BA SONTA NAKE BA
CHAPTER 8
FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
Ana saura kwana biyu Zara ta fara examz ne ta tashi da ciwon cikinta na mamaki.+
Aikuwa tun da safe da tayi wanka ta kimtsa kanta komawa tayi cikin bargo.
Haka ta dinga fama da ciwon cikin.
Tun da safe Farouq ya fita a dalilin yana da surgery har kashi biyu.
Ruqayya kuwa itama tana kammalawa ta fice abinta.
Daya daga cikin masu aikin gidan ce ta qwanqwasa qofar Zara ta shiga. Zara wadda take cikin bargo ta dan zaro kanta don gani ko waye.
Da sauri mai aikin ta duqa tace “ina wuni Anty Zara” muryarta qasa qasa tace “ki hado mun tea ki kawo” sannan ta nuna mata wata drawer tace “ki duba cikin drawer dinnnan ki dauko mun magani”
Da sauri ta miqe tana fadin “toh Anty” yayinda ta yi yadda Zara ta umurce ta.
Zara dai ko da ta sha maganin da tea komawa tayi cikin bargo. Gaba daya yinin ranar a kwance tayi shi, shiga kewaye ne kadai yake tada ta daga kwanciya.
Bayan sallan magrib ne Farouq ya dawo gidan. Ko da ya shiga Ruqayya ce kadai ya tarar wadda tare suka wuce sashen shi.
Yayi mamakin rashin jin motsin Zara domin kuwa ya kula yinin yau bai ga pogress report dinta ba sannan bata turo mishi hoto ba.
Ya so ya tambayi Ruqayya amma sai ya matse. Text message ya tura mata sannan ya cigaba da harkokin shi.
A lokacin da saqon ya shiga wayar ta tana bacci. Ko da ya ji shiru hankalin shi ya dan tashi amma kuma sanin cewa jarabawarta ta kusa ne yayi tunanin ko ta kulle kanta a daki ne kamar kullum.
Suna bisa dinning ne ya kasa jurewa ya tambayi Ruqayya “ina Zara ne ban gan ta ba” cikin bacin rai Ruqayya tace “tana dakin ta, hala karatu take yi” daga nan bai qara yin Magana ba.
Wuraren qarfe tara saura ne Zara ta farka daga bacci. Bathroom ta shiga ta samu hot bath sannan ta fito ta kimtsa kanta.
Tana tsaye tana fesa turaruka ne tayi tunanin duk yau bata ga yayan nata ba don haka ne ta fita don zuwa ganin shi.
A lokacin da Zara ta fito babu kowa a qasa don haka ne ta wuce sama, bata qarasa shiga falon bane ta hango su zaune bisa kujerar falon yayinda Ruqayya take ta jefa ma Farouq kisses kamar zata cinye shi.
Tsaki Zara tayi a ranta tana fadin “mayya kawai”
Juyawa tayi rai a bace ta koma dakinta ta shige bargo.
Wayarta ta dauko da niyyar kiran Mahmood ko ta samu ya faranta mata rai.
Kafin ta kira ne ta ga text message din Farouq kamar haka:
“Hey sis, where have you been today? Hope you good?”
Turo baki tayi tace “bayan ka tafi wurin matarka ka bar ni”
Can kuma sai na ga tayi shiru sannan tayi murmushi tace “zaki gane cewa ni karuwa ce”
(Whoa… me kuma Zara zata yi??🤣)
STORY CONTINUES BELOW
Reply ta tura ma Farouq kamar haka:
“big brother yau throughout ina daki bana jin dadi, cikina yana ciwo”
A lokacin da message din ya shigo tuni Ruqayya ta tumurmushe shi. da qyar ya kauce ya duba wayar inda ya karanta text message din Zara.2
Nan da nan yace “subhanalillah, Zara batada lafiya a gidan nan bamu sani ba?”
Da sauri ya miqe yayinda Ruqayya ta ji kamar ta sa hannu akai ta dinga rusa ihu.3
Miqewa tayi ta bi bayan shi don ganin sabon iskancin da Zara zata zo da shi.
Ba tare da qwanqwasa kofar ba ya shiga ya tarar da ita kwance bisa tiles a cikin bargo.
Cikin hanzari ya qaraso wurinta yayinda Ruqayya ta tsaya tana kallon ikon Allah.
Bargon da ta rufe kanta da shi ne ya dan ja ya bude fuskarta.
Kallon shi tayi murya qasa qasa tace “Ya Farouq” cikin damuwa yace “why didn’t you call me?”
Zara ta dan juya ta kalli Ruqayya sannan ta kalle shi tace “Ya Farouq to ai na saba, it’s just menstrual cramps”
Ruqayya ta zaro idanuwa cikin tsananin mamaki a ranta tace “lallai yarinyar nan ‘yar iska ce, yanzu tana al’adar ma har sai ta fadi mishi”
(Ni kuwa me zanyi banda dariya🤣🤣)
Farouq ya miqe tare da fadin “let me get you some drugs”.
Ruqayya ce ta matso kusa da ita tace “lallai kuwa yau na tabbatar baki da hankali, raguwar banza kawai, kina al’ada saboda ragwanta sai kowa ya sani”
Zara dai murmushi tayi tace “toh cikina yana ciwo, ya kike so inyi?” Ruqayya ma saboda takaici kasa magana tayi.
Farouq ne ya shigo riqe da magani da ruwa ya zauna gefenta ya bude ya bata.
Zara dai tana ji tana gani ta sake shan magani har tana Addu’a Allah yasa kada ya zama overdose.
(Habawa🤣)
Bayan ta sha ne ya kalle ta yace “koma kan gado ki kwanta, bana so kina kwanciya a qasa”
Zara ta miqe ahankali har tana dafa cikinta tana fadin “ooouch” yayinda Farouq ya gyara mata pillow yace “sorry, I think yakamata inyi Magana da gynaecologist dina in ji if she has something to give you wanda zai yi relieving wannan pain din naki for good”
Ruqayya ce tana zabga ma Zara harara tace “haba Honey, wannan ai ba wani abun damuwa bane, abu ne da ko wacce mace take yi”2
Girgiza kai yayi yace “amma ai ita Zara tana wahala” ya juya ya kalli Zara wadda take kallon su yace “call me if you need anything” murmushi tayi tace “thank you big brother” ta kalli Ruqayya tace “thank you Anty Ruqy” sun juya zasu fita ne Ruqayya ta juyo ta Harare ta yayinda tayi mata gwalo.
Suna fita kuwa ta fashe da dariya.
************
A yanzu kam Zara tana jin dadin zaman gidan Farouq domin kuwa duk wata hanya ta zata bi ta bata ma Ruqayya rai sai ta bi shi.
STORY CONTINUES BELOW
Ita kuwa Ruqayya ta rasa yadda zata yi da Zara, ga cikinta da yake dan bata matsala wanda yakan sa ta kwanciya bata shirya ba.
Tuni Zara ta fara examz, karatu take yi sossai. domin kuwa Zara akwai son karatu. Bata qaunar ta je rubuta jarabawa bata san abinda zata rubuta ba don haka ne bata wasa.
***********
Akwai wata ranar Saturday da daddare Zara tana kwance a dakinta tana duba instagram page dinta kamar kullum ne ta ji kawai tana son shan ice cream.
Kiran Farouq tayi a waya wanda kamar kullum bai amsa ba. sai kusan bayan minti goma ne ya kira ta yace “hey sis how are you?”
Murmushi tayi cikin shagwaba tace “I am fine Ya Farouq, please in ce ma driver ya kaini Frozenscoop?”
Shiru ya dan yi sannan yace “bani thirty minutes zan zo in kai ki, get ready”
Cikin mamaki tace “dagaske Ya Farouq?” yace “yes”
Tace “thank you so much, you are the best, I love you”
A lokacin da Farouq ya dawo tuni Zara ta shirya.
Kiranta yayi a waya ta fito daga dakinta.
Ruqayya wadda take kwance a daya daga cikin kujerun falon ne ta ga Zara ta fito.
Cikin mamaki ta kalli Farouq tace “ina zaku je ne haka?” Yace “frozenscoop, ko zaki je ne?”
Zara dai addu’a ta dinga yi kada ta biyo su don bata son harkar Ruqayya.
(Kun ji qarfin hali wurin Zara, mata da mijinta🤣)
Cikin qunar rai ta kalle shi tace “sai kun dawo”
Farouq ya duqa yayi mata kiss sannan ya shafa cikin ta yace “I love you”
Zara ce tayi saurin kallon shi yayinda yanayin fuskarta ta canza, wucewa tayi ta fita tana jiran shi a waje.
**************
A kan hanyar su ne Zara tana ta chatting da Mahmood a waya sai gani nayi ta kalli Farouq tace “Ya Farouq meyasa ni kullum idan na ce maka I love you baka acknowledging?”
(Kai.. lafiyar Zara kuwa??🙄)
Murmushi yayi yace “do you even know what it means?”
Tace “eh mana, you are my brother and I love you, its as simple as that”
Girgiza kai yayi yace “I guess you are more crazier than I thought” fashewa tayi da dariya.
Gidan su Mukhtar suka fara zuwa.
MUKHTAR ABUBAKAR MANSION
Hafsat da Mukhtar sunyi mamakin ganin Farouq da zara ba tare da Ruqayya ba.
Zara da Hafsat suna zaune a dakin Hafsat din ne tace “wallahi bestie da kuka shigo sai nayi muku kallon couple, kunyi bala’in dacewa”
Zara ta fashe da dariya tace “inaa, ya dai fi dacewa da matar shi. ni kam sai Mahmood”
Hafsat tayi tsaki tace “Ni dai Allah ya sani bana sonki da wannan yaron” Zara ta harare ta tare da turo baki.
STORY CONTINUES BELOW
Mukhtar kuwa a falo ya kalli Farouq yace “abokina ya na ga ka fito da babe ka baro wifey a gida?”
Girgiza kai Farouq yayi yace “toh sarkin sa ido, ice cream take so shine zan kaita”
Mukhtar yayi murmushi tare da matsawa kusa da shi yace “how romantic my friend, kayi sauri dai kayi signing dinta kar garin kallon ruwa kwado yayi maka qafa”
Farouq dai dafe kai yayi ba tare da yace komai ba domin kuwa a ‘yan kwanakin nan ya daina denying din Zara kamar yadda yake yi a da.
Abinda ya sani shine yana jin Zara har cikin ranshi wanda ya kasa fahimtar dalili.
Zara ta shiga rayuwar shi fiye da tunanin dan adam don yanzu haka komai nata birge shi yake yi amma fa banda surutun ta.
(Shin an zo wurin ne ko kuwa??🙄)2
Sun dade a gidan su Mukhtar sannan suka yi sallama suka tafi Frozenscoops.
**********
Ruqayya kuwa tunda suka fita take cike da bacin rai kamar zata mutu.
Mamaki take yi yadda tana ji tana gani Zara zata shigo mata gida ta lalata.
A yanzu haka abubuwan da Zara take yi mata sun kusa sa ta kamu da hawan jini.
Dole ne ta dauki babban mataki a kanta.
A yanzu haka qawarta Aliya take jira ta dawo daga tafiyar da tayi don ta taya ta neman mafita tunda dai Hajjaju ta gargade ta akan kada ta sake ta yi qoqarin salwantar da Zara a gidan ta domin kuwa hakan na iya janyo mata sharri.
FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
Washegari tun da safe Zara ta tashi ta hada French toast wanda har ta gama masu aiki suna mamakin irin abincin da Zaran take dafawa a gidan wanda suka kula mai gidan yana jin dadin kalolin abincin.
Kamar kullum da suka zauna bisa Dinning French toast din da zara tayi shi Farouq ya ci wanda itama shi ta ci.
Ruqayya ce ta dinga bin Zara da harara wanda yasa Zarar tayi murmushin mugunta tace “Anty kin taba trying French toast dinnan kuwa? Kinyi missing gaskiya”
Ruqayya tana hararar ta tace “ai ni kin san irin wadannan basu dame ni ba”
Zara ta kalli Farouq tace “Ya Farouq idan na gama last examz dina gobe zan yi maka Fruit Pizza, kana so?”
Yana murmushi yace “ofcourse little one, kin san anything fruit is bae” yayinda ya miqe yace “I am late sai na dawo”
Yayi ma Ruqayya kiss a kumatu yace “take care”
Da sauri Zara tace “ni fa?” wani mugun kallo Ruqayya tayi mata yayinda Farouq ya girgiza kai yana murmushi, itama murmushi tayi tace “sorry, just kidding”
(Ni dai ina nan a maqale ina kwasar dariya🤣🤣)
Bayan Farouq ya fita ne Zara ta qarasa cin abincin ta sannan ta miqe zata tafi dakinta don yin karatu.
Aikuwa Ruqayya ce ta janyo ta tare da fadin “zo nan dan uban ki, ni zaki wulaqanta a cikin gidana?”
Zara wadda ta cika da mamaki tace “Madam Ruqs ki qyale ni in tafi, kin dai ga kina fama da qaton cikin ki…”
Ruqayya ce ta dakatar da ita tace “rufe mun baki karuwar yarinya, kin zo zaki lalata mun gida, toh bari in fada miki wannan shine last warning da zan baki idan kika kuskura kika qara tabo ni sai na lalata miki rayuwarki”
A lokacin da suke wannan hayaniyar ne Farouq ya dawo domin daukan wasu files da ya manta.
Jin hayaniya ne yasa ya matsa don jin abinda yake faruwa.
A kunnuwan shi kuwa ya ji Zara tace “wai ke in tambaye ki, a tunanin ki zaki iya yin takara da ni? Kalli tsari na ki kalli tsarin ki, I have curves all over and you don’t, you are just flat all over. Kin dai san da ni Ya Farouq ya aura ko kallon ki ba zai yi ba ko?”
Tayi murmushi ta cigaba da fadin “Toh albishirinki, ni ba son mijinki nake ba… kuma ban taba son auren shi…”
Kafin ta qarasa ne ta ji saukan mari a kumatun ta wanda ya sa har ta duqe qasa.
**************
Duqe take yayinda take ta rusa kuka a dalilin marin da Farouq yayi mata wanda hatta Ruqayya ta girgiza.
Cikin fushi da fada yace “kina da hankali kuwa? A cikin gidana kike zagin mata ta? who gave you that right? You are very stupid”
Cikin kuka Zara ta matsa kusa da shi tace “don Allah Ya Farouq kayi haquri, wallahi Anty Ruqayya ce”
Tsawa ya daka mata inda yace “shut up” ya nuna mata hanyar fita yace “tashi ki bani wuri kafin in fasa miki baki”
Zara tana kuka ta ruga dakin ta yayinda Ruqayya tace “Honey wallahi yarinyar nan bata jin Magana, kasan fa..”
Hannu ya daga mata sannan ya wuce ran shi a bace.
Ko da ya dauki files dinshi wucewa yayi ya fita.
Ruqayya dai bayan ya tafi ta fashe da dariya yayinda ta ruga a guje zuwa dakinta don kiran qawarta a waya domin ta bata labari.
**********
Zara kwance a bisa gadon ta tana ta rusa kuka.
Marin da Farouq yayi mata ba shine yayi mata zafi ba, fushin da yayi shi ya tada mata da hankali.2
Hannuwan ta na rawa ta janyo wayarta ta kira shi amma har ta gama ringing bai dauka ba.
Haka ta dinga kiran shi tana kuka amma bai daga ba, ta tura mishi text messages bai yi replying ba.
Zara dai ko wanka bata yi ba ta sanya hijabi dogo har qasa sannan ta dauki wayarta ta fita.
Drawer din da Fraouq yake ajiye makullan motocin shi ta nufa ta dauki daya ta fita.
Masu aiki dai ganin yau Zara ko gaisuwar su bata amsa bane yasa suka san lallai akwai matsala.
**********
Da taimakon Allah ta isa gidan Hafsat lafiya domin kuwa tana tuqi ko kallon hanya bata yi yayinda take ta kiran Farouq a waya wanda baya dauka.
MUKHTAR ABUBAKAR MANSION
A lokacin da ta isa gidan kuwa Hafsat tana ta karatu.
Hafsat dai ganin qawarta tayi ta shigo tana ta rusa kuka.
Cikin tashin hankali ta riqo ta tare da rungume ta tana fadin “babes lafiya? Me ya faru?”
Zara dai kuka takeyi kamar ranta zai fita tace “Ya Farouq” Hafsat tace “me ya same shi?” Zara ta fara bata labarin abinda ya faru tun daga farko.
Ji tayi Hafsat ta ja tsaki wanda ya bata mamaki.
Hafsat tace “toh wai ke a tunanin ki saboda Anty Ruqy ya mare ki?”
Zara tana kuka tace “bestie baki ga yadda ya ji haushi bane”
Hafsat tayi murmushi tace “kin san cewa Ya Farouq ya mareki ne saboda kin ce ba sonshi kike ba?”
STORY CONTINUES BELOW
Zara ta zaro idanuwa tace “wallahi bestie..”
Hafsat ta katse ta tare da fadin “shut up babes, yanzu dai abinda nake so da ke shine ki tashi mu je kiyi wanka ki zo muyi karatu. Kin dai san examz din gobe mai zafi ce”
Zara dai ko da tayi wanka suka zauna karatu da ta fara sai ta dauki wayarta ta kira Farouq amma shiru. Hafsat dai tana yi tana kallon qawarta, bata ankara ba sai gani tayi ta fashe da kuka tare da wurgar da littafin da yake hannun ta.
Cikin damuwa Hafsat ta rungume Zara tana ta bata haquri amma inaa, kamar ma ziga ta take yi.
CENTRAL HOSPITAL
Zaune yake a ofis dinshi tun safe ya kasa yin komai.
Maganganun da Zara tayi ne suke yawo a qwalwar shi. runtse idanuwa yayi da ya tuno marin da yayi mata.
Wayar shi ya dago yana ta duba messages din da ta aiko mishi na ban haquri wadanda ya kasa replying ko daya.
Mukhtar ne ya qwanqwaso qofa ya shigo. Har ya zauna abokin nashi bai sani ba.
Ganin haka ne yasa Mukhtar ya dan miqe ya taba shi, da sauri Farouq ya dawo da hankalin shi kan abokinshi tare da sakin ajiyar zuciya.
Cikin mamaki yace “abokina yaushe ka shigo?”
Mukhtar yayi murmushi yace “me ke damunka?”
Farouq ya ajiye wayar shi a kan tebir din yace “nothing man”
Kallon da Mukhtar din ya tsare shi da shi ne yasa yace “okay, I slapped Zara this morning kuma I am not happy about it”
Mukhtar ya zaro idanuwa yace “what? Why?”
Farouq ya bashi labarin abinda ya faru yayinda Mukhtar ya fashe da dariya har Farouq din yana mamaki.
Mukhtar ya gyara zama yace “abokina saboda yarinyar tace ba sonka take ba sai ka mare ta?”
Farouq cikin mamaki yace “baka ji labarin da na baka bane? Mata ta fa ta zaga”
Tsaki Mukhtar yayi yace “we both know cewa ba abinda yasa ka mare ta kenan ba but anyways kayi mata haquri, ka dai san gobe tana da examz kuma yanzu haka ko karatun ma ta kasa yi, I am sure”
Kafin yayi Magana ne wata nurse ta shigo ofis din cikin sallama tace “sir, the patient is ready”
Bayan Farouq yayi dismissing dinta ne ya kalli abokin nashi yace “I have a surgery to perform yanzu”
Mukhtar ya miqe yace “nima bari in qarasa ofis, ina da meeting nan da awa daya but please kayi mata haquri i beg you”
Farouq ya dauki kayan aikin shi yayinda ya harari abokin nashi wanda yake yi mishi dariya sannan suka fita tare.
FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
Wuraren qarfe shidda na yamma ne Zara ta dawo gida domin kuwa kasa karatu tayi a gidan Hafsat din.
Babu abinda ta ci a gidan Hafsat din, rabonta da abinci tun breakfast din safe. babu yadda Hafsat bata yi da ita ba akan ta ci wani abu amma ta qi.
Ko da ta shiga gidan dakinta ta wuce ta nufi bathroom tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wandon sweatpant da wata polo t-shirt.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan tayi sallan magrib ne tayi kwanciyarta a nan bisa sallayar.
Tana nan kwance aka kira sallan isha’I, ko da ta idar litattafanta ta janyo ta bude amma inaa, ta kasa fahimtar komai.
Gani nayi kawai ta fashe da kuka.
Wayarta ta dauka ta sake kiran Farouq amma har ta gama ringing bai dauka ba.
**********
Ruqayya dai tun abinda ya faru da safe yau jin ta take yi cikin farin ciki marar misaltuwa.
Hatta Hajjaju sai da ta kira ta a waya ta bata labari.
Itama tun da safen da ta tafi wurin Musty sai da yamma ta shigo gidan.
Sashenta ta shige ta cigaba da harkokinta ba tare da ta waiwaye Zara ba.
***********
Wuraren qarfe goma na dare ne ya dawo gidan.
Ko da ya shiga babu kowa a main palour.
Har ya kama hanyar sashen shi sai kuma na ga ya tsaya yana tunani.
Gani nayi yayi ajiyar zuciya sannan ya dawo ya nufi hanyar dakinta.
Qwanqwasa qofar yayi sannan ya shiga. Ganin ta yayi kwance bisa daddumar sallah yayinda ta rufe fuskar ta da hannuwan ta, da alama kuka take yi.
Shiru yayi yana kallonta yana mamakin yadda a yanzu baya ko son ya ga Zara tana cikin damuwa balle kuma kukanta.
Hankalinshi a tashe ya nufi wurinta ya tsugunna a gaban ta yace “hey”
Jin muryar shi tayi kamar daga sama.
Aikuwa nan da nan ta tashi zaune yayinda hawaye ke bin fuskar ta.
Miqewa yayi tsaye yana kallonta yace “have you been crying?”
Da sauri ta miqe ta rungume shi cikin kuka tace “don Allah Ya Farouq kayi haquri, wallahi bazan qara ba. zan je in ba Anty Ruqayya haquri idan dai zaka yafe mun”
Farouq dai kasa motsi yayi domin kuwa har cikin ran shi yake jin kukan ta.
Da qyar ya banbare ta daga jikinshi ya dan tura ta baya yace “its okay”
Ajiyar zuciya tayi tace “nagode Ya Farouq” yayinda take ta share hawayen ta.
Gani yayi ta duqa ta kwashi litattafan ta zata fara karatu.
Girgiza kai yayi yace “kin ci abinci?” tace “a’a” yace “ina jin yunwa, mu je ki dafa mana wani abu and I will help you with this” ya nuna mata littatafan ta.
Da sauri tace “dagaske Ya Farouq?” ya girgiza mata kai alamar eh.
Cikin murna ta bi shi suka fita.
***********
Zaune yake a kicin island yayinda take a tsaye, tambayar shi tayi “me zan dafa Ya Farouq?”
STORY CONTINUES BELOW
Kallonta yayi yace “anything” tace “bari in dafa Minced beef pasta”
Zaro idanuwa yayi yace “what?? Kin dai san bana son pasta ko?”
Murmushi tayi tace “kar ka damu Ya Farouq, wannan ba normal Pasta din da ka sani bane” shiru yayi ya qyale ta yayinda ta fara.
Zara tana ta girki yayinda Farouq yake latsa wayar shi yana kallonta jefi jefi.
Abinda yake bashi mamaki shine yadda take yin abubuwa da qyar sannan cikin ganganci amma kuma komai yake fitowa perfect.
Bai ankara ba ya ga ta saki wata tukunya a sink tare da yarfa hannuwan ta tana fadin “oouch”.
Tambayar ta yayi “what is it?” ta kalle shi cikin shagwaba tace “ina qoqarin tsiyaye pasta din ne ruwan zafi ya zuba a hannuna”
Murmushi yayi yace “sorry” sannan ya cigaba da latsa wayar shi.
Zara kamar zata yi kuka tace “Ya Farouq qonewa fa nayi”
Ba tare da ya kalle ta ba yace “try to be more careful next time”
Ta turo baki yayinda ya girgiza kai yana murmushi.
A zahiri Zara ta bashi tausayi da ta qone amma kuma ya sani sarai idan ya nuna tausayawa abincin na iya tsayawa daga nan wanda kuwa bazai so hakan ba don yunwa yake ji.
A haka dai Allah ya taimaka ta gama abincin ba tare da ta qara qonewa ba.
Ta zuba mishi nashi a plate ta ajiye a gaban shi sannan ta zuba nata itama.
A nan kan kicin island din suka zauna don cin abincin, Kujerar da take kallon nashi ta ja ta zauna.
Farouq wanda tuni ya qagara ya ci abincin ne ya dauki cokali ya fara ci.
Zara dai kallon shi take yi tana jira ta ji me zai ce.
Gaba daya ma bai kula da tana kallon shi ba ya dinga cin abincin.
Ganin haka ne yasa tace “Ya Farouq” ya dago ya kalleta yayinda ta daga mishi gira tace “comment” hannuwan shi ya daga yayi mata alama da “weldone” wanda ya sa ta fashe da dariya.
Tuni Farouq ya cinye abincin shi.
Dagowa yayi yana kallonta yace “gaskiya wannan abincin bai ishe ni ba, a qara mun”
Tana dariya tace “Ya Farouq a gaban ka fa na juye mana duka”
Gani nayi ta dauki plate dinta ta zagaya ta koma gefen shi ta ajiye tace “toh mu ci wannan, dama yayi mun yawa”
Ba tare da bata lokaci ba ya dauki cokali suka cigaba da ci tare.
Zara dai murna tayi sossai a dalilin Farouq ya yafe mata laifin da take tunanin tayi mishi gashi har suna cin abinci tare.
Suna cikin cin abincin ne ya daga kai ya ga ta qura mishi ido yace “irin wannan kallon sai ki sa in qware ai”
Murmushi tayi tace “idan ka qware zan baka ruwa Ya Farouq”
Murmushi yayi shima sannan yace “toh ina ruwan???” miqewa tayi tace “yi haquri na manta ne, bari in dauko maka”
Hannunta ya riqo yace “come and sit, bari in dauko”
Murmushi tayi ta koma ta zauna yayinda ya tashi ya dauko.
Bayan sun gama jin abincin ne tace “thanks Ya Farouq, I am glad you accepted my apology” murmushi yayi yace “thank you too for this special dinner, i enjoyed it”.
Duk wannan hidimar da ake yi a gidan Ruqayya bata sani ba, tana can kwance tana bacci.
Kafin su bar kicin din Farouq ya kalli Zara yace “make a cup of coffee” cikin rashin fahimta tace “Ya farouq baka shan coffee ai” yace “naki ne, I want you to be sober while studying”
Aikuwa sai da ta hada coffee sannan suka fita.
***********
A falon qasa suka zauna don yin karatun.
Kallon agogo yayi yace “you better open your brain because I have just thirty minutes”
Zaro idanuwa tayi tace “thirty minutes Ya Farouq? Note din yana da yawa fa” bai ce mata komai ba suka fara.
Aikuwa dai kamar yadda Farouq ya fada cikin minti talatin duk ya warware mata komai.
Zara dai mamaki take yi yadda Farouq ya iya komai.
Kallon shi tayi tace “wai kai Ya Farouq komai ne ka iya?” murmushi yayi yace “sa’a dai kika yi na iya wannan din, kuma idan kika yi failing course dinnan sai na zane ki. Tashi ki je kiyi bacci, all the best”
Dariya tayi ta miqe tare da fadin “thank you very much big brother”
Har ta juya zata tafi sai gani nayi ta dawo da sauri ta duqo tayi mishi kiss a kumatu tace “you are the best”
Kafin farouq ya gama processing abinda ya faru har ta shige dakin ta.
Ajiyar zuciya yayi tare da dafe kanshi yace “ooh Farouq, what is wrong with you????”
Ya dade zaune a wurin yana ta tunanin abubuwan da suke faruwa tsakanin shi da Zara a ‘yan kwanakin nan wanda bai gane kan abinda yake ji game da ita ba.
Da ya gaji ne ya miqe ya wuce sashen shi.
***********
*********
NILE UNIVERSITY
Saura awa daya a fara jarabawar ne Zara ta isa school, ta tarar da qawarta Hafsat tana ta karatu a class.+
Hafsat dai ta dage da karatun ne domin kuwa a yadda ta rabu da qawarta jiya ta sani sarai ba wani karatu tayi ba, addu’ar ta ma Allah yasa ta iya rubuta wani abu.
A lokacin da Zara ta shigo class din Hafsat tayi mamakin ganin ta cikin walwala musamman da tayi la’akari da yadda suka rabu jiya.
Hafsat ce tace “babes how far, you look good”
Zara tayi dariya ta zauna kusa da qawarta ta bata labarin abinda ya faru jiya tsakanin ta da Farouq.
Hafsat tana dariya tace “amma dai kin san Ya Farouq yana sonki ko?”
Zara tayi murmushi tace “as my brother yeah, dama abinda nake so kenan babes. He is my favorite brother and i want to be his favorite sister”
Hafsat ta harare ta tace “go jor, ni ba wannan son nake nufi ba”
Zara tace “lets not go there babes, ni fa ba…”
Hafsat ta daga mata hannu tace “yeah yeah, ba sonshi kike ba, I have heard” dariya Zara tayi yayinda ta duba littatafan da suke gaban Hafsat tace “me kike karantawa ne?”
Hafsat tace “ni ina ma na san me nake karantawa babes, dan koya mun wadanda yayan naki ya koya miki ko na samu abinda zan rubuta”
Zara ta fashe da dariya tace “wallahi babes duka ma fa babu wahala”
Hafsat ta harare ta yayinda Zara ta bude littafinta ta fara koya ma Hafsat din wuraren da bata iya ba.
Ko da suka zauna jarabawar gaba daya babu tambayar da Zara bata sani ba. ita da Hafsat ne suka fara gamawa sukayi submitting suka fita suna murna.
Dayake sai next month za’a yi convocation kawai sai suka yi tafiyar su gidan Hafsat wanda daga can Zara zata wuce gida.
MUKHTAR ABUBAKAR MANSION
Zara da Hafsat suna dafa Lunch a gidan Hafsat din ne Hafsat tace “gaskiya Allah yayi ma Ya Farouq albarka, ya bashi abinda yake nema a rayuwarshi”
Zara ta fashe da dariya tace “ai if not for him da mun ci zero”
Suka dinga dariya.
Hafsat tace “Yayi deserving special appreciation, what do you think??”
Zara tayi murmushi tace “i agree with you babes”.
Da yamma ne Zara ta fara shirin tafiya gida yayinda Hafsat ta kalle ta tace “Hajiya you are not going anywhere”
Cikin mamaki Zara tace “ban gane ba, kin dai san Ya Farouq ya hana ni tuqin dare ko? I need to reach home before magrib”
STORY CONTINUES BELOW
Hafsat ta janyo Zara “tace kar ki damu you are covered for today”.
Kicin ta kai Zara yayinda ta turo baki tace “wallahi bestie yau wahala kawai zaki bani, ni fa na gaji”
Hafsat ta Harare ta tace “toh a fasa yin abincin kenan, dama na su Ya Farouq ne” cikin mamaki tace “ban gane ba”
Hafsat tace “dazu na kira sweetlove nace yayi inviting dinshi over, amma fa bai san kina nan ba”
Cikin murna ta rungume qawarta tace “kin ga sai kawai mu tafi gida tare”
Hafsat tana dariya tace “yeah, lets get to work” aikuwa nan da nan suka fara girki yayinda Hafsat ta kula da yadda qawarta take cikin farin ciki marar misaltuwa.
Bayan magrib ne Mukhtar da Farouq suka shiga gidan.
Ko da ya shiga gidan bai kula da motar shi wadda Zara ta fito da ita a tsakar gidan ba.
Hafsat da Zara suna dakin Hafsat din a lokacin, wanka suka yi inda suke ta shiri. Wata doguwar rigar atamfa Hafsat ta fitar ma Zara da shi tace “babes for once in your life try this casual native”
Zara wadda take ta faman feshe kanta da turaruka tace “ai banda choice qawata”
Hafsat ce ta daura mata dankwali wanda ko da ta kalli kanta a madubi sai gani nayi tayi murmushi tace “not bad” yayinda qawarta take ta dariya.
Hafsat tace “bari in je in duba ko sun shigo, idan kin ji ni shiru sai ki biyo ni, I really want to see his face when you appear don nasan bai san kina nan ba”
Zara tayi murmushi tace “qila ma yayi ta fada, kin san masifafe ne wani lokacin” suka fashe da dariya yayinda ta koma bisa gadon Hafsat ta zauna.
Wayarta ce da ta fara ringing ta duba, Mahmood ne.
Nan ta amsa wayar suka shiga hira.
**************
Zaune suke a kan dinning din yayinda Hafsat take qoqarin zuba ma Mukhtar abinci har Farouq yana fadin “yau naga son kai, maimakon a fara zuba ma baqo an fara zuba ma dan gida” gaba daya suka fashe da dariya.
Zara ce ta fito tana tafiya ahankali yayinda take riqe rigar da ta sa a dalilin tsawo da ta dan yi mata.
Ta kusan qarasowa ne Farouq ya daga kai ya gan ta. bai san lokacin da ya zuba mata idanuwa ba a dalilin bala’in kyau da tayi.
Mukhtar ne da Hafsat suka zuba musu ido yayinda itama zara take kallon shi tana murmushi.
Da ta iso kusa da shi ne tace “Ya Farouq stop staring at me, zaka sa in fadi”
A wayance ya Harare ta yace “what? I am not staring. Mamaki nake yi as to how you are here”
Kujerar gefen shi ta ja tace “kai nake jira mu tafi gida tare”
yace “tare muka zo?”
Cikin shagwaba tace “yi haquri big brother, you are the best”
Ya girgiza kai yace “and you are the craziest sister amongst all”
Dariya tayi sannan ta Kashe mishi idanuwa tace “nayi kyau” ya kauda kanshi tare da fadin “No” ranta a bace ta miqe zata tafi.
STORY CONTINUES BELOW
Da sauri ya riqo hannunta wanda yasa ta tsaya cak.
Ji tayi yace “You look absolutely beautiful sis”
Murmushi tayi ba tare da ta juyo ba.
Ya saki hannunta yace “please serve me”
Su Mukhtar wadanda suke ta kallon su suka kalli juna suka fashe da dariya.
Shi kam Farouq ya ma manta da cewa su Mukhtar suna wurin.
Girgiza kai yayi yayinda yake fargaban attack din da abokin nashi zai yi mishi a game da little scene dinnan da ya wakana tsakanin shi da Zara.
************
Bayan sun gama dinner ne suka koma falon Mukhtar suna hira.
Wayar Zara ce tayi ringing, sunan Mamy ta gani kuma Video call ne.
Cikin murna ta amsa suka fara hira.
Gani tayi Sadiq ya zo ya zauna kusa da Mamy harda kwantar da kanshi a bisa kafadar Mamy tare da yi mata gwalo.
Miqewa tayi cikin shagwaba tace “Ya sadiq that’s my spot” Suna dariya Mamy tace “kar ki damu Princess jibi muna nan tare da ke Insha Allah, ina yayan ki? Sai na ga kamar ba gida kike ba”
Tayi murmushi tace “eh mamy, muna gidan su bestie ne, bari in bashi”
Bisa hannun kujerar da yake ta zauna tare da zagaya hannun ta a wuyan shi tace “Mamy”
Farouq wanda bai saurari Mamy ba tukun ya kalle ta yace “meye na shaqe mun wuya, kashe ni zaki yi?”
Mamy da Sadiq suka fashe da dariya yayinda Hafsat da Mukhtar ma suke ta dariya.
Zara dai zaro idanuwa tayi tace “Ya Farouq idan ka mutu nima mutuwa zanyi”
Sadiq ne yace “toh Romeo and Juliet” yayinda Farouq ya nuna shi da yatsa yace “take time” Sadiq yace “sorry Bro” haka dai suka taba hira sannan ta gaisa dasu Hafsat tayi musu sallama.
Wuraren qarfe goma suka bar gidan su Hafsat yayinda suka bar su suna ta yi musu dariyar dramar su.
FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
A lokacin da suka dawo gida tuni Ruqayya tayi bacci.
Tun suna kan hanya zara take ta bashi labarai kala kala.
Wasu yana ji wasu kuma baya ma ganewa. Haka suka shiga gidan tana ta surutun ta yayinda take riqe da hannun shi.
Ganin ta qi sakin hannunshi ne yasa yace “ki sa pause a labarin gobe sai ki cigaba”
Murmushi tayi tace “Ya Farouq please stay with me mana, gani nake yi kamar daga yau zan dade ban gan ka ba”
Zaro idanuwa yayi tare da matse hannunta cikin nashi yace “hey shut up, lafiyarki kuwa? bana so kina irin wannan maganganun”
Turo baki tayi tace “toh please”
Farouq wanda jikin shi yayi sanyi a dalilin kalaman zara ne yace “ten minutes amma banda surutu”
STORY CONTINUES BELOW
Tana murmushi tace “deal”
Zaune suke a kan kujerar falon qasa.
Basu kunna TV ba sannan basu yi ma juna Magana ba.
Asali ma farouq latsa wayar shi yake yi yayinda Zara tayi shiru tana tunani.
Ji yayi ta matso kusa da shi tace “wallahi Ya Farouq har bana son in tafi gida, I am sooo gonna miss you”
Murmushi yayi yace “ni kuma I am glad you are going don kin takura ma rayuwa ta”
(Hahaha, kai dai fadi gaskiya…🤣)2
Cikin shagwaba tace “haba Ya Farouq, me nayi maka? Gani nayi ma fa mun fi shiri yanzu unlike before”
Shiru yayi ba tare da ya qara yin Magana ba.
Bai ankara ba sai ya ji Kan Zara a bisa kafadar shi wanda har tsigar jikin shi sai da suka tashi.
Da sauri ya kalle ta ya ga har tayi bacci.
Bakin shi ya kai saitin kunnen ta yace “hey sleeping beauty go to your room”3
Dan motsawa tayi idanuwan ta a rufe tace “ten minutes Ya Farouq”
Murmushi yayi yace “zan tafi in bar ki anan fa”
Ji yayi tace “promise me that you will never leave me Ya farouq”
Hankalin shi a tashe yace “ba nace miki bana son irin wannan maganganun ba?” daga nan sai tayi shiru.
Bayan minti goma ne ya lallabata ta tashi ta tafi daki wanda shi ya raka ta har bakin qofarta.
Har ta juya zata shiga dakin nata ne ta ji ya riqo hannun ta yace “I will never leave you I promise, do have a good night rest”
Murmushi tayi sannan tace “thank you big brother, good night”
Farouq dai har ta shiga dakinta yana nan tsaye jikin shi a sanyaye. Ya rasa dalilin da yasa yake ji kamar wani abu zai faru da Zara.
Ya dade a nan tsaye sannan ya tafi dakin shi.
************
Washegari tun da sassafe Farouq ya tafi asibiti a dalilin kiran emergency da aka yi mishi.
Wuraren qarfe goma sha daya ne Aliya ta zo gidan. Suna zaune a sashen Ruqayya suna ta hira.
Zara wadda take zaune a dakinta gaban madubi tana shafa mai ne ta tuna cewar bata ba Ruqayya haquri ba akan laifin da tayi mata wanda tayi ma Farouq alqawarin bata haquri idan har ya haqura.
Dama dai zara ba mai son rigima bace, Ruqayyar ce ta bata mata rai.
Bayan ta shirya ne ta miqe ta fito don zuwa sashen Ruqayya.
Tana gab da shiga ne ta ji Aliya tace “wai ina gimbiyar take ne”
Ruqayya tayi dariya tace “toh wa ya san inda take, ni rabona da ita ma tun ranar da ya mare ta”
Ta gyara zama tace “qawata I was so happy ranar”
Aliya tayi dariya tace “ki ce dai ana ta drama a gidan naku”
Dariya Ruqayya tayi tace “ai ranar ma da na fita wurin Musty na tafi, ban dawo ba sai yamma”
Aliya tayi murmushi tace “toh shi Musty me yace game da cikin nan naki?”
Ruqayya tace “hmmm, qawata ai har yanzu rigimar da muke yi da shi kenan, ya dage akan cewa cikin nashi ne”
Zara wadda take saurare ta dafe kai tare da zaro idanuwa, bakinta a bude cikin mamaki.
Aliya ce tace “toh ke a tunaninki na waye?”
Ruqayya ta tabe baki tace “wallahi qawata nima na fi kyautata zaton nashi ne ba na Farouq ba…”
Kafin ta qarasa maganarta ne Zara ta shigo cikin mamaki tace “Anty Ruqy, dagaske wannan cikin ba na ya Farouq bane?”1
A razane Ruqayya da Aliya suka miqe tsaye suna kallonta. Gaba daya jikin Ruqayya kyarma yake yi, ga cikin ta da ya hautsine.
Zara wadda take kallon ta cikin qyama tace “tir da halinki, kina matar aure kina aikata zina sannan har ki iya bude baki kina kiran wata karuwa…”
Aliya ce tace “ke shut up”
Murmushin takaici Zara tayi tace “ai dama na gama magana hajiya bi-ta-zai-zai”
Cikin mamaki suke kallonta yayinda ta kalli Ruqayya tace “for your kind information Ya Farouq must hear this, yanzu ma kuwa”
Juyawa tayi ta fita yayinda take ta mamaki.
Ta taho wurin steps ne zata sauka sai ta ji an biyo ta a baya, kafin ta waigo tuni Ruqayya ta tura ta.
Ihu Zara tayi yayinda take rolling a steps din.
Aliya ce ta janye Ruqayya suka koma sashenta yayinda hankulan su suke a tashe.
**********
Farouq wanda ya shigo gidan ne ya tsaya cak ganin Zara kwance a qasan steps yayinda jini yake ta tsiyaya daga kanta.
Da gudu ya qarasa wurinta cikin wani irin mugun tashin hanakali wanda bai taba shiga ba, sunan ta yake kira yayin da ya dago kan ta ya rungume.
Hawaye ne suka fara gangarowa daga idanuwan shi yayinda yake fadin “please don’t die on me, I need you in my life. Zara please don’t leave me…”2
Masu aikin gidan ne suka fito suna kallon Zara wadda za’a iya cewa ta mutu.
Gaba dayan su sun rikice yayinda wasu suke ta kuka.
Daya daga cikin su ne ta kira ambulance din asibitin Farouq yayinda daya ta ruga sama don kiran Ruqayya.
Ruqayya da Aliya ne suka sauko cikin tashin hankali har Ruqayyar tana kukan munafinci.
Farouq wanda yake rungume da Zara bai ma san yawan mutanen da ke kanshi ba. babu abinda yake yi banda surutai iri iri.
Ko da Ambulance din ta iso da qyar suka banbare Zara daga jikin Farouq.
Jiki a sanyaye ya miqe ya bi bayan su sai asibiti.
Bayan an tafi da Zara ne Ruqayya da Aliya suka fashe da dariya inda Ruqayya tace “Allah yasa ta mutu mu huta”
****************