahaifinta saboda tsananin kamannin da Abee keyi da ita, kallo ɗaya tak Alhaji zai mata ya hango tsananin kamannin da suke yi.
“Mancy kinyi shiru”, Abee ta katse mata tunaninta, “Abee wallahi jikina baya bani haɗuwar ki da Alhaji, mainene dalilin haɗuwar naku yau?”, Shiru Abee tayi kafin ta nisa ta ce ” Mancy wai kin manta na canzawa fuskata kamanni ne? Sai fa in har na sanƴa ruwa na wanke tabon ne za’a iya gane ni, don Allah ki kwantar da hankalinki mamana in sha Allah babu abin da zai sanƴa su gane ni”, nisawa Mancy tayi sai a yanzun ta tuna da canjin fuskar da Abeen tayi, murmushi tayi ta ce “Tohm Abee Allah tsareki ya kare ki ya baki nasara a dukkanin abin da kika sanƴa a gabanki”
“Ameen mamana addu’ar ki kawai a gare ni ya isheni kariya, amma Mancy waye Hammad?”
“Hammad kuma? !”, Mancy ta tambaya cikin mamaki, gyaɗa kai tayi tamkar Mancy na kallon ta kafin ta ce “Eh Mancy Ham……..
“Abeedah ki fito mutafi wallahi karki jamana fa”. Harirah da ke tsaye a bakin ƙofa tana jiran Abeen ta katseta daga maganarta. “Mancy zan kira ki anjima bye” da sauri ta ka she wayar ta fito, Suka jera da Harirah zuwa babban falon gidan.
Story continues below
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
A natse suka ƙarasa shigowa cikin falon, ni’emtacciyar sanƴin Ac da ƙamshin turaren wuta yayi azamar tarbar su. Tsit babu motsin da kake ji a cikin falon ban da ƙarar telebiji, shima muryar a hankali yake fita, Harirah ta kallo Abee wacce keta ƙarewa falon kallo ta ce ” muje mu jera abincin a dining kafin su iso ko?”, Gyaɗa kai kurum Abee tayi sa’annan suka wuce cikin kitchen suka soma ɗaukar kular abinci dake a jere a dining table dake a kitchen ɗin zuwa dining area na falo inda anan za’ayi dinner.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Bayan sun kammala shirya komai, Harirah ta danna wani ƙaramin remote kafin ta kallo Abee ta ce ” zasu ƙaraso yanzun”, Ita dai Abee na ta ido kawai , burin ta ɗaya tak shine ta sanƴa Hammad a kwayar idanuwanta tasan waye shi?? Mai yasa a ke martaba shi, a ke shakkar sa?, Tunaninta ne ya katse sakamakon shigowar Hajia Nenne, bayanta kuma Asma’u da Faruq da wasu matasan samari biyu da wata ƴar budurwa da ba zata wuce kimanin shekaru 17 a duniya ba, cikin ladabi Abee da Harirah suka shiga gaishe su, dukkanin su a daƙile suka riƙa amsawa kai kace ba halittar Allah bane ke gaida su ba. Musamman Abee data lura dukkanin su sai faman harararta suke dama fil’azal tun zuwan ta cikin gidan nan ta lura basa sonta kwata kwata musamman Asma’u, ba su bane a gabanta shi yasa abubuwan su bazai taɓa ɓata ranta ba infact an ce sai ka kula kashi yake ɗoyi sai ka kula karuwa take yanga a sannu dukkanin su zasu bar cikin gidan nan muddin Abeedah Usman Dambatta, tana raye. (Shine alqawarin da Abee ta ɗauka a cikin zuciyarta).
“Abeedah” Hajia Nenne ta katse tunaninta, da sauri ta amsa da na’am “ki kawo min ketchup da shi zan haɗa”, gyaɗa kai Abee tayi kafin tayi saurin juyawa tabar falon ta koma can babbar kitchen don dauko wa Hajia Ketchup data buƙata.
Cikin nutsuwarta ta ƙarasa shigowa cikin falon bakinta ɗauke da sallama, ɗago da kanta tayi a hankali idanuwanta babu inda suka sauka sai a kan fuskarsa yana zaune yana jiran Asma’u ta gama serving ɗin sa. Gabanta ne yayi wani kalan mummunan faɗuwa, a a jikinsa yaji tamkar ana kallon sa don haka ya ɗago da kansa, caraf suka haɗa ido, kallon juna suka yi na wasu sakanni kafin Hammad ya ɗauke sexy oily eyes ɗin sa a kanta ya sunkuyar da kansa daga haka bai ƙara koda ƙara kallon gefenta ba. Ita kuwa Abee bayan ta miƙawa Hajia ketchup ɗin ta sama guri kusa da Harirah ta zauna jikinta duk tana jin sa a takure, Sallaaman Alhaji ne ya ƙara katse mata tunaninta, a daidai wannan lokacin ji take kamar ta fashe da kuka tayi gudu ta rungume kakanta ta roƙe sa da ya yafewa Ummanta, ta faɗi masa itace babbar jikarsa amma bata da wannan damar sam an haneta shi a wannan lokacin amma ta sani komai yayi tsanani maganinsa Allah, a sannu komai zai daidai ta musu suma zasu sama farin ciki wata rana in sha ALLAH. Tsanannin kammanin Alhaji da Mancy har ya ɓaci Hammad da Mancy ma suna mutuwar kama zata iya rantsewa da Allah Hammad namijin Mancy ne Mancy kuma ta macen Hammad ne duba da tsanin kamannin dake tsakanin su har ya ɓaci. Gudun kar wani ya ɗagota ko Hajia ta tambayeta dalilin tsayawa kallon Alhaji da take yi ya sata saurin daukar plate tayi serving kanta dinner. Ita kam sai yau take ganin wani ikon Allah wai da dare ba za’aci abinci mai nauyi ba ganƴe a ke ci (vegetables), shi kam Hammad ɗin nan sai ka ce ba rainon Nigeria ba? Yo toh ita a ganin ta ƴan Nigeria basu wani cika bin balance diet ba duk abin da suka samu ci kawai a ke yi amma yau ta haɗu da mai a ƙidar nasara, fresh green leaves da cream ta sa da pieces ɗin kaza a plate ɗin ta sa’annan ta soma ci a hankali.
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
Sosai take ta sataan kallon Hammad, gani take yi kamar Mancy ce a zaune, jefi jefi kuwa tana ta murmushi yau dai gata cikin danginta tana cin abinci tare da su wani kalan sanƴin daɗi ne yake lulluɓe ilahirin gaɓoɓin jikinta. Godia kawai take ta yiwa rabbil izzati ta sani da taimakonsa da ikonsa take samun damar kusantar danginta kuma tana addu’ar in sha Allah anan kusa zata cika wa mahaifiyarta burinta zasu dawo cikin danginsu za suyi rayuwa tare da su da yardar Ubangijin taliƙai, sun kammala cin dinner inda Abee ta lura har a ka ci a ka gama babu wanda ya ce wa wani ɗan uwansa tak babu motsin da kake ji yana tashi a arean in ban da ƙarar cutleries ɗin su (cokula) wannan ma yana ɗaya daga cikin ka’idar Hammad, Bayan sun kammala suka tattara kwanukan da a ka ɓata suka wuce da su sa shin wanke wanke.