AMAREN BANA
CHAPTER 4
A safiyar wannan ranar ce kuma Abba da Momi suka dauki hanyar Gusau, kasancewar Mahaifin Hajiya Atika ya nemi ganinsu, jin abinda yake faruwa. Sai dai wani abin dariyar Momi na baya. Abba na gaba ake tafiyar.4
Yayin da Raa’id ke ta aikin fizgarsu a guje. Ba abinda yake damunsa, irin shirun da ya ji sun yi. Da ya gaji ne, suna isa Zariya ya-ce “Abba, ni kam ma a ina ka ce min ka fara ganin Momi?”1
Likita ya gano sarai dabarun dan nasa, kamar ya yi shiru ya kyale shi, amma sai ya hakura ya-ce. “Cikin makaranta, ina wucewa a cikin jami’a, ta zo ta shige min gaban mota har sai da ta fasa min wutan motata a dalilin kauce mata da na yi, ka santa da surutun tsiya, suna tafe da kawayenta tana ta zuba, kawai ta afka min.”
Ra’id ya yi dariya ya-ce. “Tab! Abba ranar ashe ka sha fada.”
“Sai na fada maka? Tsabar masifa, ta tafi ta bar littafanta a saman motata.”2
Caraf! Momi ta-ce. “Na shige maka gaban mota, ko ka bankade ni? Tuki ka ke yi kamar ba ka da ido, saura kiris! Ka daga ni sama, ba don Allah ya kare ba.”
Raa’id ya gintse dariyarsa. “To Abba tunda ta tafi a ina ka sake haduwa da ita?”1
“Akwai sunanta a jikin littafanta, nan na ga Faculty dinta da kuma abinda take karantawa, shi kenan na je nemanta, don na mayar mata da takardunta.”
“Shi kenan Abba, sai ka ga ta burgeka?”
“Waye? Ta ga dai dan hadadden saurayi da motarsa na zamani, nan ta shiga bada hakuri.”
Momi ta sake tsomo baki a hirar tasu. “Wace motar da kararta kamar kukan balbela.”14
“Oho dai ina ita aka yi ta shiga ana zuwa yawo, har ana nunawa kawaye anyi saurayi mai mota.”
Nan suka shiga sa’insa. Ra’id na jinsu, sai dariya ta kubce masa ya-ce. “Abba ko dai mu juya ne mu yi wa Baban Gusau waya mu ce kun yi sulhu?”
“Kai ungo naka, idan za ka yi tuki, ka yi abinda ke gabanka, ba na son shashanci.”4
Nan Raa’id ya shiga taitayinsa ya daina sa baki. Ita kuwa Momi ba ta ki a ci-gaba da hirar ba, ta yi kewar mijinta, amma shi ko gogan ya dake, ya daina labarin ma daga haka.
Har suka isa Funtuwa, ba me cewa komai a tsakaninsu, don haka Raa’id ya manna karatun Al-qur’ani a cikin CD din motar.
Suna isa cikin Gusau, kai tsaye unguwar su Momin suka isa, inda gidan Baban Gusau yake. Momi ta shige ciki, yayin da Abba da Raa’id suka nufi masallacin kofar gidan.
Ita abin duk kunya yake ba ta, gotai-gotai da ita wai ta zo gida sulhu da shari’a, bayan kaf! Kannenta ma an masu aure, kuma suna zaune kalau, sai dai akan wannan fadan ko gaban Sarki za a je a shirye take, fatanta daya dai kawai. Baban Gusau ya sa Abba ya mayar da auren su, ita ta san yadda za ta bullowa al’amarin.
Kafin su yi sallah. Momi ta shiga ciki ta kimtsa, sannan aka shiga gaisawa, tana yi masu bangajiyan biki. Yadikkonta marikarta ce ta-ce. “Sai kawai Alhaji ya-ce mana ku na tafe yau.”
“Wallahi yau muke tafe”.
“To ke ga azumi, ba za ki bari sai bayan sallah ku taho da yaran gaba daya ba?”
STORY CONTINUES BELOW
Da alama dai Alhaji bai fadawa Hajiya Atine abin da ya kawosu ba, don haka ta kara samun karfin gwiwa, ta san tabbas zai yi wani abu akan aurenta da Likita, kan su koma. Da aka yi la’asar ne Alhaji ya shigo. Hajiya Atine ya fara nema, sun dade sannan ta fito ta-ce. “Ki shiga ciki Alhajin na son ganinki.”
Sai dai kallon da Hajiya take mata, ya fara sa ta tunanin wane irin fushi za ta tarar a wurin mahaifinta.
Bayan sun gaisa ne, ya dubeta ya-ce. “Atika, Likita ya fada min duk abinda yake faruwa. Wai ashe ke har yanzu hankali bai shige ki ba?
Duk abin nan da yake wakana shekara da shekaru ana ja miki kunne. Amma kin ki bari, sai shegen taurin kai? Don me ki ke tsammanin diyarki ba za ta yi taurin kai ba, ko kafiya bayan ke ga yadda ki ke? To wai ki fada min da ki ka kashe auren ki, ina za ki je ki zauna?”
Tai shiru, sai wul-wul take da idanu. “Don dai gotai-gotai dake ba za ki zo gidan nan ki share ki ce za ki zanna ba, don haka mutuncin ki na dakin mijinki, idan ya ga dama ya hakura ya maida ke to, idan kuma ya ki, sai ki nemi na yi.2
Saboda ni kam na gaji ba zan yi shari’ar ki na kuma yi na kannenki da ‘ya’yanki ba.” Me Alhaji yake fada ne? Yanzu yana nufin ba zai sa baki Likita ya maida ita ba dakinta?
“Alhaji ka yi hakuri, ka saurari abin nan fa, matar nan ba ta da makiya irina, ba ta son ci-gaba na sam, ta yaya zan dauki ‘yata na bawa danta aure, alhali na sani sarai duk wayau take yi, don ganin ta hallakani da ni da zuri’ata.”
Mamaki ya kama Alhaji ya-ce. “Na ji bayaninki, amma ina fata kin sani Umaru yana da damar ya aurar da diyarsa ga duk wanda ya ga dama kuma a kowane lokaci?
To ina so ki ajiye wannan gaggarumar fadan a gefe, a hir, ki ka nemi shiga tsakanin ‘Yan-uwa, domin kuwa ke za ki kwan ciki. Kuma ni dai na fada miki, sai dai ta ki ta fissheki.”
Bayan ya gama ji daga gareta ne. Ya hada su duka ya sake masu nasiha, sannan ya ja kunnen Momi ba na wasa ba, a gabanta ya bawa Dr. Umar zabi, idan zai iya ci-gaba da zama da ita, to wannan yana hannunsa, idan kuma ya gaji, kar ya ji nauyinsa kawai ya fada masa, don shi kansa ya san halin Atika, rikon makahaukaci ne, sai Sarki.
Alal haqiqa nauyin Alhajin ya ji ya-ce, ya hakura za ta iya komawa, amma da sharadin kar ta sake dago tashin hankali kan duk wani abin da ya jibanci auren Rumaysa da yake da niyyar hadawa.2
**************
Randa suka gama jarabawa wanda ya yi daidai da ana jibi sallah. Rumaysah na dawowa daga makaranta ta samu Saleem a harabar gidansu, ba wannan bane karo na farko da yake zuwa ya kasa shaida mata ya zo wurinta, ko kuwa ya ganta ta wuce cikin gida. Yau din ma gaishe shi kawai ta yi, tana da shirin shigewa ciki ya-ce.
“Rumaysah please, ki saurara, magana na zo mu yi dake.” A hankali ta fara takawa wurin da yake, har ya fara jin dadi za ta saurare shi ne ta-ce. “Saleem, duk wani abin da ya dace ka fada, ba ka fade shi a lokacin da ya dace ba.
Domin kuwa ni tuni na wuce shafinka a rayuwa. Allah ya ba ka wacce ka ke so, wacce kuma za ka iya aura, amma ni kam, Alhamdulillah! Domin na samu wanda na ke so. Kuma kwanan za mu yi aure, domin shi a shirye yake da ya aureni.”
Ta fada ne kawai, don ta kunsa masa bakin-ciki, amma sai ta samu kanta ita ma a bakin-cikin, don ita ma yanzu ba ta san makomarta ba, tunda Momi da Abba suka koma ba wanda ya sake dago mata maganar aurenta da Yaya Fawzaan.
Tana sane da wannan irin shirun da yake faruwa ne, a yayin da wata gagarumar guguwa za ta taso, don haka ba ta jira abinda Saleem zai fada ba, ta juya ta yi shigewarta cikin gida, dama a gajiye ta dawo, wanka ta yi ta sanya riga da Skirt na dinkin atamfa mai guntun hannu.
STORY CONTINUES BELOW
Sannan ta sauka kasa. Radiyya ba ta gida, ba ta dawo daga wurin aiki ba. Don haka ita kadai ce, sai ko masu aiki, kicin ta je wurinsu ta zauna tana tayasu hira da kuma aiki. Nan ne Laminde ta-ce.
“Gaskiya, mun yi murna kwarai da Hajiya ta dawo, wannan abu ya ba mu tsoro, ganin tashin hankali haka, sam ba mu saba ganin haka tsakaninsu ba.” Murmushi ta yi, a zuciyarta kuwa cewa ta yi “Ni ma haka.”
Sai dai ga mamakinta, sam Momi ta ki ta sake mata, iyakarta da ita gaisuwa, ko hira ake yi idan ta sa baki, sai ta ki tankawa, don haka musamman ta sameta a daki ana gobe sallah, rubutu take yi a wasu takardu, tana ganin Rumaysah ce, ta shigo, ya sa ta koma kan aikinta.
A hankali ta zagayo ta zauna a saman tebur din ta-ce. “Momi, Rumaysan ki ce fa ki ke mata tamkar wata bare, kin daina bata lokacinki bare muhimmanci. Laifinta ya yi tsauri har haka ne?”
A hankali Momi ta zare gilas dinta na karatu ta-ce. “Muddin za ki kalli idanuna, ki min jayayya akan abinda ki ka san na fi tsana, me ki ke tsammani daga gareni?”
“Momi, na san na yi kuskure, abin da na yi a lokacin da kamata ya yi a tsanake na fada miki dalilina, ba kai tsaye ki same shi a sama ba. Ga shi har ta sanadina ku ka yi fada da Abba, wanda tun tashin mu ba mu saba ganin hakan ba.” Nan take ta fashe da kuka ta-ce. “Ki yafe min Momi, na saki a kunci na bata miki rai. Amma ba a son raina na yi hakan ba.”
Momi ta ja ta jikinta ta-ce. “Ba komai ai ni daman na san haka, sai dai idan tursasaki za ayi ki amince da wannan abu, amma na san zai yi wuya jinina ya so jinin Sogiji.”
Rumaysah ta dago ta dubi Momi ta-ce. “Don Allah, ki fada min wai me Mama tai miki ne haka ba kya shiri da ita?”
“Ke yarinya ce, ba za ki gane ba, amma abubuwa da dama sun faru tun kan a haife ku, wanda ni kadai na san sharrin matar nan, don haka ki bar ni kawai. Na tsani duk wani abinda ya jibanceta, ba ki san irin ciwon da na ji ba, da ki ka kalli fuskata, ki ke cewa za ki auri jininta.
Idan banda AMAREN BANA, yaushe yarinya za ta dubi idon mahaifiyarta ta fada mata ga zabinta? Ko ta yi gaban kanta a alamarin aure?” Rumaysah murmushi kawai ta yi, saboda ita kadai ta san me yake ranta.
Babban farin-cikinta daya, shi ne Momi ta bar fushi da ita, ranar ta yi kwanan farin-cikin da baya misaltuwa.
Washegari ya kama sallah, zukatan jama’a fes! Sai godiyar Allah, tun da sassafe Rumaysah ta tashi ta yi wanka, har ta fito dakin Radiyya, tana barci, ta daka mata duka “Wallahi ko ki tashi ko na yi ready a kofar Abba, yana dawowa na riga karbar barka da sallah na.”
Radiyya ta yi juyi ta-ce. “Don Allah ki bar ni na yi barci, ni na gaji, wai ke ba ki ga aikin da muka sha jiya bane? Idan kin karba, ki ajiye min nawa.”
“Deeni ya shiga uku, idan ku ka yi aure, haka za ki yi ta son jiki. Wanka ma ba za ki yi da wuri ba?”
“Na dai ji, don Allah rabu da ni.”
Rumaysa ta sauka akan gadon ta-ce. “Shi kenan, zan karbi duka kuma na rike naki kason.” Ai ba shiri Radiyya ta wartsake, ita ma ta shiga don ta shirya. Momi suka fara gayarwa tukun, sannan suka shiga dakin Abba suka gaida shi. Radiyya Sarkin son kudi ta-ce. “Abba barka da Sallah”
Rumaysah ta kyalkyale da dariya ta-ce. “Yaya Radiyya sai an sauko daga masallaci dai ake yin barka da sallar.”
“A to fada mata dai kam, idan kun je kuyi min magana da Mominku” Ba su yarda da wayon nasa ba, sai da ya ba su barka da Sallah, suka fita suna farin-ciki kamar wasu kananan yara.
Kwalliya sosai Rumaysah ta sha cikin wani dinkin shadda, mai ruwan dorawa, doguwa ce, dinkin ya kamata daga sama, sai ya sake ta daidai kugunta ta kashe dauri ya zauna daidai a kanta, ga wani setin sarka da ta sa, ta kwanta a wuyanta, sai walainiya take yi, ta yi kyau matuka.2
STORY CONTINUES BELOW
Radiyya ma zama ta yi. Rumaysah tai mata kwalliyar fuska, yaran Abba dai sun fito fes! Da su, tana jin shigowar Abba.
Bayan an taso masallaci ta taho falonsa, nan ta same su tare da su Baffa da su Bilaal, Ra’id, Sajjad da su Aasim. A take ta gaida su, sannan ta mike za ta wuce. Aasim ya-ce. “Ni ba za ki gaisheni ba?”
Harararsa ta yi ta-ce. “Kai a su wa, kiyashi a jirgin sama?”
“Wallahi yarinyar nan ta raina ni, wai ba ki san na girmeki bane ko me? Maza ki zo ki kwashi gaisuwa”.
Baffa ne ya-ce “Kai ba ka da hankali ne? Matar Yayan naka ka ke cewa ta zo ta gaisheka?” Daidai lokacin Fawzaan ya shigo falon, nan ya tsaya cak! Da ya ji furucin Baffa. “Matar Yayanka.” Shi ya dauka an wuce nan a wannan maganar, ashe dama tana nan?
“Yawwa gwamma da Allah ya kawo ka, ka ji shi nan, wai Rumaysah yake cewa ta zo ta gaishe shi, sai ka gwada masa iyakarsa tun yanzu.”
Duk suka sa dariya. Aasim ko ya ji kunya ta kama shi. “Baffa yaushe aka yi haka? To ai ku ne ba ku fada min ba, ku ka bar ni na yi kwafsi, to dai yanzu na hakura, kin ci albarkacin Yaya Fawzaan”.
Rumaysah ko sai ta ji kunyarsu Baffa ya kamata, da su kadai ne da ta ba shi amsa. Da sauri ta mike ta fice daga falon nan, kannen suka koma kan Fawzaan da tsiya.
Bayan sun karya ne gaba daya samarin suka fita lokacin ne Baffa ya dubi Abba ya-ce. “Ni yaya wannan maganar ne ina ta kwana? Ban sake tuntubarka ba, ganin kwanan nan Atika ta dawo.”
“Ai ni Yaya ka rigani magana ne, da manufata kawai ko da karshen satin nan ne a daura auren.”
Baffa ya yiwa Abba duban kasake. “Auren ‘yan tsana ne za ka ce karshen sati? Hala har yanzu dai ana takun saka da Atika akan maganar ne, shi ya sa ka fadi haka?”
“Yaya Lamido har yaushe za mu yi ta biye mata? Na riga na yanke hukunci, domin duk wani abin da ya dace na yi an yi shi, har wani hidima ne za ayi?”
“Umaru ni dai idan za ka bi ta nawa, to a bar wannan batun zuwa ko karshen wannan watan ne, amma ina amfanin gaggawar?”
“To shi kenan tunda ka ce haka. Allah ya nuna mana, ai kamar gobe ne idan da rai da lafiya.”
Jikin Momi na bari ta bar falon. “Wato dama abinda Likita ya shirya min kenan, sai na kwantar da hankali na, sannan zai bullo ta wannan hanyar ko? To Wallahi sai dai su aurawa dansu wata ba Rumaysah ba.”1
Sai da ta bari daidai shigowar Abba, sannan ta sauko katuwar akwati a sama ta hau shirga kayanta a ciki, haka ya shigo ya sameta, sai fama take yi. “Atika lafiya ki ke ta aikin gyara kaya da daren nan.”
“Ni ba gyara zan yi ba, tafiya zan yi tunda dama ba da zuciya daya ka dawo da ni ba.”
Abba ya matso kusa da akwatin nata ya-ce. “Wace irin magana ce kuma ba da zuciya daya ba, zauna nan mu yi magana.”
Fuskarta a shagwabe ta-ce. “Ni ba ni da sauran magana, tunda ka riga ka yanke hukuncin abin da za ka yi, ni kuma ka nuna min ba ni da matsayi a rayuwarka.”
Ya dago zancen, amma ya yi kamar bai fahimta ba, har sai da ta-ce. “Yanzu tsakani da Allah ko tausayina ba ka ji, idan na tada hankali kuma ka iya kai karata Gusau, bayan ni ke da gaskiya.
Ni dai tsakani da Allah na ke fada maka, ko dai na tafi ku yi abin ku ba ni ko kuwa na zauna bakin-ciki ya kasheni, tunda haka ka fi so.”
“Me ya kawo maganar mutuwa kuma? Ban ga meye aibun wannan abin ba, yara suna son junansu, me zai sa mu mu ce za mu hana su? Ki na ga shin ba za mu shiga hakkinsu ba?”2
Duk yadda ta so tausar da zuciyarta dake ayyana mata abubuwa, ta kasa ta-ce. “Ni kuma Wallahi ban yarda ba, kuma ba zan taba yarda ba, don haka idan ka ga dama ko yanzu ka je ka daura masu aure, ba sai nan da wata guda ba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Dama kin daina daga hankalin ki Atika, domin na riga na gama magana.”
Zubar da kayan akwatin nata, ta yi ta fita daga dakin tun ranar kuwa Abba bai sake samun kan Momi ba, domin tsirfa kala-kala, wataran sai bakwai take dawowa daga wurin aiki. Duk don kar ma ta zauna su hadu da Abba.
**********
Yau yana fitowa daga wurin aiki, kai tsaye ya samu Baffa, saboda yai masa maganar Meena, don gaskiya ya gaji da yin shirun, ya ga ba zai fisshe shi ba, ga shi ko da ya je wurinta a sallar nan, ta fada masa iyayenta sun ce ya iso.
Tare da Mama ya samesu a falon Baffan, suka gaisa. “Hala ayyukan sun maka yawa har suka boye ka, tun shekaranjiya na ke sa idanun ganinka.”
“Wallahi, ban dan ji dadi bane, amma dai da sauki.”
Mama ta-ce. “Subhanallah, ka ga illar zama nesa da gidan ko, sai ka yi ciwo har ka warke, amma ba wanda yake da labari? Nan gaba duk inda jiki ya matsa maka, to ka fada ko a waya ne. Kan naka ne ko?”
“Eh shi ne, amma da sauki.”
Baffa ya-ce. “Allah ya karo sauki, ga shi ko hidima na gabanka sai ka watsake, domin mun yi magana da Abbanka, mun kuma tsayar da rana nan da sati uku Insha-Allahu za a daura aurenku da Rumaysah, ko ba komai, ka samu mai kula da kai. Ya fi zaman kadai din.”2
Tunda Baffa ya iso tsakiyar maganarsa. Fawzaan ya tsinci kansa cikin dimuwa, da kyar ya tattaro natsuwarsa ya-ce. “Baffa ina da wata magana, idan ba za ka damu ba.”
Nan take suka hada idanu da Mama, ta girgiza masa kai, alamar kar ya yi magana, tabbas ta san ta takura shi.2
“Ina sauraron ka, ka ce ka na da magana”.
“Daman zan tambaye ka ne, ko wane irin shiri ku ke yi, don ni a tsarina, ba na son komai kawai dai daurin auren ya wadatar.”
“Au, to shi ne, sai ka daga hankali, ai wannan magana ce mai sauki. Allah ya nuna mana lafiya, duk wani abin da ka ke bukata, sai ka sanar da ni.”
“To, Baffa na gode Allah ya kara girma.” Ya mike zai fita Mama ta-ce. “Ka jirani a falo akwai sakonka.”
Yana zuwa falonta, hannu ya sa ya shafo fuskarsa hade da sauke hucin numfashi. Can sai ga Mama ta shigo, da sauri ya isa wurinta ya-ce. “Mama don Allah me ya sa ki ka hanani magana gaban Baffa. Bayan kin san komai.
Yarinyar nan ba na sonta, ina da wacce na yiwa alkawari, da wane ido zan kalleta? Bayan ko kaina ba zan iya duba a madubi ba. Mama ke ki ka gwada min muhimmancin cika alkawari. Shin wai farin-ciki na bai dameki bane?”
Murmushi Hajiya Sogiji ta yi, sannan ta zauna. “Ko kadan ba haka bane, yanzu ka na ganin idan ka kawowa Baffanka wata magana daban, abubuwa ba za su kwabe bane? Kar ka manta, shi daman yana tantamar yiwuwar abin nan, an samu ya yarda komai na tafiya daidai, me ya sa za ka ki, bayan ka san ba don komai ka ke wanann abin ba, sai don kyakkyawar manufa? Shawarata anan, ita-ce me zai hana ka jinkirta batun ita zabinka, har sai bayan anyi komai. Sai ita ma ka tura a shige maka gaba.”
“Gaskiya Mama ni ba zan iya ba, ni ba ni da ra’ayin ajiye mata biyu, sannan kawai daga farawa na, na yi biyu?”
“To shi kenan, sai ka bar maganar Rumaysah ka auri zabin ranka, tunda shi zai saka farin-ciki.”
Fawzaan ya san gatse Mama tai masa, don haka bai tanka ba. Yai mata sai da safe, ya wuce gida, ya kusa kwana yana neman abin yi. Allah ya gani, watan Ramadan da ya wuce, Ya mika kukansa wurin Ubangiji kuma har yanzu yana kan rokon Allah zabinsa gare shi. Amma sam baya ji a jikinsa, kamar zai iya zama da Rumaysah a matsayin matarsa.
Da yammacin ranar lahadi ya tafi gidan Abba, domin lallai ne yana so su yi magana ta fahimta.
Tana zuwa falon ta same shi, ko me zai ce mata kuma, oho? A takaice ta gaishe shi, saboda tun da suka yi maganar ta-ce, ta amince za ta aure shi, bai sake waiwayarta ba.
STORY CONTINUES BELOW
Har sai take ganin ko don ta saukar da kimarta ne, yai mata haka? Bai san da nata manufar a yin hakan ba. Tana ganinsa, ta fahimci cike yake fal! Da damuwa.
“Rumaysah, don Allah ki saurareni da kyau. Ki na da labarin su Baffa sun sa auren mu nan da sati uku ko?”
A razane ta juyo ta dube shi, domin kuwa sam ba ta da wannan labarin, haba ita ma ta san shirun ya yi yawa haka nan. “Sai yanzu da ka fada, to sai aka yi yaya?” Ta dake ta fada.
“Don Allah, so na ke yi mu samesu mu ce duka ba mu so, don a hakikanin gaskiya ina da wacce na ke so, kuma iyayenta sun dage na turo, kar su dauka ina masu wasa da hankali ne.
Wannan ya sa na ke neman alfarmar ki, yau don Allah ki samu Abba ki fada masa, muddin ki ka nuna ba kya so, to na san ba wani bata lokaci za a warware komai.”
“Wato ni ce dai ba ka so, sai ita ko?” Ta fada fuskarta a langwabe, kamar wata abin tausayi, ganin za ta kawo masa qabli da ba’adi, ya sa ya koma kujerar da take, gwiwar sa daya a kasa ya-ce.2
“Don Allah Rumaysah na roke ki, albarkacin mutuncin da ke tsakanin mu da kuma kimata, idan kin taba gani ko sau daya ne, ki ce ba kya so na.”
Kwarai ya ba ta tausayi ko ma waye yake so, tabbas da gaske yana sonta, rokonta fa yake yi ta-ce ba ta son sa, wane irin tsanarta Yaya Fawzaan ya yi haka?
Hankalinta ya kwanta, jin shi ma yana nasa sabgar, don haka ta gyara zamanta ta-ce. “Na ji abin da ka ce, ka yi hakuri da duk abinda na fada maka. Insha-Allah zan samu Abba na fada masa komai.”
Cikin farin-ciki ya dubeta, a karo na farko da Rumaysah ta ga dariyar Fawzaan kenan. “Na gode sosai, ba ki san iya farin-cikin da ki ka sa ni ba, ni ma kuma Insha-Allahu zan fadawa Baffa komai, saboda a je min tambaya.”
Rumaysah ta yi murmushi ta-ce. “Ba za a fada mana sunan Yayar ta mu bane?”
“Meena sunanta. Ameena Abdulhamid”.1
“Allah ya tabbatar da alheri”.
“Ameen, na gode ba abinda zan ce miki, duk wani lokacin da ki ke bukatar wani taimako koma menene shi, ni kuma ki fada min, na yi alqawari zan miki shi, muddin bai fi karfina ba. Ni zan wuce, ki gaida Radiyya.”2
“Za ta ji.”
Nan ya mike ya fita daga falon cikin natsuwarsa. Shiru ta yi tana bin kofar da kallo. “Meye amfanin duk wani tsarina da shirina? Bayan zai jefa mutanen da na ke so cikin kunci? Momi ba za ta iya daukar wannan abin ba.
Ni kaina ba farin-ciki na ke yi da hakan ba, sannan Yaya Fawzaan yana da wacce yake so, don haka maimakon na bata mana rayuwa mu duka, ai gwamma na danne fushina, na samu Abba da maganar nan, na ajiye alwashin da na dauka, na raba Yaya Fawzaan da farin-cikinsa.”
Dariya ta yi, da ta tuno wasu abubuwan, ta girgiza kai, sannan ta wuce dakin Momi, don ta san za ta fi kowa farin-ciki da jin ta fasa auren Yaya Fawzaan.
Turus! Ta ja ta tsaya a bakin kofar, domin kuwa akwatunan da aka kawo daga gidan Baffa na na gani ina so ne.
A bubbude a kasan dakin. Momi ta yi fici-fici da kayan ciki tana zaune gaban akwatin, sai tsuma take yi. Da gudu Rumaysah ta isa gareta ta-ce. “Momi, me yake damunki? Ba ki da lafiya ne?”
“Lafiyata kalau, ni Abbanku zai gwadawa rashin mutunci? Yanzu wai har ranar auren ki da Fawzaan zai sa, ba ni da damar cewa hakan bai min ba, ba irin barazanar da ban masa ba.
Amma ya kafe akan hakan, don haka komai suka kawo daga wurinsu, zan hallaka shi ya tabbatar da gaske na ke yi. Kuma idan ba su janye ba, zan yi abinda duk tarihin zuri’ar nan ba a taba yi ba”.
Rumaysah shiru ta yi, don wannan gabar ta Momi ya zamo cuta, ace mutum da hankalinsa da ilimi da matsayi, amma idan aka zo kan abin da baya so, sai ya rikide tamkar mai hauka sabon kamu?
STORY CONTINUES BELOW
Anya idan ta fasa auren nan, ba ta cuci Abba ba kuwa? Don kuwa za ta rusa hanya guda da zai kawo karshen wannan kiyayya.
Hawaye ne kawai suka zubo mata akan kuncinta ta share. Ta riko hannun Momi ta ja ta zuwa bakin gado, ta kwantar da ita, ta rufeta sannan ta-ce. “Momi ki huta, bari na kawo miki abin sha ki sha.”
Da sauri Corridor din dakinta ta shiga, ta dauko lemon tacacciyar abarba ta tsiyaya mata a kofi, ta ba ta, sai da ta shanye tas! Sannan ta kwanta. Rumaysah ta ja mata kofa a hankali.
Abba na dawowa, ba zancen bayani da baki, hannunsa kawai ta riko ta kawo shi dakin Momi, a hankali suka bude kofa, sun samu tana barci.
Ta nuna masa yadda Momi ta zauna ta yayyanka ko wane zanin dake cikin akwatunan da Scissors, mayukan kuma duk ta kwaba su da juna, komai ba kyawun gani.
Suna fitowa ta-ce. “Abba batun gaskiya abin Momi yana ba ni tsoro, anya kuwa ba ta bukatar ganin Likita?”
“Ba wani Likitan nan, iya shege ne kawai, ta san me take yi sarai, duk tana yi ne don a fasa auren, kuma ba zan fasa ba.”2
“Amma Abba ka na ga zuwa nan da lokacin da za a yi koma meye ne Momi ba za ta illata kanta ba? Ta dau wannan abin da zafi fa, ni gaskiya na tsorata.”
“Baby, kar ki damu. Ba komai Insha-Allahu za ta daina duk ta sauko.” Rumaysah na tafiya Dr. Umar ya yi tunani.
“Dole kawai na samu Yaya Lamido na sanar da shi, ina ga matso da auren nan kawai za ayi kusa, saboda ban san illar da Atika za ta iya yi ba, muddin ta samu dama.” Bai koma dakinsa ba, kai tsaye gidan Dan-uwansa ya isa.
Ba bata lokaci ya gabatar da bukatarsa. Alhaji Lamido kuwa ya jinjina zancen kwarai. Domin kuwa yanzu Fawzaan ya bar nan da zance mai rikitarwa.
A take a wurin ya amince da batun Dan-uwansa, sun yanke wannan asabar mai zagayowa za a daura auren Fawzaan da Rumaysah.4
Ba su gushe ba sai da baffa ya buga waya suka sanar da kaf yayunsu. Duka sunji dadin wannan abu, amma Baffa ya-ce “Ba na son kowa ya sani tukun na saboda wasu dalilai.”
Don ya san gida daya a na biyu idan maganar ta je to tamkar Momi ta ji ne. Hakan ne ma ya sa ya-ce ya hutaccesu duka ba sai sun zo ba. Amma Yaya Uwa ta kafe akan ba za ayi haka ba.
********
Cikin farin-ciki Fawzaan ya koma gida domin ya sauke wani babban nauyi a tare da shi, yana tuna yadda suka yi da Baffa.
“Wacce irin maganace za ka kawo min yanzu kuma bayan ga abin da ake ciki?”
“Baffa daman mun daidaita da yarinyar, to kuma sai aka samu rashin fahimta a tsakani, yanzu dai mahaifinta yana so na isar da magabata.”
“To shi ne banda shiririta, ka na gani aka yi ta magana, ba ka ce komai ba sai da har an sa rana za ka zo min da wani zancen wofi?”
Kansa a kasa ya-ce “Baffa, Mama ta sani ita ta hanani fada maka, amma Wallahi na sha niyyar fada maka sai wani abu ya hana.”
“To, ba damuwa ka je zan yi tunani, gobe idan Allah ya kaimu sai ka dawo ka ji me na yanke.”
Tabbas ya san idan Baffa ya duba ya ga duk ba abin kamawa zai amince musamman idan Abba ya-ce masa Rumaysah ma ta hakura.
Ba bata lokaci ya dauki wayarsa ya lalumo Meenarsa. “Albi-shirinki.”
“Na ba ka garinmu gaba daya.”
Dariya ya yi ya-ce “Wai ina ne ma nan?”
“Tab, ka fadi takarar to tunda ba ka san wannan amsar ba.”
“Ba matsala ina da iya rayuwata domin na sani, kin san wani abu?”
STORY CONTINUES BELOW
“A’a sai ka fada Barrister.”
“Insha-Allah, magana ta kusa kankama domin kuwa Baffa ya-ce zai fada min duk abin da ake ciki gobe Insha-Allahu.”
Jikinta a sanyaye ta yi murmushi domin lokuta da dama ta kan saki jiki, sai idan ta tuno da cewa kasancewar Fawzaan kila wa kala ne a gareta sai ta ji gaba daya ta rasa me yake mata dadi.
“To Allah ya sa.”
“Sai ki shirya domin ana mini tambaya ko sati biyu ba za ki kara a gidan BAba ba, za a kawo min ke gidana.”
“lallai ma auren dodonni kenan.”
“Gaskiya ne ai me kuma za ki jira bayan an gama duka wani shiri tuntuni.”
“Allah dai ya nuna mana lafiya kai kam.”
“Yawwa don Allah idan ki ka tashi zuwa, kar ki manta wannan kayanki brown din nan ki taho da su kar ki kyautar suna miki kyau sosai.”1
Dariya Meena ta yi ta-ce “Kai kuma daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi za ki.”
“Hmm ki na wasa ne, baki san yadda na gama tsara komai a raina ba ko? Ke dai Allah ya kawo ki ki ga ikon Allah”
Sun kwashe wajen awa biyu suna hira da Meena, daga bisani ta fara ce masa ita fa hamma take yi barci na damunta.
Cikin nishadi ya yi aikinsa washegari, bai bar office da wuri ba kasancewar ayyuka sun masu yawa sai wajen karfe bakwai ya tafi, yana ta Allah Allah ya ji yaushe Baffa ya tsayar domin zuwa gidansu Meena, a rashin sanin abubuwa da dama sun faru a bayansa.
Tun daga waje yake ta faman sakin fara’a ranar, Aasim na gaishe shi ya tambaya “Baffa yana gida kuwa?”
“Eh, ka ci sa’a yanzun nan shi ma shigowarsa, ina ga Sallah ma yake yi yana ciki.”
Abinci ya fara ci tukun sannan ya zauna jiran Baffa, can sai ga shi ya fito, nan ya kwashi gaisuwa “Ka ce daman da yunwarka ka taho mana.”
Dariya ya yi, sannan ya-ce “Yau Baffa wani aiki muka yi sosai, ko lokacin cin abincin ma ban samu ba.”
“To Allah ya taimaka, ni ma zubo min abincin yau Mamanku ta share ni, ko da yake hala bata san na shigo ba.”
Fawzaan dai Allah-Allah yake yi kawai Baffa ya gama cin abinci ya fada masa komai. Kamar ko Baffan ya jishi sai cewa ya yi.
“Batun maganar jiya da muka yi da kai, ina ga kawai ka hakura da batun yarinyar nan, ayi wannan muga abinda hali zai yi, idan kuma ka na ga ba za ka iya hakura ba to sai a hada duka ayi lokaci guda.”
Fawzaan ya soma rudewa bai gane ya hakura ba.
“Idan ka amince za a hada din to ba laifi ni da kaina zan je na samu mahaifinta mu tattauna, sai ayi komai. Zuwa lokacin sai ka tuntubeta ka ji ra’ayinta.”
“Baffa ban gane ba, Shin Abba bai zo maka da wani zance ba?”
Baffa ya tura plate dinsa gefe ya wanke hannu sannan ya-ce “Zancen da ya zo min da shi din ne ya sanya ni fadin hakan domin al’amura suna tabarbarewa maimakon gyaruwa wannan ce kawai mafita, ka yi hakuri da wanann Insha-Allahu Alkhairine zai fito daga cikin wannan hadin. Ko me ka ke gani?”
Hadiye sauran busasshen yawun bakinsa ya yi, sannan ya-ce “Shi kenan duk yadda ka ce Baffa.”2
Me yake faruwa ne? To ko dai Rumaysah ta manta bata fadawa Abba batun maganar da suka yi bane? “Tunda ka amince duk yadda kuka yi sai ka fada min, mun tsayar da ranar asabar mai zuwa za a daura auren Insha-Allahu.”
Wani irin mummunar faduwar gaba Fawzaan ya tsinci kansa da shi, ji yake yi ma kamar sun dawo da rayuwarsa wani shirin fim. “Baffa, Wannan asabar din fa ka ce, yaya za ayi… yaushe aka gama shi… Baffa bai yi kusa da yawa ba?”2
“Akwai dalilin sa shi haka, kai dai ka nemi wadanda suke kusa kawai ka sanar da su, idan yaso wanda bai samu labari ba ka ba su hakuri daga baya.”
“Baffa yaushe aka taba yin aure cikin gaggawa haka?”
“Ni dai na gama magana, idan kuma za ka canza wani abin ne to, ina saurare.” Ganin ran Baffa zai baci akan wannan maganar, ya sa ya hakura ya masa sai da safe, shi ya manta ma ko Mama bai gayar ba, ya zo fita a falon ne.
Ita kuwa ta shigo, a ladabce ya gaidata, sannan ya wuce. Yana zuwa gida ya kashe wayoyinsa, da zazzabi ya kwana ranar, da kyar ya iya fita zuwa wurin aiki.
Baffa da kansa ya nemi Rumaysah ya fada mata an sa rana, kuma ga dalilin yin hakan. Tabbas hankalinta ya tashi, na tunanin abin da zai je ya komo. Ga alkawarin da ta yiwa Yaya Fawzaan na cewa za ta sa Abba ya janye maganar, tabbas zai tuhumeta da saba masa alqawari.
To amma idan ta tuno Momi, sai ta ji koma meye ne, za ta iya fuskanta. Radiyya ta nema ta fada mata abin da ake ciki, nan suka kulle kofa suka sha kukansu a daki.
“Yanzu babu wani kimtsi, haka za ai miki aure tamkar na sadaqa?”
“Ba komai Sis. Insha-Allahu zan yi hakuri a yi wannan auren ,wata rana sai labari.”1
“Kin ce Abba ya ba ki kudi, ki kawo sai na je na sayo miki wasu kayan bukatun, tunda kin ga ba yadda za ayi Momi ta sani.”
“Sis, kar ki wani wahalar da kanki, ga kayana a wardrobe, su me suke yi, ba abinda zan saya, yadda na ke haka, zan je.”
“Ki yi hakuri dai don Allah, ke ma kin san muddin ki ka shiga, ba yadda za ayi ki kashe auren nan tamkar anyi tufka ne, ana kuma warwara.”
Haka Rumaysah ta dage akan ta barta kawai. Ganin haka ya sa ta bugawa Khamsa’u a Bauchi, ta zayyana mata duk gurmin da ake yi tuntuni da abin da yake faruwa yanzu. Cewa Radiyyan ta yi.
“Ki rabu da ita. Insha-Allahu ina tahowa kafin asabar din, zan yi magana da Sa’ad, duk abinda ake ciki za ki ji ni.”
******
Kwanaki biyu wayoyinsa a kasha, wannan ya sa Rayyan ya zo dubawa ko lafiya. Fawzan bai boye masa komai ba, har yadda suka yi da Baffa. “Ai kai ka ke bawa kanka wahala.
Tun farko abin da na fada maka kenan. Kawai ka je ka samu Meena ka fada mata na san za ta amince.” Nan ne Fawzaan ya samu karfin gwiwa ya wuce gidan su Meena.
Tana fitowa jikinta ya mutu, ganin yanayin da Fawzaan yake ciki, idanunsa duk sun kada sun yi jawur! Da sauri ta isa kujerar dake gefen nasa, ta zauna. “Me yake faruwa haka Fawzaan?”
“Meena, komai ma ya faru, na rasa me zan yi daya kai na ya kulle.”
“Fada min menene matsalar?”
“Meena za ki amince ki aureni, koda na auri ‘yar uwata?”
Gabanta ne ya yi mummunar faduwa, kasancewar ta dauka maganar can ta shige ne har yake mata maganar turo manya, ta shiga tashin hankali nan take.
Ta yaya za ta fara auren Fawzaan, ta hada shi da wata alhali, tana son sa ita kadai ne su zauna koda na wani lokaci ne? Bayan watanni ya-ce zai auri watan.
“Gaskiya Fawzaan ba zan maka karya ba, har ga Allah ina sonka, amma raina ya ji zafin boye min da ka yi akan har yanzu maganar, ‘yar-uwarka tana nan.”
Fawzaan ya juyo ya dubeta ya-ce. “Ki taimaka min please Meena, ki amince shi ne kawai zai sa na ji karfin gwiwar aiwatar da wannan abu, na yi wa su Mama da Baffa abinda suke so.”
Kuka kawai ta sa masa, ta mike ta bar falon, hankalinsa ya sake tashi. Jikinsa a sanyaye ya mike ya bar gidan.2
A hanya sai tunani yake yi, me amsar Meena ke nufi a gare shi? Gaba daya komai yai masa zafi. Yana isa gida kuma ya samu sakon Baffa wai da safe duka za su wuce Gusau.
“Su kawai ta kansu ma suke yi, sun ma manta mutum na da aikin yi, gaskiya sai dai kawai su yi wucewar su, ni daga baya na tafi. Ta yaya zan fara barin garin nan, ban san me Meena take ciki ba?”2
**********
Gabaki dayansu sun shirya ranar Alhamis suka wuce Gusau. Hatta Momi ta tafi. Abba ce mata ya yi za su je su dubo Alhaji ne, saboda sun yi waya an ce bai ji dadi ba.3
Abin dai ya so ya bata mamaki saboda ciwon Alhajinta dai kusan kullum tashi yake yi, amma ba su yawaita zuwa gaida shi ba, ko dai mutuwa ya yi.
Likita yake boye mata? Nan take ta lalumi wayar Alhajinta, sai ko ga shi ya dauka. Ajiyar zuciya ta saki sannan ta-ce. “Alhaji, yaya jikin naka? Likita ke fada min cewa ba ka ji dadi ba. Ga mu nan mu da yara ma muna hanyar tahowa.”
Da yake da Alhaji aka hada shirin komai sai ya ce. “To Allah ya kawo ku lafiya.” Kusan lokaci daya suka isa da Baffa.
Mama na Abuja ba ta tafi ba. Muneerah ce ta isa gidan su na Abuja ta tarar da karin bayanin abin da ke faruwa.
“Mama kuma yaya za ayi ku bari ku yarda Yaya Fawzaan ya auri Rumaysah bayan ku na sane da irin rashin mutumcin Momi, yanzu idan ta ji labari, ku ka san me za ta yi? Kin santa da hauka fa, ki tuna yadda ta kona miki kicin dinki.”
“Ba komai Muneerah. Insha-Allahu, ni na san duk abinda zai je ya dawo zuciyar Atika, za ta natsu kuma fatan mu kenan.”1
“Ku dai Wallahi kun nace shekara da shekaru ba ta natsu ba, sai don Yaya Fawzaan ya auri Rumaysah? Kun dai cuce shi kawai Mama, don kuwa yana da wacce yake so.”
“Ke rufe min baki, kin fi mu sanin hakan ne? Ai dama ba mu hana shi auren koma waye bane, mu dai fatan mu, su zauna da Rumaysa’u lafiya.”5
“To shi kenan. Allah ya sa a dace.”
“Ameen, wannan shi ne fatan mu. Yanzu abinda za’ayi ki tambayi mijinki anjima zan hadaki da masu aiki, sai ku je Guzape ku kimtsa masu gidan, Ganan kayanta nan na lefe ku kai mata a shirya komai.1
Baffa ya sayi abubuwan abinci duka, ku kimtsa masu, idan ma ba ku gama aikin yau ba, gobe idan Allah ya kai mu, sai ku karasa saboda da an daura auren, za su juyo.”2
“To ba damuwa, zan fada masa ko a waya ne ma, ba matsala.” Sajeeda ma abin ya bata mamaki matuka da ta ji abin da yake faruwa, sai dai fatan alkhairi kawai ta yi, ba abinda kowa yake ji irin Momi.
Ranar Juma’a ne Momi ta fahimci dole akwai abinda Abba yake boye mata, domin kuwa dai tun isowarsu wajen Alhaji.
Suka fara zuwa, sai dai Alhamdulillah! Ta ga jikin na sa da sauki. Yaya Zainabu ta gani da Yaya Uwa sun diro. Nan ne ta samu Abba ta-ce, “Wai me ya kawo mu Gusau ne?”
STORY CONTINUES BELOW
Zai fara kame-kame ta-ce masa. “Likita kar ka maida ni karamar yarinya mana? Dole na san akwai wani abu, haka kawai gida zai fara cika, babu gaira babu dalili, sallah ma fa wucewa ta yi, ba mu zo ba, sai haka nan?”
“Ba zan ci-gaba da boye miki abinda yake faruwa ba, saboda ke ma kin cancanci ki sani, don yadda Rumaysah take ‘yata, haka ke ma ‘yar ki ce, don haka gobe idan Allah ya kai mu za a daurawa Rumaysah aure da Fawzaan.”
Wani tsinkewar gaba ta ji, idanunta suka fito, take suka koma jajaye abinka da farin mutum. Ai kuwa ba sauran bata lokaci, ta kai kasa ta zube. “Ka cuceni, kuma za ka cuci ‘yarka akan wannan kafiyar taka, maras dalili. Domin kuwa ba ta son wannan aure.”
Abba ya dubeta, ya-ce. Duk da na san Rumaysah ta so wani a baya, amma wannan ba shi zai sa ba za ta sake yin wata soyayyar ba a rayuwarta, kuma ina mata fatan samun farin-ciki.” Take ya kira wayar Rumaysah ya-ce ta same su a falonsa.
“Baby, yaya dai? Duk gajiyar hanyar ce?” Ita dai ta san kodewa kawai ta yi tsabar kuka da take kwana yi.
Ga shi kwana da kwanaki ba ta kwalliya, shi ya sa Abba ya fadi haka. Kafin ya sake cewa komai. Momi ta-ce. “Rumaysah, fada min gaskiya, shin ke ki ka amince da wannan auren ko kuwa saki aka yi dole?”
Lokacin ne hankalinta ya tashi, ta raba kallonta tsakanin iyayen nata. A sanyaye ta-ce “Momi ni na amince, ba wanda ya sa ni dole.”
Mari ta ji ya sauka a fuskarta, irin mai gigitarwan nan. “Ke ma sun koya miki munafurcin ko? Shi ne ni za ki zo ki sameni, ki ce magana ta wuce, na yafe miki, ashe karya ki ke yi? Har ni za ki yiwa karya Rumaysah?”
“Momi, ban miki karya ba, kawai ban fada miki komai bane, ki yi hakuri ki yafe min. Duk duniyar nan farin-cikin ki ne kawai a gaba fiye da komai nawa.”
“Shi ya sa ki ka nuna min alama ai da auren dan makiyata, kin nuna min so kenan, ta hanyar yaudarata. Na gode Rumaysah. Allah ya ba ku sa’a”. Ta fada hade da mikewa ta bar falon.2
Nan Rumaysah ta zube a kasa, tana ta risgar kuka. Abba ya barta ta yi mai isan ta sannan ya-ce. “To ya isa haka, ki kwantar da hankalinki, komai zai wuce, gobe i war haka Insha-Allahu anyi mai wuyar.”
Dakinsu ta wuce tana aikin kuka. Radiyya na gefenta kamar wasa aka banko kofar dakin, sai ganin Momi, suka yi ta shigo da wata zandamemiyar wuka, wani wawan tsalle ta daka suka yi shataletale a dakin. Radiyya ta yi nasarar bude mata kofar dakin ta-ce “Rumaysah ki gudu.”11
Ai sai ta sa kuka. Rumaysah kuwa daga ita sai dan-kwalin kanta, da kyar ta suri takalma wari-wari a kofar falon Abba ta yi waje da gudu. Momi ta biyota tana huci, tana isa falo, ba ta ganta ba, ta tsaya tana mai da numfashi.
“Momi, don Allah ki yi hakuri ki bar ta”.
Yaya Uwa ta cafko hannunta. “Atika, wane irin hauka ne ke damunki? Lafiyarki kuwa, ki duba fa wuka ce a hannunki”.3
“Wallahi ku bar ni na kasheta, idan ya so sai ku hallakani ni ma, amma ba za ta jawo min bugawar zuciya ba.”
“Ki kasheta? Kin san hukuncin kashe Dan mutum ai, ba sai na tsaya fada miki ba, tunda ke mai shari’a ce. Yau ko wanda ba masulmi Rumaysah za ta aura ba, sai haka, ko shi ma ba ki isa ki kasheta ba, bare Dan-uwanta jininta. Don haka ki shiga hankalinki tun wuri.”
Yaya Zainabu da su Ra’id ne su kai mata ‘yar karfi tana turjewa suka kai ta daki suka kulle. Ita a dole a bar ta sai ta bi bayan Rumaysah ta kar banza.3
Rumaysah kuwa tana fita, ta tari mashin ta-ce ya kai ta gidan Baban Gusau, duk da babu tazara tsakanin gidaje biyun, amma ji take yi idan ta tafi a kasa.
Momi za ta iso ta, ta yi nasarar daba mata wukar hannunta. Mai mashin dai kallon mahaukaciya yake mata, don gata biji-biji, ga shi daga ita sai riga da siket din atamfa da dan-kwalin leshin Radiyya, ga takalma gambar habaru.6
STORY CONTINUES BELOW
Yana kai ta ya-ce ta ba shi kudinsa. “Bari na shiga ciki na amso maka.”
“Tab! Hankalinki daya kuwa?”
“Da hankali na, ka jirani ina zuwa.”
“Dakata, ba inda za ki je, sai kin ba ni kudina Malama.”
Mai gadin gidan Baban Gusau ne ya gansu, ya karaso kusa da su, yake tamabaya ko lafiya, shi ma dai ranar da kyar ya gane Rumaysah.
“Don Allah, Malam Ya’u ba shi kudinsa.” Da gudu ta fada cikin gida, sai dakin Hajiya Atine, tana kuka tana haki.
Cikin tashin hankali Haijya Atine ta dago ta dube ta, domin har ga Allah ta tsorata, saura kadan zuciyarta ta buga. “Ke lafiyarki kuwa? Me ya faru haka?”
“Hajiya, Momi, Momi” Ta fada tana nuna kofa, tana haki, a zaton ta Momin ta biyota har yanzu. “Za ta kasheni da wuka.”
“Subhanallahi! Mummunar mafarki ki ka yi ne?” Ta fada hade da riko Rumaysah da hannu daya da dafe kirji da daya hannun.
“A’a Hajiya, da gaske ta ce za ta kasheni, don Allah ki kulle kofarki. Allah ba don na tozarta ta zan yi auren nan ba. Hajiya wayyo ki boyeni.” Ta fada jikinta na bari.4
“Atikan ta-ce za ta kasheki da wuka? Ko dai ba ki ji da kyau bane?”
“Hajiya, biyoni ta yi da wukar fa, ki kira min Baban Gusau.”
“Ya isa ki kwantar da hankalinki, ba mai shigowa dakin nan, bare ya taba min ke. Share hawayenki, ki yi shiru.” Zuciyar Hajiya Atine cike da mamakin halin da Atika ke nunawa game da wannan auren.
Ta lallaba Rumaysah har ta daina bari da kukan da take yi, ta dauko abinci ta ba ta. Amma ba ta da kwanciyar hankalin ko da kallon abincin ne, bare a je ga ci.
Gani take yi ko wani daki ta shiga Momi na iya shigowa ta ida niyyarta. Da maghriba sai ga su Yaya Uwa har gidan Baban Gusau, nan dai aka jajanta abin da ya faru, da ba su so a fadawa Alhajin Momi abin da yake faruwa ba, amma Hajiya Atine ta-ce.
“Tunda kun ce za ku tafi da ita, yana da kyau ya san koma me ake ciki, saboda ya ja wa Atika kunne ai wannan rashin hankalin ya kai karshe, yaya za ta yi kan Rumaysah da wuka?”
Sun sa Rumaysah a mota suka yi gaba, yayin da Hajiya Atine ta zayyanawa Baban Gusau komai. Kwarai ransa ya baci, kuma a take ya kira wayarta.
Da dare Goggo Zainabu suka umarci Rumaysah ta yi wankan magarya da lalle. Saboda amarya take a washegari. Amma ita duk wannan zumudin, ba shi bane a gabanta, duk da ta samu tabbacin Momi na kulle, sai take ganin anya za ta iya yin auren, alhali Momi ta dau zafi haka?
Sai yamma lis! Angon ya iso, wani irin haushin Rumaysah yake ji, da baya tsammanin zai iya ganinta bai illata ta ba, ji yake yi gani na farko, idan yai mata, babbalata zai yi.3
Don haka ya yi zamansa a gidan Baffa. Natsuwa ya yi ya shirya tunaninsa, abin da ya fi damunsa, shi ne har yau Meena ba ta saurare shi ba, abu na farko da zai fara yi kenan da zarar ya koma.
Kusan dukkan gidan mutane daidai ne suka rintsa, cikin wadanda ba su rintsa ba kuwa Rumaysa. Yaya Fawzaan, Abba da kuma Momi. Su Radiyya kam har da minshari. Da khadija da Khamsa’u, duk a ranar suka iso Gusau. Khadija na jinsu suna ta faman bawa Rumaysah hakuri.2
Ta dubesu ta-ce. “Ku na dai ganin halin da Momi take ciki, amma dukan ku ba mai tausaya mata, kun kafe sai kun yi abinda ku ke so, wai ke Rumaysah me ki ka gani a Yaya Fawzaan ne, ki ka makale masa haka?”
Rumaysah ta goge hawayenta ta-ce. “Babu komai, hakikanin gaskiya dama zan aure shi ne saboda na rama wulaqancin da yai min, na hana shi abin da yake so, sai kuma na hakura gaba daya. Har ga Allah yanzu ba don kyawun sa ko kudinsa ko kuwa don ina son sa zan aure shi ba, zan aure shi ne don Allah kawai”.
STORY CONTINUES BELOW
Khadija ta tabe baki ta-ce. “Wane aure ne kuma wannan? Ko har zama da shi din ya sa kin fara irin tunaninsa ne? Ni dai Wallahi ina jiye miki ne, domin wulaqanci kala-kala ya iya. Bare kuma ga shi ya tsaneki ya tsani Momi.”
“Insha-Allahu zan jure.”
“Ke ki ka sani ai sarkin naci.”
Suna fita a dakin. Naja’ah ta mata waya. “Rumaysah, me na ke ji Firdausi take fada min. Wai gobe za a daura aurenki da Yaya Fawzaan?”
Murmushi Rumaysah ta yi. “Kwarai kin ji daidai. Yaya hutu da su Mama?”
“Lafiya kalau, daman na kira na ji ne, don na kasa yarda. Amma nayi miki murna Allah ya ba ku zaman lafiya.”
“Ameen”. Sai lokacin abin ya dirowa Rumaysah da gaske fa Yaya Fawzaan, wai za ta aura nan da ‘yan awanni. Kuka kawai ta sa, ta yi iya mai isarta.3
Wajen karfe tara su Yaya Uwa sun sa Rumaysah a gaba ta shirya cikin kayan da Radiyya ta bayar aka shirya mata, wani french lace ne mai laushi launin (Leave green) Turarren kore. An kawata shi da Bridal Satin ta kasan irin wannan launin, ya yi kyau sosai ya bi jikinta ya lafe, dogon hannu ne gare shi. Sai sarka kalar sa na Beads mai hawa-hawa.
Haka aka rufa mata gyalensa. Ta yi kyau matuka, tamkar wata amaryar da za ta yi auren so, sai dai kowa ya san ba haka bane.
Ba wani gayya su Baffa suka yi ba, abokan kusa kawai da ‘Yan-uwa suka gayyata, tun da aka sa lokaci. Su Bilaal suke ta sintirin kai katuna.
Da ikon Allah kuwa ba laifi, jama’a sai tuttudowa suke yi. Fawzaan kuwa hatta ogan sa a ofis bai fadawa zai yi aure ba.
Rayyan ne kawai ya zo, nan ma shi ya gayyaci kansa, don Fawzaan bai ko yi tunanin gayyatar kowa ba, saboda tsabar yadda baya son abin, haushin Rumaysah da yake ji ya ma ya rinjayi kin auren da yake yi.
Don haka ita kawai yake jira ya gani. Sai dai hakan ya kasa, saboda jama’a. Rayyan ya dube shi ya-ce. “Don Allah, tashi ka shirya dube ka, sai ka ce ba ango ba?”
“Ka san ba gayyatarka na yi ba, idan ka matsa min zan kore ka.” Ya fada a tunzure.
“Na ji, don na zo garinku, shi ne za ka wulaqantani ko? Wallahi ka tashi ka shirya kafin na kira maka Baffa”.
Share shi ya yi, ya dauki wayarsa, yau kam ya sha naci duk yadda za a yi, sai ya yi magana da Meena, don haka buga mata ya rinka yi, har sai da ta gaji ta kashe wayar.
“Ka na ganin za ta yarda kuwa, bayan abinda zan yi yau?” Rayyan ya dube shi cikin rashin fahimta, don haka Fawzaan ya-ce. “Meena, ka na ganin za ta daina so na?”
“Ka kwantar da hankalinka. Insha-Allahu zan shawo kanta, za ku koma normal.”
“I really hope so, duk wannan wawiyar yarinyar nan ce, tayi min shirme.”
“Yaya za ka kira matarka wawiya, wannan sam ba dabi’a bace mai kyau, na san ranka ya baci, amma don Allah ka daure ka danne fushinka.”3
Kuka ne kawai Fawzaan bai yi ba, da kyar ya shirya cikin wata shadda shigen babbar riga ta sha aiki na zamani, mai daukar hankali ruwan toka, hannunsa na hagu agogo ne mai kyaun gaske ta silver.
Hularsa ya sa ta zanna bukar, ta shiga da kayan sosai, sai takalma sau ciki ya yi matukar yin kyau, daman idan dai iya gayu ne, to Fawzaan ba daga nan ba.1
Sai da suka karya, sannan suka fito zuwa lokacin har kofar gidansu ya soma cika, bai san komai ba, kawai sai ganin abokansa ya yi sun nufo shi, wajen su shida. Kallon Rayyan ya yi, don ya san aikin sa ne.4
Ba yadda ya iya, haka ya rinka sakar masu murmushi yana musabaha da su, da kuma yi masu sannu da hanya.
Yaya Shatu ma a ranar ta iso, duk da su Baffa sun ce su yi zamansu dukkan su, sai da suka taho. Su Yaya Uwa ne suka tsaya kan abincin baki, suka kula da ma’aikatan da suke aiki.
STORY CONTINUES BELOW
Duk wannan bidirin da ake yi. Momi tana daki ba ta ko leko ba. Ganin haka hankalin Rumaysah ya tashi, ta wuce dakin Abba ta samu baya nan, ya fita wurin daurin aure, don haka ta kira wayarsa ta-ce, tana dakinsa.
“Baby lafiya dai?”
“Abba, Momi ta ki fitowa tuntuni, ba na son na yi abu cikin fushinta, ban san yadda zan yi ba.”1
“Ki kwantar da hankalinki, za mu je tare mu yi mata magana”.
“Ni na fi son mu je yanzu, kafin a daura auren”.
“To na ji share hawayenki, mu je. Bayan kin yi kyau sosai, kuma za ki bata gayen ki?” Sun dade a bakin kofar dakin, sannan ta gaji ta bude masu, sai da Rumaysah ta leka ta tabbatar babu boyayyiyar wuka a hannunta tukun.
Ta shiga, a kasa ta durkusa ta-ce. “Momi, don Allah ki yi hakuri ki daina fushi, ko zan samu albarka cikin abinda zan yi. Kin san cewa fushinki yana matukar daga mini hankali.”
“Ni meye nawa, kun riga kun gama komai ai ke da mahaifinki, kin nuna min ke ‘yarsa ce, ‘yar halas. Ai na fada miki Allah ya ba ku sa’a”. Hawaye ta goge a idanunta, sannan ta-ce. “Idan kun gama ku fita, kaina na min ciwo, zan kwanta ko zan samu sauki.”3
Jikin Rumaysah a sanyaye ta mike suka bar dakin. Dr. Umar dai ya san duk wannan kwantar da hankalin da Momi ta yi.
Baya rasa nasaba da maganar da Alhajinta yai mata, don musamman jiya bayan ta gama haukarta. Rumaysah ta dawo gida Baban Gusau din ya kirata a waya, yayi mata nasiha a jiya da daren.2
***********
Karfe sha daya aka daura auren Barr. Fawzaan Lamido Attahir da Rumaysah Umar Attahir, maimakon farin-ciki da jin dadi da yake sauka a zukatan ma’aurata, idan ance an shafa fatiha, wani kunci ne ya dira a zuciyar amaryar, yayin da angon kam ma bai san me zai ce yake ji ba, don baya misaltuwa.
Wajen karfe daya Baffa ya tara kowa da kowa a falon sa, aka yi addu’o’i, sannan ya-ce “To Alhamdulillah! Ga shi dai yau Allah ya nuna mana auren Fawzaan da Rumaysah, sai dai mu yi fatan zamansu lafiya.”2
Nan ya shiga masu nasiha dukan su biyu suna zaune a gabansa da Abba. Yaya Shatu ma ta dauko nata ta dora. Rumaysah kuwa ba abin da take yi sai kuka, musamman idan ta tuna Momi na fushi, ga Fawzaan ma ba ta san makomarta ba.
Tana tsakiyar kukan ne Abba ya dauki Al-qur’ani Izu sittin wanda aka adana shi a cikin gida mai kyawun gaske ya mika mata. “Karbi wannan Baby, ki rike shi sosai. Kinga Alqur’anin nan, duk lokacin da ki ke farin-ciki, ki rike shi abokin hirar ki, haka idan ki na kunci ki rike shi a matsayin maganin matsalarki, sai ki ga komai zai zo miki da sauki Insha-Allahu.3
Duk lokacin da hanya ta toshe miki, to wannan shi ne mabudin hanyarki. Kar ki taba bari Mama da Baffa su yi kuka dake, saboda karfafa zumunci aka yi a wannan auren, ina fata alkhairi ya fito daga gare shi, kar ki bari mu yi da-na-sanin wannan auren naku Rumaysah.”2
Kanta na kasa, sai share hawaye take yi. Fawzan na kallon yadda take ta sharban kuka, haka ya dauke kansa gefe guda, wani irin bakin-ciki yake ji a ransa kamar ya shaketa. Abba ya ci-gaba.
“Kar ki ga kamar ke har yanzu yarinya ce, girma ya kamaki, saboda haka kar ki rika fada da mijinki kamar karamar yarinya.” Abba ya dubi Fawzaan, ya riko hannunsa ya hada da na Rumaysah hade da fadin.2
“Fawzaan, duk lokacin da Baby na ta yi kuskure, ka yafe mata.” Rumaysah ta dago idanunta da suka yi luhu-luhu ta dube shi, shi ma kallonta yake yi ta gefen idanu, amma ita kadai ta san ma’anar kallon.
“Rumaysah, yarinya ce mai kyakkyawar zuciya, kwanan nan za ta fahimtar da kai hakan. Don Allah ka kula min da Rumaysah na.” Abba ya yi saurin share kwallan da ya zubo ta gefen idanunsa.
STORY CONTINUES BELOW
Fawzaan ba abinda yake tunawa, sai haduwarsa da Rumaysah a satin da ya wuce, inda ta ba shi tabbacin za ta fadawa Abba ba ta sonsa, za a fasa aurensu.4
Sai kuma ga shi Baffa ya kira shi yana fada masa ya hakura da Meena akan an tsayar da ranar auren su nan da sati daya. Baffa ya dubi Abba ya-ce. “To, ka bar dan naka, sai ita kadai ne za ka yi wa nasihar?”
Abba ya-ce. “Ni na riga na san Fawzaan baida haufi, shi ya sa ban ce komai ba. Domin kuwa yadda zan kula da Rumaysah, zai kula min da ita fiye da haka.”
“A’a ba za a yi haka ba. Fawzaan ka na ganin yadda Rumaysah take ‘yar gatan Abba da Baffa, abu daya da na ke sonka da shi, shi ne kai min alkawarin za ka kula da ita, za ka kuma so-ta tsakani da Allah.” Gabansa ya yi mummunar faduwa, domin kuwa wani babban nauyi ne Baffa ya dora masa.
Fawzaan ya dago kai ya kalli Rumaysah, idanunsa ya lumshe sannan ya-ce. “Insha-Allahu, Baffa.” Da sauri Rumaysah ta kawar da kanta, saboda ta san ba ta da gaskiya, amma to yaya ta iya?
Nan ta fada kan kafafun Abba, ta sa kuka mai tsuma rai. Kaf! Jama’ar wurin sai da suka tausaya masu, saboda sun san irin shakuwar da ke tsakaninsu.3
Ta mike ta isa wurin su Radiyya da Yaya Khamsa’u, ta rungume sai kuka, da kyar aka bambaresu, Khadija ko haushi take ba ta saboda ta bata masu ran Momi. Radiyya ta kama hannunta suka nufi cikin gida tare da Yaya Zainabu.
Amma bugun duniyar nan, sun yi Momi taki bude kofar dakinta. “Yau me na yi wa kaina? Ranar da ya kamata ta zama ita-ce ranar da na fi kowa farin-ciki, ranar ne na ke kukan rashin mahaifiyata da kaunarta.
Sannan kuma ban san me zan tarar ba wurin Yaya Fawzaan wanda ko tantama babu, yana cikin matsanancin fushi da ni. Allah ka ga zuciyata Allah ka taimakeni.”3
Abba da ya ga sun dauki lokaci, ya shigo cikin gidan don ya ga me yake faruwa. Ai nan ya tadda su. “Ku wuce ku tafi kar ku yi dare.”
Khamsa’u ta-ce. “Abba Momi fa ta ki ta bude kofa, su yi sallama da Rumaysah.”
“Ku rabu da ita, da kanta za ta bi-ta inda take su yi sallamar.”
Sai da suka yi azahar, sannan suka fito, domin tafiya, Baffa da kansa da Abba suka sa su a gaba har mota, sannan suka koma ciki, zukatunsu cike da tunani.
Tafe suke ba wanda ya ce wa dan-uwansa kala. Direban Baffa ne ke tuki. Malam Yusufa wannan ya sa dukan su biyu suka zauna a baya. Fawzaan ya yi haka ne, don su Abba su amince da batunsa na cewa lallai zai kula da Rumaysah sosai.
Tun da suka dauki hanya. Rumaysah gefe kawai take kallo ko kuwa cikin hannunta wanda ta ajiye kan cinyoyinta, amma zuciyarta cike take fal!
Da tunanin irin hukuncin da Yaya Fawzaan ya tanada mata. Duk tsawon lokacin nan, sai jifa-jifa idan Fawzaan na waya ne take jin muryarsa. Amma banda haka, kala bai ce mata ba, har suka shigo Abuja.
Sun zo daidai wani (Check-point) ne, na shigowa gari. Direba ya ja birki sosai, wannan ya sa Rumaysah ta yi saurin kaiwa kujerar damka, sai aka yi rashin sa’a Fawzaan ma ya rike kujerar, saboda haka kan hannunsa ta dora nata.3
Ta kalli hannayensu daidai lokacin da shi ma ya duba, yana dagowa, suka hada idanu, sai a lokacin ne ta yi saurin janye hannunta. Shi ma ya dauke nasa hannun.2
“Malam Yusufa Guzape za mu wuce can gidana.” Ya fadawa direban, a tunaninta gidan Baffa zai ajiyeta tukun, amma koma ina ya ajiyeta, ba zai kawar da gagarumar matsalolin da take fuskanta ba, ga fushin Momi ga auren rashin so, ga tsanar Yaya Fawzaan.
Suna isa (Grand Emirates Apartments) ta karewa wurin kallo, daman duk ribibin da ake ta yi na cewa Yaya Fawzaan ya sayi gida, ita ba ta taba maida hankali ba ma bare ta nemi sanin inda gidan yake, (Terrace Duplex) ne gidan. Gaskiya wurin yayi kyau, sai dai kuncin dake zuciyarta, ya hanata ganin kyaunsa.
STORY CONTINUES BELOW
Fawzaan ya sauka ya bude gidan, sannan Malam Yusufa ya sauke akwatin (Trolley) din Rumaysa a cikin falo da wata karamar jakar cikin setin, ya fito yana masu fatan alkhairi. Fawzaan ya tsaida shi, yai masa alheri sannan ya-ce. “A huta gajiya, ka gaida iyali”.
Tana tsaye cak! Kamar gunki, a bakin kofar falon, har ya gama da Malam Yusufa ya shigo cikin falon, jakarsa ya ajiye bisa kujera, kare mata kallo ya yi, da gani a tsorace take da abinda yake cikin gidan, da Mai-gidan gaba daya.
Bandakin da ke falon ya nuna mata ya-ce ta shiga ta yi alwala. Fitowarta ta samu ya saka mata sallaya, don haka akwatinta ta bude ta dauki khimar, hankalinta a tashe, saboda wato ba ta da matsayin da zai gwada mata, koda dakinta ne ma.
Tsaki ta ja, sannan ta tada sallar. Tana gama biyan sallolinta, sai ga shi ya shigo. Ta mike ta nade mayafinta, ta mayar akwatin gyalenta ta mayar jikinta. Ba zato ba tsammani ta ji ya sunkumeta, sam ba ta san yaushe ya matso kusa da ita ba, bare ta ga lokacin da yake shirin dagata.8
Ya daga ta cak! A razane ta juyo tana dubansa, fuskarta dab nasa, numfashinsu yana gaurayuwa, sai dai maimakon ta ga wannan kallon sa mai razanarwan, sai ganin fuskar ta yi ba yabo, ba fallasa, cikin idanunta yake kallo, nan da nan ta sauke ganinta, bai tsaya ba har saman matakalar ya wuce da ita. Ba tare da ya furta mata komai ba.
Suna zuwa kofar farko cikin murmushi ya-ce mata. “Sa hannunki a aljihuna ki ciro makulli.” Ita don tsabagen mamaki ta kasa tabuka komai, ji take yi kamar mafarki take yi.6
Ya-ce “Come on go ahead, ko kin manta ke matata ta-ce yanzu? Ki na da iko da komai nawa?” Ya fada yana mata murmushi.10
Hannunta na bari ta sa hannu a aljihun rigarsa ‘yar ciki na gefe, tana taka-tsantsan ta ciro makullan ba tare da hannunta ya gogi jikinsa ba, juyawa ta yi ta yi setin kofar yadda za ta iya bude masu.
Hannunta na bari, ta kasa budewa da wuri ya-ce. “Kin san fa ba kamar takarda ki ke ba, ki na da nauyi so, ki yi sauri”.7
Suna shiga, nan ma ya wuce zuwa (Pent Floor) dinsa, wato asalin dakinsa kenan, a saman wannan. Wani irin kamshi dakin yake yi wanda har sai da ya sa ta lumshe idanu.
Ga ta ma’abociyar son kamshi. “Sannunki da zuwa dakina, ko da yake yanzu kam dakinmu zan ce ko?” Ba shiri ta dawo duniyar da take ciki yanzu, har yanzu yana dauke da ita, Ita dai tsabar rudani ya hanata furta komai.5
Kan lafiyayyar gadon dakin ya direta, shi ma ya zauna a gefenta daf! Kamar zai shige mata yana kallonta, matsawa ta yi baya cike da tsoro, idanunta sun kawo hawaye sun cika dam! Zuba ne kawai ba su yi ba. Fawzaan ko ya sake matsowa kafin ya ciro wayar sa ya mika mata,4
“Ga shi karba ki kira su Radiyya ki fada masu mun iso lafiya.” Ajiyar zuciya ta yi, sannan ta yi hamdala a ranta, kasancewar ba wata manufa ke gare shi ba. Za ta ce masa ga wayarta ne, a kasa a cikin Jakarta, ya sake mika mata.
A hankali ta karbi wayar, hannayensu ya gogi juna kadan, ga-rin karbar wayar. Ta matsa gefe can ta kira wayar. “Sis, yaya ku ke?”
“Kai ku yi shiru, Rumaysah ce. Hello Sis kun isa lafiya?”
“Eh, Alhamdulillah! Mun shigo gida ma yanzu.”
“To ya yi kyau, Abba ya-ce mu ma gobe za mu kama hanya.”
“Allah ya kai mu, ya kawo ku lafiya.”
“Ameen, yaya Yaya Fawzaan, yana farin-ciki?”
Rumaysah ta dan leka shi, ta saman kafadarta, ta gan shi ya zubo mata idanu, yana murmushi.
“Eh, to ga shi nan dai kamar yana farin-ciki.” Ta fada kasa-kasa, ita ma kanta ba ta yarda da hakan ba.
“Yaya gidan ki? Na san ya hadu kwarai, don na ji ranar su Muneera suna tadin gidan.”
STORY CONTINUES BELOW
Rumaysah ta dan tsume, amma ta san halin Radiyya, idan ba ta fada ba, ba za ta barta ba don haka ta-ce. “Yana da kyau, sai kin zo, sai ki gani. Yaya Momi ba ta tambayeni ba?”
Radiyya ta dan yi jim, sannan ta-ce. “Kar ki damu, Insha-Allahu za ta sauko tana hucewa da kaina zan kiraki, na hadaku ku yi magana.”
A sanyaye Rumaysa ta kashe wayar, tana juyawa ta tarar da Yaya Fawzaan a bayanta. Mika masa wayarsa ta yi, sannan ta-ce. “Na gode.” A sanyaye.4
Maimakon ya karbi wayar, sai ya mika mata hannu, alamar ta ba shi nata.
“Ki ba ni damar na gwada miki…” Ya yi shiru yana kallon yadda ta kusa shidewa don tsoro, “Na gwada miki dakinki.” Nan ne ta saki ajiyar zuciya.
“Yaya Fawzaan yanzu ka na so ka ce min ka mance duk abinda ya gudana, da abin da na yi na saba alkawarin da na maka da kuma dalilin da ya sani yin hakan? Ba ka yi fushi da ni ba?…” Ta fara magana, don tai masa bayanin dalilinta na yin hakan da ta yi, ne ya katse ta.
Murmushi ya yi irin na gefen nan. “Dadina da ke kin faye zama akan abinda ya riga ya wuce, yanzu ina miki maganar gina rayuwar mu, ta gaba ki na batun abin da ya wuce?3
Kar ki damu komai ya shige, yau ranar mu ce, don haka ba na son ki tuno komai, sai ni dake.” Jin hakan ya sa ta bi bayansa ya fara bayani.
“Kin ga da wannan wardrobe dina ne, amma tunda kin zo, yanzu na dama shi ne naki, na hagu kuma nawa. Kin ga wannan table din rubutun, ban cika amfani da shi ba.
Don haka ya zamo naki daga yau.” Ya kara janta zuwa jikin window din Terrace din gidan, “Kin ga nan na ke zama da yamma ina kallon filin gidan nan, ina shan shayi, yanzu kuwa za mu kalla tare.”6
Suna komawa cikin dakin, ya janyota kusa dashi ta fada jikinsa, sannan ya rada mata. “Yaya komai ya miki Bebin Abba?”
Rumaysah dai yadda ka san wata mutum-mutumi haka ta zame masa, yana rada mata wannan maganar, sai da ta ji tsikar jikinta ya tashi. Murmushin karfin hali kawai ta masa.8
Hannunta ya rike, ya rausayar da ita, ba ta ankara ba ta ji ya tura ta kan gado, ta kife akan fuskarta. Ranta ya yi masifar baci, ganin da gangan ya yi mata, don duka karfinsa ya sa ya tureta.
A hankali Rumaysa ta dago kanta tana dubansa. A take murmushin fuskarsa ya dauke ya yi dif! Fuskarsa sai tsantsan tsana da kyara, ya rankwafo samanta, kafarsa daya ya daura akan gadon.5
“To Gimbiya. Mafarki ya kare (Dream Is Over), mun dawo rayuwar asali, kuma hakikanin gaskiyar ita-ce kin shigo rayuwar kunci. Kin dauka za ki shigo rayuwar da komai zai tafi miki, yadda ki ka saba ne? Kin yi kuskure.23
Na amince na aureki, saboda na yi biyayya gasu Baffa, amma kar ki yi zaton ban manta wulaqancin da ki kai min ba, ban manta yaudarar da ki kai min ba, akan za ki samu Abba Ki fada masa ba kya so na, za a fasa auren mu. Don haka sai na tabbatar da cewa duk iya zaman da za ki yi a gidan nan, na tunatar da ke matsayinki a cikinsa, wanda kuwa bai wuce na mai adana min shi ba. Don me ya sa ki ka aureni?”
Kafin Rumaysah ta ba shi amsa ya ci-gaba da cewa “Sai da ki ka gama yawon ki a gari kin ga miji a bulus shi ne za ki like mini ko? Sannan for your kind information duk abin da ki ka gani a gidan nan baki da iko da shi. Welcome to hell Rumaysah.” Ya fada a dake.7
Hawayen da suke cike a idanun Rumaysah suka samu damar gangarowakan kuncinta, zuciya ta zo mata nan take daga inda take kwance kan gadon fuskarta kawai ta dago ta-ce.
“Kai ma ka san dalilin da ya sa na amince da auren ka, ka bar zargina, an fada maka mutuwar son ka ne ya sani auren ka? Idan zabi za a ba ni a duniya kaine mutum na karshe da zan aura.
STORY CONTINUES BELOW
Ni ina da dalilin da ya sa na amince na aureka, saboda ganin halin da mahaifiyata take shiga na batar hanya. kai kuma fa me ya sa ka aureni? Ko kuwa kai ma ba a ajiye ka aka tambayeka ko ka yi na’am da ni ba? Lokacin me ya hana ka musawa? Wani abu ne ya matse maka wuya da har za ka amince ka aureni? Har ka bari har aka daura auren, idan kuwa haka ne to kaine kafi laifi a wannan tafiyar.”6
“Ni ma an fada miki zan ko kusanci inda ki ke da sunan neman aure ne? Allah ya sawwaka” ya wuce bandaki abinsa cikin takunsa na isa. Ko da ya fito bai ganta ba.
Ya karkade gadon shi ya yi kwanciyarsa game da kashe wutan gefen gado. Yana rufe idanu ya ji an kunna wutan, a zabure ya zauna yana dubanta ta daura Kafarta daya akan gadon ta-ce masa.
“Sannan abu guda kuma, Ko da ka ce min ba ni da iko akan komai na gidan nan, ka bata, domin kuwa ban gwada maka cewa na amince ba, don haka dole ka kula da ni, dole ka dauki dawainiyata.
Domin ko za ka yi yaya ba za ka taba canza cewa ni matarka bace Barr. Fawzaan Lamido. Sannan da ka ce ka aureni, don ka yi biyayya ga su Baffa ne, alhali ka na sane sarai ba hakan bane ka daukar masu alkawari, to ni kuma bari ka ji dalilina na aurenka.
Na aureka ne Fisabilillah, saboda Allah na kulla alaqar nan kuma ina son ka san da cewa Allah na tare da ni, shi zai kareni daga duk wata cutarwarka.” Tana fadan haka ta fizge filo daya a gefensa, ta sa ta wurin kafafunsa ta yaye bargonsa, ta kwanta a gefensa sannan ta rufu.19
Mamaki ne ya hana Fawzaan magana, sai ma tsakin da ya ja ya juya daya bangaren ya ci-gaba da barcinsa.
Barci yake yi mai dadi, kawai can ya ji an saka masa kafa a fuska, a take ya farka ya ga kafar Rumaysah, ba shiri ya ture ya matsar da filonta da ita kanta can gefe, sannan ya-ce. “Tsabar rashin tarbiyya ma ko yadda ake kwanciya mai kyau, ba ta iya ba.”
Ya kara komawa barci, bai dade ba kuwa, shi ma ya maka mata kafar sa, a hannunta da kyar ta daga ta zauna, tana kallonsa, maganganun da ya sharta mata dazu kawai ta tuno musamman da ya kira zaman da za ta yi a gidansa da zaman gidan wuta.
4
“Hmm idan ka san wata, ba ka san wata ba, ba zan yi shiru ka cutar da ni ba, domin kuwa sai na gwada maka HUKUNCIN ‘YA MACE a gidan nan.”
Ba ta tashi farkawa ba washegari, sai karfe shida, saboda gajiyar hanya, tsabar mugunta Fawzaan ya tashi, amma ya ki ya tasheta, haka ta shiga bandaki ta dauro alwala, sai lokacin ta tuna ta bar Khimar dinta a falon kasa can.
Don haka ta sauka, anan kan sallayar ta yi sallah, tana cikin sallar ya shigo daga masallaci ya zauna zai yi karatun Alqur’ani. Tsayawa ya yi yana ganin ikon Allah. “SubhanAllah, yau na shiga uku yanzu haka zan zauna da matar da ko sallah bata iya ba?”4
Ya tambayi kansa. Take wani haushinta ya kara kama shi, ko da yake ya fi jin haushin kansa da bai daruncewa su Baffa ba, shi a dole wai biyayya. Dama me yake tsammani daga tarbiyyar Momi.
Tana idar da sallah, ta mike ta nade sallayar, sannan ta juyo ta ga Fawzaan a zaune, dauke kanta ta yi za ta wuce sama, saboda ta watsa ruwa ko za ta ji dadi.
“Ke, Zo nan”
Ranta a bace ta dawo ta tsaya masa “Ke haka aka koya miki a gidanku, idan kin tashi kin ga manya ba kya gaishesu ne?”
“Ina kwana.” Ta fada hade da dauke kanta
Harararta ya yi sannan ya mike ba tare da ya amsa ba. Haushi ya cika Rumaysah yaya zai sa ta gaishe shi sannan ya ki amsawa? Kinkimar akwatinta ta yi da kyar, ita ba abinda yake damunta irin dan karan yunwar da take ji.
Don mugunta jiya ko a hanya bai tsaya sun ci abinci ba. Kokuwa suke ta yi ita da akwatin har ta samu ta isar da shi hawan farko, nan ta shiga lekawa dakuna biyu ne anan da bandakinsu sai falo, don haka daki daya ta bude ta duba ga mamakinta kayayyaki ne a jere wasu kuwa suna cikin akwatuna ba dinkakku ba.
STORY CONTINUES BELOW
Don haka kanta a kulle ta bar wannan dakin, ta shiga daya dakin, shi ya fi kankanta amma bata ga kayan kowa a ciki ba, wannan ya sa ta ajiye akwatinta, ta ciro ‘yar karamar jakarta da kayan wankanta, suke ciki da su brush.
Ta shige bandaki, ba ta ji mamaki ba da ba ta samu heater a kunne ba, haka ta daure ta yi wankan da ruwan sanyi, sannan ta ji dadin jikinta, ta fito ta shirya cikin riga da wando.
Rigar ruwan madara mai (Peach Flowers) a jiki tana nan yala-yala da ita ta yadin chiffon, yai mata dadas! A jikinta tsawonsa iya kugu, sai wandon kuma mai laushi kalan madara ta saka.
Ta gyara gashinta ta-ci kwalliyarta, ta feshe jikinta da turare, daman gashinta kam tamkar an haramta masa kitso gyara yake sha da mayuka. Yau din ma gyara shi, ta yi ta sake shi a bayanta, ba tare da ta saka ribbon ba.
Ledan takalmanta ta bude ta dauki silifas marar nauyi, sannan ta sauka kicin ko za ta samu wani abu a kicin din, sai dai saukanta sai ta tarar da Aasim ya zo masu da abinci.
Fawzaan ya zare ido cikin ganin rashin mutumci, bayan tana ganin Aasim me zai sa ta tsaya wani gaisawa, bayan duk macen kwarai komawa za ta yi ta suturce jikinta, tsaki ya ja a ransa ya-ce. “Allah kadai ya san maza nawa suka gama ganinta a haka na tsaya bata lokacina.” Bai ce mata komai ba.4
“Yaya su Mama?”
“Lafiyarsu kalau. Ta-ce na tambaya ko akwai abinda ki ke bukata.”
Kallon Fawzaan ta yi sannan, ta yi murmushi. “A’a babu na samu duk abinda na ke so.”
Wane irin abu ya toshe masa makoshi, ya tsani yarinyar nan.
“To Aasim mun gode, ka cewa Mama mun gode za mu fito anjima Insha-Allahu.” Fawzaan ya yi saurin fada, don bai ga alama tana da niyyar shigewa ciki ba.2
Aasim ya tashi ya fita, yana fita, Rumaysah ta dauko plate ta debi abinci ta hada tea mai kyau sannan ta zauna kan tebur din cin abinci ta fara ci kamar ba gobe saboda tsabar yunwa. Dagowa ta yi ta ga yana kallonta “Meye ka sa min idanu haka, ga can naka a food flask kar ka cinye ni da idanu.”
Girgiza kai kawai ya yi ya fice daga gidan gaba daya, “Oho, Kai ta ya shafa.” Sai da ta gama ta zo tattara kwanukan ta kai kicin.
Sai ta ga ashe duka ta juye, wani irin kunya ta kamata. “Maganinsa ba shi ya hana mu cin abinci ba, a hanya jiya, shi ya sani sai ya kara zama da wata yunwar ai.”4
Haka ta sha zamanta, can suka yi waya da Radiyya akan sun taso daga Gusau. Ta yi ta kiran Momi a waya, amma ba ta dauka hakan ya sa ta hakura ta bar bugawa.
Tana kwance kan doguwar kujera ba ta san lokacin da barci ya dauketa ba, sai ji ta yi an daka mata duka a kafafu. Da sauri ta farka ta zauna, tana sosa wurin, harararsa ta yi, ta san ai dama sai shi ne zai mata wannan wulakancin. “Meye za ka zo ina barci, ka kama ka hana ni?”
“Ki tashi ki dafa min abinci, yunwa na ke ji.”
Wani irin kallo ta watso masa. “Ni zan dafa maka abinci? Ka fita dai ka saya ko ka yi yadda ka ke yi da, tunda ai da da yanzu ba banbanci.”
Haushi ya kama shi, ga shi ba yadda za ayi ya-cewa Mama zai zo cin abinci, don haka Tea kawai ya hada ya zauna ya sha.
Rumaysah kuwa sai danne-danne take yi a wayarta. Kowa na mamakin aurenta farat daya. Firdausi ce ke mata tsiya. “Amarya a gidan Yayan mu, yaya ki ke?”
Ta tura mata amsa. “Lafiyata kalau, yaya son ranki.”
“Wuu! Na yi shiru. Idan kin gama amarcin, ki turo min address dinku, sai mu zo mu ga gidan ni da oga.”
“Ko yanzu ki ke so ki zo, don ina zaune ba abin yi dama.”
“Hmm! Zuwa dai jibi haka Insha-Allahu, kafin nan kin fara gane kan gidan naki.”
STORY CONTINUES BELOW
“Allah ya kai mu, ki gaida Mai-gidan.”
“Kin san jiya yake fada min wai Saleem a Gusau ya kwana, da ya ji labarin auren ki?”
Sai da gaban Rumaysah ya fadi, don har ga Allah har yanzu ba ta mance shi duka ba, sai dai ta maye son da take masa da tsanarsa. “Ya ji dadi lokaci ne ya ishe shi ai.”
“Haba ke ko tausayinsa ba kya ji?”
“Wani tausayi rabu da shi, shi bai tausaya min ba sai ni?”
“To shi kenan. Allah ya ba ku zaman lafiya ki gaida angonki.”
Yana kallonta sai danne-dannen waya take yi. “Ki tashi ki sa kaya, za mu je gidan Baffa.”
Ba ta ko kalle shi ba, ta mike ta tafi daki, abaya ta sa akan kayan nata ta dauko jakarta, sannan ta fita.
A rashin saninta bai bude kofar motar ba ashe, ta je ta ja da karfi. “To Malama, dakata sai kin balla min mota ne? Ke kullum ba kya koyan abu duk randa ki ka balla min. Wallahi zan saba miki.”
“Ka san ba ka bude ba,ka ce na shiga?”
Remote ya sa ya bude, sannan ta ja ta bude.(Sun glass) dinsa ya mayar ido kawai,ya shiga mota. Haka suka tafi kowa na jin zafin Dan-uwansa, ba don Mama zai je gayarwa ba,da bai ga me zai sa shi tafiya da wannan yarinyar a motarsa ba.
Mama ko farin-ciki ne fal! Ya cika ta da ganinsu tare da ta yi, dukka kamar wani hadin baki sai suka shiga sakin fuska, tamkar babu komai. “Ai ko da yanzu na ke cewa zan tashi Malam Yusufa, ya kai maku abinci.”
“Mama, ai da kin bar shi ma kawai ta-ce, za ta a yi da kanta.” Ba shiri Rumaysah ta dago idanu ta dube shi, wani murmushi, yai mata. Mama ko tana ganin haka sai ta zaci ai ya huce ne yake wa Rumaysan fara’a.5
“A’a Rumaysah, an taba haka, ki bari dai ki huta zuwa wani lokaci, sai ki fara. Su Furera da Laminde sai suna sa maku wannan ba matsala bane, idan ya so, sai kuna yin Breakfast a wurin ku.”
Da sauri Rumaysah ta-ce. “To Mama, shi kenan tunda kin ce haka.”
Cikin lokaci kadan an wadata su da abinci da kayan itatuwa. “Bari na yi sallah kafin ku kammala.”
Mama na tashi Rumaysah, ta kai masa mugun kallo, har da wani cewa ta-ce za ta yi aiki ko yaushe suka yi hakan da shi, oho?.
Tsaki ta ja a bayyane. Fawzaan bai kula ta ba, ya tashi da niyyar wucewa masallaci sallar azahar. Sai da Mama ta idar ne, ta ce Rumaysah ta shiga dakinta ta yi sallah.
Tana jin shigowarsa falon Maman ta yi zamanta a ciki, har dai ya leko ya-ce. “Asuba ne kawai ake masa dungure?” Manufarsa ta dade kenan.
Ba ta ba shi amsa ba, don haka ya-ce. “Idan kin gama ki zo mu tafi.”
Bakinta ta zumbura ta-ce. “Yanzu ba za mu jira su Abba su iso ba sai mu tafi?”
“Ina da wurin zuwa, ki bari sai wani lokaci sai mu je.”
“Kai dai kawai ka ji dadi, ka ga Mamanka, ni kuma ko oho”.
“Oh, ke ba Mamanki bane?” Ya fada yana mata kallon tuhuma. Mikewa kawai ta yi ta shirya, sai da ta kara gyara fuskarta, sannan ta fito falon. Suna fitowa falon ta-ce. “Mama ki na jin Yaya Fawzaan, wai yanzu za mu tafi?”
Kut! Yarinyar nan ‘yar rainin hankali ce, ya fada a ransa. Mama ta-ce. “Gaskiya Fawzaan iya wunin kenan? Da ka bar ta anan ka tafi sabgoginka, idan ka dawo sai ku tafi.”
“Ni gaskiya Mama idan na tafi ta can, zan wuce gida, sai dai Aasim ko wani ya maidota.”
Jin haka ya sa Mama ta-ce. “Yi hakuri ki bi-shi ku tafi. Ko da wani abin da ki ke bukata a gidan?”
Kai kawai ta girgiza mata, sannan ta amince suka tafi tare. Shi idan so suke yi ma sai ya kauro da ita gidan Maman su karaci zamansu a can.
“Wani abu ka ce?”
A tsume ya-ce mata. “Babu.” Suna cikin tafiya ne, wayarsa ta yi kara, a dokance ya daga. A (Hands-Free) ya saka kasancewar yana tuki. “Yaya dai Rayyan me ake ciki ne, duk ka sa na kagara da jin amsarka.”
“Ai mutumina kwantar da hankalinka, komai ya yi saiti, sai dai kawai mun hadu anjima Insha-Allahu za ka ji Details.”
“Zan ji details ko zan je na ga zahiri, na san na kama dahir?”
“Ba ka da kyau, kai ka faye gaggawa Wallahi, ka na ango me ya kai ka daukar wani abin daban, kuma bayan ga ka da sabuwa dal a hannu.”
Fawzaan ya juya bangaren Rumaysah ya yi murmushi, sannan ya ci-gaba da magana. “Ka san wasu sabbin abubuwan suna suka tara, masu tsadar ba su shigo hannu ba tukun, nan ne za a gane bambancin.”
“Mugu, ba ka da kyau. Na kusa na canza Party fa.”
“Gwamma dai ka kama na gasken, don kuwa canji ba abinda zai kara maka.”
Tana jin hirarsu kaf! Wato ma Yaya Fawzaan ita yake kira da suna ta tara, kuma wa abokansa, ai wannan ma zubar mata da kima yake yi, zai mata wulakanci ko ya gwada mata rashin so, to ya yi hakan mana tsakaninsu su biyu.
Yana ajiyeta a gida, ya yi ficewarsa, bai dawo gidan ba sai da dare, lokacin ta yi wankanta ta shiga kitchen, ta dafa abincinta dan daidai. Har ta gama kallonta a falo, bai shigo ba.
Don haka sama can ta wuce ta yi kwanciyarta. Ba ta dade da kwanciyar ba, ta ji motsinsa, amma ta yi kamar barcinta ya yi nisa.
“Yanzu wannan karfi da ya ji, ta gajewa mutum daki.” tsaki ya ja ya bude wardrobe dinsa ya dauki kayan barcinsa, ya fice daga dakin, ita kuwa Rumaysah ta kara bararrajewa ta-ce. “Ka ji da shi ai.”
***********
So what do you think?
Best scenes? 😉
4
Mu hadu a ci gaba don ganin yanda zamansu zata kaya.
I love fiesty Rumaysah, Fawzaan is so mean.😂
7
Bayan kwana biyu, Abba ya yi masu waya ya-ce masu zai zo ya duba su ko suna gida. Haba Rumaysah murna kamar meye, don haka da sauri ta shige bandaki, saboda ta watsa ruwa kafin Abba ya iso ta kammala komai. Tana gama shirinta kawai, sai ta taba kofar dakin, ta ji ta gam!
Ta sake ja, ta ji a kulle. Tana duba wurin makulli, ta ga babu a jiki. Ranta ya baci ta nufi wayarta domin ta fadawa Yaya Fawzaan ya zo ya bude kofar. Wasa, gaske kawai sai ta nemi waya ta rasa.
Karar tsayuwar mota ta ji, ta leka ta windon dakinta kawai ta ga Abba. Haushi ya kamata sosai, saboda Fawzaan ta gani ya fita ya tarbe shi zuwa ciki. Tana jira ta ga ya zo ya bude mata kofa ne, kawai ta ji shiru.4
Kuka kawai ta saka tabbas wulakancin Yaya Fawzaan ya wuce duk inda take tunani, yaya za ayi tana ji, tana gani Abba ya zo, sannan ya hana ta ganin sa ko ta gaishe shi?
Akan idanunta Abba ya tafi. Bakin-ciki ne dankare! A zuciyarta, kawai sai ta ji ana bude kofar dakin, goge hawayenta ta yi tana ganinsa ya jinginu da jikin kofar ya-ce. “Abba ya-ce a gaishe ki.”17
“Wane irin abu ne haka, bayan ka san zai zo, sannan za ka kama ka kulle ni a daki da gangan?”
“Wani lokacin kwa gaisa, na ga ba ki fara kewar gida ba tukun na. Har yanzu dadi ki ke ji, randa ki ka nemi tafiya da kanki sai ki je ku gaisa, for now, babu bakin da za su zo gidan nan ki gansu.”4
Maganarsa ta ba ta mamaki kwarai, hakan ne ya hanata iya furta komai, tana gani ya juya ya bar mata dakin, zama ta yi cikin fushi kawai akan gadon, ta fara aikin hawaye, daga bisani ta goge ta mike ta fita.
Kai tsaye ta haye sama dakinsa ta-ce. “Abu na farko da ya kamata ka sani shi ne, nan gida na ne kamar yadda yake gidan ka. Kuma Abba ba bako bane, duk kuma wanda na ga daman gani.
Zan gan shi a lokacin da na ke so. Bar ganin ina maka shiru–shiru, ka dauka ba ni da hanyar rama abin da ka ke min ne, da ne na ke tsoronka, amma tunda ka gwada min (True Color) dinka ni ma ka jira ka gani.